Download as doc, pdf, or txt
Download as doc, pdf, or txt
You are on page 1of 377

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH

*Assalamu alaikum lovelies, ina fatan zaku nutsu kamar yanda kuka saba ku fahimci saqonnin da ke cikin
wannan novel, mai suna AURI SAKI, labari ne da zai tabo bangarori da dama na rayuwar aure kamar
yanda na saba, sannan za a samu wasu daga kayan gyaran jiki ko gashi da sauran su inshaa Allahu, ina
roqon ku kamar kullum kuna adana page, koda baku da sha'awar karantawa yanzu, sannan in mutum
yaga abu mai amfani ya copying, ya aje saboda gaba, bana son ana min magana ta pc ya dade ban amsa
ba a ji haushi,ko a tambayi novel ban bayar ba bana jin dadi wallahi, ayi hakuri ana ajewa na gode,
HAERMEEN HAERMMAERH LOVE U ALL XOXO*❤
Page 1:

Lokacin damuna ne, dik da an kwana ruwan sama, har yanzu garin katsina da akwai sauran hadari, wata
siriryar yarinya na hango, da kayan makaranta, tana tafe kan ta a qasa, dogayen gashin idon ta sun
kwanta a qasan idanun ta, dogin hancin ta ya rufe qaramin bakin ta, in ba dagowa tai ba ba zaka gan shi
ba, baqa ce sosai, amma irin baqinnan mai sheqi mai kyau, adaidaita sahun dake maida ta gida ne ya
tsaya gaban ta, ta turo baki gaba, tare da dan alamar maida ido gefe na taji haushin dadewar shi, ta yi
hakan ne ba tare da mai adaidaita sahun ya gani ba, sa kai tayi zata shige, shima ya sako kai cikin sauri,
"Yammata dan Allah kiyi hakuri, a kaini asibiti, majinyata na jirana mota ta ta samu matsala a hanya, na
san da yardar Allah zaki samu wani, ga wannan ki shiga wani,"

Cikin yanayin sauri ya zaro 1k a aljihun shi ya miqa mata, kallon shi ta tsaya yi, dan ganin kyau irin na
Okashatu Muhammad Sani Daura, a hankali ta sauke idon ta cikin muryar ta mai sanyi tace,

"Ina ne a sibitin?"

Fada mata yayi, yana kallon ta, cikin zuciyar shi yana tasbihi ga mahaliccin wannan kyakkyawar halitta,

"To ai hanya tace, kuma mai adaidaita sahun gidan mu ne, in aka aje ni sai ya kai ka,ba nis daga nan na ci
qarfin tafiyar,"

"To masha Allah muje, pls ana jirana, kinji ma kirana ake yanzu,"
Da sauri ya daga wayar yace su bashi minti 10 yanzu zai iso, motar shi ce ta lalace, sallama yayi ya aje
wayar, hankalin shi ga a daya yayi asibitin, ga kuma tinanin wannan kyakkyawar da ke gefen shi, dik
yanda akai daga gidan mutunci ta fito, tin dazu ta kasa daga kan ta tin kallon farko da ta masa, murmushi
ya tainci bakin shi da zuciyar shi suna yi,

"Ammm meye sunan Young ladyn ne?"

Kallon shi tayi qasa, da fararen idon ta wanda suke da baqi mai kyau a cikin su, ta sake maida kan ta
qasa, sannan ta amsa shi,

"Suna na Umma Hanee Abdul kareem, Me katako, Daura,"

"Woww masha Allah sunan ki ya dace dake, naga tin dazu kina motsa baki ince dai ba laifi nayi ake
qunquni ba,"
Da sauri ta daga kan ta cikin marairaicewa, idon ta mai saurin zubda hawaye har ya fara ruwa tace,

"A'a nifa ba magana nake da kowa ba, face neman gafarar Allah, da kuma salati ga rasulullah, sai tasbihi
ga ubangijin talikai, amma ni baka min komai da zan maka qunquni ba,"

Subhanallah,ta hadu,

,"Masha Allah, amma gaskiya zan so sake haduwa dake a rayuwa ta, ko yanzu kin ban wani ilm mai
matuqar amfani,"

Murmushi tayi, a nan adaidaita sahun ya tsaya, a qofar wani gida madaidaici, wanda ba zaka kira shi na
talaka ba, ba zaka kira shi na masu kudi ba, kadaran kadahan, amma a tsaftace yake tin daga qofar gidan
har cikin gidan,
"Allah ya bada sa'a ya sa marasa lfyn su samu sauqi cikin amincin Allah,kai kuma Allah ya baka lada,"

Bata jira mai zai ce ba ta sa kai ta shige cikin gidan su, ta maida qofa ta rufe,

Wani abu yaji na tsarga masa tin daga yatsan qafar shi har cikin naman jikin shi da jijiyoyin shi, qashi d
bargon shi tare da jinin jikin shi duk sun amsa, bai taba gani ko jin labarin mace kamar Umma Hanee ba,
a gaskiya ba zai bari a barshi a baya ba, sai dai kashh, ta sha bambam da sauran mata, anya zai yarda ya
aure ta kuwa? In ya aure ta itama suka rabu fa?

"Na ga alama ka shiga tinanin Umma Hanee sosai, bana tara sani da Allah, amma gani nake kamar kun
dace da juna,kaima na ga nutsuwa da tsoron Allah a tare da kai, zan so ace Umma ta samu miji na gari
kamar ka, domin iyayen ta ma mutanen kirki ne, naga gaba daya ka shiga wani hali tin da ka dora idon ka
akan ta,"
Cikin zumudi ya matsa yanda zasu samu damar yin magana sosai,

"Malam ka santa kenan sosai? Ban labari game da ita mana?"

"Kwarai da gaske, na san ta,baban ta katakwaye yake siyarwa, na gini, babban mai saida katakwaye ne a
nan babbar kasuwar garin nan, kowa ya san shi, mahaifiyar ta kuwa sana'o'in gida take, kamar saida su
Omo da Maggi, da dai sauran kayan masarufi, suna kiran ta da Amma, baban su kuma Abba, asalin su
katsinawan dikko ne in ka kula zaka ga kyau irin na su a tare da ita, gida ne da suka gina shi cikin so da
qaunar juna, wanda qannen ta ke matuqar girmama ta, suke son ta,saboda adalcin da take tsaida masu,
Ammar ke bi mata sai autar su, mai sunan kakar maman su wato, Zainab suna kiran ta da Zee, akwai
ilimin addini sosai a gidan da na boko, dan in kaje zakaji suna yare kala2 agidan, larabci, English, Fullanci,
da hausa, kowanne yi suke, ina fatan zaka qoqarta ka shiga rayuwar ta da alkhairi a dama da kai, na san
su tin ba a haifi Ammar ba, nake kai Hanee makaranta,"

Dik bayanin nan da Malam Sabi'u ke masa gaba daya ya sashi tinani, lallai ta masa, kuma zuciyar shi a
yanzu haka da son ta da qaunar ta take bugawa, wannan shine ake kira da soyayya a ganin farko, ta
shiga zuciyar shi matuqa ainun, amma shin maganar zata yuwu kuwa?
"Malam baka fadan sunan ka b kai din, naji kayi shiru ko na cika ka da surutu ne?"

A daidai lokacin da suka isa qofar asibitin, ya nemi izinin shigewa da adaidaita sahun, dan saboda tsaro
ba kowa ake bari shiga ba, sai in da mara lfy, shima sai an duba shi sosai, an tabbatar,

"Suna na Okashatu kamar yanda kaji na fada dazu, ina ganin salon rayuwa ta da ta ta rayuwar, ba daya
bane,dan na kula tana a cikin qaramar rayuwa ne mai cike da so da qauna da aminci, da kuma kulawa,
tare da tarbiyya,tawa rayuwar kuma sabanin dikkan abinda na lissafa maka ne, dan haka ina ganin
labarin mu ya tsaya anan, na gode ga haqqin ka, ka riqe sauran, nayi niyya ne tsakani da Allah,"

Ya miqa masa kimanin dubu uku, wanda Malam sabi'u gaba daya bai wani farin ciki da su ba, a zaton shi
Okashatu zai zama masoyi na Umma Hanee har aure ya shiga tsakani, dan ya yaba da kalaman shi na
taimakon marasa lfy, da kuma yanayin kyau da arziqi daya hango, yana jin Umma Hanee kamar diyar
cikin shi, kowa kuwa zai so ace diyar shi ce ita dan tayi ta ko ina
Okasha ya kula da disappointment da Sabi'u ya samu akan maganar shi, but this is the truth, ba yanda
zai yi, kawai ya sa kai ya shige............

*Makaranta sai an min uzuri saboda wayata na da matsala, in baku ganin post dina akan lokaci kamar
yanda na saba, zan dinga posting a duk sanda na samu lokaci*

*Yawan Comment da sharhi yawan page, Comment shine ribar Online writers, tinda ta haka ne muke
sanin saqon mu na isa ana gane me muke fadakarw akai ko ba a ganewa, plsss comment and share,
thanks❤*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 2:
Umma Hanee kuwa tana dawowa ta yi dakin Amman su da sallama, sai da ta nemi izinin shiga Abban su
ya amsa da ta shiga, sannan ta shiga, ta zauna a gefen qafar Amman ta da ke kwance sakamakon zazzabi
da ya kama ta, cikin tsananin damuwa da nuna so da qaunar Amman nata ta ke kallon ta, idon ta fal
hawaye,Abban ta na ganin haka ya dafa kan ta,

"Look Hanee jikin fa ba wai yayi tsananin da zaki daga hankali bane, malaria ce kawai, kuma dawowa ta
na bata magani ta sha, ta kwanta, yanzu haka zufa take alamar saukar zazzabin, Ammar ya kammala
komai n abinci, ki mata sannu kije kici, ki wanka, ki fara wasu abubuwan da ya kamata, Allah ya miki
albarka da sauran 'yan uwan ki,"

Share hawayen ta tai, bayan ta taba jikin Amman taji ba wani zazzabi ya sauka kamar yanda yace, kawai
bacci take, kissing goshin ta tayi a hankali yanda ba zata tada ta ba, ta miqe, ta bar dakin, zuciyar ta dik
ba dadi.

Tana shiga dakin su ita da Zee taga tana ninke kayan ta da aka wanke mata tana jerawa a kayan su, da
sauri ta sake kayan ta je ta rungume ta,tana mata sannu da zuwa, ita kuma cikin sakewar fuska ta amasa,
ta shafa kuncin ta tare da turo bakin ta akalar kiss, ta sake ta ta fara cire nata kayan,bayan ta kammala,
Zee na ta bata labarin makarantar su da larabci, tana amsa mata, ta dau ki towel ta daura ta fada toilete
din su dake manne a dakin, ta shiga wanka, ta dade tana cuda jikin ta cike da tinani kala2, tana wanke
fuska ta taba lips din ta, wajen dauraye fuskar ta tina da Okashatu daya ce tana motsa baki ko qunquni
take masa, qayataccen murmushi ta tsinci kan ta tana yi, a hankali ta hade hannayen ta ta rufe qirjin ta,
gani take tana tinanin namiji a bandaki tana a tsirara ai magana ta baci, da sauri ta kammala ta fito, tana
ture tinanin shi, a fadan ta bari har ta gama komai, ta zauna tayi tinanin nashi.
Bayan ta kammala, taci abinci ta gama, su Zee sun wuce islamiyya,Amma ta tashi, ta fito tsakar gida,
Hanee na daka daddawa da kayan qamshin da zata dora tuwon dare,

"Hanee why ar u smilling? Ko kinyi tsintuwar kudi ne?"

Cikin shaquwa ta diya da uwa ta fadi hakan, bata san sanda ta qara sake wani murmushin ba, ta ja
turmin ta gavan Amman ta, ta kalle ta tace,

"Amma yau ko, wani ne ya dale min adaidaitan Malam Sabi'u, kinji har da cewa wai ina masa qunquni
dan ina tasbihi na"

Ta sake sake murmushi wanda yafi kusa da dariya,


Amman ta ce ta buqaci jin yanda akai lamarin, nan ta fara fada mata ya abun ya kasance,tana yi tana
aikin ta, bayan ta kammala hada komai ta dawo suka zauna, a kan tabarmar da Amman ta shimfida
masu,

"Matso sosai na duba idon ki anyaaaaa, irin wannan murmushi mai tsada haka daga tina mutum?"

Sunne kai tayi, can ta dago tana borin kunya tana cewa,

"Ammaaaa ni dai ki bari ba ruwana, ni ba wani anyaaa,ba ruwana da kowa, karatu zanyi, sai na kai
matsayin cikakkiyar likitan mata Amma kan in tsaya inshaa Allahu, wannan shine burina,kuma burin ki,
dan haka ki daina kiran anyaaaa kin san bakin ki mai albarka ne sosai fa Amma,"

Rungume diyar ta tayi, ta na shafa kwantaccen gashin ta, daya fito a dankwalin ta,
"Nayi shiru to my baby, inshaa Allahu Allah will give u a gud husband, d one dat will take very gud care of
u fiye da yanda Abban ku yake kula damu, kinji?"

"Ameen Ammana, Allah ya qara maki lfy da iman, ya qara maki tsahon kwana ki ci gaba da mana addu'a
akan komai namu, ina son ki Ammana"

"Ina son ki Hanee na, Allah ya albarkace ku dika,"

Tuqa tuwo ta tashi yi, dan dama sai da tai rude suka zauna, cikin turo baki Ammar ya shigo, wanda ba zai
wice shekara sha uku ba, Umma Hanee ta bashi shekara uku da watanni shida, sai auta Zee mai shekara
takwas.
"Me ya samu Ammar din Amman shiii,"

"Amma na sha fada maki addu'ar ki Allah na saurin karbar ta, duk sanda nai latti kk min addu'a ba a
dukana, amma yau naje kina ta bacci na fita, da idon ki biyu da ban sha bulala bakwai ba,"

Cikin tausayawa Hanee ta tashi da sauri taje tana duba jikin shi dan taga ko akwai wani shatin duka, bata
ga komai ba, sai dan tashi da gefen cikin shi yayi, sannu tai ta jera masa yana amsawa yana narkewa,
addu'a ta dafa wajen tayi,

*Bismillahi ×3, A'uzu bi izzatillahi wa quduratihi, min sharri ma ajidu wa uhaziru ×7*

Tana gamawa ta tofa a wajen, dan addu'a ce mai kyau da inganci, ko wanne irin ciwo ke damun ka ka
dafa kayi zaka ji sauqi da izinin Allah, sai dai in bai daina ba ka sani dama ciwo farat daya yake shiga sauqi
sai a hankali, amma tabbas zaka samu ladan adduar ka da kuma sauqi akan azabar da zaka sha a da.

Cikin wasa ta dan danna wajen ya ko saki qara,


"Kai dai kaji kunya kai ta ihu akan dan ciwon nan kamar mace, matsa ni ina da abun yi,"

Kwabe fuska yayi ya kalli Amman su,

"Ammaaaa kin ganta kooo,"

"Zo yaron Amma shalele abin kallon na"

"Kamar wani shine autaaa"


"Baki yi sallama ba ya ukhtee?"

"Opsssyyy Assalamu alaikum,"

"Wa'alaikumussalam,"

"Aunty Hanee kina gani za a min juyin mulki ko,"

"Zo nan rabu da shi, ki tayani aiki Allah ya baki lada yaje ya ci shagwaba muga yau ladan me zai samu? "

Yana jin haka ya miqe da gudu ya riga ta isa, nan da nan suka kammala dikkan abinda ya dace ace
Amman su ce tayi shi.
(Wannan na daya daga cikin kyakkyawar tarbiyyar Amman su, ta koya masu mahimmancin lada, da
girmama junan su, ta koya masu yin raha da wasa da dariya da junan su,ba zage2 da dambace2, da
hare2, da ganin ido, sannan bata nuna masu wani ya fi wani a yaran ta, ko sau daya, in fada sukai zata
ma kowa fada, daga baya ta ja kowa dayan bai sani ba, ta ba shi hakuri, ta nuna masa inda yai laifi da
gyara,sannan ta nuna masa mahimmancin hakuri da juna, da kuma girman soyayyar 'yan uwantaka, a
haka sai anjima kuga sun qulle sun qara ma junan su matsayi mai girma, dan har irin 'yar qaryar nan take
tana ce masu, dazunnan fa muka gama magana da dan uwan ka yana ce man dik gidannan yafi son ka
bayan ni da Abvan ku, amma shine kk fada da shi? Kenan ba amfanin son da yake maka, in zaka na iya
fada da shi, nan danan yaran suke shiga nutsuwar su, suji son junan su na qaruwa masu, wannan shine
tarbiyya iyaye a kula, wasu daga su zagi wannan a bayan idon shi da wannan dan nasu sai su hada su
gaba da fada, wanda daga qarshe dai akan su take qarewa)

Sai da sukai sallar magrib suka hau wankin kayan uniform, suka kammala, suka shanya, dan yau Amman
su vatai girki ba da suna dawowa daga islamiyya sukeyi,kafin isha'i kayan sun bushe Hanee ta goge masu,
taran ita take hadewa ta masu wankin, wataran Ammar, in sukace Zee ta wanke safa sai ta dage hannye
ta kar ya kai tace " i am only 8," amma in tare za a yi tana gaba wajen wanke wa.

Suna gamawa sai suyi sallah, su ci abincin dare, masu home work suyi, marasa shi suyi karatun islamiyya,
Hanee na guga, a qa'ida kan su kwanta sai sun karanta Suratul Mulk, (Tabara) har Zee ta haddace,
sannan ta haddace Kahfi saboda juma'a.
Bayan Hanee ta kammala komai, ta yi wankan dare ta kwanta, bayan addu'ar da tayi take ta maimaita
suratul ikhlas, tinanin Okasha ne ya mamaye ta,

"Hummm as promised wato sai da na kammala komai tinanin ya dawo, k lets do it then,"

"Aunty ar u talking to me?"

"No i am not,"

"But i had u saying something like lets do this,"

"I wasn't talking to u zee, so go back to sleep, may Allah protect u lil sis,"
"Ameen,"

Shafa kan ta tayi, tana hango yanda lips din Okasha ke motsawa sanda yana mata magana, Ya rabb guy
din ya hadu, cikin rada ta damqe idon ta,

"Ina ruwana da bakin shi?"

Ko da ta rufe idon ma shi take gani, runtsewa tayi sosai, ta ci gaba da karatun ta, har bacci mai dadi ya
dauke ta.

Washe gari ta tashi cikin farin ciki, sakamakon bacci mai dadi, cike da mafarkan Okasha da tayi, ta
bangaren shi ma haka, Matar shi kama ta zaci saboda ita yake cikin nishadi, hamdala tai ta godewa
bokan ta, ta sake juyi, t koma baccin asara.
Wanka tai ma Zee, dan taji motsin Amma a kitchen wajen hada abinci, leqwa dakin Ammar tayi, ta gan
shi yana kwance, a hankali ta tada shi, ta wurga masa towel din shi, dauke da addu'ar bacci ya.miqe,ya
gyara qur'anin shi da ya karanta da asuba kan bacci ya dauke shi, (wannan qa'idar su ce dika karatun
qur'an bayan sallar subh da magrib, har Zee) wanka ya shiga shaf2,ya fito, ya saka kaya,ya shafa mai, da
sauri shima ya je gaida iyayen nasu, ya fara taya Amma da Hanee hada masu abincin makatanta, Ammar
komai ya iya na aikin gida, dan da shi ake komai, sai da suka saka na su, sannan suka zauna cin abincin,
Hanee da bata saka riga ba da hijab ta fara share tsakar gida, Ammar da ya shirya kar motar makaranta
tazo bai shirya ba, ya koma dakin shi ya shirya dakin tsaf, ya fara tattara kayan wanke2 mota tazo, da
sauri ya dau lunch box din shi, da jaka, ya isa wajen Amma da Abban su, ya musu sallama suka mashi
addu'a ya fita riqe da hannun Zee tana ta iyayin gyara jakar ta, irin ratayawar Hanee, dariya dika suke ta
mata,har suka bar gidan, Hanee ce ta qarasa kusan dikkan ayyukan, kamar kullum tukwane ne kawai
bata wanke ba, Malam sabi'u yazo,abinci Amma ta miqa masa a wata roba mai murfi, suka gaisa Hanee
ta masu sallama suka fice, a hanya yai ta mata labarin Okasha, ta san halin shi da son yaga tai
saurayi,dan yaga yanda qawayen ta ke da samari tin jss 2 ma, amma ita yanzu a ss2 har yanzu bata da, yi
tai ma ita ta manta da wani Okasha, nan ko yana manne a ran ta,har addu'a take Allah yasa yau ma
motar shi ta baci su sake haduwa.

A kwana a tashi ba wahala, yau kusan sati daya da kwana uku, Okasha bai nemi inda Hanee take
ba,sannan yaqi ya cirs tinanin ta da son ganin ta a ran shi, itama ko sau daya bai taba barin zuciyar ta ta
huta da kewar shi ba, addu'a tayi ta ba iyaka,walwala da sukunin ta ya ragu sosai, aiki kawai tana yi ne a
gidan amma ba wani jin dadin abun kamar da, ana yi ana hira da jin dadin suna taya Amman su aiki zasu
samu lada kuma zata saka masu albarka, dan sun san ma'anar albarka wajen Amman su malamar su
kuma, albarka ta qunshi dikkan wani alkhair da Allah zai maka, dan haka duk wanda yace Allah ya maka
albarka ya gama maka addu'a.
Amma ta kula da halin da diyar ta take ciki, tana son mata magana bata son ta sake maimaita mata
kalaman ta na kullum, dik da wannan karon ta san qarya take koda ta ce ba komai, ba kewar Okasha
take ba, to ya zatayi? A ranta ta yanke shawarar yi mata addu'a kawai.

Yau Okasha ya fito daga gidan shi, zashi kiran Baban shi da ya aika yaje matar shi ta kai qarar shi, tana
can tin sassafe,ko nace tin duku2n asuba, ranshi bace ya shiga motar shi, yaran shi da suka kusan kai tara
suna masa a dawo lfy, ko kallon su bai ba ya wuce.

Wani tangamemen gida na gani, mai matiqar girma, wanda ba zan iya tsayawa bayyana fadin girman
gidan ba, gidane daya qunshi sashe2 guda biyar,sannann akwai wajen aje motoci mai girma, yara ne
kala2 bila adadin a gidan, wanda in qirga su aka ce kayi zaka dade kana yi cikin gajiyawa, sai gaida shi
naga wasu wadan da suke qasa da shi suke yi, wasu kuma da suka girme shi ya tsaya ya gaida su, suka
amsa ya shige ciki.

Wani katafaren parlor naga ya shige, sannan ya zauna a wata kujera ta alfarma, ya fara danna wayar shi,
sai da tai ringing sau uku sannan aka daga,
"Alhaji gani na iso,"

Cikin minti kamar sha takwas suka fito d wata mata, baqa gajera, mai fadi da timbi, sai wani karairaya
take, a dole ga macen da miji ke ji da ita, Alhaji ne ya mata nuni da ta koma ta jira shi, gashinan zuwa,
dan turo baki tai wai shagwava, ya hura mata kiss ta wani yi tsalle wai ta kama, ta koma dakin, Okasha
na kallon su, ko a jikin shi, dan shine sak uban shi, halin su daya, in dai akan mata ne, shiyasa uban ke
son shi a yaran shi,sai dai sun sha banban da mahaifin shi ta abu daya, wanda mahaifin ke matiqar jin
haushi...

..

*Okashaaaa Allah ya sa halin ka da sauqi akan na Abbas😭💃🏻 cassss*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*I can't go further without thanking my SHERRY, Thank u so much dear for everything, sharifah na
matuqar taimaka min sosai musamman in ana neman novel komai yawan wanda kk so da yardar Allah in
dai ka iya tambaya zata sambada maka gaba daya bata gajiya ko mutum nawa zasu tambaya a rana,
amma fa iri na ce bata san umarni🤣 masu bata umarnin turamin novel kaza ba pls ba komi suna ganin
dif🤣 anyways i thank u so very much,Allah ya kawo miji na gari mumini salihi amma a Nija yanda zamuji
dadin zuwa kullum2😀💃🏻 much love sweetheart*❤

Page 3:
Gyara zama yayi yana fuskantar Okasha, shi din ma shi yake kallo, fuska ba walwala, dan yasan akan me
za a masa fadan,

"Okashatou me yasa kk haka ne? A kullum ina nuna maka tinda Allah ya qaddara muna da son aure2 to
pa dole mu dinga kulawa da matan da muka kawo, in sukaji dadi ko mun rabu ba zasuji haushi sosai ba
dan b mu wahal da su ba da gwabin su sika tafi, amma ka na tare da mace kai ta faman zuqe mata
albarkatun jikin ta baka sa mata taki mai kyau? Irin haka ne yake sawa kk saurin sakin su dan kana jin su
ba kamar da ba, ni a shekarun ka mata hudu kawai na saki, amma kai har ka kai bakwai, meke damun ka
ne?"

"Alhaji qarya fa take min,kaje yanzu ko kasa a duba store shaqe yake da kayan abinci,"
"Kayan abinci ba kayan masarufi me kenan? Da me zata hada abincin ita ba sana'a ba ka hana aiki, ba
mai ba maggi, ba kayan marmari da zai tada mata komada, sannan ba dan nama ko kifi, Okashatou ka
kiyayen,"

"Alhaji ayi hakuri, za a gyara,"

"Maganar kenan kullum,in baka gyara ba zan gamu da kai ai,"

Kira yayi da qarfi, wani a cikin yaran gidan ya zo da sauri, ya durqusa, umarni yayi da a kira matar
Okashaou, mai suna Hafsa, bayan wasu mintuna kamar hudu ta shigo, gaba daya ba zaka ga Okashaou
ka ce wai wannan itace matar shi ba, ba kayan kirki, ga ta ta wani zuqe, ba kwalliya, sai tsami take, haka
ta duqa, amma sai dan neman iyayi, hakan zai nuna maka ada tana da ado da son gayu, yanzu ne ba ta
da kayan yi ko wani dalili ya maida ta hakan.

Nasihar hakuri da juriya Alhaji ya masu ya sallame su, suka fice, ya koma wajen amaryar shi ta goma sha
takwas.

Alhaji da dan shi Okashatou suna da dabi'ar son mata, amma da aure, zasu auri mace da ta kwana biyu
zasu sake ta, bambamcin Alhaji da Okashatou kuwa shine,Alhaji yana kula da matan shi da yaran shi
sosai, wanda hakan ya sa masu son shi ba kadan ba, sun bar yawan auren shi a qaddara ba son zuciya ba,
Okashatou kuwa in ya auri fara sai ta koma baqa dan wahala, da babu, kuma ya hana aiki da zuwa
makaranta, kan shi kawai yake ginawa baya kula da matan shi, da yaran shi,matan Alhaji guda biyu suna
nan, sauran biyun ne yake canjawa daga lokaci zuwa lokaci, yaran Alhaji sin fi gaban lissafi, dan sun
tasamma talatin da 'yan kai, in basu fi arba'in ba, matan da ya aura ban da su Hajiya Babba da Hajiya
qarama sun kai sha takwas, plus su ashirin kenan, Okashatou kuwa banda uwar gidan shi ya auri bakwai
kenan ya sake, yaran shi tara, a yanzu a gabam shi, banda guda hudu da iyayen su suka qi dawo da su,
wasu ma sun bar qasar da yaran, dan ba su son su rayu a qarqashin mugun mulkin Okashatou.

Idan shi yayi sha'awar cin abinci mai kyau da dadi, zai tafi katafaren wajen cin abinci mai qayatarwa ya ci
kona nawa me ya biya ya koma gidan shi tamm, a kullum kuwa in zai koma gida da naman shi ko fish
kabab din shi, da fresh milk. Ko juice dai haka, duk abinda ta dafa ya qara ya ci ya tashi, wanda ya rage su
cinye ita da yaran ta kawai, da safe a waje yake cin abinci, ko ya fita shago mafi kusa da su ya siyo
indomie da kwai ya kawo ya shiga kitchen da kan shi ya dafa, ya taho da kayan Tea ya hada ya sha, ya
fice, Okashatou yana da tsananin son kan shi sosai, unlike his Dad, suna da banbanci sosai, ko haihuwa
mace tayi Okashatou in yaga zata matsa masa da sai kaza ban kaza zai iha sakin ta da danyan jegon,
sakin da ba kome, kuma ya tattara ta ko kunya ya kaita gidan su, yace sun sai mata me take so shi bai da
shi, mahaifin shi lokuta da dama shi ke yanka ragon suna a gidan Okashatou, ta bangaren shi kuwa in
akai masa haihuwa komai zai sai wa mace, wanda ta tambaya da wanda vata nema ba, haka zai ma mace
kaya masu yawa da kyau da tsada, wannan itace rayuwa Okashatou da mahaifin shi, masu AURI SAKI.

Kwance take tana karatu, ko nace tinani, dan ta fara karatun jarabawar ta ta qarshe, sune zasu zana
jarabawar kammala babbar sakandire bana, gaba daya karatun baya shiga,hawaye ne naga ya gangaro
mata a gefen idon ta da take kwance ta gefen, hannu ta kai ta share cikin zuciyar ta take magana amma
bata san ya fito fili ba.
"Ya Allah ka sauqaqa min soyayyar wannan bawa naka da bai san ina yi ba, daga gani daya komai nawa
ya kwace min, ban da tinanin kaina sai nashi, ban da zuciya a jikina ya tafi da ita, ina tsananin son shi,
Allah ka yaye min, kar na wahal da zuciya da gangar jikina a banza, in alkhairi ne a gare ni Allah ka dawon
da shi na huta da zogin dana ke ji a qirjina,"

"Ameen"

Shine amsar addu'ar ta da taji a gaban ta, tana daga kai taga Amman ta, wadda Zee ta kira tace ga Aunty
Hanee can na kuka, zama tayi gefen ta, Zee dake tsaye ta kwabe fuska kamar zatai kuka, dan ganin yayar
ta na kuka, Amma tai ma nuni da ta vasu waje, d sauri ta wuce dakin Amman su inda Ammar ke wanke
mata toilete.

"Hanee dear, ki sawa zuciyar ki sauqi,akan wannan bawan Allah, Hanee irin soyayyar da kk masa kusan
ita ake cewa makahon so fa,ina jin tsoron kar ko auren shi kikai ki sha wahala, plsss love ki dinga addu'a
sosai saboda samun sauqin lamarin nan, nima zan taya ki sosai, kinga jarabawa zakuyi nan da wasu
satittika, in baki maida hankali ba ba zaki samu result mai kyaun da zaki karanta aikin asibitin ba, kinga
kin rusa burin ki da nawa kenan, plsss habibti ki maida hankalin ki akan abinda yafi zama farilla, kinji?"
Tinda Amman ta ta shiga dama ta rungume ta tana qarasa kokawa a jikin ta, daga kai kawai take tana
shessheqar kuka, Amman ta na shafa bayan ta, har ta samu nutsuwa,

"Amma inshaa Allahu zan kiyaye, zan maida hankalina na yi abinda ya dace, na gode Amman mu,"

Jan hancin ta tayi,

"Give me a smile then,"

Murmushin ta mai matuqar kyau ta mata sannan Amman ta amshi littafin tana taya ta karatin,tana mata
tambayoyi tana amsa mata, wanda vata sani ba ta koya mata ta mata bayani akai, domin itama tayi
makaranta, iyakar ta secondary aka mata aure, dake lokacin ba wani halin ci gaba ga shi bata shekara ba
sai da cikin Hanee wannan dalili yasa ta hakura tace gwanda ta zauna ta kula da mijin ta da yaran ta.
A kwana a tashi Hanee yau suke zana jarabawar qarshe, ita da qawayen ta suna tsaye a bakin titi suna
jiran masu daukan su,suna ta hira, a haka kowa ya tafi sai Hanee ita daya, Malam Sabi'u bai san zasu
tashi da wuri haka ba, ga shi wayar shi tin daren jiyan ba caji, ta gwada yafi sau shurin masaqi bai shiga
ba,haushi dik ya ishe ta, yanke shawarar neman wani mai adaidaitan tayi kawai ya kai ta gida, dan
takawa tayi, ta isa titin da take hangowa daga inda take tsaye,ba wani nisa, mota ta gani red colour mai
matuqar kyau ta na dawowa in da take, dauke kan ta tayi, ta qara yin gaba, dan ta san in ba Abban su ba
ba motar wani da ta taba shiga koda kuwa na 'yan makarantar su ne Amma ta hana, dik da amatse take
taje gida ba zata soma bin strenger ba.

"Umma Hanee ko?"

Da sauri ta juya,dan jin muryar mai maganar, neman faduwa take da sauri ta dafe jikin motar da ta iso
daf da ita a wannan lokacin, zuba masa fararen idon ta tayi, tana kallon shi kamar wanda zai gudu,cikin
in ina take magana,

"Dr .....Okashaou?"

"Yeh ni ne, ya na gan ki ke daya ina Malam Sabi'u? Ko bi zo bane yau?"


Mamaki tayi bai manta sunan su ba dika, wata murna tai ta yi tsalle amma a zuci,

"Eh bai zo ba, yanzu ma so nake na hau wani abun hawan na isa gida,"

"Very gud then kinga shikenan sai na aje ki na wuce asibiti kawai, tinda ga shi na zo ni in shi bai zo ba
ko?"

Murmushi tayi da yake matuqar mata kyau, she will love to, amma ba zai yu ba Amma ta koyar da su qin
shiga motar kowa,dan haka dole ta kula da kan ta.

"I will love to, but i can't come with u, na gode da kulawa zan iya qarasawa da adaidaita sahu,"

"Me kk tsoro? Bana satar mutane fa, naga dai adaidaita sahun ma ba sanin su kikai ba, ba gwanda ni
bama mun taba haduwa,"
Okashatou ya dade yana mata dadin baki dan ta bishi, musamman yanda ya gano tsabagen son shi a
idon ta, Okashatou ta san kan mace matuqa, dan haka ba wuya yake gano su da halayyar su, a haka ya yi
ta jan ta da hira, har ya qara dasa mata sabuwar soyayyar shi, ya mata sallama ya tafi tin da taqi bin shi.

Tana cikin adaidaita sahun data tsayar take ta murmushi da jin dadi. Kalaman shi na qarshe, wanda yake
ce mata zai zo gidan su, su gaisa, dan gaisuwar hanya bata dace da yarinya mai kyau da kamun kai irin ta
ba...

*Ohhhhh Allah maza kenan sai danneman dadin baki😏*

*More comment morw post, less comment less post🤣💃🏻*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 4:
Ko da ta isa gida ta tarar, Amma ta masu abinci mai dadi sosai, kala2, kowa yayi wanka yayi kwalliya har
Abban su, domin taya ta murnar kammala secondary school, itana cike da jin dadi da murna ta bisu da
kisses, sannan ta shiga daki tana tsallen murna ta cire kayan ta, tayi wanka, ta caba ado, wanda Amman
ta bata san dama diyar ta ta ta iya irin shi ba, kowa baki sake yake kallon ta, zee ce taje kusa da ita ta
mintsini hannayen ta da nade su cikin juna tana ta zabga murmushi, ta san mamaki suke, da qarfi ta
janye tayi qara,

"Ouchhh zee what is wrong with u?"

"Aunty Hanee ke ce? Dama kin iya kwalliya haka bakiyi? Nima sai an sake min wankan,"

"Ba fa wanka z a sake maki ba kwalliya kawai za a maki kema kiyi kyau faqat, muje"

Kwalliya ta mata suka dawo, da addu'a Abba ya fara sannan ya dakko mata gift din daya yi niyyar bata,
wata sarqa da dankunne ne na zinare, masu kyau su ba manya ba ba qanana ba, Hanee harda kukan
dadi, ta qanqame masa wuya tana godiya, Ammar ne ya banbare hannayen ta,
"Aunty Hanee basshi haka muma.muna son Allah ya raya mana shi mukai lokacin ki muga me za a
bamu,"

Dariya kowa yayi, tana share hawayen ta ta je kusa da Amman ta take nuna mata, dafa kan ta tayi tana
ta zabga mata addu'a itama, sannan ta sa hannun ta a bayan ta ta dakko mata kwalin waya, ta bata as
her gift, dadi sumar da itane kawai bai ba, dan dama ita ba me ra'ayin riqe waya bace, ta bari sai ta
kammala sakandiren ta, ga shi kuwa Allah ya nufa,

"Abba, Amma, jazakumullahu bi ahsanul khair, Allah ya maku arziqin shiga aljanna madaukakiya, na
gode da dikkan kulawa da soyayyar da kuke bani tin ina qarama har kawo yanzu, kune iyayen da mutum
kullum zai mafarkin samu a duniya da lahira, Allah na gode maka da ka azurtamu da Amman mu da
Abban mu, Allah ka basu yawan rai mai albarka cike da iman,"

Amma cikin share hawayen dake zuba mata ta rungume ta tana bata kisses ko ta ina, lallai ka
tarbiyyantar da yaro ka kuma yawai ta masa addu'a yana ji a koda yaushe, wataran in ya fara kwararo
maka tashi sai dadi da ni'ima ta lullube ka,

"Ni fa lokuta da dama na kan rasa wai qaye auta a gidannan"


"Zeeeeee"

"Whattt?"

A tare suka hade baki suka furta sunan ta, ta dage hannye tana bin su da kallo itama, dariya suka saka,
Abba ya ja ta jikin shi shima,

"Ke ce kk zo qarshe dab haka kece auta, soyayyar mu gare ku kuma ba babba ba yaro, amma ke din ta
daban ce saboda kece shalelen mu,"

Dadi ne ya kama ta,ta kalli Hanee ta daga mata gira, irin kinji nima ana sona dinnan.
Abincin su suka fara ci, cikin natsuwa da cika ladubban cin abinci, bayan sun kammala, Ammar da Zee
sukai wanke2, Hanee ta gyara wajen, sannan ta bi Amma daki, labarin haduwar su da Okashatou ta bata,

"Lallai yau kin karbi best gifts ever, Allah ya kawo shi da alkhairi, ya kare zuwan shi da sharri"

"Ameen Ammana,"

Hira sukai ta yi har magrib tayi, kowa yayi sallah, aka hau karatun qur'ani da wasu littatafa na addini, sai
da suka kammala, sukai isha'i, sannan ta koyawa Zee assignment, daga nan suka tattara komai suka
watsa ruwa sukai addu'a sai bacci, yau Hanee ko tinanin komai batai ba bacci mai nauyi ya dauke ta,
bata farka ba sai lokacin da take yawan tashi dan ibada da dare, wato qarfe hudu, alwala tayi ta zo tai ta
nafila, sai da tayi iya inda zata iya ta hau addu'a, tana kammalawa ta fara karanta qur'ani zuwa asuba,
bayan ta gama ta yi azkar, ta fita hada abin karyawa, kafin kowa ya fito ta kammala, ta saka ma kowa a
inda ya dace, ta shin Ammar taje taga ya fito daure da towel

"Abin kunya ne ace yanzu kina tada ni gaskiya, nai wa kaina fada daga yau da kaina zan dinga tashi,i am a
man💪🏻"
"Weelll gud to knw, ran da baka tashi ba kuma ban shigo tashin ka ba karka ga laifin kowa in kai fashi,"

Da sauri ya bita yana ta dinga zuwa, dariya tayi ta shafa kan shi,

."Gud boy, yanzu maza ka shirya kazo kaci abinci, ba maganar shara yau, zan yi da kaina, ina gida bana
aikin komai, zan yi komai yau,"

"Thanks Aunty Hanee,"

"Ur wlcm"

Ta fita, ta tado 'yar rigima, a bacci aka gama shirin, tana fitowa taji qamshin abinci tini ta ware, abinci
taci, motar su na zuwa suka wuce, shara da goge2 da wanke2 tayi, Amma na zaune tana ta mata hirar
abin dariya, Abban su ma cikin shiri ya fito, addu'a ya mata dan ya ga yau ita tai komai, sannan ya fita,
Amma har qofa ta raka shi, suka dan taba soyayar su ta dawo🙊 .
Hanee na gama komai wanka tayi, ta nemi gadon su ta dale, sai bacci, da niyyar anjima ta tashi tayi
abincin rana kan su dawo skul.

Amma vata tada ta ba,ta barta ta sha baccin ta.

Cikin bacci taji qamshi mai dadi na tashi, tinawa tai zatai girki, a kidime ta hantsilo, Zee ta gani tana yawo
da kwanon abinci a hancin ta, maida kan ta gefe tayi, ta daga hannu kamar zata dake ta, ta sauke a
hankali ta ja kumatun ta,

"Wato na dade ina bacci, har Amma ta gama kenan, yaushe kk dawo,"

"Tin dazu lokacin kina mafarkin wai ko Okashatou? Kina cewa yaushe zai zo,"

Da wani zillo ta cafko zee ta matse mata baki, tana wurga ido ko wani yaji me take fada,
"Zee....zeee da gassskkee kikee? Ddda qarrfi naaanaayii?"

Dik ta rude Allah yasa ba da qarfi take magana ba.

"Wasa nake maki Aunty Hanee, jiya naji maganar ku da Ammane kawai, nima na matsu na gan shi,"

Dukan ta tai da gaske yanzu kam, ta kora ta waje, ta zuro qafarta bakin gado, tana shafa goshin ta, tare
da lumahe kyawawan idanun ta, iska t furzar ta maida gashin ta gefe,ta miqe, Zee anyi yar latsin yarinya,
gaba daya ta sa qirjin ta bugawa, dariya tayi ta girgiza kai ta shiga dan yin alwala.

A bangaren Okashatou kuwa, kome yake tinanin Hanee yake, amma matsala daya son da yake mata
daban ne dana kowa, baya son ya auro ta shi dai ba saiya hali zai ba, ya kawo ta ta wahala kamar sauran,
in kuma yace ware ta zai yana mata komai nan ma ba zai yu ba, dan bama halin shi bane kula sa mace,
ya zai yi ne, ko hakura zai da ita ne? Kaiiii inaaa ba zai iya ba, tinani kawai yake ya kai ya kawo a cikin
dakin nashi, wanda yake a hargitse ba gyara, dakin likita guda, ga kayan alatu ya danqara kuwa amma ba
gyara, bandaki ya shiga,ya gama abinda zai ya fito, tsaf na gan shi cikin shiri, cikin manyan kaya, wanda
sukai masa matuqar kyau, suka fidda kwarjini da kamalar mazantaka a tattare da shi, turarukan daya
fesa sin fi biyar, ya dau makullin motar shi ya fita.

"Ina saka? Da ganin wannan wankan wata mara rabon zaka wajen ta,ta zo itama ka fafe ta, ka dasa mata
kwan wahala ta haifa ka zuqe mata dikkan albarkatun jikin ta ka maida ita busasshen icce, ka maida ta
gidan iyayen ta, wannan karon ba zan yarda ba, dole ne ka hakura da qarin auren nan, yaran sun isa
haka,na gaji da wahala,"

Ko kula ta bai ba ya sa kai ya fice, sai masifa take, a ganin ta in yana ta haihuwa aka tashi rabon gado in
bashi me zasu samu? Abinda zasu samu baida yawa, yaran shi kusan dika maza ne kadan ne matan,
gaskiya dole ta dau mataki, mayafin ta itana ta rufa ta fice....
*Gidan Okashatou akwai cakwakiya kenan*

*🤣🤣 na ga comments din ku makaranta, ina sane naqi yin page biyu, comments din naku ne ba sharhi
tanx ta fi yawa, da wannan👌🏻👍🏻❤ a gaskiy sharhin ku shine takina, kunga ko ko gona ce ana sa mata taki
tafi yado, a min sharhi aga rubutu, a qi sharhi aga dan neman lalaci wallah🤣🙊*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 6:

Gaba daya jin shi yake a gajiye kamr wanda yayi wani aikin, da hamma ya qarasa bude bangaren shi, ya
shige, yau Hafsatu an yi wanka, sai dai ba wani alamar qamshi, wanda laifin megidan ne, tin da nata na
lefe ya qare rabon da ya sai mata turare, amma shi turarukan shi sun fi goma, masu tsadar gaske, tsabar
son kai, bata wari bata qamshi haka ta isa da cup da juice a dan qaramin faranti,kallo daya ya mta ya
kauda kai, ai hakuri zai tayi har ya auri Hnee,sai yanzu yake ganin qazantar Hafsatu, (yau dake yaga mai
kyau ba, ga tsafta kamar ita a haka ya auro ta)

"Meye ne daga dawowa ta ba za a barni ma na kammala me zan ba zaki wani biyo ni? Malama fita,"
"Haba Abban Nour,ka ma tsaya kaji me ya kawoni mana,"

"Fita nace,bana buqatar komai daga wajen ki, ke kar fa ki zaton ban san me kike qullawa ba, nasani,
wannan karon inshaa Allahu qaryar ki zata qare, na rasa jarabar data sa nakasa sake ki, amma bakomi,
ina amfana dake nima ai, tashi ki fita,"

Cikin takaicin kalaman shi, da qin shan abun da ta kawo masa ta fita, wurgi tayi da cup din ya fadi qasa,
dama.na roba ne, yaron ta Nour ne ya je zai lasa, wani ball tai dashi daqafa,

"Dan uban ka kwadayayye ka sha mutuwa za kai, je dakkon ruwa da tsintsiya,kar ka ja min wahala ni,
ban san me zai same ka ba kai, tin da b dan kai nayi ba,"
Yaron na qunquni da rashin kunya yatafi, yakawo me take so,sharewa tai tass, ta sha sauran tarage masa
shine bai bacci ba.

Da safe yaje unguwar su, ya tadda ana maganar hada kudi a gyara pampon da kowa ke samun ruwa, yaje
akai magana yaji kudin, take ya qirga yabasu, nan akai ta murna, ana sa mai albarka, ire2n halayen nn ne
ke sawa mutan unguwar basu tona halayyar shi ga iyayen yaran dake neman tarihin shi, sai dai suyi ta
fadn alkhairin shi shi da uban shi, da sauran yayun shi da ke da arziqi.

Zuwan Okashatou shida wajen Hanee, aka fara batun auren su,nan da nn kuwa Amma ta fara gyara
black beautyn nata.

