Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 5

Page 1 of 5

MUHIMMANCIN ILMI A RAYUWAR MUSULMI


Shashin Koyar da Aikin Akanta, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria
abellodogarawa@gmail.com Gabatarwa
Ilmi shi ne mafificin abin da ya kamata a yi amfani da dukiya wajen nemansa, domin kuwa babu abin da ya kai shi daraja. Da ilmi ne ake sanin Allah domin a bauta maSa; kuma da ilmi ne ake sanin haqqoqin kowa domin a ba shi. Ilmi haske ne da ake shiryuwa da shi; yana gadar da taqawa; kuma yana jawo daraja da xaukaka ga wanda ya mallake shi. Ilmi shi ne maaunin halas da haram; kuma s hi ne maganin cutar jahilci da rarraba a tsakanin mutane. Neman ilmi ibada ce kuma bitarsa tasbihi ne; bincike a kansa jihadi ne; koyar da shi ga wanda bai sani ba sadaka ce kuma yaxa shi a cikin masu shi aikin lada ne. Ilmi mai xebe wa mai shi kewa ne a lokacin kaxaici, kuma aboki ne a halin tafiya; da shi ne ake sanin Allah kuma a bauta maSa; da shi ne ake sanin matsayin Allah kuma a girmama Shi.

Ahmad Bello Dogarawa

Maanar Ilmi

77 216
Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi Ahmad Bello Dogarawa, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria

Page 2 of 5

142 143 14

120 148

22 167 166

78

83 148

Falalar Ilmi da Kevance-kevancensa


Ilmi haske ne wanda ke nuna wa mai shi bambancin gaskiya da qarya (Saba, 34:6); yana gadar da tsoron Allah (Israa, 17:107 -109); shi ne mafificin jihadi (Furqaan, 25:52); alama ce ta masu imani (Munafiqun, 63:8); ba ya yankewa saboda mutuwa (Saheeh Muslim); laana ba ta sauka a kan ilmi (Tirmidhi); alama ce ta alheri (Baihaqi); kuma yana shigar da mutane hanyar aljanna (Muslim). Saboda falalar ilmi, Allah (Mai girma da xaukaka) Ya yi wa Annabi Yusuf da Musa da Isa da Muhammad (tsira da aminci su tabbata a gare su) gori a kan
Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi Ahmad Bello Dogarawa, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria

Page 3 of 5

ilmin da Ya ba su (Yusuf, 12:22; Qasas, 28:14; Maaidah, 5:110; Nisaa, 4:113). Ilmi ya kevanta da abubuwa guda shida: (1) shi ne gadon Annabawa (2) shi ne kaxai aka yi wa Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) umurni da yin adduar Allah (Mai girma da xaukaka) Ya qara masa (3) Allah Ya siffanta kanSa da shi (4) kowane mutum yana farin ciki idan aka danganta ilmi a gare shi, ko da kuwa ba shi da ilmi; haka nan kowane mutum ba ya son a danganta shi zuwa ga kishiyar ilmi, ko da kuwa jahili ne (5) shi ne kaxai abin da ba ya raguwa daga mai shi saboda ya ba wani (6) ilmi ba ya qarewa saboda yawan karantarwa, shi yasa ba a tava samun wanda aka ce, Allah sarki, wane ya kasance mai ilmi, amma yanzu ilmin ya qare, duk da cewa a kan ce, wane mai kuxi ne, amma yanzu ba shi da kome ko kuma wane mai mulki/sarauta ne, amma yanzu ba shi da kome.

Matsayin Masu Ilmi


Malamai su ne ke yi wa alumma tarbiyya a kan ilmi (Aal Imraan, 3:79; Maaidah, 5:44); su ne ke yi wa alumma shugabanci, matuqar sun lazimci haquri da taqawa (Baqarah, 2:248; Sajdah, 32:24); suna daga cikin Ulul Amr da aka ce a yi wa xaa (Nisaa, 4:59); su ne Ahluz Zikr da aka ce a yi wa tambaya (Nahl, 16:43; Anbiyaa, 21:7); su ne Allah Ya ce a koma gare su a lokacin da wani abu mai girma ya auku (Nisaa, 4:83); su ne waxanda Allah Ya gwama shaidarsu da shaidarSa (Aal Imraan, 3:18); su ne waxanda bin hanyarsu ke kai mutum ga shiriya (Maryam, 19:43); su ne magadan Annabawa (Abu Daawud da Tirmidhi); su ne waxanda ke tsoron Allah (Faaxir, 35:28); suna daga cikin waxanda Allah Yake xaukaka darajarsu (Mujaadalah, 58:11); kuma suna daga cikin waxanda Allah Yake nufi da alheri (Bukhaari da Muslim); su ne mafi hasken fuska kuma mafi xaukakar mutane saboda adduar Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) gare su (Ahmad, Abu Dawud, Tirmidhi da Ibn Maajah); Allah (Mai girma da xaukaka) Ya hore masu kome don ya nema masu gafarar Allah kuma ya yi masu addua (Abu Yaalaa); su ne waxanda Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya bar wasiyya game da su (Ibn Maajah).

