Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 14

Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B.

Dogarawa, ABU, Zaria

GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE:


INA MATSAYIN SHARIAH?

Rubutawa da Gabatarwar

Dr. Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahman


Sashin Koyar da Aikin Aknta, Jamiar Ahmadu Bello Zaria
08032989042 - abellodogarawa@gmail.com

Asabar, Dhul Hijjah 11, 1438 September 2, 2017

1
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

MUQADDIMA
Aure aya ce daga cikin ayoyin Allah, kuma niima ce daga cikin niimominSa.

] Ruum, 21[ ...

[Raaad, 38]

Matuqar an gina shi a bisa turbar qauna da soyayya da girmamawa da mutunta


juna, aure na ba da kariya ta musamman ga ko wa ne vangare na iyali, a
matsayinsa na ginshiqin samar da alumma; yana kyautata wa mutum tsarin
rayuwa; ya haifar wa mutum da kamala; kuma yana ba da damar biyan buqatar
shaawa ta xabia.
[Nuur, 32]

[ Baihaqi]





[Bukhari; Muslim]


Wannan yasa Musulunci ya sharanta aure a matsayin halastacciyar hanyar


hayayyafa da yawaita alumma, tare da tabbatar da xorewar jinsin xan Adam;
ya girmama alamarin aure; ya qarfafe shi; kuma ya hana xabiar qin yin aure
( )wai saboda a samu damar mai da himma wajen bautar Allah.

]Nisaa, 3[ ...



[ Abu Daawud; Nasaai]


!

" ] Baihaqi[

[Ibn Maajah]
[ Ibn Hibbaan]

2
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

Aure na da hikimomi masu yawa. Daga cikin manyan hikimomin aure akwai:
Yaxuwa da xorewar jinsin xan Adam


.....


[Nahl, 72]


[ Nisaa, 1]

Biyan buqatar shaawa ta xabia don kamewa daga zina



[ Muslim]
:

[Ibn Abee Aasim; Tirmidhi]

Samun natsuwa da sukuni da kwanciyar hankali




[ Ruum, 21]

[Aaraaf, 189]

Jin daxin duniya



[Muslim]





:
[Ibn Abi Shaybah]

Qarin matsayi a tsarin zamantakewar alumma


[Al-Mughnee] :

Maaura kan shiga cikin rayuwar aure da fatan samun walwala da jin daxi da
farin ciki da soyayya da qauna mara iyaka. Sukan yi fatan su haifi yaya masu
cikakken lafiya da hankali da basira da albarka don su zame masu sanyin ido,
kamar yadda suke adduar su yi rayuwar mutu-ka-raba a tsakaninsu.

3
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

Sai dai kuma irin wannan guri kan samu tazgaro a lokacin da xayan maaura
ya fahimci cewa abokiyar/abokin zama na tare da wata cuta ko larurar rashin
lafiya da za ta yi Karen-tsaye ga cinma waxanda gurace-gurace. Hakan ya kan
sa maaura su yi nadamar auren da suka yi, musamman idan suka fahimci
cewa da an san da matsalar kafin a yi auren, da an xauki matakin da ya dace na
neman magani ko kariya daga kamuwa da cutar ko kuma ma a fasa auren gaba
xaya. Sau da yawa, maauran da suka tsinci kansu a irin wannan hali kan rayu
cikin baqin ciki da takaici ko kuma su xauki matakin raba auren, kasancewar
soyayya da qauna sun koma qiyayya da gaba; tausayi da jin qai sun koma
tsanani da qulafuci.

Wannan ya sa a yau, masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya ke ta nuna


muhimmancin yin gwaje-gwajen lafiya ga maza da mata kafin su yi aure don a
kauce wa haxurran da ke tattare da cututtukan da ke shafar maaurata a dalilin
zaman tare ko cututtukan da ke iya shafar yayansu. Manufar it ace a samar da
alumma mai cikakken lafiya da kuzari, kuma a taqaita yawan kuxin da
gwabnati za ta kashe wajen samar da magunguna ga masu irin wannan cuta.

Kasancewar akwai kace-nace a tsakanin mutane game da dacewa ko rashin


dacewar yin gwaje-gwajen lafiya kafin aure, wannan yar maqala ta yi xan
tsokaci ne a kan matsayin Shariar Musulunci game da irin waxannan gwaje-
gwaje.

4
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

NAUOIN GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE


Masana sun bayyana cewa ana yin gwaje-gwajen lafiya ne kafin aure a kan
nauoin cututtuka guda biyar:
1. Gwaji don tabbatar da kuvuta daga cututtukan da ke qetare mai shi zuwa
waninsa a dalilin muamala ta jimai (Sexually Transmittable Diseases
STDs), kamar HIV, da hepatitis B, da hepatitis C, da gonorrhoea, da
syphilis.

