Life Partner Prt 2

You might also like

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 70

*_...‫شريك حياتي‬...

_*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻
_

_1_

*Thanks to Almighty Allah for giving me ability and power to start the other part
of the book _SHARIK~HAYATI_, many thanks to my follwers, fans and Family i luv u
all*

Kwance Ummi ta sameta ta rufo da blanket, jin motsi yasa tayi saurin
goge hawayen idanta ta tashi ta zauna, Ummi ta zauna gefenta cike da damuwa ta ce
"U haven't eat dear" dan turo baki tayi ta ce "Na koshi Ummi" shiru Ummi tayi tana
kallanta ganin yadda ta kara mungun rama akan da, ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To
me zakici?" Tayi saurin girgiza kai ta ce "Banasan abinci kuma" Ummi ta ce "Me
zakici to idan ba abinci ba, or do u need tea?" Ta girgiza kai, Ummi ta ce
"Conflask?" Ta kara girgiza kai ta ce "Awara nakeso" Ummi ta ce "To bari na bawa
Saudatu ta samo maki, tashi muje kasa" dan noke kafada tayi kamar zatai kuka ta ce
"Ummi bacci nakesan yi" Ummi ta kamo hannunta ta ce "Sai kiyi a kasan ai, zakuyi
sallama da Mummy ne, beside that ma banasan kina zama ke kadai" dan kwalinta Ummi
ta daura mata sannan ta kama hannunta suka fito a dakin. Very slowly ta dinga bin
Umminta har suka sauko a steps din, Mummy dake kallansu ta ce "Lafiya dai?" Ummi ta
ce "Wai Awara zata ci" gefen Mummy Rafi'ah ta zauna ta ce "Mummy tafiya zakiyi?"
Mummy ta kamo hannunta ta ce "Insha Allah, ina jiran driver ne, but kullum zan
dinga zuwa kallanki harki samu sauki sosai, abinda nakeso dake shine ki daina kukan
nan, idan Allah ya rubuta abu zai faru babu mahalukin daya isa canzashi, shi kuma
Yusuf ki watsar da kashin sa, ki saki jikinki ki daina damuwa dashi, banda hauka
irin naki ma mutum yaci amanarki haka amma ki zauna kina kuka akansa" share hawayen
idanta tayi tana kallan Mummy ta ce "Ni bana san shi kuma, i hate seeing him, ko
mai kamarsa banasan na gani, what is making me to cry is..." Fashewa tayi da kuka
ta kasa karasawa, Mummy ta bata side hug ta ce "Dan ya barki da ciki a kanki aka
fara? Ke dai ki kula da kanki ki haife abinda yake jikinkin ki kawai, ina guje masa
ran da zai zo yana blaming abinda kika haifa dan dansa ne, wallahi babu me rabani
dashi duk duniyar nan, saina wulakantashi kamar yadda yayi mana, sai na sa shi kuka
da kunci na har abada, kuma d'a ba nasa bane, kece uwarsa kece ubansa" ita dai
Rafi'ah sai share hawayen idanta take, bayan haka ta zame akan sofa ta kwanta akan
carpet ta rufe idanta tana addu'a, wani zafi da takaici take ji deep down her, ba
dan ba dan ba da tayi addu'a Allah yasa cikin ya bare itama ta hutawa rayuwarta.
Bayan 10 minutes Saudatu ta shigo da warmer a hannunta, Ummi dake zaune suna hira
da Mummy ta ce "Kin samu?" Saudatu ta ce "Ehh na samu" Ummi ta daga Rafi'ah ta ce
"Dear, ga Awaran an kawo maki" a hankali ta bude idanuwanta tana kallan Ummi ta ce
"I'm sleepy" Ummi ta ce "I know, try and eat ko kadan ma, tin safe bakici komai ba"
gyara zama tayi ta jingina da jikin kujera sannan ta bude warmer din, fork Saudatu
ta mike mata ta fara cin Awaran, daga Ummi har Mummy kallanta suke, kai kace tayi
sati bataci komai ba, na bakinta baya karewa take saka wani, su kam hakan yayi musu
dadi, indai zataci ai komai zaizo da sauki, kusan rabin warmer din ta cinye sannan
ta rufe ta ajiye a gefenta ta ce "Anjima zanci wannan" Ummi ta danyi murmushi tana
kallanta ta ce "Ba wanda zai ta6a" daga haka ta kwanta ta limshe ido, nan da nan
bacci me nauyi ya dauketa. Ba jimawa driver yazo daukar Mummy, a hanyarsu zuwa gida
yake fada mata Jawad ya dawo, with surprise Mummy ta ce "Har sunyi landing?" ya ce
"Wallahi Hajiya, kafin naje daukoshi wani abokinshi ya kawo shi gida" Mummy ta ce
"Inaga dai sanda ya kirani yayi rabin tafiyar".
Anty Amina ce zaune a parlorn Ummanta tana shan exotic, lokaci~lokaci
takan kalli Anty Rahama dake ta trying number Anty Khadija amma yaki shiga, Anty
Amina tayi murmushi ta ce "Maman Leemah wai menene damuwarki akan Khadija ne? Naga
randa abin ya faru munyi magana da ita tace sun bar kasar" Anty Rahama ta juyo tana
kallanta ta ce "Duk tasu?" Anty Amina ta ce "Ehh mana, ni lokacin kaina ya dau caji
ban gaya miki ba, ga zaman dole na asibiti" Anty Rahama ta ce "Amma tace tayi aure
a Kaduna da mijin ta wuce kenan?" Anty Amina tayi dariya ta ce "Kema kinsan ba zata
harshi ba ai, mijin da aka zautarwa hankali ya bar matarsa da manyan 'ya'yansa ya
aureta ta ina zata barshi, ai suna caan ko wacce kasa Allah masani, amma dai ni
banga abin tada hankali dan baki sameta a waya ba, ina dai burinmu ya cika,
shikenan sai mu barta ta sha iska" Anty Rahama ta juyo tana kallanta ta ce "Hakane
kuma, Allah ya raka taki gona" daga haka suka tafa Anty Amina ta ce "Atooh,
haushinama yarinyar da tai ciki, koba komai zasu danganta d'an da Yusuf" Anty
Rahama ta mata wani kallo ta ce "Taab ai kuwa wannan yayar uwartan ba yarda zatai
ba, lokacinfa da mukaje da Yah Muhammad gidan Yusuf wuka ta dauka tana nemansa daki
daki wai saita kashe shi, nasan dai ko zafin haushine ya sata haka baxa dai ta bari
ya kar6i abinda Rafi'ah zata haifa ba, ke nifa mamaki abin ya bani, banyi tinanin
wannan figigiyar zata daukar ciki da wuri ba, gaki nan zabgegiya dake shekara kusan
5 ba labari" nan da nan Anty Amina ta hade fuska ta ce "Dan Allah kimin cikin nan
idan zaki iya, ba dai Allah ke bayar ba, nayi maganin harna gaji babu labari, kema
naga a shekaru 22 da kikai gidan mijinki 'ya dya kawai kika haifa" Anty Rahama ta
ce "Amma dai na haifi dayar ko, to dan Allah kema kiyi zuciya ki haifo ko
nakashashshe ne" Anty Amina ta mike ta ce "Sai dai ke ki haifo, gashi mun fara gani
kin haifo mai cuta" cushion Anty Rahama ta cilla mata cikin 6acin rai ta ce "Ki
shiga hankalinki Amina, karki kara kiramin Ikleemah da mai cuta" fitowa Umma tayi a
daki taja Anty Rahama tana bata hakuri suka shiga ciki, bayan nan ta fito ta
rarrashi Anty Amina ma, wai ai sai ace basu da hadin kai, kuma abin kunya ne suyi
fada a junansu, ita dai Anty Amina baki kawai ta ta6e taci gaba da shan exotic
dinta.
Fuskarsa dauke da murmushi ya shigo parlorn, Mummy ta juyo tana kallansa ta
ce "Mutanen Cyprus" ya dan shafa tulin gashin dake kansa ya ce "Ina yini Mummy" ta
ce "Lafiya kalau, have a seat, ashe harka dawo?" ya ce "Ehh kusan awana 1 ma, fatan
na sameku lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah" mikewa yayi yana kallanta ya ce "Zan answer
call ne" ta ce "Alright no problem" daga haka ya fita a parlorn, part din Maminsa
ya shige hade da sallama, Abi na zaune a gefen Mami sai Ikram dake kan carpet a
zaune, Jawad ya danyi kasa da kansa ya ce "Ashe ka dawo, na dauka zaka kirani na
dauko ka" Abi ya ce "U don't have to worry son, kai da ka dawo a tafiya, Sadeeq ya
daukoni" kan kujera Jawad ya zauna yana kallan TV, Abi ya kalli Mami data dan hade
fuska ya ce "To meyasa bakije yau ba?" Ta juyo tana kallansa ta ce "Naga dai an
sallameta har sun koma gida, gidanma kullum zan dinga zuwa kenan?" Abi ya sauke
ajiyar zuciya ya ce "U have to go, asibiti da ban gida da ban, don't make me repeat
my self kije kawai ki duba ta" tashi yayi ya fita a parlorn Mami ta bishi da wani
irin kallo. Jawad dake kallanta ya ce "What's going on Mami?" Dan karamin tsaki
taja ta ce "Ina kana da labarin auran Rafi'ah wanda akayi bayan kwana biyu da
tafiyarka" ba karamin bugawa zuciyarsa tayi ba, ya daga mata kai yana kallanta,
Mami ta ta6e baki sannan ta ce "She's divorced" with shock ya juyo yana kallanta ya
ce "Divorced" ta ce "Saki ba, ya saketa saki daya" innalillahi Jawad ya dinga
furtawa yana kallan mahaifiyarsa, Mami ta ta6e baki ta ce "Wallahi sakin wulakanci,
daya bata takardar ya bar gidan shida matarsa, har yau ba'a san inda yake ba, ya
tafi ya barta da karamin ciki, inka ganta kamar ka hureta ta fadi, ni cewa nayi ma
da zubar da cikin sukai, yarinyar dako 18 bata cuka ba, sanda naje sunanta Ikram
dina tafi shekara 1" kasa daina kallan Mami yayi, lokaci daya yaji komai nasa ya
tsaya musamman data ambaci ciki, Mami ta gyara zamanta ta ce "Ni gani nake saboda
cutarta ya gujeta, yanzu a zamanin nan yaushe zaka auri mata mai ciwan zuciya, duk
wata fa sai sun kar6i magani ga uban tsada, shi kuwa inaga yayi na Allah yace ya
gaji, ba dan ubanta nada dukiya ba inaga gidan da zasu zauna ma sai ya gagaresu"
Tashi Jawad yayi ya shige daki, yana rufo kofar idanuwansa suka cika da hawaye, bai
bari sun zuba ba saima murmushi da yayi ya dauki key din motarsa dake kan mirror
din dakin, jin an bude dakin yayi saurin juyawa, Mami ta ce "Ya muna magana zaka
tashi ka barni ba excuse" ya ce "Na tina akwai inda zanje ne" ta ce "Ina?" Ya dan
shafa kansa yana kallanta ya ce "Wajen aiki, akwai papers din da zan kai musu wanda
na taho dasu" Mami ta ta6e baki ta zauna bakin gado ta ce "Haka dai kullum aiki
aiki, idan dai kayi aure barin wannan kotun zakayi ka nemi wata" a hankali ya ce
"Ohk, saina dawo" daga haka ya fita a dakin.
Driving kawai yake amma gaba daya tinaninsa ya tafi wajen Rafi'ah, minti 10 ya
kaishi kofar gidan, yayi parking a waje sannan ya fito walking gently ya tura gate
din, ganinsa yasa Mustapha ya kara bude kofar yana masa sannu da zuwa, daga masa
hannu yayi ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din yaji kofar a bude, ya
shiga parlorn da sallama, Saudatu dake jera dinner akan dinning ta ce "Ina wuni" ya
ce "Lafiya kalau, Ummi na nan?" Ta ce "Ehh bari in mata magana" upstairs ta nufa ta
kwankwasa dakin Ummi, bayan an bata izini ta bude dakin ta shiga da sallama,
Rafi'ah na kwance akan gado Ummi na rarrashinta, dan wani saban kuka ta kafa musu
tinda ta tashi a bacci, Ummi ta kalli Saudatu dake tsaye gefe ta ce "Kin gama
abincin ne?" Ta ce "Ehh na gama, kinyi bako ne a kasa" Ummi ta ce "Bako kuma at
this time? Babbane?" Saudatu ta girgiza kai ta ce "Ehh babbane, dogo dan fari haka,
yana da gashi me yawa a kansa" sosai zuciyar Rafi'ah ya buga, dan tinaninta ko
Yusuf ne, ta ruko hannun Ummi kamar zatai kuka ta ce "Dan Allah karkije Ummi" Ummi
ta ce "Why Rafi'ah, bari na gani ko waye" daga haka ta zame hannunta ta nufi kofa
ta fita, saukowa akan gadon Rafi'ah tayi tana kallan Saudatu ta ce "Fari ne?"
Saudatu dake tsaye tana kallanta ta ce "A'a amma dai ba za'a ce masa baki ba"
ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta kwanta, dan tasan Yusuf yana daya daga cikin
mutanen da za'a kira su asalin farare, a hankali Saudatu ta ce "Allah ya baki
lafiya" daga haka ta fice a dakin. Tana saukowa ta sami Jawad da Ummi suna gaisawa
yana mata jajen abinda ya faru, Ummi ta danyi murmushi ta ce "Toya zamuyi, haka
Allah ya tsara mana, da munsan haka zai faru ko auran baza ai ba, to amma Allah shi
yake tsara komai a duk lokacin daya so" Jawad da kansa ke kasa ya ce "Hakane" Ummi
ta ce "Bari na turo ta ku gaisa" daga haka ta mike ta wuce upstairs, kwance ta
sameta tayi shiru ta kurawa window ido, Ummi ta kamo hannunta ta ce "Daughter"
kifta idanta ta danyi sannan ta kalli Ummi ta ce "Who was d visitor Mum?" Ummi ta
ce "Ahmad ne, kije ku gaisa" tsayawa tayi tana kallanta bata dai ce komai ba, Ummi
ta ce "I mean Jawad" a hankali ta ce "Ohh" daga haka ta mike, hijab Ummi ta dauko
mata tasa sannan ta ce "U wash ur face, duk idanki ya kumbura" a hankali ta shiga
toilet ta wanke fuskarta ta goge idanta with clean towel sannan ta fito, daga haka
ta fita a dakin ta wuce downstairs, tin tana sakkowa yake kallanta ko kiftawa babu,
ita dai kanta na kasa ta karaso parlorn da sallama, zama tayi akan carpet ta ce
"Ina yini" ya ce "Fine, how are u then?" Silently ta ce "Same" Jawad yayi shiru
yana kallanta, dago kanta tayi suka hada ido tayi saurin dauke kanta, a hankali
taji muryarshi ya ce "Ya karfin jiki?" Ta goge hawayen idanta ta ce "Alhamdulilah"
tinda ta rife bakinta hawaye suka dinga sakko mata tana sharewa da hijab dinta,
Jawad ya danyi kasa da murya ya ce "Destiny, kowa da yadda Allah ya tsara masa
rayuwarsa, so u don't have to cry, one day one time u will laugh" fashewa tayi da
kuka ta ce "I will never laugh again Ya Jawad, to laugh for what? Kasan zafin da
nake ji deep down me, ni kadai nasan abinda nake ji, so nobody should tell me i
will laugh one day" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta, kallanta ya dinga yi
daga inda yake zaune, jiin ta sausauta kukan da take ya ce "May be shi din ba
alkhairi bane a tattare dake, Allah ya raba ku ne saboda ki samu wanda ya fishi
alkhairi, just erase all ur bond together with him, ki manta dashi a rayuwanki, so
don't cry for him pls" ta share idanta ba tare data kalleshi ba ta ce "I have to
cry Yayah, he divorced me without any reason, ya azabtar dani a gidanshi ban gayawa
kowa ba, after all ya tafi ya barni da cikinshi..." sarkewa muryarta tayi, hakan
yasa tayi shiru tana kuka kasa kasa, Jawad ya ce "No, u don't have to, ai shi d'a
na kowa ne, i can take care of the unborn child and still after his birth, so u
forget about that man i beg u" a hankali kawai ta daga masa kai, ya ce "Promise u
won't cry again" ta ce "Yes" ya ce "Yes what?" Ta ce "I can't make a promise to u,
nasan sai nayi, saboda yin kukan kadai zai yi preventing dina from heart attack,
inajin dadi idan nayi" Jawad ya limshe idanuwansa ya ce "To kiyi kadan" dagowa tayi
tana kallansa, yana bude idanuwansa tayi saurin sunkuyar da kanta, ya ce "I think i
have to go, kiyiwa Ummi sallama, Allah ya kara maki lafiya" silently ta ce "Ameen,
nagode" daga haka ya mike ya fita a parlorn ta bishi da kallo, yana fita compound
aka bude gate, motar Sadeeq ta shigo compound din, sosai Mami ta hade rai tana
dalla masa harara, yayi karfin halin ya karasa parking lot din yana kallanta ya ce
"Dama na gama abinda nake ne shine..." Wucewa tayi ta barshi nan wajen a tsaye, ya
juyo yana kallan Sadeeq da fitowanshi a motar kenan ya ce "Till u come back" daga
haka ya nufi hanyar gate Sadeeq ya bishi da kallo.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_2_

Shiru Rafi'ah tayi ganin Mami ta shigo parlorn, ta mike a hankali tana goge hawayen
idanta ta ce "Sannu da zuwa" Mami ta zauna kan kujera kamar bazata amsa ba, sai
kuma ta ce "Sannu, ya karfin jiki?" silently ta ce "Naji sauki" Mami ta dago kai
tana kallanta ta ce "A hakan?" Rafi'ah ta daga mata kai, sai kuma ta ta6e baki ta
ce "Aike da jin sauki sai kin haife wannan jarabar ta cikinki, bayan haka kin samu
me auranki, shine zaki ce kin fara samun sauki, dan mace ta zamu zama agidan miji
ma wani falala ne, kinga idan kika kara fitowa ai ciwo ya koma baya" kara goge
hawayen idanta tayi ta dan turo baki ta ce "Niba aure kuma zan sake yi ba" daga
haka ta nufi upstairs, Mami ta mike ta ce "To kya gaisheta daman jikinki nazo
dubawa" daga haka ta mike ta fice a parlorn Rafi'ah ta bita da harara. Very gentle
ta dinga taka steps din harta gama hawa, ta shige dakinta ta rufo kofa, har zata
kwanta aka bude kofar dakin, Abdul ya karaso yana kallanta ya ce "Sannu" ta ce
"Thank u" ya ce "We just came back with Abba, na siyo maki grapes da Apple and
shawarma" dan murmushi kawai tayi dan ita yanzu ta tsani komai idan ba dan~wake ba,
kwanciya tayi tana kallansa ta ce "So much thanks bro, nagode" gyara mata blanket
din jikinta yayi ya ce "Allah ya baki lafiya" ta ce "Ameen" ganin ta limshe ido
yasa ya mike ya fita a dakin ya jawo mata kofa a hankali. Ammi ce zaune a parlornta
Sameer na gefenta a zaune, gaba daya jikinsa yayi sanyi jin abinda dan~uwansa ya
aikata, shida yake murna zai dawo gida yaga 'yan uwansa cikin farin ciki amma kuma
yaji abunda ko a mafarki bazai yarda ba, Ammi ta dan goge hawayen idanta ta ce
"Yarinyar nan ta sha wahala Muhammad, idan ka ganta gaba daya ta rame" Sameer ya
sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce "Allah ya kyauta, kenan bai gayawa kowa
inda zaije ba" Ammi ta ce "Ba wanda ya sani, wadanda ya kamata su sani su suka
daukeshi suka tafi dashi, nasan Yusuf dina bazai iya butulci da wulakanta mace haka
ba, wallahi Sameer akwai abinda yake faruwa" kamo hannunta Sameer yayi ya ce "Stop
crying pls mother, in sha Allah wata rana zai dawo, na miki alkawarin zan kula da
yarinyar da kuma abinda zata haifa" Ammi ta kara share hawayen idanta ta ce "Allah
ya baka iko, zamuyi ta addu'a Allah ya bayyana shi" a hankali ya ce "Ameen, yanzu
dare yayi kuma na dawo da ciwan kai, gobe insha Allah zanje na dubata" Ammi ta ce
"Allah ya kaimu goben" ya ce "Ameen, amma dan Allah ki daina kuka".
Karfe 12 na dare Jawad ya dawo gida, bayan yayi parking sai daya tabbatar
gate man ya rufe gate sannan ya nufi entrance din gidan, yana murda handle din
kofar yaji a kulle, ya ciro wayarsa a pocket dinsa yayi dialing phone din Sadeeq,
bugu biyu ya dauka hade da sallama, Jawad ya ce "Open the door for me, na parlorn
Abi" da to kawai ya amsa sannan yayi hanging call din, few minutes Sadeeq ya bude
masa kofar, ya shigo sannan Sadeeq ya rufe kofar ya koma dakinsa, har zai shige
dakinsa Abi ya bude kofar part din Mami ya ce "Who's that?" Jawad ya juyo a hankali
ya ce "It's me" Abi ya ce "Ya sai yanzu zaka dawomin gida Ahmad, is exactly past 12
now" kafin yayi magana Mami ta fito tana masa wani kallo ta ce "Gashi nan saiya
gaya maka gidan ubanwa yaje daya kai dare haka bai dawo ba, tin bayan isha dana je
gidansu yarinyar nan na samu shi yana fita, daga nan ko gidan uwarsa wa ya tafi ban
sani ba" Abi dake kallansa ya ce "Where have u been Ahmad? Kaje gidan su Fatima ne"
a hankali ya ce "Ehh, but i left there since 8, naje wajen Aliyu ne baya nan, shine
naje asibiti wajen Umar anyi admitting dinsa ne, anan na zauna sai yanzu" Abi ya
sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ya koma ciki, Mami dake
tsaye tana kallansa ta ce "Kai ko tsoro bakyaji a tattaraka ubanka yana dan siyasa"
a hankali ya ce "Ba abinda zai faru by God grace Mami" ta wurga masa harara ta ce
"Aini gara kayi auranka ka barmin gida, idan yaso ka kai karfe 1 baka koma ba,
wacce ka aura ne dai sai dai tayi hakuri" dan murmushi yayi yana kallanta ya ce
"Sai da safe" daga haka ya shiga dakinsa ta bishi da harara.
Washegari ya kama Monday, da safe Ummi ta gama hada komai da taimakon
Saudatu, bayan ta shirya ta shiga dakin Rafi'ah ta sameta a kwance tana bacci, rufo
kofar tayi ta koma dakinta, Abba dake zaune yana rubutu ya ce "Haka zaki fita ki
barta at this condition kenan?" Dagowa tayi tana kallansa ta ce "I'm not staying
long, 2 hours lectures kawai zan musu, sai meeting daza muyi, amma idan kace na
zauna ba damuwa" Abba ya ajiye pen din hannunsa ya ce "No, idan kinga dai ba
matsala kije kawai, amma kinsan tana bukatar me kula da ita ko?" Ummi ta ce "I
knew, amma ga Saudatu ai, komai takeso zata bata" Abba ya ce "Ohk, Allah ya kiyaye"
ta ce "Ameen, 2 days per week kawai nake da lectures din" ya ce "Alright, a dawo
lafiya" Ummi ta nufi kofar fita ta ce "Allah yasa" daga haka ta fita a dakin, bayan
ta sauko kasa ta zauna akan kujera tayi kiran Saudatu, cike da ladabi yarinyar ta
karaso ta zauna a kan carpet ta ce "Gani Ummi" Ummi ta ce "Zan je aiki ne, idan
Rafi'ah ta tashi ki bata tea first, after then akwai dan wake cikin warmer idan
zata ci, kuma karta taita kwanciyar nan dan Allah, idan kin gama abinda kike zaki
iya zama da ita" Saudatu tayi kasa da kanta tana murmushi ta ce "To Ummi insha
Allah, a dawo lafiya" Ummi ta ce "Allah yasa" daga haka ta mike ta fita a parlorn.
Karfe 10 Rafi'ah ta tashi, ta dinga bin dakin da kallo kafin ta mike a
hankali ta zauna, yau kam Alhamdulilah jikinta ba zafi sosai, kuma batajin ciwo a
ko ina, mikewa tayi ta dauki towel ta shiga toilet, kusan 15 minutes tayi taking a
ciki kafin ta fito da towel daure a kirjinta ta zauna gaban mirror, Yusuf kawai ta
tuna a lokacin, dan mostly idan ta fito a wanka shi yake tsayawa a bayanta ya taje
mata kai ya taya ta shiryawa, jin kirjinta na bugawa yasa ta limshe idanta tana
addu'a, bayan minti 2 ta bude idanta sannan ta shafe jikinta ta mike ta bar wajen,
doguwar riga na atampa ta saka sannan ta daura dankwalinta ta shafa white powder
sai lip gloss, sosai tayi mungun kyau duk da ramar da tayi, ta jawo phone dinta
dake kan gado ta kira Mummy, sosai sukai waya, kuma jin muryarta yasa hankalin
Mummy ya kara kwanciya, bayan sunyi sallama ta ajiye phone din sannan ta fara gyara
gadon. Tana cikin gyaran Saudatu ta bude kofar, ta danyi murmushi ganinta ta ce
"Anty Rafi'ah bari na gyara miki" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "A'a Saudat bari
nayi kawai" Saudatu ta danyi shiru tana kallanta, sai kuma ta ce "Bari na kawo miki
tea" ta ce "No, zan sakko kasa yanzu, Abbana ya fita ne?" Saudatu ta girgiza kai ta
ce "Gaskiya banga fitan shi ba, amma Ummi ta fita" ta ce "Ehh jiya tacemin zata
koma aiki yau" fita Saudatu tayi a dakin tana murmushi, ita kanta dadi taji ganin
Rafi'ah a haka, ta wuce kitchen ta fara hada mata dan~waken kamar yadda taga Ummi
nayi, Bayan Rafi'ah ta gama gyara dakin ta shiga dakin Abbanta da sallama, ya dago
yana kallanta ya ce "Mother" ta danyi murmushi ta zauna gefenshi ta ce "Abbana"
murmushi yayi shima yana kallanta ya ce "Alhamdulilah, jiki ya fara sauki" ta ce
"Good morning" ya ce "Morning, how are u dear" a hankali ta ce "Banajin komai yanzu
Abba, thanks for the care" hannunta ya kama suna shaking, tayi saurin sunkuyar da
kanta tana murmushi, Abba ya ce "Allah ya kara miki lafiya" a hankali ta ce "Ameen"
sannan ta mike tana kallan warmers din dake gefensa ta ce "Abba u haven't eat" ya
ce "Yanzu zan gama naci Mamana" daga haka ta danyi murmushi ta fita a dakin ya bita
da kallo cike da tausayi. Tana sauka downstairs ta samu Saudatu ta hada mata komai,
ta zauna akan carpet ta ce "Sannu da kokari" Saudatu ta ce "Haba dai Anty Rafi'ah,
ai indai ke zanyiwa abu zan iya yini inayi ba tare dana gaji ba" Rafi'ah na
murmushi ta ce "To banaso kina kirana da Anty, just Rafi'ah pls" Saudatu ta ce
"Wallahi bazan iya ba" ta ce "Zaki iya, kin ta6a ganin inda ka cewa wadda ka girma
Anty?" Ta ce "Ehh mana, nidai koma menene bazan fasa fada ba, ya karfin jiki?" Ta
ce "Yau kam Alhamdulilah, kawai inajin weakness ne" Saudatu ta danyi murmushi ta ce
"Dama haka zakiji saboda cikin dake jikinki" Rafi'ah ta dan kalleta ta ce "How do
you know that? taya kika san hakan" ta ce "Nima nayi kuma naji" Rafi'ah ta dan zaro
ido tana kallanta ta ce "Kin ta6a aure?" Ta ce "Ehh, tin ina shekara 13 aka min
aure a garinmu, inaga shekarana 14 da watanni na samu ciki, ina da tsohon ciki
Allah yayi wa mijina rasuwa, a ranar daya rasu ranar nima na haihu amma dan yazo ba
rai, ni kuma tawa kaddarar kenan" Rafi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallanta
ta ce "Subhanallah, Allah ya jikansu" Saudatu ta ce "Ameen, amma tin daga lokacin
ban sake aure ba, naci gaba da karatuna na islamiyya har nayi sauka, shine wata
kawar mahaifiyata ta samar min aiki anan, nidai shekaruna 19 a duniya, amma wallahi
ban ta6a haduwa da mutanen kirki irinku ba, Umminku, Abbanku, kema da Abdul ba
wanda ya ta6a min abinda zanji ba dadi, Allah ya saka da alkhairi ya biya ku da
gidan Allah" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "Ameen".
Suna zaune suna dan hira aka danna bell, Saudatu ta gyara hijabinta zata bude kofa
Rafi'ah ta ce "Wait Saudat, ki fara tambayar waye" Saudatu ta ce "Waye?" Sameer ya
ce "Nine" jin muryar namiji yasa ta mike ta dauka hijab dinta akan kujera ta saka
sannan Saudatu ta bude kofar, Sameer dake tsaye yayi folding hannayensa ya shigo
parlorn yana kallan Rafi'ah ya zauna, itama zama tayi kasa ta ce "Sannu da zuwa" ya
ce "Yauwa sannu" Saudatu ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya kalau, ya mai jiki?" Ta ce
"Alhamdulilah" daga haka ta wuce kitchen ta kawo masa drinks da cup sai table
water, Rafi'ah dai na kallanta harta ajiye ta bar wajen, a hankali ta dan kalleshi
ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya kalau, ya karfin jiki?" Ta ce "Da sauki sosai" ya
ce "Allah ya kara sauki" shiru duk sukayi na kusan minti 5, Sameer yayi breaking
silent din ta hanyar cewa "Allah ya baki lafiya, jiya da daddare nayi landing,
Mother told me all what happened, Allah yasa haka shine mafi alkhairi" a hankali ta
ce "Ameen, nagode" ya ce "God knows best Fatima, shi yasan dalilin daya sa hakan ta
faru, but i think hakan ya faru ne saboda shi din ba alkhairi bane a tattare dake,
may be u will find someone better than Yusuf, so forget all what happened, i'm
there for u, insha Allah i will take care of the Baby before and after his birth"
Sameer ya karashe maganar yana kallanta, kin dagowa tayi ta kalleshi jin abinda
yace is very similar to Jawda's speech, Sameer ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah
ya raba lafiya" a hankali ta ce "Ameen, nagode" mikewa yayi yana kallanta ya ce
"I'm going" ba tare data kalleshi ba ta ce "Ko in kawo maka tea?" Ya ce "No, i'm
going with this" daga haka ya dauki Fanta daya ya rike a hannu ya ce "Ammi tace
sunyi waya da Ummi wai bata nan ko" ta ce "Yes she's out" ya ce "Ohk, i will come
back ltr" ta ce "Till u come, Allah ya kiyaye" daga haka ta tura kofar bayan ya
fita, hijabin jikinta ta cire ta dauko dan~wakenta akan dinning taci gaba da ci
tana kallan TV.

_08103810398_

*I appreciate all ur calls and messages, nagode sosai da sosai i'm more than
healthy now 🤗*
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_3_

Da yamma Rafi'ah na zaune a parlor tayi pillow da cinyar Ummi aka danna bell, Ummi
ta dan kalleta ta ce "Open the door Rafi'ah" mikewa tayi a hankali tasa Himar dinta
sannan ta bude kofar, murmushi ta danyi ganin Ammi a tsaye, Khairiyya ta rungumeta
calmly ta ce "I missed u Anty" a hankali Rafi'ah ta ce "I missed u namesake" daga
haka ta matsa gefe Ammi ta shigo. With smile Ummi ta cire glasses din idanta ta ce
"Sannu da zuwa Hajiya" Ammi ta zauna akan sofa tana kallan Rafi'ah dake tsaye ta ce
"Sannu, jiki ya fara sauki ko" Ummi ta ce "Sosai wallahi sai godiyar Allah" sake
hannun Rafi'ah Khairiyya tayi ta ce "Ina yini Ummi" ta ce "Lafiya kalau Khairi, how
are u?" Khairiyya ta ce "Fine Ummi", zama duk sukayi a kan carpet, Ammi ta kalli
Ummi ta ce "Amma ta rage aman ko?" Ummi ta ce "Ehh, yau dai tinda ta tashi ba tai
ba jikinma da sauki sosai" Ammi ta ce "Allah ya kara mata lafiya, ya kuma bata
hakurin jurewa" Ummi ta ce "Ameen". Cikin few Minutes Saudatu ta jerawa Ammi abinci
da abinsha, duk cikinsu ba wanda ya ci, Khairiyya ce kawai ta sha Mango juice,
bayan sun dan jima Ammi ta kara musu sannu suka wuce, sosai itama taji dadin ganin
jikin Rafi'ah.
A haka rayuwar Rafi'ah ta dinga tafiya wata rana ta tashi garau wata
rana taita amai harda zazza6i, duk bayan kwana biyu Jawad ya kanzo ya dubata, ba
laifi yanzu tayi sabo dashi ba kadan ba, tin tana kin gaya masa abinda takesan ci
harta fara fada masa, wata rana ma a waya zata kirashi, idan kuwa ta kira ko me
yake sai ya bari ya kawo mata abinda ta bukata, kullum kara kwantar mata da hankali
yake yana nuna mata misalai kala kala wanda suka faru kuma a yanzu komai ya zama
tarihi. A yanzu a gidansa yake kwana, abinci kawai yake zuwa yaci idan yaga dama
shima, dan mostly idan yaje gaishesu baya wani cin abinci, Mami kuwa komawarsa
gidansa ba karamin dadi ya mata ba, hankalinta kwance ya fiye mata yazo ya gaisheta
ya tafi, kayan Babies yake saya sosai yana tarasu cikin wani akwati, sai da yaga ya
cika sannan ya daina sayan kayan, gaba daya unisex ya saya saboda baisan me zata
haifa ba. Bangaren Sameer ma baiyi kasa a gwiwa ba, yakan zo ya duba Rafi'ah time
to time, shima duk abinda yasan tana so saiya kawo mata, ita dai kawai kulashi take
amma harga Allah batasan zuwan sa gidan, bata so ta sake sakin jiki da dangin
Yusuf, yawanci Jawad yana haduwa da Sameer a gidan, idan ya tambayi Rafi'ah sai
tace wani dan uwan Yusuf ne, ba wani shiri suke da Sameer ba, ko gaisuwa randa bata
kansu basa yi. Rafi'ah kuwa tin sanda cikinta ya girma take zama da hijab, idan ta
cire hijabi to tana tare da Ummi ne ko Mummy ko kuma Saudat, amma ko Abba ne yazo
yini zatai tana yawo da hijab a jikinta, musamman da cikin ya shiga wata 8, kullum
fadansu da Ummi ta tashi tayi aiki, dan tinda ta daina laulayi Ummi ta raba musu
aikin gida ita da Saudat, wani lokacin harda kuka take karasawa sabida gajiya, ga
ciwan baya da yake daminta sosai, amma hakan baisa Ummi ta daga mata kafa ba, gaba
daya ta kara ramewa tayi fari akan da.

kwanciya tayi akan gado tana sauke ajiyar zuciya, toilet dinta ta
gama wankewa shine ta mike ta dan huta, tana jin an bude kofar dakinta ta juya tana
kallan me shigowa, Ummi ce ta shigo da shirinta na zuwa aiki, ta zauna gefen
Rafi'ah dake kwance ta ce "Kin sharemin parlorn?" Girgiza kai tayi kamar zatai kuka
ta ce "Banyi ba, wallahi na gaji Ummi" Ummi ta mike tana kallanta ya ce "U don't
have to, ki tashi kije ki gyara parlorn nan, sannan kuyi abinci idan kinga dama
kuma ki gudu ki barta tayi ita kadai, idan kin huta kuma ki wanke inner~wears dinki
da kika jera min su a toilet dan bazan wanke ba" hawayen idanta ta share bata ce
komai ba, Ummi ta nufi kofar fita ta ce "Sai na dawo" tana fita Rafi'ah ta jawo
phone dinta ta kira Mummy, bayan ta daga tayi sallama, da kyar ta amsa tana danne
kukan dake cinta, Mummy da hankalinta ya fara tashi ta ce "Lafiya Fatima? Meya faru
ne?" Cikin muryar kuka ta ce "Kinga Ummi bata daina sani aiki ba, kuma bayana ciwo
yake bazan iya ba wallahi" daga haka ta fashe da kuka, Mummy ta sauke ajiyar zuciya
ta ce "To kiyi shiru ki daina kuka, kiyi abinda zaki iya sauran ki bar mata shi,
zanzo yau da yamma, ban san meyasa Zainab ke haka ba wallahi, aiki ai kina yi amma
wallahi baza kiyi abinda yafi karfin kuba, dama caan ba lafiya ba balle kuma ga
larura, zanzo da yamma idan ta dawo" to kawai tace tayi hanging call din, da kyar
ta mike ta zauna, ta kurawa kananun kafafuwanta ido ganin yadda suka kumbura, ta
zira su kasa gently ta sauko akan gadon sannan ta dauki hijab dinta ta saka, koda
ta sakko kasa kwanciya tayi akan kujera, sai sauke numfashi take daki daki, tana
nan zaune Saudatu ta fito a kitchen tana murmushi ta ce "Anty Rafi'ah lafiya dai?"
Ta ce "Ehh, hutawa nake" daga haka ta turo baki ta gyara kwanciya akan kujera ta
limshe ido, bacci ne me shegen nauyi ya dauke ta, sai karfe 12 ta tashi, tana
kallon agogo tayi sauri ta dauko tsintsiya sannan ta dawo ta fara share parlorn,
tana gamawa kuwa batai mopping ba Ummi ta shigo tayi parking, Rafi'ah ta kalli
Saudatu dake dariya kasa kasa ta ce "Dan Allah kice mata banda lafiya har amai
nayi, zanje na kwanta" daga haka ta wuce sama da sauri.
```1 month ltr```

Tsaye suke duk tasu a kofar room din da Rafi'ah ke ciki, kana ganinsu kasan suna
cikin babban tashin hankali, musamman Ummi data kasa controlling tears dinta,
tausayin Rafi'ah kawai take idan ta tuno azabar haihuwa, Mummy dai na jingine da
pillers din wajen ta limshe idanuwanta, banda salatin Rafi'ah da kiran Ummi da take
ba abinda su ke jiyowa, Abba dai na tsaye yana ta addu'a sai kaiwa yake yana kawowa
a area din wajen, bayan few minutes Dr Hisham ya fito a room din, Ummi ta mike da
sauri tana kallansa ta ce "How is she Dr?" Ya ce "Alhamdulilah kenan, amma gaskiya
ba zata iya haihuwa da kanta ba, zamuyi mata CS but sai mijinta yayi signing" Ummi
ta share hawayen idanta ta zauna, Abba ya ce "Let me sign Dr" Dr Hisham ya girgiza
kai yana kallan Abba ya ce "U can't sign both yallaboi, mijinta zai fara signing
sai kuma kai" a fusace Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "Wane irin miji kake
magana bayan ga mahaifinta nan, shekara nawa ana kawota asibitin nan kunfi kowa
sanin danginta, mijin da shekara daya ba'a san inda yake ba, idan baza kuyi abinda
ya dace ba mu kaita wani asibiti mana" sauke idansa Dr Hisham yayi ya ce "Kiyi
hakuri Madam, rules din aiki ne ba wai nina fada ba" daga haka ya kalli Abba ya ce
"Muje sai kayi signing din" daga haka Abba yabi bayansa zuwa office, cikin 20
minutes aka gama komai aka shiryata, ko magana bata iya yi sai kallon Ummi da take
hawaye na sakko mata har aka turata cikin dakin. gaba daya jikinsu ya gama sanyi
musamman Ummi da hawaye ya ki daina sakko mata, addu'a babu irin wacce batayi.
