Ibtissam Book 1 Complt by Msslee

You might also like

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 248

IBTISSAM

( Heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee

Littafina na kudi ne akan 500 kacal , banyarda wani yayi an fani da wani bangarena
littafina ba, duk Wanda labarina yazo Daidai da wani abu na rayuwarshi a rashin
sani ne.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧

BOOK 1
(The beginning )

Season _1

THE UNITED STATE

NEW YORK CITY

COLUMBIA UNIVERSITY

Cikin babbar harabar hall dake cikin Columbia university,mutanene zazzaune kowa
kaga fuskarsa zaka ga farinciki da annashuwa a cikinta, daga saman stage suma wasu
mutanene sanye da suit a jikinsu black colour , daga sama kuma gown ce a jikin su
na graduation . Cikin tsantsan turanci da ke fito dako Wana kalma ake kiran sunayen
daliban , bayan kowa ya karbi certificate din shi aka fara kiran wasu daga cikin
daliban Domin basu award dinsu. Zaune yake cikin shigar suit dinshi fuskarsa sanye
da face mask ya dukar da kai sai gashinkansa daya sakko masa har wajan idanuwansa,
time to time yana duba diamond watched din dake hannunsa kafun ya mayar kan dan
kareriyar wayarsa kirar Samsung, “ADIL BIN MOHAMMED Al_TAUFEEQ”, gabaki d’aya kowa
jira yake yaga me sunan ya tashi amma kwata kwata Har yanxu babu Wanda ya mike ,
wata babbar macece ta kara kiran sunan tana duban daliban “ the most talented
person of the session,”ADIL bin Mohammed Al taufeeq,are you around please “, wani
na gefensa ne ya dan tabosa “ADIL ,MAAH is calling you”, banza yayi wa na gefen
nasa kamar be san da wani halitta a wajan ba , gabaki d’aya idanuwansa nakan
wayarsa ,Akaro na uku aka kara kira sunan adil Mohammed Al-taufeeq, yanxu ba mashi
da alama ko niyar tashi, “ YAYA PRINCE “, sunan da ya bayyana akan screen din
wayarsa , “finally” ya furta cikin wani daddadan muryarsa kafin ya mike a hankali,
gabaki d’aya hall din tafi aka fara bakajin komai sai raf raf raf din tafi dake
tashi, da ihu aka kiran “ADEEL, ADEEL” Wanda ya mike din cikin wani irin taku ya
karasa inda ake kiransa, wani medium box ne brown colour da akayi rapping aka mika
masa, kafun matar ta nuna masa wajan mic, har yanxu kansa a sunkuye yake be kalli
kowa dake cikin hall din ba, gabaki d’aya hall din shiru ya dauka kowa jira yake
yaji speech dinsa,shi kuma ganin yanda kowa yayi shiru ne yasashi dauke kansa shima
batare da yace komai ba kusan mintuna uku,”Little Boo”,kalmar ta sauka a kunnansa,
da Sauri ya dago eyes dinsa da har yanxu gashi ya karesu,cikin sauri yake kallan
mutanan wajan ko zea gansa, daga nesa dashi yaga an daga fingers guda biyu,
murmushi ya saki duk da facemask din dake fuskarsa, a nutse ya fara bada speech din
da ya dau hankulan mutanan wajan, gabaki d’aya cameras na kansa,yana kammala speech
dinsa wajan ya kara daukar tafii da kalmar “ADEEL da ake ta faman kira, yana koma
wa aka kara kiran sunansa as the most disciplined , dan guntun tsaki ya saki kamun
ya koma, yana karba bece komai ba yayi wucewarsa, idanuwansa akan wajan da aka dago
masa fingers dazu, so yake kawai yaga ankammala gabaki d’aya a ‘kage yake da ya bar
wajan, akaro na uku aka kara kiransa , jiyay kamar ya make mekiran nasa , gabaki
daya takaici duk ya kamasa,a karo na uku aka sake bashi wani gift din , Madam flora
na kokarin bashi waje don yayi wani speech din ya bar wajan, a haka aka cigaba da
kiran ragowar mutane 4 da zaa bawa gift suma, saida y karbi wasu gift din shima duk
acikin student din ya fi kowa karbar gift din kowa ADIL TAUFEEQ zakaji yana kira
kowa burinshi yayi hoto dashi, yana gani an gama ya mike da niyar barin wajan , duk
yanda friends dinsa ke rokansa suyi hoto ba Wanda ya kula a cikinsu, cikin mutanan
ya shiga kai tsaye amma be ga Wanda yake nema ba, kamar yayi kuka ya fita daga hall
din, a tsaye ya hango wani black American sanye da black suits, idanuwansa rufe da
ba’kin google, gabaki d’aya babu fara a cikin fuskarsa, da sauri ya karasa inda
yake gift din hannunsa ya mika masa,cikin girmamawa ya amsa kafin ya sara
musu,”captain” ya kira sunan mutumin, nuni mutumin yayi masa da wasu jerarrun
motoci baka ke wuluk da suke zagane da wasu mutane masu kakin sojoji,batare da ya
bari ya kuma cewa komai ba, cikin sauri sauri ya nufi wajan motocin, suna ganin sa
suka sara masa,motocin ya fara bi da kallo yana jiran yaga ta ina zasu fito,daga
bayansa yaji an furta “Little”, cikin wani daddadan murya, da mugun sauri ya juya
tare da ware idanuwansa, beyi wata wata ba kawai ya Dane mutumin” yaya prince dina”
shima Wanda ya ‘Dane rungumeshi yayi a jikinsa a hankali ya furta “ zaka karyani fa
“, dariya ya saki yana sauka daga jikin mutumin, wani hadaddan guy ne fari tas
dashi , kwata kwata rabin fuskarsa a kulle take sabida p_cap din data rufe masa
rabin fuskarsa sai dan medium din bakinsa da ya fito pink dashi, kallan gefe da
gefen mutumin yayi kafun ya furta “ basu dawo bako,” ya furta cikin sanyin murya
kamar me shirin yin kuka , “why the pity face, so kake BIG BOSS da YAYA BOBO suyi
farfesu nane, they’re at home fa”, kugu little ya rike kafun ya furta “ ka tabbata
yaya prince”, girgiza masa kai yayi kafin ya furta “toh nayi maka karya , if you
like kayi ta zama , ni am going “, yana kammala maganar sa wani black American ya
bude masa mota ya shiga, da sauri ADIL shima ya zaga daya bangaran nan ma wani
American guy ne ya bude masa kofa , da mugun gudu motocin suka fita daga cikin
Columbia university suka hau kan babban titin New York , mintuna 15 ne suka kawosu
hadaddan street din FIFTH AVENUE dake cikin Garin new york, gabaki d’aya layin
shiru kake ji kamar babu wani halitta da ke rayuwa a wajan sai sojojin da ke wucewa
time time, Daidai wani babban area da mafi yawanci sojojin suka fi yawa suka nufa,
gabaki d’aya sojojin mikewa sukai tare da sara musu, da mugun gudu wasu soldier su
hudu suka fara bin bayan motar har suka karaso dai dai wani babban gate me shegen
girma da tsaho, ba bata lokaci aka wangale musu gate din motocin su suka shiga
ciki, kusan tafiyar mintuna biyu suka kara zuwa wani gate din da ya fi na farkon
tsaro , awannan karan sai da aka caje motocin ta waje saida aka tabbatar da
lafiyarsu kafun a wangale musu gate dinshima,wata ni’imtacciyar iskace ta fara
ratsasu sabida flowers din da suka fara cin karo dasu, a wannan karan tafiyan minti
biyar sukayi kan dogon titin dake wajan, wata kafuwar gate ne da kanta take budewa,
ta wani slide din waje motocin suka wuce bayan gate din ya aunasu.
Daga cikin motar ADIL ne ya dan kalli captain dake driving,” captain I give you 3
minutes ka karasar damu, if not zan fada wa big boss ya shigar da kai dakin duhu”,
kafun prince dake gefensa yayi magana captain yaja motar da mugun speed “
azuciyarsa kuma yana auna irin horon da zai fuskanta idan ya karasa , sassaucin
sama BOBO yayi mishi hukunci ba BIG BOSS ba, suma ragowar motocin suna ganin haka
ko wannansu ya kara speed din motar, duk da sunsan dole su karbi hukunci wajan
BOBO.ko gama parking ba ai ba Adil ya fito daga cikin motar ya arta a guje, masu
tsaran kowa sunkuyar dakansa yayi cikin girmamawa, kofar babban masion din aka
bushe masa , nan ma da mugun gudu ya shiga, wata kofar ya nufa me shegen kyau, yana
shiga babban parlor ne ya bayyana me 4 set of designers , Aljannar duniya kenan
gabaki d’aya falon sai ka dauka a wata nahiyar kake ba a duniya ba, falo ne da ya
amsa sunan sa falo da ko me kudi be isa mallakar saba, naira tayi kuka ga wasu irin
Logan modern stainless steel tiered crystal chandelier da ya kara haska falon, ko
ina ka waiga haske ne tar, ga sanyin Ac dake busa ko ina na palour , cikin daga
murya ya fara kiran “ UNCLE IRON MAN, YAYA BIG BOSS ,YAYA BOBO,Little is back”,
yana maganar yana fincike mask din dake fuskarsa, fatabarakallahu ahsanin khalikin,
kyakkyawa ne shi sosai da ya amsa sunan kyau, fari ne shi sosai duk da ba wani
babba bane amma kyawunsa ya wuce misali, har yanxu bana iya ganin fuskarsa sabida
gashin kansa da ya rufe masa rabin fuska sai kadan daga hancinsa da zaka gane
dogone daya fito, sai dan karamin ba’kin shi pink kalo daya fito shima, Prince ne
yashigo falon bakinshi dauke da sallama da sauri Little ya kalleshi duk da ba ganin
idanuwansa ake sosai ba zaka gane hararar Prince yake, P_cap dinsa Prince ya saki,
kyakkyawar sumar kansa itama ta sakko masa har wajan idanuwansa,gyara gashin nasa
yayi kyakkyawar fuskarsa ta fito waje , ware idanuwansa yayi a kan little take eyes
dinsa dasuka kasance ash colour suka fito waje sabida ware idanuwansa da yayi,
shima kyakkyawa ne na ajin karshe , fadar irin kyawunsa ma bata baki ne, fuskarsa
bame fadi bace sosai sannan ba doguwa bace, dai dai jikinsa ga dogon hancinsa daya
kara fito da kyawun fuskarsa, dan madaidaici bakinsa ya tabe yana kara bin little
da kallo ,cikin wani yare ya furta “Ni kake harara”kamar mace little ya rike kugu
tare da tura masa baki, a guje prince ya bi bayan little, shima little yana ganin
hakan yasa gudu suka fara zagaye falon,”stop there “ Prince ya fada yana jefowa
little pillow , shima little pillow ya dauka tare da jefowa prince “ I won’t , ba
kaine kace mun my loves sun dawo ba”, wani pillow Prince ya dauka ya jefawa little
a fuska, ganin hakan yasa shima little daukan pillow, gabaki d’aya sun bata falon
duk pillows din kujerun sai da suka sakko da shi kasa,wani pillow Prince ya dauka
zai jefa wa little yaji saukar muryar data sashi faduwa “ If you dare “, da Sauri
ya jefar da abunda ke hannunsu, Prince ma mikewa yayi shida little suka hade waje
daya , kana kallansu kasan basu da gaskiya , Cikin 3 quarter din wandan sojoji da
bakar armless ya karaso cikin falon, kakkarfa surar jikinsa da kallo daya mutum zai
yi masa yasan yana daga karfe, kyakkyawa ne sosai da ya amsa sunan kyau, har na
kasa banbance wanane yafi kyau a tsakaninsu duk da fuskar little ma rabi ce a bude
amma kana ganinsu zaka ga kamannin da suke da juna har ya kwayar idanuwansa light
gray ya zuba musu , “YAYA BOBO” little ya fada da niyar nufar sa, wani gigitaccen
kallo ya jefa masa kuskarsa kwata kwata ba fara’a “ if you dare ka kara one step
kaga yanda zan karya kasusuwanku “, narai narai little yayi da ido, shikansa Prince
tsoran magana yake kar lefin ya dawo kansa baki d’aya ,kallansu mutumin yayi kafun
ya nuna musu 5 fingers dinshi “ just 5 minutes na baku , ku tabbatar falon nan ya
dawo yanda yake kafun ku karbi punishment dinku”, be karasa maganar ta saba suka
fara gyara pillows din , jiya d’auke kansa yayi daga kansu kafun ya dakko wata
roughly mobile phone army dake jikin 3quarter dinsa , number 3 kawai ya danna ko
mintuna biyu ba aiba , su captain Suka shiga cikin babban parlourn, gabaki d’aya
sara masa sukai ko kallan inda suke beyi ba, cikin kwarewa captain ya kara sarawa
tun kafin BOBO yayi magana,
Cikin yaran turanci Captain ya furta “ reporting !!! Tukin ganganci a harabar gida
hukuncin bulala dari tare da zagayen gida sau dari shine hukuncin mu”, ga baki
d’aya sauran soldiers din suka hada baki wajan furta “salute”, hada ido Prince da
adil sukai, cikin zuciyar sa prince yake furta “shikenan little ka kashe ni da
raina, yanxu idan me kirar samu dawan nan ya dawo kan mu ai mummutu, “su captain
suna fita Prince be karasa maganar zucin saba Bobo ya maida kallansa akansu, gabaki
d’aya sunkuyar da kai kasa sukai, kan one sitter ya zauna kafun yayi crossing legs
dinsa yana duba a gogo “ zagaye dari!!! Starts “ kamar zasuyi kuka suka fara zagaye
falon gashi ba damar su bashi hakuri ya kara nunka musu wani wahalar, a zagaye na
20 suka fara layi kamar zasu fadi, a hankali suka fara tafiya yanxu, mikewa bobo
yayi daga kan kujeran tuni suka manta da gajiyar tasu suka ci gaba da zagaye falon,
da sunyi kokarin tsayawa zasu ga bobo na binsu da kallo, a 80 adil ya fadi kasa
tare da fashewa da kuka “ yaya bobo please kayi hakuri, kamanta little dinka ne ni
kuma yau graduation dina fa, “ shima Prince zubewa yayi a kasa cikin pleading ya
furta “ yaya bobo we’re sorry “, babu Wanda ya kula acikinsu, “ zagaye hamshin!!!
Starts”, sakin baki Prince yayi “ wani lokaci har tunanin tsakanin big boss da yaya
bobo wanane yafi wani iya mugunta dan hukuncin big boss ya fi na kowa tsauri, ba
karamin aikin sa bane yasa a jefaka caged din zakinsa kuma babu Wanda ya isa ya
futar da kai sai ta Allah. Zasu mike wani mutumi ya shiga black American da shi,
jikinsa sanye da kananan kaya shima, little na ganinsa ya kara fashewa da kuka “
Uncle iron man , please ka bawa yaya bobo hakuri kafata ciwo take mun”,kallan bobo
mutumin yayi yaga ya dauke kansa, murmushi ya saki kafun ya karasa inda little yake
“ kunyi lefi kenan, ku bashi hakuri idan ya ki hakura ku kira masa big boss sai ayi
ya’ki kowa ma ya huta”, yanda suka zaro idanuwane yaso bashi shi dariya , zasu kara
magana bobo ya nuna musu hanya dan hayaniyar su har ta cika masa kunne “ leave this
place now”, ai be karasa ba ko wannansu ya arta a guje, yanxu kam kasa rike
dariyarsa mutumin yayi saida ya dara kafun ya kalli bobo “ why are you punishing
yourself, kai da big boss kunfi kowa jin zafin punishment din da kuke sasu amma
hakan baya hana gobe insunyi lefi ku hukuntasu, ynxu da dan gwarzane sukai sai
kunfi kowa jin ciwo, in wani kuma yayi gigin koda mintsuninsune tsaf zaku harbe
mutum,please ku sassauta wannan zuciyar taku”.shafa keyarsa bobo yayi kafun ya
furta “ok uncle”, girgiza Kai uncle din yayi kafun ya nufi wata kofa , shima bobo
wajan elevator ya nufa da zea kaishi sama.
A bangaren Prince da little kuwa suna shiga dakin su kowa ya haye kan gadonsa yana
maida ajiyar zuciya Dan ba karamun horuwa sukai ba, babu Wanda ya kula junan
su ,musamman little da yake fushi, ko wannansu wanka yayi cikin kayan shan iska,
duk yanda Prince yayi da little su sakko kasa yaki, ya ma ki yi masa magana kwata
kwata sai ma Hayewa kan bed dinsa da yayi yana lullube kansa. Kusan tsawan 30
minutes yaji an bude door din, a tunaninsa Prince ne yace “ yaya Prince just leave
me alone”, shirun da yaji ne yasashi kara furta “ please yaya Prince ka tafi, yaya
bobo baya sona yanxu”yaye blanket din da akai ne yasashi waro ido ganin bobo tsaye
hannunsa dauke da babban tray, akaran farko da kyakkyawar fuskar little ta fito, a
shekaru bazai wuce shekara 21 ba dukda kyansa be gama fitowa ba kamar yan uwansa
amma shima kyakkyawa ne na karshen karshe, dauke blue eyes dinsa yayi daga kan bobo
zai koma ya kwanta “ stay still” cewar bobo, sunkuyar da kai little yayi kamar zeyi
kuka , ajje tray din bobo yayi kan wani table me zaman mutum 3,kafun ya karasa inda
little yake , a gefensa ya zauna shima kafun ya kama hannun little “ yaya bobo yayi
lefi, am sorry kar a fada wa big boss ya harbeni “, dariya ce ta kwace wa little
besan lokacin da ya rungume bobo ba, shima bobo rungumesa yayi kafun ya mikar dashi
tsaye, dakansa ya dunga feeding ADEEL abincin da ya kawo masa shima ADEEL din na
bashi abaki, saida suka kammala cin abincinsu kafin little ya kalli bobo” yaya bobo
, big boss ya dena sona har yanxu ya ki dawowa fa”, bobo be ce masa komai ba sai
wata karamar phone da ya dauko wasu number guda Hutu ya danna take a wajan aka
dauka, little dake binsa da kallo, tsawan mintuna biyar Ba’ace komai ba kuma babu
alamun za ayi magana ,”yaya” shiru yaji ba ayi magana ba “ Assalamu Alaikum “ ya
kara fada kusan mintuna biyu kafun wata ratsatstsiyar murya ta daki dodon kunnansu
“ Wa’alaykumussalm “, daga nan ba a kuma cewa komai ba “ Yaya” little ya fada kamar
me rada “ little I will called you back!” “ kafun yayi kokarin yin magana aka kashe
kiran gabaki d’aya ,” karbar wayar bobo yayi “ kaga yayan naka yana meeting and zai
kiraka , so don’t worry, and ya bani gift dinta , and if you guys need anything ku
duba dakina ko na big boss, but ba fa kyauta na baka ba , kana fara aiki zaka
biyani kudi na “ rungumeshi little yayi cikin yaran larabci ya furta “ Ina sanka
yaya bobo na ,” love you too “ yana gama maganar sa ya bar dakin.
Shima tittle wani choco ya dakko cikin sauri ya sakko downstairs, “yaya Prince “
yake kwallawa kira ,”Menene kake faman kirana ka gama fushi”, amaimakon ya amsa
masa sai kashe masa ido daya da yayi “ yaya Prince wajan simba zaka rakani , yau
kwata kwata banganshiba “,kallan tara saura kwata Prince ya bishi dashi “ dan iska
ne Ance maka da zanje wajan wancan zagin, Kai da ka ga zaka iya ai sai kai tayi “,
shima kallansa Adil yayi “ shikenan Allah sai na fada wa yaya bobo , shima big boss
sai na fada masa “ da Sauri Prince ya riko hannunsa “ Haba auta, wasa fa nake maka
zo muje wajan simba din”, fitowa sukai cikin babban mansion kafun su nufi wata
kofa, duk inda suka wuce sojoji suna sara musu, cikin wani babban cage suka shiga ,
Prince da ya shiga karshe sai be kulle kofar cage din ba, “Simba!!! Simba !!!” AdIL
yake kira,wani gurnanin zaki ne ya fara tashi me tsoratarwa, inda gurnanin yake
fitowa adil ya nufa ba ko tsoro tattare dashi,”Simba “ ya kara kiran sunansa , wani
katon zaki ne ya fito , yanda naga girmanshi nikaina sai da na razana, bakinsa ya
bude kafun yayi wani kuka amaimaikon su gudu sai nufar kusan tosa da sukai kai,
kansa Adil ya shafa “Simba yau duk ban gankaba “ Abun mamakin shima Zakin da aka
kira da simba, gashin kansa ya karkada masa kafun ya daga hannayensa ya dora ajikin
Adil, wani irin farinciki ne ya kama adil kamar Wanda ya samu mage haka yake wa
zakin wasa, Prince na gefe sai faman vidoe yake musu, ganin lokacin sallahr
magariba ya kusa ne yace wa Adil suzo su tafi kar yaya bobo ya ne mesu, ba musu
kuwa suka bar cage din.
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

ABUJA
ADEMOLA ADETOKUMBO STREET

Cikin wani babban gida dake cikin ademola , maza da mata ne ke faman shige da fice
gabaki d’aya wajan fitula ya haska , ko ina ka duba zaka ga mace da namiji rabe da
junansu, daga gefen gidan da akai wa lakabi da UWAR BARIKI, wasu kyawawan yan
matane guda 4 da a kalla shekaru baza su wuce shekara 15 ba, ko wannan su ka kalli
fuskarta zaka ga tashin hankali tattare da ita , d’aya daga cikin yan matan da tafi
kowa shiga tashin hankaline ta rushe da wani saban kuka ,” shikenan na shiga uku,
yanxu me zancewa UWAR BARIKI, na tabbata in bankai mata kudin yau ba kashe ni
zatayi “ kallanta d’aya daga cikin yan matan da ita ma zaka ga tashin hankali
tsantsa a fuskarta tayi kafun ta furta “ ki dena kuka ARWA nasan ABLA in tazo zata
neman mana mafita “, girgiza Mata kai wacce aka kira da arwa tayi “ kinsan yanda
uwar BARIKI ta tsani Abla fiya da kowa musamman yanda taki yarda tayi kudi da ita
shiyasa tafi kowa shan wahala a cikin mu, yanxu idan Abla taji bansan me ze faru
ba, kawai ina tunanin zan bawa wani kaina ne kamar yanda uwar BARIKI take bukata,
ko hakan zaisa mu fita daga kangin rayuwar nan” saukar mari taji a fuskarta da yasa
tadiye sauran maganarta, gabaki d’ayansu maida hankalinsu kan wanda tayi marin
sukai, Wata kyakkyawar matashiyar budurwace tsaye a gabansu, gabaki d’aya wahala ta
bayyana a jikinta ga wasu matattun kaya a jikinta daya fi na sauran munana sabida
yanda suka mutu , gabaki d’aya hada baki yan matan sukai wajan furta “ABLA”.

IBTISSAM
(Heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee

BOOK 1
( The beginning)

Season 2

ABLA !!!!! Wacce aka kira da Ablance ta kallesu cikin muryarta da bata fitowa sosai
ta soma magana “ Saunawa zan fada muku duk wahalar da zamusha kada mu taba yadda
muzubar da mutuncin mu, ya kamata mu yarda da kaddara, kome zasuyi mana mudunga kai
wa Allah kukan mu su basu ita su cutar da mu ba , kar na kumajin wata magana irin
hakan”, wacce aka marace ta kara sakin kuka “ Abla basu da kirki mugayene, idan
bamuyi musu abunda sukeso ba zasu cutar da mu, “ ya’ken da yafi kuka ciwo Abla ta
saki “ karki damu Allah na tare damu, nawane kudin naki da ya fadi “, share
hawayenta arwa tayi kafun ta furta “ 170 ne “, kwance gefen dankwalinta Abla tayi
taciro wasu matattun kudi, dari da saba’in din ta irga kafun ta bawa Arwa,girgiza
mata kai Arwa tayi “ Abla kinsan matarnan ba mutunci ne garetava in na karbi kudin
nan zata gana miki azabane “ bata kai karshen zancen taba daya daga cikin yan mata
ta miko mata kudin da ta kudun dune “ Abla ni ki karbi nawa , ni se ayi mun
hukunci”, kafun abla tayi magana ta gefen wacce ta miko kudin itama ta miko mata
nata “ abla ki karbi nawa , ni se ayi mun hukunci ba sai anyiwa Anee ba “ girgiza
musu kai Abla tayi “ karku damu bazan karbi kudin kowa ba , yanxu kunga dare yana
karayi in bamuje kun kai mata kudin nan ba zata sa aduke kune , kuzo muje “
rungumeta sukai gabaki d’aya su ukun banda ta karshensu da sai faman harararsu take
a fakaice , Sarai abla ta ganta shareta kawai tayi , Arwa ce ta kalleta “ husna ki
taho mutafi mana “ girgiza mata kai husnan tayi a dan yake ta furta “ ku tafi zan
taho daga baya “, bata jira cewarsu ba ta bar wajan, guntun tsaki Anee taja “ ni fa
shiyasa kwata kwata bana shiga harkar husna , sai kace yar uban shugabankasa mutum
sai fadin rai”, ta ukunsu ce me suna Ilham ta tabe baki “ matsalarta, ni bazan sawa
kaina damuwar ta ba Wallahi”, shiru abla tayi musu dan itama ta fara gajiya da
halin husna , a darare suka fara wuce mutanan wajan , Daidai bakin window suka
tsaya ,gabaki dayansu tsoran shiga suke, basuyi auneba sukaji an shako rigar abla ,
da sauri suka juyo, gabaki dayansu razana sukai da ganin UWAR KARUWAI ga wasu mata
guda uku a bayanta , “ tsinannun yara uban me kuka tsaya yi anan, wato kun tsaya
muna furcin da kuka saba ko ,zinariyya ku dakko mun su” tana kammala maganarta taja
abla kamar wata kayan wanki ga wuyanta da ta shake da kyar take iya shakar
nunfashi, Wanda aka kira da zinariyya itama kan Anee ta janyo kafin ta tsinka mata
mari tare da janta a kasa kamar kayan wanki, ragowar mata biyun da akallo daya zaka
musu kaga manyan karuwai suma haka suka janyo Arwa da ilham, duk inda suka gifta
sai dai a kallesu a dunga shewa. Can cikin wani daki da ya cika da tarkacan kwalaye
Uwar karuwai ta jefa Abla take a wajan kanta ya bugu da Gini, bata gama shiga a
zabar buguwar da tayi ba taji saukar mari dama da haku a kumatunta ,” shegiyar
yarinya gwanda inkashe ki in huta babu abunda kuke tsinananun “, Daidai lokacin da
ake shigo da su Anee suma, kallansu uwar karuwai tayi gabaki d’aya mummunar
fuskarta a hade ta ke binsu da wani mugun kallo, katan hannunta da yaci uban Jan
farce ta miko musu ba tare da ta furta komai ba , da Sauri gabaki dayansu suka saka
mata kudadan hannunsu banda abla dake nishin azaba , “ ku d’auke su anan “ cewar
uwar karuwai, ba musu kuwa suka d’auke su gabaki dayansu kukan da sukai ya bata
musu fuska . Kallan ta uwar karuwai tayi ,”ina kudin ki” cikin dishashewar murya
abla ta furta “ sun fadi”, bata Kai karshen zancan taba uwar karuwai ta hanbare
mata baki take a Wajan bakinta ya fashe “Bansan asara ba , sannan bana daukar asara
,duk acikin yaran da nake hulda dasu kece tsagerarsu, in baki sani ba na tuna
miki , ke din ba kowa bace face baiwa da ko dabba ta fiki gata , rayuwarki tana
hannuna sai yanda nayi dake tukunna, dan haka ko kina so ko ba kyaso dole kiyi
karuwanci ki kawo mun kudi” tana gama zancanta ta kwallawa zinariya kira “ ki kai
ta dakin shirgincan, ki tabbata bata samu abunda zata kwanta ko lulluba akai
ba ,abude winduna yanda sauraye zasu shiga ciki, banaso kuma naga kaske na yawa a
ciki “.wani shu’umun murmushi zinariya ta saki kafin ta ja abla data gama galabaita
zuwa wani dakin shirgi da ko mara gata sai haka , gabaki d’aya dakin dattine a
cikinsa ga uban shirgin kaya a ciki sai faman wari yake , kamar yanda uwar karuwai
ta umar ta haka zinariya tayi kafun ta kalli abla cikin lashe baki “ ki bani kanki
kawai na dan dana zumarki, zansa uwar karuwai tayi miki sassauci “ ta karasa
zancanta zata taba abla , cikin wani irin zabura abla ta hankade hannunta , gabaki
d’aya ta gama galabaita “ karki sake kazamin hannunki ya kuskura ya taba fatar
jikina, Ta Allah ba taku ba kuma mugaye azzalumai, kamar yanda kuke kokarin cutar
damu insha Allahu munfi karfinku “, shake mata wuya zinariya tayi “ kar kiga ina
binki ta lallami, ko kina so ko bakyaso sai kinzama mallakina, sai na dunga jin
dadinki “tanakai karshen maganarta tasaki wuyan abla , sai alokacin wani irin tsoro
da firgici ya kama abla ganin zinariya na kokarin barin dakin, bata gama shiga
cikin firgicin ba zinariya ta kashe fitilar wajan tare da kullo ‘kofa. Cikin fita
hayyaci abla ta soma magana “ A’a , A’a , ku budeni, banaso Wayyo ku budeni, duhu
banasan duhu , duhu zasu kamani bana so , ku bude mun kofa , ku bude mun kofa “ a
haukace ta soma dukan inda take tana kiran su bude ta , kara ta soma saki kafun ta
fara dukan kanta kamar wata tababbiya, “ Dan Allah ku bud’eni bana san duhu” yadda
nunfas yake sama da kasa kamar xai fita daga cikin jikinta, gabaki d’aya jikinta
rawa yake take a wajan ta fara shakuwa kafun nunfashinta ya dauke gabaki d’aya a
wajan.

✨✨✨✨✨

NEW YORK

FIFTH AVENUE

8:15pm Little ne zaune kan daya daga cikin ran tsatstsun designer cushions din
falon , hannun sa dauke da system dinsa dayake game, Prince na gefensa dauke da
waya shima , fitowar wannan black American dattijon da Akalla zaiyi shekara 50 a
duniya ne yasa Little ajje system dinsa “ uncle Iron man ,” murmushi mutumin
yasakar masa “ Na’am uncle little “, ba little ba hatta Prince dariyar kalmar uncle
Little din daya fada suka saki , ganin lokaci na tafiya ne yasashi kallansu “
lokacin dinner yayi , let’s go and eat “, kashe system din sa little yayi kafun ya
mike tsaye, “bari na kira yaya BOBO”, gyada masa kai sukai kafin su nufi wani
rantsats tsan dinning , da in aka bar mutum bazai taba gajiya da kallan sa ba, iya
haduwa dinning din ya hadu , ga wasu set din dinning daya ‘kara fito da haduwar
wajan, kan d’aya daga cikin kujerun da mutane goma zasu zauna suka zauna batare da
sunyi magana ba. A sama kuwa direct wani irin corridor Little ya nufa, yanda tsarin
corrider din yake shikadai ya isa kallo, wani door me dan tsaho ya nufa kafun ya
tura kofar babban door din, kayataccen falo ne me shegen girma duk da bai kai
girman falon kasa ba , iya tsaruwa da haduwa falon yayi , wani kamshi turare ne ke
tashi a cikin dakin ga sanyin falon da ya cika ko ina, ganin babu kowa a cikin
falon ne yasa shi nufar d’aya daga cikin doors din kofar.Astagfirullah ya Allah ,
babban daki ne me shegen kyau a wajan, komai na cikin dakin brown colour ne , ga
wani dan ubansun king sized bed me shegen girma da daukan ido, iya haduwa da
tsaruwa dakin yayi kamar ba ‘a anfani dashi, shiga cikin d’akin little yayi bakinsa
dauke da sallama, babu kowa a d’akin har ya juya zai fita wata ran tsartsiyar waya
ta fara haske alamun kira ya shigo ciki, ganin yaya bobo baya d’akin yasa shima ya
share zai fita ,sai kuma ya ‘kara dawowa cikin sauri zai dauki wayar aka turo wata
kofa dake cikin dakin. Fuska a hade BOBO ya kalleshi babu alamun fara’a akan
fuskarsa, “ what are you doing here “, rawa bakin little ya fara , kamar me
‘kin’kina ya furta “ Na dauka Yaya ne”, sakin fuskarshi bobo yayi kafun ya karaso
inda yake “ you’re very stubborn little, gwanda yayan naka ya dawo ko kashiga
taitayinka “, zaro masa ido little yayi zai marairai ce masa bobo ya harareshi,”my
phone”, da Sauri Adil ya mika masa wayar, wata number bobo ya danna, kusan ringing
biyu ba a dauka kiran ba, ana ukunne yaga kiran number ,da sallama abakinsa bobo
yayi magana , shiru kusan tsawan mintuna biyu banji me akace masa sai kallan Adil
da yayi “ your stubborn brother ya dameni, talk to him”, yana kammala zancan sa
bobo ya mika masa wayar da sauri Adeel ya kar’bi wayar har wani dariya dariya na
kwace masa “ Yaya big boss “, ya fada kamar me rada banji me aka ce masa ba sai
kallan bobo da yayi kafun a shagwabe ya furta “ sorry yaya Assalamu alaikum,” kusan
mintuna daya kafun ya furta “ Yaushe zaka dawo yaya nayi missing dinka , gidan ya
rage dadi fa” kallanshi bobo yayi alamun zaka sani , ga baki d’aya Adil ya manta
bobo na kusa dashi, gyada kan da Adil yayi ne yasa bobo gyara tsayuwar sa “ eh fa
yaya ,yau graduation dina amma kaga yaya bobo yayi punishing dina , Kai nake jira
ka dawo karamamun”, bai kara zancansa ba yaga bobo na dage masa gira ,”Innalillahi
wa’inna ilaihi raji’una, na mutu na lalace yaya bobo daman kana nan”, kit aka kashe
kiran daga can ‘barin, gyara tsayuwarsa bobo yayi “ ina punishing dinka ko, come
over here , zo nan”, zaro masa ido Adil yayi “ Haba yaya bobo na kasan ina sanka ,
I’m sorry kaji “, not accepted cewar bobo, ja da baya little ya fara yana kokarin
guduwa, hannu bobo yasa zai janyosa yayi saurin zillewa , cikin dariya ya furta “
nifa bazan bari ka kamani ba yaya bobo, nace fa ina sanka me and you one heart ne “
harararsa bobo yayi ,” come over here “, nace fa sorry yaya bobo, kace idan mutum
yayi lefi kuma ya bada hakuri anaso mutum ya dunga yafiya”, murmushi bobo ya saki
da yayi wa kyakkyawar fuskarsa kyau “ ni zakayiwa siyasa “, girgixa masa kai little
yayi “ yaya nifa yunwa nake ji , kuma kai kadai nazo na kira kaji yayana , I love
you “, gyada masa kai bobo yayi “ok let’s go”, da Sauri kuwa little ya karasa wajan
bobon, be auneba yaji bobo ya kama kunnansa, saurin dafe kunnan little yayi , cikin
dan kara ya furta “zafi yaya kunnena “ da sauri bobo ya saki kunnan nasa “ inane
yake maka zafi”, kunnan little ya nuna masa ,”it’s ok zea dena” kama hannunsa
little yayi “ yaya bobo,kayi mun alkawari fa ranar graduation dina zaka goyani “,
kallansa bobo yayi “ as big as you are zan goyaka , so kake ka karyani”, shiru
little yayi masa har ya kama tafiya bobo ya riko hannunsa “ hau mu tafi , kafin ka
hana mu bacci “, da sauri kuwa little ya d’ane bayan bobo, har suka sakko falourn
kasa Adil na bayan bobo kamar wani karamun yaro, murmushi uncle iron man ya saki,
shi kuma prince girgiza kansa kawai yayi , “ sorry uncle iron man, sorry yaya
Prince dina “, hararar sa Prince yayi , tun dazu yake jin yunwa da yake Adil dan
iskan yarone ya barsa yana faman shiri rita, waje bobo da little suka samu kafin
Prince ya danna wani button, cikin seconds din da bazea wuce d’aya ba wani soja ya
shigo cikin falon, sara musu yayi kafun ya fara tanbayarsu abinda za a yi serving
Dinsu, kowa fadar ra’ayinshi ya ke banda bobo da little ya zabar masa , yazo zea
tafi Adil ya sakar masa murmushi “Thank you uncle James “, shima Wanda aka kira da
james din murmushi ya sakar wa Adil kafun ya kara sara musu ya bar wajan.
Tunda suka soma cin abinci babu Wanda yace da wani kala har saida suka kammala cin
abincin su, basu kara 50 minutes a falon ba kowa ya nufi bedroom dinsa. Karfe 2 da
rabi Bobo ya fito daga part dinshi , direct dakin su Adil ya nufa ganin ko wannansu
yayi bacci, gyara musu kwanciya yayi kamar wasu yara kafun ya kara yi musu addua ya
totto fa musu, iya dum light ya bari a dakin kafun ya fito, haske kad’an ne a falon
amma duk da haka sosai falourn ya kara kayatuwa,sai da ya zagaya ko ina na falourn
kafun ya fito waje , awajan ma fitulu ne masu haske kamar rana da suka kara haska
kyan gidan, sojojine birjik a tsakar gidan tare da wasu manya manyan karan sojoji
da suke shawagi a wajan, duk inda ya gifta sai an sara masa, saida ya tabbatar da
lapiyar kowa kafun ya koma part dinshi.

WASHE GARI

Washe gari ana kiran sallah asuba wata iriyar jiniya ta karade ko ina nagidan ,
gabaki d’aya kowana mahaluki na gidan ya tashi banda Prince da Adil da suke
baccinsu,
Akaro na biyu Jiniyar ta karayin ‘karar da bata kai ta farko ba, pillow Prince ya
dauka ya toshe kun nuwansa dashi tare da kara janyo blanket yana rufe har fuskarsa,
Adil ma baccinsa yake hankali kwance, A hankali aka tura kofar d’akin, bakowa bane
face bobo dake tsaye abakin kofa, hasken d’akin ya kunna kafun ya karasa inda Adil
yake “ Adil!!! Get up lokacin sallah yayi”, ko motsi Adil beyiba, shafa gashin
kansa bobo yayi “ get up now ,ok”, dan motsi Adil yayi kafun ya soma karanto adduar
Tashi daga bacci a hankali, karasawa wajan Prince Bobo yayi , shima kiran sunansa
yayi, amma ko gezau beyi ba, kara kiran sunan shi yayi akaro na biyu sai wani
pillow da ya dauko zai toshe kunnensa, 2 fingers dinsa bobo kawai yasa ya dakawa
Prince duka a gefen hannunsa, azabure Prince ya furta “ su wanene suke shirin yin
yaki”, be karasa zancan saba yaga bobo tsaye a kansa, ga Adil dake faman kumshe
dariyarsa. “Just 5 minutes na baku, if you like ku koma and see”, yana kammala
zancansa ya bar dakin, bashiri kuwa sukai brush da Alwala ko wanka basu tsaya yi ba
, a ‘kasa suka tarar da bobo da uncle iron man , gabaki d’aya masallacin dake cikin
gidan suka nufa, sojojine suma cike a wajan suna jiransu, musulman ciki suka shiga
masallaci, ragowar kuma suka fara motsa jiki. Ana idar da sallah kowa ya koma
masaukinsa, su Prince ma basu tsaya a falour ba suka nufi d’akunansu , Prince ya zo
zai kwanta Adil ya tsayar dashi,”yaya Prince kasan yaya bobo yana jiran muko ,
wallahi ka koma bacci babu ruwana kasan babu abunda zai hana a nunka maka wani
motsa jikin”, yana kammala maganarsa ya shigo toilet, tsaki Prince ya ja kamar yayi
kuka , Adil na fitowa shima ya shiga wankan, shaf shaf suka shirya cikin kayan
motsa jiki, a tsaye suka tarar da bobo shima da nasa kayan motsa jikin , sa’banin
nasu shi kayan motsa jikin sojojine a jikinsa, sakkowa sukayi inda yake kafun su
sara masa” Salute”, shima hannunsa daya ya d’aga batare da ya sara musu ba ya furta
“salute, kun ‘kara 2 minutes Menene hukuncinku “, gabaki dayansu sakin baki sukayi
suna kallansa “ Yaya” eyes dinsa ya zuba musu , gabaki d’aya saurin sunkuyar da kai
sukai kamar abun tausayi,girgiza kai kawai yayi “ let’s go” wata iriyar ajiyar
zuciya suka sauke gabaki dayan su, cikin d’an gudu gudu suka fara tafiya , suna
fitowa harabar gabaki d’aya sojojin suka sara wa Bobo kafun su hada baki wajan
furta “Salute” hannu ya daga musu, kafun su Prince su fara motsa jiki , sai da
sukayi 2 hours suna motsa jiki kafun su koma part Dinsu.
9:30am James ya serving Dinsu breakfast , Tunda suka fara Breakfast gabaki d’aya
babu Wanda yayi magana saida suka kammala.

07041879581
MSS LEE

https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
IBTISSAM
( Heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee 💖

BOOK 1
( The Beginning)

Season _3

3:00am nayi ko munti d’aya be gotaba aka bude kofar shirgin da aka kulle Abla,
Zinariyya ce tashigo sai tangad’i take Ganin yanda Abla bata motsine yasa Zinariyya
sanar da Uwar karuwai, umarni ta bada Akawo mata ruwa masu sanyi a fridge guda
biyar, hakan kuwa akayi cikin d’an karamun roba Zanariyya ta juye ruwan masu
bala’in sanyi. Dakin shirgin suka nufa ita da Zinariyya sai wata da ake cewa Yar
shila , a yadda zinariyya ta barta a haka sukazo suka sameta, kar’ban ruwan uwar
karuwai tayi cikin rashin imani ta juyewa Abla shi a jikinta.A gigice Abla ta farka
tana Ambatan sunan Allah , gabaki d’aya jikinta rawa ya d’auka sabida wani irin
sanyi dayake ratsa jikinta, kallanta uwar karuwai tayi a wulakance “ ku tashi ku
fara aikin da kuka saba dan ba Hutu ne ya dace da kuba, matsiyata kawai”, tana kai
karshen zancenta ta kalli ‘Yar shila “ jeki taso mun ragowar tsinannun yaran,
lokaci kankani na baku su kammala ayyukansu, idan ba haka ba ku zanesu suji a
jikinsu “ tana kai karshen zancanta tayi waje , a duniya idan akwai wacce ‘yar
shila ta tsana be wuce Abla ba , shiyasa uwar karuwai na fitowa taja ta kamar kayan
wanki , Daidai lokacin da Zinariyya ta fito dasu Anee suma ko wannansu a jike sai
rawar sanyi suke . Cikin kuka arwa ta karaso Inda Abla take ,”Abla sanyi nake ji ,
ga yunwa ina ji, ga bacci da be isar mu, jikina duk ciwo yake mun ga wasu cunnaku
dasuka cijeni “, kwallarta Abla tayi saurin gogewa “ wata rana sai labari, kafun su
dawo ku tashi muyi aikin mu ko zamu samu in lokacin sallah yayi muyi kafun musamu
na abincin, kunsan idan bamu kammala ba, bazasu ta’ba bari muyi sallah ba” gyada
mata kai sukayi gabaki d’ayansu,Babban falon da ya baci da kwalaben barasa da
abubuwan sigari suka fara gyarawa , gabaki d’aya falon wari yake amma duk da haka
sai da suka gyara shi tsaf sai faman haki suke sabida galabaitar da sukayi, d’akuna
Biyar da suke jere a kasa ko wannansu ya nufi d’aya da niyar gyarawa, d’akin da
Abla ta shiga wani irin amaine ya taso mata sabida kazantar da ta dunga cin karo
dashi a dakin, gabaki d’aya d’akin a har gitse yake , da kyar ta Samu ta gyara
d’akin kafun ta nufi toilet. Tana shiga aman da take rike wa ne ya kwace mata
Sabida karo da ta dungaci dasu condom gawani uban Kazan tar dake cikin nan dakin,
da kyar ta samu ta wanke ban dakin, tana fitowa sai da ta jira su Husna suka fito
Suma , ko wannan su a waji gace sai faman toshe hanci suke, sama suka nufa shima
saida suka gyara falon tass da ya fi na kasa baci kafin su gyara rooms din cikin
falon, lokacin da suka gama wani irin juwace ta soma kamasu ga kiran sallah da ake
faman yi amma badamar suje suyi.Inda kwanukan wanke wanke suke suka nufa, sosai an
‘bata kwanuka haka suka zauna suka fara wankewa, sai wajan 8:30 na safe suka
kammala wanke wanken, Dole su gyara kitchen din gidan ga tsakar wajan da zasu gyara
shima , ga lokacin sallah na tafiya, murya a dusha she da ‘kyar take magana ta
furta “ Lokacin sallah na tafiya , ya kamata muyi sallah “ a tsorace suka kalleta
gabaki d’aya “ Abla kinsan hukuncin da zasuyi mana idan suka san munyi sallah ko”,
manyan idanuwanta Abla ta saka musu,” kuna nufin mu zauna karmuyi sallah sabida
hukunci “, da Sauri duk suka d’aga mata kai kamun ilham tafurta “ sai muyi sallar
daga baya danni tsoron muguntar su zinariya nake “, same Arwa ma abunda ilham ta
fada shi ta maimaita, Anee ce ta kalleta “ Abla Nima zanyi sallah , Taho muje “,
kallan Husna Abla tayi ko zataje amma ko kallan inda Ablan take batayi ba, a
d’arare Suka samu suka fita daga cikin gidan, saida sukai tafiya me Nisan gaske
kafun su samu wani masallaci da suka ga butocin ciki da ruwa, Alwala suka samu
sukayi kafun Suje bayan masallacin su tayar da sallar su, suna idarwa tsoran
hukuncin da za ayi musu ya kamasu. Cikin fargaba suka nufa Gidan, tsallan kwado
suka tarar ansaka ilham da arwa , fuskarsu gabaki d’aya ta baci da hawaye, yar
shila tana ganin su Abla ta rufe su da duka da wata jungegiyar doruna,kafin suma
akasu tsallan kwad’an, tun sunayi da karfin jikinsu har suka somayi a hankali kafun
su fadi a kan tiles din suna nun farfashi, yar shila ta daga hannu zata kara zuba
musu wani bulalan uwar karuwai ta fito cikin wankanta da kallo d’aya zaka mata
kasan cikakkiyar karuwa ce, “ ya isa haka yar shila so kike ki kashe mun kasuwa
ne , ga kosai can ko wanne ki basa guda bakwai kafun ku basu wankin da aka had’a
kunsan yau akwai casu, ko bara banaso suje yau sabida akwai aiki”tana kammala
zancanta tasa kai ta bar gidan, kosan yar shila ta dakko amaimakon ta basu kamar
yanda aka umarceta sai ta bawa ko wannansu biyar biyar, tana zuwa kan Abla ta Wulla
mata guda uku ba kamar sauran ba, Husna ce kawai babu a cikin falon, ayun wace suka
fara cin kosan da ko rabin cikinsu be zoba , banda abla da take bun kosan da kallo,
tayi wa kanta alkawari bazata kara cin abinda ya fito ta kazamun hanya ba , shiyasa
ta rabawa su arwa kowa daddai, harda murnarsu suka amsa kuwa kafun a tulo musu uban
wanki me shegen yawa, basu suka kammala ba sai wajan 2:30, anan ma satar hanya
ilham da Abla sukai sukaje sukai sallah suka dawo , a wannan karan Allah ya
temakesu ba aga dawowarsu ba, har lokacin su Arwa kuwa basuyi ko sallahr asuba ba
duk yadda Abla take musu magana har ta gaji . Wata iriyar masifaffiyar yunwa suke
ji , Ga uwar karuwai ta hana su zuwa baran da suke nemo abinci, La’asar nayi Abla
takara guduwa wannan karan itama ilham bata bita ba. Tana idar da sallah ta ta’be
jikin masallaci ko zata Samu sadaka amma har tagama bulayinta bata samu ko biyar ba
, shiyasa ta nufi hanyar komawa gida abunta, tana shiga ta tarar da abunda ya tada
mata hankali, da sauri ta karasa Wajan su tana tanbayarsu ina zasuje da wannan
shigar, Anee na kuka ta soma magana “ Abla nagaji, bazan iya rayuwar yunwar nan ba,
idan na kara awa d’aya banci abinci ba mutuwa zanyi , shiyasa na yadda da bukatar
su Zinariyya, Sunce ba sex zasuyi damu ba, wasa ne kawai zasuyi, kuma zasu dunga
biyan mu”, A firgice Abla ta saka salati “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,me
kuke kokarin yiwa rayuwar ku,bakusan hakan wata Babbar illace ba arayuwar ku, me
zakucewa mahaliccin ku”, a kufule Husna ta kalleta“ Ya isheki haka IBTISSAM, ke
komai kinfi kowa sani, ko ca’akai miki mu bamu da addinin ne, kullum mutum zai yi
abu sai kin kawo naki, idan muka zauna da yunwa zaki bamu abincin da zamu dunga
cine,ko zamu zauna kina hanamu abu yunwa ta kashe mu, na dad’e da fahimtar dama ba
san cigaban mu kike ba , in baki sani ba ki sani yau bazan kara zama yunwa ta kashe
niba , Nima dole na samu kudi, ga hanyar samun kud’i cikin sau’ki , idan ke bakya
san rayuwar ki to mu muna so “ tana gama maganar ta taja dogon tsaki tayi
wucewarta, Arwa da Anee ma bin bayanta sukai, ilham ce kadai ta Matso kusa da Abla
“ kuncin rayuwar nan ta ishe mu Abla , Bamu da gatan da ya wuce mu samowa kan mu
‘yancin kai, bazan iya rayuwa cikin yunwa ba, duk da bamu dad’e da sanin juna sosai
ba amma tabbas ke din Ablan muce me Kaunar mu, kin nuna mana soyayya irin yanda
yaya take nuna wa kannanta” itama tana kai karshen zancen ta tabi bayansu Husna ,
zubewa Abla tayi a kasa tana faman nanata sunayen Allah, babu abunda bakin ta yake
furtawa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” wannan masifa har ina,batasan
lokacin da wani kukan ba’kin ciki ya kwace mata ba.

✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨

UNITED STATES

Zaune Adil yake cikin shigar kayan ball a ‘kayataccen filin ball da yake cikin
gidan , ball d’in hannunsa yake ta faman bugawa shikadai, yana cikin bugawa Prince
ya karaso inda yake cikin shigar kananan kaya masu shegen tsada, “yaya Prince
“cewar Adil, shima Prince gira d’aya ya d’aga wa Adil yana zama gefen sa , cikin
rad’a rad’a ya furta “Little Yaushe zamu je siyayyar da mukace zamuje kafun after
your graduation “, kallansa little yayi kamar me tunani kafun ya furta “ kasan ko
mun tanbayi Big Boss zai ce mu lissafo ko me mike so, amma bazai barmu mufita ba “,
gyada masa kai Prince yayi , kafun little ya cigaba “ yaya bobo ma bazai barmu ba ,
Indai ba wani muhummanci ne da abun ba , shima sai an had’a ka da sojoji sai kace
wani ‘barawo”,lallausan gashin kansa Prince ya taba “ Little let’s go to uncle iron
man, kasan yaya bobo yanajin maganarsa sosai,kawai yawon 2 hours zamuyi mu dawo”.
Mikewa sukai gabaki d’ayansu ba yan Adil ya ajje ball din hannunsa , cikin
kayataccen babban falourn su suka nufa kafun su karya kwana Zuwa wata kofa, suna
shiga nan ma wani kayataccen falo ne babba a wajan da taya tara kayan more rayuwa a
cikinsa , falon ba karamun kyau yayi ba , cikin d’aya daga cikin kujerun falon suka
tarar dashi yana karatun jarida , “Assalamu Alaikum “, suka hada baki wajan fada,
d’an Dago da fuskarsa yayi kadan kafun ya amsa musu salamar tasu “ oh my boys sai
yanxu ake ganin ku ko “, sosa ke ya suka fara yi kamar marasa gaskiya kafun Adil
yayi saurin zama kusa dashi “ my iron man , you know I don’t have any one like you
ko “, sakin baki Prince yayi a zuciyarsa kuwa yana auna irin ma yau darin yaro da
za’a yi meshegen wayo , murmushi iron man ya saki “ daga baya kenan , yanxu kana
ganin big boss zaka nuna baka sanni ba”, dan karamun mursushi Adil ya saki “No
uncle , you know kaima ina sanka , I don’t have any one like you guys “, girgiza
masa kai uncle kawai yayi kafun ya kallesa shida Prince “ tunda naganku ku biyu
akwai abunda kuke bukata, just ku fadamun ,if not ku tashi ku bani waje “, suna jin
haka suka kalli junansu , kafun ko wannan su ya gyara zama , Prince ne ya soma
magana “ uncle please munaso mu d’an fita yin siyayyane , and kasan yaya bobo bazai
bari muje ba sai dai yace mu lissafo abinda mukeso “, sai da ya gama sauraransa
tsaf bece musu komai ba , ya dakko wata telephone room, number 7 Kawai ya danna,
kusan mintuna 2 , “ ina falona , am waiting for you “, yana fadar Hakan ya kashe
kiran , ba Prince ba hatta Adil dake zaune kan kujera sai da ya sakko kasa kamar
zaiyi kuka ya kalli uncle iron man “ yanxu uncle cin amanar mu zakayi , ai se kace
mana baza muje ba , ni wallahi ban shirya yin tsallan kwado ba , “be karasa
kalamansa ba yaji saukar muryar bobo “ you are very stupid”, a mugun tsorace Prince
da Adil suka mike tsaye , kallan bobo da ke sanye cikin half wando da ya kai masa
har gwiba black colour da wata white T-shirt da ya fito da murdaddun muscle dinsa
waje , fuska a had’e ba fara’a ya karaso cikin falon,ko kallan inda suke be ‘karayi
ba , sai sassauta face din shi da yayi kafun ya furta “ uncle gani”, shima uncle
din nuna masa su Adil yayi da ko wannansu ya dukar dakansa kasa ,” they want to go
out“ batare da bobo ya kallesu ba ya furta “ su lissafa abunda suke so, captain zai
karbo musu” yana fadar hakan ya juya ya bar falon, hawaye ne suka fara sakkowa Adil
, gabaki d’aya yaji besan zuwa shopping d’in , tsoran shi d’aya ma kar yaya bobo
yayi fushi da su, kallansu uncle iron man yayi “ why the pity face kuma, kuje kuyi
masa magana , zai barku “, cikin dan marairaice Prince ya furta “ uncle yanxu muna
zuwa Wajan sa idan Bamuyi wasa ba sai mun fito da kunburarrun fuska”kallan baku
daddara ba Uncle ya bi Prince dashi , wato ya mayar da bobo boxer kenan , “uhm “
kawai yace tare da mayar da hankalinsa kan jaridarsa. Jan hannun Prince , Adil yayi
har suka fito falo babu kowa a ciki sai sanyin Acn da yake busosu, direct inda zai
sadasu da bangaran bobo suka nufa , suna isa Daidai part din ko wannansu ya ja
burki kowa na kallan dan uwansa akan ya fara yin gama , cikin dan rad’a rad’a
Prince ya rad’a wa Adil abu a kunne, gyada masa kansa yayi kafun suyi knocking ,
kusan tsawan 2 minutes ba a amsa ba , kara knocking din kofar Adil yayi nan ma
shiru ba a amsa musu ba , kamar zai yi kuka Adil ya kallin Prince , shima Prince
din kallan Adil yayi cikin fuskar tausayi ,”come in “, sukaji muryar bobo , babu
Wanda bai saki a jiyar zuciya a cikin su ba , a hankali Adil ya tura kofar falon
bobo, ko wanne bakinsu dauke da sallama , a hankali ya amsa musu ba tare da ya
kallesu ba ,gabaki dayan su shan Jinin jikinsu sukai , tsugunnawa sukai kasa
kowannansu ya rike kunnuwansa “ we’re sorry yaya bobo “, cikin had’e rai yace “ get
out “, Adil kamar zaiyi kuka ya kara cewa “ we’re sorry please “, a zafafe bobo ya
daka musu tsawa “ I said get out “, ba Adil ba hatta Prince mikewa yayi da Sauri
suka nufi hanyar barin part d’in, cikin dan sakin murya bobo ya furta “ come back”,
cikin sanyin jiki ko wannan su ya koma inda yake a tsugunne, hannunsa bobo ya miko
musu , da Sauri ko wannansu ya rike hannun kafun a hankali su kara furta “ kayi
hakuri yaya bobo “, da ido ya kallesu kafun cikin dan sassauta murya ya soma magana
“ where are your manners , haka aka koya muku magana “, girgiza masa kai sukayi “
speak “ cewar bobo , “ sorry sir”, Prince be kai karshe ba yaji saukar rankwashi
akan sa , da sauri ya dafe wajan yana furta “ ouchhh yaya da zafi”, shima Adil yana
cikin kumshe dariyarsa yaji saukar nasa rankwashin, “ naga Alama harynxu baku
horuba “ ya nuna Prince “ you bari yayanka ya dawo horon LTG zansa yayi maka “ and
you , ya nuna Adil “ baruwana kai dashi”, sassaita muryarsa Adil yayi “ yaya bobo
kasan Little dinka yana sanka , please karka fadawa yaya big boss ,munyi alkawari
zamu zama Good Samaritan kaji best yayan mu “, sakin baki Prince yayi yana kallan
Adil , cikin zuciyarsa yake furta “ wai yarannan shi zasuyi wa bariki, Allah ya
dawo da big boss hmmm “, ganin yanda yake kashe masa ido ne shima Prince ya kara da
“ yes yaya bobon mu zamu zama Good Samaritan “ Sarai yasan halinsu sun fara saka
masa ciwan kai shiyasa ya furta ,” go and get ready captain zai kaiku” kafun ya
karasa yana jan kunnansu “ and if you guys misbehave, kunsan sauran “, kallan
Dagaske kake Adil ya bishi dashi, Prince kuwa da sauri yayi hugging dinsa gudur
karya ce ya fasa “ thank you yayan mu, we love you so much “, shima Adil rungume
bobon yayi “ thank you yaya “ kafun yace komai kamar wasu kananan yara suka bar
falan a guje , goshinsa bobo ya shafa , “ you guys are not matured har yanxu “.
Tsadaddiyar wayarsa kiran Samsung new design ce ta dauki ringing din BIG
BOSS ,kallan wayar bobo yayi da take langwashe gida hudu, Big Boss d’inne ya kara
fitowa cikin wayar, cikin sallama ya kara wayar a kunnansa, duk da na cikin wayar
baya ganinsa hakan be hanashi saramasa ba “ salute BIG BOSS”bansan me aka ce masa
ba kusan 2 minutes kafun ya saki yar karamar dariya , cikin sakin fuska ya furta “
yanxu ni kake cewa Small child , don’t worry duk lokacin da kaji Ance maka na zama
Daddyns son zaka san ni ba yaro bane “, be kai karshen maganar saba yaji kitt an
kashe wayar, murmushi bobo ya saki kafun a hankali ya furta “ my big boss “.

****Suna idar da sallar magreeb ko wannansu ya shirya cikin shigar kananan kaya,
tun daga kan sumar kansu han zuwa ta kalmin kafarsu abun kallo ne sai suka fito sak
larabawa musamman yadda gashin Kansu yake a murmurde gawani irin santsi da yake
d’auka,babbar wayarsa ADEEL ya dauka ‘kirar iPhone 14 pro max yana matsowa kusa da
Prince , “say ceeze “ atare suka kara kada baki wajan cewa “ ceeeze “ kafun Adeel
ya dauke su hoto, ba karamun kyau sukai cikin hotan ba, sai wani tsantsan kyau da
ya kara yiwa hoton nasu armashi ko wannansu musamman yanda kalolin idanuwansu suka
fito sosai , zai kara yi musu wani hoton Prince ya dakatar dashi “ kasan yanxu yaya
bobo zai iya canza shawara, ka ajje wannan hotan naka a gefe muna ‘bata lokaci”
okay kawai Adil ya ce masa kafun su fito,lokacin bobo baya gida shiyasa Wajan uncle
Dinsu kawai suka nufa sukai masa sallama , suna fito wa waje jerun motocin da zasu
fita dasu ba’ka’ke sai faman kyalli da daukar ido suke , gabaki d’aya sojojin sanye
suke cikin shigar suit ba’kake kowanansu a kwai bindiga a jikinsa, bakar bullet
proof Armored Toyota Land Cruiser dake cikin Jerin motocin captain ya bud’e musu
suka shiga kafun ya komawa driving seat , suma ragowar cikin motocin suka shiga
cikin wani irin salon driving motocin nan suka soma tafiya a Jere akan babban Titin
New York , tafiyar 22 minutes sukai ya kawosu Babban shopping mall din Brookfield
place ,’kayataccen shoppping mall me shegen kyau da tsada, tun daga wajan zaka gane
ba karamun waje bane ga wasu matakan tsaro da aka saka ta ko ina a cikin mall din,
ko ina ka waiga zaka ga wajan tsit ba hayaniya musamman yanda fitulun Garin ya
kara haska wajan kamar ba dare ba .suna shiga a Daidai parking space motocin sukai
parking, kallan Tarin sojojin da suka fito daga cikin mota yayi kafun ya kalli
captain “please captain mu kasu kashi hudu,” be kara zancan saba gabaki d’aya
sojojin Suka raba kansu gida hudu , ko wannansu ya soma tafiya aka bar captain
tare dasu,” Thank you “ Adil yace yana sakin masa murmushin sa da kullum baya
‘boyuwa , cikin wani side suka bi su uku da yafi ko ina shiru a cikin mall d’in,
wani doguwar Elevator suka hau kafun ya kai su floor 11th dake can saman building
din, idan mutum ya sunkuyar da kansa tsaf yana ina hango abunda ake a kasansa ,
koda suka sauka akan lifter d’in sai da suka hau kan wani luxury escalator me kamar
shape din circle . Wari irin had’addan wajene ya bayyana a wajan me shegen
kayatarwa , gabaki d’aya wajan shiru kake ji babu hayaniyar komai sai daddadan
kamshi da sanyin Ac da yake ratsa ko ina , babban wajan siyayya ne a wajan masu
shegen tsad’a, kallansa Prince yayi “ Let’s have a little fun first (bari mu d’an
ji dadi tukunna)”gyada masa kai Adil yayi , yanxu ma wani escalator din sukahau
amaimakon yayi sama dasu sai suka hau barin da yake saukar dasu kasa , wata kofa
suka nufe me girman gaske , anan ma wasu irin securities Suka gani tsatstsaye a
Wajan , hannu d’aya daga cikin security man din ya daga wa captain kafun gabaki
d’aya ragowar su sara masa , wani dan button security din ya danna take a wajan
kofar ta bude , babban wajan shakatawane na games me shegen girma , tundaga kan
geometry dash ,getting over it with Bennett foddy, ninja gaiden ,sekiro:shadow die
twice , da sauran games masu shegen dad’i cike a wajan mabanbanta, duk da yanda
wajan ya cika da kayan games na manya , gabaki d’aya wajan baka jin hayaniyar komai
sai d’an surutu kadan kadan da d’an ihu da yake fito wa , ba tare da damuwar komai
ba su Adil suka fara kutsa kansu cikin babban wajan games d’in , kallan Prince Adil
yayi , “ yaya Prince let’s play Devil daggers please “, gyada masa kai Prince
yayi , d’an tafiya kad’an sukai kafun suyi wata kwana yar kad’an , su na maso wajan
inda game d’in da zasuyi yake suna kara jiyo sautin murya na kara tashi. A Daidai
inda game d’in da zasuyi suka tarar da wasu maza guda hudu, ko wannansu da wani
irin shegen aski akansu da wasu manyan sar’ko’ki da suka rataya a jikinsu , daga
gefen su kuma wasu karatan mazane guda uku ko wannansu fuskarsa ba fara’a ,
tsakanin Prince da Adil babu Wanda ya kalli inda suke har Suka ‘karasa inda captain
yayi musu jagora har wajan da zasuyi playing games d’insu , d’aya daga cikin
samarin nanne ya d’ura wani zagi cikin English language , kafun a kakkaice ya soma
gama cikin yaran hausa da kallo idan ka kallesu bazaka taba cewa akwai mejin hausa
ba sabida shigarsu, na gefensa ne ya d’auki kwalbar barasa yana kallan guy d’in da
yayi magana “calm down Dizzy , kwantar da hankalinka , yanxu zamuyi maganin ‘yan
iska ko wanane su dan ubansu, basusan ko su wanenen BAD BOYS ba da zasu takamana
doka, ko basu san idan Bad boys suna zaune a waje ba a zama ba ”a zuciye na ukunsu
ya kalli d’aya daga cikin kartawan mazan nan yana nuna Adil “ je d’akko munshi
yanxun nan”, na cikin hudun sune yayi kokarin dakatar dasu” no please kunsan game
ne ya kawomu nan and nasan suma shine ya kawosu, let’s just enjoy and let them go,
ku rabu dasu”, wani Wawan tsaki d’aya daga cikin guys d’in me suna Oskar yayi “
matsalata dakai sometimes ka fiya yawa , just wait and watches, ka tsaya kayi kallo
kawai”, ya karasa da yiwa d’aya daga cikin yaransu da su d’akko masu Adil, cikin
cika umarni kuwa ya nufi inda suke, gabaki d’aya maganganun su akunnan Prince da
yake sakin dariya shikad’ai azuxiyarsa “ wai a dakko musu Adil, zaku ci ubanku kuwa
,”yana cikin zancan zucinsa yaji wannan mutumin da aka aiko yayi sama da Adil,
cikin fusata captain ya saka hannu zai dauko bindigarsa Prince ya damke masa hannu,
da mamaki captain ya kallesa “ ka bari muga me zasuyi masa tukunna , karmu d’auki
doka please “, captain zaiyi magana prince yayi saurin cewa it’s an order , mu
bisu”, suna karasa wajan suka tarar da Adil zaune kan kujera gashin kansa ya kara
kwantowa a kyakkyawar fuskarsa, gabaki d’ayansu binsu yayi da kallo d’aya bayan
d’aya kafun cikin sakin murmushi ya furta “ if you don’t have anything to say am
busy ( idan baku da wani abun fada, ni bani da lokaci”, Wanda aka kira da Oskar ne
ya mike a yayyake yana shirin yiwa Adil masifa shima Adil din ya kallesa har yanxu
da murmushi akan fuskarsa , “kana haukane? “, Little ,Prince ya kira sunansa tare
da karaso wa inda yake “ let’s go bamu da time “ cikin jin zafinsu Dizzy yayi
yunkurin taba rigar Prince, take a wajan Prince ya kwashesa da mari,” kanashan
kwayane, ni zaka rike , or are you insane ?”, gabaki d’aya Prince ya Jera masa
tanbayoyin , mutuwar tsaye su Oskar sukai suna bin Prince da yayi gangancin marin,
a zuciye dizzy ya daga hannu zai mari Prince yaji an lankwasa hannun ya bada
sautin’kass, cikin karar azaba Dizzy ya kalli Wanda yayi wasa wannan aikin , bakowa
bane face captain da yake tsaye kam fuskarsa ba fara’a , d’aya daga cikin samarin
ne mesu na EMESSI ne ya kalli yaransu “ ku karya munsu yanxun nan ku kawo mun su,
shima be karasa zan cansaba yaji saukar mari akan fuskar sa , da karfi ya furta
“Innalillahi “ Sabida yanda yaji saukar marin a kan fuskarsa, kara kallan Little
Prince yayi “ let’s go” mikewa Adil yayi a zuciya Oskar da aka mara ya tunkude Adil
yayi baya baya zai fadi, cikin wani zafin nawa Prince da captain suka tare sa
Daidai lokacin da sauran sojojin su suka karaso, a zuciye suka nufi inda su oskar
suke, basuyi aunewa kawai sukaji saukar duka ta ko ina a jikinsu hatta yaransu da
suke tare da su, dakatar dasu captain yayi kafun ya karaso inda suke , gabaki d’aya
an kunbura musu face, ko wannansu ya dukar da kansa katsa sabida wani azabar buguwa
da Sukai, ko wannansu da kyar yake iya maida nunfashi, kallan yanda suke zazzaro
idanuwa captain yayi “ ku yan iska ko, baku da mutunci yau zakuga yadda za a koya
muku tarbiyya “, ba shiri guy din dazu yayi saurin riko kafar captain “ we’re very
sorry sir”kafun captain yayi magana Prince yayi saurin yin magana “zakuga sorry
lokacin da aka ce kuyi wa kaza aski, ku yan iska , iskancinku har nan ko”murmushi
Adil ya saki” no yaya Prince , kamar idan sun bada hakuri its okay”. Cikin wani dan
iskan murmushi Prince ya kalli dizzy da har yanxu kansa yake a sunkuye sai faman
sakin nishi yake , “ku Bashi hakuri”, gabaki d’aya kuwa hada baki sukai wajan cewa
sorry bansa Dizzy da yake a zuciye, nuna msu kofa Prince yayi kafin ya kalli
captain ,”wannan shine marakunyar , he can’t even apologize, kawai ku sashi a buttt
akaiwa simba shi”cikin murmushin da Adil ya furta “kasan lion din Big boss bashi da
hakuri fa”, be karasa zancansaba a rude su dizzy suka dago tare da hada baki wajan
furta “BIG BOSS?Innalillahi wa inna ilaihi rajiun “ gabaki d’ayansu zuface ta fara
sakko musu duk da sanyin Acn da ke wajan, basusan ko wanene ba amma sun ‘ta’ba jin
labarin yadda yasaka ogansu yiwa dan buri tsarki sannan yasa akayi masa kwalkwal,
kamar zasuyi kuka suka fara bawa Adil hakuri hatta dizzy da yafi kowa rudewa,
Prince shi abun dariya ma ya bashi Ganin yadda suka rude lokaci guda, shikam Adil
murmushi ya sakar musu “ you can go”, ai bashiri suka arta a guje hatta takalminsa
d’aya sai da oskar ya manta, ana kiransa yazo ya d’auka amma ko juyowa bayi
ba.”yaya Prince ka tsorata sufa “cewar Adil , gashin kansa kadan Prince ya kama”
Sabida ina cikin good mood ne amma da a boot za a sasu akai wa yaya bobo
bankararrun Kaji “kallansa Adil yayi be san lokacin da ya furta “ yaya sometimes fa
kai mugune wasa wasa “yar karamar dariya Prince ya saki “ zanyi maganinka idan mun
koma , yanxu time d’inmu ya tafi a kan wayancan shashashan, let’s play kafun muga
yaya bobo a nan wajan.” Hakance kuwa ta faru game d’in Devil dragger sukayi kafun
su ‘kara yin wani game d’in ganin babu lokaci ne yasa suka fito dga wajan game
d’in, ta escalator Suka sauka , Daidai wajan siyayyar kaya Adil ya hango wata P_cap
blue colour , nuna wa Prince yayi suka ‘karasa wajan, 5 p_caps Adil yadauka, Green,
blue, red, black, white sai abubuwan ci da suka iya kusan Leda Hudu kafun su bar
Brookfield palace.

11 saura suka shigo ciki gida , masu tsaran da suka gani daban ne ya tabbatar musu
da dawowar Bobo, hakanne kuwa dan suka shigowa main gate suka tarar dashi a tsaye
ya dukar da kai, yana ganin shigowarsu ya juya cikin takun manyan sojoji ya nufi
part d’insa , suma suna fitowa 2 leda din kayan ciye ciyen da suka ibo suka bawa su
captain na su, kafun suma su shiga cikin main falour , bakowa a wajan sai james
dake tsaye bakin dinning, shaf shaf suka ci abincin su kafun su mikawa James kayan
da suka siyo suma suka nufi dakinsu. Gabaki d’aya wanka Sukai kafun su bi ayarin
gado.

2:30am aka turo kofar dakin nasu, shima sanye yake cikin kayan bacci coffee colour
masu shegen taushi,wayarshi dake kare a kunnansa ya haska ,Daidai inda Little
yake , kafin ya saita Daidai in Prince yake akwance shima ,cikin wani daddadan cool
voice kamar ba asan yin magana aka furta “ okay, Take care “, kai Bobo ya dan
jinjina duk da na cikin wayar baya ganinsa kafun ya kashe call d’in gabaki d’aya ,
kan gadon Little ya karasa kafun ya shafa kyakkyawar Sumarsa dara dan ruke masa
fuska, addua ya tottofa masa kafun ya koma kan Prince shima , sai da ya tabbatar
they’re safe kafun ya kashe musu fitular dakin ya barmusu dumm light me kamar light
green. Akofar dakin suka ci karo da uncle Dinsu yana kokarin shiga dakin shima ,
ganin bobo ya fitone yasa ya fasa shiga,cikin kulawa uncle din ya kallesa “ kaima
kaje ka huta, har yanxu baka kwanta ba “, kama hannunsa bobo yayi suka nufi part
din uncle din, shima sai da ya kwantar Dashi akan gado kafun ya furta “Good night
uncle “, cikin kuwa uncle ya shafa kansa “Allah ya tashemu lapiya ya albarkace ku
yarana “, a zuciya bobo ya amsa da Ameen kafun ya kashewa uncle din su light
shima . Still be kwanta ba sai da ya tabbatar da lapiyan gidan dukda tsaran dake
cikin gidan kafun shima ya nufi part d’insa.

https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

IBTISSAM
( Heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee

BOOK 1
( The beginning)

Season _4

ABUJA
NIGERIA

Dogon tsaki ‘yar shila taja lokacin da ta tarar da Abla na kuka har yanxu,
tsugunnawa tayi tare da kai hannunta daniyar ta’ba Abla, saurin bige mata hannu
Abla tayi , a zuciye ta kalli yar shila “kada ki kuskura ki ‘kara ta’bani , mugaye
azzalumai marasa tsoran Allah, karshen ku bazeyi kyau ba “, tana kai karshen zan
canta ‘yar shiga ta tsinka mata mari dama da hagu amma ko gezau Abla batayi ba sai
ma zuba mata narkakkun idanuwanta da suke shining me cike da zallan tsanar yar
shila tayi ,”Dan ubanki ni kike kallo da wannan mayun idanuwan naki , saukar da
idanuwanki shegiya “ ta karasa daniyar kara tsinkawa Abla mari, da sauri Abla ta
dam’ke hannunta ,sabida tsananin yunwar da takeji muryarta bata fitowa sosai” kada
ki kara gangancin marina, idan ba haka ba zan baki mamaki, mamakin da zaki dad’e
kinayi” tana kai karsher zancanta ta saki hannun yar shila da ta tsaya kallanta.
Mataccen d’akin da yazama tamkar d’akin kwanansu Abla ta nufa , da d’inta d’aya ma
ba irin store din da aka kulle ta bane wannan babu komai a cikinsa sai kwalaye da
suke a jere da alama shine abun kwanciyarsu. Can karshe wajan jikin bango Abla
tazame a wajan tana kara sakin wani saban kukun, wata yar siririyar sarka da ke
kugunta ta shafa a hankali bakinta ya soma motsawa alamun magana take har yanxu
hawayen da take be dena zubaba, Daidai lokacin sallar Magaruba Zinariyya ta shigo
tare da sakon uwar karuwai, wasu kaya ta jefawa Abla kafun ta fara binta da wasu
mayataccen kallo kamar zata had’iyeta, Adduar neman tsari Abla ta fara ganin irin
kallan da Zinariyya take binta dashi, “ga kaya nan ki canza , yanxu Alhazawan
hajiya zasu fara zuwa bata bukatar ganin kazantar jikinki, idan kin kammala kije ga
giyacan da aka tanadar musu zaki kaimusu, idan kin gama akwai dakin su Huwaila suma
suna bukatar shisha, mintuna goma uwar karuwai ta baki , idan ba haka ba Kema
kinsan sauran”, ta karasa zan canta tana hadiyar makogwaro har ta fita kuma tana
bin Abla da kallo, “ ya Allah lefin me nayi wa iyayena dasuka nesantani da kansu,
suka hanani farincikin da ko wace ‘ya take samu a wajan iyayenta, bansan ya dad’in
uwa yake ba , ban san ya dad’in uba yake ba , gabaki d’aya rayuwata a cikin duhu
nayi ta, babu Wanda yake sona , babu Wanda yake san ra’bata , bansan lefin me nayi
musu ba , Allah na rokeka Allah yasa nasan wacece ni , Menene asalina,me yasa suka
nesanta kansu dani, Allah idan kuma basa duniyar ne Allah kaji kansu ka kai
rahamarsa gareka “ hawayen da ta ke kokarin had’iyewane ya zubo mata , zuciyar ta
ba dad’i, a duniya kwata kwata ko da darana d’aya bata ta’ba samun farinciki ba ,
batasan ya farinciki yake ba , arayuwarta abu d’aya ta sani mutane basu da imani
basu da tausayi , kugin da cikinta yayine yasa ta shafa cikin sosai take jin
yunwa , ganin lokacin da aka bata na kokarin cikane yasa ta shiga Dan ‘karamin
bandakin da babu komai a ciki sai kasa da fanfo da wani abun kewaye duk ya
faffashe, ruwa ta tara a cikin fasasshen bokitin Fenti dake d’akin, dukda uban
sanyi da ruwan yayi haka ta watsashi a jikinta , tare Dayin Alwala , wasu kaya
dasuma suka gama jigatuwa duk sun mutu ta dauka tasaka , ko kallan inda kayan da
Zinariyya ta ajje batai ba , dan ta rantse saidai sukasheta amma bazata saka kayan
da duk jikinta yake a tsiraiceba, karan kida da tajine yasa ta tabbatar zinariya
zata iya dawowa d’akin shiyasa tayi saurin kabbara sallah magrib d’inta batare da
kowa ya sani ba dan dokar uwar karuwai ce ta hana ayi mata sallah kwata kwata, tana
idar wa ta mike tsaye Daidai lokacin da Zinariyya ta shigo d’akin, bin fuskar Abla
tayi da kallo da tayi kicin kicin da rai babu alamar fara’a a tattare da ita, maida
kallanta tayi kan jikin Abla dake sanye da wani madaidaicin hijabi daya fita daga
hayyacinsa, bata saka kayan da aka bata ba , da kallan mamaki Zinariyya ta bi Abla
, bata taba ganin yarinya mara tsoro kamartaba ta gwammace kome za ai mata sai dai
aimata amma inbatasan abu bazatayi ba , daman tasan za a rina, kallo d’aya zinariya
ta kara yiwa Abla kafun a ya tsine ta furta ,” taso muje “, itama Abla bata tanka
mata ba tabi bayanta zuciyar ta fal adduar neman tsari daga dukkan sharrinsu, tana
fitowa babban falon ta tarar da maza da mata ko wannansu na harkar gabansa, ko wa
kagani a wajan zaka ga mace da namiji a gefen ta ko kaga mata sun saka Namijin
atsakiyarsu rungume da juna, wani gefen ma inka kalla mata zaka gani su biyu ko su
uku, fitowar su Abla ne yasa wasu daga cikin yan falon kallanta, cikin ‘kasa ‘kasa
matan da ke gefe wata ta nuna mata Abla “ ni kam har yanxu sha’awar yarinyar nan
nakeji dan da Alama ba ‘karamin dad’i zatayi ba, gata yar chakwai dukda shegen
hijabin da take sawa kasan tana da manyan kaya” shewa matan wajan suka saka ,
gabaki d’aya hirarsu a kunnan Abla , Adduar neman tsari daga sharrinsu take
haryanxu a cikin zuciyarta, suna hawa sama nan ma wasu yan mata da mazane a Wajan
ko wa kagani da shigar banza, ga wata shisha da suke hurawa gabaki d’aya wajen ya
bad’e da hayakin shisha , anan d’in ma bin Abla suke da kallo har suka karasa wani
babban falo da ya fi ko wanne a cikinsu, suna shiga Abla ta kawar da kanta kasa,
Jikinta har ya fara rawa ganin maza kusan guda bakwai a d’akin gabaki d’ayansu kuma
babu kayan arziki a jikinsu sai boxer da singlet ,wasu ma singlet d’in babu a
jikinsu, nuna mata mazan cikin d’akin zinariya tayi , cikin kasa kasa da murya ta
furta “ wa’yannan mutanan zaki kawowa barasa ki tabbata kinsamo mana kud’i a
wajansu ko shafaki ne suyi , idan kin gama d’akin kusa dasu shine d’akin su Huwaila
kiyi sauri suma ki kai musu shishar ,” cikin ‘kasa ‘kasa take zancanta tana sakar
wa mazan d’akin murmushi, cikin kwarkwasa da ‘iya bariki ta fita daga d’akin tana
kashe wa d’aya daga cikin maza ido , gabaki d’aya mazan Abla suka zubawa idanuwa
kamar zasu had’iyeta, ko kallan inda suke abla batayi ba sai ma kara tsuke fuskarta
da tayi, inda kwalaban giyan suke abla ta nufa sai da ta tabbatar babu mai ganinta
ta bud’e kwalaban giyan tana toshe hancinta ganin tana kokarin yin amai sabida
warinta,gishirin da ta gani acan gefe ta lalla’ba ta d’akko , tsabar mugunta sai
data kusa juye leda d’aya a cikin kwalaben giyar, cikin sand’a ta fito daga Wajan
gabaki d’aya fuskarta a cin kushe , ta ajje musu kwalaban giyar d’aya daga cikin
mazan ya mike tare da kallanta yana faman lashe harshe kamar wani tsohon maye “ yan
mata ina zakije kuma , kizo ki taya mu hira mana , jikina duk tsami yake “, ya
fad’i hakan da niyar d’ora hannunsa akan girjinta, a mugun firgice taja baya tana
kiran sunan Allah, bata jira ya kara tankawa ba tabar d’akin a guje ,gabaki d’aya
mutanan dakin dariya suka saki, Wanda ya kusa ta’batan ne cikin sha’kiyanci yayi
magana “ gaskiya babyn nan ta had’u , dole na d’an d’anata gaskiya “ , wata sabuwar
dariya suka saki, nagefensa na amsa masa “ bakai ba koni na kwadaita gaskiya “, ya
karasa maganar yana bud’e kwalbar giyar da Alba ta tuttulawa gishiri, a cups duk ya
zuba musu , suka had’a cup tare da furta “cheers “, yanda suka zuba giyar nan haka
suka cikata a bakinsu, wani irin mugun kwarewa sukai kusan atare ga bakinsu yanda
yayi mugun d’ad’ewa har ma’kwo gwaransu, yar rige rigen shiga toilet aka fara ,
lokaci d’aya mugun jiri ya fara d’ibarsu dan ba ‘karamin shakar gishirin sukai ba .
A bangaran Abla kuwa d’akin su huwaila ta shiga , da sauri taja baya ganin babu
sutura a jikinsu ,sai wasu shegen pant da bra dake jikinsu duk kansu sanye da
attachment , zata bar d’akin huwaila da tafi kowa bariki a cikinsu ta dakatar da
ita ,”ina zakije kuma , kizo ki d’akko mana shishar, dogon tsaki Abla Taja tana
kawar da kanta gefe, zata fita huwaila tayi saurin dam’ko hijabin Abla tare da dawo
da ita cikin dakin “ ke dan uwarki ina miki magana kin shareni, ta kamar me kike ,
uban me ma kike boyewa cikin hijabin naki”, hannu takai zata taba hijabin Abla tayi
saurin gocewa kallan matan dake d’akin huwaila tayi “ ku rike mun ita , yau sai
naga komenene a jikinta ,” wasu hawayen bakin ciki abla ta fara saki , a zuciye ta
furta “ karku ta bani” itama huwaila kallansu tayi “ ku rike mun ita yanxun nan
bana san ganin komai a jikinta, gadan gadan sukayo kan Abla dake Jan baya hawaye
fal ranta, a Daidai lokacin da aka turo kofar d’akin, gabaki d’aya maida kallansu
sukai kan kofar, ilham ce tsaye a wajan tana binsu da kallo,”Abla wai kizo inji
uwar karuwai”, hamdala Abla ta saki cikin zuciyarta da sauri ta bi tagefan
huwaila,cikin zuciyarta fadi take “zanyi maganinku keda yan iskan matan nan da ni
kuke magana “. Suna barin d’akin ilham ta kamo hannun Abla cikin sauri suka ratsa
ta gefen wajan ganin hankalin mutanan wajan baya kansu sabida kid’an da aka kunna
gabaki d’aya rawa suke ,suna shiga d’aki ilham ta saki hannunta suna sakin ajiyar
zuciya , babu kowa a dakin nasu sai wata Leda babba da ilham ta shigo da ita ,kulle
kofar tayi tare da saka wani katako ta ydda zaai tunanin basa ciki, leda d’aya
ilham ta d’akko tare da dakko wani park din takeaway ta mika wa Abla , d’auke kanta
Abla tayi zata wuce ilham tayi saurin kamo hannunta , muryarta kamar zatayi kuka ta
furta “ na Rantse miki da Allah Abla ba abunda kike tunani bane , ni inda aka kaini
biki suke ma , mutumin da aka kaini wajan sa mutumin kirkine, ganin yadda na ke
kukane yasa ya tanbayeni idan bazan iya ba na bar masa d’aki , ina kuka na fara
bashi hakuri, tausayi na da ya jine yasa ya tanbayeni dalilin zuwa na nace masa
yunwa nake ji, Allah Abla ki yarda da maganata babu abunda yamun sai ma fad’a da
yayi mun kuma ya bani takeaway d’in abincin nan tare da 10k kin gansu ma “ ta
karasa tana nuna wa Abla “ And ya mun alkawari bazai fad’awa uwar karuwai ba kuma
zai dunga bani Abinci amma kar nayi karuwanci “, rungumeta Abla tayi tana fashewa
da kuka , itama ilham d’in kuka take “ Allah nagode ma , Allah na gode ma ,” shine
abunda Abla take nanatawa , abincin ilham ta mika mata “ kiyi Sauri Abla kici
abincin nan nasan kina jin yunwa banaso uwar karuwai ko Zinariyya suzo nan “
jinjina mata kai Abla tayi “ inaso nayi sallah tukunna dan lokacin sallah ya wuce “
girgiza mata kai ilham tayi , Abla ki fara cin abincin tukunna tun safe baki ci
komai ba , kinga ragowar kayan da ya bani zan boyeshi cikin kwalayancan sabida mu
samu abinda zai mana kwana biyu , 10k din ma ki ajje mana a wajan ki na tabbata
insu Zinariyya suka gansu a waje na bazasu barmun ba gwanda ke basa miki wani abun,
ajiyar zuciya Abla ta saki zatayi wa ilham Godiya tayi saurin dakatar da ita “ bamu
da lokaci “, da Sauri ilham ta budewa abla takeaway din dake cike da lafiyayyan
fried rice da cinyar kaza , ita kanta abla jikinta har rawa yake sabida kad’awa da
kayan cikinta sukai, da Sauri ta wanke hannunta ta soma cin abincin hannu baka
hannu kwarya, babban lemo ilham ta mika mata kafun ta boye musu ragowar kayansu
inda babu Wanda zai gani, cikin Sauri Abla take shan lemon tana sakin ajiyar zuciya
, ta dade bata ci abincin data koshi ba , a fili ta furta “ Allah na gode ma”,sai
yanxu ta dawo hayyacinta ,” Inasu Anee” girgiza mata kai ilham tayi “ ba waje d’aya
aka kaimu ba , amma suma nasan yanxu zasu dawo “, ajiyar zuciya Abla ta saki ,”
kinyi sallah ? Cewar abla “ eh nayi abla amma banyi isha’iba “, ganin lokaci na
tafiya ga dare na ‘karayi yasa sukayo Alwala , sukai isha’i ko shafa‘I da wuturi
basu samu sunyi ba Sabida motsin da sukaji kamar ana tunkaro dakin. Tsawan mintuna
5 babu wannan motsin , gabaki d’aya ajiyar zuciya suka sake sunyi mamaki sosai
ganin haryanxu su husna basu dawo ba, tun suna tsammanin ganinsu har bacci ya
d’aukesu.

✨✨✨✨✨✨

IBTISSAM
(Heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee

AREWA BOOK
https://arewabooks.com/book?id=652ff3a03fd6ffc37f68e4e2

__ Glory is to Allah , and praise is to Allah , and there is none worthy of worship
but Allah, and Allah is the most Great 💖__

__BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM__

BOOK 1
( The beginning)
Season __ 5

Karfe 3:00pm na yamma Prince ya nufi wani d’aki daya ke da girman gaske , kamar ba
a gidan ba , lokacin da ya danna wani button take a wajan wani babban office ya
bayyana , gabaki d’aya rabin jikin bangon d’akin littattafai ne da yawa Jere a
wajan, daga gefe kuma wasu manyan books ne tundaga kan The E-myth Attorney, The
Lincoln Lawyer , The secret Barrister, da wasu Book d’in da bazasu lissafu ba, daga
side d’in dama kuwa manyan wig and gown d’in lawyers ne da yawa a wajan, da suit
suit ga baki d’aya kayan wajan white and black ne kasan tuwar kayan lawyers ne a
wajan, kan wani unique chair ya zauna, daga gaban table d’insa wani symbol ne d’an
madaidaici me d’auke da harafin “Brr~Ameer Mohammed Al-Taufeeq”, wani madaidaicin
book ya d’auko jikinsa an rubuta Constitution, daga gefensa kuma wani babban Book
ne me tudun gaske , me d’auke da sunan “The Rule of Law “ a jiki, bincike ya fara
cikin littafin constitution d’in kafun ya janyo the rules of law the wasu books
d’in yana duba wa, gefe guda kuma yana kwafar abunda yakeso akan wata farar paper .

A ‘bangaran Adil kuwa wani waje ya nufa a cikin gidan da sai anyi tafiya me d’an ta
Zara kafun a zo wajan, gabaki d’aya wajan cike yake da manyan flowers da ciyawa da
suka ‘kawata wajan , duk da yanda wajan yake a cike da manyan grass hakan be hanasa
kutsakai wajan ba ko tsoro bayaji, kuka kukan da yake jiyowa da d’an ihun da yake
d’an jine kad’an kad’an yasa shi sakin d’an ‘karamin dariya , daga gefen d’an
wajan akwai wani symbol da aka rubuta The wildlife Refuge cikin wani d’an ado me
shegen kyau, dukda grass d’in da suke wajan hakan be hanasa kara kutsa kanshi ciki
ba har yazo wani madaidaicin gate me shegen nauyi, wasu sojojine maza guda uku a
wajan suna ganin Adil suka sara masa tare da bud’e masa gate d’in wajen , take a
Wajan wasu manya manya cages da yawa suka cika babban wajan da yake kewaye cikin
wani building, ta farkon cage d’in wajan ya nufa d’aya daga cikin sojojin na binsa
a baya , cage d’in farko da ya nufa wasu kyawawan gidajen a kune sa’kale a wajan
kusan guda 7, ko wana gidan cage Akune a ciki mace da namiji masu kaloli daban
daban, wani akune da ya fara ganin Adil ya soma wasa da fuka fikinsa cikin muryar
aku yasoma kuka “Ga Little nan ya zo , ga little nan yazo,wannan zuwan ya shiga
wani waje Ance za a karya shi, ga little nan yazo , ga little yazo, ya shiga wani
waje Ance za a karyashi “, gabaki d’aya kamar had’in baki sai ga sauran Akun suma
sun soma maimaita abunda akun farko ya fad’a,dariya Adil ya saki cikin shau’kin da
ya kamasa “ wannan bakin naku sai nasa an gutsireshi, ni yau bazan shigo ciki ba
daga waje zan ganku”, yana fad’in haka ya wuce zuwa next cage , shima a Nan wasu
d’an burine a wajan guda biyu mace da namiji, cages na uku ya nufa kasan tuwar ko
wana cages yana da tazara da d’an uwansa, a cage d’in gabama wasu ‘koshashshun
kangaroo ne suma manya guda biyu mace da namiji suna ganin Adil suka matso kusa da
cage d’in, da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai ya soma zagaya cages d’in da suke wajan masu
d’auke da dabbobi a Wajan manya tundaga kan cheeta ,koala , fox , Deer,
coati ,Lion,tiger , hatta zomaye akwai a wajan , ko wace dabba mace da namiji ne
awajan, cikin cages d’insu ma ko wanne da gida aciki, sosai babban ya tara dabbobi
daban daban masu shegen girma , wajan ba ‘karamun ‘kayatuwa yayi ba kamar wani zoo
haka wajan ya kasance sabida yadda ya tara namun daji da yawa a wajan. Kiran sallar
la’asar da aka fara yi cikin masallacin gidan ne yasa Adil fasa shiga cikin cages
d’in wasu damusa, da sauri ya fito daga building d’in zoo d’in ya nufi haryar da
zata sadashi da asalin Building Dinsu , ya zo zai shiga Suka ci karo da uncle, da
sauri Adil ya du’kar da kai yana sosa ‘keyarsa , da kallan tuhuma uncle ya bishi
dashi kafun ya furta “daga ina “, Sam a rayuwar Adil basu iya ‘karya ba kamar yadda
Big Boss da Bobo suka tarbiyartar dasu, cikin sauri ya kama hannun uncle da turanci
ya furta “ Dan Allah uncle karka fad’awa uncle Bobo , na shiga Zoo d’in yaya Big
Boss ne , Amma ban shiga cikin cages d’insu ba “, cikin d’an zaro ido uncle ya
kallesa cikin turanci ya furta“ Little baka ji, duk jan kunnan da Bobo ya ja mata
sai da kaje ko, toh babu ruwana a ciki, idan ya dawo sai kayi masa bayani da
kanka , sabida kaima shedane duk inda ‘kafarka zata taka yayyunka sun sani , yanxu
lokacin sallah na tafiya let’s go and pray”, goshinsa little ya ta’ba shima “ Dan
Allah uncle , ni tsoro nake ji bana so ran yaya bobo ya ‘baci please “,kamo
hannunsa uncle yayi “ then sai ka dena abunda kasan zakayi laifi , zamu rasa
jam’i , idan an idar da sallah zamuyi magana “a hankali Little ya d’aga masa kai ,
a tare suka nufi masallacin uncle ya shiga ciki, Little ya tsaya yayi Alwala shima
Daidai lokacin da Prince ya shigo masallacin duk da yadda yaga yanayin Little ya
canza bai ce masa komai ba saida suka idar da sallahn Prince ya kallesa cikin yaran
Spanish ya furta “ me ya Samu Little “ kamar ‘karamun yaro Adil ya kama gashin
kansa “ yaya Prince nayiwa su yaya Bobo laifi kuma nasan maganar taje kunnan yaya
big boss “da mamaki prince ya kallesa ganin be fahimci me yake nufi bane yasa cikin
d’an d’aga murya ya furta “Zoo d’in yaya na shiga” yanxu kam sosai prince ya zaro
idanunsa yana bin jikin Adil da kallo “ me yasa wani lokaci bakaji Little , kamanta
abunda ya kusa samun ka wancan lokacin,” shima ru’ko hannunsa Little yayi “ kawai
inaso nagansu ne na dad’e banje Wajan ba, and kaga babu abunda ya sameni” fusge
hannunsa Prince yayi “babu ruwana idan yaya bobo ya dawo sai kayi masa bayani,
sannan ka fara rubuta wa cikin diary d’inka duk ranar da yaya Big Boss ya sako
‘kafa cikin ‘kasarnan “, zai juya little ya kara riko hannunsa “ please Yaya prince
d’azu kashiga office d’inka ne fa bana so na takura maka, uncle ma na duba naga
yana bacci shiyasa na shiga Amma tunda kaima fad’a zakayi mun shikenan “, ya karasa
kamar zai saki kuka , saurin rungumoshi prince yayi “ okay karkayi kuka hakuri
Kawai zaka bawa yaya bobo , shi zai iya cecenka wajan yaya Big Boss dan wallahi
kasan ko giyar wake kasha karka kuskura kayi gigin kiran yaya big boss yanxu “,
amarairaice Adil ya d’aga masa kai jikinsa duk ba dadi, jan hannunsa prince yayi
suka shiga cikin Palourn su,” ni banasan wannan kalar fuskar , nafisan Naga Adil
d’in yaya big boss da yaya bobo, na hannun yaya Prince sannan shalelen Uncle iron
man “, yar ‘karamar dariya Adil ya saki, sosai kuwa prince ya zage yana sashi
dariya har saida yaga mood d’inshi ya dawo Daidai. Kamar Wanda aka tsikara kuma
yayi saurin hawa sama mintuna kadan ya dawo tare da wani karamin box a hannunsa ,
d’aya hannun kuma p-cap ne guda biyu red and green , Red p-cap d’in ya mi’kawa
prince tare da d’an ‘karamin box din hannunsa , cikin mamaki prince ya furta “
nawane “ gyad’a masa kai Adil yayi, p- cap d’in ya ajje agefe tare da bud’e small
box d’in hannunsa, wani siririn abun hannu ne me shegen kyalli da walwali sai faman
shining yake , sosai abun hannun ya burge prince musamman tanbarin abun sarauta
dake jiki,cikin washe baki prince ya furta “ wannan diamond d’in nawane? Only me ?
Yaushe wannan idea d’in tazo maka?” Hannunsa Adil yasaka cikin box d’in tare da
dakko siririn diamond d’in “ Haba yaya Prince duka wannan tanbayoyin Yaushe kake so
na amsa maka , Gift d’ina ne fa ,and wannan gift d’in bakamar sauran gift bane
wannan har abada kadunga sashi a hannunka “, kallansa prince yayi , shima Adil
jinjina masa kai yayi “ dagsk nake yaya prince , babu me irin design d’innan da
kaina na bada idea d’in yadda nake so a zanamun lokacin da mukaje Russia , and Duk
inda kake a fad’in duniyar nan Indai wannan abun hannun yana hannunka zan iya nemo
inda kake , please karka cire kaji”, rungumeshi prince yayi cikin farinciki “ wow
wow, gaskiya Little ya girma , yanxu kam na yadda you’re not a baby but you’re
still a baby to us”, shima Adil cike da farinciki ya rungume prince “ ina sanka
yaya prince d’ina “ , jinjina masa kai shima prince yayi “Nima haka “, saukar
muryar uncle sukaji abayansu “ Ni kuma fa “, wajan shi suka ‘karasa shima suka
rungumesa “ kai ma muna san ka uncle iron man “, suna raba jikinsu Adil ya d’auko
p-cap Green sak irin ta Prince ya mi’kawa uncle tare da ‘karamin box d’in da ya
bawa prince “ uncle wannan naka ne “, murmushi Uncle ya saki ,cikin English ya
furta “ wani lokaci in kayi abu sai ka tunamun yayanku, sak halinku yazo d’aya ,
prince kuma sai yayo wasu halayen na bobo” yana bud’e box d’in irin chain d’in
prince ne sak me shegen ‘kyal’kyali sabani na uncle wasu ‘kananan Harufane a jiki
da aka sa uncle iron man , cikin wani irin salo, p- cap d’in prince yasawa uncle
akansa , abun hannun kuma Adil yasa masa “ uncle please karka cire wannan abun, duk
lokacin da ka gansa ko bana Wajan zaka tuna dani kaji” gashin kansa uncle ya shafa
“ ka fara girma yanxu Little , Allah ya albarkaci rayuwar ku gabaki d’aya “ gabaki
d’aya a falon suka zauna Little da prince suna gefe uncle kuma yana tsakiyarsu .

✨✨✨✨✨✨
NIGERIA

ABUJA

ADEMOLA ADETOKUMBO STREET

Karfe 3:30am na safe uwar karuwai ta banko d’akin dasu Abla suke a kwance ita da
ilham , ruwan fridge d’i data shigo dashi me shegen sanyi ta watsa musu, a firgice
suka farka sabida yanda ruwan sanyin ya sauka a jikinsu ga sanyin asuba daya fara
busosu, cikin karkarwa ilham ta kalli uwar karuwai a tsorace , Abla sosai jikinta
ya soma karkarwar sanyi, cikin wani irin shegen kallo uwar karuwai tabi kirjin abla
da kallo gabaki d’aya hankalinta yana kan ‘kirjin Abla da ruwa ya ta’ba , fahimtar
hakan Yasa Abla tayi saurin saka hannunta cikin hijabinta tana adduar neman tsari
daga sharrinta ,dogon tsaki uwar karuwai taja “ dan ubanku sai nace muku ku Tashi
ku fara aiki? Tsinannun yara da basu san hanyar arziki ba, daka yanxu tsarin aikin
ku ya canza , dake da wannan shed’aniyar yarinyar ku zaku dungayin aikin komai da
komai na gidan nan tunda kun ‘kibin hanyar arzikin da na saku sannan kullum zaku
dinga kawo mun 500 kud’in zaman d’aki , duk ranar da kuka kuskura baku kawo ku
d’innan ba ku tabbata ranar sai nayi kud’i daku dan akwai Alhazawa dayawa da suke
kwad’ayinku, shegun yara masu kashe wa mutum kasuwa , idan kun gama ke “ ta nuna
husna “ ki sameni a d’akina “‘kara kallan ‘kirjin Abla tayi da kallo kamar
idanuwanta zasu fad’o ‘kasa kafun ta bar d’akin tana sakin ajiyar zuciya . Hannu
ilham ta d’ora aka “nashiga ukuna”, sauke mata hannu Abla tayi, kuka ta fashewa
Abla dashi “ na shiga uku Abla , matarnan bata tsoran Allah babu Allah aranta, Kema
kinsan duk Wanda takira d’akinta toh ba abun alkairi zatayi dashi ba , Abla ina
tsoron matar nan , ki temakamun Abla dan Allah “, idanuwanta da suka fara
‘kan’kancewa kamar zatayi kuka Abla ta lumshe kafun ta rungume ilham “ karki damu
ilham, insha Allahu Allah yana tare damu babu abunda suka isa suyi mana , ki share
hawayenki da yardar Allah ita bata isa tayi miki komai ba kinji?”, girgiza mata kai
ilham tayi zata kuma magana itama Abla tayi saurin dakatar da ita” Karki damu babu
abunda zai sameki kin manta kina da Abla “, ajiyar zuciya ilham ta saki “ nagode
Abla “ hawa yan idanuwanta abla ta goge mata “ karki damu insha Allah babu abunda
zai sameki, har yanxu su Anee basu dawo ba? Allah yasa suna lapiya suma “ hawayenta
ilham ta share “ Amin Abla Nima nayi mamaki danaga har yanxu basu dawo ba “,
jinjina mata kai Abla tayi kafun ta mi’ke tsaye “ ya kamata mu fara gyaran gidan
nan kafun su dawo , ki fara gyara d’akunan ‘kasa ni sai na hau na yi nasa kafun ayi
kiran sallahr asuba “, toh kawai ilham tace mata lokacin gabaki d’aya baka jin
motsin kowa sai su biyu da suke aiki tun kafin Garin Allah ya waye, Tun wajen
4:00am na asuba suka fara aiki lokacin da kowa yake runtsawa har akai kiran sallah
asuba basu gamaba sabida ydda d’akunan suke a har gitse, basu suka kammala ba sai
wajan karfe 9:00am, ganin lokacin sallah na kurewa ne yasa sukabar aiki suka shige
d’akinsu, saida suka tabbatar sun kulle yadda su Zinariyya bazasu iya bud’esu ba
tunda dokar uwar karuwai ne ,duk wacce aka kama tana mata sallah a cikin gida sai
tasa Ammata dukan kawo wuka kamar ba musulma ba, suna idar da sallahr azkar d’in
safe da maraice sukayi kamar yadda Abla ta saba koya musu, cikin Sauri suka mi’ke
zasu fito ilham ta tsayar da Abla , inda ta ajje musu ledar jiya ta bud’e tare da
d’akko musu manyan biscuit da zasuci “ Abla wallahi yunwa nake ji ki bari idan
munci Abinci sai mu cigaba da aikin”murmushi Abla ta sakar mata “ Tohm kiyi sauri
ki kammala kinsan ako da Yaushe zasu iya dawowa”, gyada mata kai ilham tayi kafun
ta miko mata ledar biscuit d’in guda d’aya “ da Sauri Abla ta girgiza mata kai “
Azumi nake “, sakin baki ilham tayi, itama Abla manyan idanuwanta ta lumshe mata ,
gudun karta ‘kara wata maganar yasa tace “kiyi sauri bamu da lokaci”, da Sauri kuwa
ilham ta soma cin biscuit d’in, saida ta cinye manyan biscuit d’in kafun ta soma
ajiyar zuciya , da sauri kuma ta tattara ledojin biscuit d’in ta Mayar cikin ledar
data ‘boye cikin wani fasash shen gini daya lalace. Cikin sand’a suka fito daga
d’akin gabaki d’aya ajiyar zuciya suka sauke ganin su Zinariyya basu fito ba, uban
kayan wanke wanken da aka ‘bata masu shegen yawa su Abla suka fara had’a ita da
ilham, basu suka kammala wanke wanken nan ba sai wajan karfe 12, lokacin da su
Zinariyya suka fito kowa yana hamma acikinsu . Kallan su Abla Zinariyya tayi kafun
ta ja wani dogon tsaki “ matsiyata kawai “, acikin su babu Wanda ya tanka mata
saida suka kammala komai , sai alokacin fargaba ta soma kama su Abla , musamman da
ilham ta tuna mata kiran ta da Uwar karuwai take , Jim kad’an Abla tayi kafin ta
kalleta cikin ‘kasa ‘kasa da murya “ mu gudu sai mu dawo anjima “ da Sauri ilham ta
girgiza mata kai cike da tsoro” a’ah Abla Nidai ina tsoro wallahi”, kama hannunta
Abla tayi “ idan bamuyi hakan ba kinsan me zatayi miki idan kika shiga d’akin? Ko
kin manta lokacin datasa kawayen ta su danneki tana ‘ko’karin farka miki kaya Allah
ya ceceki daga cikin zaluncinta ?” Ajiyar zuciya ilham ta saki, ganin hakan yasa
Abla taja hannun ilham Suka gudu, sunzo fita daga gidan Zinariyya ta hangosu, duk
yadda taso taresu abun yaci tura saida suka gudu, tsaki zinariyya ta saki tana
taunar le’ben kasan bakinta.

✨✨✨✨✨

UNITED STATES

karfe 6:30pm motocin Bobo Suka shigo cikin harabar building d’in gidan ,gabaki
d’aya soldiers d’in kowa yashiga taitayinsa , Adil na jin durar motocin ya zabura
zai gudu uncle iron man ya mayar dashi kan kujerar da karfi ya dam’ki hannun uncle
kuwa , Adaidai side d’in building d’insu motocin nan sukai parking tsawan mintuna
biyu da bud’e masa mota da akai kafun ya fito cikin takun manyan sojoji masu
ta’kama da izza , yana fito wa daga cikin motar gabaki d’aya sojojin suka sara masa
, basu ba hatta wa’yanda suke nesa dashi gaba d’aya kowa sai da ya sara masa ,
ganin yanda fuskarsa take a had’e ne yasa kowa ‘kara shiga taitayinsa, daga
hannunsa na dama wani farin bandage ne daya zagaye tafin hannunsa dashi, a hankali
ya soma taku kamar bayasan taka ‘kasa, duk daku d’aya da zaiyi da bugawar zuciyar
Adil da gabaki d’aya ya dure, yana zuwa daidai bakin kofar shiga wani green d’in
abu ya haska kafun ya fara kiran sunan “Bobo is back”, . Kara damke hannun uncle ,
Adil yayi gabaki d’aya tausayinsa ne ya kamasu shida prince ganin lokaci d’aya yana
neman rikicewa , Bobo na shigowa cikin falon ya tarar dasu su uku a zaune da Sauri
ta saka hannunsa me bandage d’in a aljihu, dukda yadda ransa yake a had’e hakan be
hana yasassautashi ba , cike da girmamawa ya gaishe da uncle d’insu batare da ya
kalli inda prince da Adil suke ba , cikin yar in ina prince ya furta “ welcomed
back yaya bobo “, batare da ya kalli inda prince yake ba ya d’an jinjina masa kai,
Adil ma kamar zaiyi kuka magana a rarrabe ya furta “Ya..Ya Bo…” be karasa maganar
saba ya had’iye halamansa sabida kallan da bobo ya jefa masa kafun ya nufi inda
Elevator d’insu yake . Fashewa da kuka Adil yayi ganin Bobo ya sharesa,gabaki
d’aya rarrashinsa su uncle suka fara cikin sakin yalwataccen murmushi uncle ya
furta “ Banasan wannan kukan , kaje ka basa hakuri kawai”, kallansa Adil yayi “Amma
uncle fushi fa yake dani”, girgiza masa kai prince yayi “ kamanta abunda yaya bobo
ya koya mana , idan munyi lefi mubada hakuri? Just kaje babu abunda zai maka
kaji?”, kallan uncle da prince yayi lokaci d’aya suka d’aga masa kai, da sauri
yanufi elevator shima, Daidai part d’in bobo ya tsaya ya’ki shiga, har zai juya sai
kuma yasaka turn print d’insa take a Wajan kofar wajan ta bud’e babban falonsa me
shegen kyau da ‘kayatuwa ya bayyana , kamshin freshener d’in lavender cedar leaf
linen ne ya doki hancinsa, cikin sand’a Adil yasoma tafiya sabida kar aji ‘karar
tafiyarsa, babu kowa a falon, kofar da ya gani a bud’e ya nufa bakinsa d’auke da
sallama, da Sauri bobo da ke dressing d’in hannunsa yasaka hannun cikin aljihu yana
bun fuskar Adil da kallo, sallama yayi Bobo ya amsa masa yana binsa da kallo, a
mara rai ce Adil ya furta “ Yaya bobo kayi hakuri kaji?” ‘Dan harararsa bobo
yayi ,” ni babu ruwana tunda baka jin magana , idan mesu ya dawo sai kayi masa
bayani”, da Sauri Adil ya shigo cikin d’akin “ Dan Allah yaya bobo na, kawai nayi
missing d’insane fa , shine naje na kallesu “, tausayin Adil , Bobo yaji ganin yana
‘ko’karin yi masa kuka “ fine , idan ka ‘kara rashin jinka kuma ni babu ruwana,
lokacin sallah ya kusa “, ka hakura ? Adil ya tanbaya , gyada masa kai bobo yayi ,
da Sauri yazo zaiyi hugging d’insa bobo ya dakatar dashi “ idan na fito sai ayi
hugging d’in, lokaci yana tafiya”, toh kawai Adil yace masa tare da barin d’akin
fuskarsa a washe tunda bobo ya hakura, hannunsa me ciwo bobo ya ciro yana ‘kara bin
yankan da kallo, ko da wasa yasan bazai bari Adil yaga wannan ciwanba, shiyasa ya
‘karasa dressing d’insa , kafun ya shirya cikin wasu Lious Vuitton d’in kaya riga
da wando, daga jikin rigar akwai tanbarin VL me shegen kyau d’aya ‘karawa farar
rigar jikinsa kyau , damtsen hannunsa sosai ya fito cikin farar jigar jikinsa,
yalwataccen ba’kin gashin kansa duk ya kwanta masa a ‘keyarsa kasantuwar baya tara
gashi sosai akansa . Kiraye kirayen sallar magariba ne yasa ya fito daga d’akinsa,
lokacin gaba ki d’aya su Adil suna tsaye suna jiran sa, yana fitowa masallacin
gidan suka nufa , kamar ydda suka saba kullum jam’i suke bi tare da musulman
sojojin, wa’yanda ba musulmai bane sukuma suna kula da tsaran gidan. ‘Ka ida idan
suka shiga sallahr magrib basa fitowa sai anyi sallar isha’i, suna idarwa Bobo tare
da wasu sojoji manya manya suka nufi wata hanya , Adil zai bisu uncle iron man da
prince suka dakatar dashi, zaiyi magana uncle iron man ya katse shi “ banasan musu
Adil, dare nayi lets go “, girgiza masa kai yayi ya rike hannun uncle na hagu,
dayan hannunsa kuma prince ya rike masa . Suna shiga prince ya nufi dinning daman
bashi da jumurin yunwa , shima Adil dinning d’in suka nufa shida uncle , James ne
yafito yayi serving d’insu , ko wannansu favorite food d’in sa yasoma ci, Adil ne
kad’ai be soma cin abincin saba , prince ne ya kallesa “ me yasa baka cin abincin
ka ?” , spoon d’in sa Adil ya d’auka “ ina jiran yaya bobo ne “, ‘karamun tsaki
prince ya saki tare da ci gaba da cin abincin sa, kallan Adil, uncle yayi “ kaci
abincin ka , idan ya dawo zan sashi yaci okay?” , kamar wani ‘karamin yaro ya
mikawa uncle ‘karamin d’an ya tsansa alamar Alkawari, shima uncle yatsan nashi ya
miko masa suka d’aure waje d’aya alamar promised.

A bangaran Bobo wani d’aki suka nufa me duhun gaske , kamar wani ‘karamin kurkuku
haka d’akin yake , ga wasu chains da yawa a ciki , ‘kofofi uku ne a cikin d’akin,
d’akin tsakiya Robert ya bud’e masa , nan ma wani duhu ne a wajan sai wani d’an
haske kad’an daya haska d’akin, wani abu Robert ya danna take haske ya haska cikin
d’akin . Wasu samari guda biyu ne a cikin d’akin ko wannensu da kunburarriyar fuska
, suna ganin Bobo suka mi’ke tsaye , d’aya daga cikin sune ya kalli bobo murya bata
fita sosai ya soma magana “ mun fad’a muku komai da kuke so ku sani , akan me za
Kuzo ku kullemu anan “, be ‘karasa maganar saba sabida naushin da captain ya d’auke
fuskarsa dashi, ‘kara ya saki sosai tare da dafe bakinsa da Jini ya fara zuba ,
kujera robert ya ajje wa bobo, yana zama suka koma bayansa shida captain suka tsaya
, da hannu yayi wa samarin alama dasu zauna Bashiri suka zauna , cikin kausash
shiyar murya bobo ya soma magana “ Tanbaya d’aya , Amsa d’aya , suwanene suke baku
umarni akan kwayoyin da aka shigo dasu, matan da aka samu abuge cikin maye and ko
waccen su anyi raping d’inta su wanene sukayi musu haka ?” A zabure suka kalli
junan su , gabaki d’aya tsoro da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu, saurin
kallan suna suka kafun su had’a bakin wajen furta “ mu babu Wanda ya samu”tsakanin
captain da Robert babu Wanda yace musu komai sai ma fita daga Wajan da Robert yayi,
Bobo kuwa tun bayan tanbayar da yayi musu be ‘kara d’ago kansa ya kallesu ba sai ma
wata tsadaddiyar waya da yake dannawa hankali kwance, mintuna biyu Robert ya dawo
cikin d’akin hannunsa d’auke da wani madaidaicin box me fad’in gaske black colour ,
kallan juna samarin sukai ganin Robert ya ajje Box d’in a gabansu, numbers guda uku
ya saka box d’in ya bud’e , a ido mutum sai ya d’auka ba shi da girma , amma daga
cikin sa waje ne me steps uku a jiki, ko wanne kuma da wasu ‘kananan makamai a
cikin su kamar na operations , Wani ring cutter Robert ya d’auko tare da kama d’an
yatsan d’aya daga cikin guys d’in , a tsorace guy d’in ya soma kuka yanaso ya kwaci
hannunsa amma Robert ya rike hannun gagam, a daidai d’an yatsan sa ya saka abun
fuska a cunkushe ya kalle su, “ 1…, 2….” Wanda aka rike wa d’an yatsane ya kalli
d’aya da shima gumi da tsoro ya gama bayyana a fuskarsa amma taurin kai ya hanasu
magana , Robert na furta “3”, Ring cutter d’in da yake hannunsa ya danna take a
Wajan ‘karamin finger d’in guy ya cire , gigitacciyar ‘karar a zaba ya saki tare da
zubewa wajan a sume, d’ayan da ya fara futsari a wando Robert ya kalla , amaimakon
d’an yatsan hannunsa shi d’an yatsan ‘kafarsa Robert ya kama , da sauri ya fara
girgiza kansa , cikin ‘kin’kina ya soma magana “ Me .. me zakuyi mun, me nayi
muku , kuyi hakuri , please kuyi hakuri “ shima Robert be saurare saba ya yanke
masa ‘karamin d’an ya tsan ‘kafa, kasan turar da turanci suke maganar yasa guy d’in
sakin ihu shikansa be san me yake furtawa ba sabida azabar da ya ratsa masa ‘kafa “
Wayyo d’an yatsana, zafi, kuyi hakuri , na fad’amuku babu abunda muka sani ,
Wayyo , Wayyo ‘kafata “, d’an d’ago da fuskarsa bobo yayi kadan tare da kallan
Robert, da Sauri Robert ya kalli guy d’in , finger dinsa yasaka guda d’aya alamar
yayi masa shiru , da Sauri kuwa ya kama bakinsa ya ri’ke sai faman zazzare ido
yake, Wanda ya suma Robert ya kalla kafin ya d’auko wani ‘karamin robber , me cike
da gishiri da wasu abubuwa a ciki, d’an kad’an ya dauka ya barbad’awa mutumin cike
da mugunta, azabure kuwa ya farka sabida rad’ad’in azabar da ya fi na d’azu zafi
har cikin kwanyar kansa , kamar wani ‘karamin yaro ya fashe musu da kuka , kallan
da Robert yayi masa ne yasa cikin sauri shima ya kama bakinsa yana nishi azaba,
wani fingers d’insa Robert ya kama da niyar yankewa yasaki bakin nasa , cikin kuka
ya furta “ ku tsaya zanyi magana , kuyi hakuri zanyi magana , zanyi magana “, shima
d’ayan cikin kuka yadunga d’aga kansa, “susu uku ne “, ya furta da’kyar Sabida
zafin da ‘kafarsa ke masa , shima Wanda aka yanke wa hannun jinjina kansa yayi
alamar Hakane da ‘kyar ya furta “ Logan ,Dylan,Nicholas” a zuciye Robert ya ‘kara
rike d’an yatsan sa daniyar yankewa guy d’in yayi saurin furta “ Logan d’an
Governor, Dylan dan mayor , and … and “, ya kasa ‘karasa cikon na ukun, Gigitaccen
mari Robert ya d’aukesu dashi , lokaci d’aya suka furta “Nicholas d’an matemakin
shugaban kasa “, sai kuma suka fashe da kuka suna bawa bobo hakuri. Wayarsa Bobo ya
mayar cikin aljihu , kafin ya mi’ke tsaye , ko kallan inda suke beyi ba ya bar
d’akin su captain suna Goya masa baya har zuwa building d’insu, yana shiga captain
da Robert suma suka shiga cikin wata ba’kar mota, bayansu kuma wata mota ce guda
biyu da manyan karatan sojoji a ciki sukabar gidan.

ME BU’KATAR KARANTA IBTISSAM ZAI BIYA KU’DINSA TA WANNAN ASUSUN 2681892316


AISHA UMAR , ZENITH BANK , sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee

PAID BOOK:

littafin Ibtissam na kudine akan 300kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai
tuntubeni ta wannan number tawa :07041879581.
Ko aturo kud’in book d’in ta wannan bank d’in: 2681892316 Aisha umar, sai a turo
mun shedar biya ta wannan number : 07041879581.

Dedicated this page to the family of MAI INGILA , love you all my parents 💞💞💞.

💞💞__ All praises are due to ALLAH, the forgiver and concealer of fault, The Guide
to Repentance, The one who responds to duas . AMEEN 💞💞__.

__BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM __

BOOK 1
( The beginning)

Season__6

ABUJA STATE , NIGERIA .


Tun da su Abla suka fita daga gidan karuwai gabaki d’aya barin unguwar sukai, sai
da sukayi tafiya mai Nisan gaske kafin su zauna suna hutawa , ilham kamar zatayi
kuka ta kalli Abla “ yanxu Abla kinga abunda muka jawo wa kanmu yanxu me kwatar mu
a wajan shegiyar matar nan sai Allah”, kallanta Abla tayi kafin ta d’an ta’be
bakinta ,cikin siririyar muryarta me dad’in gaske kamar sarewa ta furta “kome
zatayi mana Allah na tare da mu ai , kuma ita bata isa tayi mana abunda Allah be
nufa ba, kwanda ma ki kwantar da hankalinki”hawayenta ilham ta share duk da har
yanxu akwai tsoro a tattare da ita “ Abla kinsan halin matar nan, bata da Imani
musamman ke da ta fi nuna wa tsana , bansan Sharrin da Zinariyya zataje ta ‘kulla
mana ba , shegiya kanta kamar duwawun d’an buri”, dungure mata kai Abla tayi “ kar
ki wani dasu, ki tashi muyi abunda zamuyi kafin yamma tayi, kina an fara kiran
sallar‘karfe d’aya , damun idar zan ‘karasa layin Formella , idan basu gama karatun
suba , na saurara ko Allah zaisa na iya wasu abubuwan, Allah yasa Malam Sule yayi
Tarihi yau”, shiru ilham tayi kamar me tunani kafin tace “ Amma Abla me zai hana
yau muje kasuwar kubwa ,ko kayan kwanjone mu siya”mi’kewa tsaye Abla tayi , tare da
zubawa ilham manyan dara daran milky eyes d’inta, dukda tana cikin halin rayuwa
amma babu abunda ya canza daga kyawunsu,daga cikin idanuwanta har wasu d’igon
tauwadane guda biyu da suke ‘kara Haska kyawun kwayar idanuwanta da suke zara Zara
kamar wacce ta saka kwalli a cikin idan, ‘kara ‘kiftasu tayi akan ilham take a
Wajan dogan gashin idanunta suka soma sama da ‘kasa ba’ka’kye Wuluk kamar tasaka ,
cikin daddad’ar muryarta me kama da na sarewa ta cewa ilham “idan kika kashe su
ranar da kike bu’katan kudin ya zakiyi kenan? Karki manta su kad’aine dake duk
duniya yanxu, na d’auka zakice zakisi wani abu ki kwada siyarwa? Ni kam babu ruwana
babu wani kubwa da zanje, kinga biyu ta kusa ki taso muje muji karatun malam sule ,
banaso tarihin Annabi ya wuceni yau” Amma abla idan bamu je kasuwar ba Wana irin
abu kikeso musiyar?” Soma tafiya Abla tayi ilham tabi bayanta da Sauri “ Allah zai
haska mana ai, Kema kuma kinsan akwai sana’a sosai da mutum zai iya farawa , Nidai
yanxu damuwa ta, kar agama karatu banjiba, ga tarihin da nakeson ji, ki bari zan
fad’a miki Wana irin kasuwanci zamuyi kinji?” Jinjina mata kai ilham tayi tare da
kama hannunta suka soma tafiya , saida suka ‘karayin tafiya me Nisan gaske kafun
suzo wata makarantar Almajira da ke cike da maza, can gefe dasu Ilham da Abla suka
ra’be suna sauraran karatun Malam suke dayake ‘karawa almajiran, ganin lokacin
sallah yayi ne suka samu wani guntun ruwa sukayi alwala da sallarsu, kafin su ci
gaba da sauraran karatun. Karfe 3:00 daidai Malam sule ya dakata da karatun ya soma
yi musu tarihin annabi yusuf, gabaki d’aya nutsuwa Abla tayi tana sauraran tarihin,
ita kadai sai faman murmushi take , 4:00 ya dakata musu, d’an ‘karamin tsaki Abla
taja tare da kama hannun ilham suka bar wajan” wallahi Malam sule wani lokaci bashi
da M, saida na nutsu ina jin tarihi zai katse mana “, dariya ilham ta saki daman
tasan za a rina , duk lokacin da zasu zo jin karatun Malam sule a’karshe sai tayi
complain musamman idan tarihi ake yi lokacin , Kiraye kirayen sallar la’asarne
yasasu tsayawa daidai gefen wani masallaci, saida suka tabbatar sun shiga sallah
kafun su samu suma suyi Alwala da ragowar ruwan butocin wajen, can gefe da
masallaci su bi jam’i suma , ana idar da sallah muma suka tashi suka soma tafiya ,
wani dakali da Abla ta hango ta nufa, itama ilham zama tayi a gefenta, cikin
nutsuwa suka soma karanto adduar safe da maraice, duk inda ilham tayi kuskure sai
abla ta sake gyara mata , har suka gama sai lokacin ilham ta fara ri’ke cikinta “
Abla wallahi yunwa nake ji,”duk da itama Ablan yunwa take ji sai bata nuna hakan ba
ita , cikin tsokana ta ce wa ilham “ toh taho mu koma kurkukun mu”, tsallan data ga
ilham tayi ne yasata ‘kyal’kyalewa da dariya da har dimple dinta na both side suka
lo’ba, “ wallahi Kema kinsa in muka koma zamu san sauran balalle ma musamu abinci
ba, ga me awaracan dan Allah ko na d’ari musamu muci”, ‘karar da cikin abla yayi ne
yasa ilham ‘kara kallanta “kinga Kema yunwa kikeje, karkimun musu kawai ki taso
muje muci awaran”, batayi mata musu ba kuwa suka tsaya wajan me awara saida suka ci
ta d’arinsu suka kora da ruwa kafin su fara tunanin komawa gida , wata bishiyar
KARARA Abla ta hango da sauri ta nufeta ilham na binta abaya , saida suka ‘karaso
wajan ilham ta zaro ido “ Abla me zakiyi da karara kinsan ‘kai’kayine dashi fa
sosai, dariya mugunta abla ta saki kafun ta samo wasu manyan ledoji guda uku, biyu
ta saka a hannunta,d’ayar kuma ilham ta rike mata ,tsabar mugunta irin na abla
wad’an da Suka bubbushe ta tsutstsunka, sai da ta tara masu yawa sannan ta dakasu
da dutse , ilham gabaki d’aya ta tsorata batasan me abla zatayi dasu ba , saida ta
tabbatar ya mata yanda take so kafun suka nufo hanyar gida lokacin magariba ta
kusa, a farkon layin suka hango husna ita da wani a tsaye daga jikin bango sai wani
mammanne mata yake, tana ganin su Abla ta d’auke kai,kamar Abla zatayi mata magana
sai itama ta shareta, hannunta ilham ta kama “ Abla ki ‘kyalesu, duk wanda yace
baya bu’katarki a rayuwarsa Kema ki rabu dasu, kinyi iya kokarin ki akansu amma
basa ganin haka “, d’an murmushi Abla ta sakar wa ilham kafun ta furta “insha
Allahu “ . Kid’an da Abla ta somajine yasa ta girgiza kai, haka suke tun farkon
magariba suke sa kid’a har isha’i, a Wajan gidan kuwa kamar yadda tayi tsammani
mata da maza ne kowa tare da ‘yan matansa, wasu kuma matane kawai, ko wannen su da
‘yar iskar shiga , suna shiga Sukatar da abun yafi worse ma dan gabaki d’aya daga
wacce zaka ganta kwance jikin namiji sai wanda suke kiss da shafe shafe ba ko
kunya, kauda kanta Abla tayi tana neman tsari daga sharrinsu, da Sauri ta kama
hannun abla kada su Zinariyya su gansu, suka nufi store d’in da ya zama kamar
d’akinsu, karo suka ci da Aneesa dake ‘ko’karin fitowa daga d’akin cikin wata
doguwar Riga , mamaki ne ya kama su Abla dan basu ta’ba ganin ta da irin wannan
kayan ba “ Anee?” Cewar Abla , itama Aneesa murmushi ta sakar musu , cike da murna
ta furta “ tun d’azu nake tanbayar inda kuke akace ba’a san inda kuke ba , Aushe
zan ganku dai kafun na fita “, kallan ban gane ba Abla ta bita dashi, fahimtar
hakan Yasa Aneesa bud’e wata swag Jakarta itama da Alama sabuwa ce ta Fito da
ma’kudan kudi tana nuna musu “ A ina kika samo wannan kudin? Karkisa na fara zargin
ko sata kika fara ?” Dariya Aneesa ta saki” haba Abla ki dunga mun kyakkyawan zato
man, inda naje ne nasa mu wannan kudin kyauta , kinga tun jiya kaza da lemo nake
sha sai abunda yayi mun yanxu na dena kwanan yunwa , zan dunga samun kudi” atare
suka had’a baki wajan furta kamar ya”, bata damu ba itama ta soma musu bayani”
kawai fa hotel zakuje, Wanda aka had’a ku dashi ya d’an shash shafaku,shikenan fa”,
da mamaki Abla ta furta “ kina nufin karuwanci?” Girgiza mata kai Aneesa tayi “ ni
ba karuwanci nayi ba , nace miki shash shafa ni yayi yana mun wasa da breast
d’ina , ni kuma yace na sha masa…”, bata ‘karasa ba Abla tayi Saurin daka mata
tsawa “ ya isa haka Aneesa bana bukatar jin zancenki , Allah ya shiryeki, banga
anfanin mu’a mala da me irin halinki ba “, daga bayan ta taji an furta “ sai me
idan bazaki yi mu’amala da ita ba ? Ko kina ba’kin cikin kudin da ta fara samu
bakamar ke da kike a wahale ba? Gabaki d’aya maida kansu sukai wajan wacce tayi
maganar , Husna ce tsaye sai faman harararsu Abla take , babu Wanda ya tanka mata
tsakanin ilham da Abla, Hakan sai ya ‘kara ba’kanta mata musamman ydda Abla ta
sakar mata murmushi tayi wucewarta, itama ilham wucewarta tayi batare da tace musu
komai ba , tsaki husna taja dan ba haka taso ba “ Alhaji sammani yace na fad’a miki
yana waje yana jiran ki, karki saurari maganar su? Ba’kin ciki suke miki dan sun
fara ganin kin fara samun kudi, da suke cewa karuwanci, me kikayi a ciki dan kawai
an shafa ki? Ki rabu dasu nima ke nazo kira daman Zinariyya tace mun akwai wani
Alhaji da yake jira na, zo mu tafi “ ta kama hannun Aneesa sukabar wajan gudun kar
Abla ta fito ta hana ta zuwa.

Suna shiga d’aki Shuru Abla tayi kamar me tunani, dafata da ilham tayi ne yasata
sakin ajiyar zuciya “ na fad’a miki kidena sa damuwa aranki,ki duba kiga abunda
husna take miki, gaskiya bana jin dad’i” Abla bata tanka mata ba sai ma murmushi da
ta sakar mata,Inda suka bo’ye ledarsu ilham ta nufa Amma wayam babu ita babu alamar
ta da sauri ta kalli Abla “,Abla banga ledar da na ajje anan ba , ko kin sauya Mata
waje ?” Kai Abla ta girgiza mata alamar ah’ah suka shiga bincikar d’akin ga baki
d’aya ko zasu ganshi amma wayam babu ,kamar zatayi kuka ta furta “ yanxu Abla ya
zamuyi kenan Haka zamu zauna kenan?Ni ina tunanin ko su husna ne ma Suka d’auka “,
zato zunubi koda ya kasance gaskiya , ki kyautata musu zato, sannan idan kika yarda
da ‘kaddara sai kiga Allah ya baki sama da hakan Kinji “ cewar abla “ naji Abla
Amma kinsan su Zinariyya bazasu taba bamu abinci ba ,” idan kikai Imani da Allah
sai kiga ya baki mafita , kinji? Komai ki dunga saka Allah a ciki sai kiga komai ya
daidaita “, cewar abla , canza akalar maganar tayi ta hanyar furta “ ya kamata muyi
sallah tun kafin su Zinariyya Susan da zuwanmu “, da hakan ko wannansu yayi alwala
suka kabbara sallah bayan ‘boye kararan da tayi a inda baza a yi saurin ganin
saba , suna idar da sallah Zinariyya da ‘yar shila suka shigo cikin d’akin, wata
shegiyar ashar Zinariyya ta saki, a tsorace ilham ta kalleta Abla kuwa ko a jikin
ta, “ kun gama yawan karuwancin naku? Kun mayar da kowa yan iska ko? Yau kam sai
munyi maganin ku”, cikin daka tsawa yar shila ta kalli ilham “ dan ubanki ki tashi
kije uwar karuwai na d’akinta tana jiran ki , kafun mu had’a dake muci ubanku “, da
Sauri cike da tsoro ilham ta bar dakin, ita kuma Zinariyya ta kulle kofar daga
ciki, zuciyar abla ce ta buga amma duk da hakan bata nuna musu komai a fuska ba ,
rigar data ga sun fara cirewa ne yasa ta mi’kewa a tsorace jikinta har ya fara rawa
, ganin yadda suke ‘ko’karin cire kayansune Yasa Abla saurin kawar da idanuwanta ,
tunanin yadda zata ku’buta daga sharrinsu ta soma , karara d’in data ajje ne ya
fad’o mata , a wayance ta d’aukoshi batare da ko wannansu ya ankara ba , daga baki
d’ayansu kayan jikinsu suka cire Allah ya temaketa ma da short wando da singlet a
jikinsu, yadda suka fara nufotane yasa ta fara ja da baya da baya, suma suna bunta
suna dariya “ kwanda ki hakura muji dadin juna zai fi miki amma yau babu abunda zai
hana ban d’and’anakiba “ cewar yar tsila , ita dai Alba babu abunda tace musu sai
ma mayar da hannunta da tayi baya tana kwance karara d’in ta cikin Leda, Zinariyya
ta saka hannu zata kamota kawai Abla ta fesa musu kararar nan a jiki, tare da
kaucewa, dariyar mugunta suka saki har da tafawa , “kin d’auka ‘yar ‘kasar nan da
kika samana zai mana abu? Yau ko me zakiyi sai mun ciki”, itadai Abla babu abunda
tace musu sai ma addua da take yi cikin zuciyar ta, zasu ‘kara kama tane kamar daga
sama yar shila taji kamar abu ya tsireta tayi saurin dakatawa tana ta’bawan, bata
Ankara ba wani ‘bari wuyanta shima taji kamar abu ya tsireta, kallan ta Zinariyya
tayi tana ‘kokarin tanbayarta menene taji itama kamar abu ya tsireta, da sauri ta
saka hannu tana sosa wa , a maimakon ya dena sai kuma ya ‘Karu, da sauri da Sauri
kamar had’in baki kuma suka soma Susar jikinsu hankali a tashe , duk inda suka sosa
a maimakon wajan yayi sau’ki sai ma ‘karuwa da yayi, a haukace Zinariyya ta manne
jikin bango tana susar jikinta, yar shila kuwa burgima ta somayi a kasa tana
kururuwar jikinta , ga baki d’ayansu sun fita hayyacinsu babu abunda suke sai susar
jikinsu, Abla kam dariya da tausayin sune ya kamata lokaci d’aya musamman katakwan
data ga ‘yar shila ta d’auka zatai Susa dashi, Zinariyya kuwa kamar wata ‘kadan
garuwa sai bun bango take , ilham ce ta fad’o mata arai shiyasa tayi saurin bud’e
kofar da Zinariyya ta kulle cikin da bara gabanta na fad’uwa da sauri ta nufi
haryar da zata kai ta d’akin uwar karuwai haryanxu hannunta da ledar karara.

A bangaran ilham kuwa tana shiga d’akin uwar karuwai ta tarar da ita daga ita sai
wani ‘karamun towel , tana ganin ilham ta saki murmushi dukda abunda sukayi d’azu
ita da Abla, muryar ilham har rawa yake wajan furta “ Gani Ance kina.. kirana”,
amaimakon ta amsa mata sai ma jikinta da ta soma bi da kallo, “daukomun ruwancan “
cewar uwar karuwai, ruwan ilham ta d’auko mata jikinta na rawa musamman yadda uwar
karuwai take bunta da wani irin kallo, “ ga wayata can a kan gado d’au komun “,
nufar gadon ilham tayi itama uwar karuwai ta mi’ke , ilham bata Ankara ba sai bom-
bom d’inta dataji ta shafa da mugun tsorace ta juyo sai taga tayi mata runfa kasan
tuwar ta ‘katotuwace daman uwar karuwan,kamar zatayi kuka ta furta “ ga wayan”, a
maimaikon ta amsa wayar sai kwantawa da tayi towel din jikintadaga sama sama ana
ganin na shanunta kamar kan jinjirai guda biyu, “yimun tausa”, cewar uwar karuwai ,
kamar ta kwalla ‘kara Haka takeji sai duba ‘kofa take tana so taga ta inda Ablan
zata temaka mata, cike da tsawa tace “ ba dake nake va?” Arud’e ilham ta kama yar
lukutar ‘kafarta me shegen tauri tana matsawa, duk inda ta matsa sai uwar karuwai
ta furta “Ashhhhh da dadi”, sosai hakan ya fara bawa ilham tsoro,amma ba damar musu
Sabida yadda zubun uwar karuwai yake tsoratata, d’an zame towel d’inta uwar karuwai
tayi yanxu kam sosai na shanunta ya fito ba’ka’ke wuluk dasu waje sai mai’ko suke,
cikin rawar jiki ilham ta soma ja baya , fuska a had’e uwar karuwai tace mata ta
matso, Amma tsoro ya hanata hakan , tsawar data daka mata ne yasa ta matso kusa da
ita, mummunar fuskarta ta d’aure ba wasa ta furta “ cire kayanki na du baki “,
hakuri ilham ta soma bata amma ta d’auketa da gigitaccen marin da yasa ta cire
hijabinta , tana kuka ta soma ‘ko’karin cire rigarta, banko ‘kofar d’akin da Abla
tayine yasata sakin ajiyar zuciya , itama Abla ajiyar zuciya ta sauke ganin ta zo
adaidai, wani bakin cikine ya tokare wuyan uwar karuwai, ga samu ga rashi duk
alokaci gudu, ranta a ‘bace tana mamakin ina su yar shila da ta saka su rufe mata
Abla , Abla kam fuskarta ‘kam a kanta ko tsoron abunda zata sa ayi mata bataji, “me
ya kawo ki d’akin nan ? Ki tattara ki fice mun daga d’aki kafun ranki yayi mummunan
‘baci,”toh abla ta furta kafun ta ruko hannun ilham zasu fita uwar karuwai ta
dakatar dasu “ ke kadai nace miki ban da ita”, girgiza mata kai ilham ta somayi,
tana ‘kara rike hannunta, zasu gudu kamar na d’azu sai ganin uwar karuwai sukai a
bakin kofa gadan dagan ta nufosu bayan ta saka lock a d’akin, da Sauri Abla ta
kwance karara d’inta itama ta saka mata a jiki , uwar karuwai
Bata san me Abla ta saka mata, ta d’auka kasa ce ta d’an watsa mata, zata cafkosu
taji bayanta kamar yana mata ‘Kai’kayi, sosa war da zatayi taji wani wajan ya fara
yi mata, ga shi towel ne a jikinta, wani irin azababben ‘kai’kayi jikinta ya somayi
mata, sosawa kawai take a hau kace ,zata riko abla towel dinta ya soma kwance wa
sai kwanta tayi a kasa duk da girman jikinta, Abla na ganin haka ta kama hannun
husna suka fito babban falon gidan, a tsaye suka ga Zinariyya da yar shila rike da
katako ko wannansu susar jikinsu suke ta ko ina , gabaki d’aya kitsan attachment
din da sukayi saida ya baci a garin susa, yar shila ce ta hango Abla da Sauri ta
nuna wa wasu yan mata ita “ gata cab ku kamo ta”, abla na jin hakan tayi ‘ko’karin
guduwa da sunzo zasu kamata zata zulle musu, Zinariyya gani take wasa kawai take
shiyasa ta saka wa duk Wanda ya kama Abla zata bashi dubu goba, ai kuwa gabaki
d’aya ba mazan ba bamatan ba suka rufu zasu kama Abla amma duk da haka kufce musu
take , duk Wanda ya kusa kamata karara take fesa masa shima sai ya hau susar jiki,
duk da haka wasu daga cikin yan matan basu daddara suka cigaba da bin Abla , itama
Abla dataga bazasu ‘kyaleta ba kawai sai ta soma yi musu feshin karara, gabaki
d’aya falan sai ya har zuke kowa ne man wajan susa yake , tun tana fesa musu har
kararan nata ya ‘kare , sai a lokacin ta zuba musu kyawawan idanuwan masu d’auke da
dara daran eye ball kalar ash me duhu kadan, cikin tsakiyarsa kuma sai ya kasance
kamar adon black colour , tana juya idanunsa tauwadarta dake cikin idanta me kama
da zallan madara fitowa sosai tas. Yadda ta tsaya kallansu suma haka ko wanne ya
zuba mata ido cikin jin haushi, banko ‘kofar d’akin uwar karuwai gabaki d’aya kowa
ya mayar da hankalinsa kan kofar, Itace kuwa har yanxu sanye da towel dinta ko
kunya bataji tafi da d’aukan kirji, hannunta d’aya kuma ta kalmine data ke Susa
dashi, idanuwanta bai sauka a ko ina ba sai akan kyakkyawar fuskar Abla, a zuciye
ta nunata “ duk Wanda ya kama mun wannan shegiyar yarinyar zan bashi mace d’aya
yayi lalata”, mutanan Wajan suna jin Hakan suka soma suwa da kururuwa, husna na
ra’be a jikin bango yanda baza a ganta ba ,gadan gadan mutanan falon Suka fara nufo
inda Abla take itama tana Jan baya,zata taka step ta sauka ‘kafarta yayi skipping
step d’aya take a kan stairs d’in ta soma gangarawa , mutanan falon na ganin haka
suka soma sheya, ita kuna Abla tana kai karshen stairs d’in ta buge kafar ta, dan
karamin ‘kara ta saki zata mi’ke taji an take mata kafar, cikin azabar data fita
farko aka ‘kara take kafar damun karfi,’karar wahala Abla tayi tana d’ago fuskarta,
bata gama kallon fuskar wanda ya taka taba taji gigitaccen mari a kumatunta, duk da
zafin marin da taji ko gezau batayi ba sai ma kyalli da iya nuwanta suka soma,a
karo na biyu ta ‘kara d’ago fuskarta, wacce ta gani ne yasata bin ta da kallon
sakanni bata auneba aka fara ihun kiran sunan “ DEBEKA!!DEBEKA!!.wacce aka kira da
debeka na kalla, ba’ka kirin ce sosai gashi bata da tsaho ko kadan musamman
‘kibarta d’aya kara munanata, debeka muguwa ce sosai , ta dalilinta uwar karuwai ta
hana ayi adunga yi mata sallah a gida musamman Lolita da addinin Abla datafi komai
tsana wato musuluncin, shi yasa duk lokacin da take nan Abla ba ‘karamin wahala
take sha a wajan taba musamman yadda tafi kowa tsanar Abla. Yanxun ma suna gama
kururuwan suna dabeka ita kuma sai faman hura gajeren hancinta take , kamar wata
kayan wanki ta dam’ki kan Abla , Allah ya te maketama hijab ne a jikin da ba abunda
zai hana d’an kwalinta cirewa. Yadda ta janyo hijabin Abla ne yasa ta fara nishi
kad’an dan ba ‘karamin sha’keta yayi ba , haka debeka ta cigaba da jan Abla a kasa
har zuwa wani ‘kofa , Abla na ganin kofar ta soma girgiza kanta a tsorace , batayi
auneba taji debeka ta jefata cikin dakin ta kulle ta waje , da karfi Abla ta soma
bubbuga ‘kofar Sabida duhun wajan ga wani irin wani da matsin ‘beraye da ya ‘kara
tsoratata, jikinta ne ya fara rawa ganin duhun daki, da ‘karfi ta soma furta “ duhu
!! Ku bud’eni bana so, da duhu, zasu cinye ni!!! Ku bud’eni”, ita kadai sai faman
surutai take cikin d’akin da ko hannunka bazaka iya ganiba wai warin kazantar dake
tashi cikin wajan .
Cikin mugun tsorace Abla take maganar subud’e ta amma ko mutum d’aya babu a wajan,
duk da haka bata gaji ba sabida yadda take a mugun tsorace , da ‘karfi taci gaba da
furta “ banasan duhu , please ku bud’e ni , ku bud’eni”, d’an abinda taji ya ta’ba
mata ‘kafane yasata sakin ‘kara da karfi ta matsa daga wajan amma duk da hakan bata
tsira ba sabida yawo da berayen Wajan keyi da kukansu daya cika mata kunne , ga
warin datti dake kokarin sata a mai , cikin ‘kan’kanin lokaci tafita hayyacinta,
abin jikin katakon wajan ne ya ta’bata ta ‘kara hargitsewa a rufe ta soma neman
haryar da zata fita , jitayi tayi karo da abu zata saki ‘kara cikin ambaton sunan
Allah, jelar Beran data daka ne ya sata saki ‘kara bata aure ne ba taji beran ya
dafe kafarta , tsalle kawai Abla ta soma tana san cire beran, cikin rashin sani ta
daki wani d’an katako a cikinta da mugun ‘karfi take a wajan ta fad’i tana fad’in
“ cikina !!! Cikina !! Ku bud’eni please bana san duhu”, tun tanayi da ‘karfinta
har muryarta ya soma dusashe wa gabaki d’aya sannu a hankali idanuwanta suka soma
rufewa.

IBTISSAM NA KUDINE , Kİ BIYA 500 KIKARANTA SHI HAR KARSHE . 2681892316 Aisha umar
zenith bank , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581

https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee

PAID BOOK:
Littafin IBTISSAM na kud’ine akan 300 kacal , me ‘bukatar karantawa har ‘karshe zai
biya kud’insa ta wannan bankin : 2681892316 Aisha umar, zenith bank , sai a turo
shaidar biya ta wannan number 07041879581.

___💞💞 Ya Allah,Alhamdulillah for the unlimited blessings that I was unable to thank
you for__💞💞

💕__BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM__💕

BOOK 1
( The beginning)

Season__ 7

🍂🍂🍂🍂
🍃🍃🍃🍃🍃

UNITED STATES 🇺🇸

FIFTH AVENUE __!

Bobo yana shiga cikin falon ya tarar da bakowa a ciki, direct d’akin uncle iron man
ya nufa, yana shiga ya tarar dashi a zaune kan dadduma hannunsa d’auke da Alkurani
mai girma , sallama yayi masa saida ya ga ya amsa masa tukunna ya shigo cikin
d’akin, kan dannuman da uncle yake zaune shima a kai ya zauna tare da d’ora hansa a
kan kafad’ar uncle din, “ kayi kewar sa kenan”, murmushi bobo yayi duk da ya gane
me uncle din yake nufi amma be ce masa komai ba, shima uncle din be sake ce masa
wani abuba sai tray d’in da ya nuna masa “ Little yace na tabbata kaci abinci, if
not bazai yi bacci ba “, tray d’in bobo ya kalla shima tare da janyoshi “ uncle
kaima kasan shiriritan little da yawa yake, ni ya fara samun ciwan kai , and yasan
bazan zauna ban ci abincin ba kamar Big boss “, rufe Akur’anin uncle yayi” Little
kenan! Yayi missing d’in babban yayansa,and shine auta ka bari duk lokacin da
kashirya aure zai dena sa maka ciwon kai,” kallan uncle yayi ya d’auke kansa Sabida
maganar auren da yayi , sosai yaci abincin da James suka dafa ya kora fresh juice
yana hamdallah, ganin uncle yana ‘ko’karin zama a ‘kasane yasa bobo yayi saurin
mi’kewa “ uncle ya kamata ka huta haka , dare nayi ya kamata ka kwanta ka huta”,
jinjina masa kai uncle din yayi kafun ya furta” shikenan amma bari naje na ‘kara
duba yaran nan”, da Sauri bobo ya girgiza masa kai “ No uncle , bari zanje na duba
maka su,kaima kana bu’katar Hutu”, be jira amsar uncle d’insa ba ya zaunar Dashi
kan gado kamar Wanda ya samu little , har da lullu’ba masa tattausan blanket d’insa
fari me shegen kyau da laushi. Saida bobo ya tabbatar uncle ya kwanta kafun ya fito
daga d’akin hannunsa ri’ke da tray abincin da yaci, yana fitowa James dashi da wani
soja maisuna Samuel suka ‘karasa inda bobo yake da Sauri suka sara masa zasu Amshi
try din hannunsa ya girgiza masu kai , “ u can all go now (zaku iya tafiya yanxu )”
, yana kai karshen maganarsa ya ajje tray din akan dinning, ya wuce elevator , duk
sai da suka ga wucewarsa babu Wanda ya motsa sai bayan mintu na biyu , cikin Sauri
James ya wuce dinning yana ‘kara gayawa .

Bobo kai tsaye d’akinsu Little ya shiga gaba ki d’aya sun kwanta sabida yadda
d’akin yayi duhu, light d’in d’akin ya kunna, da sauri ya ‘karasa shigo ciki sabida
ganin yadda little yake bacci a zaune , prince kuwa baccinsa yake hankali kwance
cikin half gareran wando ko singlet be saka ba , ga Acn d’akin sosai yake fitar da
sanyi, gyarawa little kwanciyarsa yayi bayan ya Tottofa masa addua, gadon prince ya
nufa shima, 2 fingers dinsa ya had’a ya daddage ya d’akawa prince a damtsen
hannunsa, da Sauri ya farka kamar zaiyi kuka ganin Bobo tsaye a kansa yayi saurin
kallan jikinsa, bashiri ya nufi d’akin dressing d’in su ya shirya cikin night wears
d’insa cikin d’an sosa kai ya furta “ good night yaya bobo”. Kanshi bobo ya d’aga
masa kafun ya furta night too , yana kwantawa yaci gaba da baccinsa , girgiza kai
kawai bobo yayi saida ya tabbatar they’re all safe sannan ya bar d’akin, duk da
dare yayi sai da ya ‘kara tabbatar da lapiyan komai kafun ya nufi bedroom d’insa ,
shaf shaf wanka yayi ya shirya cikin flannel pajama ash colour , Daidai bakin
windows d’akinsa ya tsaya ko alamar gajiya babu a tattare dashi, motocin da su
Robbert suna fita ne suka shigo cikin gidan , cikin low speed, direct wajan wani
parking spaces suka nufa inda jerun manyan motoci suke , cikin sauri Robbert da
captain suka nufi motar bayansu, wasu samari biyu yaransu suka fito dasu waje d’aya
sai faman zaginsu yake cikin turanci yake furta “ kasan ko ni wanene da zaku kama ?
Dukanku sai kunyi na dama daga rana irin tayau dukan ku sai kun bar aiki har banzan
o ganku…” be kai ‘karshen zancan ba Sabida naushin da yaji a both side dinta ,
cikin azaba ya bud’e baki zaiyi ihu Robert ya fesa masa wani abu me shegen d’aci da
yasa ihun guduwa , d’aya guy din kuwa gabaki d’aya a maye yake sai faman tangad’i
yake ,duk abunda suke bobo yana kallansu , one of his work phone ya d’auka tare da
danna number 1 , cikin ‘kan’kanin lokaci phone work d’insu Robert ya fara
aiki ,muryar bobo da suka ji yasa suka ‘kara daidaita da sara masa dan sunsan yana
ganinsu “ina cikon na ukun?”, sarawa Robert yayi cikin girmamawa ya furta “ baya
town sir “, daga ‘bangaran bobo yana jin hakan ya saki wani simple smile da ya
‘kara masa kyau , kit ya kashe wayar ya nufi bed d’insa.

🍃🍃🍃🍃🍃

THE NEXT DAY

Tun kafin bobo ya fito ko ina na gidan angyarasa cikin zafin nama sabida gabaki
d’aya cikin gidan babu mace ko d’aya a gidan koda masu aikine , gabaki d’aya
sojojine suke aiki a gidan hatta abinci da gyaran gidan sojojine sukeyi babu single
mace a cikin gidan da sunan mai aiki. Kamar yadda suka saba kullum , musulman cikin
za a yi sallah tare dasu, ragowar kuma suna kula da tsaran gidan , kamar Robert da
kullum in bobo zaiyi sallah shima yana bakin masallacin ri’ke da bindigarsa.
Ana idar da sallah kowa komawa yayi ya shirya cikin kayan training d’insu, sojojin
gabaki d’aya dogon wandan sojojine a jikinsu sai singlet da suke sawa sanyin safiya
na Busasu amma ko a jikinsu, prince da little ma gabaki d’ayansu yau sun shirya da
wuri har sun Riga uncle iron man shiryawa, ‘karfe 8:30am suka gama motsa jikin su,
little sai faman duba inda bobo yake amma be gansaba tunbayan idar da sallar asuba,
prince kam ko ajikinsa dan yasan inda yake, kai tsaye dinning ya nufa yana jiran
uncle da su little.little Kuwa bedroom d’in bobo ya’kara duba wa still baya
ciki.”yaya prince ina yaya bobo ? Banganshi ba ?”, banza prince yayi masa tare da
danna wani abu kamar bell dake kan dinning da Sauri wasu sojoji sanye da black suit
su biyu suka fito atare ko wannansu cikin girmamawa suka sara masa“ serve me “,
kawai prince yace musu sabida gabaki d’aya bashi da jumurin yunwa, cikin cika
umarninsa suka fara bud’e masa manyan warmer din kan dinning , saida ya za’ba
abunda ya keso tukunna suka fara serving d’insa cike da ‘kwarewa, be dad’e da fara
cin abincin ba uncle da little suma duk suka ‘karasa , ynxu su james ne suka yi
serving d’insu duk yadda akai da little ya Za’bi abunda zaici ‘kin kula kowa yayi ,
hatta abincin ‘kin ciyayi sai hot coffee da shima ko rabi besha yace ya ‘koshi,
gabaki d’aya Prince da uncle kallansa sukai basu ce masa komai ba musamman “ wannan
rigimammen yaron yanxu ma wata rigimar kake shiryawa ko, toh wallahi ba ruwana a
ciki tsakaninka da yayyunka “ duk cikin zuciyar sa prince yake wannan maganar , shi
kuwa uncle murmushi kawai ya saki dan yasan inda rigimarsa ta dosa.mi’kewa little
yayi ya nufi wata door , prince zai tsayar dashi uncle ya hanashi .

BOBO
Yana shiga wajan da prince yayi wa la’kabi da “ THE DEATH PRISON” daki daban aka
sa samari biyun jiya da’aka d’akko, duk da wannan d’akin da suke ciki yafi na farko
amma shi wannan cikin d’akin wasu ‘kofofine a cikinsu har guda hud’u biyu ‘kanana,
biyu manya sai wasu ‘katan abu fari da bansan menene aciki ba , d’aya daga cikin
samarin ne ya taso azuciye cikin turanci ya soma magana “ kasan wanene ni?Kasan
wanene mahaifina ? Me mukai muku zaku zo ku d’akko
mu? “ wani irin kallo bobo ya jefa masa da ya kasa ‘karasa maganganun sa , kallansu
bobo yayi d’aya bayan d’aya musamman d’ayan saurayin da ya fi tsorata jikinsa har
ya fara karkarwa sabida kallan da bobo yake bunsu dashi,har ya ‘karasa wajan wani
table masu d’auke da box’s akai , cikin cool voice ya furta “ yana ina ?”, gudun
kar Logan ya tona masu asiri , cikin Sauri Dylan ya furta “ wa kake magana akai ?
Mu bamusan komai ba kuma zakuyi danasanin kawo mu nan gabaki d’aya..” be ‘karasa
zancansa ba sabida wani irin azaba da yaji a ‘kafarsa , da Sauri ya d’ago kansa
cikin zabura ya ja baya ganin bobo tsugunne a gabansa , sai kuma cikin Sauri ya
kalli ‘kafarsa , ‘karar azaba ya kuma saki Sabida yadda tools d’in da bobo ya caka
masa shiga cikin ‘kafarsa sosai , yanxun ma kallansu ya ‘karayi ganin Logan tun ba
‘a je ko ina ba ya soma fitsari a wando , cikin cool voice bobo ya furta “ my last
question! Yana ina?”,cike da tsoro Dylan ya kallo bobo ganin fuskarsa ba fara’a
kwata kwata, kafun ya kalli Logan da gabaki d’aya ya rud’e , duk da haka baya
tunanin zai fad’i inda yake , saidai kome zasuyi masa saidai suyi masa , Girgiza wa
Logan kai yayi alamar karyayi magana , cike da tsoro Logan ya kalli bobo da Robert
da yake tsaye bayan bobo da bindiga kafun ya ‘kara kallan Dylan , bai sai lokacin
da bakinsa ya furta “ NEW ZEALAND” lallausan murmushi bobo ya saki kafun ya kalli
Robert “ a mayar musu da kayansu su saka , and then ka sasu cikin “ THE EVIL ROOM”,
da Sauri Logan ya ri’ko kafar bobo hawaye harya fara ‘bata masa fuska “ we’re sorry
please! Munsan munyi lefi but a mistake is not a mistake until you repeat that
mistake is called a mistake ( kuskure ba kuskure bane har sai ka maimaita wannan
kuskuran yake zamowa kuskure )”, yanxu kam ran bobo ya fara ‘baci dukda yadda yake
‘ko’karin controlling kansa , sha’ko wuyan Logan da Dylan yayi a lokaci d’aya ya
buga kansu da bango , babu Wanda kansa be fasheba, sai dafe kansu da sukai waje
d’aya gabaki d’aya Logan ya gama rud’ewa har hawaye sun fara sakko masa a kumatu,
Dylan kuwa gabaki d’aya fuskarsa ja tayi sosai kasancewarsa farin Bature , kallansu
bobo yayi har yanxu yana ‘ko’karin controlling kansa , “ kuna kiran abunda kukayi a
matsayin kuskure ? Wanne daga ciki ? Dilar kwayar ? Ko kuma raping d’in mata da
kuke kuna bugar dasu?” Girgiza masa kai Dylan yayi dan shima ya fara tsorata sosai
“ please kayi hakuri ka fad’i ko nawa kake so zamu baka , ka kashe wannan maganar”,
kallan baku da hankali bobo yayi musu, tabbas sunyi nisa basa jin kira , be ‘karabi
ta kansu ba yabar d’akin duk da ro’kan da Logan yake masa . Suna fitowa cike da
girmamawa Robert ya mi’ko masa wata ‘karamar waya , tun kafin yace wani abu Robert
yayi saurin furta “ MSS ISABELLA”murmushi bobo ya ‘kara saki amaimakon ya kar ‘bi
wayar sai kawai ya nufi part d’insu.