Gayara ne irin na katsinawa mai kyau da inganci, wanda ba zai cutar da diyar ta ta ba, sai dai ya taimaka
mata a matsayin ta na qaramar yarinya da bata taba aure ba( a kullum ina qara bawa iyaye shawara,
kuskure ne ki dirkawa yarinyar ki maganin mata wai dan za a mata aure, baki san wane miji zata aura ba,
jikin shi da nata yayi daidai? In ya mata girman da sai ta matuqar wahartuwa kin ga kin cutar da ita, za a
ce ai dai ta samu qima da daraja wajen miji, ya jita a matse ko da dadi, to sister ki sani in har ya mata
girma zata iya samun budewar da zata sa nanda nan ta fita ran mijin, ko ya sa mata ciwon yoyon fitsari
musamman in ya girme mata sosai, dan dadin d zai fizge shi ga yawan da ya mata ga shi ya kasa tsaida
kan shi, me kk tunanin zai haifar hakan? Sannan in ya jita da dadi sosai, a hankali dadin na tafiya me kike
tunani, ba irin haka ne mazan ke fara wulaqanta yaran ba, saboda sun fra jin ba yanda suke so ba,
gwanda ki mata gyaran da ba za azo ana shan wahala ta kowanne bangare ba, saffa2, a hankali tana
gidan ta ki koya mata hanyoyin da zata bi dan ganin ta dawo da qimar ta, kin ga kin koya mata abu mai
dore wa, in kuma kk ce ai za a bata wasu ta tafi da shi tana sha, na farko in bai fahimci kayan gyara bane
saki zai iya shiga, yace zaku masa asiri, too much intake of anything is seriousely bad to health, yau da
gobe wallahi magungunan nan har cancer suna sawa, ruwa mai wari a gaban mace, dan haka stay
natural all the time, shine mafitar ki)

Jikin ta yayi laushi kamar audiga, tinda zancen auren ya tashi take markada mata cucumber da carrot, da
lemon tsami daya da lemon zaqi daya sai zuma ta zuba sugar cokali daya da kadan, zuma ma cokali daya
da kadan, (plsssss ga shi na fadi komai yanda ya dace, a halin yanda na sanar daku wayata na ban
matsala ko kin min magana ta pc ba lallai nai responding ba dan ban son shiha cat wayar ta qi komai ko
ta mutu aga kamar na ga chat ban amsa ba) da wannan hadin take sata gaba ta saka soso na
musamman ta siya dan gyara diyar ta, tai ta dirje mata jiki da shi, ko ina na jikin ta, inda ba zai yu ta mata
ba, kamar qasan nono hammata saboda dariya take wai cakulkuli ake mata😀, sai tsakanin cinyoyin
ta,wuyan ta dik sai tayi da kan ta, wani irin haske mai kyau da ban sha'awa take, kowa ya ga farin da tai
ya san ba na mai bane na gyara ne, a kullum kan lokacin wankan ta yayi, Amma zata jiqa lalle sabo mai
kyau da kamu, a ruwa, kan lokacin yayi jawur, ta tsiyaye ruwan, ta kai mata bayi, bayan tayi wanka tass,
da ruwa, sai ta wanke jikin ta da wannan, (in ana gyaran jiki ba a son amfani da sabulu baqi mutum yake
yi, tinda kunga datti sabulu ke fiddawa kuma an fidda mata shi da wannan kayan hadin gyaran, to da
ruwa mai dumi kawai zata na dirza jikin ta in ta gama sai ta saka ruwan lallen ta wanke ko ina) amarya fa
ko haka nan Zee da Ammar sata gaba suke da kallo, Amma kam in tana kallon ta da Abba sai dai kawai
kuji kalmar "Barakallah" na fita a bakunan su, gani suke yanzu su suka hifi wannan halitta.

Yau sati biyu da bawa Okashatou izinin auren Hanee, duk wani bincike Abba da Malam Sabi'u sun
gudanar, sun samu magana biyu wajen mutane, wasu suna fadin shi da mahaifin shi auri sakine, amma
suna da halin kirki, wasu suna gasgata halayen kirkin su, suna qaryata auri sakin, Abba ya rasa wanne zai
dauka, dan haka yau da dare sun kammala cin abinci, Hanee da Ammar sun gyara wajen, suka dawo, hira
suka fara kafin su kwanta,
"Amma su ni fa wannan lamarin na dauren kai, na ma rasa me zan yi tinani akai, zuciyata cike take da
waswasi,"

"Wanne lamari kenan, Abban su?"

"Lamarin auren yarinyar nan, kinji dai bayanan da binciken mu ya samo, bamu samu amsa daya ba, kowa
da nashi magana akan bayin Allahn nan, me kk tinani akai ke?"

"Abban su bana tinanin komai sai alkhairi, abinda na ga yafi shine, mu a yanzu da da kullum addu'ar mu
Allah ya bata miji na gari mumini salihi, dan haka in auren Okashatou shine mafi alkhair Allah ya tabbatar
in ba alkhairi ko ran daurin aure ne Allah ya baddala, ka kwantar da hankalin ka,"

Ajiyar zuciya suka sauke a tare da Hanee, dan ita dai ta miqa wuya akan kome zai faru, in iyayen ta suna
ganin a fasa, zata bi,in suna ganin a yi ne hakan tafi so, fatan ta alkhairi.
Yau ne za a kawo kayan lefe, Hanee ta gudu gidan qanin mahaifin ta tin sassafe bayan ta taya Amma
kammala abinci da tsarabar taron baqin.

Zuwa yamma aka kawo kayan lefe, wanda hajiya qarama da wasu daga dangin Alhaji, guda hudu sai
bangaren mahaifiyar shi guda biyu, sune suka zo a manyan motoci aka kawo lefen, akwatuna guda
bakwai da wata qatuwar jaka, aka kawo, kaya sun yi sai son barka.

Nan Amma da qannen ta uku, sai qanwar Abba,da yayar shi, da goggon Abban su suka karbi kayan lefen,
an kawo masu abinci da abin sha, suka fita suka basu waje, sun taba kadan suka musu sallama zasu tafi,
snaks, da kaji, da drinks, sai tukuicin dubu hamsin, suka ba su, sunji dadi sosai, ganin gidan gidan
mutunci, Hajiya qarama tausayawa rayuwar diyar tasu kawai take,dama mijin su zata aura ba matsala,
amma Okashatou da yake wulaqanta mata daya gama da su, kaiii, ji tai kamar ta sanar da iyayen yarinyar
gaskiyar lamarin, amma ba zatai haka ba, in tayi na ta auren na gab da lahancewa, haka suka tafi, kowa
na farin ciki.

An saka rana kwana goma cif2, Abba ya yi kukan murna Allah ya ara masa rana yaga wannan lokaci, Allah
ya ara masa rana yaga an daura auren diyar shi abin son shi.
Bayan ta dawo gida ne, ita da su Zee da Ammar da Amma suka hau ganin kayan, wasu kayan kunya suke
saka ta, bata ko son a bude su sosai, aikin Baban shi ne,dan dai Allah ya dasawa Alhaji son Hanee tin kan
ya gan ta, a yanda yaji labari ajen dan shi, sai ya fishi murnar samun mace kamar ta, in ta Okashatou ne
bai fi ayi akwati uku ba ko budurwa ko bazawara ba ruwan shi, amma wannan kayan daga wajen Alhaji
suke,shiyayi komai, dan yana fatan yanda ake fadan kyawawan halin zuri'ar su,shima ta mai naso a tashi
zuri'ar.

Bayan sun kammala sun gama komai kowa ya kwanta, wayar ta da ke a vibiration ta hau ruri, Zee da ta fi
kusa da wayar ta dakko zata miqa ma ta lokacin bata qarasa karanta suratul mulk ba, dubawa tayi taga
me kiran, suna ne kamar haka a jiki *Pyar* tinani ta hau yi me kenan?

"Aunty Pyar is calling u, wace ce da daren nan haka?"

Hanee na jin sunan, ta amshe wayar, lokacin ta katse, sai da ta kammala ta bi kiran, bai dauka ba, sai da
ta gana ringing, sannan ya kira again,

"Haba amarya, yanzu meye na qin daga wayata ne? Ko amarcin kk fara tin yanzu?"
Cikin shauqin son da take masa, ta miqe ta shiga toilete ta kulle, Zee ta bi ta da kallo, murmushi tayi,
lallai Aunty Hanee ta kamu da yawa, wato ba zata amsa wayar gaban ta bama.

"Ba haka bane, ban qarasa wasu abubuwan bane shiyasa ban daga ba,"

"Meye baki qarasa ba da daren nan?"

"Duk dare kan na kwanta bayan nayi azkar dina, ko kafin nayi azkar dina na bacci, ina karanta suratul
mulk, sannan nabi da suratul ikhlas,"

Runtse ido yayi sosai, rayuwar shi da ta wannan baiwar Allah kwata2 ba daya bace, akwai banbanci
mabayyani, shirun da yayi ne yasa ta fahimci baya yi shi, nan ta dinga sanar da shi falala da fa'idar yin su
kan bacci, yana sauraron yanda take kwararo masa ilimi, daga kwance, (hhhh daga toilete dai)

"Na gode sosai My lady, yanzu fadamin ya kk ga kayan, akwai abinda kk so ne a qaro,( kamar shi ya siyi
kayan😏)"
Rufe ido tayi kamar yana ganin ta, ita kam kunya take ji, musamman in ta tina kayan bacci dana zaman
gidan da aka sako sai bra din da duk sun mata kadan dan ya gan ta da qarami jiki, wataqila ya sa shi saka
qanana, bai san tana da boyayyan jiki bane, tinda ba bayyana shi take mai ba.

"Hello, babe kinyi shiru, lfy?"

Dariya tayi qasa2 tace,

"Komai yayi, amma me yasa aka saka qananan bra?"

Ta fada tana qunshe vaki, da rintse ido,

"Laifin wa?"
"Babu"

"A'a sai kin fada fa,"

"Laifina,"

"Gud, dan ba yanda ban dake ba ki fadan size na pant da bra kina dinga qunshe fuska, qarshe ma kuka
kika samin, kamae nace cire na auna da kaina,"

Dif ta kashe wayar dan wata bala'in kunya data kama ta, wai ta cire ya auna, shifa bai san kunya ba,
wataran in yana mata magana haka sai taji kamar qasa ta bude ta shiga ta rufe da ita, kira ya sake yi, ta
bangaren shi ko dariya kawai yake,wannan wace irin yarinya ce, sai ya tina auren shi da Zaliha, yarinyar
nan har so take ya je zance, wasu wasanni tin kan ma auren ta fara gwada masa, lokacin da akai auren
kuwa ba dan ya same ta budurwa ba sai yace dama bin maza take, ita ta dinga sarrafa shi kamar itace
mijin, sai da ya shiga area sosai ta fara kuka da danasani, yana kammalawa kuwa ya auna ta gidan su,
yace 'yar iska suka bashi, ya musu bayni b boye2, dan a ganin shi a wajen wasu mazan ta san romance,
koda bata bari an yi babban ba. (Masu rawar kan wai a koya min ya zan ma mijina a daren farko a kula,
wallahi mazan yanzu ankare suke dake,komai tsarkin ki da kame kan ki, mazan yanzu daidai ne ba
lalatattu ba wallahi, kamar yanda matan suka lalace, dan haka karrr yake ganin ki, mistake kadan zaki ya
diga maki ayar tambaya,wani ko da budurcin ki ya gan ki amma bai jiki yanda yake jin labari ba ana
zubda jini ana suma, sai yace ke din ba cike kk ba,bayan duk fada ne, ba kowacce mace ake samun ta
haka ba, ko sumar akai da dama mazan ke fin qarfin matan, sannan suqi saurara masu, dole akai ga
suma, sannan jini akwai masu yi akwai marasa yi, kai dai kawai ka duba kaji, a matse take kai ka fara
shiga ko ba a matse take ba, an riga ka,shikenan sai kayi hukunci da hakan, matsin budurci daban ne da
matsin kayan mata da dinki, if u knw u knw kawai🙊)
"My lady me yasa kk kashen waya?"

"Babu"

"Humm ki gama kunyar ki, sanda zaki cire a gabana na ga komai na zuwa, sanda zaki miqa min da kan ki
n....."

Dif ta kashe wayar qirjin ta na tsananij bugawa, idon ta sun fito waje,kamar gullisuwa, tsoro matsananci
ya shige ta, wayyooo hakan zata faru kuma da gaske? Inaaa bazata iya ba, shifa tinda aka ce an bashi ita
ya sake layin maganganun shi, kullum a cikin nuna mata yanda ya matsu yaji ya kusanta gare ta yake,
abubuwan da zai mata in sunyi aure, wasu su sa taji dadi, wasu su bata tsoro, ga shi nan dai.

Hankalin Hafsatu ya yi mugun tashi, ta qara figewa ta lalace, ko ina taje sai bokan ta yace mata sai anyi
auren nan fa, sai dai ta bari in anyi su ga me za ai, amma akwai rabo me yawa a tsakanin su, kar ta matsa
a yi ba ita......

.
*Okashatou kana ban kunya nima🙊🙈🙈*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 5:

Hanee na ma Amman su kitso, domin gwanace sosai wajen kitso ita ke ma Amma da Zee kitso, ita kuma
Amma ta mata, hira suke kamar wasu qawaye, tana tsokanar Amman wai kitson gaba zata kwashe mata,
in Abbn su ya dawo ba zai gane taba dan kyau, dama ga gashin Allah ya hore, dariya suke, Ammar ya
shigo, dauke da alamun mamaki a fuskar shi,

"Amma kin san me, wani ne ya ce wai na kira masa Aunty Hanee, nace masa bata zance,yace naje na
cemata wai Okashatou ne ta san da zuwan shi, nac......."

Cike dazumudi ta zagayo gaban Ammar,

"Ince dai bai tafi ba saboda shiriritar ka, da baka shigo ka fadan an zo wajena ba kaji me zan ce?"
Nan ma wani mmakin ne ya bayyana a fuskar shi, da gaske Okashatou yake ashe daya ce tana son shi
itama, yaushe ta fara kula samari? A iya sanin shi kowa yazo korar shi take, ba ta sauraren kowa, amma ji
yanda jikin ta ke rawa daga jin sunan shi, anya kuwa???

Amma ta dade da daure kan ta, ta shiga ciki, ita kuwa tana daki ta saka doguwar riga, ta fesa turaruka
masu sanyi, tai rolling kan ta da mayafin rigar, ta saka takalmi baqi mai ratsin ja kamar rigar, powder
kawai ta shafa, sai lipstick da kwalli, wani irin kyau tai, masha Allah, kamar kai ta kallon ta ba gajiyawa,
bayan ta kammala kuma taji nauyin zuwa ta sanar da Amma zata zance wayyoo kunya, diba kan ta tayi,
taga yanda tai matuqar kyau, Ammar na zaune a kujerar tsugunno ta zo zata wuce, baki bude yake kallon
ta, har ta shiga dakin Amma, sallama tayi, Amma na ninke kayan su na wanki,

"Ammm immm Amma zannn...."

"Sai kin dawo dear, Allah ya kare ki, ki kula da kan ki, Allah ya miki albarka, a koda yaushe bawa ya sani
Allah yana kallon dik abinda yake aikatawa ko zuciyar shi ke saqawa, karki jima,"

"Amma na gode"
Ta fita da sauri, ta san ya gaji da jiran ta, tana zuwa ta gan shi a cikin mota yana zaune,ya jingina kan shi
da kujera, idon shi rufe, yana sauraren waqar westlyf, kidan na tashi a hankali, kwankwasa glass tayi, ya
bude idon shi, ya sauke akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya sa ya ji kamar bai jira ta na second daya
bama, wannan sabon yanayi ne da yake ji game da ita, wanda bai taba ji akan kowacce mace ba,bude
mata yayi, ta tsaya daga waje,yaga alama ba fa zata shiga ba, budewa yayi ya fita,ita kuma t masa jagora
zuwa ciki,parlorn Abba ta bude masa ya shiga, a qasa ta zauna dan nesa da shi, shi abun ma dariya ya so
bashi meye haka? Ai an dade da daina irin wannan zancen.

"Barka da zuwa, ina wuni? Ya gida da iyali?"

"Wait what? Ya akai kk san ina da iyali?"

Dan murmushi tayi,

"Da ganin mai iyali daban yake, yanayin kamalar ka ta nuna min hakan, Abbana nacewa, mai iyali ko a
cikin dubban mutane yake mace ko namiji indai ba shashanci yake ba ana gane shi, and na yarda da
hakan,"

"Lallai Abban mu is a wise man,"


."yeh he is,"

"Iyali lfy qalaou, ya mutanen gida?"

"Lfy qalaou,"

Daga nan ta tashi taje ta kawo masa ruwa, da lemo ta aje, har zata koma ta zauna ya dakatar da ita,

"A min taimako mana ki qarasa ladan ki"

Zuba masa tai, ta miqa masa, yana sane ya kai hannun shi jikin nata, abinda bata saba ba, infact bata
taba hada jikin ta da wani ba sai bisa kure, amma wannan intentionally yayi, wani iri taji a jikin ta ba ta
san sanda ta sake cup din zai fadi ba, qirjin ta na ta bugawa da sauri, kan ta a qasa ta rintse ido taji
faduwar cup din,amma taji shiru, ya riqe cup din yana qare mata kallo, zuciyar shi na raya mashi lallai
wannan daban take a cikin mata, anya zai zauna anan kuwa, nan wajen ya dace da namiji irin shi kuwa?
Mai auri saki, kar ya lalatama yarinya rayuwar ta.

"I am so sorry, ba nufina na yi hakan ba, mistake ne, ina fatan ranki bai baci ba,"
A tinanin ta namiji mai kamala kamar Okashatou ba zai qarya ba, zuciyar ta taji tayi sanyi, daga zargin
data fara akan shi.

"Its k ya wuce,"

Daga nan suka fara hira akan rayuwar su, ta sake da shi sosai, kunsan wanda bai taba so ba, sai a
hankali🙄 anan take jin labarin shi da iyalin shi, dana mahaifin shi,amma ya boye mata auri sakin da suke
aikatawa, itama ta sanar da shi nata labarin, suna hira Abba ya dawo, yaga parlorn shi bude, bai bata
lokaci wajen leqawa yaga meke faruwa ba, ganin Hanee na zance sai da yaji wani murmushi ya kwace
masa, ina rules din nata?

"Sorry ashe da mutane ciki,"

Da sauri Okashatou ya taso ya duqa gavan Abba, yana gaida shi, cikin girmamawa Abba ya amsa,
Okashatou ya gabatar da kan shi, Abba ya yaba da ladabin shi sosai, ko kallon shi ya kasa dagawa yayi,
Abba ya masa sallama ya shige ciki,

"Gaskiya Malam sabi'u ya fadan gaskiya, gidan ku gidan mutunci ne,Allah ya tabbatar mana da alkhairi, "
Cikin jin kunya ta amsa a hankali, dan matsawa yayi kusa da ita,jin mutum daf da ita ne yasa ta daga kai,

"Baza kice Ameen ba da qarfi naji, kunya kk ji?"

Yanda nunfashin shi ke sauka a fuskar ta ya saukar mata da sabon yanayi a tare da ita, da sauri ta dan ja
baya, tana murmushi,

"Ai na amsa,"

"Amma a zuci ba"

"Amsawa nai nace Ameen,"

"Yauwa koke fa, bari na zo na wuce,na dade sosai, kar Amma taji shiru, ta zaci har na dauke amaryata
ne"
Cikin siriryar dariya ta kalle shi, ta dan kura masa ido cike da so,kamar kar ya tafi, Okashatou ya hadu
matuqa, yana da kyau na ban mamaki, ga shi a ganin ta mutumin kirki ne, yana miqewa ta miqe itama,
ta bi bayan shi, kamar wadda aka dannawa remote, sai da suka kai qofa kan ya daga labulen, ya ji
alamun tana biye da shi, amma ya tsaya, aiko ta daki bayan shi da kan ta, cikin zaro ido ta daga kai tana
kallon shi,

"Ooouch, kinci bashi dik sanda kk je gidana sai kin min tausa a wajen da kk buge ni,"

Yanayin yanda yake mata magana ba qaramin kashe mata dikkan gabobin jikin ta yayi ba, wayyooo yana
huda mata jiki da soyayyar shi, dama haka ake ji in ana so? Lallai soyayya ba abinda ya fita dadi, hure
mata ido yayi yanda ta kafe shi da ido da murmushin ta mai sashi jiri,

"Don't warry babe, i will be all urs nan da lokaci qanqani, nima ba zan iya jure rashin mace kamar ki a
kusa da ni ba,see u sooner"

Daga labulen yayi ya fice ya barta a tsaye, tana digesting maganganun shi, wani tsalle da yar qara ta sake
ta fada kujera, ta dunqule waje daya, ba abinda ya kai so dadi a rayuwar duniya, tana son iyayen ta da
'yan uwan ta, amma wannan soyayyar daban ce,ko ina take ji na jikin ta na karbar saqon soyayyar, Allah
ya sa Okashatou alkhairin ta ne, addu'a ta fara kamar yanda Amman ta ta koya mata yin addu'a kan
komai da ya taba zuciyar mumini.
"Ya dade da tafiya,in ma a wajen da ya zauna kk zauna zaki iya tashi ko basir yake da shi iyanzu kam kin
gama daukewa,"

"Ammmmaaaarrr,"

Ta fada da qarfi, ta bishi ciki da gudu, suna zagaye tsakar gidan,Amma na fitowa daga kitchen, yaje ya
rungume ta ta baya,

"Aure fa za a maki kwanan nan kk guje2 da qanne,ya kamata a fara saka rigar girma yanzu,"

"Ammaaaa kema tsokana ta zaki ko, "

Cikin shagwaba ta fadi hakan,


"Ni dai zaman daki zani ko na wata daya ne na san Amma zata bar autan ta ko?"

"In Amma ta bari ni kam ba zan bari ba, dan da dikkan alama, anayi da wanan Okashatoun, kula da
yanda aka takure ana ta zuba masa kalaman qauna"

"Abbaaa ni Allah ko ina son ka ban ce miji ba fa har yanzu,"

"Ohhhh gobe za a fada masa kenan🤔😀"

Bubbuga qafar ta ta fara, tana kukan shagwaba, rungume ta Abban ta yayi,yana shafa kan ta,
"My love, ina maki fatan alkhairi a rayuwar ki, Allah ya sa Okashatou alkhairin ki ne, karki damu wasa
kawai nake maki banji komai ba,"

Rungume Abban ta tayi, tana amsawa da Ameen, kiran magrib ne ya raba su mazan sukai masjid matan
sukai alwala sukai sallah, da sauran ibadar da suka saba kullum, yau kam Hanee farin cikin da take ciki
baya faduwa.

Gidan su ya wuce,can yaci abinci, kishiyar mamab shi dake riqon shi wato Hajiya Babba ita ke da girki,
mahaifiyar shi ita rasuwa tai ba rabuwa sukai da Alhaji ba, kusan wannan na daya daga abinda ya sa yake
sake son shi dan a fadar shi macen kirki ce, da tana da rai yasan har yanzu da suna tare.

Bayan ya kammala ne yace,

"Hajiya dan Allah ina sob ganin Alhaj, akwai magana mai mahimmanci, wannan karon daban ce data
da,kar ki ce zaki tsaya min wa'azu hajiya, wannan karon ba za a samu akasin baya ba, i promise,"
"Hummm Allah ya sa,"

Shine abinda ta furta, ta ce ya biyo ta, bangaren Alhaji suka shiga, tare da sallama, yana zaune kan
doguwar kujera, yana kallo, ga kayab marmari gaban shi, (shiyasa baya tsufa, ga shi nan cimar
carbohydrate, da fat vai dame shi ba), kallon su yayi, ya gano akwai magana abakin Okasha,
kwatankwacin wadan da ya saba.

"Ihimm a ina take? Waye mahaifin ta? Kun daidaita ne?"

"Alhaji da dauri haka?"

"To meye sabo? Na san dai akan mace ne wannan zuru2n da kai, inama nima ina da mai min fada akan
aure2n nan wata qila dana daina, anyways canja mata abu ne mai dadi yaro, kar ka damu a ina take😀"
Hajiya Babba wadda taji kamar ta shaqe su gaba daya ta furta,

"Like father like son, Allah ya kyauta, ya kare innocent souls daga halin ku,"

"Ameen" shine abinda Okashatou yace,

"Hajiya, Alhaji, wannan karon shine damuwa ta, yarinyar danake so, diyar mutunc ce sosai,an gina gidan
su akan so da qauna, d kulawa, tarbiyya da mutunta juna, in kaga yanda yaran da iyayen ke mu'mala, sai
kayi matuqar sha'awa, ba safai ake samun hakan a cikin hausawan mu ba,soyayya ce irin ta gidan
rasulullah suke gwadawa junan su, Alhaji tsoro nake karna dakko ta na azabtar da ita, kamar sauran, dik
da dauran wasu abubuwan dana ke masu ba a sona bane, amma sai naga ina aikatawa,"

"Ikon Allah, to shawarata shine ka bata bangaren ka, sai kana bin bangare2, ko ka budr wanda maqon
tsiya ya sa ka rufe, ya zama turakar ka, shikenan kaga ba su hadu ba balle ai tashin hankali, ko ya kk ce
hajiya?"
"Hakane kuma,amma shawarata in kasan zaka cutar da yarinyar mutae kar ka fara abinda ba zaka iya
qarasawa ba,"

"Ki daina wannan maganar dan Allah mu sama albarka kawai,"

"Shikenan, Allah yayi albarkq,"

Haka sukai ta tsara maganar auren da zai qara, har goman dare tukunna ya tafi.

Hafsatu na jin qarar motar shi ta fita da gudu ta zuba maganin da ta karbo a ruwan lemon da ta kashe
kudi ta siya, dan kawai ta bashi ya sha,maganar aure ta tashi..............

*Hummmm Allah ya sa ya sha ma a daga maganar ko ya kuka ce?*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*Allahummar zuqna bi husnil khatima, wala taktumna bi su'il khatima, Allah ka jiqan wadan da suka riga
mu gidan gaskiya, ka sa in tamu tazo muyi cikawa da kyau da imani, Allah ka yafe mana manya da
qananan zunuban mu, ka dawwamar damu akan aikata alkhairi, har qarshen rayuwar mu, Allah ka kawar
damu daga aikata zunubi ya kareemul mannan🤲🏻*
Page 7:

Biki ne aka fara mai cike da qayatarwa, ba a saka qarya ciki ba, amma da ikon Allah sai ya qayatar, yayi
kyau, mutane sun halarci daurin auren UMMA HANEE & OKASHATOU, amarya ta sha kuka har ta fara
zazzabi, sai yanzu take ganin ya Allah ya zatai ta shiga gidan Okasha ta bar Amman ta da sauran 'yan
uwan ta, gaskiya da ana maida hannun agogo baya da ta fasa aure, kuka take tayi an rasa mai lallashin
ta, Amma da Abba ne suka shiga dakin, ganin haka yasa Ammar yabi Abba Zee dama already taba dakin
da ita ake kokawa, ta maqale Hanee sosai wai da ita zata tafi, in ta tafi wa zai dinga mata wanka, ko kula
da ita cikin dare, da sauran su, dakin ita daya zata koma,

"Dear plsss stop crying, ki ga fa yanda kowa ke kallon ki, so kk sai kin girma kin haihu ana tsokanar ki?"
Cikin matsanancin kukan da da bata ma yi shi ba, ta tashi da gudu2n ta ta rungume iyayen ta dake tsaye
a kan ta, suma kasa riqe nasu sukai, Allah ya sani suna matuqar son yarinyar su, sai gashi rana daya zasu
bada ita ma wasu, zata shiga sabuwar rayuwa, Amma ce ta janye ta ta qara ma rungumar da diyar ta ta
ta mata armashi, da kisses, hawaye na zuba idon ta, Abba ne ya goge hawayen shi kamar bai kukan ba,
ya kalli Amma da bata da niyyar sake Hanee,

"Hey woman, sake ta haka mana, ko kin manta kema haka aka kawon ke? Ki barta haka kar ki karya mata
zuciya har ta farajin dana sanin auren tin yanzu, rabuwar gidan iyaye ba rabuwa bace ta har abada,
akwai waya, ana ziyara kuma,zakizo, zamu je, to menene, zo babyn Abba, muje su Goggo na jiran ki, kin
san daga mana qafa tai, dan itama tana jin kewar rabuwa dake da tini ta zo ta tarwatsa mu,"

Dan murmushi Amma tayi, sanin halin goggon shi, da fada, last kiss ta mata a goshi ta sake ta, ta zauna
bakin gado, ta na kallon bango, ji take kamar ta kwace yarinyar ta tace ta fasa aurar da itan, Ammar dake
bakin qofa dik cika bakin da ya dinga mata na ba zai kuka ba in zata tafi, murna ma zai saboda shi zai
zama babba, bayan bata, sai goge hawaye yake yana wani babbata rai, da hawaye ya gangaro zai sa da
dauri ya goge,ga wata siriryar majina da taqi tafiya,sai shan ta yake, Abba zai wuce da ita kenan, ya riqe
ta ta baya, suka saka kuka, Zee kuwa sai da Goggo ta mata fada sosai ta sake ta, suka saka ta a daya daga
cikin motoci bakwai da aka jere a qofar gidan, domin kai amarya, Zee ko ta ware murya tana ta kuka,
Hanee ba wata kwalliya da tai saura a fuskar ta dil ta goge ta, kamar daga sama Amma ta rugo da gudu,
ta bi motar da aka saka Hanee a ciki da kallo, tana share hawaye,

"Kar ki ba fulani kunya mana, diyar fari kk ma kuka haka? Lallai ke ko zama cikin hausawa ya bata ki,"
Wani kallo tabi diyar Goggo mai suna Hauwa suna ce mata kulu,

"Bafulatani ba mutum.bane? Ko bai da zuciya a qirjin shi? Dik wanda ya san Hanee da irin soyayyar da
take ba kowa a gidannan dole ya koka rashin ta, yarinya ce mai biyayya ga iyayen ta da kowa ma, rabuwa
da yaran kirki yana da wahala ba kamar yaran banza bane"

Gum tai da bakin ta, kowa yayi mamakin amsawa Kulu da tai yau, dan dama ta dade da sa ma Amma
karan tsana, saboda ta so matuqa Abba ya aure ta ya qi, dan a cewae shi, mace daya ta ishe shi, ba zai
iya hada son Amman su Hanee da kowa ba, ita kuma kulu taqi aure har yau, Goggo bata isa da ita ba, sai
rashin kunya ta iya, Allah2 Goggo take a samu wanda zai aure ta ta huta.

Ciki ta shige ita da yaran ta, suka zauna a dakin Abban su kamar marayu.

Ko da suka isa gidan nasu, can ma cike yake da mutane, ana jiran a kawo amarya, direct parlorn Alhaji
aka kai ta, yana zaune, ya nade qafa a kujera, yana ganin su ya miqe, ya nuna masu Goggo inda zasu
zauna sannan ya zauna, amanar ta suka damqa, a hannun su Hajiya Babba, Alhaji ya musu alqawarin
zasu kula da ita iyakacin iyawar su, ya debo kudi masu yawa ya basu tukuicin kawo masa surukar shi har
gida, wadda ya kira da a yanzu ta zama diya gare shi.

Basufi minti 8 ba suka fita, motoci suka kaisu gidan Okashatou, wanda shima da mutanen amma ba sosai
ba, Hanee duk ta gaji haka take ji, ga wani zazzabi dake damun ta matuqa, bangaren ta suka shiga,
wanda Abba yayi matuqar qoqari wajen qayata mata shi da kayan alatu, kowa sai son barka yake,haka
suka gama gani, suka tafi, sauran goggo da auntyn ta a bangaren Amma, suka gyara mata wajen, suka
saka tiraren wuta mai qamshin gaske, suka mata sallama zasu tafi, ganin yanda jikin ta ya sake ne ba
kwarin kukan ma, Goggo ta fashe da kukan tausayin yarinyar, sai yanzu taga qanqantar ta, da kyar Aunty
ta lallashe ta suka fice suma, tana nan kwance, kamar matacciya,uwar gidan tazo, da 'yan uwan ta, gaba
dayan su sai yatsina suke, Hanee ta gan su fess 'yan gayu da su, amma wadda aka ce ita uwar gidan nata,
bata da wani fasalin kirki, dik da ta saka kaya sabbi bai hana ta nuna qazantar ta ba.

"Su 'yan uwan naki da basu kawo mana ke ba mu gamu mun zo, dama haka ake a kawo mace gidan
kishiya ba a gabatar da ita ba ga kishiyar? Lallai kun nuna kuma a tafe kuke, mu zuba ni da ku muga me
riba,"

Hane da ke motsawa da kyar ta bude ido ta sake kare ma kishiyar ta ta ido, ta bude baki da kyar zatayi
magana taji ta kasa,shiru tai ta bisu da kallo,

"Ni ban taba jin amarya haka ba ba qawaye ne da aka tafi aka bar ta ita daya? Ohhh ikon Allah,in da
ranka ba abinda ba zaka gani ba,"
Tin da aka fara auren Hanee bata taba damuwar rashin qawa ba sai yanzu, bata da wasu qawayen jiki,
dan qawarta daya a duniya Amman ta,da damar qawayen nata na gaisawa sama2 ne na makaranta, ba
wanda suka shaqu din da zata zo mata aure, infact bata ma da address ko no wata da zata kira tace mata
ana auren ta, ko wajen dinner da akai 'yan uwan ta ne suka mata qawaye, taji ba dadi gaskiya suka fada,
bata da qawaye,

"Ku zo ku fita kan na maku rashin mutunci,marasa mutunci kawai masu abin kunya,yarinya qarama zaku
saka gaba da irin wannan surutun shirmen,"

"Yarinya qarama ko? Hummm maji ma gani ai,in baka gwada wa yarinya qarana munanan halayen ka ba
kan wata shekarar ta zagayo,"

"Ku fita nace ko? Ko ba zai samu bane,"


Cike da rashin kunya suka bar dakin, ganin yanda take ne ya sa shi isa gare ta da sauri, yana taba jikin ta
yayi baya da hanzari,

"Plsss love take it easy on ur self, karki jawa kan ki wani ciwon, aure ba mutuwa bane ba fa, ji yanda jikin
ki yayi zafi sosai,"

Da sauri ya shiga toilete,ya debo ruwa a roba, da qaramin towel,ya aje gaban ta, rigar shi ya cire, dika
biyun, sai vest da wandon kayan, zama yayi a gefeb gadon, ya fara da cire mata mayafin ta, a sannan ya
kula ko idon ta bata iya budewa, nunfashin ta zafi sosai, ya matuqar tausaya mata ba kadan ba,cire mata
komai yayi, daga ita sai pant da bra, ya dinga goge mata jikin ta da towel dinnan, a hankali ta fara bude
idon ta, tana bin dakin da kallo, miqewa yayi ya dakko mata magani da ruwa, ya bata ta sha da kyar,
zama yayi kusa da ita, ya janyo ledar da ya shigo da ita, ya ciro Holandiya milk, mai pineapple, ya tsiyaya
a cup din data sha ruwa ya bata, bata iya sha sosai ba, ta juyar da kan ta, mayarwa yayu ya ajiye, ya
kwanta gefen ta, tana shafa hannun ta na na dama daga sama zuwa qasa, yana bin dikkan jikin ta da
kallo, kallon da ya take matuqar jin shi a jikin ta yana shigar ta, ta rasa dalilin qurama qirjin ta ido da yayi,
a hankali ta gyara kwanciyar ta ta kalli qirjin ta, ganin ta ba riga ya sa ta fara shafa jikin ta, nan ma taji ba
komai sai pant da bra,bata san daga ina qarfi ya zo mata ba, yanda ya ga ta tsorata ya sa ya matsa da
niyyar ya riqe ta ta nutsu, da sauri ta takure jikin ta, tana hawaye,

"Dan Allah kai min rai ka maida min kayana, ko ka ban na saka, banda lfy mutuwa zan"
"Babe relax, ba a mutuwa, da ana mutuwa da tini iyayen mu sun mutu tin a dararen su na farko, plsss ki
daina kiran mutuwa,"

Kaiiii lallai ma Okashatoun nan, bata da lfy fa, da gaske abinda take gane ma idon ta a tattare da shi, zai
ksance? Bai da tausayi ne,she is just 17, going on 18, bata da wani kwari, addu'a ta rintse idon ta tana yi,
ko Allah ya taimaka mata.........

*Haba ba tausayi ne Okashatou, ko ibadane dole sai an...... a dareb farkon😭😭🤧🤧🤧*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 8:

Wasanni ya ja ta ya dinga yi da ita, hawayen ta na ta sauka, ta daina qoqarin kwacewa sakamakon


nasihar da Amma ta mata, gani take data kwace wuta zata shiga, ganin yanda ta daina motsi bata son
ma bude ido ta kalle shi, shine dalilin sake ta da yayi, yayi rif da ciki yana maida nunfashin shi, a hankali
kusan minti goma sannan ya dago, tana kwance yarda ya barta itama, hawayen ta yaqi tsayawa, dora ta
yayi kan cikin shi, yana shafa bayan ta, da sigar lallashi, yana son yayi magana amma ta maqale a wuyan
shi, abun rufa ya ja masu, ganin haka hankalin ta ya kwanta, tai lif, amma tinanin ta batai sallah bama,
sannan batai addu'o'in ta ba, sun jima a haka kusan awa daya, bacci ya dauke shi, idon ta biyu, zazzabin
ta ya sauka, sai zufa take yankawa, daga kai tayi taga yanda yake bacci cikn kwanciyar hankali, ga wani
irin kyau da yayi kamar wanda akai ma dilka na angwanci😃 a hankali ta zame jikin ta ta maida masa pilo,
ta sauka,ta saka rigar ta, Ohhh maganar da yake fada yau ta tabbata, gata jikin shi, ba kaya, wayyooo
dama auren kenan? Lallai akwai shiga uku wajen ta a gaba kenan.

Bayan tayi sallah tayi dikkan abinda ta saba, ta shiga ta watsa ruwa, ta shafe jikin ta da humra mai
qamshi, ta hada da farin musk mai dadi, mai ta shafa mai dadin qamshi, ta saka rigar bacci mai hade da
riga da wando, fita tayi, a hankali, batare da tasan ya dade da farkawa ba, qin motsawa kawai yayi, yana
kallon ta ta qasan gashin idon shi, har sauya kayan ta da sallah d karatun da tai dik akan idom shi, wuyan
shi ba qaramin tsami ya masa ba,tana fita ya miqe yana yarfe hannu yana kiran,

"Washh Allah yau garin leqe zan sa wuyana ya qame, ashsshhhh"

Yana ta matsa wuyan nashi da hannun shi, ina to ta tafi da ta fita? Me zatai a waje? Bayan ta gama kmai,
tazo su kwanta mana.
Tinanin ya bita ne ya fado masa, har ya sauka ya cire wandon shaddar yaji ya fasa, kar ya qara ruda ta,
bari ya bar ta just for today, ya koma ya kwanta, ya san sarai bai sallah ba amma ya kwanta abinshi wai
zai rama da asuba.

(Ko kunsan a yanzu haka akwai samari da magidantan da basu maida sallah abakin komai ba? Shin kina
kula da mijin ki yana sallah ko baya yi? Kina kula da saurayin ki mai ibada ne ko sabanin hakan? Ya qanin
ki ko yayan ki yake? Ke kan ki ya kk? Sallah itace gaba da kowacce ibada, in tai kyau, komai naka na
ayyuka zaka same su da sauqi, zunubin ka Allah zai rangwanta maka, wata qila ma in sallar ka tai kyau ta
karbu ba za a duba sauran ayyukan ka ba a lahira, amma ace kwata2 ma bata dame ka ba, me ke damun
ka? Dan me aka halicce ka? Dan kawai ka sha wahalar zuwa office ko kasuwa ka tara kudi ka ci su? Ko
dan ka yi aikin alkhairi ka gyara lahirar ka Allah ya saka a aljanna? Zabi ya rage namu, ke kuma in kina
ganin aikin gida,ko biki ko suna, ko kallo zasu maki maganin qin yun sallah a lahira bismillah, ba ki da
matemaki a lahira sai Allah, sai aikin ki, in kinyi sakaci zakiga sakaci,in kin kyautata Allah shine mafi kyaun
masu kyautatawa, muna roqon Allah ya kyautata mana)

A takure kuma cikin zullumin me zai je yazo tai bacci, tin kan kiran farko ta shiga toilete ta yi alwala, tai
sallahr nafila kamar yanda ta saba, Okashatou daya ji sanda ta shiga bayin yayi mamakin tashin ta
dawuri, sai da ya jiyo ta tana karatu ya miqe, yayo alwala, yai sallar isha'in da bai ba, kafin ya idar an kira
subh, anan yayi sallar shi, tana zaunen bacci mai dadi ya dauke ta, ganin haka, ya sa shi shiga a hankali,ya
daga ta, ido ta bude ta sauke su kan ta,
"Bacci nake ji plss sauke ni zan iya takawa da kaina,"

"Na san bacci kk ji shiyasa zan kai ki ciki kiyi da kyau, jiya baki samu bacci ba,"

"Dan Allah sauke ni,"

Sauke ta yayi,a ran shi yana ayyana komai abin ki yau sai na sha angwanci na, ba abinda zai min katanga.

Tana shiga ta haye gadon, ta rufe ko ina a jikin ta, har ta fara bacci Okashatou ya shige mata cikin bargo,
daga qananan wasanni ya fara da ita, sai da yaga ta kamu sosai, ta daina ture shi da kiran ya kyale ta, ya
fara qoqarin cimma burin shi.....
Ango da safe ya angwance, bai ko kula da kukan da take ba,kuka ne na abu biyu, kunyar shi da kuma
zafin da take ji, ya zatai ta sake hada ido da shi yanzu? Wayoooo kunyar ta,🙈.

Ango kuwa ko a jikin shi, sai ma wani manne mata da yake,duk a aure2n shi bai taba haduwa da mace
mai boyayyar ni'ima ba, yana qara kusantar ta yana jin ni'imar ta na qaruwa, har ya cimma burin shi,
Hanee ta daban ce a zuciyar shi da kuma gangar jikin shi, dan kuwa ya bata matsayin da bai bawa
kowacce mace ba, Okashatou bai taba kusantar mace a farkon lokaci ba kuma ya rungume ta ya ci gaba
da shinshinar ta sai Hanee, har wani lallashin ta yake, ita kuma ba abinda take so irin ya bata waje,
amma yaqi ya manne ta kamar tare aka haife su.

Sai da suka kusan rabin awa a haka sannan ya miqe,ya shige bayi ya tsarkake jikin shi ya dawo, hayewa
gado yayi, ya hau bacci, bayan ya shafa kan ta, wannan shine iya kyautatawar da yayi qoqarin bata a
matsayin ta na wadda ya kawar da budurci, kuma wadda yake so fiye da sauran matan da ya taba yi, (to
sauran kenan ba su samu wannan qaramar kulawar bama☹ ) .

Hanee kusan a dadin ta ma da bai wani maqale mata ba, a nata tana son kasancewa ita daya.
Tana kuka tana washhh da komi ta gasa jikin ta da ruwa mai dumi, wanda ta sawa ma'ul kal farin, kadan
ta zuba, bayan ta kammala, ta samu audiga ta saka musk fari mai dadin qamshi ta rintse ido ta saka,
wajen na mata zafi kadan2 amma hakan zai sa ta dan samu dama2, ga qamshi da zai zama
dawwamamme a wajen, da rigar da wandon data shiga da su ta fito, ta je wajen kayan ta ta duba wasu
atampa, riga da zani, masu kyau ta saka, Okahsatou na ta bacci abin shi, har wani murmushi taga yana yi
a baccin, abinda ta saba in ranta ya baci tayi, ta dan karkata ido ta turo masa baki, ta juya mirrow,
kwalliya ta tsara mara yawa wadda ta sata matuqar kyau, (mata ku sani cikawa fuska ado fa a koda
yaushe wallahi ba shine gayu ba, da damar lokuta wasu mazan suna son su ga kinyi kwalliya amma ba
wadda zata sa suna son maybe maki kiss m bu yagagara, kin maka wancan kin buga wannan kin mann
wacan, ya rasa ina ne idon inane bakin,habaa, wata kwalliyar ma da kk a gida wallahi ta biki ce, wata ta
dare ce zakiyi da rana, wata ta rana ce ki maka da dare, amma da damar lokuta anfi son ki duba ma ya kk
in kikai kwalliya, ke dakan ki kigani kina kyau ko muni kk yi? Dan wasu sarai sun san ba su yin kyau sai
sunyi wai kar ayi abun zamani ba su, waya saki? Ko ibada ne? Kiyi wadda take maki kyau shikenan, ke da
mijin ki da yaran ki ku zama cikin aminci, ba sai kin firgita kowa ba, mata a kula da kai, make up mara
nauyi yafi dacewa da kowacce mace, amma a kwai lokutan da zaki make up sosai, kamar in ana taro, ko
kuma kk san kayan da zaki saka suna buqatar ki caba ado abinki, ki zama dai mai kula plss sister kqr garin
a faranta masa kina bashi tsoro kuma kiji haushi kice in kinyi baya yabawa, qarya kk son yayi?)

Qamshin turarukan da ta fesa ne, ya sa ya fara bude ido a hankali, ta fesa wanda suke da kamar mai mai
haka a jikin fatar ta, masu ruwa zallah da kuma sanyi wanda in ta sa a fatar ta zasuyi zafi ta shafa a kayan
ta, sai da ta kammala ta juyo, Okashatou dagowa yayi, daga gadon, da guiwowin hannayen shi, bakin shi
bude, kamar bai mata komai ba haka ta ke kallon shi, cike da so da qaunar shi, ya tashi a bacci amma
kamar wanda ya sha ado, saboda kyau, zama ta ci gaba da yi a kujerar, shi kuma ya yunqura zai tashi,
tsabar tsokana sai cewa yayi.

"Washhhhh Allahhhh ka cece ni Ammana ku taimaka min na tashi,"


Tana jin haka ta san da ita yake, kunya kamar zata nitse cikin qasa, kawai sai ta fara hawaye, dan bata da
mafita, yana ganin haka ya taso cikin sauri, ya rungume ta yana lallashin ta,

"A gaskiya Hanee ki qara godewa Allah da ya baki iyaye na gari sun baki tarbiyya kin riqe min budurcin ki
kin kawon shi lfy ba tangarda, Allah ya miki albarka, ina son ki mata ta,"

Kwantawa ta qarayi sosai a jikin shi wani dadi na shigar ta, zuciyar ta fesss take jin ta, ta so tai gajen
hakuri, dan Amma tace in miji ya sami mace lfy, yana sa mata albarka, wasu har kyauta suke ba macen,
amma ita dazu bacci ya juya ya shaqa abin shi, ashe zai yaba mata, qara rungume shi tayi, a hankali ya
miqe da ita a jikin shi, taga yayi hanyar toilete, sai ta daga kan ta suna fusjantar juna,
"Ina zamu? Nayi wanka fa,"

"Wai da tayani zaki nayi nima,"

Ai Hanee bata san tana da wannan qarfin ba sai ranar, wani zillo tayi ta kwace ta kwasa da gudu waje, ta
damqe knob din qofar wai kar y bude, sai maida numfashi take,idon ta a waje, kamar gullisuwa, wai shi
meyasa baida kunya ne? Da wanne idon zata gan shi ba kay? Da sauri ta rintse idon ta tana kiran
"A'uzubillah, kamar wadda tai sabo, dariya yayi tayi lokacin daya ga inuwar ta jikin qofa yaji kuma baya
sake hannun qofar ba,

"Zaki daina ne watarana,"

Ya shige yayi wankan shi.........


*Sai anyi googling a gano yaushe zai daina hakan😃😃😃*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH

Page 9:
A kwana a tashi Hanee ta saba da dikkan abubuwan da Okashatou yake koyar da ita, tin tana jin kunya
har ta zama A a fannin komai, Okashatou na matuqar jin dadin hakan.

A cikin wata biyu da auren su sau biyu Amma ta bar Zee taje, Ammar ke kai ta, yini suke su koma, dan
Amma bata son su cika zuwa gidan Yayar tasu, tafi son su a kusa da ita, kuma bata son su yawaita zuwa
gidan kar a ce kwadayin abin duniya ke kai su, tinda kowa ya san ahalin su suna da dukiya, (sai rowa
amma ta bangare Okasha) a ganin ta gidan kishiya ba gidan da za a dinga kai kawo bane gudun gori.

Hanee kullum damuwar ta da kukan ta akan tana missing din su ne.

