Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 23

RUXANI GAME DA FARA AZUMIN

RAMADN 1432 (2011) A NAJERIYA:


ME NE NE ILMI YA TABBATAR?
Dr. Ahmad Bello Dogarawa
Sashin Koyar da Aikin Akanta, Ahmadu Bello University, Zaria
+2348026499981 abellodogarawa@gmail.com
Ramadn 1, 1432 (August 1, 2011)

Shaidar adali xaya ko biyu ko sama da haka,


kamar yadda Hadisin Ibn Umar, da Hadisin
Abdurrahmn ibn Zaid bn Al-Khaxxb suka nuna



][Ab Dwud; Drim

][Ahmad; Nas

8/16/2011

Dr. A. B. Dogarawa

Cikar watan Shaabn kwana talatin idan ba a gan


shi a qarshen yinin ashirin da tara ba, kamar
yadda Hadisin Ibn Umar da Hadisin Ab
Hurairah suka nuna:


[Bukhri da Muslim]

[Bukhri da Muslim]

Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

Shugaba ne ke da haqqin sanar da ganin wata,


matuqar akwai shi. Xaixaikun mutane ko
qungiyoyi ba su da haqqin sanarwa kamar yadda
Hadisin Ibn Umar da Hadisin Ribiyy ibn Hirsh
suka tabbatar:



][Ab Dwud; Drim






][Ahmad da Ab Dwud

8/16/2011

Dr. A. B. Dogarawa

Idan mutum xaya ya ga watan Ramadn ko


Shawwl, amma sai shugabanni suka qi yarda da
ganinsa, ballantana ma su ba da umurnin a xauki
azumi ko a sauke, ya ya zai yi? Akwai maganganu
guda uku a tsakanin Malamai:

Ba zai yi azumin ko ya sauke ba shi kaxai.


Zai yi azumi shi kaxai ko ya sauke
Zai yi azumi shi kaxai amma ba zai sauke ba sai tare
da sauran mutane

Idan kuwa mutum shi xaya ne a garinsu, ba ya


buqatar jiran wani da zarar ya ga wata tun da ba bu
wani sai shi
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

Ibn Taimiyyah da waxansu Malamai na ganin ba


zai xauka ko ya sauke ba, sai tare da sauran
jamaa, saboda Hadisin

Imm at-Tirmidh ya ce:
:


Ibn Taimiyyah, Majmul Fatw, 25/114; da Al-Albn,
Tammul Minnah fit Taalq al Fiqhis-Sunnah, shafi na 399

Wannan ce fahimtar da mu ke rinjayarwa a nan.


Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

Ibn Taimiyyah ya tabbatar da cewa dukkan masana


sun yarda cewa ana samun savanin bayyanar wata a
tsakanin qasashen da ke nesa da juna. Akwai
maganganu uku idan aka samu savanin ganin wata a
tsakanin qasashe biyu:

Idan mutanen wani gari suka ga watan Ramadn ko

Shawwl, aiki da wannan gani ya lazimci sauran


garuruwan da suka samu labari.
Kowanne gari zai dogara ne da ganinsa, saboda tasirin
savanin ganin wata.
Savanin ganin wata yana da tasiri ne kawai idan akwai
tazarar da ta wuce nisar kilomita dubu biyu da xari biyu
da ashirin da shida (2226 KM).
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

Matsayin Jumhr:

Ba a laakari da , ko bambancin qasa a

wajen fara azumi ko saukewa: na Ibn


bidain; da na Al-Qurxubi; da
na Ibn Rushd; da na Ibn Abdil-Barr;
da na An-Nawawi; da na Ibn Qudmah;
da na Ibn Hazm.
Sun dogara da Hadisin wanda ya
fuskantar da magana ga Musulmai na duniya.

Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

Ash-Shaukn, a cikin , da Muhammad

Nsiruddn al-Albn, a cikin


, sun yi raddi ga waxanda su ke cewa kowane
gari zai yi amfani da ganinsa, bisa wannan
hadisin na Kuraib.
Ba bu hujja cikin iyakance tsawon tafiya ko
tazarar da ke tsakanin qasashe saboda garuruwan
da ke kan iyakokin qasashe.
[Duba Majmul Fatw na Ibn Taimiyyah, 25/105]
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