A zaune ya tarar da prince lokacin uncle ya nufi bedroom d’insa “ ina little ?”
Cewar bobo,’kofar da ya nufa prince ya nuna masa “ Tun d’azu yake nemanka har yayi
fushi beci abunci ba “gashin kansa bobo ya shafa ,” and you kunci abinci?d’an sosa
kansa prince yayi , bobo na ganin haka ya juya ya nufi dinning area , cikin wani
unique plate yayi serving food aciki bayan ya rufe ya nufi ‘kofar da little ya
shiga . Nan ma wata doguwar tafiya ce me d’auke da white tiles kafun ya karaso wasu
dogayan ‘kofuna guda 5 dake Jere a wajan, Door d’in karshe ya nufa , yana bud’e
door d’in na furta wow,sosai Wajan ya had’u gwanin ban sha’awa ba komai ne a wajan
ba sai manya manyan Glass Tower masu shegen kyau kala kala , ga wasu irin colour
fishes da suke yawo a cikin ko wana tower glass, babban glass aquarium d’in da yake
farko wasu Mitsi mitsin Golden fish ne a ciki yan kanana kanana kalar golden da
yawa aciki , daga cikin glass d’in har da wani grass carfet a ciki da wani babban
dotse me ‘kofofi, sosai glass tower din yayi kyau musamman yadda golden fishes din
suke ta motsi cikin ruwa. Daka gefen hagunsa ma wani babban Glass tower ne amma be
kai girman na farko ba sabida babban shape d’in circle ne dashi daga inda kake kana
iya ganin wasu irin kala kalan kifaye da suka sha banban da na farkon, suma cikinsu
har da wasu design din shukoki da ‘kananan dutsuna suma kala kala , shima ‘kananan
fishes ne a ciki kala hudu, Orfe fish, Golden Rudd, Red shiners , koi carp fish ,
ko wan kifi a ciki da kalar jikinsa suma sai faman mosti suke a ciki, haka bobo ya
dunga ratsa manyan glass tower din fishes din har yazo kan Wanda yafi ko wanne
had’uwa gabaki d’aya jikin bangon wajan glass tower ne cike da Rosy Red Minnows ,
wasu irin kifayene suma da farko idan ka kallesu zaka d’auka jikinsu ne me colours
din sai ka matso kusa da glass din zaka ga ainahin transparent glass colour ne
jikinsu sai kalolin da ke cikin fatar su, gabaki d’aya wajan gwanin ban sha’awa ,
ko ina ka wai ga zaka fishes na yawo cikin ruwa. ‘Karasa shigowa ciki bobo yayi kan
wani unique table me zaman mutum hud’u ya zauna tare da ajje plates d’in hannunsa ,
“ come out “, cewar bobo , daka wani jikin bayan glass tower Little ya Fito bayan
ya gama barbad’a musu wasu powder me kama da abinci ganin yadda suke rububin zuwa
wajan , wani medium sink bobo ya nuna masa da hannu, shima little Wajan ya ‘karasa
tare da wanke hannunsa da wani hand wash me shegen ‘kamshi , plate d’in abinci bobo
ya d’auko tare da d’aukar spoon , kamar wani ‘karamin yaro ya d’ebo abincin ya kai
bakin Little dake kunbure kunbure , kadan ya bud’e bakin bobo ya tura masa French
Toast d’in dake cikin fork d’insa , shima little d’aya fork d’in ya dauka tare da
knife ya yanka waffles d’in gefe ya kai bakin bobo , ba musu ya bud’e masa
bakinshima ya sa masa waffles d’in babu Wanda yayi magana har saida suka kammala
cin breakfast d’in nasu “ Now kaganni ai ko? Stop been so stubborn, naje na d’anyi
wani aikine, be a good boy inna fita na dawo na tarar kayi wani laifi this time
around zan hukunta ka , ok?”, curly hair d’inshi da ya sha gara little ya girgiza
masa “ yaya bobo , I have something for you, wait for me kaji?”, be jira cin amsar
bobo ba ya fita daga wajan a guje , girgiza kai bobo yayi, a fili ya furta “ Adil
will always be Adil “, ko mintuna biyar be yiba ya dawo sai nishi yake, p-cap d’in
ya fara mi’kawa bobo da ya zaro ido kamar ya ga wani babban gift har da saka wa a
kansa , little box d’in da little ya ‘boye ya mi’kawa bobo,kallansa bobo yayi “ for
me ?”, murmushi Adil ya saki lokacin da bobo ya bud’e box d’in , with much surprise
akan fuskarsa ya kalli unique design diamond bracelet d’in dake jikin ‘karamin
box , kafun ya ‘kara maida kallansa kan Littel “ for me ?” Curly hair dinsa little
ya ‘kara jijjiga masa , har yanxu da mamaki a kan fuskar bobo ya ciro bracelet d’in
da sai faman shinning yake , sai mutum ya kula sosai zaisan da suna a jiki, hugging
d’insa bobo yayi “ finally little ya zama big boy yanxu “, dariyar da ta ‘karawa
little kyau ya saki da har saida dimples dinsa ya lotsa ,” let me help you “, cewar
little , mikawa masa bracelet d’in bobo yayi da kansa ya saka masa , a tare suka
ri’ke hannun juna kamar wasu friend suka fito daga cikin “ THE DREAMER FISH ROOM “.
Lokacin da Suka fito parlourn prince na zaune shida uncle ,kallansu uncle yayi
kafin ya harari little “ yanxu kaga yaya bobo d’in aiko?” Da Sauri little ya
‘karasa Wajan uncle din tare da hugging d’insa , “ my uncle I missed you “, ture
shi daga jikinsa uncle yayi “ daga baya kenan” gabaki d’ayansu babu Wanda beyi
dariya ba , a Gogon diamond d’inshi bobo ya kallan ganin almost 11 yasa ya nufi
elevator , shaf shaf ya nufi part d’insa , ba zauna a ciki ba direct toilet ya nufa
almost 2 minutes ya fito cikin wata ash bathrub har ‘kasa , door cikin gefen toilet
d’in ya nufa almost 10 minutes kafun gabaki d’aya part d’in ya bad’e da kamshin
ROJA , tun kafun ya futo sassanyan kamshin turaran Roja ya bad’e ko ina na cikin
d’akin. Door d’in kofar da aka bud’ene yasa na mayar da hankali na kansa ,
fatabarakallahu Ah sanin kali’kin, tubarkallah Masha Allah, sanye bobo yake cikin
wasu irin da kakken uniform d’in sojoji black colour , daga gefe gefen shoulder
d’insa wasu golden stars ne guda hudu sai faman shining suke kwanin burgewa, daga
jikin rigarsa a ‘bangaran hagu wasu abubuwane masu kaloli a wajan daga ‘kasan sa
kuma wasu tanbura ne a wajan da bansan ko na menene ba. Daga side d’in damansa kuma
wani tag ne a Wajan ‘kasan sa da harafin General A.M.A, a jiki, sosai uniform d’in
yayi amsa kyau musamman damtsen hannunsa da ke sanye wani barge, daga gefe gefe
wandan jikinsa ma wasu dogayan golden d’in line ne a both side d’in , ba ‘karamin
haduwa yayi ba na bugawa a jarida , bai saka hular ba , sai curly hair d’insa da
yake askewa fitowa sosai musamman gyara da ta samu, ra tsats tsen diamond watches
d’insa ya kalla kafun ya Fito daga part d’insa cikin takun jarumta, yanxu ma ta
elevator ya sakko, su little na ganinsa shi da prince , cikin sauri suke mi’ke suka
sara masa ,dariyar abunda sukai uncle yayi kafin ya mayar da kallansa kan bobo da
babu fara’a a kan fuskarsa,Kai tsaye inda suke bobo ya nufa “ take care ! Yanxu ma
kamar wasu sojoji suke amsa da yes sir , kanshi kawai ya Jinjina musu kafun ya nufi
kofar futa . Suna ganin ya fita kowannansu ya zube kan kujera yana sauke a jiyar
zuciya . A waje kuwa , wasu manyan lamborghini veneno masu shegen kyau gabaki d’aya
tinted cars ne black colour, ga karatan sojoji ko wannansu cikin uniform d’insa,
bobo na Fito wa cikin wani irin salo suka sara masa” salute sir “, tare da ‘kamewa,
shima right hand d’insa yasa yayi salute , kafin cikin unique way Robert ya bud’e
masa door , yana shiga ba’a bata lokaci ba jerun motocin da a’kalla zasu kai goma
suka fita daga cikin gidan , Robert ne ya furta “ sir “, dakatar dashi bobo yayi ta
hanyar furta “ BARRACK”.

✨✨✨✨✨✨

NIGERIA

ABUJA STATE _!

Misalin ‘karfe 3:00am na safe aka bud’e kofar store d’in da aka kulle Abla a ciki,
wani ruwan datti me shegen wari Debeka ta watsawa Abla a jiki , a firgice ta farka
bakinta na anbatan “ HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKIL”, bakin ta da take adduar Debeka
ta buge mata da bokiti da yasa Abla bud’e dara daran ash colour eyes dinta, duk da
gari be gama wayewa ba hakan be hana kyawawan idanuwanta ‘kara fitowa sosai
ba.kallan jikinta da aka watsawa ruwan datti tayi ga sanyi sanyin da ta fara ji
lokaci guda Sabida sanyin ruwan, Debeka na tsaye sai faman hura hanci take tana
girgiza ita kadai, cikin tsantsan tsanar da takewa Abla ta soma magana “ Dan ubanki
zaman me kike da bazaki mi’ke ki soma aikin kiba ? Shegiya me farar ‘kafa , na
tsaneki! Na tsani duk wani me san ganin farincikin ki! Ni d’innan sai na zame wa
rayuwarki kabari, Indai ina raye sai na Mayar dake karuwa , irin karuwar da kwanda
kare a kanki, sai na lalata miki rayuwa gabaki d’aya , ki tashi stupid ki fara
ayyukan ki dan yau gabaki d’aya ke zakiyi komai na gidan nan Dan ubanki “ ta
‘karasa tare da sakar wa Abla rankwashi aka dayasa ta dafe wajan . Jiki a sanyaye
tayi ‘ko’karin mikewa gabaki d’aya jikinta ba kwari musamman zazza’bi zazza’bin da
taji yana ‘ko’karin kayar da ita, ganin yadda take tafiya a hankali yasa debeka
cike da mugunta ta hankad’ata har saida ta fad’i , bata jira mi’kewar Abla ba ta
jata a ‘kasa kamar kayan wanki har saida tafito da ita babban falon tukunna tayi
wurgi da ita . “Hour biyu na baki ki share ko ina na gidannan, kije ki wanke komai
da aka ‘bata sannan duk d’akin da kika shiga ki tattare mun condums d’in da sukai
anfani dashi ki kawo mun, saura dan ubanki ki sa na zauna zaman jiranki,” tana kai
‘karshen zancanta ta buga tsaki tare da barin Wajan . Bin falon Abla ta somayi da
kallo take tsoro ya fara shigarta ganin ba kowa a falon cikin dare sai ita , sabida
tsabar mugunta irin ta debeka ga baki d’aya fitulun ta kashe sai wata mara Haske da
ta bar mata gud’a d’aya . Karkarwar da jikinta ya somayi ne ya ta tsugunna, ga
kayanta jikakku da sanyi ke faman ratsa ko ina na jikin ta, ga zazzafan zazzabin da
ya fara rufeta , gefe d’aya ga cikinta da yake murd’a mata sabida yunwar da
takeji . ‘Karar yunwa da cikinta ya ‘karayine yasa ta dafe cikin nata da duka
hannayenta biyu , cikin rawar murya ta furta “ la’ilaha illa anta subhanaka inni
kuntun minazzalumin , ya Allah kaine kace muro’ke ka , Allah kaga halin da nake
ciki , kafi kowa sanin abunda yafi dacewa dani , Allah na ro’kewa ka karemun
zuciyata daga fad’awa cikin halaka, Allah na ro’keka kasa na zama me tawakkali da
kawo kukana wajanka,Allah kai Arrahim ne , me rahma, Allah kasa ina cikin wannan
rahama taka , Allah nagode maka a yadda Kayini, Allah na ro’keka ka kareni daga
cikin Sharrin masu sharri,ka nesantani da aikata sa’ba maka “.muryarta da ta ‘kara
dusasewa tayi shiru lokacin da cikinta ya ‘kara mund’a mata, yadda ta rungume
shafaffen cikinta gwanin tausayi amma duk da haka babu ko d’igon kukan da ya sakko
kan kyakkyawar fuskarta.a hankali ta ‘kara d’ago da dara daran idanuwanta tana bin
ko ina da kallo kafun ta yun’kura ta mike tana tafiya a hankali tun lokacin da
Debeka ta hankad’ata ‘kafarta ta rike amma a hakan ta fara gyara kaca kacan falo
dake cike da kayan kwalabe, kwanukan abinci har kazantar da bai kamata a samu a
falon ba , haka ta Samu ta gyara shi da ‘kyar sai faman nishi take . Tana gama
gyarawa sama ta hau d’akin da babu mutane shima haka ta shiga ta gyarasu Saura
kad’an amai ya kwace mata da kyar take shiga d’akin ko ina ta duba zaka condums ne
da wasu abubuwan , a maimakon ta tarawa debeka abunda ta bu’kata sai gabaki d’aya
ta zuba su a shara , ta gyara band’akunan da ya gama cika da ‘kazanta, d’akin da ta
gyara na ‘karshe sai da amai ya kwace mata , gabaki d’aya ta galabaita jikinta yayi
weak . Zuwa wannan lokacin 5:30 yadda a gogo ya nuna wa tahee and tabbas tasan
debeka ta koma baccin da take, cikin Sauri ta nufi hanyar da zai sadata da
d’akinsu, tana shiga komai a hankali take har ta kunna kwan d’akin shirgin dasuke
kira d’aki yanxu . Tsayawa ‘karewa d’akin kallo Abla tayi ganin sabuwar babbar
katifa da akasa a d’akin ga ledojin kayan ciye ciye da suka ci, su su ukune kwance
akan katifar daga husna sai Arwa da Aneesa , mamakin inda ilham take a wannan
lokacin Abla ta fara ganin bata da lokaci sosai yasa ta d’auki ragowar kayanta da
ya rage mata , cikin Sauri ta fad’a toilet tayi wanka da ruwan sanyi me shegen
sanyi tare da abun buhun da ya zame mata tamkar soso haka take sawa a jikinta dukda
ba dadin anfani takeji dashi ba, sosai Abla ta wanke jikinta da tankad’addiyar
kasar da ta zame mata tamkar sabulun wanka, sai data gamane idanta ya sauka kan
wani guntun sabulun wanki kmar wacce akayi ba babbar kyauta haka ta samu ta ‘kara
wanke jikinta sosai, kayan ta da debeka ta ‘bata mata ma ‘kasa ta samu ta wankesu
sosai ta shanyasu bayan ta sakar ragowar yargalalliyar rigar da zata Iya du’kar
‘kirji take kayan ta ne , dogon hijab d’inta Amma debeka har dashi ta ‘bata mata ,
dogon mayafinta da shima ya gama kod’ewa ta yana a jikinta Daidai lokacin da ake
kiran sallah, ‘kofar d’akin ta kulle kafun ta tayar da sallahrta, tana idarwa bata
jira tayi addua ba Sabida kar mutanan falon su Fito su tarar da ita tana sallah,
sallar isha’i da batayi jiya ba ta samu tayi tana raka’ar karshe zatayi sallama
akan idan debeka da ta ‘kara farkawa , tahee na tahiyar ‘karshe da sauri debeka ta
juya Adaidai lokacin da Abla ta idar da sallarta zata soma addua taji saukar abu
meshegen zafi kamar katako a jikinta , ba abunda take sai ‘ ko’karin kare jikinta
da take yi yadda debeka ke jingarta kamar Allah ya aikota da muciya, Abla ko ihu ta
saka ganin yadda su Arwa suke bacci gashi ko d’igon hawaye babu akan fuskarta saida
debeka ga jibgeta sanranta kafun ta ‘kara janta kamar wata kayan wanki, a wannan
karan kukan da takeso tayi ma ta kasa sai kukan zuci daya fi komai ta’ba zuciyar
mutum, amma dukda haka Abla godewa Allah take ganin saida ta fara sauke abunda ke
kirjinta na sallar da tayi, a zuciye debeka ta kalleta bayan ta jefata wajan wanke
wanke “ ki tabbata kin wanke komai da komai dake wajan nan , idan kika kuskura nazo
na same ki baki kammala ba na lahira sai ya fiki jin dad’i, shegiya me kama da
aljanu”, sai kuma ta juya fuuuuuu tabar Wajan. Kallan tunin uban wanke wanken da
aka ‘bata tayi kamar wa’yanda sukai sati basayin wanke wanke amma tsabar ‘Kazan
tace kawai , kafin ta mayar da kallanta kan klin din da aka bar mata kwalli d’aya
da ko rabun wanke wanken bazai wanke su ba. Gugar rijiya ta d’auka , ta d’au tsawan
lokaci tana d’ebo ruwan wanke wanken kafun ta soma had’a kwanukan, komai cikin
‘karfin hali take yinsa ganin jiri jiri na neman kwasarta ga uban yunwar da takeji
kamar hanjin cikinta zasu fito waje , Arwa ce ta Fito tsakar wajan sanye da wani
guntun hijab d’inta , tana ganin Abla tayi saurin ‘karasowa wajan wanke wanke , “
Abla” ta furta a hankali , da Sauri Abla ta d’ago eyes d’inta da take ganin biji
biji ta zubasu akan Arwa , itama murmushin Abla ta sakar mata “ finally kin Tashi
ko? Hope kinyi sallah “, wajan d’oraya Arwa ta ‘karasa kafun ta furta “ Nayi Abla ,
bari na taya ki d’aure kwanukan sai muyi saurin gamawa “, a hankali Abla ta furta “
nagode Arwa “, Arwa bata ce mata komai ba sai d’orayar da ta somayi mata , jefi
jefi kuma suna d’an yin hira kad’an kad’an. Sai wajan ‘karfe 9:10am suka kammala
wanke wanken lokacin sosai kuwa Abla ta jigata , ji take kamar kayan cikin ta zasu
fito waje , kamo hannunta da Arwa tayi ne yasa ta mayar da dubanta zuwa wajanta,
sai da arwa ta duba gefe da gefen ta gudun kar wani ya fito , kafin cikin ‘kasa
‘kasa da murya ta furta “ Abla akwai abunda nake so na fad’a miki…”, kallan ta
sosai Abla tayi ganin kamar akwai abunda yake damunta “ shikenan inajin ki Arwa “,
‘kara maida dubanta Arwa tayi gudun karwani ya shigo wajan “ Dama Abla ….” Bata
‘karasa zancenta ba taji taku da Sauri tayi shiru tana kallan hanyar shigowa ,
Zinariyya ce ta shigo wajan tana bunsu da wani shegen kallo , kafun ta tsayar da
kallanta kan Arwa da jikinta ya fara rawa, a yatsine ta nuna mata hanya “ kije ana
kiranki yanxu “, kallan Abla , Arwa tayi kafun tayi saurin barin Wajan , “ke “
Zinariyya ta dakawa Abla tsawa , kallanta abla tayi batare da tace mata komai ba
dan magana ma wahala take mata yanxu “ ga wanki na can kije ki kwasosu, idan kin
d’akko ki biya ki d’akko na yar shila da na debeka, gabaki d’ayansu hour 1 na baki
ki wanke su duka “, shareta Abla tayi zata wuce Zinariyya ta janyo hijabinta har
saida ya yage, ta d’aga hannu zata mareta Abla tayi saurin rike hannun , a zuciye
cikin disashewar murya ta soma magana “ kashe ni kuke san kuyi ? Me nayi muku?Me
nayi muku Haka da kuka tsaneni? Me kuke so a waje na ?Me na tsare muku haka ?”, a
maimakon ta bata amsar tanbayoyinta sai ta soma bin jikinta da kallo “ ke kyakkyawa
ce,sannan duk Wanda ya ganki zaiso ya kashe ‘kishirwarki, ni na miki al’kawari
Indai zaki dunga kashemun ‘kishirwata to zakiji dad’in ki aduniyar nan zakiyi
abunda kike so , abu d’aya nake so kawai ki bani kanki, ba wani dogan abu bane zamu
dungayi fa , dad’in junanmu kawai zamu dungaji “, ta ‘karasa tana taunar le’banta,
dogon tsaki Abla ta saki tayi wucewarta, batasan sau nawa zatayi musu magana ba ,
dole ne ? Mai yasa kowa bazai temake ta dan Allah ba sai ya saka zancan yana san
jikinta ? Allah kai ne ga tana , Allah ka nesan tani da aikata wannan mummunar
aikin da zan sa’ba maka “, gabaki d’aya wad’annan zantukan a zuciyarta Abla
takeyinsu har ta ‘karasa shirgin store d’in da suke kira d’akinsu . A zaune ta
tarar da Husna da Aneesa suna yin breakfast, “ Abla na d’auka ba kya nan ai, ki zo
muci abinci mana “ girgiza mata kai Abla tayi tana zama kan kwalin da take kwana “
Karki damu Anee na ‘koshi, ina ilham ? Banganta ba “, Aneesa zatayi magana aka turo
‘kofar toilet d’in d’akin , ilham ce ta Fito d’aure da zani da Alama wanka
tayi tana ganin Abla tayi saurin ‘karasawa Wajan ta tare da hugging d’inta “ kiyi
hakuri Abla yanxu nake shirin zuwa wajan ki sai gashi kin shigo , Kinci abinci ?”,
jinjina mata kai Abla tayi “ nashigo d’akin d’azu amma banganki a cikiba, a ina
kika kwana ?” Sun kuyar da Kai ilham tayi “ kiyi hakuri abla na kwana a d’ayan
store d’in ne Sabida kar su Zinariyya suce zasuyi mun wani abu ne “, okay kawai
Abla ta ce mata , tana bin Husna da taja dogon tsaki da kallo, “ ke komai sai kinyi
shish shigi a ciki? Ina ruwanki da inda ta kwana ? Ko a shago taje ta kwana ina
ruwanki? Idan ke bakyasan kiji dad’in rayuwarki ki ‘kyaleta mana ana dole ?”, cewar
husna da tunda Abla ta shigo ta had’e ranta , amaimakon ran abla ya ‘baci sai ta
sakar mata d’an guntun murmushi “ husna kibi duniya a sannu, idan baki bita a sannu
ba to tabbas ke zata koyawa hankali, Menene abun burgewa a sa’bawa mahalicci? Kina
ganin wannan hanya ce me kyau da kike maganar jin dad’in rayuwa? Karki manta Allah
da ya saki cikin wannan rayuwar ba mantawa yayi dake ba “, da Sauri husna ta d’aga
Mata hannu “ bani da lokacin jin wa’azin ki, in wa’azi zakije ki tafi masallaci,
kin ganni nan yanxu na fara rayuwa , yanxu nasan dad’in rayuwa , jin dad’in rayuwa
kuma yanxu na fara dan sai na tara dukiyar da duk inda nashiga za’a kalleni “
d’auke dubanta Abla tayi ta mayar dashi kan Aneesa da tayi shiru tana binta da
kallo kamar akwai abunda yake damun ta , amma itama batace mata komai ba shiyasa ta
mi’ke ta nufi hanyar fita daga d’akin , tana jin muryar Husna da ke furta “
munafuka komai zakiyi sai kin nuna mana kin fimu sanin Allah , ke ubanwa yasan me
kike aikatawa da Alama ke tuni aka gana kwakuleki shine mu kike mana ba’kincikin
kud’in da zamu samu”, lumshe idanuwanta abla tayi da suka soma yi mata yaji , tana
fitowa babban falon gidan ta tarar da Zinariyya da yar shiga a zaune suna duba wasu
hotuna , “ ke “ yar shiga ta daka wa Abla tsawa, banza Abla tayi musu dan ranta ya
soma ‘baci yanxu , “ dan uwarki ba dake nake magana ba “ da Sauri rai a ‘bace Abla
ta jiyo ta zuba mata eyes d’in ta , kallo d’aya tayi mata ta d’auke kanta har ta
nufi hanyar fita da ga gidan gabaki d’aya . Kallan shila , Zinariyya tayi “ Anya
babe wannan yarinyar ba aljanune da ita ba ? Nifa wallahi tsoro take bani ko me
kika ga inayi mata cikin ‘karfin haline kawai nake yi , musamman idan ta zuba maka
wad’annan shegun idanuwan nata kamar na mayu , gashegen kyau kamar aljana “. Itama
yar shila tsaki taja “ ni kaina shegiyar nan wani lokaci tsoro take bani , amma ba
aljana ba Wlh ko uwar aljanace sai na kashe ‘kishirwata akan ta , ki duba kiga
‘kirjinta , a cike yake tam ko ni da maza suke ta’ba nawa haryanxu basu kai nata
girma ba , ga uban hips da take dashi , haushina ma yadda take saka hijab kullum
bata bari ina ganinsu sosai Kema kinsa wallahi ba ‘karamin dad’i zatayi ba .”gabaki
d’aya sai suka ajje hotunan da suke kalla suka soma zanjan Abla da surarta da irin
sha’awar da suke mata .

PAY YOUR 300 through 2681892316 Aisha umar zenith bank sai a turo da shaidar biya
ta wannan number 07041879581.

LEESHARH DATA HUB 2


MTN
1gb-240
2gb-480
3gb-720
4gb-960
5gb-1200

AIRTEL
1gb-300
2gb-600
3gb-900
4gb-1200
5gb-1500

Validity 30 days

Account number : 2681892316 Aisha umar zenith bank .

Phone number : 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of Love and Destiny)

Story & written


By
Mss Lee✨

Littafin IBTISSAM na kud’ine akan 300 , me san karanta littafin har ‘karshe zai
biya kud’insa ta wannan bank din , 2681892316 Aisha umar zenith bank , sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Masu san yimun magana zasu iya yimun direct through my WhatsApp number kamar haka :
07041879581.

__💞”Be like a diamond, precious and rare , not like a stone, found every where. “💞
__

💕___BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ___💕

BOOK 1

SORRY ! NOT EDITED.


Season_9

NEW YORK

Yau gabaki d’aya tun bayan fitar bobo ya nufi The main reading room d’insu ,
wajan sosai yake da girma ga wasu jerun books dayawa a wajan, da fari idan ka kalli
wajan zaka d’auka office ne dan har wani chairs ne a Wajan masu ‘kayatar wa daga
cikin su akwai wacce duk tafi ko wacce kyau a cikin kurejun, fari tas da ita ,
sosai d’akin ya tsaru cikin unique way, duk da d’akin karatune sosai mutum zaiyi
mar marin zama a cikinsa. Little ne a zaune kan d’aya daga cikin ba’ka’ken unique
modern chair d’in cikin d’akin, gabaki d’aya hankalinsa na kan system d’in da yake
operating cikin ‘kwarewa da basirar da Allah yayi masa , dan Adeel irin mutanan nan
ne da ake kiransu da gifted sosai yake da baiwar fahimtar abu, daga gefensa kuma
wani medium bwol ne me cike da kayan chocolate a ciki gwanin ban sha’awa , yana
cikin dannan system d’in sa , Prince ya shigo cikin office d’in, sanye da jan riga
me dogon hannu, sai ba’kin wandon da ya saka , da kad’an ya wuce kwiwar
‘kafarsa ,sosai farar fatar ‘kafarsa ta fito waje, tsadaddiyar wayar hannunsa da
yake dannawa ‘kirar iphone 15 ya saka a aljihu kafun ya d’auki d’aya daga cikin
chocolate d’in dake bwol d’in Adeel “ Little me kake yi haka? Naga ka nutsu?”, ‘kin
kulasa little yayi Sabida yadda ya bawa abunda yake yi cikin system muhimmanci ,
ganin ya ‘ki kulasane yasa prince dauke system d’in daga gabansa gabaki d’aya , da
Sauri little ya d’ago fuskarsa , yadda yayi da fuska kamar wani d’an shekara goma
sabida gyaran askinsa da yake rufe masa ido “ Haba yaya prince , abu fa nake me
muhimmanci , please ka bani “, ya ‘karasa yana mi’kowa prince hannunsa , ‘kin basa
system d’in prince yayi “ da iskancine ya hana ka amsa mun maganata? Toh bazan
bayar ba , ko me kake ka bari kayi shi daga baya “, ‘kara kai hannu little yayi zai
d’auki system d’insa prince ya ‘kara gocewa ya hanasa , a hankali ya furta “ please
yaya prince ka bani, I told you abu nake yi fa “ cikin wata sofa prince ya zauna
kafun ya nuna wa Adeel waje “ oya zauna , maganar 5 minutes kawai zamuyi sai kaci
gaba da danne dannenka “, yasan in bazama yayi ba prince bazai bashi system d’in ba
, aikuwa prince yana ganin Adeel ya zauna ya matso kusa dashi “ Yawwa ko kaifa
little , kasan wani abu?”, bai bari little ya amsa masa ba ya cigaba da maganarsa,”
yau friend d’ina yake birthday d’insa , And nine best friend d’inshi kaga ya kamata
naje ko?”, kallansa little yayi tare da d’auke kansa kamar Wanda aka sa dole “ Toh
ni me ya shafeni da birthday d’insa ,Kawai ka bani system d’ina “, cikin lallashi
shima prince ya kallesa “ Haba mana little din mu, little din big boss da yaya bobo
, shalelen uncle iron man, please rakani zakayi shaf shaf mu dawo kafun yaya bobo
ya dawo , please, please “, Nifa ba ruwana yaya prince Allah kasan yaya bobo ya
gano mun fita sai ya hukuntamu ko? Kuma yaji kamar yaya big boss ne fa yaji, Nidea
baruwa na “, cewar Adeel , a zuciye prince ya mi’ka masa system d’insa ya mi’ke “
kar kaje d’in i though you’re my dearest brother , just dan zaka rakani birthday
zaka ce mun ba ruwanki ? Fine ! Nima babu ruwana da kai”, yana kai ‘Karshen
zancensa ya juya , dukda har cikin zuciyarsa ba Dagaske yayi wa little fad’a ba
yasan wannan shine kad’ai solution d’in da ya rage masa , shashshe’kar kukan Adeel
da ya jine yasashi ya juyo a rud’e yana kallansa “ kuka ? Kuka kake ?”, hannunsa
duka biyu Adeel ya saka ya kulle fuskarsa , hankalin prince ba ‘karamin tashi yayi
ba lokacin da ya ga hawaye akan fuskar little , hannunsa d’aya ya saka ya mari
fuskarsa “ Ni da kaina nasaka little kuka ?”, ya ‘kara saka hannu ya mari fuskar
tasa da ‘karfi har yana d’an bada sauti, ya d’aga hannusa da Niyar ‘kara marin
kansa little ya rike masa hannun yana goge hawayen fuskar tasa , kamar wani d’an
yaro ya turo bakinsa “ nifa ba kuka nake ba , abune yashigar mun ido”, am sorry
little ba Dagaske nake maka ba danayi maka fad’a , please karka ‘karayin kuka ko
kad’an ,kamanta promised d’in da kayi wa yaya big boss da yaya bobo?kamanta kace
bazaka yi kuka ba ? Kana san yaya big boss ya hukunta kowa a gidan nan?” Da Sauri
little ya girgiza masa kai “ okay am sorry , zuciyata batamun dad’i idan kana
hawaye , please ka dena kaji” amma yaya prince ba kaine kake fushi dani ba ? Zan
raka ka amma sai dai muyi 1 hour mu dawo , kasan yaya bobo ya dawo ya tarar mun
tafi yawo ranshi zai ‘baci”, hugging d’insa prince yayi “ Yawwa little d’in mu
that’s why I love you , I promised bazamu dad’e ba , kafun yaya bobo ya dawo nasan
mun dawo cikin gidan , taso muje mu shirya , shaf shaf kar lokaci ya ‘Kure , hakan
ce kuwa ta faruwa , basu d’au dogon lokaci ba suka shirya , ko wannan su cikin
shigar ‘kananan kaya , gabaki d’ayansu sunyi kyau sosai , kana ganinsu kasan Jini
d’aya ne , abunda ya wanci ke banbantasu gyaran gashinsu, prince gabaki d’aya
gashinsa baya rufe masa goshi kusan irin gyran gashin bobo yake , sa’banin little
da kullum gyaran gashin kansa da yake sakko masa har wajan idanunsa .
Yanxu idan yace su tanbayi uncle shima zai iya hanasu shiyasa baibari Adeel yayi
maganar saba yaja hannunsa zuwa compound d’in, Suna fitowa wasu jerun manya manyan
motoci ne kusan guda 10 ba’ka’ke ‘kirar Mercedes Benz 300 SLR, motar tsakiya ma
ba’kace sa’banin ta sauran wannan bullet proof ce , bullet baya shigarta, duk da
ba’a san ransu suke fita da securities ba, amma basu da choice dan dokar Big Boss
ce wannan, kuma babu Wanda ya isa ya tsallaketa,
Mota d’aya prince da little suka shiga , suma ragowar jami’an sai da suka ga
shigarsu mota kafin su hau tasu, slowly motocin suka fara nufar first gate , har
suka zo second gate a slow suke tafiya , suna zuwa gate d’in ‘karshe wani
murd’ad’d’an soja sanye da ba’ka’ken kaya ya sara wa Adeel, cike da girmamawa ya
furta “ sir the black card”, shi prince gabaki d’aya ya manta da wani black card,
and yasan yanxu black card d’innan a hannun yaya bobo zasu sameshi, idan yace zai
koma ya d’akko a d’akin yaya bobo zasu ‘kara mata lokaci ne,” bamu fito dashi ba”
cewar little, yanxu ma cike da girmamawa sojan ya furta “ sorry sir , I can’t let
you, is an order”,wani irin haushine ya kama prince bai tsaya sauraran sojan ba, ya
basu umarnin Suja motar su fita . Cikin d’an jin Shakka driver da sojan su ka kalli
prince sabida suna fita sunsan me zai faru , “ me kake jira? “ cewar prince , deep
inside him shima fargabarne sabida karya doka da yayi, amma duk da hakan dole sai
yaje birthday d’innan , ba musu driver yaja motar , shima sojan sara musu yayi tare
da komawa gefe , umarnin bobo ne dama duk Wanda ya nemi karya doka a rabu dashi ya
karya d’in , ta cikin Wajan fitar motoci combo d’in su prince suka bi bayan
scarning d’in da na ura tayiwa motocin .

Ko mintuna 10 basuyi da fita ba , motocin bobo suka sha kwana , tun kafun ya
‘karaso a ka bud’e masa kofa , ta cikin motar ya ‘karewa sojojin dake tsaye kamar
an dasasu kallo har suka bar wajan,duk da uban jerun motocin da koshi bazai
irgasuba da securities suke hawa amma kallo d’aya yayiwa wajan parking d’in yasan
anfita dasu daga ciki, “ who go out ?” Ya tanbayi kansa cikin zuciyarsa , babu
Wanda ya fad’o masa arai sai prince da Adeel , shiyasa Robert yana parking be tsaya
ba yashiga cikin gida , shiru falourn babu kowa a cikinsa sai kamshin turare
electric da yake tashi, ga sanyin da ya cika ko ina na falourn sabida Acn da suke
kunne gabaki d’ayansu ,part d’in uncle ya shiga , zaune ya tarar dashi hannunsa
d’auke da jaridarsa da take karanta tawa , yana ganin bobo ya ajje ta gefe “
welcome back! How was the trip ?” It was great and annoying “, dariya ya bawa uncle
wai it’s was great and annoying “, uncle ina prince and little ? They went out
again right ?” Uncle be bashi amsar tambayarsaba sai ma wata maganar da ya bullo
masa dashi “ ya kamata ka huta first kafun komai ya biyo baya “, no uncle kasan
prince bayajin magana a Times , and shi zai saka little su fita tare , today I will
get the hell out of them “, gashin kansa uncle ya shafa “ cool down bobo , nasan
bazasu dad’e ba zasu dawo kawai suna bu’katar fresh air ne “, they are not serious
Uncle , na tabbata big boss yaji futarsu just like that , he won’t care tsaf zaisa
a kawo masa su har Inda yake and bazasu ji dadin gamuwarsu ba , uncle I don’t think
sun fad’a maka zasu fita ma ? Wad’annan rabbit suna samun ciwan kai “, cike da
dariya uncle yace “ prince da little ne rabbit d’in,? Just cool down , nasan bazasu
fi 1 hour ba zasu dawo and karka ce zaka hukunta mun yarana “, Mikewa tsaye bobo
yayi “ uncle ai dole na hukuntasu tunda basaji , let me go and fresh up”, yana
magana yana juyawa , cike da kulawa uncle yace masa , “ make sure kaci abinci
sannan ka kwanta ka huta , okay ?” Okay , cewar bobo yana barin part d’in wani
number yayi dialing cikin tsadaddiyar wayarsa ‘kiran Samsung, ana d’aga wayar ya
furta “ Follow them “, daga nan bai ‘kara cewa komai ba ya kashe wayar tare da
nufar part d’insa.

✨✨✨✨

Kai tsaye motocin su*** PRINCESS MANOR CATERING HALL****suka nufa, sosai wajan ya
‘kawatu tun daga Wajansa zaka gane sai d’an wane da wane ,duk da ba wani girma ne
dashi sosai ba amma yayi bala’in kyau , inda babu mutane sukai parking motocinsu,
shi dai little gabaki d’aya hankalinsa yana kan gida bayaso ran su yaya bobo ya
‘baci , gashi har yanxu hankalinsa bai kwanta a wajan ba , jan hannunsa da prince
yayi ne ya dawo dashi daga cikin tunanin da ya fad’a , prince bai bari securies sun
biyo su ciki ba sai mutane 2 masu sanye da suit, daga bakin wajan akwai wani A
domino mask da ake sakawa , iya rabin fuska da ya ke kulle Wajan idanuwa, suma shi
suka saka kafun su shiga ciki, cikin hall d’in sosai ya ‘kawatu ga wasu shinning
light da suke fitowa , kamar c d suke had’a parting su, duk da akai maza da mata
amma kowa da side d’insu , friend d’insa da ya janyo ya nufa , shima friend d’in
yana ganin sa sukayi shaking hannu , “ happy Birthday Charles “, Wanda aka kira da
Charles shima fuskarsa sanye take da domino mask , “ thank you prince “, ya fad’a
suna hugging d’in juna, kallan little da sai faman duba a gogon hannunsa yake ,
kafun ya furta “ Hey”, banza little yayi dashi , still Charles be hakura ba ya kara
ce masa “Hey”, ynxu ma little sharesa yayi, kallansa prince yayi kafun ya kalli
little ganin ya d’auke kansa , daman yasan za’a rina inda little ya shiga cikin
mutanan da be sansuba da wuya kaji ya kulasu har su tashi kuwa , “ don’t mind him
ok? “, kafun ya d’auko wani siririn abu da aka rufe ya mi’kawa Charles , “ happy
birthday once again !” Cikin farinciki charles ya furta “ thank you so much “, kara
kallan little Charles yai amma bai ce masa komai ba, ganin prince na ‘ko’karin
juyawa ne yasa charles yayi saurin dakatar dashi “ dude ina zakaje ? Ba’a dad’e da
farawa ba , and your place is there “,ya karasa yana nuna masa wani ‘kayataccen
wajen na musamman, “ yaya prince it’s time “, cewar little , kallan Charles prince
yayi “ sorry ! Am going ,” ya karasa yana kallan little shima “ let’s go” ynxu ma
da Sauri Charles ya ri’ko hannnun prince “ plx dude kar muyi haka , bai kamata
kamar kai kazo waje na bakasha koda lemo ba , plx ko bazaka zauna ba atleast I will
be happy idan yasha wani abun , “ bai jira jin me prince zai fad’a ba yayi dialing
wata number “ ku kawo mun drink dinnan now “, Shima kallansa prince yayi “ don’t
mind am going “, daga nan be kuma cewa komai ba ya kama hannun little suka fita ,
duk yadda wasu daga cikin friend din Charles Yaso su zauna amma daga prince har
little babu Wanda ya zauna , musamman little da babu Wanda ya kalla a cikin su.
Suna shiga cikin mota securities suka bar wajan, sai yanxu fargabar lefin da sukai
ya soma yiwa prince yawo cikin zuciya, ro’kon Allah kawai yake Allah yasa yaya bobo
be dawo ba .

NORTHWESTERN

WASHINGTON D.C

NUMBER ONE OBSERVATORY CIRCLE

cikin wani ‘kayataccen waje da ya hadu sosai da duk Wanda ya gansa zai gane
mamallakin wajan ba ‘karamun mutum bane, wasu manyan mutane ne su uku cikin babban
office d’in, daga gefe zaka ga flaq d’in U. S me girman gaske , zaune suke gabaki
d’ayansu kan chairs d’in wajan , gabaki d’ayansu fararan turawane zaune a wajan
kowa ka kalli fuskarsa zaka ga tsantsan tashin hankali, musamman yadda suke farare
sai fuskokinsu ta ‘karayin ja na tashin hankali , d’aya daga cikin su sai faman
duba wayarsa yake kamar me jiran wani abu, hasken da wayarsa ta soma ne yasa ya
d’auki kiran da Sauri yana furta “ Charles how far?” Bansan me aka ce masa ba , sai
kallan ragowar mutane biyun da yayi, yana kashe wayar, “ me ya faru?”, shiru be
amsa masa ba “am asking you amma kayi mun shiru ansamu nasara ?”, gabaki d’aya
wannan tanbayoyin da yake masa cikin turanci yake masa su “ sun bar Wajan , Charles
ya fad’a mun basu zauna ba , and basusha drinks d’in da aka zubawa pills d’in ba “,
da ‘karfi Wanda yake gabansu ya buga table d’in gabansa “ why? Why ?” Ya fad’a da
‘karfi , gabaki d’aya mutane biyun had’a baki sukai wajan furta “ sorry your
excellency”, a zuciye ya kallesu “ wanene mutumin da ya d’aukar mun d’a? Ko wanene
sai na sa yayi na dama , sannan aikin da yake ta’kama dashi zan sa a ciresa “
gabaki d’ayan su firgicine tattare akan fuskarsu Sabida zan tukan vice president da
Suka ji , da ‘kyar mayor ya furta “ your excellency sir , wannan maganar ba me
sau’ki bace , Sabida mun saka manyansu akan wannan case d’in , abune me matukar
wahala “ , wahala? Cewar mutumin yana dakatar dashi “ karka manta ko wanene ni ,
har yanxu nine Vice presidents , ina da mu’kamun da ko ku zan iya cirewa balantana
wani soja ? Wanene shi da zan zauna ina ‘bata lokaci ?ina bukatar ganin Nicholas
nan da kwana biyu kawai “, governor ne ya kalli mayor , shima mayor d’in kallansa
yayi , tunanin ta yadda zasu fad’awa vice president ko wanene ya saka a kama ‘ya
‘yan su suke , abun ba me sau’ki bane kamar yadda yake tunani duk da kasancewar sa
vice president, governor ne yayi ‘karfin halin furta “ BIG BOSS”, wayar da his
excellency ya d’auko ce ta su’buce ta fad’i, shima mai mai kalmar sunan “ Big boss
“yayi jiyayi kamar wani abu ya tokare masa makoshi da yasa cikin sauri ya d’auki
ruwa ko bi ta kan cups din wajan bebi ba ya soma sha, saida ya kusa shanye ruwan
kafin ya ajje bottle d’in “ big boss ? Nicholas yana hannun big boss ? “ sai kuma
ya mi’ke tsaye “ i can’t wait , ina bu’katar tattaunawa da his excellency , you can
all go “ Mikewa sukai gabaki d’ayansu cike da girmamawa har sunyi nisa ya ‘kara
dakatar dasu “ karku manta wannan zaman sirrine mu kayi daku sabida ‘ya’yan mu, kar
ku kuskura wannan maganar tattaunawar ta fita har his excellency yaji “, yanxu ma
cike da girmamawa suka amsa masa , suna fita cike da tashin hankali ya soma dialing
wani number gabaki d’aya kalmar “big boss da aka fad’a ce ta fi komai tsaya masa ,
dan shi karan kansa yasan wanene big boss “.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂

ABUJA , NIGERIA__!

Tunda aka d’auke wuta nunfashinta yake sizing, sosai ta takure kanta a waje d’aya
tana nan nunfashinta da yake barazanar fita daga ‘kirjinta, aduniya idan akwai
abunda tafi tsoro shine duhu sai kuma soja , duk lokacin da waje yayi duhu
hankalinta ba ‘karamun tashi Yake ba , hatta nunfashinta ya dinga barazanar
d’aukewa sabida yadda ‘kirjinta yake d’agowa sosai ,yana d’aya daga cikin dalilin
da yasa take tsoran soja musamman lokacin da take ‘yar ‘karama Umma asabe kullum
cikin ‘ko’karin kai ta wajan soja take a cewarta su harbeta su yanka namanta subawa
karnukansu, tun tana ‘yar ‘karama tsoran soja ya shiga zuciyarta, har zuwa yanxu
tsoransu be fita a cikin ranta ba. Daga ‘kasa ta tsugunna ta kame jikinta waje
d’aya ita kad’ai jikinta sai faman rawa yake , gashi ta kulle idanuwanta sosai ko
saud’aya batayi gigin bud’e suba , babu abunda take cikin zuciyarsa sai addua , ita
kanta batasan me take karantawa ba . Haka ta cigaba da zama cikin Wajan duhu na
‘kara mamaye Wajan alamar dare yafarayi sosai ,tun tana san ran ganin wani yazo
wajan har ta fara cirewa, dataji d’an motsi kuma zata firgita ta sake rud’ewa, ga
matsananciyar ‘Kishin ruwan da ta soma ji.

****A cikin gidan kuwa tun wajan ‘karfe 9 Arwa da ilham suke neman Abla amma basu
gantaba, hankalinsu ba ‘karamin tashi yayi ba musamman da Suka san Abla bata ta’ba
zama a waje , sai dai kome za’ai mata ai mata amma da Zarar Anfara kirar sallah
Magarib take nufo gida , hatta uwar karuwai sai datayi mamakin rashin dawowar
Abla , ga su zeenariya dasuke zugata akan cewa ‘karya kawai take musu idan ta fita
da Alama wajan barikinta take zuwa tunda ga alama nan har wajan 12 bata dawo ba .
Debeka ma rai a’bace so take kawai taga dawowar Abla daman ita ‘kiris take jira
akanta , sabida mugun tsanar da tayi mata , bakomai ne ya ja hakan ba sai kyau Abla
ga idanuwanta masu shegen kyau da ko ya ta ware maka su sai kaso ka ‘kara kallansu,
ga diri da Allah yayi mata duk da bata da jiki amma Allah ya bata albarkatun kirji
da hips , sai kuma ta samu ‘karin karamar ‘kugu da yawanci mutane suke wa la’kabi
da shape d’in coca-cola , Allah ya rufa mata asiri ma Sabida hijabin da take sawa
sabida hari da ake kawa mata, shiyasa ta kwammace zama cikin gidan karuwan tunda
Allah yana tsareta. Rai a’bace uwar karuwai tasa a kulle mata gida sannan ta bawa
debeka dama , da zarar Abla ta shigo gidan tayi mata mummunan hukunci sannan ko
ruwa kar abata, lokacin da Arwa taji batun uwar karuwai hankalinta ba ‘karamin
tashi yayi ba , duk wannan abunda ke faruwa husna da Aneesa basa cikin gida , da
Alama ba anan zasu kwana ba Sabida kulle gida da debeka tayi sannan ta kora su Arwa
ma kwancinsu, har zasu shiga sai ta tsayar da ilham , “ ke banan zaki kwana ba ki
kwana a d’aya d’akin shirgin” cewar debeka sai kuma ta daka wa Arwa tsawa Alamar ta
wuce , d’an guntun murmushin ciwo Arwa ta saki ta shige cikin d’akin shirgin da
suke kira d’Ali , ita kad’ai ta takure kanta sabida rashin ganin Abla da batayi
ba .
Debeka kuwa cike da mugunta ta ‘ki shigewa cikin d’aki , jira take taga ta inda
Abla zata fito , tun tana zaman tsammanin jiranta har bacci ya d’auketa kan farar
kujerar robar da take zaune . Ga baki d’aya har wajan ‘karfe 1 idan Arwa biyu
lokaci ta tabbata kowa yayi bacci acikin gidan , haka kawai ta kasa runtsawa
zuciyarta na raya mata ta ‘kara duba stores d’in shirgin gidan. A hankali ta fito
daga cikin d’akinsu cikin san d’a hatta takalmin ‘kafarta da ya gama shan duniya
saida ta cire sa , Sabida duhun da ke cikin falon da baya da baya Arwa take tafiya
batayi auneba taji ta taka ‘katuwar ‘kafar debeka, da Sauri ta toshe bakinta tare
da ‘buya bayan kujera , d’an motsi kad’ai debeka tayi , sai alokacin Arwa ta sauke
ajiyar zuciya ganin bata farka ba , store d’in falon ta fara bud’ewa , a hankali
kamar me rad’a take furta “ Abla ? Abla kina jina ?”shiru ba’a amsa mata ba , “
Abla kina jina ?” Nan ma still ba’a amsa mata ba ,sau biyu ta maimaita Abla kina
jina , ganin ba’a amsa mata bane yasa ta rufo ‘kofar a hankali, store din gefen
falon Arwa ta nufa , nan ma abunda ta fad’a a store d’in farko ta ‘kara maimaita wa
, nan ma shiru babu Alamar da mutum a ciki, wani store Arwa ta ‘kara nufa , ko da
taje a kulle yake ma Alamar ba’a shiga ba , sai a lokacin hankalin Arwa ya ‘kara
tashi ganin da gaske Ablan bata nan , har ta juya wani tsohon store d’in gidan ya
fad’o mata , duk da d’an tsoran da ya fara kamata haka ta nufeshi ta bayan kitchen
ko tsoran wani abu ya faru da ita bataji, tana zuwa wajan taga ansa abu an kulle ta
waje , a yanxu kam hope d’inta ya cire ganin store d’in a kulle , har ta juya ta
kuma tsaya wa , haka kawai taga bazata iya barin Wajan ba sai ta duba dukda bata
tunanin Abla tana ciki, a hankali shima ta bud’e wajan, bud’ewarta kuma tayi Daidai
da ware idanuwanta da Abla tayi cike da tsoro amma ta kasa motsawa “ Abla ? Abla
kina jina ?”, cewar Arwa , shiru ba’a amsa mata ba , “kara maimaita mata tayi nan
ma shiru bata amsaba , juyawa tayi daniyar fita daga sama taji muryar Abla a dushe
ta furta “ Arwa “, itama da Sauri arwa ta juyo cike da farin ciki take furta “ Abla
! Abla kina jina ? Ke ce ? Daman nasan bazaki ta’ba kwana a waje ba , kasa magana
Abla tayi a hankali kuma ta fara mi’kowa Arwa hannunta , itama arwan cikin d’an
hasken da rafito kamar na wata tafara baza hannunta har ta kama hannun Abla , sai
da ta temaka mata sannan suka fito daga cikin store d’in , suna ri’ke da juna suka
shigo cikin falourn ta inda arwa ta Fito zuwa d’akinsu , a hankali Abla ta furta “
ruwa “ , da sauri Arwa ta fita bata Jima ba kuma ta dawo d’auke da pure water a
hannunta guda biyu, tana bawa Abla saida ta shanye guda d’aya , d’ayan ma sai da ta
‘bulashi Tasha rabinsa Sabida ‘kishirwar da ya kamata , sai alokacin ta fara dawowa
daidai, hasken fitilar da ya kamane yasa Abla sakin murmushi harda ajiyar zuciya,
kallan d’akin Abla tayi taga babu kowa sai su a hankali ta furta “ ina sauran?”,
sai da arwa ta kwanta akan takwalinta ko tunanin hawa kan katifar d’azu bata yi ,”
husna da Aneesa basa gidan nan , ilham kuma debeka ta canza mata d’aki”, jinjina
kai abla tayi “, Abla ?”cewar arwa “ na’am “ ki kulle ‘kofar da kyau kizo muyi
bacci sabida dare yayi sosai kar ciwan idanki ya tashi , Hakan kuwa Ablan tayi
saida ta kulle ‘kofar sosai duk da d’akin ba fanka sai fitila haka sukayi baccin su
fitila a kunne , su arwa har sun saba ma sabida tsoron duhu da Abla take shiyasa ko
cikin dare ne basa kashe fitula saida su barta a kunne.

***
****** karfe 3:30am na safe wata irin azaba Abla taji a ‘kafarta cikin bacci da ya
sata sakin razananniyar ‘kara tana bud’e idanuwanta , debeka ce tsaye a gabanta,
yadda ta ganta tsaye ‘ki’kam sai data d’an razana ta , zafin da ta ‘Karaji a
‘kafarne ya ‘kasa ta sakin wani ‘karan har tana bada sautin “Auch”, ita kuwa
debeka cike da zallan muganci take taka ‘kafar Ablan ,bayan takalmin ‘kafarta da
tasaka med’an rud’u, har cije baki take wajan take ‘kafar, yadda taga Arwa na
baccine itama cike da mugunta ta daddage ta d’akawa Arwa dukan dayasa ta farka a
firgice, a yatsine debeka ta nuna mata kofa , cike da firgici ta mike tsaye tanayi
tana tafiya tana waiwayo bayanta dan har cikin ranta bata ‘Kaunar abunda Akewa
Ablanta, rashin gatan da basu dashine yasa ake kaskantar dasu kamar wasu bayi , duk
da a wasu lokutan uwar karuwai tana danganta su da kaskantattu ko kuma jari. Kallan
kallo Abla suke ita da Debeka , ita Abla har mamaki take tsanar da debeka tayi
mata .ruwan hannunta me shegen sanyi ta watsa wa Abla tana shirin damko hijab
d’inta , Abla ta d’angoce mata .’kara yun ‘kurawa debeka tayi zata bigi Abla, a
wannan karan ma Abla ta ‘kara kauce mata dan ta gaji da abunda debeka suke mata. “
Dan uwarki har kin isa ki kauce mun ?”, kallar uwarki da debeka ta anbata wa Abla
shine yayi mugun ‘bata mata rai , duk da har yau bata san ko suwanene iyayanta ba ,
bata sani ba suna da rai ko sun mutu, suna tunawa da ita ko sun mance da ita ? ,
amma duk da hakan ta’ki Jinin a ta’ba mata iyaye , zata iyayin hakuri da komai amma
kar mutum ya kuskura yace zai zagar mata iyaye anan ne zai ga ‘bacin ranta . Yanxu
ma a zuciye take kallan Debeka fararan idanuwanta kamar madara sun fara kad’auka ,
cikin sexy eyes da Allah ya halicceta dasu ta zubawa debeka kallo, kallo irin
natsana,sai da ta d’auki kusan 30 seconds tana kallanta kafun ta janye idanuwanta
gabaki d’aya tana mi’kewa tsaye , ko kallan inda debeka take a tsaye bata ‘karayi
ba sai toilet d’insu da take niyar shiga , bata Ankaraba taji debeka ta janyo ta
baya ta bugata da garu, duk da hakan Abla batayi mata komai ba ta ‘kara ra’bawa
zata wuce yanxu ma cike da mugunta debeka ta janyo “ Dan uwarki…” ta’bata ‘karasa
zagin da take so tayi ba taji saukar mari akumatunta, bata Ankara ba ta ‘karajin
sautin wani marin , cike da mamaki ta d’ago dan ganin ko wanene ne ‘karar kwanan da
yayi mata haka , mamakin ganin Abla tayi a tsaye rai a ‘bace “ Ni kika mara ? Yau
zaki ci uban ki kuwa “, wani saban mari Abla ta ‘kara d’auke debeka da shi dama
haka take da wuya mutum ya ‘Kure ta amma duk ranar da mutum ya kaita bango bata
raga masa , rai a ‘bace Abla ta kalleta “ kin dade kina cutar dani , me nayi miki?
Me na tsare ki ? Me yasa kika fi nuna tsanarki a kai na? Duk wannan be shafeni ba
amma daga rana irin ta yau , ba debeka ba ko sumammiya ce ke kika ‘kara kuskuran
anbatan iyayena sai na nuna miki Nima bani da mutumci , na so na dunga shange duk
abunda kike mun , nayi hakuri da halayen ki, kin Musguna mun, kin hantare ni duka
hakan be ishe kiba sai kin ‘kara da iyayena? Naso na baki girman ki na wacce ta
girmeni amma naga Alama bakya bu’katar haka , daga rana irin ta yau , ni IBTISSAM
bazan kara jurar ko wana iskanci ba , tunda so kuke na nuna muku asalin halin muzu
ha mugani shege ka fasa ,” ta ‘karasa a zafafe dan sosai ranta ya ‘baci yau ,
debeka ta kaita bango iya tsawan shekara biyun da tayi a cikin gidan nan sun mata
abubuwa da yawa amma ban da yanxu kuma , bazata ‘kara d’auka ba , bata kuma bi
takan debeka ba ta shige ban d’aki,debeka da mamakin Abla ya gama cika ta kasa
motsi tayi dan tun da Abla ta shigo cikin gidan uwar karuwai bata ta’ba d’aga mata
murya ba sai yau , har wani d’an shakkar Abla ne ya shiga ranta lokaci d’aya , amma
da yake ‘yar duniya ce kasa cewa komai tayi azuciye ta yi ‘kwafa ta bar d’akin har
cikin zuciyar ta kuma tana mamakin Abla .

Itama Abla ko da ta fito daga toilet d’in alwala tayi Sabida abunda ya faru da ita
jiya sai ynxu zata samu tayi sallahr isha’i, tana idar da sallar d’akin nasu ta
fara gyarawa dukda ba wani datti yayiba amma duk da haka sai da ta gyara kafun ta
fito falon. Kamar kullum bakowa a falon yau har debeka bata ciki, cikin sauri sauri
Abla ta fara gyara falon Sabida tanaso taje gidan ruwa , tana gama gyarawa d’akunan
sama da ‘kasa ta gyara gabaki d’aya har da band’akin da kullum baya gama gajiya da
‘kazanta musamman condum da take yawan kwasowa ko wana d’aki, kome takeye cikin
Sauri take yinsa har lokacin kuma bata ga kowa na cikin gidan ba .lokacin anfara
kiraye Kirayen sallahr asuba shiyasa sai da ta koma d’aki ta sallarta kafun ta fara
fito da uban tilin kayan wanke wanken da aka ‘bata , sai da ta fara jan ruwa a jiya
tukunna kafin ta soma yin wanke wanken , sabida yawansu sai wajan 8:30Abla ta
kammala gabaki d’aya ‘kafafuwanta sun ‘Kage kamar zasu fad’i, duk da haka bata
zauna ba sai da ta shage gabaki d’aya tsakar gidan , zuciyar ta fal tunanin inda
Arwa ta shiga, tunanin ko ta koma d’aki ne yasa ta shashantar da zancan cikin
zuciyar ta har ta kammala aikinta . Tana shiga cikin d’akinsu ta tarar babu Arwa a
ciki har yanxu Aneesa da husna suma basu dawo ba , ga ilham da debeka ta canzawa
d’aki itama har yanxu bata ganta ba , cikin sauri ta duba store d’in falon shiru
babu kowa a ciki , na gefen falon ta shiga , nan ma shiru babu kowa , da Sauri ta
nufi store d’in bayan gida shima still babu kowa , jikin tane ya bata ta duba rooms
d’in d’akunan tunda su uwar karuwai basu Fito ba har yanxu , duka d’akin ‘kasa da
sama sai da ta duba babu arwa a ciki, har zata koma d’aki sai wata zuciyar ta sa ta
le’ka d’akin su Zinariyya cikin sand’a , abun mamaki babu kowa a cikin d’akin
nasu , har saurara tayi ko zataji motsin ruwa amma shiru , da Sauri ta ‘karasa
shiga cikin dakin ta banka toilet , nan ma babu kowa a ciki sai wari wari da toilet
d’insu yake ,gabaki d’aya hankalin Abla kasa kwanciya yayi dukda fargaba- fargabar
shiga d’akin uwar karuwai da taji hakan be hanata nufar d’akin ba , zuciyar ta sai
dukan uku uku take , kamar da wasa ta tura kofar d’akin, abunda ta ganine yayi
mugun gigitata da tsoratar da ita , jikinta har faman rawa yake rai a ‘bace lokaci
d’aya taji hawaye na sakko mata , suma gabaki d’aya cike da tashin hankalin ganin
Abla a d’akin Suka juyo suna kallanta ganin yadda ta burkice lokaci d’aya ga
Tsantsan bacin rai da suka hango cikin idanuwanta, cikin raunanniyar muryar da ta
had’e da zallan tashin hankali da rud’ani lokaci d’aya har da ‘bacin rai ta furta “
Arwa ?”.

**** MASU SAN A TALLATA MUSU HAJARSU SU TUNTU’BENI TA WANNAN NUMBERTAWA 07041879581
.

Share fisabilillah 👏.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM na kud’ine akan 300 kacal , me bu’katar ya karanta littafin har
‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha
umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book
ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar
sa, to a rashi sani ne .
__💞💞”Alhamdulillah , thank you Allah ,for the countless blessings in my life”. “ O
Allah , I am forever grateful for the guidance and peace you bring into my life .”
“ thank you , Allah , for the gift of iman (faith)which has filled my heart with
tranquility “.💞💞__

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

Season__10

5th Avenue, New York _ U.S

Tun a cikin babban harabar gidan suka gane bobo ya dawo cikin gidan , Adil kallan
prince yayi tare da marairaice masa fuska “ yaya prince we’re in big mess , yaya
bobo ya dawo fa !”, shima prince kallansa yayi dan shima ya tabbatar da yaya bobon
ya dawo musamman haushin karnukan yaya bobo da sukaji, sunayin packing motocin su
Robert da suka bi bayansu suma suka shigowa ciki, gabaki d’ayansu tsakanin prince
da Adil an rasa wa zai fara shiga ciki , musamman lefi biyu da suka san sunyi na
farko basu tanbaya ba suka fita , na biyu kuma gashi sun shigo gida late , “ yaya
prince ka fara shiga ciki mana kaga kaine babba “, d’an harararsa prince yayi “ dan
nine babba sai aka ce maka bana san lafiya ta ? So kake ina shiga ya dam’keni?,
kaga kaine ‘karami and yaya bobo bayasan ganin kukanka , muna shiga kawai ka fashe
da kuka kaji?”, step biyu little yayi ya koma baya “ yaya prince duk lefin kane
fa , kai kasa muka fita , and muna shiga wallahi yaya bobo ya dam’kemu bazamuji da
dadi ba , ni kaga tafiya ta , wajan su Bruno zan zauna,kai kafara shiga “, zai juya
prince ya janyo sa “ wallahi baka isa ba , tare zamu shiga , salan nashiga ya
kamani , Gwanda ko me zai faru ya faru, kwacewa little yake ‘ko’karin yi daga
ri’kon da prince yayi masa , amma yana ganin su Robert sun kusa ‘karasowa wajan
yayi saurin shigewa falon, suna shiga suka tarar da bobo zaune kan kujera yayi
crossing legs d’insa , jikinsa sanye da ba’kin wandon kanfanin Supreme, sai red
d’in rigar da yasaka daga jikinta akwai harafin Be a man a jiki, little yana ganin
bobo yayi saurin ‘buya bayan prince , cikin kasa kasa da ido prince yake bun fuskar
bobo da take a had’e , gabaki d’aya hankalinsa yana kan system d’in da yake
operating, ‘ko’karin janyo little da ya ‘buya a bayansa yake amma sam little ya ‘ki
fitowa daga bayansa , ‘kara d’ago da idanuwansa prince yayi karaf suka sauka kan
bobo da ya d’ago da fuskarsa ,” yaya bobo kayi hakuri kaji?we’re sorry “, kallan da
bobo ya bisa dashine yasa yayi saurin had’iye maganarsa “ come out “ ya fad’a da
d’an tsawa , da Sauri little ya fito daga bayan prince zai soma bawa bobo hakuri
shima bobo ya jefa masa nasa kallan , cikin cool voice ya furta “bakwajin magana
ko? Wa kuka tanbaya da zaku fita ?”, gabaki d’ayansu sunkuyar da kansu ‘kasa
sukai , ko run’kurin d’ago da fuskarsu basayi Sabida kar ma su had’a ido da bobo ,
gabaki d’ayansu shiru sukai masa , mi’kewa tsayen da suka ga yayi ne yasa little
saurin furta “ yaya bobo kayi hakuri , ni na saka yaya prince….” Can you shut
up?”,cewar bobo yanzu a zafafe yayi maganar , yanxun ma Shiru Sukai , little kwalla
har sun fara tarar masa a ido , dan a rayuwa bayasan ganin fushin su bobo,” d’auke
kansa bobo yayi akan su kafun ya furta “ get lost “, yaya bobo kayi hakuri ? Cewar
prince , “ karna maimaita magana ta , if not I will vest my anger on you , ku
‘bacemun da gani “, da Sauri suka bar falon , shi prince ya nufi part d’insu , shi
kuma little ya nufi part d’in uncle iron man.
Komawa yayi kan kujerar da yake , wani d’an sound ne ya fito daga wajan kofar
waje , “ come in “ cewar bobo, Robert da captain ne suka shigo cikin falon , cike
da girmamawa suka sarawa bobo, jin jina musu kai bobo yayi batare da yace komai
ba , wani d’an ‘karamin file Robert ya mi’kawa bobo , kafun ya furta “ gabaki
d’ayansu Suna Washington, cikin number observatory circle , and magana ce ta sirri
suke tattaunawa Sabida futowar kowannansu da ya kasance a rarrabe “, and the other
guy?” His name is Charles sir , da Alama sunyi ‘ko’karin anfani dashi wajan bawa
prince drink , dukda nasan bazasu shaba , sabida irin takatsan tsansu sir “, good
Kawai bobo yace bayan ya kar’bi envelope din , the 2 guys ku mayar dasu Fort
Hamilton, with out my permission,kar Wanda ya kuskura yashiga inda suke , take care
of them “, ok sir Robert da captain suka had’a baki, mikewa tsaye bobo yayi da
envelope d’in hannunsa “ and the 2 stupid guys a barsu cikin death prison “, yanxu
ma ok sir suka ‘kara fad’a, bobo na juyawa Suka sara masa , tare da ‘kamewa , basu
bar Wajan ba sai da suka ga bobo ya shige , still saida suka ‘kara sara masa duk da
baya wajan ,kafun su bar wajan.

**** Adeel kai tsaye d’akin uncle iron man yanufa , lokacin da ya shiga bedroom
d’insa akwance ya tarar da uncle alamar bacci yake , shima gefen gadon ya hau ya
kwanta tare da kifa kansa kamar me bacci, motsin da uncle ya jine yasa ya bud’e
idanuwansa,mamakin ganin little yayi kwance a gefen sa duk da basaban abu bane “ Me
yasamu little d’ina ?”,shiru little yayi masa kamar me bacci , tashi zaune uncle
yayi Sosai yana kallan yadda little ya ‘boye face d’insa “ nasan fa kana jina , oya
get up”, tashi zaunan kuwa little yayi yana kokarin sauka da ka kan gado uncle ya
ri’ko hannunsa “ oya waya ta’bamun little d’ina nayi maganinsa yanxu ? Maza
fad’amun menene kake fushi haka ?” Little kamar wani yaro fuska a maraice ya kalli
uncle “ Am sorry uncle nasan munyi lefi, we’re sorry , kaga yanxu ma yaya bobo
fushi yake damu, yayi mun tsawa kaina ciwo yake mun”, yana kai ‘karshe ya ‘kara yun
‘kurun komawa cike da kulawa uncle ya hanashi hakan , “ kunyi masa lefi ne shiyasa
ransa ya ‘baci and you can go to his bed ka bashi hakuri zai hakura okay ?”, d’auke
kansa little yayi “ ni uncle yau a d’akinka zan kwana , in yaya bobo yazo shigo wa
ka tasheni sai na ‘buya,” dungure masa kansa uncle yayi “ so kake big boss ya dawo
ya harbemu?” Dariya little yasaki da both side dimples d’insa Suka lo’ba ,”ina
prince ? “, cewar uncle , nasan yana d’aki may be ma ya kwanta , Nima bacci zanyi
uncle,” zai ‘kara kwanta wa uncle ya hanasa , “magariba ya kusa , maza jeka shirya
ka kiramun prince da bobo duka ina jiran ku a falour”, yanxu ma a marairaice little
ya kallesa “ uncle na fad’a maka fa yaya bobo fushi yake damu , Shiyasa bazan je
part d’insa ba ma ,” okay bari na kira big boss shi sai ya kira mun shi, little har
da Sufa wajan danne wayar “ uncle wasa nake maka , please karka kira shi, yanxu
zanje na kira su , okay ?”, jin jina masa kai uncle yayi “ okay “,.little yana futa
part d’insu yashiga , ba kayan d’azu ne ajikin prince ba da Alama wanka yayi sai
system d’insa na dayake dubawa, “ yaya prince uncle yace yana jiran mu a ‘kasa , ba
tare da prince ya kalle saba ya furta “okay ganinan zuwa “. Yaya prince “ cewar
little yana jan ‘karshen sunan , d’ago da kansa prince ya yayi suna had’a ido da
little lokaci d’aya kuma suka ‘kyal’kyale da dariya atare ,” little you’re not
serious , d’azu da yaya bobo ya kama mu wato a fara hukuntani ko? Uhmm” yanxu ma
sabuwar dariya little ya saka,” no yaya prince , kasan wani lokaci idan yaya bobo
ya had’e rai sai ya dawo kamar yaya big boss , shiyasa na ‘buya a bayanka and nasan
yaya bobo fushi yake damu ,” let’s apologize ko? “Cewar prince , Adil ma kansa ya
d’aga masa alamar yes, saida little yayi wanka shima ya canja shigarsa tukunna
kafin su shiga part d’in bobo, babu kowa a falon sai kamshin turare da yake tashi
da sanyin Ac, sunsan tunda baya falour to tabbas yana master bedroom d’insa , a
bakin ‘kofa ma yarjejeniyar shiga suke , prince yana cewa Adil yashigashima Adil
yana cewa shine babba ya shiga ,sai da prince ya shammace sa , ba yi Auni ba sai
jinsa yayi a d’akin bobo, yana juyawa yaga wajan alamar prince ya gudu.

***** “ yaya bobo we’re sorry plx” cewar Adeel, door da aka budene yasaka Adeel
juyo wa da sauri prince ya shigo sabida ganin bobo ya shigo shima little Sauri yayi
hugging bobo, cikin murya irin ta me shirin yin kuka ya ‘kara furta “ we’re sorry
yaya bobo kaji”hannu bobo ya mi’kawa prince shima yazo yayi hugging d’insu, tare da
jansu kan lafiyayyan gadan d’akinsa , “ ba fushi nake daku ba sabida kun fita ,no ,
ina fushi da kune Sabida baku fad’a wa kowa saku fita ba , in wani abu ya sameku fa
? Ni da uncle wani amsa kuke so mu bawa big boss ?ko da yake bari na kira sama
sabida kun isheni”, ya ‘karasa yana d’akko wayar sa, tsakanin little da prince har
yar rigen rigen ri’ke hannun bobo sukai “ Haba yaya bobo kayi hakuri kaji? Nasan
aiki yayi wa yaya big boss yawa ma ka barshi ya Hutu “, cewar prince , dan harga
Allah yasan big boss yaji sun zama gassun nama “ eh yaya bobo d’in mu , kai ma
nasan ka gaji bari nayi muka tausa”, cewar little , “ yau she kuka fara siyasa
bansani ba ? In kuna da irin wanna brain din ai zaku iya yin aikin soja “, yanxu ma
da Sauri suka had’a baki wajan furta “ No yaya bobo”, cikin Sauri kuma little ya
kalli agogo , “ yaya bobo uncle fa yana jiran mu a down stairs dan yanxu za’a fara
kiran sallar magrib, ya kamata Kashirya kaji?”, yana kai karshen zan cansa yayi
saurin sauka daga kan gadon, “ bye yaya bobo “, shima prince da Sauri ya sauka yana
furta “ bari mu barka kashirya “, shi ma be jira jin amsar bobo ba yayi saurin
bakin d’akin, girgiza kansa kawai bobo yayi Sabida yasan dalilin barin d’akin
nasa .

*****
*********6:35pm gabaki d’ayansu suka nufi masallacin gidan sabida sallar magrib da
akai kira, ko da suka shiga masallacin basu bito ba har sai bayan sallar isha’i,
wannan ‘ka’idane sun saba , duk lokacin da zasuyi sallar magrib basa fitowa cikin
masallacin sai sunyi sallahr isha’i sai dai wani babban dalili me ‘karfi da zai sa
su fito kafun kiran isha’i. Ana idar da sallah prince da little ne suka fara fitowa
suna fitowa suka soma jin haushin karnuka, da Sauri little ya ‘karasa inda yake jin
kukan karnuwan , wasu manya manya karnukane wajan , kusan guda biyar gabaki
d’ayansu ko wannansu da kayar gashin jikinsa, yadda suke haushi saiya firgita ka
musamman idan kayi arba dasu, d’aya daga cikin su me kayan black da brown sai milk
colour kad’an ajikinsa sai faman karkad’a gashin jikinsa yake , yadda ko wannansu
yake huci zaka tabbatar da ba karnukan wasa bane su, me black and brown d’in ne ya
jiyo direction d’in da little yake , cikin wani irin gurnani da zai tsoratar da
mutum musamman mara gasky ya soma haushi, abun mamaki suma ragowar karnukan
direction d’in da kosashshen Karen yayi suma suka kalla, a guje suka nufo inda yake
, shima a hankali ya fara ja baya ganin sun nufoshi, yadda yake gudu suma haka suke
gudu cikin sauri kamar ba karnukaba, sosai karnukan suke gudu har saida suka kai
inda yake , gabaki d’aya kuma sai suka zagayeshi kamar sun ga nama , cikin dariya
dariya little ya kalli Karen da yake da baki da brown a jikinsa “ Bruno training
d’inku ya ‘kara bun’kasa yadda kuka biyoni haka sai kace wani mafarauci,gefen
hagunsa little ya kalla lokacin da ya mayar da kallansa kar wani farin kare shima
jikinsa duk gashine dogaye “ kaima Rosie ka koyi mugunta wallahi , ku zauna “
haushi karnukan suka soma da ‘karfi kafun lokaci d’aya su zauna kamar yadda yace ,
batare da tsoro ko shakkarsu ba ya bisu yana shashshafa musu jiki, suka sai faman
karkad’amasa gashinsu suke , lokacin da prince ya ‘karaso wajan kallan little yayi
yana d’an harararsa , “ tunda ka gansu Malam sai ka taho mutafi ko? Kasan bashiri
nake da wad’annan mafarautan ba “, ya karasa zancansa yana hararar su bruno, dariya
little ya saki “ Haba ya prince wannan harara da kake musu haka ?”, katse shi
prince yayi ta hanyar furta “ let’s go joor ! Yunwa nake ji”, kallan ya prince
little yayi kafun ya mayar da kallansa kan su Rosie , a baza ya cewa su rosie ku
kama mun shi, wani irin jijjiga sukai lokaci d’aya , ga harsunansu da Suka fara
fito dashi, yadda suke kad’a jelarsu daka gane ba ‘karamun tantiran karnuka bane ,
ko wannansu kuma akwai wani d’an karamin symbol me d’auke da sunansa ajiki,
azuciye prince ya soma hararar little ganin yadda karnukan suka soma biyosa , shima
ja da baya ya soma yi, yana bin ko wannansu da kallo d’aya bayan d’aya , suma kamar
wasu mutane haka suka soma bin prince , yana sauri suma zasu fara sauri, da yayi
alamar guduwa suma zasu fara , juyawa prince yayi a guje , dan yasan halin karnukan
musamman BRUNO da ROSIE , karnukan ma gabaki d’aya gudu suka saka shiyana gudu suma
suna biyosa , little na tsaye sai faman dariya yake musu, wani irin daddad’an Sauti
ne ya tashi , shiba kid’a ba shi ba sarewa sannan baza a kira shi da fito ba , na
tsawan sakanni 15 , a guje su bruno suka jiyo tare da nufar mutumin da yayi wannan
sautin, gadan gadan suka nufi bobo dake tsaye a Wajan yana binsu da kallo, yadda
gashin jikin karnukan suna tashi ma abun kallo ne da yadda suke haushi na asalin
karnukan sojoji, suna ‘karasowa inda bobo yake cikin wani irin salo ya ware tafikan
hannayensa , kafun ya dunkulesu waje d’aya , gabaki d’aya karnukan tsayawa sukai,
gefe da gefe guda biyu sai bruno dake tsakiyarsu a matsayin cikon na biyar d’insu,
karasowa inda bobo yake little yayi “ yaya bobo wad’annan karnukan naka maganar
mutane 2 Kawai suke ji daga taka sai ta big boss , kalli yadda suka tsaya kamar
mutane , hararar bobo yayi tare da kallan karnukan yana tsugunnawa a inda suke ,
gashin Ruby ya fara shafawa , sannan ya shafa na Roxy, ko wannansu sai karka
d’amasa gashi suke , yana cire hannunsa sai ya d’aura akan scout da gashinsa yake
fari da baki, gabaki d’aya karnukan sun zubawa bobo ido , hatta Rosie da Bruno sai
faman futo da harshensu suke “ start going “, cewar bobo , haushi suka soma yi masa
na kusan 5 second kafun gabaki d’ayansu su kashi kashi biyar kowa da side d’in da
ya nufa . Bobo yana d’agowa little ya ri’ke’ masa hannu “ yaya bobo yunwa nake ji ,
let’s it kaji “, kanshi bobo ya d’aga masa har suka ‘karaso inda prince yake , shi
kad’ai sai faman hararar little yake , suna zuwa kofar shiga suka tarar da uncle ,
shima hannunsa little ya kama suka shiga ciki, kai tsaye dinning area suka nufa ,
suna shiga wasu sojoji sanye da suit d’insu suka nufi dinning area d’in,ko wanne
suka ja masa kujera ya zauna sannan su james suka soma serving kowa favorite food
d’inshi da yake san ci.
Tunda Suka soma cin abinci babu Wanda yayi magana har saida suka koma cikin
falourn, prince da little game suka soma bugawa , bobo da uncle kuma suna zaune kan
kujera suna hira , lokacin da uncle yayi maganar dawowan big boss lokaci d’aya
prince da little suka ajje game d’insu , “ uncle Yaushe zai dawo plx ?”, cewar
little,” kana da number d’insa ai sai ka kirashi kaji “ yaya bobo Yaushe zai
dawo ?”, cewar prince , tunda yaji Ance big boss zai dawo ya shiga taitayinsa , dan
duk lokacin da big boss ya dawo sai yaji ajikinsa , bobo yafahimci hakan shiyasa
yace masa “ bayanxu zai dawo ba tukunna , akwai abunda zaiyi a Uk”, bakinsa little
ya d’an turo “ yaya bobo toh mu muje U.K sai mu ganshi muyi masa surprise “ , ba
bobo ba hatta uncle saida ya dara prince kuwa hararar little yayi “ big boss d’in
zakayiwa suprise ? Little ka zama rigimamme fa , kamanta wanene big boss d’in naka
da Alama sabida baka ganinsa kwana biyu” cikin pity face yace “ no yaya bobo kawai
nayi kewarsane and nasan aiki ya masa yawa , and duk lokacin da ya dawo bazan bari
ya tafi shi kadai ba “, shi yaya big boss din ?”, da Sauri cewar prince “ gira
d’aya little ya d’aga masa , cikin kashe ido “ sannan zan fad’a masa rashin jin da
kake yi “ cewar little hannu prince ya saka zai janyo sa little yayi saurin Tashi
ya koma kusa da bobo “ yaya bobo kaga ya prince ko ?”, wayarsa bobo ya ciro yana
mi’kawa prince “ kirawo Yayansa ka fad’a masa “, wani irin sufa little yayi ya koma
wajan prince “ Haba yaya prince d’ina nifa wasa nake Kaji ,kaga yanxu dare ma yayi
let’s go and sleep “, little ka fita idona fa , ka rainani “ ni wallahi ban rainaka
ba , ina sankane sosai kamar yadda nake san yaya bobo, yaya big boss , uncle ,
kaji yaya prince d’ina “, Allah ya shiryeka cewar prince yana mikewa , gabaki
d’ayansu hugging d’in bobo da uncle sukai kafun suyi musu sai da safe suka nufi
d’akinsu . “ he missed him, yana missing big boss sosai and ya kamata ya dawo ko
sabida little d’insa da ya bari”, shima bobo murmushi ya saki ,” Ai kwanda ya dawo
ni ciwan kai suke samun ko zasu shiga taitayinsu”, cewar bobo, “ you all missed him
and we all missed him, yana dawowa wannan rigimar ta little shi kadai ke iya
handling d’insa “, ni uncle banyi missing dinsa ba , kawai ya dawo Sabida wannan
babyn nasa yana samun ciwan kai sosai “, yanxu ma dariya uncle ya saki “ that’s why
I love you all, little shine maganinku ai musamman big boss da babu me iya
controlling dinsa , that’s why nake san naga auranku “, uncle plx cewar bobo yana
d’an Kauda fuska “kunsan it can’t be possible kuce zaku zauna babu aure ko? Hatta
yayanku, he have to get married too, duk yan matan da suke yawan sanshi kamar suyi
hauka , wannan decision d’in da kuka d’aukar wa kanku bashine solution ba “, uncle
“ cewar bobo tun da uncle ya soma maganar aure yake controlling kansa ,” uncle plx
karka yi masa maganar aure , everything can happen , kasan zuciyar sa idan ransa ya
‘baci, controlling d’insa yana da wahalar gaske , we don’t need any person more in
our life’s , mu biyar d’inmu is okay”, murmushin manya Kawai uncle ya saki “ yasani
shima bobo yana da saukin kai sosai, amma yana da zafi idan akai musu maganar
aure,duk da a yawan cin lokaci ya kwammace ayi masa maganar da a yiwa big boss dan
ko wanene ranshi sai ya ‘baci, shiyasa uncle da yaga ran bobo yana ‘ko’karin ‘baci
shima yayi shiru ya bar maganar “, mi’kewa tsaye uncle yayi “ I have to sleep early
nima , good night “, bobo be ce masa komai ba sai bayansa da yabi har zuwa part
d’insa , sai da ya tabbatar uncle ya kwanta kan gadonsa duk da beyi bacci ba sannan
ya yun’kura zai tashi uncle ya ri’ke masa hannu “ it has been years now , bazaku
yafe musu ba ? Ka fishi sau’kin kai, zuciyarsa tana da zafi sosai “ murmushin ya’ke
bobo ya saki “ uncle how many years ? Duk wannan tsawan shekarun sun damu da inda
muke ? Muna raye ko mun mutu sun sani ? Basu damu ba, we don’t need them all
Uncle , su suka zama silar zanjawar sa , ba haka yake ba Amma ta dalilinsu komai ya
canja , ya ‘bata farin cikinsa sabida yaga munyi farin ciki, ya kwana a zaune beyi
bacci ba Sabida mu , prince , Little Menene laifinsu? Hatta prince bazai iya tuna
komai ba , little fa? He’s so called father ko sau d’aya be ta’ba d’aukarsa ba 22
years of his life, and his so called mother ko d’uminta bai samu ba , big boss
Kawai ya sani as his mother and his father , uncle shine kake so mutuna su aranmu?
Please uncle stop it ! Good night”, bejira uncle ya ‘kara magana ba ya kashe masa
light ya barmasa dumm light tare da kullo masa d’akin gabaki d’aya, a babban falon
su ya zauna , ranshi a ‘bace sabida tuno abunda baya bu’katar turowa a rayuwar sa
gaba’ki d’aya , siririyar diamond d’in wuyansa ya shafa , “ why ! Why! We don’t
need you , and bazamu ta’ba zama tare ba , cire zancen yayi gabaki d’aya a ransa ,
saida ya tabbatar da lapiyar tsaron gidan gabaki d’aya , hatta zakin big boss , da
sauran ‘bangaran zoo kullum sai an tabbatar da lapiyarsu, su Bruno kuwa gabaki
d’aya an sake su sai faman shawagi suke cikin babban compound din gidan ga sojoji
da suke shawagi kamar ba dare ba . Yana shiga d’akinsu little ya tarar prince yayi
bacci saura little dake sanye da kayan bacci blue colour sai kuranin dake
hannunsa ,yana ganin bobo ya ajje kur’anin “ little dare yayi, you have to sleep up
, okay “, okay “ cewar little yana kwanta wa bayan ya ajje kur’anin a ma’a danarsa,
a gefen gadan sa bobo ya zauna har saida ya tabbatar little ya kwanta sannan yayi
masa addua, zai tashi little ya rike masa hannu,bobo na juyowa little ya sakar masa
murmushi “ ina sanka yaya bobo “, shima bobon murmushi ya sakar masa “ Nima isan
little d’ina , good night “, bobo be bar d’akin ba sai da yayiwa prince shima addua
kamar yadda yayiwa little sannan ya bar musu dumm light kawai .

🍂🍂🍂🍂
✨✨✨✨✨✨

ADEMOLA ADETOKUMBO STREETS

Runtse idanuwanta Arwa tayi lokacin da Abla ta kira sunanta, ga wasu irin hawaye
masu zafi da rad’ad’i da suke zubo mata cikin idanu, da Sauri Abla ta ‘karasa
shigowa cikin d’akin zanin gadon da tagani a ‘kasa tayi saurin raruma ta lullu’bawa
Arwa a jikinta da take faman karewa Allah ya Rufa mata asiri ma akwai under wears a
jikinta, a hankali kuma ta fara tsuntar kayan arwa tana mi’ka mata, duk abun nan da
take uwar karuwai na tsaye ri’ke da towel ajikinta, Zinariyya da yar shila ma kowa
sanye da wani d’an iskan towel , debeka na tsaye gaban wani camera da take shirin
fara d’auka , ilham nagefenta, Ko wa jira yake yaga reaction d’in Abla amma babu
Wanda ta d’ago ta kalla saida ta tabbatar Arwa ta saka kayanta taja hannunta zuwa
‘kofar d’akin, cikin ‘kasa ‘kasa ta yadda bazasu jiba Abla tace Mata ta jirata a
d’aki, da Sauri Abla ta d’aga mata kai tana barin Wajan , sai a lokacin abla ta
kallesu idanuwanta har sun d’an canza , cikin Sauri ilham zatayi magana Abla ta
dakatar da ita tana kallan uwar karuwai cikin tsana , itama uwar karuwai rai a’bace
take kallan abla ganin ta ‘bata mata shirin ta , bayan vidoe d’in da zata d’auka
suna lesbian da Arwa ba ‘karamun kud’i zata samu ba , amma lokaci d’aya Abla ta
‘bata mata shirin komai ,”idan kin za’bi lalata ‘ya’yan mutane kina tunanin baki da
d’a ko ‘ya da za’ayi wa kwatankwacin abunda kikai karki manta kina da ahali , yadda
kike ‘bata ‘yayan mutane Kema Haka za’ayi miki sabida kamatudinu tudan , ko me
kukai sai anyi muku, yadda kuka ‘bata rayuwar yara da yawa ku jira sakayya wajan
ubangiji, a haife gabaki d’aya zaki haife su amma duk da wannan shekarun naki kece
kike ‘bata tarbiyarsu Sabida basu da gata ? Tur da halinki”, ke cewar ‘yar shila “,
da ‘karfi itama Abla rai a ‘bace ta daka mata tsawan da duk na cikin d’akin saida
suka d’an razana da jin sakkunta, musamman yadda take magana babu tsoro tattare da
ita “kin dad’e kina yi mun abu ina kyaleki Amma gabaki d’ayanku baku san kawaici ba
, duk yadda mutum Yaso ya danne abu sai kunsa ya fallasashi, daga rana irin ta yau
duk Wanda ya ce zaiyi mun abu kamar yadda ya saba yimun ada Zaiga asalina , karku
d’auka a Abla da kuke yiwa komai nake muku gamana , a asalin sunana ibtissam nake ,
shekara biyu na shanye duk ‘bacin ranku amma banda yanzu,” kuma ta juya kan ilham
da take tsaye tana kallan abla da mamaki “ kin bani mamaki ilham , da hankalinki da
iliminki? Agaban idanuwanki ake ‘ko’karin lalata tar biyar yar uwarki musulma amma
kina gani ? Tir da irin masu halinki “, tana kai zancenta ta juya zata tafi taji
saukar muryar uwar karuwai “Naji kome kika fad’a Amma karki manta gida gida nane ,
dole mutum ya za’ba ko ya bautamun ko ya dinga biyana kudin kwana, tunda ko uwarki
da ubanki baki sansuba balantana kiyi fariya kina da gida ko ahali”, maganar uwar
karuwai ya ta’ba mata zuciya har kwalla taji na ‘ko’karin sakko mata tayi saurin
had’iye ta , tana jin zafi duk dokacin da aka Goranta mata ,juyowa tayi fuskarta
d’auke da murmushin bakin ciki , “ Indai akan biya ne duk sati zan dunga biyanki
kud’in kwanan store d’in da nake Amma daga yanxu babu duk wacce tayi ‘ko’karin
tunkarata ko tunanin yimun wani abu tabbas zataga‘bacin rai na , tana kai karshen
zancenta tabar d’akin ta bugo musu da ‘karfin, jikin kofar ta tsaya hawayen da take
ri’ke wa ne suka soma wanke mata fuskar sosai take hawaye zuciyar ta d’aci take
mata sosai, tuno arwa ysa tayi saurin nufar d’akinsu , zuciyar ta fall tunanin
saba’ar da zata fara har ta biya uwar karuwai.
A cikin d’akin kuma d’an tsaki ilham ta saki “ yar shila shikenan kunja Abla ta
ganeni tun farko sai da na fad’a muku kome zakuyi dani ya Xama cikin sirri amma
lokaci d’aya kun ‘bata komai , yanxu bansan na zanyi ba karku manta 3million zasu
samu idan mukai wa Arwa da Abla vidoe tsirara musamman yanxu da dama tazo mana ,sai
da nace muku ku bari dare yayi sai ayi vidoen Arwa Amma gabaki d’aya kun bata
shirin yanxu yadda kukaga Abla tayi magana babu tsoro ko shakka a cikin idanuwanta
tabbas bazata ‘kara bari wani ya takataba. Nasan Arwa yanxu zata fallasa mana duk
wani sirri. Kusa da ita uwar karuwai ta matso ba kunya ko ganin irin su Zinariyya
tajanyo ilham jikinta “ baby karki damu duk bugace take yi , dole ta zauna damu har
burin mu yacika sabida na tabbata bata da kudin da zata dunga bamu duk sati , dole
kinga tayi mun bauta kicire damuwar nan aranki, kamar yadda na gur’bata Aneesa da
husna suma sai na gur’batasu dan bariki shine jigon mu, me za’ayi da wad’an da basa
bariki, duka ilimin ‘karya take na tabbata wajen da take zuwa taba yini kwakuleta
suke suma kawai ki saki jikin ki mu shana baby, yanxu ki kwantar da hankalinki
kicire zancanta mu d’an huta , kamar ki na cikin fridge na ajje mata “, gabaki
d’aya sun gansu da bayanan uwar karuwai shiyasa debeka ta kashe musu fitula ,
dariya da cewa Suka d’auka cikin duhu sai nunfashi da Suke saki kawai.

****** Abla tana shiga d’akin ta tarar da arwa kwance tana kuka , a gefenta abla ta
zauna, itama Arwa tana ganin abla ta Tashi zaune , cikin kuka ta soma magana “ Abla
na gaji da wannan kuncin rayuwar da muke ciki, mutane kullum burunsu su lalata
marasa gata , Menene aibun mu dan muntashi cikin maraici? Ko maraicin da muke ciki
ne yasa kowa burinsa yayi lalata da mu? Dabadan kinzo da wuri ba Abla da tuni sun
lalatamun martabata, kece kadai kike sona , ban sani ba kuma bansan lokacin da
ilham take cikinsuba abun ya d’aure mun lokacin da na gansu tare ga Aneesa da husna
suma sun lalata musu rayuwa, ji nake Abla dama wani mummunan abu zai sameni na mutu
ko zan huta da wannan takaicin rayuwar”. Saurin toshe mata baki abla tayi “ inda
rai ya ‘baci hankali ai be gujewa, ko Menene ya samemu jarabawace daga Allah, yana
sane damu sannan yasan halin da muke ciki, wani jirkirin Alkairi, kindunga kyautata
Alkairi cikin zuciyar ki”, duk yadda ran abla yake a ‘bace Hakan be hana tayiwa
Arwa lallausan lafazi me kwantar da hankali ba . “Abla yunwa nake ji, ina tunanin
bara zan fara ko zamu samu abinci dan bazan kara cin komai na zunubin suba . Inda
ta ajje kudin ta ta shafa taji suna nan, “ zo mufita “ cewar abla tana ri’ke hannun
arwa, a duniya dari biyar d’in da aka bata sadaka ce kawai tayi mata ragowa gashi
tace duk sati zata dunga biyan uwar karuwai kud’in kwananta, ‘kosai ta siyowa Arwa
na hamsin, ganin kudin na yin ‘kasa yasa ta hakura daci tabarwa arwa , ita kuma ta
Samu gyad’ar ashirin taci , suna gama ci gidan ruwan da Abla ta ta’ba zuwa sukaje
amma sosai akwai layi saida suka bari aka gama zubawa manya mota ruwan kafun azo
kansu , yau ma talatin ta bayar aka bata guda 9, haka suka d’auka suka fara yawo
Dashi cikin traffic ga ranar da ake me zafi ci amma haka suka shiga cikin traffic
ko za a samu me shiyan ruwa , sun dad’e suna yawa daga traffic zuwa traffic kafin a
siye musu ruwan , cike da farinciki suka ‘kara komawa a wannan karan na 40 aka
‘kara musu guda biyar akai , su biyu sai yawo suke cikin zafin ranar, suna cikin
tafiya ko d’ad’d’an silifas din Abla da yayi mata kad’an ya tsinke, cikin da bara
ta samo leda ta kulle takalmin ta mayar ‘kafarta tunda bata da kudin siyan wani ,
ko da tanadashi ma bazata siya ba sabida kudin da zata bawa uwar karuwai. Har wajan
karfe biyu suna abu d’aya saidai su Samu waje suyi sallah kafun su cigaba , sosai
rana ta dakesu amma duk da haka sun kwammace su zauna a cikinta akan su koma gidan
karuwai.sai da sukai la’asar suna siyar da ruwa ‘kafafuwansu gabaki d’aya ya sage
sabida gajiya , duk da bawani kudi suka samu ba Amma iya ribar da suka zamu cikin
ruwan da suka siyar sosai sukai farin ciki da haka , lokacin da Abla ta bawa Arwa
wani kaso a cikin kudin ‘kin kar’ba tayi , acewarta in sun samu abinci sai su siya
dashi, yau ko daman zuwa makarantar allon Malam sule batayi ba, da zasu dawo gida
zallan rogo suka siya na hamsin d’insu . Kamar yadda ta saba dawowa kullum Anfara
tashin kid’a yau sai tayi sa’a basu kunna ba sabida itama ta dawo gida da wuri ,
babu Wanda yaga shigowarta ita da Arwa suka shige d’akinsu, suna shiga suka tarar
da husna zaune kan katifa ga wata tanfatsetsiyar waya a hannunta tana dannawa , ga
lemo da gasashshiyar kaza tana ci, da harara da Abla dashi itama Abla ko kallan
inda take batayi ba ta zauna ita da Arwa akan kwalinsu suka faracin rogonsu, wata
yar iskar dariya husna ta kwashe da ita “ a haka mutum zai ‘kare a tsiyace ana nuna
masa gabas yana runtse ido , in banda tsiya mata da maita me mutum zai ci a rogo “,
wani banzan kallo Abla tabi husna Dashi da yasa ta rufe bakinta, cike da wulakanci
husna zata d’ao gashshiyar kaza ta yaga sai ta furta “ Gaza da dadi rangen
rangengen “, babu Wanda ya kulata tsakanin Abla da Arwa , Aneesa ce ta Fito cikin
toilet tana ganin Abla ta sakar mata murmushi “ Abla har kun dawo “, tsayawa
kallanta Abla tayi ganin yadda Wajan idanuwanta sukai baki baki gata ita kanta sai
faman rangaji take kamar zata fad’i, wata sabuwar doguwar Riga ta saka mara nauyi
ta haye katifarsu nan da nan bacci ya d’auketa me nauyin gaske , Ana kiran sallah
kid’a na tashi me ‘karfin gaske da kashe dodan kunne , da ‘kyar Abla ta Samu tayi
sallah sabida yadda kid’an ya karad’e ko ina , a matsayinta na ‘ya mace be kamata
tana zama a waje ba cikin dare musamman yadda duniya ta lalace , shiyasa duk da
‘karan da yake tashi ta yi zamanta tunda babu yadda zatayi, wasu tsofaffin papers
ta d’auko sai faman dubasu take d’aya bayan d’aya tana ‘kara karantasu, har lokacin
Aneesa da ta kwanta bacci take kamar wata bawa , lokaci zuwa lokaci Abla takan
d’ago ta kalleta ganin yadda take baccinta kamar mara rai ajiki . Tunda Husna ta
fita tasan bazata dawo ba sai kuma wani ikon Allah sabida wankan da tasha, har
lokacin kuma bata ‘karasa ilham a idanuwanta ba itama kuma bata damu da inda
tashiga ba.
Lokacin da Arwa ta dawo d’akin hirarsu suka sha gwanin burgewa , 10:30 na dare
lokacin da kid’an yafi tashi suka kwanta tunda sunyi sallar isha’insu, sai da abla
ta kulle musu ‘kofa gagam kafun su kwanta , har lokacin Aneesa bacci take .
✨✨✨✨✨

WASHINGTON D.C

1600 PENNSYLVANIA AVENUE, N.W.


THE WHITE HOUSE

PAY YOUR MONEY INTO 2681892316 , AISHA UMAR , ZENITH BANK SAI A TUROMUN SHAIDAR
BIYA TA WANNAN NUMBER 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨
Littafin IBTISSAM is now 300 instead of 500 , me bu’katar ya karanta littafin har
‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha
umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book
ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar
sa, to a rashi sani ne .

___💞💞And ( Remember)when your lord proclaimed,”if you are grateful, I will surely
increase you (in favor );but if you deny, indeed, my punishment is severe “…..💞💞___

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

Season __11

WASHINGTON D.C

1600 PENNSYLVANIA AVENUE, N.W.


THE WHITE HOUSE

Babban farin gidane me shegen kyau da tsaruwa, kowa yasan yadda tsarin gidan turawa
yake musamman idan aka shigo fadar shugaban ‘kasa , anan ma hakan ce ta faru sabida
tsaruwa da haduwa da White House yayi, ga securities da sojoji ta ko ina musamman
da ya kasance His excellency Mr president yananan, ko ina ka waiga zakaga soja
Sabida irin had’uwa da tsaran lapiyar sa data ilayinsa da ake baki d’aya .
A cikin ‘kayataccen falourn da zai tabbatar maka da dukiyar da take kuka a ciki,
his excellency Vice president ne zaune kan kujera yayi crossing legs d’insa hannun
sa d’aya ri’ke da wani had’ad’d’an kofin coffee da yake sha. Bud’e ‘kofar da akai
ne yasa vice president yayi saurin ajje kofin hannunsa tare da mi’kewa tsaye
lokacin da yaga shigowar mr president, yana shigowa masu tsaransa suka dakata Amma
duk da Hakan kana iya hangosu. Farin bature ne kana ganinsa zaka ga haifaffen d’an
America, a shekaru kuma bazai haura 60 years ba , bayan sun gaisa sosai sai Vice ya
kalli president cikin girmamawa duk da yabada umarnin kar Wanda yashigo tunda
tattaunawar sirri zasuyi Amma duk da haka matsu tsaransa suna kallansu ta camera
maganar da suke fad’a ne Kawai basaji, “ your excellency sir , maganar Nicholas ne
“, kasancewar da turanci suke magana ,jinjina masa kai Mr president yayi akan yaci
gaba da magana “ it’s about Nicholas da ya ‘bata a New Zealand, bawai dagangan
‘batan yayi ba sir , d’aukesa akai intentionally “, yanxu ma cike da wani mulki Mr
president ya kallesa, “ kayi magana da president d’in New Zealand ? “, yanxu ma
cike da girmamawa VC ya cigaba da magana “ your excellency basu da hannu aciki,
asalima nasan yana hannu wa “, suite d’insa Mr president ya d’an ta’ba “ and ?shine
kazo kana fad’amun bayan kasan inda yake ?”, your excellency nayi ‘ko’karin hakan
but duk ya tashi in vain, maganar kace kad’ai zaisa ya sako su because na Samu
complain har da yaran mayor da governor New York ya kama yaransu”, rai a d’an ‘bace
mr president ya furta “ what’s this nonsense ? Na bada kwana d’aya koma wanene ya
kamasu ya gurfana sannan ya dawo da duka yaran “, Mr president na kai ‘karshe Vc ya
d’ora da “ yana da taurin kai sir na tabbata maganar ka Kawai zaiji “,you as my Vc
bazaka iya ba kenan ? Then Menene anfaninka “, sorry sir cewar Vc, Mr president be
kuma cewa komai ba tsawan mintuna d’aya kafin ya bud’e bakinsa “ ina bu’katar
ganin chief nan da 2 d’ays sannan ko wanene inasan a gurfanar mun dashi sannan
akarbi mu’kamunsa,” shi Vc ba wannan ne abunda yafi d’aga masa hankali ba , yasan
idan his excellency yasan wanene zai iya bin goyan bayansa amma duk da haka ya zama
dole ya fad’a masa tunda big boss kamar d’a ya d’aukesa “ Big boss ne “, cewar Vc ,
kallansa mr president yayi lokaci d’aya kuma ya saki murmushi me d’an Sauri da har
saida Vc ya kallesa “, kana nufin kace my son shine ya kama Nicholas ? Lefin me
sukai ?”, shiru Vc ya kasa basa amsa , ynxu ma murmushi me sauti his excellency ya
saka tare da mi’kewa tsaye “ nasan ko wanene Son dina , kome zaiyi saida dalili
inkaga ya shiga abu toh tabbas ankaisa ‘karshe , zanyi magana dashi , nan da 1 week
ina bu’katar tattaunawa ta musamman, bana bu’katar ganin kowa sai iyayen yaran ,
chief sai masu hannu a case d’in,zanyi wa son magana da kaina “, yana kai ‘karshen
maganar sa ya bar falon bayan securities sun bud’e masa door , Vc ma kofar da zata
futar dashi ya nufa ba wacce his excellency ya fita ba yasan daman za’a rina ,
bazai yi wani mistake ba yasan falourn cike take da CC Tv , rai a’bace yabar White
House a wannan karan yana ji aransa dole ya karbo d’an sa ko zaiyi anfani da
mu’kamun sa na vice president of the United state, dalili d’aya ne yasa yake bin
komai a sannu ya tabbata kome zeyi president zai d’aga masa kafa amma ban da abunda
zai ta’ba big boss , ya rasan basu da ala’ka Amma yadda yake bun goyan bayan Big
Boss da komai da ya shafesa kamar d’an sa yafi komai jijjigasa.

***** His excellency kai tsaye inda zai sadashi da ilayinsa ya nufa , lokacin da ya
shiga masu tsaro sai faman gaishesa suke dukda babu me kuskuran d’ago da fuskarta
ya kallesa , wata baturiyar matace ta fito daga wani ‘kofa kana ganin fuskarta zaka
ga damuwa kwance a kan fuskarta duk da yadda Hutu da jin dadi ya ratsa farar
fatarta musamman yadda take sanye da ‘kananan kaya a jikinsa , gashin kanta da ya
sha gyara sai faman yawo yake a bayanta ,tana ganin president Sukai hugging junna,
shima sai yayi pecking goshinta “ me ya faru naga fuskarki ta sauya ?”, cike da
damuwa matar ta furta “ Alice ce , har yanxu ta saka damuwa a ranta , ko abinci
bata san ci, I can’t take it, you’re the president of the whole u.s , you have to
keep my daughter in happiness kome take so ayi mata shi ko zai sa ran wasu ya
‘baci, daman momy Alice haka take indai abunda zai ta’ba Mata daughter d’inta
kwalli d’aya ne ta gwammace ran kowa ya ‘baci Indai yarta zata Samu abunda take so
and bata ta’ba Gaza mata ba sai a wannan karan da ta kasa bata abunda take so, “I
will check on her “, cewar sa tare da shiga inda ta fito, nan ma wani kayataccen
wajene na gani na fad’a ga masu tsaro burjic a wajan , d’akin Alice ya nufa nan ma
sosai d’akin ya gaji da had’uwa , kwance take kan kayataccen gadon ta tayi rubda
ciki ba’a iya ganin fuskarta sai santala santalan fararan cinyoyinta da suke sanye
cikin wani d’agaggen wando da ko cinya be kai mata ba sai yar fingilar rigar
jikinta da bata rufe mata ‘kugunta ba, cikin voice d’inta ta furta “ mom , nace
kawai ki futa , baba bukatar ganin ki ,just go out “, shiru be amsa mata ba sai ma
zama da yayi a gefenta, rai a ‘bace ta d’ago face d’inta ,Wanda ta ganine yasa tayi
hugging d’insa “ Dad , please ku aura munshi, I can’t leave my life without him
dad, nasan zaka iyayin komai ,inaso wannan ma ka mallakamun shi, ina san shi please
“, gashin da ya rufe mata fuska ya gara mata, ba mummuna bace , Daidai gwargwadan
kyau tana dashi musamman yadda take kashewa skin d’inta kud’i shiysa ta karayin
kyau” it’s okay , banasan kina saka damuwa aranki , nasani 1 day one time he will
marry you, and kece kad’ai zaki zama matarsa like your mom “, pecking dinsa tayi a
goshi “ plx dad , kasa ya aureni ina san shi tun lokacin da na fara ganinsa, inaso
ni ko yanxu kasa ayi mana aure “, dariya ya saki me Sauti “ kinsan wanene Wanda
kike so ki aura fa , do you think irin mutanan da ake wa aurene just like that?nan
da 1 week zamuyi wani meeting and zansa ku had’u ,just you have to convince him
with your love , okay ?”, yes dady ta fad’a tana turo baki “ oya ki tashi ki shirya
“, yes dady ta fad’a , wani pecking dinsa ta karayi a kuma tu shima hakan yayi mata
yana fita ta mi’ke tsaye dogon gashin kanta da yasha gyara ya sakko mata a bayanta,
sai yar filgilar rigar ta da ko cibiyarta bata rufeba , ga Santala santalan
kafafunta da Suka fito cikin dan mitsitsin wandon jikin ta, Inda jerin beers d’inta
suke ta nufa , cikin wani d’an karamin glass cup ta zuba giyar tana sha a hankali
cike da yanga , a hankali ta furta “ My Big boss , na matsu na ganta, I just want
to see you in my arms, ni kad’ai ce matar da akayi maka, and babu wacce ta isa ta
zama mallakinka sai ni , idan ba haka ba sai na kasheta,ko ma wacece, I’m Alice ,
babu Wanda ya isa ya Samu abunda nake so a duniya , ko me nayi niyar samu sai na
sameshi, I can’t wait to hug you so tie “.

🍂🍂🍂🍂🍂

KANO
NASARAWA G.R.A
Wani irin kid’a ne me karfi yake tashi cikin wani d’aki meshegen kyau, kana ganin
d’akin kasan d’akin macene sabida yadda aka ‘kawata d’akin da design pink colour ,
wani irin haske me kaloline yake haska d’akin, ga daddad’ar wa’kar da take tashi ,
lokaci zuwa lokaci zaka d’anji ihu kad’an na mace na tashi a cikin d’akin. Turo
‘kafar shiga cikin d’akin akai amma duk da haka wakar tashi take sosai ga kalolin
da ya ‘kara ‘kawata d’akin sai faman haskawa yake ,wacce ta shigo wani d’an button
ta danna take a wajan haske ya karad’e ko ina nacikin d’akin , lokaci d’aya fitulun
da suke haska d’akin suka tsaya sai farar hasken da ya karad’e ko ina , a zuciye
matashiyar budurwar da take jin wa’ka ta juyo cikin zafinrai “ uban wanene zai
shigo mun d’aki batare da izinina ba ?”, cewar matashiyar cikin daddad’an
muryarta , kyakkyawar matashiyar budurwace da akalla a shekaru bazata haura 17years
ba , Allah ya bata baiwar kyau duk da ba fara bace sosai Amma babu Wanda zai
kalleta yace mata ‘baka dan skin dinta me shegen kyau ne da ko chocolate baza a
kirata dashi ba sabida haskenta daya banbanta , d’ara d’aran idanuwanta masu d’auke
da ba’kin kwalli ta zubawa matar da tashigo cikin d’akin , a zuciye ta ja dogon
tsaki cikin d’an mitsitsin bakinta pink colour ,cikin kaskanci ta kalli matar da
akallo d’aya da mutum zaiyi mata zaisan yar aiki ce “ me nace miki? Uban me kike
mun ma a d’aki da xaki shigo da ‘Kazantar jikinki cikin d’akina ?”, murmushi matar
ta sakar mata ,duk da kasancewar ta mai aiki amma itama Allah ya bata baiwar kyau
sihirtacce duk da shekarunta duk wanda ya ganta sai ya ‘kara kallanta sabida
tsananin kyan da Allah ya bata , farace sosai duk da hijabin dake jikinta a gefe
gefen fuskarta zaka ga wasu kwantattun gashi da ya ‘karawa fuskarta kyau “ kiyi
hakuri hajiya ce take nemanki”, dallah yimun shiru , cewar matashiyar budurwar tana
katse ta “ duk ranar dana ‘kara ganin kazamin kafarki cikin d’akina na lahira sai
ya fiki jin dad’i haka Kawai bazaki zo ki shafa mun cuta ba irin taku ta talakawa ,
get out “ ta daka mata tsawa ,wani guntun murmushi matar ta ‘kara saki tana
sunkuyar da kai , kafun ta furta “ kiyi hakuri ‘karamar hajiya “ budurwar bata kuma
cewa komai ba sai ‘kofar fita da ta nufa tana kakkare hancinta .
Tana fita ta ‘kara jan wani tsakin rai a ‘bace “ gaskiya bazan iya ba , ko a
ina momcy ta kwaso wannan ‘kazamar ,momcy tasan na tsani talaka bansan me yasa ta
kwaso mun wannan kazamar ba , gabaki d’aya tazo ta cika mun d’aki da wari, haka
kawai bazata zo ta shafamun warin jikin taba .” Tana kai ‘karshen zan centa ta
d’akko turare ta feffesa a d’akin , jikinta sanye yake cikin ‘kananan kaya peach
color da ya d’an kama jikinta , wani half cushion shoe ta saka na zaman gida ta
fito daga cikin d’akin bayan rantsats tsiyar wayar ta iPhone 12 data data d’auko
tana dannawa kunnanta sanye da wani pod na wa’ka . Cikin babban falon su da yaji
kayan alatu ta nufa, ita kadai sai bin wakar da takeji take har ta ‘karasa ciki,
tana shigowa matar da ta gani zauna kan manya manyan kujerun falon ta nufa da gudun
ta duk da fuskar matar be fito ba , ta baya tayi hugging d’inta “ momcy na”,
murmushi ne ya Tashi me Sauti lokacin da matashiyar budurwar ta fuskanci matar da
Hutu da dukiya ta zauna mata , ga jikinta da yake sanye dan manya super holland
masu shegen tsad’a ga uban sarkar kwal da tayi ado Dashi amma duk da Haka tayi kyau
ba kadan ba musamman yadda gold din yake kyalkyali. “ my baby kin fito kenan ?” Dan
tabe baki tayi a hankali ta furta “ yes naji Ance kina kirana hope ba wani abun
bane “, cewar budurwar da aka kira da baby “ No baby bashi bane , I think am going
out now , idan dadynki ya dawo kice masa na fita because bazan iya jira ya dawo ba
kafun na fita , okay “, yanxu ma ta’be baki babyn tayi “kuma sabida wannan abun
zaki kirani ina tsaka da jin wa’ka ta , and me yasa baki saka Eshaal ba sai ni zaki
kira “, ko ajikin matar yadda baby tayi mata magana a gadarance cikin rashin kunya
sai ma lallashinta da ta farayi “ Haba baby na , kinsan banasan shabgata musamman
idan ya had’a da daddynki shegiyarcan ta shiga ,kinsan ta da shegen munafinci”,
remote baby ta d’auka “ it’s okay naji, Amma ni yanxu yunwa nake ji, kisa ta dafa
mun abinci dan banaso waccan ‘kazamar ta dunga mun girki,”wani dadi ne ya kama
momcy baby sabida maganganun baby da ya faranta mata , “ ko me kikeso haka za’ai my
baby bari na kirata yanxu”, wani telephone momcy ta d’auka tare da dialing wasu
number guda 3, ana d’aga wa cikin ta’be baki momcy ta furta “ minti d’aya na baki
ki zo ina nemanki a falo and idan kina tare da kazamar me aikinnan ki tabbata kin
wanke jikinki karki sa mana cuta ni da baby”, tana kai ‘karshen zancenta ta kashe
kiran. Ko minti biyu Ba’ayi ba , na soma jiyo takun ta kalli yana tun karo falon da
su baby suke ciki, a hankali ta shigo cikin falourn , cikin daddad’an murya tayi
sallama ,babu Wanda ya amsa mata tsakanin baby da momcy, itama budurwar da ta shigo
bata damu da amsawar tasu ba dan ta saba da irin halinsu, farace itama sosai irin
farin fulani ga tsantsan kyau da Allah ya bata iriin na fulani, jikinta sanye da
doguwar ba’kar abaya tayi rolling da farin mayafi, yadda kanta yayi tudu zaka gane
tana da gashin kai musamman yadda hakan ya nuna ta mayafinta , had’e rai momcy tayi
lokacin dataga matashiyar budurwar itama baby wani dogon tsaki taja tana binta da
kallon tsana , cike da gadara da izza tun kafin budurwar tayi magana Momcy ta
dakatar da ita” bana bukatar jin komai daga bakinki, yanxu maza ki tashi kishiga
kitchen ki dafawa baby abinda take san ci, and banazo ko wace kazama tayi mata
aikin abincin saike “, girgiza kai kai Eshaal tayi tana bin baby dake hararar ta da
kallo , “ amma mom…” bata ‘kara sa zancen da take sanyi ba momcy ta d’auke face
d’inta da mari ,” amma me ? Na saki abu kina cemun amma ? Amma d’in uwarki?zaki
tsugunna ki tanbayeta me take so ko sai ranki ya ‘baci”, kwalla ce ta sakkowa
Eshaal da Sauri ta goge ta tana durkusawar “ me za’a dafa miki?”, cewar ta tana
kallan baby, banza baby tayi mata tana latsa wayarta kamar bata san da wanzuwar
wani ba a Wajan , sai da Eshaal ta maimaita kalmarta sau uku kafun baby ta d’ago
fuska a ya mutse “ ki tashi ki had’a mun rich friedrice da coslow sannan ki
had’amun farfesun rago, nasa, da kuma na kaza , ko wanne daban daban ,sannan sai
strawberry milkshake da banana milk shake da nake so,kallanta sosai Eshaal tayi jin
abubuwan da baby ta lissafa Wanda tasan idan za’a kasheta ba lallaine taci abincin
ba wahala kawai take san sakata “ kin dai ji abunda ta lissafa, ki tashi ki bani
waje “ cewar momcy tana binta da wani kallan tsana, jiki a sanyaye Eshaal ta mi’ke
jikinta duk a sanyaye hawayen da suke sakko mata ta share , yadda momcy da baby
hatta dady da bayansa ra’barta suke mata abubuwa abun na tsaya mata a zuciya
shiyasa kullum cikin adduar Allah yajikan ammeyta take ,duk lokacin da zatayi
sallah sai tayi addua wa mahaifiyarta sabida ji take kamar bata da kowa a duniya,
mutum d’aya ce take ‘ko’karin kwantar mata da hankali a duk lokacin da take cikin
kunci ko tashiga maraicin uwa , AMMA ce kad’ai ke share mata hawayenta duk da yadda
itama bata tsiraba Wajan baby da momcy kasancewarta yar aiki kuma a ‘kar’kashinsu.
Tasan yanxu tana komawa Amma zatace zaka temaka mata , ita kuma batasan abunda
zaisa Baby ta wulakanta ta shiyasa bata tsaya a ko ina ba sai kitchen , ita kadai
sai tunanin ta inda zafa fara uban abincin da baby ta tula mata take .

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

ABUJA
ADEMOLA ADETOKUMBO STREETS _!

Karfe 2:30am ‘kishir ruwa ya farkar da Abla , Allah ya temaketa akwai haske har
lokacin ba’a d’auke wuta ba , bakinta d’auke da addua ta farka , mamakin ganin
‘kofar d’akinsu abud’e ne ya kamata , wai gawa Abla tayi taga Arwa na baccin
hankali kwance, inda Aneesa take a kwance ta kalla , babu kowa akan katifar daman
batasa ran ganin Ilham da husna ba , a hankali ta fito daga cikin d’akin cikin
tafiya a hankali da ‘yar fargabarta ta fito falourn ,still shima falourn fitilarsa
a kunne yake , shiyasa wani tsoran ya ‘kara kamata , ita tsorantama kar ace wasu ne
suka shigo suna bacci suka d’auke Aneesa ganin bata cikin d’akin,bata gama shiga
cikin mamakiba sai lokacin da taga ‘kofar falourn abud’e ga hasken fitula da Alama
wanine ya fita , cikin sand’a yanxu ma ta nufi ‘kofar wajan, da Sauri tayi
‘ko’karin janyo ‘kofar falourn Amma motsin da taji a wajane yasa ta ja burki, ga
tsoro tana ji amma zuciyar ta tana san ganin su wanene a wajan , waige waige ta
fara idanuwanta suka sauka kan sandar data hango , cikin sand’a ta rarrafa a
hankali kada suji motsinta ta d’akko sandar ta kara rarrfawa ta koma bakin kofar, a
tsugunne ta fito waje tana sand’a a hankali a hankali, Inda taji motsin ta nufa
tare da rike sandarta gam a hannu, ga addua da take cikin zuciyar ta hannunta data
ri’ke sandar shima sai rawa yake a hankali ta soma jin magana kad’an kad’an, cikin
dabara ta ‘karasa wajan mata biyu ta gani akan wani dakali ga kwalba kamar ta
magani a kusa da su , mamaki ne ya kama Abla “ idan basu da lapiya Menene na ‘buya
cikin dare kafin su sha maganin “ tana cikin maganar zuci taga kamar za’a juyo da
sauri ta ‘kara buya gudun karsuganta, muryar Aneesa da taji kamar me magagin bacci
ne ya bata mamaki “ toh me take Anan ? Baccin ne be ishetaba ? Ko bata san ta fito
ba ? Ita kadai Abla take maganarta cikin zuciyarta bata gasgata muryar Aneesa ba
sai da ta ‘kara le’kowa taga ta d’aga wani kwalbar magani tana kwankwad’a , abla
bata san lokacin da ta karasa ta warce kwalbar ta yar a kas ba ,” Aneesa baki da
hankali ne zaki dauki magani haka kiyi Tasha ? In baki da lapiya ki fad’a mana Amma
bawai ki dinga shan magani ba batare da kin aunaba, a zuciye Aneesa ta d’ago da
idanuwanta tana kallan Abla sai faman lumshe idanuwatake kamar me jin bacci, cikin
wata iriyar murya ta furta “ uban wa yace ki yardar mun dashi , eh ? “ yar shila
dake gefenta ma sai faman lumshe ido take , shurun da abla tayi tana kallanta da
mamakine yasa Aneesa tayi kokarin tashi Amma ta kasa sai faduwa da tayi , cike da
maye yar shila ta ‘kyalkyale da dariya “ rabu da ita bata san duniyar da muke ba ,
barta yar wahala , karki damu zan baki wani gobe kinji”, cewar shila yadda take
magana zakasan abuge take , itama Aneesa dariya ta saka “ shikenan toh na hakura
Amma duk lokacin da ta kara yi mun haka sai na ‘bata mata “, tana magana tana
tafiya ta jikin bango sabida yadda ta kasa tafiya sai da ta jin gina da bango a
haka tana layi ta wuce Abla da shock ya kamata , ita yar shila tana tangad’i ta
wuce Abla , kwalbar da tayar ta kalla kafun ta karasa wajanta “BRONCLEER “shine
sunan da yake jikin maganin, d’an shin shina wa tayi sai tayi saurin yar darwa tana
toshe hancinta , fasa shan ruwan tayi ta koma d’aki har yanxu mamakin ganin Aneesa
na drug abuse ya ‘ki wuce mata arai, tana shiga d’aki ta tarar da ita kwance tana
bacci kamar ba Itace ta shigo ba “, kulle d’akin tayi ta kwanta itama , ruwan da
bata sha ba kenan .

4:30am ta farka yau ta d’an makara tayi mamakin rashin tashin ta da su debeka
basuyi ba , bata damu da hakan ba itama , shaf shaf ta soma share Fallon da kullum
yake cikin ‘kazanta tana gamawa tayi mopping ta gyara d’akunan da babu kowa a ciki
da toilet d’insu , tana gamawa ta had’a wanke wanke Amma bata fara ba sabida sallar
da take san tayi, tana idar da sallar ta soma wanke wankenta har lokacin kuma babu
wanda yafito , sai da ta kammala gabaki d’aya aikinta tukunna ta samu tayi wanka
duk da bata da sabulun wanka haka tayi wankanta sannan ta sa’ba kayanta ba ko omo
sai tsofaffin ragowar ko d’ad’d’en kayanta da tasaka , Arwa ce ta bude idanuwanta
ganin Abla na shiryawa , itama mi’kewa tayi tayo alwala Abla ta Ara mata hijab
dinta zatayi sallah, sai alokacin uban tulun gashin Abla ya fito duk da yana cikin
d’an kwalunta amma yayi wa gashinta kad’an ga kwantaccen gashin ta daya kwanta ,
tanasan wanke shi amma bata da abun wanke wa shiyasa take hakura . Arwa na idar da
sallah suka fita , cikin kudin Abla suka siya kosan hamsin suka ci duk da beje musu
ko ina ba Amma haka suka hakura tunda basu da kudin siyan me yawa , yanxu ma gidan
ruwa suka nufa ga rana haka suka jira a kazo har kanzu, rana na dukansu haka suka
dunga siyar da ruwansu , yau ko cinikin arziki basuyi ba ga gajiya da sukai , ba
yadda suka iya haka suka Zara cikin kudin suka siya rogon saba’in sukaji sabida
yunwa , har akai sallar la’asar suna abu d’aya sallah ne kadai ke tsayar dasu yau
ma ko makarantar allo bata samu taje ba haka ta hakura zuciyarta fal tunanin yadda
zata biya uwar karuwai kudin ta. Har suka koma gida wannan tunaninne fal cikin
ranta.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

UNITED STATES 🇺🇸

Yau little ne ya fara farkawa daga bacci , agogon d’akin ya kalla yaga da sauran
mintuna kafun ayi kiran sallah, wanka yayi cikin shigar jallabiya da wani rawani
fari irin na larabawa , yadda ya d’aura abun sai ya zama kamar cikakken balarabe ,
kadan ya fesa turare gudun kar ya Tashi prince dake bacci ya bude kofa a hankali ya
futa , kai tsaye part din bobo ya nufa ko tsoran duhu bayayi , be tsaya a ko ina ba
sai d’akin bobo, da wani dum light green yake haskawa , a hankali little ya
salalla’ba ya nufi gadon bobo, baiyi wata wata ba Kawai ya d’ane jikin bobo, cikin
wani irin zafin nawa bobo ya juya little dake jikinsa hannusa d’aya akan ma’kogaran
little , d’ayan hannunsa kuma ya saita kan little da bunduga, murya a shake little
ya furta “ yaya bobo “, da Sauri bobo ya sake sa yana d’aga sa, fitular d’akin ya
kunna gabaki d’aya haske ya Haska ko ina na d’akin , ruwa bobo ya mika matsa yana
shafa wuyarsa “ are you okay ?”kansa kawai little ya jinjina masa , hugging d’insa
bobo yayi thank god beyi garajen sakin bullet ba ,” me yasa ka d’ane jikina ? Da
nayi maka wani abun fa ?”, cewar bobo “ sorry yaya bobo nazo tashin Kane fa , sai
kawai naji kajuyani kamar a mafarki”, keyarsa bobo ya talle “ babu kyau ka bari,
idan ni kasamu ban saki bullet dina ba , duk ranar da kayi wa yayanka sai ya
tarwatsa maka kai da bullet “, dariya little ya saki, ganin yadda yake dariya ne
yasa bobo yaji dad’in hakan .” Oya kaje ka tashi su uncle ma nasan ni kadai ka tasa
“ Tom yaya “ cewar little yana barin d’akin , d’akinsu ya koma ya tarar prince na
bacci har yanxu wani abun d’awisu ya dakko guda d’aya yazo Daidai saitin kafarsa
yana masa tafiyar tsutsa, mutsu mutsu prince ya soma Amma be bude idanuwansa ba ,
toshe bakinsa little yayi kar dariyar da yake dannewa ta fito waje ,kara sa masa
d’awisun yayi Amma still be tashi ba , sai Tin hancinsa little ya dawo , da ya saka
masa prince Zai sosa hancin, sai kuma ya koma kunnansa wani irin jutt da prince
yaji ne yasa lokaci d’aya ya ware idanuwansa akan little, dariya little ya
kyal’kyale Dashi yana ja baya, ganin yadda prince ya za bura rai a bace , “ sorry
yaya prince , yaya bobo ne yace na tashe ka kuma Allah ka ta’bani sai na fad’a masa
“, yana kaiwa nan ya bar d’akin ya nufi d’akin uncle , shima lokacin be farkava
ahankali little ya Karasa inda yake Daidai kunnan uncle ya furta “ meow meow “,
bashiri uncle ya ware idanuwansa , yanxu ma little dariya ya saka ganin yadda uncle
ya ware idanuwansa, girgixa kai Kawai uncle yayi “ sorry uncle lokacin sallah yayi
“, be jira cewar uncle ya yayi saurin barin d’akin dan yasan idan ya tsaya uncle
zai iya ja masa kunne.
**** suna idar da sallah kamar kullum motsa jikin da ya zamar muku ‘ka’ida sukai,
sai da Suka kammala motsa jikinsu sannan sukai breakfast tare , bobo be dad’e a
gida ba ya fita,gidan yayi saura su uku.

Karfe 3:00 na rana wasu friends din prince suka zo gidan daman basu ta’ba zuwa ba
sai yau da Suka dami prince akan suna san zuwa gidan su , yadda suka matsa masane
yasa yace musu zasu iya zuwa , koda suka zo ba a barsu sunshiga ba saida akai musu
full check up sannan d’aya daga cikin soldier ya kira cikin gidan , yadda suka ga
sojoji ta ko ina na cikin gidan sai da ya rudar Musu da ciki, shima prince da biyu
ya bari suka zo dan yasan daga yau ko mafarkin sake zuwa bazasuyi ba ,sai da prince
ya basu umarnin shigowa sannan aka barsu, still sai da suka ajje motarsu a gate din
farko d’aya daga cikin motocin sojojin ta karasar dasu, yadda suka ga sojoji duk
inda Suka waiga yasa kowa ya kara shiga taitayinsa ga uban bundugogin da yake
hannunsu, duk da suma ba talakawa bane amma yadda Suka ga gidan su prince sai da ya
sace musu gwiwa d’aya daga cikin su da basu fiya magana sosai ba aranshi tunanin
yadda zai kulla abota da prince Sosai yadda zatafi ta kowa yake , Daidai wani wajan
shakatawa sojan ya kaisu dan ko yana shan giya bazai tunkare cikin gidan dasu ba ,
suna zuwan suka tarar da little da prince a tsaye, ri’ke kugu little yayi yana
bunsu da kallo yadda yaga shigarsu ma kadai saida ta bashi haushi hatta prince sai
da ya ta’be baki musamman colour da suka feffesa a kansu ga wasu uwan sarka da zai
nuna maka lallai turawan ne na gaske , suna ganin prince cike suka nufeshi suna
kokarin rungumesa ya dakatar dasu , kan little suka nufa ya zuba musu eyes dinsa ,
take a Wajan suka shiga taitayinsu, James ne da wani soja cikin kaki suka yi
serving d’insu , shidai little yana tsaye yana binsu da kallo , tunanin yadda zaiyi
maganinsu kawai yake cikin zuciyarsa , suma abokanan prince lokaci zuwa lokaci suna
dago da kansu gudun kar wani soja ya nufosu dan lokacin dasu James suka zo wjan
saura kadan d’aya ya saki futsari, wata irin dariya little ya kwashe da ita lokaci
d’aya Sabida idea din da yazo masa , gabaki d’aya cike da tsarguwa suka kallesa ,
gira prince ya d’aga masa shi kuma little ya lumshe masa ido yana barin Wajan ,
kara bin babban wajan shakatawar sukai da kallo da sai faman tashin kamshi yake ,
da flower da suke kada iska me dadi, d’aya daga cikin friends din prince mesuna
john ya dago wani pizza zai saka a baki yaji kamar ‘kara , be kawo komai a ransaba
ya saka pizza dinsa a baki , wani karan ya kumaji hakan yasashi ya d’an waiga be
san lokacin da ya kifa kan center din da akai serving d’insu ba ,fitsarin da sukaga
ya sakine yasa suka tsaya kallansa ga wani farfadiya da suka ga yana kokarin yi ,
suma juyawar da zasuyi suka hango simba bakinsa abude sai faman jijjiga jikinsa
yake , gabaki d’aya rud’ewa suma sukai jikinsu ya soma rawa, Aushe lokacin da
little ya bar Wajan , simba yaje ya dakko musu, yadda suka ga simba na tunkarosune
ya kara hautsina musu ciki gabaki d’aya sun rude, a fakaice little da ya la’be ya
sakar masa fito, wani irin zabura da simba yayi ya nufesu a guje suma haka suka
saka gudu suna ihun neman a gaji, john dake karshe simba ya tarfa, fashewa da kuka
john yayi yana ihu, cikin zabura simba ya janyo wandansa ya kifar dashi take a
Wajan john ya suma lokacin da simba ya dora masa kafarsa d’aya a ciki. Thomas da
mark da suka arta kuwa basu tsaya a ko ina ba sai wajan da su bruno suke zama , sai
faman sauke ajiyar zuciyar ta shin hankali suke , bombom dinsa mark ya taba kafun
ya kai hanci da Sauri ya cire sabida warin kashin da ya fara, Thomas na mi’kewa
tsaye yaga su bruno tsats tsaye Suna kallansu, shima Thomas kashi yaji yana zubo
masa daman tun haduwarsa da simba ya saki nashi futsarin tashin hankali , suma
bruno gadan gadan suka nufosu take a Wajan suka soma haushi da karfi, duk wnda ya
kallesu sai ya zabura musamman ydda suka samu horo gasu manya , suma ja da baya
suka somayi hankali a tashe bakin marks sai motsi yake ko magana ya kasa , Thomas
kuwa karamar bishiyar dake wajan yake kokarin d’anewa , ai kafin kace me su Bruno
sun biyo su abaya , abun mamaki ko ta ‘basu basuyi ba sai gudu da Suke ta sasu
cikin gidan ,iya jigata kam sun jigata basu san ya akai ba sai ganinsu sukai kusa
da john simba na zaune a wajan, ga su bruno da suka zagaye su ba shiru suma
kowannansu ya sume , wata iriyar shegiyar dariya little da bobo Suka saki har da
tafawa , sun tabbata ko amafarki bazasu kara gigin tunanin zuwa koda hanyar nan
bace , Dan ruwa little ya fesa musu take suka farka , ko kallan inda prince yake
basuyiba Suka nufi babban gate din gidan a guje duk da Nisan wajan kosu basusan
inda suke takawaba, prince sai faman kwalla muku kira yake akan su dawo amma ko wai
waye babu Wanda yayi , little da prince tsabar mugunta har da zama” yan iskan karya
“ cewar little , hatta sojojin da suke wajan duk abunda yake faruwa sun gani amma
tsabar mugunta babu Wanda ya temakawa su john. Sai da Suka tsagaita kafun little ya
mayar da simba, saida suka tabbatar sun saita nutsuwarsu sannan suka shiga cikin
gida sabida fadan uncle da zasu sha idan ya samu labarin abunda sukai.

IBTISSAM YA DAWO 300 yanxu , pay your money into 2681892316 Aisha umar , zenith
bank sai a turo shedar biya ta wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 instead of 500 , me bu’katar ya karanta littafin har
‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha
umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book
ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar
sa, to a rashi sani ne .

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___


BOOK 1

Season__12
Karfe 9:30 gabaki d’aya suna zaune , sai alokacin suka had’u da bobo , yadda suka
ga yana binsu da kallo ne yasa suka sha Jinin jikinsu “ me kuka aikata ?”, girgiza
kai little ya soma , shima prince kallansa yayi yana sosa ‘ke ya “ yaya bobo babu
fa abunda mukayi “, fear god prince “,kun tabbata? “ bobo ya ‘kara tanbayarsu,
kallan juna sukai sabida sunsan bazasu iya yimasa karya ba, and suna gudun fad’a
masa gaskiya karya hukunta su , shurun da sukaine ya ‘kara tabbatar masa da
gaskiyar abunda sukai, kallansu d’aya bayan d’aya uncle yayi” daga kallan fuskar ku
nasan yarana sunyi lefi, oya lefin me kukai ban sani ba “, d’an shagwa’be masa
fuska little yayi zaiyi magana uncle ya d’auke kansa , “ ni zaka yaudara ka wani
karya mun wuya ? Toh bari na barku tare dashi”, da sauri little ya mike cikin
dariya kirjinsa har sama yake ya furta “ Haba uncle d’ina kayi hakuri….”, bai
‘Karasa maganar da zaiyi ba ya fad’i ‘kasa sumammme, gabaki d’ayanxu nufar inda
yake sukai cikin tsananin tashin hankali, cikin wani irin zafin nama bobo ya
d’aukesa kamar ya d’auki ‘karamin yaro ya nufi sama dashi , suma hankali a tashe
suke binsa a baya gabaki d’aya shi prince ya rud’e jikinsa sai faman rawa yake sai
da uncle ya ri’keshi, cikin wani babban waje da aka rubuta Lab a jiki suka shiga ,
komai cikin zafin nawa bobo yake yinsa , yadda lab din ya tsaru mutum sai ya d’auka
wani shahararran d’akin asibitine ga wasu irin na’u rori aiki da suke ciki, wani
gado me d’auke da na’urori bobo ya shin fid’a little , hannu biyu ya saka ya ‘barka
rigar little take wajan farar singlet d’insa ta bayyana , itama hannu biyu bobo ya
saka ya ‘barkata, da Sauri ya cire jigar jikinsa ya bar guntuwar ciki, hannunsa
duka biyu ya had’a ya soma danna kirjin little da baya motsi kamar matacce, “ get
the x-ray “ cewar bobo da karfi, da Sauri , yadda yake dannan kirjin little sai ka
d’auka zai balla masa jiki Dan da iya karfinsa yake danna kirjin little amma ko
motsi little beyi ba , cikin karaji bobo ya furta “ uncle Defibrillator “, cikin
Sauri uncle ya matso dashi kusa da bobo, da Sauri bobo ya karbi defibrillator
paddles din da uncle ya mi’ko masa , a chest din little ya saka guda d’aya daga
‘bangaran dama , daga ‘bangaran hagu kuma ya saka masa a ‘kasan nipples Ninsa ba
hagu,” charge 200”, shine abunda bobo ya furta , da Sauri bobo ya d’auki
defibrillator uncle ya dannan charge 200 bobo ya dora masa defibrillator din
hannunsa , wani irin d’agowa jikin little yayi ya koma ,” one more time “ cewar
bobo, ta jikin abunda uncle ya janyo ya kara danna charge 200 din , yana dannawa ya
ajje ya dora hanka a Daidai saitin zuciyar little sai da yaji bugun zuciyarsa ya
daidaita kafun ya sauke a jiyar zuciya , gabaki d’aya kana kallansu zaka ga damuwa
tattare da su, intubation d’in da bobo ya saka masa na nunfashi ya gyara masa , a
gefen gadon bobo ya zauna tare da rike hannun little sosai yana runtse idanuwansa ,
yadda prince yake ganin little na shiga irin wannan yanayin sosai yake bashi tsoro,
duk da girman shekarun sa hakan ba ya hana duk lokacin da yaga little d’insu a
cikin irin wannan condition din yayi kuka , yanxu ma uncle ya rungume yana fashewa
da kuka , shi kansa uncle daurewa kawai yake , muryar bobo har ta d’an canza ya
furta “ karku fad’a masa komai , I will take care of him for now “, no ya kamata ya
sani , dole a fad’a masa halin da little yake ciki karka manta , sabida rashin
lapiyar little ya karanci ‘bangaran zuciya ,” hannun little bobo ya damke cikin
tashin hankali, dan ya sani dole ya fad’a wa big boss tunda shine likitansa , da
ace yana kasar ne ma da da sauki amma yadda baya ‘kasar yaji halin da little yake
ciki kome zai iya faruwa “, yadda kukan prince yacika masa kunne yasa ya kallesa “
it’s okay , zuwa da safe zai tashi ? Okay ?”, amma yaya bobo me yasa yake suma haka
? Inajin tsoro sosai “, nuni bobo yayi masa da ya matso, yana matsowa yayi hugging
d’insa, ganin yadda prince da uncle suka tayar da hankalinsu yasa yake ‘ko’karin
danne nasa tashin hankalin Sabida ya kwantar musu da hankali “ karka damu zuwa
safiya little dinka zai tashi kaji? Yanxu dare yayi ya kamata kuje ku kwanta , ni
zan zauna dashi, da Sauri prince ya girgiza masa kai hawaye na sakko masa a fuska “
No yaya bobo bazan iya tafiya ni kadai ba, zan zauna anan tare da ku”. No prince “
shima da sauri prince ya furta Dan Allah yaya bobo” , jin jina masa kai bobo yayi
yana kallan uncle “ kadena kallona Nima anan zan kwana, ka zauna zanje na kula da
komai kamar yadda kasava “, kansa kawai bobo ya d’aga masa dan ya kasa bud’e
bakinsa sai kallan little da yake kawai “ I will never forgive you ! Sabida ku
little dinmu yake cikin wannan condition din, I so much hate you with passion “,
cewar bobo yana lumshe idanuwansa, wani red button ya danna a jikin gadan little
yake jikin bangon dake facing d’insu ya rabe gida biyu wata ‘kofa ta bayyana , da
ido ya nuna prince alamar ya tafi , zaiyi magana bobo ya furta “ No complain “ jiki
a sanye ya furta “ good night yaya bobo “, murmushi bobo ya sakar masa yana jinjina
masa kansa , har uncle ya dawo yana zaune kusa little , wayarsa uncle ya mi’ka masa
, “ he called you ! Nasan tunda be sameka ba yasa ayi masa binciken abunda yake
faruwa , try to explain everything to him “, okay uncle cewar bobo, uncle yana
nufar d’akin da prince ya shiga ya d’ago wayar hannunsa “ Big Boss “ shine abunda
ya Fito ‘baro ‘baro a jikin wayar “ besan ta yadda zai fara masa bayani ba ,
shiyasa ya kashe wayan gabaki d’aya . Yanda gashinn little ya rufe masa fuska ya
gara masa take kyakkyawar fuskarsa ta bayyana kamar me bacci duk yadda ya motsa
dimple dinsa sai ya motsa .

Har wajan karfe 3:30 idan bobo biyu bai runtsaba , sai a lokacin yayi tunanin kunna
wayarsa , har yanxu sunan big boss ne rad’o rad’o a jiki, shiga wajan calls yayi
daniyar kiransa amma ya dakata, sau biyu yana kokarin kiran sa amma yana dakatawa
sai ana ukun ya danna sunansa amma ko ringing batayi ba ta katse , sau biyu yana
kara kwada kira Amma still yadda yayi a farko hakan ne ya ‘kara faruwa . Wani irin
lallausan murmushi yasaki da ya ‘kara masa kyau, kallan fuskar little da yake bacci
hankali kwance yayi, ganin dare na ‘karayi yasa shi kwanta wa akan sofa din da yake
zaune, be jimaba bacci ya d’aukesa.

5:30 yaji ana ta’basa, kyawawan idanuwansa bobo ya bude ya saukesu akan little, “
yaya bobo”, uhm d’an langwabe masa kai little yayi “nifa banasan wannan abun da ake
Samun hanani bacci yake ba “, hararar sa bobo yayi kafun ya ciccire masa
defibrillators d’in, “ yaya bobo “little “ cewar bobo” lokacin sallah yayi bari
naje na taso su yaya prince kaji”, kanshi bobo ya jinjina masa yana nuna masa dakin
da suke da d’an yatsa , har ya nufi kofar sai kuma ya dawo inda bobo yake yayi
hugging d’insa “ am sorry yaya bobo, idan aka idar da sallah sai muyi bacci
ko?”murmushi bobo ya sakar masa , “ sure in aka idar da sallah yau ba training
bacci zamuyi “, da murya little ya nufi d’akin , sosai d’akin ya’ke da girma komai
na anfani akwia shi a ciki , da gudun sa ya d’ane gadon ya shiga tsakiyarsu, cikin
bacci prince ya furta “ little “ daman da shi ya kwana aransa , Daidai kunnansa
little ya furta “ na’am yaya prince “, da Sauri prince ya ware idanuwansa yana
mikewa zaune , beyi wata wata ba yayi hugging d’in little , cike da mugunta little
ya muntsinesa, zaburar da yayi ne ya farkar da uncle , “ Wallhi little baka da
mutum ci , me nayi maka yanxu?” Gwalo little yayi masa yana kallan uncle da shima
shi yake kallo “ uncle ka dena kallona Haka , lapiya ta ‘kalau fa “, ka tabbata ?
yess uncle nifa lapiya ta kalau , lokacin sallah yayi fa , karmu makara” uncle be
ce masa komai ba shima yayi hugging d’insa .
Atare suka nufa masallaci , yadda little ya rike hannun bobo da prince sai abun ya
baka dariya , adawowa ma haka ya rike musu hannu suka koma gida , hannun prince
kawai ya saki ya rike na bobo “ uncle ni yau yaya bobo yace bazanyi training ba ,
bacci zamuyi ko ?” Kansa ya Jinjina masa “ Nima bacci zanyi “, kallan da bobo ya
bishi da shine ysa ya hadiye maganarsa , dariya little ya saki , ya rike hannun
bobo suka soma tafiya sai da sukazo hawa lifter little ya d’aga muryarsa da d’an
karfi yadda prince zaiji” yaya prince kai ma kaje kayi bacci “, talle masa ‘ke ya
bobo yayi , da Sauri ya turo bakinsa se kace wani ‘karamun yaro , suna shiga part
d’in bobo har da wani tsalle little ya saka ya d’ane bed din bobo , girgiza kai
Kawai bobo yayi ya kwanta ,yana kashe musu light, nan danan bacci ya d’aukesu. Bobo
ne ya fara farkawa duk da baccin da yayi befi na 1 hour ba , fuskar little ya kalla
da yake bacci hankali kwance , kafun ya mayar da idanuwansa kan agogon side bed
d’insa. 8:01am , “ shitt “ ya fad’a da d’an karfi yana nausar iska , shaf shaf ya
shiga wanka , be wani jima ba sosai , gabaki d’aya 30 minutes yayi , kamshin
turaran Roja ya cika d’akin, yadda yayi shigarsa ba ‘karamin kyau yayi ba ,
‘kananan kaya ne a jikinsa black colour , tundaga wandon jikinsa har zuwa rigar
jikinsa me dogon hannu ‘kirar kanfanin versace, ba karamin kyau yayi acikin kayan
ba , sai kalar fatarsa ta ‘kara haska ba’kin kayan jikinsa, yau hatta gyaran
gashin kansa na asalin sojoji ne yayi,bakin agogon hannunsa kirar kanfanin Rolex ya
kalla yaga har yanxu 9 batayi ba , gyarawa little kwanciya kawai yayi ya bar
d’akin. Yana sakkowa yaga uncle da prince ko wannansu ya shirya suna shirin yin
breakfast, suna ganinsa gabaki d’aya suka mike tare da nufar dinning, kamar kullum
James ne da wasu sojoji guda uku, suna zama james ya fara serving din ko wannansu
abunda zai ci , zai juya bobo ya dakatar dashi ,!da Sauri su james suka tsaya cike
da girmamawa, a gogon hannunsa bobo ya ‘kara kalla , kafun ya soma magana “ make
Avocado toast, hash browns,Belgian waffles “, gabaki d’aya kallansa sukai “ na
little ne uncle wannan kallanfa “, hatta prince sai da ya saki ajiyar zuciya ya
d’auka yaya big boss ne zai dawo”. 9 Daidai bobo yabar gidan a Daidai lokacin da
little yatashi, breakfast din da bobo Yasa ayi masa akai serving din sa, yau hatta
abincin abaki prince ya bashi Sabida gata.

✨✨✨✨✨✨

KANO
NASARAWA G.R.A

Eshaal ba ‘karamin aikatuwa tayi ba a kitchen , ita kadai sai faman aikin girkin
baby take , sallah ne kawai ki dakatar da ita , lokacin da ta kammala girki a
gajiye ta fito falon, yanxu babu momcy a falon sai baby ita kadai da take kallo,
tayi crossing legs dinta ga wani d’an iskan cingum da take ci sai faman bada sautin
kas kas kas , tana ganin shigowar Eshaal ta ja dogon tsaki, “Abincin suna dinning
“, abunda Eshaal tace mata kenan tana kokarin juyawa , “ ke “ cewar baby, d’an
juyowa tayi tana kallan baby, “ haka aka koya miki? Ko uwarki da take kabari haka
ta koya miki idan aka saki abu”. Rai a’bace Eshaal ta kalleta , amma bata ce mata
komai ba sai danne abun da tayi a zuciyar ta , sau dayawa tana jin zafin maganganun
Baby amma tana rabuwa da ita ne sabida a zauna lapiya tasan yanxu tace zata biye
mata itace a ruwa , ita zata wahala , a gadarance baby ta furta “ biyoni” tana
nufar dinning din da Eshaal ta cika ga kamshi sai faman Tashi yake , amma baby na
zuwa sai ta fara toshe hanci wai bata san warin aroma din be mata va ,kallanta
kawai Eshaal tayi har ta Bud’e pepper chicken din da yasha kayan had’i sai faman
tashin ‘kamshi yake , duk Wanda yaga kazar nan sai ransa ya biya sabida yadda ta
had’u, ta’be baki baby tayi kafun ta bud’e next warmer din da kamshin fried rice ke
tashi ga veggies din da ya kara ‘kawata shi, gefe d’aya ga coslow da lemukan da
Eshaal ta had’a, a yangance baby ta furta “ serve Allah yasa na iyacin ‘kazantar
nan “, anan ma Eshaal ta so ya ‘ba mata magana amma ta rabu da ita tasan tana
tankamata baby ba akanta zata huce ba akan Amma zata huce shiyasa take shanye duk
abunda baby take mata sabida Amma, ba musu Eshaal tayi serving din baby in a unique
way duk da ashekaru Eshaal zata iya girman baby da watannin da bazasu Gaza uku ba .
Spoon d’in farko baby ta kai bakinta duk da abincin yayi mata dadi sai tayi saurin
furzarwa tana wurgar da plate din ‘kasa gabaki d’aya abincin sai yazu , “wannan
Wana irin dabbancine zaki yi mun wannan abinci sai kace wata dabba irin ki? Haka
uwarki ta koya miki?” Tass Eshaal ta d’auke fuskar baby da mari, itama bata sauke
hannuntaba taji saukar mari dama da hagu, a gigice Eshaal ta dafe kumatunta, tana
d’ago da kyakkyawar face d’inta da Tasha mari , Dadynsu ne ya mareta , yadda taga
ya had’e rai ne yasa tasha Jinin jikinta , ko kallo be isheta ba sai ma baby da ya
kalla, itama tana ganin abunda yayi wa Eshaal ta shagwa’be fuska har da fashewa da
kukan ‘karya , lokaci d’aya dadyn su ya rud’e ganin baby na kuka , ashagwa’be ta
turo masa d’an karamin bakinta ,” Dady daman sai da na fad’a maka Eshaal ba
‘kaunata take ba ka kalli yadda ta mareni dan kawai nace bazan iyacin abincin da ta
dafa ba , gaskiya dady shiyasa nace bazan koma u.s tare da ita ba Sabida zata
zubarmun da class, in karatun kake so tayi kasamo mata ko makarantar kwana ce ta
gwamnati dan dashi ta fi dacewa “, amaimakon yayi mata fad’a sai ma murmushi da ya
sakar mata “ don’t worry my dear, ko me kikeso shi za’ayi miki ai , ina momcy dinki
take ban ganta ba “ ta’be masa baki Baby tayi tare da ware masa hannu alamar ita ma
bata sani ba “ tace na fad’a maka ta fita ,so ni kuma na gaji bazan iya zuwa part
d’inka ba shiyasa ban fad’a maka ba “, cewar baby sai faman ya tsine take , yanxu
ma wani murmushin ya saki “ Toh ba komai ai bansan ma tafita ba , amma ai duk yadda
tayi shine Daidai , yanxu kishirya ni sai na kaishi shopping da kaina “, duk abunda
suke Eshaal na tsaye dafe da kuncinta tana binsu da kallo , babu abunda ya fi tsaya
mata arai kamar yadda Dadynsu ya nuna rashin wanzuwarta a wajan , gabaki d’aya
hankalinsa kaco kam yana kan baby” Dady give me some minutes bari na shirya sai mu
tafi”, okay my dear cewar kyakkyawan Bafullatanin da akallan farko zakaga tsantsan
kamanninsa da Eshaal, Baby na barin wajan shima dady ya juya zai bar wajan, murya a
sha’ke Eshaal ta furta “ Dady “, wani irin kallan tsana dady ya bita dashi tare da
jan wani dogon tsaki yana barin wajan, yadda yayi mata beyi mata dadi ba dukda ta
saba da irin wad’annan abubuwan ko ma fiye da haka amma yanda yake nuna mata
tsantsan tsana kamar bashi ya haifeta ba , wani lokaci har tanbayar kanta take Anya
shine mahaifinta na gaskiya ko kuma wanine mari’kinta , tana tsaye a wajan baby ta
fito cikin shigar ‘kananan yana da suka matse ta Amma ko a jikinta , d’an ‘karamin
mayafin da ta d’akko a hannu ta ri’kesa , sai kantamemiyar wayar ta d’aya rike a
hannu cike da yanga, tana fito wa dadynta ya fara tafa mata , fuskar sa d’auke da
murmushi “ my daughter kinyi kyau “,Thanks kawai tace masa , suna had’a ido da
Eshaal ta kashe mata ido d’aya tare da kama hannun dads dinta , sunzo zasu fita
baby ta juyo tana kallan Eshaal da tun d’azu bata motsa daga inda take ba “kishiga
ki gyaramun d’akina kafun mu dawo, sannan kada ki kuskura wata ‘kazama tashigar mun
d’akin har ta cika mun d’aki da warin jikinta , and lastly Kema ba yadda nayi dake
ba sabida duk lokacin da na saki aiki sai na nemi abu na rasa , so be careful “, ta
karasa tana jan hannun mahaifinta da sai murmushi yake sakar mata . Tana ganin
fitarsu ta juya a guje ta nufi d’akinta, dakin da ko kwatan na Baby be kai ba ,
bayan set din gado babu wani abu na ado a cikin d’akin akwai da haduwa kwata kwata
bazaka had’a shi da na Baby ba dan d’akin baby dakin yan gata ne da kome take so
ake zuba mata sabo.
Kan gadanta ta fad’a tana fashewa da kuka me ta’ba zuciya , sallamar da akai ne
yasa tayi saurin goge face d’inta tana share hawayen da suke ‘ko’karin zubo mata ,
yar aikin da tashi ga d’akin baby ce , da Sauri Eshaal ta saka murmushi akan face
d’inta “ Amma sannu da zuwa , aikine yayi mun yawa shiyasa kika ga d’azu banzo
kinyi mun kitsan ba “, murmushi Amma ta sakar mata , cikin sanyayyiyar murya ta
furta “ kiyi hakuri, komai me wucewa ne “ sai alokacin wasu hawaye Suka sake zubo
mata “ Amma nagaji da gidan nan, nagaji da abubuwan da suke , mahaifiyata ta rasu,
mahaifina da nake tunanin xai Sharan hawayena ko rabarsa bayaso nayi, wacce zan
kalla kamar uwata ta tsaneni, bayan ke babu me sona Amma , Wana irin lefi nayi musu
haka da na cancanci irin wannan hukunci?” , kowa da irin tasa jarabawar Eshaal ,
Allah yana jarabtar bayinsa ta ko wace hanya bawai dan baya san suba , ah ah Sabida
ya kwada imaninsu ne , ki dena saka komai a ranki duk lokacin da kikaji ranki ya
‘baci ki kunna karatun alkurani zai debe miki kewa “, kanta Eshaal ta jinjina “
nagode sosai AMMA , nagode Amma dan Allah Amma ki dunga hakuri da abubuwan da baby
take miki acikin gidan nan “, karki damu babu komai wallahi, “ yanxu ma naga sun
fita ne bansan me za’a dafa mata na dare bane shiyasa nace bari nazo na tanbayeki
“, hawayenta Eshaal ta goge “ Karki damu Amma yau baza muyi girkin dare ba , na
Riga na dafa yana dinning , nasan yanxu kingaji ya kamata Kema ki dunga hutawa
kinji Amma “, Allah yayi miki albarka “ cewar Amma , itama cike da farincikin
adduar Amma ta furta Ameen, Amma na barin d’akin ita kuma tashiga wanka , shaf shaf
ta Fito kaya kawai ta saka sai turare kad’an , batasan lokacin da su baby zata dawo
ba tasan kuwa intace bazata gyarawa baby d’akin ba wani karin drama ne zai faru da
zata kwana tana kukan bakin ciki. Shiyasa bata zauna a d’akinta ba ta nufi na Baby
dan ta gyara mata tunkafun momcy ta dawo itama .

🍃🍃🍃🍃
GERMANY
FRANKFURT

“Sauban meyasa kake sawa ranka abunda ya faru tsawan shekaru?shekara 22 ba wasa
bane , tsawan lokaci kasawa ranka abunda yake neman illataka , Na ro’keka ka cire
wannan damuwar dake ranka karka sawa kanka wata cutar”, cikin yaran German wata
kyakkyawar mata da ashekaru bazata wuce 50 ba , jikinta sanye da irin kayan Germany
masu shegen kyau, d’ago da idanuwansa guy d’in yayi, kyakkyawane shi na ajikin
‘karshe da za’a iya kira d kyakkyawa amma ba fari bane chocolate colour ne shi amma
kalar fatansa me kyau ce sosai kanshi cike yake da suma amma ba’a kwance take ba
irin gashinn Americans haka gashinsa yake sai faman ‘kyalli da take d’auka
ba’ka’kirin da ita “ kiyi hakuri Mameey! But I can’t , bazan iya manta suba , gani
nake duk lefina ne , if not my best friend nasan da yana tare dani, mamey lefina ne
da natafi na barsu”, kusa dashi ta samu ta zauna tare da fuskantarsa , cike da
tausayi ta kallesa “ Sauban ba lefin ka bane , it have been years now , ya kamata
ka cire wannan abun aranka , karka manta munbincika amma har yanxu babu labarinsu ,
for how long zaka sawa kanka damuwa haka ? Kanasan sawa kanka ciwan zuciya ? Ka
tashi hankalin ka sannan ka tashi hankalin mu, bana tunanin ma suna raye yanxu…”,
No please mamy, ki bari banajin dad’i duk lokacin da kike maganar basa raye , we
lost dad and now kina fad’amun suna sun mutu?please , Insha Allah sunanan da ransu
and zan bin ciko duk Inda suke , ina so naji ya yafemun, inaso mu dawo yanda muke
Ada “, kallansa kawai mamey tayi ta rasa Wana irin soyayya yake wa best friend
dinnan nasa , bata sake ce masa komai ba ta mike ta nufi hanyar fita “ kiyi hakuri
mamy “, shine kadai abunda sauban yace mata harta fita , wani diamond bracelet
d’insa ya kalla shi kad’ai yana tuna memories din abun hannun da baze taba gushe
masa a rai ba .
Babban Frame d’in sa dake cikin ‘kayataccen d’akin ya kalla, kai tsaye wajan frame
din ya kalla, bakomai bane a ciki sai wani drawing da ya d’an fara tsufa cikin sa
zanen bracelet din hannunsa ne a ciki kamar Wanda ya d’auko ya manna Sabida yadda
zanan ya fiko kamar a zahiri.

