Nasihohi Ga Malamai Dangane Da Karantawa Da Tafsiri Da Wa'Azi A Watan Ramadan 1438

You might also like

Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 18

MUHIMMANCIN TARBIYYAR YAYA

DA HAXARIN SAKACI DA ITA

Dr. Ahmad Bello Dogarawa, Abu Abdir-Rahmn


Sashen Koyar da Aikin Akanta, Jamiar Ahmadu Bello, Zaria
+2348032989042 (abellodogarawa@gmail.com)
Gabatarwa [a]
o Haihuwa niima ce da ta dace da xabia, da yanayin xan
Adam; ya`ya ado ne da a ka qawata wa iyaye shaawarsa a
zuciya, kuma su na daga cikin abubuwan da ke sanyaya
idanuwa.

[Yuusuf:
o

12:21]

[Qasas,





o

28:9]
[Aal Imrn, 3:14] ..
o

[Kahf, 18:46] o

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 2


Gabatarwa [b]
o Fatan kowane mutum shi ne ya samu ya`ya nagari, masu
albarka, masu biyayya, masu tausayi; masu sanyaya idanuwa,
da za su tsaya makwafinsa, su cike gurbinsa, su ci gaba daga
wajen da ya tsaya, idan Allah Ya xauki ransa.
[Maryam, 5-6]



.





... o


[Furqaa, 74]













o

[Ibnul Arabiy] o
o Hakan na yiwuwa ne idan Allah Ya yi wa mutum gam-da-katar
wajen yi wa ya`yansa tarbiyyar da ta dace, don ya ci
moriyarsu a lokacin da ya ke raye, da kuma bayan mutuwarsa.

April 29, 2017


Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 3
Maanar Kalmar Tarbiyya
o A harshen larabci, mafi yawan malamai sun ce asalin kalmar
tarbiyya daga
ne, wato qaruwa da daxuwa, [Hajj, 22:5;
Baqarah, 2:276; Rm, 30:39; Hqqah, 69:10]
o Waxansu malamai sun ce daga fiilin ,
wato, ya qara, ya
daxa, ko kuma ya rena [Isr, 17:24; Shuar, 26:18].
o A taqaice, kalmar tarbiyya na nufin reno, da kulawa, da
ladabtarwa, da karantarwa, da ginawa tare da kyautata
alamuran qaramin yaro, kaxan-kaxan don ya zamanto
cikakke, a vangaren lafiyarsa, da hankalinsa, da aqidarsa, da
ruhinsa, da xabiunsa, da muamalarsa, da wayewarsa bisa
karantarwar addinin Musulunci.
April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 4
Hukuncin Tarbiyya
o Tarbiyyar ya`ya a kan imani da ibada; da xabiu da
muamala; da kula da lafiyar jiki da hankali da tunani; da
tsarin zamantakewa, wajibi ne da Allah Ya xora a kan iyaye
da dangi, da malamai, da shugabanni, da sauran jamaa.
o Iyaye ne kan gaba

o
] [Tahreem, 66:6
" : " . - :-

" : ][Ibn Katheer

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 5


]Hukuncin Tarbiyya [2
o




] [Muslim

] [Nasaai

] [Nasaai

][Muslim
o : " :
" ][Baihaqi
o : :

" :

" :
" ][Tuhfatul Mauduud
April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 6
Manufofin Tarbiyya a Musulunci
o Tarbiyyar `ya`ya a Musulunci na da manufofi guda shida:
Qoqarin tabbatar da manufar halittar xan Adam;
Kai wa ga manyan xabiun girma da halayen qwarai;
Tattali da qintsi ga rayuwar duniya da lahira;
Koyar da hanyoyin dogaro da kai, da kishin addini, da
qoqarin jawo amfani ga alumma da tunquxe cuta gare ta;
Gina mafi alhairin alumma mumina; da
Tabbatar da tsarin gudanarwa da wayewa mafi havaka.

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 7


]Wuraren da a ke Samun Tarbiyya [a
o Malaman tarbiyya sun ce an fi samun tarbiyya a wurare
uku: (1) gida (2) makaranta (3) masallaci
o Dangane da gida:
o ][Bukhaari



o - " :-







" .

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 8


]Wuraren da a ke Samun Tarbiyya [b
o Dangane da makaranta:

o Dangane da masallaci, Ibn Taimiyyah ya ce:
" o .


"

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 9


Haxarin Sakaci wajen Tarbiyyah
o Sakaci wajen tarbiyyar ya`ya na jawo wa iyaye takaici da
baqin ciki a duniya, da nadama a lahira.
o ] [Taghaabun, 64:15
] [Taghaabun, 64:15








][Munaafiquun, 63:9
o ][Abu Yaalaa 1990
o " :

][Tuhfatul Mauduud

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 10


Alamomin Sakaci wajen Tarbiyyah [1]
o A cikin littafin At-Taqsr fi Tarbiyyatil Auld, Shaikh
Muhammad ibn Ibrahim Al-Hamd ya lissafa alamomin
sakaci game da tarbiyyar `ya`ya:
1) Tarbiyyantar da `ya`ya a kan tsoro da ragwantaka da lalaci da kasala, da
zaman banza ko rashin amfani da lokaci yadda ya kamata.
2) Samar wa `ya`ya duk abin da su ke so, da sayo masu duk abin da suka nema,
ko da kuwa ba su da buqatar haka, saboda qarancin shekarunsu ko yanayinsu.
3) Tsananta masu, da zafafawa a gare su fiye da qima, da rashin tausasa masu.
4) Tsananin rowa, da qanqame hannu, da tsuke bakin aljihu wajen ciyar da su,
ko xaukar nauyin karatunsu ko kuma koyon sanaa.
5) Rashin tausasawa da tausayawa da nuna jin qai a gare su, bisa laakari da
shekaru da yanayinsu, da kuma rashin damuwa da halin da su ke ciki.