Kusan 1 and half hour suna tsaye a wajen sannan Dr. Hisham ya fito, Abba ya
kura masa ido yana kallansa, ya danyi murmushi yana kallan Abba ya ce "It was
successful Sir, an samu cute baby girl" ajiyar zuciya suka sauke, a tare duk suka
amsa da Alhamdulilah, Abba ya ce "Can we see her?" Ya ce "Not yet, za a mata allura
ne bayan awa daya zata tashi, but u can see the baby, zasu kawo muku ita soon" daga
haka ya wuce office dinsa yana cire hand gloves din hannunsa. Kafin a fito da Baby
Mummy ta yiwa mutane sunfi 30 waya cewa tayi jika, bayan minti 10 nurse din ta fito
da Baby a hannunta, sai kamshi take saboda yadda aka gyarata sosai, Ummi tayi
saurin mikewa ta kar6eta sannan ta bude fuskar Babyn dake rufe da towel, sai da
zuciyarta ya tsinke ganin kamannin Yusuf karara, ta sauke ajiyar zuciya ta mikawa
Abba Babyn, shima same thing abinda ya gani, ya danyi murmushi ya kai bakinshi
saitin kunnen Babyn ya mata kiran sallah hade da addu'a, hanging wayar Mummy tayi
ta kar6a Babyn tana murmushi ta ce "Gata kamar shashashan ubanta kuwa" Abba dai ya
kalli Ummi ya ce "Bari naje sallah na dawo" ta ce "Safe" Mummy ta ta6e baki ta ce
"Wallahi da ana canza halitta dana canza miki kamannin Yusuf, dan bai kamata ki
dauko kamarsa ba, baki sanshi ba bai sanki ba, banda ma hukunci na Allah taya
zakiyi kama da Yusuf, uban me ya tsinana miki a rayuwa" goge dan hawayen idanta
tayi ta ce "Allah ya taimakeshi watarana yazo yana kirarin shine mahaifinki,
wallahi saina yaga masa rigar rashin mutunci, sai ya kwammace bai sanni a rayuwa
ba, balle dangi na" Ummi dai bata ce komai ba, tasa tissue ta goge hawayen daya ke
kokarin gangaro mata. Dakin da Rafi'ah take kwance suka shiga, bacci take sosai
banda numfashi babu abinda take saukewa, Ummi ta kamo hannunta tana kallanta ta ce
"Allah ya baki lpy daughter" Mummy ta ajiye Babyn a gadonta ta zauna gefen Rafi'ah
tana mata addu'a. Kafin ta tashi mutane sunzo ganin Baby, makwabtan Mummy da Ummi
sai kuma friends din Ummi, Anty Amina da 'yan gidansu sai daga baya suka zo, Ammi
kam ita ce farkon zuwa ita da Sameer, Mami ma tazo sai murmushi take tana yaba kyan
yarinyar kamar da gaske, duk da itama batasan Yusuf sosai ba amma taga kamanninsa
da Babyn, Sameer dai ya dinga kallan Babyn dake kwance tana bacci, bayan 5 minutes
Rafi'ah ta fara motsa karfarta, duk occupants din dakin suka dawo kallonta, ta fara
bude ido a hankali tana salati, Ummi ta mike tana kallanta ta ce "Rafi'ah" kokarin
tashi take amma ta kasa, Mummy ta dagata ta zauna ta ce "Sannu, kinajin ciwo ne?" A
hankali ta nuna mata dai dai inda aka mata surgery din, Mummy ta ce "Sannu" limshe
idanuwanta tayi ta budesu, sannan ta fara bin katon dakin da kallo, kowa na dakin
take kalla amma bata ga Jawad ba, he once told her that duk lokacin data haihu tana
bude idanta zata ganshi a gefe, but he is absent now, suna hada ido da Mami tayi
saurin kawar da kanta gefe, the same thing daya faru lokacin data kalli Umman su
Anty Amina, Ikleemah na zaune kan carpet tana ta danna phone dinta, jin Mummy ta
ta6a ta yasa hankalinta ya dawo waje daya, ta sauke ajiyar zuciya kawai, Mummy ta
ce "U didn't ask for ur Baby daughter" sauke kanta ta kara yi tana wasa da ring din
hannunta, Mummy ta ce "Bari na dauko miki ita" kan gadon Babyn ta koma ta dauko
Babyn, sai kallon towel din da Babyn ke ciki take, Mummy ta mika mata ita ta ce
"Congratulation for having her, Allah ya kare miki ita daga sharrin masu sharri"
zaro ido Rafi'ah tayi ganin fuskar Babyn, her eyes, lips, the fair skin, nose gaba
daya is exact as Yusuf's own, fashewa tayi ta kuka ta rungume Babyn a jikinta kam
kam tana fadin "Why didn't u resemble me Habibty, i was the one who take care of u
since from the day i got u, i suffered for 9 months, i cried several times because
of u dear, isn't all this a prove to resemble me dear? bana bacci da kyau, bana ci
da kyau just because of u, meyasa ni baki yi kama dani ba" share hawayenta tayi ta
kara kurawa Babyn ido, sai kuma ta kara rungumeta ta ce "Anywhere, i luv u
Habeebty, ba wanda zai miki irin son da zan maki a duniya, i still remain ur mum
and Dad, nice komai naki a rayuwa, if anyone's to blame, he's mistaken dear, i'm
only yours, ke tawa ce ni kadai na, i luv u Habeebty" ta kara rungumeta tana kuka
sosai da sosai, duk jikin mutanen dakin sai yayi sanyi, musamman Ammi data kasa
tsayuwa sai ficewa tayi a dakin.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_4_

Kar6an Babyn Mummy tayi a hannunta ta ce "Stop crying like this daughter, ke daya
kamata ki godewa Allah kuma" hannunta tasa ta share hawayen daya sakko mata, Mummy
ta zauna gefenta bayan ta kwantar da Babyn ta ce "Calm down and rest dear, what do
u want to eat?" a hankali ta ce "Kunu zan sha" Mummy ta jawo basket din da Ammi ta
kawo ta dauko flask ta zuba mata kunu cikin mug sannan ta mika mata, a hankali ta
kar6a tana kallan Umminta dake zaune tayi shiru ta ce "Thank u mothers". Kwanan
Rafi'ah uku a asibiti aka sallameta, kuma har suka koma gida Jawad baizo ba
sakamakon tafiyar da aka sa shi yayi a wajen aiki, tin kwana daya da Rafi'ah ta
haihu Mummy ta gaya masa hankalinsa ya kasa kwanciya, komai yake a wajen he's in a
hurry, so yake ya gama komai ya koma kano a ranar amma hakan bai samu ba, dolensa
ya kara kwana biyu. Da yamma Rafi'ah na zaune a dakin Ummi tana breastfeeding
Babynta aka turo kofar, ta juyo tana kallan direction din kofar, Ummi ta shigo da
flask a hannunta, ta ajiye a gefensu tana kallanta ta ce "Hope u are not in any
pain, yace idan kinajin ciwo we should let him know" ta girgiza kai a hankali ta ce
"Ni banajin komai, kawai dai wajen ne yake dan zogi" Ummi ta ce "Kina shafa maganin
ne?" Ta ce "Eh" Ummi ta ce "To idan kun gama ki kawota gun Gwaggo sai ki huta" a
hankali ta ce "Ohk zan kawota" Ummi ta mike ta ce "Abinci fa?" Tayi saurin girgiza
kai sannan ta ce "Not now" daga haka Ummi ta fita ta jawo musu kofar, few minutes
ta gama ta kwantar da Babyn a gefenta ta kwanta itama, jawota tayi very close to
her ta rungumeta ta limshe ido, nan da nan duk sukai bacci, ganin shiru~shiru basu
fito ba yasa Ummi ta koma sama duba su saboda yadda Gwaggo ta matsa a kawo mata
Babyn, tana shiga dakin ta samesu suna bacci, Ummi ta kura musu ido cike da
tausayi, sai kuma tayi murmushi ta juya, she never thought Rafi'ah zata so dan da
zata haifa haka, tana sauka kasa Gwaggo ta ce "Ina jaririyar ne Zainab, idan ba'a
so a bani ba sai na hakura ba, ni dama ba ita nazo dubawa ba jikata nazo gani na
mata ya jiki" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Hajiya Gawggo na samu sunyi bacci ne,
kuma idan zan daukota zata tashi ne" Gwaggo ta ta6e baki tana kallan Mummy da Anty
Salma ta ce "To sai a kira uban Rafi'ah ya maidani Bauchi yau, tinda dama daga cewa
anyi haihuwa yaje ya daukomu muga 'ya, gashi kusan awana 1 ban dauki 'yar a hannuna
ba" Mummy ta ce "Gobe fa zaku koma Gwaggo ai zaki dauketa harki gaji" Gwaggo ta
mike ta ce "Ba sai nama dauketa ba, 'yar da akace da ubanta take kama, gara dai na
ciccibi ita Rafi'an tinda itama bata fi a dauketa ba" Har Mummy zatai magana Anty
Salma tayi mata alamar tayi shiru.
Anty Anina ce kwance a parlorn ta ita da Anty Rahama suna hira, kamar an tsikareta
ta mike ta ce "Ni kuwa Khadija tasan Rafi'ah ta haihu?" Anty Rahama ta girgiza kai
ta ce "Ta ina zata sani, dama bamu zamu gaya mata ba, kuma kusan shekara bama waya
da ita, ta ina zata sani to?" Anty Amina ta gyara zama ta ce "Bakisan Khadija ba
kenan, zata iya sa ayi mata bincike, idan kuma taga dama zata watsar dasu ne kawai"
Anty Rahama ta ce "Shiyafi mata sauki wannan, gaskiya yarinyar akwai kyau kam,
kinga dazu da Yah Muhammad ya daukota, har ta danyi kiba, wannan da namiji ne cewa
za'ai kakinta Yusuf yayi" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "Dama ai shine me kyau din,
ita dai Rafi'ah fara ce amma bazata hada kanta da Yusuf ba, kwata kwata basu dace
ba" Anty Rahama tayi dariya ta ce "Basu dace ba kam, gashi ai sun rabu" shiru Anty
Amina tayi jin an bude kofar parlor, Ikleemarh ta shigo ta zauna gefensu tana turo
baki, Anty Rahama ta mike ta ce "Waya ta6a ki?" Kuka ne ya kwace mata ta ce "Ba
wannan kanwar Kakan su Rafi'an bace, naje wucewa ta dinga zagina wai harda cewa
nima na kwaso ciwo, ai naga su suka fara ciwon kafin nayi" Anty Rahama ta ce "Share
hawayenki, ai ciwo yanzu suka fara gani, ciwo ya wuce wata biyu a sako yarinya tazo
gida ta haihu miji bai zo ba"...
Kukan Babyn ne ya tasheta daga baccin da take, ta mike a firgice tana kallan
Babyn, dagota tayi ta rungumeta tana share hawayen idanta, daga dan baccin nan data
kwanta mafarkin Yusuf tayi yazo yana ce mata ta bashi Babynsa, ta limshe idanuwanta
tana girgiza kai ta ce "It's impossible, she's only mine" daga haka ta gyara Babyna
jikinta tana kallan idanta dake bude, silently ta ce "Ni kadai kika sani Habeebty,
nine mamanki nine babanki kinji, inma akwai wani mahaifinki a duniya to Ya Jawad
ne" hawayen idanta ta share ta sakko a kan gadon still holding her baby ta bude
press dinta ta ciro wayarta ta kunna, raban data kunna ta tin ana gobe zata haihu,
yau kwana 4 kenan, Ameera ma ta wayar Ummi suke waya, bayan wayar ta kunnu tasa
hannu zata bude lock din kiran Jawad ya shigo, ta dan turo baki sannan tayi picking
call din, Jawad yayi sallama, shiru bata amsa ba, ya sake sallama, nan ma shiru, a
hankali yake jiyo sound din kukanta, ya danyi murmushi ya ce "I apologize dear, i'm
on my knees pls do forgive me" dan turo baki tayi ta ce "Where have u been Yaya?"
Ya ce "Kaduna, but i'm now in Kano, yanzu ina gidana zanyi wanka saina zo, hope my
Baby is fine" a hankali ta ce "Yes, when will u come?" Ya ce "Just few minutes from
now" ta danyi murmushi ta ce "Sai kazo to" ya ce "Alright dear" hanging call din
tayi ta goge hawayen idanta sannan tasa hijab ta dauki babyn suka fito, tin suna
sakkowa a stairs Gwaggo ke kallansu, bayan ta karaso ta ce "Ke ba haka ake bafa,
kinbi kin kankame 'ya ko kunya bakyaji 'yar fari ce fa" Rafi'ah ta danyi murmushi
ta ajiyeta akan cinyar Gwaggo sannan ta juya zata shiga kitchen Ummi ta ce "Kinci
abincin ne?" Ta ce "Zanci" daga haka ta shige kitchen. Mummy ne da Anty Salma sai
Saudatu suna hada girkin dare, Rafi'ah ta dan tsaya gefe tama rasa ta ina zata
fara, Anty Salma dake kallanta ta ce "Lafiya dai Rafi'ah?" Mummy ta juyo tana
kallanta itama, girgiza kanta ta danyi ta ce "No, ba komai" Mummy ta ce "Ko kinasan
wani abu?" ta kara girgiza kai, Mummy dai ta fahimci tana san abu amma ta kasa fada
ne, hannunta ta wanke a sink sannan ta kalli Rafi'ah ta ce "Muje parlorn Abbanku"
bin bayan Mummy tayi a hankali har suka shiga parlorn, bayan sun zauna ta ce "Tell
me what's wrong with you, what do u want" sauke kanta tayi kasa a hankali ta ce
"Dama Yayane yace wai yana hanya" Mumny ta ce "Wane Yaya, ko Sameer" ta girgiza
kanta a hankali ta ce "Ya Jawad" Mummy dake kallanta ta ce "Yaushe ya dawo?" Ta ce
"Dazu, yacemin yana gidansa wai daga nan zai taho nan" Mummy ta dinga kallanta
kafin ta ce "Ohk, sai a kawo mishi abinci nan" daga haka ta mike ta fita a parlor
Rafi'ah ta bita da kallo, ta jima zaune anan parlor ita kadai, horn din mota data
ji ne yasa ta mike ta leka ta window, ganin motar Jawad yasa ta danyi murmushi ta
koma ta zauna. Yana parking ya fito a motar da key dinsa a hannu, ya sha farar
shadda, yayi wani kyau sosai sai kamshi yake, a hankali ya dinga takawa zuwa
entrance din gidan, bayan ya danna bell yaja ya tsaya a gefe, Ummi ce kadai da
Gawggo a parlor sai Saudatu da shigowanta kenen ta wuce ta bude kofar, a hankali ta
ce "Bismillah" Jawad ya shigo parlorn kansa a kasa, kan carpet ya zauna yana
murmushi, Ummi ta ce "Jawad ne? Yaushe ka dawo?" Ya ce "Dazu Ummi, ina yini" ta ce
"Lafiya kalau Jawad, how is work?" Ya ce "Alhamdulilah, ashe an samu Baby girl"
Ummi ta ce "Wallahi, gata nan a kwance tana ta bacci" kallan dan karamin bed din
babyn yayi kafin ya ce "Allah ya raya ta da imani" Ummi ta ce "Ameen" kallan Gwaggo
yayi data zuba masa ido tin shigowarsa, ya ce "Ina yini Hajiya" ta ce "Lafiya kalau
yaro, kai din dan wane gida ne?" Ummi ta ce "Yaran Hajiya Hadiza ne" Gwaggo ta ce
"Kishiyar Halima kike fada?" Ta ce "Ehh, shine babba" Gwaggo ta ce "Ba shakka gashi
nan kamar honorable mahaifinsa, yayi aure ne?" Ummi ta mike ta ce "Aa baiyi ba
tukunna, Saudat kaishi parlorn Abba" Saudat dake goge kan dinning table ta ce "Toh"
mikewa yayi yabi bayanta har suka shiga parlorn, ta juya ta fita, a hankali ya ce
"Nagode" kan carpet ya zauna ya dauko wayarsa a pocket yayi dailing number Rafi'ah,
harta gama ringing bata dauka ba, ajiye wayar yayi ya dan juya, hangota yayi ta
kifa kanta akan dinning table, ya mike a hankali yana murmushi ya karasa inda take
zaune ya ce "How are u dear" kin kulashi tayi, ya kamo hannunta ya ce "Pls get up
dear, ko so kike nayi miki kneel down?" Dago kanta tayi a hankali ta ce "U don't
have to, but u broke the promise u made to me" murmushi yayi yana kallan face dinta
ya ce "Aina ce maki a wajen aiki ne aka turani, amma kinsan da babu abinda zai
hanani zuwa clinic ranar, now how are u feeling?" A hankali ta ce "Fine" ya kai
hannunsa face dinta ya share mata guntun hawayen daya sakko, ta sauke kanta kasa ta
ce "And u are not happy for seeing me" ya dan zaro ido yana murmushi ya ce "Who
told u, i am more than happy Fatima" wasa taci gaba dayi da fingers dinta tana
murmushi, ya koma kan carpet ya zauna yana kallanta ya ce "Most i tell u to bring
her for me, ko rowa zakimin" ta tashi a hankali ta ce "No, ni ai bana rowa" daga
haka ta fita a parlor, a corridor ta tsaya ta leka parlorn taga Ummi ce kadai, ta
fito calmly ba tare data kalleta ba ta dauki Babyn ta koma parlorn Abba, gefen
Jawad ta zauna ta mika masa Babyn ya kar6a, kallan fuskarsa kawai take lokacin daya
kar6a Babyn, ya dago kansa yana kallanta ya ce "She's so cute, Allah ya raya mana
cikin addinin islama" shiru tayi ta fara goge hawayen idanta, ya kamo hannunta ya
ce "Why is it that kuka baya maki wahala Fatima, u waste ur tears too much, what
makes u to cry, tell me now" cikin muryar kuka ta ce "Ni shine batai kama dani ba"
ya danyi murmushi yana kallan yadda take tura masa baki as if shiya halicci Babyn,
ya ce "So u thank God and stop crying dear, mu godewa Allah daya bamu this cute
angel, is she not cute?" ta daga masa kai ta ce "She is" ya ce "Kamar ke ba, kinma
fita kyau, just that ta fiki hanci" ta dan ta6e baki ta ce "Inma kace bani da kyau
ni ina ruwana" daga haka ta fara kokarin tashi a gefenshi, ya kamo hannunta yana
murmushi ya ce "No, don't go pls dear, kin fita kyau, kawai na fada ne, do u think
zance ta fiki kyau ne bayan kena fara sani na kuma fara..." Shiru yayi ganin yadda
take kallansa, yaja hancinta ya ce "My stubborn Rafi'ah" ta kauda kanta gefe ta ce
"Let me bring food for u" daga haka ta tashi ya bita da kallo.

_08103810398_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_5_

Bayan few minutes Rafi'ah ta dawo da tray a hannunta me dauke da snacks sai exotic
da glass cup a gefe, calmly ta ajiye a gabansa ta ce "Here it is Yaya" Jawad ya
danyi murmushi yana kallanta ya ce "Thanks" mikewa tayi yayi saurin riko hannunta
ta zauna gefensa ya ce "Ina zaki je?" ta ce "Abinci zan kawo maka" ya ce "No,
wannan ma ya isa" ta juyo tana kallansa ta ce "Kace fa baka ci komai ba" Ya ce "Ai
zanci wannan" ta dan matsa baya a hankali ta ce "Alright" kara matsowa yayi gefenta
ya kamo hannunta, ya kalli Babyn dake bacci hankali kwance sannan ya kara kallanta
ya ce "Are u with me Fatima?" Ta daga masa kai a hankali, silently ya ce "I just
want to tell u that, right from the day i met u, i love the way u smile the way u
laugh, and u know what?" Girgiza masa kai tayi kanta a kasa tana kallan hannunta
dake cikin nasa, limshe ido yayi ya tattaro courage dinsa ya ce "I notice that it
was lo..." Shiru yayi jin an bude kofar parlorn, tayi saurin jaa baya tana kallan
Mummy dake kallansu, ta ce "Meye haka Jawad?" Kansa ya dan shafa ya ce "Ehh, dama
abu ne ya fada mata a ido shine na hure mata" Mummy ta zauna akan kujera ba tare
data kalli Rafi'ah ba ta ce "Yayi kyau, when did u came back?" Ya ce "Ban jima ba,
banma je gida ba, but daga nan can zan wuce" ta ce "Ohk" ya danyi kasa da murya ya
ce "Congratulations once again for the cute Baby" ta ce "Thank u, baza kaci abinci
bane?" Ya ce "No, wannan dinma ya isa" sai lokacin Mummy ta kalli Rafi'ah dake
zaune gefe tana jujjuya ring din hannunta ta ce "Kar6eta ki bashi waje yaci abinci"
mikewa tayi a hankali ta kar6i Babyn sannan ta nufi hanyar fita a parlorn, Mummy ta
mike tabi bayanta ta ce "Idan ka gama zamu wuce tare" ya ce "Ohk to" daga haka taja
masa kofar. Cikin minti kadan ya gama cin abinda zai ci ya mike yasa phone dinsa a
pocket sannan ya wuce sink ya wanke hannu ya dawo ya dauka key din motarsa, a
parlor ya tarar da duk ilahirin gidan amma banda Rafi'ah, ya dan durkusa ya ce "Zan
tafi Ummi Allah ya raya da imani" Ummi dake murmushi ta ce "Ameen" Gwaggo ta ce "To
ni tinda nazo banga Hadiza tazo barka ba dama kuma..." Da sauri Ummi ta ce "Tazo
mana Gwaggo, tin muna asibiti ai tazo" Jawad ya mike ya nufi kofar fita, Ummi ta ce
"Allah ya kiyaye" Mummy da Anty Salma suka mike sannan sukai musu sallama suka
tafi. Har suka isa gida Mummy da Anty Salma hirarsu suke, shi dai yana ta driving
but zuciyarsa ya tafi wani tinani daban, what if Mami taga ya sauke su fa? ta kuma
tabbatar tare suke? dan karamin tsaki yaja yaci gaba da tuki, Mummy ta dan kallesa
ta ce "Lafiya da tsaki haka?" Ya ce "Ba komai" ta6e baki tayi taci gaba da bawa
Anty Salma labarin yadda Rafi'ah ta sha wahala a rainon cikinta. Dai dai kofar gida
Jawad yayi parking, Mummy ta ce "Ya zaka dire mu anan young man?" Ya dan shafa
tilin gashin dake kansa ya ce "Eh, zan fita an jima kadan that's why" Mummy tayi
masa wani kallo ta ce "Ko kana tsoron uwarka ba" daga haka ta fito a motar Anty
Salma ma ta fito suka wuce ciki, sai bayan shigarsu da minti 10 sannan ya gyara
motar ya danna horn, bayan an bude gate ya shigar da motar yayi parking sannan ya
fito ya nufi entrance din gidan, Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo, ta mike
a hankali ganinsa ta ce "Yaya sannu da dawowa" ya ce "Thank u, Mami fa?" Ta ce
"Tana kitchen" daga haka ya wuce kitchen walking gently, a bakin gas ya sameta
tsaye tana gauraya pepper chicken din da take, ya rungumeta ta baya yana murmushi
ya ce "Mami" ta danyi murmushi ta ce "Ahmad, saukar yaushe?" Ya ce "Yanzun nan,
aiki kike?" Ta ce "Kai nake yiwa pepper chicken, naga basan cin abincin gidanmu
kake ba, kaga koka tafi dashi sai kai warming dinsa, ai kana da microwave ko?" Ya
ce "Yes i have, thank u mother" ta ce "To kayi wanka kafin na karasa" ya ce
"Alright to" daga haka ya fita a kitchen din ya nufi dakinsa na da, ba kowa a dakin
amma a gyare tsaf tsaf, ya cire rigar jikinsa ya dauki towel ya shiga toilet.
Kananun kaya ya saka sannan ya fito a dakin, yayi kyau sosai da sosai sai
kamshi yake, ya leka kitchen yaga bata nan, hakan yasa ya wuce part dinsu yana
balle botton din hannunsa, a parlor ya sameta tana zaune ta zuba masa papper a
plate sauran kuma tasa a warmer, ya zauna gefenta ya ce "Is this all for me Mami?"
ta ce "Sure" a hankali ya jawo center table din gabansa ya fara cin naman, kusan
minti 10 ba wanda yayi magana a cikin, Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ahmad"
dagowa yayi yana kallanta ba tare daya amsa ba, ta ce "Yaushe zakai aure ne Jawad?
37yrs kana zaune min a gida haba dan Allah, yanzu ko Sadeeq da yake shekara 25 ai
zai iya aure, ya gama degree dinsa yana masters, amma kai ka gama komai kana aiki,
kana da gida sai dai kawai kaje gidan kayi bacci ka tashi ba mace, gidanma yana
maka dadi ne a haka?" Sauke kansa yayi daga kallanta ya ce "Very soon insha Allah,
ki daina damuwa" ta ce "To a ina yarinyar take, menene dalilin da bazai sa akai
tambaya gidansu ba, why not now?" a hankali ya dauki tissue yana goge hannunsa ya
ce "Saboda ta haihu ne, so i have to wait sai ta gama shayarwa" zaro ido Mami tayi
tana kallansa, lokaci daya taji zuciyarta na bugawa, cikin sauri ta ce "Wa kake
nufi ne, a ina take?" Ya ce "Wata yarinya ce, mijinta Allah ya masa rasuwa, dama
kuma tin kafin ya aureta muna tare, so iyayenta suka aura mata shi" Mami ta sauke
ajiyar zuciya ta ce "Allah ya kyauta, amma meya kaika auran bazawara Jawad? Ga
'yammata kaca kaca a fadin duniyar nan ka rasa wacce zaka aura sai bazawara" ya ce
"Ita nakeso Mami, idan kika ganta baza kiyi tinanin ta haifi diya ba, dan itama
bata fi diyar ba, bata cika shekara 19 bama a duniya" Mami ta masa wani kallo ta ce
"A ina take, and what's her name?" Ya gyara wristwatch din hannunsa ya ce "Sunanta
Zarah, tana zaune a unguwar rimi, amma iyayenta ba anan garin suke ba" Mami ta sake
sauke biyayyar ajiyar zuciya ta ce "Tinda haka ka zabarwa kanka Allah ya kyauta, ni
dai bazan maka fatan sharri ba, fatana ka samu wacce zata kula da kai" a hankali ya
ce "Insha Allah" Mami ta ce "Kaji Rafi'ah ta haihu ko?" Ya juyo surprisingly yana
kallanta ya ce "When?" Ta ce "Kwana hudu kenan, ai tayi~tayi ta haihu da kanta ta
kasa, kasanfa ba wayo ne, da wata babbace tsaf zata iya haihuwa, to yarinya dai sai
data galabaita ko hannunta bata iya dagawa sannan aka mata CS aka ciro mata diya
mace, tana nan duk ta kara karewa kamar ba a cikinta aka ciro wannan 'yar ba, kuma
diyar sak kama da ubanta, nidai nace wannan mutumi ya bar mata babban tabo a
rayuwa, ai nasan duk inda zata shiga da 'yar nan sai dai ace kanwarta ce, ba wanda
zaice ita ta haifeta ta, shi dai ya cucesu ya maida musu 'ya bazawara" shidai shiru
kawai yayi yana saurarenta, caan ya danyi tsaki ya mike, ta ce "Ina zuwa?" ya ce
"Gidana" ta ce "Sai gadarar cewa gidana gida ba mata, Allah ya kiyaye, kuma wallahi
ka rage wannan uban gashin" ya dan shafa kansa ya ce "Gobe insha Allah" daga haka
ya dauki food flask din ya fita ta bishi da kallo.
Few minutes ya kai shi gidansa dake old GRA, ya fito ya bude gate sannan
ya shigar da motar yayi parking ya koma ya rufe gate din, key yasa ya bude kofar
shiga gidan, ya zare key din sannan ya maida ta ciki ya tura kofar, kujeru ne masu
kyau a parlorn sai TV sai kuma air-conditioner dake kunne, ya wuce upstairs ya
shiga dakin dake farko ya rufe kofar, dakin tas tas ya sha farin bedsheed, ya
kwanta saman gadon ya jawo wayarsa ya kira Aliyu, bayan ya dauka ya ce "Ka dawo ne
Aumad?" Jawad ya limshe idansa ya ce "Ehh, na dawo dazu, kazo mana sai mu karasa
magana" Aliyu ya ce "Sai na tashi a aiki kenan, kana gida ko?" Ya ce "Ina gidana,
zan baka address" Aliyu ya ce "Alright then, saina gama zan ta6a ka" daga haka yayi
hanging wayar, number Rafi'ah yayi dailing, sai daya kusan tsinkewa tayi picking,
ya ce "Dear" a hankali ta ce "Yes, i hope u reach home safe?" Ya ce "Fine, how is
my Baby" ta ce "She's sleeping" ya ce "Ki shafamin ita" ta ce "Ohk, dazu kana min
magana kuma baka karasa ba" ya ce "Zan karasa but inaso sai ina kallanki kina
kallona" ta danyi murmushi ta ce "Alright to, ya gajiya" ya ce "Ba wani gajiya, how
are u feeling now?" Ta ce "Da sauki sosai" ya ce "Allah ya kara maki lafiya, i will
call u ltr, don't off ur phone pls" ta ce "To, sai anjima" ya mike ya ce "Thanks
Baby" daga haka ya katse wayar, kallan wayar ta dinga yi tana tinani, ko to bataji
daidai bane, ko kuma ce mata yayi ta gaishe da Baby?, ta dan ta6e baki ta mike ta
shiga toilet kar ruwan wankanta yayi sanyi.
Da yamma Mami tasa Sadeeq ya kaita gidansu Rafi'ah kamar yadda Abi ya bada umarni,
bata wani jima ba saboda surutun Gwaggo, bayan taga Baby da Rafi'ah ta mike ta musu
sallama, Gwaggo ta kalli Ummi ta ce "Ya dai fi babu akan baka zo ba, ita kishiyarki
tinda nazo banga ta shigo ba, ga dai baki ga hanci amma tsit kake ji" Ummi dai bata
ce komai ba, ta gyarawa Babyn kwanciya sannan ta rufa mata net, Gwaggo ta ce "Shi
Muhammad din a wajenta yake ne?" Ta ce "Ehh, tinda akai haihuwan ya koma caan,
kinga baki suna ta zuwa, bai katura muba muma bamu takura shi ba" Gwaggo ta ce "To
dama ana suna kice ya dawo dakinki, kuma saiya rama miki kwanakin da yayi acaan,
aike ba dutse bace" Mikewa Ummi tayi ta ce "Bari na kaiwa Rafi'ah tea Gwaggo"
Gwaggo ta ta6e baki ta ce "Zandamemiyar budurwa sai an kai mata shayi saboda ta
haihu, naga ba haihuwa tayi da kanta ba, ciro yarinyar akayi, ke dai kawai kice
kina mata bauta" tin tini Ummi tayi wucewarta ta barta zaune kusa da Babyn tana ta
zance.
Bayan su Mami sun bar gidan su Rafi'ah gidan Kawu suka wuce kamar yadda ta
bada umarni, a bakin gate tace yayi parking saboda ba dadewa zasuyi ba, daga haka
ta fito ta shiga gidan, Ihsan ce kadai a parlor tana cin abinci, ta danyi murmushi
ganinsu ta ce "Ina wuni Mami, Ikram bata zo ba?" Mami ta ce "Tana caan tana baccin
nata na jaraba, ina Hajiya?" Ihsan ta ce "Tana daki" Mami ta wuce daki ta bar
Sadeeq suna magana da Ihsan, a bakin gado ta zauna tana kallan Hajiya Fatima ta ce
"Yau dai nace bari nayi kokari na karaso, ku bada zua ba muma haka" Hajiya Fatima
ta ce "Aikin kyauta, ya yaran da maigidan?" ta ce "Lafiya kalau, ina Kawu?" ta ce
"Kawu tin safe bai dawo ba, sai kuma dare" tana rife bakinta Sadeeq ya shigo ya
gaisheta sannan ya koma parlor, ta kalli Mami dake zaune ta ce "Ni kuwa ina Jawad
ne?" Mami ta ce "Yana nan kinsan yanzu bada mu yake ba, ya koma gidansa zuwa yake
yana gaishemu" Hajiya Fatima ta ce "To lallaikam, ko dai ya fara neman aure ne?"
Mami ta ce "Dazun nan ya gama gayamin, wai yarinyar ta haihu shiyasa zai jira saita
yaye dan" Hajiya Fatima ta ajiye kayan hannunta da take ninkewa tana kallan Mami ta
ce "Rafi'ah zai aura kenan?" Wani katon ashar Mami ta saki ta ce "Tabbdi ai sai dai
idan bana numfashi, sunan ita waccen Zarah fa, kuma yace ma unguwar rimi take,
sannan kuma ita mijinta ne ya mutu" Hajiya Fatima tayi murmushi tana kallan Mami ta
ce "Kije dai ki kara bincike, tin ba yau ba ninasan Jawad san yarinyar nan yake,
kuma da kike kirarin sunanta Zarah ba sunanta Fatima ba? Koba ita ta haihu ba,
kawai dai rainin hankali yake so ya miki, amma so kam yarinyar nan yake so" nan da
nan zufa ya fara karyowa Mami, ta rasa abinda zata ce tana tinani, caan ta mike ta
fara neman layinsa a waya, bugu biyu ya dauka ya ce "Mami" ta ce "Duk abinda kake
koma menene ka bari ka dawo gida ka sameni" ya ce "Mami i have some important
things..." A fusace ta ce "Cewa nayi duk abinda kake ka bari kazo gida, umarni na
baka ba shawara na nema ba" daga haka tayi hanging wayar ta dauki hand bag dinta
kamar zata tashi sama ta fita a dakin, Hajiya Fatima ta bita da kallo tana
murmushi. Kallan Aliyu Jawad yayi ya ce "Kaga mun fara maganar guy din can kuma
Mami ta kirani urgently, so bansan me yake faruwa ba, i have to go now" Aliyu ya ce
"Ba komai, gobe ai Saturday koda safe zamu iya magana, i will call u idan naji wani
bayani" Jawad ya ce "Alright thank u" daga haka duk suka mike suka fita a parlorn.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_6_

Parking Jawad yayi dai dai gate din gidansu sannan ya fito a motar ya rufe ya shiga
ciki, Ikram ne a balcony tana wanke hijab dinta na islamiyya, ta dago tana kallansa
ta ce "Sannu da dawowa" a hankali ya ce "Sannu" daga haka ya murda handle din ya
shiga ciki, Abi ne kadai a parlor yana kallan TV, Jawad ya danyi kasa da kansa ya
karasa gefensa ya zauna akan carpet ya ce "Sannu da hutawa Abi" Abi ya ce "Thank u
son, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya mike ya ce "Let me see Mami" da
kai Abi ya amsa masa sannan ya wuce part dinsu, tana nan tsaye a parlor sai kaiwa
take tana komowa, jin an bude kofar tayi saurin juyowa tana kallansa ta ce "Who was
that girl u were talking about? I want to hear more about her" zama yayi akan
kujera yana kallanta ya ce "But i have told u iyayenta baza su bari aje yanzu ba,
sai ta gama shayarwa zan baku address din gidansu sai aje tamba..." A fusace ta ce
"Ni zaka mayar 'yar iska Ahmad? Are u here to tell me what i'm suppose to do, kaika
fini sanin sharudan aurene, ko ce maka nayi auranta zakayi yanzu, so nake na santa
na san iyayenta, now give me her number or their home address" dagowa yayi kawai
yana kallanta ganin yadda take tada jijiyoyin wuya, ya limshe idanuwansa kansa na
mungun sara masa ya ce "I will u give Mami, but pls u calm down, just have a peace
of mind even for some minutes" harara ta dalla masa ta ce "Ce maka akai hankalina
ba a kwance yake ba, just give me their address before i show u the bad side of me"
ta karashe maganar tana kafe shi da ido, jin an bude kofar yayi saurin mikewa yana
kallanta ya ce "I will get it to u now" riko rigarsa tayi ta ce "Ba inda zakaje, ka
fadamin da baki" karasowa parlorn Abi yayi yana kallan Mami ya ce "Why all this
shout Hadiza, muryarki har parlorna ana jinki haka" ba tare data kalleshi ba ta ce
"Nace ka bani ko!!!" Shi dai kansa kawai ya sauke kasa, Abi ya cire hannun Mami a
jikin rigarsa ya ce "What is exactly happening Ahmad?" A hankali ya ce "Ba komai"
Abi ya ce "Ba komai as in how, duk wannan ihun a banza take maka kenan" dan kallan
Mami yayi ya koma gefe, Abi ya kalleta ya ce "have a seat" kin zama tayi still tana
ta hararan Jawad, Abi ya ce "Magana fa nake miki Hadiza" Mami ta juyo tana kallansa
ta ce "Jiransa nake ya bani address din gidan yarinyar da yake nema" da mamaki Abi
yake kallanta ya ce "Me zakiyi to? Ke ina ruwanki kina mace a matsayinki na uwa, in
dai wannan maganar ne kima barta, when the time comes zakiji komai, jeka abinka
Ahmad" a hankali ya ce "Sai da safe" daga haka ya fice a parlorn Mami ta bishi da
harara, zama tayi akan kujera ta fara share hawayen idanta cikin kuka ta ce "Meyasa
kake min haka Honorable, sai kace bani na tsuguna na haifi Jawad ba, akwai wanda
yake da iko dashi duk fadin duniyar nan idan bani ba, amma duk sanda nazo da bukata
ta saika dinga sawa yana bijiremin" Abi ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta ya ce
"Nasan ke kika haifeshi, kuma kina da iko akan Ahmad, ba wai ina sa shi ya bijire
miki bane, yanzu menene naki na neman address din yarinyar da yake nema? So kike ki
zubar da girmanki a gaban 'ya'yanki ne, Ahmad yana miki biyayya iya iyawarsa but
wallahi am assuring u this duk ranar da kika kaishi karshe kar kiyi mamaki, banda
abinki ki kyaleshi mana, shiba yaro bane yanzu, ya san duk abinda ya dace da wanda
bai dace da shi ba, so duk abinda kika ga yayi ki masa addu'a kiyi fatan Allah yasa
shine alkhairi a gareshi, amma ba ki zauna kina kara daga masa hankali ba" share
hawayen idanta tayi ta ce "To shikkenan, na hakura amma wallahi idan wacce nake
zargi yake so yama sa a ransa babu aure a tsakaninsu" daga haka ta mike ta shige
daki Abi ya bita da kallo.

_~The next day~_


Washegari ya kama jibi suna, Rafi'ah na zaune tare da Ameera a daki suna dan hira
Ummi ta shigo, Rafi'ah ta mike tana kallanta ta ce "Munyi magana da Mummy dazu"
Ummi ta ce "Kizo dakina yanzu" daga haka ta juya, kallan Ameera tayi kamar zatai
kuka ta ce "Wai fa akan sunan Babyn ne, nina ce susa sunan duk wanda suke so, nasan
ko nace asa sunan wacce nake so ba lallai asa ba" Ameera dake kallanta ta ce "Kamar
ya? Ba dai su suka ce ki fada ba?" zama Rafi'ah tayi a bakin gado tana share
hawayen idanta ta ce "Sunan Maman Doctor nakeso asa Ameera, but nasan they won't
listen to me" daga haka ta kifa kanta akan gwiwowinta tana kuka, Ameera ta ce "U
shouldn't think that Fatima, kika san ko zasu yarda" ta girgiza kai a hankali ta ce
"Doctor have no prents alive, even one Ameera, ba shi da uwa ba shi da uba, sai
Ammi kadai ce take son shi, ya sha fadamin in dai ya haifi mace zai sa sunan
mamanshi idan Baby boy ne sunan mamanshi, i have to fulfill his wish Ameera, nasan
ya min abinda bazan manta da shi ba harna koma ga Allah, amma at this time inaso na
cika masa burin daya dade yana fata, and i don't think they will accept it" Ameera
ta sauke ajiyar zuciya tana kallanta cike da tausayi ta ce "Ki gwada, idan sun ki
then u accept whatever they say" mikewa tayi a hankali ta share hawayen idanta
sannan ta bude press dinta ta dauko hijab ta saka ta fita a dakin Ameera ta bita da
kallo, jikinta duk a sanyaye ta bude dakin ta shiga hade da sallama, Ummi dake duba
abu a press dinta ta ce "Kije kawai Rafi'ah zata fita, anjima sai muyi magana idan
ta dawo" har zata juya Mummy ta ce "Come here" karasowa tayi kanta a kasa ta ce
"Gani" Mummy ta ce "Ya idanki yayi jaa?" A hankali ta ce "Ba komai" sai lokacin
Ummi ta kalleta, bata dai ce komai ba taci gaba da abinda take, Mummy ta ce "U said
nothing, amma kamar kinyi kuka?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "Kaina ne kawai
yake ciwo" Mummy ta ce "Go and make sure u take your drugs" juyawa tayi bata ce
komai ba ta fita a dakin ta koma dakinta.
