Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 5

‫ﱡ ﱎ ﱏ ﱐﭐﱠ ﭐ‬

Amma dukkanninsu ingantattu ne muta wafirai, Ma'ana: Allah ne yake da


cikakken mulki a wannan rana, babu wanda zai yi hukunci a wannan rana tare
da Allah.

‫ﱡ ﱐﭐﱠ‬
wannan kalma tana nufin: hisabi da sakamako, a dalilin haka Allah ta'ala ya
ce:
‫ﱡﭐ ﱮ ﱯ ﱰ ﱱ ﱲ ﱳ ﱠ‬
Ma'ana: " Me ya hana idan da kun zamto ba waɗanda za'a yiwa hisabiba"
Suratui-Waƙi'a aya ta 86.
MUHIMMAIYAR FA'IDA:

kalmar ‫ ﭐﱡﱩﭐﱠ‬tana zuwa da Ma'anar: shari'a, ko addini, kuma anfi amfani


da ita a haka, Allah l Ya ce:
‫ﱬﱠ‬
‫ﱭ‬ ‫ﱡﭐ ﱨ ﱩ ﱪ ﱫ‬
‫ ﭐ‬Ma'ana:"haƙiƙa addini a wurin Allahlshi ne muslunci" ana nufin addinin
da Allahl ya zabeshi ya yarda da shi.
Addinin da Allahlya aiko mazannin sa gabaɗaya da shi shi ne musulunci,
wanda ya fara tun daga kan Annabi Adamp har zuwa kan manyan
manzannin nan da aka sani da "ulul-azmi" su ne: Annabi Nuhu da Annabi
Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Isahr na ƙarshen su shi ne: Annabi
Muhammadn, dalilin hakan akwaishi da yawa acikin Alƙur'ani mai girma.
Babu abinda ya inganta game da maganar da ake ce wa: " addinan da suka
sauka daga Allahl guda uku ne" shi addinin da yake daga wurin Allahl
shi ne Musulunci, duk wanda ba shi ba kuma ɓata ne.

32
Don haka addini guda ɗaya ne, abinda ya banbanta su kawai shi ne tsarin
shri'o'i, kamar yadda Allahl Yake cewa:
‫ﱡﭐ ﲊ ﲋ ﲌ ﲍ ﲎﲏ ﱠ‬
Ma'ana:"kowanne daga cikinku mun sanya musu tsari na shari'a da tsari na
rayuwa" [Suratul-Ma'ida aya ta 48].
Keɓance mulkin Allahl shi kaɗai a ranar lahira baya kore masa mulkin
wasu ranaku, saboda ya gabata cewa shi ne Ubangijin talikai, kuma hakan ya
game duniya da lahira, amma an jingina hakanne da ranar lahira saboda rana
ce da ba mai mallakar komai sai shi.

FA'IDOJIN WANNAN AYA:


1. Tabbatar da mulkin Allahl shi kaɗai a ranar alƙiyama.

2. Faɗakar da bawa game da ranar alƙiyama, don bawa yayi aikin da zai
tseratar da shi a wannan rana, kuma yayi takatsantsan yayi tanadi.

3. Bayyanar mulkin Allahl ga dukkan halittu gabaɗaya a ranar alƙiyama,


kamar faɗin Allahta'ala:

‫ﳈﳊﳋﳌﱠ‬
‫ﳉ‬ ‫ﱡﭐ ﳆ ﳇ‬

Ma'ana: " mulkin ga wa yake a wannan rana, ga Allah shi kaɗai yake
mai ƙarfi (akan kowa). [Suratul-Gafir aya ta 16].
4. An kawar da dukkan mulki ga dukkan abin halitta a ranar Alƙiyama,
Allahl kaɗai ya keɓantu da mulki na ranar.

33
AUNA FAHIMTA:

1. Ka ambaci ma'anonin lafazin ‫ ﱡﱩﭐﱠ‬tare da kawo dalilai daga ayoyin


Alƙur'ani.

2. Menene yasa aka jingina mulkin ranar ƙiyama ga Allahl, alhali shine
mai mulki a kowane, lokaci kuma mamallakin komai.

3. Mene ne ingancin wannan magana: "cewa yahudanci da nasaranci da


musulumci su ne addinai uku da aka saukar daga sama?"

‫ﭽ ﱒ ﱓ ﱔ ﱕ ﭐﭼ‬

Ma'ana: "gareka kaɗai muke bauta kuma gareka kaɗai muke neman taimako"

‫ﱡﱒ ﱓﭐﱠ‬

Abi nufi: muna ƙanƙandakai gareka dukkan ƙanƙantarwa.