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi Ahmad Bello Dogarawa, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria

Page 4 of 5

Rabe-raben Ilmi da Hukuncin nemansa


Malamai sun raba ilmi ta hanyoyi dabam-daban. Daga ciki: Al-Ghazaalee ya raba ilmi gida uku bisa waxansu ginshiqai kamar haka: 1. Asali: saukakke/wanda aka yi wahayinsa (wanda aka koya daga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da wanda ba saukakke ba (amma ana samunsa ta hanyar zurfafa tunani ko gogayya ko saurare, kamar lissafi da ilmin likitanci da ilmin harsuna) 2. Hukuncin nemansa: wajibin kowa da kowa (yadda za a bauta wa Allah da kyawawan xabiu da sanin ya kamata) wajibin alumma baki xaya (noma, likitanci, harhaxa magunguna, zane-zane, da kimiyya da fasaha) 3. Matsayi: wanda ake buqata, da wanda aka halasta da wanda aka haramta A cikin littafin ar-Rasool wal Ilm Qaradawi ya raba ilmi zuwa 1. Ilmin Shariah 2. Ilmin sanaa Neman ilmin Shariah domin yin abin da Allah Ya xora wa kowane bawa wajibi ne (Nahl, 16:43; Anbiyaa, 21:7; Muhammad, 47:19; Xabaraani); idan kuwa na kowa da kowa ne, wajibi ne a kan alumma gaba xayanta (Ibn Abdil-Barr; An-Nawawi; Ibn Taimiyyah). Haka nan ma neman ilmin sanaa da kimiyya da fasaha da sauran naoin ilmin rayuwa, wajibi ne alumma ta samu wakilci saboda (Anfaal, 8:60) da kuma qaidar

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi


Da ilmi ne ake tabbatar da tsantsar bauta ga Allah Sanin halas da haram Sanin kevance-kevancen Musulunci da falalarsa Tunkarar qalubalen da ke fuskantar alumma (munanan aqidodi; al-gazwul fikriy, koma bayan Musulmi a fagen ilmi da tattalin arziqi da gudanarwa, da sauransu) o Kyakkyawan wakilci ga Musulmi a kowane vangare na rayuwa o o o o
Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi Ahmad Bello Dogarawa, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria

Page 5 of 5

o Bin umurnin Allah (Mai tsarki da xaukaka) da ManzonSa (tsira da aminci su tabbata a gare shi)

Wane Ilmi za a Fara Nema?

Tauhid, saan nan yadda za a bauta wa Allah Alqurani da Hadisi da maganar Malamai (Sahabbai da Tabiai) Littafan Fiqh A haxa su shi ne ya fi A vangaren fiqh, a koya ta hanyar mazhaba bisa sharuxxa guda uku: (i) bin mazhaba da yin fice wurin nemanta ba wajibi ba ne, kuma ba sharaxi ba ne; (ii) rashin taassubanci ga mazhaba; (iii) wajibcin riqo da dalili sahihi ko da ya sava wa mazhaba [Duba da na Shaukaaniy; da na Muhammad Eid Abbaasiy

Ladubban Neman Ilmi


Tsarkin zuciya da ikhlasi (nisantar shagala da kafin , da ba da fatawaba tare da tsoro ba, da son jayayya, da kutsawa cikin , d kallon banza ga wanda ya sava) Mayar da himma da tsayar da tunani wuri xaya, da haquri da kaxan da dauriya, da addua, da nisantar savon Allah, da yin aiki da ilmi Qanqan da kai ga ilmi da malamai Tsare haqqoqin malami (voye sirri, da rashin gulma, da rashin shiga sai da izni, da ba shi lokacin hutu) Yin ado da ladubba majlisi Ladabin tambaya Bi sannu-sannu kuma mataki-mataki Rashin dogaro da littafi ba tare da malami ba Rashin koyon karatu daga wanda bai qware ba

Muhimmancin Ilmi a Rayuwar Musulmi Ahmad Bello Dogarawa, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria

You might also like