Wata ranar laraba da yamma suna cin abinci, Hanee tace,

"Pyar dan Allah ina son zuwa naga Ammana, tinda akai auren nan bata tako qafarta gidannan ba, ina
matsanancin son ganin ta,"
A lokaci daya Ammar ya sauya, ya kalle ta cikin rashin kulawa,

"Ba yanzu ba,"

"Me yasa Plsss ka taimaka min, Abbana ma kullum mukai waya sai naji kamar na je na gan shi na dawo,"

"Eh ba mai hana ki jin hakan, amma gaskiya ba zaki yanzu ba,lokaci na nan zuwa da zaki ganin iyayen ki,
amma har yanzu ban gama amarci ba,"

Bata saba ja'in ja ba sai tayi shiru, amma zuciyar ta ba dadi, sai taji cin abincin ya fita a zuciyar ta sam, ta
zare hannun ta ta aje spoon ta shiga daki, zama tayi a bakin gado, wasu hawaye masu zafi na bin kuncin
ta, she really miss her Amma, tana son ganin ta matuqa, bata taba zuwa koda hutu wani wajen ba, haka
ta taso ko da yaushe makaranta ke raba ta da Amman ta, Abba kuwa dake yana zuwa aiki shi shaquwar
su ba sosai kamar na Amma ba, yanzu gashi tayi watanni har biyu, tana na uku ya hana ta zuwa, ko da
daddaren na yana da mota ya dan je sugan su amma yaqi, ba komai, ta share hawayen ta, ta sha
majinar kuka, ta miqewar nan da zatai ta gan shi tsaye jikin mirrow yana kallon ta, suna hada ido, a zaton
ta zai dan lallashe ta, taga ya shige toilete.
Bude baki tai ta bishi da kallo, daga baya ta rufe ta girgiza kan ta, lallai namijin kenan,da ake cewa ai
hakuri ashe ita anan kusa zata fara hakurin nata, yanda yake nuna mata a da in suna waya kamar har su
mutu ba zai bar hawaye ya sauka.a idon ta ba, amma dubi tana kuka ya tsaya ya gama.ganin saukar
hawayen ta ya shige abin shi.

Bayan ya fito ya ce mata,

"Na wuce hospital sai can dare zan dawo,"

"Allah ya bada sa'a ya dawo da kai lfy, Allah ya taimake ka kamar yanda kk taimakawa marasa lfy,"

Bataji sanda ya amsa ta ba ya fice, me kenan? Tambayar da taiwa kan ta kenan, tinawa da maganar
Amman ta tai, akan in taga namiji yana irin haka, wataqila laifi macen tayi, to ita me ta masa? Daga
tambayar zata gidan su kuma sai abu ya koma haka? Kenan ba zata taba tambayar zata ga iyayen ta ba?
Waya ta dauka ta kira Amman ta, tana dagaqa suka gaisa,
"Hanee love ma'asabaki ?

Kuka ne taji ya kusan kwace mata, ta danne,

"Amma ba komai,kawai ina son ganin ki ne,Amma me yasa ba zaki zo ba,bafa ki zo kinga dakina ba, ko
baki kewa ta bane?"

"Ba haka bane Hanee, yawan zuwana ba abu bane mai kyau, and daga kawo ki bai kamata na dinga
zirga2 a gidan ki ba,amma kamar kina cikin damuwa meke damun ki?"

Kuka ta sake

"Amma ina son ganin ku ne,"

Dariya ta dan yi wadda zata bata kwarin guiwa, amma itama tana kewar gudan jinin nata.
"Habaaa Hanee, me ye hakan, ke yarinyar goye ce? Ina ce kina son mijin ki yana son ki? Kuma lfy laou
kuke zaune da shi? Meye na daga hankali har da kuka, bana son haka ko da wasa kar ki ma mijin ki
maganar zuwa nan ganin mu, in kuwa kin masa ya hana ki bi umarnin shi kiyi hakuri, sannan ki nashi
hakuri akan bazaki sake tada maganar ba har sai sanda ya ga dama ya kawo ki kinji my love,"

Daga kai take tayi tana share hawayen da ya qi tsayawa,

"To Amma na gode, amma dan Allah in kin samu dama ki zo kema kiga dakina mana,"

"To inshaa Allahu,"

Hira suka ci gaba Amma nata bata labarin qannen ta da rikicin su, tai ta dariya, daga baya sukai sallama.
(Shin ko kun san kuwa akwai iyayen da in mazan yaran su suka hana su zuwa gida sa yaran suke su ma
mazan rashin kunya kuma su taho ko da izini ko babu? Musamman in iyayen na ganin suna da kudi
taimakon mijin sukai sika nashi diyar su, to fa sai yayi hakuri, iyaye plsss musamman mata wannan ba
halin kirki bane, hakan zai sa yarinya ta raina mijin,ta daina bin umarnin shi, ya zama sai abida ta ga
dama.zata na yi a gidan)

Kafin Okashatou ya dawo ta sake wani abincin mara nauyi wanda kusan dik rabi vegitable ne, ta masa
drinks na orange da lime sai ginger, da flavor na pineapple, ta aje masa, tai wanka ta shafe jikin ta da
turaruka, ta kwanta, bayan ta gama dikkan abubuwan da take kan bacci.

Wajen qarfe daya da kwata ya shigo, lokacin tayi nisa da bacci, kallon ta yayi ta matuqar tafiya da shi,
amma yana tinanin tada ta, dan haka bai tashe ta amma ya dinga taba qofa da garfi ya shiga ya fita, har
sai da ta farka, cikin gigin bacci ta kalle shi tsaye yana qare mata kallo, ta fahimci me yake buqata, dan
tin da ya dawo dakin ta ya manne mata, a fadar shi wai kwana biyu jin ta yake kamar wata sabuwa a
leda.

Miqewa tayi ta mai sannu da zuwa ta shiga bandaki, ta wanke bakin ta, ta fito, ta same shi ya na cin
abinci,zuba masa drinks din tayi,a glass cup, ta aje masa, tana bashi hakuri akan maganar dazu, kamar
yanda Amman ta ta sanar da ita.
"Ya wuce Babe, ni kawai na fi son ki yarda dani, akwai lokacin da zaki je gidan ne, amma.ba yanzu ba,
kinji?"

Daga masa kai tai tana qoqarin4 danne damuwar ta.

Yana gamawa tare suka kwashe komai suka gyara suna ta soyayyar su, kamar ba abinda ya faru.

Washe gari ta gama.komai bayan ya fita, tace bari ta leqa bangaren Hafsatu su gaisa, an dade basu hadu
ba, zaman hakan ba kyau, ta yafa mayafi akan riga da skirt din data saka, ta rufe bangaren ta ta shiga na
Hafsat, tana tsakiyar yara suna ta kallo, gidan kaca2, kamar ba mai rai a gidan,tana ganin ta ta miqe tana
tattare zani, ta daure kan ta,daya sha kitso qanana, dake ba laifi itama akwai gashi, ya zuba har wuyan
ta,zuwa kafadar ta, cikin sake fuska na 'yan bariki

"Amarya kenan sannu da zuwa, ai ni na aje makamai na ma, tinda na san kema nan da kin sauke abinda
ke cikin kine zaki shiga sahun mu,na fada maki gaskiya duk wani yunquri nayi akan auren ku kar ya
tabbata, amma na kasa samun nasara, amma na barki da halin Baban su zaki gudu da qafafun ki kema da
kin fara haihuwa, kinga wadannan yaran dikkan su na matan da ya saka ne, nawa na tura su makara
ta,sauran kuwa ko a jikin shi, bai damu da makarantar su ba, innice ke wannan cikin na jikin ki da gani
qarami ne, cire shi zan na rufawa kaina asiri har lokacin sakin nawa yayi ya sallamen na tafi ban da
tinanin na bar kowa a baya,"

Tinda ta fara maganganun ta cikin ta ya duri ruwa ba kadan ta, tashin hankali ya shige ta, ko wannan
dalilin ne yasa yace wai tajira lokacin zuwan ta gida na nan, ba yanzu ba?

Dai daita nutsuwar ta tayi, ta kalle ta tace,

"Haba Maman Nour daga shigowa ta, ko wajen zama baki ban ba fa, ko gaisawa bamuyi ba ki taren da
zancen da na riga na san shi, i am ready for anything tinda ni naji na gani ina son shi zan aure shi, ija
fatan kuna lfy? In yaran sun dawo ina gaida su, ga wannan a ravawa yaran,"

Cike da bacin rai ta bar bangaren na kishiyr ta, ta koma wajen ta tana ta tinani, tana matuqar jin tsoron
abinda kishiyar ta ta furta, ciki? Ciki fa? Yaushe take da ciki bata sani ba, kuma ma meyasa bai fada mata
ba,ai shi likita ce,a qalla da zai gane hakan, wayyoooo in ciki ne ta fara haihuwa ya sake ta fa😭😭.
Kuka take tayi, har aka kira sallah ta yi, ta dora girki,bayan ta gama ta sake wanka, tana wanka tana shafa
cikin, wai a qannan marar da ta hade da baya je take da ciki, kaiii wasa Hafsat ke mata. Bari ya dawo ya
amsa mata tambayar ta.

Tinanij kar kuma.bai sani ba ta fada ya sake ta,kuka ne ya kwace mata rasa inda zata saka ranta tayi,anya
bai sani ba ma? Ko yana sane yayi shiru, ko hakan na nufin ita yana son zuri'a da ita kenan? Wayyooo
kan ta take ji kamar zai fashe, tinani ya mata yawa.

Sai dare Okashatou ya dawo,yanayin yanda ya gan ta ya sa ya san akwai damuwa, tabbas so take ta boye
masa, amma in ya tina kafewar ta akan tana son zuwa gida, sai ya basar bai son ya tambaye ta ta fada
masa zancen zuwa gida, kawai ga ci gaba da cin abincin shi, ranar haka suka kwana suki2 daga wajen ta,
shiko ya dirje ta kamar ba zai bar ta ba, cikin farin ciki ya kwana.

"Pyar pls ina son zuwa asibiti, bana jin dadi,"


"Na san meke damun ki ba zaki ko ina ba,zan baki magani da kai na,"

"So ka sani? Shine baka fadan ba? A gaskiya ni ba zan dau ciki da wuri ba na haihu ka sake ni,"

Zaro ido yayi waje

"Waya fada maki hakan?"

"Ba kowa"

"Qarya kk, wato hanaki fitan danake saboda gulmar mutane sai da kk fara fita k? Uban waye ya fada
maki nace,"
Cikin wata gigitacciyar qara da tsawa ya mata maganar,zubewa tai a wajen tana kuka,dan ko zai kashe ta
ba zata ce ga wanda ya sanar da ita ba, ta zama silar da zai saki Hafsatu a hada ta da yara ba, in dai
hakan ne halin shi, gajiya yayi da tambayar ta ya miqe ya yi dayan dakin ya kwanta, ranshi ba dadi, a
ranshi yana ganin ko me zai faru ba zai iya rabuwa da Hanee ba, mace ce ta daban, kuma yana son
abinda zata haifa, ta bangaren ta kuwa tsoron shi ne ya shige ta sosai, alamun shi sun nuna mata abinda
aka fada akan shi, dan haka kwana itama tai tana kwancewa da saqawa..

*Hummm Allah ya kaimu gobe muji me ta qulla ta kwance, amin hakuri yau banji dadi bane, shiyasa ban
posting ba da wuri*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 10:

Yau Okashatou zai koma wajen Hafsatu, wadda ta sa yara sikai shara sama2, a ganin ta tinda wajen
Hanee yake kwana itama zai je wajen ta, taji shiru bai shiga ba, dan ko taji shigowar shi,da dare bayan
ta gama abinci, shinkafa da mai da yaji, ta yanka timari akai, ta saka a plate ta rufe da wani, sai cokali a
sama, da ruwa a jug din roba, da cup din shi, tayi wankan ta tsaf, sai dai matsala ba wani qamshi kwata2,
(wanda laifin oga ne, ko da dai akwai laifin ta ta wani bangaren wanda zan bayani a gaba inshaa Allahu).

Tana zuwa taji qofar shi a rufe, ta aje ta kwankwasa, sai da ya gama wulaqancin shi, sannan ya tashi yaje
ya bude, daga shi sai gajeren wando, yana tashin qamshi da alama wanka ma yayi, ya gama cin abincin
da ya shigo da shi, ya kwanta, wani kallon so da qauna take bin shi da shi, ta shige,rai a bace ya ke kallon
ta,

"Wai ban hana ki shigo min ba in kin san baki wanka ba? Dan Allah ji yanda qajen nan ke tashi shigowar
ki, wama ya sani ko d kayan kikai girkin,"

"Wannan wane irin wulaqanci ne Abban Nour, wai meyasa a rayuwar ka in baka wulaqanta ni ba baka jin
dadi ne, laifi na ne da bana qamshin yanda kk so??? Inace haqqin miji ne ya saiwa matar shi dikkan
abubuwan da zatai masa kwalliya dan ya ji ko ya gani ko ya taba yaji dadi? Wanne kake man tin bayan na
lefena da ya qare? Yau shekara nawa, ga Nour na Ss 1 yanzu, kana adalci kenan? Ko kayan fadan kishiya
baka min ba, dazunnan matar ka tazo tana min gorin ina zaune da qazanta shine kaima yanzu zaka min
naka gorin ko, na gode ba laifin ka bane,laifin son danake maka ne,"

"Wait a minute, what do u mean mata ta ta maki gorin qazanta? Kina nufin har wajen ki taje ta fada
maki gana akan hakan ko kuma ke kika je?"
"Itq ta shiga har bangarena tana yatsina tana toshe hanci, baka ji irin wulaqanci da baqaqen maganganu
da ta min ba,ka san ni da masifa, na so na mata kaca2, na kula kana iya sakina dan na kula ta gama da
kai, sai abinda take so kake yi, shine dalilin dayasa na fada mata in ta haihu kayan kwalliyan ta ya qare na
gani in itama bata koma kamar ni ba,"

"Ohhhhh wato Hanee sumumu kasam ce macijin sari ka noqe ko? Ina ganin ta simi2 kamar ba za a sa
mata yatsa ta ciza ba ashe ta iya wulaqanta wani, kiyi hakuri, laifina ne, zata gane ba mai taban ke ya
kwana lfy, ke din kina da matsayin uwar gida wanda komai son da ake ma amarya ba zata kamo shi ba,
banni da ita,"

Wani dadi ne ya kama ta, kamar tai ihu dan murna, amma ta shanye gudun tonon asirin qaryar da ta
shimfida, matsawa tai kusa da shi, tana shafa shi, bai ture ta ba amma dai baya wani so, dan tinanin ma
kusantar ta yake yanda ya saba da Hanee kwana biyun nan, ya san irin dadin dayake diba da kuma
qamshi da tsaftar ta,

"Abban Nour ka ci abincin mana ko kadan ne"


"Me zan ci? Wannann abun ya batan ciki? Ah haba kin ga aje ko ki kaiwa yara kar ya baci a banza su
cinye, danni a qoshe nake,"

Da sauri ta dauka ta fice,kar ya kira yaro ya bashi, dan kadan da aikin shi,maganin da ta zuba na mallaka
na ciki, ta kifa a dustbin, ta dauraye plate din tana ta masifa, in ta matsa yaci yana da saurin zargi zai iya
gano ta,kaii ita ta rasa ya zatai da wannan mutum mai tsaurin ra'ayi da wuyar kaiwa qasa.

Komawa tai suka kwanta, dik yanda ta so ya kusance ta kasawa yayi, saboda kome ya fara mata sai yaji
ta banbanta da Hanee, Hanee daya taba ta take responding, kome ya mata tana nuna jin dadin ta, tana
taimaka masa, amma ita wannan sai ta mai wani gingirim kuma gashi dai tana so dan in ta shine a kwan
ba ai ba, amma ta maqale mai jiki kuma taqi ta taimaka masa, kaiii me mace irin Hafsatu yana tare da
wahala, tsaki yaja da qarfi, ya hau mata masifa,

"Wai Hafsatu m yasa baki iya komai bane, dalla malama in kina so ki yi wani abu akai, in baki so ki barni
nai baccina,"

"Me kk so nayi ne? Da ba haka muka saba ba,"


"Tin yaushe nake koya maki baki iya ba, amma Hanee daga zuwan ta ta iya komai, ke kina nan kamar
wata sokuwa,"

"Kaga ba sai ka wulaqanta ni ba akan waccan da burin ta ta haihu ka mutu taci gadon ka ba, dan ba
abinda bamuyi magana ba jiya akai,ta fada dukiyar kuce ta kawo tq, banga dalilin da zaisa ina tare da kai
ina kyautata mata ba shekara da shekaru ka na munanamin akan wata ba,"

Tana gama fada ta kalle shi taga maganganun ta sun dake shi, kawai sai ta fara kukan kirsa, tana maida
kayan ta, tana son sauka, janyo ta yai suna fuskantar juna,

"Da gaske kike da kan ta tai wannan maganganun?"

"Qarya zan maka,"


"Amma kuwa ta rainan wayo, muje a haka nima zan nuna mata maciji ne"

A haka sika fada rayuwar auren da shi bai jin dadi, ita kadai ke jin dadin abun.

*Pls ayi hakuri da wannan, banjin dadi sosai, Masu min addu'a ta pc na gode sosai, masu min addu'a ta
groups na gode koda ban amsa a can ba na gani na gode matuqa, Allah ya ba dikkan musulmi lfy, Much
love*❤

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*Rano Country🤣this page is for u 'yar qauye,Allah ya sauke ki lfy, ya qaro masu albarka, Allah ya sa ki
waye da wuri, kafin nan kan ki haihu, dan kar yarana su koyi qauyancin 'Yan Rano🙊🤣💃🏻 MUCH LOVE
DEAR❤*

Page 11:
A kwanakin nan, Okashatou saboda baya jin dadin Hafsatu kamar Hanee Allah2 yake ya koma wajen
Hanee, a kullum sai ta mai gulmar Hanee,tin in ta fada masa ya dauka daga baya ya watsar har ya fara
riqewa, randa zai bar wajen taje ya koma wajen Hanee, ta masa sallama zata tafi, ta kwashe tarkacen ta
da ta kai bangaren nashi,

"Yanzu haka zaki tafi bazaki sharen wajen ba, kinga matsalar ki, kizo ki kwashi qamshi da AC ki qara gaba,
ba zaki gyaran waje na ba Mtss"
"Yanzu dik aikin danake a gidannan baka gani, haba Abban Nour ya kk so na kasa kaina ne? Ko ka manta
ni ke kula da dikkan yaran na ne? Aiki ya min yawa, yara nawa nake kula dasu ne, ga nawa ga wadannan
yaran, wataran wajen kwanciya ma ni nake zuwa na masu shimfida saboda wahala da yake yi, amma dik
abinda nake baka gani, sai kai ta yabon matan ka a gaban idona, bayan kowaccen su in zata tafi sai ta
barmin tsaraba daya ko biyu, habaa, ka dinga tausaya min mana,"

Sai ta saka kuka sosai, har tana dafe gini, Okashatou tausayin tane da gaske ya kama shi, tabbas ya san
yara ne ba iyaka take kula da su, ga su yawancin su kan su daya, qanana ne, wasu ma tsarki ake masu,
gasunan dai kaca2,

"Yanda za ai ki ware biyar ki maidawa Hanee, yau innaje zan mata bayani, amma ki masu wanki fess, dan
gaskiya bata son qazanta, ki gyara su, kuma wannan 'yan dauke2n da suke ki masu gargadi, dan innaji
labarin sun mata sata Allah sai na ci uban yaro, kema sai kin fuskanci fushina,"

"To meye nawa a ciki,"


"Fita, ina da abun yi,ki kiyaye me na fd maki,"

Fita tai tana ta bata rai, ko a jikin shi,bai san lallashin mace ba, in zata dige tana fushi ta dade batai ba.

Waya ya dakko ya kira Hanee, wadda ta gama gyara wajen ta dan tarbon megidan nata, matsala daya
kayan sarrafa abinci ya qare, sai shinkafa da su taliya, su cuscus, da sauran su, dan in tai girki ita tana
zubawa a babbar kula, ta miqawa yara, Hafsatu kamar wadda bata cin abinci in Hanee ta kai abinci,
wataran boyewa take sai ta hada yaran da nata, suyi ta fushi sina qunquni, ko in ta aje ta fita a bude a
diba tazo tai ta zage2 tana fada, tana a nemo wanda yaci kowa yace ba shi bane, haka zata hakura tana
zagin su,har da tsine2.

Tana tsaye ta gama daura zanin ta kenan, taji wayar ta na ringing, ta daga,
"Hello, Hanee plss kizo waje na ina son magana da ke,"

"K Pyar gani nan zuwa,"

Da sauri ta yafa mayafi ta qara fesa turare ta fita.

Tana isa ta kwankwasa qofar, cikin shiri ya bude mata,

"Bismillah shigo, amarya baki laifi ko kin kashe dan masu gida,"

"Rufan asiri ka aje maganar kisa a gefe, barka da yamma"


Abinda ke burge shi da ita kenan, tana da ladabi, amma abu daya ya rage mata qima ya kula dik na
neman wajen zama.a wajen shi ne, tinda ga shi yanda ta raina Hafsatu, murmushi yayi,

"To na ji, zauna kiji wani hukunci dana yanke, Allah yasa ranki ba zai baci ba,"

"Ina sauraron ka mijina, nidin mallakin ka ce kome kk so zaka iya zartarwa, nawa bin umarnin ka indai bai
sanawa Allah ba,"

Jita kamae gaske.

"Yauwa dama.naga yara sun ma Hafsatu yawa sun kai goma sha ga nata ga na wasu, shine nace ko za a
dan rago maki ko biyar ne, tinda kema kina fama.da kan ki,"
Sai da gaban ta ya fadi, dan sanin irin rashin tarbiyyar yaran, da rashin zuwan su makaranta,amma sai ta
dake,kamar ba wani abu,

"Masha Allah nima zan zama mama ashe, naji dadi sosai, na gode maka kuma, Allah ya raya mana su da
iman,"

Bai zata ba, dan ya daura damarar yi mata duk wani rashin mutunci in taqi, sai gashi ta amince cikin
sauqi, gaskiya ta burge shi.

"Yauwa tawa ni kadai,Allah ya miki albarka, bari na fita sai na dawo,"


"To a dawo lfy,ammmm nace kayan miya da nama sun qare ko za a bayar na ba ma yara su siya,"

Tabbb lallai wannan har wani zancen nama take,she never knw anything ooo,

"Karki damu ayi amfani da abinda ya samu kawai, bari na dawo a ga yanda za ai,"

Bata kawo komai ba ta mai addu'a yanda ta saba, ta raka shi har jikin mota,ya tafi, tana daga masa
hannu.

Bayan ya fita tana juyowa suka hada ido da Hafsatu dake tsaye , tana kallon ta, shewa tai ta yi guda.
"Zamuji kuma mu gani in ita tusa tana hura wuta ba, ahhh zamuji zamu gani, in banda abinki wayake
maqalewa namiji haka? Musamman irin miji kamar Okashatou,da idon ki zaki zo kina kuka, ina nan,
nawa na gani? Harda masu maqale shi ana mai made da wani iyayi, amma haka ya yakice su ya saki, ga
yara nan na gama shiryawa guda shida sai ki kada naki garken,"

"Hummmm Hafsatu kenan, Allah ya kyauta, ammm amma naji kamar yara biyar yace ba shida ba ko?"

"Eh biyar yace, amma in kikai la'akari da wanda ke wajena yau ko takwas na baki ai kin diba, Habibu
kuna ina kufito,"

Ganin su tayi da ledojin kayan su, kowanne wai a haka anyi wanka,sai a hankali, duk kusan kan su daya,
ba zasu fi 6 zuwa bakwai ba, babban ne Habibu shine mai 8, tana ganin shi cikin su taji cikin ta ya kada,
dan ba qaramin taqadarin yaro bane, murmushin yaqe ta musu ta sa su gaba suka shige Hafsatu na ta
dariya harda riqe ciki.
Suna shiga abinda ta fara sasu shine su cire kayan su su bar wando zata masu wanka,

"Aunty munyi wanka ai,"

"A'a wannan ai ba wanka bane, ku cire ku gani, "

Ruwa mai dumi ta saka, yana tafasa ta juye, ta dinga masu wanka daya bayan daya, wani mugun datti ta
dinga fiddawa, nan da nan sai ga yaran sun fito fess, dama kyawawa ne,qazanta ta mayar da su haka, ta
shafa masu mai, sannan ta duba a kayan su ta saka masu na sallan su, suna ta jin tsoron in suka.baci
wanne zasu saka kuma na unguwa,haka ta kwantar masu da hankali tace wanki zata masu shiyasa.
Ta koma ta dora shinkafa da wake, ta soya mai yaji albasa, ta yanka timatur da albasa, yanka mai kyau,
kayansu data jiqa ta zauna a kujera zaman wanke su, sai da ta ci sabulu daya da Arial biyu, fess kayan
sukai, ta shanya, sannan ta shiga wanka, ana ta kiran magrib, ta fito ta zira riga da hijab, ta yi sallah, tana
addu'o'in ta taji qara, da gudu ta fita, ganin an fasa mata plate ne yasa ta tsaya tana bin su da kallo, kuka
Sabir yake wato qaramin su,ya zaci zata masa duka kamar Hafsatu, sai yaga ta ce,

"Matsa can gefe inda ba kwalbar bari nazo na kwashe kar ka taba zai yanke ka,"

Hankalin shi bai kwanta ba,gani yake data gama zata dirke shi, ta kwashe ta zubar, ta zuba masu abinci
dan ta kula yuwa suke ji, suna ci suna santi, gani suke ba wanda ya fita iya girki.

Zama tai tana shafa mai, tana gyara jikin ta tana qarasa azkar din ta, sai da ta gama kwalliya tsaf, ta saka
riga da wando, masu matuqar kyau, ta dakko hijab ta dora akai, dan a ganin ta bai kai na su fara ganin ta
da qananan kaya kwatsam ba abun zai masu daban, bayan ta kammala komai, ta zauna suna kallon
cartoon data kunna masu, ta gyara murya ta kira sunan kowanne su,
"Habibu, walid, Sabir, Malam, Alhaji, Khaleefa,ina son ku juyo ku sauraren da kyau kunji 'yan albarka,"

Kallon ta suka juya suna yi,yanda take nuna masu so, sai abin yakw shigar su, suke jin dadi sosai, dan ba
wanda ya ke nuna masu so a gidan, dan haka cikin wata iriyar qauna da ta darsu a ran su suke kallon ta
da idon uwa.

"Ina son mu zauna lfy daku kunji ko, ko me kuke so ku tambayen, kar wani y taban abu ya dauka da
sunan sata ban sani ba, a rayuwar yaro ba abinda na tsana kuma yake sa yaro ya fita a raina, sannan na
masa dukan da ba a taba masa ba a rayuwar shi, shine sata, daukan abinda baka tambaya ba,in na kama
yaro haka, na farko sai na fara yanke hannun shi da wuqa ya ji zafi sosai kan na yanka masa kunne, yanda
in ya girma kowa daya ga ni za a san sata yayi dayana yaro, kunjini?"

Cike da tsoron me ta fada masu suke daga kai,


"Gud, dan in kuka tambayen abu inshaa Allah zan baku, amma in ban baku ba ku sani abuna ne dama,
ban ga dama bane,"

Daga kai kawai suke ta faman yi dan suna fahimtar ta sosai.

"Yauwa kuma banda qazanta, kullum sai anyi wanka, bana son kuna yawan yawo, fita yawo unguwa
banaku bane, inna zo na nemi yaro ban gan shi ba wai ya fita daga gidannan ya tafi yawo ba wajen 'yan
uwan ku ba lallai ba ruwana da wannan yaron komai na samu ba zan ba shi ba, kunjini ko?a hankali zaku
gane me nake son koya maku, Allah ya muku albarka,"

"Ameen,ina kk aje wayar ki ne?"


Daga kai tayi, ta kalle shi, ta sake masa murmushi,cike da jin dadi yake kallon ta,ya kula tarbiyyar ta
daban ce,

"Tana daki ne, na manta ta can,"

"Ke kuma kina nan kuna hira da yaran ki, na ji dadin ganin su haka gaskiya,"

Murmushi tayi, ta kaahe TV ta nuna masu dakin da zasu kwanta,shimfida tai ma masu fitsarin kwance a
qasa, ta saka ledojin da aka ciccire aka saka mata a qasan gado,ta masu shimfida akai, marasa fitsarin ta
sasu a gdo, sannan ta masu addu'a dan basu iya ba,ta kashe fitila ta ja qofar, sai da safe ta masu sannan
ta fice.

kitchen taje ta dau flask din da ta zuba abinci,da bowl da ta zuba mai da robar yaji, da kayan timatir data
tanada, ta dora a qaton faranti, ta aje masu ledar dake gefen shi ya zaro, nama ne a ciki, ya
bude ..................
*Cassssssss Haneee kema Allah ya kawo ki zamanin cinye kayan dadi bake, maji ma gani zai cinye sai ya
rage ya bata itana ko tare zasuci?*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*Thanks so much for commenting, a gaskiya yau groups din ma da basu comment naga an dan yi,ko dan
kunji an dakko nama za ai rowar shine ma Hanee🤣 anyways thanks so much, keep it up and i will write
more for u inshaa Allah❤*

Page 12:
Ko kallon inda yake batai ba, data gama zuba masa komai, ta koma daki, dan ta qarasa diban abinda zata
buqata a vangaren shi, dan daya zaro ledar ta kula da wani bata rai da yake,kamar tsaiwar ta a wajen
laifi ne,mamaki take tayi, saboda yanayin shi yanayin me rowa dinnan bai son a ci abin shi, amma anya
ba mummunar fassara ta masa ba, kauda tinanin tai, ta ci gaba da daukan brush din ta, a ranta take
ayyana ta san zai kira ta ne, har ta gama bata ji kira ba, fita tai da yar qaramar jakar da ta dibi kayan ta,
ta zauna tana jiran shi ya gama ta maida kwanukan su wuce, ya saka naman a saman abincin shi, yana ta
santi, dan ya rasa wanne ne mai dadin naman ko wake da shinkafan? Tana ta kallon yanda yake limshe
ido, taji dadin yanda yake ta santi, dan wasu waqe2 yake daba ganewa take ba, yanka uku ya dauka na
naman ya saka a wani plate din ya miqa mata, na gaban shi ko ta san bai iya cinye shi tabbas,

"Gashi bai kamata kina gani na cinye baki dan lasa ba,"

Mamakin duniya ya rufe ta, kl gidan su ba a bata nama kwara uku kacal, balle gidan miji, mijin ma likita
kamar Okashatou, tinanin maganganun Hafsatu ne suke dawo mata, tabbb lallai kuwa Allah ya shirye
shi, hala saboda rowa ne yasa tana gida bai taba bata komai ba in ba kudin daya taba dakkowa ya miqa
mata ba akan ta hau wani adaidaita sahu , lallai amma akwai aiki,
"Ya naga kin bishi d kallo ko baki cin irin wannan?"

"Nooo kawai na qoshi ne kasan dake ban jima da cin abinci ba yanzu haka in 7 tai bana son cin komai
ban son nai qaton tumbi, habbatussauda ma nake ci kullum kar nai tumbi,"

"Oh shikenan,"

Ya gama tass, wanda zai iya ci, ya qushe sauran zai wuce dashi dakin shi ya saka a fridge da safe ya
dumama a oven ya soya kwai daya siyo, yana bangaren shi ya aje kan ya iso,ya hada tea ya sha ya wuce.

Kasa hakuri tai, abinka da mai qaramin ciki, wani mugun kwadayi ne ya taso mata, amma gaskiya
wannan ya mata kadan, bude baki tai ta masa magana, har ya kai qofa.
"Shikenan? Just like that?"

"Ban gane just like that ba,na baki kince kin qoshi to me zan maki kuma?"

"Ba komai, amma dai kasan me juna biyu da kwadayi, musamman irin wannan naman Pyar yamin kadan
plsss ka qaramin, da na zaci zan iya jurewa ba sai na ci ba amma i can't,"

"Yau naji ikon Allah,ke kuwa kin san sai sallah sallah nake zagewa a ci nama dan saniya biyu nake
yankawa da raguna biyu(dan kar ace gidan shi ba a cin dadi, shiyasa yake haka, kuma rabar da daniya
daya da rago daya yake, sauran a ci a gida, nashi kason yafi na matan gidan da yaran) shi ake cancanawa
a na miya, in aka cinye a jira sai sanda na ga dama na siyo. Amma wannan nawa ne, in mai nemowa baya
ci ya qoshi ai watara. Sai an nemo shi, da Hafsatu ce ta riga ta san halina bama ta zuwa kusa, sai na gama
abinda na rage na dan quli2 ko ragowar tsokoki ta dauke, amma kin samu har uku kike magana akai,
laifina ne,"
Tinda ya fara magana bakin ta yake bude ta kasa rufewa, hankalin ta ya tashi da jin kalaman shi,waton
marowaci ne Okashou haka duk ilimin shi da kyaun shi da gayun shi? Lallai ba kan ta.

Bata ce komai ba tabi bayan shi, ta rufe bangaren tai addu'a ta tafi, yana shiga ya banka qofar, wai shi
yayi fushi, saka ragowar yayi a fridge, ya rufe, ya shiga toilete yayi brush ya fito, ya zauna bakin gado,
yana fesa turare,ranshi bace, ganin haka yasa taje kan cinyar shi ta zauna, ta saqalo wuyan shi, tana
kallon cikin idon shi, tana limshe nata,tana bude su, tare da murmushi mai kyau( as always babana
kullum na fada min murmushi na sa namiji in yana fushi a kaso mai yawa zai tafi, mata a riqe murmushi a
daina daure fuska, wata ta daurw fuska kamar an daure kashi da igiya, amma duk munin ki kina
murmushi zaki kyau)

"Haba pyar,ba nama ne ya hada mu ba kuma ba zai raba mu ba, ba zai sa mu fada ba, plsss smile for me,
i am sorry, ba zan sake ba, kajiii, plssss,"

Shima murmushi yayi,yana shafa bayan ta, wanda take gantsarewa, dan ba qaramin jin tabin shi take ba,
kuma dik ya tava ta sai ta nuna masa, taji, hakan shi kuma na kunna shi,
"Ya wuce,inda bana son kici ba zan ma baki wannan ba kuma....."

Bata son jin mitar kawai sai ta hade lips din su waje daya, tana mai wani kiss mai wuyar fassaruwa a
wajen shi, na lallaba nai waje

Da dare bayan yayi bacci sun gama.komai ita vata bacci, sai tayi tsarki,( shin kina daga cikin masu kwana
da janaba? Yar uwa ki bari in kina haka, kin kwana da janaba, kin ko san ba mala'ikan da zai zauna dake
kina cikin najasa? Kinyi addu'a kin karya ta da najasa baki je kinyi tsarki ba, sannan ga kwayoyin cuta da
kike gayyata da kan kanki, mu gaban mu ba irn na maza bane, namu na da saurin daukan cuta, ga warin
gaba da zaki zama kina yawan yi, saboda ya bushe ya dade jikn ki ya fara wari ga qarnin shi, ko kin
wanke, in ke ba mai amfani da musm bace dama, shikenan, wari ya kama jikin ki, da kin bude wajen ma
miji sai ya dauke numfashi, ko yayi Allah2 ya gama me zai ya fece, dan haka zabi na gare ki sis)

Bayan tayi wanka ya fito, ta dakko rigat ta ta saka, hoton naman dazu ne kawai ke dawo mata, tun tana
daurewa har ta kasa, kuka ta fara, tana son ta tashe shi ta roqe shi, in ma biyan shi ne ta yi daga baya,
amma tana tsoron kar ya ce, ta tada shi a bacci,rasa yanda zatai tayi,tina nin da take zai iya landing din ta
into very big problem, amma haka ta dake zuciyar ta ta fita parlor..
*Me kuke gani? Ta ci ko kar ta taba masa? Kar ku manta dai wanda suka san ciki, ya ake ji in ana son
abu🤤🤤🤤*🤤

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*This page is dedicated to all AURI SAKI's Fans, ina jin dadin comments din ku matuqa, Allah ya sa dikkan
abinda nake fada wanda zai zama darasi, ana kwashewa, wanda yake hani ne ana kauce masa, Allah ya
bamu ikon yin daidai, ya kare mu daga rubuta abin qi Ameen.*

Page 13:
Ta dade a bakin fridge din ta na son budewa tana tinanin wulaqanci, kar taciwa kan ta gori da rashin
mutunci, kasa hakuri tayi, ta dauka taje ta samu waje ta zauna, ta bude qafafun ta, ta sa a tsakiya, ta dau
tsoka daya ta sa a bakin ta, wani dadi le ratsa ta zuciyar ta har gudu take.dan tsabar jin dadin naman,
idon ta a lumshe, sai da ta dade tana taunawa ta gama.zuqe zaqin naman, ta hadiye, ta sake daukan
daya, nan ma ta cinye ta qara daya, ta na taunawa, ta kammala ta dau na.hudun taji magana daga sama
sai da ta firgice,

"Kinci iya yanda nai niyya kici aje na hannun ki ki maida min, kin kawo uzirin ciki amma da yanda kika qi
a baya ba zan bari ki ci.ba again,"
Ranta ba dadi haka ta, itan ba mai fushi bace, amma sai ta tsinci kan ta da yin fushi da shi, ta wuce
toilete ta wanke baki ta fito.

Okshatou tin da ta bude qofa ya farka, dan haka yana labe har sai da ta fara ci taci ukun da yayi niyya ya
bayyana dan hana tan, rigar da ta saka qarama iya.cinyoyin ta, mai matuqar kyau kalar red, ga net din
saman rigar ya bayyana albarkatun qirjin ta da suka ciko suka fi da, wani yawu ya hadiya, ya matsa daidai
inda zata kwanta dan tai magana, banza tai da shi ta sauya waje,nan ma yaje ya tare, ta sauka.a gadon
dan ta kwanta kan kujera, dake dakin, ta zari pilo, binta yayi, ya sha gaban.ta, kan ta a qasa dan ba
qaramin haushi ya bata ba, meye nama? Har da zai labe haka,gaskiya girman shi ya fadi a idon ta, qimar
shi ta ragu mata sosai.

"Dan Allah bani waje na kwanta bacci nake ji, na gaji da yawa,"

"Haba Hanee na, baki gane me nake nufi bane? Ke fa kk ce nama ba shi ya hada mu ba ba zai raba mu
ba,ba halin ki bane kauda kai ga buqata ta, kar ki fara hakan, in zaki biyewa halina Hanee ba zamu zauna
lfy ba,"
"Ohhhh kenan ka yarda halin ka ba mai kyau bane har kana alfahari da hakan? Lallai Allah ya kawo mana
sauyi, muje,"

Yaji zafin maganar ta, dan ba kowacce mace ce zata fada mai haka ba bata kwan dakin tsohuwa ba,
baida hali mai kyau, lallai wannan yarinyar ta samu waje.

Ai ko da mugunta da komai ya ke sarrafa ta,tabbas akwai gajiya a tare da itan, tinda ga hidimar yara, ga
girki,ga shi dazu ma yayi, sakewa yake,tayi2 yaje ya ya yi tsarki yayi alwala kamar yanda aka fada a
musulunce, inaaa da najasar dazu da bai tsarkake ba, haka ya sake kusantar ta,gaskiya Okashatou ya fara
fita mata a rai,dan mace ce mai ibada bata son duk wani wanda bai damu da ibada ba.

Bayan ya kammala, lokacin wajen qarfe biyu da rabi na dare, da kyar ta tashi, saboda gajiya, ta shiga
toilete tai wanka, ta gasa jikin ta da ruwan dumi, ta dade ciin bathtub,sannan ta fita, tai drying gashin ta,
ta saka doguwar rigar da ta dakko dan yin sallah, ta fara nafila, bayan ta idar ta yi karatu, sannan ta gyara
kwanciyar ta anan tai baccin ta.
Okashatou tini ya dade da bacci shi, yana gamawa dama daya kwanta gefen ta,daga maida nunfashin shi
bacci ya fara diban shi, a haka yai bacci, sai da zata tashi ta yafa masa abun rufa.

Haka Hanee ta gama girkin ta ba walwala kamar da, domin mamakin shi da kuma sabon halin shi daya
nuna mata su suka sage mata guiwa akan shi.

Haka ta fita girki, kadaran kada han, Okashatou jikin shi yayi sanyi akan canjin ta, wanda da ace wata ce
va ita ba ta nuna masa wannan halin sai ya fita dauke kai, amma ita sai yake ta bibiyar ta dik inda tai, ko
dawowa yayi, zai leqa inda take, dan yaga ya take, Hafsatu ta kula da sauyawar tasu, kuma ta kula da
yanda yake shinshinar ta ko ba ran girkin ta ba, lallai wannan sabon lamarin ya qona ran ta.

Da yamma kan ya dawo ta fada gidan malamin tsubbun ta da bai da nisa da gidan nasu, ta mai bayanin
abinda ke faruwa,
"A gaskiya ta bangaren ta ba wani taimako da zan maki, amma ta wajen mijin naku, zan iya sa masa
tsanar ta ya kauda kai akan ta kamar yanda aka daba dai, shi kuma matsalar shi ba koda yaushe yake cin
abincin ki ba kamar yanda kk fada, amma za a gwada, ko sau nawa ne har ayi nasarar ya samu yaci,kinga
shikenan an gama da shi, ba zai dinga damuwa da ita bama, kuma zai dinga mantawa tana gidan ma,
kina buqatar kayan aiki sosai a wannan karon, dan aiki za ai da baqaqen aljanu, suko sai sunsha jini, ki
kawo kayan yanka,"

"A dan tausaya malam kaga ni din ba wani hali ne dani ba, duk na saida yan kayayyakina saboda biyan
buqata ta, adan sassauta min,"

Haka dai suka sasanta abinda zata bayar, ya bata maganin da zata sawa Okashatou a a binci,ko a ruwan
sha.

Aiko da murna t koma gida, lokacin ya dawo, ai tana saka kai taga motar shi, da sauri ta koma baya, sai
da ya shige itama ta shige wajen ta da sauri.
Bangaren Hanee ya leqa wadda ya wuni kewar ta, yana shiga yaga tana.koyawa yaran shi karatun
qur'ani, duk sun zauna sun nutsu, Habibu ne kadai ke gefe, yana ta maimaita nashi, dan daban take masa
nashi qarin, yafi su saurin dauka, kuma shi babba ne, daga shi sai malam, suna da saurin daukan
karatu,dadi yaji, a lokacin tinanin saka su makaranta ya zo masa, amma yana tinanin ya zai ya kai su, a
tuhume shi me yasa bai kai yaran shi ba da wuri sai da suka.girma, kaida tinanin yayi,

"Ina ta sallama ba wanda yaji ni"

"Wa'alaikumussalam, ayya bamuji ba, barka da dawowa Rabbul bait, ina fatan ka dawo lfy?"

"Lfy qalaou, amma ni fa sai naji kamar sabo kk wataran in kina kirana da Rabbul bait dinnan,"
Dariya Hanee tai sosai, saboda ta san Okashatou qunqurmin jahili ne, bai da ilimin komai,

"Kana nufin baka san meye ma'anar Rab ba? Da bai ba?"

"Ya isa malama,muje ki ji, akwai maganar da zamuyi dama,"

"K to muje"

Tashi tayi bayan ta shafi kawunan yaran cikin so da qauna, tana son su shiyasa riqon su baya bata
wahala,ta sa sun nutsu matuqa, ga kyau irin na mahaifin su da ke bayyana, saboda wanka da gayun d
take masu da kayan gwanjo, tinda shi ba zai bada kudi ta sai masu ba, dan wanda Amman ta ke aiko
mata lokaci zuwa lokaci da Abban ta, da shi take wasu hidimomin, har girkin gidan, dan haka Okashatou
har yau bai daina cin abincin ta ba.
Tana shiga bangaren shi ta gan shi kwance alamar jiran ta yake, kuma buqatar ta yake, kuma a iya sanin
ta yau ba girkin ta bane.

"Amma pyar yau fa ba girkina bane,kuma Hafsatu na nan ba wai tayi tafiya bane ta amince mana, dan
haka ka bari na san tana nan tafe,ka qara hakuri har nawa girkin yazo kaji abin sona,"

Cikin bacin rai ya sakko yana bin ta da kallon baki isa ba ki qetare doka ta,

"Kinga malama ni anan gidan ina da yancin kwanciya da dik macen dana ga dama, nake sha'awa, da
sha'awar ki na wuni a wajen aiki, dawowa ne kawai na daure ban ba, sannan ki kawon wani shirme, dalla
muje,"
"Kaga Okashatou, ni fa ba zan bi umarnin ka na sabawa Allah ba, akan me zaka tirsasani yin abinda bai
da kyau yake haramun? Kawai dan kana taqamar auren mu kayi ai auren ba zaman gidan bariki bane,
kana son ka sa ina furta kalamai masu zafi a gare ka wanda ba su kamaci macen kirki ba,dan Allah ka
sauqaqa min hanyar shiga aljanna ta,"

Ta qarasa tana hawaye tare da hade hannayen ta biyu, suna cikin ja in ja Hafsatu ta shigo ba ko sallama,
yanda ta ga ya qanqame Hanee,ga kuma tsantsar buqatuwa a tare da shi na Haneen, shine dalilin daya
sa ta sake kwanon abincin da ta zubo masa mai dauke da maganin a ciki, kuka biyu ne ya kwace mata ta
dora hannu akai kuwa ta dinga zindima ihu, tana zindimawa Hanee ashar din jahilai, tana ikirarin sai ta
lahanta ta, yau ko ita ko Hanee.

"Abun bai kai haka ba Hafsatu, ba laifina bane, ina qoqarin sanar da shi hakan haramun ne amma ya kafe
shi ni yake so yau, sai dai in zaki yarje mana na yau kema ran girkin ki sai na bar maki shi, "
"Dan........ uban ki yau sai cin amanata ya kasance maki aikin qarshe,ni zaku dinga zagayewa kuna cin
amana, daga yau ba wanda zai sake min wannan tozarcin a gidannan"

Kitchen din shi ta shiga ta dakko qaton ludayin diban abinci,ta fito, a guje, kamar mahaukaciya, ai Hanee
da bata saba da fada ba tini jikin ta ya hau rawa, tabi bayan Okashatou ta boye, Okashatou mai abin
haushi duk wannan badaqalar da ake, bai sa sha'awar shi lafawa ba,hasalima wannan rungumar da ta kai
ta baya jin ta yai kamar an kunna shi, ai da sauri ya.dauke Hafsatu da mari, ya ja ta ya hankada waje, ya
rufe qofa yana zagin ta.

Sai kuka take ita kuma tana zunduma.masu ashar dikan su,

"Ni da haqqina a ci min mutunci haka, gaba dayan ku zaku san kunci amana ta"

Ta kade jikin ta ta shige bangaren ta tana ta kuka, yara na ta kallon ta, tana furta maganganun da bai
kamata yaran su ji ba, Okashatou kuwa tini ya kai Hanee gado, yana lallashin ta, jikin ta bai bar rawa
ba,hankalin ta tashe, yau ba abinda take so irin Amman ta, wani kuka ta sa mai cin rai,mai zafi a qirjin ta,
wannan wace irin rayuwa ce, ita da ko cacar baki bata tabayi da kowa ba, amma yanzu ake dambacewa,
bazata iya rayuwar gidannan ba, Okashatou ganin yanda ta qanqame jikinnta ba yanda zai ya shige ta in
ba qarfi zai saka mata ba, yasa a hakan da jikin ta ya biya buqatar shi ya miqe,ko lallashin ta bai ba, bai
kuma bata baki akan abinda ya faru ba, wai miji kenan.