“Assalamu Alaikum,”wata daddad’ar murya siririya tayi sallama, amsa mata yayi yana
juyo wa shima , wata fine girl ce kyakkyawar gaske , skin d’inta sak irin na Sauban
ne , ga baiwar kyau da Allah ya bata, sosai kamanninta ya fito irin na sa ,
banbancin su kawai ita macece amma kyakkyawar budurwace da a shekaru bazata wuce
17-18 ba, jikin ta sanye cikin wata farar shirt d’in Riga irin me design, sai
ba’kin falazo da ta saka ba’ki , kansa kuma wani d’an madaidaicin mayafine shima
black colour data nad’e uban tulun gashin kanta , Cikin daddad’ar murya tace “ can
I ?” Kansa ya gyad‘a mata yana sakar mata murmushi , itama martanin murmushi ta
sakar masa lokacin da take shigowa d’akin , “ Yaya BiiBii ga abincinka nan mameey
tace na kawo maka “, kan wasu kujeru biyu masu had’e da center Sauban ya nuna mata
“ Thank you SISI FANAN”, murmushi ta sakar masa “ you’re always welcome Yaya Bibi
sauban , kaci abinci please amma idan ka gama zan dawo hira nasan nan da 2 days
zaka tafi , lokacin da zaka dawo may be ankoma school ina U.S sea dea ka kawo mun
ziyara “ , toh mamey “ cewar Sauban yana hararan ta , itama fanan dariya tayi tare
da nufar kofar fita ,tunda taji yace mata mamey bazai zo mata ziyaraba kenan daman
bazuwa yake ba. Harta fita ta kuma dawowa “ and last yaya biibii plx ka rage
damuwar wannan besty din naka da har yau bantaba ganin saba sai a labari”, pillow
dinsa ya jefo mata da Sauri ta fice tana dariya .

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂

ABUJA
ABLA

yau gabaki d’aya tun da ta tashi take jinta wani iri alamar kwana kin period d’inta
na daf da zuwa , dama hakance ke faruwa da ita a duk lokacin da period d’inta ya
kusa zuwa , gabaki d’aya yau sukuku ta tashi , Sabida tunanin zuwan period d’inta
dan ba’karamun wahala take shaba a duk lokacin da take yinsa , ga tunanin yadda
zata biya uwar karuwai kudin da tace mata zata biyata duk ya tsaya mata a zuciya ,
d’ari uku da hamsin d’in da yayi mata ragowa kawai ta kalla tun bayan Awarar hamsin
d’in da taci da safe bata kuma cin wani abuba duk da yunwar da yake ji yanxu , yau
gabaki d’aya haka kawai taji bata san futa shiyasa tayi zaman ta a d’aki tun bayan
lokacin da su Arwa Suka bar d’akin. Tun tana waje take jin hayaniya na tashi kad’an
kad’an har hayaniyar ta so tayi yawa shiyasa ta tashi ta rufe ‘kofa.
A falo kuwa sai faman gyare gyare ake yi tun safe , ga wasu set din
kujerun roba da ake faman jerawa kamar masu shirin yin wata liyafar, ga sabbun
beers(giya) da shisha da ake shigo dasu , kowana table ansaka amsa giya da shisha,
ga kayan lemo da ake jejjerawa , gabaki d’aya tsarin wajan kasan na tantiran ‘yan
duniya ne da baki bazai musalta ba. Duk wannan abunda suke Abla tana d’aki bata san
wainar da suke toyawaba sabida ydda cikinta ya fara yimata ciwo ciwo alamar ako
wana lokaci period d’inta zai iya zuwa , gashi in tana period batasan kowa kusa da
ita musamman yadda take fita hayyacinta, tun tana sa abun a rai har bacci ya
d’auketa.

6:30 pm wani irin kid’a aka saka daya firgitar da Abla daga baccin daya d’ebata,
kid’a ne kawai yake tashi ga ‘kara da shewa da take jiyowa , Sabida yadda kid’an ke
tashi ko kiran sallah bata jiyowa, gashi bata san fita balantana su ganta ko wani
ya dakatar da ita har lokacin salla ya wuce ta , ba yadda ta iya haka ta hakura
tayi sallarta ga uban kid’a da yake tashi sai kace gidan arna duk lokacin sallar
magrib. Ban kad’o ‘kofar d’akin da akai ne ysa ta d’ago da lumsassun idanuwanta,
wasu kaya debeka ta jefa mata , “ kisa ka kayan nan ki fito kafun nan da mintuna
biyar idan ba haka ba mazan da kike i’kirari ba kyaso su ta’baki sune zasu d’aukoki
“, ta karasa tana sakar wa Abla harara, ko motsa Abla batayi ba balantana tayi
tunanin saka kayan dan yadda na gansu daga nesa tasan ba kayan arziki bane kwata
kwata , har tsawan minti 4 tana zaune a wajan , taso tayi taurin kai amma tasan
Itace a ruwa Sabida kamar yadda debeka ta fad’a hakan ce zata kasance dan tsaf
zasusa maza su d’akko ta . Jiki a sanyaye ta gyara hijab din jikinta, lokacin da
taji wani irin sowa ya tashi yasa tafito daga cikin d’akin, a cikin falo kuwa
dandazan maza da Mata ne yan duniya cike a falon ga kid’a da aka saka musu sai
faman rawa suke cud’e da zunansu, yadda hayakin shisha da warin giya da ya cika
falon yasa Abla tayi saurin toshe hancinta , lokaci d’aya wani kid’an ya ‘kara
tashi da ya saka Abla toshe kunnuwanta, a take a Wajan kid’a da rawar da ake ya
tsaya, daga inda take hana iya jiyo takun na kalli na shigowa ga wani irin kas kas
kas din cingum da ake taunawa , yan falon gabaki d’aya bin hajiyar matar da tashigo
suke da kallo, a kallon karfo da mutum xai mata yasan zatayi 45 to 47 years a
shekaru Amma d’in kin jikinta ya ‘kwararrun tantirai tayi musamman da tayi d’inki
zamani Kawai wata budurwa , ga breast d’inta da ake hangowa Sabida d’inkin da tayi,
ko mayafi babu a jikinta shiysa kayansuka ‘kara d’ameta, tabar dake hannunta ta
‘kara zu’ka cike da kwarewa kuma ta fesar da ita ta hanci da ta baki, cikin ya
tsina fuska ta soma bin kowa na cikin falon da kallo, yaranta na take mata baya ,
cike da ga daya ta furta “ Ni sunana BINTA SHALAGA, ni nake shagalta yara maza da
mata , zawarawa da duk Wanda yake san jin dad’i, kowa ya ji dad’insa ya huta , maza
su za’bi matan da suke so, mata ma su za’bi mazan da suke so , mata idan mace
takeso ta d’auka namiji idan namiji yake so ya d’auka , kowa yasha shagalinsa ,
yadda ko lahira akaje kun d’ana “, lokaci d’aya falon ya d’auka sowa da ihun kiran
sunan BINTA SHAGALA, hannu ta d’aga musu lokaci d’aya suka shiru gabaki d’ayansu “
kafun nan ina bukatar yarinyar da zan huta ku kuma kusha sha’aninku , idan na sake
fitowa ko wacece sa’a yazo kanta tana da babbar kyauta Dan haka zan za’ba , UWAR
KARUWAI da ta saka kowa su bubbud’e sabida aminiyarta ta za’ba yarinyar da take
bu’kata , wani wawan tsaki Abla taja , wani haushin kanta ta somaji da tafito falon
har kunnuwanta suka ji mata wad’annan munanan kalaman, ta juya da niyar barin Wajan
taji saukar sha’kar’kiyar muryar BINTA SHAGALA ta furta “ gatanan “, lokaci d’aya
haske ya kai kan Abla da BINTA SHAGALA ta nuna .

MASU BU’KATAR A TALLATA MUSU HAJARSU SUYI MUN MAGANA TA NUMBER NA 07041879581.

LEESHARH DATA HUB 2


MTN
1gb-240
2gb-480
3gb-720
4gb-960
5gb-1200

AIRTEL
1gb-300
2gb-600
3gb-900
4gb-1200
5gb-1500

Validity 30 days

Account number : 2681892316 Aisha umar zenith bank .

Phone number : 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book
ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar
sa, to a rashi sani ne .

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
Season__13.
A rud’e Abla ta juyo tana bin dandazan mutanan falon da kallo kamar yadda suke
binta dashi, lokaci d’aya wani irin shewa ya karad’e ko ina , musamman wanda suke
jin haushinta da Wanda suka tsaneta, gani sukayi ko su basu same taba tunda za’a
lalata ta hakan ma ya biyasu, wani irin shewa aka ‘kara d’auka “ sai kinyi BINTA
SHALAGA” shine abunda yan iskan samari maza da mata suke cewa , uwar karuwai kuwa
bataji dadin nuna Abla da tayi ba Sabida itama tana san cin ma burinta akan Abla ,
amma babu yadda zatayi idan tace bazata bawa binta shagala abla ba zata iyayin
rashin makudan kudaden da zata kar’ba a wajanta, shi yasa ta sakar mata ya’ke “
Amma Aminiyas ki duba kiga ratsats tsun yan mata masu Jini a jiki, komai gashinan
ya fito wara wara, idan breast ne gasunan luba luba , idan bom-bom dinne ma
gashinan Washa washa , me zakiyi da Wannan kazamar kullum cikin hijabi, bakya
tunanin ko nuna kayan ta basuyi bama “, wata yar iskar dariya Binta shagala ta saki
“ kawata baki da dama , ni nafi san d’an yan kaya ai , banasan nunannu,nafisan na
nuna kayana da kaina sannan nasa suyi tsuro, ina santa, sannan ta mun yadda nake so
duk da banga jikintaba Amma zan d’an d’anata “, cike da mugunta wayanda suka fi jin
haushin Abla suka dunga ihu cikin su kuwa harda husna da ta sha wankan ‘kananan
kaya.
Da wani irin banzan kallo Abla ta bi binta shagala dashi, tsanarta na darsan mata
cikin zuciya, duk da tsoro da bugawa dake ziyartar ta ga fargaba da yasaka
zuciyarta bugawa da Sauri Sauri , ko a fuska bata nuna ba sai a cikin zuciyar ta da
take faman kai kawo, bata shiga tashin hankali ba sai da binta shagala ta saka ‘yan
iskan yaranta mata da duk cikin su babu me shigar Arziki ta nuna musu Abla akan
sukai mata ita d’akinta , sannan ta bawa kowa kyautar yasha duk abunda yakeso ,
sannan yayi duk abunda yake so zata d’au nauyi dan tace partyn till down za’ayi,
cikin ihu da sowa cike da jin dadi , dan da zan barikin suka soma had’ewa da
junansu , Abla ma tayi ‘ko’karin guduwa Amma gabaki d’aya babu hanyar da zata ku
buta, sosai Tasha Danbe da yan mata ukun da Suka ‘ko’karin kamata , ba ita da take
danban kwacan kanta dasu ba , hatta suma matan saida suka jigata sabida yadda Abla
ta jigatasu, da bala’i da masifa haka suka kinkimi Abla zuwa d’akin Binta shagala
da har ta cire kayanta sai wani d’an iskan underwear skirt data janyo saba , sha’ba
sha’ban na shanunta da suka kwanta har wajan cikin ta ana hangosu ga ta ‘baka Kirin
da ita, da Sauri Abla ta kawar da kanta tana neman tsari daga sharrinta, yadda
binta shagala take binta da kallo zaka san ba ‘karamar cikakkiyar ‘yar bariki
bace , cikin wani irin tafiya , cinyoyinta na had’ewa kamar wata saniya ta soma
tunkaro Abla , da Sauri Abla taja baya ta nufi ‘kofar fita Amma a kulle alamar ta
waje aka kallesu,wani dan iskan dariya binta shagala tasaki “ baby na da kin
kwantar da hankalinki, bazamu dade ba ,2 hours ne kawai, zamuji dad’in mu, Kema
kiji dad’inki sannan kuma ki samu babbar kyauta daga gareni “, duk da yadda Abla
take cikin tashin hankali hakan be hana ta Dallawa Binta shagala harara ba , amma
ko a jikinta sai ma ‘kara nufo Abla da tayi , itama Abla bakinta d’auke da addua ta
fara ja baya, still binta shagala na binta har tazo wajan gaban mudubi, Daidai
binta shagala ta d’aga hannunta zata ta’ba Abla , turaran da Abla ta gani tayi
saurin d’auka irin spray dinnan, batasan lokacin da ta feshe fuskar binta shagala
Dashi ba , wani irin ihun azaba ta saki da yasaka yaranta shigowa cikin d’akin
daman suna waje suna gadinta kar Abla ta fito, yadda suka ga ta rike idanuwansa
tana ihu yasa sukayi kanta , gashi an ware kid’a babu damar aji ihunta, d’aya daga
cikinsu ce ta nufi abla , itama Abla ta bata kyakkyawan marin da yasa ta kusa
faduwa cikin sauri kuma Abla ta hankad’ata ta fice a guje , idanuwan binta har jaja
yake sabida azabar zafin turaran da yashigar mata ido, matan zasu bi Abla ta
dakatar dasu “ ku rabu da ita , kar kuyi mata komai sannan ko aminiyata karku nuna
mata komai , Indai nice Binta shagala kuma naci sunana sai na d’and’anata sannan
sai ta zama baiwata a harkar duk lokacin da naga damar anfani da ita sai nayi kamar
yadda engine baya gajiya haka zan dawo da ita , sai na mayar da ita karuwar Binta
shagala “ ta karasa tana sakin wani shegen shu’umin murmushi.
Baiwar Allah , Abla kuwa a ‘boye ta fito daga d’akin binta shagala batare da ta
bari wani ya lura da ita ba , duk ta rud’e gashi bazata iya fita ba sabida tana
tsoran fita kamar lokacin data ta’ba tunanin kwana a waje wasu yan iskan mashaya
suka so keta mata haddi da ‘kyar tasha , shiyasa jikinta har rawa yake ta nufi
store din bayan gidan daya ta’ba kulleta, ga yunwa da kishirwa tana ji, haka
tashiga cikin store d’in , sau’kinta d’aya ma akwia haske , zuciyarta fal tunanin
rashin sallar isha’in da batayi ba , still da ta shiga cikin store din can cikin
kayan shirgi ta ‘buya ga tsoro fal a ranta shiyasa ta runtse idanuwanta tana faman
karanto adduar da yazo duk bakinta, ga wasu siraran hawaye da suke zubo mata a
kuncinta.

*********
*************
WASHINGTON D.C
White House

Zaune ALICE take kan wasu irin ratsats tsun kujera , tayi crossing legs d’inta , ga
wayarta da take dannawa cike da yanga , daga gefe gefenta wasu matane sanye da
ba’ka’ken kaya , wasu suna mata tausa cike da taka tsantsan , wata kuma tana
d’aukan slice d’in fruit tana saka mata a baki, jikinta sanye yake cikin bom short,
rigar jikinta ma kamar singlet haka take yar figil ko cibiyarta be rufe mata ba ,
ga gashin kanta da ya sha gyara dukda a gida take hakan be hana fuskarta daukan
makeup ba, ta d’an muskuta zamanta lokacin da d’aya daga cikin masu aikin ta kai
mata slice banana bakinta , sai ya d’an goci gefen bakinta, cikin ‘bacin rai Alice
ta mi’ke tsaye , yar aikin baturiyarda zatayi 50 years ta d’aga hannu ta wanka wa
mari , da yaransu na turanci ta soma magana “ dan ubanki haka akace miki akeyi, me
yasa ku talakawa baku da hankali ne ? You’re very stupid , kije an koreki “, hakuri
dattijuwar matar ta soma bata hakan ya ‘kara tunzura Alice ta ‘kara wanka mata
mari, gabaki d’aya ragowar yan aikin saida suka shiga taitayinsu , sunsan Alice ba
kirkine da ita ba yanxu zata sa akoreka sannan a ci maka mutunci musamman yadda her
excellency take mugun ji da ita , ita da mijinta Sabida itace kwallin kwal din
yarsu dasuke da ita. Cike da wulakanci ta bada uwarnin afitar da yar aikin , haka
suka d’auketa kuwa duk da shekarunta sukai waje da ita , zata koma kan ragowar yar
aikin wayarta tasoma ringing, murmushi ta saki da Sauri ta d’aga wayar tana furta “
ki shirya bayan mun dawo daga Club zan yi siyayya sabida my man, I need anything
unique , All my clothes basuyi mun , “ bansan me aka ce mata ba sai murmushi da
tayi kit ta kashe wayar, yan aikin da suke binta a baya ta mika wa wayar cike da
yanga kafun su bud’e mata d’akin clothes dinta da yake shake da kayan sawa , cikin
tatta’be fuska ta soma bin kayan da kallo, duk wacce ta ciro intaga batayi mata ba
sai ta yar dar a kasa yan aikin kuma suna kwashewa , haka ta dunga zazzaro kaya
tana Wulli dasu hatta pant da bra haka ta dunga zazza’kulosu tana yar darwa , shoes
da bag gabaki d’aya sai data rikito dasu , tana zuwa gaban mudubinta dake shake da
kaya haka ta dunga wurgi dasu batare da tayi anfani da abu d’aya dake cikin kayan
d’akin ba , gabaki d’aya saidata burki ta ko ina yayi kaca kaca sabida ta wahalar
dasu sannan tayi ficewarta , kuma dole su gyara mata shi tsaf kamar yadda yake idan
ba Haka ba gabaki d’aya sun gama aiki kenan.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
KANO
NASARAWA G.R.A
kid’an da yake tashi da sanyin safiyane ya farkar da Eshaal daga baccin data koma
tun bayan sallar asuba da tayi ,dogon tsaki taja sabida tasan babu d’an iskan da
zaiyi wannan abun sai baby , d’ayan pillow dinta ta d’auka ta toshe kunnuwanta ko
zata denaji kid’an amma duk a bazan , wani tsakin ta kuma saki cike da haushin baby
data hanata bacci , a hankali ta zuro da santala santalan fararan kafafuwanta da
suke sanye cikin kayan baccinta pink colour , dogon gashinta ya soma sukurkucewa
Sabida baccin da tayi, half slipper dinta ta saka ta Fito daga cikin bedroom
dinta , ita kadai sai faman sakin tsaki take, tana shiga d’akin baby taga fitilar
d’akin a kashe sea light masu kaloli data bari a kunne , ita kanta Eshaal bata san
Baby na d’akin ba taje ta Kashe kid’an . Tun shigowarta Baby ta ganta tayi mata
shiru ne Sabida tana so ta d’anyi wani mistake d’in da zata saka dad momy hukunta
ta. Plan d’inta kuwa yayi aiki sabida kashe mata kid’a da Eshaal tayi a harzu’ke
baby ta furta “ uban wa yace ki shigomun d’aki da har zaki kashe mun kid’a ko kina
ba’kincikin ke baki dashi”, kallan sama da kasa Eshaal ta bita dashi “ sai akace
miki sabida kina da wad’annan banzayan abubuwan zai dameni? Ke kika damu dasu da
har kike tunanin kunnasu, dama karatun alkuran kika sa da an fafata a ga me
ilimi.baby taji haushin kalaman Eshaal Sabida tasan magana Eshaal ta fad’a mata ,
“Mtsww bani da lokacinki, ki koma ki kunna mun kid’ana tunda ba uwarkice ta siya
mun ba” cewar baby, a tsawa ce Eshaal ta kalleta” na fad’a miki duk lokacin da kika
kwaso shararki ki dena sako mun mahaifiyata, ko me zakiyi ya tsaya a iya kaina ,
amma bakyaji ke kullum abun tashin hankali kika iya ?” A gadarance baby ta furta “
An fad’a, idan kinyi zuciya ki tattara ki barmun gida , ko kuma yan uwan matacciyar
uwarki su d’aukeki, ko da yake ina ma Suka damu dake ? Daka ke har uwar taki data
she’ka”, da karfi Eshaal ta buge mata baki, zafin da tajine yasa ta sha’ko wuyan
Eshaal, itama da maganganun Baby suka ‘bata mata rai ta sha’ko Baby take a Wajan
Suka soma danbe daman ba wani karfi ne da baby ba sai cika kurin bala’i, da iya
karfinta Eshaal ta zage ta dunga luftar Baby, ita kuwa Baby sai faman ihu take wai
Eshaal zata kashe ta , a guje momy da Amma suka shigo d’akin, cikin fusata momy ta
cafko gashin Eshaal da karfi ta bugata da bango, wata bakar waya da ta gani me kyau
ta d’auka ta soma jubgar Eshaal dashi da iya karfin, Eshaal sai ihu take tana bata
hakuri amma kamar ‘kara ingiza momy take , Amma sai faman bata hakuri take amma
itama tsawan da Momy ta daka mata ne yasa ba yadda ta iya taja bakinta tayi shiru,
momy kuwa sai da tayi wa Eshaal shegen duka , kafun ta kalli AMMA “ munafuka daman
kece kike kitsa mata duk wani abu da zatayi, shine dan muna furta zaki biyo bayanta
kiga meke faruwa , da izinin wa ma kika shigo cikin d’akin”, kiyi hakuri hajiya”
sai alokacin Baby ta kalleta tare da jan wata ashariya “ kutumar uba! Da izinin wa
kika shigo mun d’aki da wannan warin jikin naki har ki taka mun carfet? Baki da
hankaline ? Ko cuta kikeso kisakamun?”, da Sauri AMMA taja baya tana furta “ kiyi
hakuri” ta’be baki Baby Tayi” daman ku talakawan nan haka kuka iya , ayi hakuri a
yi hakuri, kunsamu an d’auke ku aiki ma sai kunyiwa mutum shish shigi, tukunna ma
wai kinyi wanka ? Naji d’akinta ya fara wari gaskiya “, Eshaal bataji dad’in
maganganun Baby ba akan AMMA ko ba komai a haihuwa zata haifi kamarta ko wacce ta
fita , yanxu tana bud’e bakinta kuma momy zata ‘kara dasa mata wani saban dukan ta
Lura baby da gangan take yi Sabida tayi magana yadda momy zata kara dukanta , cike
da dattako AMMA ta furta “ Eh nayi “, da Sauri baby ta dakatar da ita “ a hakan ne
kikai wanka sai faman tsami kike ? Plx maza maza ki tattara kinfitar Munda ga d’aki
dan harna fara jin amai na taso mun , ga wani bashi bashi da d’akina ya d’auka,
yanxu ma “ kiyi hakuri “ Kawai Amma tace , momy kuwa tana tsaye tana kallan yadda
Baby ke wula’kanta AMMA amma ko a jikinta sai dad’in Hakan da take ji ma , kallanta
momy tayi up to down kafun ta nuna mata Eshaal da ke nishin wahala “ ki kwashe
wannan kayan wankin ki fitar da ita daga nan d’akin ,da kalar kazamai tayi kama ,
sunnan plx ko me zaki taba kisaka leda haka sabida kamar yadda baby ta fad’a Nima
na fara jin wari warin nan gaskiya “, gabaki d’aya AMMAHta tsargu shiyasa ta saukar
da kanta ‘kasa ta kasa kallansu, “ ba magana ake miki ba , kutattara kubarmun
d’aki”, rai a ‘bace Eshaal ta mike , har kunyar kallan AMMAH take sabida wulakanci
da su momy sukai mata , bata damu da yadda Suka zuba mata idanuwa ba , ta kama
hannun AMMAH suka bar d’akin, har cikin d’akinta ta kai AMMA, abun mamaki
tsugunnawa Eshaal tayi tana bawa AMMAH hakuri Sabida irin wulakancin da Suka yi
mata bakowane xai iya jurewa ba sai me ‘kololuwar hakuri , murmushi akan fuskar
AMMAH kamar babu abunda ya faru ta dakatar da ita “ Haba mana Menene haka kike
‘ko’karinyi ni wallahi babu Wanda na rike cikin raina , karki damu kinji “, banji
dadin abunda sukayi miki bane AMMA , nasan kawai kina ‘boyewa ne amma nasan baki ji
dad’in Hakan ba “,yanxu ma wani murmushin Amma ta sakar mata tare da d’akko mata
manzafi” ki shafa wannan kada kiyi ciwan jiki, ina da ayyuka “ ,toh Kawai Eshaal
Tace mata , sai da tayi wanka da ruwan dumi sannan ta shafa man zafin, komai cikin
Sauri take yinsa sabida bata san wani wulakanci baby zatayi wa AMMAH ba musamman
taga tana had’a musu breakfast, shiyasa gabaki d’aya ta d’auki ragamar yin abincin
gidan . Tana fita kitchen ta nufa ta soma kokarin d’aura breakfast, fish pepper
soup ta had’a sai chips and plantain da ta had’a musu, ga hot tea da ya sha kayan
kamshi, batasan almabuzzuranci shiyasa komai Daidai tayi , and Tasan bata isa taci
komai data girka ba Indai ba baby ce tace ta koshi ba .

A wajan cin abinci ma babu irin tujara da Baby batayi ba , iya shegenta kawai take
yi momy na biye mata , duk abunda sukai kuma daidai ne dan awajan breakfast dinnan
sai da dad ya turawa baby 200k cikin account dinta amma ko gaisuwar Eshaal be amsa
ba sai ma hade rai da yayi, baby kuwa dagangan ta’ki Tashi daga wajan dinning sai
data tabbatar komaj yayi sanyi lokaci yaja sosai kafun ta tashi tabar Wajan, sai
alokacin su Eshaal suka karya wajan around 12. Da rana ma haka tayi musu wannan
iskancin bata bari sunci abinci ba sai wajan la’asar , already momy da dad kowa
yafita sabgarsa.

9:00pm lokacin da Eshaal take ‘ko’karin kwanciya Baby ta tsuro da zancen wainar
fulawa take sha’awa, haka eshaal ta hakura da kwanciyar da zatayi ta je kitchen ta
fara kwaba kwainar fulawa , saida ta soya su duka ga bacci da take ji, tana kawo wa
baby tace mata ta manta bata fad’a mata ba wainar ta fita ranta bata sha’awa .
Eshaal jitayi kamar ta sha’ko wuyan baby ta tsuntsun ka mata mari Amma babu yadda
ta iya musamman yadda taga momy na jifanta da kallan tsana . Gabaki d’aya wainar
masu gadi ta bawa dan alokacin tasan AMMA tayi bacci, still bataje ta kwanta ba
saida baby ta gama yin duk abunda zatayi kafin ta mike ta nufi d’akinta tana cewa
Eshaal “ ki kashe TVn”. Kashewar kuwa tayi sabida babu yadda zatayi itama gashi
baccin take ji, tana shiga d’aki Kayan bacci Kawai ta saka tayi alwala itama tabi
lapiyar gado . (Asuba ta gari).
🍃🍃🍃🍃🍃
GERMANY
FRANKFURT

1pm Fanan da mameey suna zaune a falo suna hira, rabi da kwata hankalin fanan
yana kan game d’in da take yi cikin game d’in hannunta, kamshin turaran Emperial
magesty da a wajan yayanta kawai take ji ta soma juyowa, yadda kamshin ke ‘karuwane
yasa ta mayar da hankalinta kan hanyar shigowa. Shid’inne kuwa sanye da ‘kananan
kayan kanfanin fendi red colour , sosai sukayi masa kyau musamman yadda suka haska
chocolate colour skin d’insa , dogo ne sosai Amma ba irin over dinnan ba,
kyakkyawane shi da ko wace mace idanta kansa zata ‘kyasa , duk da ba fari bane amma
Allah yayi masa baiwar kyau , yana da medium size eyes farare tas dasu , sai dogon
hancinsa da yayi wa fuskarsa kyau , siririn lips d’insa med’an duhu duhu sosai yayi
wa cute face d’inshi kyau , sumar kansa da ta sha gyara sai faman kyalli take
musamman yadda take a cike ba’ka’kirin da ita. Cike da zolaya fanan ta furta “ oh
my god , yaya BiiBii kayi kyau wallahi yanda kasan American guy d’in nan , Anya
bamu had’a Jini dasu ba kuwa ?”yana karasowa inda take ya dungure mata kai “ Allah
Dagaske yayi Bibi gabaki d’aya kamannin sune dakai musamman gashin kanka , and bama
kama da mameey gabaki d’aya ,and ni kuma ban ta’ba ganin Dad d’ina a zahiri sai a
hoto, balantana na tantance “, ta karasa maganar tata a sanyaye tana cigaba da yin
game d’inta “ hey chill up ! I’m around , bansan kalar face d’innan okay ?” Cewar
BIBI, itama nodding kanta tayi “ don’t worry yaya bibi, I have you ai , Yaushe zaka
bani labarin friends d’inka? “ Na fasa “ cewar BiiBii “ common plx yaya bibi inaso
naji kana bani labarin nan naku, and har yanxu baka fad’a mun inda suke ba , the
reason why kuka rabu dukan ku , baka fad’a mun ba “, yadda taga lokaci d’aya mood
d’in sa ya canzane yasa tayi shiru , cikin sanyin murya ta furta “ am sorry yaya
bibi , I don’t mean to hurt you “, bece mata komai ba ya mike tsaye “ mameey zanje
wani waje ba dad’ewa zanyi ba , fanan see you later “, be jira amsarsu ba ya kama
hanyar barin kallon, kunnanta mameey ta kama “ sau nawa zan fad’a miki ki dena yi
masa magana akan friends dinsa haka ? Duk yadda naso ya manta abunda ya faru na
Lura kece kike dawo da komai baya ko? Me yasa bakyaji”, kiyi hakuri Mameey , but ai
yana farinciki everytime yana bani labari akansu “, ke dai kika sani cewar mamy, ki
tashi ki barmun falo tunda baki isa a yi miki magana ba “, Haba mamey nace fa sorry
, ringing din wayar ta kiran I phone 12 ta d’auka ganin besty ‘baro ‘baro a jiki “
Mamey besty ce take kirana , na tafi d’aki”, bata jira amsar mameey ba ta rufa a
guje tana picking d’in call d’in. Girgiza kai Kawai mameey tayi , a fili ta furta “
Allah ya shiryeki fanan”.

🍂🍂🍂🍂
VENEZUELA 🇻🇪
ANGEL FALLS , VENEZUELA_!

Angel falls ,Wani babban dajine dake ‘kasar Venezuela da bakowa ne yake iya
shigarsaba musamman yadda yake da mugun tsoratarwa, da yawa wad’anda suka shiga
basa iya fito wa daga cike , sai manyar criminals da suka san hanyar su ta shiga .
Venezuela tana d’aya daga cikin manyan kasar da tafi ko wace kasa a duniya
criminals shiyasa da yawa wasu daga cikin mugaye suke zamansu a can kasar.
Angel falls babban dajine me shegen girma da mutum bazai ta’ba iya hasashen
‘karshen saba , musamman babban dutsen da ke cikin dajin me shegen girma , babu
abunda yake tashi a cikin dajin sai kukan suntsu ko na wani dabbar, yawanci mugayen
jamun daji a cikin dajin suke rayuwa , sannan duk mahalu’kin da yashigo baya fitowa
da rai saidai ane mesa a rasa , ga shegen duhu da dajin yake dashi. Daga cancikin
dajin Angel falls wani irin kunane ke tashi wajan ‘Karan dutsen da a ‘kalla
girmansa zai iya had’a manyan manyan gidan antajiran billionaires sau goba , ga
tsaho da yake dashi.
Wasu ‘katun ‘katun mutanene manya manyan gaske ga su jinga jinga, suka fara
nufo babban dutsen ko wannansu jikinsa sanye da ba’kin kaya hatta fuskokinsu ba’a
iya gani Sabida wani abun shan iska da sukasaka abakunansu, cylinder da suke zu’kar
nunfashin na bayansu , duk inda zasu wuce wajan masu tsaran wajan tasu nuna musu
wani tanbari dake hannunsu sannan su yanki hannun su Jini ya fita kafun su wuce ,
sun fi su su ashirin haka suka dunga wuce wasu zaratan mutane dukda girmansu amma
mutanan sun fisu girma , kuskure kad’an suke jira su kasheka Sabida gabaki d’ayansu
babu Imani a tattare da su, haka zaratan mazan nan suka dunga wuce abubu kala kala
har suka zo ‘kofar shiga cikin dutsen , Anan ma wani abu ne me kamar na’ura jikinsa
irin na gizo gizo , ko wannansu yazo wucewa wannan abun zai cake su a hannu, haka
suka soma wuce wa d’aya bayan d’aya kuma haryanzu akwai abun shakar nunfashin nan
akan fuskarsu, idan suka shiga wasu irin abubuwan had’a chemicals ne masu had’arin
gaske , tundaga kan Acids, Thallium da sauran chemicals masu had’arin gaske ,
mutanene burjik a Wajan kowa ka ganin fuskarsa a had’e kowa da kalar abunda yake yi
a Wajan , ga wasu poisons da suke had’a wa me bala’in had’arin gaske cikin su har
da Hydrogen sulfide Wanda duk Wanda ya sha’kesa yake fad’awa coma ko kuma ya mutu
take a Wajan. Ga ‘bangaran Arsine shima da duk Wanda ya sha’ki gas d’insa take a
Wajan yake shigewa cikin jinin mutum.babban cikinsu kuwa petroleum distillates ne
meshegen had’ari bayan coma da yake saka mutum har Lung cancer yake sawa mutum ko
mutum yayi ta suma . Gabaki d’aya wajan chemicals ne ake had’awa masu had’arin
gaske , zataran mazan nan wata kofa suka shiga , suna shiga suka ajje kayan da suka
d’auko suka koma wasu suka d’auka suka ‘kara shiga , ko wannansu idan zai wuce sai
ya nuna tanbarin spider d’insa.
Daga ciki akwai wani waje da yafi ko ina mugun tsaro ,kasan tuwar da mugun
tsafi suke anfani, mutane burjin a ciki kan wasu kujeru masu shegen tsad’a , suna
da yawan gaske amma kowannansu fuskokinsu a rufe yake , babu Wanda yasan junansu
Sabida ‘ka’idar ‘kungiyar Black magic spider babu yadda ko sanin juna , amma ko me
kakeso za’a samar maka shi, ko da kuwa manyan ‘kazaman kud’i kake ko d’aukaka zasu
baka , hatta idan mutum kace a kashe mata take a Wajan za’a kashe sa, sabida yadda
suke mugun anfani da black magic. Duk zaman ko wannansu irin d’ayane ga tanbarin
spider da zoban tsafin black spider dake hannun ko wannansu , cikin wasu manyan
center alluraine da yawa cike a wajan, cikin murya mara dad’in ji da wani yare aka
soma musu bayanin alluran, gabaki d’ayansu babu Wanda ya ta’ba ganin shugaban black
magic spider sai umarninsa kawai da suke bi Wanda yayi gangancin tanbaya take a
Wajan a ke kasheshi , shiyasa gabaki d’ayansu babu Wanda ya damu da yayi tanbayar
Sabida duk cikin su kowanne ya tara duniya Sabida wasu irin kazaman manya kud’ad’e
da suke dashi , ko wace allura akwai tanbarin spider a jiki , da wani yare mara
dad’in ji ya soma magana , cikin wani irin salo suna daga zaune batare da sun
motsaba suke anfani da tsafi suna d’aukar alluran kowa guda bibbiyu yake d’auka da
ya d’auka kuma zai ‘bace ta hanyar anfani da zoban tsafin spider .
BLACK MAGIC SPIDER wata ‘kunya ce da aka kafata tsawan shekaru, kungiyarda duk
Wanda ya shigeta ko me yakeso zasu cika masa burinsa bayan yabi dokokinta, wasu ba
zuwan kansu bane ta hanyar tsafi ake juyar musu da kai har su dawo manyan mugane.
Burin ‘kungiyar kawai ta rage yawan Al’umma sabida ta mulke duniya , shiyasa suke
anfani da manya manyan abubuwan cutarwa su saka musu ta yadda zasu mutu cikin sauki
batare da wani wahala ba . A cikin kungiyar kuwa da wuya mutum ya shigeta ya fito
da rai dan da yawa ma’ai katan wajan an juyar musu da kwakwalwa komai ba cikin
hankalinsu suke ba . Yanxu saban cutar da black magic spider ta fito washi wani
Allura ce da duk Wanda akai masa bazai wuce minti d’aya ba zai mutu, kuma duk iya
bincike da likitoci zasuyi bazasu ta’ba gano me ya kashe kaba saidai ace bugun
zuciya . Yanxu ma abunda ya faru kenan kowa ya d’auki allura biyu da zai kashe
mutum biyu dashi, kana kashewa kuma zaka ‘kara samun wasu kazamun kudin , mutane
kuma zasu ‘kara girmamaka kazama ne d’aukaka.
Duk cikin kungiyar babu Wanda ya ta’ba ganin black magic spider , hatta manyan
yaransa da yake dasu suma basu ta’ba ganinsa ba , su ma dalilin zamansu manyan na
hannun daman black spider Sabida cikin ‘kasashe goma da suke so su rage
al’ummanta , ko wata ‘kasa yana da yaransa a cikin kasar . Ciki kuwa har da Nigeria
da itama za aje a sakar musu wannan allurar.
Atarihin black magic spider duk Wanda ya ga shugabansu kisa ne kawai za’ayi
masa , mummunan kisa ma kuwa sannan su cinye namanka , yawanci kuma abunda suke ci
raunanniyar zuciya Wanda mutum yake fama da ciwan zuciya irin mutanan suke kamowa
su cinye zuciyar sa , gawar kuma a kwai wani d’akin inji da ake kaita, da yake zuba
mata wani irin ruwa har su had’a wasu chemicals din dasu. Sannan duk Wanda yke
cikin kungiyar dole ya sadaukar da wasu iyalansa, ko da ya kawosu kuma sai sunyi
shekara 30 cikin wani cages kamar karnuka kafun ayi anfani dasu.

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂

NEW YORK
5TH AVENUE

Yau tun bayan fitar bobo shima prince ya fita , daman time to time yana fita
musamman idan yana da case a kotu kasancewarsa kwararran private lawyer da mafi
akasari talakawa yake temakawa badan yasamu kudi ba. Cikin shigar lawyers black
colour suit ya bar gidan tare da combo d’insa da big boss ya ajje musu shida little
musamman Sabida futa. Gidan yayi saura daga little sai Uncle , shi kuma little zama
shirun ne bayaso shiyasa ya takurawa uncle akan su koma wajan garden su zauna ,
hakan kuwa akayi, little da uncle cikin babban Wajan shan iskarsu suka nufa , wajan
sai faman kamshin jikar kiyar kasa yake da kamshin shukoki, ga kayan ciye ciye da
aka jera musu sai Wanda suka za’ba , daga inda suke zaune suna iya hango Simba , “
uncle “, little ya marairaice masa “ uhm “ kawai ya bashi amsa “ please zani wajan
simba , I promise 30 minutes kawai zanyi kaji?”, “ okay be careful “ murmushi
little ya sakar masa har jerarrun fararan hakwaransa na fitowa tas dasu , da Sauri
ya nufi inda simba yake , uncle kuma na zaune yana kallansa , ta baya little ya
rungumo simba ko tsoro bayaji, azabure simba yasaki wani irin kukan zakuna yana
bud’e bakinsa tare da fito da faratansa waje, wani irin juyi yayi wa little yana
ware masa farcansa da har saida uncle ya mi’ke tsaye , yana ganin little ya Mayar
da farcinansa tare da turowa little kansa yana karka d’a masa gashin jikinsa.
Dariya Little ya saki “ Simba yanda ka zaro wannan farcinan naka kamar kaga abun
farauta sannan kuma zaka miko mun kanka?” Yana magana yana susa mashi kansa . Shima
simba kamar wani mutumin waje ya samu ya zauna sosai irin yadda zakuna suke zama ,
little kuma yana susa masa kansa , sun dade a haka kafun su mike tsaye , wani ball
little ya d’auka yana nunawa Simba , kallan ball din simba ya farayi da idanuwa
lokacin da little ya saka gudu shima simba binsa yayi a baya da ya zo inda yake zai
d’ago da hannayensa guda biyu ya saka a bayan little sosai suke wasa kamar wasu
kananun yara, sun d’au 30minutes suna abu d’aya ganin abun nasu bana ‘karewa bane
ysa uncle dakatar dashi Sabida yadda yaga yana sauke ajiyar zuciya .
Suna komawa ko mintuna biyar basuyi ba shima prince ya dawo cikin gidan, har
d’aki little ya kai masa abincinsa , little ne yau har da tausa “ me kake so ?”
Cewar prince yasan na zuwan Allah da annabi ne ya kawo little ba , lallausan bakin
gashin kansa ya shafa “ yaya prince yau de d’ana plx mu shiga mu gyarawa yaya big
boss apartment d’insa , kaga mun dad’e bamu gyara ba , wata irin shakuwace ta kama
prince lokaci d’aya “ kasha kwaya ne ? Kai duk neman abun bala’I shi kake nema , ta
bazani ba , idan kaga naje to bana cikin hayyaci na “ dan Allah fa nace maka “
cewar little “ nace bazaniba ko ? Ka tafi kai kad’ai mana “, okay fine “ cewar
little , har ya kai bakin ‘kofa prince ya tsayar dashi, “ Naji amma ina abun music
dinmu?” Dariya little ya saki yana nuna wajan bed d’insa inda ya ‘boye , dukansu
kayan jikinsu suka canza zuwa gajerun wanduna da t-shirt mara nauyi suka d’auki
abun music d’insu zuwa elevator , floor 4 prince ya danna ko minti d’aya cikakke
beyiba suka ‘karaso , tun daga ‘kofar zaka gane ba ‘karamun waje sukazo ba, duk
jerun ‘kofofin gidan wannan kofar tafita daban da sauran, yadda take she’ki mutum
saiya d’auka da gold akayita sabida had’uwar da tayi , finger dinsa d’aya little ya
saka a jikin ‘kofar take wani blue d’in haske ya haska musu jikinsu ko minti d’aya
batayi ba ‘kofar ta tsaye tana furta “ welcome prince and Little “, tun kafun
kashiga zakaji wani irin daddad’an kamshi na tashi me shegen dad’i ,
Sun blue black light d’in haskene kawai a Wajan, suna danna wani arrow haske ya
fara karad’e wajan,woooooow kawai bakina ya iya furtawa wajan ya had’u , had’uwa ba
kad’an ba, wani ‘kayataccen corridor ne a Wajan , colour paint d’in Wajan farine,
idan mutum ya d’aga kansa dama zai iha ganin dama ko da ruwa ake kuwa sabida yadda
saman wajan yake da glass me shegen kyau.’Kofofine guda uku a cikin wajan , d’aya a
side by side sai wanda take kallan ‘kofar shigowa ,’kofar farko suka fara shiga ta
side d’in dama , nan ma dum lights ne a wajan, prince na kunna fitilar Wajan nakasa
‘kwakkwaran motsi Sabida yadda ‘kayataccen falo ya bayyana , falone had’ad’d’e da
ya gaji da had’uwa kamar ba a duniya ba , ga wasu tsadaddun chairs da suke falon
kalan Ash colour , sosai kalar tayi wa kujerun kyau musamman yadda tsarin kujerun
Suka fita daban Sabida irin kyan da sukayi, daga side d’in hagu wani dogon glass
ne a jikin bangon, ga wasu ‘kananan fitila dake haske wajan , kasantuwar set d’in
kujerun had’e yake da center d’in wajan, had’e da wasu modern design d’in deco suma
kalar ash colour , lallausan carpet d’in wajan kuwa fari tass kamar ba’a anfani
dashi ga wasu irin laushi da yake dashi kamar mutum karya dena ta kawa , kana d’aga
kanka sama zakaga yadda Ruby three tier rounded chandelier na huta da ya ‘karawa
falourn kyau da had’uwa, sannan ga wasu ‘kofa guda biyu a wajan kafun akai unique
dinning din da akai wa set d’in dinning suma ga wani tangamemen fridge a wajan me
fad’i d fari idan mutum ya gansa bazai d’auka fridge bane, yadda sanyin ac yake
buso ko ina ne mutum zai soma tunanin ta inda Acn take dan duk dubar mutum bazai
ganta ba sai sanyinta kawai da yake hurowa. kamar akwai me rayuwa a ciki sabida
yadda wajan ke tashin ‘kamshi, sosai falourn ya had’u ta yadda baki bazai iya
fasalta kyaun falon ba , basu zauna anan ba Suka nufi d’aya daga cikin door d’in
falour , nan wani falon a wajan Wanda be kai girman nan d’azu ba Amma komai na
cikin wannan falourn white ne , gabaki d’aya sanyin Ac da ‘Kamshin turarene ya cika
d’akin.
Kai tsaye master bedroom d’insa suka shiga , babban d’akine sosai sai kace
falourn wani gidan sabida girmansa, ga wani d’an ubansun king size bed dake cikin
d’akin, hatta tsarin kayan d’akin dabanne, tundaga kan labulayen d’akin, da white
2 unique coffee chairs me had’e da medium carfet d’insa, zuwa gaban mirror d’in
dake sha’ke da turaruka,komai na cikin d’akin white , gabaki d’aya dakin sai karasa
dashi da falours din wanene ya fi haduwa, a cikin bedroom d’inma kamshine ke tashi
sabanin irin na falo wannan kamshin da ban yake musamman yadda ya hade da sanyin Ac
yana bada wani cool kamshi me tsaya wa arai. Wajan labulen little ya nufa yana jan
wata igiya gabaki d’aya labulen ya bud’e, ginin glass din dake dake facing d’in
little mutum zai ga yar kofar glass ga wajan shan iska a wajan , daga inda little
yake yana iya hango. Yanda sojoji ke faman kaiwa da komowa “kallan part d’in ya isa
haka , idan mun gama komai kai Kayi Kallan “ okay cewar little “, abun music d’insu
da suka shigo da shi suka kunna sunsan yaya bobo baya gida kuma uncle bazai ta’ba
jin suba shiyasa suka kunna kid’a , suna fito da machines din da zasuyi gyaransu
( dansu basusan wani tsintsiya da abun kwashe sharaba 😹😹) prince glass toilet d’in
big boss ya nufa , daga waje bazaka taba ganin abunda na cike yake yi ba , mutum
sai na d’auka kawai glass ne na ado amma nacikin toilet ko me kake yana ganinka
koda nayi motsi bazakaji ba Sabida sound proof ne glass din , sosai little ya soma
gyara bedroom din duk da babu abunda yayi sai kura shiyasa ya d’auke abun goge
‘kura , tasss na goge kura ya canza bedsheet zuwa fari, hatta farin carfet din
dakin sai da ya fita sabida inganshi engine , yana aikinsa yana bin wa’kar da yake
ji harya gama gyarawa cikin ‘kan’kanin lokaci , a Daidai lokacin da prince ya fito
shima suka koma falourn farko , nan ma tass suka gyarasa sunayi suna tukar rawarsu
gabaki d’aya sun manta a inda suke , har suka kammala aikin su cikin raha abunsu ,
babu wani damuwa tattare dasu , sai shaukin jin dad’in aikin . Suna fitowa corridor
d’insa suna bin junansu da kallo” little karma ka soma wani magana , nagaji kaga be
dawo ba ka bari zuwa gobe sai muci gaba gaji? Duk da mun gyara part d’aya kaji”,
shima little a gaji ya furta Tom , Amma yaya prince ka goyani nagaji”, banza prince
yayi dashi ya soma tafiya “ ka kwana anan indai sai na goyaka “, Haba please mana”,
cewar little , yanxu ma banza prince yayi masa, saida yaga Dagaske guduwa zaiyi
yabarsa yasashi saka gudu” kajirani mana”cewar little yana biyo prince , ko da zasu
fita sai da ‘kofar ta ‘kara scanning d’insu, a ynxu ma ta elevator suka sakko, suna
sakkowa sukatarar da yaya bobo a tsaye , ga wasu sojoji sama da goma da suke
falan , kowa da inda yake gyarawa , duk da yadda falan yake a tsaftace hakan be
hana su ‘ki bin umarnin bobo ba na ‘kara gyara ko ina , hatta fitilun falon kara
tsaftace su ake babu ko d’ugon datti yadda mutum ko abunci zai iya zubawa a kasa
yaci Sabida yadda tiles ke kyalli. “Daga ina kuke ?” Suka ji saukar muryar bobo ,
har yar rige rigen furta masa amsa suke “ mun d’anje mun gyara part din yaya big
boss ne “, kallan sakanni ya bisu dashi , kafun ya d’auko wani box guda biyu manya
yana mika musu ko wanne “ da kuka gyara kun canza drink?” Girgiza masa kai sukai
alamar “ ah ‘ah “, kwalayen ya nuna musu ba’ka’ke masu “a mistake , isn’t a mistake
, until you repeat that mistake, it’s called a mistake , next time kuka ‘kara yin
wannan mistake din ni dakune , kuje ku canza “, da Sauri kuwa suka amsa masa suka
koma , ko 5 minutes basu ba suka sakko da wasu drinks masu tsadan gaske , soldiers
din falon ne suka amsa da Sauri suna barin falon Sabida lokacin har sun kammala
aikin nasu “ kiyaye kiraye kiran sallah magrib ne ya hana prince tanbayar da yake
san yiwa bobo, babu Wanda ya ‘bata lokacin ya koma ya kimtsa kafun su tafi
masallaci, hatta uncle yayi mamaki ganin komai a tsare rinkin baninkin yadda yake
da , basu gama mamaki ba sai da suka fito waje , tsarin komai na Wajan sai da aka
canza , duk da kullum a tsaftace yake wajan babu datti amma yanxu kana kallan
tsakar Wajan zaka ga har wani iska iskan dadi take bayarwa , flowers gabaki d’aya
an ‘kara gyara su, motocin wajan sai faman kyalli suke d’auka , basu wani mamaki
sosai ba lokacin da suka shiga masallacin suka ga ancanza komai na ciki, sabida
wanda tsarin gidan ne time to time ana canza komai amma na yau na musamman ne ,
babu Wanda yace komai har sukai sallahrsu both magrib and isha, suna komawa gida
kuma dinner d’insu sukai kowa bakinsa fall tanbaya amma be basu damar hakan ba ya
wuce part d’insa. Suma duk basu zauna ba a falon kowa ya nufi d’akinsa daman little
me saka hiran amma yau kasa yi yayi Sabida zuciyarsa da take masa zafi Amma ya ki
fad’awa ko sannan ya hanasu fahimta sabida yadda fuskarsa take d’auke da murmushin
sa, ga tsokanan uncle da prince da yake duk dan karsu gane su tayar da hankalinsu.
Yana komawa d’aki magungunansa ya d’auka yasha, lokacin ya bar prince a
‘kasa , ko minti biyar be yi ba , bacci me nauyin gaske ya d’aukesa sabida harda
maganin bacci a cikin magungunan sabida zuciyar sa ta huta sosai, prince yana
shigowa d’akin ya tarar da little har yayi bacci batare da ya canza kayan jikinsa
ba , da kansa ya cire masa riga da wando jikinsa ya bar masa wani dogon wandansa da
zai kai rabin kwiwarsa sannan ya lullu’besa da duvet me kauri yana rage sanyin Acn
d’akin, shaf shaf yayi wanka ya saka kayan baccin sha shima Dan a gajiye yake ,
shiyasa ya ka she light d’in shima ya kwanta.
Yau gabaki d’aya tunda bobo ya nufi part d’insa bai fito ba sannan bezo ya duba
su little ba kamar yadda ya saba dubasu . 1:00am na dare lokacin da mafi aka sari
mutane ke samun daman hutawa , a Daidai lokacin bobo ya fito daga part d’insa sanye
da kakin sojoji , hular sa a gefen hannunsa na hagu, shigarsa ba kad’an ba tayi
masa kyau duk da kasancewar dare yayi, d’akin su little ya nufa , ya duba
lafiyarsu, tun kafun ya fito daga d’akin ya fara jin ‘karar helicopters na tashi,
murmushi kawai ya saki yana barin d’akin, kai tsaye fitowa yayi daga part din
gabaki d’aya , wasu irin dandazan sojojine a wajan ko wannansu cikin kakin sojoji
side by side sunja layi sosai kowa da gun d’insa a hannu, ta sama kuma helicopters
ne kusan guda biyar suke shawagi daga saman gidan . Suna ganin bobo kowannansu ya
‘kara ‘kamewa tare da yi masa salute cikin girma, babu Wanda ya amsawa sai tsayawa
da yayi a tsakiyarsu yana fuskantar hanyar da zata sada ka da main gate , kusan
mintuna 30 suna tsaye a Wajan babu Wanda yayi koda kwakkwaran motsi, lokacin da
Suka ji bud’ewar gate d’in farko gabaki d’aya suka ‘kara shiga taitayinsu, hularsa
bobo ya d’auka shima , ana bud’e gate na biyu shima ya ‘kame lokaci d’aya , gate
din main door din gidan aka bude , wasu ba’ka’ken bike ne suka fara shigowa gidan a
jere side by side guda biyar ko wannansu da shigar kakin soja tare da abubuwan
jikin bike a jikinsu, tunda bike d’innan suka tunkaro cikin gidan ko wana soldier
ya ‘kameta tare da sarawa cikin girmamawa, duk Wanda kaga fuskokinsu zakaga gabaki
d’aya kawunansu a ‘kasa yake hannunsu kuma sun d’aga alamar sarawa ,lokacin da
bike dinnan suka nufo Inda bobo yake gabaki d’ayansu da hannu d’aya suka rike bike
din d’aya kuma suka sara masa shima , bayan su wasu manyan ba’ka’ken Hyundai
palisade cars ne suka shigo ba’ka’ke kirin dasu , gabaki d’ayansu kuma tinted
glasses ne dasu, saida guda bakwai suka shigo irin ta kafun bobo cikin wani irin
salo ya matsa ya juya yadda cars din zasu shigo, bike din a jere suka tsaya lokacin
da combo cars d’in nan suka shigo, daga bayansu wata irin zafaffiyar farar
Mercedes Benz GT63s ta shigo gidan babu Wanda ya ‘kara ‘ko’karin motsi sai kara
sarawa da sukai a jere cikin layi da tsari, daga kallo d’aya zaka san motar ba
‘karamar bota bace da a’kalla kudin ta zaikai 2.7 crore, sai faman d’aukan kyalli
take babu alamar d’igon’kura a tattare da su, tana shigowa sauran motocin da Suka
shigo sukai gefe ita kuma ta shiga tsakiya , daga bayantama wasu combo Hyundai
palisade ne Suka tare mata baya . Wajan shiru ya d’auka kamar babu mutum me rai a
wajan , kowa ka kalla kuma zakaga kansa a ‘kasa Alamar girmamawa hatta bobo yau sai
da ya ‘kame irin ‘kamewar kwararran soja da yaga uban gidan sa , gabaki d’aya combo
cars d’in da suka shigo fitowa sukai cikin motocinsu, ko wannansu sanye da black
suit, da black guns a hannunsu, babu d’igon murmushi ko fara’a a tattare dasu,
hatta farar motar Wanda ya kasance driver shima ya fito daga cikin motar , fuskarsa
babu ko d’igon fara’a da walwala, babu Wanda fuskarsa take a sake , kwakkwaran
motsi kawai suke jira su harbe mutum, cikin girmamawa d’aya daga cikinsu ya bud’e
‘kofar bayan cikin Farar motar, a wannan karan har bobo sai da ya sara lokacin da
aka bud’e motar, ga wani irin kamshi me dad’i da yake fitowa daga cikin motar ,
tsawan mintuna 10 suna tsaye a haka babu Wanda ya motsa kuma daga position d’insa ,
a mintuna 15 da bud’e kofar wani kyakkyawar farin hannu ya d’an sako hannunsa fari
tas dashi me had’a da farar kumba da Suka sha gyara sosai kamar ba farce ba diamond
watched d’in hannunsa sai faman kyalkyali yake na ban Mamaki da ya ‘karawa dogon
hannusa kyau, a hankali kuma ya zuro da farar ‘kafarsa me sanye da ba’kin horsebit
loafer ( wani takalmi da za a iya kiransa da half shoe )da a kalla zai kai $890 ,
yadda takalmin yake d’aukar ido haka fatar kafarsa take d’auka ido dukda tana cikin
takalmi kuwa, dogon farin wandansa da be kai har kasa wajan takalmin saba ya fito
kirar kanfanin Armani kana kallansa zakaga alamar ba ‘karamin laushine dashi ba , a
bazata ya Fito da gabaki d’aya jikinsa da ya ‘kara saka gabaki d’aya sojojin shan
Jinin jikinsu.

MESAN YI MUN MAGANA GA NUMBER TA NAN AMMA BANDA KIRA 07041879581

LITTAFIN IBTISSAM NA KUDI NE 300 , zaku iya fara biyan kudinku ta wannan asusun
2681892315 Aisha umar , zenith bank , sai ku turo da shaidar biya ta wannan number
07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM na kud’ine akan 500 kacal , me bu’katar ya karanta littafin har
‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha
umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book
ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar
sa, to a rashi sani ne .

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

NOT EDITED

BOOK 1
Season__14
# The lion of the lions….💔
Kyakkyawane ! irin kyawun da ko kalmar kyau idan aka anbatashi dashi ya zarce
hakan, wani irin extraordinary marvelous look ne dashi na ajin karshe , farine shi
sosai me kyan gaske da mutum zaiyi tunanin ko akwai Jini a jikinsa sabida irin
yadda farin fatarsa take da kyau, dogone shi kakkarfa duk da kayan jikinsa sun boye
ainahin jikinsa amma kana kallan sa kasan ba karamun muscles ne dashi ba ,
kakkarfan gaske , jikinsa sanye yake cikin dogon black coat da ya wuce gwiwarsa
kad’an, daga cikin ta kuma wata farar white shirt ce ‘Kirar kanfanin Celine da yayi
mugun had’ewa da wandan jikinsa, sosai yake da suma akansa ba’ka’kirin yadda gashin
kansa suke a murmurd’e sai ya baka sha’awar ta’bawa sosai ba’kin gashin kansa yake
d’aukan ido sabida yadda yake faman shining sai kaceba gashiba, kansa kuma sanye
yake cikin Ascot cap itama black colour , ba’a ganin fuskarsa sai iya half face
d’insa da zai ‘kara Fito maka da zallan kyawunsa, dogon hancinsa , d’an mitsitsin
unique lips dinsa da yadda dogayan eye lashes dinsa ke motsawa, ko mutum be
kallesaba Yasan yana da cikakkiyar gashin gira. Tun da ya fito babu Wanda ya d’aga
kansa ya kallesa , shima kamar besan da wanzuwar mutane a wajan ba ya soma takunsa
a hankali irin takun ka’k’karfan soja me ji da Jini a jika, kansa a sun kuye yake
kad’an , yana soma tafiya bobo yabi bayansa, sauran black American d’in da suka
shigo suna take masa baya,’ Tun kafin ya’karaso aka wangale masa ‘kofar na’uran
falour , a hankali yake taku kamar bayasan taka ‘kasa , yadda yake tafiya cike da
izza ma abun kallo ne, har ya shiga cikin falour be d’ago kai ya kalli kowa ba , an
rage hasken falourn shiyasa hasken baya kashewa mutanan falon ido musamman da ya
zama kamar adone akayi da fitulun kan d’aya daga cikin kujerun falon ya zauna hannu
yasa tare da cire Ascot cap din kasa,har yanxu half face d’insa ake gani sabida
yadda dogon gashinsa ya kare masa fuska, hannu d’aya ya saka ya ja gashin kansa
baya , take a wajan kyakkyawar face d’insa fitowa . Kyakkyawane shi sosai na ajin
karshe, fuskarsa d’auke take da kyawawan idanuwa , farare masu d’aukar hankali,
kwayar idanuwansa light green sosai ta haska farin idanuwansa da suke kama da Wanda
yake bacci, irin idanuwan da ake kira da sexy eyes , ko kallo yayi maka sai kaji
wani abu ajikinka, idanuwan da ke ladaftar da duk Wanda yayi gigin kallansa ,
mutane har tsoran had’a ido suke dashi sabida wani irin kwajini da Allah ya basa ,
eyes dinsa yana had’e da dogayan eye lashes baki , duk yadda ya motsa idanuwansa
suma zaka ga motsinsu, yana da dogon hanci daya ‘kara ‘kawata kyawun fuskarsa had’e
da d’an mitsitsin bakinsa Red colour me turuwa, fuskarsa a had’e take sosai kamar
hadari babu alamar fara’a ko sakin fuska a tattare dashi, amaimakon kyawun fuskarsa
ta ragu sai wani sahirtaccen kyau da ta ‘kara masa , yadda ya had’e fuskarsane ya
bawa cikakkiyar gashin girarsa fitowa sosai, daga gefen hirar sa ta hagu a d’an
tsage take sai ta ‘kara fito da wani kyawun na musamman. Kyakkyawan guy ne da kowa
ce mace zata so mallakarsa , ba mata kadai ba hatta maza na mararin ganinsa Sabida
kwarjini da kyawu da Allah ya bashi ga ‘ka’k’karfan jiki na cikakken soja da yake
dashi,ba kowa bane face one of the youngest Billionaire U.G.A, Umar farooq general
of the army, Big Boss , babban jami’i da ‘kasashe sama da goma suke so ya zama
mallakinsu sabida jajircewarsa akan aikinsa , soja d’aya da yake ruguza miyagun
mutane , sojan da kasashe take alfaharin samun sa , mutumin da ko kallo d’aya yayi
maka sai hantar cikin ka ta motsa , amma duk da haka babu yan jaridan da ke da
zarran saka hotan sa a media sai dai ya d’a sunansa da ake dan akwai gidan jaridan
data ta’ba gigin saka hotansa da facemask take a Wajan aka kulle gidan jaridan
bayan shegen duka da sojoji sukaiwa mutumin da yasaka sannan sukai mashi
treatment , sannan basu ‘kara gigin saka saba sai sunan sa da akeji, mutum ne da
baya magana biyu idan ya furta kalma ta tsaya kenan sannan babu Wanda ya isa ya
canza masa ra’ayinsa, babban miskiline ga izza da yake da ita , kafun yayi magana
1 da baki yayi sau goma da ido sabida yadda magana take masa wuya ,
Mutum ne me saurin fushi da wani irin hali me wuyar fassara, arayuwarsa idan akwai
abunda ya tsana ‘karya ce bayan abubuwa biyu da ya fi tsana duk duniya da duk Wanda
yayi gigin yi masa maganar su zai ga asalin Tashin hankalin da be ta’ba tsammani va
, idan kana so kaga ‘kololuwar’bacin ransa kayi masa zancan iyayensa da ya fi kowa
tsanarsu a duniya , wannan shine babban dalilin da yasa duk lokacin da yake gari
babu Wanda yake gigin yin Hausa a cikin gidan . A cikin abunda ya tsana harda
murmushi , ko dariya mutum ya cikayi take a Wajan zaisa a hukunta ka ,sabida
kallansu yake a masu double face , mutum 4 d’ine ya aminta da murmushin su a duniya
, A duk lokacin da mutum yake san yaji muryar big boss sosai to tabbas yana cikin
family dinsa, musamman lokacin da yake tare da little , ‘kafarsa guda d’aya yayi
crossing gabaki d’aya karatan mutanan suka daidai ta tsayuwarsu , idanuwansa a
lumshe yana jingina kansa a jikin kujerar, Daga side d’in kujerar da yake bobo ya
zauna , a wannan karan da ido yayi wa d’aya daga cikin sojojin falourn umarni,
cikin ‘kan’kanin lokaci su james suka cika d’auko wani center na shan coffee , ba
‘bata lokaci suka had’a masa coffee da sai faman tiriri yake , tun kafun ya bud’e
idanuwansa rabi daga cikin sojojin suka bar falourn cikin taka tsantsan, su james
ma gefe suka koma , sabida ‘ka’idane wannan duk lokacin da yake nan baya barin
wajan sai ya tabbatar da lapiyar abinci , suma ragowar soldiers din kowa da
position d’in da ya kalla dan basu isa tunkarar kallan inda yake ba koda kuwa
idanuwansa a kulle suke , duk wannan abun su da yake faruwa su Adil basu saniba
hatta uncle sabida sound proof d’in d’akinsu da yake hana aji magana. Yafi munti
biyar idanuwansa a kulle , kafun a hankali ya bud’e su gwanin burgewa amma kwata
kwata fuskarsa babu fara’a a tattare dashi, hatta coffee d’in da aka ajje masa be
kalla ba ya ‘kara mi’kewa , sojojin sa şuna ‘ko’karin kara bunsa yadda suka ga ya
‘kara murtuke face dinsa ya hanasu hakan dan sunsa me hakan yake nufi, bobo ne ya
basu umarnin tafiya , big boss kam ko kallo basu isheshi ba , lifter kawai ya nufa
shi da bobo ,yadda be yiwa bobo magana ba haka shima bobo bai ce masa komai ba ,
dan abune mafi wahala kaji muryarsa cikin mutane sosai sai dai in yana cikin family
dinsa tsabar miskilanci irin nasa bawai magana ce be iya ba . Kai tsaye d’akin su
little suka shiga , fuskar little da yake bacci kawai ya zubawa narkakkun eyes
d’insa , a Daidai bakin gadonsa ya fito da kyawawan hannayensa yana ‘Karabün fuskar
little da kallo, kafun ya mayar da kallansa sai tun zuciyarsa , right hand d’insa
ya d’ora yana jin yadda zuciyar little take harbawa tsawan one minute kafun ya
sauke hannunsa yana gyara masa kwanciyarsa sosai , shima prince haka ya duba
lapiyar sa , tare da barin d’akin ko kallo bobo be isheshiba, sarai bobo ya gane
fushi yake dashi da bai sanar masa da rashin lapiyar little ba , and yasan Indai ba
maganar yayi masa ba big boss bazai ta’ba kulasaba shiyasa suna fito wa daga d’akin
yayi hugging d’insa “ wannan fushin fa ? Banaso na tayar maka da hankali fa shiyasa
ban fad’a maka ba ,” matsawa big boss yayi zai wuce bobo yayi saurin shan gabansa “
Haba mana , ok yaya big boss am sorry”, narkakkun eyes dinsa ya zuba masa haryanxu
face dinsa na yadda take da alama haka face d’insa take kullum , cikin wata
ratsatsttsiyar murya me shegen dadi a hankali kamar me rad’a ya furta “ Menene
matakin health d’insa “, yadda kalmomin suka fito daga bakinsa mutum sai ya d’auka
sabida daddad’ar murya da Allah ya basane yake ‘kinyin magana , kaitsaye bobo ya
bashi amsa da “ komai nasa yana lapiya, we have to add 2 weeks more muga yadda
zuciyarsa zata dunga tafiya”, lumshe wa bobo eyes dinsa yayi girarsa da take a
tsare ta d’an motsa kad’an , elevator suka hau yanxu ma , bobo har ya danna floor 4
Sabida yanaso ko coffee yaga big boss yasha , sanin halinsa da yyi , sunzo Daidai
floor 3 big boss ya danna , take ‘kofar ta bud’e da hannu d’aya ya saka ya fitar da
bobo dake masa dariya , fuska ba walwala , da daddad’an muryarsa ya furta “ I
don’t need you “, yana gama fad’ar hakan ya kulle door d’in , murmushi kawai bobo
ya saki ya nufi part d’insa , big boss yana shiga part d’insa ya soma bin ko ina da
kallo ganin yadda aka gyara ko ina , d’akin dasu prince suka shiga ya shiga , nan
ma ko ina tastas, gaban center table ya nufa , one of his finger kawai ya saki ya
dankwali wajan tare da kallan fingers dinsa , yes babu datti , d’an ta’be red lips
dinsa yayi tare da shiga d’ayar falon, anan ko zama beyi ba ya nufi cikin bedroom
d’insa , nan ma dai kamar yadda su prince suka gyara ko ina tastas , cikin wata
plasma ya nufa , daga bayanta ya danna ‘karamin button din jiki,take a Wajan
tundaga shigowar su little har yadda Suka dunga ti’kar rawa a part d’insa sai da ya
gani, fuska a had’e ya d’an lumshe idanuwansa , yana cire coat d’in saman jikinsa,
take a Wajan kakkafar surar jikinsa ta fito sosai cikin fararan kayan jikinsa,
yadda muscle dinsa suka fito sosai sai ya razana ka ga kirjinsa shima d’an dashi
dan dukda jigar dake jikinsa zaka ga alamar six packs dinsa ya fito sosai Sabida
yadda yake motsa jiki, muscle din hannunsa kamar zasu fasa hannun rigar su fito dan
duk mutumin da ya rike bazaiji da dadi ba .
Door d’in cikin d’akin yashiga yafi tsawan 1 hour a ciki , tun kafun ya fito wani
irin daddad’an ’kamshi turaransa ya cika ko ina cikin ‘kan’kanin lokaci, sosai
kamshin turaran Boadicea The victorious carbon sapphire ya cika ko ina na d’akin
musamman yadda yake fitar da wani irin cool sanyi me tsayawa a rai, a hankali farar
‘kafarsa dake cikin takalmin Yeezy fitowa sosai cikin takalmin musamman yadda
takalmin ya kasance black colour , hakan ya bawa farin fatar kafarsa fitowa sosai
cikin takalmin, hatta nails din kafarsa abun kallo no gwanin burgewa , jikinsa
sanye yake cikin Brooklinen ba’ka’ke masu laushin gaske , hakan ya ‘kara bawa
kakkarfar jikinsa fitowa, fuskarsa a had’e take yanxun ma sai gyaran gaishinsa da
ya gyara bakamar d’azu ba , yanxu gabaki d’ay doğan gashinsa yayi packing d’insa
hakan ya bawa gashin damar sakko wa har wajan kafadunsa, yadda ba’kin kayansa suka
fito sosai haka siririyar sal’kar diamond d’in wuyansa fitowa sai faman ‘kyalli
take d’auka , haka wasu abun hannu da suke hannusa , black and white suma sai faman
shining suke , da ‘karamin d’anna yatsansa ya saka wajan giransa da take a yanke ya
d’an sosa wajan tare da taunar rep lips dinsa kad’ai, a hankali kamar baya san taka
‘kasa ya fara tunkarar wajan balchony d’in dakin da yake futar da wani irin sayyi
daga wajan zaka Iya ganin yadda sojoji suke faman zagaye a cikin gidan ga su Bruno
da aka saki sai faman bud’e bakinsu suke , ya dad’e a tsaye a wajan kafun ya mayar
da idanuwansa kan stars , ya jima sosai a tsaye yana bin ko mai da idanuwa ba wai
gajiya ce beyi ba , be saba kwanciya da daddare bane sai bayan sallar asuba shiyasa
a ko da Yaushe idanuwansa biyu yana kallan komai da sanin duk abunda ke faruwa ,
sai wajan karfe 4am ya bar wajan tare da fitowa daga part d’in gabaki d’aya , yaga
lokacin da bobo ya fito har ya koma alamar zai kwanta kenan, direct kasa ya nufa
cikin d’akin uncle , already bobo yayi masa duk abunda ya kamata shiyasa ko light
be kunna ba yabar d’akin , still saida ya sake shiga d’akin su little ya kara duba
lapiyarsu kafun ya nufi part d’in bobo, gabaki d’aya light din aka she sai dum
light da suke a kunne da alama shima ya kwanta, a hankali ya bud’e door d’in d’akin
sai ya tarar da light din d’akin a kunne ga bobo kwance a kan gado, har karshen
gadon ya nufa ganin kamar bacci ne ya soma d’aukar bobo batare da sanin saba ,
hannu d’aya big boss yasa jai gyara masa kwanciyarsa, azabure bobo ya d’aura masa
Binduga aka cikin zafin nama big boss ya juyar da bindugar takıma saitin bobo, da
wani d’an iskan kallo yabi bobo dashi yana matsawa gefe , zai juya yaji saukar
muryar bobo “ ya kamata ka huta kafun yan biyunka su tashi da mamakin dawowarka
musamman that Jerry of yours”, saida ya kallesa sosai kafun ya iya bude bakinsa “
zaka iya siyar dashi mana , since ka gaji da ganinsa”, ga baki d’aya maganarsu
cikin turanci suke dan ko da wasa basufiya yin Hausa ba sai ta kama idan big boss
bayana, “ in ka yadda shafshaf ai bazaiyi tsadaba”, red lips dinsa big boss ya d’an
ta’be kad’an yana juyawa sai da yazo Daidai light din bobo kafun a hankali ya furta
“ Night” yana kashe light din. Shima part d’insa ya koma amaimakon ya kwanta ya
huta sai ma zama da yayi kan wata sofa, wata azababbiyar phone d’insa da duk duniya
babu me irin ta ya d’akko jikinta har tanbarin zakine d’an mitsitsi a wjan , ba
‘karamin billions ya kashe akan wayar ba sabida da kansa ya bada idea din yadda
za’ayi masa ita, sosai Kenta ya wuce musali, ‘karin ban sha’awa bayan ninkata uku
da akeyi har Çan za tsarinta ake ta yadda kome yake cikin wayar zai iya ganin sa
gaba da baya komai na cikin wayar ana gani, ko kuma aka rage mata tsahonta, iya
had’uwa wayar ta had’u, yadda yake kallan wayar hakan ya bawa green eyes din
idanuwansa fitowa sosai ga red lips dinsa da ya d’an ciza a hankali ,sosai lokaci
zuwa lokaci yake shafa girarsa guda d’aya da alama habit dinsa ne wannan.
Sai daf da kiran sallahr asuba ya ajje wayar tare da nufar ‘kofar d’azu, bai
jima sosai ba kamar d’azu , kamshin turaransa har ya kama ko ina sabida bala’in
dad’insa, ba shigar d’azuce a jikin saba yanxu sanye yake cikin white d’in riga da
ta d’ame damtsen hannunsa kamar zasu fasashi su fito waje , sai farin dogon Wanda
sa shima fari kirar kamfanin Armani, sosai farin fatarsa ta fito , hannunsa d’aya
ya saka Wajan girarsa ya d’an sosa kafun ya sauke hannunsa, fuskarnan kamar hadari
babu fara’a Sam a tattare dashi ko kad’an , Daidai wjn shan iska d’akin ya tsaya
har yanxu sojojin suma suna nan a tsaye suna gadon gıdan, har aka fara kiraye
kirayen kiran sallah .
**** yau hakanan prince shine ya fara tashi tun kafun yaya bobo ya tashesu,
saida ya tabbata yayi wanka sannan ya Tashi little shima , yau be ‘bata lokaci ba
ya mike shima ya shiga Wanda duk iskancinsu basa so jam’i ya wuce su, shiyasa yau
da wuri suka shirya , Sabida sanyin asuba kaya me kauri sosai little ya saka sabida
sanyin da yake ji, su fito daniyar tashin bobo da uncle suka tarar da bobo suma sun
fito shida uncle , with a suprise bobo ya furta “ addua akai muku kuka tashi yau
dawuri “, dariya little ya saki yana nuna masa ya prince “ yaya bobo , shine fa ya
fara tashi yau dawuri “, da mamaki uncle da bobo suka kalli prince , shi kuma
hararan little ya ke yi “ addua kayi ka Tashi da wuri?” Cewar bobo , kamar zaiyi
kuka ya furta “ please yaya bobo ka bari” yanxu ma dariya little ya kara saki yana
sakar masa gwalo “ lokacina tafiya fa” cewar uncle , jinjina masa kai bobo yayi “
yes uncle ! But ku ‘kara 5 minutes tukunna “, lokacin sallar za’a karawa lokaci?”
Cewar uncle yana kallansa da mamaki, bobo murmushi kawai ya saki ba tare da ya ce
komai ba , elevator din da aka bude ne gabaki d’aya uncle , prince , little Suka
mayar da kansu waje cike da shakkar abunda zasu gani, banda bobo da ko juyowa beyi
ba sabida sanin ko wanene, cikin ta kunsa ya fito daga elevator fuskarsa kwata
kwata ba annuri, prince be san lokacin da bakinsa ya fara furta “ Innalillahi
wa’inna ilaihi rajiun” , Sabida yadda zuciyar sa ta buga bummmm yasan tabbas yanxu
dole ya shiga taitayinsa ,kafun big boss ya canza masa kamanni da Sauri ya toshe
bakinsa , yana zare ido , uncle ma da shock da mamakin lokacin da ya dawo ya hana
sa motsawa, sosai jikin little ya fara rawa yana ‘ko’karin magana amma ya kasa
sabida tsananin murna da yake ciki, da’kyar bakinsa ya iya furta “ yaya big boss
dina ?” Sai kuma ya kalli yaya bobo, ganin ya jinjina masa kai yasa da Sauri ya
‘karasa wajan big boss da yake tunkaro inda suke ,be tsaya ‘bata lokaci ba yayi
hugging d’insa ,cikin kuka little ya furta “ nayi missing dinka sosai, plx kadunga
tafiya dani”,sai kuma ya soma kuka kamar wani ‘karamin yaro.

********
ABUJA NIGERIA
A hankali Abla take shash’she’kar kuka gudun kar Binta shagala ta fad’awa uwar
karuwai abunda tayi mata , ita kuma ta saka su zinariyya su no mota shiysa tayi
zamanta a wajan , ba tsoron binta shagala ko uwar karuwai ne yasa ta kuka ba , zafi
da zuciyarta take matane yaşa take kuka , ji kanta take kamar acikin wata
‘kuntacciyar rayuwa , batasan
iyayenta ba , bata danginsu ba , bata san a ina suke rayuwa ba , suna mace ko a
raye ?, suna tunawa da ita ko sun mata da ita ? So? Bata san shi ba , batasan ya
yake ba, abu d’aya ta sani, tun ta sowarta har zuwa yanxu batasan wani abu wai shi
gata ba ko farin ciki , abu d’aya ta sani , ta taso cikin kuncin rayuwar, rayuwar
da tunda tayi wayo ake mata gori ita da wacce ta tausayawa rayuwar ta lokacin da
take jinjira , matar da ta sadaukar da farinciikinta tana kula da ita duk da
kasancewarta karuwa. A wannan duniyar barıkin ta koyi abubuwa da yawa aciki,abu
d’aya ta sani , in dai kana bukatar abu to tabbas zaka mayar da saka mako,a duniya
idan akwai abunda Abla ta tsana to tabbas karuwanci ne na farko, tun tana tunani
har baccin wahala ya d’auketa a yadda take a cunkushen nan.
A cikin gida kuwa sabida bariki irin na binta shagala ko a fuska bazaka ga
alamar ‘bacin rai tattare da itaba duk da abunda Abla tayi mata ya mugun ‘bata mata
rai, amma da yake ta san ta kan duniyanci fuskarta cike take da Anna shuwa a ciki,
a maimakon Abla da Husna ta tafi d’aki ganin yadda take binta da kallo tun d’azu ,
har dare ya fara ratsa wa babu Abla babu alamarta , Allah sarki Arwa tun da taga
dare yayi sosai bata ga Abla ba ta kasa zama sai faman jiran tsammanin dawowarta
take, shiru har wajan shad’aya sosai hankalinta ya Tashi ta kara komawa d’akı ko
zata tarar da ita amma shiru babu ita babu alamarta , sai ma Anee dake zaune
kankatifarsu sun bud’e ‘kartuwar gashshiyar kaza sai ci suke ga manya manyan kwalin
exotic d’insu , da kallo suka bi ta Dashi ganin kamar akwai da Muwa a tattare da
ita , ta’be baki ilham tayi kafun ta furta “ ke kuma lapiya kamar wacce akai wa
mutuwa zaki shigo mana a furgai furgai haka ?” , bansa Arwa mata , sai kum ta mayar
da kallanta kan Anee “ Anee bakiga Abla ba ?, tun d’azu nake jiran ganin ta amma
haryanxu babu ita babu alamarta..”, bata ‘karasa ba sabida dariyar da ilham ta
kwashe da ita “ Sabida wannan abun ne wai kika burkice haka ?, nasan tana can tana
kuka tunda abunda take kurin’boyewa Anta’ba zanso naganta nima ba “, kallan me kike
nufi Arwa ta bita dashi, yanxu ma wat dariyar ta ‘kara kwashewa da ita “ bani nakar
zomanba fa , rataya aka bani,rayuwar kuce dole sai kun gur’bata kamar sauran , dan
dole ki zabi d’aya ko ki fara shaye shaye ko ki fara karuwanci , kin ga Anee yanxu
shaye shaye ya bi jikinta, husna ta za fara shiga hanyar karuwanci, waccen banzar
da ita kuma kinga sai ta zama karuwar gida kawai…”, bata ‘karasa ba sabida yadda
Arwa ta daddage ta buge bakın ilham da harsaida tayi ‘karamin kara Sabida taji
zafin dukan , zata mike aneee tayi saurin ri’ko “ ki manta kawai , kiyi hakuri mana
“, fusge hannunta ilham tayi tana nuna Arwa da yatsa “ tabbas bakisan wacece ni va
shiyasa kika tafka wannan kuskuren , ada inashare duk wani haukanku Sabida na samu
biyan bu’kata ta amma banda yanxu , Wallhi dukannan da kikai zaki gane shayi ruwane
, Indai nice ilham “, tsaki Arwa ta ja duk da yadda take da tsoro yau saida ta
tankawa musu “ Menene kuma bamusani ba na halin naki? Kina tunanin bansan cewa
labarin da kika babu nacewa iyayenki sun mutu duk karya ne ? Ko kuma siyarda
mutumci na da na Abla da kuke shirin yi? Ko muna furta Anee da har kikai sanadiyar
sata ta fara shaye shaye , duk da husna kwad’ayi da san zuciyar ta ne ya ja mata
wannan ba’kar rayuwar amma kefa? Komai ma rayuwarki ‘karya ce “ batare da damuwa da
maganganun Arwa ba ilham ta ta’be baki , Aneesa kam sai faman lumshe ido take
sabida maganin da ta sha yanxu da alama batajin me suke cewa ma “ bakiyi ‘karya
ba , duk abunda kika fada hakane sabida banasan naganku cikin farinciki, inaso naga
rayuwarku ta gur’bata, inaso naga rayuwarku ta gur’bata kamar yadda tawa take a
gur’bace, sau da dama na so kawar dake Sabida idanu da kika samun har kike
‘ki’karin fad’awa abla abunda kikaji muna tattaunawa da uwar karuwai, amma shegiyar
Ablar nan kullum cikin bayyana take , maganar da kikaji Hakane,eh Hakane , ni ba
nazo nan gidan sabida gata ba , nazone Sabida na lalata rayuwar yan mata masu irin
shekaruna kamar yadda kwartan Dije yar kwal wato mahaifiyata yake tan haddi na ,
yasa na koyi bariki , sanin cewa uwar bariki aminiyar Dije ce yasa nazo gidan nan ,
kuma nayi sa’a na samekun duk da gabaki d’aya kudin gidadawane marasa tunani kun
kasa fahimta , duk da ibtissam taso fahimtar wani abu amma na wuce tunaninta “, ta
fad’a tana Kallan Arwa da ta gama shiga shock din maganganun Iham “ kınsan Menene
abun burgewar, tun ina 12 years na san d’a namiji sannan yanxu a rayuwa ta bani da
wani babban buri kamar naga lallace war Abla, wallahi na tsaneta, Sabida duk cikin
gidan nan tafi kowa kyau , tafi kowa gashi, tana da jiki me kyau , sosai hakan yake
‘bata mun rai Sabida banaso taji dad’in rayuwa , na fiso taita wahala a haka karta
samu farinciki”, idanuwanta akan Arwa ko tsoran wani ya shigo batayi ta cigaba da
maganar “ bawai na fada miki maganan nan dan naji tsoroba, na fad’a miki abunda ya
kamata ki sani sannan kema ki shirya , Indai ni Jinin Dije Yar kwalce “, ta karasa
tana bin Arwaa da kallan kaikai ce tai ficewarta daga d’akin tana barin Arwa da
Tashin hankali , hannu ta d’ora a sama tana fad’in “Innalillahi wa inna ilaihi
raji’un da ma duk wannan plan din ilham ne ? Shiysa duk lokacin da Suka kwanta suna
tashi zasu ga bata nan” tunani Arwa ta somayi , ta fad’awa Abla ko karta fad’a mata
, tasan Abla bazata ji dadi ba musamman yanxu da batasan halin da take ciki ba
shiysa tayi wa kanta al’kawarin bazata fad’a mata va . A d’akın ta zauna tana jiran
tsammanin ganin Ablaa , tun tana saka ran ganinta har bacci ya fara fuskarta,
lokaci d’aya kuma wani wahalallan bacci ya d’auketa.
Kiran sallah asuba ne ya farkar da Abla daga baccin da ya d’auketa,
bakinta d’auke da adduar tashi daga bacci da bud’e idanuwanta , idanuwanta har sun
ri’ke , sosai taji zafin wuyanta sabida yadda tayi bacci, tasan yanxu su zinariya
suna ta nemanta ganin bata nan , a hankali ta fito daga cikin store din, duk da
ydda zuciyar ta take bugawa hakan be hana ta tunkari gidan ba , tana shiga babu
kowa. Falon , kai tsaye d’akinsu ta nufa nan ma Arwa da Aneesa kawai ta tarar cikin
d’aki, kai tsaye toilet ta nufa ta tsarkaka jikinta , sai datayi sallar isha’i da
asuba tana kaiwa Allah kukan ta kafun ta tafi Arwa da Aneesa akan su tashi suyi
sallah , gabaki d’ayansu da farin ciki Suke kallanta har da had’a baki wajan furta
“ kindawo?” Kai Kawai Abla ta d’aga musu dan ko kanta bata san d’aga wa , suna shaf
shaf suka tashi sukayi sallah dan Abla ce kawai me tunatar dasu sallah arayuwarsu.
Har ‘karfe tara babu Wanda ya shigo d’akin , itama abla bata fito waje ba
Sabida zafin da wuyanta yake mata, amma abun mamaki yau gabaki d’aya yaran binta
shagala ne suka gyara ko ina na cikin gidan harda kawo musu abunci dukda abunda
tayi wa binta shagala, haka kurin bata yadda da abincin ba shiyasa bataci ba ta
barshi, tana fitowa falo suka ci Karo da binta shagala taji uban ado, yadda abla
take kallanta itama ita take kallo fuskarta cike da murmushin bari ırin nata “ baby
ba gaisuwa ?” Cewar binta shagala , banza alba tayi mata tayi ficewarta daga
gidan , girgixa kai Binta shagala tayi tana bin hanyar da Abla ta fita da kallo,
kai tsaye d’akin uwar karuwai ta nufa, ko sallama batayi ba ta banka kofar d’akin
ta shiga , lokacin da uwar karuwai take cin chips da Kwai abunta , tana ganin binta
ta Soma washe mata baki “ kina rayuwa cikin yara ‘kanana bakyaşamın kud’i ta
dalilinsu? To Menene anfanin barikin naki? Hajiya duniya ta bun’kasa yanzu da yara
zaki samu ma’kudan kudin da har zakiyi ta juya su san ransu, ya kika ganni? Kinsan
ba ‘karamin kud’ine ya zauna munba, ta ‘karasa tana juya Orobo (lukuti)d’in jikinta
, samun waje uwar karuwai tayi tana jinjina maganar binta shagala kafun ta saki a
jiyar zuciya “ban’ki ta taki ba binta amma taya kike tunanin za a fitar da yaran
batare da mutane sun Ankara ba ?, dan tabbas inaso na dunga fancanawa cikin daula
“, anzo inda take so shiyasa ta saki wani shu’umin murmushi tana kallan kawar ta “
wannan ba matsala bane, zan temaka miki amma mutum d’aya zan fara fitar miki da ita
, kina zaune zaki samu 20million”, zaro ido uwar karuwai tayi tana furta “ 20
million fa kika ce ? “, kanta binta ta jinjina mata alamar hakane , da Sauri uwar
karuwai ta furta “ na Amince amma wa za a fara fitar wa ?” Yarinyar da na d’auka
jiya “, cewar binta , katseta uwar karuwai tayi ta hanyar furta “ kardaki kice Abla
kike magana ? Kinsan taurin kan yarinyar nan kuwa ? Cikin ‘kan’kanın lokaci zata
‘bata mana shiri me zai hana ki d’auki wata a cikin su ga Arwa ga Aneesa dan bazan
iya saka ilham ba Sabida yar Dije kwalce kinsan kuma bala’inta itama cikakkiyar yar
barikice kema kinsani”,murmushin gefen baki binta ta saki tana d’age ka fad’a” tun
da baki Shirya ba ai shikenan “, zata tafi uwar karuwai tayi saurin dakatar da ita
ganin ga samu ga rashi cikin saku wa ta furta “ na amince amma taya za a fitar da
ita ?yarinyar ba ‘karamin brain ne da ita ba “, ynxu kam binta kyal’kyale wa tayi
da dariya kafun ta ciro wani farar powder a Leda tana nunawa uwar karuwai “ duk
kwakwalwarta da ilimin ta ai bata Kai wannan aiki ba ko?” Ta ‘kara tana d’aga
coccaine din hannunta . Gabaki d’aya dariya sukai saki “ shegiya binta baki da
dama duk wani shu’umancina kin dameni, shiyasa nake san harika da irin ku “, cikin
yanga binta take d’ad’d’age fuska da hura gajeren hanci ita a dole ana kod’ata .
**********
************
KANO
1:30pm kid’ane yake tashi a falon sosai sabida volume din murya da Baby ta ware
sosai sai kace gidan shed’anu ga wani irin ‘kara da ya karad’e ko ina , baby ko
ajikinta ko d’an kwali babu akanta sai gashin kanta da ta tufke jikinta sanye da
‘kananan kaya Riga da wando ga head phone d’inta da ta saka a kunne amma duk da
haka sabida neman rigima da Eshaal ta ‘kara waye volume , ko mintuna 5 bata ‘kara
ba tana rawa Eshaal ta shigo falourn rai a ‘bace , magana take wa baby amma kamar
ma bata san tanayi ba shiyasa taji haushi ta kashe kid’an , azuciye baby ta tsaya
daga rawar da take tana bin Eshaal da shigo falourn sanye da hijab da alama sallah
zatayi ko take shirin yi “ uban wa yace ki kashe mun kid’a ? Ke wace irin
ballagazace wai ? Nace ki dena shiga rayuwa ta amma sabida maita sai kinshiga,
karkiga mun had’a dad dake ki fita idona “, cewar baby, guntun tsaki Eshaal ta saki
“ ke kullum baby wai sai kin nemo abun rigima? Karki manta sallah fa akeyi , be
kamata ai kisaka kid’a lokacin sallah ba , ko ke bana Tuna’nın kinyi sallahr,
sannan idan dole sai kinji wa’kar sai ki kunnashi a d’akin ki mana ?”, a kufule
baby ta kalleta “ idan kece kika kar’barmun sallar karki karba , da nayi sallar da
banyi ba ai ba kabarin mu d’aya ba , stupid kawai, wareey daga nan wajan “, ta
karasa tana d’aukar remote , fusge remote din Eshaal tayi “ wallahi bazaki kunna ba
, kinsamu ana bin ki ta laluma amma ke sam bakısan annabi ya kafuva”, itama hannu
baby ta saka zata karbi remote din Eshaal ta hanata, lokaci d’aya suka soma kokawa
ran baby ba ‘karamun ‘baci yayi ba , shiyasa ta daddage ta gantsarawa Eshaal cizo a
wuya da yasata sakin gigitaccen kara dan mugun cizo baby ta kai mata , karar da
yasa momcy da ke waya a d’aki sai da taji amma ko motsawa batayi ba balantana ta
fito ta duba abunda ke faruwa ,AMMA kuwa lokacin da Eshaal tasaki ‘karar tana cikin
band’aki tana wanka, itama azuciye Eshaal ta cijeta da yafi wannan baby tayi mata ,
itama ‘karar ta saki dan sosai taji zafin cizan, a wannan karan karar baby da momcy
ta jine yasa ta kashe wayar tare da barin dakinta Daidai lokacin da baby ta d’auki
wani abun decoration ta kwalawa Eshaal , lokaci d’aya goshinta ya soma zubar da
Jini , zata Shako baby momy ta shigo falon , cikin kukan shagwaba baby ta nuna mata
cizan da Eshaal tayi mata , itama rai a’bace ta janyo wata bakar waya me kaurin
gaske ko la a kari da fasa mata goshi da baby tayi batayi ba ta soma jibgar Eshaal
da ba’kar wayar nan abunda da farar fata , jikinta duk yayi ja alamar duka, da
Sauri Amma ta fito ko kaya bata saka ba sai dogon hijab data zura , yadda taga momy
nan dukan eshaal ne yasa tashiga bata hakuri amma kamar zugata take , duk yadda
Amma tayi abun yaci tura dole ta hakura musamman wanka mata mari da momy tayi ,
itama baby tsaki ta ja “ wallahi na tsani munafurci, wannan mata dai muna fukace ke
, inbanda munafurci uban me ya fito dake? Dama har dake aka had’a aka zanen, Mtsww
“ taja tsaki tare da daukar tanfatsetsiyar wayarta tai wuce warta daki, itama momy
tana gama dukanta tai wuce warta ranta fess, da te makan Amma Eshaal ta koma d’aki
sai kuka take , wani man zafi Amma ta dakko cike da tausayawa ta shafa mata kafun
ta bar mata sauran, sai faman rarrashinta take tun tana kuka har ta dawo a jiyar
zuciya a haka bacci ya d’auketa rai a’bace .

*********
***********

NEW YORK

Lumshe idanuwansa big boss yayi Sabida yadda yake jin kukan little , kad’an ya saki
fuskarsa ba kamar d’azu ba yana janye little daga jikinsa, magana yake sanyi amma
izza da miskilanci ya hana sa magana , da’kyar ya iya fusgar maganar da yake sanyi
a ta’kaice “ Bana san hayaniya ko? Crying?”, kansa little ya girgixa masa sai kuma
yayi saurin bud’e bakinsa dan yasan bayasan nodding “ Na dena yaya am sorry” lumshe
masa idanu kawai big boss yayi, suka soma tafiya lokacin da little ya ri’ke masa
hannu sabida kiran sallahr da aka Soma , su bobo gabaki d’aya basu motsa daga
yanayinsu ba Sabida yadda Suka zubawa su big boss idanu, sun kuyar da Kai ‘kasa
prince yayi yana d’an sosa kansa kamar wani mara gaskiya “ welcome yaya”, ya furta
lokacin da yaga big boss ya zuba masa narkakkun eyes dinsa , shima saida ya ja
second kafin ya bud’e tattausan lips d’insa“ is the Innalillahi for me ?”, prince
zai girgiza masa kai kallan da yaga big boss yayi masa ne yayi saurin furta “ No
yaya! Who am I ? Am just so happy to see you”, ya karasa yana yiwa yaya bobo narai
narai da eyes d’insa alamar help, girgixa kai Kawai bobo yayi “ let’s pray, lokaci
na tafiya”, babu Wanda ya ‘kara magana har suka fito, anan din ma cike yake da
sojoji ta ko ina , ga fuskokinsu da ya ke a sanye da glass , fitowar su ne yasa
gabaki d’aya sojojin ‘kamewa babu Wanda yayi gigin yin kwakkwaran motsin da zaisa
big boss ya d’ago eyes dinsa , a masallaci ma kowa shiga taitayinsa yayi ko me
zasuyi cikin taka tsantsan suke yinsa , ana idar da sallah suka fito suka koma
cikin gida , gabaki d’aya kowa part d’insa ya nufa musamman su prince yau ko bacci
ba a koma ba aka shirya cikin sport d’insa shida little yau tun kafin lokacin motsa
jiki yayi suka fito ,har bobo yau saida suka riga futowa shima da jikinsa yake
sanye da kayan sport din ,bece musu komai ba Sabida yasan dalilin shiryawar tasu da
wuri, har suka gama training babu big boss , shiysa little yana komawa part d’insu
ko kayan jikinsa be cire ba ya nufi part d’insa , sanyi da kamshin turaran big boss
gabaki d’aya ya çıka ko ina da ko ina , d’akin da yafi tunanin big boss na ciki nan
ya nufa bayn ya ratsa falournsa guda biyu, a hankali yayi knocking shiru baa amsa
masa ba , ‘kara knocking yayi naji shiru , shiysa kawai ya bud’e d’akin bayan
sallamar da yayi, ko ina babu haske a d’akin sai dum light , a hankali ya furta “
yaya ?”, shiru ba a amsa masa ba , a karo na biyu ya ‘kara furta “ yaya”cikin
sand’a ya ‘Karasa king size d’in big boss, a hankali yake tafiya har ya ‘karasa
wajan gadon, hugging d’insa yayi ta wajen blanket dinsa yana dariya “ nasan kana
cikin nan “, cewar little , a duniya babu me zarrar d’anesa kamar little , big boss
najinsa amma ya bud’e baki yayi masa magana ne bazai yi ba , shima shiru little
yayi yana ‘kara nutse wa cikin blanket din da yake da mugun laushi, tsawan 5
minutes shima sai bacci ya d’auke sa a yadda ya kwanta . Kusan 10 minutes suna a
haka kafun big boss ya saka hannunsa d’aya ya gyara masa kwanciyarsa kan gadonsa me
shegen laushi, blanket din sa ya lullu’ba masa a haka sukayi bacci a tare .
BOBO….
Tunda yaga little ya nufi part d’in big boss na san yayi bacci yanxu ganin kusan
20minutes daman wani lokutan haka yake , shiysa sukayi breakfast d’insu su uku, sai
da suka kammala kafun ya nufi office dinsa na cikin gidan, kai da kaga office din
kasan ba karamin kud’ine sukai kuka a cikinsaba komai na ciki kalar uniform d’insu
ne, cike da girmamawa Robert yayi knocking door din , sai da bobo ya bashi izinin
shigowa tukunna ya shigo ciki, Seat din dake facing d’insa bobo ya nuna masa ,
shima Robert cike da girmamawa ya zauna tare da fito da envelope din hannunsa yana
mi’kawa bobo, gabaki d’aya abunda yake ciki bobo ya fito dashi, wasu hotunane a
ciki kusan guda biyar da akai snapping , ko wana hoto kana kalla zakasan bayan sun
mutune akai snapping d’insu, “ sir gabaki d’ayansu sun mutu ta hanyar attack din
zuciya , a lokaci d’aya duk da likitoci sun tabbatar da mutuwar su mintuna bayan
mintuna daga nan babu abun da likitoci suka gane sai zuciyarsu data buga hakan ne
yayi sanadiyyar mutuwarsu,” cewar Robert , sai kuma ya kara ciro wata leda da ya
shigo da ita ya mi’ka masa , “ a area din wajan na Sami wannan abun”, kallan abun
sosai bobo yayi kafun ya furta “ black spider ?” Yes sir cewar Robert “ nabaso big
boss yaji maganar black sniper dinnan ! Leave the matter on my hands, you can go “,
yes sir ,har ya juya zai fita Bobo ya kara dakatar dashi “ Dylan da Logan’s?”sir
mun fitar dasu daga gidan kamar yadda ka umarta “ kansa kawai bobo yayi nodding ,
dalili d’aya ne bobo yasa a fitar dasu Logan daga gidan Sabida tabbas idan
tsautsayi yasa big boss ya gansu sai yayi mugun nakasa musu jiki kuma babu Wanda ya
isa yayi masa komai , yasan big boss da zafin zuciya idan ya hau musamman raping da
sukayi ,bayan fitar Robert sosai yake bin ‘karamar kwalbar dake d’auke da tanbarin
black magic spider da ido, tanbarin da yake d’aya daga cikin abunda ya lallata musu
farin cikin su tsawan lokaci , duk lokacin da ya tuna ranshi ba karamin baci yake
ba ,a fili ya furta “ just a little more time”.

Kİ BIYA KUDINKI KIYI KARATU HANKALI KWANCE , IBTISSAM NA KUDINE 300 , ta wannan
account din 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo mun shaidar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

BANYARDA WANI KO WATA YA JUYAMUN LITTAFI TA KO WANA SIGABA , KO A SAKA MUN SHI A
YOUTUBE BATARE DA IZININA BA, DUK WANDA YAYI GIGIN YIN HAKAN SHIDA ALLAH WALLAHI😒.

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
S____15💞

Abubuwa da damane suka fara masa yawo cikin kwakwalwarsa, 22years, 22years komai ya
‘baci ba kamar daba,he will never forget does years back, ganin ranshi na ‘ko’karin
‘baci ne yasa ya ajje kwalbar a wani ma’a dani me security da ba kowa ne xai kai
hankalinsa wajan ba .

******** Gabaki d’aya yau Garin cike yake da manya mayan sojoji ta ko ina ka waiga
zaka tarar da zaratan sojoji ko wannansu ri’ke da bindugarsa, ba iya New York ba ,
duk Wanda ya tashi a ‘kasar U.S yasan tabbas Big Boss ya shigo ‘kasar sabida yadda
helicopters din sojoji suka dunga shawagi, daman hakan ce ke faru duk lokacin da
zai dawo zaka gansu suna Faman yawo, tako ina securities ne da manyan mukamai a
hannunsu , yadda cikin gidan ya cika da manyan sojoji sai hakan ya baka mamaki amma
babu me zarrar shiga cikin falour bayan family dinsa , amma da ga waje sosai zakaga
sun kewaye ko ina da tsaro.

Karfe 11:20am ya farka daga baccin da yake , a hankali ya fara bud’e kyawawan
eyes dinsa, abunka da me sexy eyes sai idanuwansa suka ‘karayin kyau Sabida baccin
da yayi, har yanxu fuskarsa babu fara’a ko murmushi a tattare dashi, side d’in
little ya kalla yaga yadda yake baccinsa hankali kwance tsawan 1 minutes yana bin
fuskarsa da kallo kafun ya janye eyes d’insa yana mi’kewa zaune sosai, kyawawan
long fingers dinsa farare tas dasu ya saka kan lallausan gashin little da yake
zuwar masa har wajan idanuwansa sabida irin gyaran askinsa, cikin Cool voice kamar
ba tashi ba ya furta “ Hey ! Wake up!”, ganin little ya d’an motsa kad’an ne ya
kara bud’e muryarsa a hankali “ wake up”, yadda little ya fara bud’e eyes dinsa ne
bakinsa d’auke da addua yasa big boss had’e ransa kamar bashi ba , da wani irin
kallo yabi little dashi “ who permitted you , to enter into my room , and even on
my bed ?”, hannuwansa biyu little yasaka ya ri’ke kunnuwansa , cikin d’an turo baki
ya furta “ yaya big boss nayi missing dinkane kuma na dad’e bamu kwana tare ba “,
ya ‘karasa yana turo bakinsa kamar wani ‘karamin yaro, be aune ba yaji big boss ya
d’alle masa baki da har saida yaji zafi ya furta “ouch! Da zafi”, lumshe eyes dinsa
big boss yayi duk da yaji zafin abunda yayi wa little a zuciyarsa amma a fili sai
ma kofar fita da ya nuna amsa , fuska ba fara’a ya furta “ out of my room!” Little
zai ‘kara magana cikin d’age gira big boss ya furta “ Now !”, duk da ba cikin d’aga
murya ya furta ba , sunkuyar da kansa little yayi kamar me shirin sakin kuka ya
nufi ‘kofar barin d’akin , sai da ya tabbata de ya bud’e door din tukunna kafun ya
d’ago ya kalli big boss da ya d’ago eyes dinsa shima , hawayen da ya gani akan
fuskar little ne yasa ya d’an ware kyawawan eyes dinsa amma be ce masa komai ba
sannan be motsa daga yadda yake ba , a shagwa’be little ya furta “ yaya ban karya
ba Sabida kaima bakaci abinci ba “, yana gama fad’ar hakan yayi saurin rufo masa
‘kofa dama da gangan yayi hawayen , Hakanne kawai zaisa big boss yaci abinci tunda
little be cıva . Lumshe eyes dinsa big boss yayi a karo na ba adadi kafun ya saka
hannunsa cikin lallausan gashin kansa da ya sakko masa har gadon baya , yadda ya
motsa bakinsa kad’anne ya bawa dimples dinsa lotsawa kad’an.
Cikin nutsuwa ya mike tsaye gabaki d’ayansa , sosai yanayin jikin big boss zai
baka tsoro da muscle dinsa ba ‘karamun murd’ewa sukai ba alamar yasabu babban horo
c bakar singlet dinsa sosai ya fito da ainahin kakkarfar surar jikin da Allah yayi
masa , ga baki d’aya murd’ad’d’an bakin gashin kansa ya zubo masa aka fad’unsa, har
lokacin kuma sarkar diamond dinsa na wuyansa . Cikin takun sa me cike da izza big
boss ya soma taka ‘kafarsa kamar bayasan taka ‘kasa , komai nasa cikin nutsuwa yake
yinsa duk da rashin fara’ar da yake fuskarsa direct ‘kofar da ya shiga jiya ya nufa
kai tsaye .
Little yana sakkowa main falour ya tarar da uncle , bobo da kuma prince zaune
a falour direct kujerar da bobo yake ya nufa kasan tuwar a 3 sitter yake zaune ,
gabaki d’aya binsa sukai da kallo ganin yadda ya kwanta ya d’ora kansa a cinyar
bobo, shima bobo bai ce masa komai ba sai hannunsa d’aya daya saka masa cikin gashi
yana d’an masa susa a hankali kafun ya d’aga shi zaune yana binsa da kallo “ jekayi
wanka tukunna , sai kaci abinci okay !?”, okay kawai little yaje masa yana mikewa
cike da tsokana prince ya furta “ uhm shiyasa naji gidan mu har ya fara wari Aushe
little beyi wanka ba “, kamar zaiyi kuka kuwa little ya mi’ke yana kallan prince
lokaci d’aya dariya ta zo masa amma ya danneta yana nufar hanyar elevator , cikin
d’aga murya little ya furta “ fine ai daga d’akın yaya nake , bari na koma sai kayi
masa bayanın yadda nake wari”, bai karasa zancansa Sabida sufar da prince yayi ya
nufeshi “ Haba mana little dina kai ma kasan wasa fa nake maka, kaga sai kamshin
turaran yaya ma kake , let’s go ni da kaina ma zan kai ka d’aki, ya Karasa yana
sabar little a baya ko elevator be bari sun hau ba ya nufi stairs, girgiza kansa
bobo yayi “ bazaku ta’ba girmaba”, shima uncle murmushin drama dinsu yayi “I love
it idan fuskarsu tana dauke da murmushi, kullum ina farin cikin hakan..”, ya karasa
a sanyaye, murmushin da yafi kuka ciwo bobo ya saki “uncle don’t even start dis
please, mistake d’aya sai ya shafi kowa, kasan halinsa, zai iya fitowa any time now
“murmushin manya uncle yasaki kafun ya furta “ da sannu zuciyar nan tasa sai ansamu
me saukar da ita dukda nasan Nima da wuya amma ina fatan Allah ya sanyaya masa
wannan zuciyar tasa komai ya wuce , “uhmm “ kawai bobo yace dan shima kansa baya
san a taso da maganar.
Suna zaune almost 30minutes kafun su prince su ‘kaya sakkowa wannan karan little
cikin Riga da wando red colour da sukayi matukar yimasa kyau ya kasa , ga gyaran
gashin kansa da yafi komai d’aukar hankali, kamshin turaran jikinsu gabaki d’aya ya
cika ko ina na cikin falourn had’e da sanyin Acn . “ wow ! Little wannan wanka haka
sai kace me shirin zuwa zance , da Sauri ya zaro idanuwansa sai kuma ya shagwa’be
face dinsa “ plx uncle ka bari kalli fa kallan da yaya bobo yake mun”, pillow din
side dinsa bobo ya dauka ya jefa masa “ little bakaji ko ? Kaga ina wasa da kai ?”
Dariya little ya saki yana karasa wa inda bobo yake yayi hugging Dinsa “ Haba yaya
bobo ! And nifa yunwa nake ji bari naje na kira yaya “ bai ‘karasa zancan saba
sabida elevator din da aka bud’e gabaki d’aya maida eyes dinsu sukai suna jiran
fitowarsa.
Tun kafin yafito daddad’an kamshin perfume d’insa ya cika ko ina har ba ajin
kamshin turaran su little ,ta ko ina kamshin turaransa ne yake yawo sabida Acn
falourn yadda ta ‘kara buso da sanyin ta sai hakan ya kara wa kamshin falourn dad’i
, gabaki d’ayansu kowa jira yake ya ga fitowarsa , a hankali ya fara taka kafarsa
gabaki d’aya sai suka mayar da hankalinsu sosai akansa, sosai kyawu da haduwar big
boss ta kara razanani dan ba karamin kyau Allah yayi masa ba , kyakkyawane na ajin
karshe da furta yanayin kyansama bata lokaci, iya haduwa da tsari da ko wace mace
zata nuna a sa’a big boss ya wuce tunanin hakan . Sosai ya ‘kara d’aure fuskarsa
sabida yadda yaji alamar idanuwa akansa amma gabaki d’aya babu alamar zai d’ago ko
nuna alamun akwai masu rai a cikin falon,sanye yake cikin ‘kananan kayan Ralph
Lauren black colour da Suka fito da hasken fatar jikinsa fari tas dashi sosai kayan
suka kar’beyasa musamman daya had’u da gyaran gashin kansa da ke tashin kamshi, sai
shinning ba’kin sumarsa da ta tayi mugun had’uwa yake , yadda ya tufke gashin kansa
sai ya karayı masa kyau sosai , hatta kyakkyawar face d’insa sai da ta fito fara
tas da ita duk da babu fara’a akanta ga sarkar diamond dinsa Siririn sai faman
shinning take , ‘kafarsa kuwa sanye yake cikin kyakkyawan bakin takalmin horsebit
loafer . Tunda ya fara takunsa cikin nutsuwa bai d’ago ya kalli kowa daga cikin su
ba , cikin wata kujera me shegen kyau da babu Wanda ya’ke zama akai sai shi ya
nufa, yana crossing legs dinsa prince da little suka yi saurin sauke ‘kafarsu da
Sukai crossing , a sanyaye prince ya furta “ yaya good afternoon”, shiru be amsa
masa ba sai ma lumshe eyes d’insa da yayi kusan 3 minutes har prince ya cire rai da
amsawar sa sai kuma ya tsinci daddad’ar muryar sa yana furta “ Good afternoon
uncle…” yanda yayi maganar a hankali da ace ba shi suke kalla ba da bazasu ta’ba
gane cewa yayi magana ba , murmushi uncle ya sakar masa “ Afternoon too BUBUBUBU…”
da Sauri big boss ya d’ago da eyes dinsa da suka fara kad’awa ya zubawa uncle da ke
binshi da kallo shima , da gangan ya furta bubububu Sabida yaga reaction dinsa ,
amma yadda ya ‘bata raine yasa uncle sakin wani murmushin “ Menene na ‘bata rai
kuma ?Please banasan wannan reaction din nasa, idanuwan big boss ne ya soma kad’awa
har yanxu yana bin uncle da kallo amma bakinsa yayi masa nauyin da ko harshensa
bayajin zai iya d’agawa , yadda bobo yaga reaction din big boss ne yasa yayi saurin
dakatar da maganar “ uncle please…” cewar bobo duk da shima yana kokarin
controlling kansane sabida ran big boss da yaga ya soma ‘baci, a zuciye big boss ya
d’auke eyes dinsa daga kansu ya lumshe idanuwansa yana sosa girarsa guda d’aya me
tsaga da ‘karamin d’an ya tsansa, da ido bobo ya nuna musu dinning alamar su d’auko
abincin sa Dan ko giyar wake suka sha yadda suka ga ransa ya ‘baci idan wani yace
zai kaimasa abu zai iya balla mutum a wajan , a hankali su Prince suka cika gaban
wani center me fad’i sosai da abinci kala kala gwanin burgewa har suka gama be
bud’e eyes dinsa ya kallesu ba duk da motsinsu da yake ji cikin kunnuwansa , cikin
kujerar gefansa little ya zauna a hankali ya furta “ yaya yunwa nake ji”, a hankali
ya soma bud’e eyes dinsa kallo d’aya yayiwa little kafun ya d’auke eyes dinsa yana
zama sosai abincin ya kalla da kansa kafun ya kalli little , inda suke bobo ya
nufa da kansa yayi serving d’insu sabida yasan kalan abunda kowa yake iyaci , da
ido big boss ya kalli little sannan ya kalli food din da bobo yayi serving dinsa,
yagane me yayan nasa yake nufi shiyasa ya janyo abincin nasa ya faraci a tsanake
banda big boss da ko farar ta’ba abincin beyi ba , barin wajan bobo yayi tsawan 5
minutes ya fito hannunsa d’auke da wani unique small cup me d’auke da coffee sai
faman turiri yake , har inda big boss yake ya karasa tare da mi’ka masa , a hankali
big boss ya saka dausasan hannunsa kamar ba soja ba ya karbi cup din yana lumshe wa
bobo ido, bobo ya gane me hakan yake nufi shiyasa ya d’anyi knodding kansa kadan ,
cikin wani irin unique way ya fara sipping coffee dinsa , little ma sosai ya zage
yaji abincinsa ganin yadda big boss yake shan coffee ya tabbata yana gama sha zaici
abincin ko kad’an ne , hakan kuwa a kayi Belgian waffles kawai yayi cutting kad’an
ya soma ci kamar bayasan taunawa, a nutse yake cin abincin hankali kwance ,
had’ad’d’iyar wayarsa da ta ‘kara Haske alamar kira na uku kenan Sabida yadda take
haske tun d’azu cikin silent amma mamallakin wayar ko gefen inda take be kalla ba ,
wayar bobo ce ta soma ringing , ganin wanda yake kiran sa ne yasa ya kalli big boss
yana sakin wani dan iskan murmushi har Wayan yayi cutting a karo na biyu da aka
‘kara kiransa sai da ta kuşa tsinkewa ne yayi picking , banji me aka ce masa ba sai
“okay “ da bobo yace yana nufar big boss da phone din hannunsa , tun kafin ya
karasa big boss ya dakatar dashi da narkakkun eyes dinsa , a hankali ya zari tissue
ya goge bakinsa , phone dinsa kawai ya d’auka ya nufi hanyar fita, sai da Suka ga
fitarsa alokacin prince suka saki ajiyar zuciya , murmushi bobo Kawai ya saki daman
yasan za’arina ba kowa ne yake kiran big boss ba face president danshi big boss
idan rashin mutumcin sa yana kuşa baya ragowa kowa , mayar da wayar sa kunne bobo
yayi shima yana bun bayan big boss da ya fita sai a lokacin prince ya Samu damar
tanbayar uncle abunda yake san tanbaya “ uncle Menene ma’anar Bubububu d’innan da
kake yawan fad’awa yaya and naga duk lokacin da ka fad’a Ransa sai ya baci”, a
jiyar zuciya uncle ya saki yana kallan prince da little da suke jiran amsarsa “
it’s a long time Name! Labarine da ayanxu bakwa bukatar sani har sai lokacin da
yayi niyyar kusani”. Amma uncle please kadena fad’a masa to tunda ransa zai ‘baci
ni bana jin dad’i Allah , shima fa yaya bobo ranshi ya ‘baci amma yake ‘boye “
murmushi me Sauti uncle ya saki batare da ya basa amsa ba suka canza hirarsu zuwa
wata davan.

***********
****************
*WASHINGTON*
Abunda ya faru tun lokacin da Alice taji labarin dawowar big boss ta tayarwa da her
excellency hankali a kan tanaso ta gansa ko kuma ita ta hau jirgi ta koma New York
a yau d’innan , babu yadda her excellency batayi ba itama amma ta tubure har bara
zana tasoma yi wa mahaifiyar tata akan zata kashe kanta idan ba ayi mata yadda
take so ba , shiyasa kai tsaye her excellency ta kira his excellency, sosai
hankalinsa ya Tashi sabida furucin da Alice tayi , da kansa ya d’auki phone ya
kira number big amma ba’a picking, sai da yajera masa calls har uku amma babu Wanda
big boss ya d’auka shiyasa president ya mayar da called din zuwa bobo amma duk da
haka ko uffan be ce musu ba , Alice da ke tsaye a kansa sosai ta kara dubur burce
musu har da d’auko wata knife din fruit akan idan bataji muryar saba zata kashe
kanta , da ‘kyar suka lallashe ta akan zasu je New York suyi 2 week sabida ita , da
wannan dalilin suka shawo kanta da kyar, Alice kuwa sabida murna ko ta kan iyayenta
bata sake bi ba ta nufi d’akin ta kamar wata zautacciya ta dunga burkita gabaki
d’aya kadan da ko hour 1 ba’ai da gyara su ba , duk da haka gabaki d’aya kayan basu
yi mata ba shiyasa ta fara shirin shopping din kayan da zatayi amfani dasu a New
York dan acewarta sai ta auri big boss zata dawo Washington tare dashi, su rayu su
biyunsu babu takurawa. Alice gabaki d’aya soyayyar big boss ta rufe mata ido
shiyasa kome yayi yake burgeta take karajin soyayyarsa cikin ranta .

✨✨✨✨✨✨✨

KANO

9:20pm zaune Eshaal take cikin d’akinta tana duba books dinta duk da basu koma
school ba amma hakan ya sabar mata jiki lokaci zuwa lokaci tana ‘kara bitar karatun
makarantarta dan sosai take da ‘ko’kari duk da baby itama ba kauwan lasa bace wajan
karatu amma rabi da kwata wasa ta saka a gaba , a ya tsine baby ta kalleta tana
bin books din ta da kallo “ munafuka wai ke me kokari sai muga uban da za a nuna
mana, idan kinga dama kizo dady na kiranki idan kin ga dama kuma ki zauna kinga
tafiya ta,” ta karasa tana ja mata tsoki, saida zuciyar Eshaal ya buga lokacin da
baby tace mata dady na kiransu tasan tabbas ba alkairi bane may be sunje sun had’a
ta fad’a dashi kamar yadda suka saba ne , da Sauri ta d’auki hijab dinta ta d’ora
kan kayan baccin jikinta kar baby ta ‘kara kad’ar lefin da bata aikata ba , aikuwa
tana shigowa falon da sallama kallan da momy da dad suka soma binta da shine yasa
tasha jinin jikinta, a ra’be ta zauna a ‘kasa tana kallan mahaifinta da ko kusa
bayaso ya kalli face dinta kamar zatayi kuka ta furta “ Dady gani” a zujiye dad ya
kalleta cikin ‘kyama “ saunawa zan fad’a miki idan na Kara Jin kallan dad dinnan a
bakinki sai na farfasa miki baki, kije kısa mu wani uban dai naki amma ba ni ba ,
ni yata d’aya na sani a duniya kuma ita ce baby” sosai baby taji dadin maganar dad
shiyasa ta kyal’kyale da dariya , hawayen da Suke ‘ko’karin zubomata Eshaal tayi
saurin had’iye kayanta “ muna fuka ba , gabaki d’aya Zubin uwarta ne da ita to
Menene baza tayi va ? Shegiya da wani hasken ta sai kace ungulu, Allah yasa ba wani
‘katan kike bawa jikin kiba sabida ni gabaki d’aya ban yadda dake ba , “ fashewa da
kuka kawai Eshaal tayi dan ta rasa bakın magana sabida irin cin mutumcin da momy
suke mata a kullum a guje ta koma d’akinta ko taka kıran da Dady yake mata bata
juyo ba sabida kukan da taji yazo mata , babu Wanda ya damu da reaction din
Eshaal suka ci gaba da hirarsu.

*****************
🍃🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

ABUJA
Har ‘karfe shida lokacin da Abla ta dawo babu Wanda ya tanka mata ko yace mata
wani abu, abun mamaki yau ko mutanan da ake tarawa gabaki d’ayansu uwar karuwai ta
sallamesu sabida plan din da binta ta had’a daman tun asali ba zuwa tayi dan tayi
bariki kawai ba , asalin abunda ya kawota ta samu yarinyar da zata siyar ta samu
manyan makudan kudi , shine dalilin zuwan ta gidan uwar karuwai, shiyasa tun
lokacin da taga Abla tasan ba ‘kananan kudi zata samu ba idan ta tafi da ita ,
binta shagala irin mutanan nanne masu shegen gaggawa da sun samu wata dama burinsu
kawai suyi abun cikin kankanin lokaci karya wuce su shiyasa tun lokacin da ta ga
Abla zuciyar ta soma kwad’ai tuwar tayi abunda zatayi cikin kankanin lokaci . Yadda
Abla taga su zinariya na binta da kallo duk inda ta motsane yasa zuciyata wası wası
ga wani bugawa da taji zuciyarta na mata lokaci guda , tana shiga cikin d’akin ta
tarar da Husna zaune akan katifa hannunta d’auke da dan’kareriyar iPhone tana
latsawa, tana ganin Abla ta ta’be bakinta , hanyar toilet ta nufa Allah ya temaketa
bata shiga cikin toilet dinba sukaci karo da Arwa Itama zata fito Daga toilet,
ajiyar zuciya Abla ta saki , itama Arwa murmushi ta sakar mata tana bata hanya “
Abla sannu da zuwa “, kanta Kawai Abla ta d’aga masa Sabida sarawa da kanta yake
mata , ga ciwan mara da take ji kad’an kad’an daman hakan ce ke faruwa da ita duk
lokacin da zata sake wani period din sai ta dad’e tana ciwan mara kafun Jini ya zo
mata shiyasa komai a hankali take yinsa yau, alwalar sallahr magrib tayi tana
fitowa ta tarar da Abla a tsaye tana jiran ta, a tare suka kabbara sallar su
lokacin har husna ta bar musu d’akin , ganin kamar damuwa tattare da arwan yasa
Abla tanbayarta “ meke damunki ne arwa naga duk damuwa tattare da ke ?” Ajiyar
zuciya Arwa ta saki “ Abla Nima bansan me ke damu na ba , haka kawai yau naji
zuciya ta na bugawa kamar wani abu na shirin faruwa da mu , a duk lokacin da zuciya
tayi irin wannan bugawar sai naga abunda nake ji kamar zai zama gaskiya , kamar ana
shirin rabamu ne “, murmushin ya’ke Abla ta sakar mata , itama tun safe take jin
bugun zuciyarta ya canza amma bata yadda da hakan ba ta kawar da zancan “ karki
damu Arwa insha Allah babu abunda zai same mu kinji? Ki dunga addua aduk lokacin da
zuciyarki ta buga miki ko ta raya miki wani abun, ba lallene ya zama gaskiya ba
kinji?” Insha Allah Abla , gabaki d’aya hira kadan suka ta’ba a tsakaninsu sabida
yadda kowa baya cikin mood dinsa kowa da abunda yake sa’kawa, har zasu kwanta
zinariya. Tashigo d’akin tana kallan Arwa a yatsıne “ ba’anan zaki kwana ba , a
d’aya store din zaki kwana sabida akwai masu kwana a d’akin, da Sauri Arwa ta kalli
Abla, itama Ablan batace mata komai ba sai d’aga mata kanta da tayi kad’an , jiki a
sanyaye Arwa ta bar dakin , itama Abla tajimatana jiran ganin wa’yanda zasu shigo
amma har wajan 10 babu Wanda ya shigo d’akin , sosai hakan ya bata mamaki ga tsoron
data faraji dad’inta d’aya ma akwai hasken fitila, tun tana jira taga ko su Anee
zasu shigo ko Arwa har bacci ya fara fusgarta, amma duk da hakan bata kwantaba sai
da bacci yaci karfinta.

2:00am wasu ba’ka’ken motoci suka shigo layin gidan uwar karuwai sabida ganin a
lokacin ne kowa yake runtsa wa , wasu ba’kya’kyan maza ne a cikin motar ko wannansu
fuskarsa a rufe take ga wata shegiyar binduga datake hannunsu , d’aya daga cikin su
ne yayi dialing wata number , ringing biyu aka d’auka kamar daman jiran kiran ake ,
cikin hausarsa da bata fitowa alamar ba cikakken bahaushe bane ya furta “ madam we
Dey here ooo”, banji me aka ce masa ba sai kalmar “ shikenan muna jiranki yanxu “,
ya karasa yana kashe kiran wayar .
Su Binta shagala ne tsaye a falo da ita dasu uwar karuwai, wannan karan harda
su zinariyya da yaran binta shagala rike da bag d’inta , plan din yadda zasu shiga
ciki suke tattauna har yanxu , mutane hudu binta shagala ta nuna, debeka ,
Zinariyya , yar shila sai wata yarinyar ta guda d’aya , a hankali suka had’a group
din yadda zasu shiga cikin falourn , saida suka gama tsare tsarensu tukunna suka
nufi hanyar d’akin da Abla take , Aushe wannan ne dalilin da yasa aka raba musu
wajan kwana ita da Arwa sannan aka hana kowa kwana da ita . Allah sarki Arwa tunda
ta shiga store din da aka mayar da ita ta kasa zaune ta kasa tsaye haka kawai ta
kasa samun natsuwar zuciya , ga baki d’aya bacci ya ‘kaurace mata , da ta zauna
zatayi Tunani babu abunda yake fad’o mata cikin zuciya sai tunanin Ablanta. Motsin
da taji tun d’azu ne yasa ta saka kanta wajan kofa ko zata ji meke faruwa , ganin
bata jin komai ne har zata hakura zuciyarta ta kasa ha’kura da hakan , Daidai
lokacin da su uwar karuwai suka nufi d’akin da Abla take , sosai tsoro ya kama Arwa
ganinsu da yawa cikin sand’a tabi bayansu gudun karsu ganta .
Allah sarki lokacin da suka shiga cikin d’akin bacci me d’an nauyine ya
d’auke Abla shiyasa ko motsin bud’e ’kofar da akai bataji ba sai d’an motsawa da
tayi kad’an, powder din hannun ta binta shagala ta bud’e tana faman sakin wani
shegen murmushin mugunta, dukda karfinsa haka ta zubasa a hannuta, tana nunawa su
zinariyya su rike mata Abla , d’an ta’bata da yarinyar binta tayi ne yasa Abla
farka wa , yadda ta gansu a kantane yasa ta ware manya manya eyes d’inta akan su
muryarta har rawa yake wajan furta “ me.. me zakuyi mun?… me .. kuke shirin yi”da
Sauri suka fara kici niyar ri’keta amma tana kwace hannunta, Ance sarkin yawa yafi
sarkin karfi gabaki d’ayansu sai da Suka jigatu amma duk da hakan basu riketan da
suke soba shiyasa binta shagala ta shaka mata powder din hannunta da yasata sakin
azababbiyar ‘kara Daidai lokacin da Arwa tazo bakin kofar dakin, ihun Abla da
tajine yasa tayi saurin bud’e d’akin gabaki d’aya binta suka soma binta da kallo
cikin Tashin hankali, itama hakance ta kasance da ita cikin tashin hankali take
bunsu da Kallo kafun ta d’ora eyes dinta kan Abla da fuskarta tayi mugunja ga kanta
da take faman duka , kamar mahaukaciya ta d’ago da eyes dinta muryarta kamar zata
shid’e da kyar take iya bude baki “ ki.. gudu.. zasu kasheki… ki gudu” Abla ta
karasa a zabure sabida yadda suka shaka mata powder din me shegen yaji, cikin
tsananin Tashin hankali binta shagala tasaka su zinariyya su kama Arwa , da Sauri
Arwa ta soma ja baya tana girgiza kai , bazata iya tafiya ta bar Abla a cikin
wannan yanayin ba , amma yadda taga Abla tafice daga cikin hanyacinta ne ya kara
tsoratata gadan gadan su zinariya sukayi kanta , itama da Sauri ta bude kofar fita
ta saka gudu ko kallan gabanta batayi waya binta shagala tayi wa mutanan dazu akan
su kamo Arwa, Allah ya temaketa sai data fata wuce su tukunna suka ankara da ita da
gudu suka biyota amma babu damar suyi harbi sabida kar asamu matsala , gudu sosai
Arwa take ko kallan gabanta batayi haka suma kattın mazan nan suke binta abaya , da
iya karfinta take gudu kafarta ko takalmi babu duk ya fashe sabida lungun da ta ke
shiga , tana gudu tana wai wayan mazan da suke binta a baya bata san lokacin da ta
fito babban titi ba Adaidai lokacin da wasu manyan ba’ka’ken mota kusan guda 7 suka
shararo kantitin driver da yake driving din motar baisan lokacin da Arwa ta shigo
gabansa ba shiyasa be aune ba yabi ta kanta saida tayi sama kafin ta fad’o kasa
babu alamar rai tattare da ita , lokacin da karatan nan suka ga abunda ya faru
shiyasa suka dakata tare da kiran binta shagala suka shaida mata yarinyar da suka
bi ta mutu, suna barin wajan driver da yake tu’ki yayi saurin Jan burki hakan ya
bawa ragowar motocin Jan burki suma , da Sauri y karasa wata mota dake bayansa ya
shaida musu abunda ke faruwa , wata katuwar sojece da take driving mota ta biyu
tayi saurin fitowa ta d’auki Arwa tasaka ta cikin motar su ka bar layin gabaki
d’aya.
Allah sarki Abla gabaki d’aya tafi ce daga hayyacin sai faman zabura take
lokacin da binta shagala take fad’awa uwar karuwai mutuwan Arwa wani irin zaburowa
da Abla tayi saida ta firgita su, yadda ta sha’ke Wuyan binta sai ya raza mutum , a
haukace take furta “ sai na kasheku, sai na kashe ku kamar yadda kuka kashe mun
ita,sai na kasheku…” bata karasa ba Sabida kwalbar da zinariya ta buga mata akai da
Sauri abla ta dafe da take ganin yadda ta fara ganin su dishi dishi, cikin rawar
jiki da muryar ta furta “ nayi muku alkawari wannan shine kisa mafi muni da zaku
karayi a rayuwarku idan har ina raye sai kunyi mutuwa irin mutuwar da Baku tava
tsammani, sai na zama sanadiyyar rugujewar gabaki d’aya farin cikin ku wannan
alkawari ne na d’auka “, tana kaiwa ‘karshe ta zube kasa ita ma babu alamar rai a
tattare da ita, cikin zufa uwar karuwai ta kalli binta dan ita duk hatsabibancinta
bata Kai binta ba , kamar yadda tayi hasashe binta ko a jikinta sai ma gaggawar
d’aukar Alba da tasa akai tana kallan uwar karuwai “ sai kinji alert “ kanta kawai
uwar karuwai ta d’aga dan so take su bar wajan kafun wani ya ankara yasan abunda ke
faruwa. A wulakance suka jefa Abla cikin boot din motar tare da kulle mata bakinta
da d’aure mata hannayenta ta yadda bazata iya motsawa ba koda ta farka , suma su
binta suka shige motar tare da barin layin gabaki d’aya.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃

GERMANY

Zaune Fanan take kan kujerar falourn su tana game , shigowar BiiBii ne yasa ta ajje
game din tana kallansa “ welcome back home !” Thank you dear , cewar Sauban yana
nufar hanyar d’akinsa , Fanan bata bisa ba Sabida tasan yana bukatar yin wanka ya
huta sai da ta shafe good 1 hour kafun ta nufi dinning cikin babban tray d’in sa
da ta shirya masa abinci ta d’auka ta nufi d’akinsa, saida tayi knocking ya bata
izinin shigowa sannan ta shiga cikin d’akin yana zaune kan sofa jikinsa sanye da
wasu kayan alamar yayi wanka , akan center ta ajje masa abincin tare da serving
dinsa , bece mata komai ba har ta kammala , da bismilla ya soma jin abincin sa
saida yaci ya koshi sosai yana furta Alhmdllh sai a lokacin ya furta “ ina mamy?”,
cikin zolaya itama Fanan ta bashi amsa “ kai yaya sai yanxu zaka tanbayeni ina mamy
sai da ka gama cin abinci ka koshi “, d’an hararar ta shima Sauban yayi “ tashi
kifitar mun daga d’aki tunda rashin kunya zaki mun”, da Sauri ta furta “ Haba
yayana nakaina, Haba bestyn besties ! Kayi hakuri mana “, girgiza kansa kawai
Sauban yayi “ ba kyajin magana”, Haba ya’ya Nidai ba wannan ba, mamy bacci take
yanxu shiyasa nazo a bani labarin besty ko kuma a bani labarin me dadi “, harararta
yayi yana janyo phone dinsa daga aljihu da “ ko d’aya babu Wanda zan baki , ina
ruwanki da maganar besty kuma ? Sa idanki ya fara yawa yanxu fa ? Wai Yaushe zaki
koma school ?” Sakin bakı Fanan tayi tana kallansa “ yaya Sauban ka gaji da ganina
a cikin gida kenan? Shiyasa kake tanbayar yaushe zan koma ? Bakomai bari mamy ta
tashi gobe zan koma Nigeria gidan ABBU,” ta karasa tana mikewa zata kwashi
kayanta , “ kafun a haifeki aka haifeni, ni zaki cuta wai ?oya nasan akwai abunda
ya kawo ki , me kike bukata ?”, keya Fanan ta d’an sosa ganin lokaci d’aya ya
ranfota “ dama fa yaya kayan makeup nida ne suka kare shiyasa and kaga banasan
tanbayar mamy tunda kananan “ da Sauri ya katseta ta hanyar furta “ tunda nine bank
cirar kudin ki ko?” Haba mana yaya , daga mamy sai kai fa kukai mun saura tun bayar
mutuwar Abba”, ta karasa a sanyaye shima lokaci d’aya mutuwar mahaifinsu ya shiga
cikin zuciyarsa “ya isa haka ! Don’t worry I will send you the money , okay”
yesss ! Cewar fanan tana daka tsalle daman abunda ya kawo ta wajan sa kenan shiysa
ta tattara kwanukan da yaci abinci ta fice cikin Sauri “ Allah ya shiryeki fanan “,
sai kuma ya lumshe idanuwansa kamar yana san Tuna wani abu , a hankali ya furta “
it’s all about time “, laptop dinsa dake gefensa ya kunna ya soma yin wasu mahimman
aiki da yake bukatar karasawa .

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂
NEW YORK
Bobo yana fitowa daga cikin building din ya tarar da ba big boss a harabar wajan ,
ga position da sojoji suka canza alamar fitowarsa, yasan bazai same sa ko ina ba
sai a wajan da ya fi zama wato wajan flowers , ga kamshin kasa me dadi
da take tasowa , a maimakon ya nufi inda su prince suke zuwa sai ya nufi wani side
din daban , tun daga Wajan zaka fara gani kyawawan flowers , side din hagunsa,
kamar yadda ya sanı wajan gabaki d’aya sojoji ne kewaye a Wajan amma babu me Gigi
ko zarran d’ago da kansa ya kallesa , yana zaune kan wani farin white chair,
fuskarsa a hade babu fara’a sai simba dake gefen sa shima a zaune irin zaman da
zakuna suke, sallama bobo yayi lokacin dayake tunkarosa duk da Beji ya amsa masa ba
amma yana da tabbacin ya amsa masa , Big boss kuwa yana zaune ko motsawa beyi ba
daga yanayinsa dukda yaji shigowar bobo, fuskarsa a had’e sosai yana sha’kar
daddad’an iskar wajan flowers din da tafi wacce su prince suke shiga kyau da
haduwa, yadda tsarin wajan yake shi kansa abun kallo ne, kujerar Next to him bobo
ya zauna, har lokacin big boss be d’ago ya kallesa ba ko nuna alamar akwai mutum a
wajan ba , hakan gabaki d’aya be damu bobo ba dan idan akwai Wanda xai baka labarin
halin big boss a bayansa yake “ ze shigo New York for a meeting da yakeso ayi about
yarannan da kasa Team Alpha su kama” cewar bobo yana bin fuskar big boss da kallo,
big boss be ce masa komai ba ya sharesa tsawan 2 minutes kafun ya furta “ and so?”,
murmushi bobo ya sakar masa “ suna so Kaje meeting d’in”, d’an ta’be maki kad’an
big boss yayi da ya ‘kara masa bai sake tankawa bobo ba kuma bashi da alamar tanka
masa , a hankali yayi sauke legs dinsa tare da zubawa bobo eyes dinsa masu shegen
rikitarwa “ I don’t care ! Abunda na sani daga jibi bana bukatar jin labarin su sai
a prison , if not….huh..” ya karasa yana d’agewa bobo gira d’aya , a ynxu ma
murmushi bobo ya saki da har jerarrun hakwaransa saida suka fito “ ka dena bina da
wannan eyes din naka mana , kasan suna tsoratani “, da hannu d’aya big boss ya nufa
masa hanyar da zata fitar dashi , cikin cool voice ya furta “ get lost kafun na
‘bata maka rai”, me kake shirin yi? Cewar bobo, wani irin fito da bakowa ya iya
yinsa ba big boss ya saki take a wajan simba yayi mugun razana tare da sakin kuka
me ban tsoro, kan kujerar da bobo yake ya nufa a hankali bobo ya Tashi tsaye be
auneba simba ya kawo masa hari, hari ba na wasa ba amma be fito da fara tansaba,shi
kuma bobo yana karewa cikin zafin nama ganin yanda yanayin simba yake , yanayin da
a iya lokacin fad’a yake ganinsa haka , sosai suka kacame da fad’a da ya fad’ar da
simba zai kara razana ya kawo ma bobo hari , big boss na zaune yana kallan yadda
suke fad’a bana wasa ba , amma ko uffan be ce ba almost 30 minutes suna abu d’aya ,
bobo bayasan jiwa simba rauni shiyasa tun d’azu baya attacking dinsa sai kare
jikinsa da yake , ganin sımba bazai ta’ba barin saba Indai ba big boss ne ya hana
saba yasa ya d’aga hannu ya buga masa a kai, shima simba zafin da yajine yasa yasa
duka kafarsa ya hankad’a bobo da yayi taga taga zai fad’i big boss ya rikosa da
zafin nama sai da yaga ya kusa kai wa karshe sai kuma big boss ya sake sa ya fad’i
’kasa , da Sauri simba ya karasa inda bobo yake a kwance shima ya kwanta , cikin
d’aga murya bobo ya furta “ wallahi baka da mutumci big boss a times” , add 1 word
and regret my decision” cewar big boss dariya bobo ya saki yana mikewa tsaye bayan
ya shafa kan simba “ me yayi saura kuma idan ba gidan zoo daka sani ba?” Shiru big
boss yayi masa dan doguwar maganar da yayi har ya fara saka masa ciwan kai ba kadan
va, yadda yayi shiru yana lumshe ido yasa bobo fahimtar yanayinsa , shiyasa bobo be
kuma ce masa komai ba ya zauna a side dinsa, haka suka share more than 30 minutes
babu Wanda ya kuma yin magana a cikinsu.
1:30 suka nufi cikin gida a tare , tunda ya fito sojoji suke sara masa cikin
girmamawa shida bobo amma cikin su babu Wanda ya d’aga eyes dinsa ya kallesa ,
Indai big boss na waje kada ka kuskura kayi motsin da zaisa ya d’ago da eyes dinsa,
sosai kowana soja yake jin shakkarsa bakadan ba amma dukda haka suna mugun Sonyin
aiki a karkashinsa.sabida dukda rashin fara’a da yake dashi Hakan be hana ya kyauta
ta musu dan ba karamin kudi yake kashe musu va, amma ko a fuska basu da wannan
damar da zasu gode masa saidai suyita a cikin zuciyar su. A Daidai lokacin da suka
shiga cikin falourn a Daidai lokacin little da prince suka jefo pillows din da suke
wasa dashi gabaki d’aya tunaninsu sun d’auka yaya big boss baya gida, azabure
little da prince suka ja baya lokacin da suka ga big boss da bobo a tsaye suna
binsu da wani irin kallo, da Sauri little da prince suka tsugunna tare da hade
hannunsu waje d’aya “ yaya please…”, basu karasa ba Sabida wani banzan kallo da big
boss ya jefa musu take a Wajan ko wannansu ya hadiye maganar sa , be tanka musu ba
sannan kalli side din da suke ba yayi wucewarsa, saida Suka ga yabar wajan tukunna
cikin sauri suka karaso wajan bobo” yaya bobo please we’re sorry , yanxu yaya zai
samu punishment plx we’re sorry ka bashi hakuri “, kunnu Wansu ya ri’ke tare da
murdawa har saida suka furta ouch kafin ya sakesu “ bakwajin magana saunawa na
hanaku wasa da pillows haka ? Look yadda suka yaddar da pillows ta ko ina “, we’re
sorry plx yaya “, hannunsa bobo ya daga “ dont sorry me ! Gwanda ya hukuntaku, tun
barınshi gida kuka tsuro da saban iskanci gwanda yayi maganinku ko zaku shiga
taitayinku”, yaya..” cewar little , hararar sa bobo yayi tare da daga both hands
dinsa “ 10 minute kuje kuyi alwala”yana kai karshen maganarsa ya wuce part d’insa ,
kallan juna prince da little sukai “ yaya prince we’re in big mess wlh yaya sai ya
hukunta mu shurun da yayi mana ba a banza ba , ko muje wajan uncle ?” Hararar sa
prince yayi “ kasan muka fad’a masa lefun mu zai gani kuma yaya bobo ya hanamu ,
lokaci na tafiya muje muyi alwala wallhi yaya big boss ya fito bamuyi ba wani karin
punishment din ne”, da Sauri suka bar wajan ko mintuna 7 basuyi ba suka fito falo
suka tsaya suna jiran fitowarsu, uncle ne ya fara fitowa ganin yadda suka sunkuyar
da kansune yasa ya kallesu, tun kafun yayi magana bobo shima ya fito bayan yayi
alwala, kamar wasu muna fukai suka ki dago da idanuwansu, after 5 minutes kamshin
turaransa ya cika hancinsu alamar fitowarsa shiysa suka kara shiga taitayinsu,
gabaki d’ayansu masallaci suka har aka idar da sallar prince da little basu firta
ko kalma d’aya ba , sun d’auka yaya big boss ya hakura amma kalmar field da yace
musu ya tayar musu da hankali , kamar zasuyi kuka suka kalli bobo da ya hararesu
yabi bayan big boss , zasu kalli uncle shima yayi saurin daga hannunsa sama “ babu
ruwana karku jamun”, gabaki d’ayansu bin bayan su big boss sukai little har ya soma
hawaye tunkafun a hukun tasu. Babban filine me shegen girma kana kallan Wajan kasan
wajan horon sojojine musamman Wanda yake hukuntawa, abubuwane da yawa a Wajan Wanda
duk Wanda akai aka hukuntawa a wajan sai yayi kwanaki yana jinya dan bakaramin
kayan mugunta bane a wajn Daidai wani dan karamin wasane da yake daban da sauran ga
ga jikarkiyar kasa da take wajan ko taba da yawanci idan za’ayi wa sojoji training
harda irin shi suke shiga , sojojin da suke gadin wajan suna ganin me gayya me aiki
da kansa yasan suka kara shiga taitayinsu dansu kansu da suke gadin Wajan bazasu so
a hukunta suba , sau d’aya ya kallesu ya dauke kansa ganin little dinsa na kuka ,
ga ta’bon da dan tuku kadan dukda ba wani tudune dashi ba amma yana da tsaho kadan,
yana kallansu sukayi saurin kulle eyes Dinsu suna juyawa , da ido ya kalli bobo, da
yayi knodding kansa , wani ring bobo ya jefa cikin ta’ban batare da ya kallesu ba
ya furta “ swim and found the ring”. Kamar zasuyi kuka suka cire takalmansu tare da
shiga cikin ta’ban da zasuyi swimming …..

( jama’a daman ana swimming cikin ta’bo?”…..

KO TAYA ZA’A NEMO ZOBE CIKIN TA’BO?🤣


PAY YOUR 300 into 2681892316 , Aisha umar zenith bank sai a turo shedar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

BANYARDA WANI KO WATA YA JUYAMUN LITTAFI TA KO WANA SIGABA , KO A SAKA MUN SHI A
YOUTUBE BATARE DA IZININA BA, DUK WANDA YAYI GIGIN YIN HAKAN SHIDA ALLAH WALLAHI😒.

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
S____16💞
Yadda suka shiga cikin ta’bon sai sun baka tausayi gabaki d’aya kayansu ya baci da
ta’bo gabaki d’ayansu,sai faman dubawa suke ko zasuga zoben amma kamar allura ya
‘bace ba’a ganinsa , big boss na tsaye hannayensa cikin aljihun wandansa fuskarsa
ba fara’a kwata kwata balantana suyi gigin basa hakuri, bobo ma dauke kansa yayi
akansu , yasan tunda big boss yasasu punishment dinnan babu me tsayar Dashi koda
kuwa uncle ne , bawai Kawai akan wasa da pillows din da sukai bane yake punishing
Dinsu yasan duk abunda suke cikin gidan duk da baya kasar hatta partyn da suka fita
bare da izinin kowa ba yana sane dasu gabaki d’ayansu, sosai zasu baka tausayi idan
Kagansu cikin ta’bon da hatta bakin gashin kansu da yake shan gyara ya fara baci da
ta’bon duk iya kokarin su da zasuyi sun kasa ganin zoben, uncle ma sosai tausayinsu
ya kamasa amma ko kusa yasan bazai fara bawa big boss hakuri ba dan yana basa zai
kara nunkamusu wani punishment din. Yadda ya zuba eyes dinsa akansu ko a jikinsa
zaka d’auka hakan be damunsa a zahiri amma cikin zuciyar sa ba karamin zafin hakan
yake ji ba , little har ya soma kuka shima prince kwalla ya fara dan har ga Allah
ya gaji da yawo cikin ta’bon gashi har ynxu basu ga zoban ba kusan 30 minutes ,
yadda little yake kuka ne yasa big boss binsa da narkakkun eyes dinsa lokaci d’aya
ya had’iye kukan da yake , sai da suka shafe hour guda da kyar suka samu ring din,
dan ba karamin jigatuwa sukai ba , little har ya soma layi, a tunaninsu shikenan
sai wani waje da suka ga big boss ya nufa wajan yana da tsahon da shape shape dinsa
kamar na circle haka yake duk Wanda yashiga wajan abun zai jashi tundaga sama har
kasa ruwa na masa feshi ta ko ina , yanxu ma kamar zasu yi kuka suka shiga wajan ,
yadda abun yajasu yana musu feshin ruwa sai sun baka tausayi gabaki d’aya ruwan ya
wanke musu dattin tabon jikinsu sau uku suna yin hakan , dauke kansa bobo yayi
gabaki d’aya daga kallansu yasan idan ya cigaba da kallansu zai iya kashe engine .
Sunzo karshen wajan da yake cike da ruwa kadan da balloons big boss ya kashe engine
gabaki dayansu sai suka kife cikin ruwan suna faman sakin haki da ajiyar zuciya ,
cikin kuka little ya furta “ yaya we’re sorry please! We’re sorry ! Shima prince
abunda yake furtawa kenan dan yasan wallahi big boss yace xai kara hukuntasu saidai
a daukesa a sume dan ba karamin hajijiya yaji kansa nayi masa ba . Cikin
kausashshiyar murya big boss ya furta “ come out”, da Sauri suka fito jikin su har
ya soma rawa Sabida sanyin da suke ji, yadda yaga sun kasa tsayuwane yafi komai
ta’ba masa zuciya amma a zahiri idan ka kalli fuskarsa sai ka dauka be damu da
hukuncin da ya sasu ba , ko wannansu ya sunkuyar da kai kwanin tausayi, “ we’re
sorry yaya cewar prince “, shima abunda little ya kuma maimaita wa kenan “ we’re
sorry”, har yanxu kafarsu ta kasa tsayuwa ji suke any moment zasu iya faduwa kasa ,
sarai big boss yana sane da conditions Dinsu amma yayi burus dasu sai ma juyawa da
yayi ya bar Wajan, da Sauri little da prince suka rungume yaya bobo cikin kuka
little ya furta “ nifa yaya bobo bazan iya tafiya ba nagaji,” dungure masa Kai bobo
yayi “ ni kake so na Goya ka ?Abeg let’s go ko kuma na kirasa , da Sauri suka raba
jikinsu,little harda turo baki, “ sorry little din mu kunsan dama idan ya dawo dole
sai ya wukuntaku, ku gode Allah ma punishment biyu ya baku, nasan kun gaji , kuyi
wanka kuci abinci “, kansu suka daga su kamar wasu Salihai basu kuma cewa komai ba
suka soma tafiya , gabaki d’aya sai suka basu tausayi musamman yadda suka sunkuyar
da kansu kasa , suna shiga part Dinsu baya cikin falourn shiyasa kai tsaye suka
nufi dakinsu, little da prince suna shiga daki gabaki d’aya zubewa sukai a kasa “
wallahi nagaji yaya prince “, shiru prince yayi masa danshi gabaki d’aya ya kasa
magana dan jikinsa har ya soma yi masa ciwo ganin lokaci na tafiya ga kayan jikinsu
da suke ajike yasa sukai wanka tare da canza wasu Kayan kamar basune jikinsu ya
Gama baci ba , yanxu ma kowa kan gadonsa ya kwanta babu me magana a jikinsu, lokaci
d’aya suka zabura sunsan idan suka ki zuwa cin abinci shima zasu gamu da big boss
shiyasa suka saka haf slipper Dinsu suka sakko kasa , uncle da bobo ne kawai a
falon kasan, hatta bobo ya canza kaya Sabida rungumesa dasu little sukai suka jika
masa jiki, yadda yaga suna nayi ne yasa ya kallesu da kyau “ what’s wrong with
you?” Kai a sunkuye suka furta babu komai yaya “ okay let’s eat” , ynxu ma basuyi
musu ba suka nufi dinning kansu a sunkuye, ga baki d’aya sai ka dauka babu mutane
wajan dinning Sabida yadda su james suka kame kamar basu da rai a tattare dasu,
Koda su James sukazo suka fara serving Dinsu gabaki d’aya babu wanda ya iya cin
abincin sabida big boss be sakko ba , “ sir James ka had’amun tray xai kaiwa yaya
abinci” cewar little , “ No little yaya yana wani abu, allowed him first ,
okay ?”cewar bobo , shima little amsa ya bashi da “ okay” a sanyaye ya soma cin
abincin kadan kadan , gabaki d’aya bobo yana Ankara da yanayinsa , yadda Prince
yaga little ya shiga so moody na rashin fitowar big boss shima sai hakan ya damesa
gabaki d’aya sai yaji abincin ya fita ransa sai tusawa kawai yake badan yana
Marmarin cıva , suna kammala cin abincin akai kiran sallar la’asar , yanxu bobo ne
ya sasu a gaba suka tafi masallaci , sai daf da za’a tayar da sallar big boss ya
shigo masallacin, ya canza kaya ba kayan dazu ne a jikinsa ba yanzu sanye yake
cikin ba ‘kaken kayan kanfanin Dolce , Riga da wando , sai kayan suka haska masa
fatar jikinsa , ga bakin gashin kansa da yasha gyara a tufke sai daukar ido yake
gabaki d’aya sai ya zama wani tauraro sabida yadda kullum yake kara kyau amma
fuskarsa har yanxu babu fara’a , gabaki d’aya sai kamshin turaransa ya rufe gabaki
d’aya kamshin turaran masallacin duk da yadda ake kunna musu freshener amma ba
kadan ba kamshin turaran sa ya rufe ko ina , yadda ya saka bakaken kayan sai suka
kara fito da kyawun fuskarsa sosai, duk cikin masallacin babu me zarrar kallan big
boss ko da wasa , shiyasa shuke kiyaye ko wana irin abu da zai jawo hankalinsa
wajan . Ana idar da sallar ya fito daga masallacin lokacin da wasu irin manya
manyan combo cars ne jere a wajan bakake Kirin dasu guda uku black colour sai ta
tsakiyarsu dark ash colour Audi Rs me shegen kyau da idan baka zuba idanuwanka
sosai ba sai ka dauka black ce , yadda motocin suke kyalli sai ya baka sha’awa ga
manya manya American soldier da suke sanye da suit black colour , daka bayan
ratsatstiyar motar nan wasu combo cars din ne guda uku a bayanta, Daidai saitin
inda ash colour din take wasu manyan maza ne guda biyu a wajan idanuwansu sanye da
bakin glass gabaki d’aya a cikin mutanan sune suka fita da ban , tunda ya tun karo
wajan soldiers din suka hade kafafuwansu tare da saita bindugunsu cikin azama wani
farin soja ya bude masa mota, sai da ya tabbatar big boss ya shiga da kusan mintuna
5 kafun kowa ya shiga cikin motar, cikin slow speed motocin suka soma fita daga
cikin gidan kafun su karawa motocin su gudu. Koda su Prince suka fito basu tarar da
big boss ba shiyasa suka nufi cikin gida , shima bobo be kara 30 minutes ba ya bar
gidan, sai gidan yayi musu so lonely ganin babu yaya bobo babu yaya big boss a ciki
musamman yadda little ya damu se shima prince ya damu sosai, uncle ne me tausarsu
kawai.
*******
**********
ABLA
Tunda suka saka ta cikin boot bata iya ko kwakkwaran motsi sabida yadda gabaki
d’aya ta fice cikin hankalinta , a lokacin duk wanda ya santa ya kalleta sai ya
razana musamman yadda face dinta tayi jajawur da ita cikin a zaba take iya shakar
nunfashin da take ji kamar yana barazanar d’aukewa daga kirjinta gabaki d’aya , ko
kwakkwaran motsi ta kasa sai hawaye da suke bin gefen fuskarsa , cikin zuciyar ta
babu abunda take iya ambato sai “ Ya Allah! Ya Allah “, batasan inda suke biba
Sabida yadda bata gane komai bayan kiran sunan Allah da take cikin zuciyar. Su
binta shagala kuwa suna cikin mota burin ta na gab da cika sosai suke sharara gudu
musamman da suka san dare yayi babu motoci sosai shiyasa suke sharara uban gudu
kamar basa kaunar ransu , cikin wata doguwar kwana da zaiyi maka nuni da daji suka
yanka har suka bar abuja wayan nan mutanan basu dena sharara gudu ba , har gari ya
waye suna tafiya a hanya sai wajan karfe goma suka tsaya suka siya Mai a galan
gudun kar a ganesu suka cika tanki sannan kowa yayi abunda zaiyi na mintuna goma
bayan abincin da suka siya ko takan abla dake boot basabi , anfi karfin a wannai
ana tafiya daga lokacin da suka baro gidan karuwai zuwa yanxu sunyi kusan 9 hours
suna tafiya musamman short cut din da suka dungayi ko tsoro basaji sai da suka
karayin good 4 hours kafun su bi ta wani daji, abun mamaki daga inda suke suna iya
hango border din Cameroon shiyasa suka bi ta hanyar daji gudun kar asamu matsala a
hanya , ta cikin dajin suka shiga cikin Cameroon Batare da kowa ya bincikesu ba ,
yanxu ma sai da Suka dade suna tafiya a hanya kafun su shiga cikin garin yaounde
cikin wani layi da yawanci ba’a fiya zama a cikin layin ba , motar da Abla take
ciki aka shigar cikin gidan sannan binta ta bawa yan matanta umarnin su shigar da
Abla ciki, haka suka d’auketa kamar wata gawa sukai cikin gidan da ita , ko motsi
Abla batayi kamar wata gawa.
A waje kuwa wasu makudan kudi Binta shagala ta d’auko ta damkawa mutanan suna
karba basu jira ba suka tashi motocinsu suka bar wajan, already tun acikin mota ta
canza sim dinta, wata number takira kai tsaye bugu uku aka daga phone, cikin zakuwa
ta furta “ yanxu muka karaso cameeroon, zuwa gobe sai a turo motar da zata dauketa
sabida idanuwan mutane” bansan me aka ce mata ba sai knodding kanta da ta sakeyi “
toh ina jiran kudina kunsan bana wasa dashi”, Kitt ta kashe wayar tare da bin
sahun su Abla. Cikin wani daki aka jefa Abla da ko motsi batayi suka kulleta, a
hankali ta ware eyes dinta da Sukayi mugun ja tana bin kofar da kallo bayan
idanuwanta batajın zata iya motsa jikinta, ta gefen side dinta har yanxu hawayene
suke sakko mata, Shikenan baxata sake ganin Arwa ba? Sun kashe mata ita? A duniya
babu wanda ya tava daukarta a matsayin ahalinta sai matar da zata iya kira
mahaifiyarta ko ba koma a Wajanta ta taso sai Arwa da yanxu suka Rabata da ita ,
sun cuci rayuwarta, sun sa mata dafin da bazai taba goguwa ba a cikin ranta, me
yayi saura? Me yayi saura yanxu ? Babu , sun ruguza mata komai na rayuwarta gabaki
d’aya tsoro ko halin da zata shiga a yanxu ya fice daga ranta , zuciyarta ta bushe
bata tsoron kome ze sake Samunta, tasan Allah yana sane da halin da suke
ciki,shiyasan gaibu sannan ya fita sanin komai game da rayuwar ta , “ La’ilaha
illah Anta subhanaka inni kuntum minazzalimin, Ya Allah , ya Allah , wa’u fauwidhu
amree ilallah , innallaha baseerun bil ibad, ya Allah” shine kadai abunda Abla take
nanatawa cikin ranta .
Tunda suka sata cikin dakin babu Wanda yazo ya duba halin da take ciki ko ya
damu da sanin wani irin hali take ciki. Tayi kusan 1 hour kwance a yadda suka barta
kafun cikin ikon Allah ta samu ta iya motsa hannayenta har tayi yunkurin tashi
zaune , jirin da tafine ysa tayi saurin jingina jikinta da jikin bango, idanuwanta
a bushe babu ko digon hawaye a kan fuskarta , zuciyarta ta bushe ta yadda ko
hawayen batajin zata iya sai kukan zuci, kukan Zucin da Allah ne kadai yasan yadda
take jin cikin ranta , haryanxu nunfashinta be gama saituwa ba musamman jirin da ta
fiji dan ba karamin Shaka mata sukai ba har yanxu bata gama dawowa Daidai ba lokaci
zuwa lokaci sai ta dunga zabura ko ta dunga dukan kanta kamar me kokarin zare wa .
Karfe 5:30 pm aka bude kofar dakin da Abla take ciki, binta shagala ce ta
shigo cikin wasu yan iskan kaya hannun ta dauke da ruwa da kuma bread , tun kafin
ta karaso inda Abla take ta soma furta “ da alama yunwa kikeji baby, ga bread nan
da ruwa shiyafi dacewa dake amma karki damu ina samun biyan bukatata yau zansa a
had’a miki babban liyafa yau kinji baby “ ta karasa tana kokarin shafar fuskar Abla
, duk da babu wani karfi a jikinta hakan be hana Abla shako wuyan binta shagala ba
da har sai da ta saki kara da karfin gaske Abla ta damke gashin attached din da
tayi , dukda yadda take jin ta ba kwari hakan ta daddage ta ware hannunta ta
tsunkawa binta shagala mari me zafin gaske dama da hagu, ihu binta ta soma akan a
zo a temaketa alba zata kashe ta , lokacin kuwa ba kowa a cikin gidan dan ta aikeso
daga ita sai Abla da take kokarin Birkicewa gani take damace Allah ya bata sabida
kashe mata Arwa da sukayi shiyasa ta daddage ta kara tsinkawa binta mari, sai faman
kururuwa da neman agaji take akan Abla zata kashe ta ga zafin zamlar kırsan
attachment d’inta da Alba tayi mata ga zafin Mari da Abla ta tsinka mata , dukda
haka abla bata hakura ba ta daddage ta kwara kan binta a kasa sai ji kake kasssss
sabida buguwar da yayi , iya jigatuwa binta ta jugatu duk da jikin da take dashi ta
kasa kwatar kanta a hannun abla ita kanta bata san lokacin da kukan azaba ya kwace
mata ba , ita kuka Abla kuka , “ yadda kuka kashe ta Nima sai na kashe ku ba ku
cancanci rayuwa ba , mugaye azzalumai Allah bazai barkuba “ ido arufe Abla take ta
faman surutai , binta kuwa da taji ba sarki sai Allah sai ta soma bawa Abla hakuri
gabaki d’aya sai d’akin ya kacame da kukansu, lokacin da Abla ta kara gwara kan
binta da bango a lokacin yan matan ta suka shigo d’akin da Sauri d’aya daga cikinsu
ta nufi Abla gadan gadan, yadda zuciya ta zowa Abla har wuya bata san lokacin da ta
sauke mata na ta kasan marin ba da iya karfinta da yasa sai da ta fadi, d’ayar ma
Gadan gadan tabi kan Abla , itama Abla cafko kanta tayi ta buga da bango ga layin
da take amma duk da haka bata kyalesu ba , d’aya bayan daya ta dunga bi tana tsunka
musu mari, tun tanayin abu kamar a mafarki Abla sai ta koma kamar wata zararriya
da bin hakki take marinsu, babu abunda suke sai faman bata hakuri da suke akan ta
kyalesu amma ina Abla bata san ma sunayi ba burinta kawai ta nakasa yan iska.sai da
abla ta faffasa musu baki kafun su samu su kwaci kansu hatta binta shagala sai
janta yaranta sukai Sabida sumewar da tayi suna janta da kyar suna tsinewa Abla
dan ba karamin jibguwa sukai ba.suna fita ta sulale a kasa ta kwanta, ba kuka take
ba amma yadda kirjinta yake sama kamar zai fito sai ya baka tausayi dan hatta
nunfashin dakyar take iya janyoshi.

