Download as doc, pdf, or txt
Download as doc, pdf, or txt
You are on page 1of 1

DOKA A SULEJA; MUTANE NA CIKIN TSANANIN TAKURA,

SARKI AWWAL YA YIWA JAMAA GARGADI.


Daga Mohammed Akib Suleja

Jamaar Suleja, garin da ke makotaka da birnin tarayya Abuja, sun kasance cikin yanayi na tsananin takura sanadiyar dokar da gwamnati ta kafa dangane da fitintinu da suke aukuwa na tashin Boma-bomai a garin. Gwamnati ta kafa wa jamaa dokar fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, wanda dokar ta samo asaline sakamakon wata tashin bom da ta auku a kusa da wata coci dake layin Morrocco a garin Suleja. Wani daga cikin mazauna garin wanda yayi Magana da Leadership Hausa, amma ya bukaci a sakaya sunansa yace Tabbas jamaa na cikin yanayi na tsananin takura sanadiyyar wannan doka. Yace domin sojojin dake shawagi a garin suna matukar azabtar da mutane son raayinsu ba kamar yadda akayi umurni agaresu ba. Wani dan kasuwa mai gudanar da sanaarsa a Die-Die, Edu Omoye yace saboda wannan doka ne yake barin kasuwancinsa ya dawo gida da wuri domin kiyaye kansa daga wulakanci jamian sojojin, duk da cewa sanaarsa na tasirine da yammaci domin a wannan lokacine a akasarin kostomominsa ke ziyartarsa. Ya zama wajibi ga mazauna Suleja masu aiki da gwamnatin tarayya subar maaikatu ba tare da lokacin tashi aikin yayiba, domin gudun tozarta daga rundunar jamiar sojojin dake zirga-zirga don tabbatar da tsoro a garin. Wakilinmu ya ruwaito cewa sarkin Suleja, Malam Mohammed Awwal Ibrahim ya umarci jamaa da suyi biyayya kan wannan doka da gwamnati ta kawo, sannan suyi hakurin juriya da yadda lamarin ta kasance. Sarki Awwal ya bayyana hakanne yayinda yake gudanar da jawabi a fadarsa jim kadan bayan idar da sallar jumaar makon day a gabata, inda yayi gargadin cewa jamaa su kiyaye fitowa daga cikin gidajensu a lokacin da dokar ta fara aiki. Bayan haka sarkin ya jaddadawa mabiyansa cewa an kawo wannan dokane domin samun saukin tashin bom a garin Suleja.

You might also like