Jawad ne zaune a parlorn gidansa shida Aliyu, kowa da abinda yake tinanin, caaan
Jawad ya danyi tsaki ya ce "Tabbas baya kasar nan, to amma wa kake ganin zai san
inda yake?" Aliyu yayi shiru yana tinani, sai kuma ya ce "Idan fa akwai wanda zai
san inda yake so definitely it most be me ko Mukthar, sai kuma wannan cousin din
nasa Sameer" Jawad ya cire glasses din idansa ya ce "Kenan duk baku sani ba?" Aliyu
ya ce "Ehh, ko ita maman Sameer din bata sani ba, dan kwana biyu da faruwan abun
sun zo asibitinmu ita da mijinta ko zasu samu wani bayanai akansa amma babu" mikewa
Jawad yayi yana zira hannayensa cikin pockets din wandansa ya ce "Kace baya shan
komai?" Aliyu ya ce "Kyakkyawan sani nayi wa Yusuf, kaga dai shi kikita ne ko? Amma
wallahi kwayar magani da kyar yake hadiya balle kuma har yayi shaye shaye, ni kaina
abin mamaki ya bani, i don't know what comes over him, yana san matarsa fa wallahi"
dan karamin tsaki Jawad yaja ya ce "To idan yana santa me zaisa ya saketa da ciki,
almost a year harta haihu bai dawo ya ganta ba" Aliyu ya ce "Shine kuma abin
dubawa, amma ina ganin koma menene ya faru da sa hannun mutanen gidansu, tinda duk
tasu suka tafi, kuma suka tafi harda matar da suke so ya aura, Yusuf ba zai ta6a
cutar da Fatima ba Ahmad, karkace nayi maka shishigi game da abinda kake, kai
aikinka ne ni kuma ina fadan abinda nasan Yusuf zai iya ne, Yusuf ba shi da hali
marar kyau Barrister sai dai kuma kasan dan Adam ta wani bangaren" a hankali Jawad
ya zauna gefen shi ya ce "No, ai wannan ba shishigi bane, nima a nawa fahimtar
banga alamun rashin gaskiya a tattare da shi ba, just that ni bana shiri da shi
sabida wani dalili nashi" Aliyu ya ce "Yanzu menene abinyi kenan?" Jawad ya maida
glasses dinsa ya ce "We should keep on praying, idan aka kasa gano abu sai ayi ta
addu'a, but ina tabbatar masa duk ranar daya dawo he will be arrested kuma matar
daya saka tayi masa nisa by then, dan tini ta auri wanda zai sota har abada" Aliyu
ya ce "Allah ya za6a mana mafi alkhairi, ya kuma bayyana shi" a hankali ya ce
"Ameen, thanks for ur time Dr. Aliyu" Aliyu ya mike yana mika masa hannu ya ce "Ur
welcome Barrister, in dai naji wani abu i will let u know" Jawad ya ce "Nagode
sosai" har bakin motarsa ya rakashi ya bude masa gate bayan ya fita ya rife ya dawo
ciki, phone dinsa ya dauka ya kira Rafi'ah, tana fara ringing ta dauka hade da
sallama, ya ce "How are u?" Ta ce "Fine" ya ce "What about my Baby" ta danyi
murmushi sannan ta ce "She's fine too, sai kuma kuka takemin jiya i didn't slept
well at night" ta karashe maganar tana turo baki kamar yana kallanta, ya dan shafa
kansa yana limshe ido ya ce "To ki bani ita kawai" ta ce "To kazo ka kar6a idan
zaka iya rikewa" ya bude idanuwansa ya ce "Sai dai idan tare duk zaku dawo gidana,
kinga sai mu rike babynmu da kyau" a hankali ta danyi murmushi har yana jiyo ta
sannan ta ce "Sai dai ita din dai" ya ce "A'a ni da Mummy da daughter nakeso" tayi
dariya kawai bata ce komai ba, Jawad ya ce "Ya jikinki din ya warke?" Sai data
kalli wajen CS dinta sannan ta ce "Saura kadan" ya ce "Allah ya sauwake" ta ce
"Ameen" ya ce "I will call ltr, i'm going home, tin jiya banje na gansu ba" ta ce
"Alright saika dawo" daga haka yayi hanging wayar ya dauka hula ya saka sannan ya
dauki key din mota ya fito a gidan, garin is too cloudy sai iska da ake busawa me
kura, sai daya rife duk windows din gidan kafin ya fitar da mota ya kulle gate din
sannan ya dauki hanyar gida. Kafin ya iso gida an fara ruwa sosai da sosai, yana
isa yayi horn aka bude gate sannan ya shiga yayi parking ya fito da sauri ya nufi
entrance din gidan, ba abinda ya tsana irin yaji shi a jike, ba kowa a parlorn
hakan yasa ya wuce dakinsa ya canza kaya sannan ya dawo part din Maminsa, Sadeeq da
Ikram na zaune a parlorn suna cin abinci, duk suka masa sannu da zuwa sannan ya
shige ciki, dakin ma ba kowa amma yana jiyo alamun mutum a toilet, hakan yasa ya
kwanta kan gadon ya rufe kafafuwansa da blanket, after few minutes Mami ta fito a
toilet, ta tsaya tana kallan kan gadon don dakin yayi duhu, a hankali ta ce
"Sadeeq" ya bude idanuwansa yana kallanta ya ce "It's me" ta hade rai ta juya masa
baya sannan ta nufi kofa ta fice a dakin, mikewa yayi da kyar dan sanyi yakeji
sosai, ya fito a dakin ya shiga wanda ke opposite dinsa, yana shiga Mami ta mike
daga zaunen da take ta ce "Uban me zan baka ne Jawad kake bina haka, cin mutunci da
kayimin bai isheka ba kazo ka karamin wani ne?" a hankali ya ce "Dan Allah kiyi
hakuri ki daina fishi dani Mami, i have no mother but u, ke fa kika haifeni idan
banzo wajenki ba wajenwa kike tinanin zanje naji dadi Mami, pls forgive me Mami"
tsayawa tayi tana kallansa ganin yadda ya kamo hannayenta duka biyu, sosai taji
jikinsa yayi dumi, ta ce "Are u sick?" Ya ce "Kawai sanyi nakeji Mami" a hankali ta
ce "Ka kwanta to" kwanciya yayi akan gadon yayi pillow da cinyarta, ta jawo blanket
ta rufa masa, ya limshe ido yana jin wani dadi yana ratsashi, shafa gashin kansa ta
shiga yi a hankali ta ce "I hope ba zazza6i za kai ba?" ya ce "No insha Allah" daga
haka ta kura masa ido, duk cikin 'ya'yanta ba wanda take jin shi har ranta kamar
Jawad, tasha wahala kafin ta haifeshi, after then sai da yayi shekara 11 kafin ta
haifi Sadeeq, wani lokaci saita masa abu itama taji duk bata kyauta ba, sai dai
kuma idan Rafi'ah yake so ta nan bangaren sai inda karfinta ya kare, kamo hannunta
yayi ya ce "Mami" ta dawo daga tinanin data lula ta ce "Ahmad" ya ce "Kiyi hakauri"
ta ce "It's ok" daga haka ta gyara masa blanket din tana kallansa. Abdul ne ya
shigo dakin Rafi'ah rike da baby girl, tana zaune akan sallaya ta idar da sallan
la'asar, ya ce "Anty Mummy na kiranki a dakin Ummi" ta ce "Ohk, be careful karka
jefarta" ya danyi dariya ya ce "Aina fiki ma iya rikewa" ita dai bata ce masa komai
ba ta mike ta nufi dakin Ummi, ita da Mummy ne kawai a dakin, ta nemi waje ta zauna
tana kallan Ummi ta ce "Gani" Mummy ta ce "Akan maganar sunan Babynki ne, kikace
asa sunan duk wanda aka ga dama ko" ta daga kanta a hankali ta ce "Eh, duk wanda
kuka ga ya dace" Mummy ta ce "Kar mu tauye miki hakki ne daman, idan akwai wacce
kikeso asa sunanta saiki fada" shiru tayi at first taki cewa komai, Mummy ta ce
"Ina jinki" sauke kanta tayi kasa ta ce "Sunan Maman Doctor nakeso a sa" da mungun
mamaki Ummi ta dago tana kallanta, sai kuma ta6e baki ta mike ta fita a dakin,
Mumny dake kallanta cikin 6acin rai ta ce "Uban waye shi daza asa sunan uwarsa,
shiya raini cikin? Ko shiya sha wahala dake" hawayen idanta ta share ta ce "Amma ai
shi ne mahaifint..." Kafin ta rufe bakinta Mummy ta kifa mata mari, Rafi'ah ta
fashe da kuka ta mike tana jaa da baya ta ce "Kiyi hkr pls Mummy"

*_I want to see sweets and meaningful comments_* 🤗


_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_7_

A hankali ta durkusa kasa nan bakin kofa tana goge hawayen idanta ta ce "I don't
mean to hurt u Mum, u said i should say out what's in my mind, kuma na fada miki
ban boye miki komai ba, da nasan hakan zai 6ata miki rai wallahi i won't even say a
word" daga haka ta kara fashewa da kuka, Abba ne ya bude dakin jin kukanta, ya
kalli Mummy dake zaune har lokacin ranta a 6ace ya ce "What's going on? Why are u
crying Mamana?" ita dai Mummy bata ce komai ba, Abba ya kama hannun Rafi'ah suka
fita a dakin zuwa dakinsa, a bakin gado ya zaunar da ita yana kallanta ya ce "Keep
quite and tell me what's wrong with u" a hankali tasa hijab dinta ta share
hawayenta ta ce "Sunce na fadi sunan da za'a sama Babyn shine nace sunan..sunan.."
Share mata hawaye Abba ya shiga yi ya ce "Feel free and tell me Mamana" sauke kanta
tayi wasu sababbin hawaye na kara gangaro mata ta ce "Sunan Maman Doctor nace, Abba
he has no one sai yarinyar nan, ai banyi laifi ba tinda shine dai mahaifinta, no
matter how, ko kisa yake i can't change him from who he is, he still remain her
father, but she slapped me Abba" cikin rarrashi Abba ya ce "Ya isa kiyi shiru, duk
abinda kikeso shi za'ayi, ki kwantar da hankalinki kinji ko?" kai ta daga masa
sannan ta mike ta ce "Nagode Abba" cike da damuwa ya ce "Ba komai Mamana" daga haka
ta nufi kofar fita, tana bude kofar suka ci karo da Ummi, ta sunkuyar da kanta ta
koma gefe, bayan Ummi ta shige ta fita ta jawo kofar.
Tin daga ranar har ranar suna Ummi ko Mummy basu kara mata magana akan sunan ba,
ita ma kuma bata ce komai ba, bata san kuma wane hukunci suka yanke ba, ranar suna
tin da safe Mummy ta kira mai make~up ta mata, duk da haushinta takeji hakan bai
hana ta shiryata ba, tsaf Mummy ta shiryata cikin tsadden lace dinta, tayi mungun
kyau sosai da sosai, sai dai har lokacin bata san sunan da aka sawa Babyn ba,
mikewa tayi kamar marar lafiya ta haura stairs Gwaggo ta bita da kallo, dakin Abba
ta shiga ta rufo kofar, ta zauna gaban mirror tana karewa dakin kallo, tasan an
kawo stickers jiya amma kuma bata gansu ba, mikewa tayi ta dinga bubbude drawer ko
zata gani amma babu, daga kanta tayi ta hango bakin leda akan wardrobe, ta jawo
stool ta hau kai sannan ta dauko ledan, zama tayi a bakin gado ta bude ledan,
stickers ne masu yawa a ciki, ta dauko daya tana karantawa, ta saki wani murmushi
ganin an rubuta *Fatima Yusuf Muhammad* ta limshe idanuwanta a hankali ta ce "Thank
u Abbana, i know it's you, nagode sosai" jin an bude kofar yasa tayi still a wajen
tana zare ido, Ummi ta karaso tana kallanta, mikewa tayi ta kulle ladan zata mayar
Ummi ta ce "Sai ki tafi dashi kasa ki kaiwa Mummy za suyi amfani dashi, ai
hankalinki ya kwanta tinda kin gani" bata ce komai ba ta wuce ta fita a dakin Ummi
ta bita da harara, ko data sauka ta bawa Mummy ledan ta wuce parlorn Abba ta zauna,
dan ita yanzu bata san shiga mutane kafin a fara mata bori. Da yamma liss gidan
Ummi ya cika da baki, aka ci aka sha sannan akai hotuna, sunyi kyau sosai kowa ka
gani yana cikin farinciki, Mami ma tazo gidan, Ammi dai bata zoba saboda itama
gidanta a cike yake da mutane, Mummy kuwa duk wanda ya tambayeta sunan Babyn sai ta
dan hade rai kafin ta fada, kusan magrib duk yawanci mutanen sun watse, sai 'yan
uwa, wannan karan dai ba dangin Abba da suka kwana part din Anty Amina, a cewarsu a
biki ma basu ji dadi ba, sabida haka basu ma zo da yawa ba. Wajen karfe 9 na dare
Rafi'ah na zaune dakinta tana breastfeeding babynta Ummi ta shigo da flask a
hannunta, ta dan sauke kanta kasa ganin har Ummi ta iso indan suke, tin data haihu
bata yarda tayi breastfeeding a gaban kowa ba, ko dai ta koma daki ita kadai ko
kuma tasa veil ko hijab da rufe jikinta, gaba daya she was uncomfortable, Ummi ta
ce "Kije parlorn Abba Jawad yazo" ta ce "Ohk" Ummi na tashi ta turo baki ta jawo
dan kwalinta dake kan gadon ta sannan ta kwantar da babyn ta dora dan kwalin tasa
hijabi sannan ta dauketa suka fita. zaune ta sameshi a parlor ya sha manyan kaya,
ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "U are welcome" ya ce "Thank u, ya hidima?"
Ta ce "Alhamdulilah" bayan ya kar6i babyn ta kalli Cannula dake hannunsa, dan zaro
ido tayi ta ce "Are u sick?" Ya ce "I recovered, nayi zazza6i ne" ta dan turo baki
ta ce "But baka fadamin ba" ya ce "Is because is not that critical, idan muna waya
ai bakya ganewa" ta ce "Yes, karfin hali kake kenan, amma ka rame ma" ya danyi
murmushi yana kallanta ya ce "Mind not Rafi'ah, naji sauki sosai" shiru tayi tana
wasa da fararen yatsunta, ya ce "Allah ya raya mana Fatima Zarah akan sunnah, mai
suna ki kaiwa kanki shine ko kunya babu" ta danyi dariya ta ce "No, sunan Maman
Doctor ne, kuma sunana, kaga taci sunan manya" ya ce "Hakane, i also like the name"
ta ce "Really" ya ce "Yes" shiru ne ya biyo baya, ta dago kanta tana kallansa taga
ita yake kallo, kara sauke kanta tayi, ya danyi murmushinsa me kyau ya ce "Let me
ask u" ta ce "I'm all ears" ya ce "Shi Doctor bai fada miki inda zai tafi ba? bai
kuma ta6a ce maki akwai kasar da yake son zua ba?" Kin dago kanta tayi jin hawaye
ya gama taruwa a idanta, Jawad ya dago kanta yana kallanta, tayi saurin limshe
idanuwanta nan kuma hawayen ya samu damar sakkowa, ya share mata hawayen ya ce "I
didn't ask u to cry, tambaya fa na miki, or have u forgotten my profession?" Ta
girgiza kai ta ce "No, ni bai ta6a fadamin ba" ya ce "But how was his reaction
sanda ya baki takardan sakin?" Ta dan turo baki, sai kuma ta ce "He's somehow,
hankalinsa kamar baya jikinsa, komai yi yake kamar ana controlling dinsa, but nasan
ya tsaneni ne shiyasa, i don't know why bai nunamin true color dinsa ba sai dana
aureshi, i regreat knowing him Yaya Jawad, nasan dai it's my destiny kuma raban na
haifi wannan abin ne" Jawad ya kamo hannunta yana kallan cute face dinta data wanku
da hawaye ya ce "Stop saying all this Fatima, kiyi ta addu'a kawai, idan shine
alkhairinki kuma ba shiya cuce kiba, definitely one day zaku..." Shiru yayi yana
kallanta, sai kuma ya goge mata hawayen idanta ya ce "Everything will be fine soon,
and u stop calling my baby wannan abin" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "To
Fatima" ya ce "No, she's bearing ur mother's in-law name, ba zamu kirata da sunan
ba" ta bude hannayenta alamun bata sani ba, sai kuma ta ce "Ni bansan me zan ce
mata ba" ya ce "Zamu kirata da *Imaan*" ta dan yi murmushi ta ce "Insha Allah" ya
ce "Good baby girl, to kiyi min murmushi" ta sake yin murmushi sannan ta boye
fuskarta tana dariya, mikewa yayi ya kwantar da babyn akan shoulder dinsa ya ce
"I'm going, Allah ya raya mana Imaan" ta ce "Ameen Barrister" daga haka ta mike ta
kar6a babyn, har compound ta raka shi sannan ta dawo ciki. Bayan ya karasa parking
lot ya bude boot ya ciro babban trolley yana kallan Mustapha ya ce "Ka shigar da
shi ciki, but ka budemin gate kafin nan" Mustapha ya ce "Angama oga" daga haka ya
bude masa gate, Jawad ya koma mota ya tayar sannan ya fita a gidan. Jan trolley
Mustapha yayi har cikin parlor, Gwaggo ne da wasu mata na zaune suna cin abincin
dare, ya ajiye akwatin zai fita Gwaggo ta ce "Ke kuma fa?" Ya ce "Cewa yayi na
shigo da shi" ta ce "Wa?" Ya ce "Wanda ya fita" Gwaggo ta ce "Ohh dan gidan Hadiza"
mikewa tayi zata ja akwatin taji nauyi, Abdul da fitowansa a daki kenan ya tsaya
kallanta ya ce "Ina ke ina daukar wannan Gwaggo" ta ce "Maza dauki ka kaiwa Zainab,
muje tare dan naji akwatin da nauyi" Abdul yaja trolley suka haura stairs, Ummi da
Mummy na zaune a parlor suna magana, ganin Gwaggo yasa sukai shiru, ta ce "Maza
shigo dashi" Abdul ya ajiye akwatin a tsakiyar parlor ya ce "Gaskiya da nauyi" daga
haka ya fice a parlorn, Ummi ta ce "Wannan fa Gwaggo?" Gwaggo ta zauna ta ce "Ina
na sani, dan gidan Hadiza ne ya kawo yace a shigo da shi" Mummy ta ce "Wace
Hadiza?" Gwaggo ta zauna gaban akwatin tana zugewa ta ce "Hadiza abokiyar zamanki
mana, mu a danginmu akwai me irin sunan ne?" Nan da nan Mummy ta hade rai, Ummi dai
kallan kayan cikin akwatin kawai take, pamper ne manya~manya sai kaya masu tsada
iri iri da overall, wipes, tissue, baby soap, baby lotion, baby perfume, towels,
earrings, rings, socks, vip, pants, duk wani tarkacen da ake bukata sai daya siya
ya zuba, bayan Gwaggo ta gama ciccirosu ta kalli Ummi ta ce "Kinga idan ta gama
shayarwa sai kawai ayi aure, dan tin ba yau ba nasan wannan yaran santa yake,
wannan figigiyar jaririyar na cika wata tara dama ta yayeta, ai tama mata mutunci,
naga ubanta tin cikinta bai fito ba ya gudu ya barta" Mummy ta mike ta wuce dakin
Rafi'ah, fitowanta a toilet kenan, Mummy ta ce "Yaushe Jawad yazo gidan nan?" Ta
sauke kanta kasa ta ce "Dazu, amma ya tafi" Mummy ta ce "Meye tsakaninki da Jawad
Rafi'ah?" Ta dan zaro ido ta ce "Ni kuma" Mummy ta ce "Sai kizo parlor kiga abinda
ya kawo miki" daga haka ta juya ta fita a dakin, hijab dinta ta saka sannan ta
fito, ta tsaya caan bakin kofa tana kallan tilin kayan dake gaban Gwaggo, Mummy ta
wuce dakin Ummi ranta a 6ace, Ummi ta mike tabi bayanta, a bakin gado ta sameta a
zaune, Ummi ta ce "Karfa ki yanke hukunci baki tabbatar da abu ba" Mummy ta sauke
ajiyar zuciya ta ce "Ai bazai ma yiwu mu hada zuri'ah da Hadiza ba, yanzu ma ba
abinda muka hada amma tabi ta takurawa Rafi'ah" Ummi ta ce "Allah ya kyauta" daga
haka ta fita a dakin. Komawa daki Rafi'ah tayi ta dauka wayarta ta kira Jawad amma
phone dinsa a kashe. karfe 10 da rabi Mummy ta kwashi 'yan kwananta suka wuce
gida, tana parking ta fito suka nufi cikin gida, murda handle din Mummy tayi taji a
rufe, Anty Salma ta ce "Ko dai sunyi bacci" a takaice ta ce "Akwai key a jakana"
daga haka ta ciro key a hand bag dinta ta bude suka shiga.
Washegari karfe 8 bayan sunyi wanka Mummy ta mike don ta samar musu
abinda zasu yi breakfast, a parlorn Abi ta samu Mami tana hadawa Jawad tea, shi dai
yana zaune akan kujera ya limshe ido, Mummy ta dan kalleshi sannan ta wuce kitchen,
within few minutes ta dafa musu indomie ta juye cikin babban tray sannan ta kai wa
su Anty Salma dakinta, dawowa parlor tayi tana kallan Jawad ta ce "Ahmad" ya bude
idanuwansa a hankali yana kallan Mummy, ta ce "Ka shigo parlorna zamuyi magana"
Mami ta ajiye serving spoon din hannunta ta ce "Ya za'ai kina gani bashi da lafiya
kice masa ya tashi har wani ya shiga parlor ki" daga mata hannu Mummy tayi ta ce
"Look, banfa yi dake ba, dashi nake idan kuma ba zai shiga ba, yayi wa kansa"
mikewa Jawad yayi gently yana shafa gashin kansa, Mami ta ce "Koma ka zauna tinda
nina haifeka ba wata ta haifamin kai ba" , zama zaiyi akan kujera Mummy ta ce "Ohk
sbd bani na haifeka ba saika zauna kenan" ya dan kalleta sai kuma ya kalli Mami
dake tsaye wajen dinning ta wani hade rai, Mummy ta danyi murmushi tana kallansa ta
ce "Well, idan kaga dama ka zauna saboda ni ban isa na baka umarni ba, amma fa ka
sani akwai abinda zaka zo kana nema a wajena, kana tinanin zan baka a haka?" Shiru
yayi yana kallanta sai kuma ya sauke kansa kasa, Mummy ta juya ta shige part dinta,
bin bayanta zaiyi Mami ta ce "Come back and sit down Jawad" ya juyo yana kallanta
yama rasa abinda zai ce.

😄 *Jawad zai bi Mummy ko dai ya fasa ya bi umarnin uwa?* 🤭

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _
_8_

Komawa Jawad yayi ya zauna akan sofa yana kallan Mami data kafeshi da ido, ya sauke
kansa kasa ya ce "Is Abi out?" Harara ta dalla masa ta ce "Why won't u call him"
daga haka ta wuce part dinta, mikewa yayi a hankali ya shiga daki ya zauna bakin
gado, sosai kayan jikinsa suka masa kyau, ya mike yasa glasses dinsa sannan ya fito
a dakin ya nufi part Mami, a parlor ya sameta suna zaune tana wa Ikram tsifa, ya
zauna akan kujerar dake opposite dinsu, Ikram ta ce "Yaya dan Allah ka kaini gidan
Baffa idan fita za kai" ya dan hade rai ya ce "Who is your driver?" Ta dan turo
baki bata ce komai ba, Mami ta ce "Ina zakaje yanzu kaida ba jin dadi kake ba?" A
hankali yana girgiza key din motarsa ya ce "My house" ta ce "To do what?" Ya ce
"Yau zan koma tinda naji sauki" Mami ta ce "To Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen"
mikewa yayi zai fita Ikram ta ce "Yaya na taso mu tafi dan Allah" ya ce "No, i'm
not going that way, ki bari Sadeeq yazo ya kaiki" daga haka ya fice a parlorn ya
rufo musu kofa. cikin quick light steps ya karasa part din Mummy ya murda handle
din ya shige, ba kowa a parlorn ya zauna akan kujera yayi sallama in a low voice,
Mummy ta fito rike da wayarta a hannu ta zauna tana kallansa ta ce "So u came?" Ya
dan shafa gashin kansa ya ce "Yes, kiyi hakuri abinda ya faru dazu" Mummy ta ce
"No, ba komai ai uwa ce, ni kuma kaga ban haifa ba" ya dan zaro ido ya ce "Noo, ba
haka bane, ni duk na daukeku a matsayin iyayena" ta ce "Ohk, dama akan kayan da ka
kai jiya ne, mungode Allah ya saka da alkhairi" silently ya ce "Ameen" Mummy ta ce
"Amma do u have any feeling for her?" A hankali ya dago ya kalleta sai kuma yayi
shiru, Mummy ta ce "Yes u have, but y kake ganin hakan zai faru Jawad? Ni dai bazan
muku fatan tsiya ba, amma kafi kowa sanin halin mahaifiyarka, kuma ba lallai ne ta
yarda ba, beside bama san zuwan Rafi'ah gidan nan take ba balle ace ta zama matar
dan ta" shiru Jawad yayi yana jin Mummy, bayan ta gama ya ce "Ba abinda zai faru
insha Allah" Mummy ta ce "Ohk Allah yasa, Allah kuma ya za6a muku duk abinda yafi
alkhairi" ya ce "Ameen" ta ce "And then ni baza'a ji wannan maganar a bakina ba,
idan ta amince kun fahimci junan to, amma duba da abinda ya faru da ita a baya
bazan sake takurata tayi aure nan kusa ba" Jawad ya ce "No it isn't ur fault Mummy,
ai kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa" ta ce "Hakane, but there is a
reason" daga haka ta mike ta ce "Ya jikin naka?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Allah
ya baka lafiya" daga haka ta shige daki, mikewa yayi ya karasa kofar parlor ya bude
a hankali yana lekawa, ganin ba kowa ya fito ya fice a gidan da sauri.
A ranar duk mutanen da suka halacci suna suka wuce, Ammi tazo da wasu 'yan
uwanta mata biyu suka kawo akwatina guda biyu na kayan baby dana Rafi'ah, sosai
Khairiyya ta makale Imaan a jikinta wai da ita zata tafi, bayan da suka tashi
tafiya Ammi ta danyi mata nasiha daya sa gaba daya jikinta yayi sanyi, karshe dai
sai da tayi kuka. Kwana uku da suna Ameera ma ta koma school, Ummi ta koma aiki,
gidan ya rage daga ita sai Saudatu.

*_3 YEARS LTR_*


Tsaye take a kitchen gaban gas tana soya kwai, jin motsi a bayanta yasa ta juya da
sauri, wani mungun bugawa zuciyarta tayi ganin irin tsayuwar da Imaan tayi, just as
how Yusuf used to, a hankali ta ce "What's it?" yarinyar ta dan jaa baya ta ce
"Ummi is calling u" juyawa Rafi'ah tayi tana taci gaba da abinda take, gaba daya
jikinta yayi sanyi, tinda Imaan ta taso ta fara tafiya da magana kusan kullum sai
zuciyarta ya buga, musamman idan taga ta jinginu a wani abu tayi folding
hannayenta, ko kuma in tai wani abun sai Yusuf ya fado mata, a yanzu kuma kokari
take taga ta manta dashi amma ga 'yarsa na kokarin dawo mata da ciwanta, a hankali
ta share hawayen idanta ta juye kwan cikin plate sannan ta fita a kitchen din, Ummi
na zaune a parlor da Imaan a cinyarta tana mata surutu, Rafi'ah ta ajiye plate din
kwan a gabansu ta ce "Gani" Ummi ta ce "Dama Mummy ne ta kira wai ki kai mata Imaan
idan zaki wuce school" ta wani turo baki ta ce "Ummi zanyi late fa, kuma test nake
dashi" Ummi ta wurga mata harara ta ce "Sai ki kirata ki gaya mata" daga haka Ummi
ta mike ta wuce parlorn Abba, kallan Imaan tayi ta ce "Will u eat?" ta karashe
maganar tana nuna mata fried egg din dake ajiye gabanta, girgiza kai yarinyar tayi,
Rafi'ah ta dan ja tsaki ta ce "Idan na ce bazanyi ba a takuramin gashi nan baci
zakiyi ba" kallan Imaan tayi data zuba mata ido ta ce "Go and wear your scarf" ta
mike a hankali ta wuce sama, dauke idanta tayi daga kallanta saboda zuciyarta da
taji ya fara bugawa, ta kara yin tsaki sannan tabi bayanta, zaune ta sameta akan
gado ta dauko tap dinta tana dannawa, ta kalli Rafi'ah da babu walwala a tattare da
ita ta ce "Momma what's wrong with u?" bude press dinta tayi ta dauko mata hula ta
karasa inda take zaune, zama tayi ta jawota jikinta tasa mata hulan ta ce "U stop
talking anyhow dear, banasan kina magana sosai because u distract me sometimes" a
hankali ta ce "Ohk" tashi Rafi'ah tayi ta dauka hijab dinta tasa sannan ta dauki
laptop sai side bag dinta me dauke da biro da jotter, kama hannun Imaan tayi suka
wuce dakin Ummi, ta bude dakin a hankali suka shiga, Rafi'ah ta ce "Zamu tafi" Ummi
ta ce "Safe" ta dan yatsine fuska ta ce "To wa zai daukota?" Ummi ta juyo tana
kallanta ta ce "Idan kin gama mana, ko kwana zakiyi kina lectures din" silently ta
ce "To" daga haka ta juya, Imaan ta dagawa Ummi hannu ta ce "Bye bye Ummi" Ummi ta
sakar mata murmushi ta ce "Bye bye dear" bayan haka ta juya tabi bayan Rafi'ah.
Anty Amina da Anty Rahama ne zaune a tangamemen parlorn Ikleemah, sai washe baki
suke suna karewa gidan kallo, dan tinda akai auran basu zo ba kasancewar kasar waje
da mijinta ya dauketa suka tafi sai jiya suka dawo, da murmushi Ikleemah ta sakko
daga stairs ta rungume Anty Rahama, Anty Amina ta kwalalo ido ta ce "Hummm Ikleemah
kinga yadda kikai kyau" Anty Rahama ta ce "Gaskiya auran nan ya kar6eki, maza zauna
kusa dani, shekara daya fa kenan ban ganki ba" Ikleemah ta danyi murmushi ta ce
"Ammi nagode miki, kinga daga yin aikin nan yadda yake min kamar zai maidani ciki,
matarsa ma tana gidansu" Anty Rahama ta saki wani shewa ta ce "Aina gaya miki zama
daram zakiyi a gidan nan" Ikleemah ta danyi murmushi tana kallan Anty Amina ta ce
"Ina labarin Rafi'ah?" Anty Amina tayi kasa kasa da murya ta ce "Tana caan tana
galantoyin makaranta, yarinya dai girma take ga uban surutu, har yanzu kuma banji
ana maganar aure ba" Ikleemah ta ta6e baki ta ce "Haka dai zata zauna har karshen
rayuwarta" Anty Amina ta ce "Ba shakka kuwa".
Dai dai kofar gidan Mummy Mustapha yayi parking, Rafi'ah ta fito sannan ta
fito da Imaan suka shiga ciki, Ikram na zaune a balcony tana karatu, tana kallansu
ta wani hade rai ta dauke kai, itama Rafi'ah bata kalli inda take ba ta wuce, ba
kowa a parlorn suka wuce part din Mummy, tana zaune a parlor da wata kawarta suka
shiga da sallama, Imaan tayi gudu ta dale cinyar Mummy tana dariya ta ce "I missed
u Mummy" Mummy ta bata light kiss a forehead dinta ta ce "I missed u too Fatiti"
Rafi'ah ta zauna akan kujera tana kallan kawar Mummy ta ce "Ina wuni Umma" ta ce
"Lafiya kalau Fatima, ya Baby?" ta ce "Lafiyanta kalau" matar ta ce "Masha Allah
gashi ta girma Allah ya raya ta" ta ce "Ameen" mikewa tayi tana kallan Mummy ta ce
"Zan wuce Mummy" Mummy ta ce "Ohk, idan Jawad ya dawo sai ya kawota" ta ce "Ohk to,
dama yace yau zai dawo" bayan haka ta nufi kofar fita, Imaan ta daga mata hannu ta
ce "Bye Momma" a hankali itama ta daga mata ta ce "Bye sweetheart" daga haka ta
bude kofar ta fita.
Karfe 3 su Rafi'ah suka fito daga test, ta karasa inda taga Salma zaune ta ce "Kina
nan ashe" Salma ta ce "Ehh wallahi, ina jiran Nadiya ta kawomin handout dina taje
photocopy" Rafi'ah ta ce "Ohk" Salma ta ce "Ina Imaan?" Ta ce "Tana gida" Salma ta
danyi murmushi ta ce "Inasan kanwarkin nan Fatima, musamman idan tana magana, tafa
fiki kyau amma" Rafi'ah tayi shiru kawai tana murmushi, Salma ta yi picking call ta
koma gefe, bayan few minutes ta dawo tana kallan Rafi'ah ta ce "Fatima ko zamuyi
dropping dinki?" Ta girgiza kai tana murmushi ta ce "Mind not Salma, za'a zo
daukana" Salma ta ce "Alright sai gobe, ki gaishe da Imaan" ta ce "Ohk thanks",
bata wani jima awajen ba phone dinta ya fara ringing, tayi picking call din hade da
sallama, Jawad ya ce "Banganki ba" ta dan turo baki tayi hanging call din sannan ta
fito daga inda take, harta karaso kallanta yake with passion, ta bude front seat ta
shiga ta zauna, ya ce "Ya akai Madam?" Shagwa6e masa fuska tayi ta ce "Ka barni
inata shan rana" ya danyi murmushi ya ce "I'm sorry, ko gida banje ba yanzu nan na
shigo gari wallahi" ta ce "So ya aikin?" Ya ce "Fine, Allah ya soki ban kara kwana
ba" ta danyi dariyarta me kyau ta ce "Ba saina bika ba" ya ce "Ai zanso hakan, ina
Imaan?" Ta ce "Tana gidanku" ya ce "Keba gidanku bane kenan?" Ta ce "Gidanmu ne,
but amma ai gidanku zance" ya ce "U know what?" Ta ce "Saika fada" shiru yayi yana
kallanta, sai kuma ya ce "What if aka turani zua Cyprus, sai dai in anyi auran na
barki a nan?" Ta dan turo baki ta ce "Why" ya ce "Ur school, ai kin kusa gamawa,
dama da year 2 kike da sai mu tafi, but kinga semester daya ya rage maki after this
one" limshe idanuwanta tayi ta kwantar da kanta jikin kofa, gaba daya ji take kamar
zai gudu ya barta irin yadda Yusuf yayi, jin hawaye na kawowa a idanta tayi saurin
rife fuskarta da hijab din jikinta, Jawad yayi parking yana kallanta ya ce "Banfa
ce miki zan tafi ba, tinda basu ma fada ba" ya kamo hannunta cikin sanyin murya ya
ce "I will never leave u Fatima, banasan na daina kallanki even for some minutes, a
yanzu kin zama wani bangare na rayuwana, bazan iya barinki ba, u mean alot to me,
ina sanki so kuma bana wasa ba" Dago kanta tayi tana kallansa ta ce "I know, but i
can't forget my past Yaya, ko Imaan na kalla sometimes inajin ba dadi" ta karashe
maganar hawaye na sakkowa a idanta, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Mind not, dole ne
tinda shine mahaifinta wasu dabi'unta da abunuwan da zatai ya zama irin nasa, but i
beg u dan Allah for God sake, kiyi hakuri ki daina kuka, shima tinda ya manta dake
why won't u forget him too" ta dan harareshi ta ce "Ni cewa nayi ina tinashi ne" ya
ce "Ba gashi ba kullum kina kuka a kansa kusan shekara 4 kenan" ta turo baki ta
juya masa keya, ya ce "Yess, ki cireshi a rayuwarki duka duka, Imaan kuma i still
remain her Father, face ur future and forget ur past" a hankali ta ce "But how?" Ya
ce "Ki daina tinawa kin ta6a aure a rayuwarki mana, ki manta dashi" silently ta ce
"After i have a child with him" ya ce "Yes, it's possible, sai dai idan baki sa
kanki ba" ta ce "To" hannunsa yasa ya goge mata sauran hawayen idanta, ya bude
dashboard ya dauko tissue ya mika mata ya ce "Clean ur face" ta kar6a a sanyaye ta
fara goge idanta sannan yaja motar suka wuce.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_9_

Dai~dai bakin gate yayi parking ya juyo yana kallanta ya ce "U come down" ta dan
turo baki ta ce "Kai zaka budemin" Jawad yayi murmushi yana kallanta ya ce "An gama
Madam" daga haka ya fito ya zagayo ya bude mata ya ce "Ur wish is my command Baby"
fitowa tayi a motor tana dariya zata rife kofar ya ce "Wait! Bari na karasa ladana"
daga haka ya tura kofar motar ya rife, a tare suka jera suka shiga gidan, sai da
suka kusa balcony ta dan ja baya ya wuce gaba sannan tabi bayansa, ya murda kofar
parlorn ya shiga da sallama, Imaan najin muryarsa ta sauko a kan dinning da gudu ta
nufeshi, ya dagata sama yana dariya ya ce "Is this my Imaan?" Ta washe masa baki ta
ce "Yess Daddy, where have u been?" Ya bata light kiss ya ce "Momma bata ce miki
nayi tafiya ba?" Imaan ta girgiza kai tana kallan Rafi'ah dake zaune kan sofa tana
danna wayarta, Jawad ya juyo yana kallanta ya ce "Why Momma?" bata ko kalli inda
yake ba ta ce "Ai nima saida ka tafi ka kirani" fitowa Mummy tayi a kitchen tana
kallansu ta ce "Ha'a yana ganku tare?" Ya ce "Ita na fara daukowa, Ina wuni" ta ce
"Lafiya kalau, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulillah" daga haka ya daura Imaan akan
shoulder dinsa ya ce "Let me see Mami" ganin ya nufi part dinsu yasa Rafi'ah ta
tashi tabi bayansa a hankali, da sallama ya shiga parlorn yana kallan Ikraam dake
zaune tana kallo, ta mike zaune tana kallansu, sai kuma ta dan daure fuska ganin
Rafi'ah ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Sannu" zama yayi akan kujera yana
kallanta ganin taci gaba da canja channel ya ce "Ke" ta juyo tana kallansa, ya ce
"Did u great her?" dan turo baki tayi ta ce"Who?" Ya ce "Your Aunt" kanta ta maida
gefe kamar baza tai magana ba, sai kuma ta ce "Ina wuni" ba tare da Rafi'ah ta
kalleta ba ta ce "Same" Jawad ya ce "Let's go inside Fatima" Rafi'ah ta mike ta ce
"Ohk" daga haka tabi bayansa suka shiga bedroom din Mami. A tsaye take tana shirya
gogaggun kayanta cikin press, da sallama suka shigo dakin, ta amsa tana kallan
Jawad dake rike da Imaan ta ce "Har ka dawo?" Ya sauke Imaan a wuyansa ya ce "Ehh
wallahi, ina wuni Mami" ta ce "Lafiya kalau, ya hanya?" Ya zauna bakin gado ya ce
"Alhamdulillah" a kan carpet Rafi'ah ta zauna kanta a kasa ta ce "Ina yini Mami" ba
yabo ba fallasa Mami ta ce "Lafiya kalau, ya karatu?" silently ta ce "Lafiya kalau"
Mami ta kalli Jawad dake wasa da Imaan ta ce "Akwai abinci akan dinning" ya ce
"Thank u, but i want to take my bath first" daga haka ya mike ya nufi hanyar fita,
tashi Rafi'ah ma tayi ta ce "Sai anjima Mami" Mami ta ce "Mu jima da yawa" daga
haka suka fita a dakin. Suna fita Rafi'ah ta wuce part din Mummy, Jawad ya ajiye
Imaan ya ce "Follow ur Momma dear" ta tsaya tana kallansa kafin ta ce "Daddy are u
leaving?" Ya ce "No, i want to take my bath sweetheart" hannu ta mika masa suka
tafa sannan ta juya ta shiga parlorn Mummy, abinci Rafi'ah taci bayan tayi sallah
sannan ta kwanta akan sofa tana kallan cartoon din da Imaan ke kalla, tana nan
kwance har bacci ya fara daukanta, lokaci daya taji Imaan na bubbugata, ta bude ido
a hankali tana kallan Jawad dake tsaye a bayan kujera, ya daga mata gira daya ya ce
"Let's go" ta mike a hankali ta mayar da hijab dinta sannan ta shiga dakin Mummy, a
zaune ta sameta tana waya, sai data jira ta gama sannan ta ce "Mummy zamu wuce" ta
ce "Ohk daughter, sai yaushe kuma?" ta dan juya ido kafin ta ce "Exams zan fara ai
Mummy, duk sanda na gama" Mummy ta ce "Ohk Allah ya kaimu, kin yiwa Mami sallama
ne?" Ta girgiza kai ta ce "Yanzu dai" Mummy ta ce "Safe, ita wannan mai surutun
fita tayi bako sallama ko?" Rafi'ah ta danyi murmushi ta jawo mata kofa, dan tin
tini ta dale bayan Jawad sun fita, tana fitowa main parlor ta nufi part din Mami,
ta shiga a hankali hade da sallama, Mami ta dago tana kalleta ta ce "Baku wuce
bane?" A sanyaye ta ce "Ehh yanzu zamu tafi, mungode sai anjima" Mami ta ce "Allah
ya kiyaye" juyawa Rafi'ah tayi ta fita a part din sabida bata iya hada ido da Mami
yanzu, tin abubuwan da suka faru shekaru biyu baya da suka wuce wanda ya kai har
Abi ya saketa tayi kusan wata 9 a gida, dan tsaki Ikram tayi ta ce "Mami wai yanzu
kin hakura kenan Yayanmu ya auri wannan yarinyar?" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta
ce "Idan itace matarsa Allah ya sanya alkhairi Ikram, ni dai Allah na gani bana bin
boka, nama tsani duk matar da xata kai sunan wata ko wani wajen boka, kina gani
yadda na shiga jarabar rayuwa akan hana shi auranta, da kyar na samu nawa auran ya
gyaru, saboda haka babu ruwana addu'a kawai zan bisu dashi Allah ya sanya alkhairi,
na zagi 'yar mutane bansan ya nawa 'ya'yan zasu tashi ba, na mata sharri kala kala
duk dan na cimma burina amma daga karshe Allah bai yi ba, to menene ribata anan
Ikram? Allah ya yafe mana gaba daya kuskurene kam nayi shi, na tauyewa Jawad
hakkinsa da yawa a rayuwa, badan uwa uwa bace nasan da wuya ya yafemin, amma ko sau
daya bai ta6amin abinda zanji ba dadi ba, dan meyasa nima bazan so farincikinsa ba"
Mami ta share guntun hawayenta sakamakon tuno baya da tayi, dauke kai Ikram tayi
daga kallanta ranta a 6ace ta mike ta shige dakinta, Mami ta bita da harara ta ce
"Haryanzu ke yarinya ce Ikram zuwa gaba zaki gane komai, bana fata na cuci wani
yanzu balle watarana ya juyo kaina".