Cikin sanda ta koma bangaren ta, ta gyara jikin ta,yaran duk sunyi bacci a kwance a wajen, kuka take
sosai, kamar wadda akaiwa mutuwa, sai da ta yi mai isar ta ta dakko wayar ta ta danna kiran Amman ta,
ta dade tana ringin kan Amma ta daga cikin mgagin bacci tai sallam, jin kukan Hanee ya wartsake ta,

"Amma mi don der wannuna,"

"Subhanallahi, meke faruwa? Yi shiru ki daina kuma ki min bayanin komai,"

Fada mata dikkan halayyar Okashatou tayi, da abinda ya faru yau, dan bata da wani aboki ko qawa
kamar Amman ta,itace zata bata shawarar daya dace.
"Noi ga daimi Amma?"

"Karki damu yanda zaki ki hakuri, gobe ina nan tafe, karki komai da zai sa azo ana sake tashin hankali
kinji Babyn Abba?"

Daga kai take kamar tana ganin ta, ta share hawayen ta, labaruka masu kwantar da hankali Amma ta
bata,sai da ta tabbatar tana dariya ta kashe wayar.

Amma data dawo Parlour da zama ta yi tagumi, tana tinano Hanee a gidan kishiya,dama kullum tsoron
ta kenan, kar rikici ya tashi azo ana saka mata yarinya a gaba, amma ba komai zata je dolen ta gobe, ta
kwantar ma da Haneen hankali..........
*Bari mu jira zuwan Amma ko zata taimakawa Haneen mu😭*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 14:

Da safe bayan ta gama abubuwan da suka zama mata al'ada, yaran ta suka zo karatu tace masu banda
yau, sai zuwa taji sauqi bata da lfy, dan Sabir qaramin su sai tambayar ta yake, saboda tin jiyan hawayen
ta ya qi tsayawa, wannan abun bata taba tsammanin haka daga qajen.Okashatou ba, jahilci tsabar shi a
tattare da.shi, shin le dalilin masu qaryar bata da lfy.

Daki ta tura su tace su dau littattafan su Habibu yana.qara koya masu A b c d da kuma Alif da Ba, kar su
fito, in lokacin wankan su yayi suje suyi da kan su, ba sai sun fito ba, cike da.ladabin da ita kan ta batai
zaton yaran zasu kimtsu cikin dan qanqanin lokaci haka ba, sai kawai ta ga ashe soyayya suke so, kuma
sun samu,.dan haka suke mata biyayya.

Wanke.kayan ta daya bata mata.jiyan.ta gama, ta watsa ruw,ta haye gado ta kwanta, koko ta dama, ba
ko dan mahadi, kasa sha tayi, tana ta.tinani baccin da batai ba jiya ya.dauke ta.

Cikin.bacci taji ana.tada ta, Habibu.ne ya.shiga,

"Ummee wai ki zo inji wata kuna.kama sosai,mai kyau ce itama,"

Murmushi ya sata a karo na farko tin jiya, ta sakko, tare da.daukan riga mai dogon hannu ta saka
kan.vest din ta, ta fita, tana ganin Amma ta tafi da gudun ta ta fada jikin ta,
"Ammaaaa"😭😭😭

"Shiiii, habaaa ki shiru mana, anya ba kwana kuka kikai ba, and is not gud for my grandchild, come here
and sit beside me dear,"

Zaunawa suka a kujera mai cin mutum biyu, sai da ta barta tai kukan ya ishe ta sannan Amma ta janyo
flask da ta zo da shi,

"Je ki dakko plate, da spoon da ruwan sha,"

Daga mata kai tayi ta miqe,cikin ta na nan shafe kamar mara ciki, dawowa tayi dauke da su, ta aje gaban
Amman ta,tana goge fuskar ta da take jin har yaji take mata tsabar goge hawaye.
Amma na budewa sai ga farfesun naman kaza ya bayyana,kalar girkin ta mao dadin tsinke kunnuwa,tini
Hanee uwar kwadai rai ya biya ciki. Kwanon, wata leda ta gani mai layi2, tana dubawa taga nama ne, na
zabbi dana rago an soye su sosai, suya mai kyau, rungume Amman ta tayi, tana sake sabon kuka,

"Nifa ban zo dan naji koke2 ba , i am here to see how u ar doing, kuma na baki shawarwarin da zasu
magance matsalar zaman ki anan gidan inshaa Allahu,"

"Amma dole na koka, rabon dana ga wanna hidima tin ina gida, ba dan mu bama su kwadayi bane dama
da sai nace anan ne ma za a zaci irin wannan,nan da suka fimu arziqi,amma nan ake ganin qaranta,"

"Kull bana son jin magana haka, dauki kici, dan da ganin idon ki baki karya ba,"
Har ta fara ci, ta tina da yaran ta, tashi tayi ta dakko wani plate mai girma ta zuba masu, ta kai masu
kowa da kason sa, ta ja qofa, bayan tai warning kar taga miya a jikin bedshit.

Tana kammalawa, cikin ta ya dauka har wani dagowa yayi,

"Masha Allah,ya zu sai ko sake maimaitan komai, yanda zan san amsar da zan baki,"

Sake maimaita mata halayen Okashatou tayi, sannan ta sanar da ita abinda ya faru jiya, Amma ta girgiza
kai, tai shiruuu, daga bisani tace,

"Lallai ko a da dayana zuwa,ba mai ganin shi yace zai aikata, amma ya ban mamaki, anyway,ba ruwan
mu da shiga tsaka in bawa da ubangijin shi, ba mu san ladan daya tanadar masa ba, muce zamuyi
shisshigi, wai mu masu tsoron Allah, dan haka matsalar ki kusan me sauqi ce, sana'a kawai zaki fara,
kuma babba, wadda ba zai ga qarama bace yace kina son tona masa asiri ba, a'a, dan Abban.ki ya ban
kudi wadatacce na kawo maki da zai isa, in kina da sana'a kina d na kashewa, kina da na yin lalurorin ki,
irin mijin ki wannan shine maslaha, ba kare bin damo, bakice ban ba bare ya ji haushi, baki kwadan abin
hannun shi ba bare a ji kan ku, kin gane?"

"Eh Amma na gode, amma anya zai bari kuwa? Sai daya matsalar Amma baki ban solution ba,"

"Daya matsalar kuma dik randa ba girkin ki ba tinda akai haka karki kuskura kije ke daya ko kiran ki
yayi,tafi da yaro,kuje dik abinda zai saki yaro na nan, in kk ji ya kori yaro, tsaya daga bakin qofa kema,da
ya furta buqatar shi komo wajen ki ki rufe ko zaman ki, dan babu biyayya ga bawa wajen sabawa
mahalicci,ina fatan kin gane? Maganar zai zarki kuwa in bai bari ba kina da no sirikin ku ki sanar dashi
kina son fara sana'a kina neman ya sa maki albarka,a fakaice kice masa kina mai talla in zai siyi abinda kk
siyarwa ya tina kina saidawa, na tabbata tanda yake son ki,zai ce zai siya, kinga sai ki sanar dashi ai wane
ya hana, ki sanar dashi ke kuma kina son yi, amma kin hakura,dole zai tirsasa shi ya varki da umarnin shi
zaki komai, in hakan bai samu ba ki hakuri, Abban ki zai masa magana, dan dole ne ki na sana'a a irin
wannan gidan"
"To Ammana na gode sosai, barakallahu fiki,"

"Wa fiki barakallah habibty,"

Amma bata jima ba ta ce zata tafi, kuka ta fara,tana complain akan yau ne zuwan ta na farko dakin ta
am.a take son tafiya da wuri haka, hakuri tai ta bata ta tafi, ta kwashe komai ta kao daki.

Hafsatu da ta dade a tsaye ganin Amma da kaya, a hijab, kuma ta fuska ci maman Hanee ce dik yanda
akai, ta koma dakin ta, tana tinani, ko itana wani asirin aka kawo mata,ohhh dama maman ta na da rai
itama, amma bari aunty mommy zata kira, babbar ya uwa, dama da ita ake qulle2,kuma itan tana da
kudi, a Kaduna suke mijin ta har gidan mai gare shi, tasan in ta kira ta komai zai zo yanda take so.
A cikin kwana hudu Hanee ta yanke shawarar me zata siyar, aiko da dare, suna kwance bayan sun
kammala rayuwar auren su, sai gyatsar abincin da yaci mai nama yake, yana ta son tambayr ta ina take
samun nama kwana biyu sai ya sha'afa,

"Aff ni kam nace wai ina ake samun nama ne a miya, ko a abincin dika?"

"Sana'a na fara ta kitso, da kuma sai da man kitso, saboda ina son na kyautata maka, kar ina baka abinci
mara dadi, shiyasa zan dage da neman na kaina,dan kaji dadi,"

Ai ko ya ji dadi matuqa, bai ce mata ki ci gaba ba,bai kuma ce kar ki sake ba, tini ya juya ya fara aikin
bacci abin shi, tai ta murna kuwa.

Ba wani mai da kitso data fara,amma su take ganin zata iya, shiyasa ta fadi hakan.
(A baya nace zan maku bayani akan Hafsatu, in baku manta ba Okashatou ya ci mutuncin ta bata
qamshi,to kunga da tana sana'a itama kuma bata bin malamai suna cinye mata kudi,kenan da itama zata
iya kome take so? Sannan sisters in mace na son abu wajen miji, in kk fara nuna masa amfanin abun iya
ke zaki mora wallahi da wuya ya maki, sai dai in mai yi ne, amma ki fara nuna masa amfanin abun shi zai
fima amfana, zakiga nan da nan kome kk so an gama, inshaa Allahu, sai dai irin Abbas ne mijin MUGUN
MIJI, 🤣)

A washe gari tayi ma Amma waya akan a turo mata Ammar, ta kuma sanar da ita yanda sukai, aiko, yana
zuwa ta rubuta masa list din mayukan da zai je ya kaiwa Malam Sabi'u shine me zuwa Kano, ya siyo
mata,( a kano kasuwar take, wanda ba 'yan kano ba anemi kasuwar kurmi, na manta daidai location din
wajen, amma a kurmi ana samun mayukan masu kyau)

List ne kamar haka (a rubuce ko a adana page din, ko kin tambayen ta pc gaskiya zai wahala na sake
maimaita maki, zance ki nemo page din ne kawai. Ina fatan va a ji haushin magana ta ba🙊)

*MAN SAKA TSAHO DA KYAU NA GASHI*


*Man zaitun*

*Man habbatussauda*

*Man kadanya*

*Man zogale*

*Man audiga*

*Man atile*

*Man albasa*

*Man kaninfari*

*Man hulba*

*Man lalle*

*Snake oil* (na kwalbar shi, sai a juye a ciki a hade mayukan dika ana kitso da shi, a yawaita oiling gashi
da shi, yana saka tsaho, da cika, da kyalli, da kuma rashin barin gashi ya karye, in kina son yayi kauri, zaki
iya samun candil da ake man shafawa ki narka ki hade su mayukan dika, sai kina shafawa abinki, ko kina
saidawa)

Dika ta hade, ta sa ya siyo mata robobi da dikka. Abinda take buqata, ta hada a cikin kwana uku da kawo
mata, ta zuzzuba,ta sa Habibu yayi wanka, yayi addu'ar fita daga gida ya kakkai maqota, su gani, kuma
ya sanar dasu, Amaryar Abban su na kitso,tana sai da man kitso.
Aiko bai bata lokaci ba wajen isar da saqon ta ya dawo, d dozin daya ya fita, ya dawo da hudu kacal,
sukai ta murna, ga kudin a hannun su, unguwa ce ta masu da shi dama.

"Ummee (sabon sunan da suke kran ta dashiba wanda ya saka su kuma) kina ban ina kaiwa ko za a na
siya,"

"Laaa ina son ku yi karatu, kamar yanda ba zan so na haihu yarona yayi talla ba kuma haka, zan iya
qoqarna naga kun fara zuwa makaranta,ko da kuwa ni an dakushe tawa, this is my promise to u,"

Murna sukai tayi, lokacin magrib yayi suka tafi zuwa sallah..........
*Kunji sabin mission din Hanee ko? Hummm may Allah help her oo*

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH

Page 15:
Kusan wata daya kenan, da fara saida Man kitson Hanee da kuma fara yin kitson ma mutanen unguwar
su masu kudi, wata ma in tazo haka zata zaro dari biyar ta miqa mata, ko sama da haka, tinda tana da
kirki,kuma ta iya hulda da mutane,ta dage sosai wajen koyar da yaran ta turanci, da kuma karatu, na
qur'ani dana hadisai, sai karatun boko.

Sosai suke ganewa, kuma suke jin dadi, har sauran 'yan uwan su na wajen Hafsatu kan leqo wataran ayi
da su, sai ga yaran Hafsatu dake zuwa makaranta, Yaran dake wajen Hanee sun fisu qoqari, dama cikon
aji suke, su kan su sha'awar yanda suke qoqarin hada baqi, suke, sai dai karatu akan su kam ba a
magana, rubutu ne har yanzu ake ta fama.

Wata ranar juma'a Okashatou yana dawowa da wuri, daga an yi sallah, Hanee tai ma yaran ta wanka, ta
masu gayu da kayan da ta siyo masu sabbi na gwanjo, ta shimfida masu tabarma gefe kadan da inda
Okashaou ke aje motocin shi kuma yayi seti da windon toilete din shi, blackbord da ta sa Ammar ya siyo
mata kasuwa da chalk, ta aje masu ta tsara masu dik abinda take so suyi, ta shige, tana hango su ta
windo, suna ta karatun su.

Wata mata ce tazo kitso, Hanee ta kama kan ta,tana mata,matar tace manya take so, jiran ta ake zasu
fita, nan da nan ta fara mata cikkn sauri, tana kammalawa ta bata dubu biyu ta dauki mai daya, na
siyarwa, Hanee murna kamar zata yi yaya, in zata fasa asusun ta fa yanzu zata samu kudi sosai, dan ma
tana amfani da wasu.
Qarar motar Okashatou sukaji, aiko nan da nan yara suka qara maida hankalo wajen karatun su,Habibu
ne ke koyar da su, A B C D ya rubuta A to Z yana nuna masu suna karantawa, Okashaou bai zaci qarar
karatun dayakw jiyowa ba a cikin gidan shi bane, sai da ya shiga da kyau,yai parking, Hanee ta dawo
daga aje kudi da gudu, ta zauna tana kallon su, bayan ya fito ne,suka mai sannu da zuwa, ya na tafe yana
waigen su cike da mamami, to yaushe ma yaga sun fara karatun, ace har sun iya ABCD daga farko har
qarshe,lallai Hanee alkhairi ce a gidan shi, haka ya rufe part din shi ganin yanda ya shiga tinani yasa ta
qara tsananta addu'ar ta, haka ta dauki Dambun masarar da ta masa, wanda yaji gyada, da zogale,
sannan ga nama ta yayyanka, ta saka attaruhu, da albasa, sai qamshi yake,ta soya mangyada da albasa
shima, ta zuba a mazubi da plates, da ruwan sha, na zallar kankana da lemon zaqi, sai ginger,sugar kadan
ta sa ta qara da zuma,wani orin gardi kamar a bada ajiyar kunne dan dadi,🤤 gyara kwalliyar ta tayi,inda ta
saka wani qaramin wando,da yar riga, ya fito da hips dinta sosai, da dan tulun cikin ta daya dan fito, tayi
matuqar kyau, gashin ta ya qara tsaho akan nada, da kyalli, kaii sai wanda ya ganta kawai, ga wani
qamshi dake tashi na musamman, ta zunduma hijab din ta, ta fita,ta kashe ma yaran ido, suka daga mata
yatsan su 👍🏻suna kashe mata ido suma.

Ko da ta shiga zaune ta gan shi, yana hutawa kuma yayi zurfi a tinani da dikkan alamu, sallama tayi,
sannan ta aje abinci gaban shi, ta kauda jakar shi ta kai dakida zata fito ta ake hijab din ta a dakin, bude
idon shi yayi a hankali, ya sauka a kan qugun ta,da take juyawa kamar wani katantanwa, lumshe ido yayi
tare da lashe leben bakin shi na qasa, kaiii yarinyar nan ta hadu a komai,
"Sannu da dawowa Pyar,ya juma'a? Ya kuma asibiti? Ina fatan baka gaji ma mijina, muje na maka wanka,
ka sha iska, yau ana dan zafi (tana wani yarfa hannu kamar mai firfita da yanga)"

Jan hannun shi ta yi,ya bita kamar raqumi da akala,sai toilete, suna shiga kuwa ya jiyo yanda suke zuba
karatun qur'ani ko shi sun wuce shi, dan be gane nan ba dai, kasa kunne yayi yana sauraron su, har ta
gama hada ruwan wankan, ta fara cire masa kaya, sannan ta masa magana,

"Zamuje wankan ko kuwa zaka tsaya sauraron karatun 'yan albarkan can?"

"Amma Hanee gaskiya na kasa boye mamaki na fa, taya akai yaran nan suka iya karatun nan a qanqanin
lokaci kaha?"
Tana masa wankan cikin salon qara dasa masa son ta a zuciyar shi tayi murmushi sannan tace,

"Ta yaya ba zasu iya ba bayan mahaifin su dikkan nin su suka yo, kuma Allah bai sa mahaifin su daqiqi
bane, Allah ya yoka cikin masu ilimi, masu nasara a duniya, dan ka hada abubuwan da mata ke farin ciki
in sun samu miji irin ka, ga kyau ga ilmi,likitane fa kai, yanzu suma da suna makaranta ai Allah kadai
yasan me zasu zama,"

Shiru yayi, bai ce komai ba,har suka gama, ta goge masa jiki, ta saka masa boxer da vest da ta dakko kan
su shigo, sika fita, daki yaje ya fesa turaruka, ya zauna a qasa yana jiran ta zuba masa abinci, tana
budewa a ido ma sai da yawun shi ya tsinke, ta gama zubawa tace,

"Bismillah, ga dambu, amma na masara ne wannan, ina fatan zaka so shi, kuma zai maka dadi,"
"Ni fa bana son dambu, mantawa nayi ban gaya maki ba, sai ai dambu wani waje ya dahu wani bai dahu
ba cikin mutum yazo yana baci,"

"Amma pyar zaka sacen guiwa,ka fara cin wannan ka ji mana ai ko a ido kasan ba zai bata ciki ba ko?"

"Haka ne,"

Fara ci yayi yana ta santi, da muryar shi, da ba a gane me yake fada, kamar waqa,
"Yauwa pyar me kace game da saka su skul ne?"

"A saka su mana, amma da sharadi bani zan kai su ba, dan abun kunyan zai yawa kamar su ba su taba
zuwa makaranta ba, ba zan iya kai su ba na maki izini ki kaisu da kan ki, in yaso zan biya dik kudin da aka
ce sai ko fadan na tura masu ta hanyar transfer,"

"Kaiiii amma muna godiya pyar Allah ya qara maka daukaka, ya jiqan mahaifa,"

Ta janye cokalin da zai kai bakin shi, ta maye gurbin cokalin, aiko kamar jira yake ya cafe, abincin da bai
qarasa ci ba kenan.
Ana kiran la'asar ta miqe daga jikin shi, ta shiga toilete tayi wanka, ta tada shi, shi kamar wanda ake ba
maganin bacci da an gama komai kawai sai ya hau bacci, da kyar ya tashi, tace yaje yayi wanka, yaje
masjid, sai ya debi wani abincin, bari taje ta dora na dare, ya ce kar ta dora da shi, dambunnan ya ishe
shi.

Sai da ta koma wajen ta tai sallah, tana girki tana qrasa azkar din sallar ta,yaran na dawowa daga masjid
ta basu hannu suka tfa, tace,

"Albishirin ku,"

"Goro Ummee qato fari karki mana wata tambayar kawai fada mana,"
"Habib saurin meye haka,😄tooo Abban ku dai ya yarda zaku makaranta,ni zan kai ku da kaina, inshaa
Allahu,"

"Yehhhhhhhhhhhhhhhh"

Sai tsalle suke suna murna har ita, a haka ta gama masu tuwon gero miyar kuka, data sha kifi, dik da
kudin ta take wannan hidimar, Okashataou ba ruwan shi, da sun ci ko basu ci ba, taqamar shi kawai ya
kawo abin ci, na.masarufi sun san ya zasuyi.

Sai da suka ci suka qoshi, sannan ta zauna dora masu wani karatun,
"Ummee tinda zamu makaranta a dan huta da karatun agida na gaji, kullum karatu muke, su Nour kuwa
kallo suke abinsu, sai mun hadu suyi ta bamu labarin film din da suka kallah,"

Kura masa ido tayi tana tafa hannayen ta tana kada kai, tana maimaita,

"La'ilaha illallahu, lahaula wala quwwata illa billah, subhanallahu, laaaaaaa tabbb"

Kunyar duniya ta kama Alhaji, ji yai dama dukan shi tai da wannan abun da take masa, kamar wanda ya
yi wani qaton zunubin, kallon da take mai na ka ban mamaki, ne yasa ya je ya rungume ta da gudu, yana
bata hakuri, akan ba zai sake ba,
"To sake ni, je ka zauna, na hakura,amma ka san Allah, ka sake irin wannan tinanin ma, na gane kayi shi,
sai dai kaji na saka sauran makaranta ya zama kai daya ne a gida, kasan me zan maka? (Ya kada kai) talla
zaka dinga min"

Aiko sauran suka bushe da dariya, sai yaji gaba daya bai kyauta ma kan shi ba,

"Ummee plsss ki hakuri ba zam sake ba,"

"To ya wuce Allah ya maku albarka,"

"Ameen"

Okashaou na dawowa daga masallaci da isha'i, wanda yanzu by force by fire Hanee take sashi zuwa duk
ran girkin ta, ya wuce bangaren Hafsatu, a zaune take kamar kullum yara an baibaye ta, ta kwaye cinya,
gidan kaca2, kwanuka ko ta ina da cups, tsaki yayi, ya shiga, yaran na ganin shi suka nutsu.
"Ran litinin, ki shirya yaran nan da basu zuwa makaranta, za a saka su makaranta suma,"

"Kai da kace ba zaka saka su ba me ya sauya ra'ayin ka? Allah ya kaimu, waccw zan kai su?"

"Umma Hanee ce zata kai su,ki shirya su sauran azo ana jiran su,"

Ya fice, wani ashar ta saki, lallai, in batai waje da yarinyar nan ba tana ji tana gani zata sace mata miji
tasss,duk abinda baya yi da yanzu yi yake, inaaaa da sake an bawa me kaza kai...........
*Yehhhhhhh we ar going to schoollll on monday, thanks to Hanee durling💃🏻💃🏻💃🏻

[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
*A gaskiya ba abinda zan ce ma kowa da kowa sai dimbin godiya da fatan alkhairi, daga iyayena, mijina,
'yan uwana, da qawayena na alkhairi, Allah ya biya ma kowa buqatun shi na alkhairi, Allah ya ma kowa
albarka, marasa lfy Allah ya qare mu da lfy, naji sauqi Alhamdu lilLAAH, addu'ar ku tayi tasiri sosai, kun
sani na sake gane halayya irin ta mutane kala2, wasu suyi da kai domin Allah, da zaman tare, wasu
domin wani abu da kk masu na nishadi,(novel) wanda shi kadai suka saka a gaba, ba lafiyar ka ba, ya
Allah ina roqon ka da ka barni da masoyana domin ka a duk inda suke*

😄😄 *Masu min Fatan Alkhairi,🤰🏻 na gode, komai lokaci ne, in lokaci yayi ba yanda za ai abu bai tabbata
ba, ina roqon Allah daya sa maku farin ciki kuma a rayuwar ku kamar yanda kuke man fatan hakan, na
gode sosai, Love u all domin Allah❤*

Page 16:
Hanee ta samu nasarar sanya su a makaranta, har yaran dake wajen Hafsatu, inda ta tubure hr na wajen
ta sai an cire tinda it ke biy masu kudn abubuwa da dama, in yaso a gwamutsa su dika ya na biya, kafin
Hanee ta samu yaran su fito sai da ran ta ya baci, dik hakurin ta, ta leqa ta mata magana, yaran sunyi
murna sosai, biyu daga qannen shi ne suka kai su makarantar, har Baban shi sai da yayi murna, tare da
mamakin jin wai Okashatou zai kai yaran shi makaranta, lallai Hanee ta zama daban a matan da yake
aura nan ya qudiri niyyar zuwa gidan dan nashi ya ga yanayin zaman a wannan karon, dan ya jima bai je
ba, tin wani zwa da yayi. Matan.Okashaou lokacin su uku ne, ana dambacewa, daga basu hakuri zagi ya
juye kan shi, Hafsatu mai wayo tana ganin Okashatou da daita ake zagin Alhaji ta koma fadan basu da
hankali suke zagin uban mijin su, nan Okashaou ya auna su gidan tsoffin su, daga nan Alhaji bai sake
marmarin zuwa ba,kuma ya zargi Hafsatu akan wasu abubuwa da dama.

Komai qeqe2 da qeqe2 Okashaou yayi, qannen shi nata gulmar shi, akan son kudin shi da rowar tsiya, ba
zai basu kudin a hannu ba dan kar a ci, wai sai dai a dinga fadan me dame ake buqata ya biya da kan shi,
sai da Hanee ta masu magana.sukai shiru, ta nuna masu gaban.yaran shi fa suke.maganganu haka.bai
dace ba ai.

Yaran Okashatou nada wata daya da sati biyu a sabuwar makarantar su,wanda yayi daidai da cikin
Hanee wata na bakwai kenan, makarantar su, a hade take da arabi da boko , kowanne yaro yayi settling
a makaranta, wasu sun san inda aka dosa by now, wasu kuwa ana dai zuwa ne kawai tukunna, nan fa
aikin Hanee ya qaru sosai, dikkan yaran a wajen ta nan tsakar gidan suke daukam lesson, wanda take
masu na boko sannan da kudin sana'ar ta ta samo masu malamin islamiyya,a wata take bashi dubu uku,
wanda tausaya mata yayi, yara sun kai sha hudu ko sama a dubu uku kacal a wannan qaton gidan? Ai sai
dai a yi kurum.
Ga kitso,a rana tayi kai hudu biyar, ga mai dik da ba kullum take man ba, ga kuma girki, da kula da
Okashaou daya fara zama mata qajaqa, dan ya maida ita kamar ruwan sha, ko ba ran girkin ta ba qoqarin
shi kawai ya kusance ta, dan kawai bata bashi dama.ne.

Wata ranar litinin, yara sun tafi makaranta, Hanee na hutawar ta, a dakin Okashaou data gama gyarawa,
yake ta tashin qamshi, da sanyin AC, gidan yai shiru ba kowa sakamakon tafiyar da Hafsatu tayi itana
zuwa garin kaduna, a gajiye take liss, kamar an mata duka, jira take ta dan huta, dan cikin ta na ta mata
ciwo ne, in ta huta,ko zuwa 12 ne ta dora jellop din taliya, da busasshen kifi, da alayyahu, sai su ci, in
yaso da dare ta danyi mai nauyin, dan ci ne da su ba su qoshi ta kula, na wajen ta ne kawai ta daidaita
masu cin su, amma kwana biyun nan datake kula har da na bangaren Hafsatu ta kula da hakan.

Juyi tayi ta rungumo pilo, dan taji dadin kwanciya, ta ga inuwar mutum akan ta, Okashaou ne tsaye akan
ta, yana binta da kallo, da sauri ta miqe,tana mamakin ganin shi a haka,

"Pyar lfy? Yaushe ka shigo ban ko ji shogowar ka ba?"


"Tin dazu na shigo, dan debon ruwa na sha,"

Qarasa tashi tayi da kyar, ta je ta debo masa ruwa, ta bashi ya sha, a hankali ya fara jan ta, har saida ya
samu biyan buqata da ita,suna kammalawa, ya dauki rigar ta da kan shi ya saka mata, for the first time a
rayuwar su, wai okashatou ya damu da taya ta wani abun bayan ya mori jikin ta, kallo kawai ta bishi
dashi tana murmushin jin dadin sauyin da aka samu, 12 tayi,

"Pyar naga saka rigar ma kamar baka son gama sakamin, bari naje na dora abinci yarana sun kusa
dawowa, kar au dawo ba abinci, in yaso na dawo, ko cire rigar zaka sake bazan hana ka ba,"

Har ta miqe ya dawo da ita, ya rungume ta, sannan ya umarce ta da ta dakko masa jakar shi daya dawo
da ita a palo, cikin hanzari ta dakko masa, haka nan taji jikin ta na rawa, hankalin ta taji a hankali yana
tashi.
Yana karba ya yanko takarda, tana zaune a gefen shi, ya gama.rubutu jiki ya miqa mata,ya yi sauri. Shiga
toilete, ya danne qofar, jingina yayi da qofar, yana hawayw,meke damun shi ne? Gaba daya ji yake
kamar ba shi ba, wai ya zai aikatawa macen da take masa biyayya fiye da dikkan matan daya taba aure a
rayuwar shi haka?

Tana gama karantawa jikin ta ya hau rawa, ko ina na jikin ta bari yake, kamar zata mutu dan baqin ciki,
hawaye ne suke son zubo mata amma ta maida su, ta miqe da kyar tana dafe bango ta dau sauran kayan
ta ta saka, ta yafa mayafin ta, ta fita, takardar na hannun ta, Okashaou na jin fitar ta ya bude ya fita da
gudu ta window ya n hangen ta, yanayin tafiyar ta kawai zai sanar dakai tana cikin tashin hankali.

Tana shiga ta rushe da kuka, tana buga kan ta jikin bangon dakin nata, ji take kamar marar ta zata balle
dan ciwo, take ta fadi a wajen, cikin jiri, a daidai lokacin wata jibgegiyar mota me nunfashi ta shigo
gidan, Alhaji ne ya fito, shida Hajiya Babba, da Hajiya qarama, sai amaryar shi, take bangaren Hafsatu
sukaje suka ganshi kulle, yatsina fuska amaryar shi tayi,

"Dalin dama na fada maka wannan uwae yawon da kyar a same ta"

"A'a faa, ke din sau nawa kk taba zuwa? Kuma mutum aka ce baida uzurin kan shi sai na zaman gida?
Naga dai su biyu ne,"
Murguda baki tai, dan tasu da hajia Qarama ba wai tazo daya bane dama, akwai raini tsakanin su,nan
Alhaji yayi wajen Okashatou,shi kuma yana hango su, ya tattare komai kamar baya gidan ya kai toilete
ya rufe,

Alhaji yayi ta sallama yaji shiru, ganin ba wata alama da ta nuna akwai mutum a wajen, shima Alhaji ya
dauki hanyar wajen Hanee, ihun su Hajiya Babba ne ya sa shi daina tafiyar taqamar dayake yi, Hajiya
qarama.ce jibgegiyar ciki dama, ita ta dakko Hanee kamar jaririya, ta fito da ita, Alhaji na hango su bai
tsaya bata lokaci ba ya bude motar shi, yana ta salati, su Hajiya na salati, gaba dayan su, kowa salati yake
amaryar Alhaji ce kawai ke ihun jahilci na an shiga uku an lalace, yarinyar mutane zata mutu, Hajiya
Babba dake riqe da takardar da Hanee ke dauke da ita ne, kan su isa asibiti ta bude, ganin me ke jikin
takardar ne ya sata zubar da hawaye mai mugun zafi, tare da saka kuka, tana kiran,

"Shikenan ta faru ta qare, ya kashe 'yar mutane, mun shiha uku,"

"Ku bana son sakarci fa,ku rifen baki naji da abinda ke damuna, wannan lamari ba wanda ya san me ya
faru, indai ba shigar ku ta fada maku wani abu ba, in ba wanda yasan meke faruwa ku min shiru,"
Hajiya Babba da taga kowa hankalin shi bai kai ga abinda take wa salatin ba sai ta saka takardar a bra din
ta, ta kame bakin ta da mayafi, ta ci gaba da kokawa abin ta.

Da kyar likitoci suka samu nasarar tsaida cikin dake barazanar barewa, wanda a hasashen su sun hasaso
yan biyu ne take dauke da su, Alhaji yayi murna sosai, a dika yaran shi da shi ba mai yan biyu sai Hanee,
wannan babban abin farin ciki ne a zuri'ar shi, Allah yasa kar yaron nan ya saki yarinyar nan, ta kafa tarihi
irin.na Hafsatu, Allah yasa daga kan ta ya daina auri saki, addu'ar da Alhaji ke ta maimaitawa kenan, da
qudirin daga yau ya daina auri saki shima,in ma dan yaga yana yi ne shima.ya daina.

Kwananta shida a asibitin aka sallame ta, Hajiya Babba ta hana a sanar da iyayen ta, da dadin baki ta
nuna ma Alhaji yanda iyayen ta keji da ita, in suka gano aiki ne ya sa ta fadi haka, zasu iya cewa 'yar su ta
koma sai ta haihu, dan haka ta mai dadin baki a barta a wajen ta , har sai ta haihu, ita zata din ga kula da
ita kamar diyar cikin ta.

Alhaji ya aminta da haka, dan haka yace zai gayama Okashatou ko ta waya ne, kar ya damu.
Yara sun dawo suna ta jin yunwa,Habibu ne, ya masu dabarar jiqa garin kwaki, da sugar, da gyada, yaran
Hafsatu sun so a dakko soyayyen naman da suka gani a fridge a cinye,amma Habibu yaqi, yace Ummen
su ta hana daukan abinda ba a bama.mutum.ba.

Dole d safe Okashatou ya siyo masu koko da qosai kamar zai kuka saboda a qalla saida ya kashe 1500,
har da sugar tinda ba siya yake ya aje ba.

Hafsatu bata dawo ba sai a washegarin da aka kai Hanee asibiti, ta dawo kuwa cike da farin ciki, dan ta
san abinda ta qulla ko bai tabbata ba, daga sanda ta sa qafarta gidan zai tabbata..........

*Hummmmm in ana sallah ba a magana, banso.na tsaya anan ba, yanayin jikin ne sai shukran,bana son
na aje ku kuna jira sai dole*
[11/12, 11:52 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH

Page 17:
Ko da ta shiga bangaren ta yanda taga yaran nan sun maida gidan kawai ya tabbatar mata wannan uwar
tsaftar bata nan, wani dadi ke ratsa sassan jikin ta,n nan da nan ta dau waya zata kira auntyn ta, sai
kuma ta fasa, tace bari ta tabbatar da zargin ta, Okashatou da tinda ya aikata abinda ya aikata yake
kwance a dakin, dama shi ibada ba wai ta dame shi bane, balle ace, haka ya kwanta uzurin shiga toilete
kawai ke miqar da shi, gaba daya jikin shi ya sake,dakin kaca2, yake ganin shi, kwana daya kacal, da batai
ba a gidan yaji gaba daya kamar ta shekara daya ne, zuciyar shi na raya masa me zai sa ya SAKI Hanee?
Me ta masa? Wata zuciyar tana ayyana masa kayi daidai wayasa tai ciki? Daga zuwa ko morar ta bakai ba
zata fara zube maka kajin yara itama, haba kai kasuwa ne? Kayi daidai kar ka wani bi ta, yana nan
shame2 ta leqo, hade da sallama, tana wani fari da farfara, ta saka kwancen kayan yayar ta, da suka
mata yawa, dan ita akwai ci da sha da qoshi a gidan ta ba kamar nan ba, (bance kwancen kayan yayu ko
qanne haramun bane, kar naji a gaba ana cewa......🙊😄) tana ganin yanayin shi t saka dariya a hankali ta
toshe bakin ta, an kuma kenan, dan indai ya saki matar da ta shiga ranshi sai ya kwana uku ko biyu
kwance,yana tinani, amma in dama bai damu da ita ba ko a jikin shi.

"Ah Abban su, ashe kana ta nan na je wajen Hanee mu gaisa ban gan ta ba, nazo nan ma ban ganta ba,
ko dake wata qila nai saurin fitowa ne tana qurya,bari naje mu gaisa na dawo musha hirar yaushe
gamo,"
Ko ci kan ki bai ce mata ba, sai ma gyara kwanciyar shi da yayi, nan ta hango hawaye kwance a fuskar shi,
gaban ta sai da ya fadi, hawaye fa ta gani, tabbb, ashe Allah ya taimake ta da ta fidda ta, irin aannan
soyayya haka.

Bamgaren Hanee taje ta bude, Habibu na shara, ga dai wajen nan,ba wani datti sosai, amma ba kamar
yanda in tana nan ba, qalqal, leqawa tai ko kula shi batai ba, tana tafe tana hura hanci tana lelleqa ko
ina,

"Ina kwana Mama,"

"Hmmm iyayi, harda wata Mama da wani gaisuwa, ina uwar taku take?"

"Ummee bata nan, tinda muma dawo school jiya bamu gan ta ba,"
Dariya ta dan yi can qasan maqoshi tace

"Ina zaka gan ta yaro damaaa"

"Na'am? Mama dani kk?"

"A'a ni nace maka me? Matsa ka ban waje, kare2, tin kana tsimma uwar ka ta barmin kai, shine yanzu
wai dan kana butulu, shine har wata Ummee kk ce mata, kana sinne kai in tana maka magana, zakaci
ubanka ne, dan daga yau kun dawo wajena, zan maganin ku matuqa dikkan ku, kuke kallona kamar an
tsoma bera a barkono, matsa na wuce mara kunya,"
Ta bangaje shi ya fadi qasa, akan tsintsiya tako cake masa tafin hannu, ya sa qara, dan zafi, tai ficewar ta,
da kyar ya cire, abun na ta mai zugi, amma shine babba haka.ya ma qannen wanka, ya mata wanke2,
nan sukai fess, ya taya su.homework, da dik abinda ya ga sun saba da ita, ga shi dayan rana tayi hantsi ya
fara duban luddai, sai hamma suke.

Cike da qasaita take takawa, tana kallon gidan, yanzu ta dawo kamar sanda ya auro ta, ita daya ce matar
shi, bawadda ta isa ya aura tai sharing din shi sannan tai sharing gida da ita,ya gama leqe2n shi, da ita zai
mutu ita daya jallll kamar nama daya a miya.

Tana komawa wajen shi taji wajen a qarqame, ta leqa ta window ta ga bama.ya nan, to tana ina ko
tashin mota bata ji ba?bala'i, dama aunty tace a mata na mallaka, ta tsaya shirme, gaskiya da sakel,
akwai wani aikin gavan ta.

Bangaren ta ta koma tana cika tana batsewa, Nour tasa ya tafasa taliya uku, ta yaryada masu mai da
gishiri, sai dan yaji, tace suci, gaba daya sun mance da yaran bangaren Hanee.
Su Alhaji da Malam sin gaji da shan yunwa,Sabir yayi kuka shi da Khaleefa har sun gaji, Habibun ma
daurewa yake, ga ba wanda ya damu da zuwan su makaranta, dama sun je ne, wata qila da sun san cewa
a can suke dole sai sun dawo zasuci, amma suna gida suna fama da yunwa😭, tattare su yayi suka tafi
wajen Hafsatu, tana kwance ta daura tsohon zanin ta na zaman gida, tana kallo kamar kullum, tata
taliyar harda dan kifi, ta marmasa.

"Kaiii kaiii meye haka, dalla malamai ku tsaya daga nan mana meye na shigo min haka yuuuuu kamar
qudan zuma?"

Riqe hannayen qannen shi yayi, ya tsaya yana kallon ta,

"Meye? Ba an maida ku can ba?"


"Yunwa muke ji mama, kuma naji dazu kince zamu dawo wajen ki, tinda Ummen mu bata nan,"

"Kaji min munafukan yara, da wani na nan sai yace haka na fada (tana tsoron kar wani yaji kalaman
yaron ya ce ta fadi hakan, kunsan fa akwai matan da ke murda magana, Allah ya kyauta) ko da kuka zo
bana dafa taliya nace a ba kowa ba? A gajiye na dawo nima, kuma da za a kaiku can ba ba mahaifin kune
yayi umarni ba? Sai ku bari ya dawo yayi umarni a maido ku nan tukunna, ku bacen da gani,"

Da gudu habibu ya saki hannin su ya koma ya na ta kuka irin mai cin rannan, da takaici, ga yunwa yana ji,
Okashatou da ya sako hancin motar shi a lokacin, me gadi ya wangale qofa, leda ce a hannun shi, yaci
abincin shi waje, ya dawo dana dare, yana gama parker motar ya je inda ya ga Habibu ya nufa da gudu,
ya riqe hannun Sabir,dake ta matse hawaye shima, Alhaji kuwa dama shine sarkin mita sai kuka yake
yana kiran shi yunwa yake ji.
Okashatou baya son magana sam, nan ya gane me ke damun su, kawai ya basu ledae ya koma wajen shi,
Sabir zai bi shi ya daka masa wata muguwar harara ya sake mai hannu ya je wajen su, Habibu da suka
rife qofar wajen nasu, sai murna suke, Sabir ya fisu murna yau Abban su har riqe shi yayi.

Wata qatuwar kaza ce, da fresh milk, da shinkafa, da miya, a abun take away, murna sukai tayi, Habibu
yace kar wanda ya taba vari ya dawo, flask ya dakko ya raba biyu,ya boye rabin, ya aje masu sauran yace
suci, aiko suna bismillah suka hai abinci da duka, sukai tass, suka kora da madara.

Suna gamawa ya ja kunnen su, kan karsu sanar da kowa meke faruwa, in yaji sun fada sai ya fadama
Abban su kar ya sake kawowa, aiko, gumm sukai, harda masu kama leven su, akan bazasu fada ba.

Ya kai flask kitchen ya aje, ya sa sukai alwala sukai sallah, sai baccin rana.
Bayan farfadowar Hanee, taqi yi ma kowa magana, saboda mamakin abinda ya faru take ta yi, me
kenan? Sai da ya gama biyan buqatar shi d ita, lafiya lafiya, kawai ya rubuta mata saki? Wane irin haline
da Okashatou, ashe Abban ta yayi gaskiya daya ce yaji qishin2n yana da auri saki, wasu hawaye ne masu
mugun zafi suka fara sauka mata, yau ta shiga uku,bai barta ma ta cika shekata sha takwas ba ya maida
ta qaramar bazawara, wayyooo Allah wazai aure ta yanzu, ga ciki, yanda yai qaton nan wataqila ma
namiji zata haifa,dan ance wai shike girma sosai, ( a nata hasashen kenan).

Hajiya babba ce ta shigo ta gan ta a wannan yanayin, girgiza kai tai ta taka wajen ta a hankali ta furta,

"Allah ya kyauta"

Dafa kafadar ta tai, inda ta juya ta kalle ta, tare da dake rushewa da kuka sosai,
"Umma Hanee hakuri zakiyi da wannan lamarin daya faru, kinji, kiyi magana ba kuka ba,ki sanar dani me
ya faru, ko na san ina na kama, yau satin ki daya cif gidannan kinqi cewa kowa komai, ba wanda ya san
me ya faru daga Allah sai mijin ki sai ke sai ni,"

Da sauri ta kalle ta, suna nufin basu sanar da su Amma va?

"Ammana da Abba na fa?"

"Hanee kiyi hakuri ban fasanar dakowa ba, saboda ke din na dauk ki kamar 'yr dan haifaacikina, kinajina,
dan hak ki kwantr da hnklin ki, sai nabi diddigin wanna yawan ake2n aure nashi, a qananan shekaru irin
na shi,"

"Amma in su Ammana na son ganina fa?"

"Nasan yazan da wannan bangaren banni da su,"


"Ina son roqan alfarma ko Alhaji ki sanar ma, a qalla a nan a sani, shi rife sakin aure baida afanu, saboda
haramun ne ma, ana son ashaida,"

"A nan kam kin fini gaskiya zan sanar da Alhaji, da Hajiya qarama,zamuja baki muyi shiru, a dau mataki
ba tare ra tashin tashina ba, yanzu Huwaila zata kawo abinci, ki zauna kici, 'yar auta tace, yawancin
matan sunyi aure, maza ma haka, sa'o'in naki, basu da yawa, sai maza, sai wanda suka girme ki mata, ai
naga suna leqowa gaida ki, ki zauna da kowa lfy kinji?"

Daga kai tayi, Huwaila tai sallama, ta kawo abinci, tana murmusi, ta mata godiya ta amsa, nan suka fita
suka bata waje dan ta ci.........
*NIMA a nan na gaji, sai zuwa sandana sake samun dama inshaa Allh, ban alqawari za a samu nan kusa
ba gaskiya, musamman zanyi baqi*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
*Masoyan AURI SAKI na gode sosai da uzurin da kuka min, yau ga shi zan ci gaba da maku typing
mamana d yayata sun tafi😭😭 Allah ya basu ladan zuwa dubiya daziyara, zuwan su helps alot gani garau
kamar ban kwanta ba💃🏻💃🏻 Godiya ta tabbata ga Allah💃🏻 and na gode maku kuma da addu'o'in da kukai
min da mahaifiyata, Allah ya bar mu tare domin shi.❤*

Page 18:

"Wai ni Amma kuna waya da Aunty Hanee kuwa? Na yi wajen sati biyu kullum na tambayi Abba sai yace
takira sun gaisa, ni ma dan Allah a sai min waya,tin da kin hana yawan zuwa, ban kuma san dalilin ki ba,"

Abba da ya fito yana sake gyara karin hular shi ne ya kalli Amma dake goge mashi takalmi, suka hada ido
yasakar mata murmushi, itama ta mata nata mai kwantar masa da hankali, ta miqa masa dadai qafar shi,
ya saka, y dafa kan ta, ya dago da fuskar ta, ta kalle shi, maganar Ammar suka sake ji, Abba bai sake ta ba
sai da yayi kissing goshin ta, ya sa mata albarka, tare da shafar gefen kuncin ta,

"Abbaaaaa, plssss mana, ka sai min waya,Amma bata son muna yawan ziyarar Aunty Hanee, kuma ni ina
missing din ta,"

"Me too"

Ta fito tana wani rangwada, ta daura dankwalin Amma, wai zafi take ji da sassafe, suna hutun
makaranta, tana wani fari,daturo baki, ita adole a dauke ta seriouse, Abba ne ya hade su yarungume,
sannan yaja kunnuwan su, sai da sukai qara,

"First of all yau a cikin ku wa ya gaida ni ko Amman ku?"

Saukar da ido qasa Ammar yayi cike da kunya, for the first time a rayuwar shi tin da ya girma yayi wayo
bai taba missing gaida iyayen shi ba,sai dai in Abb ya fita da wurwuri an kawo kayn u, shima in ya dawo
sai ya gaida shi, uwar iyayi kuwa kama goshi tayi, tai fari, tare da rausaya qugu tace,
"Subhanallah, i am so sorry Abba, Amma, gaba daya mun manta, coz ni dai jiya da kyar nayi bacci ina
tinanin ko wani abu ne ya samu Auntyna ba ku son fada mana i am having bad feelings whenever i think
of her 😭,"

"Shhhhhhhh come here baby, ba abinda ya samu auntyn ku fa, she is perfectly alright, kawai ta koma
gidan surukan ta da zama ne, shiyasa bana son kuce sai kun je,"

"But why, Abba?"

