Professional Documents
Culture Documents
Ashmawiasaukake
Ashmawiasaukake
net/publication/325262366
Ashma'wi Asaukake
CITATIONS READS
0 20,549
1 author:
SEE PROFILE
Some of the authors of this publication are also working on these related projects:
Assessment of the Management of Public Access Computers in Academic Libraries in Kaduna State, Nigeria View project
All content following this page was uploaded by Usman Ahmed Adam on 21 May 2018.
Fassara cikin
Fassarar
Usman Ahmed Adam
1
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan kokarin zuwa ga Mahaifi na Wanda son sa gareni yasa
yasani a hanyan karatu bai gusheba yana karfafe ni har Allah ya dauki ransa, Zuwa ga
Mahaifiya ta wacce son da take mani yasa taketa karfafe ni kan karatu tana ji dani
har gobe. Allah Ina rokon ka kasaka masu da dukkan Alheran ka, ka basu ladan
fassarawa da duk wanda kabashi ikon karantawa.
GABATARWA
Ina farawa da Sunana Allah mai rahama mai Jinkai, Dukkan godiya ta
tabbabta ga Allah mahaliccin kowa da komai, Tsira da Amincin Allah su
tabbata ga fiyayyen halitta Shugaban mu Ja goran mu mai shir yarda mu
Annabin mu Muhamadu (SAW), Tsira da Amincin Allah su tabbata ga
Matanshi da ’Ya’yanshi da Sahabbanshi da duk wanda yayi masu bi su har
zuwa ranar Sakamako.
Bayan haka bazan iya kiran wannan Fassara ba saboda nasan cewa bai isa
akirashi da wannan sunanba, amma zan iya kiranshi dan kokarin fassara, na
rubuta shine bias alkawari da nayiwa yaya ta kan cewa zamu karanta
wannan littafi da sauran littafan da ake karantasu azaure na fikhu, ganin
cewa Allah bai sa karatun ya doreba sai nayi Alkawarin zan fassara mata su
cikin harshen hausa a rubuce. Gashi Allah ya yarda na fara da Ahalari da
Ishmawi ina mai rokon sa yasa su zamo masu amfani gareni da ita da duk
wanda yasami ikon karantawa ya kuma bani ikon cigaba da Fassara sauran
har zuwa Lauwali da sani amin.
2
Kasani (Allah yai maka dace) Cewa: Abubuwan da suke warware Alwala
sun kasu kashi Biyu (2):-
1. HADASAI:
2. SABUBBAN HADASAI (Abubuwan da zasu iya haifar da hadasi)
1. Kaga HADASAI, Guda Biyar (5) ne, uku daga GABA sune: MAZIYI,
WADIYI da BAWALI (Fitsari) biyu daga BAYA Sune: BAYAN
GIDA da TUSA.
2. Sukuma SABABBAN HADASAI:
* BARCI: yakasu kashi hudu (4):-
- Barci mai tsawo mai nauyi Yana warware Alwala
- Barci Gajere mai nauyi shima Yana warware Alwala
- Barci gajere mare nauyi baya warware Alwala
- Barci mai tsawo mare nauyi an so sake mashi Alwala.
Kasani (Allah yai maka dace) cewa: Ruwa ya kasu kashi biyu
1. Wanda ya hadu da wani abu
2. Da kuma wanda bai hadu da wani abu ba
1. Ruwan daya hadu dawani abu kuma daya daga ciki suffofin sa uku
suka canza ( Launi, Dandano, Ko Kanshi,) yakasu kashi biyu:
sha da abin da yai kama da haka, ba zai yiwu ayi amfani da shi cikin
Ibadu ba, Kamar Alwala ko wanin shi.
- Idan abin bazai yiwu a raba shi da ruwan ba, kamar gishiri ko
kanwa ko abinda yai kama dasu ko kuma ruwanda yake gudana a taskar
arsenic ko kibrit duk wannan Ruwan masu Tsarkakewa ne ga wanin su, za a
iya Alwala dashi.
Allah shine mafi sani.
6. Farawa da magabacinkai
7. Yin aswaki
Allah shine mafi sani.
