Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 7

HANYOYIN DAIDAITA SAHU A ILMANCE, DA KUMA AIKACE!!!

As salaamu alaikum!!!

Malam Bala,

 Gabatarwa
 A Daidaita Sahu
 Daidaita Sahu a Ilmance
 Daidaita Sahu a Aikace
 Rufewa

GABATARWA:

Shekaru kusan biyu da suka gabata naje Kano don ziyara kamar yadda
na saba. Kafin barin Abuja limamin unguwarmu ya bani wasu kudade in
sayo wani littafi da aka sa a masallaci don karantarwa cikin wasu ranaku.
Kasancewan babu wadatuwarsa yasa aka bani sautun in naje in sayo
kamar kwafi goma. Na samu sauki a kan yadda aka bani, a lokacin da
na samu kaina a shagon masu littafai kenan na Kasuwar Kurmi. Wanda na
tambaya da farko ya ce mani bai da littafin, sai dai in zan yi hakuri zai
nemo mani. Na ce ai ba matsala, muddin za a samu ina so kuma zan jira.
A karon farko ya shigo da guda shida don nuna mani ko ina son irin bugun.
Nan take na amince cewa ina so kuma ma ya karo makamantansu. Ya
ajiyesu ya koma.

Yayin da ya dawo a karo na biyu hankalina na wajen wani littafi da na gani


kuma ina kokarin bubbudawa don sayensa. Na dai hangeshi lokacin da
ya shigo da littafai a hannunsa, kuma ya hada su da wadanda ya kawo
da farko, amma ban san ko guda nawa bane. Yana ajiyesu nan take sai
ya nemo wani buhu (na Bagco Super Sack) ya dibiyesu a ciki. Ina
waigowa sai ya ce mani, cikin murmushi: “malam ga su nan an samu a
Naira dari shida shida.” Nan take na biyashi, a matsayin guda goma kenan
na saya. Na kuma biya sauran littafan da na saya bayan ya fita. Ya dauki
littafan da ke cikin buhu ba tare da ya barni na duba su ba, ni kuma a
tunani na ai wannan shagon sayar da littafan addini ne, don haka bani da
wani haufi kan cewa za a zalunce ni. Cikin gaggawa ya yi gaba ina biye
dashi, har na samu abin hawa, na karbi buhun, ya juya yana ta waige
waige na har sai da ya tabbatar mun tashi sannan ya kule. Ni a nawa
tunanin ai duk tsaban damuwa ne da ni da yayi don na yi masa cinikin
sama da Naira dubu shida, ashe washe ni yayi tatas! Ban tashi lura ba sai
na dawo Abuja! Ashe littafai takwas kadai ya bani a matsayin goma.
Hankalina ya tashi ba wai don yawan kudin da ya cuce ni ba, a a, sai don
ganin cewa in har wannan abin zai faru a shagon sayar da littafai na addini,
to ina ne kuma musulmi zai sa kansa don neman tsaro daga zalunci?

A wani ziyara har wa yau da na kai Kano, na samu kaina a Kofar Na’isa,
bayan sallar Isha’I, yamma ta rufo bargonta a kan al’umma. Na tsallaka
bangaren kwanan Gandun Albasa kenan sai kawai naji wani a bayana
yana cewa: “. . . kiyayeka Ustaaz. . . Allah Ya sa kafi haka Ustaaz. . .!!!” na
waigo ban gane shi ba don ban san shi ba. Yana sanye da suwaitar bacci,
fara, da wando fari a zanzare, da hula hana sallah. Nace: “yauwa barka
ka dai. Yaya aiki?” ya amsa. Sai kawai na shantake da tsare mota don
samun wacce zata kai ni Hotoro, masaukina a wancan lokaci. Can sai naji
yace: “ustaaz”, na waigo nace: “barka dai, wani abu ne?” sai yace: “eh.
. .wallahi arzikin Naira goma kadai nake son kai mini.” Nan take na ciro
gudan Naira dari na bashi nace ya nemo canji don in bashi abinda yake
so. Tabbas na san akwai masu sayar da kayayyaki a bakin titi, nan
bayanmu, don haka ko juyawa in kalleshi ban yi ba. Sai da na tabbata
bana jin mostinsa a bayana, sai na waiga. Kwamfa! Ya kule kwanan
Gwandun Albasa, ko ganinsa ba a yi. Daga nan na bi bayansa, kuma ina
shan kwanan sai na hangoshi yana dawowa, a zatonsa na gaji da tsayuwa
na wuce, don yaci bulus. Yana hangoni shima sai ya shashance: “ah. .
ustaaz wallahi canji naje nema kuma ban samo ba. . .kai don Allah zan
samu canji nan wajenka?” yace ma wani dan kamasho. A takaice dai sai
hamsin biyu aka samu, na karbi daya na bar shi da guda dayan. Har na
dawo Abuja hankalina a tashe yake na abinda ya faru, don wani abu
daban na hango. Allah Ya sawwake.