Amma ce ta kalle ta tace,

"Saboda daga sanda aka ma mace aure, tana da iyaye biyu kenan,ta zama 'yar gata, ga asalin mamar ta,
ga maman mijin ta,in maman mijin ta taga ta kusa haihuwa zata iya ce wa a dawo da ita wajen iyayen ta,
sannan zata iya cewa a kai mata ita ta kula da ita, haka akai ma Hanee, kin gane?"
"Na gane, amma Aunty bata da wayo, inni ce ita wajen Ammana zance akawo ni😏 "

Dariya sukai dikan su,

"Inna biye maku ba inda zani yau, sai n dawo, i love u all, Allah ya kare min ku,"

"Allah ya kasance tare da kai, a koda yaushe, we love u too,"

Amma bin shi tai, har qofa, suka dan taba soyayyar su ta dawo,cikin son mijin ta uban yaran ta.

(Shin kin kai shekara 30? 40? 50? 60?....kina da miji? Yake 'yar uwata mace,indai ke mace ce, kuma kina
da aure, ki sani, yanda kikai sako2 da riqon mijin ki haka zai sako2 da riqon ki daga aikin shi har zuciyar
shi, amma in kk kula da shi, kk tattala shi, kika girmama shi, a kullum, ya tabbatar kina bashi matsayin me
gida, ba mijin tace ba, wallahi zai zama maki mijin kan tace, domin mata na kuskuren dole sai kema kin
bada labari ko kin nuna ma qawaye a idon su kin mallake shi kina juya shi, sai me? A wajena ni Hamida
kin zama mara aji, mai kwaikwayon abin banza,bari kiji birgewa sister, birgewa shine,aga kina bin
umarnin mijin ki,yana bin naki, a ga in yace maki dakkon.... kan ya qarasa kin isa at his service, daya
qarasa kin aikata, cikin nutsuwa bada rawar kai ko qafa ba,a ga da kin ce masa, Honey ina son..... aga
idon shi dakunnuwan shi sun bazu akan ki, zuciyar shi na sauraron ki,in abun kudi ne,aga kina furta ina
son.... hannun shi a aljihu, ya zaro kudi ya miqa mki ba tare da yatsaya bin diddigi ba, wannan shi ake
kira mallaka, ku mallake juna,ku maqalqale juna, ku guji bacin ran juna, bada girman kai, da ganin, ke
uwar garke ce, kin girma kin tafasa baki tsoron qauri, mata a kula,"
Huwaila da Hanee ke ta tattakawa acikin gidan, yamma tayi kowa na nan, 'yammata da samarin gidan an
dau wanka, ana ta hira group group, duk inda suka wuce, ana gaidata, in taga manya ne ko da ba
Okashatou ne babba amma sun girme ta sai ta duqa kadan ta gaida su, tashiga ran kowa sosai, tana basu
sha'awa yanayin ladabin ta, ga kuma uwa uba kyau,da tsawon gashin ta da ko ta sa adankwali sai ya
nuna ita mai gashi ce.

Wasu a 'yammatan na kishi da Huwaila, ganin tafi sakewa da ita kadai,amma ba su baqin ciki, sai dai suji
dama sune.

Haka suke yi kullum, tayi kyau sosai, ta yi mulmul, sai qaton ciki a gaba, fatar ta sai sheqi take, kullum
abinci mai rai da lafiya ake bata, ga kunun gero, da tuwon gero datake ci, ko amata biskin shi, saboda
Hajiya babba tace tana son tai kwari sosai jikin ta ya zama zai iya jurar wahalar haihuwar biyu b tare da
shan wahala sosai ba, a kullum da zuma mai kyau take karyawa ta kora da ruwan zamzam, sannan
dabino, kafin a bata kome zai biyo mai dadi taci, taso Amman ta ta gan ta a haka, yanda tai kyau, tai
qiba, dan tana yawan tsokanar ta ba zatai qiba ba a yanayin sirantar ta.
Wayar ta ta dauka ta kira,Amma na dauka Ammar ya amshe, ya hau gaida ta, yana ta murna, itana
murna tayi tayi, sannan ta mai kwatancen gidan, suka gaisa da Zee, suka gama hirar su, ta kashe cike da
kewar su, tana son taji ya su Habeebu suke amma ba hali, bata san ta ina zata fara ba, hawayen son
yaran da kewar su ne ya gangaro mata.

"Subhanallahi, kuka kuma? Me kk so baki sanar dani ba, Hanee na dauke ki kama diyar dana haifa a
cikina, ban taba baki banbanci da diyar cikina ba, ki fadan mene ne matsalar ki?"

"Hajiya ba komai kawai ina kewar su Habibu ne, ko suna zuwa makaranta? Ko sun dakatar? Ko ya maida
su wajen Hafsatu. Ban sani ba, amma tabbas na san suna da tarin tambayoyin ina nake, ban masu adalci
ba da ban gansu ba a qarshe,"

"Kar ki damu, sun rasa iyayen da suka haife su ma matan balle ke, ko dake ke kulawar da kk basu ta
daban ce, dan hankalin ki ya kwanta gobe zan je, zan duba maki su,"
Cike da jin dadi, kamar ta rungume Hajiya haka take ji, sai zuba mata godiya take, nan ta fra tinanin me
za a kai ma yaran, Hajiya ta gane, tai dariya tace,

"Kaza mai yara, karki damu, nasan me zan kai masu,"

Tana dariya ta miqe da kyar ta zaga.

Washe gari as promised, ta debi kayan tsaraba, dangin biscuit, chocolate, da sweet, ta saka a babbar
leda har bakin mota Hanee ta bita tana bata saqon da zata fada ma kowanne yaro, har ta gaji da amsawa
tana daga kai kawai, tana dariya,haka suka fice, kmr ta bisu, sai da suka tafi ta juya zata shiga ciki ta gan
shi, jingine a jikin ginin dakin samarin gidan, da gani daga bacci ya tashi, me yake a anan?

"Hanee gidan su ne, ko kin manta ne,"

Zuciyar ta ce ta kitsa mata hakan, da sauri2 ta fara barin wajen, zuciyar shi har wani gudu take, a bayan
ta,amma ba zai iya bin ta da qafafun shi ba, yanda yaga tayi mazaunai sosai yanzu yake mamaki, da
yanda qirjin ta ya cika kamar ba ita ba, ba dan ya san ta sosai ba zai ce ba ita bace, wani yawu ya hadiya,
kauda kai yayi, dan ya dade yana zuqa gidan, ya labe yana kallon ta, ba tare da ta sani ba, Huwaila ta
jima da sanin hakan, amma dan kar ta cire mata jin dadin zaman gidan yasa bata fada mata ba.

Tana shiga parlourn ta kwanta a kujera tai luf tana maida nunfashin saurin da tai, rufe idon ta tai, tana
tinano irin soyayyar da suke zubawa, d yanda take hakuri da halayen shi, da wahalhalun da tai na yaran
shi, da son yaran shi da ya dasu a zuciyar ta, dakin da aka ware mata ta miqe ta shige ta saki kuka mai
daci, Allah shine shaida akan son da take ma okashatou, ranta da gangar jikin ta na tsananin son shi,
kyaun shi ba kowacce mace bac zata jure rashin ganin shi, Okashatou na da matsanancin shiga rai, ga
duk wanda ya fada tarkon son shi, mutum zai ji kamar zuciyar ba tashi bace, ta Okashatoun ce, qirjin ta
ta dafe, ta dade bata ji abinda taji ba a yanzu, ganin shi ta tono mata ciwon dake ran ta.

Ji tai kamar an gogi qofar, ta na budewa kuwa yayi kamar zai fada kan ta, tai baya kamar zata fadi ya taro
ta, kyakkyawar runguma ya mata a qirjin shi, tai luf, kamar 'ya a qirjin uwar ta,har wata a jiyar zuciya mai
qarfi da shessheqa take saukewa, wani tinani ne ya zo mata zuciyar ta, da kuma jin yanayin Okashatoun
a rungumar da ya mata, nan ta tina ya fa sake ta, da sauri ta ture shi, ta danne qofar, ta kifa kai a jiki tana
kuka,

"
Me ya dawo da kai? Ko dake ba laifin ka bane, da ban bari an ajeni gidan ku ba da baka da damar da zaka
ganni, nayi kuskuren qin sanar da iyayena sakina da kai, sakin wulaqanci, sakin da in wani naka akaiwa
na tabbata sai ranka yayi ciwo, irin sakin da kamin. Ko a mafarkina ban taba ganin irin shi ba, Okashatou
ka cutar da soyayyar danake mata, ka ci amanata, ba komai, na barka da hukuncin da soyayya take ma
masoya."

Da gudu ta bude toilete ta shige, yana tsaye nan, Huwaila data kawo mata abinci, da fruit dik ta ji kuma
ta ga me ya faru, hawaye ta share, ta aje kan dinning ta juya ta fice,Okashatou, ya rufe idon shi kwallar
data taru ta gangaro masa, a rayuwar shi wannan ne karo na farko daya saki mace har sati ya wuce yana
damuwa, damuwa kuma ta gaske,gashi har ana neman wata daya ya kasa manta ta, illa ma wani sabon
son da bai mata ba na farko ke sake tsaga jikin shi yana shiga, Okashatou Hanee ce mace t farko da ta sa
har yake kula da yaran shi, yake tsayawa yaji damuwar su, dan tafiyar ta ya na kula da su fiye da tinanin
me tinani, sai ya kula a hakan ba abinda yake qare masa kamar yanda ya zata rowar dayake ita zata qarar
da arziqin shi.

Hafsatu sokuwa gani take asirin ta ne ya ci, ya sa yanzu yake sakar mata kudi, kome take so yake mata.

Barin wajen yayi ya nufi wajen alhaji, dan yana son suyi magana mai mahimmanci a yau ba sai gobe
ba..........
*hummmm yaro ka daina ma wannan tinanin, dan yanzu munfi qarfin ka, ko me kuka ce?*

*Innaji sharhi da comments da suka gamsar dani anjima ma zan sake mai yawa😄 in kukao shiru nima na
lahe gobe ma ban yi🙄*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
*This page is for u Mum manal, kwailan zakin ta😄🙊 many many thanks to u, may Allah reward u with
jannah, Allah ya raya zuri'a ya sa kuma ta zarce*

Page 19:

Ya jima yana kwankwasa qofar kan Alhaji ya bude, yanayin yanda Alhaji yaga dan nashi ya matuqar
girgiza, hawaye shabe2, kuma fuskar nan tayi jawur, ga hancin shi kamar me mura, me kenan?
"Pls come in, what happen? Dik abinda ke damun ka d gani ba qarami bane,"

Okashatou ba baki sai kuka daya sake saki qasa2.

Hajiya qarama ta fito tana taqamar nan ta ta, ta kalle shi, itama sai taji gaba daya ta ji ba dadi, me zai
sashi kuka haka?

"Okashatou ko wani ya mutu ne,"

"Alhaji dan Allah a maidan mata ta na wuce da ita yau,"

"Lallai baka da hankali, ka saki matar da ciki, tin da nake sake2 na ban taba sakin mace da ciki ba,kuma
na sha gaya maka, duk randa kai hakan zakai dana sani, to wannan ce ranar, sanan ni ba shawarata bane
aje ta anan, sai ka jira uwar taka ta dawo ka fada mata kaji ya zaku waye, b ruwan dik abinda ta maka,
zan so a maida maka ita, dn kuwa kome kayi ina da kamasho, laifina ne,"

"A toh da dai ya fi, dan hukuncin komawar ta na hannun ita kan ta da kuma Hajiya Babba, komi zamu ce
in basu amince ba ba zai samu ba,"
"To ni na ce na maida mata ta, dan Allah ku ban ita na tafi kan ta dawo,"

"Kaii ina da abin yi tashi ka fita,in ta dawo kunyi magana, karmu batawa juna lokaci mu da kai,"

A tare suka miqe Alhaji da Hajiya Qarama suka shige daki suka barshi nan zaune, ya rabka tagumi, me ya
kaishi ma sakin ta da?

Jiki ba kwari ya miqe, ya fita, motar shi ya shige dake wajen gate din gidan, kar Hanee ta gani ta san ya
zo, bai zame ko ina ba sai gida, bangaren shi ya shige ya kulle, ya fada gado, gaba daya yanzu zuwa
asibitin ma dan yana daya daga abinda yake qauna ne, da ba zai ba.

Hajiya Babba na hango, bangaren Hafsatu, suna ta hira, da dikkan alamu sun dade suna maganar,
"Ai nake fada maki kawai haka za ai, ni kaina yarinyar nan ta matsa min zama kawai nake da ita akan
dole, amma bana qaunar na bude ido na gan ta a dakina, da sunan tana zaune wai sai ta haihu, duk
wahalhalun haihuwa na nan na jirana,"

"Ai tin farko da na san zai sake ta ta zauna wajen ku da wanda zai kada ta wani wajen zan mata bayan ya
sake tan, amma ba damuwa, lokaci bai qure min ba ai,"

Gaban Hajiya Babba ne ya fadi, lokacu bai qure ba?

"Kin san me za ai? Kar ki damu kawai, ki bar komai a hannuna, ni zanji da inda zamu hankada ta, saboda
kar a zo ana zargin ki, yanzu haka idon mutane a kan ki,"

"Koh?"
"Sosai ma kuwa"

"To shikenan, na bar komai a hannun ki,"

"Bari na tafi na jima, kar a fara sani zargin kin san mutane,"

"Haka ne, bari na leqa wadancan yaran,"

Har bakin qofa Hafsatu ta raka ta, cike da murnar Hajiya Babba ma bata son Hanee, ashe komai zai zo
mata da dauqi, da har hankalin ta ya tashi data kama ta tana waya da Auntyn ta ta kd, akan sakin da ta
sa akaima Hanee,sai da Hajiyan ta nuna mata ai tayi daidai, itama dama bata son Hanee dan ta kula
Okashatou yana tsananin son ta, ya bar kowa sai ita.

Yanda Hajiya Babba taga yaran ta tausaya masu, domin sun sanar da ita irin yanda Hafsatu ke basu
abincin ganin dama, da kuma halin kewar Ummen su da suke ciki, dudduba wajen nasu tayi, taga a fridge
akwai nama, da wasu kayayyaki da za a iya ci, kiran Habibu tayi,
"Kai in banda sokon me gidane kai ga kayan ci a nan sai ku zauna da yunwa kai da qannen ka?"

"Ummee ta hana daukan abinda ba namu ba,"

Jinjina irin kyakkyawar tarbiyyar da Hanee ta ba yaran tayi, sannan ta ce,

"Na san inda Ummen ku take, ita ta aikoni da wannan,sannan tace kuci komai na ci data aje dama dan ku
aka ajiye,"

Ai nan take Sabie ya riqe ta yana kukan sai ta kaishi wajen Ummen shi, Alhaji ma mai dan dakiya sai da
ya koka, da kyar da sidin goshi ta lallashe su, tare da masu alqawarin in sukai shiru ba su sanar da kowa
ba ta kawo masu wani abu, ko ta san inda Ummeen su take zata dawo masu da ita bayan ta haihu, nan
sukai ta murna, kusan da kwalla ta bar wajen nasu, taso ta duba ko Okashatou na nan ta share, dan
yanzu haushin ganin shi take.
Bayan Hafsatu taji tashin motar ta, ta dakko waya zata kira auntyn ta, sai ta tina Hajiya tace ya zama sirei
tsakanin su, kar magana ta fito ita da Alhaji su samu sabani, ta jira tsammani, zata mata aiken maganin
da zata ba Okashatou, dan ya cire Hanee a ran shi kwata2.

Ihuuu ta saki ta na taka rawar jin dadi, yara na kallon ta,ta ce masu,

"Kai Ishaq kunna mana kidan nan na gwanja mu cashe,"

Bayan ya gama saita komai ya kunna ita da yaran suka dage sai tiqar rawa suke, ba babba ba yaro, sai da
sukai mai isar su ta sa su dora girki kamar kullum, ko nace kwaba, tinda dama tana nuna masu ya zasuyi
ne da za ai mai kyau da tsafta, amma inaa.

Shinkafa ce fara da manja, da yaji, bayan yanzu Okashatou yana kawo kayan miya, amma sai ta mai kiya
iya shi, da naman in zataci nata ta saka.
Ana gamawa taje rabawa, kamar kullum wata qaramar roba ce irin yelluwar nan ta Maggi, mai murfi, da
almajirai ke yawo da ita, ta zubama su Habibu, ta kira Nour ya kai, sai masifa yake shi ne fa babba amma
sai ana aiken shi wajen yaran can, suna son su zo ta hana da suna nan da basu dau abin su ba.

Ya dade yana kwankwasa ba su bude ba, sakamakon tattare kayan da suke ci da Habibu ya sa su yi,daya
gaji da bugu ya dire masu a wajen yayi gaba, koda Habibu ya leqo yaga abincin kawai ba kowa ya dauke
ya shige, suka dakko miyar da Hajiya ta fidda masu ta sake ba qanqara amma da sanyi, suka zuba da
nama suka ci, sukai qat, ya boye kayan da Hajiya ta kawo masu a dakin Ummen su, ya ce da safe
zasuna.tabawa, tinda wataran.mantasu take, kuma in sun tambayi Abban su ta zane su, wanki sai dai
Habibu ya musu sika, Malam na dan tayashi dauraya, Habibu dai ya koma uwa da uban su, sai abinda
Okashatou ya ga dama ya kai masu, tinda Hafsatu tayi rantsuwa ta gama riqon su.

"Sannu da dawowa Hajiya, ya su Habibu?, sun tambayen, Hajiya kinga alamar suna kewa ta?, Hajiya ya
kk gan su, akwai alamun wahala a tare da su?"

"Hanee zo ki zauna,"
Zama tayi cikin qagautar taji meke faruwa,

"Hanee akwai magana dana ke son muyi dake, zuciyar ki na da girma, ma'ana akwai so da qaunar kowa a
cikin ta, ina son ki qoqarta ki rage hakan akan yaran nan, da kuma abinda kk dauke dashi, saboda
yanayin yau, kin dai ga irin hali na mijin ku, iyaye. Yaran nan na asali har fa sin gaji sun daina zuwa,
saboda Okashatou ya iya rashin mutuncin da ke kan ki har yau baki san iyakar shi ba, balle ki tinanin ba
zai maki wani abun ba, tinda baki tsira daga dabi'ar sakin shi ba, ina fatan abin da nake fada maki yana
shiga zuciyar ki yana zama?"

Daga kai tayi ta share hawayen dake gudu a kuncin ta, ta tabbatar ta rasa yaran da ta sawa zuciyar ta son
su, wata qila Okashatou ya maida su wajen Hafsatu, ko ta maida su akan halayen su, munana na baya,
wataqila ma sun daina zuwa makara tar da ta sha wahala ta sa a saka su, gaskiya sai Allah ya masu hisabi
da Okashatou.

Kamar Hajiya ta san tinanin da take ta dafa a tana.murmushi tace,

"Yaran ki na nan lfy, na ma basu izinin amfani da kayan fridge din ki, na kuma kai masu kayayyakin da kk
ce,sannan kuma suna zuwa makaranta, sun yi hutu, anyi jarabawa,da dikka alama zasu samu nasara,
suna kewar ki, da kyar muka rabu da autan ki yana ta kuka zai zo, amma na bashi hakuri,"
Hanee kukan dadi kawai take, bata san irin son da take ma yaran nan ba, wataqila soyayyar mahaifin su
ce ta shafe su, ko kuma tsananin tausayin su, datake, ganin haka yasa hajiya ta tina hirar su da Hafsatu,
dan haka tace mata.

"Hanee ya kamata ace ki qara akan ibadar dana san ki da ita, domin ban taba ganin yarinya mai tsananin
ibada kamar ki ba, ina son ki ninka akan na da, zama dake ni kaina na koyi abubuwa da dama, Allah ya
miki albarka, ya sauke ki lfy.

Ta dan ji wani tsoro ya dan shige ta kadan amma ta daure ta amsa da Ameen.

Sun dade suna hira aka kira sallah suka miqe suka je yin sallah.

Bayan sallar isha'i, suna cin tuwo, da Huwaila sukaji sallamar shi, sai da ta kware, sosai, take ta tari,
kamar zata fiddo maqogwaron ta, ruwa ya tsiyaya a cup yama Huwaila nuni da ta fita,da ido, ranta bace
ta bar wajen,ita ko idon ta rufe tana ta tari, da kyar ta furta,

"Huwaila ban ruwa, ki rufe mana qofa,"


A zaton ta muryar Okashatou data ji,yana parlour, dan taji harda qamshin shi kar ya shigo, bude idon
nan da zatai suka hada ido, aiko zaro idon tai gaba daya waje, me yake anan, cikin dakin ta, ko dake
dakin gidan su whatever,me ya zo yu har ciki, ya wani dau wanka, ga qamshi yana bazawa, idanun sh sun
kada sunyi jawur, yana qara matsawa ta ja baya itama, tana zaro ido waje, ga tarin yaqi sake ta,

"Karba ki sha mana,"

Cikin wata muryar da bata san yana da irin ta ba yayi maganar, wani abu taji ya tsarga mata har marar
ta, ta ko sake qara, Hajiya da ta bazamo sakamakon sanar da ita da Huwaila tayi, tana jin qarar Hanee ta
isa da gudu, ganin shi gaban ta daf sosai ya sa ta dauke shi da mari, ranta a matuqar bace ta nuna masa
hanyar waje,

"Fita waje mara mutunci, FITAA NACEEE,"

Okashatou da fuskar shi tayi jawur saboda bacin rai, da kuma takaicin marin da ya sha, rabon shi da duka
ai ba zai iya cewa ga shi ba ma.
Cike da fushi ya miqe ya fita, har ya kai waje ya dawo, Hanee na ta kuka, taji zafin marin da akai masa, ga
wani ciwon son shi daya fama mata , ga wani takaicin shi da haushin shin abinda ya mata, komai ya hadu
ya mata yawa, bama ta san ya zata ji ba, ba kuma tasan me take ji ba, kuka take sosai, ga muryar ta ta
dashe da kwarewar da tai, sun zaci komai ya wuce suka ji shi a bakin qofa....................

*Allah ya sa Hajiya ta dakko muciya dan nema mai kan buta*😡

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*Thank you sisters, lfy ta qalaou jiya, Kebbi state jiya mun samu matsalar wuta ne, shiyasa bakuji ni ba,
amma lfy ta qalaou, na gode sosai da kulawa Allah ya bar zumunci*❤

Page 20:
"Me ya dawo da kai? Banace ka bar nan ba, ka tafi kar ka sake dawowa ka takura mata, Okashatou baka
taba ganin bacin raina ba kar ka sa na bata rai da kai, kace baka son ta ka sake ta, me ye hadin ka da ita
yanzu?"

"Hajiya ni bance bana son ta ba, ina son mata ta, kuma indan na sake ta ne, to na maida ta shikenan?
Dan girman Allah ki ban mata ta mu tafi, ita kan ta tana so na"

Jin kalmar "ina son mata ta," sai da ya sa qirjin ta bugawa da qarfi, a gaskiya ba zata yi qarya ba a duk
sanda ta ga Okashatou tin farkon haduwar su har yanzu dayake gaban ta, kullum son shi qaruwa yake.ba
raguwa ba, dik da abinda ya mata kuwa, dik yanda taso ta ji haushin shi ta daina son shi ta sanar da
iyayen ta gaskiyar lamari sai ta kasa, jin ya furta itama tana son shi ne ya sa ta maza ta hade fuska sosai,
taqamar shi kenannnn?

"Waya fada maka ina son ka Okashatou? A da kam ina son ka so mai yawan da ban san iyakar shi ba,
amma daga sanda kamin sakin wulaqanci, sakin da ko macen da kk qi ba zakai ma irin shi ba, daga ranar
ka janye soyayyar ka a raina, da kk maganar ka maida ni to ni nace ban maidu ba, sai ka dauken aka ka
maida ni gidan ka,"

Zuciyar ta na tsananin bugawa take maida masa da maganganun nan, saboda rashin kunya ba sabon ta
bane, musamman ga mijin auren ta,

"Kaji me ta fada maka sai ka kama gaban ka,mara kunya,"

"Hajiya na rantse qarya take, tana so na, bacin rai ne kawai, dan Allah ki bata hakuri, hajiya ke daya nake
da ita a matsayin uwa da zata sa kuma ta hana,"
"Hakane akan komai kana min biyayya amma banda zancen auren ka, Okashatou ya mukai da kai lokacin
da zaka auri yarinyar nan? Me kace mana? Ba cewa kai ita ta daban bace ba zaka rabu da ita ba? Me ya
same ka har ka rabu da ita yanzun?"

Kuka ne ya kwace masa, sai da ya kai wajen second goma yana yi, tare da duqar da kan shi sannan ya
dago yana kallon Hajiya da Hanee wadda ta dade da jiqewa da hawaye, tana tsaye jikin window, ta
jingina kan ta tana kuka, jin tambayoyin hajiya akan shi ya sa ta kalle shi, taga yanda ya koma abin
tausayi, cikin nuna shi kan shi yana cikin rudani yake ma hajiya bayani,

"Hajiya ban sani ba, bansan me ya samen ba, ina wajen aiki kawai naji ina son zuwa gida, ina shiga
abubuwan da suka faru suka wakana, a can qasan raina ban so ba amma kuma zuciyata na zigani nayi
daidai, Hajiya dan Allah ku taimaka min mata ta takoma,"

Ba qaramin tausaya masa Hajiya tai ba, amma haka ta dake tace,

"Okashatou, sai kaje gidan ka ka nemo dalilin daya sa kake yawan auri saki sannan zan baka Hanee ta
bika, in ko ka bari maganar sakin da kai mata ya riski iyayen ta ka kade, dan ba ka da hope ma kwata2,"
Dafe kan shi yayi da ke tsananin sara masa, zai magana Hanee ta wuce shi ta fada toilete, maganganun
shi sun sa ta fara zargin ko wani makircin ko sihirin aka qulla masu? Lallai in haka ne an cutar da zuciyar
ta, dik da halayen shi na rashin kulawa da mace tana son mijin ta, kuma tana son yaran shi da zuciya
daya, koma waye yayi sanadin raba su tabbat ya cika shaidan.

Ganin ta shiga bandaki ne ya sa ya jingina da qofar yana mata magiya,Hajiya babba ce ta tisa qeyar shi
har waje. Bangaren ta, ta dawo.

Tinani take akan ya kamata ta gaggauta yin maganin komai, kafin Hafsatu ta sake daukan wani matakin
da zai rusa komai.

Waya ta janyo ta kira Hafsatun,

"Hello, Hajiya ina wuni, lfy dai ko naga kin kira da dare haka?"
"Lfy qalaou, ya yaran?"

"Suna lfy,"

"Da kyau, dama na kira ki ne, dn na sanar dake gobe da yamma zan shigo, zan kawo maki magani, ki
qoqarta kiyi amfani da shi, washegarin dana kai mai, saboda a gaggauta a yi maganin wannan matsalar,
ina fatan kin gane?"

"N gode sosai Hajiyata, sai goben sai na gan ki, ina zuba ido,"

"To sai na zo, a gaidan masu gidan da ba cefane,"

"Zasuji Hajiyata,"
Haka sukai sallama, suka aje wayoyin, tinani Hajiya Babba kawai take yanda zata tsara komai, taji dadin
tinanin da ya shige ta, ta samu mafita.

Daga Okashatou har Hanee ba su samu baccin kirki ba yau, sai juyi suke, Hanee sarkin kuka, taci kuka ta
gaji, daga baya ta miqe, ta yi alwala, ta fara nafilfilu, tin tana yi a tsaye ta gaji ta ci gaba da yi a zaune, sai
da aka kusa asuba sannan ta tsahirta, ta yi addu'o'i akan Allah ya tabbatar masu da abinda ya fi alkhairi,
kar Allah ya maida ta gidan Okashatou komai son da take masa in ba alkhairi bane hakan.

A bangaren Okashatou kuwa,ba sallah ba salati, haka ya kai asuba, ido biyu, ya juya farkon gado zuwa
qarshe, sai da aka fara kiraye2n sallah ne bacci mai dadi ya fara fisgar shi,nan ko ya ja bargo ya rufe ido.

(Wannan halin bacci a lokacin sallah musamman sallar asuba, ya zama ruwan dare a wannan zamani,
musamman ga samari da 'yammata, an kwana ana chatting, ko waya, da samari, ba a aje waya ba dai 4,
ko 5, dole kuwa bacci da shaidan su yi nasara da tasiri akan mutum, ya lulluba maka bargon shi na bacci,
ka makara, shin mun manta sallar subh na da mahimmanci sosai da Magrib? Lokutan su bai da tsaho,
ana son yin su a lokacin da aka kira, fiye da sauran salloli, ana son in bawa zai kwanta ya kwanta da
tinanin zai tashi sallar subh, in mutum ya saka a ran shi da yardar Allah zai samu nasara, da babban
rabon tashi, wanda koda mutuwa kai a wannan halin Allah zai baka lada kuma zaka samu sauqin
tambayar ka da mala'iku zasuyi akan me ya sa bakai sallar subh ba? 'Yan uwana musulmi mu kula da
sallah, mu kula da ibada, domin itace mu, domin ta aka halicce mu ba domin abubuwan duniya ba)
Da wurwuri Hajiya Babba ta samu garin ararrabi ta daure, a leda, ta sana a takarda, ta aje ajakar ta,
kamar yanda tai wancan zuwa, wannan karon ma sai da ta debar ma yara kayan ciye2 ta wuce, ba tare
da tai ma kowa sallama ba.

Tana saka hancin motar ta cikin gidan, ta kula da motar Okashatou ba ta nan, da sauri ta isa wajen
Hanee, ta tura qofar taji ta a bude, ta aje ledar hannun ta, sannan ta yi wajen Hafsatu, tana wanke
kwanuka ta tadda ta, daure da baqin zanin ta na gado, cike da murna, ta zare hannun ta ta na ma hajiya
sannu da zuwa,
"Lale hajiyata, ban zaci zaki zo yanzu ba, na zaci sai yamma,"

"Banda abinki ai yanzu je ya dace na zo, baya gida, da yamma ya dawo ai sai ya gane,"

"Hakane hajiya ta,dadina dake kome zaki kina tinani akai,"

"To me yasa na girme maki, ai hankalin mu ba zai taba daya ba,"

"Wannan haka yake,mu shiga daga ciki, yaran na ta can suna ball,"

Ciki suka shige, Hajiya ta dakko maganin nan ta bata, tace ta na dafa masa a abinci, ta saka kadan ba da
yawa ba, ta tabbatar ta boye, kuma in zata diba tana toshe hancin ta, ta na gamawa ta wanke hannun ta
sosai da omo, dan maganin yana da qarfi wajen aiki.
Cike da murna da jin dadi ta karba, kamar zata kwanta ma Hajiya Babba dan biyayya, Hajiya Babba na
mamakin Hafsatun a ran ta,mijin da bai damu dake ba kk wa wannan wahalar.

"To ni bari na ga yaran na koma, kar a farga bana nan,"

"To Hajiya na gode, ba abinda zan bayar?"

"Ba abinda zaki bayar ai yiwa kai ne, ni shawarar da zan baki kawai shine ki hakuri har maganin ya fara
aiki, in km saka gajen hakuri za a samu matsala ba kadan ba, wadda zata kai ga asarar ran ki ko nawa,
dan haka ki kiyaye,"

Cike da tsoro ta ce,

"Zan kiyaye sosai hajiya, karki ji komai, fatana buqata ta biya komai jimawa, ai dama ba a samun biyan
buqata wani lokacin nan take,"
"Yauwa haka nake son ki, kina gane abubuwan danake nufi sosai,"

Zuwa tai taga yaran, ta rada ma Habibu ta kawo masu abu yaje ya daga ya adana, sanan ta masu wasa ta
wuce.

Koda ta koma, Huwaila ta so jin inda taje, ta hau ta da fadan bata da 'yancin fita kenan sai anji ina taje?

Shiru sukai suka sa mata ido, ita kuwa tinani ne fal ran ta, wannan aikin yarintar da take, Allah yasa ya
taimaka wajen warware komai cikin sauqi, Allah kuma ya sa abinda ta qudurta ya tabbata.

Hajiya ta maida hankali wajen kula da Hanee, inda Hafsatu ta maida hankali wajen barbadawa
Okashatou maganin da hajiya ta kai mata, a gida Aunty Asabe ke duba Hanee, babbar diya ce ga Hajiya
Qarama, wadda take likitan mata ce, Hanee bata da matsalar data wuce yanzu taga Okashatou, dan tin
randa ya zo, Hajiya ta raka shi har waje bata sake ganin shi ba, dan haka yau ta daura aniyar sai ta gan
shi ko da sau daya ne.........
*Hanee da Okashatoun ta na dauren kai ni, na rasa ma me zan ji game da su*🙄

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 21:

Toilete ta shiga ta yi wanka, ta qalqale jikin ta tsaf, ta fito, ta taje gashin ta, ta kwantar da shi ta daure,
sai qamshi yake, feshe jikin ta tayi da turaruka masu qamshi, ta dakko doguwar riga baqa mai stones ja,
dankwalin ma ha ne da stones baqi, bayan ta gama saka undies din ta,ta dora rigar, ta matse ta, da ko
har yawo take a cikin ta, amma yanzu ta mata cif, kallon kan ta tayi, ita kan ta ta matuqar yabawa da kan
ta, mayafin kayan ta yafa akan ta, wanda ya daga sama saboda gashin ta data daure, ba qaramin kyau
tayi ba, ko Huwaila bata jira ba, ta saka takalmin ta baqi, ta fice tattaki a cikin gidan, wanda da kunyar
yawo ita daya take.

Kamar kullum 'yammata da samarin gidan sun fito ana hira, sanyin yamma na busawa, cike da nishadi,
dik inda ta ratsa sai sun bita da kallo, yau gulmar ta da ake ta fi ta kullum, saboda kyaun da ta ma kowa,
daidai inda ta ga Okashatou rannan taje ta zauna a dakalin wajen, tana latsa wayar ta, tafi minti goma a
wajen shiru, ba ko walkiyar shi, sai d ta kai wajen minti 30 a zaune, Huwaila ta iso,
"Yau shine ba wani magana kawai kk taho ke daya,"

"Ayya kiyi hakuri,naga baki idar da sallah bane kin makara shiyasa, bana son na katse maki kina ibadar
ki,"

"Hummm Aunty Hanee kenan, ke dai fadi gaskiya, bazaki boyen komai ba, saboda na san halin ki fiye da
kowa a gidannan, na san me kk fito yi,"

Cikin zare ido ta ke kalle2 ko wani yaji me take fada, dan matsawa tayi kusa da ita,

"Huwaila me kk nufi, nifa iska kawai na fito sha,"

"Hummm ko ba iska ba, Allah saboda Yah Okasha kk fito nan wajen ku....."
Damqe vakin ta tayi, tana zaro ido cike da kunya,

"Kar ki min sharri, ni na tafi, tinda kin zama 'yar sa ido kema,"

Tashi tai da kyar, tana feeling very disappointed da bata gan shi ba, a hankali take tafiya, Huwaila na
bayan ta, tana mata dariya, Okashatou wanda ya dawo daga asibiti direct ya yo gidan su, ne ya hango
Hanee da shigar da kishi ya kusa kashe shi, ganin qanne da yayun shi na kallon ta, a sukwane ya isa
gaban ta, wani sanyin dadi ne ya wanke mata zuciya, amma ganin yanda fuskar shi tayi jawur ya sa ta
hadiye jin dadin ta.

"Meye haka Hanee? Dama haka kk fitowa kowane qato na kalle ki, wannan ai cin amanar aure ne,"

Wani haushi ne ya kamata da dana sanin fitowa domin shi, ji yanda ya taqarqare yana zabga mata fada
gaban kowa kamar wadda ta fita yawon karuwanci, kamar zata maida masa da magana ta shanye ganin
idon kowa akan su, kar hakan ya zama zubewar mutuncin ta a idon kowa (mayar wa da miji magana a
gaban mutane zubar mutunci ki ne ba nashi shi kadai ba, dan kuwa ko kece da gaskiya za a ga baki da
tarbiyya, amma in kikai shiru, ko da ba kece da gaskiya ba mutane zasu girmama shirun nan da
kikai,rashin kunya ne da rashin girmama miji mayar masa da magana a gaban mutane musamman 'yan
uwan shi, ki bari in kuka kadaice ko dafa shi ki yi🤣🙊 ba luwana amma)
Ganin bata da niyyar masa magana ne yasa ya ja hannun ta zuwa dakin da yake a matsayin nashi a da,
tana fisgewa tana ja baya amma dake yafi qarfin ta dole ta bi shi, Huwaila kuwa sai magana take masa,

"Yaya pls ka sake ta,kar ka ji mata ciwo, mun fito shan iska ne kawai fa,dubi yanda ake ta kallon ku, dan
Allah yaya ka sake mata hannu, kar ka ji mata ciwo, Yaya ka mata a hankali,"

"Zan mammake ki in baki min shiru ba,munafuka, in kina son ta da arziqi ai taimaka mana zaki Hajiya ta
barmin mata ta, amma dake kema munafuka ce baki tabuka komai, matsa kan na buge ki,"

Hanee wani takaicin shi ne ya kama ta, da danasanin abinda ta aikata,na shan gayu dan ganin shi, sai
yanzu take sake gane laifin ta na ma son Okashatou tin asalin rayuwar ta, wannan ai rashin tinani ne, da
zubar da aji da mutunci, a gaban qannen shi da yayun shi yake mata wannan tijarar, har sun kusa shiga
dakin ta ja ta tirje, dan ta qudirta a ran ta daga yau ta cire shi a matsayin da ta saka shi, ko son shi zai
kashe ta, har sai ya sauya halayen shi, fizge hannun ta tai da qarfi,ba qaramin zafi hakan ya mata ba
kuwa,ji tai kafadar ta ta amsa dan azaba, rintse idon ta tai ta bude shi fes akan kyakkyawar fuskar shi,
daga ita sai shi a wajen,
"Malam waya baka damar taba ni? Ashe baka da tinanin ka tausayawa halin danake ciki kk jana kamar
wata akuya, wai shin Okashatou ka ma san meye matsalar ka kuwa? Matsalar ka shine rashin sanin
darajar mace, baka san wace ce mace ba balle ka bata girma, sannan kana da qarancin ilimin addini, da
kana da ilimin addini da dik abinda ya faru da mu da bai faru ba, a da na so na sakko na zauna da kai a
kowanne hali, amma a yau na qudurta in baka daidaita rayuwar ka ba, ka nemi sanin Allah Okashatou ba
ni ba kai,"

Cikin sauri da kuma fushi ta ke qoqarin barin wajen, a zafafe ya fisgo ta, ya matse hannun ta na dama, sai
qoqarin kwacewa take, tana yatsina fuska hawaye ne ya silalo daga idon ta saboda tsabar azabar da take
ji, amma haka yaqi sakin ta.

Yayan shi Saminu ya hango su,yana qoqarin zuwa ya hana shi suka ji muryar Alhaji.

"Sannu mara imani, mara mutunci, wanda bai san meye sirri ba, kome ke faruwa tsakanin ka da matar ka
bazaka iya samun waje mai sirri ku tattauna shi ba, sai ka mata tijara cikin mutane? Sake ta, ka bar min
gidana, in baka gyara rayuwar ka ba kar na sake ganin ka a cikin gidana,ina dana sanin rayuwar dana
aikata har kayi koyi da ita,kk qoqarin yin abinda ni ban ma aikata shi ba Okashatou daga yau kaji ka sake
ji in baka sauya halin ka ba karna sake ganin ka a gidana mara mutumci da sanin darajar mace kawai"
Cike da fushi ya yarfe mata hannu ya dau hanyar waje, kamar zai tashi sama, kuka take kamar wadda
akaiwa mutuwa, tayi dana sanin fitowar nan da tai, yafi a qirga.

Tsayawa yayi ya juyo, yana kallon Alhaji ido cikin ido.

"Da kk cewa sai na sauya hali, naga dai a wajen ka na ga AURI SAKIN,kuma da har fadi kk kana alfahari
dani, shine yanzu akan wannan zaka min kora irin wannan?"

"Okashatou kamar yanda na fada nayi dana sanin AURI SAKIn dana yi a rayuwa ta,amma ni ina kula da
dik macen dana aura,kai fa? Bakasan mutuncin mata ba sam, a yanzu Hanee ta fi min kai Okashatou,
saboda a dalilin ta na gyara lamiran rayuwata masu yawa, nayi mamakin zaman ka da ita baka koyi
komai ba, kuma naga ba laifina bane take zaune anan, laifin ka ne, sai kaje ka gyara rayuwar ka in kana
son matar ka,"

Wani mugun kallo yayi wa Hanee kan ya fice daga gidan kwata2.
Huwaila ce da Nusaiba wadda ita kuma diyar Hajiya qarama ce suka kama Hanee da kunayr
maganganun Okashatou, da rashin mutuncin da ya mata suka hadu suka addabe ta, shiga da ita dakin
ta sukai,ta zauna a bakin gado tana ci gaba da kukan ta, tare da tinanin anya ta kyauta ma kan ta kuwa,
tana zaune a gidan surukai da ga miji na mata wulaqanci, ya sake ta sakin rashin mutunci, ya maida ta
cikin isa da izza, yanzu kuma yana mata mulki son ranshi, ba komai ne ya kawo haka ba, illa taqamar
tana gidan su, ba zai yu ba, gidan su zata koma, koma meye iyayen ta sunfi kowa son ta.

Tashi tai ta fara hada kayan ta, a akwati, tana kuka, shigowar Hajiya Babba da kwanon farfesun kifi da
yasha kayan qamshi, ne ya dakatar da ita, riqe take da hijabs din ta da ta kwaso, idon ta fal hawaye,
sunkuyar da kan ta tai qasa ganin kallon da Hajiya Babba ke bin ta da shi.

"Me nake gani haka? Ina zaki"

Durqusawa tai a gefen akwatin da kyar ta kalli Hajiya, sannan ta saka hijaban ta a cikin akwatin,
"Hajiya gida nake son na koma,"

"Me akai maki? Koma me ke faruwa ai a qalla in kin ban matsayina na uwa ya kamata ki sanar da ni kan
ki fara hada kaya,"

Jan jikin ta tai ta kwantar da kan ta a jikin Hajiya Babba tana kuka,

"Hajiya Ammana nake so ni, dan Allah ki barni naje na ga Ammana, zuciyata ba zata jure rashin ganin ta
ba a yau, i need her so much, plss, na rasa ya zan da soyayyar Okashatou dake zuciya ta, amma
Okashatou ba mutum bane daya san darajar mace, da darajar me ciki ma dika, abinda ya min a cikin
gidannan dazu Hajiya abin kunya ne, ya zan na kalli mutan gidanan da wanne ido zan kalle su? Tinda
nake ban taba ganin Amma da Abba sunyi sa'insa ba, ko fda a gaban mu, amma yau Okashatou har Alhaji
sai da ya masa magana, wannan ai ba mutunci a ciki,"

"Wannan dalilin ne kk ganin ya kamata ki bata ma mahaifan ki rai? Sanin kan ki ne kk je ma Amman ki a
haka zuciyr ta sai ta baci. Dan irin son da take maki ba zata so ganin kin wulaqanta a gidan auren ki ba,
dama meye ma'anar iyayen miji? Ai dan su zama maki garkuwa a gidan auren ki ne, ba lallai sai iyayen ki
sun san kina da damuwa ba, in iyayen ki suka tsani mijin ki, ko kun shirya ya kafa tarihin mara mutunci
kenan, a gidan ku, dan haka ina mai baki hakuri ki jure kinji, watarana sai labari, kinji Hanee na, ki gode
ma Allah a haka ke ta daban ce a wajen shi, in aka zauna aka baki labarin mijin ki da sauran matan da
yayi sai kinji dama baki san shi ba a rayuwar ki, mutum ne shi mai tsananin son kan shi, ba komai ya jawo
ba illa soyayyar da Alhaji ya nuna masa, sakamakon son mahaifiyar shi da yake,ya jashi a jiki fiye da
dikkan yaran shi, dan haka ya koyi halayen mahaifin shi har ya dora da wanda Alhaji bai da shi, dan haka
kiyi hakuriina saka ran ke zaki zama hanyar shiriyar Okashatou, ki wannan jihadin ki samu lada kinji?,"

Cikin kukan da ya fara raguwa ta ke daga kai, alamar ta hakura, zuciyar ta ta gamsu da bayanan ta, amma
zata nuna ma Okashatou son shi da take ba zai bashi damar mata wulaqanci ba............

*Caaaaaaasssssss, Okashatou mara capital M, ga ka ga Hafsatu nan ai tai ta dika maka Ararrabi kana sha
dannema mai kan buta🤣*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 22:
Okashatou nakomawa gida ya wuce bangren shi, ranshi n matuqar quna, haka take yawo, dik surar jikin
tabayyane, kowa na kallo, kum ce bai da ikon magana a matsayin shi na mijin ta? Zasu gani in ya haifu ko
zai sake zuwa gidan.

Cire rigar shi yayi yashiga wanka, yana ciki Hafsatu ta yi sallama ta shiga, dauke da abincin ta daya sha
magani, ta sha kwalliya,da wata atampa tai kyau kamar ba ita ba, ga qamshin turare tana yi, tin wada
auntyn ta ta sai mata a kd, ta sha fada da auntyn ta ta shaqi irin warin da take, dag nan ta sai mata guda
biyu masu qamshi da tsada.

Koda ya fito ya gan ta sai yaji damuwar shi taragu.

(Kunga amfanin gyara ko? Kun san dai halin Okashatou, amma dake ya ga Hafsatu a gyare yau ya mta
kallon mutunci, imagen ace da qazantr nan ta ta taje masa, gashi dama ranshi bace yake,kunsan ko sai
an kwashi yan kallo, amma tayi gayu, ga qamshi tana yi dole ranshi yayi masa sayi, har yanzu a wannan
qarni da muke ciki na kowa ta waye, har yanzu akwai qazamai marasa damuwa da warin da jikin su yake
yi, wadan dabama sa jin warin da suke, in mace ta kai wannan level dn ta kai maqura wajen qazanta,
kina wari kice kebama.ki sani ba, ba kuma matsalar hanci gare ki ba,a'a tsabar sabo da zama a dauda ne,
Allah ya kyauta.)

"Ga abinci Abban Nour ko kaci?"

"A'a aje min na gama,"


Wani dadi ne ya wanke zuciyar ta, ta sauka qasa ta bude plate din mai dauke da shinkafa da miya, da
nama zuqu2, sai ruwa a jug, ta saka masa cokalin a ciki, jallabiyya ya zura ya zauna, can qasan ran shi na
zafin abindaya faru, kawai hango yanda hips din Hanee suka cike a rigar ta, da qirjin ta daya ciko sosai, ga
'yan uwan shi maza na zazzaune an qus2, yana da yaqinin gulmar jikin ta suke, nan da nan idon shi ya
kada.

"Lfy, Abban su? Ko kana buqatr wani abu ne? Ko yau din ma tinanin gimbiyar taka ne yamotsa,"

Abincin yakai bakin shi, tare da lumshe ido, jin maganar datai, ita ko azaton ta abincin ne yamasa dadi,
bude idon shi yayi da sukai jawur,

"Kar ki sake min zancen ta, na rufe maganar ta agidannan daga yau,"

Wayyyooo dadi, tsalle ne da ihu kawai batai ba, dan tsabar murna,bata san sanda ta miqe ba tace masa
tana zuwa.
Kusan a guje ta qarasa bangaren ta, yaran na ta kallo, wasu na duba wayar ta suna kallo, wanda a wayar
akwai hotuna da vedion da bai kamata yara su gani ba, tana isata fisgi wayar tayi daki, digita din Hajiya
Babba ta danna.