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 11


Alamomin Sakaci wajen Tarbiyyah [2]
6) Mayar da himma ga alamuran `ya`ya na zahiri ko kuma ruxuwa da abin da
su ke bayyanarwa a fili, ba tare da qoqarin gyara zukatansu da kyautata
alamuransu na sirri ba.
7) Wuce iyaka wajen kyautata zato ko munana zato ga `ya`ya.
8) Nuna bambanci a tsakanin `ya`ya, a wajen kyauta ko xaukar nauyin karatu,
ba tare da wani sahihin dalilin Shariah ba.
9) Yin mummunar addua a kansu ko yawan laantarsu, da yin masu
mummunar fata.
10) Doguwar hira a qofar gida ko majalisa ko dandali, maimakon zama tare da
iyali don sanin halin da su ke ciki.
11) Aikata munanan abubuwa a gabansu, ta yadda za su yi koyi da ayyukan
assha waxanda suka ga iyayensu na yi.
12) Kawo munanan abubuwa a gida, ko barin abubuwan da ke vata tarbiyya a
cikin gida.

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 12


Alamomin Sakaci wajen Tarbiyyah [3]
13) Tilasta wa `ya`ya maza su auri matan da ba su so, ba tare da laakari da abin
da zai iya biyo baya ba.
14) Jinkirta aurar da `ya`ya mata, waxanda mutanen kirki suka zo don su aura,
bisa hujjar sai sun kammala makaranta.
15) Auren dole ga `yan mata.
16) Barin `ya`ya mata su fita su kaxai, ba tare da muharrami ba, ko su fita ba tare
da sun sanya cikakken hijabi ba, musamman daga lokacin da suka balaga.
17) Sayen wayar sadarwa ga qananan yara, ko kuma a qyale `yan mata su yi
amfani da wayar da samari suka ba su.
18) Wulaqanta `ya`ya da qasqantar da su idan sun yi kuskure, da kuma rashin
qarfafa masu gwiwa idan sun yi abin kirki.
19) Rashin saba masu da xaukar nauyin kansu ko xaukar nauyin wasunsu,
gwargwadon iko, tun suna qanana.
20) Rashin qoqarin fahimtar yanayinsu da xabiunsu, ta yadda za a san hanyoyin
magance matsalolinsu na tarbiyya.

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 13


Alamomin Sakaci wajen Tarbiyyah [4]
21) Rashin ba su damar gyara kuskuren da suka yi, ko kyautata abin da suka yi
shi batsa-batsa, bayan an nuna masu yadda ya kamata su yi.
22) Rashin damuwa da irin makarantar da su ke zuwa, ko malaman da ke
karantar da su.
23) Qin haxa kai da masu karantarwa a makaranta ko kuma hukumomi wajen
tabbatar da tarbiyyar `ya`ya.
24) Barin alamarin tarbiyya gaba xaya a hannun iyaye mata, da watsi da
haqqoqin `ya`ya, musamman `yan mata.
25) Barin tarbiyyar `ya`ya a hannun mai reno, musamman waxanda ba musulmi
ba, ko kuma musulmin da ba su san yadda a ke yin tarbiyya ba.
26) Yawan savani a tsakanin iyaye a gaban `ya`ya, ta yadda `ya`yan za su koya.
27) Sava wa abin da a ke tarbiyyantar da `ya`ya a kansa, ta yadda za a nuna masu
muhimmancin wani abu, amma su ga an aikata savaninsa.

April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 14


Sakamakon Sakaci wajen Tarbiyya
1) Rashin manufa da rashin kishin zuci
2) Yanke qauna game da rayuwa da addini
3) Karkacewar tunani
4) Lalacewar xabiu: yaxuwar vatanci da varna a cikin
alumma, shaye-shaye, aikata miyagun laifuffuka kamar
sara-suka, bangar siyasa, sata, fyaxe, d.s
5) Rashin tsaro da aminci a cikin alumma
6) Mutuwar aure
7) Ci baya ga alumma

April 29, 2017


Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 15
Qalubalen da ke fuskantar Tarbiyya [1]
1) Talauci
2) Savani a tsakanin iyaye ko kuma rabuwar aure
3) Saxaxowar munanan aqidu da hanyoyin vata
4) Daawar kare `yancin mata, da kururuta haqqoqin yara
5) Hulxa da mutanen banza da kangararrun yara da mutanen da suka
shahara da sharri, da lazimtar wuraren da ke vata tarbiyya, kamar
gidajen sinima ko wuraren kallon finafinai da qwallon qafa
6) Mummunar muamalar da iyaye ke nuna wa `ya`ya
7) Kallon finafinan banza, waxanda ke vata tarbiyya
8) Zaman banza da rashin aikin yi
9) Sakaci da alamarin tarbiyya
10) Mutuwar iyaye
April 29, 2017
Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 16
Daga Qarshe
o














April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 17


Daga Qarshe
o :







April 29, 2017 Ahmad Bello Dogarawa, ABU, Zaria 18

You might also like