"‫" "ال ِع َا َدة‬Ibada" tana nufin: sunan da ya tattaro dukkan abinda Allahl yake
so kuma ya yarda dashi na daga ayyuka da maganganu na zahiri da na baɗini.
"bawa" (na haƙiƙa) shi ne: wanda ya dace (da bin) abin bauta (Allah) acikin
abinda yake nufi na shari'a.
MUHIMMIYAR FA'IDA:
Ibada ba ta daidaituwa ta zama karɓaɓɓiya sai in takasance an yi ta ne kaɗai
saboda Allahl, kuma bisa shiryarwar Annabin, duk wanda ya farar da wani
abu ko ya ƙirƙireshi a cikin addinin Allahl to bai tabbatar da bautar da
Allahl yake nufi ga bayin sa ba.

34
A cikin wannan aya an taƙaita yin bauta da dukkan neman taimako ga
Allahl shi kaɗai, kamar yadda lafazin '' ‫ '' ﱒ‬gareka kaɗai" ya nuna akan
lafazin "‫" " ﱓ‬muke bauta" don haka kasancewar bawa bashi da ikon
tsayuwa akan yi bauta batare da samun dacewa da neman taimako daga
Allahl ba, shi yasa yake haɗawa da neman taimakon Allahl, sai ya ce:

‫ﱡ ﱔ ﱕﭐﱠ‬

"Gareka kaɗai muke neman taimako" lafazin "‫ "ضسْْْْْتعانة‬yana nufin: neman
taimakoda dogaro ga Allahl wajen neman dukkan amfani, da kuma neman
kariya daga dukkan cutarwa, tare da yarda da shi wajen neman hakan, abin
nufi bazamu bautawa kowa ba sai kai kuma ba zamu dogara ga kowa ba sai
gareka, wannan itace cikakkiyar ɗa'a ga Allahl, kuma addinin gabaɗaya
yana komawa zuwaga waɗannan abubuwa guda biyu: bauta da dogaro ga
Allahl.
Wasu daga cikin magabata na ƙwarai suka ce: fatiha itace sirrin Alƙur'ani,
kuma wannan aya ita ce sirrinta

‫ﱡ ﱒ ﱓ ﱔ ﱕﭐﱠ‬

"Gareka kaɗai muke bauta kuma gareka kaɗai muke neman taimako"
- Abu na farko barrantuwa da ga yin shirka,(haɗa Allah da wani wurin bauta)
- Abu na biyu barrantuwa daga wata dabara ko ƙarfi (ga bawa).
An juyar da yanayin magana acikin ayar daga lamarin wanda bayanan kamar
yanda yake cikin ayoyin ukun farko zuwa lamarin wanda ake magana dashi
kai tsaye, domin nuna kusanci gareshi kai kace bayan bawa ya yabi Allahl
ya girmama shi ambashi damar kusan tuwa zuwa gareshi, da bayyana a gaban
shi, sai yace:

35
'' ‫ '' ﱒ‬da lamirin wanda ake magana dashi kai tsaye.

FA'IDOJIN AYOYIN:
1. Bawa bashi da ikon bautawa Allahl sai idan Allahl Ya
taimakeshi akan hakan, wannan domin hana masu jiji da kai da masu
ruɗuwa da yawan ibadar su sudinga jin hakan (a ransu).
2. Ayar ta nuna cewa ba'a dogara ga kowa sai ga wanda ya cancanci a
bauta masa, kamar yanda yake cikin faɗinsa
:‫ﭐﱡﭐ ﲈ ﲉ ﲊ ﱠ‬
Ma'ana: "Ku bauta masa kuma ku dogara kaɗai gareshi" [Suratu Hud
aya ta 123].
3. FaɗinSa ‫ ﱡ ﱓ ﱠ‬yana nuna cewa lalle bawa yana da zaɓin yin aiki
kuma yana da ikon tsayuwa akan hakan, wannan raddi ne ga
Jabariyya1 waɗanda suke cewa: bawa bashi da zaɓi akan kansa face
shi ɗin abin tilastawane a ayyukansa.
4. Lallai bawa bashi da ikon aikata komai sai da taimakon Allahl da
ganin damarSa, a dalilin haka wannan raddine ga Ƙadariyya 2 waɗanda
suke cewa: bawa shi yake ƙirƙirar ayyukan sa da kansa ba tare da nufin
Allahl ba da ganin damar saba.
5. An taƙaita yin neman taimako ga Allahl acikin abinda Allahl ne
kaɗai yake da iko akai, kuma neman taimako irin na cikakkiyar sallama
lamarinka Allahl kaɗai ya keɓanta shi, amma ya halatta a nemi taimakon
abin halitta acikina abinda suke da iko akai.

1
wata ƙungiyace da suke da aƙidar cewa shi bawa an tilasata masa yin bautane bashi da iko akan kansa.

2
su ne masu aƙidar cewa bawa yanada ikon akan aikata komai ba tare nufin Allah ba.

36

You might also like