2. Gwaji game da rukunin qwayoyin halitta (genes) don sanin genotype


xin masu niyyar yin aure a matsayin AA, AS, ko SS don tabbatar da
kuvuta daga cututtukan da ke bin hanyoyin jini wajen yin naso da shafar
abokin zama ko yayan da za a haifa kamar cutar Anaemia (sickle cell).

3. Gwaji don gane rukunin jini: A, B, 0 ko AB, da danginsa na Rhesus


factor (positive, + ko negative, -). Kasancewar bincike ya nuna cewa
macen da ke qarqashin dangin jini na negative idan ta aure wanda ke
qarqashin positive, tana iya fuskantar haxarin yawan zubewar ciki ko
mutuwar xan da ke cikin mahaifa (intrauterine death), gudanar da irin
wannan gwajin na da muhimmanci.

4. Gwaji don tabbatar da rashin aibobin da ke sa a kai ga raba aure a


tsakanin miji da mata, kamar cututtukan da ke iya jawo rashin haihuwa,
da kuturta, da wasu nauoin cutar daji (cancer) masu haxari, da cutar
qoda.

5
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

5. Gwaji game da cututtukan da a ke gado, waxanda aka ce a yanzu


adadinsu ya kai 8000. Irin waxannan cututtuka sun haxa da ciwon hauka,
da ciwon ido da yaya ke iya gado daga iyaye kamar glaucoma.

HUKUNCIN GUDANAR DA GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE


Kusan dukkan malamai a wannan zamani sun haxu a kan muhimmancin
gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure don kaucewa wasu cututtukan da ke
yin karan-tsaye ga xorewar aure, ko su sabbaba cuta ko naqasa ga yayan da
za a haifa. Amma sun yi savani game da wajabcinsa a kan waxanda ke son yin
aure: wasu malamai na ganin cewa Hukuma ko iyaye na iya wajabta gudanar
da gwaje-gwajen lafiya a kan waxanda ke son yin aure, wasu malaman kuma
na ganin kawai a bar mutane su zavi abin da suke so, ba tare da an wajabta
masu ba.

Daga cikin masu ganin wajabcin gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure
akwai: Muhammad Az-Zuhailiy, da Naasir Al-Maimaan, da Usaamah Al-
Ashqar. Waxanda ke ganin halascin gudanar da gwaje-gwajen ba tare da
wajabci ba sun haxa da: Ibn Baaz, da Abdullah ibn Jebreen, da Abdulkareem
Zaydaan, da Muhammad Raafat Uthmaan.

HUJJOJIN MASU GANIN RASHIN WAJABCIN GWAJI KAFIN AURE


1. Tuhuma ce ga bayin Allah; da tada zaune tsaye, da jefa mutane cikin
zullumi, musamman da yake ana samun kurakurai cikin sakamakon
gwaje-gwajen da a ke gudanarwa ga mutane.

2. Munana zato ne ga Allah tun kafin a yi aure, alhali kuwa Imam Ahmad
ya ruwaito Hadisi qudusiy cewa:

6
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

3. Ba shi daga cikin sharuxxa aure ko rukunansa, don haka magabata ba su


yi maganarsa ba duk da cewa sun yi magana game da aibobin maaura da
ke ba da damar a raba aure idan ana so. Hadisi kuwa ya tabbata cewa
duk sharaxin da ba shi cikin littafin Allah, vatacce ne. Haka kuma,
wajabta gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure ya sava wa Hadisin
da Tirmidhi ya rawaito:

4. Ruxuwar da mutane ke yi cewa gwaje-gwajen lafiya kafin aure na iya


tsare su daga cututtukan da a ke gado, ko waxanda ke shafar
abokin/abokiyar zama a dalilin muamala ta jimai, kasancewar har
yanzu, sakamakon bincike game da wasu daga cikin irin waxannan
cututtuka ba shi da sahihanci sosai. Ruxuwa da sakamakon gwaje-
gwajen lafiya za ta haifar da naqasa ga imani da aqidar mutane.

5. Gwaje-gwajen lafiya kafin aure na hana wasu mata samun maaura


saboda sakamakon gwajin lafiya da aka yi masu, wanda ya nuna suna da
larura. Hakan na haifar da qaruwar matan da ba su da mazajen aure a
cikin alumma.

6. A dalilin sakamakon gwaje-gwajen lafiya, wasu kan rayu cikin jimami


da damuwa da rashin kwanciyar hankali duk tsawon rayuwarsu.

7. Ba dole ne a samu zuriyya ba don an yi aure, kasancewa Allah ne ke


azurta maauratan da Ya so da yaya. Don haka, me ne ne amfanin yin
gwaje-gwajen lafiya kafin aure?