*****
********A Abuja kuwa uwar karuwai bata sanar dasu Aneesa abunda yasamu su Abla ba
duk da yau haka kurin Aneesa ta tashi da kewarsu, tanaso ta bawa Abla hakuri akan
abubuwan da suka faru dan rashin ganin su da batayi ba sai taji duk ba dadi, Husna
na dukda ba shiri take da Abla ba rashin ganinta sai ya tsaya mata a rai amma bata
jima ba ta share zancansu taji gaba da sabgarta, ilham kam daman ko a jikinta ji
tayi duniya tayi mata sabuwa sabida rashin su Abla ba karamin dadin hakan taji ba.

🍃🍃🍃🍃🍃🍃

NEW YORK
Karfe 11:00 pm na dare gabaki d’aya sojojin da suke duty suna yin aikinsu ko
wannansu da shigar sojoji a jikinsa , gabaki d’aya gidan zagaye yake da katin katin
sojoji masu Jini a jika , kowa ka kalla fuskarsa zaka ga babu murmushi ko annashuwa
akan fuskarsa sabida yadda fuskar kowa take a had’e , first gate da aka bude ne ya
karasa gabaki d’aya sojojin shiga taitayinsu, har aka bude gate na biyu zuwa babban
gate din gidan , lokaci d’aya motocin bobo suka shigo gidan wajan karfe 11:20pm,
tsadajjan agogon hannun sa ya kalla ganin yadda lokaci ya ja , babu Wanda ya fad’o
masa arai kamar little yasan yanxu haka ya damu musamman rashin dawowar big boss
duk da ba saban abu bane, iskar bakinsa ya fitar kad’an lokacin da Robert ya bude
masa kofa, be bata lokaci ba kai tsaye ya nufi cikin gida yau ko tsayawa wajan su
Bruno beyi ba , yana shiga kamar yadda yayi tsammani suna zaune akan kujera little
har yayi bacci a zaune ga prince shima da yake gyangyadin amma ko wannansu ya ki
zuwa ya kwanta , shima uncle be shiga daki ba yana zaune hannunsa dauke da jaridar
da yake karantawa , kallan little da prince bobo yayi kafun ya girgiza kansa, “
uncle” cewar bobo , murmushi uncle ya sakar masa “ thank god ka dawo yanxu , look
at them gabaki d’aya sun ki zuwa su kwanta , especially little da yake jiran
dawowar yayansa “, shima murmushi bobo ya saki “ uncle kai ma kasani rigimar little
sai big boss ai, dare yayi yanxu be kamata suna bacci akan chairs ba” yana kai
karshen maganarsa ya sabi prince dashima ya soma bacci kamar bayajin nauyinsa haka
ya nufi part Dinsu dashi, sai da ya kaishi daki da kansa sannan ya tashesa ya canza
kayansa zuwa na bacci sannan ya gyara masa blanket dinsa sabida yadda d’akinsu ya
dauki sanyin Ac. Down stairs ya dawo har lokacin little na bacci shima d’aukarsa
bobo yayi kamar wani karamin yaro ya kaishi d’aki , be tashe saba sabida already
shi ya zansa kayansa , shima gyara masa kwanciya bobo yayi yana shafa lallausan
bakın gashin kan little , tsawan 30 seconds yana kallan face dinsa kafun ya saki
murmushi akan fuskarsa yana kashe musu light zuwa dum .
Uncle ma ya nufi part d’insa shiyasa bobo yana fitowa kai tsaye part din sa
ya nufa yayi wanka ,cikin kayan baccin Hanes yayi dressing dark blue , gyaran
gashin kansa yayi gyarasa duk da kasancewar dare ne , Daidai bakin window din dakin
ya tsaya yana jin yadda daddadar ni’imar Allah yake kadawa , sosai iskar tayi masa
dad’i shiyasa ya tsaya a wajan. Durar motar da yajine yasa ya mayar da kallansa
zuwa gate , kamar yadda yayi hasashe motocin big boss ne suka shigo cikin gidan a
jere Daidai building Dinsu motocin sukai parking shiyasa bega fitowar sa har ya
shige cikin gidan , watches din dakin ya kalla already yanxu past 12 yasan kuma big
boss beci komai ba shiysa ya saka half sleeper dinsa ya bar dakin sa.
Big boss kuwa yana shigowa ciki ko dago da eyes dinsa beyi ba balantana
yasan da mutane a cikin falourn ko babu, yadda falourn yayi shirune yasashi lumshe
kyawawan eyes dinsa , kai tsaye be zauna a falourn ba ya wuce part din sa
directly . Yadda yaga ko ina a gyarane ya bashi tabbacin su little sun shigo d’akin
. Hakan ne kuwa ya kasan ce bayan wata plasma da big boss ya kunna take a wajan
videon su little ya bayyana lokacin da suke gyara masa dakin amma idan ka kalli
fuskar little zakaga gabaki d’aya babu fara’a ko walwala akan face dinsa , lumshe
ido big boss yayi tare da ta’ba lallausan gashin kansa da ya tufke , phone din
hannunsa Kawai ya ajje kan center kafin ya shiga wata kofa dake cikin dakin. Almost
30 minutes big boss yana ciki be fito ba sai da aka kara 5 minutes kafun a turo
kofar , daddadan kamshin turaransa ya Kara cika dadin tun kafun ya Fito, a hankali
yake taka kafarsa me sanye da farin takalmin web slides , yadda takalmin yake fari
sai ya fito da dogayen yan yatsun kafarsa masu shegen kyau, sanye yake cikin kayan
bancin flannel dark ash , sosai kayan sukai masa kyau , kyakkyawar sumar kansa a
wannan karan ta zubo masa har bayansa sabida yadda ya sake ta , kyawun fuskarsa
sosai ya Kara fitowa kamar kullum kyawunsa kara kyau yake , amma gabaki d’aya face
dinsa ba fara’a ko sakin fuska , a d’aure take tamau ,hakan kuma be sa kyawun
fuskarsa guduwa ba sai ma kara wani sahir taccen kyau da yayi , a hankali yake
motsa red lips dinsa kwanin burgewa ga eyes dinsa shima da duk lokacin da yayi
motsi dasu sai dogayen eyes lashes din idan sa motsawa , yadda fuskarsa take a hade
hakan be hana kyawun tsagar gidansa guduwa ga diamon bracelet dinsa guda biyu da
haryanxu suke hannunsa , hatta sarkar diamond dinsa dake wuyansa sai faman kyalli
take . Phone dinsa kawai ya dauka ya bar dakin Daidai floor 2 akwai Wani waje da
ya’ke d’auke da wasu fararan kujeru nashan iska , yadda iska take kada wajan
shiyafi komai burgewa , daga inda mutum yake yana iya hango duk abunda ke faruwa a
cikin gidan sosai , idan bakasan glass din ya kare maka iska sosai yaka iya danna
bottun wajan ya bud’e , akan d’an table din ya ajje phone dinsa , hannunsa gabaki
d’aya a cikin aljihu yana kallan yadda weather din Garin yake ga stars da suka fito
sosai shiyafi komai kawata wajan , “ Assalamu alaikum” cewar bobo yana karasowa
Inda big boss yake , a hankali ya motsa lips dinsa da ko shi bobo bai ji muryar
saba amma sanin cewa ya amsa din ne yasa bece masa komai ba “ can I ?” Cewar bobo
yana kara tanbayarsa bayan medium tray din da ya ajje saman center , bansa big boss
yayi masa tun bayan amsa sallamar da yayi be kara motsawa daga inda yake ba ,
kananan cups din da ke cikin tray bobo ya dauka tare da zuba coffee din da ya hada
da kansa , cikin cups biyu , inda big boss yake a tsaye ya nufa tare da mika masa
cup din , kamar bazai karba ba dan ko kallan inda bobo yake be ba sai da ya dauki
30 seconds sannan ya saka hannunsa d’aya ya dauka tare da lumshe masa idanuwansa.
Suna tsaye a wajan babu Wanda yayi magana a cikin su musamman big boss da yake
shipping coffee dinsa a hankali kamar ya manta da wanzuwar bobo a Wajan, “ His
excellency gobe zai shigo cikin New York with his family and nasan suna bukatar
magana da kai akan yarancan”, cewar bobo yana kallan big boss , red lips dinsa big
boss ya tabe kadan batare da yace komai ba tsawan good 5 minutes , bobo har ya cire
ran zai basa amsa sai kuma yaji saukar muryarsa “ who are they ?”, cewar big boss ,
tsayawa kallansa bobo yayi wai who are they shi be ma sansuba, “ don’t start it
please “ cewar bobo, sexy eyes dinsa big boss ya dago yana bin fuskar bobo da kallo
na yen seconds cikin izza da ta zamar masa jiki ya furta “ daka gobe bana bukatar
jin magana akansu,”dan maganar nan da yayi sai da ya tsaya yan kusan 1 minutes
kafun ya furta “ idan na kara jin maganar wannan case din , huh zan dawo da case
din hannu na”, yana kai karshen zancansa ya bar Wajan suka kan chair din Wajan ,
cikin dan zaro ido bobo ya kallesa yasan idan har ya kar’bi case din sai yayi wa
yaran mugun illa da bazasu kara mo ruwa ba , tunda ya furta zuwa gobe ai musu
hukunci toh tabbas zuwa goben za’ayi musu, yasan wanene big boss farin sani , wani
lokaci Dan rigima ne shi sosai , shima kan chair din ya samu ya zauna kafun ya
fuskanci big boss sosai “ nasan Nicholas yana wajan ka ?” , dan tsaki big boss yaja
yana dauke kansa zuwa kan wayarsa , doguwar maganar nan da yayi har ya soma jin
kansa na dan sara masa , wasu dan danne dannensa yayi cikin waya kafun ya jefa wa
bobo wayar da yayi saurin cafkewa, da Sauri kuma ya dago da eyes dinsa yana big
boss da kallo kafun ya mayar cikin wayar , ba kowa bane face Nicholas, Dylan sai
logan a sakale gabaki d’aya an ratayesu kowanne fuskarsa a kunbure , gabaki
d’ayansu ko wannansu a tattale musu kafa daga su sai gajeran wanduna a jikinsu sai
kuka suke suna bada hakuri, a hankali big boss ya furta “Do you think zaka fitar da
wasu daga cikin gidan nan sabida karna gansu? Just one word ko wannansu za’a yanke
abunda yake iskanci dashi”, yadda bobo ya gansu ba karamin dariya suka bashi ba
kamar wayanda ake shirin yiwa kaciya ko wannansu ya fice daga cikin hanya cinsa ,
abu d’aya zai iya musu zuwa gobe a hukuntasu idan ba haka ba yadda aka tattale musu
kafarnan ba makawa big boss nacewa go on zasu yayyankewa yan iska gaba , ba VC ba
ko president ba zai tanka masa ba ko ya tanbayesa why? Dan duk Wanda yasan big boss
yasan zafin ransa, samun saukin mutum yabi tsarinsa.
“ yah nasan zaka gano inda suke but yayi wuri sabida baka dade da dawowa
ba” kallansa big boss yayi for seconds ya dauke kansa tare da saka slice pine apple
a bakinsa , yadda yake taunawa kamar Wanda aka saka dole dan a hankali yake
taunarsa kamar bazai cinye ba , be karabi ta kan bobo ba sai kallan yadda weather
ta karayin duhu yayi, maida kallansa yayi kan watches din hannunsa yaga har 1 ta
wuce “ ka kunna musu heater Sabida jikinsu”, cewar big boss yana mikewa tsaye ,
shima bobo mikewa tsayan yayi yabi bayan big boss da ya soma tafiya kai tsaye
d’akinsu little suka nufa yadda suka ga kowannansu a tattakure ne yasa suka bisu da
kallo, heater din dakin bobo ya kunna ya kashe musu Ac, tare da dakko wani man zafi
guda biyu ya mikawa big boss d’aya , a hankali big boss ya bude magani tare da
sakawa little dinsa a kafarsa, a hankali yake matsa masa kafar cike da kwarewa ,
shima bobo hakan ce ta kasance , prince yake shafawa a kafar sai da suka tabbatar
man ya shigesu sannan suka ajiye, gashin kan little big boss ya ta’ba Daidai
lokacin da little ya rike hannunsa cikin bacci, a hankali yake furta “ am sorry
yaya big boss , am sorry yaya bobo”, duk cikin magagin bacci yake furtawa , “ kansa
big boss ya shafa kawai yana lumshe eyes dinsa da hakan ya zamar masa tamkar a
jininsa tare da gyara masa kwanciyar sa sosai , kafun su bar dakin sai da ya kara
tabbatar da lapiyar bugun zuciyar little sannan suka kashe musu light, a bangaran
uncle ma lokacin da suka shiga d’akinsa yayi bacci shiyasa bobo ya rage masa sanyin
Acn dakin . Big boss na tsaye a falon hannunsa sanye cikin aljihu haka bobo kamar
yadda yasaba kullum saida ya tabbatar da lapiyar komai na gidan kafun ya dawo cikin
falon har lokacin big boss na tsaye ko gajiya da tsayuwar bayayi , sai da yaga
shigowar bobo sannan ya juya zai bar Wajan , cike da tsokana bobo yayi saurin
karaso wa inna yake “daga ganina kuma sai kajuya ? Hira fa zaka zo muyi “, big boss
bai tanka masa ba sai hannun sa d’aya daya daga ya kaiwa bobo naushi, cikin azama
bobo ya kauce yana dariya “ba’a banza ba little ya iya mugunta ba fa” cewar bobo
yana kashe wa big boss ido d’aya alallai sai ya nemi rigima dashi , dauke eyes
dinsa big boss yayi tare da soma takawa zuwa elevator har ynxu bobo na biye dashi ,
sai da ya shiga ciki tukunna lokacin da bobo yazo shiga big boss ya hanka dashi
baya ya kulle bayan wani irin kallo da ya jefa wa bobo , har yanxu bobo dariya
yake masa musamman yadda yaga ya hade rai . Gabaki d’aya light din ya kashe ya bar
dum tukunna ya koma part d’insa , ba jima ba ya kwanta shima .
Big boss kuwa yana komawa part d’insa system dinsa ya janyo ya soma
operating dinta cikin kwarewa kamar ba dare ba Sabida yadda ko damuwa da ya kwanta
ba yayi , ya dau tsawan lokaci yana operating akan system din nan sai wajan karfe 4
ya kashe system din , still be kwanta ba sai da ya kara komawa part din su little
wannan karan har dakin bobo ya shiga , duk da yadda bobo ya girma hakan be hana big
boss gyara masa blanket ba kamar yadda ya sabayi masa, sai da ya tabbatar shima
he’s okay tukunna ya koma part dinsa. Daidai Wajan balchony ya tsaya yana shakar
daddadar kamshin wajan ko damuwa da yadda dare yake karayi bayayi ga sojoji da
suke yawo ta ko ina . Yana tsaya akai kiran sallar Asuba , saida aka gama kiran
salla ya bar wajan , cikin kankanin lokacin ya kara Shiryawa cikin wasu cotton kaya
farare tas dasu , yau gashin kansa a nannad’e be tufkeba, ga kamshin turaransa ta
ko ina da ya kama dakin. Tun kafun ya sakko down stairs prince da little suka fito
falo, yau sun ruga kowa tashi daga bacci dan wallahi big boss ya Riga su fitowa
suma sun san sauran shiyasa duk lokacin da yake gida suka saka alarm, Allah ya
temakesu tun 6pm na yamma jiya prince ya saka musu alarm , uncle da bobo ma kusan
lokaci d’aya suka fito suna jiran fitowar big boss. Saida suka kara kusan 10
minutes tsaye a wajan tukunna ya fito gabaki d’ayansu suka nufi masallaci dakaga
fuskar little zai baka tausayi Sabida canjin face dinsa yau ko fara’a bayayi so
yake yaya ya kulasa amma gabaki d’aya babu Wanda ya kula a cikinsu har suka tafi
masallacin.
🍃🍃🍃🍃🍃
ABLA
Da ido ta fara bin dakin da kallo tana Tuna’nın ta yadda za’ai tayi sallah, batasan
ya zatayi ba tunda ko kwakkwaran motsi bata iyayi da gabbanta, sun cutar da iya iya
cutawa da bazata ta’ba yafe musu ba , da’kyar ta iya jan jikinta ta jingina da
bango tana lumshe eyes dinsa da hawaye suke sakko mata , yunwa take ji ba kadan ba
tun safe bata saka komai a cikin taba gashi har yamma tayi bata ci komai , jinta
take kamar ‘ya’yan cikin ta zasu fito waje , tunanin yadda zatayi sallah kawai take
cikin ranta da tayi kokarin mikewa zataji jiri na neman kayar da ita , bata da wani
zabi face tayi niyya cikin zuciyarta ta rama sallolinta. Sai wajan karfe 8 aka kara
bude kofar dakin da take , wannan karan ba a shigo ciki ba sai ledar bread da aka
jefo mata tare da pure water guda d’aya aka sake kulle ta , dukda tsananin yunwar
da take ji ko kallan inda bread din yake batayi ba ta kara silalewa a kasa ta
kwanta cikinta har wani yaji yaji yake mata na yunwa , a haka wani irin wahalallan
bacci ya d’auke ta . Binta shagala kuwa daga waje ta bada umarnin ajefawa Abla
bread da ruwa dan bil hakki lokaci d’aya taya taji wani irin tsoran Abla ya shigar
mata zuciya babu abunda yafi tsoratarda itama kar ace Abla tana da aljanu dan dukan
da Abla tayi mata har yanxu bata dena shakkar tava , gani take Aljanun Abla ne suka
tashi shiyasa bata kara tun karan ko inda dakin yake ba .

PAY YOUR 300 into dis Account 2681892316 Aisha umar, zenith bank.
Sai a tura shardar biya ta wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now * IBTISSAM*.

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
S____17💞
Karfe 10 : 30 na dare wani irin azababben yunwa ya tayar da Abla daga baccin
wahalar da ya d’i beta , Sabida yadda takejin yayan cikin ta kamar zasu tar watse
sabida yunwa ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai , ganin da wuta a d’akin yasa
cikin birgima ta Soma lalubar bread da ruwan da aka jefo mata , kamar zata fita
daga cikin hayyacinta haka ta dauki bread dinnan ta dunga turawa cikin bakinta ,
sai da taga tana kokarin kwarewa ne yasa ta Soma ci a hankali amma duk da haka
cikin Sauri sauri take tuttusa bread din da take ji ko ma’kogwaranta baya kai
mata , gabaki d’aya sai da ta cinye guntun bread din da aka jefomata , a haka kuma
ta sha pure water da take ji kwata kwata be ishetaba sai ma tasar mata da wani
saban kishir ruwan da yayi amma ba yadda zatayi Haka tayi zamanta, sai alokacin ta
soma jin karfin jikinta kadan a tattare da ita , gabaki d’aya abunda ya faru dazu
ne ya soma dawo mata cikin kwakwalwarta, lokaci d’aya ta fashe da wani saban kuka ,
cikin shash shekar kuka take furta “ shikenan Arwa, shikenan yanxu kin mutu kin
tafi kin barni?” Ita kadai take faman surutunta ga kuka tanayi lokaci d’aya, wani
abun ma gabaki d’aya ita kanta bata san me take cewa ba dan kamar wacce ta fice
daga cikin hayyacinta haka Abla ta dawo , bata dauki dogon mintuna 7 ba a wajan
nunfashinta ya soma fisgewa , da kyar take iya jansa sabida yadda kirjinta yake
mata zafi, take a Wajan ta fadi jikinta ya saki bata ko motsi.

4:00am Daidai aka bude d’akin , sai alokacin binta Shagala ta shigo cikin
dakin amma tana daga baya baya ta tura yaranta gaba gaba , suma duk Wanda ka kalla
fuskarsa zaka alamar tsorata a tattare dashi, d’aya daga cikin yan matan da ta
shigo da ruwa a hannunta ta mikawa d’ayar, kafun ta karba sai data daidaici kofar
fita kafun ta watsawa Abla ruwan. Lokaci d’aya Abla ta ware idanuwanta da ya ‘kara
firgita su sun d’auka har yanxu Aljanun da suke cewa tana Dashine suka kara tashi.
Gabaki d’ayansu zabura sukai lokaci d’aya suka bar d’akin, da kallo kawai take
binsu ganin lokaci d’aya sun firgita . Ko mintuna biyu ba’a ‘karaba kuma suka kara
dawowa cikin dakin, a wannan karan su 5 ne ragowar mata guda biyun ko wannansun
sanye yake cikin ba’ka’ken kaya fuskokinsu a rufe , batare da wani tsoro ko shakkar
yadda Abla take kallansu ba suka fara nufota, Abla bata soma jan jikin taba sai
lokacin da taga d’aya daga cikin matar ta dakko wata allura cikin jakarta, da Sauri
Abla ta soma jijjiga mata kai, gashi bata da karfin da zata gudu ko ta ce zata
gudun ma babu hanyar guduwa , da karfi d’aya daga cikin matan da suka kulle face
Dinsu ta janyo Abla tare da Matse mata ma’kogaro kamar zasu cire shi d’ayar kuma ta
dauki Allurar da ta fito da ita batare da ta duba jijiya ko wani waje da ya kamata
ayi wa Abla allura ba ta buga mata ita a kafadarta. Zafin da Abla taji ne yasa ta
ware muryarta da tayi mata saura ta saki wani irin azababbiyar kara Sabida yadda
taji allurar na shiga cikin jikinta , lokaci d’aya zafi da kaikayi ya rufeta, ji
take kamar ana ‘kona mata naman jikinta, cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta fice daga
cikin hayyacinta sai faman shure shure take sabida yadda take jin allurar cikin
jikinta. Su binta shagala gabaki d’aya basu damu da yadda Suka ga Abla ta koma ba
sai ma hanya da ta basu lokacin da suka ja Abla a kasa kamar wata kayan wanki,
kanta na buguwa haka suka dinga janta har zuwa wata bakar mota da suka shigo da
ita, haka suka jefata cikin voot suka tayar da motar tare da barin layin, Abla na
cikin mota gabaki d’aya sai taji komai na jikinta ya tsaya bayan idanuwanta da take
iya motsawa babu wani abu na jikinta da take iya d’aga wa , cikin wata bakar jaka
yan matan nan da suka kulle face Dinsu suka mikawa Binta shagala kudaden da Suke
ciki, cikin Sauri kuwa ta amshesu tana boyewa cikin rigarta, motar da aka saka Abla
ko minti biyu cikakku basuyi ba suka tada motar a guje tare da barin area din
gabaki d’aya .
🍂🍂🍂🍂
🍃🍃🍃🍃🍃🍃

Koda aka idar da sallar asuba babu Wanda ya ‘bata lokaci tsakanin prince da
little , cikin kankanin lokaci ko wannansu ya shirya cikin sport dinsa na
training , musamman yadda suka ga big boss be shigo cikin gida ba , hakan ya basu
tabbacin ko minti d’aya suka kara zasu gamu dashi . In ka kalli face din little yau
zaka ga gabaki d’aya babu walwala a tattare dashi, daga big boss har bobo suna sane
da halin da yake ciki, shi bobo yayi masa shirune sabida big boss yayi masa
magana , big boss kuma izza da miskilanci ya hana ya kulasa. Cikin Sauri gabaki
d’aya suka shirya tare da fitowa , cikin kankanin lokaci suka nufi wajan training,
Wanda suka ganine yasa suka sha jinin jikinsu ganin sa a tsaye yayi folding
hannayensa , zasu soma magana ya zuba musu rikitattun eyes dinsa da yasa ko
wannansu yin shiru . Hatta sojojin da suke cikin wajan kowa cikin kwarewa yake
motsa jikinsa dan idan tsautsayi yasaka kayi mistake babu ruwan big boss wai kai
sojane, sawa zaiyi a rataye masa kai na 2 hours shiyasa ba karamun mugun shakkarsa
suke ba . Cikin sunkuyar da kai suka nufi main dakin da suke motsa jiki, suna shiga
Suka tarar da ba kowa a ciki shiyasa wani irin dadi ya kamasu , prince harda buga
tsalle ganin bobo baya ciki yasan da wuya shima big boss ya shigo shiyasa ko
wannansu ya d’auko abun motsa jiki mara sa wahala . Shi little da yafi kowa ma wani
mat na training ya shinfida tare da daukar babbar balloon da ake motsa jiki da
ita , prince Kuma skipping rope ya dauka shima , a tunaninsu big boss bazai shigo
ciki bane shiyasa suka d’auki ‘kananan abubuwan nan ,prince yana cikin skipping
dinsa juyawar da zaiyi kawai idanuwansa ya sauka kan big boss da yaya bobo dake
gefensa, shi kansa besan lokacin da ya kusa hantsulawa ba , da Sauri ya yardar da I
giyar shi little gabaki d’aya be kula da yanayin da Prince yake ciki ba sabida
kulle eyes dinsa da yayi , kallan da big boss yake bunsu Dashi kadai ma yasa hantar
cikin sa kad’awa , da Sauri prince ya ta’ba little , shima yana bud’e eyes dinsa
yayi saurin mikewa tsaye , cikin rawar murya ya furta “ yaya please kuyi hakuri
kunji?” Ya karasa da niyar matsowa inda bobo yake sabida yadda yake tsoran Kallan
side din big boss , shima bobo kallan da ya jefa wa little ne ya hanashi motsawa
daga inda yake , big boss be ce muku komai ba sai juyawa da yayi ya bar wajan,
shima bobo kallo d’aya yayi musu kafun ya furta “ follow me” yaya please ka bashi
hakuri , we’re sorry “ cewar prince , amaimakon bobo ya bashi amsa sai ma cikin
kakkausar murya ya furta “ 2 minutes kawai na baku” yana kai karshen zancansa ya
juya yabi bayan big boss , cikin rud’ewa prince ya fara furta Innalillahi wa inna
ilaihi raji’un , little please ka bawa yaya big boss hakuri please” shima little
kamar zaiyi kuka ya furta “ fushi yake dani fa, ni tsoro nake ji” bai karasa
maganar da zaiyi ba shida prince suka bar dakin a guje sabida minti biyun da bobo
ya basu har yayi . Kamar yadda suka sani wajan horan sojojin da suka je jiya zasu
nufa , shiyasa kai tsaye cikin ‘kan’kanin lokaci suka karasa wajan , yaya big boss
baya wajan shiyasa gabaki d’aya suka saki ajiyar zuciya duk da kasan zuciyar su
fall tsoran hukuncinsa suke ji, inda bobo yake a tsaye wani waje ne me kamar
tiles ,yadda Wajan yake kyalli zai tabbatar maka da abun santsi sojoji Suka zubawa
a Wajan , kallan kallo prince da little sukai kamar zasuyi kuka dan sun gane me
zasuyi shiyasa tun kafun bobo yace su cire takalmansu Suka ciresu tare da tsayawa a
Daidai sai tin wajan , wasu sojoji guda biyu Suka karaso Inda suke tare da wani
fork a hannu saida suka rike fork din sosai kafun sojojin su saka musu kwai a kai ,
duk abunda yake faruwa bobo na kallansu bayasan ganin yadda face Dinsu take ,
shiyasa yadan daure face dinsa kadan “ you can start , duk Wanda ya fadi a cikinsu
zai fara daga farko , duk Wanda egg din fork dinsa ya fadi zai gane kurensa , you
can start “, cewar bobo, prince yana saka kafarsa a wajan yaji yana kokarin
sullu’bewa, da Sauri ya ja baya da yasa egg dinsa fashewa,” ^2” cewar bobo, shima
little yana shiga yaji yana kokarin faduwa , saura kadan ya fadi shima amma Allah
ya temakesa, saida yazo Daidai tsakiya ya su bale kwansa ya fadi, kamar zasuyi kuka
haka ya kara dawowa farko , shima prince da yayi nisa santsi yake d’ebarsu suke
faduwa , sunfi 20 minutes suna abu d’aya amma sun kasa karasa zuwa inda zasu ajje
kwan, akan idan bobo duk abunda yake faruwa , gwanda shi yayi musu hukunci akan big
boss yayi musu , idan ba hakaba ba karamun jigatasu zaiyi ba , yadda santsi yake
kayar dasu ba karamun dariya da tausayi zasu baka ba , hatta little cikin faduwar
da yayi saida ya Bige hannunsa amma ya ki bari bobo yagani shiyasa ya cigaba , ga
zafi da hannunsa yake masa amma hakan ya cigaba da shiga cikin santsin yana fad’uwa
, tun yana kokarin dannewa har ya soma hawaye , , shikansa bobo da yake kallansu
ba dadin abin ya ke jiba , a ka’ida punishment 4 zaimusu amma ba xai iya ba shiyasa
ya dakatar dasu ya bar wajan , Allah sarki little yadda fuskarsa tayi jajawur ba
karamin tausayi zai baka ba , dakyar suka taka Suka koma cikin part Dinsu , babu
kowa a cikin falourn kai tsaye d’akinsu suka shiga sukai wanka , shi prince sabida
yadda ya gaji kai tsaye lapiyar gado yabi, little kuwa kasa kwanciya yayi Sabida
tunanin yayansa da ya’ke shiyasa ya nufi part d’insa , ko da yashiga kasa tun karar
dakin big boss yayi shiyasa ya kwanta akan sofa a takure , yasan bazai fito yanxu
ba Sabida yanxu ne lokacin baccinsa , shiyasa shima yayi kwanciyarsa kan sofa , sai
da ya dau kusan 20minutes kafun wani irin wahalallan bacci ya daukesa. Tun lokacin
da ya shigo big boss ya gansa , amma miskilanci da izza ta big boss ta hana yace ya
shigo d’akin, tsawan wannan lokacin yana zaune kan sopa yayi crossing legs dinsa ,
tun lokacin da little yake kwance kan sofa da yadda ya takura har yayi bacci duk a
kan idan big boss , lokaci zuwa lokaci yana lumshe kyawawan idanuwansa sabida yadda
yaji kansa yana sara masa , saida ya ‘kara d’aukar 10 minutes zaune a wajan tukunna
ya mike ya nufi palourn da little yake a kwance, gabaki d’aya eyes dinsa ya zuba
masa yana bin kyakkyawar face dinsa da tayi ja kadan da kallo, a hankali ya soma
takawa har ya karaso inda yake a wance , hannunsa da yasa cikin aljihu ya fitowa
dasu tare da daukar little kamar Wanda ya dauki wani jariri ya nufi d’akinsa dashi,
akan lallausan king size bed dinsa ya kwantar da little tare da d’auko wani unique
roba d’an ‘karami, hannun little dayaga ya d’anyi ja ya shafawa a hankali gudun
karya tashesa daga baccin da yake yi , saida ya tabbatar maganin yayi masa yadda
yakeso kafun ya ja masa Duvet dinsa sosai sabida yadda sanyin Ac ya karad’e ko
ina . Ya jima zaune a inda little yake yana bin kyakkyawar innocent face dinsa da
kallo , lokaci zuwa lokaci kuma yana lumshe idanuwansa da suka fara canza launi
kad’an, idan mutum ya kallesa yaga yadda yake lumshe idanuwa sai ya dauka wani
izzar ya’ke kara nunawa , amma gabaki d’aya sabida saramasan da kansa yake masa ne
yake lumshesu, a wannan lokacin kamata yayi a ce yana kwance , amma ya hana kansa
haka sabida little da yasan zai shigo d’akin. Yanxu ma saida ya tabbatar baccin
little yayi nisa sosai kafun ya koma d’ayan side din ya kwanta.

A ‘bangaran bobo ma saida ya shirya cikin wani saban wankan kananan kayan kafun ya
nufi d’akinsu little , yana shiga ya tarar da babu kowa a ciki sai prince da yake
bacci a gajiye , ‘karasa shigowa ciki bobo yayi , dan karamin maganin hannunsa ya
bude tare da shafawa prince a gwiyarsa shima da tayi ja , har wani ajiyar zuciya
yake saukewa cikin baccin, yana gama saka masa ya gyara masa duvet dinsa ya bar
d’akin. A falo ya tarar da uncle yauma hannunsa dauke da jarida, suna had’a ido da
bobo ya hararesa, shi kuma bobo sai ya mayar masa da martanin murmushi yana
sunkuyar da kansa kasa “ dole kasun kuyar da Kai masa mana , tunda kun gama cin
zalin bayin Allah “,
Ynxu ma murmushi bobo ya saki tare da zama kan d’aya daga cikin kujerar kusa da
uncle “ uncle ba haka bane bafa , as big as they’re sun shiga training room suna
shashan cinsu cos basuyi tunanin zuwan muba , they’re very stupid shi prince
skipping rope wai yake yi sai kace wani yaro , little kuma mat ya shinfida gefen sa
ball, in ba so suke big boss ya gwada harbi akan suba “, murmushi uncle ya saki “
shine dan mugunta ka sakasu abu me wahala , taya zaka saka a saka abu me santsi a
tiles sannan ka basu kwai cikin fork? Muguntar tayi yawa fa”, cewar uncle , a
wannan karan dan dariya bobo ya saki “ uncle ai gaka gashi, kasan big boss lokacin
da kake ce masa no toh alokacin zai mayar da abun yes , thank god ma a waje na suka
sha hukunci ba a Wajan sa ba”, harararsa uncle yayi “ Menene banbancin naku? Ba duk
mugaye bane ku? Musamman wancan wan naka idan ya d’aure fuska sai ka dauka ba’a
ta’ba saukar da wani abu murmushi ba a Inda yake “, tun be kai karshen maganar saba
bobo ya kyalkyale da dariya sabida wani abu da ya tuna , sai da yayi dariyarsa
sosai kafun ya kalli uncle “ uncle har ka tuna mun wani abu, a kwai wani ma’aikaci
da ya dunga washe baki a wani meeting da akai, tun lokacin da big boss ya shigo
ciki kowa ya shiga taitayinsa banda guy din cos lokacin ne meeting dinsa na farko,
yadda yake murmushin ne ya bata wa yaya rai shiyasa yasaka ayiwa mutumin abinda zai
sa shi dariya yana zaune kan chair sannan ga shocking yasa a kunna , duk lokacin da
guy din ya kuskura yayi dariya zai bada umarnin a kunna shock, that guy har yau
idan yaji sunan big boss sai ya firgita Sabida amaimakon ya dunga dariyar kuka ya
soma , and at last kasan me yayi ? That his red lips ya ta’be ya bar wajan “, shima
sosai uncle yayi dariya yasan kad’an daga cikin aikin big boss , zaiyi abunda yafi
haka ma , shiyasa kowa yake tsoran shiga gonarsa.
“ uncle lets eat , yau yaran naka bacci suke” hakan kuwa ya faru su kadai sukai
breakfast Dinsu , yau hatta Prince da yafi kowa san cin abinci shima baccin yake
yi, saida suka kammala cin abincinsu uncle yaga bobo ya nufi hanyar kitchen , cikin
shock da mamaki uncle ya furta “ me zakayi kuma a nan?” ‘Dan murmushin bobo ya saki
yana kallan hanyar “ its long time now ! Na dad’e ban girka masa abinci da kai na
ba”, yanxu ma cikin dan zaro ido uncle ya furta “ who ? Are you serous ?” Fasa
tafiya bobo yayi ya kalli uncle yana dariyar reaction dinsa “ uncle kai ma kasan
yayana zan girkawa abinci ko?”, yau ba fita ?” Uncle ya kara dakatar dashi, juyawa
bobo yayi kafin ya furta “ he’s more important than my work ! Yau zan girkawa big
boss abinci ne with my own hands kafun tom and Jerry ( prince da little ) su tashi
daga bacci .

✨✨✨✨✨

GERMANY
A hankali sauban yake sakkowa daga stair case, yana tafiya yana duba agogon
hannunsa Sabida bayasan lokaci yaja masa , daga gefensa kuma Fanan ce take sakkowa
da wani unique travel bag madaidaiciya , daga nesa da shi ta d’an tsaya tana facing
Mamey dake binsu da kallo “ yaya sauban yanxu shikenan wai tafiya zakayi da gaske?
Mun kusa komawa makaranta fa, bazaka ‘kara kwanakiba kafun na tafi? Wallahi zanyi
missing dinka”, girgiza kai kawai mamey tayi , dan halin fanan sai ita wani lokacin
, shikansa sauban d’an hararar ta yayi kafun ya furta “ zakiyi missing dina ko
zakiyi missing kudina da kikeci?” Dariya Fanan ta saki a wannan lokacin “ Haba yaya
sauban kasan kai nafi missing amma kudin naka ma nayi missing dinsa kaga mun kusa
komawa makaranta” ta karasa tana kashe masa ido, sai kuma tayi saurin dafe bakin ta
sabida pillow din da ya jefa mata a baki “ kud’i dai nawane ba naki ba sai naga me
baki ai “, Haba yaya cewar Fanan tana kallan mamey , “ kima dena kallona dan babu
abunda zance muku, anjima kuzo ku bani kunya “, sim sim Fanan ta karaso Wajan ta “
mamey babu wani kunya da zan baki kawai kibi bayana , kinga yanxu yaya sauban ya
rage sona kawai ki fad’awa Abbu a aurar da shi nima nagaji da ganin sa ba aure”,
yadda ya nufo kanta da saurine yasa ta arta a guje cikin daga murya ta furta “
Allah yaya sauban ka kawo mun aunty ta , ni bazan tsaya ka kamani ba , Allah ya
tsare hanya , all the best Fleet Admiral,” bata jira cewarsaba Sabida karyace zai
kamatan, girgiza kai kawai yayi yana kallan mamy “ wannan yarinyar taki mamey ta
rainani , ranar da na kamata babu abunda zai hana na’ki karya mata hannayenta “,
hannun yar tawa zaka karya ?” Cewar mamey “ amma mameey kema kınsan halin yarnan
taki batajin magana “, dakatar dashi mamey tayi “ dadin abun awajanka ta koyi duka
rashin jin nata , you have to go nasan yaranka suna waje suna jiran ka , kansa yayi
mata knodding kafun ya rungumeta “ shikenan mamy , i will missed you , a cigaba da
hakuri da fanan, “ hannu ta d’aga zata bugeshi shima yayi saurin ja baya “ byee
mamy “, itama da Bye ta amsa masa sabida bayasan duk lokacin da zai tafi su dunga
fitowa sabida yaransa maza .

✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨

*KANO*

Eshaal ce tsaye a wajan oven tana gasa cake din da take had’awa daga gefenta kuma
AMMA ce a tsaye take temaka mata da wasu abubuwan ,musamman yadda take koya mata
wasu da barin yin cake din kala kala mutum saiya d’auka wata kwararriyar me cake ce
Sabida yadda take koya mata , itama Eshaal sosai tamaida hankalinta kan Amma dan
yawanci ta sanadiyar Amma ta iya komai, hatta karatın Alkur’ani AMMA tana koyar da
ita shiyasa ta saba da yinsa tun tana yar ‘karamarta. “ AMMA ya kamata ki Hutu tun
d’azu fa kike aikace aikace “, murmushi Amma dake tsaye tayi “ karki damu ai babu
wani gajiya , inaso naga yadda zaki gama ne ko akwai abunda kike bu’kata “, dan
jiyowa Eshaal tayi ta kalleta “ Amma karki damu babu abunda nake bu’kata , ko da ma
ina bukatar abu ai ba sai na wahalar dake ba , kawai nidai ki samu ki huta d’an
Allah kinji “, toh shiknn cewar AMMA, amma duk da hakan bata zauna ba , sai da
Eshaal ta juye cup cake din cikin oven ta saka wani , kama hannun Amma tayi ta
zaunar da ita kan dinning din cikin kitchen din , Amma Zata mike Eshaal tayi saurin
dakatar da ita “ Haba Amma kiyi zamanki karki damu kinji ? Bari na zuba miki cup
cake din Mss Eshaal kimun testing nasan wannan karan Amma sai na fiki iyawa”, ta
‘karasa tare da zubawa Amma cake din cikin wani unique plate me kyau, ta ajje mata
tare da d’auko mata d’aya daga cikin zoban da tayi d’azu “ oya AMMA kiyi mun
testing amma karkiyi Santi fa”, cewar Eshaal cikin zolaya “karki cika baki fa , dan
nasan ba wani dadi zaiyi ba”, ta ‘karasa tana cin d’aya daga cikin cake din , kamar
Wanda beyi dadi ba sai kuma ta d’an ya mutsa face dinta hakan kuma ba karamin kyau
yayi mata ba , yadda Eshaal taga Amma ta ya mutsa fuska yasa jikin ta duk yin sanyi
a tunaninta cake din ne beyi dadi ba , sai dataga Amma ta ‘kara gutsira tana d’aga
wa Eshaal 3 fingers alamar yayi dadi dan ko magana ta kasa , “ Amma yayi dadi ?”
Cewar Eshaal tana ‘kara tanbayar Amma dan tabbatarwa “ sosai ma” cewar Amma , ai
Eshaal bata san lokacin da tayi hugging Amma ba tana dariya , “ Kutmar uba ,lalle
Eshaal baki da hankali , akan abin anfaninmu zaki sa mana kazamarnan har ta zauna
akai ? Sannan taci abinci da plate dinmu?” A zuciye Eshaal ta juyo tana kallan
Baby, itama AMMA mikewa tayi daga kan kujerar tana ajje cake din , “ Menene haka ?
Kin cika shiga sabgata me ya shafeki da duk abunda zanyi ? Taci d’in ni na bata ,
iskancinki ya isheni haka” kuyi hakuri dan Allah” cewar AMMA , “ No AMMA bakiyi
mana komai ba , iskancine Kawai irin nata , dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da
aikin mu “, ni kike cewa yar iska ?”, cewar baby , a zuciye Eshaal ta furta “
Amfad’amikin kiyi abunda zakiyi “, hannu ta d’aga tare da nuna side din Amma “
wannan Itace ….” Bata karasa ba Eshaal ta d’auke fuskarta da mari, “ Duk iskancinki
ki tsaya a kaina , naga kwana biyu kanki na rawa , kada ki kuskura ki kara saka
AMMA cikin banzayen maganarki , sabida tafiye mun ku gabaki d’ayanku dan ita din
mahaifiyata ce , karki manta kamar yadda kike yar gidan nan haka nake , nice babba
bake ba , ina d’aga miki ‘kafane sabida ita, shashasha kawai , fitar mun a kitchen”
ta daka Mata tsawa , ita kanta Baby batasan lokacin da ta fice daga cikin kitchen
d’in va . Maida kallan Eshaal tayi kan AMMA , “ AMMA dan Allah kiyi hakuri , zauna
mu cigaba da cake din kinga ma yakusa ‘konewa” ta karasa maganarta tare da nufar
wajan Oven din .
A cikin falour kuwa , waya Baby ta d’auka ta soma dialing number Momy amma
gabaki d’aya calls din basa tafiya, ita kadai sai cizan yatsa take tana jijjiga kai
ganin called din mom bayashiga ne yasa ta mayar da akalar wayar zuwa phone din dady
, shima kamar had’in baki yana d’aga wa be jira tayi magana ba ya sanar da ita yana
meeting, zata katseshi ya Rigata ta hanyar kashe wayar da yayi . Dogon tsaki kawai
taja tare da barin falourn rai a’bace zuwa d’akin dan sosai Eshaal ta ‘bata mata
rai “ kamar ni zatace zata fad’awa magana ? , lalle wuyanki ya isa yanka amma zanyi
maganinki” ita kadai take maganar ta cikin zuciyarta tana Tunanin irin hukuncin da
zata saka mom tayi wa Eshaal.

✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨

Cikin wani irin mugun speed motar da Abla take ciki take rusa gudu, lokaci zuwa
lokaci d’aya daga cikin matar cikin motar tana amsa wayar da ake faman kiranta tun
d’azu. A cikin boot kuwa gabaki d’aya Abla bata san inda hankalinta yake ba ,
balantana ta saka ran ko tafiya ake , sosai jikinta ya d’auki zafi zau kamar me
zazza’bi ga allurar da akai mata lokaci zuwa lokacin sai zabura take sabida yadda
taji tana mata zafi da ‘Kai’Kayi a jiki, gabaki d’aya batajin zata iya mota jikinta
, hatta harshenta ta kasa d’agawa balantana tayi addua sai a cikin zuciyarta kawai
take iya ambatan sunan Allah . Sai da sukayi tafiyar 2 hours daidai sunzo inda suke
san zuwa wajan kamar ba a rayuwa a wajan sabida rashin mutane , parking din motar
sukai d’aya daga cikinsu ta ‘kara fitowa daga cikin motar ta nufi inda Alba take ,
wata allurar ta ‘kara tsira mata da ko minti d’aya batayi ba jikin Abla ya saki ta
fara lumshe idanuwanta Sabida ‘karfin Allurar , tana ganin Abla ta lumshe
idanuwanta ta d’aga hannuta d’aya ta saki taga baya motsi , wani salatif din toshe
baki ta samu ta rufewa Abla baki tare da d’aure mata hannuta duka biyun , cikin
mintuna da basu wuce 5 ba wata babbar mota kamar tifa da ake fitar da rice ta
karaso wajan , cikin Sauri d’ayar matar ta fito daga cikin mota lokacin da sukaga
zuwar tifar nan, a cikinta wasu gandama gandaman maza ne kana ganinsu kaga yan iska
ko wanne cikinsa da tattoo ga wani irin gyaran kai na tantiran yan iska a kansu
amma gabaki d’aya sanye suke cikin lallabiya ga carbi da suka ri’ke a hannayensu ,
wani abu me kamar bokiti suka d’auko me ‘bula ‘bula a ciki me fad’in gaske , haka
matannan suka kinkimi Abla suka sakata ciki tare da kulle , sannan aka sata cikin
bayan motar da take da irin abubuwan kusan guda goma , suna kulle motar su suka
bawa yan matan wasu card guda biyu suka canza tafiyar tasu zuwa wata hanya daban
tare da nausawa cikin daji .
10: 10am suka ‘karaso inda suke san zuwa duk da kasancewar sun fita daga cikin
dajin sun shiga cikin wani ‘kauye shima wajan saida suka kara tafiya sosai sunnan
Sukayi parking , da d’add’e da d’add’e suka dunga shigar da kayan cikin motar suwa
wani gida da duk Wanda ya gansa zaiyi mamakin ganin gıdan a kauye dan gabaki d’aya
tsarin gidan ya fita daban da kauyen da suka baro, a cikin gidan kuwa cike yake da
wasu maza da mata a ciki , wasu manyan mutane da kagansu kaga masu kudi ba fararan
mutanen ba , hatta ba’ka’ken zaka gansu kowa cikin shigar sa , ga manyan mata suma
da zaka gansu kowaccensu taci a donsu na masu kud’i , lokacin da mazan nan suka
shigo ciki haka wasu mata suka bubbud’e manya manyan abubuwan, abun mamaki gabaki
d’aya matane a cikin ko wana bokitin, haka a dunga fito dasu gabaki d’ayansu babu
wacce take nunfashi a cikin su dan ko motsi babu wacce tayi sabida allurar da
sukayi musu , da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai haka a ka dunga d’aga matan ana nunawa
maza da matan , abun mamaki yadda suka fara cikin su cikin ‘kan’kanin lokaci duk
wacce Akaji kudinta yafi yawa ita ake ajje wa yarinyar ko duk me kudin da yafi
saka kud’i shi za’a bawa, haka aka dunga cinikin matan kamar ba mutane ba , ana
zuwan kan Abla tun lokacin da sukayi arba da face dinta aka soma cinikin kud’i bana
wasa ba , cikin ikona Allah kowa so yake ya d’auketa shiyasa suka dunga saka
ma’kud’an kudi akan samun ta , sun jima suna fafata Wanda zai d’auketa dan kowa
hassada yake da akan wani ya fishi , watace ta furta zan bada 7million , tun kafin
tayi shiru wani ya furta zan bada 10 million , shima beyi shiru ba wani ya furta
zan bada 12million , haka Suka dunga cacar kudin da zasu siya Abla cikin turanci ,
wata farar baturiya da tun d’azu take shakar shisha ta kallesu gabaki d’ayansu a
gadarance ganin irin kananan kudin da suke sawa , saida ta zu’ki shishar ta iya
zu’ka ta fesar da haya’ki ta hanci da ta baki kafun ta gyara zama tana ya tsine
fuska “ zan bada 35 million” gabaki d’aya wajan sai suka mayar da kallansu kanta
daman haka matar take duk lokacin da ta shigo kasar taga kowa yafisan ya samu wani
abu sai ta saka ma’kudan kud’ad’e koda kudin ta zaiyi kasa ta mallaki abun shiyasa
ko wannansu cikin jin haushi yake bunta da kallo batare da sun ‘kara furta komai ba
sai harare Harare da ake bin juna dashi “ Sold out” wani mutum dake tsaye ri’ke da
taba ya fad’a , babu Wanda ya sake cewa sai bin Abla da Suke da kallo su kansu sun
sani ko a cikin kyawawa Abla kyakkyawa ce ga wani irin sahirtaccen kyau da take
dashi dukda basu ga gyarun idanuwanta , take a wajan matar ta saka akayi musu
transfer din 35million ta saka wata yarinyarta d’aukar Abla, ragowar yaranta suka
d’auki matan biyun da duk natane , bata kuma zamaba ta tashi ta tafi , a cikin
motar ta aka saka Abla d’aya daga cikinsune takalle ta tana washe baki “ Mah !
Wannan yarinyar ta ‘karshe ba ‘karamin kyaune da ita ba , ita wa zaki siyarwa ?”
Murmushi matar ta sakar mata tana le’ken fuskar Abla da ita kanta saida kyawun Abla
ya razanata, cikin wani irin murmushi da ta barwa kanta sani ta furta “ Da ita zan
tafi CANADA”, Canada ? Cewar yarinyar cike da shock dan bata ta’ba ji matar ta tafi
da duk Wanda take sıya ‘kasar taba sai akan Abla , gyad’a mata kan da matar tayi ne
ya kara bata mamaki cikin zuciya tana Ayyana nasara da babu Wanda ya ta’ba samu a
wajan matar kamar Abla tunda har zata tafi Canada da ita . “ let’s go” cewar matar
tana katse mata zancan zucin da take , da Sauri yarinyar ta bud’e mata mota ta
shiga suka bar wajan , sa’banin sauran motocin da batare da ita zasu tafi ba ko
wacce ta nufi hanyar da zasu kai yarinyar dake cikin motar. Abun mamakin sun dad’e
suna tafiya har suka ‘karaso wajan wani private jet daga wajan harda yan sanda da
mutananta da ta saka , bayan ma’kudan kud’in da ta basu aka saka mata Abla a cikin
jirgi kamar gawa , kasan tuwar duk lokacin da zatazo cikin private jet take zuwa
shiyasa basu ‘bata lokaci ba saida tayi settling din komai tayi wayar da zatayi
sabida karta samu matsala zuwan ta canada da Abla sannan suka shiga cikin jirgin,
cikin ‘kan’kanin lokaci jirgin su ya Tashi zuwa Canada ✈️.

(Abla bye bye 🥹🥹)

🍃🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*NEW YORK*
Yadda bobo yayi wa su big boss abinci kala kala sai ya burge mutum , sosai yayi
abinci masu kyau babu Wanda zaiyi tunanin bobo ya iya girki haka hatta su james sai
faman jinjina irin girkin bobo suke dukda shi girkawa kawai yake duk abunda ya
bu’kata suna tsaye suna mi’ka masa , ba ‘karamun ‘kawata dinning din Sukai ba , ko
ita sai faman d’aukar ido sabida sunsan me gayyane zai sakko duk da kullum haka
wajan yake a tsaftace , yana kammala abincin ya nufi part d’insa .
11:45am prince ne ya fara sakkowa ‘kasa shima kana ganin jikinsa zaka ga
alamar wanka yayi sai faman tashin ‘kamshin turare yake , yadda yake faman kulle
idanuwansa zaka gane baccin da yake ji ba ishesaba yunwace ta tayar dashi shiyasa
kai tsaye ya nufi dinning , yadda yaga komai a tsare ne yafi burgeshi su James na
gefe ko wannansu ya canza kayan jikinsa sabida ko kad’an idan big boss ya sakko
yaji jikinsu na ‘kamshin abinci sai ya sa’ba musu shiyasa suke takatsantsan sosai
dashi, prince har ya bud’e wani warmer yadda yaga abincin ya ‘kawatune yasa ya bawa
James umarnin yayi serving dinsa , cikin d’an girmamawa james ya furta “ sir we’re
waiting for big boss”, d’an dakatawa prince yayi kafun ya furta “ Yaya big boss be
sakko ba ?” Yes sir” yaya bobo fa ?” Ya Kara tanbayarsu “ shi yayi abincin”james ya
bashi amsa cikin girmamawa, shima prince cike da mamaki ya furta “ yaya bobo ? Shi
yayi abincin nan ?” Yanxu ma da yes sir James ya bashi amsa “ kamar zaiyi kuka ya
kalli abincin “ yanxu Kenan ta tabbata bazan ci abinci da wuri ba ? Wayyo yunwa”
says who?” Yaji maganar yaya bobo daga bayansa , da Sauri ya juyo yana kallan bobo
da yake ‘karasowa Wajan dinning , “ wanene yace bazaka ci abinci ba ?” Gashin kansa
prince ya shafa kad’an “ no yaya bobo I thought yaya big boss kawai ka dafawa
shiyasa” oh really ?shine yake hana ka cin abinci Kenan ? Toh bari ya sakko” da
Sauri prince ya ri’ko hannun bobo “ Dan Allah yaya bobo kayi hakuri , ni wallahi
yaya big boss be hanani abinci ba , kuma yaji wannan kalmar taka sawa zawa zaiyi a
kulle ni me dalili a hanani abincin , dan ‘Allah please” , harararsa bobo yayi “
sai shegen tsoro kamar kura , shiyasa little yake maka wayo idan kuka janyo rigima”
murmushi prince ya saki “ no yaya bobo ba haka bane duk lefin da little zaiyi
nafiso ayi mana hukunci tare banaso naga an yi masa hukunci shi kad’ai”, gashin kan
prince bobo ya shafa “ good boy, haka akesan yaya ya kasance , that’s why big boss
yake d’aga maka ‘kafa Sabida yadda kake kula da little d’insa”, murmushi prince ya
sakar masa , cikin d’aga murya ya furta “ Yaya bobo I so much love you all , I love
you , I love yaya big boss , I love little , I love uncle , you’re my family my
happiness my everything…” be ‘karasa every thing d’in da yake san fad’a ba sabida
‘kamshin turaran da ko a mafarki idan yajisa yasan ko nawane, turaran da babu ma
halu’kinda yake da irin ‘kamshinsa sai mutum d’aya Sabida yadda ake had’a masa
turaran da ma’kudan kudi masu yawan gaske da zai baka mamaki, ta ko ina kamshin
turaransa ne yake tashi, direction din da bobo yasan yake wajan ya kalla , yana
tsaye hannayensa sanye cikin aljihun farin wandan jikinsa na kanfanin Gucci fari
tas dashi me laushin gaske iya gwiwar ‘kafarsa fararan ‘kafarsa sosai ta fito cikin
wandon jikinsa , kafarsa ma sanye take cikin farin takalmin Yeezy , yadda ‘yan
yatsun ‘kafar suka fito sosai zasu baka sha’awa dogaye farare tas dasu, jikinsa
sanye yake cikin farar t-shirt din Chanel da tayi mugun fito da ‘ka’k’kar far
muscles dinsa , dogon hannunsa fari tass sosai suka fito musamman yadda hannunsa na
dama yke d’auke da abun hannu guda biya daban daban na diamond , yadda shirt d’in
jikinsa take da shape din V ga button d’aya da yake a bud’e sosai ya bawa
lafiyayyar farar fatar jikinsa fitowa , daga yadda rigarsa take kana iya hango
yadda siririyar sar’kar diamond dinsa take ‘kyalli, iya kyau da had’uwa big boss ya
had’u sosai gyaran da gashin sa ya samu ya ‘kara ‘kawata face d’insa musamman yadda
red lips dinsa yayi jaa kamar Wanda ya saka janbaki ga tsagar giransa da tafito
sosai cikin cikakkiyar girarsa, bakin gashin kansa da ya’ke amurmurd’e sosai yake
tasar da ‘kamshi na daba , iya kyau Allah ya zuwa big boss kyau na wuce hasashen me
hasashe musamman idan mutum ya ‘kiyasta kyaun idanuwansa, daga gefensa little ne
shima cikin shigar brown din Riga sai milk din wando da milk din takalmi shima da
ya saka , sosai kyaun little ya fito sosai ga gyaran askinsa da kullum yake kusa da
idanunsa, duk Wanda yaga little yaga big boss yasan Jini ba wasa ba , musamman
yadda kalar fatarsu take kusan d’aya amma duk da haka big boss ya fisa haske ,
fuskarsa har yanxu akwai murmushi akan ga dimples dinsa da ya fito sosai , gabaki
d’aya maganganin prince a kunnansu shiyasa yake ta sakin murmushi , a hankali ya
soma taku cikin ta kunsa na kullum a nutse cikin Kamala da tsantsan izza , ga face
dinsa da har yau take a had’e babu fara’a a tattare da shi amma hakan ba ‘karamin
kyau yake masa ba , yadda gyaran asking kansa yake sosai zai burge musu yana tafiya
murd’ad’d’un gashin kansa na motsawa , duk da be d’ago da eyes dinsa ba yaji alamar
ido akansa , a hankali ya d’ago da sexy green eyes dinsa , kai tsaye direction din
bobo ya kalla tare da bashi wani irin kallo da ya saka bobo d’auke eyes dinsa yana
murmushi yasani big boss bayasan kallo amma shi duk lokacin da yaga big boss yayi
dressing yana jin dad’i sosai da sosai hakan yake burgeshi dan yasani d’an uwansa
kyakkyawa ne shiyasa mata suke mugun hauka akan sa amma shi besan sunayi ba dan
samun kwanciyar hankalinki kada ya sanı idan ba Haka ba hmmm ba’a magana dan ko
wana hukunci ya mike ke Kika janyo , a kan farar one sitter kamar ta sarauta ya
zauna sai kayansa da kujerar suka ‘karayı masa kyau , yadda yayi crossing legs
dinsa yana lumshe idanuwa sai ya burge mutum , hatta su Prince gabaki d’aya sai
satar kallansa suke , hatta uncle da ya Fito shima bin big boss din yake da kallo ,
danshi ba kayane suke masa kyau ba , shine yake yiw kaya kyau , kasan tuwar kowa
yasan baya cin abinci akan dinning yasa little da prince jera masa dishes din da
bobo ya dafa masa, cikin unique way suka shirya komai dan har course suka nemo kala
kala dan ba kowane irin ajje abinci yake soba ( lalle big boss wannan izza har ina
) har suka kammala jera dishes din yana zaune idanuwansa a lumshe , ko sound d’in
ajje abu basayi sabida kar ya bud’e eyes dinsa.

PAY YOUR 300 into 2681892316 , Aisha Umar , zenith bank sai a turo shaidar biya ta
wannan Number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*


💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
S____18💞

Suna kammala jera dishes dinning suka nufa shida prince kasantuwar uncle da yaya
bobo sunyi breakfast d’insu , shiyasa ba ‘bata lokaci James yayi serving d’insu
abincin da zasuci. Bobo kuma falourn ya dawo akan d’aya daga cikin kujerun da suke
facing big boss ya zauna , uncle na d’ayan side d’in shima hannunsa d’auke da
jaridarsa. A hankali big boss ya soma bud’e eyes d’insa , yadda yake motsi dasu
haka kyawawan dogayen gashin idanuwansa suke motsawa , a hankali ya ware idanuwansa
gabaki d’aya , yadda little da prince suka jera center d’in da abincin yake kai
ba’karamun ‘kawatuwa yayi ba , da sau d’aya ya kalli abincin ya d’auke face d’in sa
, sosai abincin ya burgesa amma ko a fuska mutum bazai ga alamun hakan a tattare
dashi ba , murmushi bobo ya saki tare da matsowa , da kansa yayi serving big boss
abincin da zaici and everything da yasan zai bu’kata, kusan 2 minutes bai motsaba
saida yaga dama dan kansa , Greek quinoa salad da bobo ya ajje masa ya d’an iba
kad’an cikin spoon ya kai bakinsa , yadda yake motsi da bakinsa kad’ai abun kallone
ga red lips dinsa da suke motsawa a hankali, saida ya ‘karacin second spoon sannan
ya d’an d’ago side din bobo batare da ya kallesa ba ya d’an ta’be bakinsa kad’an ,
fuskarsa har lokacin babu fara’a akai , sosai yadda yayi ya saka bobo murmushi
hatta uncle saida ya murmusa Dan kome yayi kyau yake ‘karasa, saida ya ‘karacin 3
spoon of Greek quinoa salad tukunna kafun yaci Tortilla soup d’in gabansa, komai
cikin nutsuwa yake yinsa , yadda yake shan tortilla soup mutum sai ya d’auka baya
san cin abinci , yadda yake yin komai cikin nutsuwa zai baka mamaki dan ko sound
din plate ba’aji. Ihun da little yayi ne yasaka bobo da uncle saurin kallansa ,
banda big boss da ya d’an lumshe eyes d’insa sabida yadda ‘karar ta cika masa dodan
kunnansa, be gama nashi ihun ba shima prince ya saka nasa ihun lokacin little ya
kammala cin abincinsa, gabaki d’ayansu sabida farinciki sun manta big boss abinci
yake ci sukai hugging d’insa lokaci d’aya , little har wani sound d’in dariya
zakaji yanayi sabida yadda yake cikin farinciki , bobo na ‘ko’karin yin magana yaji
kamar shigowar message cikin wayansa , yana dubawa ya d’an zaro eyes d’insa waje
yana sakin murmushi, yadda big boss ya ‘kara shan murr ne ya ‘kara saka shi wani
dariyar, uncle be gama fahimtar murnar me suke ba shima yaji sa’kon shigowar text ,
kamar bazai bud’e ba amma yadda yaga little da prince sun zuba masa ido ne yasaka
shi bud’ewa har lokacin basu saki big boss da ya ‘kara d’aure face dinsa ba , shima
uncle yana ganin alert d’in ma’kudan kudin da big boss ya tura masa bai san lokacin
da wata ‘karamar dariyar farinciki ta kwace masa ba , shi kuma ba abun kayi masa
Godiya ba sabida kome zai musu baya basu chance d’in su gode masa sabida yadda yake
‘kara had’e ransa shiyasa gabaki d’aya suka kasayi masa magana dan yanxu zai iya
‘bata ransu duk da ba wannan ne karo na farko da yake tura musu kud’i ba , hatta
bobo murmushin kud’in da yagani yake , yasani big boss yana da kudin da shi kansa
besan adadinsu ba hatta fita wata ‘kasa idan zasuyi basa ta’ba zama a hotel sai a
cikin gidan su , shiyasa duk da halinsa na miskilanci wasu lokutan yake d’aga musu
‘kafa dan shima bobo ba’a barshi a baya ba , duk lokacin da zai turawa su little
kud’i sai ya turawa big boss hakan sosai ya zama d’abi’arsu shiyasa ko prince da
little zasu yiwa juna kyauta sai sun siyowa big boss da bobo da kuma uncle iron
man. “Will you ?” Cewar big boss yana zuba musu narkakkun eyes d’insa , cikin Sauri
sukai breaking hug din da sukai masa , yadda little ya Tashi cikin saurine yasaka
big boss kallansa kad’an tare da d’auke eyes d’insa lokacin da yake zarar tissue
yana goge bakinsa a hankali , kamar Wanda aka tsikara little ya tashi da sauri har
yana ‘ko’karin yin tuntu’be , da sauri kuma ya juyo yana kallan bobo da yaya big
boss “yaya banji ciwo ba please wait for me ”, sai kuma ya juya da Sauri ya nufi
part d’insu , ko mintuna biyu little beyi ba ya sakko hannunsa d’auke da unique box
din da ya ta’ba wasu su yaya bobo , daidai inda big yake zaune ya nufa cikin cool
voice ya furta “ yaya is for you “ lokacin da yake mi’ka masa box d’in da farar p-
cap d’in hannunsa , ba box d’in da little ya mi’ka masa ba hatta shikansa little
d’in big boss be kallesaba sai lumshe eyes dinsa da hakan ya zamar masa kamar a
jininsa yake ‘kara lumshe wa , little kamar wani ‘karamun yaro ya bud’e box d’in
tare da ciro siririyar diamond bracelet da duk İnka duba hannayensu zakaga bracelet
d’in a hannun kowannansu yana shinning , d’aya farin hannun big boss da babu
bracelet a jiki little ya sakawa , sosai abun hannun yayi wa hannunsa kyau ydda
yake bin hannun da kallo haka su prince suke bin face d’in big boss da kallo ,
mutsu Mutsu ya farayi da eyes dinsa har ya bud’e lokacin da yaga bracelet d’in da
little ya saka masa a hannu, rai a had’e ya zubawa little idanuwansa , shi kuma
little ya saukar da nasa ‘kasa cikin cool voice dinsa ya furta “ is for you,”ya
‘karasa yana mi’kawa big boss farar p-cap d’in hannunsa , kamar bazai kar’ba ba har
little ya cire ran hakan sai yaga big boss ya saka fararar dogan hannunsa ya Amshi
p-cap d’in bai zame ko ina da ita ba sai kan lallausan gashin kansa da yake a
murmurd’e , hakan da yayi ba ‘karamin farinciki ya saka little ba kuwa dan lokaci
d’aya little yayi hugging d’insa kamar me shirin yin kuka ya furta “ yaya please
karka cire bracelet d’innan kamar Sauran favorite bracelet d’in ka kaji yaya?”, a
maimakon big boss ya bashi amsa sai ma saukar rankwashi da ya Kai masa kad’an da
sauri little ya sakesa yana sosa Wajan “ idan ka karyani fa?” Cewar big boss da ko
kwayar idanuwansa ba’a gani sai red lips d’insa da ake iya gani kawai. Lips dinsa
little ya turo kad’an tare da kallan side d’in bobo , d’an harararsa bobo yayi
lokacin da ya ke mi’kewa tsaye , kusan 2 minutes Big boss ya mi’ke shima tare da
kallan direction d’in su little “ if we go out , zaku iyayin duk abunda kuka ga
dama , zaku iya juya komai na gida upside down ok?” Yana Kai ‘karshen zancansa ya
kama hanyar barin falourn , cikin murmushi bobo ya furta “ uncle zamu d’an fita ne
yanxu , ku kuma kunji abunda yace , if you like ku har gitsa gidan babu ruwana “,
kusan lokaci d’aya prince da little suka furta “ yaya bobo” harararsu yayi tare da
furta “ ni dai babu ruwana “ yana kai ‘karshen zancansa ya bar falourn cikin sauri.
A waje kuwa manya manyan sojoji ne sosai a wajan ko wannansu ya canza uniform
d’insa sai kalar uniform d’in da suka saka ya haska ko wannansu , ga manya manyan
mukamai da suke d’auke dashi , Lokacin da Big Boss ya fito gabaki d’aya kusan
lokaci d’aya suka sara masa , har ya soma tafiya be kalli Inda suke ba musamman
farar p-cap d’in little da take kansa ga ba’kin gashi kansa ya fito sosai ta
bayansa musamman yadda kayan jikinsa suke farare tass dasu , yadda santala santalan
‘kafafuwansa suka fito cikin farin wandan jikinsa sai ya burgeka, gabaki d’aya ko
wannansu ya kasa d’ago da kansa balantana yayi gigin kallan side d’in da yake ,
daidai kusa da inda manya manyan ba’ka’ken motocinsu suke wasu manyan ‘karata guda
biyu da duk cikin gidan sunfi kowa tsaho da girmane suka take masa baya , gashi duk
cikin matsu tsaran Wajan su buyune kad’ai masu sanye da suit a cikinsu ga ba’kin
glass da ke idan ko wannansu , yadda suka had’e rai sai ya baka tsoro musamman
shima da gogan nasu fuskarsa take a had’e , duk motar da suka wuce sai sojojin
wajan sun ‘kara du’kar da kansu sosai tare da sara masa , basa cire hannun su har
sai sun wuce , daidai lokacin da Bobo ya fito shima Robert da captain suna taka
masa baya , gabaki d’aya combo cars d’in da aka fito dasu sai faman d’aukar
‘kyalli suke ko wacce ka kalla zaka ga tanbarin lion a jikinta, daidai farar Rolls
Royce fara tas da ita daga Wajan tama zaka gane ba ‘karamar mota bace , sosai wajan
motar yake da kyau ga tinted d’in motar ba’ki’kirin , cikin sauri d’aya daga cikin
manyan sojojin da suke right side d’insa d’aya daga cikinsu yayi saurin bud’e masa
‘kofa , saida ya shiga tukunna ya rufe ‘kofar tare da sara masa , bobo ma da ya
‘karaso wajan da sauri d’aya guy d’in ya bude masa ‘kofa yashiga kafun ya kulle
door d’in, suna jiyowa gabaki d’aya
sauran sojojin suka shish shiga cikin motar su bayan sun danna wani button na
kunnensu lokaci d’aya , d’aya daga cikin babban yaran Big Boss me suna Victor shine
ya shiga driver seat , hakan ce ta kasance wa d’ayan yaran big boss me suna Anthony
shima d’ayan side din motar ya shiga , cikin ‘kan’kanin lokaci motocin nan suka
soma tafiya slowly kafin lokaci guda motocin su zuga a guje .
Tun da ya shiga cikin motar ya lumshe idanuwansa musamman yadda cikin motar
ya kasance kamar falour dan baza’a kirasa da cikin mota ba Sabida irin had’uwar da
yayi dan har wani center ne dashi da yake d’auke da wasu ‘kananan cups da d’an
’karamin brown plast me shegen kyau , gabaki d’aya kujerun ko wannansu zakuga
harda button a jikinsa da zai kwantar maka da kujerar kamar wani ‘karamin gado.
Yadda Big Boss ya lumshe idanuwansa zaka d’auka bacci yake gashi wajan da suke babu
Wanda zaiyi Tuna’nın cikin motar ne dan ko Victor da Anthony da sune driving seat
ba’a gani a wajan sannan ko magana zasuyi bazasu ta’ba jinsu ba . ‘Dago da eyes
d’insa bobo yayi daga kan wayar da yake dannawa yana kallan yadda Big boss yake
lumshe eyes d’insa “ Anyanke musu hukunci all, suna prison now , but iyayensu sunso
gardama expecially Vc , but anyway sha suna prison duk da haukan da Vc yasoyi akan
sai ya Gana dakai Sabida asaki d’ansa” sai a lokacin big boss ya bud’e eyes dinsa
ba tare da ya kalli bobo ba ya furta “ You don’t have to stop him da kabarsa
sunzo”, cikin dariya dariya bobo ya furta “ me zakayi masa ?” ‘Dan d’ago da eyes
dinsa yayi ya kalli bobo sau d’aya kafun ya furta “ zan bawa Abdulmaleek
kyautarsane” wani irin dariya bobo ya saki sabida jin abunda Big boss yace , yadda
yake dariyar zaitabbatar maka daga cikin zuciyarsa yake fitowa shiyasa big boss ya
d’ago eyes dinsa yayi masa kallan sakanni kafun ya Kanye eyes d’insa , ringing din
wayar bobo ce ta katse masa dariyar da yake , murmushi ya ‘kara saki kafun ya
d’agowa Big Boss sunan wanda yake kira “ His excellency?” Har zai d’aga called d’in
sai kuma yayi sauri sakata a speaker yadda Big boss xaiji. Yadda Bobo yaji muryarsa
kamar cikin Tashin hankaline yasa ya gyara zamansa , His excellency be jira bobo ya
soma magana ba ya furta “ Bobo please Alice is here , tana nan New York bayan ta zo
batare da sanin kowa ba , she’s now trying to killed her self , ko zaka iya ro’kon
Big Boss yaje wajan please , just even once , ita kad’aice daughter na bazata bari
har na ‘karaso ba zata iya kashe kan nata idan bata ga big boss , shi his
excellency be san Big Boss na wajan ba sai faman maimaita Alice tace idan bata
gansa ba zata kashe kanta yake ga sunan big boss da yake faman ambata, da Sauri
bobo ya kallesa ganin ya kashe kiran , “ why ka kashe kiran ?”cewar bobo , batare
da big boss ya kallesa ba ya furta “ in waya zakayi ka fita kaje kayi , bansan
hayaniya” cewar big boss lokacin da ya saka hannunsa guda d’aya wajan tsagar
giransa , cikin cool voice bobo ya furta “ ko zamu biya ? Since kamar ma muna kusa
da wajan , she’s trying to killed her self we have to stop her “, cikin ido da ido
Big boss ya kalli bobo kafun cikin cool voice d’insa hankali a kwance ya furta “
inta mutu Allah ya ‘kara nauyin ‘kasa “ yana kai ‘karshen zan cansa ya mayar da
idanuwansa ya kulle .

✨✨✨✨

KANO
Momy bata shigo cikin gidan ba sai wajan ‘karge 9 na dare lokacin Baby ta cika
tam sabida haushisu da take ji ga haushin Eshaal da ya cikata tun d’azu , ita
kad’ai sai kunbure kunbure take shiyasa ta ware volume d’in ‘kida sosai ranta a
‘bace tundaga kan yadda take Danna wayar tata mutum zai fuskanci haka , turo ‘kofar
da akai ba sallama ne yasa ta ‘kara Tsuke face din ta sabida tasan ko wacece ,
itama momy ganin yadda Baby ta had’e mata raine yasa ta ‘karaso cikin d’akin tare
da kashe kid’an , a zuciye Baby ta d’ago da idanuwanta ganin momy a kusa da ita
yasa ta ja wani dogon tsaki tana d’auke idanuwanta daga kan momyn , itama momyn
bata damu da yadda Baby tayi mata tsaki ba sai ma kunnawanta biyu da ta kama “ Haba
baby na wannan fushin duk da Menene ? Kiyi ha’kuri mana , lokacin da kika kirani
bana kusa da wayar sai missed calls d’inki da nagani , kiyi hakuri baby na “,
mi’kewa tsaye Baby tayi tana nuna mata ‘kofa cike da rashin kunya ta furta “ kizo
ki fitarmun daga d’aki bana bu’katar ganin ki , zan kwanta” ri’ko hannunta momy
tayi kamar ba Itace babba ta kara sanyaya muryar ta “ haba baby na banaso naga
ranki na ‘baci haka please baby na , nace kiyi hakuri , bazan sake hakan ba
kinji ?” ,d’an kwafa baby tayi tana yatsina fuskarta kafun ta samu waje ta zauna
akan fadonta “ toh yanxu fad’amun me akai miki acikin gidan nan, naga ranki
a’bace haka” sai a lokacin Baby ta kwakwulo kukan muna furci harda hawayenta ta
soma labartawa momy karyar da ta had’a har da cewa AMMA da Eshaal haduwa sukai suka
dunga dukanta bayan Eshaal ta gama zaginsu gabaki d’ayansu har Dady bata ‘kyaleba”
sosai ran momy ya ‘baci sai faman hura hanci take sabida jin karamar Eshaal , a
zuciye ta fito daga d’akin Baby, baby na ganin fitarta ta ‘kyal’kyale da dariya
tare da bin bayanta da Sauri dan ganin abunda momy zatayi musu , momy tana fitowa
ta fara kwallawa Eshaal kira , Daidai lokacin da Eshaal take karatun alqur’ani da
sauri ta mayar dashi tare da fitowa waje ko hijab d’in jikinta bata cire ba , tana
fitowa falourn ta soma ‘ko’karin dur’kusawa amma momy ta Shakira tare da furta “
ina munafukar uwar da kike cewa kina dashi take ? Ke kinzama yar iska komai ya
bayyana a jikinki shiyasa kike da bakin magana ?” Kallan baby momy tayi kafun ta
furta “ jeki kirawo mun d’aya muna furta “ cikin Sauri Eshaal ta soma girgiza mata
kai “ momy babu ruwan AMMA a ciki wallahi duk lefinane” hannu momy ta d’aga ta
wanke wa Eshaal fuska da mari “ dan uwarki ina magana kina bani amsa ? Ko uwarki
Hauwa’u bata İsa ina magana tana mayar mun ba , balantana ke da aka same ki ta gaba
da Fatiha” da Sauri Eshaal ta runtse eyes dinta dan aduniya batasan taji ana zagar
mata mahaifiyarta da ta mutu , hawaye har ya fara kwantawa akan fuskarta ga tafikan
hannun Momy da ya fito rad’au akan face d’inta , lokacin da AMMA tafito ko jira ta
tsugunna momy bata bari tayi ba daka kalli fuskar AMMA kuma zakaga alamar bacci ta
somayi aka tasota “ Muna fuka , annamimiya butulu, uban me zakimun da kike shirin
tsugunnawa ‘kasa Sabida muna furci ? Da sai ki d’ago ki kallene cikin ido ai , muna
fukar banza muna fukar hofi ke ko kunya ba’kyaji ki zauna ki dunga sharara wa
yarinya ‘karya anyama ba asirceta kikayi ba ? Dan gabaki d’aya yanxu na fara
xarginki idan bakya bin malamai , da Sauri Amma ta d’ago da idanuwanta ta kalli
momy kafun ta sauke idanuwanta tana d’an girgiza kanta kad’an “ kiyi hakuri “ cewar
AMMA , Eshaal kuwa sabida mummunar maganar da suka fad’awa Amma yasa ta fashe da
wani saban kukan har cikin zuciyar ta bataso AMMA ta bawa momy hakuri ba , dan momy
ba mutum bace azzalumace shekaru kusan nawa tana aiki agidan amma kullum da irin
wulakancin da Momy take mata , yadda take kuka ne yasa momy ta hankad’awa AMMA ita
tana karkad’e hannayenta a yatsine “ shegiya bansan ya akai hannuna ya ta’ba
jazasar jikin kiba dan kekam kamar yar shegiya haka kike turrrrrr, ku tattara ku
barmun falo keda muna fukarnan yanxu kafun ranku ya ‘baci gabaki d’ayanku.”
Hawayenta Eshaal ta goge tare da kama hannun AMMA suka bar wajan dan idan suka ce
zasu tsaya sai ta ‘kara ci musu wani mutumci harsunyi nisa momy ta sake daka mata
tsawa “ muna fukai Menene na ri’ke hannu kuma ? Dallah ki saki juya kowa ya nufi
wajan kwanansa , muna fukan banza muna fukan hofi “ rabuwar kuwa sukayi kowa ya
nufi hanyr makwancinya , Eshaal ji tayi kuka na zuwar mata sosai take a binta akan
gadon ta tuntanayi da ‘karfinta har ta soma ajiyar zuciya alamar bacci ya
d’auketa . Suna barin wajan momy ta kalli baby “ my baby kinyi farinciki ko ? Cikin
washe baki sosai baby ta furta “ yes nayi farinciki” sai kuma ta kama yanfar
d’akinta “ momy ki kira dady kice ya taho mun da ice cream sai gasasshiyar kaza da
nake so, sannan ya taho mun da kilishi , ina jira” bata jira jin amsar momy ba ta
shigo d’akin ta fara danne dannenta a waya ita kad’ai ga headphone da ta saka a
kunnanta , tun tana jiran dawowar dady har bacci ya d’auketa da headphone a
kunneta.

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*NEW YOUR CITY*

“ No please Big Boss , atleast tunda ya kira , please” cewar bobo , still shiru big
boss yayi masa batare da tanka masa ba “ ok just for me please , just for
Abdulmaleek”, cewar bobo , batare da big boss ya bud’e idanuwansa ba ya furta “ and
you who are you?” Girgixa kansa bobo yayi ganin missed called d’in his excellency
akaro nayi a wannan karan harda just message , yana shiga cikin message din yaga
vidoe Alice tsaye wajan fanka ta saka wani igiya zata kashe kanta , rai a’bace
shikansa bobo ya furta “ Wannan bata da hankali ne ?” Shima sabida yasan his
excellency ya kira big boss da wallahi shima babu Inda zaije , wata ‘karamar waya
ya d’auka tare da tura musu short message , rai a d’an ’bace yasan idan ya nuna wa
big boss wallahi bazasuje ba, shiyasa ya tura message, Big boss kuwa tundaga
lokacin da bobo ya tura message yaji alamar an shiga wata ‘kwanar amma ko a fuska
be d’ago ba sannan babu wata alama akan fuskarsa tana nan yadda take sai ma ‘kara
balance da yayi yana lumshe eye kamar me bacci , 5 minutes motocin suka d’anyi
parking , yadda yaga fuskar big boss yasan ransa a ‘bace yake shoulder d’insa ya
dafa cikin cool voice kamar bashi ba ya furta “ please am sorry, just for your
brother kaji ? Ta’be baki big boss yayi kad’an kafun ya furta “ 3 minutes only if
not saidai ka taho a ‘kafa” d’an murmushi bobo ya saki kafun ya bar motar yana nufa
cikin gidan , 2 minutes later ya turowa big boss wani short vidoe kamar bazai
dubaba sai kuma ya kalli wayar bayan second 30 , wani message d’in ne ya sake
shigowa cikin wayar yana dubawa yaga yadda ta yanka hannunta Jini yana fitowa ,
ta’be baki ya ‘kwarangwalce ko kuma aljana dan shi gabaki d’aya Alice batayi masa
kama da mutum ba da jinsin aljanu tafi masa kama “ kawar ta zancan yayi gabaki
d’aya yana sakin gajeran tsaki ganin wani message din na bobo , ba tare da ya bud’e
message din ba ya ‘karayin balance kan kujera sai da ya d’auki good 5 minutes
sannan ya danna wani button lokaci d’aya victor ya bud’e masa mota, a lokacin da
zai fito da’kafarsa sai da ya sha izzarsa san ransa kafun ya fito cikin motar rai a
‘bace amma ko a fuska bazaka ga alamar ‘bacin rai atattare dashi ba , mutane biyune
suka bi bayansa Victor da Anthony , har yanxu p-cap d’insa na kansa , yanda yake
taka ‘kasa kamar bayaso Daidai medium gidan da bobo ya shiga har cikin falour ya
taka hatta shi bobo yayi mamakin shigowar big boss d’in Alice kuma tana tsaye kan
kujera bayan ta saka rigiyar a wuyanta , big boss na shigowa kai tsaye ya daki
kujerar tayi gefe Alice ta fara wutsil wutsil tana neman a gaji , rai a had’e ya
furta “ you can die now “ yana kai Karshen zancansa ya bar falourn.

PAY YOUR 300 into 2681892316 Aisha umar , zenith bank sai a turo da shedar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
S____19💞
Yana barin cikin falourn bobo yayi saurin harbin igiyar ganin tana faman cetan
ranta sabida yadda igiyarta sha’ke mata wuya , tana fad’owa ‘kasa cike da azaba ta
fara ri’ke wuyanta ganin yadda take sha’kar nunfashi da kyar dan ba ‘karamin sha’ka
igiyar tayi mata ba , ita kanta da take ‘ko’karin kashe kan nata bata d’auka da
zafi ba haka , bata gama shiga cikin hankalintaba shima bobo ya d’auke face d’inta
da mari har saida ta d’an firgita sabida yadda taji zafin marin a kumatunta ga face
d’inta da tayi yawur sabida sha’kar igiyar da tayi mata a ma’kogwaro, cikin
kausasshiyar murya bobo ya furta “ Now zaki iya shiga kitchen ki samu babbar wu’ka
kiyayyanka na manta “ yana kai ‘karshen wayan ya bar falourn shima. Alice kuwa
dukda zafin marin da taji a kumatunda da yadda Big Boss ya daki kujerar da take
hakan be sa soyayyarsa gushewa cikin zuciyartaba ko sau d’aya duk da bataga face
d’insaba sai daddad’an ’kamshin turaransa da yake wajan, wuyanta ta shafa dan sosai
taji azaba bata ta’ba tunanin mutuwar da zafi ba shiyasa tace zaka kashe kanta da
igiya , bobo na fita ta da kawa d’aya daga cikin maid d’inta tsawan akan meyasa
bata hanata kashe kanta ba tunda kisan da zafi gabaki d’aya sai ta fara musu bala’I
, har ta saka su bata ruwa , still bata wuce ba sai da tabisu ta tsits tsinka musu
mari sannan tayi wucewarta d’aki tana danna kiran her excellency .
Big Boss na shiga cikin motar su Victor suka tayar da motar zasu bar Wajan Daidai
lokacin da bobo ya karaso wajan , cikin dariya ya furta “ ka shirya kashe musu
yarinya kenan ? Idan matar…” be ‘kara abunda yake san cewa ba sabida zazzafan
naushin da big boss ya kawo masa , Allah ya temakesa ya gansa da ba abunda zai hana
ya naushesa abaki kamar yadda yayi niyar yi.

*******
CANADA
HALIFAX , NOVA SCOTIA

Hour 16 ne ya kaisu cikin city d’in Halifax Nova Scotia dake cikin ‘kasar
canada shi yasa gabaki d’aya basu isa cikin ‘kasar ba sai wajan ‘karfe 1:00am na
safe , amma yadda Garin yake da haske mutum sai ya d’auka dare beyi ba sabida yadda
kowa yake harkar gabansa . Tun kafun matar nan ta fito daga cikin jirgi akai mata
arrangement d’in komai har aka sake fitar da Abla da bata ko nunfashi cikin wata
jaka da aka sakata , sai da ta tabbatar komai yayi settling tukunna aka saka mata
Abla a cikin jaka kamar kayan wanki , still hakan be ishe suba sai da suka junga
mata kaya a cikin jakar sannan suka tayar da motarsu suka bar Wajan gabaki d’aya .
Direct motocinsu hanyar Acadia street Suka nufa , saida sukayi 15minutes suna
tafiya cikin mota sannan suka ‘karaso Acadia street , sosai layin yake da rashin
hayaniya kamar babu masu rai a ladin dukda irin manya manyan gidajen turawa da ke
wajan , Daidai wani gida da yake d’an nesa da Sauran suka ‘karasa kai tsaye farin
baturan da yake a matsayin gate man ya bud’e musu gate , suna shiga yayi saurin
kullewa tare da duba both dama da hagu na unguwar kafun shima ya shige cikin
gidan . Cikin medium space na parking motocinsu sukai parking sai a lokacin yan
matan suka ciccire kayan da suka sa a cikin jakar da Abla take ciki , duk da bata
motsi amma sosai ta had’a gumi, Haka yan matan nan suka d’auketa suka bi bayan
matar nan , gateman d’in kuma ya d’ebo musu ragowar kayansu . Wasu matana ne guda
uku a cikin falourn ko wannensu gashin kansa a bud’e har bayansu sai wasu ‘kananan
kaya da yake jikinsu , hatta wandunan jikinsu ko gwiwar ‘kafarsu babu Wanda yazo
masa , ga sarkar ‘kafa da ko wannansu yake sanye dashi , gabansu manya manyan
shisha ne da kwalaben giya da suke sha , d’aya daga cikinsu da take shan sigarine
ta kallesu musamman Abla da suka ga sun shigo da ita babu rai , kallan matar da
take sakar musu murmushi tayi da French ta furta “ mom ina kika samo kyakkyawar nan
?”, jin abunda budurwar tace yasa matar sakin wani murmushi , suma gabaki d’aya sai
suka kalli Inda Ablan take a kwance , cikin French matar ta bata amsa da “ Wannan
ba irin sauran bace , wannan babban ‘ka yace meshirin Samunta sai ya shirya , Clara
and Mila, you guys are once doctors inaso ku dubamun ita “ with suprise d’aya daga
cikin su tace “ ok Mom amma wajan wa zaki kaita ? Naganta kyakkyawa ko zaki bar
mana ita anan mudunga samun kudi “, ‘karasowa wajan ta matar tayi tare da kissing
Clara a baki kafun ta furta “wannan ba irin sauran bace kud’in duk babies d’ina
ne ,ita mazane zasuyi anfani da ita , wanka zanyi gobe nakeso zan kaita pacifico
( Wani club ne dake cikin Garin Halifax da ba kowane yake shigarsaba)” wow cewar
d’ayar me suna Mila “ but kyakykyawa ce , har na fara ki shin kyaunta Mom “ yanxu
kam wacce suke kira da mom sosai ta saki dariya tare da furta “Don’t worry my
baby , meet me now in my room , I need you urgently “ tana gama fad’ar hakan ta
wuce wani corridor dake ‘bangaran hagu. Ta ukunsu me suna EMMA da tun d’azu bata
tankamusu bane ta d’an girgixa kanta musamman lokacin da Mila take bada uwarnin
akai Abla d’akin da yake kallansu hakan ce kuwa ta faru , yan aikin mom suna
d’aukarta itama Mila da Clara suka bi bayansu banda Emma da tayi zamanta tana shan
barasan gabanta.
Suna shiga cikin d’akin akan medium size d’in katakon gadon suka kwantar da
ita , cikin kyankyami Clara ta ta’be face d’inta data gama shan mai har wasu
‘kurajene jajawur kwance akan face d’inta , “ ku cire mun wannan abun” ta fad’a
tana nuna hijab d’in jikin Abla , batare da damuwa da yadda sukaga face d’inta ba
d’aya daga cikinsu ta yaye Hijab d’in jikin Abla , lokaci d’aya tukun breast d’inta
ya fito sosai daga cikin rigar atanfarta, ga tudun nipples d’inta da mutum zaiga
shati sabida yadda ko bra babu a jikinta , sosai farin wuyanta ya ‘kara haska
breast d’inta da suka d’an fito sabida yadda suka jefa ta kan gadon , ba’kin
Gashin Abla sosai ya rufe mata fuska duk da irin dattin da yayi mutum zai iya gane
‘bakin gashine da ita ga cikowa da tsawo da Allah yayi musu ko su basu da cikakken
gashi me cika da tsaho irin na Abla ga gashin ta duk amurmurd’e, yanda Clara ta ke
binta da kallo kamar zata cinye ta yanxu maida kallanta tayi kan ‘kugun Abla da
yake d’an ‘karamin sai kwankwato da take dashi Masha Allah dukda yadda take a
kwance mutum yasan ba ‘karamin shape ne da ita ba dan irin shape d’insu ake kira da
coca-cola shapes, hannu Clara ta d’aga zata dora akan breast d’in Abla taji anru’ke
mata hannun ta gagam a zuciye ta juya dan ganin wanene , ba kowa bace face Emma da
ta had’e rai tana binsu da idanuwanta kamar na mage da French ta furta “ ca akai ku
dubata ba ku ta’bata ba , duk yar iskar da ta cika kuma ta ta’bata tagani” ta
‘karasa zan canta tana zama kan gadon , wani irin haushi da ba’kin cikine ya kama
clara, mamakinta ma yadda Emma ta saka bakinta akan Abla , kowa a gidan ya sanı
Emma bata da mutumci bata shayin kowa sannan bata shiga sabgar kowa , shiyasa kusan
gabaki d’aya tsoran ta suke ji hatta mom wani lokaci tana shakkar tunkaranta, d’an
d’aga mata kai Mila tayi daman tafi kowa tsoran Emma “ yes clara dubata kawai
zamuyi , sorry Emma babu abunda zamuyi mata” ta ‘karasa tana kallan clara alamar
pleading dan ba ‘karamin aikin Emma bane ta lakad’a musu dukan tsiya babu abunda ya
dameta kuma babu Wanda ya isa yayi mata abu, gyad’a mata kai clara tayi suka far
duba Abla , wata Allura Mila ta d’auko tayi mata tare da tsayawa dan ganin reaction
d’in Abla da bata ko motsi , cikin min tuna da basu wuce ukuba nunfashin Abla ya
dawo a fusge lokaci d’aya ta fara bige bige da hannunta kamar tana san sha’ko wani
abu, ga kanta data ki tsayar wa waje d’aya sai faman fusge fusge take kawai tana
kai wa kanta duka , da Sauri Mila da clara sukayi ‘ko’karin ri’keta amma suma Abla
ta fara dukansu murya a sha’ke ta soma fuskar maganarta ga gashin kanta da ya rufe
mata fuska “ karku ta’bani , banaso , me zakuyi mun? Mugaye su wanene ku… me kuke
mun , karku ta’bani” shine abunda Abla take faman furtawa lokaci d’aya kuma kuka ya
kwace mata amma duk da hakan ta ‘kiyin shiru , a karo na biyu Mila tayi ‘ko’karin
ta’bata Abla ta kai mata naushi a fuska ga wani irin fusge fusge da take yi kamar
bata cikin hayyacinta , kwalbar hannunta Emma ta ajje tare da kallon Mila “ me ya
sameta ?” Cikin Sauri Mila ta furta ina tunanin cocaine d’in da aka sha’ka mata da
allurar mayen da sukai matane ya ta’bata cikin kwana uku dole babban likitoci su
dubata idan ba hakaba zata iya haukacewa gabaki d’aya , da alama tana cikin damuwa
sosai sabida yadda zuciyarta take harbawa da Sauri Sauri hakan kuma zai iya janyo
zuciyarta ta buga idan bata nutsuba” , d’an kallanta Emma tayi lokaci d’aya a
rayuwarta taji tausayin Abla ya shiga ranta duk da tsanar wani ‘kasar da ba tata ba
da tayi amma sai take ganin har cikin zuciyar ta ranta ya ‘baci akan abunda akai
wa Abla , ji take da zata ga wad’an da sukayi mata haka babu abunda zai hana ta
gutsits tsira naman jikinsu da ransu , fusge fusgen da Abla take yine yasa ta zauna
sosai akan gadon tare da rirri’ke Abla duk yadda take fusge fusgenta haka Emma ta
ri’keta , Abla tun tana dukan Emma tana shuri da ‘kafarta har tayi shiru sai
kukanta da yake tashi kad’an kad’an, kallansu Emma tayi kafin ta furta “ me zakiyi
mata yanxu?” Wata ‘karamar Allura clara ta nuna mata “ ragowar allurar da zaisa
jikinta ya d’an saki na lokaci za’ai mata ko hankalinta zai dawo jikinta nan da
5hours , idan Jininta yana da kyauma cikin 2 hours zata dawo Daidai Indai zata
kwantar da hankalinta “ gyad’a mata kai Emma tayi , allura clara ta d’auko ta
sirawa Abla , yadda ta tsira matanne yasa abla sakin ‘kara tana ‘ko’karin kwace
jikinta amma Emma ta’ki sakin ta su biyu sai faman kokawa suke tsawan mintuna uku
suna abu d’aya kafin Abla ta soma sakin ajiyar zuciya , sai a lokacin itama Emma ta
saki a jiyar zuciya tare da kwantar da ita sosai akan gadon , gashin kanta da ya
rurrufe mata fuska Emma ta gyara mata , sosai kyakykyawar fuskar Abla tayi fayau da
ita kamar wacce tayi shekara tana rashin lapiya ga fad’awa da tayi kad’an hawayene
kawai ke sakkowa daga kan fuskarta, har sun juya zasu fita Emma ta dakatar da Mila
“ ku dafa mata abunda zataci sannan ku siyo mata kayan da zata sa” cewar Emma , “
okay” mila ta furta zata sake juyawa Emma ta ‘kara dakatar da ita “ karki siyo mata
irin namu, dogaye Marasa kama ciki zaki d’akko mata”, yanxu ma “ okay”Mila tace
mata tana barin d’akin lokacin har clara ta bar d’akin . Tsayawa kallan Abla Emma
tayi sosai take kallan face d’in Abla da yadda bakinta ya bushe sai lokaci zuwa
lokaci tana juya kanta , wani lokacin kuma sai ta d’an furgita, har Emma zata bar
d’akin sai kuma ta fasa , kankujerar da take d’akin ta koma ta zauna akai tare da
kunna headphone d’in kunnanta tana sauraran wa’kar selena Gomez .

🍃🍃🍃🍃🍃🍃

NEW YORK

Tsaye little yake cikin basket ball da suke bugawa shida prince sai sojojin da suke
cikin wajan a tsats tsaye , jikinsa sanye yake cikin coffee colour d’in kayan sport
, kusan iri d’aya ne kayan jikinsu shida prince dan shima coffee d’in kayane a
jikinsa na sport sai faman sakin dariya yake ganin yadda little ya d’an ‘bata
fuskar sa , cikin d’an sauri sauri ya ‘karaso Inda yake a tsaye “ wai wannan ‘bata
fuskar da kake yi na Menene kuma ?” Shima cikin d’an rad’a rad’a little ya furta “
kalli fa abunda suke mana , wannan ai zalincine munfi 1 hour muna ball d’innan amma
sabida mugunta sunga yaya bobo da yaya big boss basanan shine suke mata mugunta,”
kafad’arsa prince ya d’an ta’ba kafun ya furta “ don’t worry muma ya kamata Musamu
‘yan team mu rama abunda suke mana” gyara tsayuwarsa little yayi yana bin face
d’insu da kallo kafin ya ta’be baki , “ yaya Prince Allah kasan da ace ni d’an
biyune da babu abunda zai hana nayi musu mugunta duk sai suna bacci zasuga kunamu,
yan banza kawai”, yanxu kam dariya sosai prince yake masa cike da sha’kiyanci,
gyad’a masa kai little yayi kad’an kafun ya furta “ am coming” , be jira jin amsar
saba ya bar wajan , sojojin da suke buga basket ball d’in dasu gabaki d’aya suna
tsaye suna jiran ganin reaction d’in little ganin ya bar wajan, ko minti 5
cikakkiya little beyi ba ya dawo bayan sa su bruno ne ko wannansu harshan sa a
bud’e , sakin baki Prince yayi yana Kallansa kafin ya d’an hararesa “ me zamuyi
dasu da ka d’akkosu? Please kamayar da su kasan halinsu mugayene Dan rai nan
sojojine” shafa kan Bruno little yayi kafin ya furta “ yaya prince kamanta lokacin
da nake ‘karami? Lokacin ban iya basket ball sosai ba , yaya bobo da yaya big boss
suka koya mun? Kamanta simba da su Bruno duk ankoya musu wad’annan abubuwan ?” ‘Dan
hararar Bruno prince yayi kafun ya furta “ kasan ba koda Yaushe nake san ganinsu ba
kasan halin wa’yan nan karnukan”, sorry dis once Kawai fa” little ya bashi amsa ,
yanxu gyad’a masa kai prince yayi batare da ya furta komai ba , fito little yayi
musu take a wajan suka soma girgiza kansu suna bud’e harsunansu, kamar almara
little ya sakar musu ball da sun je daidai wajan da sojojin suke zasu bud’e musu
farcinansu kamar zasu ya kushesu , cikin Sauri sojojin zasu kauce su kuma su little
su saka ball d’in su , sau biyu suna muku hakan , sosai kuma hakan yake saka prince
da little cikin nishad’i su kad’ai sai faman sakin dariya suke , dariyar suce ta
tsaya ganin yadda sojojin a wannan karan suke kauce wa su bruno duk yadda suka so
dakatar dasu , yanxu wani irin fito little ya sakar musu me ‘kara da sunzo inda
sojojin suke zasu hankad’asu su fad’i ’kas , gabaki d’aya a maimakon ai ball sai
bruno suka dunga fad’ar da sojojin dan sosai akai training d’insu Bruno ko
operation za’a fita da su Bruno ake fita dansu kansu sojojine kuma sosai ake biyan
su ma’kudan kud’i dukda kasancewarsu karnuka amma sojojine su , ba ‘karamun horo
suka shaba kuwa , little da prince tun suna dariyar abunda su Bruno suke har little
ya tsugunna sabida dariya , musamman yadda Roby da Bruno suka had’u waje d’aya
idan sun fad’ar da soja d’aya sai su hau kansa suyi ta tsalle, wallahi sosai
karnukan bobo suka jigata sojojin nan , little tun yana dariyar mugunta har ya so
Mayin Murmushi tare da dakatardasu , cikin d’an dariya dariya little ya furta “
next idan kuka cigaba da cin mu simba zan d’auko yayi mun filla filla daku wlh” ya
karasa yana sakin dariya , ‘keyarsa prince ya d’an duka “ wallahi little baka ji”
little bayasan ana ta’ba masa gashi idan ba big boss ne ko yaya bobo ba sai kuma
uncle da prince dukda wani lokutan idan prince ya ta’ba masa gashin zai fara mita ,
yanxu ma bakinsa ya d’an ta’be kamar zaiyi kuka yazo zai ta’ba gashin prince ,
prince yayi saurin gocewa , hakan da yayi ne ya ‘kara har zu’ka little shi a lalle
sai ya ta’ba gashin prince , lokaci d’aya suka fara yar guje guje tunda sunsa ba
yanxu su big boss zasu shigo cikin gidan ba .

( wa d’annan yaran bakwaji Yasin 😦🙄🥱)…..

✨✨✨✨

*KANO*

Lokacin da Dady ya dawo ya dawo tuni baby tayi bacci gashi Sosai ya siyo mata
abunda ta bu’kata har abunda batace ba dady ya siyo mata , gabaki d’aya sai ajje
mata a fridge akai , ko tunanin a siyowa Eshaal basuyi ba , suka zauna suka ci
kayan makwalashen da Dady ya siyo kafun su wuce part d’insu .

WASHE GARI

Ana kiran sallahr asuba Eshaal ta farka , wanka tayi ta canza kayanta zuwa wasu
kafun ta tayar da sallar asuba d’inta , tana id’arwa ta bud’e alqur’anin ta tasoma
karatun ba’kara saida ta tabbatar tayi izufi biyu tukunna ta ajje shi, ko cire
dogon hijab d’in jikinta batayi ba ta fito falo a Daidai lokacin da AMMA ta fito
falourn ita jikinta sanye da hijab , har ‘kasa Eshaal ta tsugunna ta gaisheta kamar
yadda ta saba , murmushi AMMA ta sakar mata “ kin tashi lapiya ?” Lapiya Lou Amma
hope kina lapiya“ cewar Eshaal ta furta wa AMMA a shagwa’be , d’an murmushi AMMA ta
‘karasakar mata “ lapiya Lou “, itama Eshaal martanin murmushi ta mayar wa da AMMA
tana mi’kewa ganin AMMA tana ‘ko’karin nufar d’akın Baby “ ah ah AMMA ki barshi
yanxu zanje na tayar da ita” bata jira amsar AMMA ba tayi saurin wuce sabida
ba’karamun aikin baby bane tayi mata wula’kanci shiyasa ita zataje kome Baby zatayi
mata da sau’ki akan tace zatayi wa AMMA , tana shiga kamar ta sani BABY na cikin
blanket ta lullu’be jikinta ga ubansanyin da yake tashi cikin d’akin ko tiles
‘kafarka ta ta’ba sai kaji sanyi ta ko ina Ac hurowa take , a hankali ta ‘karasa
wajan gadon baby tare da ta’ba pillow d’inta “ Baby ?” Shiru bata amsa mata ba “
baby” Eshaal ta ‘kara kiran sunanta amma babu reply , akaro na uku da ta kiratane
baby ta d’an motsa batare da ta furta komai ba “ Baby Kitashi lokacin sallah yayi
fa” wani dogon tsaki baby taja tana ‘kara jan blanket d’inta “ dallah malama ki
fice mun daga d’aki ke wace iriyar mayyace wai ? Inaruwanki idan nayi sallah ko
banyi ba bana san shish shigi, wallahi idan baki fita ba akan wacce matar zan
wuce , shashasha kawai” cewar baby , Eshaal ta san tabbas zata iya aikata abunda
yafi hakan ba shiyasa kawai ta girgiza kanta ta fice daga cikin d’akin.
Tana fitowa ko afuska bata nuna wa AMMA ba ta soma te maka mata da ayyukan
gidan daman kusan kullum haka suke tare suke gyaran gidan , abinci ne kawai Eshaal
take yiwa su baby dan tasan halin wula’kancinsu, saida ta kammala komai tukunna ta
wuce kitchen ta soma girka musu breakfast , cikin ‘kan’kanin lokaci ta kammala ,
tana duba agogo taga ‘karfe 9:30am , ganin su baby basu fito bane yasa ta zuba musu
nasu a cikin plate ita da AMMA , ta kai musu , duk yadda AMMA taso ‘kinci sai da
Eshaal ta saka ta taci , suna gamawa Eshaal ta je ta wanke plate , sai a lokacin su
baby suka fito , kallan eshall baby tayi tare da ta’be bakinta “ Malama kizo ki
zuba mun abinci ba canai ki bini da idanuwa ba” banza Eshaal tayi mata zata
tsugunna ta gaishe dasu dady kawai taji ya jefo mata wani ‘karamun envelope yana
dakatar da ita “ bana bu’katar jin komai , gashi kar akaini bakin duniya , saura
sati d’aya ku koma u.s “ sosai farin ciki ya bayyana a fuskar Eshaal dan har wani
murmushi take yi , wani ‘hangare na zuciyarta kuma tana yi mata ba dad’i sabida
zata bar AMMA , rai a ‘bace baby ta kalli dady “ dady wai kana nufin tare da wannan
banzar zan koma school ,gaskiya wallahi bazan yardaba , babu inda zan koma da ita”
tana kai ‘karshen zancanta ta wuce fuuuu rai a ‘bace , itama momy tsaki taja wa
dady tare da bin bayan baby da Sauri , Eshaal kuwa ko a jikinta , zatayi wa dady
Godiya ya daka mata tsawa akan tabar masa falour , da sauri kuwa ta d’auki envelope
d’inta tabar d’akin.

✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨

**NEW YORK**

9:30pm motocin su Big boss suka shigo cikin gidan , cikin sauri sojojin su sukai
layi har motocin su big boss suka shigo cikin compound d’in gidan , da Sauri Victor
da Anthony suka fito daga cikin mota suka tsaya a Daidai kofar motar su big boss,
lokacin gabaki d’aya ragowar sojojin sun fito suna jiran fitowar Oga big boss ,
kusan mintuna 5 kafun Victor da Anthony su bud’e musu mota, ko minti 2 bobo beyiba
yafito daga cikin motar banda big boss da idanuwansa suke a kulle bashi da alamar
fitowa daga cikin motar , kusan mintuna 10 big boss yana cikin motar har lokacin
bobo be tafi ba shima yana jiran fitowar sa, sai da ya mula yasha İska (har ya
bushe inji mss Lee 😹😂) sannan ya fito da kyakykyawar farar balarabiyar ‘kafarsa,
still sai da ya ‘kara d’aukan 2 minutes kafin ya fito gabaki d’ayansa , babu Wanda
ya kalla hatta bobo da ke jiransa bai jira saba yayi wucewarsa , girgiza kansa bobo
yayi kawai tare da bin bayan big boss suka jera a tare . Suna shigowa gabaki d’aya
su little suna zaune a falourn suna jiran dawowarsu, bobo kai tsaye inda suke ya
nufa banda big boss da yayi wucewarsa ko nuna alamar da mutane a falourn beyi ba .
Kan little bobo ya shafa lokacin da yake ce masa welcomed back , shima be zauna ba
sai kallan uncle da yake sakar masa murmushi yayi “ uncle barka !” Sai kuma ya
kalli prince da little “ kuma yadda naga kun nitsunnan nasan kunyi rashin ji ,”
kallan juna prince da little sukai tare da girgiza kai lokaci guda d’aya , gabaki
d’ayansu rangwashi ya kai musu kafun ya nufi part d’insa suna furta “ kukai wa big
boss coffee d’insa da fruit” , da ‘karfi little ya furta “ okay sir”, cikin sauri
suka nufi wani waje da coffee maker yake ga wasu abubuwa masu kaloli daban daban ,
a Wajan , sosai cikin kwarewa little ya had’awa big boss coffee sai faman turiri
yake , prince kuwa da kansa ya yanka fruit d’insa , sukayi arranging cikin tray
fari tass Dashi suka nufi part d’insa , rabansu da su shigo d’akin tun d’azu da
suka gyara masa shiyasa amaimakon suji kamshin turaran d’akın sai kamshin turaran
big boss suke ji ta ko ina , kai tsaye ‘kofar bedroom d’insa sukai knocking shiru
ba’a amsa ba , sau biyu suna knocking ba’a amsa ba sai a na ukun sukai shahada suka
shiga. Kamar yadda sukabar d’akin d’azu haka yake yanxu ma sabida duhun d’akin da
suka gani, batare da tsoro ba little ya ‘karasa wajan center ya kunna wani abu take
hasken d’akin ya kunnu tako ina ga sanyin da d’akin ya d’auka kamar zai shiga cikin
‘kashin mutum. Babu kowa a cikin d’akin sai kamshin turaran big boss , akan center
d’in d’akin suka ajje masa tray d’in tare da barin d’akin. Kusan mintuna 2 da
fitarsu shikuma big boss ya fito ba’kin gashin kansa sai faman tsiyayar ruwa yake
kad’an kad’an , jikinsa sanye yake cikin wata ba’kar t-shirt da ta matse masa
hannu, sosai muscle d’in hannunsa suka fito kamar zasu fasa hannun rigarsa ga farar
fatar jikinsa da ta ‘kara haska ba’kar rigar jikinsa , Wanda jikinsa bari tass
dashi me laushin gaske sai white half shoe da yake ‘kafarsa, dogayen ‘yan yatsunsa
sosai suka fito cikin ta kalmin ‘kafarsa. A kan sofa d’insa ya zauna tare da
d’aukar coffeee d’in da su little suka ajje masa , ya d’au mintuna a hannunsa kafun
ya fara shipping d’insa a hankali , sai a lokacin ya janyo system d’in gabansa ,
sosai yake operating a kan da alama wani aiki yake me muhimmanci sosai , har ya
shanye coffee d’in hannunsa ya ‘kara zuba wani be gama aikin da yake ba dan ko
fruit d’in da aka ajje masa be soma cıba , saida yasha 4 cup of coffee tukunna ya
ajje cup d’in , wasu short number ya danna cikin dan’kareriyar wayar sa cikin ‘yan
seconds aka d’aga wayar be jira jin abinda za a ceba ya furta “ operate on it” sai
kitt ya kashe kiran batare da ya jira jin amsar wanda ya kira ba .

✨✨✨✨✨
CANADA

HALIFAX..

Saida Abla tayi kusan 3 hours tukunna ta bud’e idanuwanta a hankali sai faman sakin
ajiyar zuciya take tana bun d’akin da take ciki da kallo , da Sauri ta mi’ke zaune
tana ‘ko’karin tashi tsaye EMMA da ta ‘karaso Wajan tayi saurin dakatar da ita ,
bangajeta Abla tayi da Sauri ganin matar da bata ta’ba gani ba , “cike da tsoro ta
furta wacece ke? Me nayi muku” bakinta har rawa yake ta soma jin jikinta , kallan
kallo suka fara tsakanin ta da Emma ganin bata fuskantar abunda take cewa da French
EMMA ta furta “ babu abunda zan miki ki kwantar da hankalinki” binta da ido kawai
Abla tayi jikinta sai faman rawa yake ganin bata fuskantar abunda EMMA take cewa ,
itama Emma fahimtar hakan hakan yasa ta dakata da hannu ta soma mata alama kafun
cikin turanci ta furta “ babu abunda zan miki” sai a lokacin Abla ta saki jikinta
dukda hakan bata bari Emma ta ta’ba taba , tray din gabanta emma ta ajje mata da
Sauri ta saka hannu ta d’ibi abincin ko loma d’aya batayi ba ta amayar dashi ganin
gabaki d’aya babu test cikin abincin ga ‘karnı da d’anyen abinci da taji abakinta
kamar zata kwayar da ruwan cikinta amma babu abunda ya fita daga cikin ta , sosai
hakan ya bawa Emma tausayi shiyasa ta janyo plate d’in fruit ta mi’ka mata , yanxu
kam da sauri Abla ta karba tare da komawa nesa da Emma sosai ko tsayawa batayi ta
dunga tura fruit din cikin bakinta , sai data cinye duk yawan fruit d’in dake cikin
plate sannan ta soma ajiyar zuciya , ganin tasha fruit din sosai yasa Emma kwashe
tray din tare da nuna mata bed yanxu ma da turanci tace mata ta kwanta , tana kai
karshen zancanta ta kunna mata Ac tare da ‘ko’karin kashe light , cike da tsoro
Abla bata san lokacin da ta furta “No”, murmushi Emma ta sakar mata kafin ta furta
“ okay goodnight” . Tana barin d’akin Abla ta takure jikinta sabida yadda ta fara
jin sanyi na ratsa mata jiki , ita kadai sai Faman bin d’akin take da kallo ganin a
rayuwar ta bata ta’ba shigowa cikin d’aki irin haka ba , yadda taji sanyi na
ratsatane yasa ‘kara bin dakin da kallo ko akwai wani aciki ganin babu kowa a ciki
yasa tayi saurin Jan ‘karamin blanket d’in gadon ta takure jikinta dashi a’kasa
sabida jin wani irin sanyi da bata ta’ba Jiba ko a gidan uwar karuwai. Sosai sanyin
d’akin ya soma sakata lumshe idanuwa Sabida yadda hakan ya fara yi mata dad’i , tun
batasan lumshe idanuwanta har take lumshe su , cikin kankanin lokaci baccin da ta
dad’e batayi irin saba ya d’auketa ga sanyin Ac da yake ratsata sosai .

WASHE GARI

Wajan 11amm su Mila gabaki d’aya suka shigo cikin d’akin har da Mom , yadda
suka ga Abla ta takure a ‘kasa yasaka gabaki d’aya Jan burki , ita kad’ai sai faman
jujjuya kanta take , tray d’in fruit din hannunta Emma ta ajje tare da karasawa
inda Abla take , tana ta’bata Abla ta farka a firgice , lokaci d’aya ta soma bige
bige da Sauri Mila ta bar d’akin itama Emma ta soma ‘ko’karin riketa ganin lokaci
d’aya ta ‘kara bir kice musu kamar zasu shid’e mila tana dawowa bata tsaya bin
shawararsuba ta yiwa Abla allurar bacci, cikin kankanin lokaci jikin Abla ya ‘kara
saki , rai a’bace Emma ta furta “ me kikai mata”, d’an kallanta Mila tayi kafun ta
furta “ wannan shi kad’ai ne best solution idan ba haka ba ranta yana cikin
hatsari” dakatar dasu mom tayi “ wannan ba wani abu bane , yanxu abunda nake so
daku just ku wanke mata kanta ku gyara masa nails d’inta naga sai ku saka mata
wancan gown zuwa anjima” ta ‘karasa tana nuna musu red gown d’in da bata da tsaho
sosai. Hakan ce kuwa ta faru mom na fita suka d’auko d’auki Abla suka shigar da ita
toilet , sosai suka wanke mata kanta da yayi mugun datti , dukda haka basu wanke
shi ya futaba, sama sama suka wanke shi dan suma basu saba yi ba yi musu ake ,
Clara tana ‘ko’karin taba zip din Abla , Emma ta dakatar dasu akan babu Wanda zai
cire mata kaya, haka suka gyara mata nails d’inta sosai yan yatsun ‘kafarta sukai
mata kyau ba kad’an ba , ga gashin kanta da bakinsa ya ‘kara fitowa dukda dattin sa
be tafi duka ba . Suna gamawa mai kawai Emma ta shafa maka akai tare da taje mata
uban tukun gashin Abla ganin lokaci d’aya cikowarsa ya fito sosai Sabida babu
murd’ewar da yayi ba tare da sun tufke mata ba suka kwantar da ita suka bar d’akin
gabaki d’aya .

Karfe 4:30pm Emma ta shigo cikin d’akin Tasha kwalliyar ‘kananan kaya, tun d’azu
take zuwa duba Abla ganin haryanxu bata farka ba , kallan innocent face d’in Abla
tayi tasan a shekaru zata bawa Abla kusan 15 years ganin fuskar yarinta tattare da
ita , gown d’in kan gadon ta d’auko tare da d’auko wani towel ta d’aurawa Abla a
cikin rigar ta , kafun ta samu ta cire wa Abla rigarta idanuwanta a kulle , red
gown d’in ta saka mata tare da cire mata town d’in , sosai tsinin nipples d’in Abla
ya fito rigar dukda rigar tana da kauri sosai mata nuna shafe amma dukda hakan sai
da tudun nipples dinta suka fito , yanxu ma kugunta ta saka towel kafun ta cire
mata skirt d’inta , lokaci d’aya fararan santala san talan ‘kafarta suka fito sosai
kasan tuwar da kad’an rigar ta wuce mata gwiwar ‘kafarta, red ribbon Emma ta d’auka
ta tufke mata gashin kanta , duk da yadda fuskar Abla ta fad’a ba ‘karamun bala’in
kyau tayi ba babu Wanda zaiganta a cikin gidan uwar karuwai yace yasanta sabida
yadda tafito fara tass ko wasu fararar bazasu nuna mata lapiyar jiki ba duk da bata
taso cikin gata ba . Wani white top d’in riga Emma ta saka mata daga sama ganin
haka Kawai taji batasan jikin Abla ya fito , tana gama wa ta kira Mom , sosai kuwa
taji dad’in ganin Abla , yadda taga kyanta ya ‘kara fitowa sosai hakan ya daki
zuciyarta , sai faman washe baki take dan tasan ba’karamun kudi zata Samu ba .
5pm ta saka su Mila d’auko mata Abla , Emma taso binsu Amma mom ta hana
hatta su Mila suka saka ta acikin motar ta ce musu badasu zataje ba duk yadda suka
so binta , bata bari sun bita ba , yan matan ta kawai ta d’iba cikin ‘kan’kanin
lokaci suka kama hanyar pacifico. 45 minutes ne ya kaisu wajan dukda kusan sun
kusan barin gari ga wani lungu da suka dunga be wajan kana ganinsa kasan matattarar
yan daba ce a Wajan haka yan matan nan suka yafawa Abla wani kyalle da ya rufe mata
duka cikinta suka kinkimeta,su da mom haka suka dunga ratsa lunguwan wajan har suka
so matattar ‘yan daba da wasu irin fitilu sai tashi suke , saida suka cajesu da
wani abu Tukunna suka barsu suka shiga bayan wani farin bature ya bisu jikinsa duk
tatoo , haka suka dunga ratsa yan baba aciki har suka ‘karaso wani waje da kid’a
yake tashi , sosai kid’a yake tashi bana wasa ba , wasu manyan yan matane da kana
kallansu kasan suna d’aga ‘karfe d’aya daga cikinsu ta dauki abla tare da musu nuni
akan su biyosu, hakan ne kuwa ya faru Daidai wajan wasu maza farare dasuke zaune
wasu yan mata duk akan cinyarsa ta sauke Abla a inda masu yan matan suke da alama
suma duk kamasu akai , cikin wani yare mom ta soma magana tana washe baki , yadda
mazan wajan suka kyalkyale da dariya ne ya bani mamaki , akan kujerar da wasu mata
suke zaune da alama su ma kamar tane dan kowannansu ya ci adın kananan kaya ya
shisha da sigarı da suke zu’ka. Da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai aka fara zakulo yan matan
ana nunawa mazan nan , duk namijin dayaga dama hakan zai bi jikinsu yana ta’basu
sai kuka sukeyi ko wannansu, cikin rashin İmanı suke ta’basu wasu har yaga musu
kaya suke ko su mare su , taka Abla da akai ne ya farkar da ita daga Allurar da kai
mata , cike da tsoro ta soma bin wajan da kallo musamman yadda taga yan mata a
gabanta sai kuka suke ko waccensu a d’aure , da sauri ta raku’be jikinta sabida
yadda yake rawa cike da Tashin hankali . Yadda ake zakulo mutanan nan ne yafi komai
d’aga mata hankali , sosai suke wa yan matan rashin mutumci musamman yadda suke
ta’ba jikinsu tako ina , ‘katuwar matarnance ta finciko Abla tare da tsinka mata
mari da ya saka Abla sakin ‘kara lokaci d’aya kanta soma juya mata ta saki wani
irin gigitaccen ‘kara , yadda santa santalan’kafarta yake yawo cikin rigar
jikintane yasa kowannansu ya fara sakin dariya cikin Sauri aka fara cinikin Abla
hakan ba ‘karamin mamaki zai baka ba , a Daidai kusa da mazan matar nan ta kawo
Abla , d’aya daga cikinsu ya d’aga hannu zai ta’ba bom bom din ta yaji kamar wani
abu ya gifta , lokaci d’aya kuma ya saka wani irin razanniyar’kasa Sabida yadda
yaga hannusa a ‘kasa alamar an yanke masa hannu ga ‘karar harbi da ya soma ji tako
ina , a gigice cikin wani irin azaba da be ta’baji ba ya ware muryarsa tare da
sakin wani irin ihun azaba .

( Allah shi’kara🥱🥱🥱🥱)

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya
lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your
mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to
the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
S____20💞

Lokaci d’aya gabaki d’aya wajan ya harzu’ke kowa ya soma ‘ko’karin cecar kansa ,
Harbin da yake ta shine yafi komai rikita mutanan cikin Wajan hatta wanda aka
sarewa hannu fad’uwa yayi a ‘kasa sumamme, Abla kuwa tuni farar baturiyar data
ri’kota ta hankad’ata Kanta ya bugu da jikin wani center ga mutane da suka dunga
tattakata, ana cikin guje gujen har wani abu ya fad’o mata da gabaki d’aya ya
rufeta ba’a ganinta.
Wani ‘kwararran harbi aka saka guda d’aya lokaci d’aya gabaki d’aya kowa na wajan
ya tsaya, musamman turawan nan da suka fi shiga Tashin hankali , hatta mom da tayi
‘ko’karin guduwa saida ta samu harbi a ‘kafarta, shiyasa kowa ya ‘kara rikice wa ,
wasu mutanene suka shigo cikin wajan gabaki d’aya ba’a ganin fuskokinsu sabida
shigar ba’ka’ken kayan dake jikinsu , cikin kakkausar murya d’aya daga cikinsu ya
furta “ Every Body kneel!” Yana kai ‘karshen zancansa masu ba’ka’ken kayan nan suka
saita su da bindugogin hannunsu, lokaci d’aya turawan nan sukai kneel down tare da
Mayar da hannayensu zuwa kansu ko wannansu ya sunkuyar da kansu , hatta su momy
irin abunda sukayi Kenan , matan da aka kama kuma suka cunkushe waje d’aya suna
kuka , d’aya daga cikin su me sanye da ba’kin face mask ne ya cire p-cap d’in kansa
, take a wajan mutanan nan suka sara masa , hannu ya saka tare da zare facemask
d’in fuskarsa bakowa bane face Bobo sanye da wasu ba’ka’ken Kaya , wandan jikin sa
duk bindugune a jiki ga wasu irin abun tashin bom da yake sanye dasu, fuskarsa
gabaki d’aya babu fara’a kamar ba bobon da yake yawan murmushi ba , rai a ‘bace ya
furta “ Arrest them all “ cikin Sauri d’aya daga cikin mazan ya dashi da niyar
guduwa Bobo ya harbeshi a ‘kafa tare da karasowa inda yake , hannunsa d’aya ya
dungule ya kaimasa naushi da har saida guy d’in ya saki ‘kara ganin yadda Jini ya
fara fito masa daga hanci, a zuciye bobo ya ri’ke hannusa d’aya ya juyar dashi
tare da kaiwa hannun naushi , lokaci d’aya kashin hannunsa ya bada sautin ‘kas
kamar na karyewar abu, sosai ya fara ihu yana girgiza wa bobo kai ganin bobo yana
‘ko’karin karya masa d’ayan hannun , cikin azaba ya fara furta “ I surrender! I
surrender “ ya dunga furtawa da’karfi sabida azabar ‘balla masa hannu da bobo yayi.
Yana juyawa gabaki d’aya masu sanye da ba’ka’ken kayannan suka soma kamasu, cikin
sauri Robert ya ‘karaso inda yake , batare da ya furta komai ba ya nuna side d’in
da matan nan suka cinkushe waje d’aya , “ yes sir” cewar Robert , tafiya Bobo ya
somayi kafin cikin kakkausar murya ya basu umarnin su ‘kona gabaki d’aya wajan .
Hakan ne kuwa ya faru gabaki d’aya mutanan nan saida aka kama hatta mom da take
kuka akan da ma batazo wajan ba gabaki d’aya sun ‘kara rikicewa musamman da sukaga
za’a ’kona musu wajan da yafi shekara 20 da ‘kungiyar su take zama , hatta guy din
da bobo ya ‘ballawa hannu da Wanda bobo ya guntulewa hannu Haka captain yajasu a
‘kasa babu ko d’igon tausayinsu a fuskarsa . Wasu matane suma sanye da ba’ka’ken
kaya suka ‘karaso inda yan matan nan suke ,hannu d’aya daga cikinsu tasaka ta yaye
abun fuskarta, ba kowa bace face LG Laura j.richardson Itama gabaki d’aya jikinta
sanye yake da bindigu ga wasu ‘kananan binduga da ta ri’ke a hannunta “ Let’s go”
shine abunda tace musu , da Sauri kuwa yan matannan suka tashi suka soma bin
bayansu bayan su Robert sun fitar da su mom, suna fita daga wajan su Robert suka
sakawa wajan wuta . Sosai wajan ya soma ci da wuta ga Abla da take kwance sai a
lokacin ta farka yadda taga wuta na ci tako inane yasa ta mike a zabure tana neman
hanyar fita amma duk inda tayi ‘ko’karin saka ‘kafarta sai wajan ya ‘kara ci da
wuta sosai tsoro da tashin hankali ya kamata da ta soma neman zaucewa babu abunda
take furtawa sai ya Allah sabida yadda haya’ki keshigar mata cikin hanci ta ko ina
wutace take kamawa sosai gabaki d’aya sai ta hargitse tarasa hanyar fita , ganin
bata da wata mafitane yasa ta fashe da kuka .
A waje kuwa gabaki d’aya cikin wasu ba’ka’ken motoci aka soma saka turawan nan ,
matan kuma LG laura ce take nuna musu motocin da za’a saka su, ga bobo da yake
tsaye hannunsa kare da wayarsa da alama waya yakeyi. Ana cikin saka ‘yan matan nan
a cikin mota bobo ya soma jin hayaniya na tashi kad’an kad’an, da ido yabi wajan
gani wata budurwa na ‘ko’karin karasowa amma sojoji sun hanata , ita kuma ta dage
akan sai ta shigo , hannu kawai ya d’aga musu , cikin Sauri suka matsa mata , ba
kowa bace face Emma da ta ‘karaso Wajan sai faman haki take fuskar ta tayi ja sosai
alamar kuka ta gama yi , cikin d’aga murya ta soma nuna musu cikin wajen da ya
soma ci da wuta sosai “ She’s inside ! She’s inside” shine kad’ai abunda bakinta
yake iya furtawa , kallan wajan bobo yayi kafun ya kalleta “ who’s inside ?” Ya
tanbayeta, girgixa masa kai ta ‘karayi cikin turanci ta furta “ ba su kenan ba
akwai ragowar macen da aka kawotanan , bata cikin yan matancan, please ku temaka ku
ceci ranta” kallan robert yayi alamar ‘karun bayani , cikin girmamawa Robert ya
furta “ sorry sir bamuga kowa ba a ciki shiyasa muka kunna wa wajan wuta” da karfi
bobo har yana dukan motar gabansa ya furta “ are you guys fool? Me yasa baku
bincika sosai ba ?”, sorry sir” gabaki d’aya suka furta cikin tsantsan girmamawa,
batare da ya kallesu ba ya ajje phone dinsa akan motan tare da bud’e bayan wani
boot ya ciro wani ba’kin Abu kamar blanket , cikin sauri sojojin nan suka d’auko
wani abu baki suka barbad’a masa akai suma suka d’auko nasu gadan gadan sojojin nan
suka tunkari shiga cikin wutar amma tun kafun su ‘karasa wajan wutar tayi wani irin
‘karan sauti ga yanda ta huro sosai kamar wacce ake ‘kara hurata, duk yanda Suka so
shiga cikin wutar basu samu wannan chance dinba sabida yadda wuta take ci sosia ,
Bargon hannunsa bobo ya karba ya saka a jikinsa zai shiga ciki gabaki d’aya
kowannansu lokaci d’aya ya furta “ sir” dan wallahi Suka bari bobo yashiga cikin
wutarnan ko me yasamesa big boss bazai d’agawa kowa ‘kafa ba shiyasa hakan ya ‘kara
razanasu ganin bobo yana ‘ko’karin tunkarar wajan, hankad’o ‘kofar wajan da akai da
‘karfine yasakasu gabaki d’aya tsayawa , cikin sauri sauri ya soma takowa gabaki
d’aya lokaci d’aya suka ‘kame sabida tsantsan mamakin ganinsa , duk da ba’a iya
ganin jikinsa ko fuskarsa Sabida facemask d’in dake face d’insa amma duk Wanda yaga
sar’kar diamond d’in wuyansa ya shaida shid’inne ba wani ba, jikinsa sanye yake
cikin ba’ka’ken kayan chanel ya nannad’e hannun rigar t-shirt d’in rigarsa da ya
bawa farin hannunsa da bracelet d’in hannunsa guda uku fitowa ras dashi, daga
kafad’arsa kuwa doguwar coat d’insa ce ‘baka da d’an tudu a jikinta kamar Wanda ya
d’auko wani abu, gabaki d’ayansu kasa motsawa sukai daga inda suke sai ‘kara shiga
taitayinsu da sukai musamman yadda ko d’ago face d’insa bayayi , hakan na nufin
kuskure ya ke jira mutum d’aya yayi tak a cikinsu , hatta bobo mamakin ganinsa ne
yasa ya kasa motsawa dukda yasan ‘karamin aikin big boss ne wannan . Babu Wanda ya
kalla a cikinsu tun da ya soma taku gabaki d’aya sojojin wajan suka bashi hanyar
wucewa kowa yana jiran wucewarsa, hatta LG laura sosai ta zuba masa idanuwanta
kamar zata had’iyeshi musamman kafad’arshi kamar Wanda ya d’auko mutum lokaci d’aya
taji saukar harbi adaidai saitin face d’inta da ya sakata ‘kamewa cikin Sauri ta
sunkuyar da kanta dan tasan ko wanane yayi mata haka. Bata gama fad’awa shock ba
sai lokacin da coat d’in Big boss ta d’an zame take awajan dogon gashinta yafito
sosai har yana ‘ko’karin rufe masa fuska , d’an ‘karamun tsaki yayi lokacin da
Victor ya bud’e masa motar Bobo, batare da ya kalli fuskar wanda ya d’auko ba kawai
ya jefata cikin motar tare da coat d’in da ya lullu’beta, d’an d’agowa yayi kad’an
ya zubawa bobo eyes d’insa da suka farayin ja na ‘bacin rai kafun ya juya cikin
takunsa na izza ya shiga farar Audi Rs d’in da Anthony ya bud’e masa , cikin Sauri
Victor da Anthony suka shiga cikin motar tare da barin wajan cikin mugun speed .
Sai a lokacin Bobo ya kalli car d’insa da Big boss ya jefa masa wacce ya
d’auko daga kallan idanuwansa da yayi ya tabbata ran sa a ‘bace yake, gashin kansa
ya shafa tare da nufar motar cikin sauri Robert ya bud’e masa , a kwance take
fuskarta tayi rigingine sabida yadda dogon gashin jikinta ya rufe mata fuska,
hannunsa d’aya ya saka ya d’an yaye gashin take a Wajan kyakkaywar fuskar Abla ta
fito rass da ita , sosai zuciyarsa ta buga lokaci d’aya daya kalli fuskar Abla,
rigar jikinta ya kalla ganin coat d’in Big boss sanye a jikinta gashi ko alamar
motsi batayi, shikansa saida yayi shock d’in ganin coat d‘ in amma ya sani big boss
akansa zai huce ‘bacin ransa sabida d’auko Wanda shi kansa yasan big boss ko kusa
be kalli face d’inta ba, hannunsa d’aya ya kai wajan hancinta amma gabaki d’aya
nunfashinta baya fitowa da alama suma tayi gabaki d’aya sabida yadda eyes d’inta
suke a kulle ga innocent face d’inta da ya ‘kara fad’awa kad’an. Ko me ya tuna oho
sai shima ya d’an ta’be bakinsa sosai kamar zaice LG Laura tazo ta fitar masa da
ita daga cikin mota sai kuma ya fasa , batare da ya kalli Robert ba ya furta
hospital lokacin da yake shiga d’ayan side d’in na motar, cikin ‘kan’kanin lokaci
motocinsa da na sauran jami’ansa suka bar wajan , motar da aka kama turawan nan ma
an tafi , sai motocin su LG da tun fitowar Big Boss ta kasa motsawa sabida yadda
wani irin ba’kin kishi ya kamata ganin wata a kafad’ar Man d’inta ga coat d’insa da
babu macen da ta isa ko ta’bawa amma yau ga wata banza ta samu damar da ta d’auki
sama da shekara goma tana jiran irin wannan damar ko kad’an ce . Sosai kishi ya
kamata takasa ko motsi har saida captain ya ‘karaso inda take “ Lokaci na tafiya”
kamar bazata tanka masa ba , sabida yadda ta kasa motsi sai kuma cikin fusata rai
a’bace ta shiga cikin motocin su tare da barin wajan dan har Emma sai da aka tafi
da ita.
THE QEII HEALTH SCIENCES shine sunan hospital d’in da su bobo suka shigo,
tun kafin motocin su suyi parking wasu doctors mata 2 da namiji d’aya Suka ‘karaso
wajan tare da gadon d’aukar Mara lafiya , da hannu bobo ya nuna musu Inda Abla take
a kwance , cikin Sauri matan nan suka sakata a gadon d’aukar Marasa lapiya suka bar
wajan . Hannu Male Doctor d’innan ya mi’kawa bobo babu musu kuwa sukai shaking
hannu , da turanci doctor d’in ya furta “ wacece ita sir !” , d’an kallansa bobo
yayi na sakanni batare da ya damu da abunda zai furtaba ya furta “ she’s my
sister !” Saurin washe masa baki doctor d’in yayi “ Okay sir , za’a bata kulawa
sosai”, kansa bobo ya jinjina masa kafun ya soma tafiya “ ku bata kulawa sosai ,
zan dawo” , yana kai ‘karshen zancansa ya koma cikin mota Robert ya tayar da ita
suka bar Wajan .

FLASH BANK
Abunda ya faru jiya bayan Big Boss da Bobo sun fita , details d’in wasu yan mata
ne guda biyu da akai kidnapping d’insu a cikin New York , cikin ‘kan’kanin
lokaci bobo ya bincika bayanan yaran har ya samu details d’in ’kasar da aka fitar
dasu , wannan dalilinne Big boss ya basu umarnin zuwa Canada tun a daran jiya ,
shiyasa washe gari da sassafe Bobo dasu Robert sukabar New York , tsakanin America
da Canada tafiyan hour 3 ne a jirgi kasantuwar private jet suka hau 2 hour 20minute
ne ya kawosu kasar Canada . Wannan ne dalilin zuwan su bobo Canada shiyasa kowa
yayi mamakin ganin big boss a ‘kasar dan babu Wanda yasan da zuwansa ko dalilin
zuwan nasa hatta bobo yayi mamakin ganinsa a canada.

******
**********
9:01pm na dare motocin bobo suka danno kai cikin asibitin, Daidai parking lot
motocinsu suka tsaya , cikin Sauri robert ya fito ya bud’e masa mota . A yanxu babu
ba’ka’ken kayan d’azu sabida yanda ya canza dressing zuwa blue d’in wando da white
shirt d’in Riga sai wata white coat dayake sanye da ita sabida sanyin da akeyi .
Tun kafun ya shiga cikin premises d’in asibitin likitan d’azu ya fito cikin sauri
ya ‘karaso Inda bobo yake , cike da girmamawa ya furta “ this way sir”, hakan ce
kuwa ta kasance, bobo be shiga da kowa cikiba sai Robert da yake binsa a baya ,
shima bobo sabida facemask d’in face d’insa ne yasaka ya shiga cikin asibitin,
sabida yadda asibitin ya d’au shiru sai d’ad’d’an kun mutane da suke giftawa. Kai
tsaye floor 5 suka nufa cikin elevator , gabaki d’aya yanda wajan yake ba hayaniya
ko kad’an ya tsarin wajan da ya banbanta da sauran zai tabbatar maka da waje na
musamman suka shigo da bakowa ake iya kaiwa wajan ba , yar tafiya kad’an sukai
kafun suzo Daidai wasu ‘kofofi guda biyu da suke nesa da sauran, tun kafun su shiga
cikin d’akin suka soma jiyo murya kadan kadan daga ‘kofar hagunsu , cikin sauri
doctor ya bud’e bobo ya shiga. Babban d’akin asibitine me girman gaske da kallon
farko da mutum zaiyiwa d’akin zaisan bakowa ake kawowa ‘bangaran ba tundaga kan
yanayin d’akin mutum zaisan a cikin d’akunan ma Wannan Vip ne .
Cikin Sauri doctor da bobo suka ‘karaso cikin d’akin ganin nurses a tsaye
sai faman furta “ calm down” suke Sabida yadda Abla ta burkice gabaki d’aya sai
kuka take tana ‘ko’karin cire ledar ruwan da aka saka mata, ga rigar big boss da
tayi mugun yi mata yawa amma Sabida yadda bata cikin nutsuwarta taki bari a cire
mata balantana Tasha iska . Cikin French doctor d’in yake tanbayarsu abunda yake
faruwa, nurse d’in kusa da shine ta basa amsa da “ Dr taki tsayawa ta kwantar da
hankalin ta, hakan kuma xai iya ja mata matsala a brain d’inta sabida allurar da
aka dunga mata ba Bisa tsari ba “, kallan doctor bobo yayi alamar ‘karin bayani
sabida maganganun nurse d’in nan duk a cikin kunnansa , yana ‘ko’karin masa bayani
Abla ta ‘karasa sakin wani saban ‘kara muryarta har sha’kewa take wajan furta “
karku ta’bani ni banaso, ina ne nan ? Su wanene ku ?” Iya abunda Abla take furtawa
kenan ga gashin kanta da ya rufe mata fuska ba’a ganin face d’inta sosai , ganin
taki na tsuwane yasa bobo ya d’an daka mata tsawa kad’an lokaci d’aya kuwa tayi
shiru kamar ba itaba, a hankali ta d’an d’ago da face d’inta basu sauka ko ina ba
sai akan fuskar bobo da ya tsaya yana kallan ikon Allah , yadda ta tsaya tana
kallansa ga gashi duk ya rufe mata fuskane yasa ya d’an harareta kafun ya nuna wa
nurse akan suyi abunda zasuyi mata , da ‘kyar tabari nurse d’innan ta ta’bata
Sabida ganin yadda bobo ya kafeta da ido, ga tsoro ya kamata sosai ganin fararan
mutane cikin zuciyarta sai addua take ganin kyaun bobo ga shi dukda ba sosai take
kallan fuskarsa taga ko murmushi bayayi, d’an ta’be baki tayi kad’an kafun ta furta
“ mugu da alama maganin mutuwa zasu sakamun, ai gwanda na mutu ma kowa ya Hutu,”
duk wannan zan tukan cikin zuciyarta take yinsu can kuma ta ‘kara ta’bile bakinta
tana had’iye kukan da yake ‘ko’karin fito mata ga tsayuwar su bobo ko nunfashi
sosai taji ja, “ yanxu shikenan uwar karuwai ta siyar dani wajan ‘yan ‘yankan
kai?”yadda bobo ya kafeta da idone yasa ta ‘kara shiga taitayinta gabaki d’aya a
tunaninta bobo shine shugaban yan shan Jinin shiyasa yake kallanta yana Tuna’nın
yadda zai tsotse mata Jini.(😂😂😂wonder shall never end 😂😂 bobo ya zama shugaban yan
shan Jini ).

Kallan Direction d’in doctorn bobo yayi kafun ya furta “ let’s talk” yana kai
‘karshen maganarsa bai jira jin amsar saba ya bar d’akin shida Robert , shima
doctor cikin sauri ya bawa nurse d’in umarnin su kula da ita kafun ya bar cikin
d’akin , koda ya fito be tarar da bobo ba shiyasa yayi Saurin
Bud’e office dinsa da ke facing d’akin da Abla take ciki, a zaune ya tarar dashi
kan kujera yayın da Robert yake tsaye gefensa cikin shigar ‘ba’ka’ken kayansa, tun
kafin ya zauna bobo ya kallesa alamar ‘karin bayani, wani files doctor ya mi’ka
masa yana zama kan kujerarsa “ wannan details din tane, alamu sun nuna tana cikin
matsananciyar damuwa da ta saka wa zuciyar ta , hakan kuma babban illa ne da zai
iya sawa ta kamu da ciwan zuciya , secondly she have stomach ulser , hakan ya
samone daga rashin abinci me lapiya da bata samu , ayyuka masu wuya da kuma rashin
cin abinci akan lokaci hakan ne yasa ta kamu da stomach ulser me mugun hatsarin
gaske da idan ba’a kula da abincinta ba zaiyi affecting kayan cikinta.” Sai kuma
yayi shiru yana tantamar karasa masa zancansa, “ And?” Cewar bobo yana zuba masa
idanuwansa , ajiyar zuciya doctor ya sauke “ alamu sun nuna cocaine d’in da aka
sha’ka mata shine yake ‘ko’karin ta’ba mata kwakwalwarta , sannan akwai allura da
akai mata da ta wuce ‘ka’ida ta maye , sai kuma wata allura last da akai mata me
mugun illa da idan ta ‘kara 2 hours tana bacci bazata ta’ba tashi ba”ya ‘karasa a
hankali yana kallan bobo, cike da mamaki bobo ya furta “Cocaine ? Wannan yarinyar?”
Cikin tabbatar da bincikensu doctor ya furta “ yes sir”, bobo be kuma cewa komai ba
ya tashi tsaye hannunsa d’auke da file d’in Abla , agogon hannunsa ya duba kafun ya
mikawa doctor hannu sukai shaking , kai tsaye d’akin da aka kwantar da Abla bobo ya
‘kara komawa a wannan lokacin an tufke mata gashin kanta , amma yadda ta takure
waje d’aya tana kuka ne zai bawa duk Wanda ya ganta tausayi , duk Wanda yaji sautin
kukanta yasan daga ‘kasan zuciyar ta yake fitowa, yadda take kuka sosai bobo yaji
ba dad’i cikin zuciyarsa da yayi sanadiyar ta’bo masa tabansu da bayasan tunawa a
rayuwa , kujerar da take side d’in gadon ya zauna , yadda take ‘boye fuskarta cikin
rigar big boss da ta kudun dune ne Yaso bashi dariya , musamman dramer da yake
‘ko’karin shiryawa da kaso 90 aciki yasan me wuyane sosai. Gabaki d’aya nuni
Robert yayi wa nurses din akan su fita, suna fita shima be ‘kara one minutes ba ya
bar d’akın yayi saura bobo da Abla kawai gashi ta sunkuyar da kanta ‘kasa taki
yadda ta d’ago da fuskarta ya lura a tsorace take gabaki d’aya , mamakin abunda
doctor ya fad’a game da lapiyar tane ya tsaya masa a rai haka kawai yaji yana san
jin ko wacece ita, da inda iyayenta suke , yafi tsawan 5 minutes zaune a wajan be
tankamata ba , shima Abla bata d’ago kanta va sai ma ‘kara tura kanta da tayi cikin
rigar jikinta. Knocking d’in da akai ne ya bada izinin shigowa , LG laura ce sanye
da wasu ‘kananan kaya a jikinta , gashin kanta ta d’aureshi ta baya sai faman lilo
yake , kallan Abla dake kan bed tayi duk da bataga fuskarta ba taji ranta ya mugun
‘baci lokaci d’aya taji wani irin tsanar Abla ya shiga cikin zuciyarta , ji take
kamar ta kasheta lokaci d’aya ta mutu musamman yadda taga tana ‘kara rirri’ke rigar
big boss a jikinta “ in kin gama kallanta zaki iya bani abunda ya kawo ki?” Cewar
bobo ya furta wa LG da French, da Sauri ta furta “ sorry sir” ta mi’ka masa
‘karamun book d’in da ta shigo dashi , har yanxu zuciyarta ta kasa ha’kura so take
taga wata me zarrarce take ‘ko’karin wasa da ranta , ganin bobo ne yasaka bata d’au
wani mataki akanta ba da tasan har da yarinyar awajan da babu abunda zai saka ta
zuwa , mi’kewar bobo ne yasa ta sara masa duk da ba uniform a jikinta na sojoji,
Daidai bakin gadon Abla ya nufa kafun ya d’an juyo Daidai saitin LG ya furta “
We’re going in not less than few minutes” sara masa tayi tare da furta “ yes sir”
tana juyawa, koda zata bar d’akin sai da ta ‘kara jiyowa ta kalli gadon da Abla
take Kai.
“ Hey !” Cewar bobo yana kalan Abla , da Sauri Abla ta zabura har tana bige
hannunta , yadda fuskarta ta ‘bacı da hawayene yaso bashi dariya , gashi ta wani
zaro masa ash eyes d’inta da ya cika da kwalla , kana ganin yanayin fuskarta zaka
fuskanci ‘kiris take jira ta ‘kara saka wani kukan , “ quel est ton nom ? ( ya
sunanki ?)”, cewar bobo , bin bakinsa da kallo Abla tayi a tsorace ko kwakkwaran
motsi batayi , shi kuma bobo atunaninsa tana Jin French shiyasa yayi mata da yaran
dan Abla gabaki d’aya bata kama da yan Africa,ganin tayi masa shiru tana binsa da
manyan idanuwanta yasa a wannan karan yayi mata turanci “ what’s your name ?”,
yanxu ma shiru tayi masa idanuwanta gabaki d’aya ya cika da kwalla, lokaci zuwa
lokaci tana kallan gefenta, kamar ace mata takkk ta arta a guje , shigowar doctor
ne yasa ya mayar da kallansa bakin door din har ya ‘karaso hannunsa d’auke da wata
farar paper yana mi’kawa bobo, d’an kallan paper bobo yayi yana ‘kara kallan doctor
d’in “ ta samu matsalar maganane?” Girgiza masa kai doctor yayi “ A tsorace take
shiyasa , idan akai mata dole kuma zai sa mata ciwan kai”, kansa bobo ya jinjina
masa , wayarsa da ta d’anyi Haske ne ya sa ya kalla kafun ya nufi kofar fita ,
doctor ma ya bi bayansa, yayi saura sai Abla kawai da ta ‘kara du’kun’kune kanta
cikin doguwar rigar jikin ta da har yanxu ta’ki bari a ta’bata. 5 minutes later
Bobo ya dawo cikin d’akin bayansa LG ce sai kuma doctor da Robert da suka shigo,
yadda LG Laura take kallan rigar big boss kamar taje ta hankad’a wacce take sanye
cikin rigar sa da ko ita da ta sansa sama da shekara 10 ko gashin kansa bata ta’ba
ta’bawa ba sai yau wata yar iska ta nanuke rigarsa kamar zata had’iye , kana kallan
fuskar LG yadda tayi jaa zakasan ranta a’bace yake tana ‘ko’karin dannewa ne
kawai.
‘Dan gajeran murmushi bobo ya saki tare da zama akan kujerar kusa da gadan Abla
da ta ‘kara ta kure jikinta , har zai mata turanci sai kuma ya fasa tuno yadda tayi
Hausa d’azu , hausan da shi kansa yayi mamakin yadda akai ta ‘iya yinsa amma bashi
da lokacin tanbayar yadda tayi shiyasa cikin cool voice ya furta “ ya sunanki?”
Itama Abla da mamaki ta d’ago fuskarta ta zubawa bobo , bata san lokacin da bakinta
ya furta “ shima farin meshan jinin nan ya iya Hausa ?” Da mamaki bobo ya kalleta
sabida maganarta wato d’an shan jini ta d’auketa , “ lalle kina da aiki babba”
cewar bobo cikin zuciyarsa . Be kuma ce mata komai ba ya mike tsaye tare da kallan
LG cikin French ya furta “ ku taho tare da ita and ku rufe mata kanta bansan ganin
gashi a waje , yana kai ‘karshen zancan ya bar d’akin, a zuciye LG ta matso gadon
da Abla take, wani farin yadi da ta gani a ‘kasa ta jefa mata tare batare da
la’akari da yaran da ta iya ba cikin French tace mata ta kulle kanta, dukda Abla
bata gane me take nufi ba itama da Sauri ta d’auki farin mayafin ta yafa akanta
tana ‘kara rike coat d’in jiginta gagam( Ni kam zan so Big boss yaga yadda ake
cakud’a masa Riga ko tsarabar mari ne ta samu😹🥹). LG ta zo zata cire mata rigar
Abla ta ‘kara ri’ke wa gagam musamman yadda batasan aga jikinta, a karo na biyu LG
ta ‘kara saka hannunta azuciye zata cire rigar Abla ta gantsara mata cizo , zafin
da tajine yasa ta tsinkawa Abla mari , itama bata sauke hannunta ba Abla ta daddage
ta tsinka mata mari dama da hannu ( kowa yasan zafin hannun bahaushe ba irin na
bature bane rainan madara da Milo) a gigice ta saka ‘kara sabida zafin marin da
taji batayi aune ba Abla ta ‘kara bata wani tsaraban cizon da ya saka LG ware murya
ta kwala ‘kara , sai kuma ta fara dukan Abla , itama Abla bata ‘kyaleta ba , duk da
yadda LG ta fita girma da ta doketa zata saka hannu ta rama dan tayi al’kawari
kafun su shanye mata jini sai ta Gana musu azaba. Da Sauri a ka tura ‘kofar shigowa
, yadda yaga suna dukan junane yasa bobo ‘karasawa wajan ya ‘ban’bare Abla , be
tsaya wani tunani ba ya d’auke fuskar LG da mari , itama Abla ya d’aga hannu zai
Mareta yaga shatin marin LG a fuskarta shiyasa ransa ya ‘kara ‘baci , hannunta
kawai ya kama zatayi masa musu itama ya daka mata tsawar da yasa ta kame bakinta ,
ko kallan inda LG take beyi ba suka fito daga d’akin, kai tsaye fitowa sukai daga
cikin asibitin d’in gabaki d’aya ,yadda Abla taga zagara zagaran maza ko wannansu
sanye da ba’ka’ken kaya da bindugu a hannunsu yasaka ta soma share hawayenta ,
jikinta har karkarwa yake sabida tsoron ganin ko wannansu da binduga datayi , sosai
kirjinta ya soma sama da ‘kasa hatta tafiyar ‘ko’karin canzawa ya fara tana lumshe
ido, yadda ta soma kakkare wa a bayan bobo tana kulle idanuwanta ne yasa ya d’an
juyo ya kalleta , zai mata magana ta ‘kara firgita zata saka gudu Sabida bindugar
da ta gani a hannun Robert , wani irin juwane taji yana ‘ko’karin kamata , ganin
yadda take ‘boyewa abayansa ne yasa ka ya d’an jiyo ya kalleta , sosai ta runtse
idanuwanta ko bud’e bata sanyi har suka ‘karaso wajan motar da Robert ya bud’e masa
, nuni yayi mata akan ta zauna , ba musu kuwa ta zauna dan sosai tsoran mutanan da
ta gani da bindugu ya kamata , ko d’ago da kanta batasan yi musamman yadda ta
rintse idanuwanta dukda sanyin Acn da yake cikin motar Alba zufar tsoroce ta fara
fito mata , babu abunda take nanatawa cikin zuciyar ta sai Innalillahi wa inna
ilaihi raji’un , gabaki d’aya ta sada’kar shikenan ‘karshenta ya zo , lokacin
shanye Jininta yayi , shima bobo ko sau d’aya be kalli side d’in da take ba da
alama abu yake me muhimmanci a cikin wayar sa , direct Airport suka nufa , a wannan
karan ma koda bobo yasata ta fito batayi musu ba amma ta ki kallan kowa sai faman
kare fuskarta take hatta bobo ta’ki yadda ta kallesa , ana zuwa wajan shiga jirgi
Abla ta d’ago da idanuwanta , karo na farko arayuwarta data fara ganin jirgi
shiyasa tana kallansa ta fashe da kuka me tsuma zuciya , tana girgiza musu kai ,
muryarta har rawa yake wajan furta “ Dan Allah kuyi hakuri”, yadda tayi maganar sai
ta baka tausayi , hatta bobo sai da yaji ba dadi cikin cool voice ya furta “ babu
abunda za’ai miki kinji? Taho mu tafi” kanta Abla ta jinjina masa kafarta har rawa
take wajan taka step din jirgi, LG tana bayansu gabaki d’aya ba’kin cikine ya
kamata kamar zuciyarta zata buga sabida tsanar Abla da tayi Alwashin tunda bobo ya
mareta sabida ita sai ta Gana mata azabar da sai ta kwammace bata duniya ( To
faaa 🥱), suna shiga cikin jirgin yawanci sojojin bobone ko tsaye sanye da blank
din kaya da Sauri ta matso inda yake dan harga Allah tsoran su Robert take , duk
inda ya taka Abla tana binsa a baya , Adai dai wani waje me shegen kyau Bobo ya
tsaya , kujerune sosai A wajan kamar ba a cikin jirgi ba , yadda tsarun kujerun
suke sai sun burge mutum , yan mata biyu da su bobo suka taho dasu ko waccensu tana
zaune kan kujera ta saka belt d’inta , itama Abla waje bobo ya nuna mata sai bin ko
ina take da kallo tana zama ya saka mata belt d’in da Hausa ya furta “ kar ki motsa
daga inda kike idan ba haka ba jirgin sai ya had’iyeki ya cinye ki” ya fahimci
tsoran jirgin ta keji shiyasa ya fad’a mata haka , yadda Abla ta ri’ke kujerar
jirgi sai ta baka dariya hatta bobo saida yayi murmushi kafin ya bar wajan , LG ma
da wasu mata suma duk a wajan suka zauna , yadda Abla taji wani irin girgiza na
tashin jirgi sosai hakan ya girgixa ta ware murya tare da kwala kara cikin Sauri
kuma ta toshe bakinta hawaye na gangaro mata cikin zuciyarta har ta fara adduar
shahada ganin shikenan ta tabbata kashesu za’ayi , tun tana tsorata yadda LG take
binta da mugun kallo itama Abla taka take binta , ga tsoro ga masifa , yadda sanyin
Ac take kad’a ko ina ne yasa Abla ba shiri bacci ya d’auketa .