one thousand Imaan ta fito dashi a pocket din wandanta tana nunawa
Rafi'ah ta ce "Mami gave me this" Rafi'ah ta sauke kanta kasa ta ce "Kince kin
gode?" Ta ce "Yes, ko Daddy" Jawad ya shafa kanta ya ce "Exactly" kallan Rafi'ah
yayi data maida kanta gefe tana kallon titi ta window, a hankali ya ce "Dear" ta
juyo a sanyaye tana kallansa, ya ce "What's wrong with u?" Ta ce "Nothing" cigaba
yayi da driving lokaci lokaci yana kallanta ta gefen ido har sukaje gida, a waje
yayi parking ta juyo tana kallansa ta ce "Meyasa anan Barrister?" Ya ce "Kinsan na
tsani idan ba jimawa zanyi ba na shigar da mota" ta ce "Ohk" daga haka ta fito ta
tura gate ta shiga, dauko Imaan Jawad yayi a shoulder dinsa suka shigo, a baya suke
bin Rafi'ah har suka shigo parlor, ya ajiye Imaan sannan ya samu waje ya zauna a
kan lallausan carpet, fitowan Ummi kenan a parlorn Abba ta tsaya kallansu, saam
bata lura da jawad ba, sai da taji muryarsa yana gaisheta, ta saki murmishi ta ce
"Lafiya kalau, yaushe ka dawo" ya ce "Dazu, ya aiki" ta ce "Alhamdulilah" daga haka
ta koma parlorn Abba Imaan tabi bayanta, zama Rafi'ah tayi akan sofa tana kallansa
ta ce "Me zan kawo maka?" Ya danyi murmushi yana shafa kansa ya ce "You" ta dan
harareshi sannan ta mike zata wuce kitchen ya kamo hannunta, ta juyo a hankali tana
kallansa ya ce "Kinsan yanzu fa naci abinci, so i'm going" ta ce "Ohk Allah ya
kiyaye" ya ce "Ameen, zakije school gobe?" Ta daga masa kai ta ce "Probably, but u
know what Barrister?" Ya kafeta da ido ganin yadda take magana kamar bata sanyi, ya
ce "Kina da damuwa Rafi'ah, what's that thing u are thinking of? Tin dazu kike
behaving somehow, did anyone hurt u dear?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "Kaina ne
yake ciwo, and my chest too, yanzu zan sha magani na kwanta karna samu attack" a
hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ohk, Allah ya sauwake, ki huta sosai" ta ce
"Insha Allah, bye bye and i luv u" a hankali ya matsa kusa da ita tayi saurin sauke
kanta kasa, ya bata very light hug ya ce "I luv u too" daga haka ya sake hannunta,
daga masa hannu tayi ta ce "Allah ya kiyaye" ya ce "Ameen" sannan ya fita ya jawo
musu kofa ita kuma ta haura upstairs.
Kwance yake a wani daki babba ya kama kansa dake masa mungun ciwo,
dakin is well furnished, komai tsaf tsaf a inda yake, hannunsa na dama drip ne a
ajiki dayan hannunsa kuma yawo yake tsakanin kirjinsa da kansa, idan yayi minti 2
dafe da kansa sai kuma ya maida kirjinsa ya dafe, mungun zafi zuciyarsa ke masa,
gaba daya yayi mungun rama, sai haske daya kara sosai, idan ka kalleshi sau daya ba
zaka gane Yusuf bane at once, Anty Khadija ne da Jiddah akansa suna tsaye, bayan
'yan mintuna Anty Khadija ta fito a dakin ta wuce dakin da Umma take, tsaye ta
ganta tana ta faman dialing phone din Malaminta, tin jiya da suka dawo Nigeria take
ta trying number amma yaki shiga, Umma ta zauna bakin gado cike da damuwa ta ce
"Anya mutumin nan bai karya aikin nan ba Khadija? Ki duba fa kiga tin wata daya
baya Yusuf baya bin abinda nace masa sosai, yanzu gashi satinsa daya a kwance baya
magana sai juyi da yake" Anty Khadija ta karasa wajen Umma ta zauna ta ce "Ba
shakka ya karya asirin nan Umma, da bai karya ba taya za'ai Alhaji Usman ya sakeni
ya taho ya barni, sannan dama yace idan aka karya masa alkawari abin ba zaiyi kyau
ba" Umma ta ce "Toba dole a karya alkawari ba Khadija, taya da auranki zaice ki
dinga zuwa yayi lalata dake saboda asara ta mana yawa, anyi wanda akayi a baya amma
yanzu kam naga ya isa haka, bazaki kara bashi kanki ba" Cike da damuwa Anty Khadija
ta ce "Umma idan ba haka ba zai wargaza min duk wani shirina" Umma ta danyi
murmushi ta ce "Ai kudi yana aiki Khadija, yanzu tashi zakiyi, ki dauki driver ki
wuce Kano sannan kije kauyan nan ki sameshi, kudade kawai zaki bashi ya gyara
komai, kinga ba wanda yasan muna da gida a Kaduna, bayan sati daya idan Yusuf yaji
dama dama mu koma Egypt" Anty Khadija ta ce "Hakane Umma, shawara ce me kyau, yanzu
bari nayi wanka na shirya, tin jiya da mukai landing nake taya Jiddah daga Yusuf ko
wanka banyi ba gashi har kusan magrib" tana fadin haka ta wuce toilet, sai kuma ta
juyo ta ce "Umma to a ina zan kwana a kano? kinsan dai ko hauka nake baxanje gidan
mu ko gidan Yusuf ba?" Umma ta ce "Ai akwai hotels Khadija, ni dai fatana ki dace,
ko nawa ya bukata zamu bashi tinda mu ba matsiyata bane" Anty Khadija tayi murmushi
sannan ta shige toilet. A hankali Jiddah ta kamo hannun Yusuf dake saman kirjinsa,
ya bude idanuwansa da suka dawo jajir yana kallanta, kuka ta fashe dashi ta
rungumeshi ta ce "Pls talk Ya Yusuf, kusan sati daya baka magana dan Allah kace
wani abu ko zanji dadi" shi dai kallanta kawai yake yana kwance, ta mike kamar
mahaukaciya ta daga masa labule ta ce "Ka gani Yaya, jiya muka dawo Nigeria saboda
condition dinka, kuma Umma taki bari a kaika asibiti sai dai a kira Doctor ya duba
ka, ka gani Yaya nan Kaduna ne, mun dawo kasar mu" limshe idanuwansa yayi kamar
yadda suke dazun, Jiddah ta fashe da kuka ta kara hawa gadon ta rungumeshi sosai ta
ce "Nice Jiddan kafa Doctor, nice wacce kake cewa kullum kana sona tin tafiyarmu
Egypt, ka manta bakaso kayi nisa dani? dan Allah kayi magana Habibina" bakinshi ya
kai saitin kunnenta, har lokacin idanuwansa a limshe suke, ya dora dayan hannunsa
da kyar a bayanta, da kyar muryarsa ke fita ya ce "Are u with me Rafi'ah?" Jiddah
ta zabura ta mike tana zaro ido, sai kuma ta kwala ihu tana kiran Umma ta ce "Na
shiga 3, ya tina ta wallahi Umma, ba Jiddah yace ba wallahi" Umma tayi kansa da
sauri tana kallansa, kamar ba shi yayi magana ba, idanuwansa a limshe sai numfashi
da yake saukewa daki~daki, number Doctor din daya dubashi daxu Umma ta fara kira,
bayan ya dauka ta sanar masa ya tashi yace ga shi nan zuwa, Umma tayi hanging call
din ta dago Jiddah zuwa jikinta ta ce "Kiyi shiru, Khadija na komawa komai zai
daidaita Jiddah, yanzu haka shiryawa take kinji" muryarsa suka sakeji a hankali ya
ce "Fatima" Jiddah ta kara sakin kuka ta ce "Yau na shiga 3 Umma dame zanji, da
rashin lafiyarsa koda sunan waccen yarinyar daya ke kira"

*The page is dedicated to the members of groups, i love u so much sisters, i


appreciate ur comments love and support 🤗*

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_10_

A hankali ya kamo duvet din kan gadon yana kokarin tashi amma ya kasa, hakan yasa
ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, mikewa Jiddah tayi ta hau kan gadon
tana kallan idanuwansa dake limshe kamar dazun, ta kai fuskarta kan nasa tana kuka
kasa kasa, Umma ta mike ta koma dakinta inda ta samu Anty Khadija ta shirya da
babban hijab dinta tasa nikab, Umma ta bata ATM card ta ce "Take care, kar ki sauka
a hotel din dake kusa" Anty Khadija ta ce "To Umma, saina dawo" Umma ta ce "A dawo
lafiya" daga haka Anty Khadija ta fita a dakin. Shiru Jiddah tayi tana sauraron
yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri, ta mike a jikinsa ta sauka akan gadon da sauri
tana kiran Umma, a bakin kofa suka ci karo, Jiddah ta rungume Umma ta ce "Na shiga
uku Umma Yaya mutuwa zaiyi ya barni" kama hannunta Umma tayi suka koma dakinta ta
zaunarta a bakin gado ta ce "Kinga yanzu na kira Dr kiyi shiru ki daina kuka zai
samu sauki" Jiddah ta share hawayen idanta ta ce "To Umma yanzu idan yace ina
Rafi'ah mai zamu ce masa, kinsan fa lokaci daya komai zai sake shi, i'm sure asirin
ya bar jikinsa by now, kawai ciwansa ne ya tashi" Umma ta kamo hannunta ta ce
"Asiri kam ya bar jikinsa amma Khadija ta koma ai, kuma bai manta da abinda suka
faru a baya ba, yana sane da komai sai dai baisan meyasa yayi hakan ba, Allah na
tuba da baya tuna komai ai sunanta ma bazai kira ba" Jiddah dake zare ido ta dan
kalli Umma ta ce "To idan ya tambaya fa?" Umma ta ce "Barmin amsar a wajena" mikewa
duk sukai jin ana knocking, Umma ta bude kofar parlorn tana kallan DR dake tsaye ta
ce "Bismillah" ya shigo da sallama yana kallan Jiddah da idanuwanta sukai jaa suka
kumbura, Umma ta ce "Ka shigo nan dakin" Dr ya bai bayanta zuwa dakin da Yusuf ke
kwance, bayan ya duba shi sosai ya masa allurai sannan ya cire masa drip din da
karewarsa kenan ya ce "Zai samu bacci na awa daya sai ya tashi, and i'm sure he
will wake up fine" Umma ta ce "Ba wani matsala kenan?" Ya ce "Insha Allah, tinda
anyi allura gobe da safe zan kawo magungunan da zai fara sha" Umma ta ce "Nagode
sosai Dr, zan maka transfer yanzu nan" ya ce "Nine da godiya Hajiya" daga haka ya
kalli Jiddah dake zaune gefen Yusuf ya ce "Madam Allah ya sauwake" kamar batasan
magana ta amsa da Ameen, daga haka ya fita a dakin ya wuce. Rafi'a ce kwance akan
sallayan data idar da sallan magrib, jin an bude kofar yasa ta mike a hankali, Ummi
ta zauna bakin gado tana kallanta ta ce "Rafi'ah" a hankali ta ce "Na'am" Ummi ta
ce "Kan naki bai daina ciwo bane?" Ta girgiza kai ta ce "Ya daina yanzu" Ummi ta ce
"Toh Alhamdulilah u come down for dinner" ta ce "Toh" daga haka Ummi ta fita a
dakin, kifa kanta tayi akan gado ta limshe ido, saam batajin dadin jikinta musamman
yadda zuciyarta ke bugawa, mikewa tayi a hankali ta cire hijab din jikinta tasa
hula sannan ta dauka phone dinta ta fita a dakin, kallan Imaan take dake zaune
saman kujera tana bawa Ummi labarin Daddynta, Rafi'ah ta limshe ido ta wuce dinning
ta zauna, Imaan ta sakko akan kujeran ta nufeta ta ce "My Daddy loves me so much ko
Mom?" Rafi'ah ta dan kalleta bata ce komai ba, yarinyar ta dan hade gira tana
kallanta ta ce"We just make call with Uncle Abdul, and shine yace wai Daddy baya
sona wai shine yake sona, Daddy used to kiss and hug me, he bought ice cream for
me, pizza and shawarma, he sometimes drop me to school or he picked me, Daddy loves
me much ko Momma" daga mata kai Rafi'ah tayi ta share guntun hawayenta daya gangaro
fuskarta, Imaan ta dan zaro ido ta ce "Are u crying Mom?" Girgiza mata kai tayi ta
ce "No, something just enter my eye now" da damuwa Imaan ta rungumeta ta ce "Sorry,
is it painful?" Ta girgiza kai ta ce "No, go and sit down" Imaan ta ce "I want to
eat with u" Rafi'ah ta danyi murmushi ta daurata akan cinyarta ta ce "Alright dear"
har suka gama cin abincin Imaan bata sake magana ba, saboda kullum Ummi na hanata
magana idan tana cin abinci, sakkowa tayi akan cinya tana kallan Ummi ta ce "Ummi
Momma didn't well" Ummi ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, kan kujera Ummi ta
nunawa Imaan ta ce "U sleep there" Imaan ta hau kan kujeran ta kwanta, bata fi
minti 10 ba tayi bacci, Ummi ta mike tana kallan Rafi'ah data kifa kanta akan
dinning ta ce "Fatima" dagowa tayi tana kallan Ummi dake kokarin zama a kujeran
dake gefenta, sauke kanta tayi kasa tana wasa da botton din doguwar rigarta, Ummi
ta ce "Are u with me Rafi'ah?" Ta daga mata kai a hankali, Ummi ta ce "Duk wannan
tinanin da kike ba shine mafita a gareki ba, sau nawa zance miki ki dinga addu'a ki
manta da komai daya faru a baya, shekara 4 fa ba sati 4 bane, bazaki godewa Allah
ki kar6i kaddararki a haka ba?" A hankali tayi wiping tears dinta ta ce "Na hakura
Ummina, na kuma gode masa a haka, but ni Imaan used to makes me cry, musamman idan
na tuna ba Ya Jawad bane mahaifinta, taya zanyi watarana na gaya mata haka Ummi"
daga haka ta fashe da kuka, Cike da tausayinta Ummi ta ce "Shiyasa nace miki kowa
da nasa kaddaran, ita nata a yadda yaxo kenan" Rafi'ah ta share idanta ta mike ta
koma parlor zata daga Imaan Ummi ta ce "Ina zaki kaita?" Kanta na kasa ta ce "I
want to spend the night with her" Ummi ta ce "To kisa tayi fitsari, sai ki
shiryata" a hankali ta ce "Toh" daga haka ta wuce upstairs Ummi ta bita da kallo, a
dakinta ta kwantar da Imaan saman gado sannan ta wuce dakin Ummi inda kayanta suke
ta dauko mata kayan bacci da sucks da hula, rigarta ta fara cire mata sannan ta
dagata suka shiga toilet, bayan few minutes suka fito ta saka mata kaya da socks
tasa mata hula sannan ta kwantar da ita, cikin bacci ta ce "Ummi" Rafi'ah ta matsa
gefenta tana shafa bayanta ta ce "It's me dear, do u need something" a hankali ta
bude idanta tana kallan Rafi'ah ta ce "Dake zan kwanta?" Rafi'ah ta daga mata kai
ta ce "Yes dear, is better u sleep with ur Mom, sai ki barmin Ummina ta huta" Imaan
ta rungumeta ta ce "I love u momma" Rafi'ah na shafa bayanta ta ce "What do u
want?" Ta ce "Water" kwantar da ita tayi sannan ta mike ta dauko ruwa ta tsiyaya
mata sannan ta bata a baki ta sha, bayan ta ajiye cup din ta ce "Ki kwanta, zanyi
sallan Isha" Imaan ta dan turo baki ta ce "That's not how Ummi used to makes me
sleep" Rafi'ah dake kallanta ta ce "What do u want then?" Ta ce "She used to hug me
nd we said a du'ah together" jawota tayi jikinta ta rungumeta sannan sukai
addu'ah, suna a haka har tayi bacci sannan Rafi'ah ta zame jikinta a hankali ta
sauka saman gadon ta shiga toilet.
A hankali Yusuf ya bude idanuwansa saboda hasken wutan dake dakin, ya
mike gently yana dafe da kirjinsa ya zauna, bin dakin ya dingayi da kallo ganin
akwatinansu duk a tsakar dakin, mikewa yayi a hankali ya zura hannayensa cikin
pocket ya tsaya bakin kofa, jin an bude toilet yasa ya juya da sauri suka ido hudu
da Jiddah, ta sakar masa murmushi ta ce "How are u?" Silently ya ce "Fine?" Komawa
yayi ya zauna a bakin gadon dan jiri yakeji kawai karfin hali yake, Jiddah ta zauna
gefenshi ta rungumeshi tana murmushi, taji dadin ganin ya tashi kuma jikin da
sauki, a sanyaye taji muryarsa ya ce "Sallah nawa nayi missing" ta dago tana
kallansa ta ce "Tin dai na asuba da kayi shine jikinka yayi tsanani" ya dan kalleta
ya ce "Wanda nayi a jirgi fa?" Ta ce "Isha na jiya kayi fa" ya sauke ajiyar zuciya
ya mike ya shiga toilet ta bishi da kallo, bayan few minutes ya fito ya shimfida
sallaya ya tada sallah. Bayan ya rama duk sallolinsa yayi addu'a sannan ya mike,
Jidda ta ce "In kawo maka abinci?" Ya ce "No" daga haka ta fita a dakin, a parlor
ya samu Umma tana zaune, ya karasa gefenta ya zauna yana kama kansa ya ce "Umma" ta
dago tana kallansa ta ce "Ya jikin?" Ya ce "Da sauki, is it true that na saki
Rafi'ah?" Umma ta kafeshi ta ce "Ni kake tambaya ne kowa?" Ya zuba mata jajayen
idanuwansa a takaice ya ce "Eh" ta ce "Shekararka nawa a Egypt?" Ya ce "Almost 4"
Umma ta ce "To shekarun sakinta kenan" a hankali ya ce "Subhanallah, Umma mai tamin
haka na saketa Umma, inasan matana wallahi" Umma ta ce "Kai zan tambaya wannan
kuma" shiru yayi yana kallan Umma da itama shi take kalla, caan ya sake furta
innalillahi kafin ya ce "Ni bansan me tamin ba, nasan dai by that time na tsaneta
fiye da kowa, and i remembered when i divorced her, she's lying down on the floor
and she's vomiting then, yes i remembered she was sick, but what comes over me?"
Umma ta ta6e baki tana kallan Jiddah dake tsaye bakin kofa ta ce "Amma meyasa baka
nemeta ba har tsawon wannan lokacin?" Ya ce "I don't know, nina manta da ita cikin
rayuwa na Umma, all i know is ina tare dake da Jiddah da kuma khadija and nasan mun
koma Egypt where i continue working with them with the help of ur classmate Alhaji
Sunusi, after then rayuwana kawai nasa a gaba, ban ta6a tinata ba sai sau, Umma
meyasa baku yi komai a kai ba kuka barni na saketa" Umma ta ce "To kace baka santa
zan maka dole ne Yusuf?" Kama kansa yayi ya kara furta innalillahi wa
inna~ilaihirraji'un, ya dago yana kallan Umma ya ce "Kenan shekara 4 tana gida?
All i can remember is lokacin da muka je gidansu ziyara, i think she was 2 weeks in
my house then, amma Umma ni bayan nan na manta ta a rayuwana ne" mikewa yayi kamar
zaiyi hauka ya ce "Why Umma, muna zuwa Kaduna once in a year amma kuma baki ta6a
tinamin ita ba, ban manta da kowa ba sai ita Umma, why? Meyasa haka ya faru dani
ne?" Umma ta mike ta ce "Ni ina zan sani Yusuf, tinda ka saki yarinyar nan kana abu
kamar kowa amma baka sake tambayarta ba, to zan maka dole saika dawo da ita ne"
kifa kansa yayi akan dinning yana karanto addu'o'i ko zai samu saukin abinda
yakeji, har yanzu he's so surprise da abinda ya faru da shi, duk yadda yake saan
matarshi amma ya manta ta lokaci daya, shekara 4 bai sake maganarta ba sai yau, da
karfi ya ce "Noo, it's impossible, i dont know what comes over me 4 years back"
daga haka ya wuce daki da sauri yana kallan Jiddah ya ce "Where is my key?" Sai
xare ido ta ke ta ce "Yanzu fa past 9pm kuma a Egypt kake da mota ba anan..." Wani
mungun tsaki yaja ya wuceta ya fice a dakin ta biyo bayansa, lokaci daya yaji
zuciyarsa ta buga, ya danne kirjinsa da hannunsa na dama yana furta subhanallah,
anan wajen ya xu6e sumamme, Jiddah ta kwala ihu tana kiran Umma, da sauri Umma ta
fito a daki ta ce "Faduwa yayi?" Cikin kuka Jiddah ta ce "Umma ya samu attack me
tsanani, pls do help Umma, mu kaisa asibiti karya mutu, nima wallahi mutuwa zanyi,
ganin Umma ta tashi ta shiga daki Jiddah ta mike ta fita a parlorn, dayan apartment
din gefensu ta nufa, dayake dama gidan haya ne ta fara musu knocking kamar zata
balla kofar. Anty Khadija na daga wayar Umma ta ce "Kin isa ne?" Ta ce "A'a Umma,
sai gobe zan karasa ina cikin Kano a hotel" Umma ta ce "To da asuba zaki fita, ya
tashi yana tambayar meyasa aka barshi ya saketa, yanzu dai ya samu attack ya sume
gashi caan parlor, ki lalla6ashi ya gyara mana aikin nan Khadija, ki bashi ko nawa
ya bukata" Anty Khadija ta ce "Toh Umma" daga haka tayi hanging call din.
Koda Umma ta fito parlor neighbor dinsu harya sa Yusuf a mota, ta zura
hijabi ta kullo kofar ta shiga motar suka tafi, wani nearest private hospital suka
kaishi inda cikin gaggawa aka karbeshi. kusan awa daya su Umma na reception a zaune
sannan akai kiransu, Jiddah banda kuka ba abinda take, Dr ya musu bayanin komai,
cewar su kwantar da hankalinsu, amma anyi admitting dinsu zuwa gobe, daga haka ya
wuce office dinsa, Umma ta shiga dakin da yake Jiddah tabi bayanta, yana nan kwance
akan gadon idanuwansa a limshe, neighbor dinsu na kansa yana masa sannu, Jiddah ta
kamo hannunsa cikin kuka ta ce " Karka maida abinda yake cikina maraya tin baizo
duniya ba, dan Allah ka tashi Yaya, idan ka barni nima mutuwa zanyi" Umma ta kama
hannunta suka fita a dakin ta ce "Ki daina kuka haka mana Jiddah, ko mutuwa yayi
munada asara ne bayan duk dukiyarsa na hannunmu, da zarar Khadija ta dawo zai sake
mance ta kuci gaba da rayuwarku" Jiddah dake kallan Umma ta kara share hawayen
idanta cikin fishi ta ce "Eh ai saboda bake kika haifeshi ba zakice ya mutu, sannan
bake kike dauke da cikinsa ba shiyasa xaki ce ya mutu, to wallahi Yaya ba zai mutu
ba idan kuma ya mutu kema bazaki zauna lafiya ba saina tona miki asiri na gayawa
duniya kece sanadiyyar mutuwar sa" Umma dake kallanta surprisingly ta ce "Jiddah ni
kike dagawa murya haka? Ni zaki kalla kina nunawa da yatsa" cikin 6acin rai ta ce
"An nunaki da yatsan nima ki kasheni ki huta, wallahi idan ba tashi yayi ba bazan
yafe miki ba, duk kece silar abubuwan da suka faru" wanka mata mari Umma tayi,
jiddah ta durkusa tana dafe da kuncinta ta ce "Ni kika mara?" Umma ta kara wanka
mata wani marin ta ce "Gobe ki dinga dagamin murya kina nunani da..." Kafin ta rufe
bakinta Jiddah ta wanka mata mari ta ce "Wallahi baki isa ki mareni ban rama ba"

_08103810398_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_11_

Washegari misalin karfe 10 Yusuf ya tashi, ya bude idanuwansa da suka masa nauyi
yana bin dakin da kallo, Jiddah da fitowanta a toilet kenan ta nufeshi tana fadin
"How are u feeling now?" Silently ya ce "Fine, naji sauki" ta ce "Allah ya sauwake"
kokarin tashi yake ta taimaka masa ya zauna, ya kalli idanuwanta da suka kumbura ya
ce "Where is Umma and Khadija?" Ta dan hade rai ta ce "Umma went back home, Anty
Khadija kuma tayi tafiya" ya limshe idanuwansa ya ce "Ohk" mikewa Jiddah tayi ta
fita a dakin tana tino maganganun Umma kafin ta koma gida, dan cewa tayi idan Yusuf
ya tashi sai ya sake ta, tana isa corridor ta hadu da matar neighbors dinsu da
basket a hannunta, Jiddah ta danyi murmushi ta ce "Sannu da zuwa" matar ta ce
"Sannu, ya mai jiki?" Jiddah ta ce "Da sauki, bismillah" daga haka ta juya matar
tabi ta a baya, suna shiga dakin Yusuf ya bude idansa yana kallansu, matar ta ajiye
basket a gefen gadon ta ce "Ina kwana" Yusuf ya ce "Lafiya kalau" ta ce "Ya karfin
jiki kuma?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Allah ya kara sauki" ya ce "Ameen" kallan
Jiddah tayi dake tsaye gefe ta ce "Zan wuce Allah ya sauwake" ta mike tana murmushi
ta ce "Mungode, ayima baban Mu'azzam godiya" ta ce "Ba komai, Allah ya kara sauki,
yaje aiki ne shiyasa bai shigo da safe ba" daga haka ta fita a dakin. Jiddah ta
zauna gefensa ta ce "In zuba maka abincin?" Ya girgiza kai a takaice ya ce "No"
bude kofar dakin akai wani likita ya shigo, ya kalli Yusuf dake zaune ya ce "Ya
jikin?" Yusuf ya ce "Naji sauki, i hope u will discharge me today" Dr ya danyi
murmushi ya ce "Idan munga ba matsala ba" Yusuf ya ce "There's not insha Allah" Dr
ya ce "Allah yasa, but i'm giving u injection now" Jiddah ta dan kalleshi ta ce
"But he didn't eat anything yet" ya ce "Ohk, idan yaci u let me know" ta ce "Toh
shikkenan" Dr na fita Yusuf ya kalleta ya ce "How is ur own body?" Ta ce "Naji
sauki, kawai banasan kamshin stew ne" ya limshe idanuwansa baice komai ba, ta sakko
a hankali ta diba masa fatan dankali da kifi, ta zuba masa tea a mug sannan ta koma
kan gadon, Yusuf ya girgiza kai ya ce "Tea kawai zan sha" mika masa mug din tayi ya
kar6a ya rike a hannu, every minutes daya wuce daga tashinsa zuwa yanzu Rafi'ah
kawai yake tinawa lokacin daya bata papern sakinta, yana tinawa by that time tana
kwance cikin amai fuskarta da hawaye. Ta6a shi da Jiddah tayi ne yasa ya dawo
hayyacinsa, ta ce "What are u thinking?" Ya ajiye mug din akan stool din dake
gefensa ya ce "My wife" Jiddah ta dan kalleshi ta ce "Ni kenan" ya girgiza kai ya
ce "Fatima na, ina tinanin da ciki na saketa, idan kuma ba ciki bane she was sick
then" mikewa Jiddah tayi tana masa wani kallo ta koma kan kujera ta zauna ta wani
hade rai, limshe idanuwansa ya sake yi inda hawayen dake makale a idansa suka
gangaro, bude idanuwan yayi ya share hawayen ya dauki mug din ya fara shan tea din
daya ke jinsa kamar gauta tsabar daci, ba dan alluran da za'a mishi ba da babu
abinda zai sha, dan dai yasan akwai matsala ne idan akai baici komai ba, bayan five
minutes ya sha half, ya ajiye mug din yana kallan Jiddah ya ce "Let him come" tashi
tayi ba tare data kalleshi ba ta fita a dakin. Ba jimawa suka dawo tare da Dr, ya
masa alluran sannan ya bashi drugs dinsa, bayan 30 minutes ya mike yana kallan
Jiddah ya ce "An biya bill din?" Ta ce "Ehh" daga haka ya ce "We are going" ta
tsaya tana kallansa ta ce "Ba suyi discharging dinmu bafa?" bai ko kalli inda take
ba ya fita a dakin, ta mike tabi bayansa taga ya shiga office, ita dai a bakin
kofar ta tsaya, bayan few minutes ya fito ta dori a bayansa suka fita a clinic din.
Rafi'ah ce zaune a school dinsu tana jiran Jawad, sai bin mutanen dake
wajen take da kallo, jin horn a bayanta yasa ta juya da sauri, ya sakar mata
murmushi ya fito a motar yana kallanta, a hankali ta karasa inda yake tsaye ta ce
"Yau dai kazo da wuri" yayi murmushinsa mai kyau ya bude mata front seat ya ce
"Gudowa nayi a wajen aiki, kinga idan aka tashi kamani sai a hada harda ke" ta
danyi dariya ta shiga motor ya rife, bayan ya zagayo yayi wa motar key yana
kallanta ya ce "Yau kin gama da wuri" ta ce "Ai yau lectures daya mukai 8-10" ya ce
"Good, ina Babynah?" Ta ce "Tana gida" ya ce "I missed her, jiya har mafarkinta
nayi" ta ce "I see, yau kuma inaga kaida ka ganta sai dai da daddare idan kazo" ya
ce "Why?" Ta ce "Khairiyya ta kirani zata zo, kuma nasan yini zamuyi" ya ce "Ohk,
tinda aka bani ke dai wancen yayan nata ya daina daminki ko?" Ta danyi murmushi ta
ce "Sure, sai dai ya kira mu gaisa, ba sosai yake zuwa ba" Jawad ya ce "Better, na
tura miki abu ta Whatsapp idan kinje gida sai ki duba" ta ce "What's that thing?"
Ya ce "U will see" ta sake murmushi kawai, kamo hannunta yayi cikin cool voice ya
ce "I still don't know how much i luv u Rafi'ah, i face so much problems just
because of u, har banaso na tuna abubuwan da suka faru two years back" a hankali ta
ce "I also, but gashi amma ya wuce ba" ya ce "Sure ya wuce, shiyasa kullum nake ce
miki ki dinga mantawa da abinda ya faru, just face ur future" ta ce "Insha Allah"
har ya sauketa a gida hirarsu suke abin shawa'a, bayan ta sauka ya ce "Baki ce min
abin ba yau" ta boye fuskarta kasa~kasa ta ce "I luv u so much" ya ce "I luv u too"
juyawa tayi da sauri ta bude gate, ta dan juyo ta daga masa hannu sannan ta shige
ciki.
Cikin gaggawa Umma ta dauki karamar trolley tasa kayanta dana Anty Khadija, sai
zufa take ta rufe akwatin, tinda aka kira daga police station hankalinta ya bar
jikinta, ganin an sake kira ta daga wayar hankali tashe ta ce "Dan Allah Yallaboi
ka bata muyi magana" DPO ya mikawa Anty Khdija wayar, cikin muryar kuka ta ce "Umma
Alhaji Usman ya ganni yasa an kamani, yasa aka min duka sannan yace saina biyashi
duk abinda ya min, Umma dan Allah kizo kar su kasheni maganarsa sukeji kamar shiya
haife..." tsawar da wani dan sanda ya daka mata ne yasa tayi shiru, DPO ya kar6i
wayar yayi hanging call din yana kallan Alhaji Usman ya ce "Insha Allah Alhaji zamu
yi hukunci dai dai yadda ya kamata, dama mun jima muna neman irinsu" Matar Alhaji
Usman dake tsaye a gefe ta wankawa Anty Khadija mari cikin kuka ta ce "Ta Allah ba
taki ba makirar mata kawai, da Allah ya fiku sai gashi rana daya Abban Muhammad ya
dawo, shekara kusan 4 bamu san inda yake ba, wallahi badan badan banzan iya shirka
ba da nima naje wajen boka an rabaki da kowa naki, kin wulakanta a duniya" da sauri
Alhaji Usman ya ce "Haba Hindatu, ya kike magana kamar baki da ilimi ne?" Ta ce
"Aikin asirine wallahi, kuma muna nan da kai saita fada da bakinta, inba asiriba ya
za'ai shekara 4 bakasan inda muke ba kake zama hankali kwance, wallahi baxan ta6a
yafe miki ba saina tozarta ki an yadaki a media tsinuwar mutane ta biki" Alhaji
Usman ya kama hannun matarsa suka koma gefe ya ce "Haba Hajiya, ba girmanki bane
kamar ni matata ta dinga fadan irin wannan kalaman" hawayen idanta ta goge ta ce
"Alhaji bakasan halin da muka shiga ba na rashinka, 'yayana dani kaina ba wanda ya
sake jin dadin rayuwa sai wancen satin daka dawo, yanzu kuma Allah ya hadani da ita
bazan ci ubanta ba, meyasa zakace in kyaleta" ya ce "Calm down pls, a hankali
zamubi komai" daga haka ya dawo yana kallan DPO ya ce "A sata cell, idan
mahaifiyarta tazo a kirani" DPO ya ce "An gama sir" daga haka ya tasa keyarta gaba,
sai kuka take tana ta shiga 3.
Umma bata fi minti 5 da fita a gidan ba su Yusuf suka iso, karfin hali kawai yake
amma shiyasan abinda yakeji, Jiddah ce ta biya me taxi din sannan tabi bayansa suka
shiga gidan, suna shiga parlor Yusuf ya dauka trolley dinsa ya fito, Jiddah ta
tsaya kallansa ta ce "Where are u going Yaya?" A takaice ya ce "Kano" ta ajiye
basket din hannunta ta ce "Nima ai binka zanyi" daga haka itama ta fito da trolley
dinta, da sauri ta shiga kitchen ta wankewa Maman Mu'azzam warmers dinta da flask
sannan ta fito ta kai mata ta musu sallama, har bakin kofa Maman Mu'azzam ta rakota
sannan ta juya, Yusuf ya duba pockets dinsa ko zai samu kudi amma babu, ya kalli
Jidda da shigowanta kenan parlorn ya ce "My ATM cards" ta ce "Duk suna wajen Umma,
kuma da alama bata gidan dan ba dayan akwatin" ya ce "Akwai kudi a hannunki?" Ta ce
"Ehh akwai 5 thousand, nasan zai kaimu Kano" ya ce "To saiki fito" daga haka yaja
trolley dinsa ya fita a parlorn itama tabi bayansa da nata, a bakin titi suka hau
cab ya wuce dasu park.