Hajiya Babba tanatare da Hanee, ita da Huwaila suna mata hira dan debe damuwar dake damun ta,
wayar Hajiya ta fara ringing, tan dubawa taga me kiran, da wuri ta maida kiran silent, ta miqe, daki
tashiga sannan ta amsa.

"Ya zaki kirani bayan na ce maki karki kirani, da wayar na hannun wannan yarinyar fa?"

"Hajiya kiyi hakuri,na sha'afa kin cekarna kira, ba zan iya bari sai da safe ba ne,"

"To fadamin"
"Hajiya dazu Abbn su ya dawo, na kai masa abinci,yana kaiwa bakin shi dana masa maganar wannan
mayyar yarinyar sai cewa yayi, kar na sake masa zancen ta a gidan shi,"

Cike da murna ta qarasa, kamar ta hadiyi rai dan murna, hajiya ji tai kamar ta shaqo ta ta wayar amma ta
saka murnar qarya,

"Me na fada maki? Ai ke dai ki ta hakuri mun kusa rabuwa da qaya,"

Yaro ne ya leqa ya kira ta wai taje inji Abban su, nan ma murna ce kamar ta tashi sama,

"Kinji ko yau har kirana yake,"

"Maza tashi ki je kar ya gaji da jira maza maza,"


"To to to Hajiyata, sai da safe,"

Okashatou bayan ya kammala cin abinci ne ya kwanta, daya rufe ido sai ya hango Hanee, a cikin kayan
daya gan ta, tinani ne fal ran shi, na ya ta koma in ba kayan,yanata zurfafa cikin tinani,sha'awar Hanee ta
hana shi sukuni, kuma yasan ba ya da damar koda ganin ta a yanzu, shine dalilin leqawa ya sa yaro yakira
masa ita.

Ko da ta shiga ta ga yanayin shi, na mai tsananin buqatuwa da mace,ya sa nan da nan itama ta ji she is
good to go,ba wata2 ta haye jikin shi, ta masa gingirim yanda ta saba, gashi dai tana tsananin buqatar shi
amma bata san ta masa wasanni ba, ko a jikin shi, dan Hanee ce kawai a idon shi, yana hango yanda take
sarrafa shi,yanajin wani qaimi da qarfin sha'awar shi naqaruwa, ya gigiceya gigita Hafsatu, bai tabazwa
mata a haka ba, bai taba juya ta yanda yake juyata yanzu ba, a da kome zai mata bata taba nuna taji sai
dai ta matse bakin ta tayi gum dadi na shigar ta ba reaction, yau kam Okashatou ya fitar mata da muryar
ta dakya2, Hafsatu ta sha kukan dadi, sai kiran sunnan shi take.

Bayan wasu mintuna masu yawa ya samu nutsuwa ya kwanta gefe yana kallon sama, ji yake ba zai iya
jure rashin Hanee ba itace rayuwar shi.
Wasu hawaye ne masu dumi suka gangare masa, Hafsatu kuwa ji take da tana da dukiyar da zata saka
Hajiya Babba da bokan tafarin ciki da ta mallaka masu.

A ranar Okashatou kasa hakuri yayi sai da Hafsatu tayi laushi liqis yabarta, bata saba ya sadu da ita sama
da daya ba, dayan ma da kyar yake lallabawa yayi ya sauka.

Farin cikin da take ciki bai da iyaka, ta qudurta daya qare zata ce suje tare taga waje, su amshi wani.

Zee ke zaune ran ta bace saboda Ammar ya bata masu lokaci, tin da yadawo daga masallacin juma'a take
jiran shi, ta ci kwalliya kamar me zuwa zaben sarauniyar kyau an kafe dauri, an sha janbaki, da jagirar da
ake yayi yanzu.
"Dan Allah Yah Ammar kayi sauri, sai 4 tayi Abba yace mu bar fitan?"

"Ina zuwa mana 'yammata, yanzu zan gama, takalmi na nake gogewa fa, ke kinyi tsaf ni ne kk so nafito
biji2 kamar mahaukaci ko?"

Dariya ta saka,

"Aiko gidan ance da 'yammata su yi ta maka dariya, nima dan ban son mazan gidan su raina ni nai
kwalliya sosai,"

Ammar dan dariya har da kwalla, wata yar mitsitsiya da ita tana maganar samari,Aunty Hanee in ba
Okashatou ba ba ta kula kowa ada, amma ji ta.
"Why ar u laughing? Bari kaji kar ka ganni haka ka zaci innaje wani agidan ba zai ce yanasona ba,"

Amma cikin dariya yace,

"Ni na isa na musa, sarauniyar kyawawa fa kk, ko kin manta ne?"

Kanta ya mata nauyi dan fasuwa, haka ya gama, sukai ma Amma sallama, tabasu abubuwa da zasu kai
ma Hanee, suka fice.
Tafiyar wajen minti 20 ne ya kai su tangamemen gidan surukan Haneen, wanda ya sa Zee bude
baki,dama anan gidan iyayen Yah Okashatou suke? Ammar ne ya rufe mata baki.

"Sai dan gidan ya fito ya ga yanda kk bude baki ya kai labari ajin ki ya zube"

Hade fuska tai ta sauka, daga abin hawan, Ammar na ta ma qanwar tashi dariya, halin ta daban a gida
nasu.

Kwankwasawa sukai, suka ma mai gadi bayani, suna fadan wajn wadda suka zo suka gane, nan da nan ya
bude masu qaramar qofa suka shiga, waya Ammar ya dakko sabuwa da Abba ya sai masa ya kira ta, wani
ihun murna ta saki,tace bari a zo a kawo su wajen ta.

"Huwaila su Ammar dina nawaje dan Allah shigo min da su nan,"


Itama cike da murnar zata ga Zee da ake bata labarin iyayin ta, tafice, tana zuwa kuwa tatabbatar da
maganar Hanee, tsaye take ta karye qugu gefe,ta ci kwalliya, sai wani shan qamshi take.

"Zee ko? Bismillah ku shigo,"

Kada ido tayi tace

"Eh nice, ina wuni?"

"Lfy qalaou mu shiga a gaisa ko,"

Haka suka shiga, Hanee murnar taba a fadi, ta qanqae zee kamar zata gudu, labari kuwa tasha shi, a haka
Huwaila ta kula da tsananin tarbiyyar da yarn suke da ita, dik da iyayin zee, akwa tarbiyya, lokacin sallr
la'asar na yi ita ta fara miqewa, wai sallah ma sai an bata hijab dogo, ta yi ta dora da addu'o'i, ta miqe, ko
da Hajiya Babba ma tazo sai data yaba da tarbiyyar yaran, har wajen Alhaji Hanee takai su,suka gaisa,
mutan gidan sun yaba masu sosai.
Yamma na kawo kai, Zee tace zasu tafi, Hanee kamar wata yarinya ta fara kuka.

"Kaji Aunty Hanee innice anan mezai batan rai? Kin ga yanda kk koma kuwa saboda hutu da jin dadi? Ki
kwantar da hankalin ki, Yah Ammar ya sa maki hotuna su Amma da Abba, yanzu muma mun dau hotuna,
to meye na bata ra?"

Tsabar surutun da tai ta zubawa ne ya ba Hanee dariya, yaro yaro ne, da Amman ta ce da ta gane tana
da damuwa, amma su basu gane ba, haka sukai sallama ta raka su har gate.

A dawowa kunya kamar ta nutse, dan rabon ta da fita tin sanda Okasha ya yarfata gaban kowa.
Cikin tsakiyar dare Hanee ta tashi da matsanancin amai, da ciwon baya, ga shi ba kowa adakin,ta yi zufa
ta yi hawaye, duk sun hade waje daya, a hankali take takawa zuwa bakin qofa, Hajiya Babba da garin
kallon news ta yi bacci a doguwar kujera taji motsi, cikin magagin bacci ta miqe tana kiran,

"Kaiii kaii waye nan? Motsin me nke ji,"

"Hajiya nice, bayana zai karye, Hajiya ki taimaka min amai nake ji,"

Ai da sauri ta miqe ta tare ta,nan ta tada Huwaila, ta leqa ta kira Asma'u, wadda take, midwife ce a nan
babban asibitin dake garin Katsina, mahaifiyar ta bata gidan ita.

Da gudu Huwaila taje kiran ta, kan tazo Hanee ta fara galabaita, kukan ma takasa, Asma'u na zuwa
taduba ta ga ai haihuwa ce, kuma tinda ana tinanin biyu ne zuwa asibiti shine ya fi.
"Hajiya mu kaita asibiti kawai,"

"To kira Sa'idu ya zo mu tafi,"

Da sauri ta fita, ta je bangaren samarin gidan ta tado shi, yana ta magagi, ana ce masa Hanee ba lfy ya
bude ido, dan tasu ta zo daya sosai, nan da nan Hajiya ta shiga ta dauki akwatin da ra shirya kayan
haihuwa tin farkon shigar ta na tara.

Basu zame ko ina ba sai asibiti, a dakin haihuwa aka mata makwanci, likitan da nurses gani suke kamar
ba zata iya haihuwa da kan ta ba.

Sai addu'o'i take, tana neman gafarar Amman ta da Abban ta, da Okashatou,

"Hajiya mutuwa zan ku yafe min, kuce ma Ammana ta yafen,"


Hajiya ta shiga damuwa, kar diyar mutane ra mace ta hana a kaita gidan iyayen ta...............

*Wayyooo Haihuwa yaqin mata, ku kawo ma Hanee Ararrabi🤣🙊, ko baya maganin haihuwa🤔😝*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 23:

Maza ta lalubi wayar ta ta kira Amma, wadda take ta qulla siga na siyarwa da take yi, tana zaune sai take
jin tana tinanin Hanee, ana sanar da ita kuwa ta miqe, tare da tambayar inda suke, Hajiya Babba na fada
mata tace gata nan zuwa, tare da addu'ar Allah ya raba su lfy.

Abba ta sanar ma shima ta waya, ya mata izinin zuwa, ta saka hijab din ta, ta bar key a maqota, dan
ranar su Zee suka koma makaranta da safen, kar su dawo ba key.
Abin hawa ta tsare sai babban asibiti, tana isa yarinya ta biyun tana isowa duniya, Hajiya Babba harda
kwalla ta dadi, ashe zasuga 'yan biyu a zuri'ar su suma, nan da nan akai ta bige2n waya, ana sanar ma
dangi, matan yayun Okashatou da ba sa zuwa hidimar gidan shi wannan karon har da su akai ta
tururuwar zuwa ganin Hanee, Hanee ta galabaita sosai sakamakon haihuwa ta biyu kuma a haihuwar
fari, ga rashin sabo, ga wuyar haihuwa ta hadu ta saukar mata da ciwon jiki, da gabobi.

Ganin yanda ake ta zuwa duba su ba qaqqautawa ya sa likita sallamar su.

Okashatou bai ta shi sanin anyi haihuwa ba sai a washegarin haihuwar,Abba ya kira ya roqe shi tin da ta
haihu lfy ko zasu basu ita ta dawo gida, yana hanyar shiga office ya dakata ya sake tambayar Abba me
yace, ya maimaita masa buqatar shi, anan ya ce ma Abba yana so zasuyi magana ina zasu hadu?

"Kazo ko wajen aikina ne indai maganar na buqatar sirri,"

"To ina nan tafe yanzunnan,"

"Sai ka iso, ayi tuqi a hankali, dan naji maganar ka kamar akwai damuwa,"
"To Abba na gode sai na iso,"

Kashe wayar yayi ya fice a dari, koda ya isa wajen aikin Abba yaran wajen sun fara zuwa wajen aikin su.

Bayan gaishe2 Okashatou ya hau sinne kai, yana sosa qeya, da kyar ya bude baki ya fara magana,

"Abba ni mai laifi ne babba, dan haka ina mai neman gafarar ku a wannan lamarin daya faru, kuma ina
roqon ka dan Allah kasa baki a mayar min da mata ta,"

"Me yake faruwa ne?"

"Ammmm Abba watannin baya da suka wuce na saki Hanee, amma na maida ta tin da wuri2,"
Wani abu ne mai daci ya taso ma Abba a maqoshi, tare da sarawar kai, diyar shi mai ladabi da biyayya
aka saka? Akan me? Bai taba sakin 'yar kowa ba shine wani banza zai sakar masa 'ya, da kyar ya lallashi
kan shi, kar ya zama dattijon banza, a zo ana raba shi fada da surukin shi, amma kadan ya rage ya rufe
Okashatou da duka.

"Ina jin ka,"

Fuskar shi ba alamar ya taba dariya yake magana.

"Tam shine su Alhaji da Hajiya suka riqe ta a gida, suka hana ni mata ta, yanzu ma ba dan ka min waya ba
ba zan san ta haihu ba, dan ba wanda ya sanar da ni,"

Wani kallon baka da hankali Abba ya masa, sannan yace.

"Amma dai Okashatou kabata wayon ka,meye a cikin yawan aure da sakin shi ne? Kafin auren ku naji
qishin2n akan hakan, Allah ya nufa sai ka auri yarinya ta ka wulaqata ta ne kawai amma da fasa auren
nan akai tin farko, dana san zaka kafa mata tarihin saki a rayuwar ta, ba zan boye makab zuciyata ta yi
min qunci da jin lbarin nan, kuma iyayen ka sun min halacci, dan haka ba abinda zan shiga, ruwan su ne
su baka ita, ruwan su ne su hana ka, zaka iya tafiya, bamu da abin magana akai kuma,"

Okashatou yazaci hakurin Abba zai kai ya yafe masa da wuri a wuce wajen, ya tafi da shi yaga yaran shi
da matar shi,(ni ko nace dake sokone Abban ba🤨).

Haka ya bar wajen a kunyace,ran Abba n tafasa kamar garwashi dan bacin rai, sanar ma da yaran shi yayi
zai fita in bai dawo ba ayi dik abinda aka saba, sai ya dawo.

Waya yayi ma Amma yaji tana ina? Nan take sanar da shi a sallami Hanee a asibiti, sun koma gidan
surukan itama yanzu ta ke shirin komawa gida,

"Kar ki tafi gani nn zuwa,"


"Abban su lfy naji muryar ka haka?"

"Lfy sai na iso,"

Tagumi tazuba, Hanee na kwance tana kallon ta, cikin murya mai sanyi tace,

"Amma lfy?"

"To Abban kune yace lfy n dai jira shi anan kuma banji lfyr ba a muryar shi,kamar ranshi bace yake,"

Qoqarin tashi Hanee tayi ta zauna, qirjin tana bugawa kar dai Abba ya san maganar sakin nan ne?

"Kin san wani abu ne?"


"A'a ban san komai ba Amma"

Gyada kai tayi tana zaune, Asma'u da Huwaila ne suka shigo, dauke da abinci,suka aje, suka leqa yaran
suka fita cikin farin ciki, koda suka fice tace

"Amma ban naci yunwa nake ji, jiya ma haka nai ta narkar abinci, Amma bana son na zama qatuwa"

Dariya Amman tayi sannan tace,

"Aiko zaki zama ko da na bayan haihuwa ne, bakiga ke qivar kyau ta maki ba ma, akan ramar nan da kk
ta fama da qasusuwa,"

Tana magana tana budewa, tuwon alkama ne miyar danyar kubewa, ya malmalu, miyar tasha nama da
man shanu, Alhaji buhun alkama niqaqqe ya aje, yace saboda ita zata gina masu jiki da yaran, jikin ta b
zai tsufa ba, dan haka yake ma matan shi in sun haihu, (musamman nonon mace ba zai yamushe ba,
balle ita da zata shayar da biyu)
Flask din Tea kuma kunun alkamar ne, sai madara fresh milk da aka aje da shi dan ta hada tasha, Amma
ba qaramin dadi taji ba, dan wannan kulawa ko ita abinda zata mata kenan qarshe, dan haka ta janye
qudurin ta na son su bata ita a maida ta gida, in bata manta ba jiya ma kan ta tafi, sai da aka mata wanka
irin na jegon daya dace, da yaran, ba abinda zata ce sai godiya.

Wayar ta ce ta fara ruri, Hanee ta tsaya da kai lomar tuwon bakin ta, ta hadiyi waji yawu mai qarfi,

"To to to gamu nan zuwa, amma abinci takw ci da an dan bari ta qarasa sai mu zo,.......to ba damuwa,
gamu nan,"

"Yi maza ki gama muje wajen Alhajin naku, ana jiran mu,"
Badan tana jin yunwa ba, fargaba ba zata bar ta ci ba, haka ta ci ta sha kunun ta dora da ruwa, sannan ta
saka doguwar riga, ta dora hijab suka fita, ita ta masu jagora, har bangaren Alhaji, Abban ta ta tarar
fuskar shi ba walwala, Alhaji kuwa yayi jugummm, Hajiya Babba kan ta a qasa, kamar marasa gaskiya.

"Tashi daga qasa Hanee, mun yafe maki zauna kan kujera,"

A kunyace ta zauna, qirjin ta na bugawa, tinda take da Abban ta bata taba ganin fuskar shi ta baci haka
ba, me ke faruwa?

"Kamar yanda na sanar daku abind Okashatou ya sameni ya fadan, wanda ni banji dadin ace a matsayin
mu na wadan da suka haifi Umma Hanee ace wai kun boye mana wannan lamari, a gaskiya ba a kyauta
mana ba, domin saki ba wasa bane,"

Cikin tsananin rudu, Amma ta kalli Hanee nan da nan wata yarintar 'yar ta ta ta bayyana mata, ace an
sake ta, wannan wace rayuwa ce haka?

"Saki fa naji kace Abban su? Me Hanee zata aikata a sake ta? Me kika masa? Innalillahi wa inna
ilaihirrajiun"
Sai ga hawaye na zuba a idon Amma,

"Dan Allah Abba, Amma ku daina damuwa, ni ban masa komai ba, ku daina son jin asalin me ya faru,
maganar ta wuce, ya maida ni tin d wuri, kuma yau ne rana ta farko da zan fadi wata magana anan, ina
kyautata zaton Abban Nour ba ason ranshi yake aikata yawan sakin dayake ba, ina kyautata zaton sashi
ake, ta wata hanyar da Allah shine mafi sani, domin abun hankali ba zai dauka ba duk wanda yaji a yanda
ya saken,"

Ta kulle masu kai, wanda Alhaji a ganin shi kawai dan tana son dan nashi ne ya sa ta fadi hakan, amma
Hajiya Babb da ta san komai ta sa ina Hanee t dosa sa mganar ta, Amma da Abba kuwa so suke suji me
take nufi da hakan, a lokacin Olashatoun ya iso, idon shi kyarrrr akan Hanee, wadda ta duqar da kan ta,
ko kyartawa baya yi, wani mugun kyau yaga ta masa, Allah ya taimake shi a bashi ita su wuce a yi sunan
gidan shi, addu'ar shi kenan.
"Saboda ka raina mu an kira ka tin dazu sai yanzu ka ga damar zuwa, biki za ka da ak ce dole sai ka yi
gayu haka,"

Cikin jin kunya ya sosa qeya gaskiya Alhaji yana yarfa shi,

"Daga asibiti fa nake shiyasa na dade,"

"To munji ina so ka sanar da iyayen yarinyar nan dalilin sakin yarinyar su qarama,"

Har zai magana Abba ya tare shi,

"Ammm Alhaji ina ganin maganar ta wuce kamar yanda Hanee tace, ni dama abinda ya bata raina shine
ba a bamu matsayin mu ba na iyayen ta, dik da kun nuna mana cewa ko bayan ba ran mu. Ku iyayen
Hanee ne ba dangin mijin ta ba, zaku iya zatar da kowanne hukunci akan ta wanda zai amfane ta, sannan
ba zaku bari dan ku ya cutar da ita ba tare da kun kwatar mata 'yancin ta ba, hakan ya faranta raina
matuqa, dan haka dolen mu zamuyi hakuri da abinda ya faru, qaddarar Hanee ce saki daya ya shiga
tsakanin su da mijin ta, dan haka zamu barta a qarqashin kulawar ku, har sanda kuka ga ya dace ta koma
dakin ta, sai dai da sharadi,"
Okashatou da ba haka yaso yaji ba, duk ranshi a dagule ya daga kai ya kalli Abba dake kallon shi, yace,

"Meye sharadin?"

"Sharadia shine, ban san meye matsalar data sa ka sake ta ba, kuma naji tana wasu maganganu dazu da
ban fahimta ba, to dole kan ta koma gidan ka sai an gano meye matsalar anyi maganin ta, sannan
sharadi na biyu ba zaka dinga roqona akan komawar ta ba dan bani na sake maka matar ba ba hannuna
ciki,"

Okashatou ya san ya kai Abba maqura, sannan ya ga mahimmanci da gatan Hanee, dan ya tabbata
iyayen ta na son ta matuqa, Amma tinda ta duqar da kai bata sake cewa komai ba, bata son ta ja da
maganar mijin ta cikin mutane, amma ranta yayi matuqar baci ji take kamar ta furta su bata yarinyar ta
su tafi gida kawai, saki da qananan shekaru?

Abba ya fuskanci haka shiyasa ya ke magana, da yanke hukunci, ya yarda da matar shi ba zata bada masa
qasa a iso ba.
(Shin mijin ki ya yarda dake haka? Ko kij yarda da mijin ki haka? Yana daya daga cikin zama mace ta gari
mijin ki ya yarda dake ko a agaban sarkin garin ku ne ba zaki bashi kunya va)

Haka suka tashi daga zaman kowa da abinda yake saqawa a ruhin shi.

Kafin su Hanee su shiga Okashatou yayi wuf ya fada dakin nata, Amma kuwa bata koma ba, ta bi Abba,
sunyi sallama akan gobe su Ammar zasu zo, cikin rashin sani Hanee ta dau hanyar dakin ta, bata san ma
me take ji ba game da yanda iyayen ta suka dau lamarin, tana murda knob din qofar........................

*Hey lovelies, na san mata da dama na mutuwar son rage tumbi, akwai sasassaqen gamji an sha fadan
na gwada shi, ban ba shi mahimmanci ba sai jiya da dare na tafasa da jar kanwa kadan, na sha, hummm
da dare kam na sha zagawa toilete🤣🙊 amma wallahi cikina ya ya sauka sosai, ku gwada ku gani, plsss
don't PC me saboda na rubuta anan ya ake amfani da shi, plsss ba dan ni ba, saboda amsa pc chats
wataran in wayata ta maqale ban amsa ba sai aji haushi, ni kuma bana son hakan ina fatan kun fahimce
ni, nayu vayani anan nasan zaku gane*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 24:
Zuciyar ta daya ta shiga dakin, yanayin labulen da aka saka red, kayan dakin ash colour ne da red carpet,
shine ya ba wa dakin launi mai duhu, yana zaune gaban yaran, da aka bari da Huwaila, wadda ta dade da
bude baki tana ta shaqar bacci, dan tin da akai haihuwar nan, kasancewar tafi kowa kusanci da Hanee,
ita ke taya ta kwana da ayyukan da suka kamata ta taya ta, dan haka ba wani baccin kirki take samu ba,
tana samu sunyi bacci itana ta bude baki tana sharar nata.

Wani son yaran ke ratsa zuciyar Okashatou saboda kyaun su, sunyo hasken fatar shi, amma yasan bai da
dimple, da dogon hanci, dik da basu motsa ba ga dimple nan ya nuna alamu, daya tafi daya duhu.

"Subhanallahi me zan gani haka? Hajiya ! Hajiya !!"

Ai kusan sufa Okashatou yayi ya damqe mata baki,ya juyo da ita ya rungume ta ta baya, yana rada mata
a kunnen ta,
"Dan Allah kar ki kira kowa, i just want to see my kids, this is my only chance, dan Allah, kar ki min haka
mana,"

"Amma dai kasan Alhaji ya hana ka shigowa gidannan gaba daya, balle kazo inda nake, ka fita ka barmin
daki, ba zai yu baka san darajar mu ba ni da yarana, yanzu ka dawo ka nuna ka damu damu, ba zai yu ba,
ai ka gan su, fita,"

A da yana taqamar ko da taba hannun ta yayi sai ta nuna jin dadin hakan, amma yanzu yaji shiru dik wani
wasa da wani shafa mata hannu ta sama da yake, ga wani kashe murya da yake amma yaji ko a jikin ta,
wanda da ya san meye a qasan ran ta da ya birkito da ita gaba daya jikin shi, kwace hannun ta tayi, ta
bude masa qofa ta nuna masa hanya, idon ta cikin nashi.

"Hanee me kk nifi da ni ne? Na baki hakuri, na maida ke dakin ki, na yi nadamar dik abinda na aikata miki
to me kk so kuma? Hakurin ki shine hakurin Hajiya da Alhaji, plss, u knw i love u much,"
Zuciyar ta karaya da kalaman shi, amma ko kadan bata nuna ba.

"Kaga wuce ka fita, bana son ka ja min magana aga kamar ni na jawo ka shigo wajena, in so kake komai
ya koma daidai kaje gidan ka ka nemo matsalar dake damun ka akan kan ka, in yaso sai ka dawo wata
qila na duba na gani,"

"Hanee ban gane matsala ba, ban gano komai ba ni, dan Allah ki samin haske a lamarin, wataqila
maganar da zaki fada ta ban haske,"

"Yanzu na tambaye ka,"

"Allah ya sa na sani,"

"Qarfe nawa kayi sallar subh?"

"Qarfe bakwai, meye alaqar maganar komawar ki da kuma sallah ta?"


"Kai ne kk ganin basu da alaqa, amma ni nasan suna da alaqa sosai, jiya qarfe nawa kayi isha'i,"

"Ya Allah, dan Allah ki daina min tambayoyi haka,"

"Shikenan jeka na daina amma kar ka sake damuna akan komawa ta, jeka, ina gaida su Habibuna"

"Da asuba na rama Isha'in saboda na manta ban ba,"

Lokacin da yake fada kan shi na qasa alamar kunya, Huwaila da ta farka taji kalaman shi kama baki tai
tace,

"Tabbb rama sallar isha'i da asuba saboda mantuwa,ikon Allah,"


"Tashi ki fita dan uban ki,"

"To ni me nayi😏"

Kai mata duka yayi, ta fice da gudu, Hanee ta kalle shi

"Hummm Abban Nour kenan, yanzu ko Nour ya rama salla irin haka ba za a dake shi ba kk tunani, balle
kai? A gaskiya ba zai yu na ci gaba da zama da kai ba, ibadar farilla bata dame ka ba, balle ace ka hada da
nafila, duk sanda ka fahimci hakan ba cin fuska bane nake maka, gyara ne da zai taimaka mana har da
yaran mu, sanda ka san darajar mace da kuma yaran ka, na maka alqawarin qofata a bude take, zuciya ta
taka ce a koda yaushe,"

Kallon ta kawai yake, yana ganin wannan uzuri nata ba uzuri bane, indan ibada ne, mata nawa ya zauna
dasu a haka, sannan itama ai tin da suna tare, meye na kawo wadannan maganganun a yanzu, ya budi
baki zai qara kawo mata wani uzurin, Hajiya Babba ta sako kai,
"Me nake gani ne? Amma Hanee baki d hankali, da danyen jegon naki kk boye miji a daki? Zo ka fita, fita
kafin na maka maka murfin kwanon nan a ka, mara kunya kawai,"

Yana bata rai da rashin kunya ya fice yana qunquni.

"Hajiya na rantae bani na shigo da shi ba, ki tambayi Huwaila ganin shi nai kawai a nan, dana dawo,
hajiya ki yarda dani plss,"

Kuka ta fara, dan gaba daya abinda take gudu kenan dama.

Hararar ta Hajiya tayi ta wuce ta ta aje kwanon farfesun naman kan da ta kawo mata, wanda ya sha
kayan qamshi, da minannas a ciki.

Zuwa tai ta durqusa a gaban Hajiyar tana kuka.


"Allah hajiya ki yarda dani, ni bani na jawo shi ba, shine ya shigo, kema kinsan ba zan taba kiran shi da
kaina ba hajiya ki yarda dani,"

Dago ta tayi, ta zaunar da ita gefen gado,

"Hanee ina son ki gane, muddin kk sake masa, sai ya dawo ya bata min dik shirin danake, so nake yayi ta
jin haushin ki a yanzu, hakan ne zai bam damar kammala abinda na fara, wanda da zarar na kammala ke
da kan ki zaki gode min, ina fatan kin amince dani, ba zan cutar da ke ba?"

"100% Hajiya, bayan iyaye na Hajiya kune mutane na farko dana yarda da su a rayuwa ta, Hajiya inshaa
Allahu ba zaki sake ganina da Abban Nour ba, sai da yardar ki,"

"Da kyau, Allah ya miki albarka, bari naje na kaiwa Alhaji abinci, anjima a yiwa wadannan 'yammatan
masu kwacen miji wanka,"
Tana share hawayen ta ta ke murmushin jin dadin sakkowar da Hajiyan tayi.

Huwaila ce ta shigo, ta kalle ta, ta zauna a daidai kwanon da Hajiya ta aje.

"Wannan fa? Bari na taya ki, dan dazu mijin ki ya kusa make ni, na ji tsoro ruwan jikina ya fita, kinga ko
gwanda na maida wani,"

"Kika kuskura kk ci wannan hadin, sai kin nemi miji da ranar Allahn nan, a toh, kuma mijina ba ke kk
shiga maganar mu ba,"

"Maganin mata ne a ciki?"

"Ban sani ba aje min, kije ki dafa naki,"


"Oh har wani tanadin koma ma miji ake maki, 'yae gatan hajiyq,"

Dukan wasa ta kai mata, tana dariya tace

"Ke wasa nake in zakici bismillah, miqon waccan me kukan,"

Miqa mata daya daga cikin yaran tayi, da take ta kuka, suka ci gaba da hirar su.

Okashatou na komawa gidan shi, ya shiga bangaren Hanee, ya fara tattara kayan dattin yara, yana gyara
wajen, su Habibu kallon shi kawai suke, sai da ya kammala tsaf ya zauna yana hutawa, ya kira su dika.

Zama sukai a qasa shina ya koma qasa, ya dauki Sabir, yana shafa kan shi.

"Wanda yake son Ummeen shi ta dawo a cikin ku ya daga hannu na gan shi,"
Cike da ihun murna suka daga hannayen su dika, Nour da ya biyo ta bayan windown su sakamakon ihun
murna daya jiyo, ya kasa kunne ya saurari me Okashatou ke fada ma yaran.

"Yauwa tinda kowa na son yaga Ummeen shi, to ni na san inda take, kuma zan kai ku, amma sai bayan
anyi sunan qannen ku da ta haifa maku mata, in a kai ku kuyi ta kuka kuce kuna son a dawo maku da ita
kunji?"

Murna sukai ta yi, ba qaqqautawa, suna tsalle,alqawarin ice cream ya musu, yace su jira shi,bari ya
dawo.

Nour yana gama ji ya bazama wajen Hafsatu, dake kwance a gado, dakin kaca2 tana karanta littafin
hausa, (mata da dama na karanta littafin hausa amma ba su koyi da abinda ke ciki, ko zan iya sanin dalili?
Inda wanda ta san dalili plss ina jiran jin qarin bayani akai)

"Mama ! Mama !! Mama !!! Wai ke sai ai ta miki magana amma ki banza da mutum, shikenan bari na
koma da labarin danaji Abba na fada akan Ummeen su Habibu,"

Ai bata san sanda tai wulli da littafin ba ya fada wata roba da ta tara ruwan wanke hannu a ciki, ta jawo
zanin ta da ya kusa kuncewa ta zauna da kyau,
"Me yace? Zo ka fadan dan Allah,"

"Tabb a banza zan fada miki wannan labarin ai yacin sai kin bada wani abu,"

"Shege dan iska mai son kudin tsiya, Allah wadaran halin ka,"

Dan kwalin da ke yashe a gefe, wanda yai baqi dan datti, ta dakko, kunce gefen shi tai ta zaro nera
ashirin ta bashi.

"Yacin sai dai hamsin kin ko san me zan fada ai ko dari zaki ban"

"Dan Allah fada min mana, n matsu naji wannan labarin ka bini talatin din ko gobe zan baka,"
Labarin dik abinda yaji ya gani ya bata, hankalin ta in yafi dubu ya tashi, gaba daya jikin ta har wani rawa
ya fara ta na zufa tace.

"Qarya kk dan uban ka, kasan bana son irin wannan wasan fita kan na ci uban ka,"

"Ke kk sani amma ni gaskiya na fada maki, kuma ina bin ki talatin,"

Cike da tsawa da baqin ciki ta ce,

"Fita dan uvan ka nace,"

Fita yayi yana ba dai uban shi ba, haka kawai a dinga zagin shi, daga kawo mata labarin abun arziqi.
Wannan itace tarbiyyar da Hafsatu tai ma yaran ta, in tana son su.mata aiki, sai ta basu kudi, koda biyar
ne, sannan in ta zage su zasu ce mata ba dai nasu ba, sannan ta sake maimaita zagin, dan haka zagi a
bakin su kamar ruwan famfo, gashi in suna zaune zata saka su aiki, indai ba su san zasu more ta ba ba
zasu yi ta dadin rai ba.

Koda ya fita ashar tai ta danna ma kowa da kowa, tana zagaye dakin, wace irin magana ne wannan,
kwana daya ne fa kawai maganin da Hajiya Babba ta bata tana mai abinci da shi, bai ci ba ya qare, shine
har ya fara zancen komawar Hanee? Da sakel, dole ne ta kira Hajiya Babba ta sama mata mafita............

*Cassssss tsafi gaskiyar me shi*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 25:
Anyi suna lfy, Alhaji shi yayi komai, har ragunan da aka yanka ma yara shi ya siyo, dan Okashatou
wannan karon ya qoqarta siyan raguna biyu, amma Hajiya tace kar ma ya wahala, Alhaji ya siya tin sanda
aka haifi yaran ba zasu jira shi ba,yayi takaici sosai, yanzu ya san ciwon uba ya yi ma yaran shi abu a hana
ya isa gare su, ya so yayi magana akai, amma sanin cewa bai da ikon hakan ya ja bakin shi yayi shiru, ya
qudurta ko shekara nawa zasuyi indai suka koma gidan shi sai anyi sabon suna. Lols😄

Hanee ta gaji sosai saboda hidimar suna, 'yan uwan Abba da Amma sun halarci sunan, inda suka tafi
dauke da abubuwan arziqi, kowa sai yabon mijin ta da iyayen ta suke, dan a ganin su mijin ne gwarzon
da yayi komai,🙄 tana kwance Hajiya Babba ra shigo, ta zauna gefen qafar ta, ganin Hajiya ne ya bata
damar tashi zaune,

"Sannu Hajiya, ya gajiyar suna, Allah ya saka da alkhair, lallai kina son kishiyoyin nan naki da yawa,"

"Ameen waya fada maki ana son kishiya,ni 'yata nake so ba kishiyoyi na ba,"
Dariya sukai sannan Hajiya ta gyara zaman ta ta kalli Hanee,

"Umma Hanee, lokaci yayi da zaki fara shirye2n komawa dakin mijin ki, saboda riqe ki anan din ba daidai
bane, kina can yafi kina nan, dan haka gobe inshaa Allahu ki samemu a bangaren Alhaji, da wuri zaki,
koda ban samu shigowa ba, ina fatan kin gane,"

"To Hajiya, ina godiya da irin soyayyar da kk nuna min, Allah ya biya ki da mafificin alkhairi,"

"Ameen Hanee, ke yarinya ce mai ladabi da biyayya,kina da sanin ya kamata, ga shi kin fito gidan
tarbiyya, kina da ibada da tsoron Allah, wanda ya hada halayen nan yafi qarfin wulaqanta a duniya, Allah
ba zai bar kowa ya wulaqanta shi ba, daukaka ce zatai ta bin shi, kuma dik abinda na maki yiwa kai ake
kiran shi, saboda nima kinga wasu daga yarana mata ai na aurar da su, in ban riqe surukata a matsayin
diya ba, ni nawa yaran wa zai kular min da su? Ai sai dai su tagayyara a tsakanin dangin miji ko?"

"Hakane Hajiya,amma qalilan ne suka san hakan, dan haka dole ne na gode maki , da Alhaji,"
"Babu komai Hanee, ki shirya wanka, yamma na sakkowa,"

"To Hajiya ta, wai ni ina raguwar nan ne,tin da aka gama suna jiya ban gan ta ba, jiya ba anan ta kwana
ba,"

Dariya Hajiya tayi, tace,

"Ai tana can dakin su na 'yammata dake bangaren Hajiya qarama, wai ramuwar bacci zatai,"

"Ita da tace in ta tashi 'yan uku ko hudu zata haifa,"

"Wace zata iya wannan, ke rabu da raguwa,"

Haka sukai ta hira irin ta barkwanci, kamar ba surukai ba gwanin sha'awa.


A wannan daren Okashatou ya shiga gurin su Habibu, da ledar kaza da ice cream, na cin hanci, yara nata
murna, ya gama kitsa masu dik abinda yake son su fada, sunyi hadda sosai, Allah2 suke gobe tayi, anan
wajen su ya kwana, hakan ya qara tinzira Hafsatu, wadda take da qudirin jiran safiya itama, ayi ta ta
qare.

Qarfe takwas na safe Hafsatu ta gama shirin ta tsaf, ta turawa Hajiya Babba saqo, dan ta san wataqila ko
tana bacci ko dai tana tare da wasu a gidan, kar aji wayar su, saqo ne kamar haka,

*Hajiya barka da safiya, ina fatan baki manta da fitar mu ba yau, zuwa wajen Malamin ki, dan gaskiya
yau nake son a kawo qarshen wannan shegiyar Haneen, ba zan iya kishi da itaba, ina jiran jin saqon ki,
Hafsatu*

Hajiya Babba na karantawa tai murmushi, ta adana saqon ta miqe zuwa wanka, ta yi wankan ta fes, ta
fito, ta yi kwalliya mamar yanda ta saba, ta ma Alhaji magana zata shiga taga me ake yi a cikin gidan, ta
sanar da shi ya shirya kamar yanda ta sanar da shi, akwai wani babban al'amari yau da zai faru a gidan,
Ahaji ya qosa yaga me zai faru yau.

Cikin kwalliya ta tadda Hanee da yaran ta, gwanin sha'awa, cikin ta da ya yi qato ya fara komawa saboda
ya sha dauri sosai, ta saka wani black material da ratsin goleden mai layi2, dinkin riga da skirt ya mata
kyau sosai, yaran sun sha fararen kaya, ga qamshi na ta tashi a jikin su.

Hajiya wayar ta ta dauka ta danna digits din Okashatou,yana dauka ta ce masa,

"Dik abinda kk yi yanzu ka bari ka zo gidan nan, kar ka sanar da kowa ina zaka,"

"Hajiya lfy?"

"Kai dai kazo ina neman ka,"


A saba'in ya dire qasa, yau an samu yayi sallah da asuba,dan haka ya koma bacci, a gaggauce ya wanke
bakin shi, ya dake kayan jikin shi, ya dau keys din shi ya fice, Hafsatu da tai shirin ta tana ganin ya fita ta
kira Hajiya tace,

"Hello, Hajiya zan iya zuwa yanzu kuwa? Dan na ga Abban su ya fice, kan ya dawo kinga na fita ba sai ya
tambayi ina zani ba,"

"Eh zaki iya fitowa yanzu, da kin zo ki shigo wajena ki jira ni ina bangaren Alhaji, ki zauna har na kammala
me nake, sai mu wuce,"

Cikin zumudi ta kashe wayar, a ran ta tana ayyana irin maganin d zata ce a bata, dan bata taba shiga
tashin hankali ba akan kowacce kishiya irin Hanee, bata taba ganin Okashatou ya damu da mace ba
kamar wannan.
Okashatou na zuwa ya ma rasa ina zai je, yanzu gidan da yake na su ya zama masa na baqi, tinda duk
inda yaje in Hanee na nan yi masa ake kamar wani barawo zai sace ta a kore shi.

"Hajiya na iso ina zan tadda ke?"

"Ka aje motar ka daga nesa yanda ba kowa zai san ka shigo gidannan ba ka zo bangare na, kar kaji nace
kazo bangare na ba wai wajen ta na kira ka kaje ba, ni ke son ganin ka,"

Kada idon shi yayi sama, dan haushin yanda ake masa akan Hanee yake ji sosai, ko yankar naman jikin ta
yayi kan su rabu sai haka.

"To"
Shine kawai abinda yace ya kashe wayar, ya samu gefen motar Sammani, wani yayan shi da mamar shi
bata gidan, ya parker tashi ya fice, direct bangaren Hajiya ya shige, da fatan ya tadda Hanee a parlour
dan in ya yi gangancin binta dakin ta bai san sharrin da za a ce ya yi ba.

Yana zama tana fitowa dauke da yaran dika biyu suna kuka, sunan Huwaila kawai take zabgawa kira, itan
ma kama r zatai kuka.

"Kawo su na taya ki,"

Kallon mamaki ta bishi da shi yaushe ya shigo? Dauke kai tai zata fice ya tare gaban ta,

"Pls allow me, tin da aka haife su ban riqe su a hannuna ba, ko da wannan aka barni ya isa ponishment,
dan Allah,"

Maganar shi haka take, dan kuwa Alhaji ne ya ma yara komai, har huduba, ya ce a barsu da sunan su
Hassana da Husaina, amma iyayin su Huwaila sunce yayi qauyanci da yawa suna kiran su da Yusrah da
Yusairah.
Miqa mashi su tayi taja baya tana kallon su, gwanin sha'awa, shiru taji sun yi, kamar sun san inda suke,

"Kin gani ko? Kin gani suma suna son Abban su,"

Kauda kai tayi tana jin son shi na ratsa ko ina na jikin ta,in za a bi na ta ta yafe masa komai a bar ta ta
koma dakin ta kawai.

Bataji takun shi ba, sai ganin shi tayi duqe a gaban ta, kallon ina ya aje mata yaran ta tayi, ta gan su
kwance saman kujera, suna bacci.

"Umma Hanee dan Allah ki yafen kome na miki, ba zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba, dan Allah
ki ce ma su Hajiya zaki koma dakin ki,"

Hawaye ne na gaske ke zuba a idon Okashatou, yanayin shi kawai zaka kalla kasan yayi nadama da gaske,
hawayen ta tai qoqarin maidawa, ta hanyar kifta idon ta, d daga kan ta sama.
Daga sama suka ji ashar din da ba a bakin kowa ake iya samun shi ba sai tantagaryar mara mutunci da
tarbiyya, ba muryar kowa ba ce face ta Hafsatu, wadda tin tana tsakar gidan ta kira Hajiya Babba akan
gata ta shigo, ta zo su tafi kar Okashatou ya koma gida basu dawo ba, Hajiya na jin haka ta ma Alhaji
magana,

"Is time, tashi muje,"

"Wai ni meke faruwa ne? Kin qi sanar dani komai,"

"Muje zaka ga komai da idon ka yau, nafi son a yi komai da shaida,"

Cikin hanzari suka nufi bangaren Hajiya Babba, wanda ya fara taruwa da yaran Alhajin qanana da wasu
daga manyan ma, dan jin zage2 da tsine2, ba su saba ji ba a gidan su.

"Ka san Allah sai nayi ajalin wannan mayyar, ka matsa ka ban waje, Abban Nour ashe zuwa kk bayan ka
saki mace kana cin amana ta a bayan idona,"
"Wanne irin cin amana na miki, na maida ta in baki sani ba ki sani,"

"Ku......... uba, in ba sai dai yau kowa ya rasa ka ba, dan ba zan hada kishu da wannan yar matsiyatan ba,"

"Meke faruwa ne haka, aka mayar mana da gida kamar gidan dambe? Kaiii kaiii kowa ya bar nan, ku bar
nan nace maza,"

A guje yaran suka bar wajen, Hanee na can maqale a qarshen parlourn tana ta zabga kuka, Huwaila na
dauke da yaran, suma kukan suke, hayaniya tayi yawa, Hanee ta tsani irin wannan a rayuwar ta, bata
saba da fada ba.

"Ke Hafsatu bama son rashin da'a samu waje ki zauna ko baki ga Alhaji ba ne?"

Kallon Hajiya tai sororo wadda fuskar ta ba alamun wasa, ko kuma boyayya lamari, gaskiya ce bayyane a
fuskar ta.
Zama tai, tana kallon Hajiyar, taji me zata ce kuma, dan yanzu ba abinda ke ran ta irin su tashi su tafi, a
mata maganin su gaba daya.

"Wai ni me ke faruwa ne? Ina son sanin me ya faru, me ya kawo ku gidannan da sassafe, har ake zage2
haka, kai me ya kawo ka?"

"Na zo ne dan na ga yara na,"

Wannan shine abinda hajiya Babba ta tsara masa ya fada ma Alhaji in ya tambayi me yazo,

"Ke kuma fa? Me yakawo ki"

Zaro ido ta fara tana kame2,


"Immm ammm, damaa immm"

"Ke muke sauraro, me ya kawo ki,"

Baki ta sake, wace irin tambaya hajiya Babba ke mata ne, ai ta san komai, ya zata tambaye ta gaban
mutane.

"Wai tsaya ma Hafsatu da izinin wa kk fito, ni dai na san baki tambayen zaki fita ko ina ba, amma na gan
ki anan,"

"Dan zan zo gidan ku yanzu sai na tambaye ka?"

"Kwara da gaske, duba da cewar ba zuwan kk ba, sai na tirsasa ki, me ya kawo ki?"

Hajiya Babba ce ta dakko wayar ta ta fara karanta saqon da Hafsatun ta turo, mata kan ta iso, cikin
Hafsatu ne ya kada, kamae zata zaga haka taji.
"Subhanallahi, hajiya me nake sauraro, dake ake zuwa neman magani dama,innalillahi wa inna
ilaihirrajiun, me zan ji?"

Hanee dake maqale a gefe, ta tsaida kukan ta ta bude idon ta sosai tana kallon Hajiya macen da ta ba
matsayin Uwa, me ke shirin faruwa ne?

"Alhaji na rantse maka da Allah, ban san hanyar gidan boka ko malam ba, wannan....."

"Qarya take Alhaji, Abban Nour ka yarda dani qarya take ita ta ban maganin da zan barbada maka a
abinci ko na dafa maka, dan ka daina tinanin Hanee kwata2, ya zama ni ce, ba wata,"

Murmushi Hajiya tayi, amma idon okashatou da Alhaji da Hanee sun yi qulu2 suna kallon ta da
matsanancin mamaki.........
*Hummmmm Hafsatu kenan, in kikai ma Hajiya haka kin sata a ramin da bazata iya fita va*😭😭

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH

Page 26:
"Ban gane kowa yana kallo na haka ba? Kuna nufin kuce min kun yarda sa wannan maqaryaciyar?"

"Bayanin ki ne kawai zai wanke ki, amma ba wai ki tsaya kina tuhumar kallon da muke maki ba Hajiya,"

"Alhaji kome Hajiya zata ce maka ba gaskiya bane, domin da hannun ta a dikkan abinda nake aikatawa,"

Kada kai Hajiya tayi cikin takaici, Huwaila ta kwadama kira da qarfi, ta ce ta kira mata Nour, nan da nan
idon Hafsatu ya fito waje, me Nour zai mata,
"Wai na tambaye ki ma, kin san Nour bai kwana a gida ba jiya kuwa?"