2 hours 45 minutes ne ya shigo dasu ‘kasar U.S cikin Garin New York , da karfi LG
ta d’akawa Abla duka da yasata zabura cikin sauri, a zuciye ta cire mata belt d’in
jikinta tana bin fuskarta da wani irin kallan tsada , agadarance ta furta “ let’s
go” kamar Abla bazata bisu ba ganin yadda sauran yan matan suka tashi yasa itama ta
tashi ta soma binsu har suka sakko cikin jirgin, Bobo na tsaye sai su Robert da
wata farar baturiya sai faman sakin murmushi take ita kadai , wad’an da Abla ta
gani ne ya saka lokaci d’aya jikinta ya soma raba da Sauri ta koma bayan bobo tana
karanta adduar da zata zo bakinta duk da a Wannan lokacin babu bindugu a hannansu ,
kallan farar matar bobo yayi bansan akan me suka tattauna ba illa “ dis is the
girl” da bobo yace mata , yanxu ma murmushi ta ‘kara saki tana nufo inda Abla take
ta kamo hannu, da Sauri Abla ta bud’e baki zatayi ihu bobo ya furta “ idan kika
Kuskura kika mun ‘kara sai na tarwatsa kanki” ba shiri kuwa Abla tayi shiru tana
zazzare idanuwa saida ya bata minute d’aya kafun ya furta “ babu abunda zata yi
miki, tafiya kawai zatayi dake kika kuskura kika bud’an baki kuma..” ya ‘karasa
yana d’auko wata ‘karamar bindiga, saura kad’an fitsari ya kwacewa Abla lokacin da
ta ga bindigar jikinta har rawa yake lokacin da farar matar nan ta kama hannunta
suka wata bakar mota , ko kwakkwaran motsi Abla ta kasa har driver ya tashi motar
suka bar wajan .shima Bobo motar da Robert ya bud’e masa ya shiga , ragowar
sojojinsu suma suka shiga cikin motocin su guda shida suka bi bayan motar bobo ,
ita kuma LG da wasu sojoji suka bita tare da ‘yan matan nan . Tunda motocin su bobo
ta soma tafiya a kan babban titin da zai kaisu 5th Avenue lokaci d’aya motocin
bayan bobo guda biyar suka fara ‘balle bottom d’in rigar su suna cireta sai bakar
singlet da suke bari hatta ta kalman ‘kafarsu ko wannansu ya cire ya nannad’e
’kafar Wandunansu zuwa gwiwa ,tun kafun ayi horn aka wangale wa bobo babban gate
d’in cikin gidan, Victor tsaye a wajan cikin girmamawa ya sarawa bobo , cikin Sauri
Robert ya sara masa shima yana fitowa daga cikin motar , Victor ya shiga ya tada
motar tare da barin wajan , lokaci d’aya gabaki d’aya sauran sojojin sukai parking
d’in motocin su suka fito , tun kafun a basu umarni ko wannansu ya kwanta a kasa a
jere cikin layi , lokaci d’aya suka soma birgima a kasa duk da Nisan da ke tsakanin
first gate da second gate haka suka dunga birgima kamar wasu kifaye suna tunkarar
gate 2, anan ma still gate aka bud’e musu suka cigaba da birgima zuwa babban gate
din cikin gidan dukda daga second gate zuwa main gate ya fi nisa haka suka dunga
birgima suna furta “ sorry sir “ har suka ‘karaso main gate kafun kamar wad’an da
aka saka tsere suka soma zaga compoud din cikin gidan cikin gudu gudu .
Bobo kuwa direct main part d’insu Victor yayi parking motar sa yana fita
Victor ya ja motar ya bar wajan cike da girmamawa , yana shiga cikin falourn ya
tarar da ko ina shiru kamar babu mutane a cikin falourn, Adaidai lokacin da little
da prince suka fito daga cikin wani ‘kofa hannun d’auke da coffee, little yana
ganin sa yayi saurin zuwa Wajan da yake tare da hugging d’insa , shima prince
hugging d’insa yayi kallan su yayi tare da kallan coffee d’insa hannunsu , fahimtar
hakan little yayi ‘kasa ‘kasa da murya kafun ya furta “ big yaya bobo help us
wannan shine coffee na 8 Kenan kuma yaya big boss ya hanamu hawa lifter ta step
muke bi, please”, murmushi kawai bobo yayi yau big boss a sama yake kowanene
tsautsayi ya fad’a bazai ji da dad’i ba . Coffee d’in hannu ya kar’ba kafun ya
furta “ dare yayi kuje ku kwanta” cikin had’a baki suka d’an zaro ido take da furta
“ yaya !” Shima nasan I don ya d’an zaro musu kafin ya furta “ shikenan ku kwana a
tsaye , yana kai ‘karshen maganarsa be basu wani damar ba ya nufi elevator , direct
part d’in big boss ya nufa , tun kafun yashi Wajan daddad’an ’kamshin turaran big
boss ya Dakar masa hanci , murmushi kawai bobo yayi kafun ya saka turn print d’insa
’kofar ta bud’e , gabaki d’aya hasken corridor d’in an kashe su sai dumm light da
aka bari, bobo be damu da rashin hasken Wajan ba ya nufi ‘kofar farko da bobo yasan
big boss yana ciki, ko da ya shiga nan ma still dum light ne a wajan sai kamshin
turaransa da yariga ya gama kama ko ina na cikin part d’in, kofar main falourn
dinsa ya shiga bakinsa d’auke da sallama . Yana zaune kan kujera sanye da wasu
fararan kaya masu laushi ga gashin kamsa da ya tufke waje d’aya a bayansa ,
fuskarsa a d’aure ko alamun fara’a babu, tunda bobo ya shigo be d’ago ya kallesa ba
, cikin nutsuwa yake operating d’in system d’in gabansa har ya ajje masa coffee
d’insa be kallesa, kusan tsawan 2 minutes ya dakata da abunda ya ke , fararan sexy
eyes dinsa ya d’ago ya zubawa bobo tare da mi’ka masa farin hannunsa guda d’aya a
hankali ya furta “ my coat” d’an zaro idanuwa bobo yayi shikansa besan lokacin da
dariya ya kwace masa ba “ Haba mana big boss , Hakana da kudin da zaka siyo adadın
da kake bu’kata fa “ d’auke kansa big boss yayi kafun ya furta “ bani dasu banda
kud’ima” yanxu ma wani dariyar bobo ya ‘kara saki wai bashi da kud’i yadda yake
dariya ne yasa ran big boss ya ‘kara ‘baci , cike da tsokana bobo ya kara furta “
Wannan ne karo na farko daga ka d’auko wata” be ‘karasa ba rai a ‘bace big boss ya
kaimasa wani irin lafiyayyan naushi da bobo yayi saurin kauce wa , duk da haka big
boss be barsaba ya ‘kara kai masa wani laushin still bobo kauce wa yayi, a karo na
uku big boss rigar bobo ya dan ‘ka tare da d’aga hannunsa zai kai masa naushi ,
kamar little bobo yayi fiki fiki da idanuwa tare da karya wuya, hankad’asa baya big
boss yayi ya fad’a kan kujera “ d’an iska kawai”, wata yar iskar dariya bobo ya
‘kara saki , bindigar gefensa big boss yazo d’auka bobo yayi Sauri nufar ‘kofa sai
da ya daidaici kofa kafun ya furta “ yadda ka fito d’innan my man kamar wani…” wani
waje big boss ya harba da yasaka bobo saurin barin d’akin yana dariya , big boss
kuwa kansa kawai yake nodding rai a ‘bace ……

PAY YOUR MONEY INTO 2681892316, Aisha umar zenith bank sea a turo shaidar biya ta
wnn number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya
lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your
mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to
the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏…

S____21💞
Ya dad’e zaune akan sofa yana operating system d’in gabansa da alama wani aikin
yake yi sabida yadda ya bawa abun mahimmanci sosai , sai around 1am ya kashe system
d’insa gabaki d’aya ko phone d’insa be d’auka ba ya fito daga cikin d’akin, kamar
yadda suka saba shida bobo saida ya nufi part d’in kowa ya duba lifiyarsu kafun ya
dawo nashi part d’in, sosai idanuwansa suka soma red baccin da beyi d’azuba ga
ciwan kai da yake sosai, 1:30am Daidai lokacin da ya kalli agogon d’akin shiyasa
kai tsaye batare da ya zauna ba ya nufi Toilet d’insa , mintuna 10 kacal ne ya fito
dashi daga toilet ga hannunsa da face d’insa da take da damshin ruwa alamar alwala
yayi, Daidai wata shinfid’ad’d’iyar farar dadduma me laushin gaske ya nufa tare da
kabbara sallah, ya jima yana nafilfilun da ya saba har wajan karfe 2:30am na dare ,
shikad’ai sai faman lumshe idanuwansa yake harya koma kan sofa d’insa yana lumshe
eyes d’insa musamman yadda ya jingina da jikin sofan, sai da ya d’auki kusan 5
minutes a haka kafun ya janyo wayarsa da ya ajje kan center yana dannawa , har
‘karfe 4:30am Big boss be kwanta ba sai ma shiryawa da ya sake yi kamar kullum
cikin white d’in kaya riga da wando sai ‘bakar sumar gashinsa da take ta d’aukan
’kamshi da ‘kyalli , ta ko ina daddad’an turaransa ne yake tashi had’e da sanyin
Ac, tsagar girarsa sosai ta fito a face d’insa musamman yadda girar fuskarsa take a
cike , hatta red lips dinsa sosai ya ‘kara turuwa , yadda yake lumshe sexy eyes
d’insa sai ya burgeka, phone d’insa kawai ya d’auka yanufi down stairs lokacin da
ake kiran sallah , babu kowa a falourn , maida kallansa yayi kan agogon falourn
batare da ya zauna ba , bobo ne ya fara fitowa shima sanye da brown din Riga sai
black d’in wando da yake jikinsa , fuskarsa cike da murmushi ya furta “ Big Boss “
shima Big boss face d’insa ya d’ago kad’an tare da lumshe masa sexy eyes d’insa
daga nan be ‘kara cewa komai ba , bobo yana zama uncle ya Fito shima hannunsa da
d’an ’karamin charbi, shima a Wannan karan Big boss be kulasuba sai d‘an lumshe
eyes d’insa da yayi masa , shima uncle cike da tsokana ya lumshe masa nashi
idanuwan, bakinsa big boss ya ta’be kad’an yana d’auke kansa , “ uncle sannu da
fitowa “ cewar bobo , amaimakon uncle ya amsa masa sai nuna masa direction d’in Big
Boss da yayi cikin ‘kasa ‘kasa da murya ya furta “ Yau yan mulkinne suka
motsa?”d’an kallan direction din big boss yayi kafin ya saki murmushi kawai , a
karo na biyu Big Boss ya ‘kara kallan agogon falourn, ganin an tayar da sallar
asuba, sai soma tafiya Prince da little suka ‘karaso wajan cikin sauri sai faman
haki little yake yi shikad’an , d’an kallansa big boss yayi kad’an tare da d’auke
eyes dinsa ya soma tafiya , suma gabaki d’aya bin bayansa sukai zuwa masallacin
cikin gidan .
Ana idar da sallah babu Wanda ya kalla cikinsu ya wuce part d’insa , bin
bayansa da kallo little yayi har ya wuce , kamo hannunsa bobo yayi suka soma tafiya
ganin yadda mood d’insa ya canza “ kafiya neman magana little ,kasan baze kulakaba
yanxu, ya gaji ka bari ya huta first “, kansa little ya jinjina masa kafun yayi
masa narai narai da ido shigen abunda bobo yayi wa big boss “ yaya bobo yau ka bamu
Hutu banda training din nan kaji?” Yes please” prince yayi saurin fad’a shima ,
lokaci d’aya bobo ya saka hannu ya tallemusu ‘keya , “ kun shirya yau darata Kenan
shiyasa kuka biyoni? Toh babu ruwana kunsan hanyar d’akinsa ai kuje ku fad’a masa”
cewar bobo , “ Haba yayan mu nakanmu kaga yanxu yaya big boss bacci zaiyi please
please yayan mu kaji?” Cewar little , shima prince a hankali ya furta “ dan Allah
kaji yayan mu rabun ranmu, kaji?” Girgiza musu kai yayi kafun ya furta “ okay karku
cikani da surutu” little har da wani dariya ya saki kafin ya furta “ we promised”
suna shiga cikin falourn ko zama basuyi ba suka gudu part d’insu “ Allah ya
shiryeku” cewar bobo shima ya nufi part d’insa .

***** 10:10am gabaki d’ayansu suka fito cin abinci kamar had’in baki banda
big boss da tunda ya shiga part d’insa be fito ba har yanxu , ko wannansu sanye
cikin ‘kananan kaya , James yayi serving d’insu favorite food d’in da suke san
ciki, tunda suka soma cin abinci babu Wanda yayi magana , lokaci zuwa lokaci wayar
bobo tana haske kusan sau uku batare da ya kalli wayar ba , a karo na hud’une
wayarsa ta fara vibrating kamar bazai d’auka ba har uncle yayi magana , “Dr Eli”
shine sunan da ya fito kan wayar sa ga uban text d’in da ya gani da sunanta shima ,
mamakin kiran ne yasa ya d’aga , banji me aka ce masa ba sai mi’kewa tsaye da yayi
yana furta “ oh shit…. am coming “ yana kai karshen zancansa ya kashe called d’in,
kallan uncle da yake shirin magana yayi “ sorry uncle zanje na duba wata patience”
lokaci d’aya prince da little suka had’a baki Wajan furta “ patience ?” Shima uncle
cike da mamaki ya furta “ patience ? Bobo ? Dagaske kake ?” Kansa ya d’anyi
knodding kad’an “ yes patience….” Ai be ‘karasa ba little yayi saurin furta “
please yaya zan bika” shima prince yayi saurin furta “ yes nima yaya please zan
bika” tsayawa kallan ikon Allah bobo yayi musamman little da yaga sai faman
murmushi yake , shima uncle a d’ayan side d’insa murmushi yake saki shi kad’ai ,
d’an harararsu bobo yayi zai yi magana little yayi saurin furta “ please karka ce
no dan Allah”, yadda ya fad’a in a cool voice ne ya saka bobo kara harararsa “
let’s go” shine abunda yace , little har da buga wani tsalle kamar ‘karamin yaro ,
“ Hey ba inda zakuje , ku zauna kuci abincin ku” narai narai little yayi masa sai
kuma ya kalli direction d’in uncle , prince ma direction d’in uncle ya kalla tare
da ‘kif ‘kifta masa ido , wani murmushi uncle ya saki me sauti yana kallan bobo “
tunda mara lapiya zaku gani why not ka tafi dasu tunda suna san zuwa” kallan yadda
suka sunkuyar da kai bobo yayi kafin ya furta “ Okay let’s go” daga nan be
‘karacewa komai ba ya nufi hanyar fita suma cikin sauri su little suka bi bayansa ,
little har da kashewa uncle ido d’aya , shima uncle d’in ido d’aya ya kashe masa
yana sakin murmushi.
Babbar farar BMW IX 1 Robert ya d’auko , ga wasu jerun combo cars ba’ka’ke
guda bakwai da sojoji suka fito dasu, little back seat ya shiga abunsa shi kad’ai ,
bobo da prince Suka zauna a tsakiya Sabida kujeru shida ne a cikin motar , biyu a
farko , biyu a tsakiya sai guda biyu a baya, tunda suka shiga cikin motar babu
Wanda yayi magana kowa phone d’insa yake dan nawa sai time to time suke d’an
magana, kusan tafiyar mintuna goma sha biyar sukai kafun su canza kwanar tafiyarsu
zuwa wani direction d’in daban, Daidai wani madaidaicin gida motocinsu sukai
parking gabaki d’aya sojojin suka fito suka zagaye motar da su little suke cika ,
Robert ne ya bud’e musu mota suka fiffito, wayar hannunsa bobo kawai ya danna ko
mintuna d’aya cikakkiya ba’ai ba aka bud’e ‘kofar gidan da sukai parking, farar
baturiyar jiya ce ta fito tare da nuna musu hanyar shigowa ciki, gabaki d’aya
sojojin a waje suka tsaya, a maimakon su tsaya waje d’aya sai suka zagaye gidan
gabaki d’ayansa , Robert kuma ya bisu cikin gidan , Daidai kofar bakin falour shima
ya dakata su bobo suka shiga , madaidaicin falour ne da babu tarkace ko hayaniya a
cikinsa gidan shiru kamar babu wani me rai a ciki , amma ko ina tas tas yake babu
datti, kan kujerun suka zauna , prince da little sai faman kallan falourn suke a
fakaice suna san ganin mara lapiyar , Dr ElI tana ‘ko’karin kiran me aikinta bobo
ya dakatar ta ita alamar ta zauna , “ where is she?” Cewar bobo, “ tana d’aki “ dr
Eli ta bashi amsa tare da gyara zamanta sosai “ But tana cikin wani hali sosai,
idan ba’a cire mata damuwar dake zuciyarta ba zata iya kamewa da ciwan zuciya , ko
ciwan damuwa, Lokaci zuwa lokaci tana girgita tana fad’in wasu word da ni bana gane
yaren da take cewa, gabaki d’aya taki sakin jikinta har magani ta’kisha , habincin
da aka kaimata bataci, danai forcing d’inta kuma ta dunga amanshi kamar bata saba
cinsa ba , and now fever d’inta ya tashi sosai taki ‘kula kowa balantana ashawo kan
problem d’in , seriously tana bu’katar ta kwantar da hankalinta sabida kwakwalwarta
tana neman ta’buwa and yes binciken da nayi tana faman da stomach ulcer Sabida
rashin cin abinci da batayi”.. tana kaiwa nan Dr Eli ta dakata da bayanan ta ,
juyawar da bobo zaiyi yaga yadda fuskar Little tayi wani irin mugun ja lokaci d’aya
, saurin dake kansa yayi sam ya manta da little yazo da bazai ta’ba bari Dr Eli
tayi masa wannan bayanin agaban little ba , dukda yadda gashin sa ya rufe masa ido
zaka fahimci kuka yake sanyi , prince ma duk da besan ko wacece ba sosai tausayinta
ya fito akan face d’insa , kujerar da bobo yake kai ya Tashi tare da zama akan
kujerar little , yadda ya dunkule hannun waje d’aya ne yasa bobo ya kama hannun a
hankali ya fara murza masa hannun, Dr Eli bata fahimta ba shiyasa tayi ‘ko’karin
cigaba wa Amma bobo yayi saurin dakatar da ita .” Hey calm down! Kwantar da
hankalinka!” A hankali little ya d’aga masa kai muryarsa har disashewa take wajan
furta “ yaya bobo inaso na ganta” shima bobo kansa ya d’aga masa “ zaka ganta amma
sai ka kwantar da hankalinka ,okay?” Yes please yaya bobo , ina so Nima na ganta ,
she need our help plx ko sau d’aya ne” cewar prince shima dukda besan akan wa ake
magana ba lokaci d’aya yaji yana san yaga yarinyar, kallan Dr Eli bobo yayi kafun
ya furta “ zaki iya nuna mana inda take ?” Da Sauri ta furta “ yes why not “ tana
mi’kewa tsaye , kai tsaye d’akin da yake cikin falourn ta nuna musu, har yanxu
hannun little yana cikin na bobo ya ri’ke masa , a hankali Dr Eli ta tura kofar
suka shiga ciki, kwance take a ‘kasa ta juyawa kofar shigowa baya , sosai ta takure
jikinta waje d’aya dukda ba’a iya ganinta sai scarp d’in kanta ga ba’kar coat d’in
jiya da haryanxu ta ke ri’ke da ita , motsin da taji ne yasa tayi sauri zabura tana
juyowa baya , sosai fuskarta ta fad’a kamar wacce tayi shekara tana rashin lapiya
ga haskenta da ya sake fitowa sosai , ja dabaya ta somayi fuskarta har d’an kunbura
tayi sabida yadda tayi kuka ga idanuwanta da suka kumbura ko bud’esu bata sanyi ,
yadda taga sun tsats tsareta da ido ne yasa ta ‘kara jin tsoro ya kamata musamman
bobo da ta gane shi, suna shigowa cikin d’aki ta ‘kara ja baya sosai tana binsu da
kallo, sosai little da prince suke kallanta musamman yadda sukaga tana Jan baya,
jikinta sanye yake cikin simple riga me d’an kauri sai cap din kanta da gashin
goshinta ya Fito sosai, akan wata kujera bobo ya zauna yana fuskantarta ganin yadda
hawaye ke zubo mata sosai a fuska gashi ta takure waje d’aya tana kallansu ,
bakinta har rawa yake wajan furta “ Dan Allah kuyi hakuri” tana kai karshen
zancanta ta sunkuyar da kanta tana shashshekar kuka , gabaki d’ayansu babu Wanda be
shiga shock ba yadda tayi magana , ‘karin mamakinsu ma yadda tayi Hausa , shiyasa
little suka kalli junansu, dan shi little tunda yake a rayuwarsa bai ta’bajin wani
yayi Hausa ba , bayan yan gidansu hatta big boss bazaice ga ranar daya ta’bajin
Hausa a bakinsa ba tunda yake dashi kuwa , “kinajin Hausa ?” Little ya fad’a mamaki
fal ransa , itama da mamakin ta d’ago kunburarrun idanuwanta ta d’orashi akan
little haka kawai taji ta yadda bazai cutar da ita ba “gashi kyakkyawa” tafad’a
cikin zuciyarta , ita kanta tana mamakin yadda akai ya iya furta Hausa “ may be a
wani wajan yaji” ta ‘kara nanatawa a zuciyarta , shi little gabaki d’aya sai yaji
wani irin farin ciki ya kamashi lokaci d’aya da yaji tana Hausa shiyasa ya ‘karaso
Inda take zaune a ‘kasa shima sai ya zauna yana bin fuskarta da kallo , abun mamaki
bata ja baya ba ita ma, yadda yake murmushi ne yasa ta tsaya tana kallansa , a
hankali ya furta “ ya sunanki?”, bobo kam ya kasa motsawa ma , ganin ta saki
jikinta da little , har yanxu kuma yana mamakin yadda little yayi mata magana a
saninsa little baya ta’ba sakewa da Wanda be sanshi ba shiyasa abun ya d’an basa
mamaki, “ Ibtissam” cewar Abla tana kallan little , “ yar rainin hankali tana
magana ni na tanbayeta tamayar dani d’an yankan kai ?” Cewar bobo cikin zuciyarsa ,
murmushi little ya saki me sauti kafun ya nuna kansa “ Ni sunana little” sai kuma
ya nuna mata Prince da shima sai murmushi yake sakar mata “ wannan sunanshi yaya
prince “ again ya nuna bobo “ wannan kuma sunan shi yaya bobo” kallan bobo tayi
kasa kasa kafun ta kalli little da yake mata murmushi, cikin kasa kasa da murya ta
furta “ bayashan jini?”, lokaci d’aya little da prince suka kyalkyale da dariya “
wai yaya bobo ne me shan jini , toh idan taga big boss kuma shugaban ‘kungiyar masu
shan jini zata ce kenan cewar prince cikin zuciyarsa , bobo tsaya kallansu kawai
yayi ganin farinciki shinfid’e kan fuskarsu musamman little da kullum yake so yaga
murmushi akan face d’insa , girgiza mata kai little yayi “ Yaya nane fa , bayashan
jini”, kanta Abla tayi knodding “ kayi hakuri , na d’auka yana shan jini”, shikenan
na hakura , amma ne yasa kika ‘kinshan magani? Ko bakyaso ki warke ?” Wasu hawayene
suka soma gangarowa Abla , “ zasu cutar danine kamar ydda suka kashe mun Arwa” da
Sauri prince ya kalleta , little ma kallanta yayi jin kwalla na zuwar masa ganin
tana kuka , shima bobo yadda yaga sun canza reaction d’in face d’insu ne yji babu
dad’i cikin ransa , karki “damu babu Wanda zai miki komai kinji?” Cewar prince yana
‘karasowa kusa da little, itama kanta ta jinjina masa “ bana san nan wajan ku tafi
dani” lokaci d’aya little da prince suka juya wajan bobo , harararsu yayi alamar
baku da hankali, “ yaya…” cewar little , d’aga masa hannu bobo yayi , “ let go ,
ina da abunyi”, be basu chance d’in magana ba ya bar d’akın , kallanta prince yayi
little sukai , sudai harga Allah sunji suna san tadawo gidan su amma sunsan big
boss bazai ta’ba yadda ba , da Sauri little ya mike yana furta “ ina zuwa “ shima
prince bayan sa yabi suka bar d’akin, suna fita Abla ta zame ta kwanta akan tiles
din hawayen da take d’azu ne suka cigaba da sakko mata .
Suna fitowa falour suka tarar da Bobo yana jiransu da Sauri little ya
‘karasa inda yake “ yaya please ! Yaya please mutafi da ita gidan mu, Dan Allah”
kallan baka da hankali bobo yayi masa kafun ya furta “ bansan wannan shiriritan
little kasan abunda kake fad’a bazai faruba…” be ‘karasa prince ma ya furta “ Dan
Allah yaya bobo, nasan zaka iya ro’kan yaya big boss”, girgiza kansa bobo yayi “
bazai ta’ba yadda ba da alama har yanxu baku san yayankuba,”Lokaci d’aya little ya
soma hawaye tare da folding hannunsa “ yaya dan Allah? Just for me please, idan ta
warke sai ta tafi kaji” No” cewar bobo, kafun ya kallesu rai a had’e “ stop this
dramer , let’s go home” yana juyawa lokaci d’aya kamar almara jikin little ya soma
jijjiga bana wasa ba, hannunsa d’aya dafe da zuciyarsa, da ‘karfi prince ya furta “
Little” , juyowar da bobo zaiyi yaga little da fe da zuciyar sa , da Sauri ya
‘karaso Inda yake , “ Little Menene haka ? Nace ka kwantar da hankalinka ko?” Amma
ina little gabaki d’aya baya jin me yake cewa sabida yadda kirjinsa yake sama da
kasa , abunda be ta’ba faruwa ba, hugging d’insa bobo yayi cikin cool voice ya soma
magana “ calm down please zamu tafi tare da ita , just calm down” a hankali rawan
jikinsa ya soma raguwa , bugun zuciyarsa ya fara daidaita , da Sauri da Sauri ya
soma ajiyar zuciya , hawaye na sakko masa a ido ya kalli bobo, a hankali ya furta
“ am sorry yaya bobo, ni ina daku amma ita bata da kowa , just once please mu tafi
da ita”, murmushi bobo yayi masa “ zamu tafi da ita just calm down ok?” Kansa
little ya jinjina masa , yana tashi zaune, shima prince hugging d’insa yayi “ calm
down kaji?” Mi’kar dashi tsaye bobo yayi tare da ri’ke hannunsa shi kansa yasan
abunda yake ‘ko’karin yi bame yiwuwa bane , amma kuma dole ya saka little da prince
cikin farinciki, 22 years basu ta’ba ro’kon wani ya zauna da su ba sai yanxu? Bazai
iya kallo ciwan little ya Tashi ba , Allah ya sani Little shine rauninsa a rayuwa ,
yadda yaga little ya ‘kura masa ido ne yasa ya sakar masa murmushi “ ke ka kirata”
wani irin murmushi little ya saki me sauti yana nufar d’akin , tana kwance kamar
d’azu , murmushi kwance akan face d’insa ya furta “ Hey !” Da Sauri Abla ta d’ago
kanta , tana ganin little ta tashi zaune , murmushi ya kara sakar mata “ taho
mutafi ko bakyasan zuwa gidan mu?” A hankali Abla ta furta “ zaku tafi dani?” Shima
little da Sauri ya d’aga mata kai “ yanxu zamu tafi yaya yana jiran mu, taso
mutafi”, da Sauri kuwa ta mike tsaye hawaye fal ranta ta nufo inda yake, suna
fitowa falourn ta tarar da Dr Eli da bobo sai prince shima sai murmushi yake,
fuskar bobo ma ba’a had’e ba yace musu “ Let’s go” wani Leda Dr Eli ta mi’ka wa
little “ Her medicine” kar’ban ledar prince yayi tare da furta “ thank you “,
dakanta tayi musu rakıyi zuwa bakin gate , Abla tana sa ‘kafarta a waje ta saka ihu
tare da komawa ciki da saurin ta , kallanta little yayi tare da le’kawa waje babu
kowa sai sojojinsu, ganin yadda jikinta ya d’au rawa lokaci guda “ menene?” Bobo ya
tanbayeta , cikin rawa ta dunga nuna musu waje har ta soma hawaye ga wani irin
Tsoro da ya bayyana akan face d’inta lokaci d’aya , “ babu kowa fa” cewar little ,
da Sauri ta fara girgiza musu kai hankali atashe gabaki d’aya ta birkice, dakansa
bobo ya fita , sojojinsu daya gani kowa da bindiga a hannunsa ne ya fahimci tsoron
su take ji , “ Babban aiki” cewar bobo cikin zuciyarsa, gabaki d’aya umarni ya bawa
sojojin akan kowa ya shiga mota bayasan ganin su a waje, hakan ce kuwa ta faru
hatta Robert cikin mota ya shiga , yayi saura babu kowa a waje , “ babu kowa let’s
go” kanta ta soma girgiza masa , “ fine bari na kira su” da Sauri ta fito daga
bayan little da ta ‘buya “ kayi hakuri” ta fad’a a sanyaye,” oya let’s go, kuma
kika bud’emun baki sai na tarwatsa kanki da bindiga “cewar bobo, a hankali ta soma
tafiya kamar bazata fitowa ba dan harga Allah bata san sojoji tana fitowa waje kuma
ta tarar da babu har wani ajiyar zuciya tasauke, dakansa little ya bud’e mata back
seat da ya zauna shi ya fara shiga sai itama ta shiga , bobo da prince suka zauna a
inda suke , d’ago fuskar da zatayi kawai idanuwanta suka sauka kan kayan Robert ,
kuka take ‘ko’karin yi amma tana tsoran yi Sabida bobo da yake wajan , shiyasa ta
takure jikinta waje d’aya ta ‘ki bari ta bud’e idanuwa, “ babu abunda zai Miki”
cewar little shima ya gane tsoran so Robert take ji, ganin ta’ki sakin jikinta ne
yasa ya kalli coat d’in jikinta , tun d’azu yake jin kamshin turaren big boss a
ciki , kuma kamar ya ganta jiya a jikinsa shiyasa ya d’an kalleta tare da nuna coat
din “ a ina kika sami wannan rigar?”itama kallan rigar tayi har wani murmushi ne ya
d’an fito mata , cikin kasa kasa da murya ta furta “ Nima bansani ba , kawai ya
lullu’beni da itane lokacin da wuta zai fad’o mun”, kinsan wanda ya temakekin?
Little ya ‘kara tanbayar ta , kanta ta girgiza masa alamar ah ah, daga nan shima
little be kuma tanbayar taba yayi mata shiru , gabaki d’aya maganar su a kunna bobo
dan duk yaji me suke cewa duk da yadda sukai maganar ‘kasa ‘kasa , cikin ‘kan’kanin
lokaci suka ‘karaso gida , sabida yadda ta sunkuyar da kanta ‘kasa ne yasa bata ga
sojojin da suke layin ba , har suka shigo cikin gidan kuwa bata d’ago balantana
taga sojojin da Suke wajan. Direct apartment d’insu sojojin nan sukai parking,
lokaci d’aya suka fito gabaki d’ayansu,suka zagaye motar da su bobo suke ciki, bobo
ne ya fara fitowa sai prince , sai kuma Abla da Prince ya bud’e wa ‘kofa tana
fitowa little shima ya fito , d’agowar da zatayi ne taga sojojin d’azu zagaye da
ita , wani irin ‘kara ta saki jikin har tsuma yake lokacin da ta gansu, fahimtar
hakan yasa little ya ri’ko hannunta ganin yadda take ‘ko’karin komawa cikin motar “
babu abunda zasuyi miki” duk da haka taki tsayawa waje d’aga ga idanuwanta data
kulle taki yadda ta bud’e su , alama bobo yayi musu da su bar Wajan , cikin
‘kan’kanin lokaci kuwa suka bar wajan , dukda ta ko ina akwai sojoji a cikin gidan
“ shikenan karki bud’e idanuwanki yanxu zamu bar Wajan kinji?” Da Sauri ta girgiza
masa kai amma har yanxu ta ‘ki bud’e idanuwanta , a haka suka nufi cikin part d’in
idanuwanta a kulle , wani irin sanyi da ‘kam shine ya daki hancinta, duk da bata
bud’e idanuwanta ba , laushin da taji a ‘kafarta jitake kamar kar ta dena jin sa
Sabida yadda yake mata dad’i a ‘kafa , Uncle na zaune kan kujera suka shigo ,
mamaki ne ya kamasa ganin little tare da wata yarinya kyakkyawa ga idanuwanta a
kulle ga little ya ri’ke mata hannunta har suka tsakiyar falourn, “bud’e idanuwanki
babu kowa” a hankali kamar mara gaskiya ta fara bud’e idanuwanta , cikin Sauri kuma
ta kulle su jikinta har rawa yake , hawayene suka soma sakko mata sosai a kan fuska
, cikin rawar murya ta furta “ kace mun ku ba masu shan jini bane amma shine kuka
Kaşönü Wajan yan yankan kai , dan Allah kuyi hakuri bazan kara binkuba” wani irin
dariya ne ya kama Prince , kallan da bobo yayi masa ne yasa yayi saurin had’iye
dariyarsa , uncle dai tsayawa kallansu yayi mamaki fal ransa , shi babban mamakinsu
yadda yagansu da mace abunda bai ta’ba faruwa ba kenan “ gidan mune karki damu babu
Wanda zai yanka miki kai” cewar little , cike da d’an masifa ta furta “ kayi
al’kawari?” Eh nayi” cewar little cike da dan masifa Abla ta furta “ wallahi idan
kayi mun karya kuma kai da Allah , Allah na yana ganin ka wallahi “ yanxu ma little
amsa ya bata “ Na miki Al’kawari ai Nima Allah yana gani ba yanka mutane muke ba”,
toh shiknn na yadda cewar Abla tana bud’e idanuwanta , yadda ta ga suna kallan ga
tsarin gidan falourn su ne yasa ta kalli little kamar zatayi kuka hatta falourn
taki yadda ta kalla “wallahi Allah sai ya kamaka , ko dai mutuwa mukai? Akasamu a
aljanna?” Ba little da ya soma dariya ba hatta bobo da su uncle sai da sukayi
dariya , cikin dariya little ya furta “ wallahi baki mutu ba” sai a lokacin ta
d’ago kanta kad’an ta kalli falourn tare da daga hannunta sama “ Allah kana gani
yace basashan Jini basa yanka mutane ,” sai kuma a karo na biyu ta ‘kara bud’e
idanuwanta tana bin falourn da kallo, duk da a tsorace take kallansa sosai wajan
yayi mata kallo, “ kai ta d’akin da zata zauna” cewar bobo yana zama kan kujera ,
“toh yaya”cewar little , itadai Abla sai binsa a baya take , duk yadda yayi su
shiga elevator Abla kin shiga tayi wai zai siyar da ita , dole sai ta kan stairs
suka biyu, itadai sai bin ko ina da kallo take a tsorace ta ki yadda tayi masa
kallan kurinta, a 1 floor cikin wani d’an corridor little ya bud’e d’aya daga cikin
doors d’in wajan da take da nata corridor d’in daban, Babban d’akine a wajan me
shegen girma da ‘kayatuwa , cikin d’akin milk colour ne hatta designer din royal
bed din dakin milk colour ne , ga wasu set da suke dashi da ya ‘ka wata d’akin
kasan tuwar gadon d’akin me kamar shape din circle ne sai ya yiwa dakin kyau, gaban
mudubin d’akin kamar ana rayuwa a ciki yadda yake cike taf da kaya a ciki, komai na
set din gado kawai a ciki hatta bed side da kwaba duk a kwai a ciki ga wani medium
milk carpet a cikin d’akin , daga gefensa ma doguwar sofa ce milk colour sai d’an
center d’insa shima, iya haduwa d’akin ya haduwa ko wasu masu kudin albarka dan
ba’karamun dukiya aka kashe wa d’akın ba , sosai Abla ta saki baki tana bin d’akin
da kallo cike da tsantsan mamaki , haryanxu ba ta yadda ba mutuwa tayi ba Sabida
ydda take ganin sabanin abubuwa masu kyau , shima d’akin sai tashin kamshi da
sanyin Ac yake ta ko ina , murmushi little ya d’an sakar mata “ Nanne d’akin ki”
kallan inda yace d’aki Abla tayi cike da mamaki , kafun ta ‘kara kallansa “ nan ne
d’aki ? Kaji tsoran Allah fa” kansa ya jinjina mata “ Nanne d’akinki Dagaske , ki
zauna a ciki kafun na kawo miki abinci , zo muje na nuna miki band’akin ki” yana
fad’ar hakan ya nufi wata ‘kofar da Sauri ta bi bayansa suna shiga cikin ban d’akin
ta kara ja baya “ nan kuma wani d’akine ?” No band’akine “ cewar little, yadda
tsarin toilet din yake sosai zai bawa duk
Wanda ya kalli band’akin sha’awa mutum ko yaddar da abu yayi akasa zai iya daukan
kayansa Sabida yadda yake da matukar haske babu ko datti a cikin toilet , komai
macikin ban d’akin na zamani ne sosai , ga wani dogon glass da yake sha’ke da
sabulan wanka , sink ya kunna tare da nuna mata “ idan kina san kiyi alwala “
sannan ya nuna mata yadda zata kashe shima , sau biyu yana nuna mata , cikin toilet
ma sai da ya nuna mata, hatta shaya da yadda zata shiga cikin glass wajan wanka
saida ya nuna mata da sabulan wanka da shampoos gabaki d’aya sai da ya nuna mata ,
sosai tayi mamakin komai tunda take aiki a cikin gidan karuwai bata ta’ba ganin
waje ne kyau kamar nan ba , cikin ‘kan’kanin lokaci ta fahimci duk abunda ya nuna
mata , hatta mayuka da turare saida ya nuna mata , “ ki zauna anan yanxu zan kawo
miki abinci “ zatayi magana yayi saurin furta “ Allah yana gani “ yana kai karshen
maganarsa ya bar d’akin , sai a lokacin Abla take ‘karabin wajan da kallo , sosai
ko ina tayi mata kai , tana kallan gaban mudubi ta kalli fuskarta bata san lokacin
da murmushi ya kwace mata ba da har saida dimples dinta ya lo’ba , ko minti 5
little be yi ba ya dawo dauke da tray babba sha’ke da irin kayan abincinsu, sai
alokacin yunwar da take ji sosai ya ‘kara tasar mata ganin Abinci , da Sauri ta
saka hannu zata soma cin abincin harta manta da little da yake wajan cikin sauri ta
d’aki wani samosa da gani tana sawa a baki tayi saurin futo dashi sabida bata saba
cin irin abin cin ba , kamar zatayi kuka ganin ta kasa ci, fruit din da ta gani ne
ta dauka, tana sawa a baki ta saki wani ajiyar zuciya , sosai ta soma cinsa ,
fahimtar yunwa take ji sosai ne yasa little barin mata dakin dan taci abincinta
sosai.
Yana sakkowa falourn direct kujerar da uncle yake zaune akai ya zauna tare
da ri’ko hannunsa “ please uncle ku Barta ta zauna “ gyara zama sosai uncle yayi
yana kallansa , “ Bobo yayi mun bayanin komai little amma ko na Amince kasan
yayanka bazai ta’ba amincewa ba , kasan halinsa sosai , ka bari bobo zai samar
mata wani wajan da ban” bobo bai ce masa komai ba, prince shiru yayi shima , a
hankali little ya furta “ please uncle just for me, mu kwada yi masa magana dan
Allah “ dungure masa kai uncle yayi “ shikenan karkayi mun kuka naga kunnanta sun
farayin red alamar kiris kake jira , bari ya zo amma ban maka al’kawarin zamanta ba
Indai be amince ba , kansa Little ya jinjina duk da shima shi da cikakken hope d’in
yaya big boss xai amince da zamanta , gabaki d’ayansu babu Wanda ya kuwa cewa komai
banda bobo da ya nufi part d’insa , basu fi mintuna goma da zamaba Robert ya shigo
da wasu manyan ledoji guda shida sai wata ‘karamar jakar trolley tare da ajje musu
cike da girmamawa ya furta “the trolley is for madam from Dr Eli and this is for
sir “ yana kai karshen zan cansa ya juya ya bar falourn , “ kayan da bobo ya sa
aka wo mata ne “ cewar uncle , d’aukan kayan prince da little sukai tunda sun
fahimci natane gabaki d’aya har trolley din suka nufi d’akin da take lokacin har ta
gama cin abincin ta gaji da jiran dawowar little , Bakinsa d’auke da sallama suka
shigo cikin d’akin shida prince , ko wannensu da murmushi kwance kan face d’insa ,
nuna mata kayan little yayi “ ki shirya sai ki Hutu idan , idan lokacin sallah yayi
sai kiyi sallah , kinji “ wasu hawaye ne suka sakko mata “ Nagode sosai “ girgiza
mata kai little yayi “ ki dena gode mana Allah zaki godewa , ki huta kinji baki da
lapiya “ daga nan basu ‘kara bata chance d’in magana ba ,suka bar d’akın , sosai
Abla Tasha kuka tunda take a rayuwa babu Wanda ya ta’ba kautata mata kamar yadda
sukai mata , har cikin zuciyarta take jin kaunarsu, kallan kayan tayi sosai ta gane
trolley din da suka shigo da ita Sabida irinta baturiyar jiya ta bata amma taki
ta’bawa , kamar bazata ta’ba kayan ba sai kuma ta nufi inda trolley din take , tana
bud’ewa tayi saurin rufewa sabida abinda taci karo da su, akaro na biyu ta ‘kara
bud’e har kulle idanuwanta tayi sabida kunya , cikin akwatin wasu set din pant ne
dayawa a ciki sai bra da ta sako mata a ciki , hatta pad sai da ta saka , duk
yawanci abunda mace zatayi anfani dashi sai da ta sako mata Sabida tun kafin su
shigo Us jiya bobo ya tura mata kud’i kan tayi wa yar 19 years siyayya, shiysa
komai ta siyo mata da yawa , sauran ledojin gabaki d’aya dogaran rigunane a ciki ,
sai kananan kaya, wani irin farin cikine ya kamata kamar wacce aka yiwa kyautar
aljanna, har hawayen farin ciki saida Abla tayi , ita kadai sai faman yi musu
addua take ga wani irin soyayyarsu da ta shiga cikin zuciyarta . Inda little ya
nuna mata a matsarin toilet ta nufa amma gabaki d’aya a tsorace take white bucket
d’in da tagani ta d’auka tare da nufar wani waje me kamar fanfo da little ya nuna
mata d’azu , tana kunna kuwa sai ga ruwa ya kunnu wani irin dad’ine ya kamata
lokaci d’aya inda jerun samulan wankan yake ta nufa shima kamar yadda little ya
nuna mata ta dauki d’aya tare da wani sosan wanke me laushi, bata shiga inda little
ya nuna mata ba sbida tsoran shiga da take shiyasa a filin wajan ta dunga dirje
jikinta dan hatta sabulun wankan da ‘kyar ta iya bud’e shi, yadda take watsa ruwa a
jikinta har wani kulle idanuwanta tayi saida ta watsa ruwa Sanranta tukunna ta fito
, cike da jin kunya ta d’auko fant da bra dake cikin trolley ta saka , kamar kuma
an aunata sabida yadda kayan sukai mata cif cif a jiki, wata maroon d’in doguwar
riga ta saka a jikinta da tayi mugun haska fatar jikinta ,ga uwan tulun gashinta da
ya dakko mata har gadan maya me shegen tsaho da cukowa , Daidai lokacin da ake
kiran sallahr azahar, idanuwanta ne suka sauka kan simfid’ad’d’iya daddumar da take
d’akin, ajiyar zuciya kawai ta sauke tare da tada sallar azahar dinta , tana idarwa
wani irin bacci ne ya kamata sabida yadda bacci da bata samu tayi ba , ga wani
sanyin Ac da ya ‘kara sanya dad’in shiyasa wani irin bacci me dad’I da ta dad’e
batayi irin saba ya d’auketa , ba ita ta tashi ba sai lokacin kiran sallar la’asar
shima da kyar ta iya bud’e idanuwanta , alwala tayi ta yi sallar la’asar din , tana
idarwa shima wani bacci ne ya ‘kara d’aukarta.
Allah sarki little tunda ya bar d’akin tunanin yadda xai ro’ki big boss ya
bar Abla ta zauna a gidan yake , haka kawai yaji yana kaunar ta zauna a tare da su
shiyasa gabaki d’aya ya kasa sakewa , duk yadda prince yake kwantar masa da hankali
ya kasa kwantar da hankalinsa duk da shima prince ‘boye fargabarsa yake sabida
little , uncle ma Sosai ya fuskanci yanayin face d’insu ya canza amma be ce musu
komai, lokacin bobo ya fita daga cikin gidan shiyasa hatta abincin rana Kasa ci
yayi sai fruit da ya d’an sha , har aka yi sallar azabar babu Wanda ya kula ,
la’aşar ma haka gabaki d’aya ya kasa samun nutsuwa Sabida yasan any time big boss
xai iya dawowa cikin gidan, shima prince gabaki d’aya be ya kasa sakewa Sabida
zullumin dawowar big boss .
Karfe 9:00na dare lokacin har little ya ‘kara kaiwa Abla wani fruits din da
lemo sai kayan ciye ciye da yakaimata ganin bata iya cin abincin su ba , shiyasa ya
d’ebo mata fruits da yawa sosai da zai isheta da fresh lemuka masu sanyi , lokacin
bobo ya dawo daga fitar da yayi . 10:01pm motocin Big boss suka danno kai cikin
gidan , yadda suka shigo haka bugun zuciyar little da prince ta buga a lokaci
d’aya , bobo da uncle suna zaune kan kujera , suma little suna zauna amma gabaki
d’aya sun kasa nutsuwa , tun kafin ya shigo daddad’an’kamshin turaransa ya sanar da
isowarsa, sanye yake cikin wasu fararan suit fari tas dasu , ba’karamun sukayi masa
ba , fuskarsa a had’e kamar kullum musamman yau da fuskarsa tafi had’e wa ,yau
gashin kansa a sake suke be tufkesu ba amma a mummurd’e suke sosai , tun da ya
shigo babu Wanda ya kalla cikin falourn kamar ma besan da zaman kowa ba yayi wuce
warsa part d’insa , yana wucewa little da prince suka saki a jiyar zuciyar a tare ,
d’an kallansu bobo yayi kafun ya d’auke idanuwansa, yadda yaga big boss ya shigo
cikin gidan be kula kowa ba har little yasan tabbas kowa yayi taka tsantsan amma
still dole sai su little sunyi masa maganar yarinyar da suka kawo idan ba haka ba
sai ransu yayi mugun ‘baci shi kansa ya sani , zafin zuciyar big boss Allah ne
kad’ai zai iya kwantar masa da ita . Suna zaune a falourn kowa tunanin fitowar big
boss a cikin ransa , sannan kowa da abunda yake sa’kawa cikin ransa , kamar daga
sama suka jiyo ‘kamshin turaran big boss tun kafun ya fito kowannansu suka shiga
nutsuwarsa , da Sauri prince da little suka nufi dinnig tun kafin big boss ya
fitowa suka fara d’auko masa food d’insa sukai jera masa kan wani chair din cin
abinci, yanxu ma yana fitowa babu Wanda yakalla sai zama da yayı kan kujera yayi
crossing legs d’insa , ya canza shigar suit din d’azu yanxu wani brown din Riga ce
a jikinsa me gajeran hannu hakan sosai ya bawa farin damtsen hannunsa fitowa ,
cikin kuma sanye yake cikin farin wandon jeans sosai kayan sukayi masa kyau , har
yanxu gashin kansa ba a tufke yake ba , da kansa little ya fara serving din big
boss , hannuns har rawa yake , gabaki d’aya tunda ya shigo cikin falourn yaga san
kowa ba a cikin mood dinsa yake ba amma duk da hakan babu Wanda ya tankawa ko yayi
alamar yasan suna yi, har ya d’auki spoon zai fara cin abinci sai ya dakata tare da
d’aukan glass cup din da little ya cika da ruwa , a fusge ya furta “ talk”, jikin
little har rawa yake wajan furta “ yaya big boss ! Dama..n” a karo na biyu big boss
ya ‘kara furta “ talk..” , lokaci d’aya jikin little da prince ya soma rawa ganin
yadda yayi magana a ‘bace , wani irin gigitaccen tsawa big boss ya dakamusu lokaci
d’aya har glass din hannunsa sai da ya fashe Sabida irin matsar da yayi wa glass
din , lokaci d’aya Jini ya fara fito masa a hannu, da Sauri bobo ya nufi inda yake
“ ka rabu dasu , ni I will explain” akaro na biyu rai a ‘bace big boss ya d’aga
hannu ya bigi abincin da su little sukai serving dinsa , hannunsa sosai ya soma
Jini ga wani irin jijiyoyin kansa da suka tashi lokaci d’aya na tsantsan ‘bacin
rai, Allah sarki little har ya soma hawaye , cikin ‘bacin rai ya juyo ya kallesu, “
how dear you !” Da karfi ya ‘kara furta “ who the hell are you?” Ga hannunsa da
yake zubar da Jini shi bobo bata bacin ransa yake ba so yake ya fara dressing din
ciwan da yaji a hannu, da ido kawai ya kalli little rai a ‘bace ya furta “ ko ina
take kafi to da ita yanxu “ ya ‘karasa a tsawace “ you have to cool down big boss
hannunka na zubar da Jini “ cewar big boss , da hannunsa da yake Jinin ya sha’ko
wuyan bobo, shima bobo kallansa kawai yake Batare da ya motsaba daman yasani dole
ransa ya ‘baci “ 2 minute na baka kaje duk inda take ka fitar da ita da kanka”,
girgixa musu kai little ya soma yi hankali a tashe , uncle ma zai yi magana big
boss ya ‘kara dakawa kowa tsawa , yau ran maza ya ‘baci idan basu bishi a sannu ba
komai xai iya faruwa , prince ma sosai tashin hankali ya bayyana akan face d’insa ,
cikin rawar murya little ya furta “ yaya big boss kayi hakuri please karkuyi fad’a
lefi na ne gabaki d’aya , dan Allah yaya please ka bari amaka dressing “ be karasa
ba Sabida wani irin mugun kallo da big boss ya jefa masa , cikin cool voice bobo ya
furta “ kabarta ta zauna , ko na 2 days…” ne be ‘karasa ba big boss ya wanke face
d’insa da mari , abunda be ta’ba yi masa ba , cike da shock bobo ya d’ago ya kalli
fuskar big boss da ya gani tayi mugun jaa sabida yadda ransa ya ‘baci, yasan
dalilin bacin ran nasa shiyasa ko kusa be ji zafin marin da yayi masa ba , cikin
cool voice bobo ya furta “ 22 years kenan, just for little ka barta”, hannu big
boss ya dun’kule xai kaiwa bobo naushi, sai kuma ya buga hannunsa kan wani abun
decoration take a wajan wani saban Jini ya soma fito masa , stair case big boss ya
nufa da Sauri bobo ya sha gabansa , cikin d’an d’aga murya shima ya furta “ me yasa
bazaka iya hakuri ayi maka bayani ba ? Why ? Why ?” Idanuwan big boss har sun rine
sabida bala’i “ on my way “ cewar big boss , d’an murmushi bobo ya saki yana kallan
face d’in big boss “ dis time around am sorry bazan barka ba “ a karo na biyu ya
d’aga hannu xai kai wa bobo naushi little da tunda suka fara fad’a wani irin Juwa
ya soma d’ibarsa , be ta’ba ganin sunyi fad’a ba sai a yau ta dalilinsa “ cikin
d’aga murya ya furta “ please yaya ku bari , please ku bari banaso zuciya ta tana
mun zafi please ku bari dan Allah” be ‘karasa ba Sabida wani irin aman Jini da ya
somayi lokaci d’aya ya sulale a Wajan baya nunfashi………
( Tofa ana wata ga wata 😳🥹)…

PAY YOUR MONEY INTO 2681892316 Aisha umar , Zenith bank sai a turo shaidar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.


O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya
lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your
mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to
the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏…

S____22💞

Gabaki d’ayansu kan little sukai, cikin azama big boss yayi saurin ri’koshi, da
Saurinsa yake taka step musamman yadda yake tsallakesu, ko nauyin little da ya
d’auka bayaji, kai tsaye clinic room d’insu suka nufa ko ta kan hannunsa da yake
zubar da Jini bayabi, suna shiga cikin d’akin bobo ya turo ‘kofar yadda prince
bazai ma Shigo ciki ba , akan gado big boss ya kwantar da little , shi kuma bobo ya
kunna na urorin da suke anfani dashi , cikin wani irin zafin nama Big boss ya
‘barka rigar little , hatta farar singlet d’in jikinsa bai bari ba sai da ya yagata
gabaki d’ayanta, sai tin zuciyarsa ya soma dannawa , amma gabaki d’aya little be
motsa ba , a karo na biyu Big boss ya ‘kara danna zuciyar little amma gabaki d’aya
baya motsawa , cikin Sauri Bobo ya matso masa da Defibrillator, d’aya a Daidai
wajan chest dinsa ya saka masa daga ‘bangaran dama , d’ayan kuma daga ‘kasan
zuciyar sa , exactly yadda bobo ya ta’bayi masa a kwanakin baya, “ charge 200”
cewar big boss , bobo yana murd’awa big boss ya danna wa little , sosai little yayi
d’ago sosai kamar Wanda aka janyo sa ya ‘kara komawa , a karo na biyu big boss ya
‘kara furta “ charge 200” bobo yana murd’awa Big boss ya sawa little , a Wannan
karan ma d’agowa yayi sai aka ci sa’a nunfashinsa ya dawo da , cikin zafin nama Big
boss ya saka masa abun ‘karin nunfashi a fuskarsa , tun yana nunfarfashi da Sauri
har nunfashinsa ya Daidai , duk da yadda idanuwansa yake a kulle hakan be hanashi
ri’ke hannun Big boss ba guda d’aya , sosai ya ri’ke masa hannunsa kamar bayasan ya
tashi daga wajan, d’ayan hannunsa big boss yasaka yamayar da gashin kansa baya ,
gabaki d’aya fuskarsa babu walwala a tattare dashi ga wata irin jijiya da ta fito
masa sosai a wuya , kallan yadda little ya dam’ke masa hannu yayi tare da lumshe
idanuwansa kawai batare da ya zare hannunsa ba , kusan 5 minutes suna zaune a haka
babu Wanda yayi magana a cikinsu, sai lokacin bobo ya bud’ewa su uncle ‘kofa suka
shigo,cikin Sauri prince ya ‘karaso gadon da little yake kwance akai idanuwansa a
kulle sai nunfashinsa da yake fitowa ta cikin abunda big boss ya saka masa, gabaki
d’ayansu kasa magana sukai sai bin fuskar little suke da kallo hatta Big boss da ya
sunkuyar da kansa, daga sun kalli little zasu kallesa, suna zaune a wajan almost 10
minutes ‘yan yatsun little ya soma motsawa, lumshe eyes dinsa Big boss yayi tare da
kallon yatsun little sai kuma ya mayar da kallansa kan face d’in little da yake
‘ko’karin bud’esu , da Sauri su bobo suka matso kusa da shi , tun yana Mutsu mutsun
bud’e har ya bud’esu sosai akan big boss , wasu sıraran hawayene suka sakko masa ,
abin nunfashin sa yake ‘ko’karin cirewa , dakanshi Big boss ya cire masa , dukda da
yadda face d’insa take a had’e ya d’an saki face d’insa bakamar d’azu ba , a
hankali little ya furta “ Am so sorry Ya’ya ! Zance mata ta tafi tunda baka san
zaman ta “ eyes d’insa Big boss ya lumshe kamar bazai tankamasa ba sai kuma ya
bud’e bakinsa, a fusge ya furta “ it’s okay”, d’an d’agowa little yake ‘ko’karin
yi Big boss ya gyara masa zamansa sosai yadda zaiji dad’in zaman, har a muryarshi
zakaji dad’in da yaji “ yaya ka yadda ta zauna ? Ka yadda ?” Gashin kansa Big boss
ya shafa a hankali tare da lumshe masa sexy eyes d’insa “ As you wishes “, cikin
wani irin Sauri little yayi hugging d’insa , cikin sautin dariya ya furta “ Thank
you so much yaya ! I so much love you “, mu kuma fa ?” Cewar bobo da yake sakin
murmushi , yanxu ma cikin shaukin farin ciki Little ya furta “ I so much love you
all” . “ it’s okay ! Just relax” cewar Big Boss , be kalli kowa a wajan ba yayi
‘ko’karin mi’kewa , da Sauri little ya ri’ke hannunsa, d’an d’ago da idanuwansa
yayi ya zubawa little “ yaya zan kwana d’akinka please”, yanxu big boss bai kuma ce
masa komai ba sai idanuwansa da ya lumshe masa , yana barin d’akin, ‘karasawa inda
yake a kwance bobo yayi tare da shafa kansa “ Good boy! Am coming “ cewar bobo yana
d’aukar wani ‘karamin first Aid Box , tare da bin bayan Big Boss , ko da ya fito
babu kowa a Wajan shiyasa ya nufi down stairs, a tsaye ya tarar dashi , gashin
kanda duk ya rufe masa gefe gefen fuska, ga hannunsa da ya ri’ke ra baya, cikin
husky voice d’insa ya furta “ Why?” Murmushi Bobo ya saki tare da matsowa kusa da
shi yana bin hannunsa da kallo “ Nasan bakasan kowa ya ra’bemune sabida kar a cutar
damu amma trust me ! Bana tunanin zata iya cutar damu sabida itama kamar tana
bu’katar temakon mu sabida ….” Gabaki d’aya Bobo ya sanar dashi halin da take ciki
lokacin da yake masa dressing hannunsa ,tun be kai ‘karshe ba because big boss ya
d’an ta’be bakinsa , cikin I don’t care ya furta “ hey surutunka ya fara samun
ciwan kai”, wata shegiyar dariya bobo ya saki “ labarin nata ne surutu?”, banza big
boss yayi masa batare da ya amsa masa ba ya nufi part d’insa.

***** Allah sarki Abla batasan meke faruwa ba , bayan sallar isha’i da tayi , ta
koma tayi alwala tana jiran shigowar little amma har 10 be shigo ba , tun tana
murza idanuwanta har ta soma lumshe su Sabida wani irin bacci da take ji, daman
bata san duhu shiyasa ta d’an ta’ba gadon dukda ta san gadone amma bata yarda Itace
zata kwana ba shiyasa ta d’an zauna daga baki baki tana jira taga little ya shigo,
tun tana sa rai har wani irin bacci me shegen dad’i ya d’auketa ga sanyin Ac da
yake hurota ta ko ina .

***Yana shiga cikin part d’insa yaga light d’in wajan gabaki d’aya a kunne , tun da
yayi wa wajan kallo d’aya be kuma kallan wajan ba ya nufi bedroom d’insa , kwance
ya tarar da little har ya canza kayansa zuwa kayan bacci, yana ganin Big boss ya
furta “ yaya” d’an harararsa Big boss yayi batare da ya tankamasa ba yayi
wucewarsa, gyara kwanciyarsa yayi sosai akan gadon “ Nidai tunda kace ta zauna ai
shikenan ko be ma zan nuna maka ita”, cewar little , tun yana tsammanin fitowar big
boss har ya soma hanma shiyasa ya gyara kwanciyarsa sosai a kan fadon, tare da
‘kudundunewa cikin blanket din big boss me shegen kamshi da taushi, hankali kwance
bacci ya soma d’aukarsa . Be fi mituna 10 da kwanciya ba Big boss ya turo ‘kofar da
ya shiga d’azu , shima yanxu ya canza kayan jikinsa sai wasu Blue d’in kaya masu
tausayi da d’an sanshi daya saka , gashin kansa a taje yake ya nannad’e ta baya
shiyasa kyakkyawar face d’insa da babu fara’a ta fito tass da shi musamman eyes
dinsa , kan gadon ya kalla ganin little yana bacci da left side d’insa shiyasa ya
‘Karasa wajan tare da jiyowa dashi ‘bangaran dama , duk da baccin sa be nisa ba a
hankali ya soma magana cikin baccinsa , fasa tashi Big boss yayi yana sauraran me
yake furtawa “ Dan Allah yaya ka barta ta zauna..” shine abunda ya fad’a , Dan
‘karamun tsaki ya ja kad’an yana ‘kara lullu’be little da blanket d’insa tare da
rage masa ‘karfin Ac sabida kar yayi mura .

WASHE GARI

Da wari little ya farka daga bacci tun kafin Big boss ya tashesa, Lokacin da akai
kira sallah tare suka jera suka fito daga part d’insa , hannunsu ri’ke da na juna
sabida yadda little ya ri’ke masa hannunsa gam kamar Ance masa zai rabu dashi, suna
fitowa bobo da prince ma suka fito sai uncle gabaki d’ayanxu masallaci Suka nufa…
Ana idar da sallah kamar yadda suka fita tare haka suka dawo, direct Big boss part
d’insa ya nufa shi , shima Bobo nasa part d’in ya koma , little kuma kai tsaye part
d’in da Abla take ya nufa , yana zuba bakin ‘kofar ta yayi knocking ‘kofar,
alokacin itama ta idar da sallar ta sabida tun kiran sallar farko ta farka , cike
da tsoro ta furta “ wa..wanene….” Little be ce mata komai ba ya turo ‘kofar d’akin
tana ganinshi ta saki ajiyar zuciya, gabaki d’aya kayan da kawo mata ta matsar dazu
gefe ta gyara Inda ta ‘bata duk da bata share ba amma komai a kintse yake , “ Na
d’auka bazaka dawo ba “ cewar Abla , kansa little ya d’an girgiza mata “ No zan
dawo mana , yanxu ma kishirya kiyi wanka idan zamu ci abinci zamu ci a ‘kasane
gabaki d’aya kinji?” A maimakon ta amsa masa sai furta “ Nagode sosai..” No karki
damu kinji kinga na zama yayanki yanxu duk Wanda ya ta’baki kawai ki kira Little da
d’an ‘karfi zaki ganni kinji “ da Sauri tayi knodding kanta zata ‘kara masa Godiya
yayi saurin ficewa daga d’akin. Kamar yadda ya umarcetan kuwa wanka tayi kamar
yadda tayi jiya har wani iskane yake shiga ‘kofofin jikinta Sabida yadda take wanka
sosai take dirje jikinta ba kamar lokacin da take gidan uwar karuwai ba da sai tayi
kwana biyu bata samu tayi wanka ba , ko tayi ma sai cikin dare babu sabulu ko omo
sai da tayi da toka , amma daga jiya zuwa yau har wani iskace take hura ‘kofofin
jikinta. Wata doguwar Riga data gani pink colour ta d’auka ta saka , kamar an auna
jikinta sabida yadda kayan suka fito sukai mata kyau sosai a jikinta , kusan Daidai
tsawanta gashi ko kusa jikinta be nuna ba , gaban mudubin d’akin ta nufa yadda taga
wajan cike da mayuka da turare daban daban, ita kanta batasan lokacin da take sakin
murmushin farin ciki ba , tun zuwan ta jiya gidan taji gabaki d’aya zuciyarta tayi
mata dadi sosai , bata ta’bayin farincikin da tayi jiya ba arayuwarta , shiyasa ta
saka hakan a wata ‘kila Sabida sun temaka matane. Bin gaban mudubin take da ido
yadda yake sha’ke da kayayyaki a ciki, murmushi ta saki da har saida dimples d’insa
suka lotsa , wani pink turarene ya burgeta shiyasa ta d’auko shi tana sakin
murmushi, kad’an ta fesa ajikinta har wani lumshe idanuwa take wai Itace ta saka
abu me ‘kamshi, hular kanta ta cire gashin kanta duk ya cikurkud’e ga alamar datti
yana nunawa , a hankali ta mayar da turaran ta ajje ta koma inda ta d’auki rigar
jikinta, white d’in veil da tagani ne ta d’auka ta yafa a kanta , ga uban tulun
gashinta da ya Fito sosai ta cikin mayafin, gefe gefen fuskarta ma wasu irin
kwantaccen gashine a wajan da yayi wa fuskarta kyau duk yadda ta rufeshi baya
Rufuwa , Ta dad’e zaune a d’akin har ta fidda ran dawowar little sai kuma taji ya
kwankwasa mata , da Sauri ta tashi da niyar bud’ewa yashigo cikin d’akin bakinsa
d’auke da bismallah, gabaki d’aya little mamakin yadda ta koma yayi lokaci d’aya
gabaki d’aya ta sauya kamar ba ita ba , yadda yake kallantane yasa itama ta bi
jikin Nata da kallo, “ kinyi kyau “ cewar little yana sakar mata murmushi “ itama
murmushin ta sakar masa jin ya yaba shigarta “ Dagaske fa amma nayi mamakin yadda
kika iya hausa Sabida bakiyi kama da su ba” yadda ta waro masa eyes ne ya sashi
‘kyal’kyale wa da dariya “ wasa nake miki, taho mu tafi su yaya suna jiran mu” ,
kasa motsawa tayi lokaci d’aya jikinta yayi sanyi “ nace miki karki damu kin manta
na zama yayanki? Babu kowa fa kar su dunga jiran mu” kanta ta d’aga masa zata biyo
bayansa , ganin babu takalmi a ‘kafarta yasa ya janyo wani takalmi white colour ya
mi’ka mata, duk da yayi mata yawa haka ta zurashi a ‘kafarta , duk inda suka wuce
sai tabi wajan da kallo sabida tsananin mamakin wai gidane gabaki d’aya Wajan,
sosai ko ina ya burgeta, ita kadai sai murmushi ta ke saki ,irin murmushi da ta
manta yadda akeyinsa, suna tafiya little yana janta da dariya tun bata sakewa sosai
har ta soma yi masa dariya , suna fitowa falourn gabaki d’ayan bobo, uncle , prince
idanuwa suka zuba mata ganin yadda akwana d’aya tak ta canza bakamar jiya ba da
fuskarta take a kunbure , yau gabaki d’aya babu kunburar fuskar ga shi sai faman
murmushi take wa little , shi kansa bobo tantamar yadda akai ta iya hausa yake ga
kuma tsantsan mamakin da yake akanta tun ranar farko da ya fara ganinta , amma
gudun karya gayawa big boss yasa ya ajje komai a gefe har ya gano hakan da kansa ,
wannan shine babban dalilin da yasa ya taho da ita Us, babban dalilin da ya barwa
zuciyarsa sani .
“ wow my daughter kinga yadda kikai kyau sosai “ cewar uncle yana sakar mata
murmushi, saurin du’kar da kanta ‘kasa tayi kafun tayi saurin tsugunnawa har ‘kasa
da gaishesa, hakan da tayi ba ‘karamun burgesu tayi ba , ko ba komai ta nuna musu
daga cikin gidan tarbiya ta fito, side din bobo ta kalla shima ta gaishe da shi,
hatta prince da yake tsaye sai da ta gaishesa, ko wannansu cikin sakin fuska yake
amsa mata, ‘kugu little ya ri’ke ganin ta gaishe da kowa ban dashi “ Ni kuma fa ?”
Komawa tayi har ‘kasa shima ta furta “ Yaya little ina kwana”, wani irin dadi
little yaji karo na farko arayuwarsa da aka kirasa yaya shima , yadda yake dariya
gabaki d’aya sai yasaka kowa na cikin falourn farinciki, har da tsallan sa kamar
wani ‘karamin yaro wai ankirasa yaya shima , dakatar dashi uncle yayi “ kadai ji
kunya kuwa , sai faman buga tsalle kake kuma a haka kake cewa kazama yaya? Let’s
eat joor “ yana kai ‘karshen zancan sa little ya d’an turo bakinsa , Haba uncle
please na fad’a muku yanxu na girma , I have a sister nifa zai fad’awa yaya big
boss Adena cemun little , yanxu na zama Yaya Adil “ ya karasa yana kara kyal’kyale
wa da dariya . “ Big Boss “ shine sunan da Abla ta maimaita cikin zuciyarta ,
lokaci d’aya bugun zuciyarta ya canza ya somayi da Sauri sauri , tun bataga me
sunan ba lokaci d’aya taji wani irin tsoran ganinsa ya kamata , ita gabaki d’aya
bata ji me little yake cewa ba tun bayan kiran suna Big Boss da yayi , lokaci d’aya
taji nutsuwarta tana ‘ko’karin gudu”, Aushe tun d’azu little yake mata magana
bataji harsaida ya kira sunanta da d’an ‘karfi “ Ibtissam “ da Sauri ta firgita
tana amsa masa da “Na’am…” kına lapiya ?” Ya kara tanbayarta , kasa bud’e masa baki
tayi sai kanta kawai da ta jinjina masa , “ okay taje muci abinci “ yanxu ma kanta
ta ‘kara jinjina masa , tun kafun su ‘karasa dinning taja burgi da Sauri jikinta
har ya soma rawa , gabaki d’aya dakatawa sukai da tafiya ganin lokaci d’aya ta
burki ce tana ‘ko’karin Jan baya , bakinta har ya soma rawa , ba komai ne ya haifar
mata da hakan ba sai james da ta gani da shigar sojoji, yadda ta ‘kura masa ido ne
yasa kowa ya kalli direction d’in, da hannu bobo yayi masa alamar ya tafi, tana
barin wajan kuwa ta saki wani irin ajiyar zuciya da gabaki d’ayansu sai da sukaji “
kına jin tsoronsu?” Cewar little , da Sauri ta jinjina masa , “ ya tafi ai bazai
miki komai ba “ yanxu ma kanta ta jinjina masa tsoran da take ji na d’an raguwa , a
haka har suka ‘karasa dinning d’in da yake cike da abinci kala kala , tun daga ido
zaka san ba’kamin kud’i aka kashewa abincin ba , “ yau ni zanyi serving din kowa da
kowa “ cewar little kafun ya jawa Abla kujera, a ra’be ta zauna gabaki d’aya takı
sakin jikinta , da kansa little yayi serving d’in uncle favorite food d’insa , yayi
serving yaya bobo da yake gefensa shima haka yayi serving dinsa shi da prince ,
abla kuwa mamakin Tulin abincin da aka girka take ganin uban abinci da yawa , ita a
rayuwarta bata ta’ba ganin irin abincin nan ba da suke ‘ko’karin ci gashi ko
wannansu kalarsa da ban shiyasa take mamakin yadda akai suke cinsa , little ya
fahimci bata iya cin abincinsu ba shiyasa yayi saurin barin Wajan yana furta “ am
coming “ be jima ba ya dawo hannunsa d’auke da wani kwalin yoghurt madaidaici tare
da cup a hannunsa , sosai ya cika mata cup d’in sannan ya ajje mata fruit agaban ta
sosai , ganin duk sun kallesa a fakaice cikin French ya furta “ bata iya cin kalar
abincin muba”, daga nan babu Wanda yakuma magana , bayan little ya zuba abincinsa
shima , tunda ya ajje mata cup din yoghurt din da fruit ta ke binsu da kallo
batare da ta ta’ba komai ba , ji tayi hawaye na sakko mata , lokacin da ta soma
shash she’kar kuka gabaki d’aya dakatawa sukai daga cikin abincinsu suna binta da
kallo, “ bakyasan abincin na canza miki?” Shima little kamar me shirin yin kuka ,
da Sauri ta girgiza masa kai “ zan iya d’aukan guda d’aya na kaiwa Arwa ?” , ita
kanta tun kafin ta ‘karasa maganar ta kuma sai kuka ya kwace mata , sosai take yin
kukan little na ‘ko’karin dakatar da ita bobo ya hanashi,gabaki d’aya sai suka zuba
mata idanu ganin kukan mata bame ‘karewa bane ya furta “ da alama tana bukatar masu
shan jini” da Sauri Abla ta furta “Kayi hakuri na dena “abun cinta ya nuna mata “
oya cinye abincin ki “ hannunta har rawa yake lokacin da ta d’auki Youghurt din ,
tunda ta saka shi a bakinta bata saukeshi ba , ita gabaki d’aya ta manta da suna
zaune a wajan sabida yadda zakin Youghurt din ya yi mata mugun dadi dan arayuwarta
bata ta’ba Shan yoghurt ba sai yau da little ya bata , yadda Tasha Youghurt din
sosai hakan yayi musu dadi dan gabaki d’aya yoghurt din ta shanye sai data ga babu
tukunna ta ajje cup , sai kuma kunya ya kamata ganin lokaci d’aya ta shanye farin
abunda little ya bata dan ita Batasan ma yoghurt bane , babu Wanda ya nuna mata ya
ganta kowa abincinsa yake ci, hatta fruit din da suka bata shima ta shashi sosai ,
suna gama breakfast din suka koma falourn gabaki d’ayansu banda bobo da ya fita ,
little da prince sai faman janta da iri suke tun bata sakewa sosai har ta sake
kamar sunyi shekara guda take sai faman dariya suke wa junansu , uncle na gefe da
jarida a hannunsa sai faman murmushi yake saki shi kad’ai, sun dad’e sosai suna
hira ganin almost 12 little yasan a ko wana lokaci Big Boss zai iya fitowa shiyasa
ya kalli fuskar Abla yaga tana murmushi, bayaso Big boss ya sata kuka shiyasa
gabaki d’aya hope dinsa ya ragu sabida besan me big boss xai mata ma idan ya ganta
dukda yasan bazai ta’ba korar taba tunda yace yana san zamanta a wajan , wani idea
ne ya fad’o masa ganin anytime big boss zai iya fitowa , can d’akin kifayensu
little ya ja ta , yadda taga kifayen suna motsi kwanin sha’awa ita kanta bata san
lokacin da ta ‘karasa jikin glasses Dinsu ba tana shafawa, yadda suke motsi cikin
kaloli masu burgewa sai sun baka sha’awa itama hakance ta kasance a ‘bangaran ta
batare da tsoron ganin suna motsi ba ta soma shafa glasses din , ita kadai sai
faman murmushi take saki , little na tsaye shima yana bin kifayen da kallo saida
sukai kusan 40 minutes a d’akin , alokacin ya d’auka big boss ya fita daga falourn
shiyasa suka fito daga d’akin little sai faman labari yake bata ita kuma tana masa
murmushi kawai, saida suka zo tsakiyar falourn kamshin turaransa y dokesu gabaki
d’aya musamman Abla da taji bugun zuciyarta ya canza lokaci d’aya ta dunga jin wani
irin fad’uwar gaba ga kamshin da take ji na shigar mata hanci , yadda kamshin yayi
mugun yi mata dad’i har wani lumshe idanuwa tayi tana ‘kara sha’kar daddad’an
kamshin, ga wani irin da ta faraji lokaci d’aya da taji ‘kamshin turaran ,Little
kuma gabaki d’aya kasa motsawa yayi Sabida ganin baki big boss zaune akan kujera
yayi crossing legs d’insa ga idanuwansa da suke a lumshe , uncle na gefensa shi da
prince , a hankali little yayi sallama yana shigowa cikin falourn, ita gabaki d’aya
Abla bata san da zaman Big Boss ba sabida yadda kanta yake a sunkuye har ta ‘karasa
shigowa cikin falourn Sabida yadda takejin zuciyarta , little yana shiga suka da
Big boss ya nufa tare da zama a kan carpet yana yiwa Abla signal akan ta matso kusa
dashi amma ita gabaki d’aya bata san yanayi ba sabida yadda ta sunkuyar da hanka
‘kasa tana tafiya , a shagwa’be little ya furta “ Yaya Big boss “ wani irin bugawa
zuciyar Abla tayi da ‘karfi cikin sauri ta d’ago da idanuwanta , basu sauka ko ina
ba sai kan kyakkyawar face d’insa da ya lumshe , kasa sha’kar nunfashi Abla tayi
sabida yadda kyan Big boss yayi mugun rud’ar da ita da Sauri sauri zuciyarta ta
cigaba da tsanan ta gudu, ga wani irin rawa da jikinta ya somayi lokaci d’aga ,
mugun tsoransane ya kamata gashi ta kasa d’auke idanuwanta akan sa musamman red
lips dinsa da yayi mugun tafiya da ita sai kuma tsagar girarsa da ta zubawa idanuwa
, tunda take bata ta’ba ganin kyakkyawa kamarsa ba dukda tsananin kyan dasu little
suke dashi sai taga kamar nashi kyan na dabanne, tana cikin tunanin da ta fad’a ya
soma bud’e eyes
d’insa dan tun lokacin da little ya zauna a carfet yaji alamar ana kallansa ,
gabaki d’aya eyes d’insa ya bud’e basu sauka ko ina ba sai cikin idanuwan Abla da
ta kafe shi da kallo, lokaci d’aya yayi mugun had’e ransa tare da tsuke fass d’insa
sosai, wani irin kallo da ya jefa matane yasa tashiga hankalinta , cikin Sauri ta
d’auke idanuwanta tana sunkuyar da kanta ‘kasa , gabaki d’aya ko d’an yatsanta ta
kasa motsawa Sabida wani irin shakkarsa da ya kamata ,maida kallansa kan little da
ya zauna a ‘kasa yayi , shima nasa raban kallon Big boss ya jefa masa , amaimakon
ya Tashi daga ‘kasan sai ya shagwa’be masa face d’insa “ please Yaya, please”,
d’auke eyes d’insa Yayi daga kan little da ya shagwa’be fuska, cute red lips d’insa
Big Boss ya d’an ta’be Batare da ya ‘kara kallan Little ba ko Abla data ‘kame kamar
gunki ta kasa motsawa , shi kansa prince tsoran ya ce mata ta zauna yake kar Yaya
ya bashi na sa kasan, uncle kuwa da gangan ya’ki tanka musu, kowa jiran reaction
dinsa akan Abla yake , gabaki d’aya idanuwa suka zuba masa suna jiran suka abunda
zaiyi mata , Allah sarki little sai faman Addua yake cikin zuciyarsa, a bazata
little yaji muryar Big Boss “ should I?” Da Sauri ya girgiza masa kai sai kuma ya
bud’e baki “ No yaya bari na zuba maka da kaina”, da kansa little ya zubawa Big
boss abinci ga Abla da tun da ta tsaya ta sunkuyar da kanta itama ta kasa d’agowa ,
har wani zufane ta soma ganin suma gabaki d’aya babu me magana a cikin su, ganin ya
soma cin abincinsa a tsanake yasa little sakin ajiyar zuciya , da sunga yana
‘ko’karin d’ago da eyes dinsa suke saurin d’aukewa dan sosai Big Boss ya tsani
kallo, yadda yake tauna abincin hankali kwance kamar be san suna wajan ba amma
gabaki d’aya ya karanci ko wannan su tsaf, kad’an yaji abinci yana gyara zamansa
sosai a kan kujerar da yake , yanxu kam gabaki d’aya jira Suke suji Wana hukunci
zai d’auka akan Abla dan idan yace No toh tabbas No d’innance babu me canzata, amma
ga mamakinsu kwata kwata be tanka musu ba, sai ma diamond watched d’in hannunsa da
ya kalla sau d’aya yana mi’kewa tsaye , har yanxu Abla tana a yadda take dan
Dagaske ta kasa motsawa daga inda take tun kallan da ya jefa mata . Sosai little ya
zuba masa idanuwa a shagwa’be, shi kuma amaimakon ya basa amsa sai ya lumshe masa
idanuwansa , da’kyar ya iya bud’e cool husky voice d’insa , cikin ‘kasa ‘kasa da
murya big boss ya furta “ Take care “, sabida yadda suka nutsune yasa gabaki d’aya
sukaji me yace , hatta Abla da taji saukar muryarsa saida ta lumshe idanunta. Bai
kuma tanka musu ba ya nufi hanyar barin falourn , gabaki d’aya da ido suka bisa har
ya wuce , yana fita gabaki d’aya suka saki a jiyar zuciya kusan a tare , cikin wani
daka tsalla Little yayi hugging Uncle “ uncle yayi approving ko?” Shima uncle
murmushi ya sakar wa little yana jinjina masa kai , Big boss ba ‘karamin mamaki ya
basu ba ganin gabaki d’aya be tankaba, tabbas little d’in ya cika little , tunda
har ya amince wata ta zauna Sabida little , dukda be fito ya fad’a musu da baki
ba , amma dole kam Abla tayi taka tsantsan dan kamar yadda yake saka su little
punishment babu abunda zai hana ya’ki saka ta itama . “ Daughter ki zauna mana “
cewar uncle yana kallan ta, haka kawai yarinya ta kwanta masa arai , besan dalili
ba yaji ita kad’ai ce zata iya yi masa aikin da yake so dukda be sani ba Daidai ne
hakan abunda zaiyi ko kuma yana ‘ko’karin yin kuskure ne ?amma duk da hakan bazai
ha’kura sai yayi abunda ya ‘kudurta cikin zuciyarsa.” A hankali Abla ta d’ago da
idanuwanta ganin baya wajan gabaki d’aya sai kamshin sa da ya bar musu , ita kanta
saida ta saki ajiyar zuciya , maganin ta little ya d’akko mata duk yadda yake da
mugun tsoran shan magani yau little yana bata Tasha sabida gani take kamar
kyakkyawan mutumin da ta gani d’azu yana wajan , cikin zuciyar ta kuma addua take
ko aljani ne ta gani . Ta kasa sakewa gabaki d’aya kamar d’azu tun ganin big boss
da tayi, saida duk maganar da little da prince zasuyi mata saidai kawai ta sakar
musu ya’ke, amma bakinta gabaki d’aya yayi mata nauyi .
Ana kiran sallahr azahar little ya rakata har d’aki shikuma ya koma suka tafi
masallaci . Tana shiga cikin d’akin tayi saurin dafe saitin zuciyarsa , tana kulle
idanuwanta taga fuskarsa lokacin da yake ‘ko’karin bud’e eyes dinsa , da Sauri ta
bud’e idanuwanta tana karanto addua dan ita gani take kamar gamo tayi , ga kamshin
turaransa da har yanxu take jinsa cikin hancinta , da tayi ‘ko’karin kulle
idanuwanta zata ga kamar yana wajan , kallan da yayi mata d’azu sai da tantar
cikinta ta kad’a musamman idanuwansa da yafi komai bata tsoro. Da kyar ta iya tashi
tayi sallar azahar , sabida wani irin kasala da takeji , tana idar da sallanta
little ya kawo mata fruits da yawa da yogurt shima ,lokacin da zai fita har ajiyar
zuciya ta sauke ganin be ce mata ta Fito ba , kad’an ta iyasan yoghurt din dan ji
take cikinta a cike yake taff batajin yunwa ko kad’an.

****karfe 8:30pm gabaki d’aya suna falourn ‘kasa har Abla da little yasaka tafito
dan dole , ko wannansu yayi wanka ya canza kayan jikinsa , yau uncle yana d’akinsa
daga little sai prince sai kuma Abla da take sakar musu murmushi, yadda suke fara’a
sosai kamar a tsakaninsu mutum zaiyi tunanin yan uwane gabaki d’aya musamman yadda
suka dage wajan sakata murmushi. Little agaba gaba Wajan bata labarin dariya, sosai
ta sake dasu kuwa itama tana basu labari sai faman dariya suke yi abunsu, sallamar
bobo ne ya katse musu hirarsu da Sauri little ya ‘karasa wajan da yayi hugging
d’insa “ welcome back yaya bobo” zaka karya nifa” cewar bobo ganin yadda little ya
d’anesa , “ welcome back yaya bobo”, shima hannu bobo ya daga musu kafin ya kallesu
gabaki d’aya “ gaskiya fa kun canza yau bakuyi futunawa” saurin rufe idanuwansa
little yayi “ Haba yaya bobo” kunnansa bobo yaja “ ba gaskiya na fad’a ba?” Da
Sauri little ya amsa “ gaskiya yaya amma ynxu ai zamu dena tunda muma muna da
sister” sai a lokacin bobo ya kalli Abla da take wasa da kyanta , a hankali ta
furta “ sannu da zuwa” cikin sakin fuska itama bobo ya amsa mata “ Yawwa kanwar
little” hau wani sautin dariya zakaji little yana yi sabida ya zama ya ya shima,
bobo bai zauna a falourn ba ya wuce part d’insa . Sai wajan 10pm bobo ya fito ganin
basu kwanta ba,” you guys baku kwanta ba har yanxu ? Babu ruwana idan yayanku ya
dawo” little zai shagwa’be masa fuska bobo yayi saurin furta “ Nidai babu ruwana,
you guys ya kamata ku kwanta especially kai da sister d’inka tunda baku da lapiya ,
kana yin musu kuma zan kirawosa yanxu”, haba mana yaya just one hour more “ cewar
little amma ganin bobo na ‘ko’karin daukar phone dinsa little yayi saurin furta “
shikenan yaya zamu kwanta yanxu , good night, sister taso na rakaki d’akinki “ ba
musu kuwa ta bisa , har d’aki ya rakata ganin dare beyi ba sosai yasa kawai ya
kunna mata Tv acewarsa idan ta gama kallo sai ka Tashe light din. Shima direct basu
kuma zama a falourn ba suka nufi part d’insu shida prince . Bobo yana zaune a
falourn yana jiran dawowar Big boss amma har wajan ‘karfe 12 na dare babu big boss
babu alamarsa , yau a gajiye ya dawo shiyasa ya nufi d’akin su little dan ya
dubasu, lokacin gabaki d’ayansu sunyi bacci , hatta uncle da ya shiga d’akinsa
bacci yake shiysa ya rage fitilin falourn ya nufi part d’insa, har wajan karfe 2 na
dare na jiran tsammanin dawowar big boss , har bacci ya d’aukesa sabida yadda ya
gaji.
3:30am motocin Big boss suka danno kai cikin gidan , a wannan lokacin yasan
gabaki d’aya sun kwanta shiyasa be wuce part d’insa ba saida ya duba lapiyarsu
dukda shima yau a gajiye ya dawo cikin gidan sabida headache din da yake fama dashi
ga idanuwansa da sukayi mugun red sai faman lumshe su yake .

WASHE GARI

Ana kiran sallar asuba gabaki d’aya suka fito falourn , yau abun mamaki kowa ya
fito kamar yadda suka saba fitowa amma banda big boss , sun dad’e suna jiran
fitowarsa amma basu ganshi ba , little har ya damu yana ‘kokarin zuwa part d’insa
bobo ya hanasa sabida sallah da ake ‘ko’karin yi , haka gabaki d’ayansu suka nufi
masallacin banda shi , dan kuwa abune me matukar wuyane xai hana sa fitowa kowa
kuwa rashin lapiya yake yana fitowa sallah dukda shima rashin lapiyan da wuya su
gane bashi da ita . Ana idar da sallah tun kafin kowa ya fito daga masallacin bobo
ya nufi part d’in Big Boss dan yasan ba lapiyar sa kalau ba tunda be fitowa
sallaba, yana shiga part d’insa ya kulle door din ta ciki ta yadda ko su little sun
saka turn print d’insu bazai bud’e ba, gabaki d’aya ko ina da duhu , cikin Sauri
bobo ya tura ‘kofar bedroom d’insa da yaga alamar hasken fitula, yadda yaga Big
boss a zaune ne yasa yayi saurin ‘karasawa inda yake , yana kokarin ta’basa big
boss yayi saurin hankad’asa baya “ don’t touch me” shine kadai abunda ya iya
furtawa, Bobo bai damu ba yakara yunkurin ta’basa big boss yayi saurin bige masa
hannu, Allurar da yagani akan center ne yasa gabaki d’aya mamaki ya kamasa , xai
d’auki allurar big boss ya ‘Kara bige masa hannu, wata allura ya janyo xai yiwa
kansa bobo yayi saurin ri’ke hannunsa sai alokacin yaji yadda jikin Big boss yayi
mugun zafi, zai ta’ba masa goshi big boss ya kara bige masa hannu , cire hannun
bobo yayi yana ‘ko’karin yin allurar cikin Tashin hankali bobo ya kai hannu zai
fusge amma ina tuni big boss ya yi allurar , cikin Sauri Bobo ya fita daga d’akin,
be jima ba ya dawo d’auke da babban ruwan roba me shegen sanyi, gashin big boss
gabaki d’aya ya rufe masa fuska a Bobo na kokarin ta’basa big boss ya hanasa
hakan , tunda ya sunkuyar da face d’insa kasa be katta dawo da ita ba sabida yadda
jijiyoyin wuyansa suka tashi sosia , idanuwansa sunyi jajawurrr ba kad’an ba ,
lokaci bobo ya kalla da Sauri ya bude ruwan nan duk da yadda yake da mugun sanyi
haka ya fara tuttulawa big boss akansa…..

PAY YOUR MONEY INTO 2681892316, Aisha umar zenith bank sai a turo shardar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya
lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your
mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to
the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏…

S____23💞

Lumshe idanuwansa yayi sosai sabida ruwan da bobo ya watsa masa me shegen sanyi da
har cikin gashin kansa saida yaji sa , a karo na biyu bobo ya ‘kara bud’e wani
saban ruwan ya tuttula masa har farar shirt dinsa sai da ya ji’ke , daga inda mutum
yake xai iya hango white singlet d’insa da farin fatar jikinsa. A maimakon bobo ya
rage ‘karfin Acn sai ‘karawa ma dayayi, a hankali ya Mayar da kansa baya ya jin
gına da jikin sofa d’in da yake , sosai jijiyoyin kansa suka mi’ke, wata allurar ya
janyo batare da ya bud’e eyes din saba , da Sauri bobo yayi saurin d’auketa yana ja
baya “ why please? Kanaso kaji wa kanka raunine? Please kabar allurar nan haka “,
ko ta kan maganarsa Big Boss be biba sai ma hannun sa d’aya da ya sake wa dressing
ya mi’kamasa “ Give it back !” Cewar Big boss , Baya bobo yayi kad’an “ am sorry
gaskiya bazan baka ba “, Lokaci d’aya big boss ya bud’e idanuwansa da sukai mugun
yin jaa sosai , yadda idanuwansa sukai jaa sai ya ‘kara fito da kyawun idanunsa
kamar ya saka kwalli, “ kasan illa kake ‘ko’karin yiwa kanka , me yasa duk lokacin
da ranka yake a’bace bazaka iya dannewa ba sai kayi wa kanka wannan allurar ?
Please !”cewar Bobo, yanxuma hannunsa Big boss ya mi’ka masa a d’an zuciye ya furta
“ Give it back “, shima bobo a zuciye ya furta “ Bazan bayar ba ! So kake kayi wa
kanka illah ? Wazai kula da little? Prince? Uncle? Please ka rage zafin zuciyar nan
taka please “, cikin cool voice big boss ya furta “Get out of my room “, bobo zai
‘kara magana cikin zafin rai Big boss ya ‘kara furta “ I said get out of here “,
girgiza kansa kawai bobo yayi batare da ya ajje allurar ba ya sata cikin aljihunsa
tare da barin part d’in . Yana fita Big Boss ya lumshe idanuwansa da sukayi ja
sosai, ya dad’e zaune a wajan jikinsa a ji’ke , kusan 10 minutes sai kuma ya tashi
ya nufi toilet d’insa .
Bobo yana sakko wa ya tarar dasu little a tsaye duk sunyi sarko sarko suna
jiran sakkowansa , murmushin da ya sakar musu ne yasasu ajiyar zuciya “ why kuka
tsaya anan ? Ku dena damun kanku babu abunda ya sameshi , kunsan yanzune lokacin
baccinsa , anytime ya tashi zaku gansa ya Fito okay?” A d’an shagwa’be little ya
furta “ yaya ko zanje na dubasa? Tunda ya fita jiya ban ‘kara ganin saba fa “
hannunsa bobo ya kama suka nufi kan kujera “ little banda rashin ji kuma kasan
yayanka ayyuka sun masa yawa ko?” Kansa little ya d’aga masa “ then allowed him to
relax jiya be dawo gida da wuri ba ! Kaga yau ko training baza muyi ba , Nima
guduwan training din zanyi “ da Sauri prince ya matso kusa dashi “ Dagaske kake
yaya bazayı ba?” Daman a cikin su babu Wanda yafi tsanar motsa jikin nan kamar
prince shiyasa bobo yana amsa masa har da wani juyawa yayi na farinciki “ hannunsa
d’aya ya dunkule tare da furta “ yessss”. Yaya “ little ya ‘karakiransa , shima
amsa masa bobo yayi yana kallansa “ yaya please yau munasan zuwa siyayya kaji “
tell me what you want sai a kawo muku har gida “ da Sauri little yace “No yaya
wannan siyayyar little sister ne , kaga ya kamata ta za’bi kayan da take so ko?
Please just say yes and bata iyacin abincin mu bafa “kumatunsa bobo ya shafa “ Are
you happy?” Yes yaya sosai , be bari bobo ya kuma magana ba ya furta “ yaya ina
farin ciki sosai, I also have a sister now , inaso na sata farin ciki itama , bata
da family , ni kuma ina da ku my only family, and now we are 6 not 5, okay ?” Kaifa
fi’ilinka ya maka yawa tunda ka samu sister kake behaving sai kace wani babba ….”
Uncle bai’karasa maganar da yakeso yayi ba Sabida ‘kamshin turaran Big boss da
suka ji daga sama , gabaki d’aya cikin sauri suka kalli direction d’insa , yana
tsaye daga bakin elevator d’in da ya fito fuskarsa gabaki d’aya babu fara’a , ba
kamar ko da yausheba yau face d’insa tafi ta ko Yaushe had’ewa shiyasa lokaci d’aya
little da prince Suka shiga taitayinsu , uncle da bobo kuma idanu kawai suka zuba
masa. Kamar ko da Yaushe sanye cikin wasu white d’in kayan Hermes farare tas dasu
riga da wando said’an jikin rigar da aka yiwa ado da d’an ba’ki kad’an, Sabida
yadda rigar ta kama damtsen hannun sa sosai muscle dinsa suka fito farare tass da
su , ‘kafarsa sanye take cikin black d’in Nike Air Max din ta kalmi ,yau hatta
gashin kansa be tufkeba kamar yadda ya saba sai nannad’e shi da yayi , hakan ya
bawa farar kyakkyawar fuskar fitowa sosai ga Diamond necklace d’insa da kullum baya
rabuwa da shi, sau d’aya ya kalli ko wannansu yana d’auke kansa , dan gabaki d’aya
yaji maganganunsu, yadda su uncle suke binsa da kallo ne yasa ya ‘kara had’e face
d’insa yana takowa a hankali kamar bayasan taka ‘kasa , har ya ‘karasa sama akan
white sitter suna binsa da kallo, ko sau d’aya be d’ago ya kallesu ba sai yayi
kamar ma baisan da zaman suba, “ Morning yaya” cewar prince da little da suka had’a
baki kusan a tare , bai amsa musu da baki ba sai lumshe eyes d’insa da yayi kad’an
alamar amsawa , gabaki d’aya falourn shiru ne ya biyo ba , sabida mamakin fitowar
Big Boss a wannan lokaci , dan yawancin lokuta a wannan lokacin ne yake bacci ,
d’ago da eyes d’insa yayi ya zubawa little , cikin Sauri little yayi masa fiki fiki
ido, d’an motsa lips d’insa gefe d’aya big boss yayi da hakan ya bawa dimple dinsa
lotsawa , gabaki d’aya sai suka tsaya kallansa duk da abunda yayi baza’a kirasa
murmushi ba sannan baza’a kirasa ya’ke ba , ganin yanda suka wani kallesa ne yasa
ya tsuke face d’insa , cikin cool voice d’insa kamar bashi ba ya furta “ You are
happy because of that thing ( Abla 😂) ryt”, yadda ya kira thing d’inma kamar Wanda
aka saka dole , da farko little begane wa yake nufi ba saida yaga kallan da prince
yake masa , da Sauri ya furta “ yes yaya”, hannu d’aya big boss ya saka ya shafa
girarsa da take a tsage kamar ba zai kuma tanka wa ba sai kuma ya ‘kara furta “ you
all want to leave with her ?” Ya ‘karasa yana kallan prince da little , cikin Sauri
suka furta “ yes yaya” dan ko magana yayi bayaso ayi masa knodding , sannan bayasan
‘bata lokaci koda kuwa sai yi hour kafun yayi magana . Kansa yayi knodding a
hankali, shi kansa bobo kasa magana yayi yasan tunda ya fara kiran Abla da thing ba
lalle inuwarsu tazo d’aya ba , bai kai ga ‘Karasa maganar zucin saba sabida saukar
muryar big boss da ya ‘karaji “ bring her here”, lokaci d’aya gabaki d’aya Suka
zaro masa ido, little kuma cikin sauri ya nufi d’akin Abla , “ Ba ka yadda ta zauna
ba ?” Cewar bobo dan har ga Abla Bayaso big boss yayiwa Abla komai , amma ganin ya
sharesa ba tare da ya tanka masa ba ne yasa yayi shiru shima yana jiran yaga me
zaiyi, uncle kam sarautar Allah ya zubawa ido shi kansa ya kasa magana dan besan me
Big boss zaiyi ba . Ko cikakken 3 minutes little beyi ba suka sakko shida Abla da
wani irin masifaffen ‘kamshin turaranta ya do’kosu dukda ko kwatan kamshin turaran
big boss beyi ba , kanta a ‘kasa cikin shigar doguwar rigar da tayi purple colour
da yayi mata kyau sosai sai veil d’insa da ya ‘kara haskota, tun kafin su ‘karaso
cikin falourn bugun zuciyarta ya fara da Sauri Sauri, hannunta har ya fara rawa duk
da bata d’aga Kai ta kalli mutanan falourn ba amma ta gane masifaffen ‘kamshin
turaran jiya da ta dad’e tana ji cikin hancinta, lokaci d’aya taji kayan cikinta
sun juya sabida tsoro dukda bata d’aga fuskarta ba Sabida shakkar d’ago da face
d’inta da take , hatta tafiyarta saida ta canza sai faman hard’e ’kafa take , suna
shigowa cikin falourn ta d’an d’ago kanta da niyar gaishesu, idanuwanta basu sauka
ko ina ba sai a kan face d’insa da ya lumshe , lokaci d’aya ta fara ‘ko’karin
birkicewa har wasu kwallane da ita kanta batasan dalilin fitowarsuba suka tarar
mata cikin idanuwa, cikin sauri ta d’auke eyes d’inta , muryarta har rawa yake
wajen furta “ ina.. ina.. kwana…” gabaki d’aya sai suka ‘kara kallansa sabida sunsa
da shi take amma kamar Wanda akai magana da gunki, akaro na biyu ta ‘kara furta “
ina… kwana “ be amsa mata ba , shi kansa little a tsure yake dan gabaki d’aya ya
manta be fad’a mata kada tayi Hausa ba, koda ace bata iya turanci ba zai fi mata
alkairi akan tayi Hausa a gaban big boss dan yana d’aya daga cikin abunda yayi
mugun tsana shiyasa duk lokacin da yake gida basa amfani da Hausa, lokaci d’aya
Abla ta fara shash she’kar kukan da bata san dalilin fitowar sa ba, prince har da
dafe kai ganin tana ‘ko’karin janyo musu wani hawan ruwan, rai a ‘bace ya bud’e
eyes dinsa da sukai mugun ‘kad’awa na ‘bacin rai, wani irin mugun kallo da ya zuba
mata lokaci d’aya tayi kneeling dan sosai wani irin tsoran sa ya ‘kara shiga cikin
zuciyarta , ita kad’ai bakinta sai rawa yake sabida tsananin tsoran da ya kamata ,
d’an ta’be bakinsa yayi kad’an yana d’auke eyes dinsa zuwa na little da yayi tsutsu
dashi kamar mara gaskiya , akaro na biyu ya ‘kara bud’e bakinsa cikin tsantsan
American English d’in da ya zauna masa ya ‘kara furta “ duk kun amince da
zamanta ?” Da Sauri cikin turancin prince da little suka basa amsa , direction din
bobo ya kalla da ido , wani murmushi bobo ya saki kafun shima ya furta “ yeah “,
the same amsar da uncle ya basa kenan, wani irin murmushin gefen baki big boss yayi
da yayi mugun basu mamaki ba kad’an ba , banda Abla ta sunkuyar dakanta ‘kasa tun
bayan tsugunnawar da tayi, bakad’an ba tsananin mamaki ya kamasu dan abune me mugun
wuya kaga ‘karamun murmushin gefen bakin big boss . “ she will stay”… cewar Big
boss yana katsemusu tunaninsu, cikin murna little ya fara gode masa “ thank you so
very much yaya” hannu kawai big boss ya d’aga masa lokacin da ya zubawa Abla
narkakkun idanuwansa da yasa tayi saurin ‘kara sunkuyar da kanta ‘kasa ga hawayen
da suke sakko mata suma , hannunta sosai yake rawa haka bugun zuciyarta ma da take
ji kamar zata fito waje , “ My orders !” Ya ‘kara furtawa a gajarce dan bayasan
magana me tsawo gabaki d’aya , shuru falan yayi lokaci d’aya kowa yana jira yaji me
zai kuma fad’a , sai ya d’auki good 1 minutes kafun ya iya bud’e bakinsa kad’an
kamar me ciwan baki “ from today kece sabuwar me aikin Simba”, cikin cool voice
bobo yayi saurin furta “ big boss please!” Big boss bai saurareshi ba ya cigaba da
maganarsa “ 7:00am zaki kaiwa Simba abinci , 3:00pm for his lunch and 8pm for his
dinner , in fact komai nashi ke zaki kula dashi” ya ‘karasa da d’an ‘karfi , cikin
sauri cike da tsoro Abla ta furta “ Toh…”duk da bawani turanci ta iya sosai ba tana
jin me ake cewa mayarwane bata iya ba sosai amma dukda haka ta gane maganganun da
dukda yadda turanci yake fitowa , bobo zai sake magana Big boss ya ‘kara bud’e
bakinsa , “ 7:00am for the training time ko 1 minutes kika ‘kara , zaki gane
kurenki, anytime idan zan dawo I need my coffee and also dis is your job , idan
kika kuskura kika kwana without my coffee… “ bobo zai ‘kara magana ya furta “ kin
yarda ko baki yardaba “ yadda ya fad’a cikin d’an tsawane yasa Abla tayi saurin
furta “ Na Aminci” dukda yadda little yake girgixa mata kai amma aikin gama ya gama
tunda tace masa ta amince, be kuma cewa komai ba ya mi’ke tsaye tare da zuba
hannayensa cikin aljihu “ Daga yau na ‘karajin wannan banzan yaran naki ki tabbata
sai na mugun sa’ba miki” yana kai ‘karshen maganarsa ya nufi hanyar fita , cikin
Sauri bobo ya mi’ke zai bisa uncle yayi saurin ri’ke masa hannu , da French uncle
ya furta “ No bobo karka bisa kasan yanzu kana masa magana akanta zai ‘kara nunka
mata wani aikin, thank god kad’an ya bata yanxu amma kana sake yin magana zai ‘kara
ninkamata and ta riga ta amsa da ace bata amsa bane da abun yazo da sau’ki” ,
ajiyar zuciya bobo ya sauke cike da tausayinta ya kalli direction d’in da take ,
suma little da prince gabaki d’aya idanuwansu suka zuba mata musamman little da
yake ji kamar yayi kuka, ita kuwa Abla gani take zata iya yi musu ko wana irin
aikine tunda har zata zauna a cikinsu, gani take ai aiki me sau’ki tunda simba
kawai zata dunga yiwa abinci, ita gabaki d’aya ta d’auka
simba mutum ne da zata dinga kaiwa abinci safe zuwa dare sai kuma coffee d’inda
zata dinga kaiwa wanda ganintake ba aikine masu wahala ba , abu d’aya ne ya sakata
cikin tsoro da damuwa , rashin turancinta sosai tunda ya fad’a idan ta sake Hausa
sai ya ‘bata mata , a tausha she little ya furta “ me yasa kika yadda zakiyi aikin
nan ?” Murmushi me ciwo kawai Abla ta sakar masa sabida tuna rayuwarta a gidan
karuwai da tayi “ wannan ai bame wahala bane na saba yin aikin da suka fi wannan
yawa ma “ , shiru little yayi Sabida abinda tace , a hankali ya ‘kara furta “
kinsan wanene simban ?” Itama Abla amaimakon ta basa amsa sai ta ‘kara sakar masa
murmushi tana d’aga masa kanta alamar Eh , cikin daddad’ar muryarta ta furta “
Shima ba d’an uwanku bane ?” , sakin baki sukai gabaki d’aya suka zuba mata ido ,
gabaki d’aya tunaninta ta d’auka Simba mutum ne Kenan , Tashin hankali” cewar
prince cikin zuciyarsa , little “ Innalillahi “ kawai yake maimaitawa ganin bata
san wanda zata dunga yiwa aiki ba “ shi kansa bobo da uncle sun tausaya mata ganin
bata fahimci Wana irin aikine zata dunga yi ba , maganar turanci duk me sau’kine ko
su little zasu iya koya mata . abu me wahalar yadda zata dinga kula da simba ,
ganin lokaci na tafiya sosai bobo ya dakatar dasu gabaki d’ayansu “ let’s it first
“ hakan ne kuwa ya faru gabaki d’aya suka nufi dinning , yau babu James Sabida bobo
ya hana sa zuwa sabida gabaki d’aya sun fahimci Abla tana tsoran sojoji Wanda
dolene ta dena jin tsoransu tunda batasan Inda ta shigo ba . Little da prince ne
sukai serving d’insu ba lefi yau ta d’anci wani abun dukda ba sosai ta iya ci ba
sai Youghurt data sha sosai . Har suka kammala cin abinci babu Wanda yayi magana ,
tsakanin little da prince kowa tunanin yadda zai temaka mata yake shiyasa suna
kammala cin abincinsu suka Jata zuwa office d’in prince banda bobo shima da ya fita
, uncle ma part d’insa ya koma dan babu yadda za’ai su hana big boss , wasu manyan
books suka fito dashi duk a ciki zasu fara koya mata turanci, a hankali a hakali
little ya fara kowa mata ‘kananan kalmomi Marasa wahala , cikin sau’ki kuwa Abla ta
soma fahimta tunda duk abinda ya koya mata sai yayi mata bayanında da turanci yanda
zatafi saurin fuskanta.sun fi ‘karfin 2 hours suna koya mata ‘kananun words , suna
yi suna janta da hira , kiran sallar azahar ne ya katse musu karatun da suke ,
yanxu itama Abla ta gane hanyar komawar ta d’akı shiyasa lokacin da suka nufi
masallaci itama ta koma d’akin, da ta kulle idanuwanta husky voice d’in Big boss ne
yake mata kuwwa cikin kunne, kyansa , muryarsa, da kuma idanuwansa , shine abu uku
da ya kasa
’bace mata , gabaki d’aya ita ta manta da zancan kaiwa simba Abinci dan yadda
sanyin Acn yake huro mata har wani irin bacci take ji yana fusgarta, ko mintuna 30
batayi ba little ya kwankwasa mata ‘kofa tana bud’ewa ya sakar mata murmushi “
let’s it lunch”, itama martanin murmushin ta sakar masa dan yana d’aya daga cikin
‘kananun abunda suka fara koya mata shida prince “ okay yaya little”, murmushi
kawai little yayi mata suka sakko ‘kasa , yanxu su uku zasuyi lunch d’insu, a
wannan karan ma little ne yayi serving d’insu , shima abincin kad’an ta ci ganin
bazata iya cıbane yasa little d’auko mata fruits masu yawan da zata sha sai kuma
Youghurt wannan karan strawberry ya d’auko mata sai da suka kammala cin abincinsu
zaku koma falo idanuwan prince ya sauka kan agogo da ‘karfi ya furta “ Innalillahi
wa inna ilaihi raji’un” da Sauri little ya jiyo ya kallesa , a gogon ya nunawa
little shima cikin sauri ya zabura ganin saura 2 minutes 3 tayi , cikin wani irin
Sauri ya ja hannunta gudu gudu sauri suka fito daga cikin part d’in , tun kafin su
cigaba da tafiya tayi wani irin jan burki da saura kad’an ta fad’i ’kasa sabida
yadda taci karo da sojoji ta ko ina , cikin tsananin tashin hankali fara girgiza
musu kai jikinta har ya fara rawa lokaci guda Sabida sojojin da ta gani, “ oh my
god “ shine abunda little ya furta , zata juya prince yayi saurin dakatar da ita “
No sister , babu abunda zasuyi miki ki kwantar da hankalinki, 3 ta kusa idan baki
bawa simba abinci ba da matsla babba , kawai ki kwantar da hankalinki , ina Abla
gabaki d’aya ta tsure , so take ta samu hanyar guduwa amma prince na ‘ko’karin tare
mata hanya , yadda take mugun tsoron sojoji ko kallansu bata san yi shiyasa a duk
lokacin da ta gansu jikinta ya ke d’aukar rawa , ganin sun hanata wucewa ne yasa ta
fashe musu da kuka dan Allah kuyi hakuri ni bana san mutanan nan tsoro suke bani ,
kuyi hakuri dan Allah ni zan bar muku gidan kuma amma dan Allah ku dena kirawo
wad’an nan mutanan , shima little cikin Tashin hankali ya furta “ babu abunda
zasuyi miki sister ki kwantar da hankali , gida fa kawai suke bawa tsaro kin manta
zaki bawa simba abinci by 3 ? Ko so kike yaya big boss ya dawo ? Dan Allah ki nutsu
“ sai a lokacin ta d’an dakata cike da tsoro Sabida ambatan Big boss da little yayi
amma duk da hakan jira take ace tak ta saka gudu yadda take ganin sojojin nan da
bindigu ta ko ina , da ‘kyar da ‘kyar little da prince suka saka Abla ta wuce shima
sai da suka sakata a tsakiya sabida yadda tayi mugun furgice lokaci d’aya , tanayi
tana wai gan sojojin sabida kar wani ya biyosu, har suka ‘karaso Inda gidan simba
yake , ita Abla gabaki d’aya bata san inda suke nufa ba Sabida yadda hankalinta
gabaki d’aya yana kan sojojin gidan da take faman bi da kallo cike da tsoro , suna
zuwa wajan gidan simba suka tarar da Victor a tsaye hannunsa d’auke da wani bucket
da Alama abincine a ciki, anan ma Abla ta so guduwa saida su little suka dunga
ro’karta tukunna ta tsaya , hanya Victor ya bud’e musu suka shiga yana gaba suna
binsa A baya Daidai d’akin Simba ya ajje bucket d’in tare da tsaya wa , little xai
d’auka Victor yayi saurin dakatar Dashi dan umarnin Big boss ne kar a barsu su
shiga , little kamar zaiyi kuka sabida yasan dole sister ta firgita da ganin simba
tunda ba saba ganinsa tayi ba , kamar zaiyi kuka suka tsaya suna kallan Abla da
itama ta tsaya , a hankali ya furta “ sister ga abincin simba nan , yaya ya hanamu
shiga da mun biki , amma zamu tsaya anan Mujira ki kinji?” Itama Ablan a tsorace ta
jinjina masa kai cike da tsoro ta d’auki bucket din ta d’auka Victor zai biyota
ganin shima ya tsaya ne yasa ta saki a jiyar zuciya , ‘kofa kawai Victor ya bud’e
mata tana shiga ya rufe ‘kofar, Itama Abla ganin d’akin da Haskene yasa bata damu
ba mamakinta me d’an uwansu yake yi a waje irin haka take , bata ‘karasa tunanin da
take ba Sabida motsin da ta fara ji, fuskarta d’auke da murmushi ta juyo daniyar
mi’kawa simba abinci, abinda ta gani ne yasa gabaki d’aya Abla ta ware murya ta
kwalla ‘kara, shima simba sabida yadda tayi ihu ne yasa ya bud’e bakinsa tare da
sakin wani irin kukan zakuna, Ko motsi Abla bata kumayi a wajan ba ta zube
sumammiya .

SORRY UPDATE DIN YAU BA YAWA 👏👏…


https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya
biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo
da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya
lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your
mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to
the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏…

S____24💞

Ihun ‘karar da tayine yasaka cikin Sauri little da prince Suka tunkari d’akin simba
, cikin Sauri Victor ya tare Hanya, kamar little zaiyi kuka ya ‘kara kauce wa zai
shima amma still Victor ya tare masa hanya, a zuciye ya furta “ wallahi Victor idan
baka matsamun a hanya ba zankira yaya na fad’a , dan zalimci kana ji sister tana
ihu amma zaka hanani shiga”, kamar Wanda yake magana da gunki dan gabaki d’aya
tunda Victor ya tsaya be motsaba , gashi ko kusa be d’ago kansa ba balantana su
suka ran zai basu amsa , shima prince cikin cool voice ya furta “ Victor allowed us
to enter plx , ba abinci kawai yaya yace ta tunda kaiwa ba ? Then ka barmu mushiga
muga lagiyarta “ nan ma shiru Victor yayi masa dan ko d’agowa ya kallesu bayayi,
duk yadda suka so shiga ciki Victor ya’ki tanka musu balantana su saka ran zai amsa
.
A cikin d’akin kuwa tunda Abla ta ga simba ta sume bata ‘kara motsawa ba kamar
wata matacciya, shima simba Abla ya soma zagayewa tunda ga farkon kafarta har zuwa
Kanta , lokaci zuwa lokaci kuma yana bud’e bakinsa kamar me shiri kai mata hari,
daya ga bata motsi kuma sai kawai ya zauna a gefenta yana kallanta , banko ‘kofar
da akai da ‘karfine yasa ka Simba tashi tsaye yana bud’e bakinsa da farcinansa .
Bakowa bane yashigo cikin d’akin face little da prince da sukai ‘ko’karin ture
victor suka shigo dukda kasancewar sa right side din big boss amma bazasu iya barin
sister d’insu cikin ma wuya cin haliba musamman da ya kasance karo na farko da ta
fara yin arba dasu , gabaki d’aya little ya rud’e kamar yayi kuka haka yakeji ganin
gabaki d’aya bata motsi , simba yazo zai ta’basa little ya banka masa harara kamar
Wanda zai fahimci harararsa ake. Dube dube little da prince suka soma ko zasu ga
ruwa a cikin d’akin amma gabaki d’aya babu sai wani ruwa da may be simba ya sha shi
shiyasa basu yi ‘ko’karin d’ibarsaba . Cikin Sauri prince ya bar d’akin shikuma
little ya saka gabaki d’aya hannunsa guda biyu yana fiffita mata , simba na gefe
shi kuma ya tsura musu kamar Wanda yasan me suke yi , ba a d’au dogon lokaci ba
prince ya dawo cikin d’akin dauke da bottle water , cikin Sauri little ya zuwa a
hannunsa tare da fesawa Abla amma kamar Wanda yayi da gawa dan ko kad’an Abla bata
motsawa ba , hankali a tashe little ya ‘kara d’ibar ruwan ya fesa mata , cikin ikon
Allah taja wani irin doguwar ajiyar zuciya , tun kafin ta bud’e eyes dinsa tasaka
wani irin ‘kara tare da fashewa da kuka “ Dan Allah kayi hakuri bazan sake ba , Dan
Allah zai cinye ni ku fitar dani daga Wajan nan , daman nasani babu Wanda yake sona
gashi anyi kyautar namana, shikenan zakine xai cinye ni , Wayyo Allah na, shikenan
na mutu, na mutu Wayyo zai cinye ni”, abunda Abla take iya fad’a Kenan cikin shash
she’kar kuka , ga idanuwanta da ta’ki yarda ta bud’e duk atunaninta naman jikinta
simba zai cinye, yanda yake faman zai cinye ta da surutun da take yasaka gabaki
d’aya little da prince tsayawa , shi prince dariya ce ma ta kusa ‘kwace masa
lokacin da take furta “ shikenan na mutu, na mutu “ ganin ta’kiyin shiru ne yasa
little jijjiga ta “ sister bud’e idanuwanki babu abunda zai miki” ai Abla tana jin
hakan amaimakon ta bud’e idanuwanta sai ta ‘kara fashewa da kuka “ Aidaman nasani,
na mutu kawai ,Wayyo Arwa please kizo ki temakeni” da karfi little ya furta sister
da yasaka cikin sauri Abla ta bud’e idanuwanta, tana bud’ewa kuwa ta ‘kara cin karo
da simba, wani saban kukan ta ‘kara fashewa dashi gabaki d’aya fuskarta tayi ja na
tashin hankali sumamman hancinta, da Sauri zata ‘kara sakin wani kukan little yayi
saurin furta “ sister kiyi shiru babu abunda zai miki, kika cigaba da masa ihune fa
zai cinyekin” ba kai ga ‘karasa maganar saba Sabida d’if d’in da Abla tayi kamar
ruwa ya cinyeta, sai faman muzurai take, gana ganin yadda ta ‘bata face d’inta
’kiris take jira simba yayi wani motsin ta ‘kara fasa ihu. “ babu abunda zai miki
fa , simba d’in yaya big boss ne fa”, kamar zatayi kuka Abla ta furta “ daman ba
d’an uwan ku bane simban? Dan Allah ka bashi hakuri kalli yadda yake kallo na , da
bakuzo da tuni ya cin ye na mana ya bar ‘kasu suwan”, shima little yanxu dariya ce
ta’ke ‘ko’karin kwace masa dan bin hakkı Abla iya gaskiyar ta take magana , “ ki
kwantar da hankalinki simba fa baya cizo, kalla ma kigani “ ya ‘karasa yana shafa
kan simba, kamar wata aljana haka Abla taja bata tsaya a ko ina ba sai a bakin
‘kofa , cikin d’an ’bata rai kad’an ta bankawa simba harara “ mugu kawai Allah sai
ya saka mun kuma namana kurrr” sai kuma fitt kamar wata aljana tafi ce daga d’akin,
little da prince me zasuyi kuwa Inba dariya ba , tsabar dariya prince handa
tsugunnawa ‘kasa , wannan shi ake kira “ ga tsoro ga ban tsoro” duk Wanda ya kalli
fuskar Abla 100% zai bawa kowa tabbacin innocent ce ita amma da alama za’ayi yar
bala’I , gabaki d’aya wannan zan tukan cikin zuciyar sa yake yi , shi gabaki d’aya
ya fara hango irin dramer da za’ayi dan wallahi yasan ba ‘karamun cud’ata big boss
zaiyi ba kamar kayan wanki, ganin shirun yayi yawa ya cikin Sauri little ya janyo
wa simba abincinsa suka fito, babu kowa a wajan sai Victor da yake can bakin gate ,
tunda Suka gansa kuma sunsan Abla tana wajan tun da ba lalle ta iya ‘karasawa
wucewa ba , amma abun mamaki babu ita babu alamarta, har sunzo giftawa ta wani
bishiyar mangwaro sukaji kamar siiissii da baki, cikin Sauri gabaki d’aya suka jiya
bayansu amma basu ga kowa ba , a karo na biya aka ‘kara yi musu siiii siii , shima
still ‘kara juyawa sukai basu ga kowa ba , sharewa sukai suna ‘ko’karin cigaba da
tafiyarsu kamar wata aljana sai ganinta kawai sukai daga sama ta diro daga saman
bishiya, cikin Sauri sukaja baya prince har yana ‘ko’karin saka gudu , Abla da Suka
ganine yasa gabaki d’aya mamakinta ya kamasu “ sister me kikeyi asaman bishiya ?”
Kamar zatayi kuka ta nuna musu direction d’in da Victor yake , “ Na kasa wucewa ne”
shiyasa kika d’ane bishiya ?” Cewar prince , kanta ta jinjina masa kafun ta furta “
tsoro suke bani Wallahi, saura kad’an zuciya ta tabuga sabida halittar da nagani”,
cikin yar dariya dariya little ya furta “ Ai zuciyarki bazata buga ba Indai kina
gidannan, amma fa simba ba d’an uwan mu bane, zakin big boss ne” lokaci d’aya Abla
taji kwalla na tarar mata a ido “ Toh dan Allah ku bashi ha’kuri kunji”, had’a ido
little da prince sukai cikin sauri prince ya furta “ karki damu indai kinajin
maganar yaya toh bazai miki komai ba , duk lokacin da ya bada umarni kawai kibi
kinji” Kanta ta jinjina musu cikin sauri dan ita yanxu bata san abunda zai had’a ta
dashi tunda har yake ‘ko’karin sawa a cinyeta “ Allah saiya saka mun”, cewar Abla
cikin zuciyarta , Tunanin me kike ?” Prince yayi saurin katseta, “ babu komai”,
cewar Abla , “ oya taho mu tafi toh , ya kamata mu koya miki yadda ake had’awa yaya
coffee d’insa , yanxu hud’u takusa ya kamata ki koya kafun ya dawo , idan ba haka
ba a d’akin simba zai kulleki”, cewar prince “ Dan Allah da gaske kake ?” Cewar
Abla, ganin tana ‘ko’karin yin kuka ne little yayi saurin kallansa “ yaya prince
Menene haka plx , kanaso ka sata kuka ? Allah zan fad’awa yaya idan ya dawo “ cikin
Sauri prince ya furta “ sorry yaya Adil , nayi shiru ku taho mu tafi “ daga nan
basu kuma cewa komai ba , lokacin da su Abla zasu wuce Victor shima sai da kyar ta
iya wucewa , hatta cikin farfajiyar gidan da ‘kyar Abla tayi wucewa Sabida sojojin
da suke wajan shima saida prince da little suka kakkareta , da ‘kyar da ‘kyar Suka
samu ta wuce shima tana tafiya tana juyowa , ko kuma motsi kad’an ta zabura , saida
suka shiga cikin falourn ta saki wani irin ajiyar zuciya da har saida little ya
bata ruwa Tasha. Basu dade ba suka nufi coffee maker , gabaki d’aya yadda ake
had’awa big boss coffee saida suka koya mata , da abunda ake samasa da abunda ba’a
sawa , hatta irin cup d’in da ake saka masa coffe d’in saida suka nuna mata ,
gabaki d’aya babu abunda basu koya mata ba na tsarin shan coffee d’in big boss, abu
na farko da suka fara fad’a mata ba’akawo wa big boss coffee me d’imi sai me zafin
gaske , dan idan ya salamce kada ta kuskura ta bashi, cikin ‘kan’kanin lokaci
gabaki d’aya Abla ta gane yadda ake had’a coffee d’in cikin sau’ki sabida baiwar
kwakwalwa da saurin fahimtar abu da Allah ya bata . Lokacin sallahr la’asar nayi su
little suka tafi masallaci itama kuma Abla ta koma cikin d’akinta, tana idar da
sallah d’akin ta gyara tunda little ya nuna mata komai na , hatta kayan da Suka
siyo mata suna cikin kwaba a ninke, rayuwa ce daman ta mayar da ita ‘kazama amma
mutum ce me sam tsafta musamman turare da take mugun so , a d’aki tayi zamanta dan
gudun kada ma ta had’u da sojojin gidan ko d’au uwan kyakkyawa ( sunan da ta sakawa
big boss ), tunda ta shigo d’aki shine yake faman yi mata yawo a cikin zuciya , duk
lokacin da ta tunasa kuma sai taji bugun zuciya ko taji wani irin yar a jikinta,
tana kanta na neman yi mata ciwo ne yasa ta ‘karasa wajan window d’in d’akin, tana
d’agawa ta hango sojoji, cikin Sauri ta saki labulen d’akin tana dafe zuciya ,
kamar wacce aka saka sai kuma ta ‘kara le’kawa kad’an , cikin Sauri ta ja baya tana
sakin ajiyar zuciya “ su gidan nan gabaki d’aya ‘kartin mutane ne a ciki? Toh Ina
maman su da babansu?”ita kad’an sai tanbayar kanta take , amma duk da haka bata
daddara ba sai le’kensu take ta window d’in musamman wasu flowers da take hango wa
masu kyau kamar taje ta tsun’kosu haka taje ji.

*** su little suna dawowa daga sallar la’asar motocin bobo suka shigo cikin gidan ,
cikin Sauri little ya ‘karasa yayi hugging d’insa “ welcomed yaya ! Dama kiranka
nakeso nayi yanxu fa “, kallan sa bobo yayi lokacin da suka fara tafiya “ kana bina
bashine ?”, dariya little yayi “ yaya ai kaima kasan da bashi nake binka da tuni na
dad’e na Kwashe maka kud’in d’akin ba , but yanxu ni ba little bane , I have a
sister , yanxu na zama yaya Adil nagaji da little , little d’in nan”, be aune ba
yaji bobo ya talle masa ‘keya “ little baka da kunya yanxu fa , ni kake gayawa
yanxu basunanka little ba ? Sannu ! Bari yayanka ya dawo sai na tanbayesa saban
sunan da kasa mu,” shagwa’be fuska little yayi “ Haba yaya bobo kaima kasan ni
little d’in kune and ni little din yaya big boss ne, kawai fa yanxu na samu sister
ne fa “, ‘karamar harara bobo ya bisa dashi har Suka shigo cikin falourn , shima
prince yana ganin sa ya taso yayi hugging d’insa “ ina uncle ?”, yana part d’insa ,
cewar prince , “ yaya please zamu je siyayya before yaya ya dawo kaji? Cewar
little, “ kana da kud’i Kenan ?” Shima bobo ya dakatar dashi , yadda little ya turo
bakine kamar wani yaro “ Haba yaya sister fa zanyi wa siyayya kuma kasan kud’ina
bazai isa ba , kuma ni banga black card d’in yaya ba “ yana kai ‘Karshen zancensa
yaga bobo ya ciwo wani black card kamar ATM ya mi’ka masa , “ gashi amma babu ruwa
na idan ya dawo ,” wani irin shegen dariya little ya saki “ yaya ka yadda muje
Kenan ?” Kansa bobo ya jinjina masa “ yes amma karku dad’e , just 1 hour kuje ku
dawo , in kuka wuce 1 hour ba ruwa na and ku bari ayi magrib prayer “, da Sauri
little yayi hugging d’insa “ thank you yaya ! I love you “ be jira bobo yayi magana
ba ya saka gudu cikin d’an d’aga murya ya furta “ yaya zan fad’awa sister ta
shiryane munayin sallah sai mu tafi kafun yaya ya dawo “ girgiza kansa kawai bobo
yayi “ bazaka ta’ba girmaba little “ shima kai tsaye part din uncle ya nufa
amaimakon part d’insa .

**** Ana idar da sallar magrib ko zaba little beyi ba yaje ya fito da Abla itama
sanye take cikin wata doguwar riga maroon colour da ya wuce kwiwar kafarta kadan
sai wani white wando da ta saka , sai wani farin shoe da little ya dakko mata ,
tayi rolling da mayafin kayan maroon , duk da ba kwalliya tayi ba sosai kayan
sukayi mata kyau, gudun ma kar uncle ya dakatar dasu ko part d’insa basu shiga ba ,
yaya bobo ma yana part d’insa , suna fitowa da motoci hud’u zasu tafi , da’kyar
Abla take tafiya sabida ganin sojojin gidan amma yau gabaki d’aya wad’an da zasu
fita dasu suit ne a jikinsu shiyasa taji sau’kin Abun. Tunda Suka soma tafiya take
kalle kalle musamman yadda ko ina yake da haske kamar ba dare ba , ko wana barin
fata yana aikin gabansa gwanin ban sha’awa, sosai sukayi tafiya me Nisan gaske na
kusan mintuna 15 kafin su ‘karaso Nora Gardner , babban shagone na mata da ake
siyar da sababbun kayan sawa na mata designers masu shegen kyau da tsana , shiyasa
wajan ya zama private bakowane yake iya siyan kayan wajan ba , face mask prince da
little suka saka , kafin su fito tare da Abla da sai faman kalle kalle take ,
gabaki d’aya jikinta sai yayi sanyi duk da bata san dalilin zuwan nasu ba , Robert
ne kawai ya bisu gabaki d’aya ragowar suka tsaya a ba’kin Wajan suna jiran
fitowarsu, daga prince sai Little da Abla suka shiga Wajan sai kuma Robert da shima
ya dakata suka shiga cikin wajan , da murna wata farar baturiya ta nufosu musamman
ganin Abla , ita atunaninta Abla yar ganin ce Sabida yadda take da hasken fata me
kyau , cikin French Little ya nuna Abla Sabida kada ta fuskanci me yake cewane yasa
yayi anfani da French “ madam ga sister na, kayan sawan da zasuyi mata kyau zaki
d’auko mata da yawa amma ba Wanda zasu dameta ba , kamar na jikinta sai kuma
English wears suma masu kyau , infact duk abunda xai yi mata kyau ki tafi da ita
kizabar mata , bag , shoe , designers everything for a lady , ki d’auko mata su
masu kyau” farar baturiyar nan tana jin haka har wani zaro ido take ganin lokaci
d’aya za’ayi musu siyayya me yawan gaske, gabaki d’aya ta kasa magana, tana tsayan
wata matar ta fito daga wani ‘kofa da Alama Itace me wajan , cikin Sauri ma’ai
kaciyar nan ta je ta sanar mata , itama da Sauri ta ‘karaso Inda suke har ta washe
musu ha’kora , da kanta ta ja Ablan dan taje Itace zata nemo mata abunda ya dace
ganin lokaci d’aya zasuyi uban ciniki, kan wasu chairs masu shegen kyau su little
suka zauna , Wajan sai ya kasance kamar Vip, ga me coffee da take tsaye idan suna
bu’katar wani abun. Tunda Suka hau sama madam d’innan ta nufi VIP set da Abla ,
wasu irin shegen kaya shegen kyau ta dunga za’bar wa Abla tunda basu fad’i adadin
kayan ba , shiyasa duk Wanda taga zai yi wa Abla kyau shi take d’auko mata ko
‘kirgawa batayi , Abla sai binta da ido take dan ita har yanxu bata gane me Sukazo
yi ba , bayan dogayen designers din da ta d’ibarmata sai ta dawo d’auko mata
‘kananan kaya masu kyau, suna ajjesa, daga nan ‘bangaran inners suka nufa , kallo
d’aya tayiwa Abla ta dunga fito mata da pants da bras masu shegen kyau gasu da
yawan gaske , ita Abla har kunya ma abun ya bata ganin yadda take kallanta , daga
nan ‘bangaran designers shoes and bag suka nufa , nan masu tsad’an ta dakko mata
fashions , kuma yawanci hill shoes ta d’ebowa Abla sai shoes da ta saka mata , ga
veils da ta d’auko mata , hatta fashion chains na mata da sar’ka da abun hannu
gabaki d’aya sai da ta d’akko wa Abla , ba ‘karamin kaya ta d’ebowa Abla ba ,
sannan ta saka aka sassa ka musu a cikin jaka suka sakko Sabida gabaki d’aya tayi
calculation d’in kud’in kayayyakin, ba ‘karamun ma’kudan kud’ad’e aka aka kashe wa
kayan nan ba , suna sakkowa Aka fad’awa su little kud’i, Black card din Big Boss
kawai ya saka da pin d’insa , suka zare ma’kudan kudaden da mutum sai ya girgiza
amma da alama tsakanin prince da little babu Wanda ya damu da adadın kud’in.
Kallanta matar tayi cikin turanci ta furt “ gaskiya ked’in kyakkyawa ce , and kina
da sa’a sabida kayan da yan uwanki suka siyo miki” ‘kura mata idanuwa Abla tayi
kamar tana so ta gane me matar take so tace , ido d’aya little ya kashe mata
suprice, lokacin da ake fitar da kayan , bakin Abla har rawa yake ta kasa magana
sai nuna kayan da take da hannu , idanuwanta har sun kawo ‘kwalla , da Sauri little
yaja hannunta suka fita “ Haba don’t cry sister , just kayan sawar kine” cikin
Sauri Abla ta fara girgiza masa kyau , gashi ta kasa bud’e baki tayi magana sai
rawa da bakinta yake , lokaci d’aya kawai ta fashe da wani irin kuka , kuka take
babu ‘ka’k’kautawa ganin abubuwan da suka siyo mata , abunda wani mahalu’ki be
ta’ba yi mata ba a duniya , wai yau Itace ake nuna wa soyayya? Kamar a mafarki
daman zata iya yin farin ciki a rayuwarta ? “ abunda kawai take iya tunani kenan ,
kuka sosai take bana wasa ba , so take ta bud’i baki tayi magana amma ta kasa ,
harshenta yayi mata nauyi , bakinta bai isa ya nuna d’unbin godiyar da ke zuciyar
ta ba , soyayyar su mara misaltuwane a cikin zuciyarta, wani irin soyayyarsu da
kimarsune yake ratsa ko wana bargo na cikin zuciyarta , ganin ta’ki yin shirin ne
kamar zai yi kuka shima ya furta “ ki dena kuka mana , kin manta ke sister din muce
ko so kike Nima nayi kuka ?” Da Sauri ta girgiza masa kai , ta bud’e baki zatayi
musu Godiya amma ta kasa bazata iya ba, Allah ne kad’ai zai iya yi musu abunda
sukayi mata , shi kad’aine zai iya saka musu, da kyar suka samu suka lallasheta
tayi shiru , ko godiyar da take ‘ko’karin yi musu sun’ki bata damar hakan , gabaki
d’aya basa suba time shiyasa har ‘karfe 8pm na dare ya wuce basu sani ba , gashi
gabaki d’aya sun manta da zancan kaiwa simba Abinci. Har zasu dawo gida prince yasa
suka ‘kara mi’ka babban mall d’in Hudson yards , shima wani irin babban waje ne na
siyayya , Abla gabaki d’aya kasa d’ago kai ta kalli wajan tayi Sabida har wani
zazza’bi zazzabi take ji kamar zai kamata sabida kukan da tayi ga idanuwanta da
suka d’an kunbura , bayan sunyi parking Daidai zasu shiga cikin mall d’in Abla tayi
karo da wata , ta jiyo zata bata ha’kuri matashiyar budurwar ta d’aga hannu zata
mareta , cikin Sauri Little ya hankad’ata tayi baya saura kad’an ta fad’i kasa
ma , ba kowa bace face Alice da tafito siyayya , batare da little ya kalli fuskarta
ba yaja hannun Abla suka soma tafiya , wani din kallo suka dunga jefa wa tsakaninsu
Abla da Alice , a karan farko wani irin kallan tsana ne sukayi wa junansu, Alice
kuwa mamakin yadda aka turetane yasa ta kasa tashi ga manyan security da tagani
tare dasu , ita kuma bata san a ganeta shiyasa ko security bata yadda sun biyota
ba, amma a kallo na farko da tayi wa Abla taji wani irin tsanar ta ya shigar mata
zuciya , ga wani ‘bacin rai da bugun zuciya da ta samu sabida tsananin kyan Abla da
take hango wa , ta sani ko kusa bata da irin kyan yarinyar shiyasa tsanar Abla ya
‘kar shigar mata zuciya . Abla ma a kallo d’aya da tayi wa Alice taji wani tsanarta
ya shigar mata zuciya dukda bata san dalili ba , a haka suka shiga cikin babban
mall d’in, ‘ban garan kayan siyayya, dukda sunsan suna da su a gida haka little da
prince suka dunga d’ibar kayan ciye ciye duk Sabida Abla suka siyowa kuma ga manyan
ice cream suma da suka d’auko mata , chocolate , sweet da wasu abubuwan ma da
bazasu lissafu ba , nan ma ba’karamun siyayya sukai mata ba dukda basu fito sunce
ita suka siyowa ba Sabida kartayi musu kuka , ita dai binsu kawai take abaya , tana
kallan yadda suke d’aukar Abu kamar basu san zafin kud’in ba ( Nace Abla toh daman
taya zasu sani tunda da kudin yaya big boss suke ta anfani 👀🤭😹). Sai da Suka shiga
cikin mota sannan prince ya d’auko wayansa , pass 9 , shine abunda ya nuna masa ,
besan lokacin da ya saki wani salatiba, a rud’e ya nunawa little time , shima
lokaci d’aya ya saki salati , Abla kuwa gabaki d’aya bata fahimta ba shiyasa ta
zuba musu manyan eyes d’inta da suke shinning sabida kukan da tayi, cikin Sauri
little yace wa su Robert su ‘kara gudu , sai addua yake Allah yasa yaya big boss be
dawo ba, har suka ‘karas adduar da Suke yi kenan, ana shigowa cikin gidan
zuciyoyinsu tayi wani irin mugun harbawa a tare sabida ganin Anthony, tunda Suka ga
Anthony da Victor to tabbas big boss ya dawo gida , ita kuma Abla bata san dalili
ba , kawai taji wani irin bugawa da ‘kirjinta yayi kamar wacce tayi wani babban
laifi, sai a lokacin kuma abincin da akace zata Tunga kaiwa ya fad’o mata arai,
wani irin tsorone ya kamata, gabaki d’aya kamar Marasa gaskiya suka nufi cikin
gidan su Robert kuma tuni sun shigar musu da kayayyanki siyayyar da sukayi me
matu’kar yawa, suna shiga har wani jan Burki suke a tare ganin Big Boss zaune kan
kujera yayi crossing legs d’insa da alama ya jima da dawowa Sabida farin wandan da
yake jikinsa iya kwiwa sai faman shirt shara shara da take jikinsa , gashin kansa
kuma ya tufke ga wani irin tsuke face da yayi, sau d’aya ya kallesu gabaki d’aya
suka sha jinin jikinsu, musamman kallan da ya jefa wa Abla , lokaci d’aya taji
nutsuwarta na neman guduwa , kamar Marasa gaskiya suka shigo cikin falourn, diamond
watched dinsa ya kalle dake tsintsiyar kyakkyawan farin hannunsa , a kausashe ya
furta “ just 15 minutes na baku kuyi sallah, if your dare ku ‘kara 1 minutes “ ai
be kai ‘karshe ba gabaki d’aya ko wannansu ya nufi part d’insa hatta Abla da
hankalinta yayi mugun tashi, ko takan siyayyar da sukayi basu biba, sallah kawai
suka idar suka dawo kusan a tare da ko minti d’ayan basu ‘kara ba . Wani irin mugun
kallo ya jefa musu da gabaki d’aya sai da ‘ya’yan cikinsu suka kad’a , kamar had’in
baki uncle da bobo suka fito Daidai lokacin, kallan babban yayi kafin ya furta “ ku
zagaye falourn nan sau 5 da gwiwowinku “ cikin Sauri bobo ya furta “ Haba mana big
boss yayi yawa ba , jinjina na masa kai big boss yayi “ sau bakwai zakuyi “ shima
cikin sauri uncle ya furta “ plx big boss ka rage musu “ rai a ‘bace ya furta “
10^”, bobo zai sake magana uncle yayi saurin dakatar Dashi dan suna ‘kara magana
zai ‘kara yawan punishment din nasu , haka suka fara zagaye falourn tun a round 3
suka fara had’a gumi kuma ba daman suyi kuka ,Abla ma sosai ta jigata kamar zata
kife daman sai da bobo yace musu karsu dad’e gashi bata Kai wancan aljani simba din
abinci ba , yana zaune kan kujera suka cigaba da crolling gashi ba damar su bashi
hakuri saida sukayi round 10 d’innan, suna gamawa kuwa suka zube gabaki d’ayansu,
hannu d’aya big boss ya mi’kawa little , cikin Sauri ya fara zazzare idanuwa
lokacin daya mı’ka masa black card dinsa dan su karan kansu sunsan sunyi masa
‘barna da kud’i, ba fara’a ya furta “Leave this place “ da Sauri suka mi’ke kuwa
dan har bobo da uncle sun bar falourn Sabida sunsan zasu iya magana kuma big boss
bazai gaji ba zai ‘kara ninkawa su little punishment, Abla kam gabaki d’aya kasa
tashi tayi sabida yadda ‘kafarta Tayi mugun yi mata tsami, batare da ya kalleta ba
ya nuna mata steps “ 2 minutes na baki ki hau sama ki sakko” kamar bashi yayi
maganar ba , a tsorace Abla ta mi’ke har tana ‘ko’karin fad’uwa kamar zatayi kuma
sabida tsahon stairs din kuma tasan bazata iya gudu ba , da’kyar take taka steps
dinnan , saida takai har ‘Karshe sannan ta sakko ‘kafarta kamar zata karye dan har
ta soma hawaye “ again “ ya kuma furtawa , haka Abla ta sake komawa sama ‘ kasa
‘kasa tana kuka Sabida karya jita, tun kafin ta sakko ma taji tana ‘ko’karin faduwa
amma still sai da big boss ya ‘kara mayar da ita tana yi tana kuka ga fuskarta da
tayi mugun ja har zufa ta had’a ta ‘kafafuwanta da suke mata azaba, sai da tayi sau
biyar lokacin ko d’aga ‘kafarta Abla bata yi , kamar besan da wanzuwarta ba ya
furta “ coffee “ baiwar Allah duk ta galabaita haka ta daddage taje ta had’a masa
coffee kamar yadda su little suka nuna mata , kamar zatayi kuka ta furta “ gashi “
shima da turanci ta furta masa gudun karya sata wani punishment tunda gashi ya sata
hawa step Sabida bata Wana Simba abinci ba , kamar besan da halitta a wajan ba Haka
ya share ta gabaki d’aya , a karo na biyu ta ‘kara furta “ ga coffee din” nan ma
still babu amsa , ga zafin da ‘kafarta ta somayi mata dan har rawa ‘kafarta ta
somayi gashi a tsaye take ba daman ta zauna , sau uku tana masa magana amma be
motsawa sai ma latsa Wajan sa da yake hankali kwance , ‘kafar Abla sosai ta soma
rawa dan ko bakinta ta kasa motsawa , kamar wacce Hajijiya zai fad’ar, tafi ‘karfin
20 minutes ri’ke da coffeee a hannu, shi be kar’ba ba sannan bece mata ta tafiba,
sai datayi almost 30 minutes a tsaye sannan ya mike tsaye batare da ya kalli ko
inuwartaba yayi wuce warsa part d’insa, fashewa Abla tayi da kuka ganin ko kar’ban
coffee din be yi ba gashi ya tsayar da ita, da’kyar ta iya mayar da coffee din ta
daddafa ta wuce d’akinta, ko kayan jikinta bata cireba, sai takalmi kawai , yau ko
alwalar baccin da ta sabayi batayi ba sabida yadda ‘kafarta tayi mata tsami, cikin
‘kan’kanin lokaci baccin wahala ya d’auketa ko kyakkaywan kwanciya batayi ba Sabida
yadda ta gaji. Su little ma suna shiga ko wanka basu yi ba Suka bi lafı yar gado
dan dole baccin wahala ya d’aukesu. Fitowar bobo ne ya tarar da kayayyakin da sukai
siyayya ya tabbata gabaki d’aya su Adil sunyi bacci shiyasa ya dunga d’aukar
siyayyar ya kaisu part d’in Abla , batare da ya shiga ba ya dinga ajje mata su
abaki, ices creams din kawai ya cire ya aka a fridge sannan ya duba lafiyarsu
little , yadda suke bacci sosai dariya da tausayinsu ya kamasa lokaci guda , ya
rasa kan big boss , tun Wanda ya ta’basu ya ta’bo wa kansa rigimar da bashi da
maya’ka dan sai yayi mugun sa’bawa mutum, amma shine oga Wajan punishment dukda
shima yana musu amma Big boss, Boss d’inne da gasken gaske, be wani jima a falourn
ba shima ya nufi part d’insa .

WASHE GARI…..
Pay your money into 2681892316 Aisha umar, zenith ban wai a turo da shaidar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

WATTPAD
https://www.wattpad.com/user/Msslee__

AREWA BOOK
https://arewabooks.com/book?id=652ff3a03fd6ffc37f68e4e2

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta
wannan number 07041879581.

S____25💞

WASHE GARI
Duk da yadda ‘kafafuwanta suke mata tsami hakan be hana ana kiran sallah asuba ta
kasa farkawa ba, har wani lumshe idanuwa take sabida yadda baccin gabaki d’aya be
isheta ba , da’kyar ta iya mi’kewa tayi Alwala tare da kabbara sallah , saida ta
farayin nafilarta kamar kullum sannan tayi sallahr asuba d’inta , ko da ta idar
bata Tashi akan daddumar ba sai datayi karatun Alqur’ani mai girma kafun ta tsaya
yin addua , ta dad’e a kan daddumar nan tana addua har wasu ‘kwalla ne suke sakko
mata a cikin idanuwanta musamman abunda su little sukayi mata , duk da basu san ko
wacece ita ba sun jata a jikinsu kamar yar Uwarsu batare da damuwa da sanin asalin
ko wacece ita ba , sosai tayi wa Allah Godiya akan canjin da ta samu arayuwa
shiyasa ta d’auki al’kawarin kome suke bu’kata Indai zata iyayi musu shi toh tabbas
zatayi shi koda hakan zai zamto akasin farın cikinta .

Big boss ne ya fad’o mata cikin rai musamman lokacin dayake lumshe idanuwansa,
hakan da yake ba ‘karamun narkar mata da zuciya yake ba , taka sa gane dalilin da
yasa duk lokacin da ta zauna ita kad’ai take Tuna’nın saba kamar yadda take yi a
yanzu ,ganin bugun zuciyar ta na ‘ko’karin canzawa ne kamar yadda ya saba mata tun
lokacin da ta fara ganinsa yasa tayi saurin ajje komai a gefe , ta fara gyara cikin
d’akin tunda ynxu tasan yadda ake anfani da kayan sharan, Agogo ta kalla ganin
‘karfe 6:05am na safe yasa cikin sauri ta shiga toilet , shaf shaf tayi wanka bayan
ta wanke toilet d’in, ko nutsuwa ta kasayi tanayi tana kallan time, cikin
‘kan’kanin lokaci ta Shirya cikin wata Doguwar riga Ash colour duk da bata Kai mata
har ‘kasa ba sai wani black din wando da tasaka , hakan kuwa da tayi ko kusa babu
inda jikinta ya fito ,kanta da yayi mugun cukurkud’ewa ta kalla gashi da uban
tsaho da cikowa amma ita kanta bata iya wankeshi Sabida yadda yake da mugun yawa
hatta ribbon sai dai a saka mata Inba haka ba gabaki d’aya sai ta cikurkud’e
gashin nata , da Sauri ta yi rolling d’in ba’kin mayafin ta da gabaki d’aya ya rufe
mata gashin kanta sai uban tudu da yayi na alamar gashi.

Iya kwana kinnan da Abla tayi ba’karamun canzawa skin d’inta yayi ba , farar fatar
ta sosai ta fara washe wa daga duhu duhun da tayi , yadda take yin fresh sosai
mutum sai ya d’auka wani mugun gyara take yiwa skin d’inta , ga farar fatar skin
d’in ta da ya soma murjewa Sabida rashin aikin wahalar da bata yi yanzu, babu
tension kamar lokacin baya da take aiki gidan uwar karuwai. Mood d’in fuskar ta ne
ya soma canzawa Sabida kalmar uwar karuwai da ta tuna lokaci d’aya kuma da mutuwar
Arwa da bazata ta’ba yafe Musu ba Sabida sun cutar dasu , su azabtar dasu kamar ba
mutane ba , cikin Sauri ta share hawayen da suka zubo mata ganin time na wucewa .

A karo na biyu ta ‘kara kallan lokaci, da Sauri ta dafe ‘kirjinta ganin saura ‘yan
mintuna 7 tayi,ga mugun tsoron da take ji musamman yadda take hango simba cikin
idanuwan ta . Cikin Sauri Sauri , gudu gudu ta fito daga cikin d’akin, uban tilin
kayan da ta gani a ‘kofar d’akin tane yasa ta ja burki tana binsu da kallo, ta gane
kayan da suka siya jiya ne , ga time yana tafiya bata tsaya duba komai ba ta soma
d’aukan ledojin tana shigar dasu cikin d’akin, saida ta saka komai gabaki d’aya
taja kofar ta fita batare da ta ‘kara bi ta kansu ba .

** Babu kowa a falourn sai ‘kamshin turaran da ya cika ko ina, gashi gabaki
d’aya falourn yayi fes babu alamar datti ko ‘kura , tana tsaye a falourn tana bin
ko ina da kallo , kullum ta kalli falourn sai taga kamar ‘kara masa kyau ake , duk
da yadda falourn ya d’auki shiru hakan be sa ta zauna kan kujera ba sai gyara
tsayuwarta da tayi , gani take kamar tana zama za’ace mata ta tashi , gashi har
yanxu ‘kafarta bata dena zafi ba sabida hawa da sauka da ta dunga yi jiya.

“Sister?”cewar little lokacin da yake fitowa daga cikin elevator, sanye cikin kayan
motsa jiki black colour ga gyara gashin kansa da kullum ‘kara masa kyau yake ,itama
martanin murmushin ta mayar masa da har saida dimples dinta suka motsa na both side
“ yaya little ina kwana ?”, A maimakon ya amsa mata sai ma wani murmushin da ya
‘kara sakar mata , sabida yanaso yaji tana kiransa da yaya little , inda take a
tsaye ya mufa har lokacin da murmushi akan fuskarsa “sorry sister jiya mun barki a
wajan yaya big boss” a hankali cikin siririyar murya Abla ta furta “bakuyi mun
komai ba ai and nagode sosai da sosai”, kansa yayi mata knodding kafun ya furta “
yanxu kenan kin saba da simba tun da kika iya kai masa abinci ko?”, a zabure Abla
ta ja baya , ga tashin hankali da ya fito mata kan face d’inta , cike da tsoro
little ya kalleta “Menene?” Abla kamar zatayi kuka ta furta “ Namanta bankai masa
ba , kuma ni tsoran sa nake ji” , lokaci d’aya little ya furta “ Innalillahi, me
yasa baki kai masa ba ? Kinsan yaya kuwa ? Yanxu 7:10 fa , taho mutafi kafin ya
fito please” cikin Sauri Abla tabi bayansa dan ayanxu tafi tsoran hukuncin da big
boss zaiyi mata akan sojojin da take gani a cikin gidan, dukda yau ta d’an wuce a
raku’be bakamar sauran lokuta da sai su little sun kare taba .

Cikin Sauri Sauri little yake tafiya dan yasan idan big boss ya sakko bazata ji da
dad’i ba , babban Tashin hankalinsu suna zuwa suka tarar da Victor ya kulle door
d’in, little har zai soma magiya akan ya bud’e musu Victor ya sanar dashi umarnin
big boss , 7:01am nayi na safiya za’a dunga kulle ‘kofar ,lokaci d’aya little ya
tsure , Abla kuwa kwalla ce tabb ta cika mata cikin idanuwa musamman tuno
punishment din da ya bata jiya. “Don’t cry bari na kira yaya bobo kinji?” Yana kai
‘karshen zancansa ya zaro phone d’insa tare da dialing number Bobo, ringing biyu
kuwa bobo ya d’auki wayan , bansan me ya ce wa little ba sai d’an zaro nasa eye
d’in da yayi shima yana kallan time , a hankali kamar zaiyi kuka ya furta “ okay
yaya am coming”, yana kashewa little ya kalli Abla “ am sorry sister , yanxu yaya
bobo yana kirana nima na makara wajan training , kuma idan yaya big boss ya ganmu
zai hukunta mu,” cikin Sauri kuma ya furta “ but karki damu insha Allah bazai miki
komai ba kinji?” Kamar zatayi kuka tayi masa knodding kanta , da kansa ya rakata
part d’insu kafun shima cikin Sauri ya wuce Wajan training.

Kamar wata mara gaskiya Abla ta soma sand’a cikin falourn tanasan guduwa d’aki
Sabida kar tsautsayi yasa ta had’u da big boss , shiyasa a hankali take taka
‘kafarta yadda bazai bada sauti ba , daga sama taji sautin muryar prince “ Little
sister ?” A tsorace Abla ta juyo jikinta har ya soma rawa bata gama gane muryar ko
wanene ba ta furta “ Dan Allah kayi hakuri , anjima zan basa abincin”, kallanta
prince yayi har yana d’an zaro mata idanuwansa , fuskarsa da mamaki ya furta “
Baki bawa simba abinci ba ?”, Kanta ta jinjina masa kamar zatayi kuka , a fili
Prince ya furta “ Tashin sense , kinsan me yaya yafi tsana kuwa ?” Ya tanbayeta
yana kallanta , itama a d’an tsorace ta furta “ Ah, Ah “, ya tsani ya bada umarni
mutum ya sa’ba masa , ki dunga kiyayewa kinji? And yanxu kinga yaya bobo yana
jirana, kiyi sauri ki gudu d’aki kafun ya fito” yanxuma cikin kalar tausayi ta
gyad’a masa kanta, yana barin wajan Abla ta turo bakinta a shagwa’be kamar zatayi
kuka “ sai yayi ta d’aurewa mutum fuska kamar tuwan Alkama , mutum ko fara’a bayayi
fisabilillah, Dole adunga yayya fa maka ruwan Alwala”, sai kuma ta d’an ta’be
baki tana kwaikwayar muryarsa. “ 7:00am Kikai wa simba abinci, 3pm ki kaimasa, 8pm
ma ki kai masa , bazaki kwanta ba sai kin had’a coffee , yen yen yen , yen yen
yen , da zan samu bindiga da sai na harbe kan zakin nan , mugu kawai….“,kalmar
mugun ce ta tsaya ma ta cikin ma’kogwaranta lokaci d’aya ta zabura ta na to she
bakın ta sa bi da ganin Wan da ba ta yi tsammanin ga ni ba.

Yana tsaye yayi folding hannunsa ya na kallan ikon Allah , dan shi gabaki d’aya
yadda ya ga tana magana ita ka d’ai ya d’auka aljanu ne a kanta , ran sa a ‘bace
yake je fa mata wani mugun kallo dayasa tayi saurin had’iye yawun ba kin ta, a
hankali ya soma ta kowa cikin falourn, itama Abla a tsorace ta fara ja baya ganin
yana nufo in da take , hannunta d’aya ta fara yarfewa kamar za ta yi kuka ta furta
“ Dan Allah kayi ha’kuri ni badakai nake ba,” sai kuma tayi saurin toshe bakinta
ganin ta ‘karayin wani lefin tunda ya hanata magana da Hausa , yadda take ja baya
bata san lokacin da ta ‘karasa wajan kujera ba , shima still be dena nufo hanyar ba
, tanagani yazo daf da kujerun ta hantsila baya kanta yana bigewa , cikin kuka kuka
ta furta “ Wayyo Allah na”, kafarsa d’aya big boss yasa ya taka mata ‘karamin d’an
yasan ‘kafarta , cikin azaba Abla ta saki ‘kara ta soma bashi hakuri sabida zafin
da taji a d’an ya tsan naka , amma ko gezau big boss beyi ba sai ma ‘kara taka shin
da yayi sosai yadda zata ji zafin ,cikin husky voice d’insa ya daka mata tsawa ,
lokaci d’aya jikin Abla ya soma rawa , cikin kallan tsanan da yake jefa mata ya
soma magana “ just because na barki ki zauna ba shike nufin ke ahalin gidannan bace
, ko wanene ya baki plan d’in shigowa cikin gidan nan , just wait and see , and
this is my last warning , idan kika Kuskura na sake ganin face d’inki a inda nake
sai na mugun sa’bamiki , stupid !”a hankali cikin shashshekar kuka Abla ta soma
bashi hakuri , rai a ‘bace ya daka mata tsawa “ Get lost”, cikin kuka sosai Abla
ta ruga stairs inda d’akinta yake , tana gudu tana share hawa yan da suke zubo mata
.