Rafi'ah na zaune dakinta Imaan ta shigo da gudu, ta dago da sauri tana kallanta ta
ce "Do u want to fall down Imaan?" Ta ce "No Momma, i just want to check if u are
at home, banasan ki sake fita ki barni" murmushi Rafi'ah tayi tana kallan cute
girl dinta ta ce "Ai bance maki fita zanyi ba so u feel free" Imaan ta juya ta fita
a dakin ta ce "Bye Momma" Rafi'ah ta daga mata hannu ta ce "Bye" jawo phone dinta
tayi ta shiga Whatsapp, bayan messages sun gama shigowa ta bude na Jawad wanda
shine second to the last, pictures taga ya turo guda 8 sai a karshe ya rubuta "You
choose two sets" bayan sun gama budewa ta kurawa akwatinan ido, duk cikinsu ba
wanda bai mata ba, sunyi kyau sosai different design and color ko wanne guda 6, ta
danyi murmushi ta fita a whatsapp din sannan tayi dialing phone dinsa, cikin cool
voice dinsa ya ce "Wife" ta sauke kanta kasa kaman yana gabanta ta ce "I saw them,
sunyi kyau duka" ya ce "Alright you resend me the one u choose, Anty Jamila zata
dawo next week so ita zata taho dasu" Rafi'ah ta ce "Ohk to, Allah ya dawo da ita
lpy" ya ce "Ameen, za muyi zama a court i will call u ltr" a hankali ta ce "Ayi
adalci barrister" ya ce "Insha Allah Fatima na" ta sake yin murmushi ta ce "Alright
then sai anjima" ya ce "Bye" daga haka tayi hanging call din, tana ajiye phone din
Khairiyya ta shigo da Imaan a hannunta, Rafi'ah ta dan zaro ido tana murmushi ta ce
"Graduate" Khairiyya ta sauke Imaan tana dariya ta ce "Ina wuni Anty Fatima"
Rafi'ah ta ce "Lafiya kalau, kun gama Neco ko?" Ta ce "Ehh Anty" Rafi'ah ta ce "All
d best" Khairiyya ta kama hannun Imaan ta ce "U are following me to our house ko
Imaan, Ammi nata nemanki" Imaan ta ce "Noo, i won't leave my Momma" Khairiyya ta ce
"U must, baki ta6a kwana mana ba" Imaan ta hau damfe tana buga kafa ta ce "I won't
follow u"

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_12_

Karfe 1 da 'yan mintuna su Yusuf suka iso Kano, bayan an fitar musu da kayansu ya
tare napeep a cikin park din, kamar bayasan yin magana ya ce "Sharada" mai taxi din
ya ce "To bismillah Alhaji" Yusuf ya bude back seat ya shiga, Jiddah dake tsaye a
gefe ta ce "Malam ga kaya fa" mai taxi din ya fito ya dauki trolley dinsu yasa a
boot, sannan ya dawo ya kunna motar, kallan Yusuf tayi daya jingina da kujera ya
limshe ido, tinda suka taso a Kaduna ko magana ba suyi ba har yanzu, ta danja tsaki
a hankali ta dauke idanta a kansa, tafiyar minti 10 sukayi suka iso dai~dai gate
din gidansa, bayan anyi parking Jiddah ta dan kalleshi ganin ya bude ido, bude
motar yayi ya fito ya tura gate din yaji a rufe, ya juyo yana kallan Jiddah a
takaice ya ce "Key?" Ta bude hannayenta alaman itama bata sani ba, Yusuf ya sauke
ajiyar zuciya ya kara juyawa yana kallan padlock din dake jikin kofar, mai taxi din
ya kalleshi ya ce "Yallaboi ko ana bukatar taimako?" Yusuf ya ce "Makulli nakeso
wanda zai bude wannan kwadon" mai taxi din ya ce "To bari na kar6o a nan bakin
titi" Yusuf ya kalli Jiddah dake tsaye tayi folding hannayenta ya ce "Ki bashi
kudi" ta ciro 1k ta mikawa mai taxi din, mota ya koma ya kunna yana kallan Yusuf ya
ce "Saina dawo" daga haka ya wuce, Jiddah ta juyo tana kallansa ta ce "What if he
run away?" Yusuf ya kafeta da ido bai dai ce komai ba, kamar daga sam taji ya ce
"Kansa yayi wa" ta juyo tana kallansa amma sai yayi kamar ba shi yayi maganar ba.
Sun kusan minti 7 sai gashi ya dawo da key har iri buyu, ya fito yana kallan Yusuf
ya ce "A cikin daya zamu dace insha Allah, hala kun manta naku makullin ne" Yusuf
ya ce "Ehh" ana gwada na farko kuwa padlock din ya bude, Yusuf ya dan kalli Jiddah
ya ce "Give him another 1k" daga haka ya kalli mutumin ya ce "Nagode" yaja trolley
dinsa ya shiga ciki bayan mutumin yayi masa godiya, kamar bayasan taka kasa ya nufi
entrance din gidan, ga wani jiri dake shirin dibarsa, shi dai kawai tafiya yake,
tin daga tsakar gidan zaka gane anyi shekaru ba mutane a gidan, saboda duk datti ne
ta ko ina, ga ganyen flowers din gidan da suka bushe sun zubo kasa. Yana murda
handle din kofar parlor yaji a bude, ya bude ya shiga yana karewa parlorn kallo, ta
ko ina kurane tin daga kan kujerunsa TV stand, TV, center table da kuma tiles din,
ya nufi part din Rafi'ah ya samu ba komai aciki, sai kura a kasan tiles din, ya
karasa dakunan ma ya leka, ko labule babu a ciki, hannunsa yasa ya share hawayen
daya gangaro a idansa, ya tabbata kenan dai ya saki Rafi'ah kamar yadda yake
tinawa, ya cije lips dinsa still hawaye na sakko masa ya fita a part din ya bude na
Jiddah, itakam komai nata yana nan yadda suka barshi, wani abin ma kura ta
lullubeshi, ya juya ya fito a hankali kamar bayasan taka kasa, yana fitowa
parlornsa ya zauna akan 3 seater saboda jiri dake shirin jefar dashi, Jiddah da
shigowanta kenan tabi shi da kallo, gaba daya ya 6ata farin kayansa dake jikinsa,
caan bakin kofa ta tsaya tana karewa parlorn kallo, bayan minti 10 ta sauke ajiyar
zuciya ta ce "To yanzu a cikin kurar nan zamu kwanta yaya?" Bude idanuwansa yayi ya
kalleta, yayi shiru yana tinanin taya zai fara zuwa gidan Ammi, da wani ido zai
kalleta, mai zaice mata Rafi'ah tayi masa ya saketa? Maiyasa bai nemeta ba all this
while? Sauke ajiyar zuciya yayi Jiddah ta ce "Doctor magana fa nake maka" ya kara
dago kansa ya kalleta, ta ce "A haka zamu zauna dust everywhere?" A hankali ya ce
"Ki gyara nan parlorn ki zauna" da mamaki ta ce "Bayan ina dauke da cikinka sannan
kace nayi wannan uban gyaran ga kura, mutuwa zanyi kenan?" mikewa yayi gently ya ce
"Then kije gidanku, duk ranar da zaki iya gyaran gidan sai ki dawo, i'm leaving
too, dama na biyo nan ne na huta in other not to stress my heart again, tinda na
samu relief tafiya zanyi" da mamaki ta ce "Ina zakaje to?" bai kalli inda take ba
ya mike yana jaan trolley dinsa ya fita a parlorn ta bishi da harara.
Umma ce zaune cikin cell ita da Anty Khadija dake faman kuka, babu abinda yake
damunta sai rashin zuwa wajen bokan nan da tayi, tasan yanzu ko ta yaya Yusuf
kokari zaiyi ya dawo gida, sauke ajiyar zuciya Umma tayi ta ce "Gaskiya bamu ta6a
shiga kunci irin na yau ba, kema sai da nace karkije inda za'a ganki amma kika
fita, yanzu ga shi nan kotu za'a turamu mu shiga 3" Anty Khadija ta kamo hannun
Ummanta ta ce "Abin takaicin bai wuce dawowar Yusuf ba, wallahi Umma ko shekara 10
zanyi anan indai Yusuf zai shiga duniya ba damuwata bane, kuma na fito a hotel zan
hau Napeep na tafi tasha kawai naga Alhaji Usman da matarsa, naso guduwa amma ya
taramin jama'a Umma, mutane nata zagina haka aka taso keyata har nan, amma duk abin
nan daya faru gara ninkinsa ya faru da Yusuf ya dawo" ta kifa kanta akan cinyar
Umma tana kuka ciki ciki, Umma ta ce "Ai zamu fita ina nan dake sai na kadashi
duniya" jin an shigo yasa Anty Khadija ba tai magana ba, dan sandan ya tsaya yana
kallansu ya ce "Ance ku kira mutum daya cikin 'yan uwanku saboda jibi zaku fara
zama a kotu, shi zai wakilce ku da wani abin daya kamata" Anty Khadija ta kalli
Umma ta ce "Kawu na mararraba za'a kira ko?" Umma ta hade rai ta ce "Allah ya
kiyaye wallahi, mutumin daya cimun mutunci gabanki rannan, wallahi gara nayi hayan
dan uwa na kawo" Dan sandan dake kallanta ya jefa musu waya daya daga cikin wayoyi
uku da suka kwace a hannunsu yayi tafiyarsa, Anty Khadija ta share hawayen idanta
ta ce "Na shiga 3,yanzu fa idan asirinmu ya toni duk wasu manyan mutane da nake
mingling dasu zasu gujeni, a gujeni wajen aiki, a gujeni a ko ina ma" fashewa tayi
da kuka ta ce "Ga Yusuf na dab da bayyana Umma, nasan da an sallameshi zai dawo
gida, Allah yasa ya rasa komai nasa a rayuwa, Allah yasa tayi aure mijinta ya
kulleshi, ita kuma Jiddah data mareki Allah ne kadai zai rabani da ita wallahi"
Umma ta ce "To ga shawara, ba sai mu kira Yusuf din muce masa gamu station ba,
kinga yana zuwa zaiyi komai a gama, muna fita kuwa sai kauyen Marke mu kara kada
shi" Anty Khadija ta ce "Kina ga zai zo?" Umma ta ce "Sai dai banyi kuka ba, amma
muddin na nuna masa ina cikin tashin hankali zuwa zaiyi, kinga ba zai samu
kwanciyar hankalin zuwa gidan kanwar uwarsa ba, nan zai taho direct"
Dai dai kofar gidan Ammi aka sauke shi, ya zira hannu a aljihunsa ya ciro 100
naira daya gani dazu, ya mikawa mai Napeep din sannan ya tura kofar gate din ya
shiga, zuciyarsa banda bugawa babu abinda take, da kyar yake takawa saboda yadda
yakeji, a balcony ya sake trolley din ya fadi, ya murda handle din kofar ya shiga
ciki, Ammi na zaune akan sallaya ta idar da sallan la'asar, ta juyo da sauri dan
tinaninta Khairiyya ce ta shigo, Yusuf ta gani tsaye hawaye sun wanke masa fuska,
ta zabura ta mike tana kallansa ta ce "Yusuf, is that really you?" Sai kuma ta
fashe da kuka, a daddafe ya karasa inda take ya rungumeta sosai yana kuka ya ce
"It's me Ammina, ki yafemin dan Allah bansan meya faru dani ba Ammi, i left without
u knowing, i divorced my beloved wife, i lost my job, na rabu da duk masoyana na
koma caan wani waje na kafa saban rayuwa, dan girman Allah ki yafemin it wasn't
intentional Ammina, i have no one but u, kece komaina Ammi dan Allah ki gafarfeni
kimin rai ko zan samu saukin abinda nakeji" Ammi kam banda kuka ba abinda take, jin
ya sake jikinsa yana shirin faduwa yasa ta rikoshi da sauri tana jijjigashi amma
ina ya sume a hannunta, anan tsakiyar parlorn ta kwantar da shi, ta dauka bottle
water dake kan dinning ta zuba masa a fuska, yayi wata ajiyar zuciya ya bude
idanuwansa da suka ciko da hawaye, Ammi ta dagoshi cikin tashin hankali ta kira
Daddyn Sameer a waya ta fada masa abinda ke faruwa sannan ta katse wayar tana
rungume da Yusuf still tana kuka tana kara godewa Allah hade da masa addu'a.
*_2 hours ltr_*
Kwance yake akan gadon Ammi, Sameer na rike da hannunsa yana masa sannu, Yusuf ya
daga masa kai kawai yana kallan Ammi dake share hawaye har lokacin, a hankali
Sameer ya ce "Zaka tashi ne" Yusuf ya daga masa kai, Sameer ya taimaka masa ya
tashi zaune, zira kafafuwansa yayi kasa yana kallan Ammi ya kamo hannunta cikin
sanyayyar murya ya ce "I know it's hurt Ammi, nasan nayi abinda ko a mafarki bakiyi
tinani ba, Ammi ban tafi dan nayi rayuwa me dadi ba wallahi, ban gujeku dan bana
sanku ba, no one loves u more than i did Ammi, bansan meyasa na tafi ba, i left my
wife crying na tafi na barta cikin amai, wallahi Ammi it wasn't intentional, kin
fitar da hawaye a kaina yafi a kirga, dan Allah kice kin yafemin Ammi" rungumeshi
Ammi tayi tana share idanta ta ce "U never hurt Yusuf, nasan ba laifinka bane,
nasan dole watarana zaka dawo indai kana raye, ai addu'ar iyaye bata faduwa banza"
hawayen idansa ya share yana kallan Sameer dake hawaye shima, Daddy ya karaso yana
masa sannu, Yusuf ya ce "Alhamdulilah" Ammi ta mike ta fita a dakin Daddy yabi
bayanta, a parlor ya sameta tana zaune tana share hawayen dake gangarowa a idanta,
ya ce "Aisha ai sai mu godewa Allah daya bayyana shi" Ammi ta ce "Mungode masa
Engineer" Daddy ya ce "To dan Allah ki daina kuka haka nan, bari na kira mahaifin
Fatima na sanar masa" Ammi ta ce "A'a dai tukunna, yanzu idan yayi wanka sai muje
gidan gaba daya" Ya ce "To Allah ya kaimu" daga haka Daddy ya fita a parlorn, ana
kiran Magrib Sameer ma ya fito a dakin, Ammi ta mike ta shiga dakin da Yusuf yake,
fitowansa a wanka kenan, ta kura masa ido ganin yadda ya rame sosai, nan da nan
kuma idanta ya kawo ruwa, Yusuf ya sauke kansa kasa ya ce "Naji sauki Ammi, u worry
not" Ammi ta ce "Idan kayi sallah u meet me in my room" daga haka ta juya ta fita,
kaya ya saka yayi sallah sannan yayi addu'a, karfin hali kawai yake amma shi kadai
yasan abinda yakeji, mikewa yayi gently ya nufi dakin Ammi, da sallama ya karasa
ciki ya zauna, ta ce "Kayi sallan?" Ya ce "Ehh" ta zauna gefensa ta ce "Ina ka
shiga all this while Yusuf?" A hankali ya ce "Egypt" ta ce "You and who?" Ya ce
"Umma, Khadija da kuma Jiddah" Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Where are they?"
Ya ce "Jiddan na gidansu, but Umma da Khadija ban sani ba" nan ya bata labarin
dawowarsu zuwa kwanciya a asibiti da yayi har tahowansu Kano, duk yadda Ammi taso
ta danne kukanta kasawa tayi, ta dinga share hawaye, Yusuf ya sauke kansa shima
yana goge hawayen idansa ya ce "Wallahi Ammi bansan meke faruwa dani ba, tin daga
ranar dana tafi ban sake tina taba sai jiya, i cried alot Ammi, musamman idan na
tuna yadda na tafi na barta" Ammi ta dago kanta tana kallansa ta ce "Kasan ka barta
da ciki ne?" With shock ya dago kansa yana kallan Ammi ya ce "Ciki kuma? Nasan dai
bata lafiya then, but bansan meyeke daminta ba" Ammi ta share hawayen idanta cikin
sanyin murya ta ce "Ka barta da ciki Yusuf, she suffered alot har kamar ba zatai
rai ba, haka tai ta rainan cikin har Allah ya kawo ranar haifansa, nan ma ta kasa
sai CS aka mata aka cire mata yarinya" kuka ne ya kwace mata ta kasa karasawa,
Yusuf dai still yayi yana kallanta, ji yake kamar ba dashi take ba, Ammi ta dago
tana kallansa ta ce "Ur Baby is now 3 years old, ina tinanin idan akwai wacce zata
yafe maka kaji dadi bai wuce Rafi'ah ba" mikewa yayi ya rasa abinda zaice, sai
kuma ya zauna bakin gado yana furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un,, ya dinga
share hawayen dake zubo masa cikin kuka ya ce "I don't know she's pregnant Ammi,
this was the biggest sin i have ever made, meyasa nayi haka" ganin kamar ba
hayyacinsa yake ba yasa Ammi ta kamo hannunsa ta ce "Stay calm Yusuf, u know ur
condition, karka samun attack pls" rungume Ammi yayi yana kuka ya ce "This is all
my fault Ammi, nasan da wuya ta yafemin" Ammi ta share hawayen idanta ta ce "It's
not your fault Yusuf, Allah zai tona asirin duk wanda yakesan yaga bayanka" saketa
yayi ya mike yana share hawayen idansa, Sameer ne ya shigo dakin shida Daddy, Yusuf
ya ce "Bani key din motarka" Ammi ta mike tana kallansa ta ce "Ina zakaje kuma?" Ya
ce "I'm going to see my wife Ammi" ta ce "Amma kasan ba matarka bace a yanzu ko?"
Ya ce "Na sani" daga haka ya fita a dakin suka bi bayansa.
Rafi'ah ce tsaye a kitchen tana wanke hannunta, bayan ta gama ta goge hannun da
towel ta fito tana kallan Mummy dake zaune a parlor ta ce "Nifa na kira wayar Ammi
several times bata dauka ba, kawai mu fara sauke Khairiyya sai mu kaiki" Mummy ta
ce "An fasa jiran Jawad din ne, naga yace yana hanya" Rafi'ah ta dan 6ata rai ta ce
"Yanzu fa bayan magrib ne, kuma Ammi zatai fada Mummy, sai dai kuma idan zaki bari
a fara sauketa" Ummi dake canzawa Imaan kaya ta ce "To ba sai a fara sauketa ba
what's in it?" Rafi'ah ta ce "Allah sai Mummy tace sai mun sauketa sannan mu wuce"
Mummy ta dalla mata harara ta ce "To badan Jawad ya matsa na jira ba da tin tini
nayi tafiya ta, dama 'yar uwata nazo gani ba kowa ba, indan take da 'yarki ne ai
bazan zo ba" Khairiyya ta danyi murmushi tana taya Ummi sawa Imaan takalmi, ita dai
Rafi'ah tin data turo baki ta samu waje ta zauna, bata mike ba sai da taji horn, ta
tashi ta saka hijab Mummy ta ce "To Zainab Allah bamu alheri, gobe dai a kaimin
Imaan ta wuni" Ummi ta mike zata rakasu ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ta kalli
Khairiyya dake saka shoes dinta ta ce "Kin dauki ledan karki manta" ta ce "Ehh
gashi nan, nagode Ummi sosai" Ummi ta ce "Ki gaishe da Amminki" ta ce "To zataji"
suna fita compound motar Daddy ta shigo gidan, Mummy ta ce "Bako kukayi ne, ashe ba
Jawad din bane" tana rife bakinta motar Jawad ma ta shigo, Imaan ta wara ido ta
tafi da gudu tana kiran "Daddy" dai dai nan Yusuf ya fito a motarsu ya kurawa cute
girl din ido, Ammi ma duk suka fito a motar, Rafi'ah ta dafe kirjinta zata durkusa
Ummi ta rikota, cikin 6acin rai Mummy ta nufi Yusuf ta shako shi tana fadin "Ubanme
kazo yi gidan nan Malam, kazo ka karasa kasheta ne?" Shi dai Yusuf banda kallan
Imaan ba abinda yake, harta dale jikin Jawad sannan ya sauke idansa a kansu, yana
juyowa kuwa Mummy ta sauke masa mari a kumatunsa hawaye na sakkowa a idanta ta
ce...

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_13_

Bude idanuwansa yayi a hankali ya fara bin dakin da kallo, Ammi dake zaune gefensa
tayi saurin matsowa ta ce "How are u?" Silently ya ce "I'm fine Ammi, where is my
daughter?" Ammi ta ce "Don't stress yourself again pls, everyone is fine, Rafi'an
ma a jiyan aka sallameta tana gida" Yusuf ya dan kalleta ya ce "U said?" Ta ce
"Rafi'ah" shiru yayi yana tina incident din jiya daya faru, Ammi ta ce "Pray first
sai mu wuce gida" mikewa yayi a hankali yana kallan agogon dakin dake nuna karfe 7
saura, da taimakon Ammi ya shiga toilet yayi alwala sannan ya fito yayi sallah,
idan ka ganshi zakace bashida damuwa saboda ya saki ransa yau ba kadan ba, sai dai
kuma in kaga ramar da yayi. Kafin ya idar da sallah Daddy da Abi da kuma Abba da
saukarsa a garin kenan suka shigo dakin, bayan sun gaisa da Ammi, Yusuf ya juyo a
hankali yana kallansu, sai kuma ya sauke idansa kasa ya ce "Ina kwananku?" A tare
duk suka amsa, Abba ya ce "Ya karfin jiki?" Ya ce "Alhamdulilah" Daddy ya kalli
Ammi ya ce "Tinda an sallameku Sameer zaizo ya maidaku gida, sannan karfe 10 akwai
meeting a guest house dina da akai organizing just because of this case, and i hope
kowa zaiyi attending dan samun kwanciyar hankali" Ammi ta ce "Allah ya kaimu" Abi
ya ce "Allah ya kara maka lafiya" daga haka suka fita a dakin, sauke kansa kasa
yayi yana kallan Ammi ya ce "Good morning" Ammi ta ce "Morning too, ya karfin
jiki?" Ya danyi murmushin karfin hali ya ce "Da sauki" ta ce "Allah ya kara sauki"
shiru yayi yana san ya tambayi Imaan amma sai yaji nauyin hakan, jinginar da kansa
yayi jikin gadon yana addu'a kasa kasa, sai daya ji an bude kofar dakin sannan ya
dago yana kallan direction din kofar, wani dan uwan mahaifinsa ne tare da Sameer
suka shigo dakin, Yusuf ya danyi murmushi yana kallan Kawun nasa ya ce "Ina kwana
Kawu Umar" Kawu ya ce "Alhamdulilah, ya karfin jiki" ya ce "Da sauki Kawu" daga
haka suka gaisa da Ammi, Sameer ya durkusa yana kallansa ya ce "How are u feeling
now" Yusuf ya ce "Better" Sameer ya ce "Masha Allah, dazu Faruk ya kira zan hada ku
ku gaisa kuma kana bacci" Yusuf ya ce "Ohk anjima sai muyi waya" mikewa Ammi tayi
ta fara tattara duk kayansu ta bawa Sameer ya kai mota, sannan suka fito zuwa gida
bayan sun kara siyan wani magani guda daya.
Rafi'ah ce kwance akan gadon dakin Ummi tana faman goge hawaye, tinda aka
sallameta a asibiti jiya da daddare bata rintsa ba har yanzu, Mummy dake zaune
gefenta ta ce "Allah dai ya isa wallahi, yaushe raban da ciwanki ya tashi haka sai
bayan dawowar wannan yaran" tana rife bakinta Abba ya shigo Ummi na biye dashi, ya
zauna bakin gado yana kallan Rafi'ah ya ce "So u didn't stop crying, u forgot all i
told u ko?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "No Abba, just that i can't control my
tears" Abba ya ce "Try and control it then" daga haka ya kalli Ummi ya ce "Zamu je
meeting din da sukayi organizing karfe 10" Mummy ta ce "Meeting din me kuma? bayan
gamu da marar lafiya a gida" Abba ya ce "Wannan ba dalili bane Halima, u have to
attend" Mummy ta hade rai ta ce "Aini banga wani meeting da za'ai ba, bayan ya
saketa ai magana ta kare meye kuma za'a ce sai mun kara haduwa duk tamu" Abba ya
dafa Imaan dake kwance tana bacci ya ce "For the sake of her, ya kamata ace an
saurari bayani daga bakinsa, tinda koma menene shine mahaifinta, bayan an gama
meeting din komai sai ya biyo baya, but we can seperata him with his daughter"
Mummy dai bata ce komai ba a wannan karan, Ummi ta ce "Allah ya kaimu, sai dai
bamusan wajen ba" Abba ya ce "Munyi waya da Jawad, zaizo ya kaiku sun bada address"
Ummi ta ce "Allah ya kaimu". Khairiyya na zaune a parlor tayi tagumi su Ammi
suka shigo, tayi saurin dauke kanta daga kallan Yusuf hawaye ya fara zuba a idanta,
ba abinda take tinawa sai ranar daya saki Rafi'ah, ta mike da sauri ta wuce dakinta
tana kuka sosai, dakin Sameer Ammi ta rakashi ta hada masa ruwan wanka ta ce "Bari
na hada maka breakfast kafin ka gama" ya ce "To nagode Ammi" daga haka ta fita,
dakin Khairiyya ta shiga ta sameta kwance tana kuka kasa kasa, Ammi ta zauna bakin
gado ta ce "Kukan ne bazaki daina ba har yanzu?" Tayi shiru kawai tana goge hawayen
idanta, Ammi ta ce "Kije ki gaishe da Yayanku sannan ki wuce kitchen ki fara
feremin dankali, i want to bath first, banajin dadin jikina" mikewa tayi a hankali
tana hade rai ta fita a dakin, direct kitchen ta nufa ta farayin abinda akace, duk
bayan miti daya sai ta tsaya ta share hawayen idanta kafin taci gaba.
Kafin karfe goma sun gama shiryawa, Ummi ta gama shirya Imaan ta ce "Go and call ur
Momma for me" Imaan ta tafi da gudu zuwa dakin Rafi'ah, a bakin gado ta sameta
zaune ta gama shiryawa tasa hijabi, Imaan ta rungumeta ta ce "Ummi is calling u"
Rafi'ah ta rungumeta itama ta ce "I'm coming" daga haka ta mike ta kama hannun
Imaan suka fita a dakin, da sallama suka shiga dakin Ummi, bayan sun zauna Ummi ta
ce "Ki kwantar da hankalinki kinji ko, babu abinda zai faru insha Allah, saki ne ya
riga daya sake ki, babu sauran alakarki da shi" Rafi'ah ta ce "To" Ummi ta ce
"Ina Anty Halima?" Ta ce "Ta sauka tin dazu, suna tare da Yaya ne" Ummi ta ce "Ohk"
juyawa tayi ta fita a dakin Imaan tabi bayanta, tinda suke sakkowa a stairs Jawad
yake kallanta, ita kuma taki bari su hada ido, ta dan tsaya bayan kujera ta ce
"Good morning" daga haka ta nufi hanyar fita ya bita da kallo, Mummy ta ce "Ai
wallahi yayi attempting kar6an yarinyar nan kotu zamu kaishi" Jawad ya mike yana
gyaran hulan kansa ya ce "Is better" daga haka ya fice a parlorn, parking lot ya
duba baiga Rafi'ah ba, ya zagaya backyard ya ganta a zaune ta kifa kanta da
gwiwowinta, ya karasa inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "Dear" kin dago
kanta tayi, ya ce "Tashi ki gani" taki dagowa, hannunsa yasa ya daga kanta dake kan
cinyarta ya ce "Are u still crying?" Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, ya shafa
bayanta cikin rarrashi ya ce "Calm down pls, ur heart beats too fast, taba kiji"
daga haka ya dagata a jikinshi ya dora hannunta saitin heart dinta ya ce "Kinji" ta
daga masa kai, ya ce "Then keep quite, insha Allah alkhairi kawai zakiji, ki daina
jin tsoro" ta turo baki ta ce "Ni banasan ganinsa kuma" ya ce "To bazan bari ya
kalle kiba, aike ce duk kika jawo mana, kikace ke karatu zakiyi ba aure ba, kinga
da munyi auran mu a acikin babban rigana zan saka ki ba yadda zai kallan min ke" ta
danyi murmushi tana kallan shigar da yayi ta ce "Ya maka kyau sosai" ya ce "Ko?
Kema kinyi kyau, just that idan nan ya kumbura kinyi kuka sosai" ta ce "Kuma inajin
bacci ma" ya ce "Don't worry idan mun dawo sai kiyi baccin" ta ce "To" mikewa yayi
jin muryar Mummy a parking lot ya ce "Karfa kibi bayana, ki koma ta kitchen" daga
haka ya bar wajen, ta danyi murmushi ta tashi ta koma ta kofar baya ta shiga cikin
gidan sannan ta kara fitowa ta parlor, duk suna tsaye a parking lot, yayi reverse
sannan suka shiga motar yaja suka wuce.
Suna isa katoton guess house din Daddy Jawad yayi horn aka bude masa gate, babban
gidane sosai amma ba kowa a ciki, Jawad yayi parking yana kallan motoci hudu dake
pake a wajen, da alama dai su kadai ake jira kenan, bayan duk sun fito Imaan ta
daga masa hannu alaman ya dauketa, ya dagata sama sannan ya sauketa kan shoulders
dinsa suka shiga ciki, duk ilahirin mutanen na zaune a wakeken parlorn, suka shigo
da sallama sannan suka zazzauna, caan gefe Rafi'ah ta samu ta zauna kanta a kasa
bata bari koda wasa ta hada ido da mutanen parlorn ba, Yusuf ya sauke idansa daga
kallan Imaan ya wani sauke ajiyar zuciya, godiya ga Allah yake cikin ransa daya
bashi this cute girl, kowa ya ganta yasan shine mahaifinta, Daddy yayi sallama
sannan ya bawa Yusuf damar magana akan ya fadi dalilinsa na sakin matarsa sannan
meyasa ya tafi ya barta almost 4 years ba'a san inda yake ba, shiru duk mutanen
parlorn sukayi suna kallan Yusuf da kansa ke kasa, Rafi'ah ce kawai bata yarda ta
kara kallansa ba, Cikin cool voice dinsa yayi musu bayanin komai, tin daga ranar
daya farajin tsanar Rafi'ah har ta kai ga ya saketa sannan ya kara da cewa tinda ya
tafi Egypt bai kara tina taba sai ranar, duk mutanen parlorn jikinsu yayi sanyi
sosai, Kawu Umar ya ce "Ninasan wannan aikin Fatima ne, wallahi zata iya yin komai
dan dai ta rushe farincikin yaran nan, yanzu ina take ita da 'yartata" Yusuf ya ce
"I don't know Kawu, tinda aka sallameni a asibiti ban sake ganinsu ba" Kawu ya ce
"Baka da number dinsu ne?" Ya ce "Ina dashi, sai dai banbi ta kan wayar ba, ga dai
ta nan a pocket dina" Kawu ya ce "Kira mana ita" Yusuf ya ciro wayar ya danna yana
kallan screen din, 25 missed calls ya gani, ya duba yaga kiran Umma ne, cire wayar
yayi a silent sannan yayi dialing phone dinta, Kawu Umaru dake kallansa ya ce "Kar
kace mata kana gida" shi dai shiru yayi yana kallan phone din dake ringing, bayan
Umma ta daga yasa a hands free, ta ce "Yusuf" ya ce "Na'am" ta ce "Kana ina?" Yayi
shiru sannan ya ce "Ina hanyar zuwa kano" Umma ta fashe da kuka ta ce "Yusuf gamu
nan a cell wallahi, mijin da Khadija ta aura shiyasa aka kama mu, bayan ya saketa
yace sai an biyashi duk kudin daya kashe mata, to nidai ga ATM's dinka dukka a
hannuna ba damar ciran kudi, yanzu abinda nakeso da kai ka wuto station din ka
kar6i ATM card ka ciro kudi a biyasu muma duk mu huta" Yusuf ya ce "To gani nan
zuwa, a wani station ne?" Ta ce "Na nan unguwar Rimi, kusa da first bank" ya ce "To
in zuwa" daga haka yayi hanging call din, Abba ya sauke ajiyar zuciya ce "Then sai
muje station din ko?" Yusuf ya ce "Ohk to" Abba ya mike yana kallan Ummi ya ce "Ku
wuce gida, mu zamu je staion din, koma me ake ciki i will call u" Ummi ta ce
"Alright safe" Juyawa Abba yayi yana kallan Jawad dake gyarawa Imaan gashin kanta
ya ce "U follow us too barrister" Jawad ya ce "Ohk" duk mazan mikewa sukai suka
fita, Yusuf ya sauke kansa kasa ya fita Mummy ta bishi da kallo, itama duk jikinta
yayi sanyi, Jawad ya nufi kofar fita Imaan tabi bayansa da gudu kamar zatai kuka ta
ce "Zan bika Daddy" daukanta yayi suka fita a parlorn, Ammi ta kalli Khairiyya ta
ce "Kije Sameer ya baki key din motar karya manta ya tafi dashi" Khairiyya ta mike
ta fita bayan ta amsa da to, ba jimawa ta dawo da keys guda biyu, ta mikawa Ummi
daya ta ce "Yaya Jawad ne yace in kawo, wai ya tafi da Imaan tana kuka saita bishi"
Ummi ta ce "Ohk" Ammi ta kalli Mummy dake zaune tayi shiru ta ce "Kuyi hakuri dan
Allah Hajiya Halima, nasan abubuwan da suke faruwa akwai ciwo, amma ba wanda ya
wuce kaddararsa, Allah ya kaddara hakan zai faru, kuma indai aka sameshi da laifi
nayi alkawarin zan bada goyon baya a hukuntashi dai dai da abinda kotu ta yanke
masa" Mummy ta ce "Allah ya mana me kyau, amma kuwa idan matar caan ne tayi
sanadiyar wargaza mana zuri'a wallahi Allah ne kadai zai rabani da ita, me muka
mata? Me muka tare mata a rayuwa Aisha? Meyasa zata sa yarannan cikin wani rayuwa?"
Ummi ta ce "Allah ya rufa asiri" Ammi ta ce "Ameen" sannan ta mike ta ce "Zamu wuce
mu kam" Ummi ta mike itama ta ce "To sai anjima" daga haka su Ammi suka fita, Mummy
ta dago Rafi'ah dake kuka tin tini ta ce "Kiyi shiru Rafi'ah, insha Allah duk wanda
yakesan yaga bayanki ba xai ci nasara ba" ta kama hannunta suka fita a parlorn Ummi
tabi bayansu.
Tafiyar minti 6 sukai ya kaisu station din saboda dama a unguwar ne, Jawad na rike
da Imaan suka shiga ciki, shima har lokacin basu hada ido da Yusuf ba, direct
office din DPO suka shiga, kawu Umaru ya masa bayanin komai, DPO ya musu bayanin
dramar da akai lokacin da aka kamo Anty Khadija, shi dai Yusuf na gefe duk jikinsa
yayi sanyi, lokaci lokaci yakan kalli Imaan dake hannun Jawad tana wasa da hular
kansa, DPO ya ce "To yanzu dai yace court za'a tura su dan sai anyi musu shari'ah"
Kawu ya ce "To muma akwai case din da muka kawo a kansu, ina ga zamu rubuta
statement sai a hada rana daya" DPO ya ce "Ba matsala insha Allah" juyawa Yusuf
yayi ya fita a office din yana kallan dan sandan dake tsaye bakin kofa ya ce "Dan
Allah akwai wasu mata da aka kawo jiya, inasan ganinsu" dan sandan ya ce "Ko kaine
wanda suka kira" ya ce "Ehh nine" dan sandan ya nuna masa inda suke sannan ya dawo
bakin aikinsa, a hankali Yusuf ya karasa wajen ya leka, suna nan zaune aka kasa
dauro duk yaci ubansu sai susa suke, Umma ta taso da sauri ta ce "Dan Albarka, ga
ATM din guda 4 bansan dai da wanne za akai amfani ba" Yusuf bai kalleta ba ya ce
"Ohk, zaku fita nan yau insha Allah Umma" daga haka ya kar6i ATM cards din ya yasa
a pockets dinsa ya juya, Umma na murmushi ta kalli Khadija dake zaune ta ce "Aina
gaya miki zaizo, amma me zaisa zan kira Umaru, banda wa'azi ba abinda zaizo ya mana
a wajen nan, karshe ma yasa a kaimu kotun".
bayan an gama rubuce~rubuce Jawad yayi signing ya kuma tura case din
zuwa court dinsu, ba 6ata lokaci akai printing takarar yasa a pocket dinsa, Abba ya
ce "Yanzu akwai wani abu kenan?" Ya ce "A'a, idan naje office zan karasa komai sai
asa date din da za'a fara zaman" Abba ya ce "To Allah ya kaimu" Daddy ya kalli
Yusuf dake zaune kan bench kansa a kasa ya ce "Are u alright" Yusuf ya ce "Sure
Daddy" kiran da DPO yayi wa Jawad ne yasa ya mike ya fita, sai lokacin Yusuf ya
bishi da kallo, Imaan dake jikin Abba ta 6ata fuska kamar zatai kuka, Yusuf ya mike
yana kallanta ya ce "Come" ta mika masa hannu ya dauketa suka fita a office din
Daddy ya bisu da ido, fita sukayi a station din ya tsaya a ATM machine yayi
withdrawing 30k sannan yasa a pocket dinsa ya tari cab, bayan sun shiga ya ce "Old
GRA" mai cab din ya ja suka tafi, a hankali Yusuf ya kalli Imaan da tai collapsing
ajikinsa ta rungumeshi, ya rungumeta shima yayi kissing kanta ya ce "I luv u
daughter"

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_14_

Dai~dai kofar gidansa me cab din yayi parking, ya fito rike da Imaan a hannunsa ya
ciro 1k ya mika masa ya ce "Nagode" daga haka ya juya ya tura gate din mutumin ya
bishi da kallo harya rufo kofar, entrance din gidan ya nufa ya bude kofar parlor,
gidan yana nan yadda suka sameshi ya karasa part din Jiddah ya bude, ba kowa a ciki
da alama ta tafi kenan, Imaan ta yatsine fuska tana kallansa ta ce "Why is your
house very dirty Uncle?" Yusuf ya danyi murmushi yana kallan cute face dinta ya ce
"We are leaving now sweetheart" daga haka ya wuce dakinsa ya bude, sauketa yayi
akan bed side drawer tana ta yatsina fuska, ya ce "Wait for me here" daga haka ya
daga katifar kan gadon ya dauko wata babban leda ya ajiye gefe sannan ya maida
katifar, jikinsa duk ya baci da kura, ya dauki ledan ya karkade sannan ya shiga
toilet ya kunna tap ya wanke hannunsa ya kade wandan jikinsa daya 6aci, bayan ya
gama ya dauki Imaan dake tsaye uncomfortable a wajen ya sata a shoulder dinsa dayan
hannunsa na rike da ledan suka fita, bayan sun fito a gidan ya jawo kofar parlorn
suka fita gate, sauketa yayi ya ciro padlock din dake jikin kofar ya datse kofar,
bayan haka ya dauketa suka fara tafiya a layin har suka iso bakin titi, ya tare mai
Napeep ya ce "Hamdala hotel" mai Napeep din ya ce "400" Yusuf ya shiga ya daura
Imaan a cinyarsa sannan ya ajiye ledan hannunsa, ta dago tana kallansa ta ce "Where
are we going Uncle?" ya limshe ido yana shafa bayanta bai ce komai ba, tafiyar
minti 30 sukayi dan wajen da nisa sannan akwai hold up, bayan ya tsaya Yusuf ya
bashi 500 sannan ya dauko Imaan da ledan gefensa suka fito, hotel din suka shiga ya
tsaya a reception suka fara gaisawa da mutumin wajen, bayan sun gama ya ce zai biya
kudin daki ne, mutumin ya tambayeshi kwana nawa, ya ce "2 days" ya ce "U pay the
some of 50k" Yusuf ya ciro ATM card dinsa ya mika masa, ba 6ata lokaci akai making
payment ta POS, suka bashi key da room number, matar dake gefen Mutumin nata kallan
Imaan, bayan ta fada masa sama zasu hau taja hancin Imaan ta ce "Like father like
daughter" Yusuf ya danyi murmushi yana shafa kan Imaan suka bar wajen zuwa
upstairs, dakinsu shine na biyu by the left, yasa key ya bude dakin suka shiga ya
rufo kofar, komai neat dakin sai kamshi yake, ya sauke Imaan akan gadon yana kallan
fuskarta ya ce "Are u sleepy?" Ta girgiza masa kai, daukanta ya sakeyi ya dan
cillata sama ta fashe da dariya, ya sake cillata ta kara fashewa da dariya, ya
rungumeta yana shafa bayanta suka fita a dakin ya rife sannan ya zare key din yasa
a pocket dinsa, downstairs suka sauka suka fita a hotel din, wani babban boutique
dake gefen hotel din suka shiga, ya sayi kaya set 2 sannan ya siyawa Imaan set 5 da
takalmi biyu, bayan ya biya kudin suka fito suka shiga provision store, ya kalli
Imaan dake bin shop din da kallo ya ce "Do u take cornflakes?" Ta daga masa kai ya
ce "What of custard?" Ta ce "No, biscuit instead", cornflakes da biscuits, da kuma
chocolate sai milk na sachet, bayan ya biya kudin suka fito suka koma cikin hotel
din, sauketa yayi a bakin kofa ya bude dakin sannan ya shiga ta biyo bayansa, ya
ajiye kayan akan gado ya rufe kofar da key sannan ya jefa shi saman wardrobe, phone
dinsa ya ciro a pocket ya kashe duka duka sannan ya dora akan gado, kallan Imaan
yayi dake kallansa tin dazu ya ce "What?" Kamar zatai kuka ta ce "My Daddy" yaja
dan karamin tsaki ya wuce toilet yayi alwalan azahar sannan ya fito ya shimfida
sallaya ya tada sallah, bayan ya idar yayi addu'a sannan ya juya ya kalli Imaan
dake kwance saman gadon ta rufe ido, ya kura mata ido yana murmushi ya mike ya
karasa gefenta ya kwanta shima.