7
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

8. Rashin kiyaye sirrin waxanda ke zuwa a yi masu gwaji saboda qarancin


amana da kiyaye ladubban aiki a tsakanin maaikatan lafiya ya sa wasu
daga cikin waxanda aka yi wa gwaji sun shiga cikin quncin rayuwa
saboda an yaxa sirrinsu.

9. Xawainiyar kuxi da ke tattare da gudanar da gwaje-gwajen na haifar da


qunci da takura ga mutane, musamman masu qaramin qarfi.

HUJJOJIN MASU GANIN WAJABCIN GWAJE-GWAJE KAFIN AURE


1) Manufar yin gwaje-gwajen lafiya kafin aure ita ce a ba da kariya da ga
aure, don ka da ya samu matsala bayan an qulla shi. Ke nan, gudanar da
gwaje-gwajen lafiya kafin aure ya dace da qaidar: ""

2) Sanannen abu ne cewa Musulunci ya ba da kulawa ta musamman ga


( zuriyya/yaya), har ma ya sanya shi cikin larurori guda biyar

( ) da ya zama dole a ba su kariya. Gwaje-gwajen lafiya kafin

aure zai taimaka wajen tabbatar da wannan.

3) Annabawa kamar Annabi Zakariyyah (AS) sun riqa roqon Allah (TWT)
Ya azurta su da zuriyya ta qwarai, mai tsarki da lafiya. Haka kuma, yana
daga adduar muminai roqon Allah (SAW) Ya azurta su da samun
yayan da za su zame masu sanyin ido saboda tarbiyya da lafiyar jiki da
zuciya. Gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure zai ba da damar
samar da yaya masu nagartaccen lafiya.


[ Aaali Imraan, 38]


[Furqaan, 74]

8
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

4) Manzon Allah (SAW) ya kwaxaitar da yin aure bisa niyyar hayayyafa.


Haka kuma, ya kwaxaitar da wanda ke son yin aure da ya kalli wadda zai
aura don tabbatar da kuvutarta daga cututtuka mabayyana, da samun
natsuwar cewa ta yi masa. Gwaje-gwajen lafiya kafin aure zai taimaka
wajen tabbatar da haka:

:
[ Nisaai]

"

" : : ":



[ Muslim] "


" :
[Tirmidhi] "

5) Yin gwajin lafiya kafin aure naui ne na rigakafi wanda Shariah ta


tabbatar. Sanannen abu ne cewa rashin gudanar da gwaje-gwajen lafiya
kafin aure zai hana samun damar kaucewa cututtuka masu haxari:

:[ [Bukhari] [ Bukhari]


[Bukhari da Muslim]

]

ABIN DA YA FI RINJAYE A WAJENA DANGANE DA GWAJE-GWAJE


Bisa laakari da maganganun malamai da bibiyar hujjojinsu, abin da ya fi
rinjaye a wajena shi ne a yi tafsili game da nauoin gwaje-gwajen lafiya kafin
aure kamar haka:
Wajibi ne a gudanar da gwaji don tabbatar da kuvuta daga cututtukan da
ke qetare mai shi zuwa waninsa, kamar HIV da hepatitis B da hepatitis C
idan akwai yiwuwar samuwarsu tare da xayan waxanda ke son yin aure,

9
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

ko akwai rashin kwanciyar hankali game da abin da ya yi sanadiyyar


mutuwar abokin/abokiyar zaman xayan waxanda ke son yin aure a can
baya (a haqqin waxanda suka tava yin aure). Dalili a kan haka shi ne
faxin Allah (SWT):
[ Baqarah, 195]; da faxin Allah
(TWT): [ Nisaa, 29]. Amma ba wajibi ba ne a yi gwaji game

da irin su gonorrhoea da syphilis, kasancewar ba su cikin cututtukan da


ke da haxari sosai.
Ya halasta a gudanar da gwaji game da aibobin da ke wajabta raba aure
tsakanin miji da mata kafin a yi aure. Malamai sun ce duk wani aibi da
ke sa xayan maaura ya guje wa abokin zama ko ya qaurace masa gaba
xaya, ko ya hana jimai ko gamsuwa wajen jimai, za a ba da zavin
rabuwa ko ci gaba da zaman aure, idan ba a san da aibin ba kafin auren.
Shaikh Abdullah ibn Jibreen na ganin ko da kamar asthma, da diabetes,
da bilharzias, da rheumatism, matuqar ba a yi bayanin ana da larurarsu
ba a lokacin neman aure, idan suka bayyana bayan aure, za a iya ba da
zavin rabuwa ko ci gaba da zama. Ciwon matsalar shafar aljannu ()

da cutar farfaxiya ( )na cikin nauoin aibobin maaura waxanda za a

ba da zavin raba aure idan ba a san da su ba kafin auren. A cikin Zaadul


Maaad, Ibnul Qayyim ya ce:


...

