Hukuncin Bikin Ranar Valentine A Musulunci

You might also like

Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 8

Page 1 of 8

Hukuncin Bikin Ranar Valentine a Musulunci

Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmaan (abellodogarawa@gmail.com)


Sashen Kayar da Aikin Akanta, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria

MUQADDIMA
 Kowace al’umma na da bukukuwan addini waxanda ta ke taqama da su, kuma
su ke maimaituwa gare ta, lokaci zuwa lokaci. Irin waxannan bukukuwa hanya
ce ta gane xabi’ar al’umma, kuma alamomi na fahimtar abubuwan da suka
kevanci kowace al’umma.

 Misali waxanda ba Musulmi ba suna da bikin Alhamis xin da aka ce an saukar


da maa’idah; da sabuwar shekara, da kirsimati, da godiya, da hutu, da sauransu.
Haka kuma, Zoroastrians na da bikin Mahrajaan da Nauruuz, su kuma
Baaxiniyyah na da Eidul Ghadeer.

 Musulmi na da bukukuwa guda biyu a cikin shekara, kuma suna da guda xaya
a kowane mako. Bukuwan Musulmi na shekara-shekara su ne: ranar salla
qarama da ranar sallar layya. Bikin mako-mako kuwa, shi ne ranar Juma’a.

(892) 952

1134

 A wajen Musulmi, bukukuwan addini na daga cikin Shari’a kuma nau’in ibada
ce da a ke kusantar Allah (Mai girma da xaukaka) da su.

(1/207).

 Magabata a cikin al’ummar Musulmai sun riqi al’amarin bukukuwan addini da


matuqar muhimmanci, kuma sun xauki matakan ganin cewa ba su ruxu da
Page 2 of 8

kowane irin bikin al’ada ko na addini da ya shahara a cikin waxanda ba


Musulmi ba, ballantana su yi tarayya da su. Ta haka, sai suka kuvuta daga
kamanceceniya da kafirai, kuma suka tsare aqidar Musulunci da kyawawan
al’adunsa daga kisisiniyar kafirai.

 Amma a yau, abubuwa sun canza! Munanan aqidu da gurvatattun al’adun da


ke gangarowa cikin Musulmi daga qasashen kafirai sun sanya waxansu
Musulmi, musamman `yan boko a cikin matasa, maza da mata, suna ba
bukukuwan kafirai muhimmanci, wani lokaci ma, suna zaqewa wajen yin
tarayya da waxanda ba musulmi ba a cikin bukukuwan su a addini.

 Daga cikin irin waxannan bukukuwan addini da suka gangaro wa Musulmi


daga waxanda ba Musulmi ba, akwai bikin murnar zagayowar ranar Valentine
(Valentine’s day), wato ranar nuna tsananin soyayya da qauna ga masoyi, ko
kuma , kamar yadda a ke kiransa da larabci.

TARIHIN BIKIN RANAR MASOYA (RANAR VALENTINE)


 Asalin bikin Ranar Masoya na daga bukukuwan Romawa a lokacin da suke
kan addinin maguzanci fiye da qarni goma sha bakwai da wuce. An ce bikin
ya samo asali ne daga aqidar Romawa cewa wai wata macen kyarkeci ta
tava shayar da Romulus, wanda ya assasa garin Rome nono, kuma hakan ya
ba shi qarfin gaske da kuma hikima ta musamman.

 Romawa sun riqa yin gagarumin bikin murnar zagayowar wannan rana a
tsakiyar wata Febreru na kowace shekara. A lokacin bikin, ana yanka kare
da akuya, a inda qartin matasa, majiya qarfi za su shafe jikinsu da jinin,
sannan, su wanke jinin da madara. Daga nan, sai su jagorancin faretin
zagaya gari a kan tituna, suna riqe da fatun da za su bugi duk wanda ya
faxo masu. Matan Romawa suna faxa wa waxannan matasa don a buge su,
kuma hakan yana faranta masu rai saboda imanin da suka yi cewa yana
maganin matsalar rashin haihuwa.

 An ce Valentine sunan wani malamin kiristoci ne wanda ya mutu a dalilin


cutarwar Claudius, shugaban Gothic a shekarar 296 CE. A shekarar 350 CE
an gina coci a wurin da ya mutu, domin a riqa tunawa da shi. Da Romawa
suka shiga cikin kiristanci, sun ci gaba da bikin soyayya, illa iyaka, sun
canza shi daga bikin soyayyar ruhi irin na muguzanci zuwa bikin shahidan
soyayya don tunawa da Valentine, kasancewar, a cewar su, ya yaxa qauna
da soyayya da zaman lafiya, abin da kuma ya kai shi ga rasa ransa.

