Download as rtf, pdf, or txt
Download as rtf, pdf, or txt
You are on page 1of 1

Mu Jama'a musulmi na nigeria dake zama anan Houston daga masallachi

da ake kira MASJIDUL MUMINEEN, mun zo yau domin muna son nuna
takaichin mu game da qungiya na Boko haram. Sa' annan kuma musamman mu
na nuna rashin yarda da rashin aminche wan mu game daukin yara en-mata da
wannan qungiya ta Boko haram tayi a Chibok, jihar Borno Nigeria.
Gamu nan muna fadin qarqara chewa Boko haram: wanda ke da nufin
chewa karatun boko haramun ne, qungiyar ta'adda ne, wanda ba ya da wani
asali a musulunchi.
Islaamu addini ne dake haramta ko wani irin zulumchi, daga karyan
mulki zuwa ga na ta'addanci. Muna tabbata chewa a chikin Quraani ALLAH
(s.w.t), yana umurni da adalci da kykyawar ayyuka. Islamu ya koyar da chewa
babu tiilastaawa a chikin addini, domin haka mun tabbatar da chewa bamu
amince da tiilastaawa zuwa ga yara en-mata su karbi addinin musulunchi,
domin yin haka haramun ne.
Sabo da haka muna kiran qungiyar Boko haram su gaggawta da mayar
da yara en-mata da suka dauke a Chibok. Su daina ta'addanci, kuma su koyi
zaman laafiya a chikin umma akan koyar wa na addinin musulunchi.
Muna kuma kiran gomnatin America da gomnatin Nijeria, da duka
jama'a masu nufin alheri su hada kai domin cheton en-makarantan Chibok.
Mun gode kwarai.
Many thanks for your patience.

You might also like