***** Tana shiga d’aki kan bed ta fad’a tare da fashewa da saban kuka , kuka
kawai takeyi abunta ,duk da irin abunda yayi mata yanzu kwata kwata bata ji zafinsa
ko d’aya a cikin zuciyarta ba, sai ‘kara tuno face d’insa da tayi da yadda dogon
murd’ad’d’en gashinsa yake motsawa , a hankali face d’insa ta soma yi mata gizo
kamar yanxu ne yake mata fad’an shiyasa ta ‘kara fashewa da wani saban kukan, tun
tanayi da ‘karfi har ta somayi a hankali sabida muryarta data d’an dishashe, lokaci
d’aya kuma ta soma sakin a jiyar zuciya alamar bacci ne ya d’auketa, ga d’an
mitsitsin bakinta da ta turo lokacin da take baccin.

****Big Boss
Tana wucewa sama ya ja siririn tsaki , cikin ‘kasa ‘kasan ma’koshi ya furta “
stubborn rat”, doguwar maganar da yayi yanxu har kansa ya soma yi masa ciwo, ga
face d’insa da ya ‘kara had’ewa kamar har yanzu tana gabansa, diamond watches
d’insa ya kalla da fararan idanuwansa a karo na biyu ya ‘Karajan wani siririn tsaki
tare da nufar part d’insa .

************
10:00am Little , Bobo , prince da uncle suka shigo cikin falourn , babu kowa a ciki
shiyasa ko wannansu ya nufi part d’insa sabida su canza kaya, Prince sai mita yake
wa little lokacin da yace zai je part d’in yaya , da kyar ya samu little ya hakura
sabida shi yunwa yake ji, da Zaije d’akin Abla ma saida prince ya ro’ke shi akan ya
dawo da wuri, cikin rashin sa’a yana shiga ya tarar da Abla tana bacci shiyasa ya
dawo falourn , lokacin gabaki d’aya suna kan dinning suka jiran fitowar su , ganin
babu Abla a bayansa yasa bobo tanbayar sa “ ina little sis d’in taka ?”, d’an kalar
tausayi little yayi “ yaya tayi bacci sai dai kafun ta farka ayi mata wani
breakfast d’in ita da yaya “ kansa bobo ya jinjina masa “ it’s okay ! Let’s eat”,
daga haka gabaki d’aya Suka zauna James yayi serving d’insu tunda Abla bata wajan .
Suna gama cin abinci little be jira kowa ba ya nufi part d’in Big boss , kusan
kullum light d’in part d’insa a dum yake shiyasa basa damuwa da hakan , direct
bedroom d’insa ya nufa bayan yayi knocking sau uku ganin big boss be amsa masa bane
yasa ya shiga cikin d’akin, nan ma still dum light ne a wajan , a hankali little ya
furta “ yaya ?!” Shiru yaya be amsa masa ba , a karo na biyu ya ‘kara ambatan
sunansa amma still be amsa masa ba duk da yana jin lokacin da little ya shigo cikin
d’akin amma ya sharesa , cikin turo baki little ya hau kan gadon tare da fara yaye
masa white blanket d’insa , be bud’e eyes dinsa ba sai cikin cool voice d’insa ya
furta “ little what do you want?”, muryar little d’auke da murmushi ya furta “ yaya
ni fa maganar sister nazo nayi maka ya kamata ta fara zuwa school please and naga
kana bacci fa” shiru big boss yayi masa ba tare da ya amsa masa ba , a shagwa’be
little ya furta “ please yaya kaji?am your little ka manta , ina so sister ta fara
zuwa makaranta please”, shiru big boss ya ‘kara masa har saida yace masa “
please” , yanxu ma cikin cool voice kamar bashi ba ya furta “ bani da kudi” wani
irin dariya little ya saka da har saida big boss ya bud’e lumshash shun eyes d’insa
“ haba yaya taya zaka cemun baka da kudi? Please just for my sake kaji?” ‘Dan ta’be
baki big boss yayi lokacin da ya zubawa little idanuwansa “ kana da kudi sai ka
sata mana , ni na hana ka ?” Girgixa masa kai little yayi “ but yaya kace fa ko me
nakeso na fara tanbayar ka !” Dakatar Dashi big boss yayi ta hanyar furta “ jiya da
kuka kashemun kud’i shima kun tanbayeni?” No yaya , cewar little “ okay fine !
Allowed me to sleep”, yana kai ‘Karshen zancansa yaja duvet dinsa , d’an turo baki
little yayi tare da kwanciya a side d’insa ba tare da ya ‘kara furta komai ba shi a
dole yayi fushi.

✨✨✨✨✨✨✨

NIGERIA
KANO STATE

Tun lokacin da dady ya furta komawarsu Eshaal U.s baby take fushi dashi sabida
batasan komawa da Eshaal ta fisan ta yi tafiyarta makaranta ita kad’ai shiyasa tace
wa dady ya samo mata wani school a cikin Garin Kano. Sosai ta tada bala’i cikin
gidan daga momy har dady babu Wanda ta ragawa dan sai da tayi kwana uku bata kula
kowannansu, kullum cikin rarrashinta suke yi dady har kyautar mota yayi mata dan ta
wuce shiyasa ta d’an sassauta fushinta, amma duk lokacin da taga Eshaal ko AMMA ta
fara ci musu mutumci kenan musamman Amma da take gani Itace ta Shirya ko wani
makirci na komawar Eshaal U.S. Duk da ta ha’kura ta d’au Al’kawarin sai ta
musgunawa Eshaal har sai taji tafisan zamanta a Nigeria , kullum cikin kawowa dady
da momy ‘karar Eshaal take , musamman momy da tafi kowa tsanar Eshaal haka zata
kamata tayi ta dukanta kamar wata jaka , sau biyu momy tana tsinkawa AMMA mari
lokaci na farko da Baby taji babu dad’i cikin zuciyar ta Sabida Momy bata ta’ba
Marin ta agabanta ba , bata kawo komai aranta ba ta share tunanin duk da lokaci
zuwa lokaci hakan na fad’o mata arai .
Yau ya kama saturday, ranar da yayi Daidai da saura kwana biyu su Baby su koma
U.s karatu, tun safe Baby ta fita ita da momy da dady sabida siyayyar da suka fita
da baby ta za’bi duk abunda take san siya amma ko kusa dady be bawa Eshaal 5k ba ta
siyayya kuma ba kowa ne ya hana hakan ba face momy, a cewarta idan baby ta dawo
zata bata tsofaffin kayanta sai tayi anfani dasu . Eshaal ko ajikinta inda sabo ta
saba da irin halin momy da take nuna mata tsana a fili , shiyasa tana gama abincin
rana kayan sawarta ta zauna ta goge duk da yadda Amma ta so ta bata amma Eshaal
ta’ki bata sai ma zuwa da tayi ta kwantar da Amma akan ta huta . Tun tana yar
‘karamarta bata da uwa kamar Amma Sabida dukda yadda AMMA take aiki a karkashinsu
ta fisan ta fiye da kowa na gidan har Dadyn ta. Sabida yadda ada ya nuna mata
soyayya amma tun bayan mutuwar mahaifiyarta soyayyarsa ta koma kiyayya baya san
ganinta , bayasan ta ra’beshi bayasan komai da ya dangan ce ta shiyasa itama take
jan jikinta, yanxu a rayuwa bayan Amma bata sakewa da kowa Sabida ita kad’ai ce
sırrın ta .

**** Ana idar da sallar la’asar Eshaal ta shiga cikin kitchen Sabida sha’awar d’an
malelen da take , cikin d’an ’karamin tukunya ta d’ora musu ruwan d’an malelensu ,
gabaki d’aya saida ta yanka tomato, cucumber ,albasa da zasuci d’an malelensu ,
ruwan da ta d’ora yana tafasa ta saka tsakinta da ta wanke tare da barbad’a masa
gishiri kad’an, tun kafun ya dafu ta soya musu manja . Tana gamawa har wani
murmushi take saki , cikin wani medium tray ta juye musu d’an malelen , ta saka
manja , tumatur , cucumber , da albasa , sai tabi kansu da wani irin yaji me shegen
dad’i da AMMA ta daka , tun kafun ta faraci har ta fara had’i yar miyau ita kadai.

Direct d’akin Amma ta wuce lokacin tana zaune daga kan carfet , da sallama ta shigo
cikin d’akin , itama Amma fuskar ta d’auke da fara’a ta amsa mata , d’an malelen
Eshaal ta ajje mata a gabanta , “ Amma ina zuwa yanxu zan dawo “,
Cewar Eshaal, bata jira cewar AMMA ba ta fita cikin d’akin da Sauri . Cikin
‘kan’kanin lokaci kuma ta dawo d’auke da wani tray din da ban , cikinsa lemo ne da
ruwa da ta d’akko musu “ AMMA yau d’an malele nake sha’awar sha , shiyasa na yi
mana shi yanxu , and plx AMMA karkice mun azumi kike dan yau ba Monday bace kuma ba
Thursday bane , Dan Allah kisha kinji” murmushi Amma tayi mata ta saka hannu suka
soma shan d’an malelen, lokaci zuwa lokaci Eshaal tana bata labari masu dad’i dan
tayi dariya , ganin tana ‘ko’kwarin kwarewa ne yasa AMMA dakatar da ita “ ya isa
haka Eshaal ya kamata ki dena magana idan kina cin abinci kinga yanxu ma kin kusa
kwarewa.” Insha Allah AMMA “ cewar Eshaal.

Adaidai lokacin da suke tsaka da Shan d’an malelensu a Daidai lokacin su kuma su
Baby suka dawo gidan, tacı black abaya da wani ba’kin glass da ta saka akan
fuskarta , sai faman ya tsine fuskar take musamman yadda take tauna cin güm d’in
bakinta . Bata tsaya d’aukan siyayyar taba tayi wucewarta . Tana shigo cikin
falourn ta tarar da bakowa , har wajan kitchen baby ta le’ka amma bata ga Eshaal ko
AMMA ba , bakinta ta ta’be zata wuce sai kuma ta dakata tare da nufar d’akin Eshaal
, nan ba still bata ciki , cikin Sauri baby ta nufi d’akin AMMA tare da banka ‘kofa
, da Sauri Eshaal ta juyo saitin ‘kofar , itama AMMA kofar ta kalla tana cire
hannunta daga kan abincin .Wani irin sallallami BABY ta saka da ‘karfi kamar wacce
taga wani mugun abu “ Mommy , Mommy kina ina ?”, muryar momy sukaji tana cewa
menene ya faru baby na ko sun ‘kara yi miki wani saban rashin kunyar ne…” itama
dakatawa tayi tana bin su Eshaal da kallo “ munafukan Allah abunda kuke yi kenan?
Wato idan mun fita zuwa kuke ku satar mana abinci batare da sanin mu ba ? Uban wa
ya baku damar ta’ba mana kaya wato har da d’aukar lemo da ruwa tunda ga gidan
ubanku ko? Halin matsiyata a jikin ku yake kenan ko ?” Da Sauri Eshaal ta girgiza
mata kai “ momy babu ruwan AMMA a ciki , hasalima ni ce na dafa na kawo mata babu
laifinta a ciki.” A zuciya momy ta shigo cikin d’akin “ dan ubanki zaki rufe mun
baki ko sai na gurza miki shi da bango? Duk salan iskanci da bari ta koya miki
shine har kike da zarar fad’amun babu ruwan ta a ciki?” Sun kuyar da Kai ‘kasa AMMA
tayi amma kwata kwata yanayin face d’inta be canza ba , a hankali ta furta “kiyi
hakuri “ dogon tsaki Momy taja “ muna fuka daman kullum abunda kika iya kenan ayi
hakuri ayi hakuri , banzaye kawai dangin matsiyata ,“ tana kai ‘karshen zancanta ta
juya , itama baby cikin ta’be baki ta kalli Eshaal “ ki tashi kizo ki jera mun kaya
na a cikin kwaba , idan kinga dama kuma ki zauna karkiyi , dan gin matsiyata” tana
kai ‘karshen maganarta itama ta juya tana banko musu ‘kofa. Fashewa da kuka Eshaal
tayi , wannan cin mutunci har ina dan kawai ta sha d’an malele shine suka cancanci
wannan wula’kanci? Lallashinta AMMA ta soma “ kar kisaka wannan abun cikin ranki ,
komai me wucewa ne , kinji ? Ki goge hawayenki ko so kuke su ‘kare kirasa na kuka
ranar Auranki?” ‘Boye fuskarta Eshaal tayi tana goge face d’inta , time to time
kuma tana murmushi Sabida maganar AMMA ita da bata da ko da saurayi ina taga mijin
aure ? Murya a sanyaye itama ta furta “ AMMA dan Allah kiyi hakuri akan abunda su
Baby suke miki?” Girgiza mata kai AMMA tayi “ karki da mu ni babu abunda sukai mun,
ya kamata ki tashi ki bita , kar ta sake miki wani abun, ni ki bari zan kwashe
kwanukan” da Sauri Eshaal ta girgiza mata kai “ No AMMA be kamata ina wajan kice
zaki kai ba , kawai kiyi zamanki ki huta Sabida kar ciwan ‘kafarki ya tashi
kinji ?” Murmushi AMMA ta sakar mata “ Allah ya albarkaci rayuwar ki , ya banı ikon
sakaki farinciki kamar yadda kika sani “, da Ameen Eshaal ta amsa lokacin da take
kwashe kayan da har taji d’an malelen ya fita a ranta.

Tana kaiwa kitchen d’akin Baby ta wuce gabaki d’aya ta har gitsa d’akin shigowarta
dan kafun su dawo saida Amma ta gyara mata , tana kan gado hannu d’auke da wayar ta
, ga lemo da take sipping, kunnanta kuma pod ne da alama wa’ka take ji sabida yadda
take gyad’a kanta , Eshaal bata ce mata komai ba ta fara kimtsa mata d’akin Sabida
kwana biyun nan neman abun fad’a Baby takeyi, tana gama gyara d’akin kayan
siyayyar da su baby sukai ta fara jera mata bayan uban tulin kayan Baby da ta ‘kara
gyara wa , kana kallansu kasan da gangan kuma baby ta ‘bata su, tun da ta soma
gyaran baby take neman hanyar janta da fad’a amma ko kusa Eshaal bata kula taba ,
tana gamawa tayi wuce wat ta itama batare da ta kula taba.

✨✨✨✨✨✨✨

*NEW YORK*

11:45am Abla ta farka daga baccin da ya d’auke ta , bakinta d’auke da adduar bacci
ta soma bud’e idanuwanta da Suka d’an kunbura, lokaci d’aya kuma ta lumshe su ta
sake bud’ewa tana mikewa zaune “ Yah Allah Yaushe barci ya d’auke ni haka ?” Cewar
Abla lokacin da Mike tsaye , Daidai gaban mudubin d’akin ta tsaya tana bin fuskarta
da kallo , sai a lokacin ta tuno da zafin da d’an yatsan ta yake mata , cikin Sauri
ta tsugunna ta shafa wajan , a hankali kamar me rad’a da wani ta ta’bile bakinta “
mugu kawai , Allah sai ya sakamun tsabar mugunta harda takan d’an yatsa Sai ya wani
dunga d’aure fuska kamar bread, ai ko shi bread yana fara’a tunda yana da dad’i ,
me fuskar tuwo kawai” ya ‘karasa tana turo bakinta kamar da wani take . Face d’inta
ta wanke lokacin da ta kalla Agogo , bata zauna a cikin d’akin ba ta sakko down
stairs . Bobo ne zaune kan kujera sai uncle da prince , har ‘kasa Abla ta tsugunna
ta gaishe da uncle kafun ta kalli yaya bobo shima cikin fara’a ta gaishesa “ har
kin tashi daga baccin Kenan ?” Kanta Abla ta jinjina masa tana murmushi kafin ta
juya Side d’in prince shima ta gaishesa , da murmushi akan fuskarta ya furta “ fine
lil sis , kinga tun da wuri little ya saka a miki abinci ya kamata kici yanzu”
d’ayan side d’insa ta duba taga little d’in baya wajan fahimtar hakan yasa ya furta
“ karki damu little yana d’akin yaya big boss yana bacci but nasan any moment from
now zaki gansa”, tunda ya ambaci Big boss taji zuciyarta ta buga da ‘karfi daurewa
kawai take shiyasa a hankali ta furta “ okay “, har zata mi’ke sai kuma ta fasa ta
fuskanci su bobo da suka zuba mata ido, kamar zatayi kuka ta furta “ Nagode sosai,
Allah yasaka da Alkairi, Allah ya saka muku da mafificin Alkairi, Allah ya dauwamar
daku cikin farin ciki, Nagode sosai.., “ zata cigaba da adduar bobo ya katseta “ ki
dena wannan godiyar , we’re all family now ! Banaso kinji ? Ko so kike little ya
sakko ya saka mana kuka yace mun ta ‘ba masa lil d’insa ?” Ya ‘karasa yana d’an
zaro mata ido , murmushi ne ya kwace mata lokaci d’aya ta furta “ Ah’ah “ shima
fuskarsa cike da murmushi ya furta “ Good ! Now yaya prince a bawa lil d’in mu
abinci “ mi’kewa tsaye prince yayi kafun ya furta “ Now” tray din abincinta ya
dakko mata ya kawo mata har inda take , da kanshi yayi serving d’inta , cikin d’an
tsokana ya furta “ yaya naga alama lil d’in nan ta fara sabawa da abincin mu”,
murmushi kawai Abla ta sakar masa tana kare face d’insa , “ don’t mind him daughter
, ci abincin ki karyayi sanyi “ cewar uncle .

Balaifi ta soma cin abincin su duk da ba sosai ta iya ci ba amma ba kamar dama
tunda yanxu bata Amansa , tana cikin ci taji muryar little yana furta “ my lil”,
at the same time ‘kamshin turaransa ya daki hancinta , jikinta har ya soma rawa
kad’an lokacin da ta d’ago face d’inta ta kalli saitin sa , da Sauri kuma ta sun
kuyar da kanta ‘kasa tana wasa da spoon d’in hannunta , duk taku d’aya da yake
kamar da bugun nunfashinta yake , addua kawai take karanto wa cikin zuciyarta ,
ganin suna ‘kara kusan to Inda suke “ lil sai yanzu kika tashi?”, cewar little yana
katse mata rud’anin da ta jefa kanta , da Sauri ta jinjina masa kanta murya na rawa
ta furta “ ehe..eh mn”, shima kansa little ya jinjina mata “ thank god kin fara cin
abinci da d’ure zamuyi miki”, kasa magana tayi sai kifkifta idanuwanta da take
kamar zatayi kuka , ta kasa d’ago eyes d’inta ko sau d’aya ta kalli direction
d’insa gashi ya hana ta zo inda yake.

Tunda big boss ya shigo cikin falourn babu Wanda yayi wa magana har ya zauna akan
kujerar da yake yawan zama , fuskarsa gabaki d’aya ba annuri a tattare dashi ,
cikin nutsuwa yake danna wayar hannunsa , “ yaya sannu da zuwa”cewar prince ,
amaimakon ya amsa masa sai ya lumshe masa eyes d’insa kamar yadda ya saba , bobo da
uncle kuwa face d’insa suke bi da kallo shiyasa ya ‘kara d’aure face d’insa .
Suna zaune har little ya d’auko wa big boss abinci ya jera masa kamar yadda suka
saba , ga Abla dake facing d’in inda yake , gabaki d’aya sai taji ta ‘koshi bata
jin yunwa dan ko kwakkwaran motsi ta kasa , har little ya gama serving din yaya big
boss . “ Lil ya kika dena din abincin ?” Cewar bobo bayan ya kalli big boss da ya
‘kara shan kunu, yasan Sabida big boss ne ta kasa cin abincin , muryarta na rawa ta
furta “ Na ‘koshi ne…” girgiza mata kai bobo yayi “ No lil ai bakici sosai ba , ko
kuma kawai ki tafi dashi d’aki “ kamar jira take kuwa ta jinjina masa kai da Sauri
tana d’aukan tray d’in, little zai dakatar da ita bobo ya hanasa . Big boss kuwa
kamar be san me ke faruwa a falourn ba , hankali a kwance yake cin abincinsa ,
lokaci zuwa lokaci kuma yana danna wayar hannunsa. Cike da d’an zolaya bobo ya
furta “ yaya big boss mufa yadda kake d’aure mana face d’in nan yana bamu tsoro
kaga ka saka sister d’in mu guduwa”, wani irin kallo big boss ya zubawa bobo da
yasa ka babu shiri bobo ya saki dariya “ maida wukar yaya bani na kar zoman bafa “,
big boss be ce masa komai ba ya cigaba da cin abincinsa , saida ya gama tukunna ya
mi’ke tsaye yana kallan black Rolex d’in hannunsa . Da Sauri bobo ya furta “Are you
going out ?” Ba tare da ya kallesa ba big boss ya d’an yi knodding kansa , murya
ciki ciki ya furta “ yeah ! See you all” yana kai ‘karshen maganarsa yayi hanyar
barin falourn , da d’an ‘karfi little ya furta “ yaya please karka manta ! Love “.

Sai da prince ya ga fitar Big Boss kafin ya kalli little “ me ne ne “ d’an


harararsa little yayi “ Allah yaya prince kana san jin gulma “ babu komai fa ! Lil
nace asaka makaranta “ kusan lokaci d’aya prince da uncle suka furta “ ya amince ?”
Kansa little ya girgiza akan Ah’ah , murmushi bobo kawai ya saki batare da yace
komai ba , har ya juya sai kuma ya d’an tsaya “ I think you get some visitors may
be “ cikin tsokana Uncle yace “ kodai sirikai nane?” Lokaci d’aya bobo ya d’aure
face d’insa , bai bi takan maganar uncle ba ya juya ya bar wajan.

Abla tana shiga cikin d’aki ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ‘kirjinta , kamar
zatayi kuka ta furta “wallahi wannan zuciyar tawa matsoraciya ce , ko uwar karuwai
da take kawo mun hari bana jin wannan bugun zuciyar ! Haba fisabilillah”, gabaki
d’aya sai taji abinci ya fice mata arai har ta ‘koshi , a fili kamar me magana da
wani kuma ta ta’be baki “ Mutum kullum sai ‘kara kyau yake kamar wani aljani”.
Ledojin jiya ta janyo ta fara bubbud’e kayayyakin da aka siyo mata , ba’karamun
kyau sukayi ba ita kad’ai sai faman dariya take . Gabaki d’aya kayan jera su tayi
cikin wardrobe , ta kalmi da jaka ba gabaki d’aya kowa da inda ta saka su hatta
kayan za’kin da Prince ya kwaso mata , lokaci d’aya sai d’akin ya canza ya zama na
cikakkiyar budurwa me ki da gata .

✨✨✨✨✨

2:50pm ta sakko daga d’akin ta gudun kar ta sake yin wani laifin , tasan idan bata
Kai wa simba abinci ba , ita big boss zai mayar simba , ga tsoro da take ji, dad’in
ta tana sakkowa taga little zaune akan kujera , “ yanxu nake shirin kiranki Lil ,
ya kamata ki kaiwa simba Abinci kai ki sake wani laifin ko ?” Da Sauri Abla ta
furta “ Eh” suna tafiya suna hira dan yanxu ta rage tsoran sojojin sosai . Suna
shan hanyar da zata sadasu da d’akin simba wasu manya manya motoci suka shigo cikin
gidan kusan guda takwas, cikin Sauri wasu sojojin Suka kare wata mota , kafun
lokaci d’aya su bud’e musu both side , His excellency ne ya fara fitowa daga cikin
motar , sai Her excelling da ta fito itama cikin shigar ‘kananan ‘kaya , a
gadarance ta furta “ let’s go sweetheart” wata farar ‘kaface ta soma fitowa da ta
cin red jan farce a ‘yan yatsun ‘karta , cikin iyayi ta fito daga cikin motar , ba
kowa bace face Alice da taci wankan turawa hirar jikinta black colour ko cibiyarta
bata rufe mata ba , sai red d’in wando da shima ko kwiwar ‘kafarta be kai ba , ga
wani uban hill shoe da ta saka , sai Faman ya tsine face take , dukda kasancewar ta
yar president ba ‘karamin tafiya da imaninta tsarin gidan yayi ba kasancewar wannan
ne zuwanta na farko , ta ko ina kamar kiran president Jami’ai ne , Jami’an da suka
ninka nasu a yawa da girma , lokaci d’aya wani murmushi ya su ‘buce mata “ soon I
will be the queen of this house ! Zanyi ruling kowa ! Wow”. Sweetly let’s go “
cewar her excelling , cikin yanga Alice ta soma ta ku, so take kawai ta saka big
boss cikin idanuwanta , tun accident din da ya faru har bobo ya tsinka mata mari
bata sake ganin sa ba duk yadda taso hakan kuwa . Har ciki Robert yayi musu iso ,
lokacin uncle ya fito daga part d’insa bobo ba haka , hugging din bobo his
excellency yayi “ my son how are you “ fine Kawai bobo yace masa , itama Alice
ganin Dadynta na wajan ta mi’ke wai zatayi hugging d’insa , kallan da yayi mata ne
yasa ta waske ta koma ta zauna sai faman zuba ido take taga ta inda Big boss zai
‘bullo .

A ‘bangaran Abla kuwa suna zuwa wajan d’akin tsoro ya kamata , dad’insu ma yau ba
Victor bane dukda kusan halinsu d’aya amma Ana bud’e d’akin simba Abla ta je fa
masa abinci kamar yadda suka shirya plan d’insu ita da little , suna tafiya suna
dariya abunsu, a hanyar komawarsu gida sukaga manyan motocin da suka shigo , sau
d’aya little ya kalli motocin ya san bana yayansa bane , suna tafiya suna hira
abinsu gwanin burgewa , suna shiga cikin falourn sukai sutus Sabida mutanan da suka
gani zazzaune a falourn, Lokaci d’aya Alice ta mi’ke tsaye rai a ‘bace “ me wannan
‘kazamar take anan kuma ?”kallan tara saura Abla ta bita dashi lokacin da suke
shigo cikin falourn , shima little cikin ido ya kalleta “ she’s the sister of the
family kinga ba ‘kazama bace “, dakatar Dashi bobo yayi “ it’s okay little calm
down !” Turo bakinsa little yayi kafun ya gaishe da su mr president duk da ya sansu
amma kwata kwata face d’insa ba fara dan gabaki d’aya basuyi masa ba , itama Abla
gaishe dasu tayi zata juya little yayi saurin furta “ Lil ! Zo muje garden “ toh
kawai Abla tace zasu juya Alice tayi Saurin furta “ sorry guys zan iya binku”
little har Zaice mata ah’ah sai yaga bobo yayi knodding kansa , kamar yadda big
boss yake magana a fusge shima yau haka little yayi kafin ya furta “ why not “ Abla
lokaci d’aya kamar little ya rikid’e ya koma mata Big boss , suna tafiya yana janta
a hira banda Alice da sukayi kamar basu san da zuwanta ba . Suna shiga cikin garden
d’in Abla ta fara furta “ wow ! Wajan nan yayi kyau sosai “ murmushi little ya
sakar mata “ ko muje wajan pool? Zaifi “ da Sauri ta furta yes , haka suka bi wani
side duk a cikin garden d’in lokaci d’aya ya kawosu wani babban pool me shegen kyau
da fad’in had’uwarsa ‘bata bakine . Wani shu’umin murmushi Alice tayi batare da
tace musu komai ba , little har zai zauna a bakin pool d’in sai kuma ya dakata tare
da furta “ Lil ina zuwa “ okay Abla tace masa lokacin da ya bar wajan yayi saura
daga ita sai Alice , kallan ta Alice tayi daga sama har ‘kasa cikin wani irin
kallan tsana ,” how dare you ? Waya baki izinin zama a cikin gidan nan ?” Kallan
baki da hankali Abla ta bita dashi batare da ta tanka mata ba sai ma pool da ta
zubawa ido ganin yadda yayi blue , cikin tsawa rai a ‘bace Alice ta furta “ how
dare you ! Ina miki magana kin shareni? I can easy killed you ! Stupid !” Yanxu
banza Abla tayi mata hakan ya ‘kara ‘bata wa Alice rai da ‘karfi ta janyo rigar
Abla “ how dare you ?” Itama Abla rai a ‘bace tayi ‘ko’karin kwace rigar ta batare
da ta tankawa Alice ba , ko kawa suka soma yi Abla tana ‘ko’karin kwace rigar ta
Alice kuma tana ‘kara ri’keta, a zuciye Kawai ta jefa Abla cikin pool, gashi Abla
bata iya ruwa ba , lokaci d’aya ta fara wutsul wutsul a cikin ruwan ta na mi’ko da
hannunta, ga ruwa da ya’ke shigar mata hanci, sosai Abla ta soma ‘ko’karin fitowa
Amma kamar ruwan janta yake , tsaki Alice taja ta juya tabar Abla tana wutsur
wutsur gashi ko idanuwanta bata iya bud’e , lokaci d’aya nunfashinta ya soma sar
tsewa sabida rashin nunfashi da bata sha’ka, tun tana ‘ko’karin cecan kanta har ta
dena motsi da hannunta , gabaki d’aya jikinta ya soma nutsewa cikin ruwan.
PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta
wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

WATTPAD
https://www.wattpad.com/user/Msslee__

AREWA BOOK
https://arewabooks.com/book?id=652ff3a03fd6ffc37f68e4e2

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta
wannan number 07041879581.

NOT EDITED
S____26💞
A dai dai lokacin da Alice ta fito daga wajan , a dai dai time d’in shima Little
ya nufi fool d’in, ganin yadda gabaki d’aya kamar ba’a cikin nutsuwar ta take ba
yasa ya d’an ta’be bakinsa dan shi gabaki d’aya yarinyar bata yi masa ba , yana
shiga ya tarar da babu Abla , da ‘karfi ya furta “ Lil sis kina Ina ? “ shiru ba’a
amsa masa ba, a karo na biyu ya ‘kara furta “ Lil na dawo “ nan ma shiru babu amsa
dan gabaki d’aya hankalinsa bai kai cikin ruwan ba , har ya juya zai fita yaga
kamar abu ya fad’a cikin ruwa , ‘kirjinsa ne ya buga da ‘karfi lokacin da ya hango
kayan Abla , da ‘karfi ya furta “ Lil? Lil? Lil?” Kusan sau uku Abla bata amsa ba
gashi ta nutse cikin ruwa , hankali a tashe little yayi ‘ko’karin shiga cikin ruwan
amma an hanasa sabida condition d’insa , gashi bazai ta’ba iya barin Abla a cikin
ruwan ba, danger ya danna dake jikin pool d’in batare da ya damu da yadda nasa
rayuwar zata kasance ba ya fad’a cikin ruwan. Cikin kwarewa yake yin iwo cikin
ruwan duk da yadda shima nunfashinsa yake ‘ko’karin sar’kewa dan sosai Big boss ya
hanasa shiga cikin pool yanxu sabida condition d’insa , dai dai inda Abla take
little ya nufa yana ‘ko’karin zaro ta , shima lokaci d’aya nunfashinsa ya soma
sar’kewa ga sanyin ruwa da bayaso yana ratsa masa jiki, amma duk da haka cikin
‘karfin hali yake janyota, at the same time shima yana ‘ko’karin fusgo nashi
nunfashin da yake ‘ko’karin sar’kewa, da saurin sa yake janyo hannun ta da ko kusa
babu alamar rai a tattare da ita ,Tun kafin suyi nisa shima ya saki hannun ta da ya
ri’ke mata Sabida yadda nunfashinsa ya tsaya lokaci d’aya , kamar yadda ta soma
nutsewa a cikin ruwa haka shima little ya soma nutsewa.

***** Lokacin da Little ya danna danger take a wajan wani jan na’ura ya karad’e
gabaki d’aya cikin gidan, a zabure sojojin suka saita bullet d’in bindigogin su,
Bobo na zaune akan 1 sitter lokacin da Alice ta shigo cikin falourn kamar arud’e,
yana ‘ko’karin yi mata magana yaji ‘karar danger ,da wani irin mugun zafin nama ya
mi’ke tsaye , lokaci d’aya kawai ya kalli direction d’in Alice , babu Wanda yayi
wa magana shida uncle cikin gudu gudu su Bobo sukai ‘ko’karin fita , tun kafun ya
fita shima prince da ya fito daga cikin d’aki ya ‘kwalla wa bobo ‘kara yana furta
“yaya bobo suna swimming pool “, Bobo bai jira jin ‘karshen zancan saba ya saka
gudu cikin mugun speed , shima prince sakkowa yayi yana bin Alice da kallo dan
gabaki d’aya yaga abunda ya faru , cikin tsana ‘karara ya furta “ zaki gane kin
shigo gidan da ba’a hauka “ daganan be ‘kara ce mata komai ba shima ya saka gudu
yabi bayan Bobo.

Her excellency ce ta kalli Alice cikin d’an rud’u “ Sweaty me ya faru?” Ita ma
Alice da jikinta ya fara rawa kallan Dad d’inta da Her excellency tayi ganin suma
gabaki d’aya sun zuba mata ido suna jiran jin amsarta, bakinta har rawa yake
lokacin da take magana “ Dad bansan me ya faru ba ! Bani da laifi ! Ta ri’keni da
fad’a mistakenly ta fad’a ruwa , I don’t know Anything “, shi kansa His excellency
be san lokacin da ya dakawa Alice tsawa ba , karo na farko a rayuwarsa ,” Are you
mad ? Baki da hankali ? Kinsan Gidan suwa kika shigo? No! No!No! We have to leave
now kafin Big Boss ya shigo , Let’s go”, da Sauri suka fito daga cikin falourn ,
Sojojinsu suka bud’e musu mota suka shiga , Allah Allah His excellency yake su fita
daga cikin gidan Inya so koma menene zai yi sau’ki Amma abinda basu sani ba sun
makara sabida tun kafin su fita daka gate 1 , Manya Manyan motocin Big Boss suka
shigo cikin gidan da mugun speed , wani irin gefe motar Big Boss tayi har wajan
garden d’in, cikin zafin nama ya nufi Pool d’in shima . Victor da Anthony da suma
sam babu fara’a a tattare dasu suka shiga gaban motocin president , cikin Sauri
sojojin president suka fito tare da saita su Victor da bindiga, basu ankara ba sai
gani sukai gabaki d’aya sojojin Big boss sun zagayesu tare da saita ko wannansu da
bindiga , umarni kawai suke jira su saki bullet uban kowa ma ya mutu.

****** Bobo na zuwa bakin pool be jira komai ba ya fad’a cikin ruwan , Little ne a
farko farko cikin kwarewa Bobo yake yin iwo cikin ruwan, Little ya fara cirowa
Sabida sanin halin conditions d’insa ,
Duk da shima ba kasafai yake san ruwan sanyi a jikinsa ba , haka ya koma cikin
ruwan yana ‘ko’karin ciro Abla , Duk yadda yake tunanin abun ba me sau’ki bane
sabida yadda Abla ta ma’kale ta hanyar da ruwan pool d’in yake tafiya , idan yace
zai cirota ta ‘karfi kuma zai iya ji mata rauni, duk yadda yaso ya janyo ta abun ya
ci tura shiyasa ya nutse cikin ruwan kamar wani kifi ga idanuwansa da suke a bud’e
yana kallan cikin ruwan, ‘kafar Abla ce ta ma’kale , idan kuma yace zai janyo mata
zai ji mata mummunan rauni, kamar daga sama suka ga Big Boss a wajan pool d’in ,
cikin Tashin hankali Prince ya nuna masa pool d’in “ yaya zata iya mutuwa any
moment tafi 10minutes a cikin ruwan”, d’an ‘karamin tsaki Big Boss kamar bazai
shiga ba , lokaci d’aya kamar wani iska ya fad’a cikin ruwan , yadda yake yawo
cikin ruwan zaka tabbatar ba ‘karamun iya ruwa yayi ba ,cikin Sauri sauri ya nufi
inda Bobo ya nutse , Bobo yana ganin Big Boss ya saki ‘kafar Abla da yake ‘ko’karin
cirowa , cikin Sauri ya fito daga cikin ruwan ya nufi little da har uncle da prince
sun fara fitar masa da ruwan da ya shigar musu ciki, batare da ‘bata lokaci ba Bobo
ya sa’bi little a ka fad’arsa suka bar wajan gabaki d’aya , wajan yayi saura Abla
da Big Boss .

Almost 2 minutes Big Boss yana cikin ruwan nan shida Abla , idan mutum ba lura yayi
ba sai ya d’auka baya cikin ruwan sabida yadda yayi mugun nutsewa, cikin ‘yan
seconds d’in da basu wuce 30 ba inda suke ya soma yin ja alamar d’aya daga cikin su
ne ya ji ciwo. Ko mintuna d’aya cikakkiya basu ‘kara ba ya janyo ‘kafarta ya fito
da ita daga cikin ruwan, gashi ya had’e face d’insa da tayi mugun yin ja na ‘bacin
rai . Guntun tsaki yaja ganin yadda kayan jikinta suka manne mata , har yanxu face
d’insa ba fara’a ya kauda kansa tare da mi’kewa batare da ya kalli side d’in da
take ba ya d’auki Coat d’insa white colour xai ‘bar wajan , bayajin zai iya temaka
mata amma idan ta mutu shine da lefi a Wajan Allah , wani ‘karamin tsakin ya ‘kara
saki ya nufo inda take a kwance bata ko motsi, kamar zai kai
Hannu kan face d’inta ya ‘kara jan wani tsakin , gefen face d’inta ya d’an duka
tare da furta “
Hey !” Shiru Abla bata motsa ba , a karo na biyu ya d’an mari d’ayan side d’inta
yana furta “Hey” still ba’a amsa masa , ganin yadda ruwa ya fara fito mata daga
gefen bakinta kad’an yasa ya ‘kara sakin wani gajeran taki , Hannunsa d’aya ya kai
Daidai saitin cikin ta yana yatsine fuska, yana dan na mata cikin, sai ga ruwa nan
ya fara fitowa daga bakinta sosai , akaro na biyu ya ‘kara danna cikin kamar Wanda
akai wa dole ,wani ruwan ne ya ‘kara fitowa daga bakinta,lokaci d’aya ta soma tari,
idanuwanta da ta fara bud’ewa sosai take ganin bishi bishi a cikinsu, a karo na uku
ya ‘kara danna mata cikin , lokaci d’aya gabaki d’aya ta fito da ruwan bakinta ,
bai tsaya a ko ina ba sai a kan face d’in Big Boss .
Cikin tsananin ‘bacin rai ya sha’ko wuyanta, lokaci d’aya ta ware kyawawan
eyes d’in ta akan kyakkyawar face d’insa , jijiyoyin kansa sosai suka fito rud’u
rud’u na ‘bacin rai , ga kwayar idanuwansa da lokaci d’aya ta ri’kid’e ta koma ja,
kakarin mutuwa Abla ta fara Sabida irin mugun sha’kar da ya kai wa wuyanta, hannu
d’aya ya d’aga zai tsinka mata mari tayi saurin runtse idanuwanta gagam tana jiran
jin saukar marin sa , ‘karamin tsaki yayi a ‘kasan ma’koshi tare da mi’kewa tsaye ,
cikin Sauri Abla ta ware idanuwanta ganin be mare tan ba da Sauri ta mi’ke tsaye
zatayi masa magana wani saban jiri ya ‘kara d’ibarta da ‘karfi ta furta “ Wayyo
Allah..” tana ‘ko’karin fad’awa swimming d’in, cikin zafin nama ya ri’ke rigar
hannunta batare da ya ta’ba taba, lokaci d’aya Abla kamar me iska ta fad’o jikinsa
a sume ,gabaki d’aya jikinta ya saki sabida tsananin tsoran da ya kamata. A hankali
Big boss ya furta “ Huh”, be kuma bi takan taba ya nad’e ta cikin coat dinsa kamar
wani bargo, yadda ya d’auketa kamar Wanda ya d’auki Baby , dan hatta face d’inta
ba’a gani
Haka ya d’auke ta ya Fito daga cikin Garden d’in, cikin Sauri gabaki d’aya sojoji
suka sunkuyar da kansu musamman yadda ‘ka’k’karfar muscles din Big Boss Suka ‘kara
fitowa Sabida ji’kewar da rigarsa tayi , ko kallan side d’in motar su president
beyi ba ya wuce cikin part d’insu. Gabaki d’aya sojojin president suna ganin
fitowar Big boss suka sauke bindugunsu tare matsawa gefe suma sara masa.
Hannu Alice ta d’ora aka kamar zatayi hauka “ No!!!! No!!! Dady ! Me yasa zai
d’aukota ?Ni ya kamata ya d’akko! No Dady , Do something now ! Just bana san komai
a d’aura mana Auran mu yanxu !”, cikin cool voice her excellency ta furta “ No
sweety calm down ! He’s your husband ki bari musamu mu fita daga baya sai ayi
maganar auranku “ Girgiza mata kai Alice tayi a hauka ce ta furta “ No mom ! Baki
ga wata banza ya d’auko ba ni ba ! Dad say something ko kuma ni naje na saukar da
ita “, cikin tsawa president ya furta “ shout up stupid ! Baki ji abinda mom dinki
tace ba ?” Cikin mamakin Alice ta furta “ Dad ? Ni kake wa shouting ? Good !” Itama
cikin tsawa ta kalli babanta babu d’igon girmamawa akan face d’inta ta furta “ Na
fuskanci yanxu baka soma , it’s okay mom ce kawai take sona then I will killed
everyone sannan na rayu da Wanda naka so”, tana kai ‘karshen maganarta ta fito daga
cikin motar gabaki d’aya idanuwanta sun rufe da kishi , Her excellency ce ke faman
furta “ No! No sweety! “ shima rai a ‘bace His excellency yasa sojojin sa su tada
mota, Her excellency zatayi masa complain shima rai a ‘bace ya daka mata tsawa, sai
alokacin sojojin Big boss suka matsa masa ya wuce , da zasu fita har sara saida
sukai. Sai a lokacin tsoro yashiga Alice ganin Dad d’inta ya tafi , ta d’auka zai
fito ya lallasheta ne , da d’an ‘karfi ta furta “Dad! “ tana ‘ko’karin bin
bayansu,wani irin bugu da Victor yayi mata a kafad’a sai data zube ‘kasa bata
motsi.
***** Big Boss yana shiga cikin falourn ya tarar da ba kowa , Daidai kan 3
sitter ya saki Abla kamar wata kayan wanki yayi wucewarsa . Yadda ya saketane yasa
ta gangaro ‘kasa sai ji kake kummm ta bige ‘keyarta, cikin Sauri ta bud’e
idanuwanta Sabida ta ji zafin buguwar da tayi a ‘kasa , mamakin ganinta A falour
tayi , cikin Sauri ta kalli rigar jikinta kamar me san tuna wani abu, a hankali ta
kai hancinta kan rigar tana sunsunar ‘kamshin jiki, lokaci d’aya ta lumshe
idanuwanta sabida yadda taji ‘kamshin turaransa ya Dakar mata hanci , har wani
ajiyar zuciya take saukewa , a hankali ta tashi a daddafe tana ‘kara rungume coat
d’in jikinta , ganin babu kowa a falo ga sanyi da take ji yasa kai tsaye bata zauna
ba ta wuce d’akın ta .

********* Direct d’akin little ya nufa , yana shiga ya tarar dasu gabaki d’ayansu
sun zagayesa ga babban duvet da aka lullu’be masa jiki dashi , hatta yanayin d’akın
prince ya mayar masa dashi warmer , yana ganin Big boss ya tashi tare da duvet
d’insa be yi wata wata ba ya fad’a jikin Big boss , shima da both hand d’insa yayi
hugging little yana lumshe eyes d’insa , kamar me shirin yin kuka little ya furta “
yaya ina Lil ? Babu abunda ya sameta ko ?”, amaimakon Big boss ya amsa masa
tanbayarsa sai ma kallansa da yayi cikin cool voice ya furta “ are you okay ?” Da
Sauri little ya jinjina masa kansa , maida kallansa Big boss yayi kan prince ,shima
cikin Sauri ya juyowa da Big boss system d’in gabansa “ yaya watches this please !”
Kallan system d’in Big boss yayi , hatta bobo da uncle duk gabaki d’aya system d’in
Suka zubawa ido , gabaki d’aya abunda ya faru tun zuwan su little pool da lokacin
da ya barta ita da Alice da abunda ya faru tsakaninsu har ta jefata cikin ruwan sai
da suka gani, rai a ‘bace bobo ya furta “ She’s too much ! Har kisa ?” Yana kai
‘Karshen zancansa ya bar d’akin , Big boss kuwa ta’be bakinsa yayi kad’an kafin ya
ri’ke hannun little suka bar d’akin zuwa part d’insa .

✨✨✨✨

Abla tana komawa d’aki wanka ta shiga shaf shaf,sannan ta canza kayan cikinta zuwa
wasu masu kaurin kad’an , coat d’in Big Boss da ta ajje kan gadon ta d’auka , bata
san lokacin da murmushi ya su’buce mata ba , har wani rungume rigar take , yadda ta
hango face d’insa a had’e lokacin da ta far fad’o ne ya ‘kara fad’o mata a rai ,
cikin sauri kamar wacce akace yana kallanta ta ‘boye face d’inta cikin rigar,
gabaki d’aya murmushi ya ‘ki ‘boyuwa akan face d’inta ,ga abunda ya faru yana ‘kara
fad’o mata arai kamar yanxu ne yake faruwa , akaro na ba adadi ta ‘kara shinshinar
rigar ta saka ,kafin ta zurata a jikinta duk da yadda tayi mata yawa a jiki sosai ,
Daidai bakin Mirror ta tsaya tana bin jikinta da kallo ga murmushin ta da shima
ya’ki boyuwa har yanxu , hannu d’aya ta saka lokacin da ta kalli mirror d’in kafin
ta saki wani blow kiss a tafin hannunta , ita kad’ai kamar zararriya zai juyi take
cikin d’akin tana sakin murmushi.
Knocking d’in ’kofar da akai ne Abla tayi saurin cire rigar Big Boss ta jefata a
cikin wardrobe kafun ta bud’e ‘kofar, Prince ne tsaye a Wajan hannunsa da wani
coffee me zafi da sai faman turiri yake d’auka , yana kallanta ya sakar mata
murmushi tare da mi’ka mata coffee d’in “ just for Lil , ya kamata kisha da zafinsa
kar kiyi mura “, Godiya Abla tayi masa sosai bayan ta Amsa cup d’in, kafun ya juya
yabar wajan ita kuma ta koma cikin d’aki dan ita batasan da fad’uwar little cikin
ruwa ba .
Sosai ta sha coffee d’in dan sai data shanyesa gabaki d’ayansa tana sakin ajiyar
zuciya, ga jikinta da ya fara d’aukar d’imin la’asar, Alwala kawai tayi ta zauna
tana jiran kiran sallar la’asar ga tinani barkatai dake ‘ko’karin hana zuciyar ta
sakat.

Bobo yana fita direct waje ya fito ganin Alice kwance a ‘kasa ga su Victor da suka
saita mata kai da bindiga , cikin bada umar yasa su sakata a cikin mota, babu ‘bata
lokaci kuwa Victor ya bud’e boot d’in motar Bobo ya sakata tare da kulle wa ,
Robert yana driving seat ko sauran sojojin bobo be d’auka ba da gashi sai a Robert
sai kuma Alice da aka jefa cikin mota, babu ‘bata lokaci Robert ya tayar da motar
cikin mugun speed tare da barin gidan gabaki d’aya .

✨✨✨✨
Lokacin sallar la’asar nayi Big boss ne suka fara fitowa shida little da ya canza
kayansa zuwa masu kauri kad’an hatta gyaran gashin kansa yau ya canza , gefed’aya
Daidai wajan idan sa , d’aya gefen kuma ya had’e da gyaran gashin kansa . Gabaki
d’ayansu masallaci suka nufa sabida kiran sallar la’asar da akeyi ,ana idar wa Big
boss part d’insa ya wuce shi kuma Little ya wuce d’akin Abla . Sau biyu yayi
knocking lokacin da take addu’a , tana zuwa ta bud’e masa ‘kofa , face d’insa cike
da murmushi ya furta “ Lil kina lapiya ?” Itama murmushi Abla ta sakar masa kafun
ta furta “ eh mana , bayan tun d’azu nake jiran ganin ka amma ka’ki zuwa ni fushi
nake da kai “ shima kamar zai shagwa’be face d’insa ya furta “ Haba mana Lil ! Kiyi
hakuri naje part d’in yaya ne , lokacin da zan zo kuma ana Kiran sallah shiyasa da
ban zoba” dariya Abla ta ‘kyal’kyale masa dashi , hakan da tayi kuwa ba ‘karamin
kyau yayi mata ba “ Nifa yaya little wasa nake maka , kaga yadda ka shagwa’be face
kamar ta mace “, d’an harararta Little yayi “ Nine ma ta mace ?”, da Sauri ta
girgiza masa kai tana dariya “ okay let’s go “ bata koma cikin d’akin ba suka sakko
Abla sai faman zolayan little take a hanya , suna sakkowa game little ya saka musu
sabida yasan bata iya mota ba , da Anfara sai ta fad’i shiyasa yake ta faman yi
mata dariya cikin mugunta , ganin ta kasa cinsa a wajan ne yasa tayi saurin fusge
game d’in ta gudu , shima little cikin Sauri ya biyo bayanta amma sai ta ‘boye
bayan kujera , cikin dariya little ya furta “ Allah Lil ki bani kinga fad’uwa kika
bani ne na fad’ar da ke ba “ itama Abla cikin gwalo ta furta “ Allah bazan baka ba
ai cutata kake , kasan ban iya ba shiyasa sai faman fad’ar Dani kake “, zai biyo ta
ta ‘kara waskewa dai dai lokacin prince ya shigo falan shima , cikin Sauri Abla ta
gudu bayansa , da little yazo zai kamata zata goce sai dai ya kama Prince , gabaki
d’aya sun ‘ki tsayawa balantana prince yayi musu sulhu sai suka mayar dashi abun
wasan su, cikin dariya prince ya furta “ Allah idan baku tsaya ba zan fad’awa yaya
Big boss kasan dai yana cikin gidan nan “ lokaci d’aya kuwa ga baki d’ayansu suka
tsaya , cikin Sauri little ya fusge game d’insa “ Allah sister zaki gane , yanxu ni
yunwa nake ji lets eat”, girgiza masa kai Abla tayi “ Ni na ‘koshi “ kusan lokaci
d’aya prince da little suka had’a baki “ me kikaci?” Batare da damuwa ba ta basu
amsa “ Yaya Prince ya banı coffee banajin yunwa ?”, shine kika ‘koshi ?” Cewar
prince yana katse ta , yanxu manta ta jinjina masa “ Allah yaya prince na ‘koshi
bana jin yunwa “, shima little prince ya kalla “ Sister tace bata jin yunwa , toh
Nima na ‘koshi “ cikin Sauri Abla ta girgiza masa kai “ yanxu fa kace kana jin
yunwa ! Toh shikenan wasa nake masa Zanci kaji, let’s eat “, murmushi little ya
sakar mata yana jinjina masa kanta, daga haka suka nufi dinning su uku , yau Abla
tayi serving d’insu , suna ci suna kira abinsu gwanin burgewa . Saida suka kammala
cin abincin su gabaki d’aya suka koma falour , Abla sai labari take basu su kuma
suna dariya , mi’kewa tsaye Little yayi yana kallansu “ am coming back “ daga haka
ya wuce
sama abinsa , cikin ‘kan’kanin lokaci ya dawo hannun sa d’auke da System d’in Apple
, Abla ya mi’kawa yana furta “ For you “kallansa Abla tayi kamar zatayi kuka ,
gashi ta ‘ki amsan system d’in , kasan tuwar a 2 sitter take hakan ya bashi daman
zama a kusa da ita “ I told you we’re family , banasan inna baki abu kina ‘kin
karba , we are now the family of 6, yanxu banzo kice komai idan ba haka zan fad’awa
yaya kinji “ kwalla ne suka tarar wa Abla a ido a hankali ta furta “ Na gode Allah
ya.. “ dakatar da ita yayi lokacin da ya kunna system d’in “ ni nace miki banasan
godiyar ki , Nima zan sa yaya ya kawo mun wata, ynxu zan nuna miki yadda zakiyi
angani da komai , hatta English da komai da kikeso zaki iya kalla , bazai kinsa
data ba , tunda datar yaya Big boss a kunne take kawai kiyi ta anfani dashi”
murmushi ne ya su’buce wa Abla lokacin da little ya ambaci sunan big boss , gabaki
d’aya yadda zatayi anfani da system d’in Little ya nuna mata da komai da take san
shiga da kallo ma idan tana san yi , ga games nan ma da ya fito mata dashi sasoi ,
cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta gane komai da ya nuna mata , lokaci zuwa lokaci sai
faman sakin murmushi take , suna gamawa wani saban hiran suka saka , sai da sukaji
kiran sallar magrib sannan kowa ya nufi part d’insa . Amma wanka ta sake yi sannan
tayi sallar magrib, tana idarwa bata tashi a wajan ba ta soma karatun al’kur’ani
har
Saida aka kiran sallar isha, cikin nutsuwa take yin sallar ta har tayi shafa’I da
wuturi, ko zama bata ‘kara yi ba ta sakko ‘kasa da mayafinta data yafa , little na
zaune yana jiran ta , d’akin simba suka nufa yanxu ma bata shiga ba daga waje suka
jefa masa abincin suka gudu. Amaimakon su koma cikin gida sai suka tsaya a Wajan
garden suna kallan stars ga sanyin iska da wajan yake dashi, har ‘karfe tara da
rabi suna Wajan , gabaki d’aya sun manta Big boss na gida sabida yadda suke hirar
su abun sha’awa , sai 10:34pm Suka ankara da yadda tare ya fara , cikin Sauri suka
nufi cikin gidan. Big boss da suka zaune cikin shigar ba’ka’ken kayane yasa
zuciyarsu bugawa da ‘karfi, kana kallansu kasan basu da gaskiya , ko kallansu Big
boss be yi ba sai system d’in gabansa da yake dannawa , ga hasken system d’in da ta
nuna yadda page d’insa take a hard’e , a hankali little ya ‘karasa kusa dashi ya
zauna , wani irin bombastic Side eyes Big boss ya bishi dashi , cikin Sauri little
ya gudu sama sabida kar ya ce ze masa abu. Abla kuwa kasa motsawa tayi daga inda
take , sai ma sunkuyar da kanta ‘kasa da tayi, still big boss be d’ago face d’insa
ba aikin gabansa kawai yake , ganin ta gaji da tsayuwar kusan 10 minutes be ce mata
komai ba , cikin ‘karfin hali ta je ta had’a masa coffee , hannunta har rawa yake
lokacin da ta mi’ka masa tana furta “ gashi….” Da ita da coffee d’in sai a ga me
magana dan kamar wacce tayi da dutse sam be d’ago ba sannan be kalli inda take ba ,
tafi 15 a tsaye kamar zatayi kuka gashi ta gaji da tsayuwar, a karo na ba a dad’i
ta ‘kara furta “ ga coffee d’in “ kamar zatayi kuka Sabida yadda ya share ta , sai
faman satar kallansa take ta ‘kasan ido. A ta’kaice saida Abla tayi kusan 2 hours a
tsaye Big boss yana aiki a system sai da tabbatar ‘kafarta tayi tsami tukunna ya
ajje system d’in a kausashe ya furta “ 10 cups of coffee” , cikin Sauri Abla ta
amsa masa ganin tana kai masa coffee d’in itama zata huta , bata d’au dogon lokaci
ba ta fita da wani tray white colour ga cups din coffee kusan guda goma Ajera , kan
center d’in gabansa ta ajje masa tana furta “ ga coffee d’in” sai da ya mula dan
kansa kusan 2 minutes ta d’auka bazai tanka mata ba sai kuma taji saukar muryarsa “
shanyesu duka “ azabure Abla ta furta “ me..me.. ka..ce ?” Banzan kallan da yayi
mata ne yasa tayi saurin tsugunnawa ta d’auki 1 cup ta soma shansa kamar zatayi
kuka , ta d’auka zaice ta barshi taga har ta shanye cup 2 be ce mata komai ba ,
kamar zatayi kuka ta d’auki cup 3 shima har tazo kan cup 6 , lokaci fuskarta tayi
jajawur har hawaye sun so ma sakko mata , ga shi cikinta ya cika bazata iya shan
ragowar ba , amma tana tsoran wani hukuncin nasa , har amai ta soma ji Sabida yadda
ta cika cikinta, amma bawan Allah be tsayar da ita ba , tana zuwa cup 9 ta fashe da
kuka , yana d’ago dakansa ta d’an turo bakinta tana had’iye kukan. Sai da ta shanye
gabaki d’aya cup d’in sai faman nishi take da ‘kyar , a hankali ta furta “ na gama
“ still big boss be kulata ba saida ya ‘kara 20 minutes lokaci saura ‘kiris fitsari
ya kwace mata , addua take Allah yasa ya barta ya tafi dan zata iya yinsa a ko
ina . Kamar yaji me tace ko kalla bata ishe shiba ya saka black p-cap d’in data
kusan rufe masa fuska ya fita daga falourn, cikin wata babbar ba’kar Lamborghini
Victor ya bud’e masa , Victor ya shiga driver set, Anthony kuma ya shiga d’ayan
side d’in suka bar gidan su kad’ai , har lokacin bobo be dawo ba kuma. Abla tana
ganin ficewar sa har wani gumin bala’I take had’awa , a guje ta nufi d’aki, ko
tsayawa batayi ba sabida fitsarin da ya kamata . Sai da tayi tukunna ta saki ajiyar
zuciya tana safa cikinta da take ji cike taff da ruwa , ko minti goma batayi ba ta
sake komawa yin fitsari, ita kad’ai sai faman zaryar yin fitsari take dan 10 cups
ba wasa ba , saida tayi zaryar yin fitsari, ana biyar d’inne har da kwalla kafun ta
Samu ta kwanta , cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya d’auketa.

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂

KANO
Yau ya kama ranar dasu Eshaal zasu koma Us, duk hanyar da baby ta bi danganin ba’a
tafi da itaba abin ya ci tura Sabida duk lokacin da zata takaleta da fad’a Eshaal
bata biye mata , Musamman yau da ta sha kuka Sabida zasu rabu da Ammi, Baby kuwa
tana wajan su dad sai lallashinta sukeyi akan kome take so ta saka Eshaal idan
ta’kiyi mata ta kirası , bayan doğan gargad’i da Tasha wajan su dad , lokacin da
zata su tafi Airport kamar karta tafi Sabida Amma , ita kanta AMMA sai da ta share
‘kwalla , baby kuwa sai faman taunar cingum take abunta su dady suna lallashinta
har suka tafi Airport. Acikin Airport din ma ko kusa mutum bazai ce tare baby take
da Eshaal ba Sabida yadda taja gefe wai zata bata masa class d’in ta . Acikin
jirginma Baby tana ‘bangaran Business class , Eshaal kuma tana inda normal people
suke , cikin ‘kan’kanin lokaci jirginsu ya tashi zuwa U.S .

*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta
wannan number 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨

KAR AMANTA AYI FOLLOWING DINA


👇👇👇👇

WATTPAD
https://www.wattpad.com/user/Msslee__

AREWA BOOK
https://arewabooks.com/book?id=652ff3a03fd6ffc37f68e4e2

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
Book 1 free ne, book 2 kuma 300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a
turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

S____27💞

Yau Abla da wuri ta farka Sabida ta sakawa kanta hakan cikin ranta , tana idar da
sallar asuba d’akin ta gyara gabaki d’aya kafin ta yi wanka, yau ba lefi ta gwada
wanke kanta , dan sosai ta dirje kan nata da yayi mugun datti, har wani brown brown
yake tsabar datti, tana wanke wa gaban mudubin d’akin ta dawo tana bun jerun kayan
wajan, d’aya daga cikin mayukan wajan me suna HEMANI ta d’akko, daga cikin oil d’in
zakaga hotan Black seed a jiki. Sai data bari kanta ya bushe sosai sannan ta shafa
oil d’in a kanta , binciken inda zata samu comb ta soma, cikin sau’ki kuwa ta same
wani black comb , daga ‘kasa ‘kasan gashinta ta soma tajewa Sabida zafin da yake
mata , tanayi tana runtse ido ga nishin da take lokaci guda sabida wahalar tajewa
da take ji . Da ‘kyar ta iya taje kan shima sama sama ta tattara ta ajjesa , sabida
yadda ya ‘kara cikowa ko d’aure kan ta kasa sai mayafi da ta yafa akan ta , duk
Wanda ya kalli kanta sai yayi mata dariya sabida yadda gashin kanta ya ciko sosai
cikin mayafin kamar wani bishiya. Cikin d’an turo bakin da ya d’an zamar mata jiki
ta fito daga falourn, 7 ta kusa shiyasa bata tsaya jiran Little ba yau ta wuce
kaiwa simba abinci da kanta , dukda yanxu ta d’an rage jin tsoransa ba kamar daba ,
hatta sojojin gidan ma yanxu ta rage jin tsoransu sosai dan yanxu ma da kanta ta
wuce ga tulin gashin kanta da yake nunawa. kamar yadda Little ya koya mata , tana
bud’e d’akin simba bata shiga ciki ba ta jefa masa abincinsa tayi saurin guduwa
cikin gida.

Tana shiga ta tarar da su Bobo a tsats tsaye da alama daga masallaci suka dawo,
sai da tabi kowannansu ta gaishesa amma bata ga Big boss ba , har cikin ranta taso
ganin nasa ko saud’aya shiyasa gabaki d’aya mood d’inta ya canza . Cike da zolaya
Little ya nuna Kanta “ Sister Menene a kanki haka kamar bishiya?” Kan nata ta ta’ba
itama , kamar zatayi kuka ta girgiza masa Kai dan ta rasa Wana irin amsa zata bashi
ma ,” oya muga bishiyan kanki “ cewar little yana ‘kara mata dariya , da Sauri Abla
ta saka hannu zata kare kanta , shima little ya dage sai ya ga kan nata , ita kuma
ta ‘ki barin sa ya bud’e mata kai , da ya matso zata goce masa , su Prince suna
tsaye suna musu dariya , ganin Sauri zata gudu mayafin kan nata ya zame , wata
iriyar shegiyar dariya prince da little suka saki lokaci d’aya sabida uban tulun
Abla suka gani gashi kamar bishiyar sabida yadda ya mimm’ke tsaye, shima Bobo sosai
yayi mamakin uban tulin gashin kan Abla , ydda ta sunkuyar da kai kamar zatayi kuka
ne bobo ya dakatar dasu little daga dariyar da suke mata “ rabu dasu anjima zan sa
akai ki saloon a wanke miki , idan angyara miki karki nuna musu kinji ?” Da Sauri
ta jinjina masa kai “ Thank you so much yaya bobo” sai ta kalli side d’in su little
tayi musu kwalo tare da yan kwane hannunta kamar wata horror, gabaki d’ayansu
dariyar reaction d’inta suke , hira kad’an suka ta’ba ko wannansu ya koma part
d’insa Sabida zuwa training . Itama Abla d’aki ta koma ganin bacci be isheta ba
yasa ta fad’a kangado kamar me shirin komawa baccin , a hankali kuma ta furta “
Amma me yasa be fito ba ?” Kamar zata kawar da zancan daga zuciyarta amma hakan ya
faskara , so take kawai ta saka shi cikin idanuwanta koda ace hukunta ta zaiyi ,
haka kawai taji tayi missing d’in ganinsa , tun tana tunanin kyakkyawar fuskar sa a
zuciyar ta har bacci ya d’auketa.

10:50am Abla ta fito daga cikin d’akinta haryanxu kanta yana a yadda yake dan kuwa
sosai ya tashi kamar bishiyan, prince ne kawai a falour shima lokacin game yake ,
batare da ya kalle taba ya furta “ sister breakfast d’inki na dinning,Little yace
idan baki cıba idan ya dawo na fad’a masa “, kamar yana kallanta ta Jinjina masa
kan nata tare da furta “ okay yaya “. Tana zuwa dinning d’in ma ba wani abun kirki
taci ba , coffee Tasha sai waffles data gani , daganan kuma bata ‘kara cin komai ba
. Tana gama wa falour ta dawo , d’an satar kallan elevator Abla tayi kamar tana
jiran fitowar sa , sai kuma ta d’auke eyes d’inta “ Yaya prince ina yaya little ?”
Har yanxu game d’insa prince yake , still be kashe ba ya furta “sun fita da yaya
bobo”, Tom Allah ya dawo dasu lapiya “ cewar ta , shima da kalmar Ameen prince ya
bita dashi, yadda yake cin game d’in take kalla amma idan kayi mata kallan nutsuwa
zakasan gabaki d’aya hankalinta baya kan game d’in prince , ta fad’a wani tunanin
ne kawai daban. Lokaci d’aya taji zaman falourn ya isheta shiyasa tayi excusing
kanta ta koma cikin d’akinta , a fili ta furta “ me ya hanashi fitowa ? Ko bashi da
lapiya ne ?”, sosai damuwa ta hau kan fuskarta irin damuwa da bata ta’ba shiga ba
na rashin ganin wani, amma yanxu gashi ta damu da sanın halin wanda ya fi tsanar ta
a cikin gidan . Lokaci zuwa lokaci tana duba time , sau 2 tana sakkowa ‘kasa koza
ta gansa amma still babu alamar sa , ji take kamar ta tanbayi Inda yake amma haka
ta ‘kara komawa cikin d’akinta, a karo na 3 data ‘kara sakkowa bata ga prince ba
shiyasa ta sauke a jiyar zuciya . Gabaki d’aya ta damu da san ganin Wanda bata ma
isheshi kallo ba . Ha’kura tayi da sakkowan ta koma d’akinta ganin shirun na neman
gundurarta yasa ta d’auke system d’inta da little ya bata , kamar wacce ta ‘kware a
harkar computer haka take sarrafata sabida gabaki d’aya ta gane yadda ake anfani
dasu.

****** Big Boss

Tunda yafita daran jira bashi ya dawo ba sai washe gari da asuba , yadda kowa ya ga
face d’insa a had’e yasa suka soma kaffa kaffa dashi dan kuwa zai iya huce ‘bacin
ransa idan ka kuskura ka shiga gonarsa yau , hatta little idan yagansa a irin
condition d’in nan baya takura masa . Shiyasa gabaki d’aya gidan kowa ya shiga
cikin hankalinsa , musamman su little akan lokaci yau suka fito training batare da
sun ‘bata lokaci ba . Babu Wanda ya kalla yayi wucewarsa part d’insa . Direct
toilet ya nufa ya sakar wa kansa ruwa me mugun sanyi, ya dad’e a cikin ruwan kafin
ya danna wani button da glass in wajan ya zama kamar tinted , mutum bazai ta’ba
ganin me ke faruwa ba sai dai shi da yake ciki yaga abunda akeyi.
Be d’au dogon lokaci ba ya fito daga cikin toilet d’in d’aure da wani white
d’in rigar wanka sai gashin kansa da yake a ji’ke alamar wankesa yayi shima , ga
face d’insa da har yau babu fara’a kanta itama da alamar ruwa , d’ayan door d’in
d’akin ya shiga , ko 30 minutes be yi ba kamshi turaransa me shegen kamshi da
tafiya da zuciyar mutum
ya bada isowarsa, dan tun kafin ya fito daga cikin d’akin ko ina ya karad’e da
kamshi. cikin wani Dogon farin wando me laushi ya fito daga cikin d’akin, kana
kallan wandan zakaga da kad’an ya wuce gwiwar’kafarsa. Sai fararar kafafuwansa da
suka fito farare tass dasu musamman yanda suke cikin wani white din takalmi. lokaci
d’aya murd’ad’d’iyar surar jikinsa ta bayyana cikin farar singlet d’in jikinsa,
yadda singlet d’in ta kama masa jiki sosai hakan ya fito da six pack d’in jikinsa,
wani remote ya dakka lokacin da ya kwanta akan king size bed d’insa, take a Wajan
sanyin d’akin ya ‘karu sosai ga wani irin black dummm da d’akin yayi kamar babu
kowa a cikinsa.
****** karfe 12:10pm su little suka dawo cikin gidan , dan bobo ko zama beyi ba ya
‘kara ficewa bayan little ya shiga cikin gida . A kwance ya tarar da Abla kan 2
sitter ganin bata ji shigowar sa ba yasa ya lalla’ba bayanta Daidai saitin
kunnuwanta ya fara kukan mage “ meow ! meow !”da Sauri Abla ta bud’e idanuwanta
ganin little a gefen ta yasa ta tashi zaune “ Allah yaya little ka bani tsoro fa”
d’an murmushi yasaki kafun ya bata amsa “ naga baki ji shigowa taba kuma ba bacci
kike ba shiyasa na miki haka “Tom
Shikenan , yanzu dai sannu da zuwa , bari na kawo maka ruwa ko ?” Cewar Abla tana
mi’kewa tsaye , mayar da ita yayi kan kujerar yana girgixa mata kai “ No bana
bu’kata keda ya kamata ki fara tanbayata ina naje ?”, itama kanta Abla ta girgiza
masa “ But atleast ya kamata kasha ko ruwane kaji?”, zaman shi ya gyara kan kujerar
kafin yace mata “ okay”, cikin ‘kan’kanin lokaci ta dawo d’auke da ‘karamin tray me
cup da lemo da ruwa , ruwan kawai ya d’auka yasha tun kafin ta zuba masa , wani
envelope ya mi’ka mata , tun kafin tayi magana ya rigata “karki bud’e ki bari sai
kin koma d’aki”, bata kawo komai aranta ba ta amsa masa da Tom Daidai lokacin da
yake mi’kewa “ bari naje wajan yaya kinji ?” Bata san lokacin da bakinta ya su’buce
ba ta furta “ lapiyansa ‘kalau?” Murmushi little yayi mata kafun yayi knodding
kansa “ yeah ! Yaya yana lapiya nasan yanxu yana d’akinsa , bari naje wajan sa and
don’t forget sai kinje d’aki zaki bud’e envelope d’in kinji ?” Da toh Abla ta amsa
masa bayan ta tafi, itama d’akinta ta koma da Sauri dan ta matsu taga menene a
cikin envelope d’in, tana shiga ta bud’e su wata farar ta karda ta gani guda biyu
aciki paper d’in farko ta ‘kurawa ido tanbarin sunan “ HORACE MANN SCHOOL” ‘kurawa
paper d’in ido tayi sosai kamar tana san fuskartar abunda yake jiki, a hankali ta
soma karanta application d’in jiki, kamar wacce akai wa abu kuka ya ‘kwace mata ,
wani irin kuka take kamar Ance mata zata mutu dan dagasken gasken kuka take sosai,
ta jima tana kuka har ‘kirjinta ya soma yi mata zafi sannan ta soma ajiyar
zuciya , hawayen ta basu tsaya ba , ga murmushi da dariya da ya kwace mata lokaci
d’aya “ ni ? nice zan fara zuwa makaranta ? Dagaske ne ko wasa ? Da gaske daman zan
koma makaranta , Arwa ta kina ina kizo ki ga zan koma makaranta” ita kad’ai sai
magana take wa kanta sabida application d’in shiga Horace mann school da ta samu,
cikin Sauri ta ajje paper , ta shiga toilet tayo alwala , sai da ta yi na fila
raka’a hudu sannan ta zauna ta dinga addua Sabida tsananin farincikin da ta shiga ,
ga hawaye da murmushi kwance akan face d’inta . Tana idarwa paper ta d’auka da
gudunta ta fito daga cikin d’akin tana niyar sauka , suka ci karo da little , cikin
Sauri tayi hugging d’insa , murmushi ya sakar mata kafin a hankali ya furta “
suprised” itama murmushi da hawayene akan face d’inta yadda ta kwa’be face kamar me
shirin yin kuka “No katkı yi kuka mana ! Let’s go for the other surprised” yana kai
‘Karshen zancansa ya kamo hannunta suka sakko ‘kasa , a tsats tsaye ta tarar da
yaya bobo , yaya Prince sai uncle , Big boss ne kawai baya falan, suna ganin ta
suma suka had’a baki Wajan furta “ surprised”, zatayi kuka prince yayi Sauri cewa “
No LiL d’in Little , haka kikeso ki fara zuwa school kana kuka ? Ko so kike mu kıra
miki simba ?” Yanxu ma ‘kara ta’be face tayi zatayi kuka bobo ya harari prince “
rabu dasu Sister , zan rama miki , let’s enjoyed the cake together kar yayi
melting”, daga nan suka zauna bayan sun yanka medium cake din da aka yi tanbarin
school a jiki. Murmushi da hawaye suna sakko mata ta kalli uncle da yaya bobo nata
sun kuyar da kanta “ Nagode sosai Allah ya saka muku da mafificin alkairi, Allah ya
biya muku bu’katun ku na aikairi , Allah yasa ku gama da duniya lapiya, nagode
sosai”.ta karasa tana kallan little shima dan bakinta bazai iya misalta godiyar da
take so tayi musu ba , Allah ne kad’ai zai iya biyansu, ahankali ta furta “ yaya
little nagode sosai”murmushin da baya ‘boyuwa har yanxu ya sakar mata “ you don’t
have to thank me , ai bani na saki a school , makarantar da aka sakaki marabaci zan
zama” ya ‘karasa a zolaye Sabida tayi dariya , sosai kuwa tayi murmushi tana
sunkuyar da kanta ‘kasa . Wani Brown a kwati dake gefensu little ya matso mata
dashi “ ga uniform d’in makarantar ki , kinga yau Friday, Monday kuma zaki fara
zuwa school amma bazaki tafi da wannan kan naki me kama da na bishiya ba “,
rankwashi bobo ya kai masa aka da harsaida yace oushhh, “ kai me yasa tsokananka ya
fiya yawa ?” Cewar bobo kafun ya kalli Abla “ sister je ki shirya su kaiki saloon
yanxu “ da Sauri prince ya ce masa yaya bobo ai bamu bata namu gift d’in ba ,
mi’kewa tsaye yayi tare da wani black box d’an ‘karami ya mi’ka mata “ wishes you
all the best sister , nasan zaki karad’e kowa a class d’in ku , this is my gift,”
da murmushi akan face d’inta ta furta “ thank you yaya prince “, shima little wani
box ya mi’ko mata siriri “ Nima ga nawa gift d’in” shima fuskarta cike da murmushi
ta furta “ thank you so much yaya little”, bobo kuma wani ATM d’insa ya mı’ka mata
“ duk lokacin da kike bu’katar kudi zaki iya d’auka , it’s your gift , little yace
duk kyautar da batayi ba sai ansake “ dariya ce ta kwace mata , da hawaye. Face
d’inta ta furta “ ‘nagode yaya bobo “ dan gabaki d’aya ta rasa me zata ce musu, “
ah’ah ni kuma sai ku tsaya na bawa my only daughter gift d’inta okay “ box d’insa
shima ya mi’kawa little “ oya karkayan suyi mata yawa help her , it’s also my
gift”, gabaki d’aya she’s speechless, bata ta’ba kawowa akwia wad’an da zasu sota
arayuwa ba makamanciyar ydda su little suke mata , murmushi da kuncin face d’inta
ya kasa ‘boyuwa , kar’ban kayanta prince yayi ,little kuma ya ri’ke box d’aya da
akwatin school d’inta “ let’s go sister , kafun ayi sallah sai mu kaiki inyaso sai
mu dawo mu d’auke ki , okay ?” Kanta kawai tayi masa knodding da harshenta yayi
mata nauyi, ko da zasu wuce sai data kalli elevator ganin har lokacin bataga big
boss .
Har cikin d’akin sai da suka kai mata kayan , gashi sai faman tashin kamshi yake
ko ina tsaf tsaf da shi , kasa hakuri little yayi saida ya tanbayeta “ sister waya
gyara d’akin nan ?” Bata damu da tanbayar tasava shiyasa kai tsaye ta furta “ Ni na
gyara mana “, shima prince yayi mamaki da tace ita ta gyara dan ko ina a tsaftace
yake .
Basu zauna a cikin d’akin ba sai takalmi kawai da Abla ta canza suka sakko, ATM
d’insa bobo ya mika wa little “ oya ayi mata gyaran da ya fi nakowa and karku dad’e
okay ?” Okay ya’ya kawai little yace masa suka kama hanyar fita , yau bala’I little
yasaka akan babu me bunsu har saida bobo ya dakatar Dashi motoci biyu kawai suka
tafi da ita .
Mintuna 34 ya kawo su Heena’s saloon, tundaga wajan saloon d’in mutum zai san
ba na ‘kananan yara ba , saloon ne da manya mata masu ji da naira , ta’kama da
tun’kawo suke zuwa saloon d’in sabida yadda ake kashe ma’kudan kudi a wajan dan
sosai kayan wajan suke da tsad’a . Cikin harabar filin da manya manyan motoci sukai
parking suka shiga amma tun kafin su ‘karasa wajan motocin su Robert sukai parking,
little , prince da Abla suka fito, suna tafiya suna hira abunsu kwanin burgewa ,
Robert da captain kuma suna bunsu a bayan , sauran sojojin kuma suka tsaya a wajan
motocinsu.
Suna shiga wata ma’aciyar Wajan ta ‘karasa inda suke da murmushi akan face
d’inta ta furta “ how can I help?” Tanayi tana bin ko wannansu da kallo , sabida
wani irin masifaffen kyau da sukai mata kamar karta dena kallansu “ da hannu little
ya nuna mata kan Abla kafun ya furta “ Munasan saloon ne “ da Sauri ta nuna musu
hanya tana furta “ this way “ tana gama suna binta a baya , tun farkon shigarsu
wajan yan mata suka dunga bin su little da kallo , ko waccen su sai farii take yi
ko zasu kulasu amma ko kallo basu ishesu ba shiyasa wasu daga cikinsu cike jin dole
su samu hanyar yi wa Abla magana Sabida su sami damar yiwa su little magana , mata
uku da ga cikin yan wajan ganin su Abla sun nufi ‘bangaran saloon yasa suma gabaki
d’aya suka fasa abunda ya kawosu suka bi bayansu , acewarsu suma saloon za’ayi
musu, wata matace ta fito daga office da alama Babbace a wajan ta kalli su Abla
tana sakar musu murmushi dan sosai itama sukai mata kyau , duk da ashekaru zatayi
43 amma lokaci d’aya taji soyayyar little ta shigar mata zuciya , shiyasa ta
sallami ma’aikaciyar ita kuma ta bud’e musu wani vip rom, sai faman gyara rigar
jikinta take sabida ya kalleta , amma da ita da matacciya haka little ya d’auketa
dan ko uppan be ce ba , apart from his family bakowa yake wa magana ba, hatta yan
school d’insu kuwa , dan kwanda prince wani lokaci idan aka masa magana yana amsawa
sama sama , amma banda little da ya koyo halin rashin kula bare a wajan big boss .
Inda suka shiga kamar vip haka wajan yake dan sosai wajan yake da kyau ,
yan mata ne guda 5 a Wajan sai wasu ma’aikata , komai na wajan a tsare yake cikin
yanga matar ta nuna musu waje su zauna duk da yan matan da suke wajan , babu Wanda
ya bi ta kanta sai Abla da Prince ya nuna mata , “ ayi mata da most expensive
gyaran gashi , in ba damuwa zamu dawo nan da 1 hour in Angama mata “ cikin washe
baki jin abinda prince yace matar tace “bakomai ko yanxu kuka ce ayi muku ma za’ayi
muku” su kuma ragowar yan matan Wajan Abla suka zubawa ido Sabida gabaki d’ayansu
ta karesu a kyau bazasu ta’ba had’awa ba , duk cikinsu kuma jikinta ya fi nasu
gogewa dukda uban mayukan bleaching da suke anfani dashi , ga mamakin maganganun
prince . Hannu little ya d’aga mata “ Lil zamu dawo okay ?” Itama hannu ta d’aga
musu tare da furta “ Byee “ little har zai tafi sai kuma ya dawo bayan ya ciro
phone d’insa a aljihu “ oya kiyi game or anything karki zauna so boring okay ?”
Kanta tayi knodding tana furta “ thank you yaya little ,” shima prince hannu ya
d’aga mata “ bye lil” itama “ bye yaya Prince tace masa “ tana juyowa bayan sun
fita taga gabaki d’aya kusan hankalin yan matan suna kanta tunda Suka shigo hatta
fitan su little akan idanuwansu.
Babu Wanda ta kula a cikinsu dukda yadda suka so na ni’ke mata amma ta
d’aure face d’inta , tana har kar gabanta har akazo kanta , yadda suka ga gashin
kanta sai da Suka kusan sakin baki , itama ma’aikaciyar wajan sosai ta yaba da
yawan gashin Abla , cikin kware da sanin aikinsu ta fara gyarawa Abla gashinta , ko
cikakkiyar 1 hour din ma ba’ayi ba aka kammala mata , ga wani ado da akai mata da
gashin, ita kadai sai murmushi take wa kanta dan sosai kanta yayi kyau har wani
iska iska takeji a kanta . ‘Daya daga cikin matan taso kar ‘bar number Abla wai
zatayi ‘kawance da ita amma ganin babu fuska yasa ta waske amma duk da haka lokaci
zuwa lokaci tana satar kallan Abla . Bata ‘kara 10 minutes a zaune ba su little
suka dawo yanxu sun canza shiyar jikinsu , wasu kud’i prince ya d’auko a pocket
dinsa masu yawa ko irgawa be yiba ya mi’ka musu , cikin Sauri Matar takar’ba dan
kudin ya ninka kudin gyara Abla sosai.
Basu ‘bata lokaci ba suka bar saloon d’in , kai tsaye gida suka nufa ,
itama Abla d’akı ta koma tayi wanka sai bin dogon gashinta da aka gyara mata take
da kallo ga yadda suka nannad’e mata gashi sosai yayi kyau , wani baby link d’in
riga da wando ta saka sai top din ma pink sai rigar jiki da ta kasance white hatta
wandan jikinta ma pink ne , wani baby pink d’in mayafi ta d’aura akanta bayan tayi
sallar azahar d’inta, ta yi mamakin yadda period d’inta be zoba tuntuni sai yanxu
da take jin alamun kamar ya kusa zuwa . Tana sakko ‘kasa lokacin da su little
zasuci lunch, gabaki d’ayansu suka ci abin su , cikin rarrashi little ya furta “
Sis can you do me a favor plx ?” Da Sauri Abla ta jinjina masa kai dan ko me suka
ce mata indai zata iyayinsa tayi wa kanta al’kawari zatayi dan bata da kamar su “
please zaki gyara mun part din yaya ?” Yadda ta zaro eyes d’inta ne cike da tsoro
yayi saurin cewa “ yaya baya gida ai, please kinji ? Kafun ya dawo ai kin gama
gyarawa , please “, murmushi ta sakar masa tana mi’kewa tsaye “ toh bari na fara
kai wa simba abincinsa “, girgiza mata kai little yayi “ No karki damu da wannan
already an kaiwa simba abincinsa , kawai part d’in yaya zaki gyara fa” , Tom
shikenan cewar Abla, yau duk gabaki d’aya bata sanyashi cikin idanuwanta ba , jinta
take kamar wata mara lapiya dan har cikin zuciyarta take san ‘kara sanyasa cikin
idanuwanta.
Ta elevator su kahau har suwa part d’in Big boss, tun kafin ta shiga ciki
taji wani irin daddad’an sanyi da kamshin turaran da ko a mafarki tajisa ta san
mamallakin wanene , suna zuwa floor d’insa zuciyar ta cigaba da tsananta har wajan
door d’in part d’insa sa Little yasaka turn print d’insa , lokaci d’aya gabaki
d’aya ’kofar wajan ta bud’e , saurin lumshe idanu Abla Sabida wani irin abu da taji
yana tsagar mata tun daga ‘kafarta har zuwa kwakwalwarta, lokaci d’aya wani irin
dad’i ya ziyarceta duk yadda takeji d’azu sai taji komai ya tafi. Tunda Suka shigo
cikin corridor d’insa take bin ko ina da kallo dukda ba wasu abubuwane Wajan ba
amma sai da ta ‘karewa kowa ina kallo , d’akin da su little suka shigo kwana bin
baya nan ya ‘kara bud’ewa bakinshi d’auke da sallama , itama Abla sallaman tayi
lokacin da take shigowa ciki, a hankali bakinta ya fara furta “wow wow wow”Sabida
yadda taga kyan falourn , sai take ga kamar yafi ko wana falo kyau a duniya duk da
falourn ‘kasa ta sani amma sosai take bin tsarin wajan da kallo, “ let’s go” cewar
little , ‘kofar next door da ya bud’e sai ta kasa tantance Wanda ya fi kyau
tsakanin Wanda ta baro da wannan dan bil hakkı ta zama yar kauyen gaske ,abubuwa
anfani little ya d’auko mata kafun ya nuna mata ‘kofar d’akin big boss “ sorry
Little sister ! Idan kingama sai cikin bedroom d’in yaya “ murmushi ta sakar masa
da har saida dimples dinta ya lotsa “ babu komai ai “ daga haka little ya bar
falourn gabaki d’aya , ‘kugu Abla ta ri’ke Tanabin tsarin ko ina da falourn da
kallo , sosai ta bawa idan ta abinci , gashi falourn gabaki d’aya babu datti , tass
tass yake , a haka ta fara komawa falourn farko , shima saida ta bawa idanuwansa
abinci sannan ta gyara ko ina , tsabar karanbani irin nata duk abunda taga be mata
ba sai ta canza masa waje , cikin ‘kan’kanin lokaci ta canza tsarin gabaki d’aya
falourn ya fito tass da dashi kwanin burgewa , d’ayar falourn ta koma shima ta
gyara sa tasss kafun ta canza komai da ya dangance sa , shima bata d’au wani dogon
lokaci ba ta gyara sosai , wani burder turare ta kunna ga sanyin Ac da yake ratsa
ko ina , sai yake bata wani irin daddad’an ’kamshi me ‘kyatarwa .
Sanin cewa Big boss baya cikin gidan ne yasa ta nufi cikin bedroom
d’insa Kai tsaye , mamaki da shock ne ya kamata lokaci d’aya dataga dan ‘kareran
dakin Big boss da yayi biyar d’in nata , duk yadda take ganin kyaun d’akinta sai
taga wanda ya ci uwan wancan a komi , hatta kayan cikin d’akin kowa ya gansu ya san
ba ‘karamun nairace tayi kuka ba ,sai faman waigawa take tana kallan ko ina cike da
‘kauyanci, da ta juya wannan Side d’in sai ta juya wannan d’in ta kara kallansa , a
maimakon ta gyara d’akin sai ta tsaya bin ko ina da kallo, tafi tsawan 10 minutes
tana ‘karewa d’akin kallo musamman king side bed dinsa da komai na kai ya kasance
white colour , a gyare tass dashi ji take kamar ta je ta d’ane kan gadon taji
yadda laushin sa yake , ganin mayafin ta na ‘ko’karin damunta yasa ta ciresa gabaki
d’aya ,lokaci d’aya dogon tulin gashinta da ya zo mata har wajan kwankwasanta
sabida yadda yasha gyara sai roto yake dan hatta nad’in da akai mata ya warware,
top d’in rigar ta ma cireta tayi sabida taji dad’in yin aikin da kyau , yadda kayan
jikinta suka fito da ita sosai Coca Cola shape d’inta ya fito dukda Wandan jikinta
be matse ta ba , ga baiwar gashi da Allah ya bata , ga hasken fatarta da akullum
‘kara murjewa take , lokaci d’aya farinciki ya mamaye zuciyarta, cikin nishad’i ta
gyara d’akin gabaki d’aya , da karan baninta ta d’auko wani turaren da ta gani ta
geffesa a d’akin cikin ‘kan’kanin lokaci wani irin kamshi ya karad’e d’akin dukda
lokacin da ta shigo cikin d’akin a gyara yake hakan be sa da ‘kara gyaramasa ya
banbanta ba , duk Wanda yaga gyaran d’akin yasan kwararriyace ta gyara sa dan
sosai tagyarasa, ‘kofar da ta gani ta nufa acewarta zata le’ka taga yadda toilet
d’insa yake , amma tana bud’e ‘kofar bakin ya soma rawa dan sosai cikin wajan yayi
bala’in tsaruwa , gabaki d’aya sip sip ne a ciki na jerun kayan sawarsa da yayi
mugun kyau, ga ‘bangaran takalma daban, suits daban , belet da ban hatta hat d’in
da yake sawa kowa da abun sawarsa, d’akin ba ‘karamin girmane dashi ba amma duk
gabaki d’aya kayan Big boss ne a ciki masu kyau da tafiya da hankalin mutum, duk da
hakan Abla daddara ta shigo cikin d’akin yadda zata kyan sa sosai sai kace wani
Wajan saida kayan sa wa , da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai take bin kayan tana kallansu
dan gabaki d’aya hankalinta ya karkata kan hatan sawarsa , Daidai wani gaban mudibi
da yake tsa’ke da turaruka kala kala ta nufa, wani kwalbar turaran Dior ne ya d’au
hankalinta shiyasa ta d’akkosa tanasan jin kamshin sa,ba zato ba tsammani aka bud’e
kofar cikin wajan , a firgice Abla ta saki kwalbar turaren Dior d’in hannunta tana
juyowa .

MANAGE 👏👏👏👏….

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅🦅


M.W.A

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

S____28💞

Wanda ta ganine yasa lokaci d’aya ta saka ihun da ya ‘kara razanata , cike da rud’u
jikinta ya soma rawa musamman yadda taga Babu kaya a jikinsa sai farar rigar wanka
da ya saka , mamakin ganin sa ne yasa lokaci d’aya wani irin shock ya kamata har ta
kasa motsa ko da finger d’inta ne , bakinta yayi mata nauyin da bazata iya furta ko
kalma d’aya ba ,sai zuciyarta da take harbawa cikin sauri kamar zata tsaga
‘kirjinta ta fito waje , “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Kawai take maimaitawa
cikin zuciyarta “, sosai ‘kafafuwanta suka sage kamar me shirin fad’uwa ‘kas , dan
wani irin jiri jiri ne take ji kamar yake ‘ko’karin kayar da ita .
A hankali ya d’an lumshe eyes d’insa Sabida ihun da tayi har cikin kunnansa
da ya ‘Kara tunzurashi, amma ko kad’an babu me fahimtar hakan Sabida yadda face
d’insa take kullum babu fara’a sai damshi damshin ruwa da yake sakkowa tundaga kan
ba’kar sumar gashin kansa da ta sakko masa har wajan kafad’unsa .

A hankali ya nufi right side d’in d’akin , inda wasu jerun wasu white towels
suke da yawa ya nufa , guda d’aya ya d’auko , lokaci d’aya ya soma goge kansa a
hankali kamar Wanda aka saka dole , ko cikakken mintuna 3 beyiba ya fara takawa a
hankali cikin takun izzarsa kamar kullum da ya saba , cikin nutsuwa da kwarjini ya
nufi gaban mirror Inda Abla take tsaye a wajan, har Lokacin kuma be nuna yasan da
wata halitta a cikin d’akin ba , yadda taga yana nufo gaban mirror d’innan ne ya
‘kara haushina mata ciki, wani irin fitsarine ya kamata lokaci d’aya , da ‘kyar ta
iya jan zuciyarta lokacin da tayi Sauri barin gaban mudubin. Cikin rawar murya da
take shirin saka kuka soma magana a rarrabe “ Dan Allah kayi hakuri , wallahi
su’bucemun yayi dan Allah kayi hakuri ,” kamar wacce tayi magana da gunki dan
gabaki d’aya idan ka kalli face d’insa sai ka rantse babu kowa a jikinsa , ko nuni
da alamar da zai nuna yasan da mutum a cikin d’akin babu , komai cikin nutsuwa yake
yin abubuwansa , kuka ne ya zo wa Abla amma tayi saurin had’iyeshi cikin yar fa
hannu ta ‘kara maimaita wa “ Dan Allah kayi hakuri…” bata kai ga ‘Karshen maganar
da take so tayi ba taga Big boss yana ‘ko’karin kwance whiterobe d’in jikinsa .
Cikin wani irin zabura Abla ta ‘kara sakin kukan da ya saka ya d’an d’ago da kansa
dukda be kalli side d’inta ba amma yadda idanuwansa lokaci d’aya ya soma ja zaka
gane ba ‘karamin baci ransa yayi ba . Abla kuwa tunda ta ‘kara sakin ‘karar nan
bata dira a ko ina ba sai bakin ‘kofa , ganin ta samu damar barin d’akin yasa cikin
azama ta bud’e ta saka gudu da iya ‘karfinta . Tana fitowa mayafinta kawai ta
d’aura a rud’e sai Top d’in rigar ta da ta d’ora ko damu da yadda ta saka a bai bai
batayi ba , hatta mayafin kanta kawai yafawa tayi shima , cikin Sauri ta nufi
‘kofar fita daga cikin d’akin tajira a rufe gam , a fili ta furta “ na shiga uku ni
Abla , wani karan banine ya sa na shigar masa cikin d’aki , nasan yau shikenan,
shikenan na mutu na lalace “ ita kanta wasu maganganun batasan tana furta suba ,
sabida yadda ta rud’e so take Kawai taga ta fita daga cikin d’akin dan any moment
fıtsarin da take ji zai iya kwace mata . Hankalinta gabaki d’aya baya jikinta ,
password d’in bud’e d’akin take ta gwadawa amma da ta saka wani red d’in na’ura xai
bada Sauri “ No” , tun tana tunanin bud’e kofar me sauki ne har ta fashe da kuka
tana zamewa ‘kasa ganin yanxu gabaki d’aya bata da wata hanyar tsira ta sani yau me
kwatanta a wajan sa sai Allah , musamman idan ta turo simba sai taji wani saban
kukan yana ‘kara mata , yadda ta zama a ‘kasa haka ta had’e waje d’aya ta ‘kara ta
kure jikinta ga kukan da ta soma tun kafin yayi mata komai, fuskarta harta soma
komawa red colour , batasan lokacin da ta kwanta a Wajan ba , tun tana kukan kad’an
kad’an har nunfashinta ya fara canzawa alamar bacci ya d’auketa.
Almost 30 minutes Abla tana baccinta a bakin ‘kofar Wajan , a hankali ya
bud’e kofar d’akin , sanye yake cikin ba’ka’ken kayan Valentino , tundaga kan rigar
jikinsa da shape d’in wuyanta ya fito sosai kamar V har zuwa wandan jikinsa duk
ba’ka’kene, hakan ya bawa faffad’zan farin ‘kirjinsa fitowa sosai tare da sarkar
diamond din wuyansa , gabaki d’aya fuskar Big Boss babu annuri akanta hakan ya bawa
ba’kin sumar gashin kansa fitowa sosai musamman da ta sake shan wani gyara na
musamman har wani Santsi take yi. Yadda yake sanye da black d’in kaya Haka takalmin
‘kafarsa yake black colour ‘kirar Leather loafer , hakan ya bawa farar fatar
‘kafar sa fitowa kad’an, gabaki d’aya hannayensa ya saka cikin aljihu , kallo d’aya
yayi wa Abla ya d’auke kansa , mamakin aljanun yarinyar yake , tayi laifi sannan ta
soma bacci ?” Red lips d’insa ya d’an tauna kad’an cikin nutsuwar sa da izzar da
take yawo cikin jikinsa ya nufi medium size fridge dake gefe kad’an daga inda
yake , kaloli hud’u ne a jikin fridge d’in , blue d’in ciki ya danna lokaci d’aya
wani side na fridge d’in ya bude sai ga wasu manyan ruwa masu shegen sanyi da suka
fara ‘kan’Kara fitowa , Daidai saitin inda take kwance ya nufa tare da bud’e
bottle d’in bai tsaya bata lokaci a ya tuttula mata ruwan sanyin a fuska .

A firgice Abla ta bud’e idanuwanta sabida ruwan sanyin da ta ji a jikinta


lokaci d’aya kuma ga sanyin Acn da yake ratsa mata jiki, ita kanta bata san lokacin
da mayafin kanta ya zame ba , uban tulin gashinta ya fito sosai . Yadda ta gansa
tsaye akanta yayi folding hannunsa yasa ta ‘kara shiga taitayinta , zuciyar sai
bugawa take da Sauri sauri gashi tutaran da ta fasa gabaki d’aya ya ‘bata mata jiki
shiyasa ta ko ina take jin ‘kamshinsa cikin hancinta. Gabaki d’aya takasa d’ago da
fuskarta Sabida gudun had’uwa da tasa dan tasan mugun kallan tsanar da ya saba yi
mata zata gani , tsoran ta d’aya ma karya ce sai ta biya shi kud’in turaransa,
cikin kausashshiyar murya cike da natsuwarsa ya furta “ Are you mad ?yadda yayi
maganar mutum sai yayi tunanin bashi yayi taba , kanta Abla ta soma girgiza masa
dan bakinta yayi nauyin da bazata iya magana ba , ji take kamar wacce aka kulle wa
bakin da gangan dan sosai yayi mata nauyi ita ka d’auki sai faman zaro eyes d’inta
take sabida tasan bata da gaskiya . Hakan da tayi ba ‘karamun ‘kara tinzurashi tayi
ba, shiyasa cikin ‘bacin rai ya d’aga hannunsa ya wanke face d’inta da mari da har
saida taji d’igon fitsari akan pant d’inta still sai da ta d’auki wucin gadi kafun
jinta ya dawo mata Daidai sabida bala’in da take ji ta shiga , neman kukan tayi ta
rasa gabaki d’aya , cikin zafin rai ya dam’ko gashin kanta da batasan lokacin da ta
ri’ke masa hannu ba Sabida azabar zafin da ya jiyarci ganta , muryarta kamar zata
shid’e ta furta “ Dan Allah kayi hakuri, Dan Allah , Dan Annabi, yaya little ne
yasa na gyara maka d’akin bansan kana ciki ba.” Tsaki ya saki tare da hankad’ata a
maimakon ta fad’i Daidai sai ‘kugunta ya bugu, da ‘karfi ta saki ‘kara sai kuma
tayi saurin toshe bakinta dan ba’karamin buguwa ‘kugunta yayi ba , sosai ta yi
‘ko’karin had’iye kukanta dan ba ‘karamun buguwa tayi ba awajan, wani ‘karamin
cutter ya je fo mata , batare da damuwa da condition d’in da take ciki ba ya nuna
gashin kanta cikin yatsına fuska “ yanke gashin kanki” cikin azama Abla tayi saurin
waye masa idanuwanta , har ta manta da zafin da ‘kugunta yake mata , gashin da su
Little suka kashe masa kud’i sosai d’azu wajan gyara wa , tun da take ba’a ta’ba
gyara mata kai haka ba , shiyasa tun da suka dawo daga saloon d’in taji tana
‘Kaunar ganin kayanta amma yanxu lokaci d’aya yace ta yanke , kamar zatayi kuka ta
bud’e baki zata ‘kara bashi a hakuri a karo na biyu kallan da yayi mata yanxu ne
yasaka ba shiri Abla ta d’auki cutter d’in hawaye sam sun’ki tsaya wa haka ta soma
yanke uban tulin gashin kanta da hannunta . Sai da ya tabbatar da ta yanke rabi da
kwatan gashin sannan ya bar wajan yana Jan wani ‘karamin tsaki.
“ For my perfume just 1 week na baki duk inda turarena yake ki dawo mun dashi ,
if you dare to this obey , next time ba gashin kanki zance ki yanke ba , d’an ya
tsan hannunki zansa ki yanke , get lost stupid” ya ‘karasa a d’an tsawace . Cikin
sauri ta mi’ke tsaye hannunta ri’ke da dogon gashin kanta da ta yanke ,ita kanta
batasan ya akai ‘kofar ta bud’e ba , tana ganin ta fita daga cikin bedroom d’insa
ta bar part d’insa a guje .
Allah ya temaketa babu kowa a cikin falourn ,shiyasa bata tsaya ba ta wuce
bedroom d’inta , tana shiga ta jefar da mayafin hannunta , gashin hannunta da ta
ri’ke ta jefar shima tare da ‘karasawa gaban mutubi, gefen face d’inta da big boss
ya mata sosai wajan ya d’an tashi yayi ja , ga gün ta gashin kanta da ko tufkeshi
tace zatayi bazai tsayuwa ba , kamar wata ‘kamar ya rinya ta zube ‘kasa ta soma
birgima ita kad’ai ga kuka da take yi duk a lokaci d’aya .
Ya jima a ‘kasa tana kuka har saida taga sallar la’asar na ‘ko’karin wuce
ta, ta tashi tana turo unique cute lips d’inta, a haka tayo alwala tayi salla ranta
duk ba dad’i , babu abunda ya fi tsaya mata kamar yanke gashin da yasa tayi, tana
‘idar da sallan ta kwanta a kan gado kamar wata me zazzabi yau ko addua bata tsaya
tayi kwakkwara ba.

**** 8:10pm yau takai wa simba abincinsa, tunda ta je ‘kofar wajan take hararar
‘kofar kamar Itace ta sa a aske mata gashin kan nata , cikin masifa masifa Abla ta
jefa wa simba abincinsa tana binsa da wani irin harara duk da balefi ta rage
tsoransa yanxu sosai , ta jima tana harararsa kamar idanuwanta zasu fad’o ’kasa ,
sai da ta gama harararsa sannan ta ja wani ‘karamin tsaki tana barin wajan. “ yadda
yake mugu daman ai dole ya raini muguwar halitta, ga fuskarsa kamar anna kiyar da
aka buga a kwata , Allah dai zai saka mun, kuma kayi wa turaranka dan yadda ka
guntulen gashi wallahi babu wani kud’in turare da zan biya , sai shegen kyau kamar
aljani “ita kad’ai take surutunta har ta wuce cikin gida .

✨✨✨✨✨

8:35pm su Big Boss suka fito daga cikin masallacin , shi kad’ai sai faman lumshe
idanuwa yake , “ yaya bari na tafi Wajan little sister kaji?” Kansa Big Boss ya
jinjina masa kawai batare da ya bud’e bakinsa ba , gabaki d’aya sai little da
prince da kuma uncle suka koma cikin gidan banda Big Boss da Bobo . Cikin Sauri
bobo ya ‘karaso Inda yake a tsaye cike da tsokana ya furta “ UGA da kansa , our
humble Big Boss “, sau d’aya Big Boss ya kalleta ya d’auke kansa “
Haba mana my G wannan d’aure face da kayi mun kamar jira kake nayi magana ka kawo
mun naushi ? Nifa na manta when last kayi ma murmushi , just d’anyi mun ko da ya
‘Kene mana “ ko kallansa Big boss beyi ba ya furta “ leave this place “, cikin
Sauri bobo ya d’aga masa hannu “ maida wu’kar, we need to talk please , ina
Alice?”Banza Big Boss yayi masa kamar be ji shi ba”please mana answer me ko sau
d’aya ne , I know definitely His excellency ya kira ka time , and bazasu samu peace
of mind ba , idan basu ga yar suba “ , dakatar Dashi Big boss yayi cikin I don’t
care ya furta “ And so ?” Gashin kansa bobo ya ta’ba yasan halin Big boss da kafiya
me tankwarashi kam sai Allah “ nasan you’re aware of hukuncin da nasa su LG su yi
mata , nasan kasani sarai but why again kasa a d’akko maka ita ? And to a place da
babu Wanda ya sani har yanxu ? Family d’inta sun shiga damuwa “ rai a ‘bace kamar a
zuce Big Boss ya makawa Bobo wani irin kallo “su family d’in nata basu san da
ta’bin haukan kanta ba ? If you dare ka ‘karamin maganar wata so called aljana a
wajan you will see how I will maltreat her sai naga Wanda ya isa ya kwace ta ,not
even her father “, har ya juya kuma ya ‘kara kallan Bobo cikin ido “ if not baka
gida , ko prince what do you think will happen to him? Zaka d’auki blame d’in
abinda zai samu little ? Hey not even so called that people ( his parent)”, yana
kai wa ‘Karshen maganar sa ya bar wajan yasan idan ya tsaya ransa ne zai ‘baci and
every thing can happen”, Murmushi kawai bobo ya saki Daidai lokacin da wayar
hannunsa tayi flash alamar kiran waya, “CHIEF “shine sunan da ya fito kan wayar
sa , cike da girmamawa Bobo ya d’an ’kame dukda mutumin baya kallansa , kusan
mintuna biyu kafin shima ya bar wajan har lokacin kuma be kashe wayarsa ba .

****** Abla kuwa tun lokacin da su Little suka koma cikin gidan suke janta da
hira , dukda yadda take tsoran had’uwa da ita dan yanxu kam ta bashi shugaban
malintar mugaye tunda ya yanke mata gashin kan ta, duk yadda taso gudu little ya
‘ki bata wannan chance d’in dan dole ta zauna sukai hira tun bata sakewa har ta
warware gabaki d’aya, basu wani jima sosai ba suka wuce dinning dan yau fruits
kawai unclee yasa akai masa d’akinsa , shiyasa susu uku kawai sukai dinner d’insu,
suna kammalawa little yaje Zaije d’akı ya dawo, Abla tana ganin haka ta gudu d’aki
itama , tana Tuna’nın yadda zata Kai masa coffee batare da ta ganshi ba . Ita kad’a
a cikin d’akin sai faman masifa take kamar yana kallanta , lokaci zuwa lokaci kuma
bud’e drawer da ta ajje gashin nata sai kuma ta kalli Wanda yayi saura akanta , ji
take da za’a bata dama itama da sai ta aske masa gashin kansa tass , batasan
lokacin da maganar da take so tayi ya fito fili ba “ kuma wallahi kwalkwal zanyi
maka kamar kod’ad’d’an farantin Zinariyya “, ita kanta maganar da ta fad’a ta bata
dariya .
Ba ita ta sakko daga cikin d’akin ba sai wajan around 11 , lokacin gabaki
d’aya babu kowa a falourn da alama ko wannansu ya koma part d’insa , Tuna’nı Abla
ta soma akan ta tsaya ta kai masa coffee d’inne ko kuma itama tayi wucewarta dan a
gajiye take yau , haka ta cigaba da Tuna’nın mafita , daga ‘karshe sai tayi
deciding ta fara bashi coffee d’insa kar ya zuba mata kwando kwandon bala’in sa,
Tun tana jiran dawowar sa har bacci ya d’auketa a cikin falourn.
Sai wajan ‘karfe 2am Big Boss ya shigo cikin gidan , yadda yaganta kwance
akan kujera ne yasashi ya d’an ta’be lips d’insa kafun ya danna button d’in falourn
, gabaki d’aya fitilun suka d’auke ya sama sai dum light mara haske , ko takan inda
take be biba ya nufi part d’insa . karfe 3:20am fitsari ya farkar da Abla , lokaci
d’aya ‘kirjinta ya buga sabida duhun da ta gani, da ita ‘karfinta ta kwalla ihu ,
tana faman dube duben hanyar guduwa , yadda take fusge fusge kamar wacce take
‘ko’karin ficewa daga cikin haryacinta, cikin kuka ta soma maganganun da ita kanta
bata san me take cewa ba “ Duhu , Wayyo dubu banaso, banasan duhu, Wayyo Allah na ,
please wani ya temaka mun dan Allah,” bata fi mintuna biyu tana maganganu ba Abla
ta fice daga cikin hayyacinta gabaki d’aya ga kanta da ya soma sara mata sosai ,
amma dukda hakan ‘ko’karin neman hanyar barin falourn take , cikin Sauri take ta
zagaye d’akin tana ‘ko’karin guduwa amma Sabida yadda ta kasa kwantar da hankalinta
waje d’aya yasa bata lura da haske kad’an d’in da yake wajan stairs ba , burinta
taga ta fita daga Wajan shiyasa ko kula da inda take ta kawa bata yi , har ‘kafarta
ta daki wani waje tayi baya baya zata fad’i, da hannu d’aya ya ri’ke mata hannun
duk da kasancewar cikin duhune , Abla kuwa tunda taji an ri’keta ta ‘kara fashewa
da kuka tana fad’in “ please ku kunna fitula , banasan duhu dan Allah “, be furta
ko uffan ba ya kunna light d’in falourn , gabaki d’aya ta had’a gumi ga face d’inta
da ya ‘baci da hawaye sosai , tana ganin haske tana soma a jiyar zuciya , ko uffan
be ce mata ba ya juya ya bar wajan , itama cikin Sauri ta nufi d’akin tana sakin
wani ajiyar zuciyar.

WASHE GARI
Tunda akai sallar asuba Abla bata koma bacci ba sai data gyara d’akinta sosai
ta wanke toilet shima sannan tayi wanka cikin doguwar ‘bakar riga har ‘kasa , kamar
tayi kuka duk lokacin da ta kalli gashin kanta ta gansa a aske , bata tsaya ‘bata
lokaci ba yau ta kaiwa simba abinci har cikin d’akinsa , ganin be motsaba yasa ta
‘kara tura masa abincin, nan ma still yana zaune ba kamar da ba da duk lokacin da
aka kai masa abinci zai mi’ke ba , kamar wata mara gaskiya ta sand’a zuwa inda yake
, a hankali kuma kamar me rad’a ta fury “Simba ? Simba ? Baka jina ? Ka tashi ga
abincin ka nan karkasa a sakani wani punishment d’in dan Allah kaji?”ganin har
lokacin be motsaba yasa Abla ta ‘kara matsowa inda yake dan yanxu bata tsoranshi
sosai “ Simba ?” Nan ma still shiru simba be kula taba sai idanuwansa da yake
motsawa , finger d’inta d’aya ta saka ta dankwali kansa sai ta daka tsalle tayi
gefen ‘kofa, a karo na biyu still ganin be motsa ba ya ‘kara matsowa inda yake ta
kara dan gwalar kansa , sosai ta matso inda yake tana furta “ simba ? Dan Allah ko
zabura ne kayi, tsakanin da Allah kar me gidan ka yace guba na baka kaga jiya yasa
na yanke gashi yau kuma ina tunanin hanci ko baci zai sa na guntule ,”’ita kad’ai
kamar wata me iskokai ta furta “ Toh ko dai bashi da lapiya ne ? Oho Nidai nasan
ban baka guba ba dan haka wallahi bazan tsaya a hukun tani ba “ ko da zata fito
daga d’akin sai data le’ka wai sabida kar wani ya ganta tukunna ta wuce ta bar
wajan, ita kad’ai sai mita take a cikin zuciyar ta wai simba ya mayar da ita yar
iska , Sabida tana masa magana (🙄🙄Abla dole Big Boss yace kina da almatsu tsai
akanki, daman zaki yana magana ? Ko kema kinsha abunda yasha ne ?🙄🙄 Team Abla
wallahi kuyi mata fad’a dan mu ba ruwanmu duka zata sha 🤭).
Tana koma cikin gida ta tarar da uncle shi kad’ai zaune a kan kujera, cike da
girmamawa ta ‘karasa har inda yake ta gaishe dashi, “ uncle ina kwana ?” Da
murmushi akan face d’insa ya furta “ Lapiya Lou daughter kin tashi lapiya ?” Itama
Ablan face d’inta d’auke da murmushin ta furta “ Lapiya Lou Alhmdllh “, suna cikin
zamansu Bobo shima ya fito , cike da girmamawa ta gaishesa shima , a Daidai lokacin
da su little suka fito “ Sister yau har kin tashi ? Kwanda ma ki more baccinki na
yau da gobe kafun ki koma school Allah , karkizo kina school kina lumshe musu
idanuwa” cewar little , gabaki d’aya dariya suka saki Sabida abunda little ya
nufa , kallan yaya bobo little yayi “ yaya ina yaya Big Boss yake ?” Harararsa bobo
yayi kafin ya furta “ na siyar dashi , ina kasan kara ganin sa kaje kasuwa “, cikin
d’an zaro ido prince ya furta “ kai….. yaya bobo, yaya big boss din zaka siyar ? Su
kuma Victor da Anthony suna ina ?” Direct bobo ya bashi amsa da “ suma na siyar
dasu” yanxu gabaki d’aya kuma dariya suka saki jin abinda bobo yace , cikin dariya
dariya little ya furta “ ni fa yanxu ku dena sakani dariya sosai , sister zaki
yadda na dunga rakaki school ?” Da murmushi akan face d’inta ta furta “ eh “ satar
kallan inda bobo yayi yana d’an langwa’be masa “ yaya ai zaku dunga bari na ina
raka sister makaranta ko?” Da bud’ar bakin prince shima sai ya furta “ Nima yaya
please zan rakashi , tunda ba court zan dunga zuwa ba yanxu for a while “ cike da
tsokana shima uncle ya furta “ Nima zan dunga rakasu “yanxu ma kusan tare sukai
dariyar Sabida yadda sukamayar da abun joke , daga nan dinning suka nufa gabaki
d’ayan sukai breakfast, sai da suka kammala su uncle suka dawo falour shi kuma bobo
ya fita. Haka suka cigaba da hirarsu gwanin burgewa har Suka d’auko game sunayi.
12 nayi Abla ta koma d’aki ta d’auko system d’inta tana anfani dashi har
lokacin sallah yayi , tana idar wa kuma tabi
Lapiyar gado ta kwanta .

******** Tun wajen ‘karfe 12:00 motocin sojoji suke yawa a cikin Garin New York ,
ta ko ina zaka tsarin ya canza Sabida sojojin da suke shigowa cikin Garin, hatta
Chief da kansa ya shigo cikin Garin New York duk sabida Big Boss , shiyasa kowa
yake taka tsantsan.
Cikin babban office dinsa da ya gaji da had’uwa ya zauna kan wani kujera
white colour sai wani dattijon mutum da kana kallansa kasan ba ‘karamun soja bane,
ya dad’e yana fama da mugaye, cikin shigar ‘kananan kaya , sosai yake kama da LG,
fuskarsa d’auke da murmushi yake kallan Big boss da yayi mugun had’e ransa , cikin
kwantar da kai ya furta “ cool down Big Boss , she maid a mistake abunda tayi , and
she will apologized, but ya kamata kayi hakuri yanxu , okay.? “ Big boss zai yi
magana Chief yayi saurin magana “ please Son kar kace No , nasan halin ka sosai ,
just for my sake please , please ,please “, gashin kansa Big boss ya shafa kamar
bazai ce komai ba sai kuma ya furta “ it’s okay zata koma gida , but if she dare ta
‘kara saka ‘kafarta a inda nake , this time around ba Victor ko anthony ne zasu yi
mata hukunci ba , I will do it my self “ mamaki ne ya kama Chief ganin Big Boss ya
ha’kura dan kusan halinsu d’aya shima Chief a zamanınsa kusan kowa tsoran sa yaje
amma yadda akejin tsoran big boss ya wuce tunanin me tunani ,still da mamaki akan
face d’insa ya furta “ for real da gaske kake zata dawo “ kansa kad’an Big boss
yayi knodding , cikin farin ciki Chief ya mi’ke tsaye ya ‘karaso inda Big boss yake
yayi hugging d’insa , “ that’s my boy ! Thank you so much, I have to go now jirgina
ya kusa tashi, Big boss yana mi’kewa chief yayi hugging d’insa “ take care son”,
okay Kawai big boss yace masa dan kusan wani lokaci halayensu d’aya ne yanxu ne
chief yayi sanyi amma yana da mugun zafin rai duk de kai Big boss ba.

******* Abla 3 nayi ta kaiwa simba Abinci lokacin da taje bacci ma yake da alama
yaci abincin da ta kawo masa , cikin ta’be baki kamar yana jinta ta furta “ Dan
iska aushe lapiyar ‘kalau da kake ‘ko’karin d’ora mun laifi”, tana komawa cikin
gida su little sun tafi buga table tennis shiyasa itama tazauna a falour tayi game
d’inta , yau gabaki d’aya bata sanya big boss cikin idanuwanta ba , kuma bata
adduar ganin nashi yau dan gani take kamar zai sa ta yanke gashin kan nata.Gabaki
d’aya wunin ranar haka bata gansa ba sai cikin tare wajan 11 da ta kai masa
coffee , har ta ‘karacı tsayuwarta Big boss be kalli direction d’in da take ba ,
kuma a haka yadda coffee d’in yake da zafi ya salamce , kusan sau biyu tana ‘kara
had’a wani amma tafi 1 hour a tsaye , daga ‘karshe ma phone d’insa ya d’auka ya
wuce part d’insa . Zama Abla tayi kanku jera tana hararar bayansa “ na dena wahala
Yasin duk lokacin da nayi coffee baka sha ba ni zan shanye abuna , ina dalili” tana
gama shanyewa ta nufi stairs har da gwad’a yadda Big Boss yake tafiya, motsin da
taji ne yasa ta ruga a guje ta wuce d’akin.

✨✨✨✨ Yau ya kasance Sunday sosai Abla tayi bacci yau , kamar kullum yadda ta saba
time d’in kaiwa simba Abinci na yi ta kai masa , tana komawa suka cigaba da hira
da little bayan white shoes din da aka kakkawo mata da ‘karin uniform da aka kawo
mata basu babu abunda suke sai hira gwanin burgewa . Yau tun wajan 9 Abla take jin
bacci gashi daman little ya ce mata ta kwanta da wuri sabida gobe zata gara zuwa ,
har 9:30 tana zaune tana jira ko zai dawo amma gabaki d’aya be dawo ba , 10 nayi
bacci ya fi ‘karfinta shiyasa tayi wuce warta d’akin, inyaso da asuba sai tayi masa
addua Allah yasa kar yayi mata fad’a ko kuma ta dawo yayyafawa coffee d’inshi ruwan
Allah ko ya dena wannan fad’an.

*********
✨✨✨✨✨✨✨
MONDAY

IBTISSAM
https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

S____29💞

✨✨✨✨✨
MONDAY
Da wuri Abla ta tashi yau tun bayan sallar asuba da tayi ta kasa komawa , sanin
cewa Little ya fad’a mata da wuri zasu fita yasa bata zauna ba ta gyara d’akin ta
wanke toilet kamar kullum , tana yi tana duban agogon gudun kar lokaci ya ‘kure ,
ita kad’ai sai faman sakin murmushi take ga murnar fal cikin zuciyarta, wai Itace
zata fara zuwa Makaranta, Sabida zumud’i jiya bacci rabi da rabi tayi,cikin sauri
ta fito daga cikin d’akın, babu kowa sai hasken fitila , batare da damuwar komai ba
ta nufi ‘bangaran simba , yau ko tsayawa magana da shi batai ba tayi wucewarta,
tazo zata shiga cikin gida ta had’u da little da prince ,” yaya prince ina kwana ,
yaya little ina kwana ?” Kusan lokaci d’aya suka samar mata murmushi me ‘kayatarwa
kamar had’in baki kuma suka amsa “ kintashi lapiya LIL?” Da murmushi akan fuskar
Abla ta jinjina masu kanta dan yau ko murmushin face d’inta ya kasa ‘boye tsananin
farin cikin da tashiga ,” Let’s go LIL, kinsan yau akwai school ya kamata kiyi
breakfast sannan ki shirya , it’s now 6:40am , and kinga 7:35am to 7:40am zamu bar
gida , okay ?” Suna cikin tafiya Abla ta furta “ okay yaya “ a haka suka ‘karasa
cikin gidan Abla ta nufi d’akin ta dan kar suyi latti, suma su little d’akinsu suka
koma dan su shirya Sabida gabaki d’aya yau ko training bazasu yi ba Sabida
Ablansu.
Tana shigewa d’aki bata zauna ba toilet ta wuce tayi wanka, cikin mıntunan
da basu gaza 15 ba tafito daga toilet d’aure da wani pink robe na wanka , yadda
fuskarta take ta ‘kyalli mutum sai ya d’auka abu ta shafa , tana zuwa gaban mirror
ta cire abun kanta take a wajan gashinta da Big Boss yasa ta yanke ya fito , da
tuni da abunda zata tafi makaranta yau, “ Allah sai ya saka mun ai , kuma zan gyara
gashina tunda yana da saurin fitowa d’an ba’kin kuma shida Allah”, cewar Abla tana
‘karewa kan nata kallo da yake black colour sosai . Wani pink Baby oil ta d’auka
ta shafa a jikinta , duk uban mayukan da suke wajan bata shafasu ta fi shafa baby
oil d’inta , tana gamawa inda ta ajje akwatin kayan ta nufa sabida bata samu damar
bud’e su ba tun jiya , tun da ta bud’e ta kasa motsawa Sabida yadda kayan sukayi
masifar yi mata kyau tun kafun ta sanya a jikinta , yadda taga ko wanne da set
d’insa a had’e yasa ta zaro set d’aya, bayan ta mayar da jakan, underwear d’inta ta
fara sakawa kafin ta d’auko Dark blue d’in wandan da ta ciro , ita kad’ai sai bin
wanda take da kallo kamar wacca aka gwada dan sosai ya zauna a ‘kugunta, white
shirt d’in ciki ta saka itama Daidai jikinta , kamar wacce ta san kan tsarin shigar
haka tayi tokking d’inta cikin wandon, daman Abla akwai san yin dressing Allah ne
be yi ba sai yanxu, kafun ta ‘kara saka komai turare ta fesa ka d’an , d’an
‘karamun half rigar da ake d’ora wa a sama ta saka , itama Dark blue dan ta ta’ba
ganin yadda ake sawa a cikin system d’in da little ya bata .cikin Sauri ta d’auko
babbar dark Blue din rigar sama da ta sakko mata har kusan Gwiwa duk da bata
‘karasa ba sai mad’aurinta da ta d’aure . Gaban mudubi Abla ta ‘karasa , Yadda ta
ga ta koma ita kanta saida tayi mamaki , tanbayar kanta take Anya Ita ce kuwa ? Dan
ba ‘karamun had’uwa Abla tayi ba, musalta yadda kyan da tayi ma ‘bata baki ne , ga
white glowing skin d’inta da ya ‘kara haskata cikin kayan, har yanxu ta kasa
gaskatawa ita d’ince ko canza ta akayi, “ Tubarkallah Masha Allah tuf tuf” cewar
Abla bayan ta gama ‘karewa kanta kallo, white sock d’inta ta saka mara tsaho yar
guntuwa , wani medium white# hijab ta d’auko da ko ‘kirjinta be wuce ba amma sabida
yadda kayanta Suke asabe babu ta yadda shape ko wani ‘bangare na jikin Abla da ya
fito. Beret d’in kan gadon ta d’auko tana ‘kare masa kallo , batasan yadda ake sawa
ba shiyasa ta rike a hannunta kawai , ganin befi saura mintuna 10 su tafi ba ta
d’akko white shoe din da uncle ya bata , yadda Abla ta fito a cikakkiyar d’aliba
zata burgeka, ga kyau Allah ya bata, ga sanin ya kamata duk da batayi makaranta
sosai ba amma tayi na islamiyya kuma tana alfahari da hakan, a karo na ba ‘adadi ta
‘kara kallan kanta tunda babu school awajan , bata tsaya ‘bata lokaci ba ta fito
daga cikin d’akin hannunta ri’ke da beret d’in da ta kasa sakawa.
Lokacin gabaki d’aya familyn suna zaune a falour banda Big boss hatta
Bobo yana falour yau, little ne ya fara hangota, cike da wani irin excitement da
mamaki ya mi’ke tsaye yana furta “oh my God , you look so awesome, adorable,cute ,
beautiful,oho lil “ gabaki d’aya kallan direction d’in da little ya kalla suka
kalla, cikin lokaci ‘kan’kani suka fara furta “ Tubarkallah Masha Allah”, wani irin
kunya ne taji yana kamata , cikin sunkuyar da kai ta ‘karaso wajan, a hankali ta
gaishe da uncle , ya amsa mata cikin sakin fuska, gaishe da bobo tayi lokacin da
yake binta da wani irin kallo da shi kad’ai ya san ma’anarsa , cikin muryarsa ya
furta “ kinyi kyau a cikin uniform dinki” kanta a sunkuye ta saki murmushi tare da
furta “ nagode sosai yaya bobo”, turn d’insu little tayi tana kallansu cike da
murmushi da har saida dimple d’inta ya lotsa “ yaya prince ina kwana ?” Amaimakon
ya amsa shima sai ya furta “ Tubarkallah Masha Allah , Lil Sis kinga yadda kikai
kyau ? “ still murmushi tayi masa batare da ta ce komai ba ,” wait wait ! Nifa I
think ko lokacin da nake zuwa school Lil ta fini kyau a kayan makaranta ko ?” Cewar
little yana tanbayar prince , da Sauri prince bashi amsa da “ yeah ! Ni karku fara
rud’ar dani , because sister kinyi more than kyau “. Mi’kewa tsaye bobo yayi yana
kallan uncle “ uncle wad’annan yaran idan na biye musu zasu ‘bata mana lokaci , sai
mun dawo”, kansa uncle yayi knodding kafin ya d’aura da “ ku kula please “, oya
let’s go all “ cewar bobo yana nufar ‘kofar fita har lokacin beret d’inta tana
hannunta bata saka ba , suna fita wasu manya ba’ka’ken motocine kusan guda 5 sai ta
tsakiyarsu da tafi gabaki d’aya sauran motar kyau duk da kasancewarta black colour
itama , yau gabaki d’aya sojojin da zasu fita dasu ba’ka’ken kayane a jikinsu sai
ba’kin glass da yake kan fuskarsu, Robert ne ya bud’e Musu mota , little da Abla
suna back seat kamar wancan lokacin sai bobo da prince da suke middle seat, cikin
wani unique way motocin suka bar gidan, duk inda motocin nan suka gifta sai sojoji
sun sara musu, ko tsayawa traffic basa yi da motocinsu sun danno kai za a bud’e
musu hanya. 20 minutes ne ya kai su babbar makaranta HORACE MANN SCHOOL, tundaga
tsarin gidin makarantar da building d’insa mutum zai san ba ‘karamun kud’i aka
kashewa makarantar ba , makaranta ce ta Wana da wane , makaranta ce da ya’yan masu
kud’ine kawai suke da zarrar shiga makarantar Sabida yadda take da tsad’a sosai ,
sosai makarantar ta ‘kawatu ta ko ina , tunda babban gate akai scanning motocinsu
lokacin da suka shiga , babbar makaranta ce sosai me shegen girma da ‘kawatu wa ,
ga abubuwan zamani na stundent, gabaki d’aya motocin nan cikin harabar makarantar
suka danno kai lokaci d’ad’d’ai kun student zaka gani awajan da alama sun shiga
cikin class ne , Daidai wani medium building motocin su sosai parking, daga wace
wasu malamai ne kusan guda 4 , mata 2 , maza 2 sai faman sakin murmushi suke
lokacin da suka ga motocin su bobo, kallanta little yayi “ sis ya naga ban kisa
beret d’inki ba “, kamar zatayi kuka ta furta “ ban iya sawa ba “ kar’ba little
yayi ya saka mata a kanta tare da karkatar mata da ita “ haka ake sawa ok ?” Kanta
ta jinjina masa tana furta “ thank you “. “ let’s go all “ cewar bobo , face mask
little ya d’auka ya saka a face d’insa , itama Abla sawan tayi ya zamo ba’a ganin
face d’insu gabaki d’aya sai kyawawan idanuwansu masu matu’kar ‘kayatarwa, yanxu
ma Robert ne ya bud’e musu motocin , tun kafin su fito sojojin sun zaganesu gabaki
d’aya ko hangosu ba’a yi , Abla ce ‘karshen fitowa , “ welcome sir ! Welcome “
cewar wata baturiya da alama tasan da zuwansu yadda take faman gaishesu a girmame,
kansa bobo ya jinjina mata lokacin da take nuna musu hanya , haka suka hau ta
elevator suwa second floor , Robert da captain ne kawai suka biyo bayansu gabaki
d’aya ragowar sojojin suna waje sai faman zare ido suke.
Office d’in da suka shiga babban gaske ne , me shegen kyau , ga wasu set
d’in kujera Ash colour masu kyan gaske, akan kujerun suka zauna bayan Dr din ta
bawa bobo wasu files ya ciccike , yana gama wa ya mi’ka mata , cike da girmamawa ta
amsa tana ‘kara dubawa kafun ta washe masa baki “ you guys don’t have to worry ,
tunda sir bobo ya riga da yayi mun bayanin komai tuntuni , yanxu class kawai za’a
bata bayan d’an tanbayoyin da Dr Haris zai yi mata kad’an, and wanna cards d’inta
ne , ta ‘karasa tana d’aiko wasu card guda uku “ d’aya is for her meal ko me take
bu’kata zata iya kar’ba a captaria, the other one shi kuma all her necessary school
things za a bata su tundaga kan school bags , shoes, book etc and the last one na
library ne , hope you get it all “, okay thank you “ cewar bobo lokacin da ya ke
mi’kewa , sukuma su little zasu bar office d’in , face a d’an shagwa’be Abla ta
kalli little , shima gira d’aya ya d’age mata , don’t worry ok ? I will be back
soon, study hard okay ?” A hankali ta furta “okay” ganin ydda suka sha’kune yasa Dr
tace zata iya rakasu , da fara’arta tabi bayansu kuwa har wajan motocinsu, lokacin
da zasu tafi ma sai taji ba dad’i dan har fara kewarsu, saida ta ga motocin sun bar
harabar filin gabaki d’aya sannan tabi bayan Dr suka koma office d’inta , cikin
kwarewa ta dunga tanbayar Abla , sosai kuma Abla yake bata amsar duk abunda aka
tanbayetan, hakan ba ‘karamin mamaki ya saka Dr ba kuwa sabida yadda taji Abla na
amsa mata tanbayoyinta babu gargad’a ko tsoro kwata kwata a ciki, kasa shiru Dr
tayi sai da ta furta “ excellent, you’re so brilliant oh my god “babu abunda Abla
tace mata sai wasa da fingers d’inta da take har lokacin kuma bata cire face mask
d’in fuskarta ha. Kusan mintuna goma kafin a turo ‘kofar office d’in wata mata ce
me ‘kiba baturiya tashigo office d’in dukda baza’a kira ta da me ‘kiba over d’inna
ba , nuna mata Abla Dr tayi , “Mss Atem here is your new student, take good care of
her Sabida umarnine daga sama”, cikin murmushi Mss Atem ta furta “su’re Dr” ta
‘karasa tana kallan Abla “let’s go dear”, mi’kewa Abla tayi ta bi bayan Mss Atem
gabaki d’aya wani part suka nufa da an suka nufi wani da yake matsayin part d’in
student, yadda tsarin makarantar yake kamar a wata Jami’ar , ko mai cikin muhallin
da ya kamata ga flowers masu ‘kamshi ta ko ina . Ta Amaimakon su hau ta stairs , ta
elevator sukai hau, Daidai floor 2, tunda Suka shiga wajan taga gabaki d’aya tsarin
makarantar ya ‘kara birgeta , class ne da yawa a jere ga doors d’insu gabaki d’aya
babu hayaniya a wajan , idan mutum yana so zai iya tsayawa awajan ya dunga kallan
me ake yi a ‘kasa , class na biyar Mss Atem ta bud’e daga Wajan an rubuta SS 2
Diamond in a unique way , sosai mamakin hakan ya kama Abla ganin ajin da aka kawo
ta, abunda bata sanı ba Dr ce ta sa asakata’a Class d’in sabida yadda Abla take da
brain ko a university aka ajje ta zata zauna. Gabaki d’aya student d’in suna ganin
Mss Atem suka mi’ke kusan lokaci d’aya suka furta “ Good morning ma’am” alamu tayi
musu da su zauna gabaki d’aya hakan ce kuwa ta faru, ko wana student kuma zaka
ganshi da irin shigar Abla dukda da yawa daga cikinsu babu hijab a jikinsu sai
beret, nuna musu direction d’in da Abla take tayi tare da kallan Mr. Jabcon “ sir
here is another new student her name is Ibtissam Mohammed Al_taufeeq” sai kuma ta
kalli student d’in class daga roll 3 ta nuna wa Abla waje , “ you can go and have
your seat” cewar Mss Atem, a hankali Abla ta furta “ thank you “ lokacin da take
‘karasawa , wasu daga cikin class d’in sai binta suke da wani irin kallo musamman
yadda sukaga ta saka face marks ba’a ganin komai a face d’inta sai black eyebrows
d’insa da kuma kyawawan idanuwanta ash colour , mutane Bibbiyune a seat d’in sai
kujerar da aka nunawa Abla Wanda mutum d’aya kawai zaune a kujerar, itama kamar
Abla da face mask a face d’inta , sai d’ankwalin da ta saka a maimakon hijab d’in
amma itama gabaki d’aya ba’ a ganin jikinta, sai a class d’in ya dawo Daidai bayan
barin Dr Atem, a haka Mr jancon ya musu sallama sabida lokacin fitar sa daga class
d’in yayi, class d’in yayi saura student kawai kowa sai harkar gabansa yake
musamman yanda class d’in ya tara ‘yan iyayi da yawa , mi’kewa ta kusa da ita tayi
zata fita , tun kafin tace mata “excuse me wasu ‘yan mata suka zo zasu fita “ cikin
cool voice matashiyar budurwar ta furta “ Nabila we’re having another class now !”
A gadarance wacce aka kira da Nabila ta juyo , ba kowa bace face Baby da tajiyo ta
kalli budurwar sannan ta mata tsaki “ke awa karan kad’a miki?” Kallan budurwar tayi
batare da ta sake ce mata komai ba , cikin hau shin rashin tanka mata da batayi ba
baby ta ‘karaso ta fincike mask d’in fuskarta, take a Wajan kyakkyawar fuskar
Eshaal ta fito, gabaki d’aya class d’in dariya suka saki banda Abla da ko kallansu
bata yi ba, cikin rashin mutumci Baby ta furta “ can you imagine ? Wanda bata da
matsayi ko a gida shine take kokarin yin magana ? A slave ? Yarinyar da ko me na
sata dole tayi mun , stupid,” yanxu ma gabaki d’aya dariya suka she’ke da ita, inda
sabo Eshaal ta saba da kalan wula’kancinnan da Baby take mata a cikin mutane , bata
ji shakko Disgata a ko ina , yanxun ma tasan tayi hakan ne Sabida new student din
da aka kawo, kusan hakan ne ke faruwa kuwa duk lokacin da aka kawo new student sai
Baby tayi yadda zata Rabata da Eshaal dan ta ‘ki Jinin Eshaal tayi ‘kawa shiyasa
har yanxu bata da friend , ba kamar baby ba da take da friends har a cikin mazan
school d’in , d’aya daga cikin yan matanne ta kalli Baby ba kowa bace face Fanan “
please Besty ki dena irin wannan abun, na fad’a miki ba dad’i she’s your sister “,
a zabure baby ta kalleta tare da kallan Eshaal “ Wannan banzar… “ bata ‘karasa
abunda zatace ba Sabida ‘kofa da suka ji an ta’ba , cikin Sauri kowa ya koma seat
d’insa , hannu fanan ta had’awa Eshaal alamar ro’ko sabida duk cikin makarantar ita
kad’ai ce take mata magana cikin raha da mutum batare da ta ‘kyamace ta ba duk kuwa
da abunda Baby take mata , ba sau d’aya ba , ba sau biyu ba Baby taso rabasu amma
hakan ya ci tura. Wani Cristian makamı ne ya shigo class d’in ko fara’a babu a face
d’insa ya rubuta Biology kafun ya kalli kowa dake class din musamman Abla da ta
saka face mask yafi ‘kurawa ido, “ Duk Wanda bai d’auko text book dinsa ba ya fice
daga class , babu Wanda ya mi’ke sai Abla , tana ‘ko’karin fita Dr ta shigo class
din, da Sauri Wannan Cristian din ya gaisheta. School bag din Abla mi’ka mata tare
da furta “ littafan da zakiyi amfani dasu yau suna ciki ko ? “ kanta Abla ta
jinjina mata lokacin da ta koma ta zauna , Biology din ta dakko, cikin wari irin
kallan kurilla Cristian teacher dinnan ya furta “ hey get up ! And introduce your
self “ mi’kewa Abla tayi cikin cool voice dinta ta furta “ I’m Ibtissam Mohammed
Al_Taufeeq “yadda yake kallan Abla kamar wani maye yasa gabaki d’aya be kula da
abunda ta furta ba , cikin tsuke face ya furta “ meet me in my office after the
class “, okay Kawai Abla tace masa lokacin da ta koma ta zauna , a haka ya fara
koya musu biology idanuwansa kam akan Abla kamar yaje ya rungumota shiyasa Yau be
koya musu wani abu me yawa ba ya basu Assignment, yau ko question din da ya saba
tanbaya be tanbaya ba sai seat da ya samu ya zauna kamar yana nemo wani abu amma
idanuwansa ‘kam akan Abla , d’an kallan Eshaal , Abla tayi kafin ta furta mata hi ,
cike da murmushi akan Eshaal itama ta furta mata Hi d’in, kamar me tsoran magana
Abla ta furta “ please ko zan iya samun note d’in baya da aka yi ?” Fuska da fara’a
Eshaal ta amsa mata da “ Eh “ kafun ta mi’ko mata maths din ta sai wasu note din
guda biyu amma banda biology sabida assignment din da ya bayar, “ thank you “ cewar
Abla lokacin da ta kar’bi books din, duk wannan maganganun nasu akan idanuwan Baby
da haushi sosai ya kamata gani Abla daga zuwa ta har ta fara Eshaal ba kamar sauran
new student din da ake kawo wa ba , ita kad’ai sai faman hararar su take . Mr
Christian din nan da aka fi kira da Mr Mj ko da zai fita sai da ya ‘kara jaddadawa
Abla idan anfito break ta samesa a office , yana yi yana satar kallanta har ta fita
, yana fita kuma Mss Atem ta shigo class d’in itama ta d’au kesu chemistry dukda
baa fara karatun da Abla ba sai taji gabaki d’aya ta fijin dad’in class din Mss
Atem , yadda take koyarwa sosai yadda mutum zai gane da alama ta na da kirki, sun
jima kafun a fito break ko da zata fita sai da ta kalli Eshaal “ Eshaal help her
please sannan ki nuna mata abubuwan da akai bata nan okay ?” Da murmushi akan
Fuskar Eshaal ta furta “ okay ma “, Wanda ba haka Baby ta so ba ganin lokaci d’aya
Eshaal zatayi ‘kawa a nata tsarin so take Eshaal ta ‘kare rayuwarta ba ‘kama sabida
taji bakinciki da kad’ai ciki, da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai student suka fara fita
Sabida lokacin break yayi, suma su Baby lokacin da zasu fita break d’in saida ta
gama hararar su Abla kafin ta fita tana Jan wani dogon tsakin ba’kin ciki , a gogon
hannunta Eshaal ta bud’e duk da zuciyarta tana raya mata kar taje capteria Sabida
tasan irin wula’kancin da zata tarar açan musamman idan su BAD BOYS suna ciki,
ganin Abla tana ‘ko’karin d’akko book d’in karatun ta Eshaal ta kalleta fuskar da
murmushi ta furta “ Sunana Eshaal “ itama Abla murmushi ta sakar mata kafin ta
furta “ sunana Abla”, Niced to meet you !” Cewar Eshaal , “ same here “ Abla ta
bata amsa , kamar me tsoran magana Abla ta furta “ please ko zaki iya rakani office
d’in teacher din d’azu?bansan office d’in ba “ why not “ cewar Eshaal , a tare suka
fito daga class duk inda suka bi sai kallansu ake gani Eshaal yau tare da wata amma
duk da hakan basu damu ba tunda sunsan Daga yau Abla bazata kuma tarayya da ita
ba . Har office d’in Mr Mj Eshaal ta rakata amma bata shiga ciki ba ta tsaya a waje
tana addua Allah yasa ba haukan da ya saba yiwa Cristian student din makarantar zai
ce zai kwada mata ba , Abla tana shiga ta tarar shi kad’ai ne a cikin office
din yana ganin ta ya washe mata hakwara tare da nuna mata Seat d’in zama , zaman
kuwa tayi tana jiran jin me zaice Sabida gabaki d’aya she’s not comfortable , ganin
ya zauna a chair din kusa da itane yasa ta d’an ja baya kad’an ‘kara matso da chair
d’insa yayi “ you’re new student right ? Ki cire face mask dinki mana let me see
you sosai ,” Abla bata gama shiga mamakin halin saba taga yana ‘ko’karin ta’ba mata
fuska zai cire mata facemask, da Sauri ta mi’ke tsaye, dariya yayi yana kallanta “
what’s diş ? Come over here , you will get a lot of mask , and I will make you the
overall “ ya fad’a yana ri’ko hannunta , Abla bata san lokacin da ta d’aga hannu ta
tsinka masa mari ba , harta fara tara kwalla a idanuwanta sabida ta kaici, ko kuma
kallansa batayi ba ta bar office d’in, ran Mr Mj ba ‘karamin ‘baci yayi ba , babu
student d’in da ya ta’ba gigin marinsa kamar yadda Abla tayi , sosai ransa ya ‘baci
, amma da ya tuno yadda yake sha’awarta sai ya saki wani murmushi da shi kad’ai
yasan ma’anarsa “ I most get you no matter , kin burgeni and I will teach you a
lesson marina da kikayi” ya ‘karasa yana shafa gaban wandansa kafun ya saki wani
yan iskar dariya shikad’ai. Abla tana fitowa ta tarar da Eshaal na jiran ta , itama
Eshaal tunda taga reaction d’in Abla tasan Mr Mj yayi mata halin nasa ne , a
hankali Eshaal ya furta “ kiyi hakuri haka halin Mr Mj yake sai kinyi hakuri da
halinsa kinji ?” Kanta Abla ta jinjina mata kafun ta furta “ thank you “ ganin
lokaci na ‘ko’karin wuce wane Eshaal ta ja ta zuwa capterian makaranta, yadda yake
da kyau da tsari mutum sai ya d’auka wani Restaurant d’in ne ga chairs a Wajan da
ban da ban wasu student na kai wasu kuma karban abunda zasu ci, card d’insu suka
nuna lokacin da zasu shiga, tunda Suka shiga nan ma kusan gabaki d’aya student din
zuba musu ido sukai ganin yau Eshaal da wata dan Baby har ta riga ta had’asu acikin
restaurant d’in, Abincinsu sukai order dukda ma ‘karfin yi Eshaal ce tayi musu
sabida ita bata san kan abincin su ba , gashi duk ta ‘ki sakewa Sabida yadda taga
ana binsu da kallo, can nesa da student suka koma suka zauna sai a lokacin Abla ta
cire facemask dinta , kyakkyawar fuskar Abla ta fito sosai , d’an kallanta Eshaal
tayi kafin ta furta “ you’re so beautiful , da alama shiyasa kika kulle face
d’inki” murmushi Abla tayi mata da har saida jerarrun hakwaranta suka fito kad’an ,
a haka suka soma cin abincin duk da Abla ba wani ci take ba Sabida yadda taka an
‘kara zuba musu ido musamman yadda aka ga ta cire mask d’in fuskarta , suna cikin
ci aka bud’e kofar da karfi gabaki d’aya d’ago wa akai aka kalli ‘kofa banda Abla ,
daman ita Eshaal ta san ko su wanene “BAD BOYS , BAD BOYS , BAD BOYS” shine sunan
da student suke faman fad’i lokaci guda , wasu mazane guda biyar guda biyun cikinsu
zakaga turawane sabida yadda skin din su yayi yayawur d’ayar daga cikin su kuma
ba’kar fatane sai wasu guda biyu da kallo d’aya idan kayi musu zakagane fulanine
amma gabaki d’ayansu ko wanne da kitso akansa ga wani zazzago da wando da sukayi,
d’aya daga cikinsu da ya fi kowa d’aura fuska ya soma binsu da kallo d’aya bayan
d’aya dan duk Wanda ya ke a makarantar yasan su wanene BAD BOYS dan basu da mutunci
ko kad’ai ga rashin kunya da take d’awainiya dasu , duk Wanda suka ga dama su taka
sau uke
kenan suna repeating Sabida wasa da suka sa da rashin mutum ci a cikinsu kamar
kamar be , Baby ce ta shigo wajan daman friends dinta ne tana ganin su tayi shewa
tare da furta “ BAD BOYS “ bafullatanin cikin sune ya mi’ka mata hannu suka tafa,
daman ita ce ta kirasu da ido ta nuna musu inda su Abla suke , tunda ya kai
idanuwansa wajan ya kasa d’aukewa sabida lokaci d’aya wani kibiyar soyayyar Abla ta
shiga cikin zuciyar sa kowa nutsuwa yayi yaga me BAD BOYS zasuyiwa su Eshaal dan ba
sau d’aya ba ba sau biyu ba suna ciwa Eshaal mutumci a bainar nas, a gadarance ya
kalli Eshaal tare da furta “ ke !” Dan d’agowa Eshaal tayi ta kallesu, Abla ya nuna
mata cikin bada umarni ya furta “ kawo mun wannan yarinyar nan wajan “ kallan Abla
tayi kad’an kafun ta furta “ yana kiranki “ banza Abla tayi mata , a tausashe
Eshaal ta ‘kara furta “ yana miki magana plx” kallanta Abla tayi kafun ta furta “
kin gama cin abin cinne?” Da Sauri Eshaal ta d’aga mata kai dan batasan Abla ta
shiga Sabgar BAD BOYS, mi’kewa sukai kowa yayi tunanin Abla wajan su Bad boys din
zata har Eshaal kuwa, ganin tayi gefe zata wuce ne yasa wanda yayi wa Eshaal magana
ya sha gabanta “ke har wacce ana miki magana zaki share mutum “ banza tayi masa
zata wuce ya ‘kara shan gabanta Sabida yadda ransa ya ‘baci yasa ya d’aga hannu ya
tsinka mata mari gabaki d’aya wajan ihu ya d’auka , rai a ‘bace Abla ta d’aga
hannunta itama ta wanka masa mari gabaki d’aya Wajan tsit yayi Sabida mamakin ta ,
be gama shiga mamakin marin da tayi masa ba ta ‘kar d’aga hannu ta tsinka masa Mari
saida ta yi masa maruka uku kafun ta kallesa rai a’bace tayi wucewarta , Eshaal ma
da Sauri ta bi bayan ta suka koma class , ga mugun mamakin da ta bar kowa da shi
ganin ta ta’bo me gayyan BAD BOYS, suna komawa class sauran teachers din sune suka
shish shigo , yan class din lokaci zuwa lokaci suna kallan Abla hatta baby da take
sakin wani murmushin mugunta. Lokacin short break nayi ita da Eshaal basu fita ba ,
sbida karatun da ta fara koya mata . ‘Karfe 1:45pm aka tashesu gabaki d’aya , tare
suka fito da Eshaal ta na fitowa ta hango Little sanye da face mask shima , sallama
tayi wa Eshall ta nufi wajan sa Sabida gabaki d’aya motocin suna waje ya hana su
shigo sai mota d’aya , yana ganin ta ya sakar mata murmushi “ weldone Lil da alama
kin gaji sosia “ sosai ma kuwa “ cewar Abla dariya Little yayi mata “ with time
zaki saba let’s go” da haka suka shiga cikin mota saida da suka hau babban titi
sannan motocinsu suka shiga Gana da bayansu har suka ‘karasa cikin gida , tana
shiga d’aki ta wuce tayi sallah sannan tayi wanka dan ta huta, 2:15pm little ya
kira ta cin abinci tana gama ci ta koma d’aki ta kwanta sai around 3 ta farka da
Sauri ta fito daga cikin d’akin dan gabaki d’aya ta manta da kaiwa simba Abinci,
shaf shaf ta kai masa ta dawo falourn lokacin su little suna falour , itama a
falourn ta zauna suka ci gaba da irarsu gwanin burgewa har ta d’auko assignment
d’in tayi suma suna mata bayanın wanda akai bata da ta note d’in Eshaal.

9:30pm suna zaune a falourn gabaki d’ayansu suka ji Horn dirar motocin Big boss
kusan lokaci d’aya suka dawo da bobo dan atare suka shigo cikin falourn , “ Welcome
yaya” kansa Big boss ya d’anyi knodding , shima Bobo ya amsa masa da baki , prince
ma hakance ta kasan ce a nashi ‘bangaran, Abla ma sannu da zuwa tayi musu amma ko
kallanta Big boss beyi ba balantana ta saka ran zai amsa mata , a hankali Big Boss
ya d’ago da eyes dinsa yana lumshe wa Uncle , shima uncle cike da tsokana ya lumshe
masa nasa idanuwan ya lura yau ‘yan mulkine akansa , be zauna a falourn ba yayi
wucewarsa , suma sun fahimci yana bu’katar hutawa , yana tafiya little ya nufi
wajan coffee maker d’insu ya had’a masa coffee me zafin gaske , yana fitowa ya
kalli Abla , “Lil please can you help me ? Ki kaiwa yaya coffee d’insa da alama yau
yana bu’katar shan coffee din, tuna warning din da yayi mata tayi wani Wayu ta
had’iye a ma’koshinta gashi bazata iya Musawa little ba ganin Uncle na zaune a
falourn, ‘karfin hali Kawai tayi ta amsa masa tare da karban coffee d’in, har zata
wuce ya fad’a mata pin d’in ’kofarsa ganin babu turn print d’inta a jiki, tana
tafiya zuciyarta na dukan uku uku Sabida batasan tayi abunda zai sa ya hukuntata,
kafun ta shiga cikin d’akın ma sai da tayi adduar kariya sannan ta saka pin ta
shiga , Wajan sanyi sosai , kar tsaye falournsa na biyu ta nufa zata ajje sai taga
rashin kyautawar hakan karya zo nagani ba, cikin ‘karfin hali tayi knocking
‘kofar , shiru babu amsa , a karo na biyu ta ‘kara knocking nan ma still ba’a amsa
ba , bakinta d’auke da Bismillar ta saka hannu zata bud’e ’kofar Daidai lokacin da
shima Big boss ya saka hannu a kan handle d’in , d’ayan hannunsa kuma akan shirt
d’insa da ya d’an bud’e, lokacin da Abla ta tura ‘kofar alokacin shima ya janyo
‘kofar baya kusan lokaci d’aya sukai karo da juna , coffee d’in hannunta me shegen
zafi ya zuba a white shirt d’insa , ganin ‘barnan da tayi masa yasa lokaci d’aya
bata san lokacin da cup din ya su’buce a hannunta ba gabaki d’aya ya faffashe a
‘kasa….

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____30💞
Kallan white shirt d’insa da ta ‘bata tayi kafun ta sun kuyar da kanta ‘kasa zuwa
inda kofin ya zube,a hankali ta saci kallansa ganin wani irin mugun kallo da yake
jefa mata yasa tayi saurin sunkuyar da kanta ‘kasa , Tuna’nın hanyar guduwa kawai
take dan Allah na gani bazata bari ya ‘kara yanke mata gashi ba dan ya ga tafisa
gashi. Yadda yake binta da wani irin kallo rai a’bace shi kad’ai yasan irin
hukuncin da zaiyi mata, zai bud’e baki Abla tayi saurin taran numfashinsa “ Dan
Allah kayi hakuri , Dan Allah Dan Annabi , Dan Darajar Annabi muhammad S.A.W”lumshe
eyes d’insa yayi kad’an batare da ya bud’e su ba ya furta “ leave this place “ da
Sauri Abla ta juya zata koma cikin d’an zafi zafi ya furta “ Are you mad ?wa ze
gyara miki inda kika ‘bata ?” Da Sauri ta furta “ kayi hakuri” inda kayan gyaran
suke ta nufa cikin ‘kan’kanin lokaci ta gyara Inda ta ‘bata d’in, ta juya zata
kuma fita ya d’ago da narkakkun eyes d’insa , a hankali ya ‘karasa ‘balle button
d’in rigar jikinsa , cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa sabida yadda taga
jikinta yana ‘ko’karin d’aukar ruwa amma duk da hakan ta danne gudun karyace zai
mata wata mugun tar, bata ‘kara sa Tuna’nın taba ya jefo mata white shirt d’insa da
sai faman tashin ‘kamshin turaransa take , cikin kakkausar murya ya bud’e bakinsa “
just 20 minutes na baki, I need my shirt, idan kin isa ki ‘kara one minutes ,your
time start “, da Sauri ta juya ta bar wajan , guntun tsaki yaja tare da koma cikin
bedroom d’insa . Abla tun kafin ta sakko take Tuna’nın yadda zatayi da rigar Big
boss kar su Little su ganta dashi , bata na wata hanyar bayan ta nannad’eta ta tusa
cikin wular ta , sai yayi kamar gashinta, tana sauka little ya furta “ LIL kin kai
masa ?”Fuskarta cike da murmushi ta furta “ eh na kai masa “, thank you so much ,
little ya bata amsa yana mi’kewa ,” uncle good Night, yaya bobo good night , and my
Lil sis good night too, kema ya kamata ki kwanta da wuri Sabida school d’in ki
kinji?” Tana wasa da hannu ta furta insha Allah, gashi ta rasa ta yadda zata wuce
d’akin Sabida lokacin da ya bata, shima prince sallama yayi musu suka nufi part
d’insu shida little . Saida taga sun ‘bace wa ganinta tukunna itama tayi wa su Bobo
sai da safe ta wuce d’inta , a nutse take tafiya abunta amma zuciyarta hasaso mana
lokacin ta kawai yake , tana ganin ta zo daidai wajan d’akin da ta bar Inda su Bobo
suke ta ruga a guje ta nufi cikin bedroom d’inta , Tana shiga cikin d’aki direct
toilet ta wuce , cikin sauri ta tuttulawa rigar omo ta soma wanketa, kusan sai data
d’auki 7 minutes tana dirjarta gudun kar yace mata be fita ba , tana gamawa ta
d’orayeta tass ta tsaneta yadda zata saurin bushewa . Tafi ‘karfin 10 minutes tana
jira rigar ta bushe amma sabida sanyin Ac d’akin ta ko kad’an bata butsewa sai
sanyi da ta ‘kara d’auka , ganin 20 minutes d’in da ya bata na gaf da ciki yasa
tayi shahada kawai ta d’auko rigarta ta fito, babu kowa a falourn, sosai taji
dad’in hakan kuma , ko ba komai bazasu tanbayeta ba , gudun kar wani ya ganta yasa
ta ‘kara komawa part d’insa da sauri dan ta kai masa rigar tasa,Amma tana shiga ta
tarar da baya cikin falourn farko, d’ayan falourn ta nufa nan ma still baya ciki,
kamar ta ‘kara knocking d’in d’akin sa sai kuma ta tuna abunda ta faru d’azu,
tunanin mafita kawai ta somayi, ko ta ajje masa rigar idan ya fito ya gani ko kuma
idan ya fito ta bashi, da wannan idea d’in ta juya batare da ta ajje masa rigarba
ta nufi part d’inta itama . Shaf shaf tayi wanka cikin ‘kan’kanin lokaci ta shirya
cikin kayan baccinta , rigarsa da ta ajje kan kujerar mirror d’in ta janyo ba tare
da ta kalleta ba , lokaci d’aya taji sautin ket alamar yagewar abu , cikin tsoro ta
kalli rigar hannunta , sai ganin rigar tayi a yage alamar yanzunnan ta yage , kamar
zatayi kuka ta furta “ Nashigasu Ni Abla yanxu ya zanyi ? Gashi na ‘barka masa riga
again , innalillahi, wallahi nasan idan na fad’a maka kuli kulin kubra zaka mayar
dani , sai kayi hakuri wallahi Allah yayi wa rigarka rasuwa “ tana kai karshen
maganar ta nunke rigar tare da saka ta daga can ‘kasan kayanta, daman ta sani kuma
ta zama matacciya idan ta bari suka had’u shiyasa ko da zata kwanta saida ta kulle
door dinta tukun ta kwanta , bata jima ba bacci ya d’auketa.

