Download as doc, pdf, or txt
Download as doc, pdf, or txt
You are on page 1of 1

FADI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU

Annabawa da Waliyai sun koyar da ilimai daban'daban wayanda ke koyarwa


zuwa ga kwanciyar hankali na jasadi don ruhi ya zauna lafiya. Idan ruhi ya sake
wurin zama sai ya zamto wani bai gane wani abu ba sai yayi adalci ya tanbaya,
misali Annabawa da waliyai kamar likitocine na duniya idan mutum yakarbi
magani sai bai gane ba kuma baiyi tanbayaba to maganin ya iya cutar dashi
kenan. idan kaji wani irin ilimi wanda baka taba ji ba, idan abunda ya shafeka
ne sai kayi tanbaya idan kuma bai shafeka ba to sai kayi shiru kabar wayanda
abun ya shafa. To idan abu bai shafeka ba sai kuma kasa bakinka aciki Kanata
bata abun to bakayi adalciba. Sannan idan ya zama maganace ta addini Allah
yakira kansa da suna adalci to kace adini kake to amma kuma kana iya sakin
bakinka akan addinin, anya bazai zama kuskureba kuwa? saboda ankasa samun
wanda aka hadu ake yabonsa aduk duniya kamar yadda ba asamu wanda aka
hadu aka qishiba aduk duniya. an saba a tunani an saba a harsuna an saba a
manufa an saba a ji da gani na zahirin da na batinin, me zai hana ayi la akari da
haka idan wani zai baka labarin abunda ke cikin jikinka to mai zai sa kayi musun
abunda baka sani ba. Idan lokacin abu yayi to komin dabarar mutum bazai iya
kautar da wannan abun ba indai wanda yake dauke da sirrin khilafa uzuma
yace ga abunda zai faru to ai sai dai ajira kawai. yahudawa sun tabbatarda
cewa Muhammadu shine Ahmadun nnan da akayi masu albishir da zuwansa
amma suka qi shi qiyayya. Shikenan abunda suka iya yi masa don babu abunda
suka iyayi domin ayau babu inda Sunan Manzan'Allah s a w bai shiga ba a
duniya duk da irin karfin da suke gani suna dashi. Abunda mutane da dama
basu fahimta ba shine babu wani mai qarfin da yakai mujaddadin zamani babu
wani mai dabara akansa babu wani mai bakin addu a akan abunda yace zai
faru. Dan Abu lahabi ya batawa Manzan'Allah rai sai Annabi s a w yace masa sai
kariyar Allah ta cika, wata rana zasu tafi fatauci sai Abu lahabi yace su kula da
dannan, dan Muhammadu yace kariyar Allah sai taci shi, hakan kuma ya faru
awannan tafiyar suka barshi adaki yana bacci kura ta cinyeshi. To Abu lahabi ya
yarda idan Annabi s a w ya fadi magana tabbas sai tafaru, amma wannan
hassadar bazata bar shi ya sallama ba.
ISA ZAHIRAN KHAIRAN ZAHIRAN AMEEN SUMA
AMEEN —

You might also like