Kasancewar ba bu tsari na bai xaya kuma ba bu


khilfah a cikin alumma, kowace qasa ta yi

amfani da ganinta:
Kwamitotin fatawa na duniya, irinsu , da
, da da
sauransu sun ba da fatawa da haka.
Ita ce fatawar Ibn Bz; da Al-Albn; da AlUthaimn; da Ibn Jibrn; da Bakar Ab Zaid
[Tamm al-Minnah, shafi na 398; Taudhul Ahkm min Bulghil
Marm, 3/454 455 da Fatwal Lajnatid Dimah Lil Buhthil
Ilmiyyah wal Ift, 10/100 102]
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

10

Tarihi ya nuna cewa tun da daxewa, ana samun

savanin ganin watan Dhul Hijjah a tsakanin Makka da


waxansu garuruwan musulmi.
Ya tabbata cewa a shekarar hijira 828 da 848, an samu
savanin ganin watan Dhul Hijjah a tsakanin Makka da
Masar; a 747 da 748 a tsakanin Dimashq da Makka
[Ibn Hajar Al-Asqalni, Inbul Gumr bi Abnil Umr fit Trikh, Tahqq
Muhammad Abdul-Mud Khn, 8/78, 9/225-226; Aliyyu ibn Abdil-Kfiy AsSubk, Al-Alamul Manshr fi Ithbtish Shuhr, Tahqq Jamliddn Al-Qsimiy,
46-48]

A 1970 da 1993 da 1995 da 2001 da 2005 da 2008 a


tsakanin Najeriya da Saudia
[Ahmad Bello Dogarawa, Tasirin Savanin Ganin Wata, 17]
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

11

Ba bu dalilin taallaqa azumi ko di ko arfah ga ganin


watan Saudia. Kowace qasa na iya amfani da ganinta ko
kuma ta taallaqa ga Saudia. Kowanne aka xauka, ya yi.
: Fatawar


-
:
Ibn Jibrn



.
12

8/16/2011

Dr. A. B. Dogarawa

Shaikh Hniy ibn Abdillah game da yin azumin


Arfa bisa savanin ganin watan Makka, ya ce:


.
Wannan ke tabbatar da cewa idan a ka samu
savanin ganin wata a tsakanin qasar Najeriya da
Saudia, kuma shugabanni suka ce mu yi aiki da na
mu, za a yi azumin Arfa, a yi sallar Idi, a yanka
dabbobin Layya bisa ganin wata a Najeriya, ba
tare da laakari da Saudia ba.
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

13

Sanannen abu ne cewa an samu savani tsakanin

Musulmai a Najeriya game da xaukar Azumin


Ramadan a wannan shekara ta 1432 (2011).
A yayin da mafi yawan Musulmai suka xauki Azumi
bayan cikan watan Shaaban kwana talatin, bisa
sanarwar Sarkin Musulmi, kamar yadda Shariar
Musulunci ta yi umurni, waxansu sun sava wa
sanarwar da aka ba da cewa ba a ga wata ba a
yammacin ashirin da tara, kuma suka tashi da Azumi a
ranar Lahadi, 30 ga watan Shaaban bisa sanarwar
qungiyar Izala (Jos), da waxansu Sarakuna, da
waxansu Malamai, musamman a Sokoto.
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

14

Waxanda suka yi riga-malam-masallaci wajen xaukar


Azumi sun ce sun dogara da waxansu hujjoji ne na
Sharia. Ga wasu daga cikin dalilan da suka dogara da
su tare da sharhi a kan qarfi ko raunin dalilan na su:
Sun ce: Mutane da yawa sun gani, kuma sun ba da
shaida, amma a ka qi ba da sanarwa, kamar yadda ya
faru a shekarar 1431.
Sharhi: Ba kan su farau ba! Tarihi ya nuna cewa
waxanda suka fi su imani da tsoron Allah sun tava ba
da shaidar ganin wata, amma ba a karva ba, kuma
suka haqura. Manyan Malamai sun ba da fatawar
cewa idan haka ya kasance, mutane su yi haquri.
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

15


][Abdurrazzq da Ibn Hazm
Ibn Taimiyyah ya ce:



" :
[Majmul Fatw,
]25/114-118
;Ash-Sharbni, a cikin Mughnil Muhtj il Maarifati Man Alfzhil Minhj, 1/499
da An-Nawawi a cikin Raudatux Xlibn wa Umdatul Muttaqn, 1/319; da AlHaxxb a cikin Mawhibul Jall li Sharh Mukhtasar Khall, 3/96
16