*WASHE GARI*
Da sassafe ta tashi tun bayan kiran sallar asuba da tayi bata koma ba , gashi
tsoran fita take gudun kar tsautsayi yasa ta had’u da Big boss shiyasa ta ‘ki
fitowa daga cikin d’akin har saida ta shirya cikin uniform d’inta da sukayi bala’in
yi mata kyau ba kad’an ba , 7:28am shine abunda tagani a jikin bangon d’akin ,
cikin sauri ta d’auki school bag d’inta tayi shahada ta fito daga cikin d’akin
cikin sand’a tana yi tana waiwaye bayanta , kusan karo ta kusa ci da little da yake
‘ko’karin zuwa d’akinta shima ganin bata fito ba har lokacin, bakinta har rawa yake
lokacin da ta gansa dan ta d’an ji tsoran hakan , da ‘kyar bakinta ya iya bud’ewa “
yaya little ina kwana ?” Kallanta little yayi da mamaki kafun ya amsa mata gaisuwar
tata “ LILI are you okay ?” Da sauri Abla ta jinjina masa kai alamar eh , shiru
kawai yayi kamar me tunani kafun ya ‘kara furta “ are you sure?”cikin sakin
‘karamin ya’ke kamar murmushi ta ‘kara furta “ yes Dagaske nake lapiya ta ‘kalau “
sai kuma ta wayance da “ naga time ya tafine gashi ban kaiwa simba abinci ba “ cike
da gamsuwa little ya furta “ you dont have to worry your self , Simba baya gidan
nan , sun fita tun safe da yaya Big Boss “sai a lokacin ta saki wani ajiya zuciya
ganin baya cikin gidan gabaki d’aya , da kwata kwata ba a sake take ba ganin
bayanan ne yasa hankalinta ya d’an kwanta “lets go”cewar little yana katse mata
tunanin da ta d’an fad’a , a haka suka sauka ‘kasan lokacin har breakfast d’inta
prince ya shirya mata , da kansa yayi serving d’inta abinci, ganin lokaci na
‘ko’karin wuce wa yau batare da bobo zasu tafi ba shiyasa basu jirashi ba suka wuce
cikin jerun motoci guda uku da zasu rakasu cikin makaranta , ba su d’au dogon
lokaci ba suka ‘karasa school d’in nasu, ragowar motocin gabaki d’aya a waje suka
tsaya hakan kuwa ba ‘karamun dad’i yayiwa Abla ba, shima tun kafin a ‘karasa
haraban school d’in tace a sauketa , prince cikin tsokana ya furta “ kingado halin
little kenan shima bayaso yaga anshigar dashi da mota lokacin da yake school “,
murmushi Abla ta saki lokacin da aka sauketa , “ wait “ cewar little , wani medium
box me kyau ya mi’ka mata “ take this chocolate d’in school d’inki ne , in kin koma
gida zan d’ebo miki sauran okay? “ Abla da shegen san za’ki shiyasa batayi masa
musu ba ta ‘karba” thank you yaya little “. You are welcome lil ya kamata ki shiga
kar a fara class babu ke , duk wanda ya nemi takura miki idan kin dawo just tell me
okay?” Kanta ta jinjina masa kafun tayi musu waving tana nufar cikin makaranta ,
sai da ta shiga asalin cikin makarantar sannan ta fara had’uwa da student d’ad’d’ai
ku , ta fuskanci inda take kamar ‘bangaran junior ne da kuma ‘bangaran seniors suma
, ta gane building din da class dinsu yake shiyasa kai tsaye ta nufi can , tun tana
tafiya ta fuskanci sai kallanta ake amma babu wanda ta d’ago kai ta kalla ko ta
nuna alamar tasan da wanzuwar su , harta ‘karasa cikin class d’insu , bakinta
d’auke da sallama a hankali, idan ba kallan bakin ta kayi bama bazaka d’auka tayi
sallamar ba dan gani take kamar babu musulmai a cikin a jin, tun da ta shigo gabaki
d’aya yan class d’in suka zuba mata ido dan kowa ya samu labarin tsinkawa Mai dala
mari da tayi , tun safe gangs din Bad boys suka shigo cikin class d’in amma basu
sameta , Eshaal ma tana ganinta ta saki ajiyar zuciya tana sakar mata murmushi
sosai taji dad’in rashin had’uwar su da Bad Boys dan yadda suka shigo cikin class
d’in komai zai iya faruwa , gashi gabaki d’aya duk cikin su yaran manyan ‘kasane
shiyasa suke iskancinsu san ransu, bata manta da warning din da sukai mata ba akan
idan suka ga Abla sai sun wula’kanta taba, shiyasa take ta zuba ido taga ta inda
zata shigo . A seat d’inta Abla ta zauna tana sakar wa Eshaal murmushi dan tun
shigowar Abla murmushin face d’inta ya ‘ki ‘boyuwa itama “ Hey !” Cewar Eshaal , a
maimakon itama Ablan tace mata hey sai ta furta “ ya kike?” Alhamdulilah Eshaal ta
furta mata , daga nan babu wanda ya sake magana a cikinsu sai littattafan su da
suke dubawa , duk wannan abun akan idan Baby da bakin ciki ya cika mata zuciya ,
ita kad’ai sai faman knodding kanta take , kallan direction din Abla fanan tayi ,
tasan abunda zata fad’awa sai ya ‘batawa Baby rai amma duk da hakan halinsu ba
d’aya bane fanan bata da wula’kanci ko neman rigima kamar Baby, shiyasa duk cikin
makaranta babu me jure halin Baby sai faman “ besty kinsa tun lokacin da naga new
student dincan kawai naji ta burgeni, shes so cute “, dogon tsakin da baby ta jane
ya hana fanan ‘karasa maganar ta , a wulakance tana hararanta ta furta “ sai kije
ki kwad’ata kicinye “ ta karasa tana ‘kara jawa fanan tsaki, d’an murmushi kawai
fanan tayi mata dan wani lokaci idan baby tayi mata abu kawai tana mata shiru ne
sabida bata fisan tension ba , amma ita kanta ta gaji da halayen Baby, babu wanda
ya ‘kara kula juna a cikin su musamman Baby da time to time tana jan tsaki ko ta
harari Fanan , amma hakan be hana fanan sakin murmushi kawai. Gabaki
d’aya Abla da Eshaal sunji maganganun su kasan cewar da hausa sukai maganar amma
babu wanda ya nuna alamar hakan daga ita har Eshaal dake side d’insu . Suna zaune
teacher din English ta shigo musu , cikin tsantsan kwarewa Mss Ema ta saka Abla ta
gabatar da kanta ganinta new student kafun ta fara teaching d’insu, ba ‘karamun
enjoying class din Abla tayi ba ganin yadda take fahimtar abunda ake koya musu ,
koda Mss Ema ta gama tanbaya ta soma yiwa Class members din , ‘ka ida duk teacher
din da zatayi tanbaya zata nuna wanda zai amsa mata ne , yanxu Abla ta fara
nunawa , cikin American English d’in da zai bawa kowa mamaki Abla ta amsa mata
questions dinta , duk da haka Mss Ema tayi mamakin kwazon Abla shiyasa ta ‘kara
mata wani question din, still Abla ta amsa mata , wata dabara ne ya fad’ow Mss
Ema , question din farko da ta farayiwa Abla shi ta ‘kara yi mata amma ta wani
salon daban ga mamakinta sai gani tayi Abla ta amsa mata ,lokaci d’aya Mss Ema ta
soma ta fa mata kafun ta saka gabaki d’aya class din su tafa mata , babu abunda
take cewa sai “ bravo my girl “, maida akalar tanbayarta tayi zuwa Eshaal , nan ma
Eshaal amsa mata tayi dan ko Mss Ema bata yi mamakin Eshaal ba dan kusan itace top
best a cikin class d’in sai yanxu kuma da ta ga Abla, tana fita teacher d’in
Further maths ya shigo masu, farin bature ne balefi yana da kyau gashi ba wani
babba bane dan bazai wuce 29 years ba , koma a hankali yake yinsa amma fuskarsa
babu fara’a , lokaci d’aya gabaki d’aya class din suka nutsu dan sosai gabaki d’aya
set din suke tsoran Dr Adams, dan babu ruwansa da kowa a cikin makaranta ga brain
shima da Allah ya basa , gabaki d’aya kusan lokaci d’aya members din class d’in
suka gaishesa , idanuwansa dake sanye da wani white glass be sauka akan kowa ba sai
akan Abla da kanta yake sunkuye, sau biyu yana kai idanuwansa direction d’inta
kafun cikin basarwa ya furta “ muna da new student ne ?” Cikin sauri suka amsa masa
da “ yes sir “, kallan Abla da kanta yake a du’ke yayi kafun ya furta “ cant you
introduce your self ?” d’an d’agowa Abla tayi ta kallesa sau d’aya kafun ta mike
tsaye cikin daddad’an turan cinta ta furta “ My Name is Ibtissam Mohammed
Al_taufeeq “ ( kamar yadda Mss Atem ta fad’a musu jiya )” ,sai da ya nanata
Mohammed Taufeeq cikin ransa kafun ya furta “ you can seat down “ cewar Dr Adams,
ba musu ta zauna, sai a lokacin ya fara yi musu introduction din Binary
operation ,sai da yayi musu bayani sosai yadda zasu gane sannan ya fara teaching
d’insu topic din cikin zallan kwarewa da sanin aikinsa , shima da ya gama sai da ya
tanbayi students questions ciki kuwa harda Abla , itama yadda yayi musu bayanın
haka ta zauna tayi masa ba gargada ba kad’an ba yayi mamakinta , “ Good “ cewar Dr
Adam’s kafun ya bar class d’in, third class d’insu kuma Bio chemistry shine teacher
d’insu na mijine , still saida Abla tayi introducing kanta , lokacin break nayi
kowa ya fita banda Abla da arwa sai kuma fanan da basu fita tare da Baby ba , dan
ko kallanta baby batayi ba tayi wucewarta , Seat d’insu fanan ta ‘karaso kafun ta
mi’kawa Abla hand dinta alamar su gaisa , babu musu kuwa Abla itama ta mi’ka mata
nata ,” sunana Fanan”, ni kuma Ibtissam” cewar Abla , murmushi fanan tayi mata “
Nice name , zamu iya zama friends ai ko?” Itama Abla da murmushi akan face d’inta
ta furta “ why not “, Ni kuma fa ?” Cewar Eshaal , a tare suka had’a baki wajan
furta “ kema haka” lokaci d’aya kuma suma suka saki dariyar maganarsu “Lokacin
break ya kusa ‘karewa ki taso mu tafi Capteria” ba musu suka mike gabaki d’aya gasu
kyawawa gabaki d’ayansu babu mummuna, a tare suka nufi capteria gwanin burgewa ,
duk inda suka wuce sai an kallesu, har suka shiga cikin capterian kuwa kallansu ake
, kamar jiya Çan nesa suka zauna yau su uku, fanan , Abla , sai Eshaal, suna cikin
cin abincinsu aka danno ‘kofar wajan da ‘karfi, lokaci d’aya Wajan ya kara dauka
sowa daman tun d’azu Bad Boys suke jiran zuwan Abla , itama Baby tare suka shigo da
Bad Boys, ganin Fanan a wajan su Abla yasa ranta ya ‘kara ‘bacı ga wani haushin
fanan da take ji, kujera d’aya daga cikin gang d’in Bad Boys ya janyowa Mai dala ,
cikin wani babba sarwa ya zauna tare da kallan direction d’in Abla , cikin jijji da
kai ya d’aga murya akan ta zo ta tsugunna ta bashi hakuri, idan ba haka ba ya sa’ba
mata , kallan baka da hankali fanan ta jefa masa dan ba ta tsoransu kwata kwata ,
tana d’aga masa ‘kafa ne shima Sabida ala’kar da ke tsakaninsu,” bakiji abunda nace
ba ?” Cewar Mai dala , kamar yayi magana da dutse haka Abla ta mayar dashi,
abincinta take ci hankali kwance , ran Mai dala ba ‘karamin ‘baci yayi ba shiyasa
ya bawa d’aya daga cikinsu ya d’akko masa Abla, dariyar shakiyanci yasaka ya nufi
inda Abla take , a zuciye fanan ta kallesa “ baka da hankali ? Sai kuma ka ta’bata”
girgiza mata kai gayen yayi “ ah ah fa fanan kinsa ke ta gida ce muna d’ağa miki
‘kafa sabida eh ke Family Mai dala ce amma fa ki kiyaye “ zai ‘kara
saka hannu zai ta’ba Abla fanan a zuciye ta furta “ wallahi idan kuka kuskura kuka
ta’bata , sai na kira NANI na fad’a mata “ jiyo inda MAI DALA yake yayi , cikin
ta’be baki MAI DALA ya furta “ share ta yi abunda na saka “. Hannu kuwa ya saka
zai ta ‘bata yaji saukar mari a kumatu biyunsa sai sautin Tassss kawai da suka ji,
shi kansa Wanda aka mara saida ya saki ‘kara sabida zafin marin da yaji , ba kowa
bace face fanan da Abla , fanan ta Maresa a left kuma tunsa , Abla kuma ta Maresa a
‘bangaran daman da , cikin harara Fanan ta kalli Mai Dala “ ka shirya amsa kiran
Nani” daga nan ta kalli su Eshaal akan su zo su koma class , babu musu kuwa suka
bar capterian , Bad boys zasu bisu Mai d’aya yayi saurin da katar dasu “ karku bisu
, fanan ta shiga cikin wasan , nasan zata iya kiran BiiBii kuma ba abunda zai hana
yazo , let’s go” .
Suna shiga cikin class Fanan ta basu hakuri, babu Wanda ya nuna wani abu sai
ma chocolate d’in da Little ya bata ta fito musu da shi , kamar sun dad’e da sanin
juna suka dunga hirar su wanda kusan gabaki d’aya hirar akan further maths ne da
suk fara koyawa Abla Wanda akayi a baya . Lokacin da yan class suka fara shigo wa ,
duk Wanda ya shigo sai ya kalli su Abla ko kiji suna kuskus , a teacher ya shigo
class suka fara , a haka idan teacher ya fita wani zai shigo har lokacin short
break , yau ma basu fita ba suna class har aka dawo sauran teachers din suka
shigo, lokacin Tashi nayi duk suka fito. A lokacin anzo d’aukar Abla , sallama tayi
musu ta ‘karasa Wajan little da yake sanye da black p-cap sai wani black mask don
fuskarsa , tana zuwa Daidai inda yake ta d’an ta’ba kafad’arsa sai kuma ta sun kuya
‘kasa , dube dube ya fara Abla ta saka masa dariya , sai a lokacin ya kula da ita “
Lil ni kika tsoratar ko ?Dont worry zan rama , let’s go home “ a haka suka shiga
mota suna bar harabar school sai da suka fita babban titi sannan motocin sojojinsu
sukai musu combo har gida .

Yau Big Boss baya cikin gidan shiyasa ta sake sosai , lokacin kai abincin simba
nayi ta kai masa , tana dawowa suka d’anyi karatu da yaya little, sannan ya d’akko
musu game d’insu suka dunga yi , ciki kuwa harda Abla akeyin game d’in .
Tun da rana take ji kamar ta kusa yin al’ada sabida d’an murd’awa da
cikinta yake yi kad’an amma bata kawo suwansa yau ba , har ta idar da sallama ta
fara jin cikinta yana murd’a mata kad’an kad’an, lokacin da taje wanka ne taka
zuwan al’adanta ga ciwan maranta da ya fara tsanta mata , a daddafe ta samu ta saka
pad kafin ta shirya ko kwakw kwaran tsayuwa batayi sosai ga ciwan ‘kafarta da shima
yake mata zafi sosai , tun tana iya küre wa har ta kwanta a ‘kasa kan tiles tana
musu ‘musu ita kad’ai , murd’awar da cikinta yayi mata da ‘karfi ne yasa ta fashe
da kuka , cikin ‘kan’kanin lokaci ta nemi ficewa daga cikin hayyacinta, hannunta
dafe da cikin ta sai faman jujjuya face d’inta da ta ji’ke da gumi take , tun tana
iya nishi har ta ‘kara tsanta kukan ta , ko iya bud’e idanuwanta batayi Sabida
azaba, bakajin motsin komai sai kukan Abla da take yi da iya ‘karfinta, tanayi tana
birgima a cikin d’akin, knocking d’in ’kofar d’akın akai kusan sau biyu, Abla tana
ji amma babu damar ta bud’e bakinta Sabida yadda ta galabaita sosai, Little ne ya
turo ‘kofar, yadda yaga Abla ne yayi matu’kar tayar masa da hankali da Sauri ya
‘karasa inda take yana tanbayar ta meke damunta amma ina kwata kwata Abla batasan
ma me yake cewa ba, fahimtar hakan ne yasa ya fita daga cikin d’akın a guje , Big
boss ne zaune Kawai a falourn sai uncle da prince , yau bobo baya cikin d’akin , a
rud’e little ya ‘karaso Inda yake “ yaya !” Yadda yaga face d’insa tayi ja ne yasa
ya d’an kallesa “ Yaya lil bata da lapiya please kazo muje ma dubata dan Allah “
banza Big Boss yayi masa kamar ba dashi yake ba , prince yana so yake ya dubata
amma yana tsoro Sabida ganin big boss , tunda ya shigo uncle kad’ai yayi wa magana
da alama zuciyar sa tana kusa kusa , ganin ya ‘ki kulasane yasa little fashe masa
da kuka “ please yaya kazo ka dubata zata iya mutu wa “ rai a ‘bace Big boss ya
furta “ And so ?”, No please Big boss rashin lapiya aka ce , ko sau d’aya ne ka
dubata “ a miskilance ya furta “ uncle…” daga nan be kuma cewa komai ba , cikin
kuka little ya furta “ please yaya just for my sake kazo ka dubata” yanxu ma shiru
Big Boss yayi masa , cikin kuka little ya furta “ kace kana sona ? Zaka iyayin
komai a kaina ? Amma yanxu I beg you for a thing ka ‘kiyimun shi , why yaya , idan
momy na da dady sunanan zasu …” be ‘karasa ba Big Boss ya d’auke fuskar Little da
mari, karo na farko a rayuwar little da aka Maresa , Daidai lokacin da Bobo ya
shigowa cikin falourn , idanuwan Big Boss sunyi mugun jaa na tsananin ‘bacin rai ,
jijiyoyin wuyansa gabaki d’aya sun fiffito shi kansa little sai da ya tsora ta ,
yasan Big boss ya hana maganar iyayensu ko kad’an shima yayi ne bawai dan ya damu
dasu ba Kawai so yake ya duba masa lil d’insa , cikin Sauri Bobo ya ‘karaso Inda
Big Boss yake sabida yadda yaga condition d’insa, lokaci d’aya little ya fashe masa
da kuka , shima prince sosai ya shiga Tashin hankali ganin yayan su, Bobo zai
ta’basa ya hankad’ata , a hankali ya ‘karaso Inda little yake , cikin tsananin
‘bacin rai ya furta “ how dare you?”, cikin rawar murya little ya furta “ please
yaya kayi hakuri kar ranka ya ‘bace, please kayı hakuri “, a tsawace Big boss ya
buga masa tsawa , karo na farko da little yayi maganar iyayensu dan shida Big boss
sunfi kowa tsanarsu tun little bashi da wayo, rai a d’an ’bace Big Boss ya lumshe
eyes dinsa be kuma kallansu ba ya wuce part d’insa , fashewa da kuka little yayi
tare da hugging din bobo “ yaya bobo ! Yaya bobo please ka bashi hakuri yana fushi
dani dan Allah ka bashi hakuri, Nima bana sansu kawai na fad’ane sabida ya dubamun
sister ne , please yaya am sorry “ babu Wanda jikinsa beyi sanyi ba , shi kansa
bobo saida jikinsa yayi sanyi ga Tuna’nınsa da ya raba gida uku, be san wani irin
hali Abla take ciki ba , da dinsa d’aya Dr tana kan hanya dan tun kafun ya ‘karaso
prince ya tura masa message, ga Big Boss s yasan yanxu ransa yayi ‘kololuwar tashi
duk Wanda yayi gigin masa magana xai iya sa’ba masa , mutum d’ayane yake iya masa
magana ko ransa yana a ‘bace shine little gashi yanxu da little din yake fushi
abunda da wuya ya faru dan Big boss xai iya hukunta kowa ya bar little Sabida san d
yake masa , ga little da yake ‘ko’karin tayan da hankalinsa, ,idan ba’a masa abunda
yake so ba ciwansa xai iya tashi, gabaki d’aya kwakwalwarsa neman tarwatsewa take ,
ga kukan da little yake masa har cikin zuciyar sa yake jinta , prince kuwa tuni
yabar falourn dan beso little yayi maganar mutanan da suka d’auka matattuba , kasa
magana uncle yayi sai zama da yayi akan kujera yana nanata “ Innalillahi wa inna
ilaihi raji’un”. A Daidai lokacin da abunda yake faruwa a ‘kasa , Abla tana Çan
cikin mawuyacin hali Sabida ciwan mara , tun tana mutsu mutsu har ta dena Sabida
yadda cikin ta ya murd’a mata , lokaci d’aya ta dena nunfashi alamar ta suma gabaki
d’aya.
( Tofa yau Big Boss na fushi da little 🥺🥹)…..

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____31💞
Hugging d’insa Bobo yayi sosai a jikinsa yana shafa bayansa “ it’s okay ! Bar kukan
haka , yanxu Dr zata ‘karaso ,” tun be ‘karasaba ba Dr din da Abla ta zauna a Wajan
ta ta ‘karaso hannun ta d’auke da wani ‘karamin kit “ Kagama ta ‘karaso let’s show
her the room” gyad’a masa kai little yayi amma haryanxu bai dai na kukan ba , sai
da suka rakata har ‘kofar d’akin Abla amma basu shiga ba suka barta ita kad’ai.
Kama hannunsa bobo yayi zuwa bedroom d’insu , yana shiga yaga fitila a kashe, yana
kunna wa kuma ya tarar da Prince ya kwanta ya lullu’be jikinsa , idan mutum be lura
sosai ba sai ya d’auka bacci yake , shima little abunda yayi kenan, bed d’insa ya
hau ya kwanta tare da lumshe idanuwansa , sosai face d’insa tayi fiyau babu
murmushi ko fara’a a kanta , bakamar little da kowa ya sanshi me murmushi da dariya
ba. Kallan direction d’insa Bobo yayi kafun ya mayar da kallansa kan prince , bece
musu komai ba ya kashe musu light ya bar dum kamar kullum, shima ransa ba dad’i
gabaki d’aya ko magana bayasan yi Sabida yadda ransa yake a Jagule.
Doctor tana shiga tamakon gaggawa ta bawa Abla fahimtar abunda ya sumar da ita ,
cikin ‘kan’kanin lokaci ta farka Sabida allurar da akai mata, da kyar take iya
motsa jikinta sabida wani irin kasala da ya kamata , wasu drugs Dr ta bata da
bayanın yadda zatayi anfani dasu, face d’inta tayi fiyau kamar ba ita ba , babu
abunda bakinta ya iya furtawa sai “ thank you “ daga nan bata kuma cewa komai ba,
ganin Dr d’in ta fita daga d’akın yasa taje ta ‘kara tsaftace jikinta tare da yin
alwalar bacci ( mata please idan zamu kwanta mudunga yin alwala sabida ita Alwala
babban tsarice ga dukkan Wanda yaso nufarmu da sharri , Mata muna sakaci lokacin
Al’ada , lokacin da mace ya kamata ta ru’ke addua sosai musamman yin alwala yana da
babban mahimmanci lokacin Al’ada , duk mutumin da yayi ‘ko’karin nufinka da sharri
sai kaga Allah ya kubutar da kai ta inda bakayi zato ba , please mata mu lura ),
tana fitowa Bed d’inta kawai ta hau sabida lokaci d’aya taji gabaki d’aya cikin
nata ya dena yi mata ciwo gabaki d’aya , bata d’auki tsawan lokaci ba bacci me
nauyi ya d’auketa sabida allurar da Dr tayi mata har da ta saka baccin tayi mata .
Dr tana fitowa ta had’u da bobo, fuskarta da murmushi ta furta “ you don’t
have to worry , ba wani abu bane babba , nayi mata allura nasan anymoment yanxu
tayi bacci , and she need to rest for atleast good 2 days “, kansa kawai bobo ya
jinjina mata “ sure ! Thank you !”daga nan ya wuce part d’insa , itama ta fita
Robert ya rakata har waje .
******* Big Boss
Ransa a’bace ya wuce cikin bedroom d’insa Daidai gaban mirror ya tsaya, kan sa a
d’an sun kunye , gefe da gefe na gashin kansa sun rurrufe masa fuska, ransa yayi
mugun ‘baci shiyasa ya kaiwa glass naushi, cikin ‘kan’kanin lokaci hannunsa ya
fashe Jini bana wasa ba ya fara fito masa , amma ko kad’an be damu da hakan ba ,
sosai ransa yake ta farfasa, dukda yadda jine ke fita daga cikin hannunsa hakan
besa ya tsaya kula dashi ba , a hankali ya bud’e eyes d’insa musamman tuno marin da
yayiwa little , abunda be ta’ba faruwa ba a tsakaninsu , d’aya daga cikin drawers
din ya bud’e tare da d’auko wani allura , Daidai jijiyar hannunsa ya saka wa
allurar kafin ya lumshe eyes d’insa yana zama kan sofa, ga hannunsa da haryanxu
jinin da yake zuba bai tsaya ba . “ Nasan ko me kakeyi kana yin sane Sabida su ,
but please you have to calm down, nasan basu cancanci ku yafe musu ba , but atleast
lokaci yayi yanxu, 22years isn’t a joke”cewar uncle da yake shigowa d’akin , bud’e
rinannun idanuwansa Big Boss yayi ya zubawa best uncle d’insa , “ I hate it when
someone talk about so called them ! I hate it” yadda ya fad’a a gajarce da ‘bacin
rai mutum zai san har cikin zuciyarsa a ‘bace yake , murmushi uncle yayi masa
“Nasan ranka a’bace yake har yanxu, amma ya kamata kasani, ko ba dan kai ba ,
atleast for Little”, Kyawawan lips dinsa na ‘kasa Big boss ya d’an tauna da har
saida lips d’insa suka fashe, be kuma tanka wa uncle ba sai ma lumshe eyes dinsa da
yayi , Sabida yadda yaji kansa na sara masa. Murmushi uncle ya saki kad’an yasan
halin Big Boss sarai kamar yunwar cikinsa , ya san yanxu yana ‘kara magana
amaimakon abun yayi sauki sai ma worst da zai ‘karayi, mai da kallansa yayi kan
hannunsa da ya nuna shedar fashewa Sabida glass din da ya daka me shegen kwari ne ,
cikin tausasa murya uncle ya furta “ take care of your self, good night “ da haka
ya juya ya bad’ar d’akın ba tare da damuwa da rashin tankawa da Big boss be yi ba .
A Daidai ‘kofar falonsa na farko suka kusan cin karo da Bobo yana kallansa ya
jinjina masa kai ganin shima face d’in bobo babu wani fara’a akanta sosai , Duk
cikin su Big boss ya fi kowannansu zuciya dan da gasken gasken ya ci sunan masu
sunansa , shima uncle be tanka masa ba ya furta “ wannan face din da ka ‘ki saki ba
magana zan yi maka ba , take care of your brother , good night”, a hankali Bobo ya
furta “ Good night uncle “ daga haka Bobo ya nufi cikin bedroom d’in Big Boss shi
kuma uncle ya bar part d’in.
Bakinsa d’auke da sallama ya tura ‘kofar d’akın, a tsaye ya tarar da Big boss
hannunsa d’aya ya d’anyi dressing dinsa , yana ganin Bobo ya d’an ta’be baki zai
cike cikin dressing room d’insa , cikin tsokana Bobo ya furta “ yanxu tafiy zakayi
kabarni ? Bayan kasan wajan ka nazo ?” Batare da ya kallesa ba Big Boss ya furta “
Get lost ! You headache “ ynxu kam murmushi Bobo yayi “ Ni ne ma ciwan kan ? Nifa
lallashin ka nazo yi , haka Kawai ka tsinkawa little d’ina mari , ka saka bawan
Allah cikin damuwa…” dakatar Dashi Big boss yayi ta hanyar furta “ kaima baka fi
‘karfin marin ba ai“ yana kai ‘karshen zancansa ya shine dressing room d’insa .
‘Dan girgiza kansa Bobo yayi cikin d’aga murya sosai yadda Big Boss zai jisa ya
furta “ Babu Inda zani, yau a cikin d’akin nan zan kwana ..”be kulle bakinsa ba
yaji kamar ana ta’ba kofar alamar xai bud’e , cikin Sauri Bobo ya gudu yana
murmushi ‘kasa ‘kasa .

****2:00am Big Boss ne zaune kan wasu kujeru masu shegen kyau yadda yanayin Wajan
yake mutum zai fi kiran sa da Wajan sha’katawa dan sosai yanayin tsarin Wajan ya
had’u musamman yadda yake d’auke da wasu kujeru guda masu shegen kyau, system ce
kawai akan medium glass table d’in gabansa , sai ra tsats tsiyar wayar sa da ke
gefen side d’insa . Cikin kwarewa Big boss yake operating d’in ta , yadda ya zuba
mata narkakkun eyes dinsa sai ya ‘kara yiwa fuskarshi kyau, musamman yadda hasken
system d’in ya ‘kara hasko da tsananin kyan sa . Jikinsa sanye yake cikin wasu
fararan kayan pajamas masu shegen kyau da santsi, ga ba’kin lallausan gashin kansa
da ya nannad’e a bayansa.
Shigowar Bobo wajan ne yasa ya d’an d’ago da idanuwansa , sau d’aya ya kallesa ya
mayar da kallansa kan system d’in gabansa . Shima Bobo ‘karasa shigowa yayi
hannunsa d’auke da 2 cups of coffee sai faman turiri suke, a kusa da system d’in
Big boss ya ajje d’aya , d’ayan kuma ya ri’ke a hannunsa , babu Wanda ya tanka a
cikin su sai coffee d’insu da suke sha , sai da bobo ya tabbatar Big
boss ya gama aikin nasa sannan ya zauna a kujerar da take facing d’in Big Boss , “
we’re sorry! A dena fushi da mu” sai kuma ya d’an saki wani murmushi kad’an saman
la’b’ban sa “ wannan ne karo na farko da naga little yana san abu da gasken gasken
with all his heart, yasan duk abunda yake so ko be fad’a ba za kayi masa , but this
time around he just need your support, we all know his conditions, ya kwanta cikin
damuwa , you too , yarinyar da yake matu’kar d’auka sister dinsa , I, uncle ,
prince , banasan ganin ku haka , it’s hurt me so mentally “. Yana kai ‘Karshen
maganarsa ya kalli Big Boss da yake danna wayansa hankali kwance kamar ba dashi
Bobo yake magana ba , A hankali ya mi’ke cikin cool voice d’insa ya furta “ Good
night “ daga haka be kuma cewa komai ba ya bar part d’in Big Boss gabaki d’aya ,
sai a lokacin Big boss ya d’an d’ago da eyes dinsa ya kalli hanyar da Bobo ya fita
kafin ya ‘kara mayar da kallansa kan wayarsa da yake operating, ya d’au kusan 1
hour tukunna ya tashi daga kan kujerar da yake , ya nufi cikin master room
d’insa . Bashi ya Fito ba sai Wajan around 3:20am, tundaga kan part d’in uncle ,
Bobo , da su little gabaki d’aya saida ya duba lapiyar su musamman yadda yaga
little ya kwanta a takure , ga guntun hawayen da ya bushe akan face d’insa , be
jima ba ya nufi part d’insa sabida yadda kansa yake sara masa.

WASHE GARI
Lokacin sallar asuba nayi Little ne ya fara tashi , yau da kansa ya tashi
prince, sannan ya nufi d’akin uncle ya tashe sa , hatta Bobo yau little ne ya
tashesa amma ya kasa zuwa part d’in Big Boss , kamar xai yi kuka ya koma d’akinsu
yayi wanka ya shirya , Daidai lokacin da suka saba fitowa gabaki d’ayan su suka
fito, ko minti biyu basu yiba , Big Boss ya fito cikin shigar ‘kananan kayansa blue
black sai ba’kin wando da yake jikinsa , yau ko arzikin tufke gashin beyi ba sai
mummur d’ewa da sukai a bayansa sabida yanayin gyaran gashin da kansa ya samu.
Tunda ya Fito little ke kallansa kamar yaje yayi hugging d’insa , Sarai Big boss ya
gansa, kamar zai wuce sa sai kuma ya mi’ko masa hannunsa , cikin sauri little yayi
hugging d’insa kamar zai yi kuka “ kayi hakuri yaya , I promise bazan sake ba “,
gashin kansa Big boss ya shafa kamar Wanda aka sa dole sai yayi magana ya furta “
it’s okay ! Let’s go “ daga haka suka nufi masallacin ga baki d’ayansu , hannun
little yana cikin na Big Boss kamar Wanda aka ce masa Big boss d’in zai gudu. Ana
idar da sallah yanxu tare suka shigo cikin falourn hannunsa cikin na Big Boss ,
kowa part d’insa ya nufa Sabida lokacin training ya kusa.

*****A makare yau Abla ta tashi daga baccin da ya d’auke ta sabida Allurar da Dr
tayi mata , a gogo ta kalla ganin 7 ta wuce , cikin sauri ta shige toilet tayi
wanka , komai cikin sauri take yinsa , har ta shirya cikin uniform d’inta bayan ta
gama gyara cikin bedroom din ta , babu Wanda ya fad’o mata sai simba da bata bawa
abinci ba ga time yana ‘ko’karin wucewa , shaf shaf ta gama abunda zatayi ta fito
daga cikin d’akin. Babu kowa a falo da alama sun tafi training d’insu na kullum ,
bata tsaya tunanin komai ba ta nufi inda simba yake , ga mamakin ta sai ta tarar da
Simba yana cin abinci da alama tuntuni an kai masa , babu tunanin da ya fad’o masa
sai little a fili ta furta “ Allah sarki may be yaga ban fito bane shiyasa ya kawo
masa abincin , Nagode sosai yaya little”Da wannan Tuna’nın ta koma cikin part
d’insu amma duk da haka bata ga su Little ba kamar yadda ta saba , a gogon falourn
ta kalla taga 8:00am ta kusa alamar ta kusa makara Kenan , maida kallanta tayi
wajan hanyar shigowa ko zata gansa amma still shiru , ita kad’ai sai kallan time
take , har wajan ‘karfe 8:20am na safe tana zaune a wajan, mi’kewa tayi da niyar
nufar d’akin ta taji sallamar su shida prince , sai a lokacin ta saki ajiyar
zuciya, duk a tunaninta zasu ce mata ta d’auko school bag d’inta su tafi ne amma
sai taji sa’banin hakan “ Lil ya jiki ?” Cewar little , fuskarta da murmushi ta
furta “ naji sau’ki yaya little “ shima prince ya jiki yayi mata ,sai alokacin Abla
ta samu damar gaishe su , kallanta little yayi ganin uniform a jikinta “ Lil sis
yau fa ba zakije school ba , yaya Bobo ya fad’a mun Dr tace kina bu’katar Hutu na 2
days , ya kamata ki canza su any time yanzu zamuyi breakfast okay ?” Itama Ablan
“okay”tace masa kafun ta juya zuwa bedroom d’inta . Tana shiga kayan jikinta ta
cire , ta saka wata red doguwar riga da tayi matu’kar yi mata yau, lokaci d’aya
taji tana jin baccin daman ba isar ta yayi ba , fasa futar tayi koma kan gado
abunda, mintuna kad’an bacci ya d’auketa .

*****9:30am gabaki d’aya suna zaune ban da Big Boss , ko wannan su sanye yake cikin
shigar ‘kananan kaya daya zamar musu jiki , dan ko little be ta’ba saka wani kaya
wai shi kayan Malam bahaushe ba , ko wanne ka ga face d’insa zaka ga annashuwa
kamar basu ba, daddad’an ’kamshin turaran Big Boss da suka jine yasa suka d’ago da
idanuwansu kusan lokaci d’aya , sanye yake cikin wata long sleeve ash d’in riga sai
wani wandan jeans black colour da yake sanye da shi, gashin kansa kamar kullum sai
kyalli yake kamar ‘kura bata hawa kansa , cikin Black d’in takalmin gucci yake
takowa a hankali kamar baya san taka ‘kasa , duk da yadda yaji idanuwa akan sa
alamar kallansa suke hakan be sa ya d’ago da idansa ko sau d’aya ya kallesu ba har
ya ‘kara so cikin falourn , “ Am hungry “ cewar little yana kallan Big Boss ,
harararsa Bobo yayi “ tunda baka ce kana jin yunwa ba sai yanxu ? Salan rigima ?” ,
murmushi little yayi “ No yaya Bobo ina jin yunwa da gaske , yaya nake jira ya
sakko muci shiyasa ban fad’a muku ba “, ko kallansu Big Boss beyi ba duk da gabaki
d’aya magan ganunsu akan kunnansa sukayi shi , Diamond watche d’in da ke farin
kyakkyawan hannunsa ya kalla na ‘yan sakanni kafin ya mi’ke tsaye , da Sauri gabaki
d’aya suka kallesa “ Am out “ shine abunda ya iya furtawa , da sauri little ya
furta “ yaya yunwa fa nake ji?” d’an hararansa Big Boss ,“Come and eat me “murmushi
little yayi masa da har saida hakwaransa ya fito farare tass dasu , shima prince
cikin kwaikwayar little ya furta “ yaya nima yunwa nake ji fa “. Mi’kewa tsaye
uncle yayi “ then let’s eat together all as a family” ya ‘karasa yana kallan Big
Boss , suma su Bobo kallansa sukai suna jiran jin amsar da zai bayar, sai da ya
gama karantar yanayinsu har sun sad’akar sai sukayi saukar muryarsa “ okay “, kamar
wani babban abu yayi little har da d’aga hannu ya furta “ yes” a haka suka ‘karasa
dinning gabaki d’ayansu , yau ko james basu bari yayi serving d’insu ba , da kansa
little da prince sukai serving d’insu, har cikin ransa yana so Lil d’insa ta sakko
suci abinci amma bayasan ‘bacin ran Yaya Big Boss, kowa ya kula da yanayin face
d’in sa hatta Big Boss da ya d’an d’ago ya kallesa ya d’auke eyes d’insa ganin be
fara cin abincin ba dukda shima be soma ci ba , Kamar Wanda aka sa dole ya furta “
called her let’s eat “, cikin tsananin mamaki da jin kalamansa suka zuba masa eyes
d’insu kamar Wanda suka samu hoto, Big Boss kuwa kamar bashi yayi maganar ba ya
‘kara tsuke face d’insa , sunsan halinsa yana iya canza ra’a yi shiyasa cikin
tsananin farinciki Little ya furta “ I love you yaya ! You’re the best “, be jira
jin amsar Big Boss ba ya ruga a guje gudun karma ya tsayar dashi , Direct d’akin
Abla ya nufa , knocking d’aya yayi mata , lokacin tana tsaye a gaban mirror tana
saka wani golden chain d’in sar’ka yar siririya me shegen kyau sai d’an ‘karamun a
danta da ya ‘Kara yiwa farin wuyanta kyau. Cikin sauri ta je ta bud’e door d’in ,
Wanda ta gani a bakin ‘kofar ne yasa ta sakar masa lallausan murmushi , tun kafin
tayi magana yayi saurin furta “ Let’s go lil we don’t have time “ dan babu abunda
Big Boss ya tsana kamar a ‘bata masa lokaci, ko bari ta koma d’aki beyi ba yasa ta
sakko ‘kasa , sai binsa da kallo take , a tunaninta kamar yadda suka saba cin
abinci ne zasu ci shiyasa bata damu ba lokacin da suka nufi dining, lokaci d’aya
zuciyarta ta buga sabida ganin Wanda bata yi tsan manın gani ba , cikin sauri ta
fara karan to adduar datazo cikin zuciyar ta , sai lokacin lefin da tayi masa ya
fad’o mata cikin zuciya da ‘karfi zuciyar ta tabuga bakinta har ya d’an soma rawa
a tunaninta hukunta ta zaiyi akan laifin da tayi masa ne shiyasa ko side d’in da
yake batayi gigin kallan ba,Uncle ya katse mata tunanin da ta fad’a “ Daughter kin
tsaya a tsaye , ki zauna mana “, cikin d’an rawar baki ta na d’an dur’kusawa ta
gaishe da uncle , shima cikin fara’a ya amsa mata yana ‘kara cewa ta zauna, bakinta
har rawa yake lokacin da take gaishe da Big Boss, duk da har cikin zuciyarta tasan
bazai ta’ba amsa mata gaisuwar ta ba , kamar wacce tayi magana da dutse dan ko
‘kurar da ta kawo ta be kalla ba , bayan abincin gabansa da yake ci cikin salo a
hankali cike da nutsuwa , jikin tane yayi sanyi amma duk da hakan murmushin kan
face d’inta be gushe ba , Bobo ta gaisar last , kamar yadda ya sama cikin sakin
fuska ya amsa mata , little ne yayi serving d’inta , gabaki d’aya ta kasa sakewa ,
Sabida jin present d’insa a Wajan sai faman wasa take da spoon d’inta , ko 5
minutes batayi a wajan ba ya mi’ke bayan ya goge bakinsa da tissue , “ take care
yaya !” Cewar little Sabida yasan fita zai yi , kansa ya d’anni knodding kamar me
rad’a ya furta “ take care “ ya ‘karasa yana kallan uncle da yake sakar masa
murmushi. Sai da ya bar wajan gabaki d’aya sannan ta saki a jiyar zuciya kad’an ga
masifaffen ‘kamshin turaransa da take ji har yanzu cikin hancinta , a hankali ta
soma cin abincin ta , ko 5 spoon batayi ba taji gabaki d’aya abincin ya fita
ranta , ji take gabaki d’aya cikin ta ya cika, amma gudun kar suyi magana yasa take
tura abincin a hankali , da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai suka soma tashi har yayi saura
ita kad’ai a Wajan , tana ganin sun watse gabaki d’ayansu itama ta mi’ke ta wuce
bedroom d’inta ganin su little basa falourn.

****** Gabaki d’aya yinin ranar a d’aki ta wuni tana duba littattafan ta , su
Eshaal ne suka fad’o mata arai musamman yadda taga Baby tanayi mata abu kamar wacce
taga bai warta, tuno da halin Babyn yasa ta d’an saki wani murmushin da kaici, duk
rawar kanta husna ta da meta dukda ko wannansu yana da banbanci halaye musamman
Baby da taga rashin kwa’bane ya fi lallatata, da ta tuno Eshaal da fanan yadda suka
sake da ita duk da babu san ko wacece ba hakan yasa wasu ‘kwalla suka taran mata a
cikin ido “ Allah sarki Arwa bansan inda kike ba amma har yanxu ina ji a jikina
kinanan a raye, Anee kema bansan wani hali kike ba a yanxu amma ina fatan kina
hannu na gari “, lokaci d’aya Abla ta saka kuka Sabida tuno irin ‘bakar u’kubar da
Suka sha wajan uwar karuwai, ta azabtar dasu sosai kamar ba mutane ba , sabida
ganin basu da gata , musamman ita da Arwa, bata san dalili ba , batasan me sukai
mata ba amma gabaki d’aya ta fi nuna tsantsan tsanar ta akan ta .

Cikin ‘kan’kanin lokaci ta dunga tuna rayuwar ta a cikin gidan uwar karuwai ,
moment d’inta da Arwa, Anee , Husna , harta Ilham , “ Abla yunwa nake ji” Wannan
kalmar kusan kullum idan zata ci abinci da ita take ci cikin zuciyarta sabida yadda
Arwa ta saba fad’a mata duk lokacin da ta ji yunwa , ta d’au dogon lokaci tana
tunaninsu kafin ta tattara komai ta ajje , ta mayar da hankalinta kan littattafan
school d’insa .
3 nayi ta ‘kara nufar d’akin simba , yanxu ma ba ‘karamun mamaki taji ba ganin har
ankawo masa a binci, ita kad’ai sai addua take wa little ta dan wannan aikin sane
ko aikin prince. Lokacin da ta koma cikin gida Prince ya fita Sabida wani urgent
case da yake so ya duba , sai little shima da yake filin Basket Ball, cartoon ta
d’an kalla kad’an , lokacin sallar la’asar nayi na koma d’akinta itama .
9:30pm fruit kawai ta d’ansha ta kwanta , sabida duk lokacin da take Al’ada bata
san zama cikin mutane dan ba ‘karamun ta kura take yi ba, ta jima a kwance a kan
gado kafun bacci ya d’auketa Sam ta manta da coffee d’in da zata kai masa . Sai
wajan 11 su Little suka nufi d’aki suma ganin Abla bata fito bane ya sa ya fara
zuwa d’akınta, sau biyu yana knocking ba’a bud’e , shiyasa kai tsaye ya bud’e
d’akın, acan saman gado ya hango fuskarta jikinta sanye da duvet ga light da ta
bari a kunne, batare da wani damuwa ba ya kashe mata light d’in gabaki d’aya ya
rufo mata ‘kofar.
*****”Wani irin dogon tsauni take hango wa masu shegen tsawan gaske , gashi
ta ko ina wajan babu haske sai duhu ga kukan da ya cika d’urmur dajin, wasu irin
manya manya mutanene suka soma biyosu, ta ko ina suna cunna musu huta , da ta juya
zata gudu zata ga ana mi’ko mata hannu alamar ta cecesu, kafin tayi wani yun’kurun
mutanan wajan zasu ‘kara sakin wani kuka ne gigita mutane da gabaki d’aya dajin,
mutane ne daban daban suke mi’ko mata hannu ta cecesu ta ko ina , ga kukan mutane
da take ji , wani lokaci kuma kukan ya ri’ki d’e zuwa kukan na miji. Gabaki d’aya
manyan halintun sun gama rikita wajan ga feshin Jini ta ko ina “ a rud’e Abla ta
kwalla wani irin ‘kara sabida mummunan mafarkin da tayi , bud’e idanuwan da zatayi
taga gabaki d’aya d’akin yayi duhu, wani ‘karar ta kuma saki a karo na biyu tana
toshe kunnuwanta , ji take kamar yanxu ne mutanan suke mata magana, da karkinta
take toshe kunnuwanta, nunfashinta har ya fara seizing musamman yadda ta tsani duhu
, yau ko iba bud’e bakinta batayi sai jikinta da ya d’au rawa lokaci d’aya .

SORRY FOR THE LATE POST👏👏.


https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____32💞

Hankalinta ba ‘karamun tashi yayi ba sabida bala’in duhu da ta ga d’akin yayi


mata , ko bakinta bata iya motsawa sabida yadda tayi bala’in rud’ewa , ga wani irin
zufa da ya fara wanke mata fuska , a gigice ta fara bin kan gadan da hannu har ta
sauka daga kansa , duk da haka bakinta yayi mata nauyin da zata iya yin ihun neman
a gaji sai bin bango da take yi cikin tashin hankali , ‘kirjinta har sama da kasa
yake yi sabida tasanin tsoran da ya kamata, da ‘kyar ta iya bud’e ‘kofar d’akin ta
fito, a rud’e sai faman wai wayan bayanta take , gani take kamar yanzu take yin
mugun mafarkin, tun kafun ta ‘bar wajan corridor d’in ta fara ganin duhu duhu na
dum light a Wajan . Gashi bazata iya koma wa d’aki ba sabida tsoran da ya kamata ,
da kyar ta nufi kan stairs nan kuma akwai light me kaloli a wajan, bin ‘katan
falourn tayi da kallo ganin ko ina shiru , hatta su little da ta saba ganin su a
wajan basa nan , ta juya da niyar komawa kawai tajiyo kamar sautin mutum, a zabure
ta juya zata gudu ‘kafarta ta d’an daki d’aya daga cikin stairs din, cikin tsananin
bugun zuciya ta yi baya zata fad’i ’kasa , har ta sadakar mutuwa zatayi. Ga
mamakinta sai taji kamar abu ya tare ta , cikin sauri ta bud’e idanuwanta ganin
lokaci kad’an kuma an hankad’o ta tayi taga taga zata fad’i kafun ta tsaya da
‘kafafunta. Ba kowa bane face Big Boss da tun ihun ta na farko ya jita Sabida yana
zaune a falourn , amma gabaki d’aya yadda yake operating system d’in gabansa bazaka
ta’ba kawowa yaji wani ihu ba . Lokacin da zata fad’i kuma a maimakon ya ri’kota
sai ya d’an tare ta da hannunsa d’aya kafun ya hankad’ata ta Mi’ke da ‘kafafunta.
Sun kuyar da kanta ‘kasa Abla tayi ganin ko inda take be kalla ba yayi juya warsa .
A hankali ta furta “ Nagode !” Kamar wacce tayi magana da Dutse dan ko juyowa be yi
ba balantana ya nuna yaji abunda tacen. Dogon ba’kin gashinsa ta zubawa ido har ya
wuce daga ganin ta , a hankali ta furta “ komai akai wa mutum baza’a ta’ba burgesa
ba,jibi kamar wata kayan wanki ya tareni da hannu kamar yaga wani abun cutar wa ,ko
ma dai mene ne oho , amma tunda ka tai makeni Nagode “ motsin da ta kuma ji ne yasa
ba shiri ta ruga a guje ta koma part d’inta , saida tsaya tayi addua sosai kafun ta
iya komawa cikin d’akin, wani ajiyar zuciya ta saki lokacin da hasken d’akin ya
dawo, har ta ‘karasa kan gadon bakinta da addua , ganin bazata iya koma wa bacci
bane yasa ta fara addu’o cikin zuciyar ta , tun tanayi a zaune har ta zame kan
gadon kafin baccin da ya ci ‘karfin ta ya d’auketa.

‘Karfe 8:20 yau ta farka daga baccin da ya d’auketa sabida little ya riga da ya
fad’a mata bazata je school yau ba, zuwa yanzu ta ji sau’ki sosai babu inda yake
mata ciwo amma ba damar tace zata je school tunda an hanata zuwa. Shaf shaf wanka
tayi ta shirya , yau shigar ‘kananan kaya tayi da yayi mugun fito da surar
jikinta , kamar a jikinta aka d’inka kayan dan ba ‘karamin shape din jikin ta ya
fito mata dashi ba,rigar jikinta Baby pink top ce da ta fito da breast d’inta sosai
kamar zasu tsaga rigar su fito waje daga Samanta sai ta saka wata rigar ta d’aure
igiyarta yadda jikinta bazai fito ba , a cikin yan kwanakin nan da ta ‘karayi
jikinta ba ‘karamun smooth yayi ba , yadda fatar jikinta tayi kyau ko ta wani me
samun hutun albarka. Gaban mudubin d’akin ta ‘karasa tana ‘karewa kanta kallo,
kyakkyawar yarinyace Abla da fad’in kyaunta ‘bata bakine, sosai Allah ya bata
baiwar kyau na fili da na ‘boye, tun daga kan round face d’inta har zuwa kan
fararan idanuwanta masu kama da madara , kwayar idanunta ash colours ne masu shegen
kyau sai wani ba’kin d’igo dake cikin kwayar idanta kamar tauwada da ya ‘kara
haskaka kyan idanta , koya tamotsa idanuwanta sai dogon black lashes d’inta sun
kad’a gashi long lashes ne da ita , ko ya mutum ya kalleta sai ya so ya ‘kara
kallanta musamman idan ta zuba maka dararan eyes d’inta me matu’kar rikita mutum,
gashin girar ta a cike yake sosai gashin black colour kamar wacce akai wa gyaran
gira sabida yadda shape d’in girar ta ya fito sosai , hancinta dogo ne da ya ‘kara
fito da tsantsan kyan fuskarta, gashi Siriri me kyau duk da baza’a kirashi da
siriri ba , d’an kad’an Abla ta motsa lips d’inta , sosai kyawunsu ya fito sosai
kalar pink , musamman yadda shape d’in bakinta yake kamar na love , daga gefe gefen
fuskarta kyantaccen gashine masu kyau kalar ‘baki da suka kwanta luf luf a kan face
d’inta, koya Abla ta motsa bakinta Dimples d’inta ne suke fito wa ta both side
kumatunta. Irin su Abla ake kira da coca cola shape , dan ta ko ina Allah ya basu
dan a cike suke taf.

Tana gama ‘karewa kanta kallo , wani farin lipgloss ta d’auka ta saka cikin cute
love shape lips d’inta , da ya ‘kara haska mata pink lips d’inta , gashin kanta har
ya fara fitowa dukda ba’a dad’e ba lokacin da Big Boss ya sa ta yanke amma ba lefi
har ya fara dawo, mayafin kayan tayi rolling tare da fesa turare ka d’an ajikinta,
duk da ba da yawa ta saka ba , amma ‘kamshin ya cika ko ina ta cikin d’akin , duk
Wanda ya san Abla a da ya ganta a yanzu kuma zai iya rantsewa da Allah ba ita
bace , Sabida yadda tafito sak a kyakkyawar matashiyar balarabiya. White half
slippers ta saka da ya fito da fararan ‘yan ya tsunta , bata zame a ko ina ba sai
falourn ‘kasa Inda su little suke , kamar kuwa ta sani , su ka d’ai ne a falour shi
da prince kamar daman jiran fitowar ta suke , daga nesa little ya fara furta “ wow!
Wow! Wow!Lil wannan kyan naki ko a gasar kyau aka je sai kin lashe kowa a
kyau”,face d’inta ta d’an kare sabida kunya da maganar sa ta bata “ haba yaya
little , ka dena tsokana ta fa , kaima kasan ka fini kyau “ murmushi ya sakar mata
kad’an “ No little ki tanbayi yaya Prince , kin fini kyau , da ke da Yaya Big Boss
bansan wanene yafi wani kyau ba , ko yaya prince ?” Shima murmushin yayi lokacin da
ya furta “ yes Lil , kinga da gasar kyau da little ake amma tun ba’aje ko ina ba ya
fad’i tunda kin lashesa” wani murmushin Abla ta daki da yasaka dimples d’inta
lotsawa “ please yaya ku bari kuna sani jin kunyar ku fa “ lokaci d’aya suka
‘kyal’kyale da dariya , cikin tsokana prince ya furta “ it’s okay mun dena , bakiyi
breakfast ba , kar abincinki ya wuce “ haka suka jata har dinning sukai serving
d’inta abinci, sai da taci da ‘koshi sannan suka dawo falourn,wani channel prince
ya saka musu sai suka ci sa’a kuwa ana quiz , kallan little , prince yayi kafin ya
mayar da kallansa kan Abla , wani tunanine ya fad’o masa , lokacin d’aya ya ‘kara
kallansu “ I have a quiz for you ! Duk Wanda ya cinye yana da babbar kyauta!”
Murmushi kawai Abla tayi dan tasan ban da ita a ciki ai , “ Menene prize d’in mu ?”
Cewar little yana kashe masa ido , “ Anything you want “prince ya bashi amsa ,
cikin Sauri little yace are you sure ?” Da yes kawai prince ya bashi amsa kafun ya
furta “ your time starts now! Duk question d’in da aka fad’a Wanda ya riga fad’ar
amsa shine yake da mark” Lil kin yarda ?” Cewar little , kanta tayi knodding alamar
Eh , da haka suka fara game quiz d’in, a karan farko little ya cita akai 1-0, a
second round ma haka yaci ta akai 2-0, ana 3rd round ne Big Boss da Bobo suka shigo
cikin falourn, gabaki d’aya basu kula da shigowarsu ba Sabida yadda suka maida
hankali a cikin quiz din da ake, saura kad’an little ya bada amsa tayi saurin
fad’an amsar , Daidai lokacin da aka fita short break, amsar da ta fad’a ne little
yayi saurin cewa be yadda ba , ba Daidai bane , itama Abla ta kafe akan cewa Daidai
ne , cikin dariya prince ya furta oya little explain your self, calculation d’in
little ya fara step by step har ya kammala ,murmushin da ya ‘kawata face d’inta
Abla ta saki, cikin shau’kin quiz din da suke ta ‘kara furta “ Dagaske nake fa yaya
little this time around ka fad’i”, amma still little yaki yadda, Big boss da Bobo
na bayansu har yanxu basu san da shigowarsu ba , “ Sis I told you kece kika fad’i”
yanxu ma murmushi Abla ta ‘kara saki “ shikenan na yadda idan nice ma fad’i zan
zagaye duka gidan nan da rarrafe amma idan ka fad’I zakayi mana rawar monkey ka
yadda “ cikin sauri Bobo ya toshe bakinsa , baya so yayi dariya har su kula dasu
wai rawar monkey , Big boss kuwa fuskarsa na a had’e babu ko single murmushi akan
ta , Daidai lokacin da aka dawo bayan Abla tayi explaining nata , a duba mark kuwa
Ablan ce tayi Daidai , cikin surprise little ya furta “ how comes sister ? Bayan
nima abunda nayi kenan” yes Daidai kayi mistake d’inta , 1 d’in da ka saka lokacin
farkon solution dinka , zata ‘kara bashi amsa taji daddad’an ’kamshin turarensa , a
hankali ta d’ago da eyes d’inta zuwa direction d’in da zuciyarta tafi mata a
hasashe, cikin Sauri kuma ta du’kar da kanta ‘kasa , ganinsa shi da Bobo a tsaye
hannun gabaki d’aya jikin aljihu sai dogon curly hair dinsa baki da yake shinning,
murmushi Bobo ya saki lokacin da little ya furta “ welcome back yaya “, har yanzu
da murmushin akan face d’in Bobo lokacin da ya ‘karaso falourn , banda Big boss da
ya nufi part d’insa batare da ya ‘kara kallan direction d’in da suke ba . Cikin
tsokana Bobo ya furta “ yau finally little zai yi mana rawar monkey ,” gabaki d’aya
dariya suka saki lokaci d’aya, ko good 5 minutes beyi a falourn ba shima ya wuce
part d’insa, yayi saura Little da prince sai kuma Abla , a haka suka shiga ba da
game d’insu har aka gama suka tashi da equal mark.

Kallan time little yayi ganin lokaci yaja sosai “ Lil please can you help me ?
Ya’ya zaki kaiwa abinci , Nima sai prince ya tayani na kaiwa yaya nasa food d’in.
Yadda ya kira Big Boss da Bobo da sunan yaya sai tayi Tuna’nın Bobo zata kaiwa
abinci , su kuma su kai wa Big Boss shiyasa batayi musu ba ta amsa masa da toh ,
sai da aka gama had’a komai na breakfast d’insu taga little da prince sun d’auki
nasu , tana ‘ko’karin tanbayar du part d’in Bobo taji maganar little da ya saka
zuciyar ta harbawa kad’an “ kiyi Sauri ki kai masa Lil , Ya’ya Big Boss baya san
jira , daga haka be gama jira tayi magana ba suka wuce Shida prince , elevator ta
kalla kad’an tana sakin ajiyar zuciya “ Yau kuma bansan wani kalar hukunci zan samu
ba idan nayi wa wannan bawan Allah lefi, Allah yasa baya cikin falourn ma “ ta
fad’a a hankali , kafun ta d’auki kayan breakfast d’insa ta nufi part d’insa .

A Daidai ‘kofar falon sa ta tsaya ga baki d’aya ta kasa bud’e kofar, tafi tsawan 5
minutes a bakin ‘kofar kafun tayi ‘karfin halin bud’ewa bakinta d’auke da sallama
‘kasa ‘kasa , a tsanake ta shigo falon , daddad’an ’kamshin turaransa na dokar mata
‘kofofin hancinta , ganin babu kowa a falourn ne yasa ta d’an saki ajiyar zuciya,
Daidai kan dinning d’insa ta shirya masa kayan breakfast d’in kamar yadda taga su
Little suna masa , motsin da taji kamar ana shirin bud’e ’kofa ne yasa ta ruga a
guje ta bar falourn Daidai lokacin da shi kuma ya ke shigowa cikin falourn, Dinning
ya kalla kafun ya kalli ‘kofar da ka fita yanxu, kansa ya d’anyi knodding kafin ya
zauna kan d’aya daga cikin kujerun falourn , ko ‘kara kallan inda abuncin yake beyi
ba . Abla tana ganin ta fita daga cikin d’akin tayi ajiyar zuciya , ko
ba komai ta tsira, hankali a kwance ta fito daga part d’in, suma lokacin su little
sun dawo daga part d’in Bobo , da d’an mamaki akan face d’insa little ya furta “
har kinyi serving d’insa ?” Abla bata gane wa yake nufi ba shiyasa ta tsura masa
ido , fahimtar hakan ne yasa ya ‘kara maimaita maganarsa “ kin serving d’in Yaya
Big Boss ?” Kanta ta girgiza masa tana kallansa, goshinsa ya d’an dafe kafun ya
‘kara kallanta “ sorry Lil ba’a kai wa Yaya abinci ba’ai serving d’insa ba , hurry
up kije kiyi serving d’insa “, kamar tasaka hannu aka tayi ihu taka takeji sabida
tsoro , babu yadda ta iya bayan ta amsa masa , a hankali ya furta “ Thank you “
lokacin da Abla ta juya zuwa part d’in Big Boss , yanxu ma tafi ‘karfin 5 minutes a
bakin ‘kofar , da ta saka hannu kamar zata ta’ba kofar sai tayi saurin d’auke
hannunta , shahada kawai tayi ta bud’e ’kofar bakinta d’auke da sallama duk da bata
da tabbacin yana cikin falourn. Yana zaune kan kujera yayi crossing legs d’insa ,
hannun sa d’aya kare a kunnansa da alama waya yake yi me mahimmanci sabida yadda ya
mayar da hankalinsa kan wayar, daga gefe dashi can ta tsaya tana jira ya gama wayar
da yake dan gabaki d’aya bata fahimtar yaran da yake , yafi 30 minutes yana wajan,
Abla kuma na tsaye sai musu musu take da legs d’inta da ta soma gaji ganin har
yanxu be gama wayan da yake yi ba , 20 minutes later ya ajje wayar hannunsa gabaki
d’aya alamar ya gama wayar da yake sanyi. ‘Dan turo baki Abla tayi kad’an ganin
yadda ya share ta kamar be san da mutum a cikin d’akin ba , kayan abincinsa da ta
jera a dinning ta ‘kara kwasowa ta jera su kan center d’in gabansa, a hankali ta
furta “ ina kwana ?” Shiru be amsa mata ba , ‘kara maimaita masa gaisuwar tayi amma
still ko bud’e idanuwansa da ya lumshe be yi ba , itama share sa Abla tayi dan ta
tsani shariya , “ Me zan zuba maka ?” Yanxu ma kamar wacce tayi magana da wunki ,
dan yadda idanuwansa suke a kulle sai ka d’auka babu Wanda yayi existing a gabansa,
haushin hakan Abla taji har ranta amma still ta ‘kara dannewa , “ Wana abincin zan
yi serving d’inka ?” Yadda ya ‘kara shareta ne yasa taji kamar kwalla na tarar mata
a cikin idanu, da sauri ta goge tare da bud’e warmers d’in, ranta har ya soma ‘baci
shiyasa ta zuba masa abunda ta ga tama ta kama hanyar barin falourn nasa da
wulakanci yana d’aya daga cikin abunda ta tsana , har ta ta’ba hannun handle zata
bud’e tayi daddad’an muryarsa a gajarce ya furta “ Are you mad ? Who permits you to
go out?”shiru Abla tayi masa sai sunkuyar da kanta ‘kasa da tayi “ karki bari na
maimaita “ kamar zatayi kuka ta dawo cikin falourn Daidai lokacin da yake bud’e
eyes dinsa , abincin da ta zuba ya kalla sau d’aya kafin cikin husky voice d’insa
ya furta “ eat them all “ da Sauri Abla ta kallesa sannan ta kalli tulun abincin da
ta zuba masa a cikin plate dinsa, kamar zata yi ta furta “ Na ‘koshi” kallan da ya
jefa mata ne yasa ta ‘karaso ta d’auki abinci zata fita “ if you dare make another
step !just 5 minutes na baki , sannan ki fice mun a part with those your smelling
odo “ cikin Sauri Abla ta share hawayan da suka zubo mata , bata ‘kara musa masaba
ta zauna ta fara tulin abincin da ta zuba masa , yadda take turawa kamar zatayi
amai Sabida bata jima da cin abinci ba , ta naci tana share kwallar idanunta , da
‘kyar ta cinye abincin ita kad’ai sai nishi take , tana gamawa warmers d’in ta
harhad’a zata kwashe ya kalleta da idanuwansa da suka d’an rine “ Don’t you dare !
Kada ki kuskura ki ‘kara ta’ba abinda zanci da ‘kazamun hannunki, get out of my
room with your poisoned hands of yours “kasa kallansa Abla tayi sai “ okay da ta ce
masa , yanxu ma zata futa ta ‘kara jin muryarsa “ ki tabbata kin saka su a trash
“cikin sauri Abla ta fice daga d’akin tare da bugo masa ‘kofa da ‘karfin gas’s ke
da har saida ya lumshe idanuwansa , a bakin falourn ta tsaya ta gyara face d’inta
sosai ta yadda su little basasu gane reaction d’in face d’inta ba , tana sakkowa
‘kasa ta kwakwalo murmushin da ake kira yafi kuka ciwo ta yafa akan face d’inta ,
“Lil kin gama serving d’insa ?” Murmushi Abla ta sakar masa “ yes har ya gama ci “
kansa little ya jinjina mata “ thank you Lil” da haka ta ‘karasa ta ajje warmers
d’in tare da nufar d’akınta .

Tana shiga kuka ta fashe dashi, wula’kancin Big Boss be ta’ba tsaya mata a zuciya
ba sai yanzu , ji tayi da tana da yadda zatayi da ko inuwarta bazai sake ganin ba ,
balantana ya samu hanyar wula’kanta ta amma ba yadda zatayi tunda a gidan take
rayuwa , su suka tallafi tata rayuwar, ko me zai yi mata zatayi hakuri . Ko sau
d’aya bata ‘kara Tuna’nın futa falourn ba tayi zamanta a cikin d’aki.

Gabaki d’aya wunin bata ‘kara bari ta had’u dashi ba ko sau d’aya , sai yazama
kamar wasan ‘buya ta somayi dashi , yau ko zuwa kai wa simba abinci batayi tayi
zamanta a d’aki, da daddare ma ‘karfe 9:00pm ta gudu d’aki Sabida batasan
had’uwarsu balan tana tace zata had’a masa coffee , tunda ya furta da bakinsa bazai
ci abinda ya fito daga ‘kazamun hannunta ba , yanzun ma zai iya maimaita mata
abunda yayi mata d’azu tunda ya ta’ba sakata shan 10 cups of coffee . Tana yin
wanka ta ‘kara dudduba books d’inta, har wajan 11:00pm na dare , kafun ta ajjesu
itama ta kwanta bacci Sabida ta tashi gobe da wuri.

******
FRIDAY
kamar yadda tasa aranta zata tashi da wuri , da wurin kuwa ta tashi, toilet d’inta
ta fara wanke wa sannan ta gyara d’akin sai faman tashin kamshin freshener yake ,
tana gamawa wanka tayi ta shirya cikin uniform d’in makarantar ta , harta d’an yi
missing school Sabida yadda tayi kwana biyu bata zuwa, tsaf tsaf ta shirya cikin
uniform d’in ta amma ta’ki fitowa falour sai daga 7:35am tayi sannan ta
fito ,Little na tsaye yana jiran ta , yana ganinta ya ‘karaso Inda take “ yau kin
kusa makara Lil , and bakiyi breakfast ba “ cikin Sauri Abla ta furta “ bana jin
yunwa na ‘koshi “ girgiza mata kai little yayi “kin manta baki da lapiya ne kike
san zama da yunwa , ki tafi da Youghurt ko snacks kice kafin lokacin break “
murmushi tayi masa “ kaya zamu ‘kara makara yaya little , karka damu da wuri muke
fitowa break , I promise zan ci abinci okay ?” Okay cewar little “ But still zan
d’auko miki Youghurt okay ?” Kanta tayi knodding tana furta “ Thank you “ cikin
sauri yaje ya d’auko mata wasu Youghurt masu shegen dad’i ’kanana gashi sunyi sanyi
sosai , cikin wani bag ya saka mata tare da su chocolate a ciki. Tunda Suka fito
take kallan hanya , so take kawai su fita daga cikin gidan , tana ganin motocinsu
ta d’auki hanyar school ta saki a jiyar zuciya , Sabida yadda Robert yake gudu
sosai akan titi basu dad’e ba suka ‘kara so makarantar, Bag d’in kayan za’kin
Little ya mi’ka mata “ take care ! Yau ba’a Tashin ku da wuri ! So da wuri zan zo
kinga yau Friday , okay ?” Itama okay tace masa kafin suyi wa juna waving ta wuce
cikin school . Lokacin da ta shiga class babu mutane da yawa a ciki sosai Sabida
tafiya lap da ake, Daidai lokacin da Eshaal take ‘ko’karin tafiya itama , suna
ganin juna suka sakar wa kansu murmushi “ kwana biyu ina kika shiga ? And I don’t
have your contact balantana ta tanbayi lapiyarki “ cewar Eshaal , itama Abla
murmushi ta ‘kara sakar mata ganin yadda ta damu da rashin zuwan nata “ sorry !
Bani da lapiya ne kwana biyu shiyasa , But Alhamdulillah naji sauki “ in a pity
face Eshaal ta furta “ Eyya sorry bansan baki da Lapiya ba , so ya jikin naki yanzu
?” Ajje Bag d’inta Abla tayi tana furta “ thank you so much Eshaal , naji sau’ki fa
, ina Fanan ? Yau gabaki d’aya banganta ba” daga bayansu sukaji muryarta “ ganinan
wake ne mana?har an fara practical bamu fa , Let’s go idan an fito break sai ayi
hiran sannan kiyi mana bayanin da yasa baki zo school kwana biyu ba “ murmushi
Kawai Abla tayi mata , bayan ta ajje small bag din da little ya bata , basu tsaya
bata lokaci ba suka nufi lap d’in gabaki d’ayansu, sai a lokacin itama fanan tasan
Abla bata da Lapiya , basu tsaya ‘bata lokaci ba suka wuce Lap abunsu. Suna shiga
gabaki d’aya student suka d’ago suna kallansu, musamman Baby da tun shigowarsu take
banka musu harara. Babu Wanda ya kulata a cikin su har Malamin Bio chemistry ya
shigo suka fara practical d’insu , sai da sukayi good 2 period suna abu d’aya kafun
class d’insa ya ‘kare, yanzu further maths ne dasu yanzu , gabaki d’aya class d’in
babu Wanda ya tsaya wasa , gabaki d’aya class aka koma don Dr Adam’s baya shiga
shirgin kowa amma yana Discipline student , shiyasa duk cikin set din su anfi
tsoran sa , gashi mata da yawa suna crushing akansa sabida ba lefi shima kyakkyawa
ne kuma ga iya d’aukar wanka . Suna koma class yana shigowa , kusan lokaci d’aya
suka gaishe sa , inda Abla take zaune ya kalla kafun ya d’auke idanuwansa , “ Duk
Wanda beyi assignment ba ya fitar mun a class “ babu Wanda ya mi’ke a cikin su sai
Abla , sai taji ba dad’i ganin ita kad’ai ce batayi ba, zata fita ya furta “ Go
back and meet me in my office “ okay kawai Abla tace masa ta koma , Sabida present
d’insa a class d’in ne basu fara kus kus ba ganin lokaci d’aya ya bar Abla a class
d’in , ba kamar daba da duk Wanda beyi assignment sai ya hukunta sa , tunda ya fara
teaching yake satar kallan side d’in da Abla take , yana yi yana basarwa har
lokacin sa shima yayi ya bar class d’in. Jakar kayan zakinta ta nuna wa Eshaal “
‘Dauka kafun na dawo! Or zan same ku a capteria okay ?” Girgiza mata kai Eshaal
tayi “ No bari nazo na rakaki “ da haka suka fita suma bayan Fanan da Baby ta ja ,
dan har wani ki shin magana da fanan take musu take . Direct office d’in Dr Adam’s
suka nufa , a waje Eshaal ta tsaya ita kuma Abla ta shiga , babu kowa a office d’in
sai shi, tunda Abla ta shigo yake kallanta har ta ‘karaso Inda yake , a hankali ya
furta “ have a seat “ zama tayi kamar yadda ya umarce tan amma ta kasa sakewa
sabida kallan da yake jefa mata , “ me ya hanaki zuwa makaranta “ kanta a sun kuye
ta furta “ bani da lapiya “ d’au zaro idanuwansa yayi kad’an “ Oh God ai ban sani
ba , are you okay now ? Kin je asibiti ? Kinsha magani ? Babu Inda yake miki ciwo ?
Ko na kira Dr ta Dubaki “ cewar Dr Adam’s , Abla kuwa cikin zuciyar ta sai faman
mitar tanbayoyinsa take “ sai kace ubana” ta fad’a cikin zuciyarta kafun ya bud’e
bakin ta “ No Dr ta dubani a gida , am okay “ duk da hakan sai da ya ‘kara girgiza
mata kai “ let’s go to da clinic “ tsuke face d’inta Abla tayi dan ta gaji da
tanbayoyinsa , a hankali ta furta “ sir lokaci ya kusa yi and banyi break ba “
yadda ta tsuke face d’inta ne yasa ya sakar mata murmushi “ na cika ki da surutu ko
? Okay am sorry ! You can go , idan kina bukatar wani abu let’s me go “ thank you
Kawai Abla tace masa , tai fitowar ta . “ sorry Eshaal na tsayar dake “ babu
komai , Eshaal ta bata amsa , yau basu had’u da Bad Boys ba gabaki d’aya har suka
dawo daga break, Sauran 2 teacher d’insu ne suka shigo , kowa ya gama subject
d’insa zai bar class d’in , yanzu period d’in karshene dasu na Mr jabcon Wato
Biology. Tunda ya shigo class yake bin Abla da kallo sai kace wani tsohon maye , ko
tsoran aka masa ba yayi , musamman kirjinta da yake ta kalla duk da ta saka hijab
amma kamar yake ya d’aga hijab d’in haka yake ji,gabaki d’aya rabi da kwata kallan
Abla ya ke lokacin da yake teaching har ya gama , Abla kuwa ko sau d’aya bata d’ago
da fuskar taba , har ya gama surutunsa kanta na ‘kasa , ko da ya gama haka yace wa
Abla ta same sa a office kafun ya bar class din, karamin tsaki Abla taja , dan
wallahi ta yi rantsuwa babu Inda zataje. Jakarta Eshaal ta mi’ko mata amma Abla ta
girgiza mata kai , “ ki ajje a wajanki “ Youghurt d’aya kawai Abla ta d’auka , “ Ga
fanan na itama kice mata Tasha ,” daga haka suka fito waje , kowa yayi hanyar koma
warsa gida bayan sunyi sallama , Abla tana wucewa itama Alice da tazo makarantar
ita da friend din ta suka wuce amma ta ga Abla , Abla ce bata ganta ba , da Sauri
ta ja burki tana kallan ‘kanın friend d’inta da ya kasance d’aya daga cikin yaran
Bad Boss , Abla ta nuna masa “ kasan waccan yarinyar?” Kansa ya jinjina mata “ yes
ita ce yarinyar da nake fad’a muku “ wata shegiyar dariya Alice ta saki good , take
my phone , inaso kaje ka d’auko mun hotan fuskarta sosai , kana mun wannan aikin
zaka samu 500k “ da Sauri ya karba wayar kuwa ya bi bayan Abla , kallan Alice
‘kawar ta tayi “ friend what are you up to ?” Wata dariyar Alice ta sake “ kin tuna
labarin da na baki?” Kanta ta jinjina mata “ waccan ce yarınyar and I promise my
self duk hanyar da zan bi dan na wulakanta ta sai na bi “ Daidai lokacin da ya dawo
d’auke da wayar Alice “ Done na d’auko miki “ kallan kawar Alice tayi “ ina san
number wannan yaran naki jabcon or what “ Mr jabcon wai ?” Yeh yeh “ Cewar Alice
tana bashi amsa “ suna cikin tafiya Alice ta kira wata number , bansan me aka ce
mata ba sai dariya da naga tayi “ zan turo maka wani hoto akwai abunda nake so kayi
mun, and don’t forget to send your account “ da haka tayi ending calls din tana
sakin murmushin mugunta .

Abla kuwa wajan little dake jiran ta karasa , ita gabaki d’aya bata san lokacin da
akai snapping din taba , basu wani jima ba suka kama hanyar komawa gida suma .

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____33💞

Tun tsawan yinin yau, gabaki d’aya bata sa shi cikin idanunta ba , tun tana guduwa
d’akı dan kar ta gansa har ta defa guduwa tayi zaman ta , sosai Little da prince
suka koya mata subjects d’in da akai batanan , cikin ‘kan’kanin lokaci kuwa ta
fahimta Sabida yadda suke mata bayani dalla dalla yadda zata gane . Sun dad’e a
falourn suna lessions kafin Abla ta koma d’akinta. System d’inta da Little ya bata
ta kunna , haka kawai yau ta shiga youtube, abubuwan da take bu’kata kawai tayi
searching , tana yi tana jotting d’insu cikin ‘karamin jotter , sai data gama kuma
ta koma ‘ban garan girki, a hankali ta fara kallan yadda suke yin abin cinsu , duk
acikin girkin da ta kalla abinci d’aya ne yafi d’aukar hankalinta da taga ansa
Apple pie alamar shine sunan girkin , daki daki take kallan vidoe d’in girkin tana
koyan wasu abubuwan , musamman yadda take da bala’in dan girki.

***Da magrib tayi still Abla bata kaiwa simba abinci ba , gabaki d’aya tana falour
abinta , karfe 9 na dare nayi ta d’akko Youghurt d’inta da sukai sanyi , d’ayan
hannunta kuma d’an ‘karamun robber ne unique colour , gabaki d’aya cikinsa kayan
za’kine a ciki. Sai da ta tabbatar ta kaisu d’aki sannan ta d’auki ruwa shima ta
wuce Bedroom d’inta , bayan tayiwa uncle da su Little sai da safe , dan hatta Bobo
be dawo ba a lokacin.

***The Next Day


Yau babu makaranta shiyasa Abla Tasha baccin ta, sai wajan ‘karfe 10 na safe ta
farka , wanka kawai tayi ta shirya ta sakko ‘kasa , babu kowa a falourn, Dinning ta
wuce kai tsaye tayi serving d’in kanta, gudun kada ta had’u da Big Boss ta koma
d’aki abinta . 12:10pm akayi knocking d’in d’akin ta , “ Am coming “ shine abunda
Kawai tace lokacin data nufi ‘kofar , “ yaya prince ina kwana “ ganin prince tsaye
a bakin ‘kofar ,” Lapiya Lou , yau me ya hanaki fitowa falour? Ko sabida babu
makaranta “ murmushi Abla ta sakar masa “ No ba haka bane , lokacin da na fito ba
kwanan ne shiyasa ban fito ba , amma tunda kun dawo mayafi kawai zan d’auko Nima na
sakko “ kansa ya jinjina mata “ oya kiyi sauri sabida quiz d’in ku za’a fara , shi
wancan ya tafi d’ebo kayan wad’ayi wai yadda zaiji dad’in cinyeki “ ‘yar ‘karamar
dariya Abla tayi jin abinda prince ya fad’a, yana wuce wa itama ta koma d’aki ta
d’akko veil d’inta , white lipgloss ta saka a bakin ta d’an kad’an shima ta sakko
‘kasa . “ kinga har kin dawo amma shi be dawo ba , wannan brother d’in naki sai a
hankali “ zata yi magana suka jiyo muryarsa a bayan su , “Me nayi kuma ? Allah yaya
Prince babu kyau haka fa “, d’an hararar sa prince yayi lokacin da yake zauna wa “
Yaya Little ina kwana?” Murmushi kwance akan face d’insa ya furta “ Ai ni fushi
nake dake , tun safe ban gan kiba sai yanzu”, fiki fiki Abla tayi masa da ido “
kayi hakuri Yaya Little , kaga lokacin da na fito ba kwanan shiyasa na koma d’aki”
Murmushin da ya saka kumatun sa lo’ba wa yayi “ it’s okay! Nima wasa nake , kinga
ankusa fara quiz d’in have a seat, dan yau kam ni ne winner “ dariya prince yayi
masa “ ka shirya kenan ? Mutatis mutandis kai dai sai kaci” d’an turo bakinsa
Little yayi “ Nifa yaya prince nace maka ka dena mun wannan latin maxims d’in ka
bari idan ka shiga court sai ka fara yi musu”, Murmushi suka saki gabaki d’ayansu
lokacin da za’a fara quiz d’in, Biology aka fara, tashin farko Abla taci Little 1-0
Sabida shine Topic d’in da akayi musu jiya amma ta ‘ki fad’a masa sai dariya da
take masa ‘kasa ‘kasa, d’an hararar ta yayi kad’an , ana ‘kara fad’an questions din
ya bud’e baki zai fad’i amsa Abla tayi saurin cewa “ Yaya Little kalla” inda ta
nuna masa ya kalla d’in , be aune ba yaji ta fad’i amsar da yake shirin fad’a ,
hararar ta yayi kafun ya furta “ Lil wannan cheating ne ai , kinsan zan fad’i masa
shine kika sa na kalli wani waje , ban yadda ba’a sake” kamar had’in baki prince da
Abla suka furta “ No “ yaya Lil babu wani cheating, kawai bakasan amsan bane “
pillow d’in gefen sa ya jefo mata “ Ni zaki yi ma wayo ? Don’t mind ,you will
definitely fail “ da haka suka ci gaba da quiz d’in kowa yana so yaji, prince shine
judge d’insu, har aka gama da equal mark suka tashi kowa ya ‘ki barin kowa yayi
winning , Lokacin sallah nayi ,su little suka nufi masallaci ita kuma Abla ta koma
d’aki.

5pm Abla ta ro’ki su Little su nuna mata yadda ake using kayan kitchen bayan ta
fad’a musu abinda ta ke bu’kata , kamar da gaske suma suka ce zasuyi girkin dan
tare zasuyi suna so suga ko Abla za tayi me dad’i da kanta ko kuma sai ta kalli
vidoe , da wannan gasar kowa ya saka apron a jikinsa dan tace musu kunnan su sai
yayi girgid’i, idan ka kalli Prince da Little yadda suka saka Apron d’in kansa sai
mutum yayi dariya dan yau ne karan su na farko , Duk abunda take bu’kata ta lissafo
musu sai da James ya zo ya d’auko musu dan su kansu basusan inda kayan suke ba ,
Apple pie Abla tace musu za’a fara , Little yace a bashi shine zai kwa’ba da
kansa , tunda Abla ta zuba masa flour gabaki d’aya kusan rabinta a jikinsa ya
kwashe ta , idan ka kalli fuskar Little futu futu da flower kamar Wanda yayi dan be
, hatta kansa gabaki d’aya flour ne ,” Ya’ya Little ka ganka kuwa , kamar d’an
Aljani “ dariya prince ya kwashe da ita shima ga knife a hannunsa yana yanka albasa
, ko ‘bareta bayayi yake dadda tsata gida uku, shi kadai sai matsar kwalla yake ,
Abla na gefe tana ‘bare tafarnuwa sai dariya take musu, ganin dariyar da take musu
yayi yawa shima Little ya d’auki flour ya kwatsa mata , a ta kaice sai da suka
‘bata cikin kitchen d’in da flour , ko wannansu kuma kamar sunyi dan be musamman
Prince da Little . 6:10pm suka gama abincin da suke , Abla ta fara gyara kitchen
d’in su kuma suka fito da Abincin zasuje Dinning dashi, kamar daga sama suka ji
sallar Bobo, ga spoon d’in da yake ba’kin Little shi a dole ba zai yi’ke a hannu ba
, be san lokacin da ya saki spoon ya fad’i ’kasa ba ganin Big Boss a bayan Bobo,
sakin baki Bobo yayi yana kallansu ganin duk gabaki d’aya sun ‘bata jikinsu da
flour , shi dariya ma suka bashi, banda Big Boss da yayi mugun had’e masu rai ,
cikin tsokana Bobo ya furta “ mun samu sababbin chefs a gidan kenan?” Fiki fiki
sukayi da idanuwansu “ yaya abinci Kawai mukayi fa kad’an !” Cikin tsare gida Big
Boss ya furta “ yau she aka fara haka ?” Shiru sukayi suna sunkuyar da kansu, taku
d’aya yayi Prince yayi saurin furta “ No yaya bari nayi maka ba yani, we just made
it for fun..!” Kallan da ya jefa wa prince ne yayi saurin sun kuyar da kansa ‘kasa
“ For fun right?Good !” A na tsaka da haka itama Abla ta fito jikinta futu futu da
flour ,” even you Sister ?” Cewar Bobo yana d’an ware eyes d’insa sabida mamaki,
har bawa zuciyarta tayi “ shikenan na kad’e har ganye na “ cewar Abla cikin
zuciyarta, sau d’aya Big Boss ya je fa musu wani mugun kallo, kafin ya juyar da
kallansa zuwa Bobo, d’an girgiza kansa Bobo yayi kad’an kafun yayi danne danne a
wayar sa , cikin mintunan da basu fi biyu ba James ya shigo falourn cikin girmamawa
, a fuske Big Boss ya furta “ The menu” James ya gane me yake nufi shiyasa cikin
girmamawa ya furta “ yes sir” yana nufar hanyar kitchen , be jima ba ya dawo d’auke
da wani Book , fiki fiki Little yayi da idanu, ko kallan sa Big Boss be yi ba sai
ma umarnin sa da ya daki kun nuwansu “ from now henceforth, kune chefs d’in
gidan,all the details of food , one mistake hmm “ ya na kai karshen maganar sa yayi
hanyar part d’insa , da sauri Little ya furta “ Yaya Sister tana zuwa makaranta “
da katawa yayi da tafiyar kafun ya d’an jiyo da kallansa side d’in Little “ And ?”
Da sauri Little ya girgiza masa kai “ Zamu yi as you wished “ , yana barin wajan
suka kalli Bobo gabaki d’ayan su , murmushi ya sakar musu “ Ni babu ruwa na , ku
dena kallo na , ai you guys kun iya girki tun daga shigar jikinsu” yaya cewar
little “ babu wani yaya , yanzu za’ayi sallar magrib kuje ku canza kayan jikin ku ,
Lil sister aikin yayi kyau daman ya kamata su iya , Dan ko ruwan zafi basu iya
dafawa “ yana kaiwa nan shima ya wuce part d’insa , kallan juna sukai su uku ganin
punishment d’in da suka janyo wa kansu, ga kuma yadda ko wannan su yayi futu futu
kamar ‘yan bori yasa ba shiri suka ‘kyal’kyale da dariya , sai da sukayi dariya mai
isar su sannan kowa ya wuce part d’insa ganin an kusa tayar da Sallah.
****Abla tana koma wa d’aki wanka tayi ta tsaftace jikin ta tunda bata da tsarki, a
maimakon ta fito falo sai ta ‘kara d’auko notes d’in ta na makaranta tana ‘kara
duddu basu, abunda bata fahimta ba sai ta d’anyi d’igo a wajan , sai da ta gama
gabaki d’aya sannan ta fara searching abubuwan da bata gane ba , tun bata gane wa
har ta fahimta gabaki d’aya .

9:00pm suka fito cin abinci ban da Big Boss , cikin tsokana Uncle yane lumshe
idanuwan sa , wannan ‘kamshin abinci daga ina yake fitowa , shima Bobo murmushi
yayi wa Uncle “ Uncle yaran ka sunyi hankali ai tunda gashi sun iya abinci kaga
James ya huta na kwana biyu” kamar zai kuka Little ya furta “ Haba Yaya kai da zaka
bawa Yaya Big Boss hakuri ? Amma shi kenan nasan Uncle d’ina zai bashi “ tun kafin
ya ‘karasa Uncle yace “ Wana Uncle d’in ? Ai ko ni bazan bashi hakuri ba , yadda
nake jin ‘kamshin girkin nan har kwakwalwata nasan ba ‘karamun dad’i zai yi ba ,
yanzu Kawai ku tashi kuyi serving d’in mu “, kallan sa Prince yayi “ But Uncle Yaya
be fito ba “ da hannu Uncle ya nuna masa hanya “ maza je ka fad’a masa ya sakko ya
d’an d’ana abincin ku , nasan har rewards zai basu” yadda Prince ya zazzaro idone
ya saka Bobo girgiza kansa ,” Shima ya san sauran ne yayi gigin zuwa , mu da muke
bayin Allah talakawa azu ba mana abincin nan kafun ‘ya’yan cikin mu su fito saurin
toshe bakinta Abla tayi Sabida dariyar da taji tana ‘ko’karin kwace mata , da haka
suka wuce Dinning gabaki d’ayansu, Abla ce tayi serving d’in su. Tun kafun su fara
d’an d’ana abincin suka fara santi, Little aka fara sawa yayi testing d’in abinci ,
shima da farko kamar bazai ci ba har yana ya mutsa fuskarsa, tun da yaci 1 spoon
yaji yadda abinci yayi mugun yi masa dad’i ko uffan be ce musu ba ya cigaba da cin
abincin sa . Ganin hakan yasa suma suka soma cin abincin , babu Wanda beyi mamaki
yadda d’an d’ana girki ya fito ba kamar wacce tayi rayuwa wajan masu girkin, shi
kansa Bobo be san lokacin da ya furta “ Amma Sister daman tun tuni kin iya abincin
nan shine ba kya mana ?” Murmushi Abla ta saki dan har ya d’an bata kunya “ Yaya ba
fa ita kad’ai tayi ba , muma har da namu contribution d’in “ , hararar su Bobo yayi
“ contribu ba contribution ba “ shima Uncle sosai ya yaba da girkin har yana
tsokanar su zai saka Big Boss ya bar musu punishment d’in girki har na tsawan
shekara suna yi musu” bud’ar bakin Bobo ya furta “ Don’t mind Uncle ai daga yanzu
sun zama Chief bawai na tsawan shekara ba , prince da ya fi kowa tsanar aiki ya
furta “ Haba Yaya Bobo fisabilillahi, I swear lokacin da nake yanka onion lokacin
da naji idanuwana suna hajijiya ‘karar harbi kawai nake ji cikin kunne na “ gabaki
d’aya dariya suka kwashe da shi “ ko jira ga kake ji sai ka yanka onion , Sister
idan akwai pepper ma duk ki basa yayi, idan bakuyi wasa ba Restaurant za’a bud’e
muku ku soma girki” ‘bim Prince ya rufe bakin sa yana cuno baki , Abla da Little
sai faman dariya suke masa ‘kasa ‘kasa . Ana kammala cin abincin falour aka koma ,
ko hirar minti 30 basu yi kowa ya nufi d’akin sa musamman Little da Prince da suke
rakin bayan su zai cire Abla ta yau dare su , sun d’auka girkin ba wahala amma ta
sasu suna ciwan baya, rakı kala kala kamar ba maza ba , suna shiga d’aki tunda
sukayi wanka suka shirya ko wannan su ya d’ane Bed d’insa .

WASHE GARI
Gabaki d’ayan su da wuri suka tashi tun bayan sallar asuba da sukayi suka fad’a
kitchen tun da Big Boss ya mayar dasu chiefs d’in gidan, prince sai kunbura baki
yake shi a dole ya gaji , da yasan tsautsayin da zai hau kansu da bayi gigin zuwa
Kitchen d’inta , a fakaice Little yayi mata rad’a a kunne kafun su had’a baki
lokaci d’aya su furta “ Chief Yaya Prince “ hararar su yayi , ya’ki kula su kuma ,
wani idea ne ya fad’o wa Abla ta saka suka suka soya plantain, sai Chips da musu
kamar sugar Nigeria, Ga scrambled eggs da tayi musu da yaji Kayan ‘kamshi da albasa
, farfesu Little yace yana so , duk da babu kayan had’in da zatayi na Nigeria amma
tayi amsa irin yadda taga ni a vidoe , tun kafun a gama abinci suma soma nishi dan
hatta Clam Chowder sai da sukayi da Bagel and Lox . Suna gama suka jera abincin su
a dinning daman ko gigin fad’a wa Big Boss babu Wanda yayi , a wannan karan ma
haka su Uncle suka dunga santin abincin su , abu kad’an suce shikenan sun samu
chefs tunda gabaki d’aya sunsan efforts d’in Abla ne tunda Bobo yace ko ruwan zafi
su Little basu iya tafasawa ba.
Da rana ma the same abunda ya faru kenan su sukayi lunch , dad’in su d’aya ma Big
boss da Bobo basa cikin gidan shiyasa sai da suka gama game d’insu san ransu kafun
suyi lunch d’insu.

8:30pm nayi Little yace yau fruit za’a sha, daman Yaya Big Boss yace su dunga motsa
jiki bayana uban chocolate da snacks da ya kai d’akin sa , shiru kawai Bobo yayi
musu Sabida lokacin Big Boss be dawo cikin gidan ba . 9:10 nayi Little ya gudu
d’aki sabida karma su had’u da yaya, yace musu bacci yake ji, shima prince da Abla
guduwa d’aki sukai kai hukuncin ya dawo kansu.

MONDAY

Da wuri Abla tayi shirin makaranta , bata dad’e basu Little sukai dropping d’inta a
makaranta, tana shiga class ta tarar da Eshaal tana duba Books d’inta “ Hey” cewar
Eshaal , itama Abla “ Hey “d’in tace mata tana zama , juyo mata da Book d’in Eshaal
tayi “ Thanks God kinzo , kinga sai kiyi mun bayanin wannan topic d’in dan naga
wannan karan da gaske so kike ki ‘kwace mun position “ murmushi kawai Abla tayi
mata wai zata kwace mata position , bayanin topic d’in tayi mata dallah dallah
yadda zata fahimta, suna cikin yi fanan itama ta shigo class d’in ganin suna karatu
itama tayi saurin ‘kara sowa wajan su “ yanzu tsakani da Allah haka zamuyi daku ?
Aushe kuna nan kuna karatu salan in anzo exam ku barni da zare ido” d’an girgiza
kanta Abla tayi tana murmushi da kuma suka cigaba da d’akko topic d’in da basu gane
ba , Wanda ya fi iyawa a cikin su yana yi musu ba yani. Teacher na shigowa kowa ya
nufi seat d’insa , Mss Atem ce ta fara shigowa class d’in, lokacin ta nayi ta fita
sauran teacher suka shigo har zuwa lokacin break. Tsakanin ta da Baby sai harara da
ba’ka’ken magana amma ko sau d’ay bata ta’ba tanka mata ba sai dai tayi murmushi.
Suna shiga capteria order abunda suke so sukai su uku dan yanzu Baby gaba ta farayi
da Fanan tunda taga tana yiwa su Abla magana . Suna cikin cin abincin su Bad Boys
suka shigo student d’in Wajan suka fara kururuwan kiran su nan su , dan ko ba komai
idan a ka gansu dole ne a saka wani yin abu su kuma abunda suka fi enjoying Kenan
shiyasa suke ‘kaunar Bad Boys su shigo ko dan dramer da zasu gani.

Table d’in su Abla MAI DALA ya nufa , d’an hararar sa Fanan tayi “ Me kuma kazo yi
mana anan , kaman ta warning d’in da Nani tayi maka ko?” Tsaki Mai Dala yayi bayan
ya ja kujerar da tayi ragowa a wajan su “ koma Menene ni ba Wajan ki nazo ba , so
better stay out of me , idan ba haka ba wallahi yanzu na saka ai miki wula’kanci “
hannu ya mi’kawa Abla yana furta “ Hey” ko inuwar da ta kwa sosa Abla bata kalla ba
, balan tana ya saka ran zasu gaisa d’in, shiru Fanan tayi masa dan ta kula itama
Abla ba kanwar lasa bace “ ina miki magana kina share ni , ba lalla’ba ki nazo yi
ba , nazo miki da umarnin kar’bar soyayyata , ko ina so ko ba kyaso , yanzu ma
Number wayan ki na zo ki bani dan bani da lokaci”, hauka Abla ta watsa masa shi
yasa hakan ya tun zurashi ya daka mata tsawa yana ‘ko’karin ri’ke mata hannu, cikin
had’e rai ta d’auki juice din gabanta orange ta watsa masa a farar white uniform
d’insa , gabaki d’aya wajan shiri ya d’auka sabida kowa yana so yana reaction d’in
Mai Dala , kallan banza Abla ta je fa masa “ Duk haukan ka , Duk rashin mutum cinka
kasan a inda zaka dunga yinsu , idan kanaji da rashin mutumci akwai Wanda suka fika
, idan wukanci kake ji dashi akwai Wanda suka danne ka iya rashin wula’kanci,
wannan ne last warning d’ina akan ka , duk lokacin da ‘kaza min hannun ka yayi
gigin ta’ bani “ tana kai karshen maganar ta tayi wucewar ta , a bokansa zasu bita
yayi saurin dakatar dasu “ wannan wasan ba naku bane , sai na wula’kanta ta , irin
wula’kancin da bata ta’ba zato ba , sai ta san tayi kuskuran shigowa gonar Mai Dala
“ da haka ya nufi hanyar fita a fusace suma friends dinsa suka mara masa baya .
Hankalin su Fanan ba ‘karamin tashi yayi ba dan sun san tunda Mai Dala ya fad’a
hakan sai yayin da gaske. Har aka tashi suna zuba ido suga ne zaiyi amma shiru.
Lokacin da Little ya zo d’aukan tane suka had’u da su Fanan , cikin fara’a ya furta
“ Lil wad’an nan ne sababbin friends d’inki?” Kanta Abla ta jinjina masa tana
murmushi “ that’s good , What’s your name ?” Ya ‘karasa yana nuna su , Fanan ce ta
fara furta “ sunana Fanan” kafun Eshaal ma ta fad’a masa sunan sa “ sunayen ku masu
dad’i hope babu Wanda yake takurawa Lil a makaranta, if they is any kawai ku fad’a
mun “ kallan suna sukai kafin su d’an girgiza masa kai alamar ba kowa , da haka
sukayi sallama su Fanan suka wuce suma su Little suka kama hanyar gida .

*******Tun daga wannan lokacin wani irin sha’kuwa yashiga tsakanin Eshaal , Fanan
da kuma Abla , kusan duk inda kaga d’aya to zakaga sauran suna wajan, itama Fanan
yanzu ta watsar da Baby sabida wula’kancin da take mata . Ga wani irin amin ta da
ya shiga tsakaninsu musamman da gabaki d’ayan su masu san karatu ne . Duk lokacin
da Little ya zo d’aukar ya sai sun gaisa dashi har suka zama kamar yan uwa suma duk
lokacin da zasu tafi sai ya tsokane su.

Yau ya kamata 3 weeks da zuwan Abla makaranta , kusan satı d’aya da ‘yan kwanaki
kenan bata saka Big Boss a cikin idanuwan taba , duk lokacin da yake gida tayi
gigin yin kuskure daman tasan sai ta d’auki haukan ta a hannu.

Gabaki d’aya su ukun suna zaune a class bayan teacher ta fita suna jiran last
period d’in da zasuyi suka ji an shigo cikin class d’in, ba kowa bane face Mr
Jabcon, kusan satı 2 Kenan yana kiran Abla office d’insa amma bata zuwa , last
kiran da yayi mata ne lokacin da taje yake ‘ko’karin jire belt d’in jikinsa Abla ta
hanka d’asa ta gudu hakan ne ya haifar masa da gocewar ‘kashi a ‘kafa shiyasa yayi
Alwashin duk hanyar da zai bi sai ya wula’kanta Abla. Kamar da gaske ya fara yi
musu teaching d’in da ya kawo sa , ana saura 5 minutes a tashi ya fito da wasu ‘yan
envelope masu d’auke da wasu ‘kananan hotuna , ganin suna da yawa ne yasa ya watsa
su tare da umartan kowa ya d’auka , d’aukan kuwa sukai suna duba abunda yake cikin
hotan, duk Wanda ya kalla sai ya jiyo ya kalli Abla sannan su fara ‘kus’kus a
tsakaninsu, lokaci d’aya hayaniya ya fara tashi a cikin ajin , haka Kawai Abla taji
zuciyar ta tabuga da ‘karfi, ganin surutun yayi yawa yasa itama Fanan d’aukar hotan
, tana ganin jikinta ya soma rawa tayi saurin yaddar da hotan tana kallan Abla , “
Menene ?” Cewar Eshaal dan gabaki d’aya Abla ta kasa motsawa ma Sabida yadda taji
‘kirjin ta yana bugawa , inda suke Mr jabcon ya ‘karaso kafun ya d’aga murya yana
nuna musu Abla “ kunga wannan hotan ? Lokacin da take iskancin da wani ne aka
d’auka, da Sauri kirjin Abla ya fara har bawa cikin sauri ta d’auki hotan guda
d’aya kafin ta saki wani ihu tana jefar da hotan “ ‘karya ne , ‘karya ne wannan ,
bani bace ba wallahi “ lokaci d’aya Abla ta fashe da wani matsanan cikin kukan
ganin hotan ta ‘karara a tsirara jikin wani na miji ga hannunsa d’aya da ya d’ora
kan breast d’inta , ita kuma Abla tana masa murmushi, ‘kin d’aukar hotan Eshaal
tayi ganin itama jikinta ya soma rawa lokaci guda.

Allah sarki Abla sai girgiza musu kai take ta kasa magana ma sabida yadda kirjinta
yayi mata nauyi , ga jabcon da yake ta maimaita kalmar prostitute ce Abla , da
sauri ta kama hanyar fita a guje ko school bag d’in ta bata d’auka ba , zata fita
aka turo ‘kofar a jikin, LG ce a tsaye cikin kakin sojoji, tana ganin Abla ta
tsinka mata mari “ prostitute , na dad’e da fahimtar cewa ke karuwa ce daman tun
tuni , kinzo kin fake sabida my man? You as a prostitute ? Matar da tayi karuwanci
a Garinsu, “ sai kuma cikin d’aga murya ta nuna musu Abla “ wannan da kuke gani
prostitution take yi , har aka siyar da ita tazo ‘kasar nan , duk Wanda ya ra’be
tama zai ta koya masa ne “ cikin kuka Abla ta bangaje ta ta gudu, suma Eshaal da
fanan bags dinta suka d’aukar mata sukayi saurin bin bayanta suma ko wanne da
kwalla a idanunsu dan sun san sharri ake mata musamman jabcon da Eshaal ta lura
dashi yana yawan kallan kirjin Abla.

Abla kuwa da iya ‘karfin ta take gudu gabaki d’aya bata san Inda zata take saka
‘kafar taba , kuka Kawai take ido arufe , saura kad’an su Little su kad’eta. Ganin
gadda take kuka hankali a tashe ne ya d’aga masa hankali gashi ta ‘kiyi wa kowa
magana , mota kawai ta shiga ta sunkuyar da kanta tana ‘kara fashewa da kuka ,
shima Little kamar zai yi kuka ya tanbayesu abunda ya faru , babu abunda suka ‘boye
masa , gabaki d’aya sai da suka zayyane masa komai , wani irin kwallan ‘bakin
cikine suka tarar wa Little a ido da ‘karfi ya furta “My sister ?” Har yana
tsoratar dasu fanan, Rai a ‘bace bai kuma cewa su Eshaal komai ya kar’bi jakarta,
shi kad’ai sai faman girgiza kansa yake , a mota babu yadda beyi da Abla tayi shiru
ba amma kamar ‘kara tun zura ta yake dan jikinta har ya d’au ki wani irin zafi
Sabida kukan da tasha, hankali a tashe Little yake kallan ta ganin yanayin da be
ta’ba ganin Abla a ciki ba , tun kafun ya ‘karasa gida ya kira Yaya Bobo ya fashe
masa da kuka , tun kafin Bobo ya tanbayesa kuma ya kashe kiransa , lokacin fita
Bobo zai yi har ya shiga mota ya fita ya koma cikin gida hankali a tashe .

Big Boss na tsaye shima yana shirin fita motocin su Abla suka shigo cikin gidan ,
babu Wanda ta kalla ta ruga cikin gida a guje tana kuka shima Little cikin Tashin
hankali ya bi bayanta.

Abla ta shiga cikin gida babu Wanda ta kalla , tunda ta saka gudu sai saurin kukan
ta da suke ji, tana shiga cikin d’aki toilet ta kulle ‘kofar tare da sakar wa Kant
ruwa me sanyi, ita kadai sai kuka take kamar ‘kirjinta zai fito , idanuwanta har
sun kunbura , ga mugun ja da face d’inta tayi.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____34💞

“Me ya faru ? “Cewar Bobo ganin yadda hankalin Little ya tashi lokacin da ya shigo
cikin falourn , ga Abla da itama ta wuce ta na kuka , kasa magana Little yayi sai
kansa da yake girgiza musu , cikin Sauri ya bi bayan Abla , shima prince da uncle
bin bayan sa sukai dan ga baki d’aya little ya tayar musu da hankali, fahimtar
kamar da matsala yasa Bobo bin bayansu banda Big Boss da tun bayan kallo d’aya da
yayiwa Little be ‘kara kallansa ba, har yanzu yana tsaye a inda yake sai ma folding
hannunsa da yayi waje d’aya , face d’insa kamar kullum babu fara’a kwata kwata a
kanta.
Little be zame ko ina ba sai d’akin Abla , cikin Sauri ya shiga Bedroom
d’inta ganin ‘kofar d’akin abud’e amma gabaki d’aya bata cikin d’akin , ‘karar
ruwa da yaji a toilet da kukan ta ne yasa yayi saurin nufar ‘kofar kamar zaiyi kuka
yasan har yanzu kuka take, knocking d’in ’kofar ya somayi da d’an ’karfi “ Lil !
Lil ! Please open the door let’s talk , please ki kwantar da hankalin ki , komai
zai dai dai ta“, shurun da yaji babu amsa ne yasa hankalinsa ‘kara tashi Daidai
lokacin da su Bobo suka shigo cikin d’akin suma “ Please sister na ro’ke ki , ki
bud’e ’kofa zaki iya raunata kanki “ ya kasa maganar sa shima yana hawaye dan har
cikin zuciyarsa yake jin wani irin d’aci da ba’kin cikin abunda akai wa Lil
d’insa , kallan sa Bobo yayi cikin d’an d’aga murya ya furta “ I’m asking you kamun
bayani , me ya faru ? Wani ne ya ‘bata mata rai ?” Kansa little ya girgiza masa
hawayen face d’insa basu dena sakkowa ba , hankali a tashe prince ya furta “ Dan
Allah little ka fad’a mana ka ta yar mana da hankali , and kaga may be tana using
bathroom ne ma ba wani abun bane “ kuka little ya fashe musu dashi yana nunawa Bobo
‘kofar toilet d’in” No yaya zan muku bayani daga baya , just please yaya ku bud’e
’kofar nan , zata iya jiwa kanta rauni , d’an Allah yaya “ ya ‘karasa yana ‘kara
sakin wani kukan dai dai lokacin da suka ji kamar fad’uwar abu a cikin toilet d’in,
lokaci d’aya suka soma bugun toilet din suna kiran sunan ta “ Sister ? Sister ?
Sister ?” amma babu amsa, Shirun da suka jine ya Matu’kar tayar musu da hankali ,
da iya ‘karfinsa Bobo ya saka ya daki ‘kofar da kafad’unsa , amma kamar Wanda ya
daki kataho ko motsi batayi ba, a karo na biyu ya ‘kara da kar ‘kofar da ta d’an
motsa kad’an , kafad’unsa ya ta’ba tare da kallan Little da face d’insa tayi ja
sosai , cikin ‘yar damuwa Bobo ya furta “ called your brother “ da sauri Little ya
nufi down stairs har lokacin Big Boss na tsaye Inda suka barsa , Little yana
ganinsa yaji wani saban kukan na zuwar masa da Sauri yayi hugging d’in Big Boss
yana yin kukan sa ‘kasa ‘kasa , lumshe eyes d’insa Big Boss yayi Sabida yadda yaji
zuciyar Little ya bugu da Sauri kamar ba zai yi magana ba sai kuma cikin ya mutsa
face ya furta “ what happen?”
A hankali Little ya sauke ajiyar zuciya , yasani ko be fad’a wa kowa ba dole zai
fada wa Big Boss , shiyasa cikin sanyin jiki ya labartawa Big Boss abunda ya faru ,
tun lokacin da ya ganta tana kuka da bayanin da su Eshaal sukai masa , shiru Big
Boss yayi batare da ya tanka ba sai ma d’an ta’be bakinsa da yayi kad’an , kamar
wanda aka saka dole ya furta “ wannan ya saka kuka ?” Kansa Little ya jinjina masa
wasu hawayen na ‘kara taruwa cikin eyes dinsa , Ya bud’e baki zai yi magana sai ya
tuno da abunda ya sakko dashi ‘kasa , cikin kwantar da murya Little ya furta “ yaya
please ‘kofar toilet d’inta aruf…e ta..ke” kallan da Big Boss yayi masa ne ya sa
ragowar maganar sa ta rarrabe , cikin rashin damuwa Big Boss ya furta “ And ?”
Hawayen sa Little ya share ,” Yaya Dan Allah ba danni ba , ka bud’e ’kofar toilet
d’inta , zata iya jiwa kanta rauni” kallan diamond watched dinsa Big Boss yayi
kafun ya d’an ya mutsa face d’insa kad’an “ am going out “, shine kad’ai abunda Big
Boss ya iya furtawa , cikin Sauri Little ya haura sama yana goge kwalla har ya wuce
d’akin Abla, yana shiga yatarar da har lokacin Bobo na du’kar ’kofar amma ta ki
bud’uwa , almost 2 minutes gabaki d’ayansu suka juyo saitin bakin ‘kofa sabida
‘kamshin turaran Wanda basu ta’ba Saran zai shigo d’in ba, Little har da murnarsa
ganin Big Boss a bakin ‘kofar Abla amma duk Wanda yaga face d’insa zai ganta a
had’e sama da sauran lokuta, babu Wanda ya kalla a cikin su har ya ‘karaso cikin
d’akin, gabaki d’aya matsa masa hanya sukai har ya ‘karaso wajan ‘kofar, da iya
‘karfin da Allah yayi musu shida Bobo suka daki ‘kofar da ‘karfin gaske , amma
Sabida ‘koface bata wasa ba yasa ta motsa Batare da ta bud’u ba , a karo na biyu
suka kara dakar ‘kofar wannan karan sai data d’anyi ’Kara , a karo na uku da Big
Boss yayi mata wani irin Wawan bugu ‘kofar ta jijjige gabaki d’ayan ta , rai a
‘bace Big Boss ya hankad’a ‘kofar ciki da har saida Bobo yayi saurin dafe ta , daga
inda yake yana iya hango ta cikin jacuzzi, da alama ruwa ta sakar wa kanta ,
gabaki d’aya bata motsi gashi Jacuzzin ya cika taf da ruwa har yana zuba ga abun
side d’in jacuzzin da ya faffashe a ‘kasa , ransa ba ‘karamun ‘baci yayi ba
Sabida ‘bata lokacin sa da yayi, d’an ’karamun tsaki ya saki kad’an lokacin da yake
‘karasowa cikin toilet d’in , da hannu d’aya ya d’ago da ita cikin ruwan , Sabida
yadda jikin ta ya saki gabaki d’aya baya tayi zata fad’i yayi saurin taro ta da
d’ayan hannun nasa , d’aya daga cikin ‘bathrobe d’in cikin toilet d’in ya na d’a
mata tare da d’aukar ta gabaki d’aya kamar wata Baby, babu Wanda ya kalla a cikin
har ya kwantar da ita kan gadon d’akin, cikin Sauri Little ya ‘karaso wajan gadon
ganin Lil d’insa bata motsi, kamar me rad’a ya furta sunan wata allura , Bobo dake
bayansu jinjina masa kai kawai yayi ya juya , shima prince da uncle juyawa sukai
suka bar d’akin, yayi saura Big Boss da ke tsaye lumshe da idanuwansa sai kuma
Little da ya ‘kurawa Abla idanuwa shima kamar zaiyi kuka Sabida yadda eyes d’insa
suka fara red . Cikin ‘kan’kanin lokaci Bobo ya dawo d’auke da wani ‘karamun kit
ya mi’kawa Big Boss tare da allura da ya fad’a , shima little yana ganin allurar ya
fara kulle eyes dinsa dan harga Allah baya san abunda zai ‘kara ta’bata , ganin
yadda yake faman kawar da kaine yasaka Bobo kama hannunsa suka bar d’akın. Kusan 2
minutes yana tsaye a wajan be motsa daga inda yake ba , a hankali ya d’auko allurar
tare da had’a ta yadda yake so , hannu d’aya ya kai Daidai saitin hancinta, yadda
yaji nunfashinta baya fitowa ne yasa ya d’an matsa cikin ta kad’an batare da ya
kalle taba , lokaci d’aya Abla ta fara fito da ruwa daga bakin ta tana tari , tun
tanayi da ‘karfi ‘karfi har ta fara ajiyar zuciya kafun ta ‘kara fashewa da kuka
tuno abunda ya faru, ko uffan be ce mata ba ya d’auko allurar zai mata , sai
alokacin Abla ta farga, yadda ta gansa ne ya ‘kara firgita ta ga hawaye sun ‘bata
mata face d’inta sosai , cikin muryar kuka ta furta “ Ni banaso Dan Allah kar kayi
mun allura “ ta ‘karasa fad’a tana yarfa hannayen ta , be bi ta kanta ba ya ‘kara
d’aga allurar zai yi mata ta ‘kara fashe masa da kuka , a wannan karan sosai ransa
ya ‘baci, yadda take kukan ne ya ‘kara harzu’kashi, cikin tsananin ‘bacin rai ya
daka mata tsawa , ita kanta bata san lokacin da ta had’iye kukan da take ba , sai
idanuwa da take zazzaro wa , har ya gama allurar bata sani ba sai da ya zuba mata
rikitattun idanuwansa masu ladaftar da mutane , cikin kausash shiyar murya ya furta
“ Just 10 minutes na baki ki sakko , idan kin isa ki ‘kara even a minutes “. Yana
Kai ‘karshen zancan sa ya bar d’akın. Da kallo Abla ta bishi har ya fice daga cikin
d’akin ga hawayen ta har lokacin ya ‘ki tsayuwa , ganin time d’in da ya bata ya
fara yasa cikin sanyin jiki ta koma ta watsa ruwa tare da saka wata doguwar riga me
kauri Sabida sanyin da take ji a cikinta .

A hankali Abla take sakkowa daga kan stairs din cikin sauri tun kafun ta ‘karaso
little ya nufi inda take ,” Lil are you okay ?” Ko magana ta kasa sai kanta da ta
jijjiga masa alamar eh , hannunta ya kama suka ‘karaso cikin falourn, suma gabaki
d’aya su Bobo ita suke kallo banda Big Boss da gabaki d’aya baya cikin falourn ,
cikin d’an fad’a fad’a Bobo ya furta “Karka bari na ‘kara tanbayar ka , Little me
akai mata ? “Kallan Abla Little yayi ganin lokaci d’aya ta soma hawaye ga kanta
data sun kuyar ‘kasa , a hankali little ya bud’e bakinsa tare da labarta musu
gabaki d’aya abunda ya faru, wani irin shegen murmushi Bobo ya saki kafun ya furta
“ Woow!, wannan ne dalilin da yasa kika tayar da hankalin ki ?” Cewar Bobo yana
kallan Abla , shima face d’insa d’auke da tsantsan ‘bacin rai , sai kuma cikin cool
voice ya furta “it’s okay , kukan ya isa haka ! Wannan ba babban dalilin da zaisa
ki kulle kanki a toilet ba , kinsan da kin ‘kara wasu minutes din shikenan sai dai
wani labarin ake ?” Ya fad’a mata cikin d’an ’bacin rai , da Sauri Abla ta girgiza
masa kai , a hankali ta furta “ Kuyi hakuri “, shiru kawai Bobo yayi mata, shi
kansa uncle mamakin Wanda yayi wannan aikan, banda prince da wata shegiyar dariyar
mugunta da ta so kamasa dan yadda yaga mood d’in Yaya Bobo yasan ba ‘karamun cin
‘kaniyar ko wana d’an iska zai yi ba .
A hankali yake takowa zuwa cikin falourn , gabaki d’aya ya canza shigar d’azu
da alama wani saban wankan ya sake , daddad’an ‘kamshin turaransa da suka ji ne ya
ankarar dasu fitowar sa , face d’insa gabaki d’aya a had’e take har ya ‘karaso
cikin falourn, Daidai kan one sitter ya zauna tare da crossing leg d’insa , ‘kara
sunkuyar da kanta ‘kasa Abla tayi , kamar bazai yi magana ba sai kuma ya furta
“what happen? “ Little ya bud’e baki zai bashi amsa shima ya samu kasan nashi
kallan, kamar zata yi kuka ta labarta musu gabaki d’aya abunda ya faru, d’an ta’be
bakinsa Big Boss yayi kad’an kafun ya furta “ wannan abun ne yasa kika sa muka
‘balla ‘kofa ?”ya mutsa fuska Abla tayi zata sake wani kukan ya d’an daka mata
tsawa , a hankali Abla ta furta “ kayi hakuri”, wani ‘karamun locker Big Boss ya
bud’e tare da ciro wasu gun a ciki guda uku yana sakawa kan center “ idan kina san
ki mutu basai kin saka wa kanki ruwa ba , ga gun nan ko wanne akwai bullet a ciki,
idan basuyi miki ba , zaki iya hawa last floor sai ki fad’o , it’s most be easier
ki mutu”, da Sauri uncle da Bobo suka furta “ Please Big Boss ….” Yanzu ma lips
dinsa ya d’an motsa kad’an batare da ya kallesu ba ya furtawa Abla “ Get lost “ da
Sauri Abla ta mi’ke ko kallan inda yake batayi ba tayi wucewarta, sai da ta shige
d’aki sannan kukan da take so ya zo mata, wato in mutuwa zatayi ma taje ta mutu ?”
Wannan maganar tasa sosai ta ba’kanta mata rai shiyasa bata ‘kara Tuna’nın sakkowa
ba tayi zamanta a d’aki .
Sai da Bobo yaga ‘bacewar ta ya kalli Big Boss da ya mi’ke tsaye “ Haba
please? It can hurt her more ! Why please ?” Dakatar Dashi Big Boss yayi ta hanyar
furta “ Am out “ yana kai ‘Karshen maganar sa ya bar falour shima . Gashin kansa
Bobo ya ta’ba , a hankali ya furta “ why please ?” ‘Dan karamun murmushi Uncle ya
saki “ it’s okay Bobo , yasan yanzu kai ma akwai wajan da kake san zuwa , inasan
kumar maganar for now ! Okay ?” Kansa Bobo ya jinjina masa shima kafun ya bar
falourn, kallansa Little da prince sukai “ uncle yanzu shikenan guy d’in can ya ci
bulus?”d’an harararsu uncle yayi lokacin da yake mi’kewa , “ Me isa baku tanbaye su
ba har suka fita ?” Haba mana uncle “ cewar prince “ nace abar maganar nan “ daga
haka ya bar falour , jijjiga kai prince yayi “ you know what Little ? Inda yaya zai
bani Victor da Anthony ko hmm” a hankali Little ya furta “ Sabida duk a jikin
sojojin gidan right side d’in Yaya Big Boss sun fi kowa iya hoto ki ?” Kansa Prince
ya jinjina masa .
Yau gabaki d’aya basuyi hira ba sabida basa cikin good mood d’insu, kowa d’aki ya
koma abunsa, har dare Abla tana d’aki sai da little da prince suka lalla’bata
sannan ta iya cin abincin da ko spoon 10 be kai ba, still tana ‘ko’karin komawa su
little suka hanata sabida yadda gabaki d’aya ta sauya musu ko magana batayi sai dai
ta amsa musu da eh ko ah’ah,ko 9 batayiba Abla ta koma d’akin dan ko san kallan Big
Boss yau bata sanyi.
Har wajan karfe 12 idan Abla biyu abunda jabcon yayi mata yayi mugun tsaya
mata arai , ba shi kad’ai ba , hatta LG ta gane ta , wani irin tsanar tane ya dar
sar mata a zuciya na ‘ka zafin karuwanci da sukai mata , duk lokacin da ta kulle
eyes d’inta hango yadda mutane suke kallan hotan da aka sa fuskarta a jiki take.
Murmushi Abla ta saki me ciwo tare da d’aga hannunta sama “ Allah kafi kowa sanin
Daidai da kuskure, Allah kana ganin halin da baiwar ka take ciki , Allah na ro’ke
ka , ka saka mun ta hanyar da basu ta’ba zato ko tsammani ba , Allah na ro’ke ka
duk Wanda yake da hannu akan sharrin da akai mun Allah ka saka mun “ tanayi tana
kuka , har wajan ‘karfe d’aya idan ta biyu , cikin ‘kan’kanin lokaci zazzafan
zazza’bi ya rufe ta , da ‘kar bacci ‘barawo ya d’auke ta.
Washe gari ma da zazzafan zazza’bi Abla ta tashi amma tana iya bakin ‘ko’karin ta
wajan ‘boye hakan, komai cikin sanyi take yinsa, ji take kamar kar taje makarantar
Sabida bata san wani irin fassara za’a yi mata ba , cikin Sauri take yin komai har
ta gama shiryawa cikin uniform d’inta , amma duk Wanda ya kalli face d’in ta zai ga
rashin walwalar dake tattare da ita.

Tana sakkowa down stairs ta tarar da Little da Prince har sun shirya mata break
fast d’inta , cikin d’an ya’ke Abla ta furta “ Yaya prince ina kwana ? Yaya little
ina kwana ?” Yadda Little yaga tana magana cikin cool voice ya furta “ Bazaki fasa
zuwa makarantar nan ba kuwa ? Are you okay ?” Murmushi Abla ta sakar masa kad’an “
I can manage , muna da speech yau ne “ kansa ya Jin kina mata kamar yace ta hakura
sai kuma yayi shiru , dan dole suka sa ta ci abinci duk da yadda tace musu a ‘koshe
take , da zasu tafi makaranta ma bata had’u da su Bobo ba , har suka kama hanyar
idanuwan ta a rufe suke bata san lokacin da aka ‘karaso ba saida Little ya d’an
ta’ba ta , “ please nace ki dena damuwar nan kinji ?” Kanta ta jinjina masa yanzu
ma , wani black face mask ya mi’ko mata “ zaki iya sawa a face din ki in kina so “
d’an ‘karamun ajiyar zuciya Abla ta saki ka d’an ko ba komai face mask d’in zai
kare mata face d’inta . Kamar kullum waving sukai wa juna suka tayar da motar suka
tafi ita kuma ta nufi class d’insu . Tunda ta shigo ake binta da kallo ga wani
‘kus’kus da suke yi suna nunata , wasu zafafan hawaye taji suna ‘ko’karin sakko
mata tayi saurin mayar dasu , harta ‘karasa seat d’inta babu Wanda ta kalla , tana
zama Eshaal ta ri’ke mata hannunta “ kiyi hakuri nasan sharri akai miki amma Allah
zai saka miki kinji ?just be you , okay ?” Kanta Abla ta jinjina mata ko bakomai ta
samu wadda ta yadda da ita “ Nagode “ cewar Abla , itama fanan seat dinta tazo ,
ita da Eshaal suna so ta sake kamar da , amma zazzafan zazza’bin da take ji ya hana
tayi magana sai dai ta jinjina musu kai ko kuma ta furta “eh ko ah ah “ shine
kad’an abunda bakinta yake iya furtawa , gashi ko karatun abunda zatayi a speech
bata karanta ba Sabida abunda ya faru da ita jiya. Ba’a d’au 2 minutes ba Baby ta
shigo cikin class d’in, Daidai seat din da su Abla suke ta nufa , da Sauri Eshaal
ta had’e hannayen ta alamar ro’ko, hararar ta Baby tayi tana kallan Abla, a bazata
ta fusge mask d’in Abla cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa , karo na farko
da Baby taji babu dad’i dan anyiwa mutum abu, “ ‘boye fuskar ki da kike bashi zai
hana mutum ya yadda da abunda aka gani ba , ko ma su wanene sukai miki Haka raunin
ki suke so kamar yadda kike ‘ko’karin nuna wa yanzu, bance sai kin yadda da
maganganu na ba , kwanda ki fito ki nuna wa ko wana d’an iska daidai kike dashi ,
ta hakan ne zaki iya kwatar kanki a hannun kowa “ tana kai ‘karshen maganarta ta
juya , d’an ’karamin murmushi ne ya fitowa Abla ,” Na gode “ shine abunda ta iya
furtawa Baby , kanta Baby ta jinjina mata kafin ta harari su Eshaal da suka saki
baki suna kallanta , sosai suke kallanta da tsantsan mamaki , karo na farko da Baby
ta fad’i maganar arziki, shiyasa cikin Sauri fanan ta koma Seat d’inta . Har
lokacin kuma ba’a dena gulmar Abla ba , ga zazza’bin da yake ‘ko’karin cin ‘karfin
ta , duk yadda Eshaal da fanan sukayi da ita akan suje clinic ta ‘ki yadda. Har 9am
suna class babu teacher din da ya shigo sabida speech din da za’ayi na seniors,
wani irin fargaba Abla take ji a ‘kasan zuciyar ta ,babu abunda take sai adduar da
ta zo bakinta. 9:40am aka bu’kaci duka students suje babban filin hall din da
za’ayi program din , duk yadda Eshaal tayi da ita suje Abla ta kasa zuwa ,
zuciyarta ba dad’i da kyar ta hakura ganin time na tafiya suka nufi hall din , duk
Wanda ya ganta sai su fara magana kasa kasa ko su dunga nuna ta , Daidai zasu shiga
hall din suka tarar da Mr jabcon a tsaye sai faman murmushi yake wa Abla, a bakin
‘kofar ya tsaya ta yadda dole sai sun ra’bashi tukunna , kallan da yake bun Abla da
shine ya ‘kara tunzurata, Daidai zata shiga cikin hall d’in yayi ‘ko’karin rike
mata kwankwaso, bata damu da d’aliban da suke wuce ba wa , ta d’aga hannunta da iya
karfinta , ta tsinka masa mari, tare da tofa masa miyau tayi wucewar ta . Wannan
abunda tayi masa ne ya ‘kara tun zura jabcon, shi kad’ai sai jijjiga kansa yake
yana ‘kwafa , wayar sa da ta d’anyi ringing ya d’auka, banyi me aka ce masa ba sai
wata shegiyar dariya da ya saki lokacin da yake komawa gefe , “ kamar yadda aka
shirya plan , komai yana kan shiri nan da ‘yan mintuna kad’an aikin ki zai kammalu
kamar yadda kike bu’kata” yanxu ma banji me aka ce masa ba sai wata shegiyar dariya
da ya ‘kara saki kafun ya furta “ zan turo miki da account din yanzu “ sai d’iff ya
kashe wayar yana shiga cikin hall d’in.

Tunda Suka shiga cikin hall d’in yan set d’in su Abla suke kallanta , gabaki d’aya
ta tsargu da irin kallan da suke bunta dashi, har suka zauna a Inda aka tana dar wa
yan set d’insu waje , daga bayan ta Abla taji d’aya daga cikin yan Ss2 tana nuna
Abla , cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta furta “ she’s a prostitute” da mamaki d’ayar
ta gefenta ta furta “ no wonder kullum take Simi Simi Aushe karuwa ce at her ages”
da Sauri Abla ta damtse idanuwanta dan gabaki d’aya taji maganganun su , itama
Eshaal Sauri ri’ke hannun Abla tayi ganin tana ‘ko’karin tashi “ Na fad’a miki ki
dena saka irin wannan abun a ranki , koma wanene yake da hannu akan abunda sukai
miki Allah bazai barki ba , idan kinji sauyi cikin zuciyar ki toh kiyi addua
kinji ?” Kanta Abla ta jinjina mata Batare da tace komai ba , tunda Suka zauna
jabcon ya zuba musu ido shikad’ai sai murmushi yake yi abunda duk da marin da Abla
tayi masa lokaci kawai yake jira . Ba’a d’au dogon lokaci ba aka fara gabatar da
program din da za’a yi , Abla gabaki d’aya hankalin ta da gangan jikinta basa tare
da ita shiyasa bata san speech d’insu yayi ba . Sunan Eshaal da aka fara kira ne
ya fad’ar mata da zuciya dan tasan daga Eshaal sai ita a speech d’in. Cikin nutsuwa
da kwarewa Eshaal ta fara gabatar da speech din ta gwanin burgewa lokaci lokaci ana
ta fa mata har ta kammala , wata malama ce ta furta “ the second person is Ibtissam
Mohammed Al-Taufeeq “ daram Abla taji zuciyarta ta buga da ‘karfi ,’kafarta tayi
mata sanyin da nazata iya me’kewa ba , sai da aka kusan kirata sau uku sannan ta
iya mi’kewa bakinta d’auke da addua . Mr jabcon na ganin Abla na nufar Inda zata
gabatar da speech shima yayi Sauri nufar wajan , Abla na ‘ko’karin fara speech d’in
ta Mr jabcon yayi saurin taran nunfashinta , cikin d’aga murya ya furta “ am so
sorry da na katse muku speech din nan da ake yi , amma akwai babban abunda ya
kamata kusani yanzu amma sai d’alibar nan ta gama speech d’inta , please ku tafa
mata” gabaki d’aya kuwa aka hau tafa mata musamman Wanda suke san hotunan jiya zai
rabawa Malam suma , Eshaal da Fanan ne kawai basu tafa ba sai Baby itama da bataji
dad’in abunda akwai Abla ba dukda itama tana mamakin me yasa ta damu akai ma . Abla
duk da tasan wula’kanta ta yake so yayi hakan be hana lokaci d’aya ta dake ba ta
fara gabatar da speech d’inta yadda ya kamata cikin tsan tsan turancin da ya burge
kowa , tana gamawa gabaki d’aya hall d’in ya d’au tafi. Zata koma Mr Jabcon yayi
saurin dakatar da ita , yana kallan gabaki d’aya mutanan cikin hall d’in, Daidai
lokacin da yake furta gabaki d’aya kowa da kowa ya kalli Abla wasu irin manya
manyan motoci ba’ka’ke suka danno kai cikin makarantar da mugun gudun gaske , Abla
dake cikin hall da gudu ta fito sabida bazata iya kallan cin mutum cin da yake
‘ko’karin yi mata ba, Eshaal da fanan ma cikin Sauri suka biyo bayanta suna
‘ko’karin dakatar da ita , Daidai lokacin da take gugu a dai dai lokacin wasu manya
manyan combo cars suka danno kai cikin makarantar, su Abla suna Barin wajan
ratsatstun Ba’ka’ken jerin motocin nan sukai parking Wajan babban harabar hall
d’in, babu abunda ake ji sai diran motoci , yadda combo cars din suka shigo ajere
sai ya burge mutum , lokaci d’aya motocin da akalla zasu kai 15 suka yi slow down
sukayi parking, cikin Sauri motocin farko suka fito da Sauri sanye da kayan sojoji
ga wasu irin makamai a jikinsu , dayawa daga student d’in da suka fito kallan
motocin suke daga gefe kowa yana so yaga wanene a cikin motar , cikin Sauri gabaki
d’aya sojojin cikin combo cars d’in nan suka fito gwanin burgewa ko wannan su sanye
da kakin sojoji da bindugu a jikinsu, kafun kace me gabaki d’aya motocin sun zagaye
farar Bugatti La Voiture Noire d’in da ke tsakiyar su, cikin zafin nama Victor da
Anthony suka fito daga gaban mota, da Sauri sojoji suka yi layi , abun sai gwanin
burgewa , cike da tsantsan girmamawa Victor ya bud’e door d’in bayan farar
Bugattin, kusan tsawan mintuna 3 kafun mamallakin motar ya fito da farar ‘kafar sa
me sanye da ba’kin Gucci loafer , ga farin wandansa d’aya fito me shegen laushi, be
d’auki ko cikkaken mintuna ba gabaki d’aya ya Fito daga cikin motar cikin fararan
suit da sukayi mugum amsar sa , fuskar sa sanye cikin wani black sunglasses da yayi
matukar ‘kawata face d’insa , hatta gyaran gashin kansa na dabanne yau , yadda
fuskarsa take a had’e cikin ba’kin glass din idanuwansa sai ya matu’kar girgiza
mutum ba kowa bane face Big Boss da fuskarsa babu ko d’ugon fara’a akai, cikin
Sauri sojojin suka soma tafiya sai yazama kamar Big Boss aka saka a tsakiya , ga
Victor da Anthony da suke taka masa baya , tun da ya fito maza da matan makarantar
suke san ganin fuskar sa amma abun ya ci tura Sabida sojoji suka karesa ta ko ina ,
kai tsaye cikin hall d’in suka nuna Daidai lokacin da Jabcon ya d’auko wani and
envelope zai bud’e bayan ya gama surutun da yake san yi, kamar daga sama yaji
saukar abu a bakinsa , a razane ya fasa ihu lokaci d’aya sabida Jinin da bakinsa ya
fara yi masa , manya manyan sojojin da Suka fara shigowa ne ya matukar tayar musu
da hankali , cike da tsoro teachers da student suka mimmi’ke sabida bindugun dake
hannun sojojin gasu da uban yawa, lokaci d’aya hall d’in ya nemi ya rikice amma
kallan da sojoji sukai musune yasa sukayi saurin yin shiru , ta ko ina sojojin Big
Boss ne da bin dugu a cikin su . A hankali ya shigo yake da kowa cikin hall d’in,
Daidai wata lafiyayyiyar kujera da d’aya daga cikin sojojin ya shigo da ita Big
Boss ya zauna kamar kullum yayi crossing legs d’insa waje d’aya ,
Cikin Sauri Victor da Anthony suka ‘karasa wajan jabcon da yake du’ke a ‘kasa
jikinsa sai rawa yake ga Jinin da yake fita daga bakinsa , hannu Victor ya d’aga ya
kaiwa bakin Jabcon duka , wani Jinin ne ya ‘kara fitowa abakin jabcon sai ihun yake
yi Sabida azabar da yaji, hanya d’aya daga cikin sojojin sukai wa student cikin
Sauri suka fara fitowa banda yan set d’insu Abla da aka dakatar dasu sai kuma
teachers , duk da sauran student d’in ma sunso tsayawa , wata waya aka jefowa
Anthony yayi saurin jafewa,Big Boss na zaune Anthony ya d’aga hannu ya tsitstsinka
wa Jabcon mari da har saida gefen fuskarsa ya kunbura , tsabar azaba ko ihun ya
kasayı sai kukan sa da yake fitowa kad’an kad’an, wani kujera d’aga daga cikin
sojojin ya janyo Victor ya hankad’a Jancon ciki tare da saka masa d’aya daga cikin
wayoyin wutan cikin wando , cikin wani socet aka saka wayar , cikin tsananin tashin
hankali jabcon ya saki fitsarin da kamasa, ana kunna socet d’in wutar Jabcon ya
fara jijjiga , ga fitsarin da yayi ya ji’ka wando , a karo na biyu suka ‘kara kunna
socet d’in yanzu ma ihu kawai jabcon yake yi cikin a zaba , sai a lokacin sojojin
suka bud’e yan class d’in Abla hanya da sukayi mugun tsorata Sabida tashin hankalin
da suka shiga , ko wannan su cike da tsoro suka har hall d’in har teachers d’in da
kowa jikinsa ya d’au ruwa , wani medium Box aka d’akko , da yake d’auke da cutters
kala Kala a ciki, da ya bud’e baki zaiyi ihu zai ji saukar mari a bakin ta , tun
yana fahimtar abu har ya dena ga hakwaransa guda biyu da suka fito waje Sabida
azabar shan mari da yayi. Tsabar mugunta toshe masa baki d’aya daga cikin sojojin
yayi ga hannunsa da aka rike, Daidai babban finger din kafarsa Anthony ya saka ya
datse dan yatsan, cike da azabar da yaji ya dunga girgiza kai yana so ya basu
hakuri amma sun toshe masa baki , d’ayan finger d’insa Anthony ya ‘kara Yankewa da
har saida jabcon ya suma , Victor na ganin ya suma ya saka hannunsa guda biyu ya
bawa fuskar jabcon tass , ba shiri ya farfad’o daga suman da yayi fuskarsa gabaki
d’aya ta kumbura , wani babban cutter Victor ya d’auko sojojin suka tu’be masa kaya
suka barsa sa singlet , Allah ya temakesa a kwai dogon wando har wajan gwiwarsa ,
hannu d’aya Victor ya saka zai zame wandan Jabcon da yayi mugun galabaita ya dunga
girgiza musu kai da iya ragowar ‘karfinsa ga d’an yatsansa da yake Jini, Big Boss
na zaune kamar be san abunda ke faruwa a Wajan ba sai phone d’insa da yake dannawa
hankali kwance , duka sosai akai wa jabcon sai da suka tabbatar sun masa jina jina
kafun Anthony ya furta “ waya saka?”batare da ‘bata lokaci ba Jabcon ya furta “
Alice “ dan iya bugawa ya bugu ko d’an yatsan sa baya iya motsawa, jin sunan wacca
suka fad’a ne yasa wasu daga cikin sojojin Suka fita dai dai lokacin da Bobo ya
shigo cikin hall d’in bayansa wani saurayine kamar za’a ‘ballashi jikinsa duk taba
ta zu’ke shi , ta ko ina jikinsa a kunbure yake sabida uban dukan da yasha ga LG da
itama ta sha mugun duka jikinsa sanye da kakintq na sojoji wasu mata soldiers ne
suka janyota har zuwa inda Jabcon yake a baje shima Sai faman nishin wahala yake ,
LG sai faman kuka take tana ‘ko’karin ’karasowa wajan Big Boss amma ba hali dan iya
buguwa ta bugu, yadda Bobo ya jefa mata wani mugun kallo ne yasa tayi sauri ha
d’iye kukanta, ba’a fi minti 15 ba aka shigo da Alice da itama tayi wujiga wujiga,
matan da suka d’akko ta suna zuwa sukai wurgi da ita , ihu ta saka da Sauri tayi
kan Big Boss zata rungumeshi, barin da ya sauke mata a fuska ne yasa nunfashin ta
d’aukewa na wucin gadi cike da zallan tsoro da tashin hankali har tana ‘ko’karin
fad’uwa , sojojin itama basu ‘kyale taba sai da sukayi mata jina jina , babu abunda
bakinta ke kira sai “ Dady ! Dady “ wani irin murmushin mugunta Bobo yasaki sabida
gabaki d’aya an goge hotunan da sukai wa Abla, Wanda jabcon yake ‘ko’karin bud’ewa
Victor ya mi’kawa Big Boss . Cikin tsana Bobo ya furta Zee“ LG? Alice ?” Da Sauri
suka soma basu hakuri amma tsawar da ya daka musu yasa gabaki d’ayansu yin shiru ,
ga su jabcon da sai nishin azaba suke , ji suke da zasu samu Alice da LG sai sunyi
mugun sa’ba musu Sabida gabaki d’aya su suka ja musu. Sau d’aya Big Boss ya d’ago
da eyes dinsa yana binsu da wani mugun kallo , babu Wanda be tsure ba a jikinsu
musamman Alice da tasan hukuncinta sai ya fi na kowa , bayan hukuncin da za’a yi
mata har d’akın horon sojoji sai ta shiga na sati biyu, ta sa ko kasheta Big Boss
zai yi chief bazai ta’ba basa hakuri ba duk da kasancewar ‘yarsa , diamond watches
d’insa ya kalla kafun ya mi’ke tsaye “ Congratulations husbands and wife “ yana
gama fad’ar hakan ya juya ragowar sojojin suka taka masa baya, a razı ne Alice ta
furta “ Me.. ne…nee” dakatar da ita Bobo yayi ganin yadda ta kasa maganar ma ,
cikin mugunta Bobo ya furta “ you guys enjoy da game abi, “ Alice ya fara nunawa
tare da jabcon “ kune tsinannun farko da kuka fara had’a plan, tunda kunsan kan
mugunta , zakuyi kyau da ma’au rata , in short your crush , Big Boss da kike so ya
d’aura miki aure da Wannan “ ya ‘Karasa yana nuna mata jabcon”, wani irin ihu Alice
ta saka a gigice lokaci d’aya ta sume a Wajan , hankali a tashe LG take kallansa
itama , yanzu ma murmushi Bobo ya sakar mata “ yes abunda kike tunani Hakane kema
da d’an iskan da kuka had’a plan are married to each other , wait for your
punishment all” lokaci d’aya itama LG ta nema zaucewa musamman idan ta kalli
tsomararrran guy da ya kama sa cewa Sabida sigarı, gabaki d’ayansu su hudun sojoji
suka ja su Ammar kayan wanki suka suna ‘kokarin barin hall din .
Big Boss na fitowa itama Abla tana fitowa sabida sojojin da taji ance mata sun
fito ga student da kowa yake le’ke gabaki d’aya sun kasa fitowa fili sai Abla ,
Daidai Wajan hall d’in ta nufa , lokaci d’aya sukai karo da Big Boss , bata san
lokacin da tayi hugging d’insa ba tana ‘kara fashe masa da wani saban kukan.
https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____35💞

Tun da tayi hugging d’in sa be motsa ba , cikin Sauri gabaki d’aya sojojin suka
sara mata tare da juya musu baya , hakan da sukai ba ‘karamun jawo hankalin mutane
yayi ba , kowa mamakin sa Mene ne had’in Abla da wad’an nan mutanan , musamman
yadda suka ga sojojin sun sara mata cikin girmamawa , hatta Eshaal da fanan da suke
d’an nesa da ita mamaki ne ya kama su , Abla kuwa bata ma san suna yi ba sabida
kukan da take ga zazzafan zazza’bin da ya ‘kara rufe ta , Lumshe eyes d’insa Big
Boss yayi musamman yadda yaji Abla ta rungumesa , kusan second 30 suna a haka kafun
ya saka hannun sa yana ‘ko’karin zame ta daga jikin sa , Daidai lokacin da Bobo ya
fito dasu Alice , gabaki d’ayan su sun farka sai faman ihu suke , Alice babu abunda
take kira sai sunan “ Big Boss “ gabaki d’aya ta fita daga hayyacin ta , fuskarta
gabaki d’aya tayi jaga jaga da ita,suna fitowa ta hango Big Boss da Abla , cikin
Sauri ta nufi wajan su a haukace , yadda ta nufo wajan ne yasa Big Boss Fasa ture
Ablan yayi sai ma ‘kara hugging d’inta da yayi sosai a jikin sa, kasa motsi Alice
tayi sai zamewa da tayi ta soma burgima tana ihu “ bazai faru ba, bazan yadda ba ,
Big Boss kai nawa ne , ni kad’ai zaka so , sai na kashe ki , sai na kashe ki da
hannu na “ ta ‘karasa tana nufo inda Big Boss yake , gabaki d’aya sojojin nan
bindugu suka saka wa Alice , da hannu d’aya Bobo ya dakatar dasu dan shima so yake
yaga karshen iskancin Alice , tana zuwa zata ta’ba hijab d’in Abla , Big Boss ya
tsunka mata mari dama da hagu da har saida Alice ta fad’i ’kasa lokaci d’aya jinta
ya d’auke mata , idanuwan ta ne kawai suke motsi da ta mugun zazzaro suna bin bayan
Abla da kallo , a hankali Big Boss ya soma tapping bayan ta , kamar Wanda aka yiwa
dole ya furta “ it’s okay ! Let’s go home “ sai a lokacin Abla ta Ankara da abunda
tayi cikin sauri tayi ‘ko’karin zamewa ya ‘kara hugging d’inta yana tapping bayan
ta , ga Alice da LG da gabaki d’aya sukayi suman wucin gadi, zameta Big Boss yayi
a jikinsa , kallo d’aya yayi mata ya d’auke kansa tare da jefa mata Wannan mugun
kallan nasa , cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta Sabida wani yar da taji lokaci
d’aya , bata tashi sumewa da al’amuran Big Boss ba sai da ya bud’e mata mota da
kansa , hannunta d’aya data ri’ke rigarta ya kamata har wajan motar ya saka ta ,
tana d’ago da kanta ya jefa mata mugun kallan sa , yadda yayi gabaki d’aya sai ya
‘kara zama kamar masoyan da suka dad’e cikin gogin soyayya, wasu tunani ma suke ko
shagwa’ba Abla take masa lokacin da ya kallesa, hakan da yayi ba ‘karamun mamaki ya
bawa kowa ba , hatta Bobo kasa motsawa yayi Sabida shock , duk da yasan halin Big
Boss sarai yasan abunda yake , mamakin sa be gama ‘karewa ba sai da Big Boss ya
rufewa Abla mota, ya zagaya d’ayan side d’in , cikin Sauri Victor ya bud’e masa
mota ya shiga.
Jabcon, Alice da LG kuwa gabaki d’aya jansu sojojin sukai har da cikon na hud’un su
, ko arzi’kin zama a mota basu samu ba , sai a boot da Robert ya sassakawu, cikin
Sauri kuma Robert ya bud’e Bobo mota, ba’a d’auki cikakken mintuna ba gabaki d’aya
motocin suka soma tafiya a guje , tun kafin su fito gabaki d’aya aka bud’e musu
gate, manya manyan motocin tawagar Big Boss ta nufi right side , motocin Bobo kuma
sukayi left side . Gabaki d’aya suna barin wajan makarantar neman hargitsewa dan
babu Wanda be shiga rud’un abunda ya faru ba , yan class d’in Abla kuwa kasa magana
sukayi sai zazzaro idanuwa da sukai, babu Wanda hankalin be tashi ba , musamman
yadda sukaga yadda sojojin nan suka sara wa Abla , kowa tunanin da yake cikin
zuciyar sa wacece ita ? Dan ko tanbayar juna sun kasa gani suke suna maganar ta
sojojin na zasu dawo, Su Eshaal ma gabaki d’aya jikin su sanyi yayi , da ‘kyar suka
iya koma class ganin Abla bata tafi da jakar ta yasa Eshaal ta d’aukar mata.

A cikin mota kuwa tunda Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa ta kasa koda
kwakkwaran motsine sai addua da take ta nana tawa cikin zuciyarta , ko idanuwan ta
takasa d’akko wa balantana tayi gangancin kallan side d’in da yake . Big Boss kuwa
kamar be san da wanzuwar wani halitta a cikin motar ba , musamman yadda ya lumshe
eyes d’insa ,Ya d’an jingina da kujerar sa , Abla kuwa neman nutsuwar ta tayi ta
rasa sai hannun ta da take mamma tsawa, har suka ‘karasa gida bata sani ba sabida
sun kuyar da kanta ‘kasa da tayi , tana jin anyi parking tayi saurin d’ago da
idanuwanta , ba shiri ta kama hannun ‘kofar zata fita ganin sun ‘karaso cikin gidan
, rai a ‘bace Big Boss ya finciko hannunta, har tana bige wa da abun coffee d’in
wajan , d’an ‘karamun ‘kara Abla ta saki kad’an Sabida zafin matse mata hannun ta
da yayi , cikin kausash shiyar murya Big Boss ya furta “ Are you mad ?” Shiru Abla
tayi masa tana d’an sunkuyar da kanta ‘kasa , hannun bata ya ‘kara murd’ewa da
Sauri Abla ta saki wani ‘karan tana girgiza masa kai “ Dan Allah kayi hakuri”,yar
far da hannun nayi kafun ya nuna mata ‘kofar fita , da Sauri ta bud’e kofar ta nufi
cikin gida ko wai waya bata yi , su jabcon ma d’akin horo aka kai su , Big Boss na
cikin motar amaimakon ya fito sai Victor ya tayar da motar suka bar gidan, a guje
suma ragowar sojojin suka mara musu baya.

Da murmushi akan face d’inta ta shigo cikin gidan, gabaki d’aya mi’kewa sukai
ganin face d’inta d’auke da annashuwa “ Lil kin dena fushin yanzu ?” Cewar Little ,
kanta Abla ta Jinjina masa tana ‘kara sakar musu murmushi , shima da d’an mamaki
Prince ya furta “ Da gaske kike ?” Yanzu ma kanta Abla ta jinjina masa , shiru
Little yayi kamar me tunani sai kuma ya furta “ Amma zaki ci abinci idan muka kawo
miki ko?” Kanta ta jinjina masa kafin ta bud’e bakinta “ Yunwa nake ji Yaya Little
“ gabaki d’aya ta d’aure musu kai ganin lokaci d’aya annashuwar ta ya dawo dai dai
ko kula da rashin school bag d’in ta basuyi ba . Tana shiga d’aki wanka tayi cikin
blue d’in riga da wando palazzo, gashin kanta da yayi tsawo sosai , shima sai da ta
gyarasa kafun tayi Rolling da peach d’in mayafi da ya ‘kawata face d’inta , wani
half peach shoe ta saka a ‘kafarta , sosai shigar tayi mata kyau kamar ba Itace a
cikin damuwa ba jiya . Yunwa take ji sosai shiyasa tana sakkowa suka nufi dinning ,
har yanzu basu dena mamakin yadda ta sauya ba lokaci guda , ‘dan marairaice musu
face Abla tayi “ kuzo mu fita yawo please “ d’an zaro mata ido little yayi “ yawa
kuma Lil?” Kanta ta jinjina masa tana langwabar da kanta , “ kawai futa zamuyi fa
mu dawo, babu Inda zamuje “ shiru Little yayi mata kamar ne tunani, prince zai yi
magana little yayi saurin furta “ shikenan Lil amma baza mufi 20 minutes a waje ba
kin yadda ?” Da Sauri Abla ta “ Eh na yadda “ cikin Sauri prince ya furta “ Baku da
hankali ne ? Kunsan Yaya Big Boss da Yaya Bobo na nan fa ,” Haba mana Yaya prince
bazamu dad’e ba just 20 minutes “cewar Little , girgiza masa kai Prince yayi “ babu
ruwana , kasan me zai biyo baya ai ko?”Little zai ‘kara masa musu Abla ta dakatar
Dashi “ Hakane fa! Yaya little karmu ‘bata musu rai kawai muje garden” cikin cool
Little ya furta “kin tabbatar ?” Kanta Abla ta jinjina musu “ yes kwana biyu ban ga
simba ba “ da haka Abla ta kashe maganar suka nufi wajan simba gabaki d’ayansu ,
yanzu ko tsoransa da take ji ma ta dena, sun dad’e a wajan simba kafun su koma
garden , sai alokacin Abla tasan da karnukan Bobo, duk yadda Little yayi da ita su
je wajan su ta’ki zuwa , ganin tana shirin guduwane ya hakura shima . Suna zaune a
Wajan har sai da suka ji kiran sallar La’asar tukunna Abla ta dawo cikin gida , su
kuma suka wuce masallaci. Yau gabaki d’aya jinta take kamar a iska , babu kunci ,
babu damuwa aranta , ko ba komai sun wanke ta daga cikin sharrin da akai mata.
Rungume shi data Tuna tayine yasa tayi saurin rintse idanuwanta kamar wani yana
ganin ta , a fili ta furta “ Na shiga uku na , yanzu ya zanyi ?” Rashin samun
mafita yasa Kawai ta ha’kura tayi sallar la’asar d’inta , tana idar wa ta tashi da
nufin duba books d’inta, gabaki d’aya ta manta bata d’auko jakar taba sai da ta
gama duba ko ina, kamar zatayi kuka ta koma ta zauna sai system d’in ta data
kunna , Allah ya te make tama babu teacher d’in da ya shigo class d’in. Abla bata
‘kara fitowa ba sai bayan sallar isha’i, shima yunwa ce ta ishe ta , ga baccin da
take ji yau da wuri , cikin d’an guntun kuzarin da ya rage mata ta nufi kitchen
lokacin babu kowa , cornflakes ta had’a kad’an cikin cup sai yoghurt da ta d’auka
guda d’aya ta dawo falourn, tana ajjewa tayi saurin komawa d’aki ta d’akko system
d’inta , Wani Korea da ta fara kallo ta kunna tare da d’ora ta kan center yadda
zata fi jin dad’in kallan ta , ta nutsu sosai tana kallan ta dan ba ‘karamun dad’i
novel d’in yayi mata ba.
A hankali ya shigo cikin falourn, duk da babu fara’a akan face d’in sa amma ba
a had’e take kamar kullum ba , kamar yadda ya saba shigowa tun da ya shigo be d’ago
da kansa ba , muryar film d’in da Abla take kallo yana tashi sama sama , gabaki
d’aya batasan da shigowar sa falourn ba sabida yadda ta nutsu sosai tana kallan
ta , Daidai lokacin da jarumin film din zai yiwa jaruwar kıss Abla tayi saurin
kifar da system d’in , jikinta har rawa yake , lokaci d’aya ta dafe saitin zuciyar
ta , ta mi’ke da nufun komawa kitchen idanuwansu ya sar’ke cikin na juna , cikin
Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa , “ sannu da zuwa “ cewar Abla, ta’be baki
Big Boss yayi cikin husky voice d’in sa ya furta “ coffee “ daga nan be kuma tanka
mata ba ya wuce part d’insa . Kallan hanyar da ya nufa tayi kafin ta ta’be bakinta
kad’an “ ni ina ruwana tunda dai ka ‘Karo mun hacci na , shine zaka dunga d’auran
fuska , coffee , coffee , coffee “ cewar Abla tana Kwaikwayar ‘karshen maganar ta ,
cikin Sauri kuma ta wanke cup din cornflakes d’in ta koma wajan coffee maker, har
ta d’auko flavors d’in da Little ya koya mata sai ta idanuwanta suka sauka kan wani
strawberry flavor da ginger flavor , da karan baninta ta had’a coffee d’in dasu,
lokaci d’aya kuma ‘kamshin su ya ban ban ta da sauran Wanda take yi, da Sauri ta
d’auki cup d’in ta nufi part d’insa , zuciyar ta fal fargaban abunda zai yi mata
tunda ya hanata shigar masa part , ta fi minti d’aya a wajan gudun kar coffee d’in
sa yayi sanyi ne tayi knocking falourn sa na farko shiru babu amsa , still ta ‘kara
kwankwasa wa a karo na biyu babu amsa , ‘karfin hali tayi ta bud’e ’kofar tana
ganin baya ciki ta nufi d’ayan falourn , shima sau biyu tana knocking ba’a amsa
ba , da sallama ta shiga falourn sai kuma tayi saurin Jan burki ganin sa zaune kan
d’aya daga cikin kujerun falourn , ga system d’insa da yake operating akai . A
nutse ta ‘karaso cikin falourn Daidai Wajan center d’in ta rankwafa kad’an “ ga
coffee d’in” shiru bai kalleta ba balantana ta saka ran amsawa , a karo na biyu ta
‘kara furta “ ga coffee d’in “ nan ma shiru yayi mata kamar be san da zuwan ta ba ,
Yadda ya nuna kamar babu mutum a falourn ne ya ‘kular da ita , juyawa tayi da niyar
komawa ya mi’ka hannunsa kad’an ba tare da ya kalle taba “ My coffee !” A fakai ce
Abla ta d’an harari side din da yake kafun ta juyo ta mi’ka masa coffee d’in, yanzu
ma sai da ya gama shan ‘kamshi tukunna ya saka hannu ya kar’ba , ta juya zata tafi
ya ‘kara furta “ Come back “ Abla kamar zatayi kuka haka ta juyo ta tsaya batare da
ta kalli side d’in da yake ba , kamar da wasa taga ya kai cup d’in bakin sa ,
kad’an yayi sipping kamar me tsoran sha , ta d’auka zai mata fad’a sai taga ya
‘kara kai coffee d’in bakinsa a hankali yana sipping. A hankali ta saki a jiyar
zuciya ganin yau ta tsira bazai mata punishment ba , ta fi tsawan 7 minutes tana so
ya gama shan coffee d’in ko zai barta ta tafi sabida gabaki d’aya ta kasa sakewa ,
a hankali ya ajje cup d’in batare da ya furta komai ba, itama Abla ganin ya gama
sha ne yasa ta d’auka da niyar komawar ta ‘kasa , tana juyawa ta kuma jin saukar
muryarta “ Coffee “,d’an ya mutsa face d’in ta Abla tayi kad’an kamar zatayi kuka
dan yau sosai take jin bacci, cikin Sauri ta ‘karo had’a masa wani coffee d’in har
lokacin su Little basa falourn , yanzu ma ta d’auka zai barta ta tafi sai ya ‘kara
dakatar da ita , sai da ya mula dan kansa sannan yasha coffee d’in a karo na biyu,
duk wannan abun Abla ta tsaye kamar zatayi kuka Sabida yadda ‘kafar ta ya gaji, a
karo na uku ya ‘kara sa ta had’a wani coffee d’in , tun tana tunanin d’aukar abun
da wasa har ta dena ganin sai da ta koma ta ‘kara had’a masa wasu coffee d’in,
kafafuwanta gabaki d’aya ciwo suke mata sabida hawa da saukan da tayi gashi sama da
awa d’aya tana tsaye ko zama be barta tayi ba , kamar ta ro’keshi akan ta tafi amma
itama taurin kanta ya hanata magana yau sai kawar da face d’in ta da tayi kad’an
kwalla har sun tarar mata cikin ido. Sai da ‘kara mintuna 25 a tsaye ga bacci ga
cikin kafa amma ko kusa ya hana ta tafiya , Sai da ya tabbatar ya horata da tsayuwa
kafun ya furta “ get out “ ko kallan inda yake yau Abla batayi ba tayi fitowar ta ,
“ mugu kawai” cewar Abla kafun tayi sauri barin Wajan . Tana sakkowa ta tarar da
Prince da little sai kuma uncle , “ yanzu nake shirin kiranki sai gaki ma kin
fito , ina kika je ?” A sanyaye ta furta “ coffee na kaiwa Yaya Big Boss “ cikin
fara’a Little ya furta “ sorry Lil nasan kin gaji ko?”Girgiza kanta kad’an Abla
tayi duk da ta gaji amma ko kusa bata nuna musu hakan ba “ No yaya Little ai ba
wani aikin nayi ba , ko kuna bu’katar wani abune ?” Girgiza mata kai sukai “ No Lil
yaka mata ki huta haka tunda gobe kina da school , okay ?” Cewar uncle , jinjina
masa kai tayi kafun ta furta “ Tom uncle sai da safe “ side d’in su Little ta kalla
suma tayi musu sallama kafun ta nufi part d’inta .
Tana shiga d’aki ta fad’a kan gado sabida yadda taji ‘kafafuwanta suka ri’ke,
tafi tsawan 10 minutes a kwance kafun ta iya zuwa toilet ta watsa ruwa ajikinta ,
lokaci d’aya abubuwan da suka faru d’azu suka dunga dawo mata cikin zuciya ta,
tasan baya santa , baya ‘kaunar ta , baya san ganin ta a inda yake , amma kano na
farko , mutum na farko daya ta’ba kwato mata martabarta ta ‘ya mace, baza ta ta’ba
mantawa da hakan ba arayuwarta,tana cikin wannan tunanin bacci ‘barawo ya d’auke
ta.

