Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 6

Rumbun Ilimi

Katafaren Ɗakin Karatu Cikin Harshen Hausa; Na Farko a Tarihi

Me ka ke nema?

Shafin Farko

Tatsuniya: Gizo da Ɓaure Zube

Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta. Zube

A wani gari an yi wani attajirin sarki, yana da Tatsuniyoyi


wata babbar gonar ɓaure. Wata rana wannan
sarki yana zaune a fadarsa tare da fadawa ana
fadanci, sai ya ce da su, “Ina so a samo min Tatsuniya
wani mutumin da zai tsinken mini ɓaurena
kuma ba tare da ya sha ko ɗaya ba. Idan ya Gizo
gama zan aurar masa da ‘yata tare da gara mai da
yawa a matsayin ladan aikinsa”. Da fadawa Noman
suka ji haka sai suka saka sanƙira (magawata) Gyaɗa
ya yi shela (yekuwa) a gari cewa sarki yana Gizo
neman jama’ar gari a fada. da
Saniya
Da magawata ya yi shela jama'ar gari suka ji sai Gizo
dukkansu suka taru a fada, da Gizo ya hango da Ƙoƙi
wannan taron mutane sai shima ya je ya samu da
guri ya zauna. Bayan jama’a sun taru sai sarki Kantu
ya sanar da su dalilin wannan taro. Da kowa ya Gizo
ji wannan buƙata ta sarki sai aka yi shiru kowa da
ya kasa magana. Can sai Gizo ya ce da sarki shi Ɗanrago...
:
zai iya. Gizo
Ɓarawon
Daga nan sai sarki ya sallami jama’a, ya kuma
Gyaɗa
saka fadawa suka raka Gizo zuwa gonar ɓaure.
Gizo
Gizo ya je ya taras da ɓaure ya nuna likif yana
da
ƙanshi. Gizo ya hau tsinkar ɓaure kuma yana
Ɓaure
sha. Dama yana da tsinken sakatar haƙori da
Biri da
kuma madubi a jakarsa. Idan ya yi aiki sai ya
Kura
dakata ya sha ɓauren nan sannan ya fito da
Kura
madubi ya sakace haƙori ya kurkure bakinsa.
da
Idan jama’a suka zo wucewa sai Gizo ya tsiri
Kare
tofadda yau (yawu ko miyau). Haka Gizo ya yi
Auren
ta aiki, ashe bai sani ba wata kurciya tana
Barewa...
kallonsa.
Kuturu,
Da Gizo ya gama aiki sai ya je ya sanar da sarki Makaho...
cewa ya gama. Sarki ya sake haɗa Gizo da Alhaji
dogarawa su kuma ya basu buhuna su je su da
ɗebo ɓaure. Da suka je gona suna ɗura ɓaure a Hajiya
buhu shi kuma Gizo yana ta tsirtar da yau Wasu
(yawu ko miyau). Da dogarawa suka ga Gizo Mutane
yana ta tsirtar da yau sai suka tambaye shi Gizo Huɗu
me yasa ka ke ta tsirtar da yau? Sai ya amsa da Baban
cewa ai warin ɓauren nan ne baya so. Rogaji
Yarinya
Da dogarawa suka koma ga sarki sai suka gaya da
masa cewa lallai Gizo ya yi aiki mai kyau kuma Ƙawayenta
bai ci ɓauren nan ba, saboda sun ga cewa a Mutum
lokacin da suke ɗura ɓauren a buhu shi Gizo da
warin ma damunsa yake yi. Zabi
Ƙuda
Daga nan sai sarki ya ce da Gizo ya je ya gyara da
gida. Bayan ya gyara gida aka ɗaura musu aure Kwaɗo
da ‘yar sarki. Aka haɗa masa goma-ta-arziƙi a Ɓarayin
gararsa. Aka haɗa amarya da tsofaffi ‘yan Rake
ɗaukar gara suka kama hanyar tafiya gidan Maraya
Gizo. Ɓarawon
Gwal
Bayan sun kai amarya gidan Gizo sun ɗan Tsiniyama
zauna suna hutawa kafin su watse, sai kurciyar
:
nan ta zo ta hau kan danga tana waƙa tana da
cewa: Lafiyana
Yusufu
Kai Gizo, kai Gizo,
da
A can ka ci ɓaurenka,
Bala
Har ka kurkure bakinka,
Har ka manto jallonka.
Daidaitacciyar
Kurciyar nan ta yi ta maimaita wannan waƙar
Hausa
har sai da matan nan suka ji. Da suka ji sai suka
Fassara
ce kai kutsaya ku ji waƙar da kurciyar can take
Insha'i
yi. Da Gizo ya ji haka sai ya ce kai kurabu da
A'antawa
ita shirmenta take yi. Sai mata suka ce wane
irin a rabu da ita kuma, sai suka yi shiru suka ji Bukukuwa
abin da kurciya take faɗa tsaf! Da suka ji sai
suka ce da Gizo, dama ka ci ɓauren ka yi ƙarya
ka ce baka ci ba. Daga nan sai suka kwashe Aure
gararsu da amaryarsu suka koma da ita gida. Suna
Bikin
Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya. Sallah
Bikin
Hawan
Daba

Wasanni

Wasan
Dambe
Wasan
Shaɗi
Wasan
Kokawa

Karin
Magana

Karin
magana
Karin
:
Magana
I
Karin
Magana
II
Karin
Magana
III
Karin
Magana
IV
Karin
Magana
V

Wakokin
Makaɗa

Waƙoƙin
Makaɗa
Makaɗan
Fada
Makaɗan
Sarauta
Makaɗan
Jama’a
Makaɗan
Maza
Makaɗan
Mata
Makaɗan
Ban-
Dariya
Makaɗan
Sana’a

Kayan Kiɗan
Hausa
:
Kayan
Kiɗa
Ganguna
Kayan
busa
Kayan
izga
Kayan
girgizawa

Tura
wannan
shafi zuwa
ga abokai
ta:

Share 960
Post

Latsa
madannin
"Like" ka
nuna goyon
baya ko
kuma
"Share" ka
yaɗa shafin

Like Share 8.2K people like this.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi Maidarasu Balangada Tashar Yutub


© Tsangarwa ICT Limted 2017- 2020Tuntuɓa: +234 803 964
:
8244
:

You might also like