8/16/2011

Dr. A. B. Dogarawa

Sun ce: Shugabanni sun sava a tsakaninsu: qungiyar


izala (Jos), da wasu Malamai a Sokoto, da wasu
garuruwa sun ce a yi azumi, alhali Sulxn ya ce sai
ranar Litini, don haka su bi raayin waxancan
Sharhi: A qaidar Musulunci, idan shugabannin
alumma suka sava dangane da ganin wata, wanda
ke da sanannen matsayi na shugabanci da hukunci a
idon hukuma shi za a bi, matuqar bai nuna son
zuciya ba qarara, bisa qaidar ,
kamar yadda ta nuna a cikin
2527, 10/100-102.
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

17

Wannan ita ce fatawar manyan Malamai.


Al-Utahimn ya ce:



[Majmuul Fatwa lish-Shaikh Al-`Uthaimin,
mujalladi na 19 da na 20]

Don haka, Sulxn ne ke da haqqin a yi masa


biyayya cikin sanarwar da ya ba da, ba shugaban
Izala ko wani Malami ba.
Qololuwar a bin Malami ko shugaban wata qungiya
zai ba da, ita ce fatawa, amma hukunci sai Sulxn
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

18

Sun ce: Sulxn ya iyakance lokacin karva da sanar da


ganin wata, kamar yadda a ka ce ya bayyana wa
waxansu Malamai a Sokoto da suka je wajensa dangane
da ganin wata. An ce waxansu Sarakuna ma sun
danganta irin wannan magana gare shi.
Sharhi: Sulxn ya yi amfani ne da shawarar da aka ba
shi a shekarar 2008 cewa a taqaita lokacin da mutane
za su ce sun ga wata, kuma a yarda, saboda qorafin da
aka daxe ana yi cewa idan da gaske ana ganin watan
da a ke sanarwa, me ya sa a ke bari sai can cikin dare a
sanar, alhali ya kamata watan ya vace bayan faxuwar
rana da misalin minti goma sha biyar.
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

19

Idan ya tabbata cewa an tabbatar da ganin wata a


gaban Sulxn amma ba a yi aiki da shi ba saboda dare
ya yi, ya kamata a san cewa:
Matsalolin hanyoyin sadarwa da irin matakan da a
ke bi wajen tantance ganin wata a Najeriya na iya
haifar da jinkirin sanar da Sulxn har sai cikin dare.
Don haka, iyakance lokacin da za a karvi sanarwar
ganin wata, matuqar dai an tantance gaskiyar
shaidar ganin, kuskure ne.

Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

20

Sun ce: Qoqarin haxin kai da Musulmai na Kudanci ne


ya sa ba a yi aiki da shaidar ganin wata da mutane suka
ba da ba.
Idan hakan ya tabbata, ya kamata a san cewa:
Haxuwa tsakanin Kudu da Arewa a azumi ba shi ne
zai kawo haxin kai na gaskiya a tsakanin Musulmai
ba, kamar yadda Shaikh Bakar Abdullah Abu Zaid ya
bayyana a cikin littafinsa
Maganganun da Shehu Xhiru Uthmn Bauchi ya yi a
taron JNI, a ranar Alhamis, 28 ga Juli, 2011 alama ce
da ke nuna cewa haxin kai daban, haxin baki a
tsakanin mutane cewa sun yarda su haxa kai daban .
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

21

Sun ce: Ana da shakku game da Sulxn da sauran


Sarakuna, kasancewar suna nuna rashin ko oho da ko in
kula ga harkokin da suka shafi Musulmai a Najeriya: Jos,
Maiduguri, Kudancin Kaduna, Bankin Musulunci, da
sauransu
Sharhi: Wannan duka zargi ne. idan ma haka xin ne, ba
bu hujjar qin yin biyayya ga Shugabanni cikin dukkan
abin da suka ce a yi, matuqar bai sava wa addini ba.
Wajibi ne Shugabanni su yi gyara cikin abin da a ke
qorafi idan dai ya tabbata, kuma su ji tsoron Allah game
da shugabancin da su ke wa alumma, sannan su yi
qoqarin kare martabar kujerar da su ke kai.
Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

22

Xaukar azumin Ramadn 1432 ranar

Lahadi, 31 ga Juli ,2011 a Najeriya,


Ijtihdi waxannan Malamai suka yi ko
Tawaye ga Shugabanni?

Dr. A. B. Dogarawa

8/16/2011

23

You might also like