12:30am aka bud’e ‘kofar d’akin horan da aka kulle su Alice ,gabaki d’aya tun suna
kuka har suka dawo ajiyar zuciya dan gabaki d’ayan su sun fice daga hayyacin su. Da
victor ya tashi kulle su kuma sai ya had’a ko wannan su mata da miji ko a d’aki
d’aya , Alice da jabcon sai LG da mijin ita da ya kuma shan wani dukan a wajan ta ,
gashi daman a buge aka d’auko sa shiyasa LG taji dad’in bugun sa.

Victor ne yashigo cikin d’auki ko wannan su ya jefa musu blanket da wani Leda “ yau
ne first night d’in ku , and also congratulations you guys go be zaku tafi
Greenwich Village anan zakuyi honeymoon d’in ku na tsawan sati d’aya
congratulations “ a haukace Alice ta mi’ke tsaye tana d’ora hannunta aka
Honeymoon ? What ? Ni zanje kauye ? Bazai yuba , no dole dady ya zo bazai ha’ba
faru ba , babu Wanda ya isa ya kai ni kauye balantana wannan d’an iskan kwartan da
aka cewa ya zama miji na , “ kallanta Jabcon yayi daga sama har ‘kasa , “ Ni
gaskiya ina san matata “ cewar sa , ai be kai ‘karshe ba Alice ta tsinka masa
mari , banza Victor yayi musu ya nufi d’akin da aka kulle LG, the same abunda ya
fad’a wa Alice shine abunda ya fad’a wa LG, ita LG da ta fi kowa rud’ewa ma sume wa
tayi a zaune , tasan wanene Chief , tasan tunda Big boss ya yanke hukunci shikenan
ta zauna musamman da shima mahaifinta ya kasance me tsauri kamar Big Boss, mijin ta
da aka fi sani da Ozzy a tsorace ya kalli Victor “ kuyi hakuri , kashe ni zatayi
d’azun nan ta gama Zane ne , kuyi hakuri ni bansan abunda zai faru ba kenan” sai
kuma ya soma kuka kamar wani ‘karamun yaro.
‘Karfe 2:10am Abla ta farka sabida ‘kishir ruwan da ya dame ta , a hankali
ta sakko daga kan gadon daga ita sai riga da wandon ta na bacci da suka fito da
shape d’in ta sosai , hularta kawai ta d’auka ta fito daga cikin d’akin , har
ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ga fitilun falourn a kunne , batare da wani
damuwa ba ta wuce kitchen ta d’auko babban bottle d’in ruwan ta , tun daga kitchen
d’in ta soma shan abunda hankali a kwance , tana fitowa zata nufi sama kamar wacce
aka tsiyaka sai kawai ta juyo bakin ‘kofa Daidai lokacin da Big Boss zai shigo
cikin falourn , batasan lokacin da ta yardar da bottle d’in hannun taba ,
mistakenly ta tsallake step d’aya sai ‘kafarta ta zame a ‘kasa , ‘kugunta ya bugu
da step d’in, da ‘karfi ta saki ‘kara Sabida zafin da tanı a kugunta, a hankali ya
d’ago da idanuwansa zuwa ‘bangaran da take, ganin yadda da ri’ke ‘kugun nata ne ya
d’an ta’be baki tare da d’auke idan sa ya nufi hanyar part d’insa , da harara Abla
ta bisa ganin a dalilinsa taji ciwan, cikin rashin sa’a kuma lokacin da take
hararar sa ya d’an jiyo sai ya sauka akan idanuwansa , kallan zaki sani ya bita
dashi , kafin ya juyo zuwa side d’in da take , tun kafin ya ‘karaso ta soma yarfa
hannun ta ganin ya kamata dumu dumu tana hararar sa , hannun ta d’aga ta finciko da
‘karfi Abla ta furta “ouch “ Sabida ba ‘karamun buguwa tayi ba , yadda taga yana
binta da kallo ne yasa lokaci d’aya jikinta ya soma d’aukan rawa , gashi babu kowa
a falourn balan tana tanemi te maka , kamar zatayi kuka ta shagwa’be masa face
d’inta, zai bud’e baki Abla ta fashe masa da kukan ta’bara, kallan da ya jefa mata
ne yasa tayi saurin yin shuru sai ‘kif ‘kif ta idanuwa take , “ Me kike ‘bukata?
Ouh” shiru Abla tayi masa dan gabaki d’aya bata fahimci abunda yake nufi ba sai ma
‘ko’karin Jan baya da take , a zuciye ya murd’e hannun ta d’aya ga ciwan kwankwaso
ga hannu duk ita kad’ai , a tsiwace Abla ta furta “ Ni kasakar mun hannu na “
d’ayan hannun ya murd’e tare d juyo da ita , yadda taga kusancin su yayi yawane
yasaka jikin ta ya soma rawa lokaci d’aya , har yana jin yadda jikinta yake rawan ,
ga wani irin tsoro da ya bayyana akan face d’inta sosai,motsa bakin sa yayi kad’an
kafun ya saka hannun sa d’aga zuwa kwankwasan nata , yadda ta kwalalo masa idanta
waje ne yaso sawa bakinsa ya motsa amma sai ‘kara tsuke face d’insa da yayi “ I
think shine abunda kike so ko? And “ ya ‘kara matso da ita kusa da jikin sa
kad’ai , face d’inta yakalla ganin yadda tayi saurin runtse idanuwanta gagam ga
bugun zuciyarta da yake d’agowa sosai , daga gefen idanuwanta wasu irin siraran
hawaye ne suka kallo mata , ‘karamun tsaki yaja kad’an kafun ya saketa , a bazata
Abla taji ta ‘kara fad’uwa ‘kasa , the same ta ‘kara bugewa a kugunta, kuka kawai
ta fashe dashi lokaci d’aya dan ba’karamin zafi taji ba , “ You are nothing but
just a pieces of mess “ cewar Big Boss lokacin da Abla ta d’ago da idanuwanta
hawayen ta gabaki d’aya ya’ki tsayawa “ just because kina zaune a gidan ba , ba
hakan ke nufin ke yar gidan bace, your no body , I hate to see this your ugly
face , kinsan me ? From the moment kika shigo cikin gidan nan like kinyi poison
d’insu ne gabaki d’aya , I seriously hate you! That’s why naso jiya harbe kanki
kikai , okay ? “ d’an huci Big Boss yayi dan doguwar maganar nan da yayi har ya
saka masa ciwan kai ,” Sai da ya ‘kara d’auka second 10 kafun ya ‘kara kallanta “
duk Wanda ya aiko ki , you guys both will pay, ‘kazama , Villager “ da haka ya juya
ya bar wajan , wani irin kukan ba’kin cikine ya kwace wa Abla , tasan ya tsane ta
amma bata ta’ba tunanin tsanar da yake mata ta kai haka ba , ya tsane ta , yaso
mutuwar ta ? “ hawayenta Abla ta share lokaci gudu gabaki d’aya soyayyar da taji
tana yi masa ta goge ,dukda ita Kanta batasan a wana matsayi ta d’auke saba , hatta
tsoran sa da takeji gabaki d’aya ya fitar mata cikin zuciya , babu abunda yake mata
yawa cikin zuciya sai “ ‘kazama , Villager “ kallan jikin ta tayi sosai kafin ta
‘karasa goge hawayen face d’inta, da ‘kyar ta iya mi’kewa tsaye , da ‘kyar ta ke
taka steps Sabida yadda ‘kugunta yake mata zafi. Tana shiga d’akı gaban mudubin ta
tanufa ko zata samu man zafi, cikin sa’a kuwa ta samu, a ‘kugun ta shafa sosai
kafun ta kwanta bacci, kalaman sa sun dad’e suna mata yawo cikin zuciya , tsabar
takaici da hawaye takwana.

Da safe da wuri ta shirya cikin uniform d’inta , tana gama shiryawa kallan kanta
tayi a madubi “ ‘kazama , Villager “ shine abunda ya ‘kara yi mata yawa cikin
zuciya , sosai ta ‘kurawa fuskarta ido a fili ta furta “ tabbas ni ‘kazama ce ,
tunda bani da gata bansan iyaye naba a ‘kazanta na taso , sannan nid’in yar ‘kauye
ne , amma sai na nuna maka banbancin ‘yan ‘kauye da ‘yar burni, daga yau na tashi
daga Abla ta koma asalin Ibtissam , wannan Al’kawari ne na d’auka “……….

https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨
🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____36💞

‘Kasa Abla ta sakko cikin shigar uniform d’inta , bata tarar da kowa a falourn ba ,
shaf shaf ta shiga kitchen ta d’auko milkshake, bata damu da d’aukar cup ba ta fara
sha , tun a kitchen d’in, cikin sauri ta d’auki youghurt medium size ta fito bayan
ta gama shan milkshake d’in ta , yau ko Breakfast bata samu tayi ba , time ta duba
ganin ta kusa makara gashi har lokacin bata ga little ba , kamar ta zauna sai ta
yanke shawaran fitowa waje ko zata gansa a waje amma babu shi babu alamar sa ,
hatta yaya prince da take tunanin samu gabaki d’aya bata same suba , kallan motocin
da suke gefe da ita kad’an , tunani ta fara ko Little yana cikin motar ne ? Ganin
babu me bata amsa yasa ta juya zata koma cikin gida , da sauri wata macan soja ta
‘kara inda take tare da sara mata,” Madam sunana captain sarah , daga yau nice zan
dunga rakaki makaranta “, shiru Abla tayi kamar bazata ce komai ba , sai kuma ta
jinina mata kanta , cikin sauri Sarah ta ‘karasa ta bud’e mata mota , sai data
tabbatar Abla ta zauna sosai sannan itama ta shiga front seat , cikin ‘kan’kanin
lokaci motocin suka kama hanyar makarantar su Abla , tun kafun su ‘karasa makaranta
take ganin motocin sojoji suna ta wuce wa , ta ko ina akwai mata kan tsaro a
hanyar, bata kawo komai a ranta ba har suka ‘karasa makarantar, cikin Sauri Sarah
ta sakko ta bud’ewa Abla mota tare da sara mata , zata bita a baya Abla tayi
saurin tsayar da ita “ No please kar na wahalar dake nagode “ cikin Sauri Sarah ta
furta “ thank you ma’am “, tun da Abla ta fito daga cikin mota student d’in da suke
waje suke binta da kallo , babu Wanda ta kalla nufi class d’insu, tana shiga gabaki
d’aya class d’in ya d’au shiru kamar Wanda ruwa ya cinye su , Eshaal da fanan ma
sai binta da kallo suke har ta ‘karaso seat d’inta . Yadda taga suna kallanta ne
yasa ta d’an harare su kad’an , “wannan kallan fa ? Na mene ne ?” Ajiyar zuciya
Eshaal ta sauke “ ba dole mu kalle kiba ? ,ni ai har kin fara bani tsoro ma “ kara
‘kallan su Abla tayi lokacin da take zama “ da nayi muku me ?” Kusan lokaci d’aya
suka had’a baki wajan furta “ su wane ne wad’an nan mutanan ?” Shiru Abla tayi musu
dan ta fahimci maganar su, zasu ‘kara yi mata magana Mss Atem ta shigo class d’in,
itama da kallo tabi Abla ,duk lokacin da Abla ta d’ago kuma sai Mss Atem ta sakar
mata murmushi, tun Abla na tsarguwa da kallan ta har ta share ta. Sai da sukayi
period biyu na English kafun Mss Atem ta fito, yanzu Biology ne dasu gashi jabcon
yana hannun sojoji shiyasa kowa ya mayar da hankalinsa kan books d’inta, har zuwa
time d’in break .

A hanyar zuwa capteria ma haka akan dunga bin Abla da kallo gabaki d’aya ta tsargu
da irin kallan da taga ana mata , cikin tsokana fanan ta furta “ Matar soja da
alama jiya kinja hankulan mutane da yawa kalli yadda kowa yake zuba miki ido ,
Wanda basu sanki bama yanzu sun sanki “ shiru Abla tayi mata ta’ki tanka mata ,
itama Eshaal d’aga wa fanan gira tayi “ karki damu fanan yanzu zamu fara gyara
Matar soja ai , kınsan kamar sarauniya take dole mu tarairayeta “ harararsu Abla
tayi gabaki d’ayansu ta ‘Kara sa d’aya daga cikin table d’in, anan ma kusan
hankalin kowa kanta ya dawo ganin yadda ta had’e rai yasa kowa ya koma aikin
gabansu. Order abinda zasu ci su fanan sukai , har suka ‘karaso seat d’in Abla “ me
yayi zafi kuma matar soja ? Kırarın da mukayi miki ne ba ‘kyaso ko kuwa ?”ajiyar
zuciya Abla ta saki ganin bazasu ‘kyale taba ,”please mubar wannan maganar haka,
they are my brothers..” kallan juna Fanan da Eshaal sukai tare da kashewa juna
ido , a ku fule Abla ta kai musu duka “ Haba mana me yayi zafi? Salan muma ki saka
akarya mu? Maida wu’kar mana please “,yanzu kam hmm kawai Abla ta ce musu tare da
canza zancen zuwa wani zancen daban, saura mintuna biyar akoma class suka fito daga
capterian, yau gabaki d’aya basu had’u da su Bad Boys ba , a class ma kallan Inda
Baby take zama Abla tayi kafin ta kalli Eshaal , “ ina sister d’in ki kuma yau
banganta ba” itama Eshaal kallan chair d’in Baby tayi kafun ta furta “ Bata da
lapiya ne shiyasa amma kema kinsan Baby da shegen bala’i, nayi mamaki ma da naga
bata miki wad’annan abubuwan “murmushi Abla ta sakar mata “ kema wata rana komai
zai wuce a tsakanin ku , zakuyi rayuwa kamar babu abunda ya ta’ba faruwa a tsakanin
ku “ murmushi kawai Eshaal tayi mata dan ta san halin Baby sarai kamar yunwar
cikinta . Gabaki d’aya duk teacher d’in da zai shigo cikin class sai ya kalli Abla
, har hakan ya soma bata Yaushi ta fara d’aure face d’inta , da aka tashi ma haka
su Fanan suka dunga tsokanar ta da matar soja tun tana mayar musu da martani har ta
‘kyalesu. Ko cikakken 5 minutes basu yi ba , motocin su Abla suka shigo cikin
makarantar yau yadda Little , “ Sorry Lil yau bana gida shiyasa ban kawo ki
makaranta ba , but I hope Sarah ta miki abunda kike so ?” Kanta Abla ta jinjina
masa , gaishe da shi su fanan sukai shima cikin sakin fuska ya amsa musu “ yau dai
ku shigo mukai ku gida ko ?” Cewar Little yana kallan su, cikin Sauri suka girgiza
masa kai “ No ai Inda muke ba nisa, bazamu jima ba zamu ‘kara sa “ hararar su Abla
tayi “ Yaya Little ai daman haka zasu ce maka , mune kawai basa so mukai su
musamman wannan “ ta ‘karasa tana nuna Fanan , hararar ta fanan tayi “ ki dai jinga
jin tsoran Allah, ni yanzu me nace ? Ba Eshaal ce tayi magana ba ?” Cikin Sauri
Little ya ka tseta “ yes Eshaal ce tayi magana ba fanan ba , amma yanzu ta bakin
fanan nake zan ci , zaki bi mu ai ko ?” Shiru fanan tayi kamar me tunani Abla tayi
saurin furta “ kagani ko ? Daman na fad’a maka bazata bi muba “ wai haka ? “ cewar
Little yana kallan ta , d’an hararar Abla tayi kad’an kafun ta furta “ okay zamuje
“ cike da tsokana Abla da Eshaal suka furta “Awwwwn” musamman lokacin da Little ya
bud’e musu mota ida da Eshaal, har gidan da suke suka kai su kafin ya musu
al’kawarin fitar dasu yawo idan ya zamu time , Haka suma su Little suka kama hanyar
goma wa gida .

***************
**CABINET ROOM,WASHINGTON,DC 20500,USA**

Cikin babban ‘kayataccen d’akin taron cabinet room , wasu manya mutane ne masu
fad’a a ciki kowa shigin shigar tsadaddiyar suit da ta amsa sunan ta suit , ciki
kuwa har da president da kana kallan sa kasan baya cikin mood d’insa gabaki
d’aya , sai Chief da wasu manya yan mutane su hud’u suma , daga gefan chief akwai
wani bature da ya kasance former vice chief a lokacin su , tun d’azu sai faman
d’add’aure fuska yake kamar wanda yake jiran ‘kiris ya fashe .
Turo ‘kofar da akai ne ya dawo da hankulan su gabaki d’aya , wani soja ne ta
bud’e ‘kofar tare da sara musu gabaki d’aya , cikin sauri kuma ya koma gefe ya bawa
ya bayan sa hanyar shigowa . Ba kowa bane face Bobo da ya shigo cikin d’akin taron
cikin ainahin shigarsa ta soja , yau fuskar sa gabaki d’aya babu fara’a , kamar
yadda tsarin su yake , hular da ya ri’ke a gefen hagunsa ya saka akan lallausan
gashin kansa da ya sha gyara , ‘kafarsa ya bud’e kad’an sai kuma ya had’e ta ,
hannun sa d’aya na dama ya d’aga tare sara musu, Chief dake kallan sa kansa kawai
ta jinjina masa alamar amsawa , hatta president sai da ya jinjina masa kai tare da
wasu daga cikin manyan mutanan nan , banda mutumin d’azu me suna James Mingus wanda
shima ya kasance former vice chief a lokacin baya . ‘Daya daga cikin kujerun wajan
Chief ya nuna masa “ have your seat son “ cikin girmamawa Bobo ya ‘kara sara masa
kafun ya samu waje kan kujerar da chief ya nuna masa , fuska a had’e tun kafun Bobo
yayi magana Vice chief yayi saurin tarar nunfashin sa “ ya naganka haka ? Ko shi
d’an wula’kancin bashi da lokaci ne ?” Kallan sa kawai Bobo yayi batare da yace
komai ba , tun bayau ba ya fahimci yadda james mingus ya tsani Big Boss , musamman
yadda ya so a bawa d’an sa position d’in Big Boss , girgiza kai kawai Chief dan
shima yana sane da tsanar da mingus yake wa Big Boss shiyasa gabaki d’aya inuwar su
bata zama waje d’aya musamman yadda mingus yaso yayi controlling Big Boss amma abun
ya ci tura tun yana nuna masa tsana a ‘boye har tsanar da yake masa ta fito fili ,
d’an gyara zamansa President yayi ganin Bobo ne kad’ai yazo meeting d’in banda Big
Boss “ i think zamu iya fara abunda ya tara mu , tun da shi Bobo yasan komai , ina
ganin babu matsala “ kallan Bobo Mr president yayi “ Naga sa’kon ku akan laifin
Alice da kuma hukuncin auran da kukayi mata , but i think hakan yayi tsauri da yawa
, na yadda ku hukun tata amma akwai hukunci kala kala ba sai wannan ba shiyasa akai
meeting d’in nan domun samun masalaha “ murmushi Bobo ya sakar musu kafun ya mi’ka
wa Mr president da Chief wasu white paper , yana ‘ko’karin magana cikin tsawa da
wani irin kallo Mingus yayi saurin soma magana “ Har su wanene ku da zaku d’aurawa
‘yar president aure ? Ciki har yar chief ? Su wanene ku yaushe wuyanku yayi kauri
haka ?” Eye’s d’insa Bobo ya d’an zuba masa , murmushin gefen baki kawai ya saki
yana ‘ko’karin controlling temper d’insa, “ we’re here for a solution Mingus “
cewar Chief cikin bada umarni , har wani ajiyar zuciya Mingus ya saki shikad’ai sai
kuci yake kamar shi akai wa auran , biyu daga cikin manyan mutanan ma suma fad’i
suke a nemo solution kawai , yayinda ragowar suke goyan bayan Mingus , ganin Big
Boss bai so meeting d’in ba alamar ya rainasu , cikin yanayinsa na kullum chief ya
furta “Now suna ina ? “ batare da wani damuwa ba Bobo ya furta “ Sun tafi Villages
Honeymoon d’insu “ wani irin murmushi Chief ya saki dan ko d’aya bai ji zafin
abunda sukai ba , dan ko shine hukuncin da zaiyi kenan , president kuwa kasa magana
yayi sabida shikad’ai yasan tension d’in da zai samu wajan her Excellency, musamman
lokacin da ta samu labarin Auran Alice , kamar zararriya haka takoma , aranar sosai
ta kori mutane . Gabaki d’ayan su Mingus ya fi kowa har zu’ka a cikin , musamman
yanzu da ya kuma jin inda aka tura su Alice d’in wanda yana d’aya daga cikin burin
da ya d’auka na aurawa d’an sa Alice , ko ba komai sun samu hanyar da zasu dungayin
abunda suka ga dama . A ‘kufule Mingus “ waya baku izinin yanke wannan hukuncin? Su
wane ne ? Dan kuna da position babba ba hakan ne ya baku damar yanke hukuncin da
kuka ga dama ba , umar ni na baku , duk inda kuka kai su ku dawo dasu cikin kwana
d’aya “ wani d’an iskan murmushi Bobo ya saki yana ‘kara bin mingus da kallo , a
karo na uku da ji Bobo yayi masa shiru ta furta “ ita yarinyar da sukayi wa abun
‘karya ake mata ? Ko dan kuna i’kirarin yar uwarku ce ? Ku ina naku iyayen da har
kuka samu ‘kanwa? Ko anfada muku b…” be kai ‘karshen maganar saba sabida yadda Bobo
ya buga table d’in gabansa , rai a ‘bace yake kallan Mingus da ya d’an ja baya
lokacin da ya buga table , mi’kewa tsaye Bobo yayi sabida yadda ransa ya ‘baci ya
tabbata idan ya tsaya komai zai iya faruwa , “ No please come back son “ cewar Mr
president, cikin kwantar da kai da shiga abunda ba’a saka shiga Mingus ya furta “
Your excellency ka kwantar da hankalin ka , ni nan zan saka yar ka ta dawo ko suna
so ko basa ko , idan ba haka ba gabaki d’aya a ‘kwace mu’kaman su “ kusan lokaci
d’aya president da chief suka kallesa dan suma ya fara ‘bata musu rai , “ you can
do as you wishes “ cewar Bobo yana juyawa , tun kafun ya soma tafiya aka bud’e
‘kofar wajan , Victor da Anthony ne suka fara shigowa cikin kakin sojojinsu ,
lokaci d’aya suka matsa gefe , cikin takunsa na kullum ya soma takowa , gabaki
d’aya yau shigar ba’ka’ken kayan company celine yayi hatta takalmin ‘kasarsa da
yayi mugun yi masa kyau , gashin kamsa da kullum yake shan gyara nannad’e a
bayansa. Murmushi president ya sakar masa , chief kuma ya jinjina masa kai, har ya
‘kara ciki , ko kallan side d’in da Mingus yake be yiba , hugging d’insa president
yayi , shima kusan haka the same abunda chief yayi “ welcome Son , na d’auka ma ba
zaka zo ba “ cewar president , shiru Big Boss yayi batare da ya ce komai ba , kowa
yasan halin sa shiyasa gabaki d’aya basu damu da hakan ba “ Finally tunda ya
‘karaso nasan everything will be okay “ cewar d’aya daga cikin manya manyan
mutanan, Mingus kuwa sosai ya sha’ki abunda Big Boss yayi masa yanzu , so yake
kawai ya tunzura su yanda zai ‘kunsa musu ba’kin ciki , shiyasa yake fad’awa Bobo
maganganu , ganin Big Boss d’in da kansa Mingus ya furta “ Me kake ta’kama dashine
da har kake tunanin yin duk abunda ka ga dama ? Tun wuri ina shai da muku , kuje ku
d’auko yaran nan ku dawo dasu har gida kafun ranku ya ‘baci “, kyawawan idanuwansa
Big Boss ya zuba masa me ladaftar da mutane , shi kansa Mingus yadda Big Boss ya
kallesa sai da yasa maganar da yake sanyi ta d’auke , kallan second 4 Big Boss yayi
masa ya d’auke eyes d’insa akansa, wasu papers d’in Bobo ya mi’kowa Big Boss , sau
d’aya Big Boss ya bud’e papers d’in kafun ya ajjeta kan table d’in wajan , cikin
cool voice d’insa ya furta “ na tura su honeymoon for a week, after that ko waccen
su zata dawo da mijin ta”, mingus ganin haryanzu Big Boss ya’ki kula sane ya d’auki
paper d’in da Big Boss ya ajje ya yaga sune tare da ajje masa su , chief na
‘ko’karin magana suka ga Big Boss ya mi’ke daga kan kujerar da yake , Diamond watch
d’insa ya kalla tare da lumshe ido , ko step biyar Big Boss beyi ba ya dakata
sabida maganar da Mingus yayi “ karka manta kai d’in ma ba wani bane balantana ko
iyayen ka da ba’asan da su ba , balanta na kace zakayi tun ‘kawo dasu” ran Big Boss
ba ‘karamun ‘baci yayi ba , a hankali ya juyo da face d’insa , duk wanda yaga face
d’in sa bazai ta’ba cewa ransa a ‘bace yake , wani irin murmushin gefen baki Big
Boss ya saki da yayi mugun yiwa Mingus ciwo , cikin i dont care ya furta “ idan
na’ki sakin su me zakayi ?“ lokaci d’aya Mingus ya furta “ Zaku bar aikin da kuke
tun’kawo dashi, ko babu ‘kasa zata zauna “, saida yayi maganar tukunna kuma yaji
zuciyarsa ta bunga , dan baisan maganar da ya fad’a yanzu a fili ya fad’a ba ,
gabaki d’aya tunaninsa ya d’auka a zuciya yayi maganar, cikin tsantsan mamaki Chief
ya kallesa shi da president, hatta sauran mutanan saida sukayi mamakin maganarsa .
President zai yi magana Big Boss ya d’an mi’ka hannunsa , cikin sauri Victor ya
saka masa wani doguwar sar’kar diamond , daga gefe gefenta wasu abune tare da
tanbarin tutar ‘kasar da Big Boss bai ta’ba sawa ba , gabaki d’aya hankalin mutanan
wajan tashi yayi musamman ganin abunda Big Boss yake ‘ko’karin yi , chief zai yi
magana Big boss ya ajje musu sar’kar tare da kallon Mingus ,tun bayau ba yasan
munanan aikin Mingus Shiga gabaki d’aya basa ji tuwa dashi ,dukda ya kasance babba
amma mutum ne, me mugun sai kai , komai ya fiso ya samu akan wani, cikin husky
voice Big Boss ya furta “ Yes idan bana cikin ‘kasar ku zata fi samun kula , from
now on! Zaka zamu Wanda zai kula da ita “ yana kaiwa ‘karshen maganar sa ya juya ,
hankalin president ba ‘karamun tashi yayi ba musamman idan Big Boss ya ce ya ajje
aikin nasa , basu gama shiga rud’u ba Bobo ba ya ajje nasa ya bar wajan , hatta
Victor da Anthony gabaki d’aya ajje sar’kar su sukai dukda tasu bata diamond bace
kamar ta Big Boss da Bobo,suna fita President ya kalli Mingus cikin tsananin ‘bacin
rai , “ Daga yau an dakatar dakai , tare da kwace gabaki d’aya mihimman ta kaddun
ka , 24 hours kake dashi kawai idan har Big Boss da Bobo basu kar’bi sar’karsu ba ,
gabaki d’aya family d’inka sai sunyi prison “ yana kai wa ‘Karshen maganar sa ya
nufi wata ‘kofa shima mutanan nan guda hudu , chief ma ransa a’bace ya furta “ ina
bu’katar ka a d’akin amsa tanbayoyi “ gabaki d’aya Mingus neman fita hayyacin sa
yayi , a Tuna’nın sa abunda Big Boss yayi musu zai sa su fusata su yanke masa ko
wana irin hukunci ne shiyasa ya dunga fad’ar maganganun da zasu ‘bata musu rai ,
hannayensa gabaki d’aya ya d’ora akai , cikin rud’ewa ya ke furta “ Jesus”, ko
minti biyar beyi a wajan ba wayarsa ta soma ‘kara , d’aga war da zaiyi yaji labarin
d’auke masa ‘ya da kai , Mingus gabaki d’aya ya zare babu abunda yake furtawa sai “
Jesus “ , ya zaune a ‘kasan wasu sojoji guda biyu suka shigo falan , kowa kaga face
d’insa zaka ganta a d’aure , basu tsaya yi masa magana ba suka d’aga shi gabaki
d’ayansu.
Big Boss kuwa yana fitowa gabaki d’aya sojojin sa suka sara masa , cikin Sauri
Victor ya bud’e masa mota ya shiga , Bobo ma ya shiga d’ayan side d’in , gabaki
d’aya ragowar sojojin suma shiga motocin su sukai tare da mara musu baya ,kai tsaye
Dulles International Airport suka nufa , cikin ‘kan’kanın lokaci jirgin su ya tashi
zuwa New York.

****************

Tsaye Abla take jikinta sanye apron da ta d’aura a ‘kugunta sai cap d’insa da ta
d’aura shima , gaban ta Flour ne a ciki sai Luru ( kuka ) da ta d’auka a cikin
kwalinsa, sai kuma ji’ka’k’kiyar potash ( kanwa ) da itama sai da ta saka aka nemo
mata , a dole ta gaji da abincin su, shiyasa take itama taci d’an wake yau , su
Little suna falour suna mata dariya sabida jin abinda tace zata yi musu, shi little
tunda yake be ta’ba jin sunan d’an wake ba sai a bakinta , hatta Prince ma bai
ta’ba jiba sai ayau , ko wannan su sai tsokanarta suke akan ita kad’ai zata ci abin
cinta , itama tana musu dariya , uncle na gefe shima yana supporting d’in Abla ,
sosai tayi musu d’an wake me kyan gani da burgewa , sai cucumber da ta yanka tare
da tunatur da attaruhu tare da onion da Koran tattasai cikin wani bwol me shegen
kyau, ta samu fresh attaruhu guda biyu ta d’an daddakasu tare da matse leman tsami
a ciki , sai wani Maggi cube na ruwa da ta saka tare da mai da ruwa ta had’a ta
juya yanda komai zai ji ( Gaskiya duk wacce bata ta’ba cin d’an wake da wannan
had’in na Nijer ba gaskiya anbarta Abaya ). Tana gama wa Oil ta soya , Little suna
ganin ta fito da d’an waken suka dunga mata dariya “ Little yanzu wannan ‘kazantar
zakici ? I bet you bazai yi dad’i bafa “ dariya tayi masa tana girgiza masa kai “
No yaya little kar kazo kuma kace zaka cifa “ d’an ya mutsa face d’insa yayi “ Ni
bazan ci wannan jagwalgwalan ba “ hmm kawai Abla tace , cikin wani unique plate ta
zuwa ba uncle tare da ruwan Gee da ta had’a , sai cilli powder d’in da sai da ta
‘kara gyara sa shima , tunda Suka ga na uncle suke kallansa , d’an hararar su uncle
yayi “ ba ci zakuyi ba , tun da kunce ‘kazan tane, mu ku bar mu zamuci “ , yes
uncle kunce jagwalgwalo ne , but atleast zaku temaka mugada ci muji ya d’an d’anan
sa yake , ko little ?” Cewar Prince , da Sauri Little ya furta “ yes yaya prince ,
mu daman bamu ce zamu ci mata ba “ ta’be baki uncle yayi “ Kunji da gulmar ku “,
suma cikin wani plates din ta zuba musu, kafun su soma ci kamar zasu kai baki sai
suyi saurin ajjewa suna ya mutsa face , ganin hakan yasa Abla d’auke plates d’in “
No Lil please zamu ci fa “ da haka Little ya runtse idanuwansa tare da yin 1
spoon , shima prince kallan sa yake yana kira yaji ko zai yi amai, sai da ya cinye
tass na bakinsa tukunna ya fara ta’be face d’insa , “ bari dai na ‘kara 1 spoon
naji”tun daga 2 spoon d’in nan little ya share prince ya soma ci ganin haka shima
prince ya d’an d’ana “ Amma Little kai mugu ne Wallahi , shine zakayi mun shiru ?”
Ita dai Abla dariya kawai take musu, sosai suka ci d’an waken nan , sai da suka ci
suka ‘koshi tukunna suka saka game , sun dad’e abunsu suna game , saida suka gaji
dan kansu tukunna suka soma hira har wajan 11 idanuwansu biyu, “ Naga alama anan
zaku kwana “ cewar Uncle lokacin da ya mi’ke , shima cikin sauri prince ya mi’ke “
har na kusa mantawa da aikina “ gabaki d’aya sai kowa ya koma part d’insa .
Abla ko da ta koma d’aki ba bacci tayi ba dan yau gabaki d’aya neman baccin tayi ta
rasa , “King The Land “ ta saka ta cigaba da kallan korea d’inta , ita kad’ai sai
murmushi take , ta dad’e tana kallo har ta soma yin hamma abunta , tun tana tunanin
cigaba da kallan har bacci ya soma fusgarta, sai kashe system d’in tayi tayo
alwalar baccin ta , cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya d’auke ta .

Washe gari Abla tana idar da sallah bacci ya ‘kara d’aukar , ba ita ta farka ba sai
wajan ‘karfe 10 na safe , shaf shaf wanka tayi ta shirya cikin milk d’in riga sai
wandon jeans da ta saka da yayi bala’in yi mata kyau , turare ta fesa ka d’an sai
ta d’ora doguwar riga akai tare da rolling ta fito falourn , ta tsats tsaye ta
tarar dasu Uncle ga wani mutum da sai ro’kan uncle yake akan yana so yana Big
Boss , Bobo kuwa na zaune kamar be san yana yi ba , ba kowa bane face Mingus da
gabaki d’aya ya fice cikin hayyacinsa , tun jiya yake ‘ko’karin san ganin su Bobo
amma sojoji sun hana sa , da ‘kyar ya samu uncle ya sa baki har ya shigo cikin
falourn, uncle yana ganin Abla ya sakar mata murmushi “ Yawwa Daughter, please jeki
kira wo mun Big Boss a sama “ shiru Abla tayi kafun fa amsa masa da “Toh “ ta nufi
hanyar part d’in sa , tana zuwa sau biyu tayi knocking falourn sa shiru babu amsa ,
tana bud’ewa taga wayam babu kowa a cikin , na biyun ta bud’e ganin baya cikin
falourn , kafa d’unta ta d’aga cikin rashin damuwa ta juya da niyar komawa , Daidai
lokacin da shi kuma yake bud’e ‘kofar, sau d’aya Abla ta kallesa ta d’auke kanta,
kamar wacce aka saka dole ta furta “ Ina kwana?” Shiru yayi mata batare da ya amsa
ba , itama bata sake gaishe saba ta fad’a masa sa’kon Uncle , ta juya zata soma
tafiya ya finciko hannun ta da har sai da tayi ‘kara , ‘ko’karin kwace hannunta
take ya ‘kara matse hannun, cikin tsiwa Abla ta d’ago da dara daran idanuwanta da
suke faman shinning kamar zatayi kuka , bata re da ta kallesa ba ta ‘kara furta “
ka sakar mu hannu na “, ‘kin sakar mata hannun yayi , takai cine ya kama Abla bata
san lokacin da ta dam’ki hannun nasa ta gantsarawa cizo ba , sakin hannun nata yayi
tare da kallan inda ta cizan har hakwaranta sun fito sosai a wajan, ta juya da
niyar barin wajan ya finciko ya ‘kara dawowa baya , cikin Sauri Abla ta soma ja
baya zata ‘kara guduwa , ganin yadda yake ‘kara matso tane yasa ta ‘kara ja baya
bata san lokacin da ta jingina da bango ba , sai ganin ‘karasowar sa tayi, kauda
kai Abla tayi tare da tsuke face d’inta , sosai ya ran’kwafo Daidai face d’inta
yana kallan yadda ta tsuke face d’in ta , cikin cool voice ya furta “ my food “,
yana fad’an hakan ya d’an matsa , itama Abla bata kalle saba tayi wucewarta , sai
data ga tabar falourn tukunna ta saki ‘karamun tsaki “My food !” Ajje ni kayi da
zan kawo maka abincin, wallahi sai dai ko menene kayi mun amma babu wani abinci da
zan kawo maka .

Tana sakkowa ta fad’awa Uncle gashinan zuwa , Mingus na zaune ya buga ta gumi kamar
bashine ya gama kuri ba jiya , Abla kitchen ta koma ta had’a kayan breakfast d’inta
dakanta cikin d’an ‘karamar tray ,ita kad’ai sai mita take , mistakenly pan d’in da
take anfani dashi ya goce gabaki d’aya yayo kanta zai fad’o mata , bata san ya akai
ba sai ji tayi an fincikota……

https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅
AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____37💞

A jiyar zuciya Abla ta saki ganin wanda ya fincikotan,” Lil baki ji dai ciwo ba
ko ?” Cewar Little d’auke da bottle water a hannunsa , “ yes ban jiba , thank you
so much Yaya Little “ , kansa ya jinjina mata , “ its okay ! But next time ki kula
sosai , kinga zaki iya jima kanki ciwo !” Cewar Little , murmushi kwance akan face
d’inta ta furta “ Insha Allah , but Yaya little kana bu’katar wani abu ne yanzu ?”
‘Dan kallan kitchen d’in yayi tare da knodding kansa “ yes ina tunanin na girka wa
Yaya Big Boss abinci ne , and naga kema abincin zaki ci yanzu” shiru Abla tayi masa
kamar bazata bashi amsa ba sai kuma ta nuna masa mata tray d’in , “ it’s okay ! Ka
kai masa nawa ni sai na had’a wani “, “ No! No ! Kici abincin ki , inyaso sai na
samar masa wani abun” girgiza masa kai tayi duk da bataso “ it’s okay , ai ba
wahala yanzu zan gama , okay?” Murmushi Little y sakar mata “ thank you dear but
zaki had’a masa coffee please? Kafin yaci komai yana san fara shan coffee , please
just 1 cup”murmushin ya’ke Abla ta sakar masa “ it’s okay zan had’a masa yanzu”.
Little na barin kitchen d’in Abla ta shagwa’be face d’inta kamar me shirin sakin
kuka , har ga Allah bataso had’awa Big Boss coffee d’in ba , zata yi masa ne kawai
sabida Little , ita kad’ai sai kunbura face take , irin coffee d’in kwanaki ta
had’a masa amma wannan ma ta canza flavor , har zata fita wani tunani ya fad’o
mata, ‘karamun dariya Abla ta saki kafun ta dawo cikin kitchen d’in, cilli powder
ta d’auko da babu komai a cikinsa ta barbad’an , duk da hakan be i she taba sai da
ta d’Akko ji’ka’k’kiyar potash ( kanwa)shima ta d’iga a ciki, spoon ta samu ta d’an
d’ana , cikin Sauri ta fito dashi sabida yajin da taji, ga kuma uban kansa da ta
saka sai coffee d’in ya zama kamar magani, a hankali ta furta “Mutum kullum cikin
kugun ta , kaima kaji idan da dad’i”sai kuma tayi saurin toshe bakin ta Sabida kar
wani ya jita . Tana fitowa taga babu mutumin d’azu , shima Bobo baya falourn sai
uncle da prince , kamar tayi ihu haka taji ganin dole ita zata kaiwa Big Boss
coffee d’insa , duk a tunanin ta Little na jiran ta shi zai kai mata , d’an turo
bakinta tayi kad’an kamar wata yarinya sai kuma ta shagwa’be face d’inta , “ Lil
yana ga kin tsaya anan ? Ki zo ki zauna mana “ cewar Prince , kamar tayi kuka ta
furta “ Zan kaiwa Yaya Big Boss coffee d’insa ne “, okay kawai prince yace mata har
ta juya zata soma tafiya Little ya fito daga elevator , ajiyar zuciya Abla ta saki
a Tuna’nın ta zai kar’bi coffee d’in sai kuma ya nuna mata hanya “ thank you Lil ,
nasan yanzu yana sama yana jiran coffee d’in, please kai masa “ kanta ta jinjina
masa tana juyawa ta turo d’an ‘karamin cute lips d’inta , Daidai ‘kofar falourn sa
da zata shiga sai data ‘kara duba coffee sosai ganin bazai gane ta saka wani abun
ma ta saki ‘karamun murmushi kad’an. Knocking ‘kofar tayi taji shiru daman tasan
za’a rina dan bata ta’ba ganin sa ya zauna a wannan falourn ba , tana shiga kuwa
taga baya ciki, ita kad’ai sai ‘kun’kuni take har tayi knocking d’in falourn , sau
biyu tana knocking ganin be bud’e ba ta tura ‘kofar a ‘kufule kamar Itace tayi mata
laifin.
Big Boss na zaune kan sofa yayi crossing legs d’insa , idanuwansa ma a kulle
sai d’an siririn gashinsa ya d’an hau kan face d’insa , a tunanin ta bacci yake
shiyasa tayi sallama a hankali ta yadda bazai jiba , hatta takalminta cireshi tayi
ta soma sand’a a hankali kamar mara gaskiya, inda taga breakfast d’in ta na d’azu
ta nufa a hankali da nufin ajje wa , daga sama taji saukar muryarsa “ My Coffee”
kallan coffee d’in tayi lokaci d’aya zuciyarta ta buga sabida tuno abunda tayi masa
, ita gabaki d’aya ta manta da cizan sa da tayi d’azu sai yanzu, amma gabaki d’aya
Abla ta shanye tsoranta a ciki kafun ta juyo a hankali fuskarta ba a sake ba ,
sannan ba a d’aure ba . Ka d’an ta matso tare da mi’ko masa coffee d’in amma ko
uffan bata ce ma , shima da har yanzu idanuwansa a kulle suke be bud’e ba sannan be
kar’bi coffee d’in ba, d’an hararar sa tayi kad’an kafun a hankali ta furta
“Mugu”, karaf maganar ta sauka a cikin kunnan sa , a hankali ya soma bud’e eyes
d’insa har ya gama bud’e su gabaki d’aya , lokaci d’aya Abla ta ja baya kad’an
Sabida yadda taga ya koma mata asalin Big Boss d’in sa , wani irin kallo ya je fa
mata , cikin Sauri ta d’auke idanuwanta itama tana ‘kana shan kunu, kallan second 5
yayi mata ya d’auke kansa , a hankali ya motsa cute lips d’insa kamar me sanyi
magana , Abla tafi 2 minutes a tsaye bece mata komai ba itama bata ce masa ban,
ganin ta gaji da tsaruwar ne ta furta “ ga coffee d’inka “ shiru yayi mata kamar be
ji taba , ganin yayi banza da ita yasa itama bata kuma ‘ko’karin yin magana ba.

Sai da ya mula dan kansa tukunna ya mi’ka hannunsa alamar ta bashi coffee d’in,
cikin ‘kasa ‘kasa da idanu Abla ta harare sa yadda bazai ganta ba , tana ajje masa
coffee d’in kuma ta juya da saurin zata bar falourn ya furta “ wait “ dummmmm Abla
taji zuciyarta ya buga tsoranta ma karya coffee d’in agabanta, duk plan dinta ta
dauka Little ne zai kawo masa coffee d’in shiyasa ta zuba , d’an waiwayo wa tayi
kad’an dan ta duba ko ya ajjesa , ga mamakinta shan coffee d’in yake a hankali, ya
wun ma’kogwaranta ta had’iye gabaki d’aya ta tsargu, sau uku King yasha coffee d’in
tare da mi’ko mata , cikin sauri Abla ta ‘kara juyawa zata bar wajan, “ come back “
ya fad’a a hankali batare da ya d’ago ya kalletan ba , kallan coffee d’in Abla
tayi taga ko rabi be shaba , kana kallanta kasan bata sa gaskiya kamar wacce take
jira a tankata ta fashe da kuka , a hankali ya ‘kara furta “ just 3 minutes na baki
ki shanye ki bani cup d’in”,marairaice fuska Abla tayi dan tasan bazata iyasha ba ,
cikin sauri ta furta “ Na ‘koshi “ d’an d’ago da eyes dinsa Big Boss yayi “ idan
bazaki iya sha , bari na baki a baki” cikin sauri Abla ta d’aga coffee d’in tana
sawa a baki ta futo dashi sabida uban yajin da taji , ga kanwar da ta saka sosai a
ciki ya fito, bece mata komai ba sai ma ‘kara crossing legs d’insa da yayi , ‘kara
kallan coffee d’in Abla tayi kamar zatayi kuka , ganin ya kalli agogon hannunsa ta
‘kara banka masa harara kamar idanuwanta zasu fad’o ‘kasa. A karo na biyu ta ‘kara
saka coffee d’in a bakinta , da ‘kyar ta iya had’iye sa sabida uban yajin da taji
ga tsamin kanwa ya ‘kara ‘bata mata bakinta , yadda take shan coffee d’in nan sai
ta bawa mutum tausayi ga uban gumi da ta had’a tana sha tana hawaye fuskarta har ta
fara ja , amma tsabar mugunta irin na Big Boss bai hana ta sha ba ,itama kuma da
taurin kai ta ‘ki basa hakuri, tana gama ta juya sabida haushin sa da take ji
kamar ta samu takalmi tai ta dukansa , sai da yaga taje daf da handle ya ‘kara dawo
da ita , yanzu kam a ‘kufule Abla ta dawo batare da ta ce masa komai ba , kallan
tray d’in da Little ya ajje yayi kad’an , kafun ya furta “ Eat them also” wani irin
kukane Abla taji yana ‘ko’karin kwace mata , gabaki d’aya haushi da takaicin Big
Boss ne ya cika ta , bata san sanda kwalla ta sakko mata ba , a zuciye ta d’akko
tray d’in zata wuce , nan ma still sai da yasa taci abincin , tun kafun tayi rabi
ya mi’ke tare da furta “ wait here “ kallan bayan sa Abla tayi tare da jan siririn
tsaki ganin yashige cikin d’aki , “ Mugu, Azzalumi , Allah sai ya saka mun mutum
babu abunda ya sani sai mugunta, fuska fara zuciya ba’ka , “ ta fad’a har da
hawayen ta , cikin sauri ta mi’ke ko d’aukan kayan abincin batayi ba ta yi saurin
nufar handle , cikin sauri kuma ta dawo ganin white handkerchief me kyau a ninke a
inda ya tashi, sabida haushin da ya bata cikin sauri ta d’auka ko tsoran ya
kamata bata yi , takalmin ta da ta shigo dashi ta d’auka ta goge takalmin dashi ,
sannna ta cukur kud’eshi, ita kad’ai sai hararan handkerchief take kamar shi yayi
mata lefin. Motsin da taji kamar ana nufo ‘kofa yasa ba shiri ta mayar masa da
handkerchief d’in ta arta a guje , sai data fita daga part d’insa tukunna ta goge
hawayen face d’inta , ga bakinta sai yaji yake mata.

Tana sakkowa ta tarar da Uncle da Yaya bobo zaune a falo sai prince , gaishe da
Yaya Bobo tayi sabida yadda harshanta yake mata yaji ko magana bata sanyi “ how are
you Lil?” Cewar Bobo, cikin sauri tayi knodding kanta kad’an “ Alhamdulilah yaya
bobo” kallan side d’in prince tayi ganin Little baya wajan , a hankali ta furta “
bari naje na d’auko abu sai na dawo , “Okay “ cewar prince, a hankali ta soma
tafiya , tana ganin ta ‘bacewa ganin su ta saka gudun, kitchen kawai ta fad’a tare
da d’akko strawberry smoothie me sanyi ta bud’e shi ko neman cup batayi ba ta kafa
a bakinta tana sha , sai da ta sha kusan rabin sa tukunna ta ajje , amma still
yajin be tafi ba yadda take so kwanda kanwar da take ji kad’an kad’an. Inibin
cikin ta d’auka kad’an shima ta soma ci, kad’an taci a tajje tuno da chocolate d’in
d’akinta , cikin sauri ta ‘kara guduwa Allah ya temaketa su Bobo baza su ganta ba ,
tana shiga chocolate da alawoyi kawai ta d’auka ta soma sha , tana sha tana hawaye
idan wani chocolate d’in be mata ba ta soma mita kenan, sai da ta sha kayan za’ki
sosai tukunna ta dakata tana ajiyar zuciya ganin yajin saura kad’an, yadda ta
kwanta d’in ba ‘karamun dad’i yayi mata ba shiyasa tayi kwanciyar ta kan unique
carfet d’in d’akin. Ko minti 30 Abla batayi ba akwance sabida yadda taji cikin ta
ya d’aure , cikin sauri ta nufi toilet, at least sai da tayi 10 minutes a ciki
kafun ta fito sai faman zare idanuwa take, ga wani uban gumi da ta had’a a fuskarta
, hancin ta har wani ja ja yake , ga gashin ta da ya fito duk waje. Kamar zatayi
kuka ta furta “ Mugu kawai me kamar da Elizabeth , mutum kullum cikin d’aure fuska
dole ka dunga kula da zaki ai, Allah sarki jama’a bayın Allah , nasan banı kad’ai
yake cin zaliba, kai sai kace Bishiyar giginya ”, yadda Abla ta dafe tana masifa
wani sai ya d’auka Big Boss d’in ne a gabanta take surfa masa bala’I, babu abunda
ya fad’o mata sai kararan da ta sakawa su Zinariyya, ji take da zata samu kararan
nan da babu abunda zai hana ta fesa masa shima.

*****Gabaki d’aya wunin ranar a d’aki Abla tayi zamanta sabida haushin Big Boss da
take ji , sai da ta tabbatar baya cikin gidan tukunna ta fito falour, har lokacin
hancin da d’an jansa. Tana fitowa kuwa suka saka game abunsu, tun suna yi har suka
gaji , prince yaja wayar sa , Little ma yaja tasa wayar banda Lil da ta koma kallo,
d’an d’agowa Little yayi ganin Abla na kallo kafun ya mayar da kallansa kan Tv da
take kalla , ganin ba wani abun ake ba sai labarai, tashi yayi ya bar falourn
gabaki d’aya basu kula da mi’kewar saba , kai tsaye d’akın su ya nufa , cikin
mintuna da basu fi 5 ba ya dawo d’auke da wani kwali a hannun sa , yana zuwa be ce
mata komai ba sai ya d’ora mata kwalin akan cinyar , kallan kwalin tayi kafun ta
kallesa alamar ‘karin bayani, ido d’aya Little ya kashe mata “ For you” da Sauri
Abla ta zaro ido dukda bata gama tantance abunda yake cikin kwalin ban, tana shirin
fara masa Godiya yayi saurin toshe kunnuwanta “ A beg karma ki fara , ni banaso “,
murmushi Abla tayi masa fuskarta cike da annashuwa “ thank you so much Yaya Little
“ d’an hararar ta little yayi kafin ya furta “ ban kar’ba ba , just open it my
friend “ murmushi Abla ta ‘karayi tare da furta “ thank you “, ‘karamun box d’in ta
kalla duk da bata gama Tantance abunda ta gani ba , a hankali ta bud’e kwalin cikin
sauri ta zaro idanuwanta waje ganin iPhone 12 babba a ciki, har wani kwalla ne suke
‘ko’karin tarar mata cikin ido “ Yaya Little… “ cikin Sauri Little ya furta “ it’s
okay bari na nuna miki yadda zakiyi anfani da ita, everything yana ciki nuna miki
kawai zanyi akwai sim akwai card and data every is intact “, ita dai Abla sai faman
murmushi take gabaki d’aya tarasa abunda cewa gashi ya d’aure mata face a dole baya
bu’katar Godiyar ta . Cikin ‘kan’kanin lokaci Little ya nuna mata yadda zatayi
anfani da wayar , komai sai da ya nuna mata , Abla babu abunda take sai murmushi
hatta phone number d’insa sai da ya saka mata da ta su Prince , gabaki d’aya
Numbers d’insu sai ya saka har da ta Big Boss da iya familyn ne zasu sameshi duk
lokacin da suka kira sa , har wajan la’asar tana suna zaune a falourn tunda babu
Wanda zatayi hira dasu a wayar , ana kiran sallar la’asar ta koma d’aki , sai da
tayi sallah tayi komai tukunna ta d’auki wayar da little ya bata , Duk abunda ya
koya mata sai data ‘kara shiga ta gani gabaki d’aya , last wajan numbers tashiga ,
lokaci d’aya taga numbers d’insu gabaki d’aya , hararar ta Big Boss tayi kamar
idanuwanta zasu fad’o , har zata goge number sai ta fasa ganin Little yayi mata
saving da Yaya Big Boss , sai tayi sauri ta goge sunan ta saka masa HORROR tare da
hotan d’an Aljani agefe. Camera Abla ta shiga ganin yadda face d’inta ta fito
sosai , guda d’aya tayi snapping tana gwalo , tana ganin yadda hotan yayi ta
‘kyalkyale da dariya har tana kulle face d’inta , ita kad’ai sai dariya take abunta
har da fad’awa kan gado.

************
********
GREENWICH VILLAGE
( Honeymoon lover’s😹🤣)

Wasu irin tsofaffin gida je ne aje aje cikin ‘kauyen Greenwich, amma ko wana layi
zaka ga tsaf tsaf babu wani hayani ko surutun mutane a Wajan . A bakin wani gini
motocin su Robert suka tsaya, tundaga subun ginin mutum zai san ba ‘karamun dad’ewa
gidan yayi ba , tun kafun a ce su fito Alice ta soma zazzaro idanuwanta , tun
shigowar su Garin take tottoshe hancin, tundaga sama har ‘kasa take bin ginin da
kallo da ko gate babu a jikinsa sai ‘kofa , LG kuwa kukan takaici kawai take ganin
irin Wajan da aka kawo su , ko ina ka wai ga zaka tarar da tsofaffin gida je gabaki
d’ayansu kusan yanayin su d’aya gashi ko wana idan ka duba babu gate a ciki, daga
can d’an nesa dasu wasu tsofaffun turawa ne suke kallan , musamman lokacin da
sukaga su Alice na kuka sai suma su bud’e bakinsu da ko hakwara babu suna
kwaikwayon su Alice , da su Alice sun kallesu zasu yi Sauri su koma , suna juyawa
tsofaffun nan zasu ‘kara fitowa gabaki d’aya gashin kansu fari ga fuskarsu d’aya
gama ya mutsewa alamar tsufa .
Fito da su jabcon da suka gama jigatuwa akai dan kafun su fito ma sai da Robert ya
‘kara musu shegen duka . Wata mata ce ta fito daga cikin gidan hannun ta d’auke da
sanda tana dogarawa, itama gabaki d’aya tsufa ya gama bayyana a jikinta ga gashin
ta da yake fari tas dashi, kallan ta su Alice sukai ganin yadda take dogara sannan,
itama matar kallan su tayi d’aya bayan d’aya kafun ta kalli Robert “ wad’annan ne
‘yan iskan yara ?” Ta fad’a cikin turanci , cikin girmamawa Robert ya furta “ Yes
Mah” kanta ta jinjina masa tana ‘kara bun su Alice da kallo da lokaci d’aya gabaki
d’aya sukaji shakkar matar ya shigesu, a tsawa ce ta furta “ ku biyo ni, ‘yan iskan
yara “ cikin Sauri gabaki d’aya suka biyo bayanta har da su Ossy da duk lokacin da
LG ta waiwayo yake ‘boye kansa sabida be manta da irin dukan da tayi masa ba . Suna
shiga suka soma bin falourn da kallo gabaki d’a wasu tsofaffun kayane a ciki, ga
uban abubuwan da aka zubar da ya ‘bata gabaki d’aya falourn , hatta jikin bango sai
da aka ‘ba’b’bata , lokaci d’aya Alice ta soma amai Sabida yadda ta ga gidan,
sandar ta matar nan ta d’aga ta kwala mata tare da jefo mata wani ‘kyalle ta goge ,
kuka Alice ta saka tun da take bata ta’ba d’aukan ko jaka ba sai dai a mi’ko mata ,
yau gashi zata goge aman da tayi Wanda bata ta’ba , zata yi complain matar ta ‘kara
buga mata sanda tare da zazzare mata mitsi mitsin idanuwanta , cike da tsoro Alice
ta d’auki ‘kyanlan shima tana yatsuna face , jinjina kai kawai matar tayi ganin
abunda Alice take , kallan su Robert tayi kafun ta furta “ Babu matsala zaku iya
tafiya “ okay mah “ cewar Robert kafun su bar cikin gidan , tsayawa kallan yadda
gidan yayi kaca kaca sukai cikin daka tsawa MADAM GLO ta sa su kalleta , suna
kallanta ta soma tattakawa tana kallansu d’aya bayan d’aya kafun ta dam’ki kan
Alice da ta soma ihu kamar wata mahaukaciya haka MADAM GLO ta dunga jijjiga mata
kai , a tsorace LG ta soma ja baya ganin yadda Itama GLO ta soma kallanta , ware
‘kafafuwanta madam glo tayi ta biyo LG a guje , itama LG tana ganin haka ta saka
ihu ta arta a guje, yadda GLO take gudu kamar wata a gwagwa shine ya ‘kara tsorata
LG suna su Alice Suka soma ihu, a hankali kuma ta juyo da kallanta zuwa su Jabcon
da suma suka fara ra’bewa a jikin bango, gadan gadan ta biyo su da sanda suma suka
dunga ihu , gabaki d’aya sai MADAM GLO ta hauka tasu suka fara guje guje da ihu su
had’ai , sai da ta tabbatar tsoran ta ya shiga zukatansu tukunna ta dakata , a bun
mamaki Aushe lokacin da Madam Glo take rikitasu Ozzy d’anewa hannun LG yayi, idan
ka kallesu sai ka d’auka Wanda ya d’auki yaro tana Ankara da abunda tayi ta nakasa
a ‘kasa kuwa , itama Alice ganin ta d’ane a cinyar Jabcon ta wanke face d’insa da
mari. Cikin had’e rai MADAM GLO ta tuna musu kayan gyaran gidan , “ hour d’aya na
baku ku gama gabaki d’aya aikin da zan saku idan ba ranku ya ‘baci “ cikin Sauri
Suka d’auki kayan suka soma gyara falourn , sai haki suke gwanda jabcon da ossy da
suke aikin amma Alice da LG babu abunda sukayi gabaki d’aya sun jigata , suna
gamawa madam glo ta sakasu gyara wasu d’akuna guda uku, kowanne da tsohon gado a
jikinsa , ga kuma ban d’akin guda biyu d’aya a cikin d’akı sai d’ayan a tsakan
kanin d’a kuna guda biyu, suna gamawa madam glo ta basu flowers akan su watsa akan
gadon , hakan kuwa sukai d’aki d’aya ne kawai basu sawa flower ba , wasu mattun
kaya takawo musu akan su canza kaya , cikin su babu Wanda yayi Tuna’nın shiga
toilet musamman LG da Alice da suke ‘kan’kamunsu, suna gamawa ta kawo musu wani
irin taliya me shegen ruwa gabaki d’aya kasa ci sukai sai kallanta da suke, banza
Madam Glo tayi musu tayi wucewarta.

********9:30pm gabaki d’aya ta kora su d’aya , Alice da Jabcon, itama LG da Ozzy ,


gabaki d’aya ta saka su hawa kan gadon da suka watsa wa flower , saida zata fita
tace musu kusha soyayya lapiya, tana fita LG ta kalli Ozzy cikin Sauri Ozzy ya
sauka daga kan gadon ya koma gefe a ‘kasa , a d’akin su Alice ma , cikin Sauri
Jabcon ya saukar mata daga kan gadon sabida irin kallan da ta jefa masa , gabaki
d’ayan su kallo kallo suke jefa wa juna musamman su Alice da suke ji kamar suje su
sha’kesu su mutu, suna zaune ko wannensu yana jefa wa d’an uwan sa mugun kallo suka
ji gabaki d’aya wutar gidan ta d’auke , cikin sauri Alice da Jabcon suka rungume
juna dama duk matsorata ne , basu san ya akai ba sai ganin ‘karamun haske kawai
sukai da ya ‘kara har gitsasu suka kuma kurma ihu, a hankali ta d’ago da fuskarta
da gabaki d’aya wasu abubuwane a fuskar ga farin gashin ta a hargitse, gabaki d’aya
sai tazama hoto musamman yadda take wangale hakwaranta , su Alice babu abunda suke
sai ihu, bakinta ta turo musu alamar kiss , cikin wani irin murya ta furta “ Kiss!
kiss “ a hargitse su Alice suke kallanta ga wani irin gumi da suke yi cike da
tsoro, ihu ta saka suma su Alice suka saka ihu, gashin Alice ta janyo ta tsinka
mata mari kafin ta janyo kan Jabcon shima , hakan be ishetaba dan dole ta dunga
had’e musu fuska a dole sai sunyi kiss , gabaki d’aya ta haukata su Alice ,ita
kad’ai sai faman firgitasu take.
A d’akin su LG ba lokacin da aka d’auke huta cikin Sauri ta nufi ‘kofa da
niyar guduwa suka ga an bankad’o musu ‘kofa , tsofaffin d’azu ne suka shigo cikin
d’akin gabaki d’aya sun canza kamannin su sai suka koma kamar wasu ‘kananan aljanu,
da sun kalli su LG zasu ‘kyal’kyalle musu da dariya , suma kamar abunda Madam Glo
tayi suna haka sukai musu , su da suka fi kowa har kan gado suka sasu kwanta suna
watsa musu flower , Sabida tsabar firgita LG bata san lokacin da fitsari ya ‘kwace
mata ba , gabaki d’aya cikin daran nan madam glo da tsofaffin nan suna hana su
Alice sakat sai da suka tabbatar sun wajigasu, a dole sai da suka su rungume juna ,
idan kunga yadda Alice take toshe hancin ta sai ta Baku dariya musamman yadda
Jabcon yake nunfashi gabaki d’aya hudodin hancinsa a fuskarta.

https://chat.whatsapp.com/EgRmBePVeNnLUQh1Rrzm1F

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____38💞

***NYC****
Gudu take sosai cikin kurmun daji da babu ko d’igon haske banda ba’ki’kin da wajan
yayi, daga gefe wasu irin kukane yake tashi ta ko ina a cikin dajin me tsoratar
wa , yadda take jin kuka na nufo ne yasa ta ‘kara ‘karfin gudun nata , tana gudu
tana jin sunanta da ake ta faman kira , data wai ga sai taga rami kamar za’a ja
wota, daidai zata wuce ta wata ‘kofa taji wasu murya na kiran sunanta suna mi’ko
mata hannu wansu, lokaci d’aya Abla ta tsaya tare da waiwayo wa , gabaki d’aya bata
ganin fuskokin mutanan sai da muryarsu da take ji, cikin sauri ta nufi inda take
jin muryoyin su , “ ki temaka mana , ki temaka mana “ shine abunda mutanan suke
cewa , saurin ta Abla ta ‘kara daniyar zuwa wajan su, ko step uku batayi ba taga
kamar muryar mutanan da take ji yayi ‘kasa alamar sun fad’a rami amma duk da hakan
bakin su be dena ambatan “ ki temaka mana ba “****

A firgice Abla ta farka daga bacci da ya d’auketa , gabaki d’aya gumi ya


ji’kata kamar babu sanyin Ac a d’akin , runtse idanuwanta Abla tayi tana karanto
duk adduar da ta zo bakinta , jikinta har yanzu be dena rawa ba , shiyasa tayi
saurin janyo wayarta ta kunna ‘kirar sudais tana ‘kara lumshe idanuwanta,ta jima
tana sauraran karatun Al-qur’anin kafun ta soma a jiyar zuciya sabida sau’kin da ta
samu cikin zuciyarta . A hankali ta ‘kara matso da wayar daidai saitin ta, tana
‘kara karanta addua cikin zuciyarta , kafun ta samu kwanta har lokacin karatun da
take ji bata kashe ba.

THE NEXT DAY


ko da safe haka Abla ta tashi a sukuku, gabaki d’aya mafarkin da tayi jiya ya tsaya
mata arai , da ta kulle idanuwanta sai taji kamar suna ambatan sunanta . Kawar da
tunanin tayi a gefe lokacin da Little yake sakkowa , “ Lil yau kin tashi da wuri fa
“ d’an ‘karamun murmushi tayi sabida gabaki d’aya yadda take jin kanta not in the
mood “ Yaya Little ina kwana?”, sosai ya kalleta ganin tayi magana in a cool way ,
“ Lil lapiyan ki ‘kalau kuwa ? Ko baki da lapiya ?” ‘Dan zaro masa ido tayi da
mamaki “ No! Lapiya ta ‘kalau fa “ har yanzu be d’auke idanuwan sa a kanta ba ya
furta “ Are you sure?”! da sauri Abla ta furta “ yes”, knodding kansa yayi alamar
gamsuwa kafun ya furta “ in a few minutes su Yaya zasu fito , sai muci breakfast
d’in mu all a tare , ko ?” A wannan karan itama Abla knodding kanta tayi batare da
tace komai ba , haka kawai take jinta wani irin kamar ba ita ba .

9:30am gabaki d’aya suka fito banda Big Boss , a maimakon su jira sai suka nufi
dinning abun su , tunda sun san ba yanxune zai fito ba , har aka gama breakfast
d’in Abla bata ci wani abinci dayawa ba , ganin idanuwansu ne yasaka take tuttura
abincin gudun kar suyi mata magana. A na gamawa ta mi’ke zata tafi Bobo ya dakatar
da ita “ Lil can you make a cup of coffee ?” A hankali Abla ta furta “ yes !” Tana
nufar inda coffee maker yake , komai cikin sanyi take yin sa yau, tana gama had’a
coffee d’in ta d’akko masa , girgiza mata kai yayi tare da nuna Mata upstairs da
hannunsa guda d’aya “ Not for me ! Ki Kai masa sama “ ta gane abunda yake nufi, “
Toh Abla Kawai tace masa ta nufi hanyar part d’insa . Tana hawa kai tsaye falournsa
na biyu ta shiga tunda tasan bazata tarar dashi a cikin falourn farko ba , ana
biyun ma sai taci rashin sa’a baya falourn , kamar zata ajje masa coffee d’in ta
wuce sai taga rashin dacewar hakan , ‘kofar bedroom d’in sa tayi knocking sau
d’aya, shurun da taji anyi mata yasa ta ‘kara knocking a karo na biyu , still ba’a
amsa mata ba , zata juya taji kamar an bud’e ’kofar kad’an , a hankali ta shiga
cikin d’akin bakin ta d’auke da sallama , da Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa
ganin sa sanye da Singlet sai dogon ba’kin wandon jikin sa , sau d’aya ya kalleta
ya d’auke eyes d’in sa , tun kafin tayi magana ya d’an nuna d’akin da hannun sa ,
kamar Wanda aka saka dole ya furta “ Ki gyara mun”, be jira jin amsar taba ya shige
cikin dressing room d’insa , bin bayan sa da kallo Abla tayi tana hararar sa ‘kasa
‘kasa ,ganin bata da wani za’bin yasa ta ajje coffee d’in hannun ta ta soma gyara
masa d’akin , mistakenly bata san ganin ya akai ba , sai ganin light d’in d’akin ya
d’auke gabaki d’aya , a mugun rikice Abla ta kwalla ihu, lokaci d’aya mafarkin da
tayi d’azu yana ‘kara dawo mata cikin kai , ga gudun d’akin da gabaki d’aya ya
‘kara hautsina ta , almost 2 minutes sai faman ihu Abla take gabaki d’aya ta
birkita kanta , ita kanta batasan me taneyi ba , ji tayi an finciko ta , lokaci
d’aya Big Boss ya kunna light d’in da kashe , wani ihun Abla ta saki tare da
sulalewa ‘kasa a sume , Sabida yadda tayi arba da ‘ka’k’kar far damtsen hannun sa
ga shi ko riga babu a cikin sa . ‘Karamin tsaki Big Boss ya ja ganin yadda ta sume,
a hankali ya soma bin d’akin da kallo gabaki d’aya Abla ta ‘kara binkita shi ,
hatta saman bed d’insa gabaki d’aya ta cukur kud’asa. Lips d’insa ya taune kad’an
tare da komawa cikin dressing room d’in sa , almost 10 minute yayi a ciki kafun ya
fito har lokacin Abla tana kwance a ‘kasa , ruwa ya d’akko mana sanyi ya soma zuba
mata a fuska , a firgice Abla ta farka sabida ruwan da taji a kanta , har lokacin
be dena zuba mata ruwan ba sai da ya juye mata shi gabaki d’aya a jikinta .
“ Just 10 minutes na baki ki gyara abunda kika ‘bata , sannan ki d’auki dirty
legs d’inki and leave this place immediately “ ko kallansa Abla batayi ba Sabida
abunda yayi mata , da tayi niyar barin d’akin saidai in kashe ta ne yayi sai kuma
ta fasa , ganin ya d’auki system d’insa ya bar cikin d’akin. Cikin hanzari ta soma
gyara masa d’akin, hawayen da bata san na mene ne ba suna sakko mata cikin idanu,
tana gamawa ta fito daga cikin d’akin sabi sanyin da takeji bakinta har rawa yake .
A falour ta tarar dashi yana operating system d’insa , batare da ta kallesa ba ta
furta “ na gama “ har ta wuce ya dakatar da ita , cikin wani black wallet me shegen
kyau ya d’auko wani paper note na kud’i guda d’aya ya jefa mata, ko arzi’kin kar’ba
da hannun ta bata samu ba , cikin ta’be baki ya furta “ For your work”, kallansa
tayi tare da kallan kud’in da yake fad’i a ‘kasa , ji tayi hawaye na shirin zubo
mata tayi saurin had’iye su , hannu ta saka ta d’auki kudin lokaci d’aya wani
murmushin ta kaici ya fito mata , ko uffan bata kuma ce masa ba ta fice daga
falourn, kusan saura kad’an suci karo da Bobo da yake ‘ko’karin shigo cikin d’akin,
sau d’aya ya kalleta ya girgiza kai , cikin tausasa murya ya furta “ ki je ki canza
kayan jikin ki , kar mura ya kama ki , nan da 2 hours ki same ni a garden “ a
sanyaye Abla ta furta masa “Tom “ , shi kuma ya wuce falourn Big Boss .
“ Na d’auka kayi accepting nata ? Why please Dude? “ cewar Bobo Lokacin da
yake shigowa cikin falourn , ko sau d’aya Big Boss be d’ago ya kalle saba ya cigaba
da abunda yake , sama Bobo yayi yana ‘kara fuskantar Big Boss “ magana nake maka fa
, why are you treating her like this ? Yaushe zakayi accepting d’in ta as a family
of this house ?”da kawa tawa Big Boss yayi cikin ido ya kalli Bobo ,” She will
never be !” , d’an murmushi Bobo yayi kafin ya furta “ Really ? Nasani Kai ma
kasani , da aiko ta akai dan ta cutar da mu da a tun ran farko zamu gane , da
bazata ta’ba yin kwana d’aya a cikin gidan nan ba , please ka sassautawa yarinyar
nan , duk da bansan labarin taba nasan itama ta sha wahala a rayuwar ta” d’an ta’be
bakinsa Big Boss yayi batare da ya sake cewa komai ba , shima Bobo mi’kewa yayi
tsaye yana kallan Big Boss , “ Bana so kayi abunda zai zamo maka matsala nan gaba ,
i know you very well , bansan menene ka ke shiryawa ba , but please don’t hurt her
“, yana kai ‘karshen maganar sa ya bar falourn , shima Big Boss ba tare da damuwa
da abunda Bobo ya fad’a ba ya cigaba da aikinsa.
Kamar yadda Bobo ya umarce ta , wajan ‘karfe 12:10pm ta nufi garden d’in, a
zaune ta tarar dashi cikin wata runfa me kyau , ga kujerun zaman sha’katawa suma a
wajan , gaban sa wasu drinks d’in da alama sha yake sabida yadda ya nuna a cikin
d’aya daga cikin cup d’in wajan , yana ganin Abla ya sakar mata murmushi tare da
nuna mata wajan zama . Jiki a sanyaye Abla ta zauna gabaki d’aya ta tsargu sabida
batasan akan me yake nemanta ba , shima ya fahimci hakan daga reaction d’in ta ,
wani murmushi ya ‘kara sakar mata “ karki damu baki mun laifin komai ba , “ itama
Abla murmushi ta saki ganin ya gano ta , book d’in hannun sa ya ajje yana fuskantar
ta da kyau “ Nasan kin yi mamakin dalilin kiran ki da nayi ko ?” Kanta Abla ta
jinjina masa , “ karki ‘kullace sa akan abunda yake miki, and karki tunanin tsanar
ki yayi , its not like that”, d’an kallan sa Abla tayi dan bata fahimci maganar
sa , wani murmushi Bobo ya saki kafun ya furta “ Big Boss ! Yeah Big Boss nake
magana , ba mugu bane kamar yadda kike tunani zan iya cewa he’s the best soul ever,
yana yin rayuwane ya mayar dashi hakan ba wai ke kad’ai ba , kowa ma hakan ne ,
idan baka san halinsa ba , bazaka ta’ba sanin ya yake ba ,” yana kai ‘karshen
maganar da yayi shiru , Abla kuwa tunda ya fara yaban Big Boss ta d’an ta’be baki
cikin zuciyar ta “ Wannan mugun ne zaka ce yana da kirki mutumin da be san komai ba
a rayuwar sa sai mugun ta “ katse mata tunanin ya yi tahanyar ci gaba da magana ,”
Nasan zaki yi mamaki maganganu na “ ya ‘karasa yana kallanta “ lokaci kawai zaki
basa , he will trust you too! Yana da dalilin da yasa baya yadda da kowa , bawai
sabida yana tsoran za’a cutar da shi ba , No ! Yana yin komai ne for his family,
Little kamar d’an sa haka yake ,no matter abunda zai masa , ya fishi jin zafin”
d’an ‘karamun dariya Bobo yayi , “ He’s a bit arrogant sometimes i think, but he’s
the best brother i have ever in my life , farin cikin family d’in sa shine na farko
a wajan sa “ shiru Bobo yayi lokaci d’aya mood d’in sa ya canza , lokaci ya kalla
kafun ya sakar mata murmushi kad’an “ idan lokaci yayi zaki san komai amma kakki
‘kulla ce sa please “shiru Abla tayi masa sai kallan sa da take , mi’kewa tsaye
yayi yana d’aukan wani ‘karamar waya dake kan table d’in wajan “ zamu cigaba wata
ran yanzu ya kamata ki koma cikin gida okay ?” Itama mi’kewar Abla tayi tana furta
“ Na gode sosai Yaya Bobo “ , kansa ya jinjina mata “ its okay “ , bata kuma cewa
komai ba ta juya , sai da yaga ta ‘bacewa ganin sa tukunna ya saki wani shegen
murmushi, cikin dariya dariya ya furta “ Dude”, dai dai lokacin da ake kiran
sallah , shiyasa ya bar duk abunda yake ya nufi masallacin gidan.
Abla taba komawa cikin d’aki Alwala tayi , tayi sallar azhr d’inta , kud’in
da Big Boss ya jefa mata ta d’auka tana ‘kara bin ta da kallo , lokaci d’aya taji
ranta ya soma ‘baci, “ ‘kazama ! Villager “ shine ya ‘kara fad’o mata cikin rai,
murmushin ya’ke Abla ta saki tana girgiza kanta kad’an. Ganin tana ‘ko’karin sawa
kanta dawu ta ajje tunanin komai a gefe ta fara duba books d’inta na makaranta.
Da daddare ma hakan ne ya faru , suna zaune su hud’u a falourn daga ita sai
Little , prince sai kuma Uncle , tare sukai dinner d’in su , su hud’u gwanin
burgewa , suna gamawa suka dawo falourn suna hiran su , Abla sai data daidai ci Big
Boss ya kusa shigowa gidan ta gud’u d’aki abun ta .

**** MONDAY
Yau ya kasan ce Monday , da wuri Abla ta shirya cikin uniform d’inta, tana fitowa
gabaki d’aya su Little sun tanadar mata breakfast d’inta , ita kad’ai taci banda su
sannan suka had’a mata wani box shine na kayan za’ki, yau basu bita makarantar ba ,
tana fitowa madam sarah ta kar’bi school bag d’inta , Abla zata hanata Madam sarah
tayi saurin bud’e mata ‘kofa , tazo zata karfi chocolate box d’in hannunta Abla
tayi saurin dakatar da ita , a haka motocin su suka bar cikin gidan , cikin sa’a
kuwa bata had’u da Big Boss ba , hakan ba karamun dad’i yayi mata ba kuwa.
Tana shiga school ta tarar dasu Fanan a class duk da yawanci kad’an ne wanda
suke ciki. Hugging d’in juna sukai gabaki d’aya su ukun, kafun Abla ta samu seat ta
zauna , “ kin kusa fara cin dukan makara fa “ murmushi Abla ta sakar wa fanan da
tayi maganar “ amma kece zaki yi dukan ko ?” Ido d’aya Fanan ta kashe mata kawai ,
“ Ni kuma gaskiya sai dai naciki tara babu wani duka “ , hannu Abla ta mi’ka mata “
oya give me five “ itama Eshaal ta d’ago hannun ta da niyar su tafa sai taga Abla
tayi saurin janye hannun ta tana dariya , d’an hararar ta Eshaal tayi “ wallahi
Allah dai ya hana mugunta “ wani gwalan Abla tayi mata tana furta “ Oho dai “ .
Baby ce ta shigo cikin class d’in yadda take so calm yau sai ta bawa kowa mamaki ,
ga face d’in ta da mutum ya kalla yasan tana cikin damuwa, a seat d’in su ta zauna
tare da kifa kanta , kallan Eshaal , Fanan tayi “ Me aka yiwa Baby ? Tun ran friday
naga sauyi a face d’in ta gabaki d’aya batasan yiwa kowa magana, bata cewa a fita
yawo yanzu ko music bana gani tana sawa , idan nace ta shirya mu fita yawo sai tace
No”, ‘karamun murmushin Eshaal tayi mata “ Fanan nima bansan meke damun taba , tun
ran Thursday take a haka , ko abinci bata ci sai taji yunwa ta isheta , duk lokacin
da zan farka sai injita tana kuka , i try to asked her but tace mun bakomai “,
shiru sukai gabaki d’ayan su , fanan zata kuma magana teacher ya shigo class d’in,
fasa fad’an abunda take so ta fad’a tayi tare da komawa seat d’inta . Har teachers
suka shigo suka fita Baby bata cewa kowa komai ba , itama Eshaal time to time tana
kallan Baby, haka kawai taji bata san ganin ta cikin wannan mood d’in, ta fi san
ganin ta a ‘yar rigimarta.
A na fita break yawan ci class suka fice kamar had’in baki yayi saura su
hud’u , Abla , Fanan, Eshaal, sai Baby da ta sunkuyar da kanta . Kamar zasu wuce
sai Eshaal ta nufi inda take , cikin taushin murya ta furta “Baby ?” Shiru Baby
tayi mata batare da ta amsa ba , a karo na biyu Eshaal ta ‘kara furta “ Baby?” Uhm
kawai Baby tace mata “ Me zaki ce na taho miki dashi ?” Cewar Eshaal , a hankali
Baby ta furta “ Nothing Just go “ kallan juna Fanan da Eshaal sukai , sabida basu
ta’ba ganin Baby cikin wannan condition d’in ba , alama Fanan tayi wa Abla ko zata
yi mata magana , kanta ta jinjina mata gabaki d’aya suka dawo seat d’in , a hankali
Abla ta furta “ Baby ?” ‘Karamun tsaki Baby tayi zata tashi tabar wajan Abla ta
dawo da ita , ta bud’e baki zata yi magana itama Abla cikin fad’a fad’a ta furta “
shout up , me ke damun kine ?Tun d’azu ana so ayi miki magana kina yi wa mutane
wula…” bata ‘karasa ba Baby ta fashe da kuka tana rufe face d’in ta , gabaki d’aya
jikin sune yayi sanyi ganin yadda take kuka, cikin sanyin murya Abla ta furta “
kiyi hakuri banayi haka dan kiji haushi naba “, kukan face d’in ta Baby ta shara
tana kallan su da itanuwanta da sukayi jajawur har sun fara kunbura sabida kukan da
tayi , a hankali ta furta “ Ni ba kuyi mun komai ba , just go and leave me alone “,
hannunta Abla ta kama cikin tausasa murya “ kinsan me ? “ cewar Abla, girgiza mata
kai Baby tayi tana ‘kara share hawayenta , ya’ke kad’an Abla tayi sabida abunda
zata fad’a “ Nima ina da Sister kamar ki , Sunan ta Arwa “ sai kuma tayi shiru ,
gabaki d’aya idanuwa suka zuba mata , a hankali ta furta “ itama batajin magana
kamar , ko me yake damun ta bazata bud’e baki tayi magana ba sai dai tayi ta kuka ,
tun ina lallashin ta, har na soma yi mata fad’a , amma kin san ita tana da sau’kin
kai bakamar keba , idan na tanbayeta abu tana fad’a mun, kema ko bazaki fad’awa
kowa damuwar ki ba , ki dunga ro’kan Allah ya sassauta miki abunda ke ranki zaki ji
dad’i kinji?” A maimakon Baby ta amsa mata sai jefo mata mata tanbayar “ Tana
ina ?” Kwalla ce ta so tarar wa Abla cikin sauri ta goge tana ‘kara ‘ka’karo
murmudhi akan face d’inta “ Ta mutu, Arwa ta mutu , ta tafi ta barni” gabaki d’aya
sai suka zuba mata idanuwa cikin su kuwa har da Baby da take goge eyes d’in ta ,
kamar zatayi kuka ta soma magana “ Kusan kwana hud’u kenan ina yin wasu mafarkai,
wasu mutane mace da namiji suna ta ambatan sunana , ko wannan su yana mi’ko mun
hannu akan na cece sa , gefe d’aya kuma kamar suna mun fad’a , musamman muryar na
mijin da yake cewa ni ba yarinyar kirki bace , na canza halina ko kuna babu shi
babu ni,bansan ko su wanene ba , amma kusan kullum sai nayi mafarkinsu , duk
lokacin da suka mi’komun hannun dan na cece su sai naga wasu irin gizo gizo ba
‘ka’ke , jikin su duk jini suna tunkaro inda nake , kullum nayi mafarkin nan sai
nayi kuka musamman yadda gizo gizon suke tsoratar dani sai naji kamar suna inda
nake, duk lokacin da na kulle idanuwana muryar mutanan nan nake ji, duk da bansan
ko su wanene ba amma sai nake jina jima da zan dauwama a inda suke , ina san ganin
su ko sau d’aya ne , zuciya ta tana mun ciwo”, ta ‘karasa tana fashewa wani saban
kukan . Wani iri Abla taji cikin zuciyarta ‘kafarta kamar ana mata tafiyar tsutsa ,
lokaci d’aya mafarkin da tayi itama ya fad’o mata , bata san dalili ba , haka kawai
taji zuciyar ta na bugawa , kukan Baby ne yasa ta kawar da nata tunanin, suma face
d’in su Eshaal duk ya canza kamar zasuyi kukan , murmushi Abla ta sakar mata , “ ki
dunga yawai ta addua , mafarki ba gaskiya bane kinji? Duk lokacin da zaki kwanta
bacci ki tabbata kinyi Alwala sannan ki saka addua insha Allah zaki dena mafarkin “
hawayenta Baby ta share tana jinjina mata kai “ Na gode “, zaro ido Eshaal da Fanan
sukai ganin yau Baby tana yin godiya , ganin yadda suke kallanta ne yasa ta banka
musu harara, gabaki d’aya kuma sai suka saka dariya , seat d’inta Abla ta koma ta
d’auko chocolate box d’in ta , “ Nasan yanzu za’a dawo class , lets just have this
chocolates” Kallan Eshaal, Baby tayi a hankali ta furta “ kiyi hakuri!”, a tare
gabaki d’aya suka had’a baki Wajan furta “ Awwwn..” cike da tsokana Fanan tazo dai
dai kan Baby ,” ya Allah idan aljanune suka saka Baby ta shiryu Allah yasa su
‘kara saka ta , ta shiryu idan taki shiryuwa kuma su lakad’a mata duka ,” yanxu ma
gabaki d’ayanzu sukai a hankali Baby ta furta “ Am sorry Eshaal , duk abubuwan da
nayi miki a baya , idan banyi miki ba bana jin dad’i a raina sai inji kamar zan
zauce shiyasa bana jin dad’in idan ban miki ba “ Murmushi Eshaal tayi mata kafun ta
furta “ zan yafe miki with just one condition “ shiru sukai gabaki d’aya su suna
jiran abunda Eshaal zata fad’a “ har sai kin nemi yafiyar AMMA”, kanta Baby ta
jinjina mata “ yes I have that intention”. Ko mintu 3 basu ‘kara ba aka dawo daka
break shiyasa kowa ya nufi seat d’insa , a haka teachers suka cigaba da shigowa
har zuwa time d’in short break, yanzu ma basu fita ba a class suka zauna su
hud’un , yadda suke hira suna dariya kwanin burgewa lokaci zuwa zuwa lokaci sai
Baby ta kalli Abla , har Abla ta lura da ita, cikin tsokana tsokana Abla ta furta “
Yan mata ko na miki kyau ne ?” Murmushi Baby tayi mata tana girgiza mata kai ,
batare da damuwa ba ta furta “ I just feel having talking to you “ sosai Abla ta
sakar mata murmushi , “ Nima haka , I feel the same way “ da haka suka cigaba da
hirarsu. Ko da aka tashi sai da Baby tasa Abla ta bata number d’inta , amma Abla
tace bata haddace ba, shiyasa Ita Baby ta rubuta mata tare da fad’a mata idan ta
koma gida tayi mata magana . A haka suka Abla ta nufi inda su zata sami su Sarah ,
suma su Fanan sukai mata sallama suka tafi. Bata san dalili ba , she just enjoyed
the day with gurls , taji dad’in kasan cewa da su ko ba komai sun rage mata kewa ,
har ta ‘karasa gida kuma tana Tuna’nın mafarkin Baby.
Tundaga wannan lokaci wani irin ‘kawance ya shiga tsakanin su , ko ina
zasuje a school suna tare da juna su hud’u, in basu da school kuma zasu hau group
d’in da Fanan ta bud’e musu , sosai wani irin ‘kawance ya ‘kullu a tsakaninsu.
Cikin tsawan lokacin nan kuwa gabaki d’aya Abla ta fita har kar Big Boss , ko
had’uwa dashi batasan yi shiyasa da ta Daidai lokacin dawowar sa ko shigowarsa gida
zata gudu d’akin, sai ya zama kamar wasa ‘buya take dashi, gabaki d’aya duk hanyar
da zata had’asu ta toshe ta gabaki d’ayan ta . Har zuwa yanzu kuma a makaranta bata
had’uwa da su Bad Boys , tun bayan Alkawarin wula’kanta ta da yace zai yi bata
‘kara ganin su ba , ita gabaki d’aya ta manta dasu ma .

****ABUJA , NIGERIA…

Wani irin hayaniya ne yake tashi tako ina kamar masu danbe , hakan ce kuwa ta
kasance gabaki d’aya fad’a ne ake yi ga ihu da iface iface da ake ta faman yi,
d’aya daga cikin ‘yan matan da ake danbe da ita ta janyo gashin attachment d’in
’yar uwar fad’an tata , itama buga tsalle tayi ta sha’ko ta wani danben ya sake
‘kauce wa a tsakaninsu, wata matace ta so ma daka musu tsawa “ ku dakata , ku
dakata , bansan iskanci ‘kananan karuwai idan fad’an zakuyi ku fita waje ,” ba kowa
ne yake maganar ba face Uwar karuwai ta fuskarta tayi baki da ja lokaci guda Sabida
uban bleaching d’in da take yiwa kanta , kalar jikinta ta sauya zuwa kala biyu,
tsaki d’aya daga cikin su taja “ Mtswww ! Malama ban saka dake ba dan haka kiyi mun
shiru , na ‘kara fad’a miki kiyi min shiru idan ba haka ba muci uwar sabada dan ni
ba tsoran uwar uban kowa yake jiba “, cewar İlham da take faman bankawa Uwar
karuwai harara , a zuciye zinariya da Suke fad’a ta hayayya’ko mata, “ ah ah lalle
gaskiya wayanki ya isa yanka , dole ki bud’e baki mana , yar iska”, dariya İlham ta
saka tana tafawa da husna da itama tazama ‘kwararriyar yar hannu yanzu, ga cingum
da take faman taunaya , irin taunar karuwai.” Bani da wannan lokacin yanzu, abunda
na saki kawai ki bani 2k d’ina idan ba haka ba naci Uwarki wallahi babu abunda ya
shafeni, karkiga ina d’aga miki ‘kafa ko uwata Dije tayi mun wallahi sai na rama
balantana ke banza , ni banza, mu banzaye rainar bariki,” jijjiga jiki zinariya
kawai take “ idan naki biya kuma ?” Lokaci d’aya İlham ta furta “ muci uban juna “
ai bata ‘karasa ba Zinariyya ta kawo mata duka , idan wata kujera ta dauka ta
bugawa Zinariyya a baki , lokaci d’aya wani irin fad’a ya ‘kaure cikin gidan uwar
karuwai , itama a Garin ta matsa da gangan ilham ta saka mata ‘kafa sai jinta tayi
ragaf a ‘kasa dan yanzu gabaki d’aya basa jin maganar uwar karuwan , sai ga ta a
‘kasa tana ‘ko’karin tashi suka Yaushe ta , sai ya zama kamar da Ita aka fad’an ,
duk wacce aka tashi kaiwa duka sai ta kauce a doki uwar karuwai, ita kadai sai
faman ihun ate maka mata take amma bata ‘karasa maganarta suke ‘kara kai mata
duka .

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee ✨

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅


🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____39💞 ( second to the last free page)

ADX FLORENCE U.S.A


**PRISON**
Tsaye suke cikin babban prison d’in ADX me shegen hatsarin gaske , da ya zamto
d’aya a duk duniya baki d’aya me suna ADX Florence da ke ‘kasar America , prison ne
da duk Wanda yayi gigin guduwa yake fitowa a mace, har zuwa yanzu da ba a ta’ba
samun koda mutum d’aya daya ta’ba tsira daga cikin saba, shiyasa gabaki d’aya
prison d’in yake da manya manyan criminals masu hatsarun gaske, tare mata kan tsaro
sosai , sabida hatsarun wad’an da suke cikin sa.
Ga baki d’ayansu sanye suke cikin ba’ka’ken kaya , musamman Big Boss da
gabaki d’aya mutum
Bazai gane saba sabida shigarsa, hatta ‘kafarsa sanye take cikin ba’kin takalmin
David stone , da duk Wanda ya duka da takalmin nan sai ya ji a jikinsa , hatta
fuskarsa baka iya ganin ta sabida Black facemask d’in da ya’ke face d’insa , gashin
kansa sosai ya tufkesu a bayansa , hakan ya bawa bucket hat d’in da ya saka rufe
masa ido , shiyasa idan basanın shine a wajan ba , babu mahalu’kin da zai gane sa
da wuri. Bobo ma sanye yake cikin ba’kaken kaya kamar Big Boss , sa’banın shi face
mask Kawai ya saka a kansa , sai gyaran gashin kansa shima da ya so rufe masa ido
duk da bai saka hula ba. Suna tsaye cikin wani waje da idan mutum ya kallesa bazai
ta’ba tunanin a cikin prison bane , kusan mintuna 10 suna tsaye a Wajan , time to
time Bobo yana duba agogon hannunsa . Yanzu ma agogon hannun sa ya kalla duk da
face mask d’in dake face d’insa mutum zai gane yayi murmushi ta ciki. A hankali ya
far irga ,5,4,3,2,1, yana kai wa 1 ya furta done , lokaci d’aya wani irin ‘kara ya
karad’e cikin prison d’in, cikin sauri aka bud’e inda suke tare da jefowa Bobo wani
black Leda me d’an kauri , zip d’inta ya bud’e tare da ciro guns d’in da suke ciki,
d’aya ya mi’kawa Big Boss , shima ya saka ta sa daga bayan rigarsa kamar yadda Big
Boss yayi. Cikin sauri suka bud’e ’kofar Suka futa , da Sauri Sauri gudu gudu Suka
nufi inda yawanci criminals d’in suke cin abinci ga mata kan tsaro sosai a wajan ta
yadda babu Wanda zai yi ‘ko’karin yin kuskure. ‘Karan da suka ji ma d’aya daga
cikin prisoner d’in ne ya samu na sarar samun gun ya saita akan d’aya daga cikin
masu tsaran wajan. Daga gefen sa wani mutum ne da ashekaru zai wuce shekara
kamshin, jikinsa duk tatoo d’in spider ne a jiki ba’ki hatta face d’insa , gashi ya
sa anyi masa surgery a fuska ta yadda aka iya ganin ‘kofofin hancin sa , bakinsa
idan ya Lura sosai zai gane alamar raba lefen da yasa akayi masa . Tunda d’aya daga
cikin prisoner d’in ya samu gun yake binsa da idanuwansa da shima aka canza masa
zuwa ba’ki, shiyasa gabaki d’aya ya canza halitta zuwa wani abun daban sai kace ba
mutum ba . “Ka ajje bindiganka”shine abunda wasu masu tsaran suke cewa , cikin
zafin nawa me ri’ke da gun d’in ya ciro bindigar da ya ‘boye a bayansa ya je fawa
d’aya daga cikin prisoners d’in, shima cikin sauri ya kama tare da saita ta daidai
kan d’aya daga cikin masu tsaran, a daidai lokacin da su Big Boss suka shigo wajan
da gun a hannun su , cikin kakkausar murya Big Boss ya furta “ ku ajje maka manku”
kamar ‘kara tinzirasu yayi cikin sauri suka saka kuna ma zasu yi harbi, cikin sauri
Bobo ya furta “ ya isa haka ! Me kuke bu’kata ?” Gun d’in hannun Bobo prisoner din
ya kalla tare da nuna wani daga cikin d’an uwansa prisoner da gabaki d’aya aka saka
su kwanta , cikin sauri ya furta “ your gun! Ko kuma na harbesa “, hannu Bobo ya
d’aga sama tare da sunkuyawa ahankali zai ajje gun d’insa , akaro na biyu Big Boss
ya furta “ ku ajje makamanku !” Yana furta hakan yaja kunama shima zai yi harbi ,
da sauri Bobo ga bangajesa Gun d’in sa shima ya fad’i ‘kasa , pito na tsayen yayi ,
cikin sauri d’aya daga cikin prisoner d’in ya d’auke gun d’in Big Boss tare da
saitashi akanka , gabaki d’aya suma masu tsaran sai suka saita bindugogin su ,
cikin sauri Bobo yake musu alama da asu ajje gun d’insu, suna cikin hakan Big Boss
ya shammaci na bayansa lokacin da ya kai masa irin irin Bugu da saida gun d’insa
yayi ‘ko’karin fad’uwa , Big Boss ya kwace. A bazata d’aya daga cikin prisoner d’in
ya harba Bullet , daidai lokacin da Bobo zai jiyo , cikin rashin sa’a Bullet d’in
ya same sa , Big boss na ganin haka shima ya harbi d’aya daga cikin su a ‘kafa
bindigarsa ya bawa Bobo shi kuma wani security ya jefo masa tasa , Big Boss na kama
d’aya daga cikin su ya sakar masa naushi a kumatu, saura guda d’aya da yayi saurin
ja baya , gabaki d’aya sai ya nemi rud’ewa ganin yadda aka saba team d’insa za’a
fitar dasu , cikin kururuwa yayo kansu shima yaji saukar bayan bunguka akansa ,
gabaki d’aya yayi baya zai fad’i, guy d’in dasu me tanbarin spider yana ganin hakan
cikin sauri ya tare sa tare da rungumesa, batare da sanin ma’aikatan wayan da suka
yo kansu ba , ya saka wa guy d’in wani abu a aljihu yana ja baya , shima Big boss
hannun Bobo ya ri’ke suka fita daga wajan , ga prisoners d’in dasu ma gabaki d’aya
aka sa’besu akai waje dasu , Big boss na fitowa shugaban prisoner din ya sara
masa , kansa kawai Big Boss yayi knodding lokacin da yake cire bucket hat d’in
kansa . Har inda helicopter d’insu Big Boss suke shugaban prisoner din nan ya
rakasu, ganaki d’aya prisoner guda ukun a ciki aka saka su , sai Big Boss da Bobo
da suka hau wani helicopter d’in, ragowar helicopter guda biyu kuma su Victor ne a
cikin ta. Cikin ‘kan’kanin lokaci jirginsu ya tashi sabida gabaki d’aya wajan
prisoner d’in babu wani abu me rai ko mutane a gabaki d’aya wajan gabaki d’aya .
Cikin sauri d’aya daga cikin sojojin ya nufi Bobo lokacin da yake ‘ko’karin cire
rigar jikin sa ta sama , hannu kawai Big Boss ya saka ya yaga hannun rigar inda aka
harbi Bobo, lumshe eyes d’insa yayi kawai tare da matsawa gefe , shima soldier d’in
ya samu yayi wa hannun Bobo dressing bayan ya cire masa Bullet d’in ciki.

**************
************************

***NYC ***

Wani littafine a hannun Abla gabaki d’aya rabun tunaninta yana kansa sabida
yadda ta mayar da hankali akai , bata ankara ba taji an fuske Book d’in, cikin
sauri ta d’ago da dara daran eyes dinta tana hararar Fanan ,” Kin fiya rigima fanan
, bani book d’ina “ cikin tsokana fanan da ke bud’e Book din ta furta “ wallahi
bazan baki ba , ki bari sai antashi wannan nasan tabbas zan iya baki , amma gabaki
d’aya tun d’azu muna magana ke hankalin ki yana kan Book “ shiru Abla tayi tana
‘kara hararar ta , kallan yadda ta ‘bata face Eshaal tayi kafin ta kalli fanan
itama “ kinsan Allah fanan ki fita idan mu, ina ruwanki da littafinta ? Kun bi kun
ishemu da surutu salan kusa mana ciwan kai “ kallan Baby fanan tayi “ kinji fa ! Mu
zasu yi wa bariki waisu best friend , ki fad’a musu mu a ‘kawancen namu ma , mu
indiyawa ne “ gabaki d’ayan su kuma sai suka ‘kyal’kyale da dariya sabida jin
abinda fanan tace , “ ke dai fanan kin shiga uku da surutu zanga yadda mujin ki zai
yi fama dake “ cewar Baby, da sauri fanan ta mi’ke tsaye tana toshe kunnuwan ta “
Ni bana jin hausa da safe , kunga yanzu time zai wuce , ko kuma a hanyar komawarmu
muga an shiga class “ cikin tsokana Eshaal ta furta “ zakiyi bayani ne ma ! Mu
zakiyi wa wayo ? Amma dont worry akwai lokacin da zakiyi bayani” da haka suka mi’ke
zasu koma class , kamar ance wa Baby ta juya sai taga flowers suna motsi kamar an
bangaje su an wuce ta wajan , gashi gabaki d’aya su kad’ai a wajan flowers d’in “
Me kike nema ?” Cewar Abla ganin yadda Baby take zare ido , d’an jijjiga mata kai
Baby tayi “ No babu komai , mu tafi” kanta Abla ta d’aga mata kafun ta furta “ Okay
“ a haka suka nufi hanyar class kwajin burgewa suna tafiya suna hira abinsu , a
karo na biyu Baby ta ‘kara tsayawa jin kamar anta’ba mata hannu, tana kallan side
d’in kuma taga babu kowa a wajan “ Lapiya ?” Suka had’a baki a wannan karan,
waigawa Baby ta soma yi lokaci zuwa lokaci kuma tana kallan hannun ta da kuma wajan
flowers d’in da suka bari “ ji nake bayan mu akwai wasu anan wajan, sabida anta’ba
mun hannu yanzu” d’an murmushi Abla ta saki lokacin da ta matso kusa da Baby “ ki
kwantar da hankalin ki mana , wane zai ta’baki apart from us ?ki duba kiga a kusa
da student meke zaune ba , kawai da kinji irin haka kiyi addua kinji ?” Okay Baby
tace mata amma gabaki d’aya ta kasa sakewa sabida bugawa da taji zuciyarta ta
soma ,kamar wasu yara suka ri’ke hannun juna , zasu shiga class Baby tayi saurin
janye hannun daga na Abla , kallan menene Abla tayi mata suma su fanan gabaki d’aya
ido suka zuba mata , hanyar da suka baro Baby ta nuna “ sorry nayi mantuwa , ku
shiga class nima yanzu zan dawo “ da sauri fanan ta furta “ okay ni bari na
rakaki , inyaso su sai shiga class “ da sauri Baby ta girgiza mata kai “ No no no
ki shiga class d’in kema , karki damu ko 5 minutes bazan ba zan dawo “ tana kai
‘karshen maganar ta bata bari sun yi magana ba tayi saurin barin wajan , gabaki
d’aya bayanta suka zubawa ido , cikin d’an tantama fanan ta furta “ anya lafiyar ta
‘kalau kuwa ?” Ajiyar zuciya Abla tayi kad’an ganin suma sun fara shiga dawuwa da
reaction d’in Baby “ No karku damu , nasan yanzu zata dawo tunda ta fad’a , mushiga
class kawai “ toh kawai suka furta , suna shiga ciki kuwa teacher d’in Maths ya
shigo class d’in.

Direct Baby wajan flowers d’in da suka baro ta nufa , lokacin gabaki d’aya babu
student sabida komawa class da akayi, tunda ta tunkaro wajan take jin ‘kafarta
kamar ana tsigarta , amma duk da hakan bata dena tafiya ba ga wani irin zufa da
take ji gabaki d’aya jikinta , saura kad’an ta ‘karaso wajan flowers d’in taji
‘kafafuwanta kamar ana zuba mata wani irin abu mara dadin ji , cikin sauri ta saka
hannunta ta soma sosa wa , kamar wacce ake ‘karawa abu tana sosawa tana ‘karajin
abun yana ‘kara yawa , tun tana d’aukan abun wasa har ta soma hawaye sabida yadda
take jin ‘kafarta, da sauri ta juya zata bar wajan taji an hankad’ata , d’ago kan
da zatayi kuma ta babu kowa a wajan , cikin sauri ta kuma ‘ko’karin mi’kewa ta ji
kamar an ‘kara ta’ba mata ‘kafa , a razane Baby ta furta wayyo Allah na , adduar da
Abla ta koya mata take ‘ko’karin yi amma kamar wacce ake sha’kewa ma’koshi , gabaki
d’aya sai ta kasa magana, a razane ta mi’ke ta saka gudu zata koma wajansu Abla ,
tun kafin tayi nisa taga wani irin ba’kin abu na tunkaro ta ,da sauri Baby ta soma
ja baya gashi gabaki d’aya bakinta ya kasa bud’uwa balantana ta iya addua, yadda
abun yake nufota gadan gadan ne yasaka Baby yanke jiki ta fad’i a wajan su
mammiya . Kamar jira abun da tagani yake , yana gani ta sume a wajan ya rikid’e ya
koma gizo gizo, a hankali ya zoma zagayeta yana bud’e bakinsa, da ya kai daidai
kanta sai ya kasa ta’ba , ya kai sau uku yana ‘ko’karin saka bakinsa a kanta, a
karo na hud’u da d’aya daga cikin’kafafun sa suka ta’bata ya saki wani irin gurnani
mara dad’in ji , cikin sauri ya soma ja baya , ko second biyar be ‘kara a wajan
ba , wasu ba’ka’ken gizo gizo suka ‘kara fitowa kamar wasu aljanu, duk wanda yayi
‘ko’karin ta’bata sai ya kasa , sun dad’e suna abu d’aya kafin su zagayeta gabaki
d’ayansu suna binta da ba’ka’ken idanuwansu.

***** Tunda teacher d’in maths yashigo su Abla suke kallan ‘kofa suna jiran
shigowar Baby , amma har teacher d’in maths ya gama teaching d’insa Baby bata dawo
ba shiyasa gabaki d’aya babu abunda suka fahimta a maths d’in, suna ‘ko’karin
mi’kewa teacher d’in geography ya shigo , nan ma gabaki d’aya kasa samun nutsuwa
sukai gashi 2 class ne dashi a jere , kusan Allah Allah suke kawai ya fita , time
nayi babu wanda ya tsaya jiran books d’insa a cikin su , haka suka nufi wajan
flowers d’in da Baby ta ce musu . Adaidai lokacin da su Abla suke tunkaro wajan
adaidai lokaci suma gabaki d’aya gizo gizon suka ‘bace , sai Baby dake kwance a
wajan a ‘kasa kamar matacciya.

Eshaal ce ta soma hango ta, hannunta har rawa yake lokacin da take kallan
Baby , suma gabaki d’aya inda suka ga Eshaal ta kalla suka kalla, cikin sauri suka
kwala kiran sunanta tare da nufar Inda take a gwance , Abla kam kasa ta’bata tayi
sai binta kawai da take da kallo, Eshaal da Fanan kuwa sai faman jijjigata suke ,
lokaci d’aya kuma suna kiran suna ta , ganin ta’ki motsa yasaka Fanan barin Wajan a
guje, amma ko mintu biyu batayi ba ta dawo d’auke da wani bottle wata, cikin sauri
ta bud’e ruwan tare da yayyafawa Baby, wani irin jannufashi Baby tayi sai a lokacin
Abla ta iya matsowa wajan ta , a firgice Baby ta bud’e idanuwanta tana bin ko ina
da kallo , suma kallan wajan suka soma kama ganin babu komai , a hankali Baby ta
saki ajiyar zuciya “ Menene ya faru Baby ?” Cewar Abla , Baby ta bud’e baki zatayi
musu bayani kamar almara ta manta duk abunda ya faru, hannu kawai ta bud’e tare da
furta “ Nima bansan me ya faru ba ! Sai yanzu da naganku a Wajan “baki suka saki
gabaki d’aya suna kallanta “ kudena kallo na ! Ku taso mu tafi “ tana kai wa nan ta
juya , suka suka bi bayanta suna mamakinta .

Har lokacin tashi yayi basu dena mamakin Baby ba , gashi gabaki d’aya ta ‘kiyi
musu bayanin abunda ya faru da itama , musamman Abla da take lura da ita, lokaci
zuwa lokaci tana d’an firgita. Ana tashi su Eshaal suka koma hanyar gida , itama
Madam sarah time d’in tashi nayi tazo d’aukar Abla suka tafi gida .

*****Abla tana shiga cikin gidan ta tarar da babu kowa a falourn, a tunaninta su
Little suna d’aki shiyasa itama bata zauna a falour ba ta wuce cikin d’akinta tayi
wanka ta shirya cikin maroon d’in doguwar riga . Tana sakko wa ‘kasa still bata
tarar dasu Little a ciki ba , batayi tunanin komai ba ta wuce dinning zatayi
serving kanta , kamar Ance mata ta jiyo taga su Little sunfito daga wata ‘kofa ,
prince na gaba little na binshi a baya ga hannayensa biyu da ya ‘boye duka a
bayansa . Murmushi Abla ta sakar musu “ Na dawo gida nan gankuba , na d’auka
bakwanan ai “ , murmushi a face d’insu suka furta “ No Lil mun tsaya wani abune “
kallan bayan prince Abla tayi ganin yadda Little yake kakkarewa , cikin ‘yar dariya
Abla ta furta “ yaya little me kake ‘boyewa a bayanka ?” Kanshi ya girgiza mata ga
face d’insa da har yanzu akwai murmushi akanta “ No ! No! Babu komai “ zatayi
magana prince yayi saurin furta “ No please karki yi magana “ shiru Abla tayi tana
Kallansa , da Sauri ya zagayo ta bayanta ya kulle mata ido da wani bakin abu, ita
Abla gabaki d’aya dariya suka bata ma yadda suka kulle mata fuskarta , “ karki
magana “ cewar prince , batayın ba kuwa har prince ya kama hannunta suka zaunar da
ita kan kujera , tana zauna prince yayi dialing number din uncle da shima ko
mintuna 5 beyi ba ya fito face d’insa fal murmushi. Da ido Little ya nunawa prince
ya bud’e wa Abla idanuwanta , yana cire kyallan prince da little suka had’a baki
wajan furta “ Happy Birthday princess “, at the same time kuwa ya fito da wani
medium cake da ya ‘boye a bayansa . Lokaci d’aya gabaki d’aya murmushin fuskar Abla
ya ‘bace sai ja da fuskarta ya soma yi , da Sauri ta sunkuyar da kanta ‘kasa tana
taunar le’ben ’kasan bakinta ,” Lil ?” Tun bai ce sister d’in ba Abla ta kulle
idanuwanta tare da fashewa da kuka , cikin Sauri little ya ajje cake d’in tare da
zama a side d’in ta , “ Lil me akai miki? Waya ta’ba ki ? Ni ne ? Yaya prince ne ?
Me akai miki?” Shine tanbayoyin da Little ya soma yi wa Abla ganin yadda take kuka
sosai , uncle kuwa waje ya samu ya zauna yana kallan Abla ganin yadda take kukan ta
da gasken gasken, Little zai sake magana Uncle yayi saurin dakatar Dashi “ it’s
okay Little “ da Sauri little da prince Suka kallesa , da kai kawai ya amsa masa
yana ‘kara Kallan yadda Abla take kuka . Suma shirun sukai suna ‘kara binta da
idanuwa , musamman little da shima yake ji kamar yayi kukan.ta d’auka kusan 5
minutes tana kuka ganin kukan nata bame ‘karewa bane yasa uncle dakatar da ita “
it’s okay Daughter, kukan ya isa haka , tunda birthday d’in ne bakyaso bazasu sake
miki ba , kinji ?” Sai kuma ya ‘karasa yana kallan su Little “ karku ‘karayı mata
tunda bata kunji ?” Cikin Sauri Abla ta girgiza masa kai , muryarta kamar me kuka
ta furta “ Ah.. ah ni basuyi mun komai ba uncle , abune ya shiga cikin ido na ,
babu abunda ya sameni “ , shiru sukai mata suna kallanta ,kafun prince ya furta “
kuka kikai magana , bamusan hakan zai ‘bata miki ba , we’re all sorry “ wani kukan
Abla yaji yana san sake zuwar ta , murmushi me ciwo ta saki sosai kafin ta furta “
Dagaske nake yaya prince ni bakuyi mun komai ba , ku dena bani hakuri “ then me
yasaka ki kuka ?” Cewar little yana tsareta da ido, shiru Abla tayi masa tana bin
cake d’in gabanta da kallo , shima prince murmushi ya d’an saki kad’ai kafun ya
furta “we’re not family ? Da bazaki fad’amun abunda yake damun ki ba ? I thought
we’re family ! We can share our issues ! Amma it’s okay tunda bakya san kowa ya
sani “ ya ‘karasa yana ‘ko’karin mi’kewa , da Sauri Abla ta ri’ko hannunsa “ No
please ka zauna “zaunawar yayi kuwa yana kallanta , wani murmushin Abla ta ‘kara
saki “ ba yau ne birthday d’ina ba , bansan Yaushe bane , bansan ranar ba Nima “
cikin Sauri prince ya furta “ Sister “ kanta ta jinjina masa “ yes ! Yaya prince
bani da family, bani da kowa , bansan su wanene suka haifeni ba ,bansan mamana ba ,
bansan babana ba , sun mutu ko suna raye duka bansani ba “, hawayen da suka zubo
mata Abla ta share tana sakar musu murmushi ganin yadda reaction d’in face d’insu
ya canza gabaki d’aya , a jiyar zuciya ta dauke ahankali kafun ta cigaba “ cikakken
sunana shine Ibtissam amma cikin wad’an da na rayu dasu suna kira da Abla, kullum
cikin godewa Allah nake da irin rayuwar da na tashi , kuma bazan daina gode masa ba
, kamar yadda na fad’a muku bansan su wanene suka haifeni ba , nasan kawai na taso
cikin ‘kunci da ba’kin cikin rayuwane,da farko na taso cikin gidan haka , matar da
ta d’auke ni ta shaidamun batasan su wanene suka haifeni ba , ta tsinceni ne cikin
wata ‘kauye a daji cikin cijayawa duk Jini a jiki na , ga ruwa anayi lokacin wannan
ne babban dalilin da yasa ta tausaya mun ta d’auke ni, nayi rayuwa da Ita cikin
bautawa , kamar baiwar ta haka ta mayar dani dukda nafijin dadin sosai akan inda na
rayu , ko ba komai tayi mun hallaci,ita ta sakani makaranta, take boyamın kudin
makaranta , abinci na , komai ita take yi mun shi , hatta sunan da na mahaifinta
nake anfani a makaranta Sabida bansan wanene nawa uban ba.” Sai da ta saki a jiyar
zuciya kad’an kafun ta cigaba , “ rayuwata ta soma gur’bacewane tun bayan rasuwar
ta , Sabida tsangwama da mutane suke nuna muna , suna Kirana da yar karuwa , bani
da yadda zanyi , babu Wanda zai tai maki rayuwa ta , da farko na soma kwana a cikin
kwango amma Sabida yadda mutane ke ‘ko’karin lalatamin rayuwa tsoran hakan ya
kamani, Tuna’nı na kullum ya zanyi na tsira , kwatsam wata hajiya ta so temaka mun
duk na so na ‘ki amince mata amma sabida ba yadda zanyi dole na amince mata ,
haushe ‘ko’karin fad’awa rami nake, a ranar farko da naje gidan ta , ta kula dani
sosai kamar yar data haifa har na soma sha’kuwa da ita Sabida Itama ta fad’a mun
ita kadai take rayuwa bata da yan uwa, shiyasa Nima na sake sosai da ita , a cikin
kwana na biyar da nayi a cikin gidan ta wasu mutane suka d’auke ni daga wajan ta,
Aushe siyar dani tayi , ta siyar dani ga macen da ta fi kowa san lalata dani ,
karuwa, mara tsoran Allah , mara ‘kaunar addinin Allah, nasha wahala sosai , bana
bacci sai cikin dare sai ayyukan da nake yi , ga kiran da ake saka wa cikin dare ,
hakan baya hana ‘karfe 3 na dare a tashe ni daga bacci ni da ‘yan matan da aka
siyar dasu , ka zame mun tamkar yan uwana na Jini , Arwa, ilham, Aneesa, muna shan
wahala sosai , basa bamu abinci, kullum burin su , su sami Wanda zaiyi lalata
damu ,” gabaki d’aya sai da Abla ta zaiyane musu irin rayuwar Da tayi cikin gidan
uwar karuwai da ‘kalubalen data fuskanta har kashe mata Arwa da sukai da yadda suka
siyar da ita har zuwa lokacin da su Bobo suka tsinceta, tana kaiwa nan ta fashe da
kuka tana kulle fuskarta, cikin Sauri Little ya goge hawayen fuskarsa “ waya ce
miki baki da family ? Ku kuma fa ? We’re all family! Na miki al’kawari I will
always be by your side , kin manta ni yayan kine ?” Kanta Abla ta jin jina masa
tana murmushi kad’an , shima prince hannunta ya ri’ke “ we’re family ki dena cewa
baki da family , duk Wanda ya ta’baki just karki manta Prince and Little will
always be there for you , kinji?” Yanzu ma kanta Abla ta jinjina masa gabaki d’aya
sai sukayi hugging d’in juna . Uncle kuwa tun da ta soma basu labarin ta be motsaba
sabida zurfin Tuna’nın da ya fad’a , ganin yadda mood d’insu ya canzane suma Abla
ta furta “ Nifa yunwa nake ji ! Let’s eat the cake “ kasa magana sukai gabaki
d’ayansu, da kanta Abla ta yanka cake d’in , ta basu, zasu magana Abla tayi saurin
furta “ let’s enjoyed our life komai da sanin Allah ! Okay ?” Kansa little ya
jinjina mata, gefe d’aya kuma yana jin badad’i ko kad’an, zuciyarsa yaji ta soma
zafi shiyasa ya kawar da komai amma duk da hakan yana ‘ko’karin dannewa sabida
bayasan tayar musu da hankali .A ‘bangaran Abla ma dannewa kawai take sabıda kar
suga rauninta, shiyasa Ta kawar da duk wata damuwar ta Sabida tana san ganin farin
cikinsu , suna zaune a falourn har lokacin kuma babu abunda uncle yace sai binta da
kallo da yake. Lokacin sallah nayi suka wuce masallaci itama kuma Abla ta wuce
d’akın ta . Cikin Sauri ta kulle ‘kofa tare da tsugunnawa a Wajan , kukan da take
‘boyewa yana ‘kwace mata .

******NYC****
********* wajan ‘karfe 3:20 helicopters d’insu Big Boss suka sauka cikin wani gida
da kallo d’aya idan mutum yayi masa zai ga sojoji tako ina suna shawagi a cikinsa ,
ga bindigu dake hannun ko wannansu , suna sakkowa gabaki d’aya sojojin suka zagaye
wajan suna jiran fitowar su Big boss, a hankali ya fito daga cikin helicopter din
shida Bobo, yanxu babu face masks a fuskarsa sai face d’insa da take d’aure babu ko
d’igon fara’a , suna ganin fitowarsu suka sara musu cikin tsantsan girmamawa , babu
Wanda Big Boss ya kalla a cikinsu ya nufi cikin gidan , cikin Sauri su Victor suka
bi bayansa , Bobo kuwa helicopter d’in da aka d’auko prisoners d’in ya kalla Daidai
lokacin da Suke fitowa , abun mamaki gabaki d’aya sun canza kayan jikinsu zuwa wani
kayan da ban , ga ‘kafar d’aya daga cikin su da aka harba da bandage alamar anyi
masa treatment , sojojin nan suka ganin fitowar su suka saramusu lokaci d’aya ,
suna prisoners din sara musu sukai kafun su kalli Bobo da ke tsaye a gefen su ,
fuskar ko wanne da murmushi aciki sukai hugging d’in juna. “ Good job “ cewar
Bobo , kallan hannun Bobo da aka harba d’ay daga cikin su yayi “ Sorry Dude ! Dole
yasa nayi maka haka , but am sorry “ bugu Bobo ya kai masa mutumin yayi sauri kauce
wa , a haka suka nufi cikin gidan da Big boss ya shiga ،a tsaye suka tarar dashi ya
zuba hannayensa cikin aljihun wandansa , lokaci d’aya suna ‘kame tare da sara masa
kafun biyu daga cikin su, su nufesa tare da hugging d’insa “ Long time ! Big Boss “
banzan kallo Big Boss ya jefa masa , dan ‘karamun dariya Bobo yayi kafin ya furta “
snoopy kwanda ka rabu dashi kafin kasamı Kasan naushin ka now “ Wanda aka kira da
snoopy yayi dariya kafun ya furta “ Bobo it’s now 4 month fa muna prison just a
work , kaga yanzu dole na takalosa tunda shi ya saka mu wannan aiki, and if to say
shi na harva d’azu I think muna shigowa nan zai saka a tsireni “, gabaki d’aya
shiru sukai tare da zama kan chairs din wajan. Almost 5 minutes suna zaune a haka
kafin Big Boss ya furta “ Welcome Back Alpha team”da Sauri wani farin bature ya
furta “ yeah the team is back ! Now lokacin operation ne “ kansa Big Boss yayi
knodding kafun ya samu waje ya zauna , d’ayar guy din da tunda Suka shigo beyi
magana bane ya ciro kwalbar da mutum d’azu ya saka masa a prison , cikin tsokana ya
furta “ Mun Samu kwalbar! Yanxu aikin mu zai tashi zuwa wani stage din! Work time !
Black operation 111 “….., daga haka suka cigaba da tattauna maganar da suke sanyi
cikin sirri batare da kowa ya jisu ba.

Har bacci ya kwashe Abla bata sanı ba sai farkawa da tayi taga shida ta kusa ,
cikin sauri ta wanke face d’inta tayi wanka tare da yin alwala sabida kiran sallah
da ake yi , Sabida baccin la’asar d’in da taji sai taji gabaki d’aya ranta a’bace
yake har tayi sallah kuwa , har zata zauna a d’akin sai ta fasa kuma ta sakko
falourn , Daidai lokacin da prince xai wuce , yana ganin Abla yayi saurin dakatawa
“ Yawwa Lil ! Please come and help me kinji , shaff namanta su yaya Big Boss zasu
dawo and namanta bamu gyara part d’insa ba , please ko zaki temaka ki gyara , irin
gyaran sa kikai masa kafun mu dawo ?” Kanta Abla ta jinjina masa dan ko magana bata
sanyi, “ Thank you dear” cewar Prince , ynxu ma kanta Abla ta jinjina masa, sabida
süne akwai zata gyara masa d’akin amma idan ta Ita ne har abada ta dena shiga part
d’insa shiyasa bata ‘bata lokaci ba ta nufi part d’insa gudun karsu had’u ,
mayafinta kawai ta zame da doguwar rigar jikinta tabar guntun wandan ta da ya wuce
cinyarta kad’an sai white shirt d’inda ta saka matsatsiya, kanta kuma ta d’aura
wani white cap , cikin ‘kan’kanın lokaci ta soma gyaran falourn sa , komai sai data
gyara cikin falourn , kafun ta koma second falourn nasa shima tana gyarawa ,
batasan ya akai ba lokaci ya ja sosia , har wajan ‘karfe 8 tana aikin gyara masa
part d’insa , tana gamawa da falourn ta koma cikin bedroom d’insa , lokaci d’aya ta
tuno yadda ya ji’kata da ruwa da yanke mata gashi da yayi , ‘karamun tsaki Abla
taja lokacin da ta soma gyara d’akin , har yanxu ranta a’bace yake Sabida tuno
tarihinta da bata ‘Kaunar tunoshi, tana cikin gyara d’akin ta janyo wani white
envelope bata sani ba , ya Garin d’akko su wasu hotuna suka fad’a daga ciki, da
Sauri ta tsugunna ta soma tattara su batare da ta kalli ko d’ayansu , Adaidai
lokacin da shi kuma ya shigo cikin d’akin ga black shirt dinsa da ya soma cire
ma’ballinta har ana ganin singlet din jikinsa . Ido cikin ido Suka kalli juna
Daidai lokacin da idanuwansa suka kai , kan envelope d’in hannun ta , yana zuwa be
tsaya ba ya tsinka mata mari, kasa d’ago da face d’inta Abla tayi Sabida marin da
yayi mata , a zuciye ya daka mata tsawa cikin kausashshiyar murya ya furta “ how
dare you ? Ke wace irin mutum ce ? Baki da hankali ne ? “ shiru Abla tayi masa ga
hawayen da suke sauka kan face d’inta , a zuciye ya sha’kota idanuwansa har sun
soma ja sabida ‘bacin rai “ How dare you ina magana ki mun shiru , ko duk cikin
rashin tarbiyar da iyayenki suka koya miki?” A hankali kuma ya furta “ I won’t be
surprised tunda iyayenki a gidan karuwai suka ….. “batasan ya akai ba , batasan
dalili ba , jikinta har rawa yake , tun kafin ya ‘karasa maganar sa Abla ta d’auke
kyakkyawar face d’insa da mari…

PLX MASU NEMANA BASA SAMU NA A WHATSAPP ZAKU IYA MUN MAGANA TA TELEGRAM KO KU
KIRANI ! Na d’an samu matsla da WhatsApp dina.

https://chat.whatsapp.com/CsKAjdD6LxZ8ue0YL5gPxQ

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written


By
Mss Lee ✨
🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD ✨

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer)
Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da
flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana
matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin
gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan
zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan
number 07041879581.

NOT EDITED

S____40💞
( Last free page)

Cikin wani irin shock Abla ta ja baya ganin abunda tayi, jikinta har rawa yake ,
gashi sai faman girgiza kanta take hawaye na sakko mata a kan face d’inta , a
hankali Big Boss ya d’ago da eyes d’in sa yana binta da wani irin kallon da shi
kad’ai yasan ma’anar sa ,yadda yaga ta tsoratan ne yasa shi d’aga girar fuskarsa
kad’an tare da matsowa inda take, itama Abla cikin sauri ta soma ja baya hawaye duk
ya ‘bata mata face d’in ta , ko kusa ta ‘ki d’ago da idanuwanta balantana ta
kallesa , haryanzu kuma be mata komai ba sai matsowa inda take da yayi, yadda taga
yana matso ta sosai yasa bata san ina take zuwa ba har ta cigaba da ja baya itama,
bata ankara ba taji ta a bango zata matsa yayi saurin saka hannun sa guda biyu a
both side d’inta.
Abla kamar zatayi kuka ta kawar da face d’inta tare da kulle idanuwanta gam
tana jiran jin irin hukunci da zai mata.
Murmushin gefen baki ya saki kad’an duk da be fito sosai ba , face d’insa ya
matso da ita Daidai fuskarta kafun ya furta “ open your eyes “kamar ya ‘kara zugata
kuwa ta ‘kara kulle idanuwanta gagam, lumshe eyes dinsa Big Boss yayi tare da ‘kara
bud’esu yana bin face d’in Abla da kallo, Babu mahalu’kin da ya ta’ba Marin sa ko
da namiji ne sai ita , Wanda shi kad’ai yasan punishment d’in da zaiyi mata , a
hankali ya ‘kara furta “ open your eyes “ yanzu ma kulle idanuwanta Abla ta ‘karayi
a hankali ya sakko da hannunsa kan cikinta yana zagaye mata shi da öne finger
d’insa , a razane Abla ta ware idanuwanta a kansa wasu hawayen suna ‘kara sakko
mata, duk da yadda ta bud’e idanuwan nata be dena zagaye cikin ta da 1 finger d’in
saba, cikin Sauri Abla tabuge masa hannun nasa , duk da ‘karfin hali ne take yi ,
cikin d’an masifa masifa ta furta “ Ni karka ‘kara ta’bani…” bata kai ga ‘karasa
maganar taba ya had’e lips d’insu waje d’aya , a razane Abla ta ware idanuwanta
kamar zasu fito waje , lokaci d’aya jikinta ya soma karkarwa , ‘kafafunta sun mata
sanyi, ‘ko’karin zamewa take ya saka hannunsa guda d’aya ya talla’bota , har yanzu
kuma be saki lips d’inta ba duk da yadda taso kwace wa , ji tayi gabaki d’aya
nunfashinta yana ‘ko’karin d’aukewa ga wani irin abu da yake ratsa mata tun daga
d’an yatsar ‘kafarta har zuwa kwakwalwarta, duk yadda taso kwace lips d’inta Big
Boss ya ‘ki bata wannan damar,a hankali wani irin hawayen takaici suka soma sakko
mata daga cikin idanuwanta ,Ji take kamar lips d’inta zasu tsinke sabida tsabar
rad’ad’in da suke mata, cikin ‘karfin hali da ragowar ‘karfin da yayi mata saura ta
cije a lips d’in sa itama. A hankali ya soma bud’e eyes d’insa da suka soma canza
kala zuwa launin ja , yadda yaga ta kawar da kanta gefe tana ‘ko’karin kwace
jikinta yasa ya motsa lips d’insa kad’an kamar Wanda yake shirin murmusasu, cikin
cool voice kamar bashi ba ya furta “ Marin da akai mun kuma da me zan rama ? “
banza Abla tayi masa sai ma faman kwace hannunta da take ‘ko’karin yi , a hankali
ya furta “ it’s Okay “ cikin ‘kasan ma’koshi kamun ya soma bud’e bottom d’in
rigarsa cikin Sauri Abla ta ja baya , wasu hawayen suna ‘kara sakko mata, gabaki
d’aya ta tsorata da yanayınsa , ita kad’ai sai faman Kallan ‘kofa take , a hankali
ta furta “ kayi hakuri”, tsayawa yayi da ‘balle button d’in da yake kafun ya matso
da face d’insa Daidai saitin kunnanta , a hankali ya furta“ we’re so sweet Mrs Omar
Farooq”, da wani irin ‘karfi Abla ta bangajesa ta arta na kuje cikin sauri ta janyo
doguwar rigar ta , tunda ta turesa be motsa ba har ta ‘karasa wajan ‘kofa, da
manyan idanuwan ta da suka cika da kwalla sakar masa harara cikin ‘kasa ‘kasa da
murya ta “ Allah sai ya saka mun d’an iska kawai “ , sarai yaji abunda tace ,
shiyasa yayi kamar zai mi’ke , cikin tsoro Abla ta bud’e ‘kofar ta arta a guje,
wani irin lallausan murmushine ya su’buce masa akan lips d’insa , har hakwaransa
suna fitowa waje kad’an, yadda yayi murmushin ba’karamun kyau yayi ba kamar
fuskarsa ta tsaya a hakan , ga dimples d’insa da suka lotsa sosai , a hankali ya
fesar da iskar bakinsa , cikin ‘kasa ‘kasa da murya ya furta “ Batajin magana”.

Hotunan da suke zu’be a ‘kasa ya kalla, lokaci d’aya mood d’insa ya soma canzawa ,
d’aya daga cikin hotunan ya d’auka me d’auke da hotan jariri a ciki, gabaki d’aya
jikin yaron jinine da alama kuka yake aka d’auki hotan , a hankali Big boss ya
lumshe idanuwansa ,tun bayan tsawan shekara 22 hotunan suke ajje, Sabida ko kusa
bayasan tuno da abubuwan da suka faru,lips d’in sa na ‘kasa ya d’an ciza Kafun ya
mayar da pics d’in cikin envelope . Gucci watches din hannun sa ya kalla , a
hankali ya furta “ Oh God “ sai kuma ya mi’ke cikin nutsuwar sa ya nufi dressing
room d’in sa .

Abla tana barin part d’insa cikin sauri sauri ta saka doguwar rigar ta , ga hawayen
face d’inta da suka ‘ki tsayawa , har ta wuce uncle a falourn bata sani ba , gabaki
d’aya bata cikin nutsuwar ta , kai tsaye d’akin ta ta wuce tare da saka wa ‘kofar
key , cikin masifa masifa Abla ta furta “ ‘Dan iska , mugu kawai , Allah sai ya
saka mun , idan ka tashi hukuntani karka barni da raina kayanka ni gunduwa gunduwa
“, tana surutun tana cire kayan jikinta , bata tsaya a bedroom d’in ba ta wuce
toilet tayi a wanka . Ta d’au kusan mintuna 15 a cikin toilet d’in kafin ta fito ,
kallan fuskarta tayi a mudu bi, lips d’in ta har ya d’anyi ja sabida muguntar da
yayi mata , lokaci d’aya kuma ta saka kuka me ta’ba zuciya “ akan me kake ‘ko’karin
zagar mun iyayen da bansani ba suna raye ko sun mutu, bana san ka , bana ‘kaunar ka
, Nima na tsaneka kamar yadda ka tsaneni , mugu kawai “ ita kad’ai sai sanbatu take
yi, lokaci zuwa lokaci kuma tana mitar abunda yayi mata. Doguwar Riga kawai ta saka
ajikinta , tunda ta kwanta akan gado take juyo , gabaki d’aya ta rasa meke mata
dad’i, da ta kulle idanuwanta abunda ya faru a tsakanin su yake sake dawo mata ,
cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta rud’e jikin ta yasoma rawa kamar me zazza’bi, duk
yadda taso bacci ya d’auke ta abun ya ci tura , sai fuskar Big Boss da ke faman yi
mata gizo a duk lokacin da ta kulle idanuwanta , har wajan ‘karfe 2 idanuwanta biyu
, sai juyi take akan gado da ‘kyar wani irin wahalallan bacci ya d’auke ta .
***** 3:10am
Cikin wani irin d’aki me duhun gaske ta tsinci kanta , ga wasu irin abubuwan tsafi
dake cikin d’akin ta ko ina , a tsorace Abla ta soma bin cikin d’akin da kallo
hankali a tashe , “ Abla ! Abla ! Abla “ sunan dake faman kira Kenan , cike da
tsoro Abla ta d’aga kanta sama Sabida muryoyin wad’an da taji , a gigice ta ‘kwalla
kara kafun ta soma kiran “ Eshaal , Baby ,Fanan ku matsa zasu kashe ku, ku matsa ,”
cikin kuka Fanan ta girgiza mata kai “ Abla mutuwa zamuyi, suna bin mu duk Inda
muke , ke kad’ai ce zaki iya cecen rayukan mu,” cikin Sauri Abla ta soma ‘ko’karin
kwance kanta , amma igiyar kamar merai da tayi ‘ko’karin kwance wa zata ji igiyar
ta ‘kara matse mata jiki . Da ‘karfi su Fanan suka furta “ Abla…” suna furta sunan
ta gabaki d’aya Jini ya fara fito musu ta baki da ta hancin su , ihu Abla ta saki
tana ‘kokwarin kwace kanta , da tayi ‘ko’karin Yin addua zataji an matse mata ma
‘koshi , gasu Baby da suma sai fitar da Jini suke ta baki , cikin azaba Abla ta
furta “Ya Al…Al…Allah”, cikin ‘kan’kanin lokaci igiyar data d’aure ta , ta ‘bace
batt babu ita , tana kai dubanta idan su Fanan suke taga nan ma wayam babu su babu
a lamarsu, wani irin jiwane ya soma kamata , gani take kamar ba’kin dakin yana juya
mata , da’karfi ta toshe kunna wa tare da kurma ihu *****
Bakinta cike da addua Abla ta farka daga baccin da ya d’auketa , gabaki d’aya
jikin sai faman d’aukar rawa yake ga wani irin zufa da ta had’a ta ko ina , wayar
ta tayi saurin janyowa tare da kunna karatun alqurani, kusan mintuna 5 tana zaune
tana sauraran al_qurani me girma, kafun ta soma a jiyar zuciya a hankali Sabida
nutsuwar da ta soma samu cikin ranta .

***WASHE GARI***

Washe Gari da wurwuri ta farka daga baccin da ta koma , wanka kawai tayi ta Shirya
cikin uniform d’inta , yau ko jiran su Little batayi ba , tunda taga basa falourn ,
hatta breakfast d’inta bata tsaya tayi ba sai Youghurt da ta d’au ka , Burin ta
kawai taje taga su Eshaal . Tana fitowa ta tarar da su Madam Sarah, cikin Sauri ta
nufi motar, madam sarah ta bud’e mata suka nufi makaranta . Ko kallan su sarah
batayi ba , motocin su na tsayawa ta wuce class d’insu. A zaune ta tarar dasu ko
wannansu da book d’insa a hannu tana ganin su tasaki wani irin ajiyar zuciya , “
meyafaru haka kike ajiyar zuciya ?” Cewar Baby , kanta Abla ta girgiza mata “ No
babu komai kawai na d’auka bakwanan ne “ kin tabbata?” Cewar Fanan, yanzu kanta
Abla ta d’aga mata , “ yes da gaske nake babu komai, just I wanna check on you
gurls “ ta ‘karasa tana sakar musu ‘karamun murmushin da ko cikin zuciyar ta be kai
ba , bakin ta Eshaal ta nuna tana kallan Abla” me ya samu lips d’inki? Ya fashe ?”
Ta’ba lips d’inta Abla tayi kad’an , cikin sauri ta furta “ Bugewa na d’anyi amma
yanzu it’s okay ya dena mun zafi ma “, Eyya sorry dear “ cewar Fanan , wani
murmushin Abla ta saki tana ajje school bag d’inta , gabaki d’aya sai suka zuba
mata idanuwa kuma , cikin tsarguwa ta furta “ Menene kuke bina da kallo haka ?”cike
da tsokana Baby ta furta “ kin tsargune ?” ‘Dan harararta Abla tayi “ yadda kuke
bina da idanuwa haka ba dole na tsarguba”, da haka suka canza topic d’in hirar su
zuwa wani daban kafun teacher ya shigo class d’insu.

Da aka fito break ma , gabaki d’aya hankalin Abla baya jikinta, mafarkin da tayi
jiya gabaki d’aya ya tsaya mata arai, dafatan da Baby tayi ne yasa ta d’an firgita
“ Abla meke damun kine ? Ko akwai abunda kike ‘boye mana ne ? “, cikin Sauri Abla “
No Baby seriously Babu komai trust me , Kawai ciwan kai nake ji sama , but don’t
worry nasan stress ne ina komawa gida na huta zai dena” hugging d’in ta Baby tayi “
it’s okay zai daina kinji? “ kanta Abla ta d’aga mata , da haka suka soma cin
abincin da sukayi order , time nayi kuma suka koma class a binsu.
Lokacin Tashi nayi kamar kullum suka fito abunsu su uku, har zasu bar building
d’in Abla ta daka sorry gurls ku bani 2 minutes na bar littafina a class , zan same
ku a inda muke tsaya wa , “ Toh “ kawai suka ce mata suka wuce ita kuma Abla ta
nufi class d’insu. A Daidai inda suke suke tsayawa d’in suka zauna zaman kiran
fitowar ta , almost 10 minutes sai ga motocin su Little sun shigo , Yana fitowa
shida prince inda su Eshaal suke ya nufa dan ya ganesu, murmushi akan face d’insu
suka furta “ yaya little barka da zuwa “ shima face d’insa cike da murmushi ya
furta “ Gurly d’in Lil ! Ya kuke “ a had’e Suka furta Alhamdullhi kafun su juya
wajan prince shima su gaidasa, da kai ya amsa musu kafin ya furta “ ina Lil take ?”
Cikin d’an damuwa Fanan ta furta “ ita muke jira tace zata d’auko book d’inta but
almost 10minutes Kenan bata dawo ba.”

Cikin d’an mamaki little ya furta “ and shine kuka tsaya anan ? Me ya hana ku
dubata ? Kuzo muje ku nuna mana class d’in” da toh suka amsa masa kafun su nufi
hanyar class d’insu gabaki d’aya , abun mamaki suna shiga cikin class din basu
tarar da kowa,” kuka ce ta zo class “ Baby ce ta furta “ Eh haka tace mana but may
be munyi kuskuran hanya ko ita ta koma tana jiran mu , let’s go back “ har zasu
juya Fanan tayi Saurin furta “ ku daka , wancan ba jakar Abla bane ?” Kallan
direction d’in sukai gabaki d’ayansu, cikin sauri Little ya ‘karasa wajan school
bag d’in” yeah jakar tane amma me yasa na ganta a ‘kasa ?”Cikin d’an shakku prince
ya furta “ something is wrong, lets go back “ , cikin tashin hankali gabaki d’aya
suka dawo inda Abla tace su tsaya ko zasu ganta amma babu ita babu alamar ta ,
zuciyar Little ne ta buga da ‘karfi shiyasa yayi saurin tafe ta “ yaya prince we
have to check the school , ka kira su robert “ kansa Prince ya jinjina masa kafin
yayi dialling number Robert , su fanan ma gabaki d’aya sun tsure , cikin su babu
wanda be soma hawaye ba a cikinsu. Cikin mintunan da basu wuce 5 ba motocin su
Robert suka shigo cikin makarantar, da sauri little ya furta “ Robert we have to
check da school , bamu ga lil ba ,” shi kansa robert din sai da ya sha jinin
jikinsa , cikin ‘kan’kanin lokaci sojojin su soka rabu kashi kashi , suna su little
d’in basu zauna ba ,suka soma bin class suna dubawa ko zasu ganta , su fanan kuwa
toilet d’in makarantar suka soma zazzagawa amma babu ita babu alamar ta , kamar
wasa tun suna dubawa su kad’ai har little yatayar da rigima sai teachers sun fito
sun nemo masa ‘kanwarsa . Haka gabaki d’aya aka taru ana neman Abla hatta security
d’in makarantar sai da suka bincika babu ita , cikin bada umarni robert ya hana ko
wace mota wucewa sai anyi checking d’inta , har 4 su little suna makaranta, wani
irin hajijiya ne ya soma ji cikin sauri ya furta “ lets go home “ yana magana yana
dialling number yaya bobo, har suka ‘karasa cikin gidan yana dialling number
d’insu.

Su Baby ma gabaki d’aya hankalin su a tashe yake , babu abunda suke sai kuka da’kar
aka sa su koma gidan ana ganin ta za’a sanar dasu, da haka suka yadda amma kowa
hankalin sa a tashe yake .

Motocin su na shiga gida ko parking basuyi ba little da prince suka fito daga
cikin motar cikin tashin hankalin , daga wajan ‘kofar Little yake ‘kwalla kiran
sunan “ Yaya Big Boss , yaya Bobo , uncle ku fito please, ku fito “ yadda yane
‘ko’karin fad’uwa ne yasaka prince saurin ri’kesa shima , cikin damuwa ya furta “
please please little ka kwantar da hankalin ka , may be ba missing tayi ba , please
ka kwantar da hankalin ka ko ina ta shiga zamu ganta ,” da ‘karfi little ya furta
“No “ kafun ya nufi wani red bottun, yana dannawa gabaki d’aya gidan ya karad’e da
‘kara , amma duk da haka he dena dannawa ba shiyasa ‘karar ta cika ko ina , cikin
yan mintunan da basu fi biyu ba gabaki d’aya wasu manyan sojoji suka shigo falourn
a guje kowa da bindiga a hannunsa , uncle da bobo ne suka fito suma cikin sauri
suka nufi su little , hannansa bobo ya kama kafun ya furta “ whats wrong Little me
yasame ka ?” Cikin kuka little ya furta “ yaya i lost her , i lost her kunemomin
ita duk inda take yanzu banasan jin komai , just ku nemo min ita please “ ya
‘karasa yana kara fashewa da kuka , kallan prince da shima hankalin sa yake a tashe
sukai kafun Bobo ya furta me ya faru prince ya rugasa “ yaya bobo , we lost her ,
mun nemo lil sister mun rasa gabaki d’aya su robert sun duba makaranta amma babu
ita “ gabaki d’aya sai da prince ya zaiyane musu abunda ya faru , cikin mamaki Bobo
ya furta “ what ? Sister ?” Zaku nemota ko ?” Cewar little da sauri bobo ya jijjiga
masa kai “ yes little ka kwantar da hankalin ka kawai, zamu nemota , i promise you
amma sai kayi mun al’kawari zaka kwantar da hankalin ka “ yanzu ma cikin sauri
little ya jinjina masa kansa “ zanyi ! But please ka nemo mun ita yanzu” kallan
prince Bobo yayi “ rakasa cikin d’aki ku canza kaya , dont worry she will be back “
yana gama maganarsa ya d’auko phone dinsa gabaki d’aya sojojin da suka shigo
falourn suka bi bayansa, falourn yayi saura uncle kad’ai da tun d’azu beyi magana
ba , a maimakon yabi bayan su little kamar yadda ya saba sai ya nufi part d’in Big
Boss kai tsaye . Be tsaya ‘bata lokaci ba ya shiga har second falourn d’insa , inda
yake zaune yayi crossing legs d’insa , ga coffee da yake sipping a hankali , kan
d’aya daga cikin kujerun uncle ya zauna kafun ya mayar da hankalinsa gabaki d’aya
kan Big Boss “ she’s lost!” ‘Dan d’ago da face d’insa Big Boss yayi sai kuma ya
kamar da kansa yana ‘kara sipping coffee d’insa , cikin d’an d’aga murya uncle ya
furta “ nasan kaji abunda ya fad’a amma kayi shiru ?” Yanzu ma kallan uncle Big
Boss yayi kafun ya ajje cup d’in hannun sa , cikin rashin damuwa ya furta “ ta
za’bi hakan! So just let her be”.
Da mamaki a fuskar uncle ya furta are you serous Farooq ?” Shiru Big Boss yayi
kamar be zai tankaba “ I don’t have anything to do with such matter “, yana karwa
‘karshen maganar ya mi’ke zai bar Wajan uncle yayi Sauri dawo Dashi ba “ are you
serous farooq ? Nace maka Abla is lost amma kana cewa ba matsalar ka bace ? “
gashin kansa Big Boss ya shafa kad’an kafun ya furta “ I have a lot to do uncle “
zai ‘kara wuce cikin daka tsawa uncle ya furta “ kana ce mun kana da aikin yi bayan
ba’a san inda matar ka take ba ?” Da sauri Big Boss ya kalli uncle idanuwansa har
sun fara canzawa ya furta “ kasan da ita a matsayin matar tawa ka ke ‘boye komai ?
Till the last moment kake fad’amun? Do you think you can hide this from me ? Yaushe
ka fara ‘boye mun komai uncle ?” Ajiyar zuciya uncle ya sauke ganin yadda ran Big
Boss ya soma ‘baci “ my intention wasn’t that! Ba na ‘boye maka sabida karka sani
ba , na barshine for the mean time , you have to understand bayanzu ne ya kamata
muyi wannan maganar ba please kaji ?” Huh “ Kawai Big Boss ya furta ya nufi hanyar
bedroom d’insa , maganganun uncle suka d’an dakatar Dashi kafin ya d’an jiyo kad’an
“ Nasan halin ka sosai farooq, da ilimin ka da Tuna’nın ka , sannan da sa hannun ka
, ka Auri Abla , bazaka ta’ba bari ta kwana a cikin gidan nan ba , batare da kayi
bincike akantaba, all this while she’s you wife, in bazaka kula da ita ba , then
kayi for the happiness of your family koda kad’an ne , this once please “, yana
kaiwa karshe uncle ya juya ya bar falourn shima Big Boss ya wuce cikin bedroom
d’insa .
After an hour , motocin su Bobo ne suka shigo cikin gidan, little yana jin
motocin su ya fito da sauri yana Tuna’nın ta inda zai ga Abla amma gabaki d’aya bai
ga ta inda take ba , hannunsa da Bobo ya ri’kene ya dawo dashi cikin duniyar
tunanin sa, “ Don’t worry ! Zata dawo it’s okay ?” Zai yi magana Bobo yayi saurin
furta “ No please nace ka kwantar da hankalin ka ! It’s okay ! Zanyi magana da Big
Boss okay ?” A hankali Little ya jinjina masa kansa ,

Bobo na shiga shima part d’in Big Boss ya wuce ganin baya cikin falourn sa shiyasa
ya wuce bedroom d’insa direct , sau biyu yana knocking amma babu amsa , a na ukun
ne ya bud’e ‘kofar, yana zaune kan kujera da alama wanka yayi Sabida kayan jikinsa
da ya canza , gefe d’aya kuma wayace a hannunsa yana dannawa hankali a kwance .
Bobo bai zauna ba ya furta “ I have to go back to Nigeria “ tsayawa Big Boss yayi
da pressing phone d’insa da yake , cikin wani irin kallo yake bin Bobo dashi , “ in
your dream “, cikin Sauri Bobo ya furta “ I have to ! Wannan abun it’s a plan! Her
life is in danger , I have to go back to Nigeria , idan ba Haka ba komai zai iya
faruwa da ita , “ cikin daka tsawa Big Boss ya furta “ in your dream! Har abada !
Don’t you think of going out”, cikin sauri Bobo ya juya zai bar d’akin , ko kusa
Big Boss be hanasa tafiya NBA , saidai yazo main ‘kofar falourn Big Boss ya jita a
kulle, gabaki d’aya pin din jikin kofar ya saka amma ta ‘ki bud’ewa hatta turnprint
d’insa dake jikin ‘kofar shima ya ‘ki bud’uwa , da Sauri ya koma cikin bedroom d’in
Big Boss , yananan a inda ya barsa “ why please? I’m going back to save her life! A
part from that babu abunda zai ‘kara had’ani da ‘kasar , ka tuna condition d’in da
Little zai shiga plx “ banza Big Boss yayi masa kamar besan da mutum a wajan ba ,
sai ma lumshe eyes dinsa da yayi. Daman bobo yasan za’arina da wahala Big Boss ya
yadda da zuwan sa Nigeria, amma dole ya lalla’basa , if not duk yadda Big Boss
zaiyi sai yanasa shiga Nigeria , shiyasa ya dawo ya zauna kan d’aya daga cikin sofa
d’in Wajan yana bin Big Boss da kallo. Ya fi hour a Wajan amma gabaki d’aya Big
Boss ya ‘ki bashi chance d’in hakan.

Wayar Big Boss ce ta bada wani cool sauti, amma ko kusa be d’auka ba , har kiran ya
katse wani yashiga amma be d’auka ba , sai a na ukun shima sai da ya kusa tsinkewa
ya d’aga kiran, “ follow them “ shine kad’ai abunda Big Boss ya furta ya na kunna
cameran wayansa , cikin Sauri Bobo ya matso kusa dashi , Little suka gani a bakin
door yana ‘ko’karin shigowa d’akin a Daidai lokacin da Big boss yace babu Wanda zai
ce Nigeria , shiyasa cikin sauri little ya ja da baya ya bar falourn , hiran wayar
Bobo shima akai cikin sauri yayi picking d’in called d’in yana kallan Big Boss “
kushirya “ cewar bobo yana kashe kiran ya furta “ Mingus”, kallan Big Boss yayi
shima kafun ya furta “ Mingus ?” Daga haka be kuma cewa komai ba ya wuce d’ayan
d’akin nasa , shima Bobo cikin Sauri ya bar d’akin yana zuwa ya tarar da lock d’in
abud’e shaf shaf ya canza shigarsa cikin wasu irin ba’ka’ken kaya, kusan ko ina na
cikin kayan aljihu ne da ya zuba abubuwa mabanbanta a cikinsa . Almost 20 minutes
yana jiran fitowar Big Boss amma be fito ba shiyasa ya wuce part d’in uncle ko jira
ya shirya be tsaya yayi ba , phone d’insa Kawai ya d’auko masa kuma ya ‘ki fad’a
masa inda zasuje , cikin mintunan da basu wuce 30 Big Boss ya fito cikin wasu
shegen ba’ka’ken masu shegen santsi, a fuskarsa kuma wani sun glass ne da ya saka
gabaki d’aya ba’a ganin kwayar idanuwansa, ga Black p-cap shima da ya saka akan
face d’insa,fuskarsa gabaki d’aya babu fara’a akanta ,cikin Sauri Victor ya bud’e
masa mota suma su uncle suka shiga , basu ‘bata lokaci ba motocin su suka soma gudu
cikin babban titin New York har motocin su suka ‘karasa John F. Kennedy
international airport , kai tsaye Inda jirgin Big Boss yake suka nufa , tun da Big
Boss Yashiga cikin jirgin suka neme sa suka rasa , kallan Bobo uncle yayi cikin
d’an had’e rai “ Bobo meke faruwa ? Tun d’azu Ina muku magana babu Wanda ya
kula ,look at your brother yadda ko kallo bamu ishesa ba , and ina zamuje haka ?
Ina little ina prince? Explain to me please “ gashin kansa Bobo yaja gabaki d’aya
ya rasa me zai cewa uncle , ganin hankalin uncle ya ‘ko’karin Tashine ya furta “
uncle Little yaji conversation d’ina da Big Boss “and sai me ya faru ? Ka barni a
duhu please just explain it to me “, shiru Bobo yayi yana Tuna’nın ta yadda zai yi
masa bayanin “ uncle they went to Nigeria and the risk thing Mingus yasa anbisu,
anything can happen , ban ta’ba ganin ‘bacin ran Big Boss haka ba , sun kai shi
‘karshe , I don’t know what will happen next, Mingus yasan kan harin ya’ki, the
most dangerous thing yasan kan yadda ake harba boom zuwa jirgi, uncle yaran nan sun
‘bata mun rai sosai “. Shiru uncle yayi masa gabaki d’aya ya rasa abun cewa ma ,
lokaci d’aya su little suka fad’o masa a rai shida prince , idan wani abu ya samesu
yasan Big Boss da Bobo bazasu ta’ba ha’kura ba sai dai uban kowa ma ya mutu, yanzu
babu abunda ya d’aga masa hankali sama da yasan condition d’in da Big boss yake
shiyasa cikin Sauri ya furta “ Bobo je kaduba sa” murmushi Bobo Kawai ya saki
kad’an yana girgiza wa uncle kansa “ it’s better uncle ka barsa shi kad’ai yanzu ,
he want to be alone for now, if not every thing will happen musamman idan ya cigaba
da tuna abubuwan da suka faru.”yanzu kam shiru Uncle yayi addua kawai yake Allah
yasa suna lapiya ga Abla itama a wani ‘bangaran an nemeta anrasa.

*******After 12 hours….

Jirgin su Bobo ya shigo ‘kasar na Nigeria , uncle har wani lumshe idanuwa yake , a
hankali ya furta “ it have been years now, a lot of things has change , “ Bobo kuwa
ko d’ago da kansa ba yayi tunda aka shigo Nigeria , time to time yana kallan hanyar
da Big Boss ya nufa , gabaki d’aya hankulansa sun kashi kashi uku, ga Big boss da
bai san halin da yake ciki ba , ga su prince , ga Abla da itama ba’a ganta ba ,
jirgin su na landing su Bobo suka fito daga jirgin tare da sauran sojojin da suka
taho tare dasu, amma banda Big Boss da su Anthony da har yanzu basu fitowa ba
sabida jiran fitowar Big Boss da suke.almost about 15 minutes kafin ya soma sakkowa
daga matattakalan jirgin, ya canza shiga ba shigar da ya zo da ita bane amma still
ba’ka’ken kayan ne a jikinsa ,kwata kwata ba’a ganin yana yin face d’insa Sabida
p_cap d’in dake kansa , Har ya wuce su babu Wanda ya kalla sai sojojin da suka mara
masa baya , suma su Bobo bin bayansa sukai tun kafin su fita daga cikin airport
d’in suka soma jin ‘karar harbi ta ko ina , cikin Sauri soka zagaye su Big
Boss ,Victor da Anthony kuwa ba’kar bullet proof d’in hannunsu suke ‘ko’karin sawa
su Big Boss amma Big Boss ya dakatar dasu tare da nuna musu uncle , kowa yasan yau
ba M Big Boss ya Fito shiyasa kowa yake ‘ko’karin taka tsantsan dashi, hakan kuwa
sukai Bobo suka sawa Bullet proof d’in shima uncle rigar Big Boss ta bullet proof
suka saka masa , Victor sai cire tasa Big Boss ya dakatar Dashi da hannu, suna
shiga ciki suka ‘kara jin wani ‘karar harbi ta ko ina ga mutane da suke ‘ko’karin
kwacen kansa , Bindiga Bobo da Big Boss suka amsa tare da yiwa Victor da Anthony
umarnin su fitar da uncle da ka wajen , Bobo bai gama magana ba yaji an sako musu
harbi , cikin Sauri suka rabu Big Boss da Bobo suka Kutsa kai wajan da suka jiyo
harbin, wasu sojojin suna biye dasu , Big Boss ko bullet proof babu ajikinsa amma
haka yake kutsa kai duk da darene a kwai haske ta ko ina , suna shigowa filin suka
cigaba da jiyo harbi sosai musamman jirgin da ake kai wa hari, kusan gabaki d’aya
mutanan cikin jirgin sun fito kowa yana ‘ko’karin cetar ransa har Wanda ba jirginsu
d’aya ba ma suna cin kushe waje guda , kamar daga sama suka ji murya little yana
furta “ Yaya Big Boss “,a tare Big boss da bobo suka jiyo direction d’insa , yana
tsaye shida prince suna d’aga wa Big Boss hannu, cikin azama Big Boss da bobo suka
nufesu, Big Boss tunbeyi nisa ba yaga wani mutumin yayi baya zai fad’i da hannu
d’aya ya janyo mutumin, Daidai lokacin da hiramin mutumin ya fad’i ,take a Wajan
kyakkywar fuskar dattijan mutumin ya Fito , cikin rawar murya ya soma nuna Big Boss
kafin ya furta “ Farooq!”, cikin Sauri Big Boss ya d’ago da eyes d’insa , a Daidai
lokacin da kuma aka sani wani harbin, kusan ara Zane Bobo da mutumin kusa dashi
suka d’aga murya wajan furta “ Big boss “. Sauban da shima yake wajan kasa motsawa
yayi sai nuna ‘bangaran Big Boss da Bobo da yake yi, cikin sha’kewar murya ya furta
“ Besty”…..

END OF BOOK 1

***SU WANENE BIG BOSS ?


***MENENE DALILIN DA YASA BASA TARE DA AHALINSU?
***** SHIN SUWANENE BLACK SPIDER ?
***** ANYA ARWA NANAN DA RANTA KO TA MUTU.
****SU WANENE ESHAAL ?
WANENE BESTYN DA KULLUM SAUBAN YAKE ANBATA ?
**** MENENE GASKIYAR LAMARI?
***MENENE YA FARU TSAWAN SHEKARA 22 DA BASA SAN TUWANA?

Gabaki d’aya amsoshinku suna cikin book, ku biyoni dan jin ya zaka kasan ce , Mesan
karanta book 2 har karshe zai biya kudinsa ta wannan bank d’in 2681892316 Aisha
umar , zenith, zaku same ta wannan number kamar haka 07041879581.

Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah na ro’keka kamar yadda nagama


rubuta littafin nan kashi na d’aya Allah ka bani ikon gama rubuta ragowar ,
Alfarmar Annabi Muhammed (SAW)! Allah nagode maka da ka nuna mun wannan Rana !
Alhamdulillah ya Allah .

MASU COMMENT INA MATU’KAR GODIYA SOSAI , MSSLEE FANS GROUP SA’KON JINJINAWA TA
MUSAMMAN A GARESU TARE DA YAN IBTISSAM UPDATE , INA MATUKAR JIN DA’DA’DAN COMMENT
‘DINKU , NAGODE SOSAI!.
MSSLEE CE TAKU HAR KULLUM.

You might also like