BABIN TAIMAMA
FARILLAI SUNNONI DA MUSTAHABBAN TAIMAMA
FASSARA DA HAUSA
(Ya Allah ga reka muke neman taimako, gunka muke niman ga’fara, munyi imani
dakai, kuma gareka muka dogara, muna maka yabo da duk wani alheri, muna gode
maka, bama kafirce maka, muna masu biyayya gareka masu kaskantar da kai, muna
barin duk wanda ya kafirce maka, Ya Allah kai muke bautama muna sallah muna
sujjada garela, kuma gareka muke muke taruwa muna kaunar rahmarka muna
tsoron azabarka kwarai, lallai azabarka mesaduwace ga kafirai.)
1. Anso ga baligi yai sallar nafila kafin sallar azuhur da bayanta, da kafin
Laasar, da bayan magariba, sannan anso yawaita nafiloli bayan
magariba, wadannan ba wajibai bane mustahabbaine.
2. haka nan kuma anso sallan walha da tarawihi.
3. Gaisuwan masallaci ( raka a’ biyu duk lokacin da mutun yashiga
masallaci)
4. anso sallan Shafaii ( Mafi karancinsa Raka a’ biyu) da rakaa’ daya
Wuturi bayan sa wannan Sunnane muakkada, “maikarfi”
10
HANZARI
Anyima Wanda Yasami Kansa Cikin Daya Daga Wadannan Yanayi
Rangwamin Zuwa Juma’ah:-
1. Ruwan sama mai yawa.
2. Tabo mai yawa.
3. Kuturta wacce zata cutar da mutane da warinta.
14
4. Ciwo ko Jinyar mai ciwo, kamar mata, Da, ko daya daga cikin
Mahaifa kuma ba wanda zai kula dasu kafin a dawo, Kamar yadda in
Ciwo yayi tsanani da daya daga cikin makusanta ko dan uwa shima
yakan zama hanzari, IMAMU MALIK yace : Idan ciwo yai tsanani
balaifi daya daga cikin yan’uwa ko makusanta ya kula da harkansa ko
da zai bar zuwa Juma’ah
5. In Mutun yaji tsoron Daurewa ko dukan azzalumi ko fashi.
6. Mai matsanan cin hali in yaji tsoron kar masu bashi su kamashi.
7. Makahon da bashi da Jagora.
Ya haramta ga Wanda Juma’ah ta wjjaba a Kansa yai tafiya bayan
rana ta take, Hakanan Magana ko Na’fila ta haramta lokacin da liman
yake Huduba (hudubar farko ko takarshe) sai dai in yariga ya fara
nafilan kafin liman yashigo sai ya cikasa nafilan sa.
Saye Da Siyarwa Ya haramta Bayan Kiran Sallah na Biyu, Sannan
kuma ana bata cinikin in yafaru.
Anki barin aiki ranar Juma’ah
Nafilan Liman lokacin kiran sallar Farko,
Anki Zuwan Yarinya Budurwa Masallacin Juma’ah
Hakanan kuma anki Tafiya Bayan fitowan Al-Fijir,
Allah Shine mafi sani.
FASSARA DA HAUSA
(Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ke kashewa da rayawa, godiya ta tabbata
ga Allah wanda yake rayar da matattu, girma da daukaka da mulki da iko da yabo
duk sun tabbata gareshi, Shine mai iko akan kowa da komai, Ya Allah kai tsira ga
annabi Muhammadu (saw) da alayen annabi Muhammadu kayi albarka ga annabi
Muhammadu da alayen annabi Muhammadu kamar yadda kayi tsira kayi rahama
kayi albarka ga annabi Ibrahima da alayen annabi Ibrahima, Allah Kai abin
godewane kuma Kai me germane,Ya Allah mamacinnan bawankane, dan
bawankane, kuma dan baiwarkane, Kai kahalicceshi Ka azurtashi kuma Kai
kakarbi ransa kuma kaine zaka rayashi, Kafi kowa sannin abinda ya boye ko
yabayyana Munzo muna masu neman ceto gareka Ka bamu cetonsa, Ya Allah muna
kusanta da abinda yakusantaka da shi don kai mai Alkawari ne mai kuma cikawa
da Alkawane,Ya Allah Kakiyeshi daga Fitinar Kabari da azabar wutar Jihannama,
Ya Allah ka yafe mashi Kayi mashi rahama Kayi mashi ran gwami Ka kiyayeshi Ka
girmama masaukinshi Ka yalwata mashiganshi Allah Ka wankeshi da ruwa da
kankara da raba, Ka tsarkakeshi daga dukkan zunubai da kurakurai kamar yadda
ake wanke tufafi fari daga datti, Allah Kamusanya mashi gida wanda yafi nashi,
Ka musanya mashi iyalai wadanda sukafi nashi, ka musanya mashi mata wacce
tafi tashi, Ya Allah in ya kasance ma abocin ayyuka masu kyaune ka kara masa
akan ayyukansa in kuma ma abocin muna nan ayyukane Ka yafe mashi, Ya Allah
to gashi ya sauka gareka kaine fiyayyen mai ma sauki, Allah yana mabukaci zuwa
rahmanka Kai kuma Ka wadata da azabtar dashi, Ya Allah ka tserar dashi wajen
tanbaya, Allah kar Ka jarrabeshi da abinda ba zai iyaba, Ka sadashi da Annabinshi
Muhammadu (SAW) Ya Allah kar Ka haramta mana ladanshi kar Ka fitine mu
bayanshi.