 A wani qaulin kuma, an ce bikin ranar Valentine ya samo asali ne daga


lokacin da Romawa suka shiga cikin kiristanci. Sarkin Rome, Claudius II ya
sanya dokar hana sojoji yin aure a qarni na uku bisa hujjar cewa aure zai
Page 3 of 8

shagaltar da su, kuma ya kau da tunaninsu daga yaqi. Valentine ya bijire wa


wannan doka, kuma ya ci gaba da xaura wa sojoji aure a voye. Da sarkin ya
gano, sai ya jefa shi cikin kurkuku, kuma ya yanke masa hukuncin kisa.
Yana cikin kurkuku ne ya kamu da ciwon son `yar sarkin, amma a voye,
duk da cewa haramun ne ya so wata mace ko kuma ya yi aure, a matsayinsa
na babban malamin kirista, kasancewar dokokin kiristanci ya hana. An ce
daga baya, sarkin Romawa ya nemi Valentine ya bar kiristanci, ya bauta wa
gunkin Romawa, shi kuma zai mai da shi xaya daga cikin makusantarsa
kuma ya aurar masa da `yarsa. Kasancewar Valentine ya qi yarda da haka,
an kashe shi a ranar 14 ga Febreru 270 CE, a daren 15 ga watan Febrerun da
aka saba yin bikin Lupercalis. Daga nan aka canza sunan bikin ya koma
ranar tunawa da Valentine, ko dai saboda dagewar da ya yi a kan kiristanci
ko kuma saboda goyon bayan da ya nuna wa sojojin da suka faxa cikin
soyayya, har hakan ya kai shi ga rasa ransa.

 Daga nan, sai Pope, shugaban kiristocin da ya gaji Saint Peter, ya mai da
ranar 14 ga Febreru 270 CE a matsayin ranar bikin soyayya, kuma ya
shar’anta wa dukkan kiristoci murnar zagayowar wannan rana a kowace
shekara.

 Da ma Allah (Maxaukaki) Ya ba da labarin yadda kiristoci ke xaukar


malamansu a matsayin abin bauta, ta yadda su ke bin abubuwan da suka
halatta ko suka haramta masu sau da qafa, ba tare da neman dalili a cikin
littafinsu ba.

ABUBUWAN DA A KE YI A RANAR VALENTINE


 Bayyanar da farin ciki da jin daxi a wannan rana, kamar yadda a ke yi a
sauran manyan bukukuwa

 Musanyar jajayen fulawa, waxanda ke alamta soyayya, wato soyayyar ruhi


irin ta maguzawa ko kuma tsantsar soyayya irin ta kiristoci

 Aika wa da katin gaisuwa, wato, greeting cards. A jikin waxansu katin, a


kan samu hoton ubangijin soyayya na Romawa a siffar wani yaro mai
fikafikai guda biyu, da ke riqe da baka da kibiya.

 Rubuta kalmomin soyayya da amfani da lafuzzan da ke motsar da sha’awa a


jikin katin. A wani lokaci a kan rubuta ‘be my Valentine’, wato ka zamanto
tsantsar masoyina a wannan rana. Haka kuma a halin yanzu, a kan aika da
saqonnin batsa da rahin kamun kai ta hanyar wayar tafi da gidanka.

 Musanyar kyaututtukan da suka haxa da fulawa da alawa, a tskananin


ma’aura ko samari da `yan mata
Page 4 of 8

 A waxansu qasashen, ana shirya qasaitaccen biki (party) ta yadda maza da


mata za su cakuxe da juna, a yi rawa, a yi anashuwa tare, wani lokaci kuma,
a haxa da masha’a.

ABUBUWAN LURA DANGANE DA RANAR VALENTINE


 Asalin bikin ranar Valentine daga Romawa ne waxanda ke bin aqidar
maguzanci. A wajensu, biki ne da ke nuna soyayyar da su ke wa gunkinsu
mai suna ubangijin soyayya.

 Tarihin wannan biki a wajen Romawa ya qunshi tatsuniya da surkullen da


duk wani mai hankali zai qaryata, ballantana kuma Musulmin da ya san
abin da ya ke yi. Hatta ma a wajen kiristoci, akwai savani mai yawan gaske
a tsakanin malamansu dangane da gaskiyar alaqar Valentine da wannan biki

 Biki ne da ya qunshi kamanceceniya da mushrikan Romawa da kuma


tarayya da kiristoci. Yin kamanceceniya da kafirai ko tarayya da su a cikin
addininsu ko aqidarsu ko ibadarsu ko wata al’ada da ta kevanta da su,
haramun ne.

329 25

193 4

442 441 1 (
Page 5 of 8

2/519-520

MATSAYIN BIKIN RANAR VALENTINE A MUSULUNCI


199 16


Page 6 of 8

MATSAYIN MUSULMI GAME DA RANAR VALENTINE


 Ya kamata kowane Musulmi ya xaukar wa kansa wannan matsayi:
 Qin yin wannan biki ko tarayya a cikinsa ko halartar wurin da a ke yi
 Qin taimaka wa kafirai da sauran kangararrun Musulmi ta kowace irin
hanya wajen samun nasarar wannan bamagujen biki, kamar ba da kyauta
ko karvar kyauta ko buga katin gaisuwa ko ba da aron wani abu da ya
mallaka ko sayar masu da wani abu da zai taimaka masu wajen gudanar
da wannan sakarci
 Yin inkari gare su, da bayyana qyama ga abin da a ke yi a wannan rana
 Qin yin gaisuwar taya murna ko amsa irin wannan gaisuwa idan aka yi
masa
 Yin nasiha ga Musulmin da ke irin wannan bamagujen biki,
gwargwadon iko, matuqar akwai maslaha.

