Usman Abba Ringim

You might also like

Download as docx, pdf, or txt
Download as docx, pdf, or txt
You are on page 1of 3

Haƙiƙa, sanin inda kalmar hausa ta samo asali abin bukata ne a garemu, duba da yadda muke da

ƙauna gami da soyuwar son jin tarihi mafi gaskiya na wannan harshe namu.

Idan wasu sunce asalin kalmar ‘Bahaushe’ wadda ake laƙabawa wanda duk ya fito daga masu
yara harshen Hausa, ta fito ne daga kalmar ‘Baushe’, ma’anarta kuma mafarauci, to sai muce ita
kalmar hausa kuma daga ina ta samo tushiya?
Kalmar Hausa ance baƙuwa ce, wai daga baya tazo. Ance ma masanin tarihi Leo Africanus ya
tabbatar da cewa a zuwansa Katsina da Kano a ƙarni na sha biyar, baiji a na ambaton sunan
‘hausa’ ba, kuma da yaren gobiranci yaji ana magana.
Haka kuma manazartan littafin nan mai ɗauke da tarihin kano mai suna ‘Kano chronicle’ sun
tabbatar da cewa tun daga zamanin Bagauda har zuwa kan Abdullahi Burja, ba’a yi amfani da
kalmar hausa ba. Sai a wuraren karni na sha biyar, lokacin ɗansa Yakubu aka soma jinta
Babu mamaki, wasu daga waɗannan zantuka na sama na iya zamowa gaskiya, sai dai akwai-ja a
wasun su, musamman a maganar yaren gobiranci da akace Leo Africanus ya tarar ana yarawa a
kasar hausa.
Domin masu bayar da tarihin Gobirawa sunce asalin su daga misira suka zo, yaƙi ne ya korosu,
suka rinka sauka da tashi a wurare mabanbanta, sai a karni na sha biyar suka riski birnin Lalle da
Gwararramu. Kunga kenan a wancan lokacin (karni na shabiyar) ba su iso inda kasar hausa take
ba a yanzu.
Sannan kuma a wancan lokacin, wasu littattafai sun bada tabbacin wanzuwar wasu kabilu a
wannan yanki namu. Misali, kabilun Maguzawa, Katukawa, Gazargawa, Tokarawa,
Damarguzawa da sauransu.
Hakan na iya nufin Kabilar hausa mai yara yaren hausa itama ta wanzu amma dai ba da Hausa
ake kiranta ba, kuma sai daga bisani ne ta bunkasa tare da haɗiye ɗaukacin kabilun dake
makwabtaka da ita.
Binciken masana ne kaɗai zai iya bamu tartibin bayani fame da hakan, amma dai ga binda wasu
masana suka faɗa dangane da asalin kalmar Hausa:-
-Mr C.R Niben (1971) cewa yayi: Hausa daga buzaye ta fito, domin sunan da ake kiran mutanen
dake zaune a arewacin kogin kwara kenan.
-Farfesa Skinner (1968) cewa yayi :Hausa daga kalmar Aussa ne na mutanen songhai wadda ke
nufin Arewa. Kuma yace akwai daɗaɗɗiyar alaƙa tsakaninsu ta yadda har hausawa sun aro
kalmomi a wurinsu. A cewarsa ma kalmomin Bene da Soro duk nasu ne.
-Marigayi Mal Aminu kano cewa yayi hausa daga Kalmar Habsha ne. Domin shi yana ɗaya daga
masu cewa asalin hausawa mutanen habasha ne tun lokacin daya riski habashan yagano akwai
kamance-ceniyar al’adu a tsakaninsu da hausawa. A cewarsa ‘Habsha’ ne asalin sunan, sai aka
koma Habsa, sannan daga baya ya dawo Hausa.
-Sarkin Ningi Marigayi Alhaji Haruna cewa yayi an samo kalmar Hausa ne daga labarin
Bayajidda sa’ar daya kashe macijiya shi ne sai tsohuwa ayyana ta rinka cewa ‘ai wani mutum ne
ya kasheta wanda ya HAU-SA’ maimakon tace yahau doki.
-Marigayi Dr Uba Adamu ya kawo a littafin sa mai suna ‘Sabon Tarihin Hausawa’ cewa kalmar
Hausa ta samo asali ne daga wani mutumi mai suna ‘Hausal’, shi kuwa jika ne gurin Firaunan
Misira Lamarudu.
Shin mene ne ra’ayinku game da asalin kalmar ta Hausa?

asana tarihi sun bayyana yaren Hausa a matsayin yaren da Misiriwan zamanin Fir’auna suka yi
amfani dashi.

Bayan wani rahoto da sashin Hausa na rediyon DW ya fitar akan batun, rediyon ta tattauna da
wani masanin tarihi dan kasar Nijar wanda ya tabbatar da ikirarin kasancewar yaren Hausa a
matsayin yaren da mutanen zamanin Fir’auna suke yi.

Masanin tarihi, Sule Garba, ya kara da cewa mutanen zamanin Fir’auna sun fara rayuwarsu ne a
kauyen ‘Dan Baki’ dake garin Damagaram na Jamhuriyar Nijar.

Hakan na zuwa ne bayan da aka gano wani ginin tubalin ‘Pyramid’ irin na kasar Misra, ginin da
turawa, masana tarihi suka tabbatar da Misirawan da sukayi kaura zuwa kasar Misira ne suka
ginashi. Kuma shine ginin ‘Pyramid na farko kafin su gina na kasar Misra.

Haka zalika ya tabbatar da cewa yaren da Misirawan zamanin Fira’auna sukeyi mai
suna Hieroglyphs, Hausa ce ba wani abu ba. Domin babu wani yare da ake rubuta “RAna” da
ma’anar Rana (Sun) take fitowa idan ba yaren Hausa ba.
DABO FM ta gudanar da binciken cewa an fara tabbatar da alakar Hausawa da Misirawan
zamamin Fir’auna shekaru 200-300 da suka gabata.

A shekarar 1938, fitaccen marubuci Werner Vicychl, ya tabbatar da alaka a cikin wani littafi da
ya wallafa.

Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya ‘UNESCO’ ta tabbatar da
alakar yaren Hausa da yaren Misirawan zamanin Fir’auna a wani littafi mai suna ‘The peopling
of ancient Egypt and the deciphering of Meroitic script‘.

Binciken DABO FM ya kara lulubo wasu kalmomi da suke kara tabbatar da Hausa a matsayin
Misirawan zamanin Fir’auna;

An gano daga cikin fassara da akayi a yaren Misirawan lokacin, Misirawa suna kiran Fir’auna da
sunan kalmar ‘Saraki’ wanda har ila yau yana amfani da ita a kasar Hausa wajen kiran Sarki.

A cikin kalmomin yaren Fir’aunawa akwai ‘Tuta’ – wacce take da ma’ana daya da ta yaren
Hausa da kalmar ‘Qasa’ da nufin Ƙasa da sauren dubban kalmomi.

You might also like