16
FASSARA DA HAUSA
(Ya Allah kagafarta ma rayayyimmu ka jikan mamatanmu wadanda muke tare dasu
da wadanda bamu tare dasu, manyanmu da yaranmu mazanmu da matanmu, Allah
Ka san inda muka sanya gaba kasan makomanmu, Allah Ka yafe mana da iyayen
mu da wandada su ka riga mu iimani, ga fartawa mai wanke dukkan zunubai,
Allah ka ga fartawa musulmai maza da mata, mu’uminai maza da mata masu rai
da matattu. Ya Allah wanda karayashi a cikin mu Karayashi a akan imani wanda
kuma Ka dauki ranshi Ka daukeshi akan Musulunci, Ka azurtamu da saduwa
daKai, Ka da dada mutuwa garemu, ka da dada mu ga mutuwa, Ka sanya hutu da
jin dalin mu a cikinsa.)
daran khairan min darihi wa ahlan khairan min ahlihi wa a’fihi min
fitnatil qabri, wa min azabi Jahannam.
FASSARA DA HAUSA
(Ya Allah Shi bawanka ne dan bawanka ne Kai Ka halicce shi Ka azurtashi
sannan Kai Ka matardashi Kai kuma zaka rayashi, Ya Allah Ka sanyashi (Bashi,
Asusu, Kundi, Lada) ga iyayenshi, Ka nauyaya mizaninsu dashi, ka girmama
ladansu, Allah kar ka haramtamasu ladanshi, muma kar ka haramtamana ladanshi,
kar Kafitnesu bayanshi muma kar Kafitnemu bayanshi, Ya Allah Ka sadashi da
ya’yan mu’minai cikin rainon Annabi Ibrahima, ka canza mashi gida wanda yafi
gidanshi, da iyalai wandanda suke fi nashi, Ka kiyayeshi da fitinan kabari, da
azaban Jahannama)
Zaka fadi haka bayan kowani kabbara amma bayan kabbara ta hudu
kace:- Allahummag-fir li as-lafina wa afradina wa liman sabaqana
bil’iimani, Allahumma man ahyaytahu minna fa ahyihi alal-iimani,
waman tawaffaitahu minna fa tawaffahu alal-islami, wag-fir lil-
muslimina wal-muslima’ti wal-muminiina wal-munina’ti, Al-ahya’I
minhum wal- amwa’ti.
FASSARA DA HAUSA
(Ya Allah kajikan wanda suka rigamu da wanda suka gabacemu da wanda suka
riga mu da imani. Ya Allah wanda Ka raya shi a cikin mu Ka rayashi akan iimani
wanda Ka dauki ranshi acikin mu Ka daukeshi kan muslunci, Ka ga fartama
musulmai maza da mata da mu’minai maza da mata masu rai da mutattunmu.)
Sannan sai ka sallame.
Allah Shine mafi sani.
BABIN AZUMI
Azumin Watan Ramalana ana farawa lokacin da watan Sha’aban ya cika
ko da ganin Adilai biyu ko mutane masu yawa wadanda bazai taba
yiyuwa su hadu akan karya ba, kuma ana barin azumin don cikan watan
kwana 30 ko ganin Adilai biyu ko Jama’ah masu yawa.
Ana yin niyyar Azumin adaren farko ne badole bane ayi Niya kullum,
Ana cika azumi har zuwa faduwar rana
Yana daga cikin Sunna, Gaggauta Shan-ruwa da Jinkirta Sahur
In ganin Wata ya tabbata bayan Al-Fijir Kame baki da ramuwa sun
wajaba.
18