"Nour na tare dani jiya har magariba, a gida ya kwana sai dai in da safennan kika dakko shi, dan ki qullan
wani sharrin,"

"Wannan kadai ya nuna rashin tarbiyyar ki, ki kalli tsabar idona ki dinga nuna ni maqaryaciya ce akan
abinda ni dake mun san ya gaskiyar take,"

Murguda baki tai tai fari da idanun ta, amma zuciyarta sai bugawa take Nour kusan da shi take komai, sai
abinda ba a rasa ba.

Ko da ya shigo bakin shi dumu da mai, tin jiya da dare ta sa Huwaila zuwa ta taho da shi, tin d daren
Hajiya ta dinga dura masa kayan dadi, ta bashi dubu biyu cass a aljihun shi, tinda tarbiyyar mahaifiyar shi
kenan, sannan Hajiya ta masa alqawarin ya zana jarabawar shi ta aji uku na secondary zata sai masa
waya mai kyau da tsada, in dai ya yarda ya fada ma Alhaji da Abban shi gaskiyar Maman su na zuba
magani a abinci, amma in ya san bata yi kar ya fadi qarya akan ta, a nan take ya dinga ba Hajiya labaran
da bata san Hafsatu zata iya aikatawa ba ma, a daki mai kyau ya kwana cikin jin dadi, ga sanyin AC na
ratsa shi.
"Alhaji a gaskiyar magana shine, sakamakon yawan auri sakin da Okashatou ke yi, wanda a gaban ka yayi
mana magana akan Hanee ita din ta daban ce ba zai sake ta ba, kuma tinda akai auren muka tabbatar da
ita din ta daban ce, kai shaida ne, sakin da ya mata sakine na tozarci, shin ko kasan yana wajen aiki ya
dawo ya sadu da ita, yana kammalawa ya rubuta mata takardar saki? Wanne irin saki ne wannan? Kaima
kasan ba banza ba, sannan kar ka manta da kalaman shi na shima bai san meke damun shi ba,wadannan
dalilai ne yasa nace sai na gano komai, amma ta hikima,"

A take Hanee ta fara tinano wasu abubuwa, nan take ta gano tarkon da ta danama Hafsatu, cikin jin dadi
da kauda zargin zuciyar ta ta gyara zama, tare d rufe jikin ta da mayafin jikin ta tana ba yaran nono.

"Ina jin ki, har yanzu baki fadi abinda zai warware maganar tare ake komai dake ba"

"Me kake ci na baka na zuba? A lokacin da Hanee ta zauna a gidannan, na samu na je gidan Okashatou
da sunan zan duba ma Hanee yaran ta su Habibu kenan, dan ta damu matuqa har kuka take, tana tinanin
ya suke, sai na ce zan duba su, kan na tafi na debi garin maganin ararrabi, kai Alhaji kafi kowa sanin
maganin meye ararrabi, na je na tadda Hafsatu na waya akan yanda za a ci gaba da cutar da Hanee, na
kula indai sakin da ya mata ta dalilin maganin da ta ce sun yi mata ne, abinda ta qudurta zasu mata inna
bari ban shiga lamarin ba, to fa zai kama shi, wato ya tsane ta kwata2, ya manta da ita, shine dalilin nuna
mata fuskar na tsani Hanee nima, har na bata wannan maganin, nace tana saka masa a abinci,"
Okashatou ne ya miqe cikin fushi, ran shi a bace Alhaji da Hajiya sun matuqar razana dan basu taba
ganin shi haka ba, kafin Alhaji ya miqe tare shi, yayi ma Hafsatu wani dukan da ya sa ta bajewa a wajen,
numfashin ta na fita kadan2, Alhaji ne ya riqe shi, kawai ya zauna a wajen yarafff yana kuka,

"Haba Alhaji, ka duba gidana yara kashi2 kowa da mahaifiyar shi, meye laifina a auren ta da nai? Ita gata
ba macen da zata ba namiji kwanciyar hankali ba balle na ce, ta tagayyara rayuwa ta. Ta batan suna,"

"Calm dwn boy, ni fa ban ma gama fadin abubuwan da zan fada ba zaka sheme 'yar mutane, ka jira kaji
qarshen magana ta mana,"

"Hajiya na amince da dikkan maganganun ki na fari, na yarda Hafsatu za ta aikata komai, domin na sha
ganin wasu abubuwan da ban aminta da su a raina ba amma nayi shiru, me na mata? Meye laifina,"
"In an ban izini zan yi magana,"

"An baki mana Hanee ai zaman naku ne dika,"

"Yauwa, a gaskiya Abban Nour dik abinda ya faru kusan laifin ka ne, domin Annabi yace maza su zabar
ma 'ya'yan su uwa ta gari, amma kai baka zabi macen kirki ba tin fari, ka zabi Hafsatu a matsin matar
aure, sannan kuma baka bawa ibadar ka mahimmanci, balle asirin da take maka Allah ya katange ka da
ga gare su, koda zai kama ka ba kamar yanda k dinga shiga wahala ba, a gaskiya ko da an gama wannan
zaman, ba zan koma ba har sai naga yanayin riqon ka da addini, wanda muma munyi kuskuren rashin
binciken ibadar ka, dan ba zan koma ba ta tafi ta sake mako mana wani mugun abun ba, i am sorry to
say,"

"Baki laifin komai ba Hanee, domin kuwa na goyi da bayan ki,"

Hafsatu da ta farfado sosai, ta kalli irin kallon da kowa ke mata a wajen, jikin ta ya hau rawa,
"Dan Allah Abban Nour ka min afuwa, Allah ma na yafe laifin bayin shi, nayi....."

"Kin san Allah Hafsatu, ko dake baki san shi ba, da kin san shi da baki dinga kashe aure ba wajen guda
takwas kenan fa, ba dan Allah yasa na maida Hanee ba da shikenan kin takaice ni, da kin lalata min
rayuwa fiye da yanda kikai, kin san ba zaki sake kwana daya a gidana ba, ko leqa qofar gidana ban yarda
ki sake yi ba yanda kk sa nai ta rubuta saki kamar wani wawa, kema sai kin karbi naki a rubuce kuma a
baki, Hafsatu na......."

"Kar ka qarasa dan girman Allah ka tausaya min, dan Allah,"

"Kayi hakuri kar ka qarasa,"


"Okashatou Umarni na ne sake ta, nine uban ka, na san ba kyau saki, daga lokacin da ka auri wannan
baiwar Allah, yarinyat kirki, amma akwai matan da zama da su hadari ne, in ba rabuwa akai ba, zaman su
tare ba zai yu ba, na ma ka alqawarin tsaya maka ka auri kowacce mace kk so, amma banda wannan
baqar kadarar,"

"Alhaji kayi hakuri yarana, dan Allah ka dawo, kar ka dakko,"

Hafsatu ta gigice sosai, Hanee kuwa tausayin ta ya gama kashe ta a zaune, yanda ta hada zufa, take kuka,
majina da hawaye, ga wani baqi da tai, sai kawai ta tuno tashin hankalin da ta shiga lokacin da ya sake
ta, ba shiri ta miqe, tana bada hakuri itama, wani mugun kallo Okashatou ya maka mata na baki da
hankali, baki san kishin kanki ba, nan ta janye jiki gefe, amma sai firtawa take da ya yi hakuri.

"Yara nawa kika mayar marasa iyaye mata a gidan? Yara nawa kk raba dani, iyayen su mata suka dauke
su suka tafi, ko sisi ban taba aikawa kowa ba, Hafsatu kin cutar dani, ga takardar ki nan na rubuta, Allah
ya isa tsakanina dake, kuma Allah ya isan yarana da matan dana saki, na sake ki saki uku, da an halatta
goma goman zan miki, bana son ganin ki har abada, fita ki bamu waje,"

Nan take Hafsatu ta fadi sumammiya, domin duk duniya ko iyayen ta bata so sama da yanda take son
Okashatou, Okashatou shine rayuwar ta, sun dade tare, tsananin son shi da kishin shi yasa bata son taga
ya auri kowa, bata son yaran shi ma ya so fiye da ita, shiyasa ta raba shi da kowa, Okashatou ficewar shi
yayi, ya shige mota,ya dade a ciki, yana kuka, kuka mara lallashi, ba mai ce masa yi hakuri, ba mai ce
masa qara volume,Alhaji ma bai bi ta kan ta ba, tsayawa yayi a bakin qofa yana,

"Saleh, Rabi'u kuzo ku fidda wannan matar a gidannan, maza,"

Ganin halin da Mahaifiyar shi ke ciki, yasa Nour sakin kuka, yana taba ta yana kiran "Mama" Hanee kam
idon ta kamar an bude famfo, ta aje yaran ta dake kuka, ta kama Hafsatu, tana shafa mata ruwa, qannen
Okashatou da Alhaji ya kira, sina kllon ikon Allah, lallai Hanee nada tausayi, ji yanda take kuka, kamar ita
aka saka.

Hafsatu na bude ido, hankalin ta ya fara dawo mata a hankali, ta fara tina me ya faru, ta damqi hannun
ta, taji takardar, da ya bata, ta tina kalaman shi a gare ta, wani ihu ta saki ta shaqo wuyan Hanee da
dikkan qarfin ta,
"Inna yarda Allah ya tsinen albarka, dan bur........ uban ki, baki isa daga zuwan ki ki rusan dik wani abu
dana gina ba, Okashatou nawa ne ni daya, ba wata yar ....... da zata kwacen shi a dare daya.......

*Hummmmm yau ana wata ga wata, Hanee a hannun Hafsy ga Oga ya fece, me kuke ganin zai faru*

*Yeeeeehhhhh yau nasan wasu suna murna na sa anyi saki a novel dina, eh yau kam na sa anyi saki,
masu cewa komai akai bana yarda a raba aure, ba haka bane, maslaha kullum ake nema a gidan aure, ba
yawan saki ba, amma akwai wani limit sa in an kai dole ne fa a rabu, shine mafita, kuyi murnar ku ba laifi
bane💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*🤣🤣🤣 wato jiya na sha dariya sosai ba kadan ba, comments din ku sun min dadi, chaiiiii halin ku ba kyau
dai, anyi saki kuna ta murna🤣 Hansatu tace ku kula in ta kama ku sai ta maku matsar gyada, ko rama, a
toh🤣*
Page 27:

Shiru2 yaga Hafsatu bata fito ba, har ya tada mota zai tafi ya fasa, tazo ta wuce a gaban idon shi ya gani,
sannan ya koma gida ya bada umarnin kar wanda ya budr mata qofa, ta shiga masa gida.

Cikin gidan kuwa ana ta qoqarin kwace Hanee, wadda muryar ta ta daina fita sosai, saboda shaqa, sai
miqa hannaye take ko za a samu mai fisge ta, Hafsatu kuwa sai ashar take tana sai dai kowa ya mutu, sai
ta kashe Hanee ta kashe kan ta, ja tai da baya ji kake qumm ta buga Hanee a jikin gini, Nour sai kuka
yake yana kiran ta bari, Alhaji ya shiga rudu, sandar dayake dogarawa ma ya kasa jingina a jikin ta ya
mata nauyi, zamewa yayi ya zauna a kujera jikin shi na rawa sawa yayi a kira mazan gidan, suzo ko da
bala'i a banbare Hanee data galabaita matuqa.
Okashatou daya shigo yaga qofar dakin ta cika dam da 'yan uwan shi, ana ta sa'insan shiga,saboda ba
yanda za ai a kwaci Hanee ba a ji mata ciwo ba, kutsawa yayi, Nour na ganin shi ya diba da gudu wajen
shi, yana kuka, yana roqon Abban su daya taimaki Ummen su Habibu.

Cike da fushi matsananci ya tinkari Hafsatu, yanayin fuskar shi da alhaji ya gani yasa ya yi ma qannen shi
umarni da su riqe shi kar a yi kisan kai a gidan shi, Hafsatu na hada ido da shi, taga iya tsahon shekarun
su bai taba shiga wannan yanayin ba ba shiri, ta sake Hanee zata falla da gudu waje, cunkoson mutan
gidan ne ya bashi dama ya fizge ya cafke ta, hannun shi a dunqule ya dinga kirbar ta, kwata2 ya haukace,
sai dukan ta take, ko ta ina, sai da ya mata laga2 idon ta ya wani lafke guda dayan ya shiga ciki, yana
budewa dishi2, da kyar take tafiya tana neman mafaka, Alhaji ne ya daka masa tsawa ganin zai bi ta.

"Okashatou ! Baka da hankali ne kashe ta zakai? Kar ka kuskura ka sake koda taku daya ne, ranka zai fi na
masu kwasar kashi baci, na fada maka,"

Tsayawa yayi jikin shi na rawa, hannuwan shi a dunqule, idon shi da farar fuskar shi sun koma ja, da bai
dawo ba kenan sai dai ta kashe mashi farin cikin shi, uwa a wajen yaran shi gaba daya, wadda take son
taga ta gyara rayuwar shi duniya da lahira, lalli da ko court ba zai bri a je ba zai kashe ta da hannayen shi,
ya daga hannayen yana kallo, da tsantsar baqin ciki.
Wata qara sukajia bayan su, tare da jan numfashi sau ba iyaka, Hanee ce ta watssake, daga shaqar da ta
sha, take bude murya dan azaba, kuka mai tsanani ta fashe dashi, yatsun Hafsatu kwance a wuyan ta, dik
da baqa ce ita sai da ya nuna, da gudu Huwaila da Okashatou, da Hajiya suka nufe ta, fadawa tai jikin
Hajiya tana maida numfashi tare da koka azabar da ta sha.

Suna haka Hafsatu ta samu dama ba wanda ya gan ta.ta sulale zata gudu, ta damqo hannun Nour, sai da
suka kusa zuwa gate ya fizge, juyowa tai ta kalle shi tace,

"Dan uban ka mu gudu, kan ya dawo ya illata mu,"

"Ya illata ki dai, nayi nadamar kasancewar ki uwa a wajena, da ana sauya mahaifiya dana sauya ki, ba zan
taba bin ki ba, zan zauna da Ummeen su Habib, nima ta zama uwa ta daga yau, bana son ki bana son ki,
tinda har kisa zaki iyayi, wataran zaki iya kashe ni saboda ni jinin Abba ne"
"Me kk fada haka, kasan ba zan taba cutar da kai ba, kai ne abinda nake so a duniyar nan na biyu bayan
mahaifin ka, ka zo mu tafi ko zan ji sanyi a raina, kar na zama banda kowa,"

"Ba ind zani, gwanda ma ki gudu kan Abba ya juya yaga baki nan ya biyo ki, ban yard kina so na ba, dan
baki taba nuna min hanya mai kyau ba, a zaman nan da akai na fahimci meye ma'anar kyaun hali, Mama
ba inda zan biki, bana son ki,"

Da gudu ya koma ciki ya barta a wajen, sai kwala masa kira take tana kuka, ganin Okashatou, riqe da
Hanee a hannu, da dikkan alamu asibiti za su kai ta, ya sa ta falla waje da gudu tana kuka, dik wanda ya
gan ta ba zai raba dayan biyu ba mahaukaciya ce.

Asibiti yaje da Hanee aka duba ta, aka bata magunguna, amma maganar ta ta shaqe sosai bata fita, in ta
zauna ita daya sai tayi ta kuka, meye laifin ta daga haihuwa suna kwana daya ta sha wannaj azaba? Ko
azabar naquda bata manta ba.

"Allah na gode maka da jarabawowin daka ke jarabta ta da su, Allah ka ban ikon cinyewa,Alhamdu
lilLAAHi ala kulli halin,"
Jiyo maganar Okashatou tai ta waje, da su Alhaji,

"Dan girman Allah ku ban mata ta na wuce da ita da yarana, yara na gida suna buqatar ta yanzu, Abba
ina buqatar mata ta. Kar ku shiga haqqina dan Allah,"

Cikin tsananin karaya ya ke maganar.

"Ikon Allah, sai yanzu ka san haqqin ka? Ita da da ka tauye mata nata haqqin baka yi tinani ba sai da aka
tauye naka ko? Son kai ko? To sai likita ya gama da ita, mun gani, motar ka zata shiga ko tamu, muddin
ta shiga tamu kasan allah gida zamuyi da ita, kar kaji da wai,"

Shafa kan shi yayi, yana furzar da iskar bakin shi, roqon Allah yake yasa ta bi shi, in ba haka ba yau sai
zuciyar shi tayi bindiga.
Likita na gamawa da ita, Okashatou ta tallabo ta, yi tai kamae bata ji me ya faru tsakanin su ba, ta bi
bayan Okashatoun bata kwace ba, suna fita ya sake ta, yaga ina zata zaba, motar ta nufa ta bude ta
shige, Hajiya Babba da Alhaji da Okashatou suka bude baki gala2 suna kallon ta..................

*Cassssssss Hansai an sha nada, aje ai jinya🤣🤣🤣*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 28:

Motar Sa'id da su Sammani ta shiga, Sa'id ya dage qafa, ya ziro ta ta window, tana shiga ya juya shi da
Sammani suka kalle ta, Okashatou da su Hajiya ma ba su daina kallon ta ba, tana shiga ta jingina bayan ta
a jikin seat din motar ta lumshe ido,
"Yah Sammani pls mu je gida,"

"To to to to shikenan,"

Da sauri Sa'id ya gyara qafar shi suka fara tafiya, anan Alhaji ya fahimci ta ji su, kuma wannan kamar
magana tayi tana son komawa gidan mijin ta, kuma tana son zama da su, ke nan su zasu zauna suga
abinda ya dace, murmushi yayi, Hanee na burge shi matuqa.

Shigewa motar su sukai, aka bar Okaahatou da bai gane komai ba, zuciyar shi baqiqqirin na ganin rainin
hankali irin na Hanee, yanzu duk abinda ya faru ba zata tausaya masa ta gane ba laifin shi bane, and he
loves her so very much, what is with her?

Hannun shi a jikin window yana shafa kan shi, cikin bacin rai ya ke tuqi, yana zuwa gida ya bada umarnin
kar a kuskura abar Hafsatu ta zo kda bangon gidan shi ne bare ta shiga, duk wanda ya barta a bakin aikin
shi, tadda yaran cirko2 yayi, wasu sunyi kuka sun gaji, jansu yayi zuwa bangaren Hanee, ya dafa masu
indomie, kafin ta dahu shima ji yake kamar yayi kukan, yara ko ta ina, gutsi2 hakan nan,ina AURI SAKI
yaga amfani? Yanzu ga shi wanda zai kular mashi da su ma babu, yau koda cewa akai Hanee zata dawo ai
aiki ya mata yawa, ba zata taba iya kula da yaran nan ita daya ba, dole sai an taya ta.
Bai san sanda hawayen takaici da tsanar Hafsatu ya kufce ma idon shi ba, sai qaramin dan shi gaba daya
gidan ne ya kwanta a jikin shi, yana kuka shima, yana kiran "Mama"

"Shiiiiii Usama, maman ku bata nan, amma Ummen su Habibu na nan dawowa inshaa Allahu,kuyi
hakuri,"

"Abba haka kk cewa kullum Ummeen mu na nan dawowa amma har yanzu bata dawo ba,"

"Wannan karon da gaske nake, inshaa Allahu zata dawo, yau dai ba zuwa makaranta, a jira malam yazo,"

Gyada masa kai sukai, ya tashi yaje ya juyo masu abincin, ya zuba nashi, yara suka ci sukai dam, nan da
nan wasu suka fice wasa tsakar gida, yau bai ga ta fita ba yara su kadai, dan haka ya zauna cikin su, ko
bari2n da ya dinga yi, shi kadai sai da ya sa shi jin ciwon kai, ashe mata na qoqari?
Hanee wadda ta shigo daki ta tadda Huwaila jage2 da zufa,yara na ta tsala kuka, iya qarfin su, ta amsar
mata su, ta zauna, bata ce komai ba, saboda ko tai magana ba fita maganar take sosai ba, nono ta fara
basu, da kyar suka karba saboda kuka.

"Ya jikin ki?"

Cikin shaqaqqiyar murya ta amsa ta

"Da sauqi,"

"Masha Allah, Allah ya kiyaye wannan mummunan lamari, Allah yasa kun rabu da wannan baqar
qaddarar har abada kenan,"

"Ameen"
"Hanee me kikai kenan? Me hakan ke nufi muna tsaye ki wuce ki barmu?"

"Hajiya kiyi hakuri, amma naji hirar ku, bana son na bi shi ya zaci dan shi zan koma, sannan bana son na
biku ku zaci ina son na ci gava da zama nan, ina son komawa wajen yarana,they need me now, they
really do, plss i want to go back, they have no one to take care of them,"

"Haka ne, amma ki bari ki qara sati ko biyu ne mana? Kinga kema jikin ki ba kwari, kina buqatar kulawa,"

"Haka ne, amma Hajiya me zai hana gidannan akwai 'yammata da yawa a bamu ko uku ne su taya ni kula
da su mana, barin su su kadai har sanda zan koma matsala zai haifar, bamu san me zasu aikata ma juna
ba,and bamu san me ye plan din Hafsatu ba akan yaran ta,"

"Kinyi tinani mai kyau, bari zan sanar da Alhaji da Okashatoun tinanin da kikai,"
"Hajiya kiyi hakuri in tahowa ta bata maki dadi ba naga baki sake ba har yanzu😔"

"Ba komai Hanee ke yarinya ce mai biyayya,gaki qarama amma sai hankali, ban fushi da ke ba, sai dai ina
roqon ki kar ki sanar da iyayen ki abinda ya faru yanzu har sai kinji sauqi sosai, gudin kar hankalin su ya
tashi,"

"Amma Hajiya boye masu wani abu daya shafe ni na bata ran Amma da Abbana, ina ganin ya kamata na
sanar da su, in yaso sai na fada masu komai ya wuce,"

"Kin yi tinani mai kyau hakan yayi OH ni, yanzu haka za su ji wannan mummunan labari"

Dan murmushi Hanee tai, ta ce,


"Haka abubuwan ke ta kasancewa ba wanda ya zata,"

"Haka ne, bari na dan je na huta,"

"To hajiya a fito lfy,"

Bayan fitar Hajiya Huwaila ta gyara kwanciyar da tai, tana kallon Hanee,

"Allah ya sa dai ba dani zaki ce a je gidan ku mai yara mitsi2n nan ba, dan in ba rainon wadannan
qananan ba ba yaron da zan iya kula da shi, dan ubansu ma ba mutunci ne da shi ba ehe,"

"Haba Huwaila, ni da ban hada jini da uban su ba da iyaye su mata nake jin soyayyar su a ruhina, balle ke
da kk qanwa a wajen.mahaifin su, kk Goggon su, habaa, meye ma'anar zumunci.ne?"
"Ke kina da zuciya.me.kyau, bance banda zuciya.mai kyau ba amma ba zan iya irin naki ba, dan a gaskiya
yaran ku ba su da tarbiyya, har zagin manya suke,"

"Hummm Huwaila kenan, wato a yanzu zumuncin mutanen yanzu na ban mamaki, in fa da ke kk haife su
ko mai rashin kunyar su, haka zaki so abinki, ki ta ririta su, amma na dan uwan ki kk qi, haba, in baki je
kin daidaita masu rashin kunyar tasu da kunya ba wa kk ganin shine mafi cancanta da yayi hakan? Kina
nuna min kema kina daga mutanen zamani masu nafsi nafsi, daga ni sai 'ya'ya na, na 'yan uwana ba
ruwana da su, shikenan ni da nake auren uban su na kula da su, kar Allah ya gajiyar dani,"

"Murya a shaqe sai bayani, shikenan, naji nasihar ki, gaskiya ban kyau ta ba, amma inshaa Allahu zan
taimaka matuqa wajen gyara tarbiyyar su, na gode danuna min mahimmancin zumunci"

"Ba komai meye na godiya, na dauke ki a matsayin 'yar uwata ne, kuma haqqina ne na tunatar dake,
kamar yanda yake haqqin ki ki tunatar dani akan abinda ya dace,"

"Haka ne"
Hannun ta ta dan shafa a saman na Hanee, sannan ta juya ta kwanta,

"Kar a tashen sai an kira sallah, in wadannan yan mitsitsin na kuka ku tafi parlour "

Dariya Hanee tai kawai ta ci gaba da kallon yaran ta, tana tinani kala2, na zama bai gan ta ba,saboda dole
ta miqe wajen ibada da addu'o'in tsari, saboda bata san me Hafsatu zata qulla mata ba.

Bayan fitar Hafsatu kuwa, ta dade a sakade a wani lungu tana kuka, da.dana sanin biyewa Hajiya Babba
da tai, sai yanzu take ganin wautar ta, ko asirin zatai yama zata biyewa umae miji dama? Kaiii amma she
is so stupid, dan marin kan ta tayi ta ko zunduma ihu, saboda tabo ciwon fuskar ta, ba abinda ke bata
tsoro irin yanda fatar idon ta ta sake a jikin idon, d kyar take gano abu da idon, Allah yasa bata nakasa
ba, dama ga ta ga kamar ta wa zai kwasa a hakan?

Tana gama.kukan tai ta tsaida masu abin hawa su kaita unguwar su ta samu ko yara biyu a nata ta kwasa
kan Okashatou ya koma gidan, amma dik wanda ta tsaida ya gan ta a haka sai su hau tinanin kar dai ko
bin ta ake su dauke ta su jama kan su bala'i, sai da tai kusan rabin tafiyar a qafa, sannan wani ya dauke
ta, a make yake, dan haka tana fada masa ya figi adaidaita sahun , ba su tsaya ko ina ba sai a qofar gidan,
tace ya tsaya yanzu zata fito, ta dade a bakin qofa tana buga gate kan.me gadi ya leqo, yana ganin ita ce
ya koma, dan Okashatoun bai jima da shiga ba, yace kar ya ko kula ta, in ya kuskura ya kula ta to a bakin
aikin shi.
Ai komawa yayi ya zauna, ya sake rufe gate din, haka tai ta bugu ba wanda ya kula ta, Okashatou na ciki
yana faman bari2 da yara ko ji bai ba ma.

Kuka ta fashe da shi, tana cikin kukan taji muryar mai adaidaita sahun,

"Yahhhhh Hajiya ban boza ta na qara wuta amma ba ta qiyama ba,"

"Kar ka kuskura ka nunan tasha zan nuna maka mu muka haifi 'ya'yan cikin ta,ko baka gane va, ka barni
na ji da abinda ke damuna,ba biyan ka zan ba ko nawa ne tinda ni na dakko ka"

"Kayya kayya Hajiya yaqar ne billahillazi, ke din banza dube ki fa,har kk kiran kin san hanyar tasha ma,
vaki sanni bane yanzu na miki kuyaaaa ehhhh"
"Abun ba a fuska bane, ka kama kan ka yanda nake a zuciyen nan, dan matsiyata ga kudin ka na nemi
wani ya kaini tasha,"

"Eh bani kudina, kece matsiyaciya, wa ya sani ma ko kilaki ce farkan ki ya jibge ki ya rufe gidan,
kutu......... uba😆"

Yana maganar yana dukan adaidaita sahun nashi yana dariya, gaarda duqawa, Hafsatu ta kai ko ina
wajen fushi,amma ba zata iya masa komai ba, saboda ta kula ba qaramin dan daba bane, kudin ta zaro ta
miqa masa, ganin damman kudi a jikin ta yasa ya sauya shawara.

"Hajiya kinga banda canji kawai muje na aje ki tashar ko ya?"

Jimmm tai tana tinani, ganin ya kamata ta samu mai fidda ta, ga shi rana ta kwalle, ga nisa tsakanin titi
da inda suke, shigewa tai bata ce masa komai ba, ranta bace, sai da ta shiga ta furta,a hankali
"Qaramin dan iska, da kar ka sakko mana"

Ya jita sarai bai kula ba, abinda yake saqawa a ran shi, da zata sani da ta fita a guje.................

*Lalinya in kina takalar salihai kina sha ga 'yan duniya wanda ta haifa ido rufe muje zuwa*😃😆

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

_Makaranta wannan novel ayi hakurin rashin jina da ba ai ba, ya faru ne sakamakon gobara da
maqotana sukai, ina mai ma mata nasihar su kula da wuta a wannan lokaci da muka fara shiga na sanyi,
maganin sauro ne, wutar lantarki ne ko ta murhu, a dinga kiyayewa gudun haifar da gobara, Allah ya sa
yanda muka fara shiga sanyin nan lfy ya sa mu fita lfy, Allah ya kare mu daga hadarin dake cikin shi._

Page 29:
Sunyi nisa taga ya dauki hanyar wata unguwa dake kusa da su, wadda tafi tasu kyau da shiru, ta rasa
gane me ya hada hanyar tasha da wannan hanyar, jikin ta ne ya fara sanyi, cikin ladabi tace,

"Malam ya naga mun biyo tanan? Mu tafi inda zaka kaini mana,"

"Hhhhhhhh haba qaramar 'yar tasha, ya naji har kinyi sanyi ne? To uwar ki zan ci anan din, dan sai kin
gane da Algus kk sa'insa,"

Wata qara cikin ta yayi, ta damqi cikin tana yamutsa fuska, zafin da taji a fuskar ta ne yasa ta daidaita
fuskar,
"Dan soyayyar da kk wa manzon Allah kar ka taba lfy ta, indai duka je na daku iya dakuwa yau, banga me
zaka diba a jikina ba yau, ka taimaken mu rava kudin jikina ka kaini tashar nan dan Allah,"

"Amma ke muguwar yar rainin hankali ce, kawai sai na barki haka? Ai yacin sai kin ci uwar ki yau, ai na
fada maki dan tasha ne ni, zan nuna maki tasha, ke sai ku nunan yanda kkai kk haifi yan tashan,"

Awa ni waje ya tsaya, gidaje ne manya sosai, kantangar gidajen masu nisa da juna su ne, wajen shiru, za
a iya fiye da awa biyu zuwa uku mota ma bata wuce ba, parker wa yayi, ya fizgo ta, jikin ta sai rawa yake,
naman jikin ta kan shi rawa yake, dariya ya dinga yi, yana kiran ta da sunaye kala2, roqon shi ta dinga yi
ko na mota ya bar mata, zata Kaduna ne,maruka masu kyau fiye da biyar ya wanwanka mata, in ta sa
hannu yace sun zube, dan ya qirga iya ya yayi niyyar mata, fuskar Hafsatu, kamar an watsa mata barkono
mai tsananin zafi take ji,

"Kwanto kudin, yar......."

Da sauri ta ke qoqarin kwancewa amma rawar da jikin ta keyi ya hana saurin, ware zanin yayi da kan shi,
nan da nan kuwa zanin ya kunce, ko skirt bare pant babu jikin ta, da sauri ta rufe qafafun ta, tana
kyarma, idon ta da suka lafke ta ke qoqarin dagawa jin da tai ya daina qoqarin kwace kudin,kallo ya bita
da shi.

"Dama nace kilaki ce ke kin musa min, me ye na yawo ba komai cikin jikin ki, kiran customers ko,
shikenan, ban kudin,ki gani,"

Da sauri ta duqa ta dakko kudin, ta miqa masa, ta daura zanin ta, ciwo dubu biyar yayi a kudin ya bata,ya
ja ta cikin a daidaita sahun ya sake labulayen, kwance zanin ya sake ya kwanta saman ta,

"Ga kudin ki nan na biya ki, kilaki, wataqila farkan daya dake ki ne ya biya ki ya jibge ki, da nai niyyar
kwace wa dika amma ga shi nan na ma maki mutunci zan biya,"
Wani irin kuka mai matuqar ban tausayi ta saka, muryar ta tasauya saboda kuka,

"Ka min hakuri, ni din uwa ce, ina da yara har bakwai, mijina ne ya min wannan dukan, amma kudin na
rantse maka nawa ne, kayana na saida zan amfani dasu, dan Allah kar ka aikata zina dani, ban tava aikata
zina ba tin kan aure na balle yanzu, ka ji qaina,"

Make bakin ta yayi, ya fara qoqarin aikata masha'a da ita, wata mota ta tsaya daidai wajen, masu motar
suka bude, ganin yanda fuskar Hafsatu tayi, gashi yana qoqarin danneta ya sa suka fisgo shi, a bige suka
gan shi, wani mari matashin ya wanka masa, ba zai wuce shekara sha takwas va, dan masu kudi ne da
dikkan alama, dayan matashin kuma da qafa ya tokare shi a ciki, nan ya dinga zunduma ihu, yana neman
taimako kamae yanda Hafsatu take yi a baya.

"Farka ta ce mun dawo daga gidan karuwai ne take min gardama,"


"Qarya yake shege, qarya yake, mijina ne ya saken saki uku, ina son na kona kaduna na ce ya kaini tasha
shine ya kawoni nan, ya amshe kudina, yana son yayi lalata dani, Allah ya kawon ku, ina da da daya kusa
girman ku na gode maku Allah ya muku albarka,"

"Ba surutu muke so ba, kai kana da kayan aiki? Dan na gan ka na gida ne kaima, ke wuce ki bar nan, ai
mun taimaka iya yin mu ko?"

Cikin sauri ta fara tattara kayan ta tana mamakin wanne irin kayan aiki suke magana akai?

"Akwai kayan aiki, amma da tsada, shiyasa na ke son na kwace kudin hannun ta naje na siyo wani,"

"Baka da matsalar kudi, je gaba muna baya ka kaimi wajen siyarwa,"


Tafawa sukai da abokin nashi, Hafsatu tayi nisa da su sosai, ga shi bata san ma unguwar ba, bata taba
zuwa ba sai suna abaki, haka suka wuce ta, aiko ta sa kuka tana zagin su, ga rana, yau dai taga duniya,
haka ta fita titin da zai sada ta da babban titi, a qafa, nan ma ta dade kan ta samu mai adaidaita wani
dattijo ne ya dauke ta, ya tausaya mata ne shima, ya kaita tasha, yau sai gidan Aunty mami, taga duniya,
ko gida ba ta isa zuwa ba, bata da sauran abinda ya rage mata dama.

Bayan ta biya kudin mota ne, ta jingina sai baccin wuya ya dauke ta, har mota ta cika aka fara tafiya bata
sani ba.

Bayan Hanee ta kammala komai, bayan sallar la'asar tayi wanka da yaran ta, sunyi fess da su, kwanin
sha'awa, tayi matuqar kyau, tayi dum2 da ita ko ta ina ta cika, cikin ta na ta sauka, yana komawa yana
lafewa, sai hips da tai, kwanin kyau, ta daura wani lace mara nauyi, kalar marun, ya amshi kalar ta mai
duhu, tana kwance yaran ta zube gaban ta, Yusrah nata kalle2, Yusairah na bacci, wayar ta ta dakko ta
nemo no Amman ta, tana tinanin yanda zata fara bata labarin abinda ya faru.
Wayar bata dade tana ringing ba Amma ta daga, suka gabatar da sallama, da gaishe2, shiru ne ya biyo
baya,

"Hanee dear meke faruwa, da dikkan alamu bakin ki nada magana, me kk son fadan?"

"Amma labari zan baki,wanda bana son ki daga hankalin ki, yanzu haka danake maki magana, kwance
nake a kan gado da yarana, cikin kwanciyar hankali da cikakkiyar lfy,dan haka baki buqatar tada hankalin
ki akan abinda zan fada maki dan komai ya wuce,ba dan kar kiji daga baya ba ranku ya baci ma da bazan
fada maki ba,"

"Nikam surutun nan ya isheni, sanar dani me ya faru,"


Gyara kwanciyar ta tai zuwa zama, ta labarta mata komai, bata rage komai ba,ta sanar da ita gaskiya,
Amma ji take kamar zuciyar ta zata fashe dan takaicin jin abinda ya sami gudan jinin nata, abin son ta,
amma ba zata karyawa diyar ta kwarin guiwar da only gods knw ina ta same shi ba, dan ita kan ta bata
shiga rudanin rayuwa kamar yanda Hanee ta shiga ba, amma takw hakuri, dan haka gwarin guiwa zata
bata.

"Amma gaskiya abinda ya faru bai dadi ba, na gode wa Allah dayasa iyayen mijin ki ke tsaye akan ki akan
komai, da yake faruwa dake, ba surukai gare ki ba iyaye gare ki, dan haka ina maki nasihar ki riqe su da
amana, Allah ya qara kauda abin qi, kuma ita Hafsatu zamu mata addu'a Allah yasa ta gane, kuma Allah
ya tsare ku daga sharrin su, domin kuwa sai kin dage akan yanda kk addu'a bamu san meye shirin ta ba
yanzu,"

"To Amma na gode da kk fahimci komai,"

." Ba komai Abban ki ma ba sai ya sani ba, dan nasan zai fini daukan zafi, zaice anyi wancan ga wannan
ba zai bari ayi na uku ba, saidai game da riqe yaran nan aikin fa zai maki yawa zaki iya?"

Cikin tausayawa irin ta iyaye take mata tambayar.


"Ammaaaaa i am not a kid anymore, i can do it, kin manta da ina yi? Yanzu ma zan iya,"

"Yaran da dana yanzu akwai bambanci ai,"

"Amma za a ban wasu 'yammatan su taya ni komai karki damu kinji Ammana?"

"To shikenan, Allah y taya ki ruqon su kinji? bana jin ki sam wajen wannan, dan ke 'yace, yaya kuma uwa
ta gari inshaa Allahu, sai anjima zanje na hada ma Abban ku zobo,"
"Na gode Amma da yarda dani da kikai zan iya, hakan ya ban kwarin guiwa, Amma nai missing din zobon
ki mai dadi kamar na zo nasha, infact nai missing gida sosai,"

Muryar ta ce ta fara rawa, ita kan ta Amman nasu tana kewar diyar ta, dan haka a gurguje ta mata
sallama.

Lumshe ido tai hawayen ta ya gangaro, ta share da hannayen ta, a hankali ta furta.

"Aure mai sauyawa mace rayuwar ta, daga yanda take hasashen ta zuwa yanda batai tinani bama,"

Wayar ta ta duba wajen hotuna tana kallon hotunan su da sukai ita da Okashatou lokutan da yaje jin
nishadi, matsananciyar kewar mijin ta ke damun zuciyar ta, sai take jin kamar bata da kowa data damu
da shi a gefen ta, ni ko nace uwar son miji kawai😏uffararan ba haramun bane🙊😃
Motar su Hafsatu na isa, daf da magrib, taji wata nutsuwa na shigar ta, a ganin ta tazo inda za a share
mata kukan ta, ko da kudin ta ko ba kudin ta, tasan Auntyn ta ba zata bada mata qasa a eyes ba............

*Cassssssssss maji ma gani in tusar Mum Manal na huta wutar iccen marke*🤣🤣🤣😝😝

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI. 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

*Ayi hakuri page dinnan ba yawa, dan kar kuji shiru ne yasa nayi gaskiya, amma abubuwan sai shukran
lillah kawai, thanks all*

Page 30:
Aunty Mommy ta fito daga kitchen da duhun magariba ta ga mace shajaran majaran kwance a qasan
center carpet din ta, ihu ta sa ta sake cup din hannun ta ta juya kitchen da gudu, tana fadin,

"Wayyooo Alhaji kazo ka taimaken mahaukaciya ta shigomin parlour, wayyooo Allah dan Allah kiyi
hakuri, me gadiiii"

Sai sambatu take, jin haka Hafsatu a gajiye ga tsami da jikin ta ya yi mata ta miqe a hankali tayi hanyar
kitchen din itama, tana furta,

"Aunty nice fa, Hafsatun kice, ki fito,"

Inaaa Aunty Mommy ba jin ta take ba sosai. Muryar ta tayi qasa ita kuma ta daga murya tana ta zuba
ihu, mijin ta na fitowa daga toilete yayo waje dan jin ihun ta,ita ko ta dakko plate ta wurgo ma Hafsatu
tana bata hakuri kar ta shiga mata, ta yi hakuri, da kyar ya gane Hafsatu shima, da qarfi ya shiga yana ma
ta bayani,
"Haba Mommy ni na gane Hafsatu balle ke? Meye haka kk yi kamar wadda tai gamo?"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Hafsatu me ya same ki kk sauya haka gaba daya kamar ba ke ba, ido ya
zazzago haka, na shiga uku,"

Kama hannun Hafsatu da ta fara kuka saboda tausaya ma kan ta da tai, suka zauna a kujera, mijin
Mommy ya debo masu ruwan sha, Hafsatu taqi sha, tace abinci za a bata, bata son ruwa, ai ko french
rice da miyar kaji ya debo mata, Mommy har lokacin jikin ta bai bar rawar tsoratar da tai ba, ya sha asiri
mijin nata har ya gaji, komai shi yake yi, sai in ita taga damar yin abu, hatta masu aiki in ba maza ba dake
gyara waje bata da ita shine matsayin me aiki, yayi share2 wanke2 da girki, tana zaune, wataran ma ko
wanka sai tace shi zai mata, da iko ba wai dan soyayya ba,sai ya gama mata komai da sassafe yake fita,
amma a waje kamar wani zaki.

Hannu baka hannu kwarya take cin abincin, kamar wadda ta shekara bata ci ba, tana gama ci ta sha
ruwa, ido ya fara lumshewa, a wajen ta bingire sai bacci, zama sukai suna kallon ikon Allah,me ya faru?
Amma sun barwa kan su sai ta farka su tambaye ta.
Hafsatu ba ita ta farja ba sai goma na dare,ba sallah ko daya a cikin sallolin farillai, da miqa ta tashi, d
sauri ta aje hannun ta dan tsamin da yayi, jitai Aunty Mommy tace,

"Kinga je ki wanka kiyi brush,ki zo ki fadan me ya faru, kk taho kamar wnda mugayen 'yan fashi suka
tarfa suka lafta,"

"Hummmmm Aunty ba gwanda 'yan fashi ba da abinda ya samen, bari dai na fito,"

Wanka taje tayi, ta saka doguwar riga ta baccin auntyn ta, wata kalar ruwan goro, kai ba dankwali, gashi
ya yi duqun2.
A bakin gado Auntyn nata ta zauna tana fuskan tar ta umarni ta bata na ta sanar da ita me ya faru? Sai
da tai ajiyar zuciya ta zayyane mata komai, aiko ran auntyn nata ya baci sosai,wato bata yarda da ita ba
tafi yarda da uwar miji? Ai gashi nan sun mata halin dangin miji, a fadar ta.

"To da kk taso kk zo nan, me zan maki yanzu,sanin kan ki ne bana yafiya, kuma kin min laifi, na rantse ba
taimakon da zan maki, tinda ke baki da hankali, dik abinda na maki a rayuwa har zaki iya juyan baya wai
ki hada kai da wata ba zaki zo na taimaka maki ba, har fada maki nai kome kk so ki min magana kin raina
nawa ko? Sai ki koma wajen uwar miji ta maki,"

Cike da tashin hankali,saboda ta san halin yayar ta ta, in tace bazatai ba ba shegen da zai satayi, damqe
qafafun ta tai, dik da zafin da gefen fuskar ta da hannayen ta ke mata,tana bata hakuri, akan kar ta barta
ta wulaqanta,

"Aunty ki tausayan na san na yi kuskure, ba kadan ba, dan Allah ki yafen ki maidan martaba ta a gidan
Okashatou, in ba shi mutuwa zan,"
Kukan da take ya daga mata hankali sosaia hankali ta zauna ta rungume ta tana lallashin ta,

"To ya wuce, amma saki nawa ya maki?"

"Saki uku,"

"Tabdi, aiko da kyar ya yarda ya maida ki, "


"Dan Allah aunty ki taimaken, ke ce fa mai kaini inda ake sharewa kowa hawaye,sai dai in baka ce
ba( banda ni wallah Allab kadai ke sharen hawaye na,ke fa? Kai fa?) Aunty dan Allah ki sa a maida auren
nan, na maki alqawarin ba zan sake maimaita kuren da nai a baya ba,"

"To shikenan, amma abun da kamar wuya, tunda kinga anyi saki Uku fa,"

"Dan Allah ki taimakan aunty, ke ni ko ba aure zan iya zama da shi,"

"Allah ya kaimu gobe to,sai ki shirya da wuri, dan kin san wajen da muke zuwa akwai layi sosai,"

"To aunty na gode,"


.

"Sai da safe,"

Tashi tai tana taku cikin takalmin ta mai tsini, duwais dinnan a sama,suna kaduwa, Hafsatu hango ta take
an mata asirin da zai hana Okashatou rawar gaban hantsi, ko tashi sai da umarnin ta ta bashi ikon yi,
wani murmushin mugunta ta sake,fusnar ta tayi wasai yanzu, idon ya bude tarr, bayan duka harda
yunwa da wahala.

Da safe Auntyn ta ta shirya,mijin na shara, yana tsaye yana kallon yanda taci kwalliya, qamshin turaren
ta in ta fesa ko tabar waje da awa daya yana nan, cikin ran shi kamar zai bindiga, dan kishi da takaici.

Kwalama Hafsatu kira take tayi, amma ba amsa, gajjya tai da tsaiwa ta bude qofar, abinda ta gani ya
firgita ta kwarai, ya sa ta zamewa qasa sumammiya............................
*Wayyooooo Haermeebraerh me ta gani a ci gaba😭😭😭🤣🤣🤣😝😝😝😝😝💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻sai gobe thanks all da yava
min da kuke, hakan ke sawa nima nake dagewa dan faranta ranku*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAEH

Page 31:
Da gudu ta qarasa gaban ta, bayan ta tura qofar, kuka ta fashe da shi, mai ban tausayi, ganin abinda ya
faru, hasashen ta ya bata cewar, fitowa tai daga wanka, santsi ya kwashe ta, ga glass cup din data sha
madara jiya kan ta kwanta, ta fada akan shi ya fashe ya soke ta a kan ta,jini ya wanke wajen da kan nata,
dubawa ta hau yi kamar mahaukaciya ko zata ga alar rai a jikin ta, shiru ba ko nunfashi, ihu ta zunduma,
mijin ta ya shigo da sauri, yana ganin ta a haka ya ja ya tsaya, ganin ya tsaya a bakin qofa yasa ta daka
masa tsawa,

"Shigo mu shirya ta muje asibiti ko tana da sauran nunfashi, na shiga uku,"

Da sauri ya shiga suka sa mata kaya, ya ciccibe ta sai mota, Mommy da aka saka takalmi mai tsini nan da
nan ta sauya, ta saka flat shoe, ko da suka je asibiti, likitoci suka duba ta suka tabbatar da rasuwar
Hafsatu, kusan haukacewa Mommy tayi,ta dinga birgima tana ihu, ba wanda ya iya controlling din ta, sai
sambatu take,
"Hafsatu dan Allah ki tashi, na miki alqawari zan kwatar maki 'yan cin ki, ba zan sake bari a cutar dake ba,
wayyooo Allah na shiga uku,"

Mutanen da ba su san asalin meke faruwa ba sai suka fara tausaya ma Hafsatun, suna tinanin wata qila
cutar ta ake a wani wajen, bsu san ita ke cutarwar ba.

Gawar ta aka basu suka nufi gida,Aunty Mommy ta daina kukan yanzu sai tinani kala2, jiya2n nan fa tazo,
tazo zasuje wajen boka domin ya biya masu buqatar su akan Olashatou, amma wai kwalba tai sanadin
ta,ta koma ga mahaliccin ta, nan da nan wani imani ya fara shigar Mommy a hankali, tare da tsoron
Allah, kenan Allah ba ruwan shi zai iya daukan ran ka a sanda yaso, kuma a duk yanda ya so, ga dai
Hafsatu ta gama iya shegen ta kwalbar cup tai ajalin ta, wa ya zata? Nan da nan wasu sabbin hawayen
nadamar rayuwar ta ya fara ziyartar ta, ta tafka babban kuskure a rayuwar ta, me ya kaita mallake miji ta
hanyar tsafi, ita yanzu a iya jibgin malamai dibbu da bokayan ta bata san waye ma yayi nasarar mallake
mata mijin ba balle taje a karya a sirin, kuka take mijin ta da masu gadi na bata hakuri, amma inaaa, ba
ta isa daina wannan kukan ba nan kusa.