A ranar da na samu bayanan gabatarwa na A DAIDAITA SAHU babu


abinda ya fado hankalina da tunanina sai wannan hali da na shiga lokutan
baya. Wannan ya sa na dauki alkawarin lallai in ce wani abu dangane da
wannan tafiya da Malam Shekarau ya assasa ta. Har wa yau, da yake ni
marubuci ne ga daya daga cikin jaridun dake fita sati sati a Kano, nayi
alkawarin in Allah Ya yarda zan ci gaba da rubutu akan abubuwa
makamantan wannan, don wannan ba wani abu bane da za a yi sau daya
ba kawai a shantake. Na so har wa yau in rubuto da turanci, amma sai na
ga lokaci zai kure mani, kuma bayan haka ma, zan fi gabatar da cikakken
ma’anan ababen da nake son fadi cikin harshen Hausa, ko banza
shugaban wannan hukuma shahararren dan jarida ne wanda na fara jin
bayyanarsa a kafafen watsa labaru na kasashen turai tun 1998 ko kasa da
haka. Don haka a min hanzari a kan wannan.

A gaskiya na yaba ma gwamnatin kano wajen kokarin da take yi na ganin


cewa al’umma ta samu sararawa. Daga ciki har da wannan shiri da ta
bullo dashi na DAIDAITA SAHU. Alal hakika rayuwar al’umma na bukaatar
gyare gyare, musamman ma ta bangaren tunaninsu. Don wannan shine
bangaren da yafi kowane bangaren jikin dan Adam amfani. Kuma ba
wani abu bane tunani illa abinda ya haifu daga zuciya ya haura zuwa
kwakwalwa, don haddasa aiwatar da abinda shi zuciyan ya yanke. Don
haka muddin tunanin mutum ya gyaru, to babu shakka duk wasu
harkokinsa sun gyaru.

A DAIDAITA SAHU:

A gaskiya da akwai matsaloli da dama cikin sahun al’umma a halin yanzu.


Akwai kafofi da muka bari har son zuciya da lalaci da zalunci da kwadayi
da sharholiya da karya da sauran al’amuran assha suka shige. Ga shi an
wayi gari sallarmu tayi rauni. Muddin aka zauna kara zube ba tare da
daidaita sahun nan ba, za a wayi gari tsayuwan sallar ma zai yi ma
al’umma wahala. Don kafofin da ke cikin na yanzu ma sun raunana shi.
Fahimtana da wannan shiri na DAIDAITA SAHU shine, wani shiri ne da zai ba
da muhimmanci ga gyara tunanin al’umman Kano da dukkan sasanninta,
kamar yadda ka aiko mani gabatarwa a kwanakin baya. Don haka
wannan ‘yar gajeriyar kasida tawa zata ta’allaka ne a kan yananin tunanin
mutane a yanzu da kuma yadda wannan hukuma zata yi don sauya su ta
bangarori biyu, kamar yadda na ayyana a sunan kasidar a sama. Hanya
na farko shine gyara tunanin mutane a ilimance; wannan ya faru ne
saboda shi mutum, a bisa fitirar da Allah Ya yishi, wani halitta ne da yake
da baiwa sama da baiwar da Allah Ya yi ma sauran halittu ‘yan uwanansa.
Yana magana, su basu yi; yana da kwakwalwar tunani, su basu da shi;
yana kuma da daman mulkan halittu ‘yan uwansa da wannan kwakwalwa
nashi don a matsayinsa na khalifan Allah a bayan kasa, shi ya cancanci
haka saboda samun zaman lafiya a duniya da yi ma Allah biyayya a bisa
yanda yake so ba yanda su halittun suke so ba. Wannan ta sa kwararo
kyakkyawan ilimi cikin wannan kwakwalwa na mutum daidai yake da
kwararo ma duniya ruwan sama – zai amfani kowa da kowa. DAIDAITA
SAHU a daya bangaren kuma shine mafi muhimmanci kuma nauyi ne a
kan gwamnati, tunda ita ce ke da daman sa wa a yi ko a bari. Wannan
shine bangaren aikata hanyoyin da ake son jama’a su bi don daidaita
sahun tafiyar da ake cikin yinta a halin yanzu.