Murmushi kawai Jawad yayi bayan Abba ya fada masa Yusuf ne ya tafi da Imaan, bayan
sun iso gida Jawad yayi horn Mustapha ya bude gate din suka shiga, bude kofar Abba
yayi ya ce "Sannu da kokari Barrister" Jawad yayi kasa da kansa ya ce "Ba komai
Abba" daga haka Abba ya fito, ganin zai juya Abba ya ce "Ba zaka shigo kayi lunch
ba?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya juya motar Abba ya shiga cikin gida, yana
fita gate ya nufi gidan Ammi, bayan ya isa yayi parking a waje ya fito ya shiga
cikin gidan rike da key din motarsa, a parking lot ya samu Sameer yana kokarin rife
mota, Jawad ya karasa ya bashi hannu, Sameer ya ce "Ya kokari?" Ya ce
"Alhamdulilah, Yusuf yana ciki ne?" Sameer ya ce "No, muma dawowanmu kenan Ammi
tace basu dawo ba, kuma bama wanda yake da contact dinsa na yanzu bare a kirashi"
with surprise Jawad ya tsaya yana kallan Sameer, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Yana
tare da Imaan fa" Sameer ya ce "Eh, shiya dauketa tin a station, may b lokacin suka
taho" Jawad ya ce "Amma ina kake tinanin zan ganshi?" Sameer ya ce "Sai dai ko
gidansa, ko gidan Ummansu" Jawad yasa hannayensa cikin aljuhunsa ya ce "Dan Allah
ka rakani mana" Sameer ya ce "Ba damuwa" daga haka suka fara tafiya zuwa gate,
bayan sun fita Jawad ya bude lock din motar suka shiga ciki yaja suka tafi.
ba jimawa Yusuf ya tashi daga baccin daya sace shi, ya zame Imaan dake kwance kan
kirjinsa ya shiga toilet, bayan few minutes ya fito ya zauna bakin gado, ya dinga
kallan Imaan dake baccinta hankali kwance, ya durkusa dai dai goshinta ya bata
light kiss, knocking da akayi ne yasa ya mike ya dauko key ya bude kofar, matar ta
mika masa babban tray me dauke da fried rice da kaza sai chips a gefe, ya kar6a
tray din ya ce "Thank u" daga haka ya tura kofar, ajiye tray din yayi yasa key a
kofar ya zare shi ya maida inda yake, yana zama Imaan ta bude ido, ya dagota yana
murmushi ya ce "Dear" ta ce "I'm hungry Uncle" ya dagata suka shiga toilet ya wanke
mata fuska da baki suka fito, tray din abincin ya dauko ya ajiye a gabansu sannan
ya cire transparent ledan dake kan abincin yana kallan Imaan ya ce "Kina cin
wannan?" Ta daga masa kai, ya danyi murmushi ya ce "So u speak Hausa?" ta ce "Eh,
very well" ya ce "That's good" spoon ya dauka ya fara bata abincin a baki tana ci,
ganin tafisan shinkafan ya daina bata chips din, sosai taci ta koshi, ya bata ruwa
ta sha sannan yaja hancinta ya ce "Zaki sha tea" ta girgiza masa kai ta ce "When
are we going back home Uncle?" Ya dan bude ido yana kallanta ya ce "Meyasa kike
cemin Uncle?" Ta ce "Is because Ummi tace duk babba in ce mishi Uncle" ya wara ido
yana kallanta ya ce "Really" ta ce "Yeah" rufe abincin yayi ya ajiye a gefe ya
dagata suka koma kan gado ya ce "From now henceforth sunana Papa" ta juyo tana
kallansa ta ce "Why?" ya ce "Because i'm ur Daddy" ta dan kalleshi sai kuma tayi
dariya ta ce "No, my Daddy is at home" ya ce "Nine Daddynki daughter" daga haka ya
dauko ledan dazu ya ciro babban album din bikinsu da Rafi'ah ya bude, first picture
hotonsu ne su biyu, ta wara ido tana kallan picture din ta ce "My Mum" ya nuna
hotonsa ya ce "And who is this?" Ta kalli picture din ta dago ta kalleshi sannan ta
kara kallan picture din ta ce "It's you" ya danyi murmushi ya rungumeta ya ce
"Don't call me Uncle again" ta ce "Papa?" Ya daga mata kai ya ce "Tashi muyi sallan
la'asar dear" ta mike tana nade dogon hannun rigarta ya tsaya yana kallanta with
passion.
Rafi'ah ce zaune a dakin Ummi tana ta trying number Jawad, sauke ajiyar
zuciya tayi jin ya shiga, bayan yayi picking ta ce "Sweetheart" ya ce "Yes
sweetheart, ya kike?" Ta ce "Lafiya, har yanzu baku gama bane naga almost 4 yanzu"
shiru yayi yana jinta, ta ce "Hello, are u there?" Ya ce "Yes, inajinki kikace
mene?" Ta ce "Baka dawo da Imaan ba" Jawad yayi kasa da murya ya ce "Abba bai fada
miki bane, yanzun nan muka gama waya" kallan phone din take kirjinta na bugawa ta
maida wayar kunnenta ta ce "Ni banga Abba ba, may b yana apartment din Antynmu,
Yana tare da ita kenan?" Ya ce "No, mahaifinta ya tafi da ita, naje gidansa baya
nan, naje gidan Ummansu nan ma baya nan ba kuma ya gidansu Sameer" mikewa tayi
jefar da wayar ta fasa ihu, Ummi ta shigo da sauri jin ihunta ta ce "Lafiya
Rafi'ah?" Rafi'ah ta kankameta tana kuka ta ce "My Imaan Ummi, Doctor ya tafi min
da ita, dan Allah Ummi ku kirashi ya bani diyata wallahi baxan bashi ita ba, nice
komai nata a rayuwa Allah bazan yarda ba" Ummi ta janyeta a jikinta ta ce "Keep
shut now" tayi shiru tana goge hawayen idanta da yaki tsayawa, Ummi ta ce "Waya
fada miki?" Cikin kuka ta ce "Ya Jawad ne, wai Abba ma ya sani" daga haka ta fashe
da kuka ta ce "Nidai amin adalci a bani yarinya na, naji zan yafe masa komai amma
ni ya barmin Imaan dina" ta sulale nan bakin kofa tana rera kuka, Ummi ta juya ta
fita a dakin.
Shiru Mami tayi tana sauraron bayanin da Jawad yake mata, bayan ya gama ta sauke
ajiyar zuciya ta ce "To duk inda yaje ai dole zai dawo da ita" Jawad ya limshe
idanuwansa ya ce "Nasan zai dawo, but Fatima ba lallai ta fahimci hakan ba, gani ma
zatai nine na bashi ita" Mami ta danyi murmushi ta ce "Kunfi kusa kuma wannan" ya
dan shafa kansa yana murmushi ya mike ya ce "Is Mummy back?" Ta ce "A'a ai inaga
yau ma kwana zatai" daga haka ya juya ya fita a parlorn. Ammi na zaune a parlornta
tana tinanin ina Yusuf ya tafi da Imaan, Sameer ya dago yana kallanta ya ce "Duk
munje inda kike tinani amma baya nan" Ammi ta ce "The only way to have his contact
shine ka koma station kace a baka numbersa" Sameer ya ce "Numbersa kuma?" Ammi ta
ce "Ehh shiyafi sauki, tinda akwai numbersa a wayansu Khadijan ai, tin karfe 12 har
4 saura babu labarinsu" Sameer ya mike ya ce "Ohk bari na kira Barrister sai muje
tare" daga haka ya fita a parlorn, Khairiyya ta ta6e baki ta mike ta bar parlorn,
har yanzu haushin Yusuf takeji har cikin ranta.
Abbane ya shigo parlorn da sallama yana kallan Ummi dake zaune ya ce "Ina Rafi'an?"
Ta ce "Tana sama" Abba ya zauna kan kujera ya ce "Let her come" Ummi ta mike ta
haura stairs, tare da Mummy ta sameta a dakin, har lokacin kuma kuka take sosai,
Ummi ta ce "Kizo Abbanki yana nemanki" ta mike a hankali tasa hijabi sannan ta
fita, Mummy dai na zaune bata ce komai ba har lokacin, Ummi ta fita a dakin itama,
a tare suka sakko kasa, Rafi'ah ta zauna akan carpet kanta a kasa ta ce "Gani Abba"
ya ce "Meya saki kuka?" Tayi shiru tana wasa da hijabin jikinta tana sauke ajiyar
zuciya, Abba ya ce "Your daughter right?" Ta daga masa kai ya ce "To menene abin
damuwa bayan tana tare da mahifinta? I see nothing in it, dole zasu dawo ai, ba
guduwa zaiyi da ita ba" hawayen idanta ta share ta ce "But Abba dan meyasa zai
dauketa bayan baima san ya akai na haifeta ba, shidai ne mahaifita amma Abba bata
samu kulawars ba, batama san shi ba" Abba dake kallanta ya ce "Yanzu ai zata san
shi, pls let's stop all this drama, zai dawo miki da ita u cool ur mind" daga haka
Abba ya mike yana kallan Ummi ya ce "Abdul ya kira bai sameki ba" ta ce "Ehh, dazu
munyi waya" Abba ya bude kofar ya fice a parlorn, kuka me cin rai Rafi'ah ta fashe
dashi ta kifa kanta akan kujera.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_15_

*The page is dedicated to my Phiaa 🤗 thanks for d alawan madara* 💃🏻

Da daddare Yusuf na zaune a daki da Imaan a cinyarsa yana mata wasa, ta kalli
wayarsa dake kan gado ta ce "I want to play game" shiru yayi yana kallanta, ta ce
"Ohh sorry Papa u warn me not to ask again" murmushi Yusuf yayi ya kai fuskarta
saman nata ya ce "I will give u sweetheart, but sai idan kinci abinci" cike da jin
dadi ta ce "Yesss, zan ci" daga haka ta sauka akan gadon ta zauna a gaban tuwan da
aka kawo musu, lafiyyen tuwo ne da vegetable soup, sai kamshi yake yaji cow meat da
crayfish, duk da bata ci amma saboda yace zai bata game ta kar6a, ya dinga bata
tana ci amma ba a san ranta ba, ta danci sosai sannan ta kauda kanta gefe ya ce
"Kin koshi?" Ta daga masa kai ta ce "Yes Papa, yaji ne da yawa" bottle water ya
dauko a gefensa ya bude ya zuba mata ruwan a cup sannan ya bata a baki ta sha,
bayan ta koshi suka mike a tare ya kama hannunta suka shiga toilet, hannu ya wanke
mata sannan yayi mata brush suka fito, ya dauko ledan kayan da siyo mata ya dauki
kayan bacci da socks ya cire mata kayan jikinta sannan ya canza mata, kayan sunyi
mata kyau sosai da sosai, mikewa yayi ya rage AC dakin saboda garin ma akwai sanyi,
yana zama Imaan ta bashi phone dinsa ta ce "U promised" ya kar6a wayan ya bude
bayanta ya cire sim card dinsa sannan ya maida marfin ya kunna wayan, akan bed side
drawer ya ajiye sim card sin, bayan wayan ya kawo ya dan zaro ido tinawa da yayi
babu games a wayan, kuma idan downloading zaiyi sai yayi amfani da sim card, kallan
Imaan yayi data kura masa ido tana jira ya bata, ya sauke ajiyar zuciya ya kara
bude bayan wayar ya maida sim card din sannan yayi restarting wayar, bayan ya kawo
yana kunna data kira ya shigo wayar, kallan number ya dinga yi amma bai daga ba
harta katse, aka sake kira for d second time, yayi picking call din ya kai kunnne
amma baice komai ba, Ammi ta ce "Yusuf" da kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce
"Na'am" ta ce "Fisabilillahi ka kyauta kenan, ka daga mana hankali kasa mun fara
wani tinani da ban" silently ya ce "I'm sorry, this is the only way dazan jawo ta
jikina na kuma ganta, zan dawo da ita insha Allah" Ammi ta danyi tsaki ta ce "Baka
kyauta ba wallahi, Dazu danaje kuka Fatima take kamar Imaan tayi sati bata nan" ya
dan ta6e baki ya ce "Kiyi hkr" Ammi ta ce "Yanzu ina Imaan din? Kuma kuna ina?" Ya
ce "Gata nan, muna hotel" Ammi ta ce "To dama gobe da safe ka dawo da ita, ana
kokarin a kashe wata wutar amma kana kara jawo mana magana haba Yusuf, yarinyar nan
ba wanda xai rabaka da ita idan kayi hakuri, kowa yasan kaine ubanta menene na daga
hankalinka haka" limshe idanuwansa yayi ya ce "Insha Allah zan dawo da ita gobe"
Ammi ta ce "Kar kuma ka sake kashemin waya" ya ce "Ohk". Bayan yayi hanging call
din ya juyo yana kallan Imaan dake wasa da gashin kansa ya ce "Wane game kike so"
ta danyi murmushi ta ce "Anyone" cikin few minutes yayi mata downloading games guda
4, ya bata wayar yana rungume da ita, mamaki ta bashi ganin ko wane game ta iya
perfect, ya kalli time sannan ya kar6a wayan ganin quarter to ten, juyo da ita yayi
tana facing dinsa ya ce "Wane sura kike?" Ta ce "Al-Humaza" ya ce "Karanta min" ba
musu ta kwanta akan kirjinshi ta fara da bismillah sannan ta karanta har karshe,
yayi kissing forehead dinta ya ce "Idan kina karatu zan saya maki tablet" ta wara
ido ta ce "Ina dashi ai" ya ce "Waya siya maki?" Ta ce "My Dad" Yusuf ya rungumeta
ya ce "Zan siya maki Laptop i know u don't have it" ta ce "Irin na Momma?" Ya daga
mata kai sannan ya ce "Kiyi addu'a ki kwanta i'm also sleepy" a hankali ta fara
karanto ayatul qursiyyu sannan tayi addu'an bacci tayi nasi da falaq, ta kwanta a
jikinsa ta ce "Good night Papa" ya ce "Night daughter" daga haka ta rufe ido, ba
jimawa kuwa tayi bacci, zameta yayi a jikinsa ya mike ya nufi bakin window yana
kallan motoci da mutanen dake kasa.
Washegari Rafi'ah na dakinta ta fito a wanka kenan phone dinta ya fara haske, ta
leka screen din ta dauke kai taci gaba da abinda take, shiryawa tayi cikin atampa
doguwar riga sannan tasa hijabi ta dauki laptop dinta da side bag ta fita a dakin,
dakin Ummi ta shiga ta sameta zaune ita da Mummy suna magana, ta sauke kanta kasa
ta ce "Zan tafi Ummi" Ummi ta ce "Allah ya bada sa'a, ki kwantar da hankalinki kiyi
exams dinki da kyau, nothing is going to happen Mamana" a hankali ta ce "Insha
Allah" daga haka ta kalli Mummy ta ce "Kafin na dawo kin tafi ko?" Ta ce "Eh, Allah
ya taimaka" ta ce "Ameen" sannan ta juya ta sauko downstairs, tana fita compound
phone dinta yaci gaba da ringing, ta maida ta silent ta shiga mota Mustapha yaja
suka tafi. Karfe takwas Imaan ta tashi a bacci, tayi mitsi mitsi da ido tana kallan
Yusuf dake zaune akan kujera, a hankali ta ce "Papa" ya juyo yana kallanta sannan
ya mike ya karasa inda take ya dagata ya ce "How are u daughter" ta ce "I'm fine"
daukanta yayi suka shiga toilet, bayan 10 minutes ya fito da ita a dukunkune cikin
towel, kan gado ya direta ya goge mata jiki sannan ya saka mata kaya, tayi kyau
sosai da sosai, ta dan kalleshi ta ce "U didn't comb my hair" ya ce "I don't have
comb here" ta dan turo baki zatai kuka ya rungumeta ya ce "Don't cry pls daughter,
idan munje gida Ammi zata miki" jin ya fadi haka ta dan saki ranta sannan ta ce
"Baka samin perfume ba" ya kalli kan mirror sannan ya dauka perfume din daya gani
ya fesa mata sau daya ya ce "Saura breakfast" ta sauko akan gadon tana kallansa ta
ce "U look so handsome Papa" ya danyi murmushi kawai yajawo breakfast din ya fara
bata a baki, bayan ta gama ya hada mata tea shima ya bata a baki, sai daya tabbatar
ta koshi sannan ya ajiye mug din a gefe yana kallanta ya ce "So ur name is Imaan"
ta daga masa kai, baima san sunanta ba sai jiya da Ammi ta fada, ya dauketa suka
koma kan gado ya ce "Me ake ce maki a school?" Ta ce "Fatima Yusuf Muhammad" ya dan
bude ido cike da farinciki ya ce "Whose name are u bearing?" Ta ce "My grandmother,
haka Momma tace min" limshe idanuwansa yayi ya ce "Which class are u" ta ce
"Nursery 1" ya ce "Good, which school?" ta ce "Prime College" ya danyi murmushi
kawai yana kallanta, juyawa yayi jin phone dinsa ta fara ringing, ya dauka ya kai
kunne hade da sallama, Jiddah ta ce "I have been expecting your call since
yesterday but u didn't" ya ce "Ina busy ne that's why" ta ce "To yaushe zamu dawo
gidan mu?" ya ce "Saina gama abinda nake" ta dan hade rai ta ce "Amma kasan ba kudi
a hannuna ga cikin dake jikina sai wahala nake" ya ce "Zan maki transfer i'm sorry,
how are u now?" Ta ce "Lafiya, amma dai inasan na ganka" ya ce "Ohk, kizo Hamdala
hotel, room 32" dan zare ido tayi ta ce "Hotel kuma Ya Yusuf, me kazo yi Hotel?"
Yusuf ya ce "I don't like noise much Jiddah, idan b zaki zo ba ki zauna it isn't by
force, xan miki transfer din" ta ce "To ina zuwa" yayi hanging call din yana kallan
Imaan dake wasa da button din shirt dinsa.
_45 mins ltr_
Knocking kofar dakin Jiddah tayi, Yusuf ya mike ya dauka key ya bude mata kofar,
rungumeshi tayi ta ce "Shine ka gudo nan ka barni kuma..." shiru tayi ganin Imaan
tsaye akan gado tana kallansu, nan da nan zuciyarta ya hau bugawa, Yusuf ya janyeta
a jikinsa ya tura kofar sannan ya dawo gefen gado ya zauna, cike mamaki da takaraso
inda suke ta ce "Who is she Doctor?" Yusuf ya kalli Imaan sannan ya kalleta ya ce
"My daughter" daaaamm taji kirjinta ya buga, ya ce "Yarinyar da Fatima ta haifa
bayan na tafi" Jiddah ta zaro ido tana kallan Imaan, ita da take takama tana da
ciki zata haifa masa diya ko d'a sai gashi da yarinyar da ta kai shekara 3 yace
mata 'yarsa ce, nata cikinfa watansa biyu kacal, durkusawa tayi hawaye na bin
fuskarta ta ce "Anya Doctor kaika haifi wannan babbar yarinyar, baka tinanin sun
makala maka ita ne dan su cimma burinsu" Yusuf ya mike yana kallanta ya ce "Look,
don't pretend like baki ga kamana da yarinyar nan ba, duk inda na shiga da Imaan
kowa ya kalleta yasan jinina ne" Jiddah ta mike tsaye ta nufi kofa ta fita ya bita
da kallo, Yusuf ya juyo yana kallan Imaan dake bin kofar da kallo ta ce "Who is
she?" ya ce "Ur Aunt" bata ce komai ba ta fara tsalle akan gadon tana wasanta,
wayarsa ne ta fara ringing yayi picking ya kai kunne, ahankali ya ce "Ina kwana
Ammi?" Ta ce "Lafiya kalau, ya baku dawo ba har karfe 10" ya ce "Yanzu insha Allah"
ta ce "Bari Sameer yazo ya dauko ku" ya ce "To, muna Hamdala Hotel idan yazo ya
kirani" Ammi ta ce "To" daga haka ta katse wayar.
Within some Minutes Sameer yayi parking a kofar hotel din, yayi
dialing phone din Yusuf ya ce "Naxo" Yusuf ya ce "I'm coming" kallan Imaan yayi
dake kwance akan gado ya ce "Dear, we are going back home" ta mike ta ce "Ohk, are
we going with Napeep" ya ce "No" durkusawa yayi ta dale bayansa sannan ya dauki
babban ledan da kayansu suke ciki suka fita a dakin, yasa key ya kulle bayan sun
sakko ya basu key din ya nufi kofar fita, a parking space suka samu Sameer na
tsaye, Yusuf ya karasa gefensa ya bashi hannu ya ce "Ya gida" Sameer ya ce "Lafiya
kalau" daga haka ya bude musu back seat Yusuf yasa kayan sannan ya rufe ya dawo
front seat suka zauna, Imaan ta kalli Sameer ta ce "Good morning Uncle" yaja
hancinta ya ce "How are u beauty?" Ta ce "Fine" daga haka ta kwanta jikin Yusuf,
har suka je gida Yusuf na rungume da Imaan, Sameer yayi horn aka bude mishi gate ya
shiga yayi parking, Imaan ta kalli motar Jawad dake parke a gefe ta ce "Daddy"
Yusuf ya juyo ya kalleta sai kuma tayi murmushi ta ce "I saw his car" bai ce mata
komai ba suka fito a motar, ya kama hannunta suka nufi cikin gida, Ammi ce da
Khairiyya sai Jawad a parlorn, ya shiga hade da sallama yana kallan Ammi ya zauna
gefenta ya ce "Ina kwana" ta ce "Lafiya kalau" Khairiyya ta dauke kai ganin sun
hada ido, mikewa Yusuf yayi ya bawa Jawad hannu ya ce "Morning" Jawad ya ce "How
are u" ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya sake Imaan ya wuce dakin Sameer, Imaan ta
bi bayansa da gudu Jawad ya bisu da kallo, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Alright yanzu zan masa bayanin komai insha Allah" Jawad ya ce "Ohk ba damuwa"
mikewa Ammi tayi tabi bayan Yusuf, Khairiyya ta mike zata wuce dakinta Jawad ya ce
"Come here" tsayawa tayi sannan ta juyo tana kallansa sai kuma ta sauke kanta ta
kara 2 steps ta dan matso, ya ce "Sit down" ta zauna akan kujera, Jawad ya ce "Why
didn't u great him?" Ta hade rai ta dago tana kallansa ta ce "Who?" Murmushi Jawad
yayi ya ce "Your brother"

_08103810398_

*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_16_

A hankali Khairiyya ta dago ta kalleshi kafin ta ce "Zan gaishesa idan na shiga"


Jawad ya shafa beards dinsa yana kallanta ya ce "Promise" ta daga masa kai daga
haka ta juya ta koma ciki. A kan gado Ammi ta sameshi ya dora Imaan a cinyarshi, ta
zauna bakin gado tana kallansu ta ce "Gobe insha Allah zamu fara zama a kotu" yayi
kasa da kansa yana rike da Imaan ya ce "Allah ya kaimu" shiru ne ya biyo baya sai
karan game din da Imaan keyi in a low volume, Ammi ta sake kallansa ta ce "Yaushe
zaka maida musu da yarinyar?" sai lokacin ya dago kansa ya kalle ta ya ce "Gobe
insha Allah but..." Shiru yayi ya kara sauke kansa kasa, Ammi ta ce "But what?" Da
kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya ce "They're giving me my daughter Ammi"
murmushi ta danyi ta ce "Why? Meyasa baza ta zauna inda ta saba ba" ya limshe
idanuwansa ya ce "Zamu koma gidana tare, i don't think zan iya zama babu ita" Ammi
dake kallansa ta ce "All these years da kai spending baka nan kasan da ita ne? Kaga
karka sake jawomin wani rigimar Yusuf, ka barta kawai ta xauna da mahaifiyarta, sai
dai kuma idan ita da Fatiman zasu koma gidanka" da sauri ya juyo yana kallanta ya
ce "I don't think so Ammi, ita din dai ita ce mallakina so i'm going with her no
matter how" sauke ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce "Allah ya za6a mana abinda yafi
alkhairi, that's all my wish" a hankali ya gyarawa Imaan zama a cinyarsa ya ce
"Ameen" Ammi ta mike ta nufi hanyar fita ta ce "Bari a kawo maka abinci" daga haka
ta fita ta rife masa kofar, dakin Khairiyya ta shiga ta sameta zaune akan gado tana
danna waya, Ammi ta ce "Are u done with the food?" Ta ce "Yes" Ammi ta ce "Sai ki
kaiwa Yayanku" hade rai tayi ta ce "Nafa daura akan dinning Ammi, kuma yanzu 7
minutes past 12 ai lokacin lunch bai yi ba" Ammi ta dalla mata harara ta ce "Ai
inada hannu ba sai na kai masa ba" daga haka ta juya, da sauri Khairiyya ta sauko
akan gadon tabi bayanta, a wajen dinning ta samu Ammi zata dauki warmer tayi saurin
riketa ta ce "Pls Ammi ki kawo zan kai" Ammi ta mika mata ta ce "Rashin hankali ne
banaso, ba sai nayi da kaina ba wani abu ne" dan 6ata rai tayi ta nufi dakin Sameer
da Yusuf ke ciki, ciki ciki tayi sallama ta ajiye warmer din a kasa ta juya ta
fito, ta dauki dan karamin warmer da miyar ke ciki sai cabbage da cucumber cikin
wani dan bowl shima ta kai, sake fitowa tayi ta dauki serving spoon guda 2 da spoon
sai table water da plate hade da cup, duk akan plate din ta dora sannan ta koma
dakin ta ajiye masa, har ta juya zata fita ya ce "Khairi" ta hade rai ta juyo tana
kallansa ya ce "I need to talk to u" dawowa tayi ta tsaya caan gefe, ya ce "Zoki
zauna" ta dan kalleshi sannan ta wuce ta zauna ganin kallan daya ke mata, ya ce
"Mena miki da bakya kulani, or do u think saboda kin girma yanzu sai ki daina
gaishe da mutane" tayi saurin saukar da kanta kasa ta ce "No" ya ce "To menene?"
nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa, ya ce "Idan ba zaki magana ba u can go" share
hawayen daya gangaro mata tayi ta ce "I'm seeing what u did to Anty Fatima up till
now, anytime i saw u, or i heard ur voice inajin ba dadi, that's why banasan na
ganka, i feel hurt deep down me" kallanta kawai yake baice komai ba, caan ya sauke
ajiyar xuciya ya ce "After mun gama da court i will apologize insha Allah" da sauri
ta juyo ta ce "Bana tinanin zata yafe maka Yaya" ya ce "I don't care, as far as ba
laifina bane babu abinda zai dameni, koba laifina i will still apologize saboda
Imaan, after all zan kar6i yarinyana suje suyi auransu" Khairiyya ta sake kallansa
ta ce "Ai an kusa dama, baifi 2 months ba" ya mike yana gyarawa Imaan zama ya ce
"Allah ya sanya alkhairi" daga haka ya nufi toilet yana nade hannun rigarsa, juyowa
yayi yana kallanta ya ce "Zanyi alwala ne" daga haka ta mike ta fita a dakin tana
share sauran hawayenta.
Karfe 1 Rafi'ah ta dawo daga exams dinta ta samu Mummy ta tafi, duk ji tayi babu
dadi gidan, ta wuce dakinta tayi wanka tayi sallah sannan ta sauko downstairs,
abincinma kansa kasa ci tayi, ganin phone dinta na haske yasa ta jawo wayar tana
kallan screen din, da kamar bazata dauka ba sai kuma tayi picking tayi shiru, on
the orther side Jawad yayi sallama cikin cool voice, dan ta6e baki tayi sannan ta
amsa, ya ce "After 26 miseed calls sai yanzu kika dauki wayana" nan da nan idanta
ya cika da hawaye, ya ce "Ina waje" ta share hawayen daya sakko mata da bayan
hannunta ta ce "I'm coming" daga haka tayi hanging call din, mikewa tayi ta xura
hijabi sannan ta fita a parlorn, tana fita gate ya bude back seat yana kallanta ya
ce "Bismillah" kamar iska zata dagata ta karasa inda yake ya ce "U come in" daga
haka ya matsa mata ta shigo ta rife kofar, rife fuskarta tayi da hijabin jikinta ta
ce "Where is my daughter Barrister?" daga haka ta fashe da kuka, Jawad dake
kallanta ya danyi murmushi ya ce "Is that what makes u not to pick my calls?" Bude
fuskarta tayi hawaye na sakko mata ta ce "Ai is all your fault, ka bari ya tafimin
da yarinyana" Ta karashe maganar tana turo baki, ya kamo hannunta cikin rarrashi ya
ce "Is not my fault sweetheart, na barta wajen Abba ne bayan DPO yayi kirana, i
don't know how he managed to go with her" ta fara bubbuga kafa with serious ta ce
"Allah saiya bani Imaan dina, ai ba shiya haifamin ita ba, ko yasan wahalan dana
sha na haifeta ne" daga haka ta kara fashewa da kuka, rungumeta Jawad yayi
unexpected, ya bubbuga bayanta ya ce "U stop crying love, ki barta a wajenshi ki
gama exams dinki peacefully" ta dago kanta a kirjinsa hawaye na sakko mata ta ce
"Did u said peacefully?" Ya ce "Yes" ta ce "Ni rashin ganinta shine yake sani kuka
inajin ba dadi, kuma ai naga gobe zan gama exams din" kallan lips dinta yake dake
motsi a hankali kamar ba magana take ba, ya ce "Nasan gobe zaki gama, sai kuma ki
bari idan an gama zaman court sai ya baki idan har ya yarda, kinsan shine yake da
iko a kanta bake ba" kuka ta sake fashewa da shi ta ce "After all i gone through
sabida shi, wallahi bazan yarda ba, da kaina zanje na dauko yarinya na" jin
bakinshi kawai tayi akan lips dinta, tayi shiru zuciyarta na bugawa da karfi, da
sauri taja baya tana kallansa ta ce "Ni banaso" ya danyi murmushi yana shafa
gashinsa ya sauke kansa kasa, wani mungun kunyarta yaji lokaci daya, ta ce "Pls
help me and get my daughter back" jin yayi shiru ta kifa kanta jikin kujera tana
share idanta ta ce "Pls Barrister i can't do without her, bata da mahaifin daya
wuce kai wallahi, nina baka Imaan har abada" sai a lokacin ya dan kalleta yayi
murmushi ya ce "Kin ta6a ganin anyi kyautar diya da ubanta?" Ta turo baki ta ce "Ni
dai na baka" hannunta duka biyu ya kamo yana kallan cute face dinta data 6aci da
hawaye ya ce "Let him go with her Fatima, wallahi court shi zata bawa yarinyar nan,
sai dai kuma idan ta sameshi da wani hali wanda zai iya 6ata tarbiyyar Imaan, shine
kadai abinda zaisa a baki ita" kwace hannayenta tayi ta fara rera kuka, ya matso
gefenta ya bata light side hug ya ce "Bakya sona kenan?" Ta dago da sauri tana
kallansa zuciyarta na bugawa, ya ce "Idan kina sona to ki yarda mu bashi Imaan, i
promise u 2 weeks after our weeding zamu samo baby" ta dan wara ido tana kallansa
saam bata manta da hawalan da tasha a cikin Imaan ba, ta maida kanta gefe, ya ce
"Are u with me love, ko bakya so?" ta kara kauda kanta gefe bata ce komai ba, Jawad
ya ce "Karfe nawa gobe zaki gama exams din?" Ta ce "12" ya ce "Alright zan dauko ki
and we are going straight to the court" ta juyo tana kallansa kamar xata kara
fashewa da kuka ta ce "I'm scared Barrister, banasan kallan Doctor again"
murmushinsa me kyau yayi ya ce "Ba sai ki kauda kanki ba" ya kara kamo hannunta
cikin rarrashi ya ce "Don't be scared Fatima, inaso ki zama barrister kema, idan
kina tsoro ai bazaki iya ba" ta sauke kanta kasa ta zame hannunta a hankali ta ce
"Ohk, kuma bazan dawo gida ba" ya ce "Ehh, kafin ki gama kowa yaje" ta dan 6ata
fuska ta ce "My Imaan" ya ce "Goben zaki ganta ai" ta share dan guntun hawayenta ta
ce "Kuma bata da kaya ko daya ma" Jawad ya kashe mata ido daya ya ce "Zai siya mata
ai" ta turo baki ta bude kofar motar zata fita ta ce "Zaka zo da daddare?" Ya ce
"Sure, insha Allah" ta danyi murmushi bayan ta fita ta ce "Kuma kayi kyau sosai"
daga haka ta rife fuskarta ta juya ta shige gida ya bita da kallo yana murmushi,
fitowa yayi a back seat ya koma gaba ya kunna motar ya bar layin.
Anty Amina ce zaune a parlorn gidansu ta buga uban tagumi, Anty Rahama ta kalleta
da kyau ta ce "Ba zakije gidan Ikleeman ba?" Anty Amina ta girgiza kai ta ce
"Bazanje ba" Anty Rahama ta saki baki tana kallanta ta ce "Zaki kashe kanki fa
Amina, kawai daga ji Yusuf ya dawo kin bi kin daga hankalinki, ni wallahi Jawad
dinma shiri nake na kada shi yace ya fasa" Anty Amina ta juyo tana kallanta ta ce
"Ai tinda ya dawo nasan asirin Khadija ya karye, kuma ni bani da numbernta bare na
kirata, ni tinda Ya Muhammad yace min Yusuf ya dawo naji ba dadi, kuma bansan
meyasa ba da fargaba nake kwana, karfa asirinmu ya toni Anty" Anty Rahama ta ta6e
baki ta ce "To sai me? Ai wallahi ko kama su akayi tace dasa hannunmu koda rantsuwa
sai mun kwaci kanmu, tinda dama sun nuna basanmu suke ba, kinga ko munce karya suke
yarda za'a yi" Anty Amina ta ce "Kuma hakane, Amma jikina yana bani wani abu yana
faruwa, tin bayan dawowar Abban Rafi'ah da nace zanzo gida ya barni, kinga yau
kwanana 3 baice na koma ba, sai waya, kuma innace akwai abinda yake faruwa sai yace
babu, abun daya fadamin shine Rafi'ah ba lafiya kuma Yusuf ya dawo" Umma dake
kwance tana jinsu tayi murmushi ta ce "Yoo dama dole tayi ciwo mana, balle ma ga
ciwan da yake daminta ai dole ya tashi idan taga bawan Allah nan, ki dai kwantar da
hankalinki a gama komai caan ki koma gidan mijinki" Anty Rahama ta ce "Ai bazan
bari tayi auran jin dadi ba, wallahi koda ta auri Jawad dinma sai ta fito, saina
san yadda nayi ta kara fitowa" Anty Amina tayi murmushi kawai tana danna wayarta.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_17_

Washegari karfe 8 Ammi ta gama breakfast ta dora akan dinning, dakin Yusuf ta shiga
ta sameshi a tsaye ya goyi Imaan suna xagaye dakin, suna hada ido da Ammi ya sauke
kansa kasa silently ya ce "Good morning" Ammi ta karasa shigowa dakin tana kallansu
ta ce "How was your night?" Ya ce "Fine" Ammi ta kalli Imaan dake bacci a bayan
Yusuf ta ce "Ai ta koma baccin ka kwantar da ita mana" murmushi kawai Yusuf yayi
bai dai bari sun hada ido ba, Ammi ta ce "To ga breakfast a parlor kasan 11 ya
kamata mu tafi court din" ya ce "Alright" Ammi na fita ya sauke Imaan a bayansa ya
rungumeta, bude idanuwanta tayi a hankali tana kallansa, ya gyara mata gashinta
daya sakko fuskarta ya ce "Sweetheart" ta ce "Papa" ya kara rumgumeta ya ce "Na
goya ki har kin sake bacci" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Thank u"
hannunta ya kama suka shiga toilet ya wanke mata baki da fuska sannan suka fita a
dakin, a parlor suka sami Khairiyya tana zaune, ta juyo tana kallan Yusuf ta ce
"Ina kwana" a takaice ya ce "Lafiya" bayan ya zauna ya daura Imaan a cinyarsa yayi
serving dinsu. Cikin 10 minutes suka gama breakfast, Yusuf ya mike yana kallan
Khairiyya ya ce "Ki mata wanka" ba tare data kalleshi ba ta ce "To sanda kuke hotel
waya ke wankanta?" Dago kansa yayi yana kallanta ta mike a hankali ta kama hannun
Imaan suka shiga ciki, yayi nodding kansa ya ce "I will surely deal with u" yana
zama akan kujera Ammi ta fito a daki, ya ce "Zanje gidana" ta ce "Me za kai kuma?"
Ya ce "Zan sa a gyaramin ne" Ammi ta tsaya kallansa ta ce "Why not after
everything?" Ya dan shafa kansa ya ce "Ammi inasan na koma can ne" a hankali ta ce
"To, sai kayi kokari ka dawo kafin time din yayi" ya mike ya ce "Insha Allah" daga
haka ya nufi daki ya dauko key din gidan ya futo, dakin Nabeel ya shiga ya samu
Sameer na kwance yana bacci, ya duba kan mirror ya samu key din motarsa ya dauka
sannan ya fita, yana fita compound din gidan ya wuce parking lot yayi warming motar
sannan yaja ya bar gidan. Cikin minti 10 ya isa gidansa yayi parking a waje sannan
ya fito yasa key ya bude padlock din ya shiga ciki, bayan few minutes ya fito ya
rife gidan sannan yaja motar ya bar layin, ba jimawa ya dawo da wasu samari su 2,
suka fito a motar bayan ya bude gate din suka bi bayansa, bude musu kofar parlor
yayi ya nuna musu broom da mop sannan yasa face mask dinsa ya bude part din Jiddah
suka bishi a baya, yana tsaye bakin kofa suka gyara dakin tass sukai mopping, baza
kace shine ya hada wannan kuran ba, rufo dakin yayi suka fara gyaran parlor, yana
nan tsaye bakin kofa yana kallansu, da sauri yasa hannu a pocket dinsa ya ciro
phone dinsa dake ringing, ya daga ya kai kunne hade da sallama, Jiddah ta ce "Naga
kudin yau da safe, amma dai kasan ba zai isheni ba ko" limshe idanuwansa yayi ya ce
"I will call u ltr, ina wani abu ne" daga haka yayi hanging wayar. Cikin 30 minutes
suka gyara gidan, har part din Rafi'ah daba komai a ciki saida suka share sukai
mopping, bayan sun gama suka fito tsakar gida suka hau sharewa yaja kofar parlorn
ya rufe, cikin few minutes suka share tass suka fitar da sharan, Yusuf ya basu 4k
yana musu godiya, suka masa sallama suna masa godiya suma suka fita, padlock yasa
ya rife gate din sannan ya shiga motar ya dau hanyar gidan Ammi.