Mijin ta ne yayi ma Okashatou waya ya sanar da shi rasuwar Hafsatun, ya shiga tashin hankali sosai, da
yaji ya abin ya kasance,saboda ko ba komai matar shi ce a da,kuma ya so ta, itace macen shi ta farko da
suka shekara kusan sha shida zuwa sha bakwai tare, bai san sanda hawaye ya zubar masa ba, Nour dake
goge masa mota zai fita, ya kalle shi, Okashatou da sauri ya dauke kan shi, yana sake jin wani yanayi
game da rasuwar, mai bi ma Nour ne ya fito, dauke da qaramin qanin su, da sauran yaran gidan suna mai
a adawo lfy,dan yanzu ya matuqar jan su a jiki, kuka kawai ya saka, sai ya dinga dana sanin sakin ta,
dama yayi hakuri ta mutu a dakin ta, ba wanda yasan me gobe ko anjima zata haifar sai Allah, amma dan
adan nada mantuwa, yana shuka dikkan abinda yake so.

Ganin mahaifin su na kuka suka zo gaban shi, wasu na kukan wasu na kallon shi kawai, ba su san me ya
same shi ba, Nour ne mai wayon cikin su, amma bai iya tambayar me ya faru ba,sai da Habibu ya
tsugunna gaban Abban nasu yace,

"Abba kayi hakuri akan kome ya faru,ka shiga cikin gida,ko ka isa inda zaka,in baka da lfy ne kaje
asibiti,amma ka daina kuka gaban mu munajin kamar zamuyi kuka muma, kaga su Safwan kuka suke,"

Wani hawaye ne mai yawa mai zafi ya zubo masa, yayi saurin goge wa, ya shafa kan Habibu, sannan ya
ce Nour da sauran qannen shi masu wayo su shiga mota, zasu raka shi wani waje, Habibu ya kula da
gidan dik da yana da yayu biyu amma ya fisu hankali.
Da dauri suka shige,ya ja motar sai gidan Alhaji,yana zuwa yace su zauna ya fito, direct bangaren Hajiya
Babba ya shiga,ya samu Hanee ta fito wanka, an gamawa yaran wanka,ta na goge jikin ta,wajen ta ya
nufa gadan2, ya rungume ta yana kuka, kuka sosai, Hajiya Babba dake shirya yaran mamaki ya ishe ta, a
tinanin ta kukan Hanee ta koma ne yakeyi,

"Kaiii kaiii meye haka? Me zan gani? Kai me yasa baka da kunyar aikata dik wani abu da kaso a rayuwar
ka ne? Wato ka gama iskancin da zakai, shine yanzu zaka zo ka wani duqunqune ta dole ta bika kk? Sake
ta sai ta gama jego k zata koma"

Hanee ko ba kunya jin yanda yake kuka tasan akwai wani abu bayan nan, da hannu tai ma Hajia Babba
alama, da tai shiru, kallon ta Hajiyar tai, ta girgiza kai, na mamaki, irin ji 'yar zamani, gani tai ta dago da
kan Okashatou tana fuskantar shi,ta sharw masa hawayen shi, sannan tace,

"Abban Nour me ya faru, naga kana kuka haka? Bani labari zauna,"

"A'a Hanee ku shirya muje Kaduna, yanzunnan aka min waya Hafsatu ta rasu,"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un ta rasu ?"

A tare suka hada baki suka furta, daga masu kai yayi, kowannen su jiki yayi sanyi, Hanee uwar tausyi, nan
da nan ta fara kuka, Okastaou da kyar yake lallashin ta shima, maza tai ta fara saka kayan ta,

"Me kike yi? Ba inda zaki fa,ki bari mu mujen zamu samu zuwa da yawa daga mutan gidannan dan zan sa
kowa ya shirya, amma ke ki zauna, kina da danyen jego zaki tafiya me nisa? Sannnan ga yara har biyu, a'a
ki ta mata addu'a daga nan, ita tafi buqata ba zuwan ki ba, ki yi hakuri,"
Ta san gaskiya hajiya ta fada, dan haka ta fara kuka sosai, ta zauna, qarasa zuge zif din rigar ta tai, ta
dauki Yusaira dake kuka,

"Ina su Nour sun sani kuwa?"

"Na kasa fada masu, amma in mun je zasu gani, mu ake jira ma ba a kai ta ba,"

Sunkuyar da kan ta tayi ta na share hawayen tausayin yaran da rayuwa, duk abida kk yi a rayuwar ka
yana da lokaci.

Yana zaune a nan, yana kallon ta da yaran cikin so da qauna, da fargaba, Allah yasa kar ya rasa ta har
abada, Allah ya sa ta dawwama da shi, ko mutuwa ya fi son ta dauke shi kafin ta dauke ta, wani sabon
son ta k shigar shi musamman ganin ganin yanda take kuka, akan kishiyar da ta azabtar da ita, take son
ganin bayan ta,Hanee ta daban ce, mace ce mai son kowa da kyakkyawar zuciya.
"Sannu Okashatou, Allah ya jiqan ta,ku tashi muje, mun shirya, da wasu daga cikin yaran, su Hajiya
qarama ma, zasu samu zuwa,"

Daga kai yayi suka fice, ya juyo ya kalli Hanee, da ido ta mai alamar Allah ya kiyaye, ta kauda kai, ficewa
yayi, yabi bayan su Alhajin, a mota kuwa yaran ba abinda ba su tattauna ya faru ba, motoci hudu ne suka
dauki hanyar KD.

Zuwan su an shirya ta, mutane qalilan ne ba wasu masu yawa ba suke zaune a gidan, wasu daga cikin
'yan uwan su ne, sai maqotan Mommyn da basu fi biyu ba, sanda suka fita yaran wasu sunyi bacci,
Mommy na ganin sy taje da gudu ta rungume su tana kuka, tana jajanta rasuwar qanwar ta ta.

Nour me wayon ciki ne ya fara gane me ya faru,ganin zanin maman shi lullube a jikin matar dake kwance
qasa, da ala rasuwa tayi, wajen ya nufa ya bude, yana ganin itace ya saka kuka, saudan qannen shi mada
suka gani sukai ta kuka, •sun ba mutane tausayi sosai, ba kadan ba, wasu kuka sukai tayi, wasu jimami.
Anan aka sallace ta, suka je a ka kaita gidan da kowa ke jira, babba da yaro, mai kudi da talaka, mashayi
da mushiriki da mumini, azzalumi da mai adalci, gida ne da iya aikin ka mai kyau iya jin dadin ka a ciki, ya
Allah ka karbi rayuwar mu muna muminai salihai.

Sai da aka kai yamma Okashatou da su Alhaji sukai salla zasu tafi, Aunty Mommy ta roqi a bae yaran in
anyi bakwai a dauke su, haka suka tfi suka bar mata su, yaran sun zama abin tausayi.

A hanya Okashatou ya fara tinanin yau ba zai koma ba sai da matar shi.
*Maji ma gani in Hajiya zata yarda ka dauke ta*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH

Page 32:
Suna isa gida ya aje Alhaji da Hajiya Babba da suka biyo motar shi a dawowa, shima ya bi bayan Hajiya
Babba bangaren ta, a ranta tana ayyana wannan ba zai wuce gida bane?

Suna shiga Hanee ta fito daga daki tana masu sannu da zuwa, kiran Huwaila tayi ta kawo masu abinci,
bayan yaci, ya sha ruwa, ta sake fitowa, ta masa ta'aziyya, kawai ya fashe da kuka, hankalin ta ne ya
tashi, ta rasa me zata ce, da kyar ta samu kalaman masa magana da shi,

"Pyar kayi hakuri mana, haka Allah yaso zata rasu ta bar mu baki daya, in baka kwarara kan ka ba su
Nour ya zasuyi? Kaine jigon su"
"Ni ba kukan komai nake ba illa tinanin baki tausayi na kwata2, haba Hanee, ki duba kiga ba mace a
gidannan, kuma ba laifina bane, kun san dalilin auri sakina yanzu, amma kowa yaqi min uzuri, sai azabtar
da ni kuke, ya kuke son nayi? Neman matan banza zan tafi yi waje, ko kuma ni zan dinga zuwa aiki kuma
ina kula da yara? So kuke na fadi na mu......."

Da sauri cikin kuka ta toshe bakin shi, tana kada masa kai, idon ta kamar an kunnan famfo dan zubar
hawayen tausaya masa, a gaskiya itama tana son bin mijin ta,amma bata da ikon bin shi ba tare da izinin
manya ba.

"Pyar kayi hakuri kaji, nima ina son na kasance tare da kai, amma kasan ba zan taba furta ina son bin ka
ba ba tare da izinin Hajiyata ba, dole sai manya sun aminta zan bi ka,haka nan ba zan dau kayana nace
zan koma ba, ba fa ni na kawo kai na ba,"

Suna cikin magana suka ga Hajiya Babba ta fito daga kitchen ta nufi dakin Haneen, bata ce masu komai
ba, dan matsawa Hanee tai nesa da shi, kar a sake gifta su a gansu manne, satar Kallon Hajiya yayi,a
ranshi murna ta kama shi,dan in bai bata sanin da yayi ma hajiyan tashi ba yau matar shi a dakin shi zata
kwana, ko dan wasa yayi ya rage zafi, bai san sanda murmushi ya sake kwace masa ba.
Hanee kuwa ta tafi duniyar tinani, taji maganar shi, cikin wani sabon kukan da daga murya.

"To naji ki roqa min Hajiya ko yarannan a ban suje su taya ni kula da yaran nan, dan aikin na min yawa,
dik da wasun su suna taimakawa wasu, plssss love,"

"To shikenan, ya isa kar ka ban kunya mana, me yasa yanzu ka zama rago ne komai kuka, zan ma Hajiya
magana, ko su huwailan su fara gaba, in yaso dik sanda taga ya dace sai na koma, domin ni gaskiya ba
zan tsallake maganar ta ba,"

"Allah ya miki albarka Hanee, a gaskiya iyayen ki ba qaramin qoqari sukai ba wajen baki tarbiyya matuqa,
kin san ya kamata, dan haka ni Hajiya Babba na maki izinin komawa yanzu da mijin ki, gidan ku wajen
yaran ki, zaku tafi da Salma, da Huwaila da Asma'u, domin au taimaka maki, bana son na je ko da leqe ne
na ga kina aiki baki cika arba'in ba, in naga haka ranku sai ya vaci dikan ku, dan haka ki taso muje ai ma
Alhaji bayani, sannan a sanar da Amman ki da Abban ki, in da hali ma a kira su nan ayi maganar zai fi,"
Wani irin dadi da kwanciyar hankali ne ya ziyarce su, ajiyar zuciya mai qarfi sukai a tare, ya kalle ta, yana
wani lumshe kyawawan idon shi, ita kuwa nan da nan ta sunkuyar da kan ta, qarshe ta miqe tai daki da
sauri, fadawa gado tai, tana wani girgizar murna da yar qara, ta rufe idon ta da tafukan hannayen ta, jin
motsin qofa ne ya sa ta nutsu,

"Dole ki murna mana, qarar ki har Parlour, dalla matsa na bude na dau kayana, ke wato har ma kin hada
kayan ki, snnu dadi miji,"

Kallon inda Huwaila ta kalla tai itama, taga akwatin ta a hade, dana yaran,

"Ke ba ni na hada ba, Allah hajiyata ce, ni da yanzu na dawo dakin ma, tsaya da gaske qarata har
Parlour,"

"Sosai ma, qarya zan maki, da baki ba ai da ban jiyo ba,"


Toshe baki tai tana yarfa hannaye, wannan abun kunya har ina, hijab ta saka, ta janyo har gaban fuska,
ta fita, bata ga kowa ba, itama wajen Alhaji ta nufa.

A zazzaube ta gan su, Alhajin bai fito ba ma, Okashatou kamar ya lashe ta daga saman ta har qasa dan
kallo, yatsun qafar ta dogaye yake ta kallo, da suka sha qunshi ja, ga yatsun hannun ta ma sun sha lalle,
ja da baqi, tin na suna, yawu ya hadiya, a ran shi yana ayyana su Abba zasu dade kan su iso dama bashi
matar shi sukai ya tafi,a fada masu ta waya.

Alhaji sai da yayi wanka, yaci abinci yana shan ruwa yaji sallama ana sanar da shi su Amma sun zo, yace
ga shi nan, Hanee ta lafe jikin Amma, dik da ture ta da take, dan su Hajiya Babba manya ne a idon
Amma, da kunya suga diyar fari ta manne mata haka, ita ko qin tashi tayi, tana mata dariya, hira suke
qasa2 tana tambayar ta su Ammar, tana bata amsa.

Bayan Alhaji ya fito, ya ma su nasiha, musamman yaran shi da zasu taimaka ma Haneen, ya ma
Okashatou nasiha sosai akan riqo da ibada, sannan ya ce masa in Hanee ta ga bai sauya ba ta dawo gare
su suko suka riqe ta ba zasu bashi ita ba sai ta ga dama tai magana, a gaggauce yace,
"Hakan ma bazata faru ba inshaa Allahu, yanzu na san mahimmancin riqo da addini, akan Hafsatu na yi
hankali na samu izinah, ibada itace mutum, ita kuma Allah ya yafe mata, Hanee ki yafeni, dik abinda na
aikata, akwai halina kuma akwai sawar sihiri, ta kowacce siga na cutar dake, na maki alqawarin ba zan
sake ba,"

Kanta a qasa tana murmushi, shima ita yake kallo, daga kai tayi a hankali, suka hada ido, ya kashe mata
ido daya, da sauri ta kalli Amman ta da Abban ta da suka dauke kai kamar ba su gan su ba,Alhaji ne yace,

"To mara kunya, zaka iya bari in kunje gidan naku kabar ido dayan ma a liqe,"

Dariya su Huwaila suka saka, Okashatou ya danqara masu harara, Hanee kuwa kamar zata shige qasa.
"To godiya ta tabbata ga Allah, haka ake so, kowa ya gane kuren shi ya nemi gafara, haka dama ake so,
Allah ya jiqan ita uwar gidan, Allah ya mata rahama, mubari mu koma, dare na yi, Allah ya basu zaman
lfy,"

"Ameen"

"Ni ba abinda zance sai godiya a gare ku, kun nuna mana halacci,kuma kun nuna mana kuna bin gaskiya
ne ba son zuciya ba, kun tsaya akan gaskiya Allah ya bar qauna da zumunci,"

"Ai Amman Hanee mu zamu gode maku, domin zuwan yarinyar nan zuri'ar mu alkhairi ne, ni kaina na
shiryu ba dana ba kadai, ga yara har biyu ta haifa mana, ta zama wata kadara a zuri'ar gidana, kun yi
qoqarin bata tarbiyyar da kowa zata shiga ranshi, Allah ya qara ma dikkan yaran mu albarka,"
"Ameen"

Sallama sukai da juna, mutan gidan duk aka firfito ana ta sallama, Amaryar Alhaji ta ba Hanee wata
qunshin leda, ta mata rada zasuyi waya, Hajiya qarama ma haka, 'yammatan na ta huging din ta, suna
sallama, haushin su dik ya kama Okashatou, bata tai yayi,

"Kuna bata mana lokaci,yaran nan su kadai ne fa tin safe, in banda nai waya an kai masu abinci na san da
tini sun galabaita, yanzu ga dare yayi,"

Qus2 sukai ta yi, akan ya cika fada, kamar ba tafiya zasuyi ba, Hanee motar Sa'id zata shiga da, dan kunya
taji kowa na kallon ta ta fada motar miji, shi ko ba kunya ya ja ta ya tura tashi, Huwaila dake riqe da
yaran ta shiga baya, tana kada ido, a ranta tana ayyana ta san suna zuwa ba zai bari ma su sake ganin ta
ba sai washe gari.
Sa'id ne ya dau su Asma'u, suka yi gaba, sannan su Okashatou ke biye.

Amma da Abba ma suka dau hanyar nasu gidan, cike da farin cikin yanda suka ga diyar tasu, sannan sun
tabbata dik wani quncin gidan aure kuma ya kau masu.

Ta bangaren Mommy kuwa, da yara, ji take kamar ta maida su cikin ta, a cikin 'yan zaman makokin ne,
akai wani mutum ya zo wajen dan miqa ta'aziyya, zai wuce yaga an saka rumfa ana zaune, ana miqa
gaisuwa, ya tsaya, kallon Mijin Mommy ya ke tayi, bayan ya kammala gaisuwa ya ce masa yana son ganin
shi in ba damuwa, mijin Mommy ya miqe ya bi bayan shi, waje suka samu da ba kowa, suka tsaya, nan
mutumin yake sanar da shi, shi dn yana aiki da manyan rohanai, Allah ya shirye shi, yanzu ya bari, dan
haka dik inda mai dauke da sihiri yake yana ganewa, ya ce masa ya je ya nemi maganin karya sammu, ya
fara masa ayoyin karya sihiri yana rubucewa a wayar shi.

Matsala daya bai iya karatun qur'ani ba, ya zai yi to? Nan ya roqi mutumin ya ce ya taimaka ya zauna a
gidan shi, ya mai addu'o'in dan ya sha ya shafa din, saboda shi bai iya ba, mutumin yayi mamakin babban
mutum mai kamala ace bai iya karanta qur'ani ba, lallai akwai aiki, ya amince dan baida dama wani
sana'a da wajen zuwa.

( kar kuyi mamaki idan kuka ga qaton mutum bai san Allah ba, bai iya karanta al'qur'ani ba, akwai su
sosa, amma ta bangaren kudi, da boko ba a magana, shi yasa da damar irin su, auke aikata abubuwan
sabo da jahilci a addini, amma komai sukai ace ai 'yan boko ne, nan ko tsabar jahiltar addini sukai, nawa
ne sike da bokon mai zurfi,dake sun hada d islama sike bin dokokin Allah? Ya kamata iyaye in suna son
yaran su su kubuta daga sharrin matsafa da aikin zunubai to su dage wajen bawa yaran su ilimin bokon
tare da islamiyya, mahimmin ma shine ilimin islama, domin shine duniyar mu da lahirar mu)

*Toh mommy shawarata a je a fara share gidan tsoho, ko dake ban sani ba wata qila ya bar ki, kaiiii na
ma rasa tinanin me zan, ku ya kuke ganin lamarin zai kasance ne?*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼


BY HAERMEEBRAERH

Page 33:

Motar su Okashato na shiga, yaran suka tsaitsaya suna jiran mishi Oyoyo, Hanee sarin kuka tana hango
su idon nan ya fara ambaliyar hawaye, bata zaci zata gan su cikin hayyacin su ba tsaf, duqar da kan ta tai
a cinyoyin ta tana kukan dadi, Okashatou jin sonta na sake ratsa kowacce gaba ta jikin shi yake, haka ma
Huwaila, domin sun sani wannan ba iyakacin son ganin ido bane, dan taga uban su, ba yanda za ai dik
makircin ta kuka na gasken gaske kamar wannan ya fita a gare ta, kuka ne da ka gan shi ka san na ganin
masoyin da ka dade baka gani bane, kowa ya fita basu ga Ummen su ba, ga 'yan biyu a hannun Aunty
Huwaila, wadda zuwan Hanee ta sa suke ce mata Goggo, haushin hakan take ji wai sun.maida ta
tsohuwa.

"Ina Ummeen mu Abba?"

"Laaaa na.manta ta a gida,🤭"

Leqowa tai bayan ta share idon ta tas, ta fito,

"Tinda alewa ce ni an mance ni a gida mana, yarana kuzo wajen Ummen ku i missed u so so very much,"

Wani ihuuu yaran sukai a tare, har da yaran da bata saba da su bama, sun sha labarin abubuwan dadin
da take masu Habibu, da kuma irin yanda take nata hukuncin in anyi laifi, nan soyayyar zama da ita ta
darsu a ran su suma, dan ba haka ake nuna masu ba.
Rungume ta sukai tayi daya zuwa biyu, ana ta murna, Habibu na gefe yana ta risgar kuka, iya ganin ta
bata gan shi ba, shi da Sabir, Sabir na ciki yana.bacci.

"Wai ni ina Habibi na ne?"

"Umme ga shi can yana kuka kamar mace,"

"Awww😍 my baby, come here,"

Yana kuka kafadun nan a dage, yana babbasar da kai , ya isa gare ta, yana jin gata ga shi ya qanqame ta
sosai, kamar wadda zata koma, ya saka sabon kuka,

"Ummee dan Allah kar ki sake tafiya ki barmu, dan Allah Ummee ba dan mu ba, ke ce a madadin Iyayen
da muka rasa, Umme kece cikakken gatan mu,"
Ba wanda vai zubda kwalla ba a wajen, Hanee kam kun san ba a magana,kisses kawai take bin Habibu da
su, tana shafa kan shi, Okashatou ne ya je ya kama hannun su, suka shiga ciki, Habibu kamar shine
qaramin da, ya maqalqale ta sosai,

"Ni fa banga Sabir dina ba, ko baya murna da dawowa ta,"

"Ummee yana bacci,"

"Ok, shikenan a qyale shi, ya ci abinci ko?"

"Dik munci abinci munyi sallah,"

Alhaji ne ya je yana tada shi a kujerar da yake kwance, Hanee ma ta samu daya daga manyan kujerun
parlourn nata da tai missing ba kadan ba ta zauna, tana shaqar qamshin wajen, a hankalu ta furta,

"Home sweet home,"


"Sabir tashi ga Ummen mu ta dawo, ta shi, ka tashi dalla ga Ummen mu ta dawo,"

"Annnnn ni ka kyale ni qarya ne, ba ita bace, Abban mu yace mafarki nake, amma zata dawo,"

Miqewa tai taje gaban shi, tana shafa kan shi,

"Sabir bude idon ka,na dawo din da gaske, in da kana mafarki ne yanzu gaske ne tashi, ga Ummeen ka ta
dawo,"

Jin muryar ta yasa shi warrsakewa, idon nan tarwai, yana ganin ta ya daka tsalle ya maqale ta,

"Yehhhhh Ummen Minti ta dawo,"


Kowa dariya ya saka, saboda basu sweet da take wato shine ya kira ta da Ummen minti,

"Auuuu Sabir dama minti kawai kk tinawa ko, ya maka kyau, sauran karatu, zan zo naji ina kowa ya tsaya
ai, maza koma baccin ka nima hutawa zan je nayi,"

"Ni bana jin bacci sai gobe,"

Nan ma dariya ya basu, Sa'id ne ya ce,

"Immm ba ri nima na tafi wajen tawa tsohuwar na ga alama gidannan akwai son kai, an fi son uwa sama
da uba, sai da safen ku,"
Asma'u ce ta amsa shi da,

" ba komai koma wa aka fi so,tafi gida ka je ka kwanta a 'yar katifar ka, mun gode,"

"Asma ya ishe ki fa, wai ni ban girme ki ba?"

"Baka da hankali dalla tafi sai da safe,"

A rana daya aka haife su, Asma'u aka fara haifa sannan maman Sa'id ta haife shi da yamma, dan haka
kowa a cikin su son girman yake.

Yana tafiya, Hanee ta raba yaran, biyu, taba Asma'u kaso daya tace ta tafi da su bangaren marigayiya su
kwana, ita da Salma, sai Huwaila da sauran, kada ido tai sama, dama ta san ita daya za a bari da yara da
yawa, 🙄 kama hannun su sukai suka tafi, tare da furta sai da safe, Okashatou kuwa ya ce ma Hanee yana
zuwa, bari ya dan samo masu wani abin tabawa, ka r a kwana ba komai a gidan, ya fita.
Ai su Asma'u na isa suka ga yanayin wajen suka tattaro suka dawo, amma sai da suka nuna ma yaran
wajen kwanciya,

"Allah matar broth ba wajen kwana acan, mugun datti da wari, a bari dai gobe ido na ganin ido mu gyara
mun koma, yau kam gaskiya ba za mu iya baccu can ba, ko a qasa ne zamu kwanta anan din,"

Dariya Huwaila ta fara, Hanee ta gyara murya tana kallon ta, sannan tai shiru.

Nan suka samawa kan su wajen kwanciya, aka kafa hira kuma, yaran nata bawa Hanee labari, manyan
cikin su nata daukan 'yan biyu, kowa na yaba kyaun su.
Can Hanee ta zame jikin ta ta shiga ciki ta dau kayan ta zata kai wajen Okashatou, Huwaila ta karba ta
taya ta, can suka nufa,ita kuma ta dau na yaran, suna zuwa suka ga wajen, dik qura, shara Huwaila ta yi
tana ta masifa, wai kamar ba gidan likita ba, ba wajen arziqi in ba wajen Hanee ba shima din sai a
hankali, ko ci kan ki Hanee bata ce mata ba, dan ta san Huwaila da mita.

Kafin ta gama nan Hanee taje ta wanke bandakin tass, ta fara wanka, tana gamawa ta fito daure da
towel, tana tsane gashin ta ta inda ruwa ya taba, pant din ta ta dauka ta saka pad, ta mayar jikin ta
sannan ta zauna,tana cikn shafa mai Huwaila tace,

"Matsa ki samu ciki da wuri, daga dawowa har kin fara qalqalar jiki, shi Yaya ba ruwan shi, in kin kula
yara akai2 a gidannan, ki qoqarta ki bari yarannan suyi kwaru, kar ki je ki kunika,"

"Ina ruwan ki in tayi kunikan, kinga Huwaila akan surutun ki zamu bata, ki kiyayen in son zama dani lfy a
gidannan tam, fita,"

Fita tai tana murguda baki, tana qunquni, ai gaskiya ta fada, daga bada shawara, za a dinga wani mata
fada😏.
Abinci ne leda2, ya dauka yace ma Hanee yana zuwa, ta daga kai, tana murmushi, dan da ganin shi,
akwai magana,

Abincin ya rarrava masu, suka karba kowa na murna, dan kuwa abinci ne na more wa musamman ga
yaran an dade ba a hadu da irin cimar nan mai dadi ba.

Suna kammalawa wanda basuyi sallar isha'i ba sukai, koqa ya nemi wajen kwanciya.

Okashatou, dawowa yayi, yana bin Hanee da ta shirya cikin wata rigar bacci kalar baby pink, mai mugun
kyau, wadda ta bayyana manyan boobs din ta da hipa din ta sosai,ta daure gashin ta da hair band, ya
kwanta a bayan ta, sai qamshi takw budawa mai kwantar da rai, yana cikin takawa wajen ta cike da
kwadayin ta da son kasancewa da ita Yusairah mai rikicin ciki ta farka,tana kuka, aiko Hanee ta juya
wajen ta,

"Really? Haka zamuyi da ku? In ba maganin baccin yara zan dinga baku ba da dare,"
"Tab gwanda da Allah ya sa na ji ashe? Na rantse kar ma ka fara, baka san haka. Na jawo illoli da dama ga
yara ba, yana bata kwakwalwar yara, ya sa su zama addicted tu kayan maye tin suna yara, kar ma ka
sake fadan hakan plss, beside u ar a Dr. Ka san illar hakan ai,"

"Waiii lallai sai nayi da gaske , ji bayanin da kk ta zuqan ba ko shan nunfashi, ni fa wasa nake, na kula
gaba daya kin fi son yaran gidannan akaina,"

Ya wani ja ya nade hannu irin na yara sunyi fushi, fiddo nono tai zata ba wa Yusairah dake ta tsala kuka,
wani yawu ya hadiya mai qarfi, sai da Hanee ta kalle shi, ganin yanda suka cika sukai kyau, amma gaskiya
yaran nan zasu kwafsa masa matuqa.

Zama yayi kusa da ita, yana shafa saman, kallon juna sukai, ba su ko qiftawa, a hankalu suke matsar da
fuskokin su kusa da juna, sai da dukai daf Hanee ta kauda kai, ta kalli yusairah d tasake nonon, ta koma
bacci, kwantar da ita tayi, ta matasu addu'a, kan ta juyo taga ba ya nan, motsin ruwa ta jiyo ta san ya
shiga bandaki kenan.
Bayan ya fito ya shirya suka ci abinci, suka sake brush, sanan sukai shirin kwanciya, Okashatou yana son
sauya hali wannan karon sosai, dan haka bai taba ta ba, sai da ta taba shi, bai son taga kamar jikin ta
kawai yake so, Hanee cikin dabarun ta sai d ta sa Olashatou jin kamar ma ya sadu da ita ne, saboda
yanda ta biya mas buqata da jikin ta, gaba daya ta aje kunyar shi a gefe, ta sarrafa shi.

Bayan komai ya lafa ta umarce shi da ya yi wanka kan ya kwanta, nan kuwa ya miqe ba musu yaje yayi
wanka.

Bacci mai dadi ne ya dauke su, suka saka yaran su a tsakiya gwanin sha'awa.

Kwana bakwai akai ana ma mijin Aunty Mommy addu'ar ayatusshifa'a da na ruqya, gaba daya ya daina
jin abubuwan da yake ji a da, musamman na tsoron Mommyn, nan ya fahimci kenan ita ta masa asirin da
zai na binta kamar yanda ya dinga yi mata biyayya a baya.
Ai kuwa kiran ta yayi babban parlourn su, ya tsire ta, sai da ta mai bayani tana kuka, tana bashi hakuri,
daure fuska yayi shima kamar zai kukan,

"Haba Mommy? Me na miki mara kyau a rayuwar zaman auren mu? Kome kk so ina maki da 'yan uwan
ki., da qawayen ki dika, meye na min asirin da har ni na maki shara wanke2, da arziqina, d ilimina, ina da
halin dakko masu aikin da ko tafiya naji bana son yi zasu daga ni, meye ribar ki kenan?"

"Rudin duniya dana shaidan ne, ka yafe min, ba dan halina ba, in baka yafen ba na shiga uku, dan
mutuwar Hafsatu tasa nai nadama ban san ya zan na warware sihirin bane kawai, dan Allah ka yafen,
tsananin son ka ne da kishin ka ya sa bana son ka min kishiya, amma ba wai dan dukiya ko wani abu
bane,"

"Ba zan sake ki ba Mommy, ba zan rabaki da gidannan ba, amma mata sai nayi hudu in har naji ina
buqata, sai dai kishin ya azabtar dake,"

Kuka ta saka tana ta bashi hakuri, dan akan kishi ji take kamar ana dana mata wuta a qirjin ta..........
*Ya Allah ka rabamu da mummunan kishi, kima gode Allah ba a baki red card ba ko yellow ne oho,*

[11/12, 11:53 AM] Shareefah Nijer: 💅🏼 AURI SAKI 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH
Page 34:

Mijin Aunty Mommy ko wata daya baarufa ba, ya auri wata matar, a dangin shi, sun jima da tsanar
Mommy, saboda sanin halin ta na mugayen asiran da take ma dan uwan su, dan haka harda hadin bakin
mahaifiyar shi akan ya auri wata a dangi, a ganin ta koma me zai je yazo, za su dinga ziyartar 'yar uwar
su, sabanin da da ake haa su zuwa gidan kwata2.

Yarinya ce da bazata fi 21 ba,dan haka idon ta a bude yake da ilimin da ake zubawa a duniyar whatsapp
da su Facebook, da sauran su, Allah2 take dama tai aure ta fara gwada irin soyayyar da ake koyarwa, dan
haka wata irin soyayya ake bugawa a gidan ta maqi gani ya kau da idon shi, Mommy a hankali, tinani ya
fra mata yawa,da damuwa, na tsananin kishin mijin nata.
"Ihummmmmm ni sai ka goya ni ka kaini daki, ba zan taka ba,"

Amaryar mijin Mommy ke wannan shagwabar, sanye take da wandon da bai gama rufe mata duwais ba,
sai riga bingilalliya, da zata daga hannun ta da an gano albarkatun qirjin ta, ga shi ta saman ma ba wani
rufuwa sukai ba, amma ta bayan rigar ta dan sauka, sai gashin ta da ba za a kira mai tsaho sosai ba kuma
ba za a ce mata mara gashin ba daya sha gyara matuqa sai sheqi yake da qamshi, sai buga qafa take tana
kada qirjin ta tana maida hips din ta gefe da gefe, gaba daya ya rikice da salon shagwabar ta, ya fita
hankalin shi, da sauri cikin zafin nama ya janyo ta, ita ko idon ta kyarrr akan shi, tana lashe lips din ta,
yanda ya ja ta haka ta tafi ta fada qirjin shi, cikin salon sace dikkan lakar dake jikin shi, soyayyar su suke
zubawa kamar sun manta ba su kadai bane a gidan, kissing din ta yake kamar wani mai jin matsananciyar
yunwa ya samu abinci, daga baya haka ta maqale shi ya daga ta sama, ta banqare qirjin ta, yana wasa da
shi sai ga Mommy, ta dawo da plate da cup data ci abinci, wani irin bugawa qirjin ta yayi,duhu ya
mamaye ganin ta, tare da daukewar jin ta na wasu seconds,Amarya da ta gan ta ko gezau batai ba,dik da
qarar faduwar plate da cup dinnan mijin na su bai juya ba, sanda yayi qoqarin juyawa yaga meke faruwa
amaryar shi ta sake tura masa na shanun ta tare da kamo kan shi gamm jikin ta,tini ya manta da qarar
me ya ji.

Qara ta saki ta silale qasa, cikin kissa, irin ta gwanayen mata amaryar ta sauka tana kuka, ta nufi
Mommy, a hankali ganin shi ya fara daidaita, ya kalli inda matar tashi t tafi, a hanzarce ya isa shima, daga
ta sukai, suka kai parlour, ruwa suka yayyafa mata, sai da ta dan jima kan ta bude idon ta, fashewa tai da
kuka tana roqon shi akan ya barta ta koma daya bangaren, dik sanda take da girki ya dinga zuwa wajen
ta, shi kuwa ya ce Allah ya kashe shi ba zai wahal da kan shi ba wajen yawon bin mata, sashe zuwa sashe,
nan yayi niyyar barin ta in zata zauna ta zauna in ba zata zauna ba ta bari,
"And ni bana son ku haihu ya zama yarana an raba kan su, dik da ke naga alama ba haihuwa kk ba, tinda
muke dake ko bari baki tabayi ba, dan haka sai ki zauna tinda ita har Allah ya bata rabo, ki taimaka wajen
kulawa da ita,"

Cikin alamun jin kunya amaryar ta dan kai masa dukan wasa,

"Kaiiii baby ka iya tonon asiri, cikin da ko sati uku bai gama rufawa ba shine har sai ka fada,"

Tana magana tana wani rufe fuska wai ita kunya, wani malulun baqin ciki ne ya tokare Mommy, ta tashi
daga tsakiyar su cikin jiri tayi daki, ta sani ko ba a fada mata ba hawan jini gare ta, wanda ya mata mugun
kamu, dan in ta na jin kishi har daina gani take, sai ta suma take jin dadi, kullum addu'ar ta Allah ya yaye
mata kishin dake damun ta, yayi yawa, amma inaaa, kamar qara mata ake, ta rasa yanda zatai.

Ta fahimci amaryar mijin nata, d gayya take wasu abubuwan, dan haka ta auri zaman daki, sai ta
tabbatar bata jin motsin kowa take fitowa, in abinci zatai ko zata diba da yawa take yi ta aje, in ran girkin
ta ne kan ya dawo wajen ta sai ta yi bacci, wataran ya tada ta wataran da safe take ganin shi, yana bacci.
Mommy ta rame tayi baqi, ga dai komai kamar da na dukiya bai rage ta da shi ba, amma wannan mulkin
da take zuba masa ba shi, ga qarin kishiya data ke guma mata baqin ciki, wataran tana daga dakin ta zata
jiyo qarar dariyar ta suna 'yar guje2, toshe kunnen ta take tai ta kuka, shi ynzu jin shi yake kamar wani
yaro dan 27 ko qasa da haka ma, har wani haske yayi da qiba, mahaifiyar shi kuwa kullum sa ma amaryar
albarka take, data dawo mata da danta gare ta, dan kuwa dik qarshen sati sai ya je gidan su ya wuni,
zubur shida maman shi, ya ci abincin ta, ya gana da 'yan uwan shi, qannen shi kuwa aiken kudi ba fashi,
da kayan abinci, gidan kusan ko da yaushe baqi zuwa suke,ko da wasa ba wanda yake tambayar Mommy
balle yaje wajen ta,Mommy ji tai da wannan rayuwar gwara ya sake ta, amma kuma in ya sake ta ina
zata? A haka take hakuri, ta maida hankali wajen tuba ga Allah, da nema wa 'yar uwar ta gafarar Allah.

(Wannan itace rayuwar dan Adam, a aune take, ko kayi mai kyau k ga kyakkyawan sakamako, ko kai
mummuna kaga mummunan sakamako, ga dai shi kowa ya ga qarshen Hafsatu, kuma naji dadin yanda
kuka dau darrusa akai, domin na fahimci hakan ta commenta din ku, sannan ga shi anan ana nuna mana
cewar komai aikin zunubin ka lokaci bai qure maka ba as long as kana numfashi, zaka iya neman gafarar
mahaliccin ka,ka daina aikata zunubin, kar ka ce har sai Allah ya shirye ka, hakan na daya daga alamun
rashin rabo da tavewa, Allah ka kare mu.)

Bayan shekara hudu Nour ya kammala makarantar secondary, inda Habibu ke a ajin qarshe, ana saka ran
next year shi ma zai kammala, duk wanda ya ga Habibu badan yarinta ba sosai sai yace Okashatou ne,
kyaun su da kamannin su daya, sai bambancin nutsuwa da kamala,😆 (Okashatoun ku sai a hankali😆) 'yan
biyu su Yusairah sun zama manya, inda suke da qani daya, da satin da ya gabata Hanee ta yaye shi, mai
suna, Saifudden, yaro mai kama da Maman shi sak, Huwaila da tai aure suke garin Abuja da mijin ta 'Dan
baqi take kiran shi, Hanee tace ba komai, tinda dik gidan yafi kowa kyau.
Kasuwancin Hanee na mai, ya bunqasa, inda yanzu har man shafawa tana yi, cream da lotion, har da
sabulun wanka na gyaran jiki da saka hasken fata naturally,kitso dai ta daina, dole aka daukar mata masu
aiki, saboda kula da gidan ya mata yawa, masu girki daban masu shara da wanke2 daban, ba abinda take
yi na aiki sai girkin Okashatou da gyara bangaren shi, da mishi wanki, da guga, ko kayan sana'ar ta tana
da masu aiki, masana'anta guda mai girma ya bude mata, ba qaramin bunqasa abun nata yayi ba, sai
wanda ya gani kawai.

A yanzu Okashatou ko a hanya ka gan shi zaka ga mutum mai tsananin tsoron Allah da nutsuwa, tare da
kamala,da kwarjini, sakamakon yawan tasbihi da yake da ibada, a kullum wani ya yabe shi, ya tambaye
shi meye sauyin kalmarshi daya itace,

"Mace ta gari,"

Wani irin soyayya ake zubawa a gidan, ba ta wasa ba, iyayen yaran da suke a wajen Hanee wasu sunyi
aure, wasu ana nan ana zawarcin, haka sike zuwa ganin yaran su, wataran har ta bada su suje hutu
wajen iyayen su mata, amma still soyayyar Hanee a matsayin uwa a wajen su ba mai goguwa bace, dan a
hakan kan Oakshatou ya masu abu sau daya ta masu sau uku.

Yara qanana haka zaka dinga jin haddar qur'ani a bakunan su, Zee in tazo kamar innar su, Aunty zee
Aunty zee, iyayin nan sai abinda ya qaru musamman ta ga yanzu ta zama 'yammata, ga samari nan kala2,
dama ita tin tana qarama ta qudurta ba zatai rayuwar Hanee ba, ta takura kan ta, duk wanda yace yana
son ta zata bashi dama, bata san inda rana zata fadi ba ai( 'yar rikicin amma kenan).
Ammar ya shiga University, inda ya tattare ya koma zariya gaba daya da zama, Abba bai so tafiyar shi ba,
ya so yana kusa yana ganin yanda yake gudanar da kasuwancin shi, amma is like Ammar baya sha'awar
wannan, burin shi ya zama cikakken likita shima.

Amma in taga Hanee wataran har hawaye take zubdawa na murna da farin ciki, gab daya ta zama wata
babbar mace da qananan shekarun ta, ga jikin ta da yayi wani kyau alamar hutu, da jin dadi, a kullum
hamdala take tana sake nema mata zaman lfy da kwanciyar hankali a gidan auren ta.

A yanzu gidan Alhaji ya ragu sosai, saboda daga mazan har matan an yiyyi aure, ya aurar da yara sama da
sha biyar, dan haka an ragu, sannan wasu basu garin da aiki, wasu qasar ce ma ba sa nan dika aiki ko
karatu ya kaisu waje, Alhaji ya ji dadin kasantuwar Hanee a zuri'ae shi, saboda har matan yaran shi maza,
wato faccalolin ta, yanzu suna bashi girma, fiye da da, kowa son kyautata masa take, ganin Hanee ta
samu matsayi mai girma a wajen shi, suma sai suke qoqarin samun matsayi, a kullum sai yakan ce masu.

"Duk mai son matsayi ma daukaki a waje na ta qoqarta saka yarona a hanya managarciya, banda kamar
ta to a cikin ku, na san na gaza wajen tarbiyyar su, amma kamar yanda ku da kuke mata maza zasu ci
gaba da baku tarbiyya a gidan aure, haka kuma zaku ba su, ba bu banbancin haka a musulunci,"
Amaryar Alhaji ta wice haihuwa, amma qoqarin ta bai wuce ta samu da a gidan ba, kullum Alhaji sai ya
tsokane ta yace,

"Ahhh Ramatu ko ciki gare ki ne? (Hhhhh Hajiya Ramatu a dage ayi ciki ai wa Baffa qani😆)

Sai ta turo baki da shagwabar ta me ba yaran gidan dariya ta burge Alhajin ta,dan ta san tsokanar ta
kawai yake.

Yau bayan an dakko yara daga islamiyya sun cire kayan su, sun watsa ruwa, masu homework nayi, masu
hadda nayi, Hanee ta debo kayayyakin data dinka masu, ta rabawa kowa na shi, murna sukai tayi, suna
tsalle, sai addu'a suke mata, dadi taje ji in tana ganin farin cikin su, auta yayi bacci a cinyar ta tana karbar
haddar yaran nata, bayan ta gama, tace kowa yayi magrib, ya ci abinci, a jira isha'i, sannan a kwanta.
Yanzu mazan sun kona, bangaren Hafasatu, Habibu ne da su Sabir sunqi barin wajen Ummen su, daki
daya na bangaren Hanee shine na 'yammatan, ita ta tattare ta koma wajen Okashatou, komai nata na
can.

Zuwa tai ta ma Saifudden shimfida ta sa yai fitsari, ta kwantar da shi ta masa addu'a, ta fita.

"Kar ku tada shi, kun san ya tashi a farkon dare ba komawa, baruwana dan kar ma kunemen, ah toh,"

Dariya yaran sukai dan sun san halin shi sarai.

Bangaren su ta wuce, ta samu tai alwala tai sallar magrib itama, zama tai dan yin azkar da karatun
qur'anin ta, kamar yanda ta saba, sai da akai isha'i sannan ta miqe ta fada wanka, ta na fitowa ta gyara
jikin ta, da wasu kayan bacci kalar purple, masu santsi, rigar diguwa har qasa, amma daga sama ta matse
mata boobs sun yi kyau sun fito ta saman net din jiki, hannun rigar kamar na vest, gashin ta ta daure a
bayan ta ta kitse shi ta qasa ta nannade, ya kyaun da Hanee tai ba mai misaltuwa bane, sai dai
Okashatou ne kawai zai san irin shi😉 hijab din ta ta zurma ta nufi wajen yaran ta taga ya suke.
Wajen samarin ta fara zuwa, ta gan su fess, kowa ya yi abinda ya dace wasu na hira wasu na karatu,
wasu sun kwanta,

"To takwas da rabu ta yi, ya kamata a kwanta,kunsan da safe baku da lokacin hutu,yanzu ne zaku huta
abin ku, da safe ku nemi ilimin da zai taimake ku dunya da lahira,"

"Yes ma'am, sai da safe,"

Dariya sukai dika, dan maganar ta ke nan kullum, su kuma su amsa da yes ma'am, tin tana daukan abun
nasu shirme tana fada tace hau masu bayani, har ta gane tsokana ce kawai da Nour ya qirqiro.

Sallama ta musu ta fice, wajen su Habibu, nan ma sai da ta tabbata suna lfy sannan ta rufe kashe kayan
wuta, ta bar fanka kawai da fitilar dakin qananan, a kunne, ta rufe qofa ta fice.
Ko da ta shiga bata ga Okashatou ba, tayi mamaki, to ina ya je? Qamshin chips da gas meat taji, nan ta
gane ya dawo, ya buya,

"Come out will u? Na san ka nan nan, wai har yanzu mun tara yara gari guda ba zaka daina irin wannan
wasan ba,"

Sama taji an yi da ita yana juya su, sai da yaji dariyar ta ta qi qarewa ya dire ta gado suna maida
nunfashi, kallon ta kawai yake tana dariya, bai san wane irin so yake mata ba da tsantsanr qauna mara
algus, Hanee mace ce da bata da mahadi a rayuwar shi.

A hankali idon su ya shiga na juna, wata matsananciyar sha'awar junan su ke taso masu kamar wasu
sabbin aure, a zafafe Oksahatou ya fara sarrafa ta, zamewa tayi tana maida numfashi.
"Pyar i am so hungry, na san halin ka in ka fara sai naji sabuwar yunwa ko da nacu abinci balle ban ci ba,
bari na qoshi tukunna,"

Dariya take mata, yana shafa cikin shi,

"Anyaaaa maman 'yan biyu bata da cikin 'yan uku kuwa,"

Wani yawu ta hadiya maqwat jin kiran uku, habaa inaaa,bata da komai ita.

Bata rai tayi ta jawo babbar ledar da ya siyo gas meat ta san har da yaran sai gobe ta dumama masu,
diba tai ta fara ci, fuskar ta ba wasa.

"C'm on wasa fa nake maki, ai ke da ki sake haihuwa sai Saifudeen ya kai 5yrs,"
Dan murmushu tayi, ta kalle shi da gefeb ido, zama yayi suka ci tare, suna hira, qasan ran shi yana mata
dariya, dan tabbas yasan ciki gare ta, amma yaga alama bata san da shi ba.

Suna gamawa suka wanke bakin su, tana saka sauran naman a fridge ya je ya dakko ta cakkk tana
zamewa irin na shafwavar nan, tana rura masa wutar qaunar ta, yana aje ta a katafaren gadon su na ja
masu qofa nace.

"Hanee Allah ya qara zaman lfy, mahakurci dama mawadacine,"

*Heyyy guys this is the longest page dana taba rubutawa ina jin🤔 anyways hope u love this page da
yawa, kuma an dau darussan da dama a ciki if u do, i want to see ur comments, iya comments din ku iya
sake sabon novel mai dadin daya fi wannan, inshaa Allahu, ma'assalama, Allah ya yafe mana dani daku
akan kuskuren mu da kuma aikin da muka aikata da sanen mu*

Edited by flasher Yar dakin ta hamma.

You might also like