"

Wajibi ne a gudanar da gwaji don sanin rukunin qwayoyin halittar


waxanda ke son su aure juna (genotype) don gujewa cututtuka masu bin
hanyoyin jini wajen yin naso da shafar yayan da za a haifa, kamar cutar
Anaemia (sickle cell) bisa qaidar:

10
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

Ba dole sai an yi gwaji game da cututtukan da a ke gado ba, kafin aure,


kuma bai halasta a lazimta wa mutane yinsa ba, kasancewar masana sun
tabbatar da cewa har yanzu, ba a gama fahimtar yanayin qwayoyin
halittar mutum ba (genes), kamar yadda ba a sallama wa sakamakon
binciken da aka yi ba game da tasirin qwayoyin halitta wajen gadon
cututtuka, musamman idan xayan iyaye ne ke da larurar, ba dukkansu
ba. Amma idan yan uwa da dangin xayan waxanda suke son yin aure
sun shahara da wata cuta wadda a ke iya gado, gudanar da gwaji kafin
aure na da muhimmanci a haqqinsu bisa qaidar: .

FAIDODIN GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE


a) Waxanda ke nufin qulla alaqar aure za su san nauoin cututtukan da ake
iya gado daga iyaye, ko waxanda ke naso zuwa ga yaya ko waxanda ke
qetare wanda ke xauke da su zuwa ga abokin/abokiyar zama, waxanda
za su iya hana qulla aure ko hana haihuwa ko sanya zubar da ciki a wani
yanayi, ko haifar da qyama ga abokin zama ko sabbaba cuta ga yaya.
Hakan zai ba da damar a ba su shawara game da neman magani kafin
auren, ko xaukar matakan kariya, ko fasa auren idan hakan ya fi zama
maslaha.

b) Yana taimakawa wajen hana aukuwar mushkiloli a tsakanin maaura a


dalilin gano cewa abokin/abokiyar zama na da wata larurar rashin lafiya
da ba a bayyana ba kafin aure, wanda kuma ke iya kaiwa ga mutuwar
auren.

c) Magance yiwuwar aukawa haxarin kamuwa da cutar da abokin zama ke


fama da ita a dalilin jimai ko zaman tare, ko kuma yaxa wani nauin
cuta a cikin alumma.
11
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

ABUBUWAN LURA WAJEN GWAJE-GWAJEN LAFIYA KAFIN AURE


1. Gwajin ya zamanto an yi shi ne a qarqashin manyan manufofin Shariah
( ) da ke da alaqa da aure don ba da kariya ga ,

kasancewar yana daga cikin larurori biyar ( ) da Musulunci ya

ba su kulawa ta musamman.

2. Gwajin ya zamanto zai taimaka ne wajen tabbatar da manufofin aure ko


ya qarfafa su.

3. A taqaita gwajin ga abubuwan da larura ko buqata suka kawo, bisa


laakari da qaidodin Shariah da suka haxa da:
" " " " " " "

"" "" " "

4. Ka da gwajin ya yi tasiri mara kyau a kan imani ko ingancin aqidar


Musulmi.

5. Ka da a yi amfani da gwajin lafiya kafin aure cikin abin da bai da alaqa


da dalilinsa gudanar da gwajin.

6. Wajabcin tsare sirrin wanda aka yi wa gwajin lafiya.

7. Tabbatar da qwarewa da kuma amanar wanda zai gudanar da gwaje-


gwajen lafiyar.

8. Ka da xawainiyar yin gwajin ta jawo rashin yin aure a cikin alumma.

12
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

KAMMALAWA
Gwaje-gwajen lafiya kafin aure don tabbatar da matsayin lafiyar masu son yin
aure, da tabbatar da kuvuta daga cututtuka masu haxari da a ke iya xauka a
dalilin alaqar aure ko ta hanyar gado, abu ne muhimmi, musamman idan ana
zaton akwai cutar. Kusan dukkan malamai a wannan zamani sun qarfafi
gudanar da irin waxannan gwaje-gwaje kafin aure don tabbatar da lafiyar
alumma. Amma sun yi savani game da wajabci ko rashin wajibcin gudanar da
gwaje-gwajen, bisa hujjojin da ko wa ne vangare ya dogara da su.

Amma, wanda ke da lafiya, kuma yake rayuwa a cikin alummar da ba ta


shahara da cututtukan da a ke tsoron yaxuwarsu ba ta hanyar aure, kuma ba a
tsoron cewa wadda za a aura na xauke da cutar da ke iya jawo matsala ga aure
ko yayan da za a haifa, ba dole ne a gudanar da gwaje-gwajen lafiya a kansu
ba.

13
Gwajen-gwajen Lafiya kafin Aure Dr. A. B. Dogarawa, ABU, Zaria

DAGA CIKIN LITTAFAN DA AKA NAZARTA

)1

)2

)3 -

)4 - .

)5

)6 " " -

14

You might also like