Bayan yayi horn aka bude gate din ya shiga yayi parking, ya fito ya nufi entrance
din gidan, da sauri Imaan ta fito a parlor fuskarta da hawaye ta nufeshi, ya dagata
yana kallan idanta ya ce "I'm back sweetheart" cikin muryar kuka ta ce "You ran
away Papa" ya shafa bayanta ya ce "I didn't dear, ba gashi na dawo ba" ta danyi
murmushi tana kallansa ya shiga share mata idanta, suna shiga parlor Ammi ta ce
"Tin dazu take mana kuka" Yusuf yayi murmushi yana kallan Ammi ya ce "Na dawo ai"
daga haka ya ajiyeta akan kujera ya ce "Wait for me here" ya shige daki ya barta
anan wajen zaune.
Cikin kankanin lokaci suka shirya zuwa court, Daddy da Ammi da kuma
Khairiyya a mota Yusuf kuma da Sameer sai Imaan, sai da suka biya suka dauko Jiddah
a gidansu sannan suka wuce court din, sai kumbura take tana hararan Imaan, kuma
tayi alwashin saita tonawa Umma asiri ta wulakanta, suna zuwa Jawad ya kaisu har
inda zasu zauna, babban court ne sosai, ba kowa a kan stage din saboda kowa shirye
shirye yake, ba jimawa su Mummy suka zo, Yusuf ya karasa har inda suka suka gaisa
sannan su Ummi suka taso suka gaisawa da Ammi, karfe 11 da rabi Jawad ya dauki
motarsa yayi school din su Rafi'ah, kafin ya karasa har sun fito a exams dinsu,
bayan ya isa yayi parking ya fito yana kallanta, juyawa tayi da sauri jin alamar
motsi, ta sakar masa murmushi tana kallan kayan jikinsa ta ce "Woow Barrister, kaga
yadda kayi kyau, kayan ya maka kyau sosai" yau ne ranar farko data fara ganinsa da
kayan sai dai kuma a hoto, ya ce "Thank u sweetheart, muje Fatima we don't have
much time" daga haka suka shiga motar yayi reverse suka fita. Within 10 minutes
suka iso court din an gama komai Rafi'ah kawai ake jira, tinda suka fara shiga
zuciyarta ya hau bugawa kuma ta dauki alkawarin yau sai ta kar6i Imaan dinta, ta
sunkuyar da kanta dan karma ta hada ido da Yusuf, Imaan ne ta dan wara ido ta ce
"Papa here is my Mom" ta karashe maganar tana nuna masa Rafi'ah data zauna dan nesa
dasu taki kallansu, sau daya ya kalleta ya dauke kai, Jiddah ta dallawa Imaan
harara hakan yasa tayi shiru ta kwanta akan kirjin Yusuf, signing Jawad yayi sannan
ya mikawa na gefensa takardar shima yayi signing, bayan haka Alkali ya bada unarnin
a shigo dasu Umma, ba jimawa aka shigo dasu duk sunyi baki, Anty Khadija ta gwalalo
ido ganin mutanen dake zazzaune, aka wuce dasu aka kullesu a inda aka tanada dan
masu laifi irinsu, bayan komai ya kammala kotu ta bada dan brief na abinda ta sani
akan su Umma, Alhaji Usman shima da iyalansa na zaune gefe guda, bayan haka Kotu ta
bada dama Yusuf yayi introducing kansa da kuma takaitattcen labarinsa, da kyar
Sameer ya rike Imaan dake ihu saita bishi, bayan ya karasa wajen yayi sallama cikin
sanyi murya ya fara bada tarihin rayuwarsa daki daki har zuwa yanzu, bai rage koya
kara komai ba akan abinda ya faru, harya gama kuwa Rafi'ah bata kalleshi ba kanta
na kasa idanta ya cika da kwalla, bayan ya zauna ita ce next da aka kira itama ta
taso duk jikinta yayi weak, Jawad da shine zai mata tambayoyi ya dan kashe mata ido
daya, silently ya ce "feel free" ta shiga wajen ta tsaya kanta a kasa, itama cikin
sanyin murya ta fada musu labarinta tin haduwarta da Yusuf har auransu da kuma
rabuwarsu da yadda tasha wahala kan cikin Imaan har aka mata CS, tana kaiwa nan ta
tsaya ta share idanta, sai lokacin Yusuf ya kalleta na seconds sannan ya dauke kai.
A sanyaye ta koma ta zauna bayan an sallameta, daga nan aka kira Jiddah, dama Allah
Allah take a kirata, babu 6ata lokaci ta tashi ta tafi Rafi'ah ta bita da kallo,
tana shiga wajen ta fadi alakarta da Yusuf a takaice sannan ta danyi murmushi, hada
ido sukai da Umma dake ta kifkifta mata ido amma tayi kamar bata ganta ba, Jiddah
ta dan yatsina fuska tana kallanta ta fara bayani kamar haka "Wannan matar dake
tsaye ita da 'yarta su suka jefani hanya karkatacciya, kuma su sukai sanadiyyar
raba auran Yusuf da waccen yarinyar Rafi'ah, su suka san yadda sukai suka shiga
suka fita yaji ba abinda ya tsana a rayuwarsa sama da ita" Jiddah ta danyi murmushi
tana kallan Anty Khadija ta ce "Bazan manta ba, shekara 4 da suka wuce Khadija tazo
gidana tace in hada mana kayanmu zamu bar kasar sun gama shirya komai, bayanta tafi
Umma ta kira Yusuf ta umarce shi daya saki Rafi'ah, shi kuwa ganin a lokacin ba
wacce yake jin maganarta sama da ita yayi abinda tace, kamar yadda ya fada ya tafi
ya barta tana laulayin wannan yarinyar, a ranar da muka sauka a Egypt wani bawan
Allah wai dan ajin su Umma yazo ya taremu ya kaimu masauki, ba mufi sati ba da
taimakaonsa Yusuf ya samu aiki, ana haka ana haka duk bayan wata daya sai Umma ta
turawa bokanta kudi saboda ya sake dora aikin karna baya ya warware, sannan ya kafa
musu sharadi na cewa sai Khadija taje wajensa a shekara sau daya ya sadu da ita, to
dai sau biyu ya faru ana ukun suka ki zuwa, duk karshen shekara muna dawowa Nigeria
mu sauka a Kaduna amma Yusuf bai ta6a budar baki yace ina Rafi'ah ba, komai kuma
normal yake amma cikin ransa ji yake babu mutanen daya keso sama damu, Kwatsam wata
sati 3 da suka wuce Alhaji Usman ya saki Khadija, ana haka a karshen shekaran nan
Yusuf ya fara ciwo sosai, harta kaiga baya iya magana, ganin haka yasa Umma ta
tattaro mu muka dawo Kaduna, anan kuma muka fuskanci tinanin Rafi'ah ya dawo masa
yayinda ya fara kiran sunanta, shine Umma ta tura Khadija da tazo wajen bokan ta
bashi kudade danya maida mata aikin sabo kuma ta bashi hakuri akan batazo wajensa
ya kwana da ita ba, to anan ne na samu labarin an kama ta, yayinda asirin Alhaji
Usman ya bar jikinsa shima" tinda Jiddah ta fara magana Yusuf kansa na kasa sai
data dasa aya hawayen idansa ya gangaro, nan da nan ya fara furta innalillahi wa
inna ilaihir raji'un, Jawad ya kalli Jiddah dake tsaye ya ce "Amma meyasa all this
while da abubuwan suka faru baki zo kin sanar da kanwar mahaifiyarsa ba" Jiddah
tayi kasa da kanta ta ce "Saboda nima ina sanshi, matukar nayi niyyar tona asirinsu
zasu rabani dashi" Jawad dake kallanta ya girgiza kai ya kara ce wa "To yanzu wane
dalili ne yasa ki kai magana?" A hankali ta ce "Saboda naga suna hannun hukuma kuma
sannan tayi fatan Yusuf ya mutu saboda bata da asara, saboda taga ni nake dauke
dauke da cikinsa, hakan yasa har mukai fada ta mareni nima na rama" with shock duk
mutanen wajen suka tsaya kallan Jiddah, Abba ya girgiza kai ya maida kansa gefe
yana addu'a kasa kasa, gaba daya tausayin Rafi'ah yakeji, lokaci daya suka canza
mata rayuwa tin tanada karanci shekaru har zuwa yanzu, ita dai Rafi'ah ta kifa
kanta akan kujerar wajen tana kuka sosai.
Wani abokin aikin Jawad ne ya mike yayi rubutu a wata farar takardar sannan ya
mikawa na kusa dashi ya ce "Zaki iya tafiya" Jiddah ta fito a wajen ta koma ta
zauna, Yusuf dai na zaune kansa a kasa shima, tsabar bakin ciki kasa kuka sosai
yayi, Jawad ya kalli Umma dake tsaye gefen Anty Khadija ya ce "Hajiya Fatima kin
daiji abinda matar Yusuf tace, ko a maganganunta akwai abinda baki yarda kun aikata
ba?" Umma tayi wulli wulli da ido ta rasa abin cewa, sai kuma ta ce "To idan tone
tone ne ba sai ayi ba, aiba mu kadai mukai wannan aikin ba akwai wasu wanda suka
bamu gudumawa kusan ma nasu yafi yawa" ganin abinda Alkali yayi yasa Jawad ya sauke
kansa kasa irin yadda sukeyi alamar girmamawa sannan ya karasa wajen Alkali ya
kar6i takardar hannunsa, duk sauran lawyers din wajen mikewa sukai suma, Jawad ya
ce "Kotu ta daga shari'ah nan zuwa jibi wato 9 ga watan 9" police din dake gefe
suka kara tasa keyar su Umma da hannunsu na daure da handcuffs suka wuce dasu.
Mikewa Yusuf yayi ya saba Imaan a kafadarsa suka fita, Rafi'ah ta dago kanta ta
kalli direction din da yake zaune taga bayanin, mikewa tayi da sauri ganin su Mummy
na magana da Ammi, Abba yana gaisawa Daddy, fitowa tayi daga court din ta tsaya a
compound tana kallan motocin dake parke a wajen amma bata gansu ba, hakan yasa ta
nufi gate da sauri ta fita, tana fitowa a gate taga Napeep dinsu ya tashi, tayi
saurin taran wani Napeep din ta shiga ta ce "Dan Allah wannan Napeep din zaka bi"
daga haka ta gaya masa number Napeep din. A kofar gidansa aka sauke shi, ya bashi
kudinsa sannan ya ajiye Imaan a kasa ya zaro key din gidan ya bude padlock din,
daga haka ya tura gate din ya dauki Imaan suka shiga, da sauri Rafi'ah ta sakko a
Napeep dinta ta bashi 500 ta juya da sauri ta shiga gidan, Yusuf ya juyo jin an
bude gate din, da mamaki yake kallanta sai dai bace komai ba, hawaye na sauka a
idanta ta ce "Nazo na tafi da Imaan, baka da wani dalili da zaka rabani da
yarinyana" Yusuf ya mata wani kallo ya ce "I'm her Father, so u let me idan na
yanke shawara zan baki ita from now till tomorrow" cikin tsawa ta ce "Stop saying u
are her father Doctor, u don't know anything about her, idan ma akwai wanda ya dace
ta kirashi mahaifi to Yaya ne" a hankali ya gyarawa Imaan zama a hannunsa ya ce
"Tinda shiya miki cikinta sai kice masa yazo ya kar6a miki ita, and get out in my
house now" daga haka ya juya ya bude kofar parlor ya shiga ya rufo kofar yasa
sakata, yana zama wasu hawaye masu zafi suka sakko masa, bubbuga kofar da Rafi'ah
keyi ne yasa ya mike ya share hawayen idansa ya bude kofar yana kallanta da jajayen
idanuwansa cikin 6acin rai ya ce "What do u want then? get out and stop knocking my
door before i show u the bad side of me" ya karashe maganar ransa a 6ace yana nuna
mata hanyar gate.

*DEDICATED TO MY GROUP MEMBERS *

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _
_18_

Kuka sosai ta fashe da shi tana kallansa, ya juya ya shiga zai rufo kofar tayi
saurin tarewa ta ce "Pls don't do this to me Doctor, meyasa zaka rabani da
farincikina, nina riga na yafe maka ka bani Baby na mu tafi for God sake" ta bude
kofar ta shiga cikin parlorn ta dauki Imaan zata fita ya tare kofar, share hawayen
idanta tayi ta ce "Let me go out pls" Yusuf yadan kalleta kafin ya ce "Idan kinaso
ki fita ki ajiyemin daughter na" ta masa wani mungun kallo cikin tsawa ta ce "Stop
calling her your daughter, she is not, wallahi kaiba mahaifinta bane, gara na bawa
wani caan da bansan da shi ba, baka da wani maraba da mutumin da yayi raping mace
baisan ta samu cik..." Wanka mata mari Yusuf yayi tayi saurin dafe wajen ta durkusa
a kasa, ganin haka yasa Imaan ma ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta, limshe
idanuwansa yayi hawayen dake makale a idansa suka zubo, gaba daya ya rasa me yake
masa dadi, maganar da Jiddah ta fada zaiji dashi ko kuma rashin hankalin da Rafi'ah
ke masa, mikewa tayi ta gyarawa Imaan zama a jikinta ta ce "Wallahi saina tafi da
ita, i'm going with her no matter how, ka matsamin na fita" ta karashe maganar tana
kuka sosai, juyawa yayi yasa sakata a kofar sannan ya fisge Imaan a hannunta ya
ajiyeta gefe yana kallanta ya ce "Idan kinasan tafiya kije ke dai" tayi kan Imaan
zata dauketa ya fisgota ta fado jikinshi, daga ta yayi ta fasa ihu ya shiga da ita
part din Jiddah ya ajiyeta akan kujera, yana jin Imaan na kuka haka ya rufe kofar
yana kallan Rafi'ah dake kuka ya zauna gefenta ya ce "Sai ki fadamin abubuwan da
kika mata yanzu yanzu na biyaki ki fita min a gida" ta dalla masa harara tana ci
gaba da kuka, mikewa yayi yasa hannayensa a pocket dinsa ba tare daya kalleta ya
fara magana cikin cool voice dinsa kamar haka "I thought you heard all what Jidda
said, kinga ba laifina bane, su suka sa na tsaneki naji banasan rayuwa dake, nayi
tinanin idan kikaji abinda ya faru kece mutum ta farko da zaki tausayin, kinsan
yadda nake sanki more than anyone else, i can't betrayed u for no reason Fatima,
nace maki ki bari gobe zan kai miki ita but u followed me and start shouting at me
kamar wanda na miki sata, ko sata na miki ba zaki hakura da tsawan kimin magana a
nutse ba, shekara nawa na baki a duniya Fatima? do i deserve such things, wane irin
soyayyane ban miki ba kafin a shiga tsakaninmu? Or do u think i'm just pretending
ba sanki nake ba?" Shiru yayi yana kallan yadda take kuka, ya sauke ajiyar zuciya
ya ce "And u are trying to said bani da maraba da wanda yayi raping mace baisan ta
samu ciki ba, how do u call this a rape? nasan akwai wahala laulayin ciki da kuma
haihuwa, but this doesn't mean ki zauna kina fadamin maganganu marasa dadi akan
yarinyar dana haifa, at first ur Mum slapped me, she insulted me and she called me
munafiki macicu azzalumi ta kara da cewa na cucesu Allah ya isa sannan na fita muku
a gida kafin ta min illa, this words touch my heart more than u know" limshe
jajayen idanuwansa yayi ya ce "Anywhere ki yafe min duk abinda na miki, it wasn't
intentional na kuma gode maki with this cute Baby, Idan a zaman da mukai akwai
abinda na miki bakiji dadi ba u pls forgive me, zan baki Imaan amma ba yanzu ba
kamar yadda na fada miki a farko" bude idanuwansa yayi ya bude kofar parlorn ya
fito, Imaan na kwance saman kujera harta fara bacci ya dagata ya goge mata hawayen
idanta sannan ya sa6a ta a kafada suka shiga ciki, Rafi'ah na zaune a parlorn har
lokacin tana goge hawayen idanta, ya wuce da Imaan daki ya kwantar da ita akan
gadon sannan ya zauna bakin gado har yanzu mamakin Umma yake ba kadan ba, yasan
bata kaunarsa amma baiyi tinanin zasu wargaza masa rayuwa irin haka ba, ajiyar
zuciya ya sauke ya share hawayen daya gangaro a idansa. Kusan minti 10 Rafi'ah na
zaune a parlorn, ta mike jikinta duk a sanyaye ta fito a parlorn ta bude kofar main
parlor tasa shoes dinta ta fita a gidan, har ta isa bakin titi hawaye yaki tsaya
mata, ta tare Napeep ta fada masa inda zai kaita, tana shiga kuma ta fashe da kuka
sosai. Within 14 minutes suka iso gida, Mustapha dake zaune a kofar gida yayi
saurin mikewa ganinta ya ce "Hajiya nata cikiyarki Rafi'ah" a hankali ta ce "Ka
bashi kudinsa" daga haka ta shige ciki, tana bude kofar parlor suka hada ido da
Ummi, tayi saurin sunkuyar da kanta Ummi ta ce "Daga ina kike, kinsa inata tambayar
makwabta bakya nan, Mummy ma ta tafi caan gidanta bakya nan phone dinki kuma is
off" a hankali ta ce "Naje gidansu Ameera ne, phone din kuma na motar Yaya" Ummi ta
dinga kallanta kafin ta ce "Ohk, wuce ki rifemin kofa" tura kofar tayi ta wuce
upstairs tana share idanta, tana shiga dakinta kuwa ta zube a tsakiyar gadon ta
fashe da kuka.
Ajiyar ziciya Mummy ta sauke bayan tayi hanging call din, ta kalli Jawad dake zaune
gefenta ta ce "Ta koma gida yanzu, wai gidan su kawarta taje" Mami dake zaune gefe
itama ta ce "To masha Allah" Mummy ta kara kallan Jawad dake zaune ta ce "Gaskiya
mutanen nan sun cucemu wallahi, sun wargaza mana farincikinmu lokaci daya, ni yanzu
wallahi kunyar hada ido da Yusuf nake irin abinda na masa ranar, kuma kaga yau ma
har zuwa yayi ya gaishe mu, nidai dama zuciyata ne kawai a kusa na zazzageshi
wallahi da nasan haka ne babu ruwana, dama ai baiyi kama da macuta ba, ga kunya da
ladabi, Allah yasa dai ya yafemin" Jawad ya danyi murmushi yana kallanta ya ce
"Irin cases din nan Mummy basu da iyaka, suna faruwa sosai, wani sai sihirin ya
karye zakiga ya dawo, wani ma har abada ya tafi kenan shari'a kuma sai anje gaban
Allah, to akwai matar da da kanta tayiwa diyarta asiri saboda wasu bukatu nata na
duniya, so irin abubuwan na faruwa" Mami dai na zaune tayi shiru, ita kanta lamarin
mamaki yake bata, Mummy tayi tagumi ta ce "Allah ya kara karemu, shiyasa ba'aso
mutum ya shagala baya addu'a, at least ko abin ya sameka zaizo da sauki" Mami ta ce
"Hakane kam Allah yasa mu dace" Jawad ya ce "Ameen" mikewa yayi ya nufi dakinsa ya
ce "Sadeeq bai dawo ba?" Mami ta ce "Ya dawo, Kawu ne ya kirashi" ya ce "Ohk" daga
haka ya shige ciki.
Mikewa Yusuf yayi yana kallan agogon dake manne jikin bango sannan ya kalli
Khairiyya dake cin fried rice cikin take away ya ce "Do fast dear" zama yayi akan
kujera ya jirata ta gama sannan ya wanke mata baki suka fita a parlorn ya rife
bayan sun fita gate ma ya datse da gwado, daukanta yayi suka karasa bakin titi suka
hau Napeep zuwa gidan Ammi, After 10 minutes suka iso gidan, ya biya mai Napeep din
sannan suka shiga ciki, Sameer ne kadai zaune a balcony yana waya, ya dan kauda
wayar a kunnensa ya ce "Ka dawo" Yusuf ya ce "Ehh" daga haka suka shiga cikin
gidan, Ammi ta dago kanta jin an bude kofar, Yusuf ya danyi kasa da kansa ya zauna
ya ce "Sannu da gida Ammi" ta ce "Yauwa, ina kukaje haka?" Ya ce "Gidana" ta ce
"Ohk, yaushe zaka maida musu Imaan ne?" Kallan Imaan yayi dake kwance ajikinsa ya
ce "Idan an gama komai" ta ce "To dazu dai nacewa Umminta suyi hakuri zata dawo"
kai kawai ya gyada mata, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Sannan abinda nakeso da
kai shine karka saka komai a ranka, insha Allah duk wanda yake da hannu a lalacewar
rayuwarka sai sun girbi abinda suka shuka, kaci gaba da addu'a insha Allah soon
komai zai zama tarihi" a hankali ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya ajiye Imaan
kusa da Ammi ya ce "Inasan hutawa ne" Ammi ta ce "Kana shan magani kuwa?" Ya ce
"Ehh" Ammi ta ce "To Allah ya kara lafiya" daga haka ta shafa kan Imaan ta ce
"Kinsha tea ne" ta daga mata kai ta ce "Since morning".
Da daddare Jawad yayi parking kofar gidan Ummi, ya fito a motar ya
nufi inda suka saba zama ya zauna akan daya daga cikin kujerun wajen, bayan sun
gama gaisawa da Mustapha ya ce "Dan yi mata magana" Mustapha ya ce "To" sannan ya
juya, bayan 10 minutes ya hangota ta tana tahowa da hijabinta har kasa, ya maida
phone dinsa cikin aljihu yana kallanta harta karaso ta zauna a gefensa, ya ce "Ya
kike?" A hankali ta ce "Alhamdulilah" ya ce "Dazu kuma sai kika tafi" ta danyi
shiru tana wasa da fingers dinta ta ce "Ehh naje gidansu Ameera ne" ya ce "To
meyasa baki bari kun dawo dasu Ummi ba" ta dan turo baki tana kallansa ta ce "Na
gaji da zama ne kuma naga sunata magana" Jawad ya girgiza kai yana kallanta ya ce
"This is not strictly true, kin daibi Yusuf ne ko?" Ta dago tana kallansa ta ce
"Who told u ni ban bisa ba" ya danyi murmushi ya ce "Nayi karya kenan" ta ce "Ni
bance maka ba" ya ce "To meyasa zaki bishi, bayan kinsan zai baki diyarki" ta dan
hararshi bata ce komai ba, ya mika mata wayarta da side bag dinta sannan ya mike ya
ce "Zan koma" ta ce "Bakaci abinci ba" ya ce "Na koshi, good night" daga haka ya
bar wajen.

*I'm much better today thanks for the care 🥰*

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_19_

Ranar Saturday karfe karfe 11 kowa ya iso kotu, kamar jiya yauma Yusuf sai daya je
ya gaishe dasu Ummi, can gefe ya samu ya zauna yasa Imaan a cinyarsa, Rafi'ah dai
na zaune ta turo baki fuskarta ko walwala babu, sau daya ya kalleta ya dauke kai,
ba 6ata lokaci aka taso keyar su Umma aka kaisu inda aka tanada musu, bayan an gama
komai Alkali yayi sallama ya kuma sanar da kowa cewa yau ne ranar da sukayi
alkawarin cigaba da wannan shari'ah, bayan haka duk lawyers wajen suka mike tsaye
kafin suka zauna, wani lawyer ne ya tashi yana kallan Umma da idanuwanta sukayi
pulu pulu ya ce "Hajiya Fatima ta gamsu da laifin da tai ta kuma kar6a ba tare data
bawa kotu wahala ba, sai dai a wancen zaman ta ambaci akwai wasu wanda suma dasa
hannunsu" jin haka yasa Anty Amina tayi wuru wuru dama da kyar Abba yasa ta tazo,
kuma ita ta titsiyeshi cewar saiya fadamata koma menene yake faruwa ita batasan
boye boye, lokaci daya kuma tsoro duk ya cikata kana kallanta kasan she was
uncomfortable then, Umma dake kallan kowa na court din ta ce "Hakane kam, akwai
mataimaka a harkar da yawa" ya ce "To muna sauraronki Hajiya" tayi shiru sai kuma
ta ce "Akwai kishiyar uwar Rafi'ah wato Amina da kuma yayarta Rahama, suma ba irin
fadi tashin da bazasuyi ba don su hana wannan aure amma a karshe aure ya yiwu, kuma
dasa hannunsu ta fito a gidanta" With much shock kowa na court din yake kallan Umma
da kuma Anty Amina, Abba dai jin abin yake kamar a drama, Anty Amina ta mike cikin
fishi da borin kunya ta ce "Ki rasa wacce zakiwa sharri sai ni Haiiya Fatima,
wallahi karya take ina ruwana da yarinyar da zan mata asiri auranta ya kare, naga
dai Rafi'ah koba aure tsakanina da ubanta 'yatace" ta karashe maganar tana nuna
Umma da yatsa, wani ritaccen tsawa daya daga cikin manyan lawyers din yayi mata,
with much serious ya ce "Malama nan fa ba filin dambe ne, idan baki nutsu ba muna
da maganin irinku" hakan yasa tayi guum da bakinta ta zauna, Abba dai ya kasa cewa
komai sai kansa daya dafe, lawyer din yana kallan su Umma ya ce "To akwai shaida da
zai nuna mana suna da hannu cikin wannan laifin?" Anty Khadija ta ce "Ehh akwai a
wayata" nan Alkali ya bada umarnin a bata waya ta nuna shaidar, handcuff din
hannunta aka cire aka bata wayar, ba 6ata lokaci muryar Anty Amina ya bayyana cikin
wayar lokacin da Anty Khadija taje mata, da kuma irin abinda takeso ya faru a
rayuwar Rafi'ah, bayan ya kare Anty Khadija tasa wani sanda suka fara zuwa wajen
bokan, ga muryarta nan radau kanaji tana bayani, mikewa Abba yayi ya hau kikkifa
mata mari yana cankinta, Daddy da wani police suka rikeshi, nan itama aka saka mata
handcuff akayi wajen su Umma da ita, sai kuka take tana sharrin shaidan ne, kukan
Rafi'ah yafi na kowa kara a wajen, Ummi dai banda share hawaye ba abinda take, haka
Mummy ma, shidai Yusuf na zaune kamar an dasa shi a wajen, duk Jawad ma jikinsa
yayi mungun sanyi, rubuce rubucen da yake sai na gefensa ya bawa, lawyer din ya
kalli Anty Amina dake kuka ya ce "Ke kuma menene dalilinki na yin hakan? Meyasa
kika za6i ki raba ma'aurata" cikin kuka Anty Amina ta ce "Wallahi kishi nakeyi, ina
bakincikin naga sun karu da wani abu, nafiso kullum na gansu cikin wahala, kuma
gashi ni ban haihu ba kusan shekara 7 kenan yanzu, ko 6ari ban ta6a yiba, kuma ba
irin magungunan da uwata bata bani ina sha amma shiru ba labari" Lawyer ya danyi
murmushi ya ce "Yanzu kenan kun amsa laifinku a hannu" Anty Khadija na hawaye ta
daga masa kai, bayan haka Alkali yayi rubuce rubuce ya mikawa wani daga gefe,
mikewa mutumin yayi ya ce "Kotu tayi alkawarin kamo sauran masu laifin kamar yadda
aka zayyana, sannan zatai musu hukunci dai dai da abinda suka aikata nan da sati
daya, sannan kotu ta kar6arwa Yusuf Muhammad duk wani dukiyarsa dake hannun uwar
rikonsa haka zalika zasu ci gaba da zama gidan horo har ranar da za'a yanke musu
hukunci" kuka me karfi Anty Amina ta saki tana kallan Anty Khadija ta ce "Kin
cuceni Khadija, duk ke kikazo kika kara rikirkita al'amuran, da baki zo ba nasan da
bankai ga haka ba, wayyo Allah Ummana naga ta kaina" tasa keyarsu akai police suka
fita dasu, Rafi'ah ta mike da sauri tayi wajen Abbanta ganin har rikeshi ake zai
daki Anty Amina da zasu wuce, rungumeshi tayi ta fashe da kuka ta ce "Abbana" Abba
ya rungumeta yana share hawayen idansa da suka ki tsayawa, tinda yake bai ta6a
shiga kunci da tashin hankali irin na yau ba, Ammi ta dinga share idanta tana rike
da hannun Yusuf daya kasa motsi sai hawaye dake gangarowa idansa, mikewa yayi a
hankali ya nufi kofar fita da baya ma kallan gabansa sai duhu kuma idanuwansa a
bude suke, basu ankara ba kawai sukaji yayi collapsing a kasa, Ammi ta mike da
sauri tana jijjigashi hade da kiran sunansa, Sameer yayi kansu yana masa addu'a
ganin ko motsi baya yi, kuka Imaan ta saki tana rike da hannunsa tana fadin "Papa
wake up" da taimakon mutanen wajen aka fita dashi aka sakashi a mota, jin Rafi'ah
tayi shiru yasa Abba ya dagota a jikinshi, a razane yake kallanta ganin suma tayi
lokaci daya, ya dagata kamar Baby yana jijjigata suka fita da ita.

_7 hours ltr_
Dawowansu kenan a asibiti bayan an sallamosu, Ammi na hada masa tea yana kwance
akan 3 seater duk idanuwansa sun juya launi zuwa jaa sosai, ya limshe idanuwansa
yana kallan Ammi ya ce "I want to bath first" Ammi ta ce "Ka sha tea din mana sai
kasha magani, kuma alluran ma ai bai gama bin jikinka ba, da dai ka bari zuwa karfe
9pm sai kayi wankan" kai kawai ya gyada mata ya tashi ya zauna, ta mika masa tea
din ya kar6a ya rike a hannu, Ammi ta zauna gefensa ta ce "Ka sha mana" a dole ya
kai tea din bakinsa dan bashida appetite, da kyar ya sha kadan ya ajiye mug din kan
center table ya koma ya kwanta, Ammi ta kamo hannunsa tana masa nasiha hade da
kwantar masa da hankali.
Washegari karfe 10am Rafi'ah ta fito a dakin Ummi bayan tayi wanka, ita kam jikinta
da sauki sosai, sai ciwan ai kadan kadan, jikinta duk a sanyaye ta karasa parlorn
da Abba ke zaune Ummi na gefensa, ta dayan side din kuma Mummy ce zaune taci kuka
harta godewa Allah, a hankali Rafi'ah ta kalli Abba dake zaune yayi shiru,
idanuwansa sun kada sosai, bata ta6a ganin Abbanta cikin tashin hankaki iri haka
ba, murya caan kasa ta ce "Ina kwana Abba" ya dan kalleta cike da damuwa ya ce
"How are u daughter?" Ta ce "Fine" Rafi'ah ta gaishe dasu Ummi ta zauna a wajen,
kukan Imaan da sukaji a daki yasa Ummi ta mike ta shiga dakin, wanka ta mata tayi
brush sannan ta shiryata suka fito, Ummi ta kalli Rafi'ah dake gefen Abba ta ce
"Kije kiyi breakfast mana" mikewa tayi a hankali Ummi ta mika mata Imaan suka wuce.
karfe 11 Abba ya ce "Suje su duba jikin Yusuf dan an maidashi asibiti ana kara masa
jini" duk jikinsu yayi sanyi musamman Rafi'ah da idan ta tuna rashin kunyar data
masa jiya sai kuka yazo mata, key din mota Abba ya dauka duk suka bi bayansa dama
ko wacce da hijabinta, har suka isa clinic din baifi sau 3 sukai magana ba shima
Imaan ne duk tayi causing,
Bayan Abba yayi parking suka fito suka shiga ciki, Daddy ne da wasu 'yan uwan
mahaifin Yusuf da suka iso da safe su 3, bayan sun gaisa Daddy yace su shiga ciki,
a kwance suka sameshi yana bacci ana kara masa jini, gaba daya ya gama ramewa sai
haske daya kara sosai, Ummi dai juyawa tayi ta fita, Mummy ta masa addu'ah itama ta
juya, Imaan nata kallansa a tsorace sai dai ba tai magana ba, bayan few minutes
Abba ya fita dakin ya rage daga shi sai Rafi'ah sai kuma Imaan, Hawayen idanta ta
share ganin ko numfashi da kyau baya yi, taja kujera ta zauna a gefen gadon, bude
ido yayi jin karan kujeran, suna hada ido ya maida kansa gefe hawaye na gangaro
masa, daurewa tayi ta ce "How are u" da kyar ya daga mata kai, Imaan ta kalli
Rafi'a dake kuka a hankali ta ce "Momma is Papa sick?" Juyawa Yusuf yayi ya kamo
hannunta ya ce "But i recovered dear, i missed u yesterday" dan murmushi tayi ta ce
"I missed u too" mikewa Rafi'ah tayi ta fita a dakin har lokacin kuka yaki tsaya
mata. Har dare Yusuf yana asibitin, Ummi ta koma gida tayi dinner ta kawo musu,
Mummy dai na tare da Ammi, sai Sameer da Rafi'ah, su Abba kam tintini sun koma da
Ummi, tindaya farka da safe ya koma bacci bai sake tashi ba, jininma daya kare suka
kara saka masa wani, karfe 9 Ammi da Mummy suka tafi salla, Sameer ma tinda ya fita
sallan Isha bai dawo ba, Rafi'ah na zaune ta buga uban tagumi ta kuma yi nisa a
duniyar tinanin data tafi, jin tarin da yayi yasa ta mike ta karasa kusa dashi, ta
ce "Sannu" ya ce "Uhm" zama tayi a akan kujerar dake gefen gadon, silently ta ce
"How are u feeling now?" Ya ce "Alhamdulilah" ta share dan guntun hawayenta ta ce
"I'm sorry with what happened yesterday, i shouted at u which is not fair dan Allah
ka yafemin" Yusuf ya mike da kyar ya zauna ya jingina da bango yana kallanta ya ce
"Ba komai ya wuce, and u forgive me too, i cause too much pain in ur life" a
hankali ta girgiza kai ta ce "They did but not u" shiru yayi yana kallan hannunsa
daya kumbura saboda neman vains, a hankali ya ce "Imaan fa?" ta ce "Sun tafi gida
da Ummina" ya ce "Ohk" juyowa yayi suka hada ido tayi saurin sauke nata idon, ya ce
"Bani ruwa" ta mike a sanyaye ta nufi Fridge din dakin ta dauko bottle water sannan
ta wanke cup din ta xuba masa, zama tayi a bakin gadon har ta kai cup din bakinsa
sai kuma ta mika masa a dayan hannun, ya kar6a ya sha kadan sannan ya mika mata ta
ajiye a gefe, komawa tayi gefe ta zauna kanta a kasa, Yusuf ya dan kalleta ya ce
"Did u forgive me?" Da sauri ta kalleshi sai kuma ta daga masa kai tana share
hawayen idanta ta ce "Yes i did, Allah ya yafe mana gaba daya" ya ce "Ameen" bude
kofar dakin akai wani Dr ya shigo, suka gaisa da Yusuf ya masa ya jiki, ganin
hannunsa ya kumbura ya ce "Bari a canza maka hannun ya huta" daga haka ya kashe ya
maida masa dayan hannun sannan ya kunna yana masa sannu, daga haka ya fita a dakin,
sun kai minti 5 a zaune kowa da abinda yake sakawa cikin ransa, ya dan kalleta ya
ce "Pls help me with some water" ta mike ta dauko ruwan dazu ta mika masa, yana
kar6a hannunsa yayi kasa cup din zai fadi tayi saurin rikewa, sai lokacin ta tuna
hannunsa da ciwo, kamar baza tai ba kuma ta kai cup din bakinsa tana bashi ruwan,
hakan yasa ta kauda kanta gefe bata bari sun hada ido ba, bude kofar dakin akai
Jawad ya shigo rike da babban leda a hannunsa me dauke da fruits kala kala, yayi
saurin dauke kansa ganinsu a haka, itama da sauri ta zare cup din a bakinsa ta
ajiye a gefe kanta a kasa, Jawad ya karaso cikin dakin yana kallanta ya ce...