Wani abu kuma da ya zamo wajibi gwamnati tayi ta hanyan wannan


hukuma da ta kafa shine tayi duk yadda za ta iya don ganin an samu
dorewarsa har sauran gwamnatocin da zasu zo baya su amfana, ko da da
wani suna ne daban. Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai da yi don Allah,
hakuri, da kuma jajircewa. Dole ne a samu wadanda zasu kawo matsaloli
iri iri, da sharri kala kala, amma babu yanda aka iya. Wannan wani abu
ne da shugabanci, musamman ma na gari, ya gada.
Ina son har wa yau ayi min afuwa saboda saibi da nayi wajen aiko da nawa
gudummuwar. Wannan ya faru ne saboda yanayin aiki na. Allah Ya
amfanar da mu gaba daya kuma yasa a samu cin ma nasaran abinda ake
son kaiwa gareshi cikin kyakkyawan manufa, amin. Bisimillah, wai an
hada malamai fada:

DAIDAIATA SAHU A ILIMANCE:

Duk wata gwamnati da aka samar da ita a doron kasa wajibi ne ta lura
kuma ta kare ma al’umma tunaninta, kada ya gurbata. Don wannan
bangare shine abu mafi muhimmanci ga al’ummar gaba daya. Har wa
yau shine zai ba al’umma yi ma gwamnati adalci a kan tayi mai kyau ko
bata yi ba. Amma idan ya zama tunanin al’umma a gurbace yake, to ta
hanyar son zuciya, kowa zai iya fadin abinda ya ga dama a lokacin da ya
ga dama, a kuma inda ya ga dama, ba tare da ya kiyaye da mai zai je
ya kawo ba na sakamakon maganganu ko aikinsa. Da wannan na ga ya
zama wajibi ga wannan hukuma ta tsara yadda gwamnati zata canza ma
al’umma tunaninta dangane da:

 Addini – Mutane da dama basu san me ye addinin musulunci ke


karantarwa danagane da ibada, zamantakewa da sauran al’ummai
da rayuwar yau da kullum ba. Sau tari idan hayaniniya ya faru
tsakanin musulmai da wanda ba musulmai ba a wata nahiya daban,
sai kawai a yi ta kashe mabiya dayan addinin a inda ake tare dasu.
Wannan ba karantarwar addinin musulunci bane. Tabbas a fili yake
cewa wannan na faruwa ne saboda rashin adalci da ya yi kakagida
a harkar shugabancin duniya gaba daya ma ba wai a Najeriya
kadai ba, to amma duk da haka tunda musulunci bai tanadi haka
ba, to bai dace ba. Har wa yau muna son a danganta mu da addini
amma mun ki mu koyi ibadan a ddinin da muke tutiyar karewa.
Musulmi da dama basu iya daidaita sahun sallah ba. Kowa yadda
ya ga dama haka yake yin ibada. Don haka dole ne hukumar ta
sanar da al’umma cewa ba ginshikin addinin musulnci ya kafu ne a
kan abubuwa kamar hudu. Na farko yin ilimi dangane da Ubangiji.
Mutane su san wai shin ma wa suke bauta ma ne? Wannan kuma
babu abinda ke bin bayansa sai imani. Idan mutum bai san
Ubangijinsa ba, babu yadda za a yi ya san da wa zai yi imani. Don
haka abinda ke bi ilimi shine cikakkiyar imani. Wannan a kullum ana
karantar damu, amma matsalar ita ce bamu mayar da hankali mu
yi masa kyakkyawar karatu. Na biyu kuma shine aiki da abinda aka
sani. Inda musulmi na aiki da abinda suka sani na ibada da addini,
da babu wanda zai yi musu kallon cin kashi balle wai har ya nufe su
da wata manufa mummuna da zai shi ga daukan rayuwakansu. Na
uku shine yin kira zuwa ga addini. Babu yadda za a yi musulmi yayi
ilimi da imani ya kuma aikata abinda aka umurceshi, sannan ya
zauna haka ba tare da kira zuwa ga addini ba. Mun san cewa
musulunci cike yake da kyawawan dabi’u da kyawun tsari. In har
kowa da kowa zai rinka kira zuwa ga wadannan babu yadda za a yi
mu kasance cikin halin da muke ciki. Abu na hudu shine hakuri a
yayin gabatar da dukkan wani aiki na addini. Babu yadda za a yi
ba a shiga halin kunci a lokacin kira zuwa ga addini, musamman a
wannan hali da muke ciki mai cike da rudani da hayaniyar zamani.
 Al’adu – Tabbas musulunci ya zo ne don yin fada da munanan
al’adu, to amma wannan ba yana nufin cewa babu wani alkhairi
bane cikin al’adu. Don haka dole ne hukumar da wayar ma
al’umma da kai dangane da muhummancin kyawawan al’adunmu
na gargajiya wadanda basu saba ma musulunci ba. Haka kuma
akwai wasu ‘yan boko daga cikin samari wadanda sun gwammace
da bin al’adu turawa (yahudu da nasara) da su bi al’adun mu na
gargajiya. Dole ne a wayar ma al’umma da kai a kan wannan.
 Ilimi – Wannan shi ma wani bangare ne da al’umma ke da babban
matsala a kansa. An kasu kashi uku: wadanda ba ruwansu da
neman kowane nau’I na ilimi; sai masu neman na boko kadai ba
ruwansu da na addini; sai kuma ‘yan addini tsantsa. Watau addinin
musulunci bai kayyade ma al’umma neman wani ilimi ban da wani
ba. Ana son a yi bokon, musamman ma a wannan yanayi da halin
rayuwa ke canzawa cikin kiftawar ido. Wanda basu neman kowane
nau’I suna cikin hadari. Masu neman na boko kadai – su suka fi
yawa – suma basu tsira ba. Wadanda kuma suka takaita da addini
tsantsa, su suna bukatar cikakkiyar wayarwa mai cike da hujjoji na
zahiri. Dole ne hukumar ta nuna ma al’umma muhimmancin ilimi,
duk da yake an sha tattaunawa a kansa, amma dan Adam akwai
shi da yawan mantuwa, musamman in ya samu kansa a halin yalwa,
wacce ke rudinsa. Kowane ilimi abin nema ne, kuma ya zama dole
gwamnati tayi anfani da karfin ikon ta wajen canza nau’in
bangarorin da matasa ke karkatuwa zuwa gareshi don wasu
bukatunsu na duniya, zuwa ga fannonin da al’umma ta fi bukatuwa
zuwa garesu. A tabbace yake kan cewa bukatuwar al’umma ita
ake fara gabatrwa a kan bukatar mutum daya, don neman maslaha.
 Zamantakewa – Mutane na bukatar wayarwa wajen zamantakewa
wallahi, don kusan Kaman ma mun mance da irin rayuwar da
kakanninmu suka yi ne mai cike da zumunci da hakuri da wadatuwa
da sauransu. Rayuwarmu a halin yanzu ta zama cike da kyashi da
rowa da gilli da rashin kana’a da karya da zamba da sauran dabi’un
tir. Dole ne a wayar ma al’umma da kai a kan cewa fa wucewar
zamani ba yana nufin zuwan bala’I bane da yin yadda aka ga
dama. Canji ya kan zo ne da fuskoki iri biyu; mai kyau da maras
kyau. Don haka dole a koya ma al’umma yadda zata rinka sarrafa
anfanonin da ke tattare da zuwan zamani.
 Bin doka – Saboda tsarin zamantakewa irin na Najeriyanci, mun
