Download as doc, pdf, or txt
Download as doc, pdf, or txt
You are on page 1of 7

LITTAFI ISHAYA 54:1-13

KAUNAR UBANGIJI GA ISRA'ILA

1 Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa. Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda
murna. Yanzu za ki ƙara samun 'ya'ya fiye da na Matar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!

2 Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki! Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!

3 Za ki faɗaɗa kan iyakar ƙasarki a kowane gefe, Jama'arki za su karɓi ƙasarsu Wadda al'ummai suke
mallaka yanzu, Biranen da aka bari ba kowa, za su cika da mutane.

4 Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba, Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da rashin
amincinki irin na matar ƙuruciya, Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki, Mai kama da na gwauruwa.

5 Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki, Sunansa Ubangiji Mai Runduna! Allah Mai Tsarki na Isra'ila
mai fansarki ne, Shi ne mai mulkin dukan duniya!

6 Kina kama da amarya Wadda mijinta ya rabu da ita, tana baƙin ciki ƙwarai. Amma Ubangiji yana kiranki
zuwa gare shi, ya ce,

7 “A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.

8 Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci, Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.” Haka Ubangiji
mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.

9 “Na yi alkawari a zamanin Nuhu, Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba. Yanzu kuwa ina
miki alkawari, Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba, Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.

10 Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika
alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.

11 Ubangiji ya ce, “Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba ki da
wanda zai ta'azantar da ke. Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.

12 Zan gina hasumiyarki da jan yakutu, Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta,
Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu'ulu'ai.

13 “Ni kaina zan koya wa mutanenki,

ISHAYA 40:18-31
YAYI MAGANA AKAN KWATANCIN ALLAH DA WANI ABU KO KUMA MUTUM

18 Da wa za a iya kwatanta Allah? Wa zai iya faɗar yadda yake?

19 Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi, Maƙera kuma suka dalaye da zinariya, Suka sa shi
cikin abin da suka yi da azurfa.

20 Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba, Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.

Yana neman gwanin sassaƙa Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.

21 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?

Ashe, ba a faɗa maka ba tuntuni?

Ashe, ba ka ji yadda aka fara duniya ba?

22 Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta, Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama,

Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar 'yan ƙananan ƙwari. Ya miƙa sararin sama kamar labule,

Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.

23 Yakan kawo masu mulki masu iko ƙwarai, Ya kuwa mai da su ba kome ba ne,

24 Suna kama da ƙaramin dashe Wanda bai daɗe ba, Bai yi ko saiwar kirki ba. Sa'ad da Ubangiji ya aiko
da iska, Sai su bushe, iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.

25 Da wane ne za a kwatanta Allah Mai Tsarki? Ko akwai wani mai kama da shi?
26 Ka dubi sararin sama a bisa!

Wane ne ya halicci taurarin da kake gani? Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji, Ya sani ko su guda
nawa ne, Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa! Ikonsa da girma yake, Ba a taɓa rasa ko ɗayansu
ba!

27 Isra'ila, me ya sa kake gunaguni, Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba, Ko ya kula ya daidaita abubuwa
dominka?

28 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya. Bai
taɓa jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.

29 Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.

30 Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala, Samari sukan siƙe su fāɗi,

31 Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da
fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala
ba.
ISHAYA 40:1-30

YANA KARFAFA MU NE CEWA ALLAH ZAI IYA TAIMAKON MU

1 Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa
Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.

Allah Ya Tsauta wa Al'umma Mai Zunubi

2 Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! 'Ya'yan da
na goya sun tayar mini. 3 Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su
abinci. Amma wannan ya fi abin da jama'ata Isra'ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”

4 An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji,
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya. 5 Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku
hukunci ne? Ya Isra'ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo. 6 Daga kanki har zuwa
ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a
tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.

7 An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da
ko'ina kufai. 8 Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai
ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana. 9 Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran
jama'a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.

An Kira Su Tuba

10 Ya Urushalima sarakunanki da jama'arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga
abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku. 11 Ya ce,
“Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa
hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da
na awaki. 12 Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa'ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya
roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina? 13 Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa
amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata,
da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.

ISHAYA 42:1-17
Bawan Ubangiji

1 Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da
ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.

2 Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba, Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.

3 Zai lallaɓi marasa ƙarfi, Ya nuna alheri ga tafkakku.Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.

4 Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba, Zai kuma kafa gaskiya a duniya, Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna
jiran koyarwarsa.”

5 Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da
numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,

6 “Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya. Ta wurinka zan yi
wa dukan mutane alkawari, Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai.

7 Za ka buɗe idanun makafi, Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.

8 “Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka. Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata, Ba zan bar gumaka su sami
yabona ba.

9Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa, Tun kafin ma su soma
faruwa.”Yabo ga Ubangiji domin Cetonsa

YABO GA UBANGIJI DOMIN CETONSA

10 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji, Ku raira yabo ku dukan duniya! Ku yabe shi, ku da kuke tafiya ta
teku, Ku yabe shi, ku dukan halitta a teku! Ku raira, ku manisantan ƙasashe, da dukan waɗanda suke a
can!

11 Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah, Bari mutanen Kedar su yabe shi! Bari su da suke zaune a
birnin Sela Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!

12 Bari waɗanda suke a manisantan ƙasashe su yi yabo, Su kuma girmama Ubangiji!

13 Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi, Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi. Ya yi gunzar yaƙi
da tsawar yaƙi, Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa. Allah Ya Yi wa Mutanensa Alkawarin Taimako

14Allah ya ce, “Na daɗe na yi shiru, Ban amsa wa jama'ata ba. Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani
abu, Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.
15 Zan lalatar da tuddai da duwatsu, In kuma busar da ciyawa da itatuwa, Zan mai da kwaruruka inda
akwai rafi hamada, In kuma busar da kududdufan ruwa.

16 “Zan yi wa mutanena makafi jagora. A hanyar da ba su taɓa bi ba. Zan sa duhunsu ya zama haske, In
kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu. Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.

17 Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka, Masu kiran siffofi allolinsu, Za a ƙasƙantar da su, su kuma
sha kunya.” Isra'ila Suka Kāsa Koyo

ISHAYA 55:1-13

1 Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan!

Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome
ba!

2 Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba?

Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa?

Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa, Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.

3 “Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai!

Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.

4 Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai, Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.

5 Yanzu kuwa za ku kira al'ummai, baƙi, Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya, Amma yanzu za su
sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku! Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra'ila Zan sa dukan
wannan ya faru, Zan ba ku girma da daraja.”

6 Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu'a gare shi, Yanzu da yake kusa.

7 Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi
mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.

8 Ubangiji ya ce,
“Tunanina ba kamar irin naku ba ne, Al'amurana kuma dabam suke da naku.

9 Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, Haka al'amurana da tunanina suke nesa da naku.

10 “Maganata kamar dusar ƙanƙara take, Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe
duniya. Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba, Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma
domin a ci.

11 To, haka maganar da na faɗa take, Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata, Za ta yi kowane abin da na
aike ta ta yi.

12 “Za ku fita daga cikin Babila da murna, Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama. Duwatsu da tuddai
za su ɓarke da waƙa, Itatuwa za su yi ta sowa don murna!

13 Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu,

Sunday service 27-November25-34

Topic Our God can control all sercumstance

Matthew 6:25-34

Filibiyawa 3:4-7

You might also like