SHUBUHOHI DA RADDIN A KANSU


 Musulunci ya kwaxaitar da soyayya a tsakanin mutane, kuma ranar
‘Valentine’ dama ce ga Musulmi su yaxa soyayya a tsakaninsu. Don haka,
mene ne aibi?
 A Musulunci, idi ibada ce da a ke kusantar Allah da ita, kuma yana daga
manya-manyan alamomin addini. A Musulunci babu idi sai Juma’a da
idin kammala azumi da idin layya. Ibada kuwa ce, ba a farar da ita
sai da dalili na Shari’ah. Ke nan, murnar zagayowar ranar Valentine
bidi’a ce, kuma qari ne a cikin addini, sannan kuma kamar yin gyara ne
ga Allah (Maxaukaki) da ManzonSa (tsira da aminci su tabbata a gare
shi)
 Bikin ranar Valentine ya qunshi kamanceceniya da Romawan da ke
bautar gumaka, sannan kuma da kiristocin da suka shiga gaxa a gicciye.
Alqur’ani da Sunnah da Ijma’in Sahabbai (Allah Ya yarda da su) duk
sun hana kamanceceniya da waxanda ba Musulmi ba a cikin aqidunsu
da ibadunsu:

105

16 (

4021 50 2
Page 7 of 8

314 1

248 8

725 722 2 454 1

 Manufar murnar zagayowar ranar Valentine a wannan zamani ita ce


yaxa soyayya da qauna a tsakanin mutane ba tare da la’akari da
bambancin addini ba. Shi kuwa Musulunci ya yi amanna da .
 Soyayyar da a ke nufi a ranar Valentine ta qunshi bege da qauna da
shauqi ne a tsakanin masoyi da masoyiyarsa, wanda ke haifar da zinace-
zinacen da babu qaidi, da shashanci mara misali da fitsara iri-iri.
 Soyayya a Musulunci ba ta taqaita ga wata rana ba, kuma Musulunci ya
tsara yadda a ke soyayya, da waxanda za a so ko kuma a qi.

 Ranar Valentine na ba ma’aura damar su jaddada soyayyarsu da qaunarsu


ga juna. Shi xin ma babu kyau?
 Idan kuma ana maganar ma’aura ne, a Musulunci, soyayya da qauna a
tsakanin ma’aura ba ta taqaita ga wata rana ta musamman ba. Abu ne na
ko yaushe, kuma ana buqatarsa a kowane hali da lokaci. Mujarradin
murnar Valentine ba za ta qara wa aure danqo ba. Hasali ma, murnar
zagayowar ranar Valentine ba ta taimaka da komai ba wajen
zamantakewar aure, a qasashen da suka ba bikin matuqar muhimmanci.

 Binciken da aka yi a Jami’ar Azhar dangane da auren da aka gina shi


bayan tsananin soyayya (auren soyayya, wato, love marriage) da
kuma wanda aka yi shi a bisa kyawawan al’adun mutane (traditional
marriage), ya nuna cewa 88% na nau’in farko yana rushewa bayan
wani qanqanen lokaci, shi kuma xayan 70% yana yin nasara
(Risaalah ilaa Mu’minah, shafi na 255)
 A shekarar 1987, binciken da aka yi a Amurka ya nuna cewa 79% na
maza suna dukan mata, musamman ma’aura (Jaridar Al-Qabas,
15/2/88).
 Binciken da National American Office for Mental Health ya gudanar
ya nuna cewa 17% na matan da ke zuwa sashen taimakon gaggawa
(emergency) na asibiti, sakamakon duka ne da mazajensu ko
samarinsu suka lakaxa masu, kuma kashi 83% na waxanda aka tava
kwantarwa domin magance raunin da ke jikinsu, a sakamakon duka
ne.
Page 8 of 8

 Rahoton da Central American Agency for Examination ya ba da, ya


nuna cewa a cikin kowane sekan 18 (18 seconds), wata mace a
Amurka tana shan xan banzan duka daga mijinta.
 Mujallar American Times ta bayyana cewa kusan mata 4,000 ne su
ke mutuwa a kowace shekara daga cikin kusan mata 6,000,000 a
dalilin dukan da su ke sha daga mazajensu ko samarinsu.
 A qasar Germany, mata fiye da 100,000 ne ke shan nau’o’in azaba
daga mazajensu a kowace shekara, kuma ana jin cewa alqaluman sun
wuce 1,000,000.
 A France, kusan mata 2,000,000 ne ke shan dukan tsiya a kowace
shekara

You might also like