zama kara zube babu bin doka balle hukunta wanda yayi laifi.
Wadannan halayya su suka hallakar da al’ummomin da suka
gabata. A halin yanzu kananan dokoki irin tsaya a kan danja, zuba
shara cikin kwandonsa da aka tanada, ko kuma a daya bangaren,
yin fitsari/bawali a kan titi, zubar da yawu a inda jama’a zasu iya gani
su cutu, duk dokoki ne bai kamata wai har sai gwamnati tayi wani
abu kafin a bi su ba. A tsarin rayuwar dan Adam ya san cewa basu
da kyau, don haka ana ganin ba ma sai an ce masa kada ya aikata
su. To amma mu a najeriya ba haka bane. Wannan abin bakin ciki
duk jahar da kaje haka zaka gani. Dole a koya ma jama’a
muhimmancin bin doka. A nuna masu cewa ba fa gwamnati ta bullo
da dokokin nan don anfanin kanta bane, a a, don anfanin su ne. Don
haka duk wanda ya bi ba yayi ma gwamnati wani alfarma bane,
kan sa yayi ma.
 Zamani – A halin yanzu kowa ya san halin da al’umma ke ciki na
sauye sauye da ke faruwa a fagen na’ura mai kwakwalwa, da ci
gaban da ake samu a fannonin rayuwa gaba daya. Dole mutane su
yi tafiya, iya gwargwadonsu, daidai da na zamani. Allah Ya sanar
da mu cewa ba duk jama’a ta taru ta zama daya ba. Akwai
wadanda duk yadda zamani ya kai da bunkasa, ba zasu taba
kasancewa da shi ba. Mutane masu irin wannan ra’ayi na bukatar
wayarwa don sanin sakamakon ra’ayinsu, ko da an san ba zasu bi
abinda aka gaya musu ba. A matsayin gwamnati kuma, tana da
damar da zata iya sauya al’amura don kawo sauyin da take bukata.
A ilimantar da jama’a a kan muhimmancin wannan al’amri.
 Dabanci – A gaskiya wannan bangare na da muhimmancin da ya
kamata gwamnati ta bude masa nasa hukumar daban. Amma a
babin fadakarwa, mun san cewa dabanci wani bangare ne
burbushin al’adar bahaushe, wanda a lokacin da wannan al’amari
ya samu, an dauke shi kamar yadda aka dauki sauran al’adun
Hausa. Amma daga baya sai ya zama dabanci ya samu wani salo
da har ta kai ana danganta shi da “sana’ar zaman kasha wando”,
wanda hakan shi kawo babbar matsalar al’umma ke fama da ita na
sace sace, da zamba da sauran dabi’un assha. Al’umma na bukatar
sanin cewa muddin aka jawo su jika aka shigar dasu cikin tsarin
al’umma, za amfana da su.
 Kudi – Wannan kowa ya san muhimmanci ko illarsa. A bayyane yake
cewa al’amuran rayuwa yanzu sai da kudi. Wannan yasa mutane
suka wayi gari komai ya zama na kudi kuma don kudi. An wayi gari
mutane basu banbancewa tsakanin halal da haram da kuma
cakudadden kudi. Duk wanda ya samu kawai ci ake yi. Tabbas
muna iya cewa wannan na daga cikin alamun tashin kiyama, to
amma ba hujja bane gwamnati ta zuba masa ido. A fahimtar dasu
muhimmancin cin halal da munin cin haram, da kuma kauce ma
duk dukiyar da yake cakudadde ne; watau akwai haram da halal a
cikinsa. Har wa yau al’umma na bukatar sanin cewa ba fa komai da
komai bane kudi ke iya yi. Mutunci da karamci da zumunci wasu
ababe ne da kudi ba ya iya sayansu. A fahimtar da al’umma sosai
cewa addini fa bai ta’allaka komai a kan kudi ba. Har wa yau, zafin
nema, a ka’idar rayuwa, ba shi ke kawo samu ba. Muddin mutum
na da kana’a, to duk karancin abinda ya samu, muddin ya nemi
albarka, to Allah zai sa masa a ciki har ya samu rayuwa
ingantacciya.
 Talauci – Tunanin al’umma a wannan bangare ya kasu kashi biyu;
bangaren farko sun yarda cewa lallai akwai talauci a kaddarance,
amma wannan har wa yau bai hana su neman arzikin halaiyarsu ba.
Wannan shine tataccen tunanin musulunci dangane da talauci.
Kashi na biyu basu yarda cewa talauci wani bangare bane na
kaddara, sun tafi kawai ne a kan cewa Allah bai yi mutane don su
zama cikin talauci ba. Shi yasa, a cewarsu, ya nuna ma dan Adam
ilimin yin abubuwa kala kala. Don haka tun da haka, suna ganin
hauka ne mutum ya zauna yace shi talaka ne. dole ne ya nema
kuma ya kudance ya zama mai dukiya. Tunani na biyu tunani ne irin
na ‘yan jari-hujja, watau capitalists. Don haka a ilimantar da
al’umma cewa kowa ya tashi ya nemi abincinsa, ba da hadama ba.
Sannan kuma wajibi ne ga duk wanda ya yi iya bakin kokarinsa bai
samu abinda yake name ba, to Allah bai kaddara yana daga cikin
wadanda zasu yi dukiyar bane. Amma mutum ya dage kan cewa
sai yayi kudi ta kowane hali, shi ke jawo mana bala’ai iri iri a cikin
zamantakewarmu. Hakkin gwamnati ne ta fahimtar da al’ummarta
wannan ta kuma dora su kan wannan tunani.

Wassalaamu alaikum!!!

Abdullahi Salihu Abubakar


Anguwar Hausawa,
Garki Village,
Box 5331
Abuja.

You might also like