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_20_

Jawad ya karaso cikin dakin yana kallanta ya ce "Ya gama shan ruwan ne?" Ba tare
data kalleshi ba ta daga masa kai, Ya ajiye ledan hannunsa yana kallan Yusuf ya ce
"How are feeling now?" Yusuf ya ce "Alhamdulilah" Jawad yaja kujera ya zauna ya ce
"Allah ya sauwake" ya ce "Ameen" zaro wayarsa a pocket yayi yana dannawa, kusan
minti 10 suna zaune kafin ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Ina Imaan?" ta ce
"Tana gida" bude kofar dakin akayi Ammi da Mummy suka shigo, Jawad dake kallansu
yayi murmushi suka sake gaisawa da Ammi ya ce "Ya mai jiki?" Ta ce "Da sauki sannu
da kokari, Allah ya maka albarka" Sameer ne ya shigo dakin rike da ledan Apple,
Mummy ta ce "Jawad muje ko?" Ya ce "Ohk to" kallan Yusuf yayi ya ce "Allah ya
sauwake" Yusuf ya amsa da "Ameen" daga haka ya fita, Mummy ta ce "Hajiya sai gobe
Allah ya yaye masa" Ammi ta ce "Ameen, Allah ya kaimu" mikewa Rafi'ah tayi tana
kallan Ammi ta ce "Allah ya sauwake Ammi" ta ce "Ameen, mungode" ta gefen ido ta
kalli Yusuf ta ce "Sai da safe" bata jira ya amsa ba ta fice a dakin Mummy tabi
bayanta, a parking space suka sami Jawad yana zaune a mota, Rafi'ah ta shiga front
seat Mummy kuma ta shiga baya, kallan Mummy yayi ta mirror ya ce "Yau kam gida zan
kaiki ko?" Mummy ta ce "Aa sai gobe zan koma, danma jikin Rafi'ah da sauki" ya
danyi murmushi yaja motar suka tafi ya ce "Mami tace ai yau zatazo duba Fatima nace
bata gida" Mummy ta ce "Gobe idan ka kawota sai mu koma, shi dai Sadeeq bazai shiga
mutane ayi komai dashi ba, kullum yana wajen abokai suna yawan banza" Jawad ya ce
"Day before yesterday ma Mummy sai dana masa magana, bayasan shiga mutane saam"
Mummy ta ta6e baki ta ce "To watakila zai daina, kai naka ada ai saida mukaita
rokon Allah, gara shima yana shiga abokai" Jawad ya shafa kansa yana murmushi, ita
dai Rafi'ah tana zaune tayi shiru, bayan 10 minutes suka karasa gida, Jawad yayi
parking a waje Mummy ta fito ta ce "To saida safe" daga haka ta shiga ciki, kamo
hannun Rafi'ah yayi cikin sanyin murya ya ce "Dear kinyi shiru" ta danyi murmushi
ta ce "Ba komai" sai kuma ta sauke kanta kasa, ya gyara mata hijab din jikinta ya
ce "Ohk, kici abinci sosai, sai ki kwanta" a hankali ta ce "Pls kayi hkr abinda
nayi dazu, naga hannunsa da ciwo ne kuma..." Duk da baiji dadin abinda ya gani ba
amma ya danyi murmushi ya daura Finger dinsa akan lips dinta ya ce "U don't have to
explain, ba komai" murmushi ta sakar masa ta bude kofar zata fita ya ce "Good
night" ta daga masa hannu ta rife kofar sannan ta shiga ciki. Washegari karfe 12
Yusuf na zaune akan gadon asibiti yana lunch Khairiyya ta fito a toilet, ta zauna
gefenshi ta ce "Ya jikin Yaya?" ya ce "Lafiya lou" ta ce "Baka jin komai?" Ya ce
"Naji sauki" dan murmushi tayi tana kallansa ta ce "Yaya Nabeel ya kusan dawowa,
tare zamu koma inji Daddy, in fara makaranta shi kuma yana Masters dinsa" Yusuf
dake jujjuya abincin hannunsa da spoon ya ce "Ina din?" Ta ce "America mana"
girgiza kai yayi ya ce "No, ba dai keba, dan bazaki jeba" ta ce "But Daddy yace
idan inaso inje fa Yaya" ya ce "Ki bari ki nema admission anan, i think it will be
good for u, it's not safe mace karama irinki ta tafi wata kasa karatu" dan 6ata rai
tayi ta ce "To ai angama bada admission Yaya" ya ce "Then u wait till next year"
bata daice komai ba ta mike ta fara diban abinci tana hade rai. Kwanciya Imaan tayi
saman carpet taki kar6an Apple din da Rafi'ah ke mika mata, Rafi'ah ta zare mata
ido ta ce "Will u collect it like this or no?" kamar zatai kuka ta noke kafada ta
ce "That's not how Papa used to gave me" cikin fishi Rafi'ah ta bar wajen ta shige
dakinta, Imaan ta fashe da kuka tana shamba kafa hade da kiran Papa, Abbane ya fito
a daki ya dauketa yana jijjigata ya ce "Me aka miki haka little Fatee?" cikin kuka
ta ce "I want to eat Apple" Abba ya dauki daya daga cikin Apples din kan plate ya
bata taki kar6a, ya ce "Ba kyaso ne kuma?" Ta dan turo baki ta ce "Daddynah yana
yankamin ai, not that Daddy with Blue car, the fair one" sai kuma ta kara 6ata
fuska ta ce "And he was sick" dakin Rafi'ah Abba ya bude ya sameta kwance tana
waya, tayi saurin mikewa ganinsa, ya ce "Jeki yanka mata ki bata, ya za'ai ki barta
kuma tana kuka mamana?" Hannun Imaan ta kama kamar zata fashe da kuka ta ce "To
Abba sai tace ita sai abinda takeso, tin dazu nake mata hidima kamar wata baiwa"
Ummi da shigowanta dakin kenan ta dalla mata harara ta ce "To karkiyi idan kinga
dama, nan kika kafa mana kuka sanda ubanta ya dauketa, yanzu common ki yayyanka
mata Apple zakice kina mata hidima, ai ke ba'a miki ba da kina karama girma kawai
kikai" daga haka ta kama hannun Imaan dake share idanta, Abba ya ce "To menene abin
fada anan kuma Madam?" Ummi ta ce "Saita zauna ai idan taga dama ta shekara tana
kwance" daga haka ta fita da Imaan, Abba ya kalli Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce
"Are u happy with what u did?" Ta girgiza masa kai, ya ce "Ki daure kina mata
abinda takeso kinji mamana, ke kinsan irin rigimar da kikai ne?" Ta danyi murmushi
ta boye fuskarta da head tie dinta, Abba yayi saki murmushi ya nufi kofar fita ya
ce "Allah ya miki albarka".
Karfe 1:30 Mami tazo ta duba Rafi'ah, ta kawo mata fruits iri da kala, sun jima
suna hira da Ummi kafin Sadeeq yazo ya dauketa, karfe 3 Ummi ta gama shirya basket
din asibiti, Rafi'ah ta fito sanye da hijab tana kallan Ummi ta ce "Ke baza kije
ba?" Ummi ta ce "Naga da safe naje, kuma munyi waya da Ammin tace may ba a
sallamosu yau da daddare" Rafi'ah ta ce "Ohk" Ummi ta ce "Zaki tafi da Imaan ko?"
ta wani hade rai tana kallan Ummi ta ce "Gaskiya ni zata takuramin Ummi, naga itama
dazu da ita kikaje, yanzu mafa da kyar na samu na bata wayana kafin tayi shiru"
Ummi ta ta6e baki taci gaba da kwashe abinci a warmer, Rafi'ah ta dauki basket din
ta ce "Saina dawo" Ummi ta ce "A dawo lpy" daga haka ta fita zuwa parking lot
Mustapha yaja suka bar gidan.
Within few minutes suka iso asibitin, Mustapha yayi parking sannan ta fito ta shiga
ciki, da sallama ta tura kofar dakin ta shiga, Sameer ya dago kai yana kallanta
sannan ya amsa, Yusuf na kwance akan gadon yana kallan ceiling, by now babu komai a
hannunsa jininma ya kare, ya mike a hankali ya zauna yana kallanta, sauke idanta
tayi ta ajiye basket din a gefe ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau" ta ce "Ya
jikin?" Ya ce "Da sauki" kallan Sameer tayi dake danna wayarsa ta gaishe shi ya
amsa mata da fara'ah ta ce "Ammi fa?" Ya ce "Basu jima ba suka koma gida ba ita da
Khairi" ta ce "Ayyah" shiru tayi ta zauna caan gefe, wayar Yusuf dake gefenta ne ya
fara ringing, ta kalli screen din sannan ta dauke kai, harya katse shima Yusuf
baibi ta kan wayar ba, aka sake kira for d second time Rafi'ah ta ta6e baki ta kara
kauda kai, Yusuf ya bude idanuwansa dake limshe yana kallan wayar ya ce "Pls help
me with the phone" ta dauki wayar ta mika masa sannan ta koma kan kujeran ta zauna,
a hankali yayi picking call din ya ce "Jiddah" ta fashe masa kuka ta ce "Wai meyasa
baka kula dani ne Doctor, ko bakasan abinda ke cikina ne? u just left us aside
kamar bamu da hakki akan ka" Yusuf ya ce "Banajin dadi we will talk ltr or
tomorrow" daga haka ya katse wayar ya kashe phone din baki daya, mikewa Sameer yayi
yana kallansa ya ce "Bari naje waje na huta Doctor" Yusuf ya ce "Ba komai, a huta
lpy" daga haka Sameer ya fita, kusan minti 2 basuce komai ba, kowa yana zaune inda
yake, Yusuf ya sauko a kan bed yana gyara zaman rigarsa ya nufi toilet a hankali,
gaba daya jikinsa yayi weak, yana isa bakin kofar yayi saurin riko handle din jin
zai fadi, Rafi'ah ta ce "Subhanallah" hannu ya daga mata alamar ba komai sannan ya
shiga toilet din ya rufo kofar, bayan few minutes ya fito a toilet din, still dai
he's not normal wani jiri yaji ya debeshi, Rafi'ah tayi saurin rikoshi ya fada
jikinta, sai da sukai kamar zasu fadi sannan yayi karfin hali ya riko kujera suka
fadi a nan wajen, bude kofar Jawad yayi ya shigo da sallama, Rafi'ah rayi saurin
janye jikinta daga nasa ta matsa gefe, karasowa Jawad yayi yana kallan Yusuf ya ce
"Are u ok?" Yusuf ya daga masa kai ya ce "U pls help me to my bed" Jawad ya kamashi
ya mike sannan suka karasa kan gadon ya zauna, Rafi'ah na zaune kan kujeran kanta a
kasa, kirjinta banda bugawa babu abinda yake, Jawad ya zauna a kan karamar kujera
dake gefen bed din ya ce "Amma ya jikin?" Yusuf ya ce "Da sauki" Jawad ya ce "Masha
Allah, yau an gama kama duk wani wanda yake da hannu a tafiyarka, sannan takaddun
filayenka da gidajenka na wajen Umma yana office dina, dukda bincike ya nuna akwai
abubuwa da dama da suka siyar, gobe insha Allah zan kawo maka takardun, abinda
sukai amfani dashi ko suka siyar ka barsu da Allah, that's your own destiny in
life, Allah kuma ya kara tsaremu daga sharrin masu hali irinsu, and i wish u quick
recovery" sauke ajiyar zuciya Yusuf yayi ya kamo hannun Jawad dake gefensa ya ce "I
don't know the words i will used to thank u Barrister, u have been there for me
right from the beginning till end, jazakallahi khairan, u made so much to me which
i can never pays u back, ka zamo gatan yarinyana a lokacin da take neman soyayyar
mahaifi, ka bata gata wanda ko a wajena inaga da wuya ta samu kamarsa, u are a real
man Ahmad, abinda ya faru a baya ka yafemin" Murmushi Jawad yayi me kyau yana
kallansa ya ce "Allah ya yafe mana baki daya" Yusuf ya ce "Ameen" mikewa Jawad yayi
ya basa hannu ya ce "Allah ya sauwake sai goben" daga haka ya nufi hanyar fita,
yana fita Rafi'ah tabi bayansa da sauri, a parking lot ta sameshi tsaye yana
kokarin bude mota, ta ce "Yaya zamu tafi tare" sau daya ya kalleta ya dauke kai,
nan da nan idanuwanta suka cika da kwalla, ta ce "Kayi hkr, wallahi faduwa zaiyi
shine na rikesa, i didn't do it intentional" ko ya daga kai ya kalleta, ta fashe da
kuka ta dora kanta a bayansa ta ce "Wallahi i love u Yaya, i love u more than
anyone else, pls don't leave me here" ta kankameshi tana kuka sosai and she didn't
mind the way people are looking at them.

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_21_

A hankali Jawad ya zame hannayenta a jikinshi ya juya yana kallanta ya ce "And why
are u crying?" Ba tare data kalleshi ba ta ce "Naga kamin fishi ne" ya sauke ajiyar
zuciya ya ce "Shiga mu tafi ya wuce" dan murmushi tayi ganin shima ya mata
murmushi, ta zagaya ta bude front seat ta shiga sannan ya tada motar suka bar
clinic din, juyowa Jawad yayi yana kallanta ya ce "U didn't wipe your face clearly"
turo baki tayi tana kallansa ta ce "Na share mana" murmushi yayi yaci gaba da
driving ya ce "Ohk, i called u but u refuse to pick" dan zaro ido tana goge sauran
hawayen idanta ta ce "Why did u used the word refuse?" Ya ce "Uhum naga kamar yanzu
bakyasan daukan wayana ne" girgiza masa kai tayi ta dan hade rai, ya sakar mata
murmushi yana kallanta ya ce "To kiyi hkr, amma meyasa baki daukan wayana?" A
hankali ta juyo tana kallansa idanuwanta tap da hawaye, kamar batasan yin magana ta
ce "Is not like u think Barrister, jiya Imaan tayi tamin kuka ban kwanta da wuri
ba, inaga sanda nayi bacci ka kira, yau ma kuma wayar na hannunta na taho" Ya ce
"Ohk, how is she?" Ta ce "Lafiya take" daga haka ta share kwallan idanta. A bakin
gate dinsu yayi parking ya jiyo yana kallanta ya ce "I will come back in the night"
ta ce "Allah ya kaimu, baza kaga Imaan ba?" Ya ce "No, ina sauri zan koma office ne
yanzu, idan nazo anjima zan ganta" ta ce "Thank u" ya ce "Mention not" fita tayi ta
daga masa hannu sannan ta shige gate, ya danyi murmushi yaja motar ya wuce.
bayan sallah Magrib aka sallami Yusuf, Daddy yazo ya daukesu suka koma gida, suna
isa Ammi ta hada masa ruwan wanka ya shiga yayi, da towel ya fito a kunkuminsa ya
zauna bakin gado, Khariyya ta bude kofar dakin ta shigo hannunta rike da fruits
salad cikin dan bowl, zaro ido tayi ganinsa a haka ta juya da sauri, ya danyi
murmushi ya tashi ya dauko kayansa ya shirya, kwanciya yayi akan gadon ya kunna AC
ya limshe idanuwansa. Bude kofar dakin tayi a slowly tana lekawa, ganin ya shirya
ta karasa cikin dakin ta zauna a gefensa tana murmushi ta ce "Yaya" ya bude
idanuwansa yana kallanta, ta ce "Me zakaci na dafa? na hada maka fruits salad"
murmushi yayi yana kallan bowl din ya ce "Thank u, ba sai an dafa komai ba wannan
ma ya isa" ta dora hannunta akan goshinsa ta ce "Allah ya sauwake" ya ce "Ameen"
daga haka ta ajiye masa bowl din a gefensa. Rafi'ah na zaune a dakinta tana shafa
powder kiran Jawad ya shigo wayarta, ta danyi murmushi tayi picking call din, ya ce
"Dear" ta ce "Uhm" ya ce "Nazo amma zan shiga mosque, an kira isha" ta ce "Ohk to
sai ka idar" ya ce "Alright" katse wayar tayi ta ajiye a gefenta taci gaba da
abinda take, sosai tayi mungun kyau sai kamshi take, ta dora dankwalinta sannan
tasa hijabi tayi sallah, tana idarwa tayi addu'a ta cire hijab din ta yafa babban
veil, call din Jawad ne ya kara shigowa phone dinta, tayi picking hade da sallama,
ya ce "I'm done" ta ce "Ohk ka karasa BQ" ya ce "Why not inda muka saba zama?" Ta
ce "Akwai sanyi a waje ai kuma da hadiri" ya ce "Ohk to" hanging call din tayi ta
fita a dakinta zuwa dakin Ummi, a hankali ta tura kofar dakin ta shiga, suna zaune
akan gado ita da Imaan, Rafi'ah ta sauke kanta kasa ta ce "Dama yazo ne?" Ummi ta
ce "Waye?" Dago kanta tayi ta kalli Ummi sannan ta ce "Ya Jawad ne" Ummi ta ce
"Ohk" mikewa Imaan tayi ta nufeta da gudu ta ce "Fita zakiyi?" Rafi'ah ta kama
hannunta suka fita a dakin. Har suka isa BQ Imaan na tambayarta fita zasuyi, bude
kofar parlorn tayi suka hada ido dashi, tayi saurin sauke kanta tana murmushi,
Imaan ta nufesa da gudu ta dale jikinsa ta ce "I missed u Daddy" ya rungumeta yana
kallan Rafi'ah dake tsaye ya ce "How are u beauty?" Ta ce "Fine Daddy" ledan
chocolates din daya kawo mata ya mika ya ce "This is yours beauty" tana dariya
sosai ta ce "Thank u Daddy" daga haka ta mike a jikinshi tana kallan Rafi'ah ta ce
"Bari na nunawa Ummina" daga haka ta fice a parlorn. Kallan Rafi'ah yayi dake tsaye
bayan kujera ya ce "Yau a tsaye zamuyi hiran ne?" Ta sauke kanta kasa bata ce komai
ba, ya ce "Ko saina daukoki?" Taki kallansa kuma bata ce komai ba, ganin ya taso
yasa tayi saurin zagayowa ta zauna akan kujera, ya zauna a gefenta ya ce "Kinyi
kyau sosai" silently ta ce "Thank u" ya dan wara ido ganin ring din daya bata ne a
hannunta ya ce "Ya maki kyau" ta danyi murmushi tana kallansa ta ce "Bayan oversize
ka bani sai kwanan nan yamin dai~dai" ya kamo hannunta yana kallan ring din ya ce
"Uhm, ai ba laifi bane tinda dama bansan size dinki ba then, amma yanzu duk abinda
zan siya ma..." Hannunta tasa ta rufe bakinsa ta ce "Ai naga dai ba kai na gayawa
ba Anty Na'ima ne" zame hannunta yayi a bakinsa ya ce "Aita fadamin, kuma dani ake
zuwa siyo komai" dan harara ta mishi ta kauda kanta gefe, ya danyi murmushi yana
shafa kansa ya ce "Let me ask u something, banasan kuma ki fadamin abinda ba haka
bane a zuciyarki" a hankali ta juyo tana kallansa, ya ce "Kinasan ki koma gidan
Yusuf?" With shock ta kara kallansa sai kuma ta sauke kanta kasa, ya ce "Talk to me
Fatima" fadawa tayi jikinshi ta fashe da kuka, ya bubbuga bayanta ya ce "I didn't
ask u to cry, tashi ki fadamin" dago kanta tayi a kirjinshi ta ce "Ni banaso kuma"
ya ce "Are u sure?" ta daga masa kai hawaye na sakko mata ta ce "Insha Allah i will
finish my whole life with u, I thank God every time because He gave me you, ka sani
farinciki a lokacinda bani da kowa, duk da ba laifinsa bane wallahi i can't stay
with him anymore" ta kara maida kanta kirjinsa cikin sanyin murya ta ce "I had my
heart broken during my first love, But when I think of it....." Kuka sosai ta
fashe dashi, yana jin yadda hawayenta ke sauka a jikinshi, ya bubbuga bayanta ya ce
"It's ok, ni bance kimin kuka bafa" silently ta ce "My future will be Good with u
insha Allah, shima Allah ya bashi wacce zata so shi tsakani da Allah" sai kuma ta
dago tana kallansa ta danyi murmushi ta ce "You are my first love and you will
certainly be the last". Murmushinsa me yayi ya kara bata light hug ya ce "I luv u
more" ta sakar masa murmushi ta matsa a gefensa ta ce "Dama kenan haushina kakeji
ko?" Ya wara ido yana kallanta ya ce "No niba haushinki nakeji ba" ta dan turo baki
ta ce "Hakane mana" matsowa yayi kusanta ya zaro handkerchief a pocket dinsa ya
shiga share mata sauran tears dinta, bayan ya gama goge mata tass ta juyo tana
kallansa ta ce "Inasan kamshin perfume din nan" silently ya ce "Nasa maki a kayan
auranki ma" tayi saurin rife idanuwanta tana dariya a hankali, murmushi yayi ya
mike ya ce "Zan tafi Baby, akwai abinda zanyi sannan kuma gobe karfe 6 zan fita" ta
bude fuskarta ta ce "Safe, amma pls Yaya Anty Na'ima ta fada maka maganan da mukai
da ita" ya ce "Ehh mana, ta fadamin komai" pillow ta wurga masa ta ce "To wallahi
bada kai za'aje siya ba" ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce "Na nawa kuma, har
mun gama cika akwatin ma" pillow ta sake jefa masa ta ce "To nayi fishi ma" ya
durkusa dai dai fuskarta yana dariya ya ce "Gobe da Yamma zamuje ki gaishe da Mami"
ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ya nufi kofa tabi bayansa, har mota ta rakashi
tana ta daga masa hannu ya tafi. Washegari Yusuf na zaune a daki bayan yayi
breakfast Khairiyya ta shigo, ya dago yana kallanta ya ce "Ina zakije?" Ta ce
"Kamar ya?" Ya ce "No naga kinyi kwalliya ne" ta danyi murmushi ta zauna gefensa ta
ce "Yaya kasan menene?" Ya ce "Sai kin fada" rife idanuwanta tayi ta ce "Dama fa
wanine na hadu dashi a wajen Jamb, he's so kind and humble so shine yace wai zaizo
mu gaisa, na bashi address" tinda ta fara magana yake kallanta, ya sauke ajiyar
zuciya yana kallanta ya ce "Kin fasa yin karatun ne kika fara soyayya?" Bude
fuskarta tayi ta ce "No ban fasa ba, amma yace wai zaijira na gama" Yusuf ya danja
tsaki ya ce "Karya yake, ba namijin da zaice zai jira mace ta gama karatu bayan ba
farawa tayi ba kuma nasan babbane" ta ce "Yess he's 33 but yace wallahi zai jirani"
ya girgiza kai ya ce "That won't be possible, idan auranki zaiyi ya aureki sai kiyi
karatun a gidansa idan kuma ba haka ba ya tafi ya kyaleki" da mamaki take kallansa
ganin yadda yaci serious, ta ce "Amma Yaya ni sai nayi aure yanzu, i'm just 17 fa"
harara ya dalla mata ya ce "And if u are just 17 what makes u to fall in love with
someone" ta dan zaro ido sai kuma ta ce "To ai na kai" ya ce "Aurene baki kai ba
kenan?" Ta ce "Uhm" mikewa tayi jin wayarta na ringing a dakinta, ta dan kalleshi
ta ce "Amma pls Yaya karka gayawa Ammi, yau ne first day da zamu hadu kuma na kasa
gaya mata" ya ce "Baza taji ba" daga haka ta juya tana murmushi ta fita, tana fita
ya mike ya wuce parlor ya kulle kofar da key sannan yasa key din a pocket dinsa ya
dawo ya kwanta, hanging wayar tayi ta yafa dan karamin veil dinta sannan ta fito a
daki, leka dakin Yusuf tayi ta ce "Yaya saina dawo" ya daga mata kai yana murmushi
ya ce "My regards to him" daga haka ta juya ta koma parlor, murda handle din tayi
amma taji a rufe, ta duba taga ba sakata key ne, kamar zatai kuka ta koma dakin
Yusuf ta ce "Dan Allah ka bani key din Yaya" ya ce "Key din me?" Ta ce "Na kofar
parlor" ya ce "To bansan inda yake ba" ta tsaya tana kallansa irin na rashin yardar
nan ta ce "Wallahi kaine ka rufe" ya mike tsaye yana kallanta ya ce "May be Ammi ce
ta rife" ta kalli wayarta dake ringing ta ce "Na shiga 3 Ammi dake bacci kuma Yaya,
daga nifa sai kaine Ya Sameer baya nan" ya ce "May b taji kina fada" ta durkusa a
kasa tana hawaye ta ce "Yanzu ni mezance masa Yaya" ya ce "Bani wayar" ya kar6a
wayar ya bar wajen ya koma parlor, picking call din yayi ya kai kunne, mutumin ya
ce "Baby" Yusuf ya ce "U pls stay away from my wife, wani satin za tai aure sbd
haka ka kyaleta karka sake kiranta, if not duk abinda ya faru fa kai is your fault"
bai jira yaji abinda zaice ba yayi hanging call din ya koma daki, a zaune ya sameta
akan carpet tana ta share hawaye, ya ce "Na bashi hkr" ta ce "Da gaske, ya kuma
hakura?" ya daga mata kai ya ce "Ehh" bell sukaji an danna Yusuf ya mike ya fita
parlor yaga ta biyo bayansa, juyawa yayi ya ce "Daukomin wayana a daki" ta ce "To
waye Yaya?" Muryar Daddy sukaji yana fadin "Open the door Fatima" da sauri ta ce
"Bari na tashi Ammi ta bani key di..." Ganin Yusuf ya zaro key a pocket dinsa yasa
ta saki baki tana kallansa, bude kofar yayi Daddy ya shigo, Yusuf yayi kasa da
kansa ya ce "Sannu da dawowa Daddy, ina kwana" Daddy ya ce "Lafiya Yusuf, naje
morning meeting ne kana bacci" ya ce "Sannu da dawowa" kallan Khairiyya Daddy yayi
ya ce "What's wrong with u?"

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_22_

'Bata fuska Khairiyya tayi ta koma dakinta ranta a 6ace, Yusuf ya danyi murmushi
yana shafa kansa, ganin Daddy ya shiga daki ya nufi dakinta yana dariya, a hankali
ya bude kofar dakin ya hangota caan karshen gado tana kuka, ya maida kofar ya rufe
ya karasa inda take yana murmushi ya ce "Ya akai Khairiyyan Yaya?" Fashewa tayi da
kukan bakin ciki ta ce "Ni karka sakemin magana Yaya, mena maka daza ka hanani fita
wajensa" side hug ya bata cikin rarrashi ya ce "It's not safe dear, naga baki
sanshi ba, kullum waya kuke bakisan ya halinsa yake ba, watakila ma guduwa yazo
yayi dake" ta dan zare ido tana kallansa ta ce "Guduwa kuma Yaya?" Ya ce "Uhmm, an
gaya maki kidnappers suna da kama ne" jikinta ne yayi sanyi sosai, ta share guntun
hawayenta ta ce "Kuma hakane, Allah ya kara karewa" ya ce "Ameen, kimayi deleting
contact dinsa" ta daga masa kai da sauri, ya ce "kisa a black list ma" ta ce "Ohk"
shiru tayi tana kallan Yusuf dake kallant ta ce "But Yaya what if he's innocent?"
Ya ce "Just do what i said now" ta dan ta6e baki tasa number a black list sannan
tayi deleting baki daya, duk yana kallanta harta gama, ta dago kanta tana kallansa
ta ce "Yaya meyasa bazaka dawo da Anty Fatima ba?" Ya danyi murmushi yana girgiza
kai ya ce "Kefa kika cemin ta kusan aure?" Ta ce "Yes, but nasan Ya Jawad zai
hakura ya baka indai kaso hakan" kanta ya dora akan shoulder dinsa ya ce "Sankai
kikeso nayi, ai Allah yace musowa 'yan uwanmu abinda muke sowa kanmu, kuma suna san
junansu is hardly nace ta dawo ta yarda, and u know what?" Ta girgiza masa kai ya
ce "Koda tace zata dawo bazan iya ba saboda Ahmad, he sacrificed alot Khairiyya
wallahi da inada wani abin dazan saka mishi bayan Rafi'ah da zanyi, but haryanzu
ina tinanin zan bashi Imaan idan har yanaso" Khairiyya ta danyi murmushi ta dago
tana kallansa, sai kuma ta dan 6ata fuska ta ce "Yanzu shikkenan Yaya kun rabu?" Ya
ce "No akwai zumunci Khairiyya, ga kuma Imaan sannan nima na cireta a raina by now,
Allah ya hada auranmu tun farko saboda akwai raban Imaan tazo duniya, sannan
auranmu shine silar kaddararmu" Khairiyya ta goge guntun hawayenta tana kallansa ta
ce "Allah yasa haka shine mafi alkhairi" ya hade goshinsu yana kallan idanta ya ce
"Ameen" jin an bude kofar yasa yayi saurin janye fuskarsa akan nata, Ammi ta
kallesu sau daya ta kauda kai ta ce "Ka sameni a dakina" ya ce "Ohk to" mikewa
yayi yana kallan Khairiyya ya ce "Till i come back" ta daga masa kai sannan ya fita
a dakin. Da sallama Yusuf ya shiga dakin Ammi, ya nemi gefe ya zauna ya ce "Gani"
Ammi ta ce "Toda farko dai mungode Allah daya kwatar maka 'yancinka ya kuma kubutar
daku a hannun wannan mutanen" a hankali ya ce "Allah ya kara tsarewa" ta ce "Ameen,
sai kuma maganar Rafi'ah, ka dawo kuma gashi tana shirin yin aure" a hankali ya
dago yana kallanta sai kuma yayi murmushi ya ce "Allah ya sanya alkhairi Ammi, koda
ba aure zata yi ba idan Allah ya kaddara zamanmu ya kare dole haka zamu hakura"
Ammi ta ce "Toh fatanmu Allah yasa haka shine mafi alkhairi" ya amsa da "Ameen"
Fitowa tayi walking slowly tana murmushi harta karasa kusa dashi, ya cire
glasses din idansa ya ce "Amaryar Ahmad" ta sunkuyar da kai ta ce "Ina yini" ya ce
"Lafiya kalau, kin shirya muje?" Ta daga masa kai ya ce "To bismillah" daga haka ya
bude mata front seat ta shiga ta zauna, shima ya zagaya mazauninsa yayiwa motar key
suka bar layin. Hannunta ya kamo yana kallan idanta ya ce "How is Imaan?" Ta ce
"Tana nan lafiya" ya ce "Haka akeso" zame hannunta tayi a cikin nasa ta ce "Ummi
tace za'a kaita wajen Babanta" ya ce "When?" Ta ce "Inaga yau" Jawad ya sauke
ajiyar zuciya ya ce "Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" shiru tayi tana kallan sajen
fuskarsa daya kwanta sosai, ganin zai juyo yasa tayi saurin juyawa tana kallan
window, murmushi yayi mai kyau ya ce "I caught you, me kike kalla a fuskana" ta
danyi murmushi ba tare data juyo ba ta ce "Nothing" ya ce "There's" ta ce "To idan
baka yarda ba shikkenan" ya ce "To zuwa zanyi na aske tinda bakyaso" tayi saurin
juyowa tana kallansa ta ce "Nooo pls" ya juyo ya dan kalleta sai kuma ya maida
hankalinsa ga titi, in a very low voice ta ce "Yana maka kyau sosai" ya juyo yana
kallanta tayi saurin rife fuskarta da hijabi, ya ce "Wallahi wannan kunyan naki
rana daya zan cire miki shi" bata dai dago ta kalleshi ba sai dariya take a
hankali. Da sallama Ummi ta shigo parlorn Abba ta sameshi zaune yana rike da Imaan,
kallanta kawai yake amma tinaninsa da hankalinsa na wani wajen da ban, jin bai amsa
sallaman ba yasa Ummi ta kalleshi, ta sauke ajiyar zuciya ta zauna gefensa ta ce
"Abbu Rafi'ah" ya juyo yana kallanta ya ce "Harkin gama ne?" Ta ce "Na dai kusa" ya
ce "Ohk, Fatiman ina tafi ne? bamasan yawan fitan nan fa" Ummi ta ce "Taje gidan
Anty Halima, kuma ta dade bata je bane shiyasa" Abba ya ce "Allah ya dawo da ita
lafiya" ta ce "Ameen, dan Allah Abbu Rafi'ah kayi hkr da abinda ya faru karka sawa
kanka wani ciwo" a hankali ya kwantar da Imaan akan kirjinsa ya ce "Ina kokarin yin
hakan Zainab, amma kinsan abin da ciwo wani lokaci gani nake kamar mafarki ne" Ummi
ta ce "Hakuri dai zakayi, tinda abinda ya faru ya riga ya faru, kuma dai koma
menene 'yan uwanka ne, bazaka ta6a canzasu ba" Abba ya limshe ido ya ce "Hakane
'yan uwanane amma a yanzu da abin ya faru na cire hannuna akan lamarin su, ita Umma
uwace a gareni sbd haka zanci gaba da kyautata mata kamar da, amma 'ya'yanta bani
da sauran alaka dasu, abinda suka min suje suda Allah" duk jikin Ummi sai yayi
sanyi, a hankali ta ce "Allah ya kyauta" ya ce "Ameen" daga haka ta mike ta daga
Imaan dake bacci a jikinsa suka shiga daki. Jawad na parking Rafi'ah ta fito da
sauri ta nufi entrance din gidan, bayan ya rife mota ya bi bayanta. A parlor duk ta
samu ilahirin gidan, tayi saurin sunkuyar da kanta ganin sun hada ido da Mami, ta
samu caan gefe ta zauna kanta a kasa ta ce "Ina yini Mami" cike da fara'a Mami ta
ce "Lafiya kalau Fatima, ya karatu ana ta hutu ko?" Ta ce "Ehh" dai dai nan Jawad
ya shigo rike da key din motarsa ya zauna kusa da Rafi'ah that wasn't comfortable,
a hankali ta ce "Ina yini Mummy" Mummy ta ce "Lafiya kalau, yasu Umminki?" Ta ce
"Suna nan lafiya" Ikram dake zaune ta ce "Ina yini Anty" a hankali Rafi'ah ta dan
kalleta ta amsa, Sadeeq ya ce "Antynmu ina yini" kunya taji ta rife fuskarta da
hijabi, Ikram ta mike tana dariya ta shiga kitchen, ba jimawa ta jerawa Rafi'ah
different kind of fruits a gabanta, a hankali ta ce "Thank u" Ikram ta ce "Never
mind Anty, tin jiya Yaya yake cewa zakizo wai sai Mummy ta miki dambu" ita dai
kanta a kasa tana ta murmushi, ganin Mami ta tashi yasa ta mike da sauri ta shiga
part din Mummy, Jawad ya danyi murmushi yana kallan Mummy ya ce "Sai ta zauna ita
kadai ko? Dan mu yanzu anan muke yini" Mummy ta ce "Atoh idan ta gaji ta fito"
Ikram ta dauki tray din tabi bayanta ta ce "Ni dai bazanbar Antynah ita kadai ba"
daga haka ta shige part din Mami tana dariya.

*1 Month 2 weeks ltr*


Yau ya kama saura sati 2 bikin Rafi'ah kuma yau ne za'a kawo lefenta, tinda
safe suna daki ita da Ameera sai yanzu da Ameera ta tafi sannan ta fito, lace ne
ajikinta da yayi mungun kar6anta sosai, sai sheki take tana kamshi, bude dakin Ummi
tayi ta shiga da sallama, suna zaune ita da Anty Salma da wata kawarta, Rafi'ah ta
danyi kasa da kanta ta ce "In ayini" kawar Ummi ta amsa tana murmushi ta ce "How
are u" a hankali ta ce "Fine" Ummi dake kallanta ta ce "Menene kuma?" ta ce "Dama
Banci abinci bane" Ummi ta wurga mata harara ta ce "And who do u expect will bring
food for u?" Sauke kanta tayi kasa tana wasa da fingers dinta, Anty Salma ta danyi
dariya ta mike ta ce "Bari na kawo maki daughter" Ummi ta ce "To meyasa baza taje
ta diba ba, bakinta ne a parlorn kasan" ita dai Rafi'ah murmushi tayi tabi bayan
Anty Salma, dakinta ta shiga ta zauna a bakin gado, danna wayarta tayi taga message
din Jawad, ta bude message din bayan ta gama karantawa ta danyi murmushi sannan ta
masa reply. Karfe 3 motoci Hudu suka iso gidan Abba, cike da girmamawa aka tarye su
suka shigo katon parlorn, duk yawanci 'yanuwan Abi ne saina Mami kalilan saboda su
ba a gari suke ba, aka jera akwatina 12 a tsakiyar parlorn, wata babbar mata ce ta
fara addu'a bayan an gama suka gaggaisa cikin mutunci sannan Ikram ta tashi ta bude
ko wane akwati na parlorn, aka jejjera musu abinsha da snacks kala kala,,,, su Anty
Salma nata yaba kayan suna Allah sanya alkhairi duk da dai ba daddagawa sukai ba,
basu wani jima ba suka tashi tafiya, aka basu cartons din lemuka different types
da kuma snacks suka tafi dashi, kowa ka ganshi yana cikin fara'ah da walwala. Bayan
sun tafi Anty Salma ta shigo dakin Rafi'ah, ta sameta zaune akan sallaya ta idar da
sallah, Anty Salma ta ce "Ba zaki sakko kiga kayan ba?" Sauke kanta tayi kasa ta ce
"Anjima" Anty Salma ta ce "To ba damuwa, kin cin abincin dazun" ta daga mata kai,
juyawa Anty Salma tayi ta fita a dakin Rafi'ah ta mike ta jawo wayarta dake
ringing, a hankali tayi picking ta kai kunnen, Jawad ya ce "How are u?" Silently ta
ce "Fine" ya ce "Kayanki sunzo ko?" kamar yana gabanta tayi saurin rife idanta bata
ce ko mai ba, ya ce "Are u there?" Ta ce "Uhm" ya ce "Talk to me" ta ce "Ehh an
kawo" ya danyi murmushi ya ce "Nasan an kawo, but how did u saw it?" rife
idanuwanta tayi ta ce "Ni banma gani ba" ya ce "Why?" Ta ce "To 'yan uwan su Abba
sun cika parlorn" ya danyi murmushi ya ce "Kema ai 'yan uwanki ne" ta ce "Uhm" ya
ce "To anjima zamuyi magana, Mami ta kirani" ta ce "To nagode" ya ce "Thanks too,
and never get tired of praying" ta ce "Insha Allah" daga haka sukai sallama.

_08103810398_
*This page is dedicated to LUBABATU KASEEM & ZARAH MUHAMMAD, thank u sisters for
the gift 😇 i appreciate the both of u 💃🏻💃🏻 Allah ya sanya alkhairi yasa ku gama lpy,
my love for u is real and endless, thank u once again*
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_23_

Daren ranar Yusuf na zaune a parlor yana kallo Ammi ta fito, ya danyi murmushi yana
kallanta ya ce "Sannu da fitowa Ammi" ta zauna gefensa ta ce "Yauwa Yusuf, kaji an
kawo kayan auren Rafi'ah ko?" Ya daga mata kai yana kallan TV ya ce "Eh, dazu munyi
waya da Ahmad yake fadamin" Ammi ta ce"Bikinma sati biyu ya rage" ya ce "Duk munyi
magana, Allah ya sanya alkhairi" Ammi ta ce "Ameen ya Allah" fitowa Khairiyya tayi
a daki tana yatsine fuska ta ce "Ammi kinga ya kwacemin wayana tinda safe yaki ya
bani" kin kulata Ammi tayi ta mike ta shiga daki, Khairiyya ta karasa gefensa ta
zauna ta ce "Give me my phone" daga haka ta cusa hannu a pocket dinsa, hannayen
gaba daya ya damke yana kallan idanta ya ce "Idan kika kwace na yarda zan baki"
cije baki tayi ta dinga fincikan hannunta amma ta kasa kwacewa, shi dai sai kallan
TV yake dayan hannun kuma yana kur6an tea, ya ce "Kin yarda ba karfinmu daya ba
kenan" ta dan ta6e baki ta ce "Dama kai wannan katon ba dole kayi karfi ba" ya dan
zaro ido ya ce "Nine katon?" Ta ce "Aiba kiba ba, kalli fa nan dinka babba" ta
karashe maganar tana nuna kirjinsa, sake hannunta yayi ya mike ya ce "Keda wayarki
sai kinyi aure idan na yarda na baki" daga haka ya shiga daki ta bi shi da gudu.
Parking Jawad yayi a kofar gidan Abba sannan yayi dialing phone din
Rafi'ah, tana kwance a daki kiran ya shigo, dan tinda aka kawo kayanta bata fito ba
duk da mutanen sun watse sai Anty Salma kawai, picking call din tayi ta kai kunne
hade da sallama, ya danyi murmushi ya ce "Are u sleeping?" silently ta ce "No" ya
ce "Ohk i'm outside" a hankali ta mike ta ce "Toh" daga haka tayi hanging call din
ta dauko hijab ta saka ta fita a dakin, a parlorn sama ta tadda Umminta da kuma
Anty Salma, ta danyi kasa da kanta ba tare data kallesu ba ta fara sauka a stairs
din. Very gentle take tafiya harta fito compound din gidan ta fita, tayi saurin
sunkuyar da kanta ganinsa a tsaye yayi folding hannyensa ya jingina da mota, yayi
mungun kyau sosai, ta karasa kusa dashi ta ce "Ina yini Yaya" ya ce "Lafiya kalau
wife, how was today?" Ta ce "Fine" bude mata back seat yayi ya ce "Bismillah" ta
shiga sannan shima ya shiga ya rife kofar, limshe ido tayi jin kamshin tirarensa
daya hade da sanyin AC, kamo hannunta yayi ya ce "Kinga kayan?" Ta girgiza masa
kai, ya ce "Why?" Ta ce "Babu" ajiyar zuciya ya sauke ya ce "How is everyone?" Ta
ce "There are all fine, Abdul zai dawo ran Monday" ya ce "Allah ya kawo shi lpy" ta
ce "Ameen" shiru ne ya biyo baya, ta daga kanta a hankali taga kallanta yake yana
murmushi, da sauri ta sauke idanta kasa, cikin cool voice dinsa ya ce "Munyi waya
da Yusuf dazu" ta dago kanta tana kallansa ta ce "Meya faru?" Ya ce "Nothing
zumunci kawai mukai, na fada masa ranar auranmu kuma yau an kawo kaya" ta ce "Ohk"
ya ce "And u know what?" Ta girgiza kai, ya ce "Ya bani Imaan har abada" with
surprise ta dago kanta tana kallansa, sai kuma tayi murmushi ta ce "Allah na gode
maka, dama ni abin na damuna yace zai kar6eta, inajin Imaan har cikin raina" ya ce
"Shima haka yake ji, kuma ya bani ita saboda wasu dalilai nasa" ta sauke kanta ta
ce "I'm so happy Yaya" ya ce "Really?" Ta ce "Yes" wayarsa ne ya fara ringing ya
dauka ya kai kunne, kallansa kawai take harya gama, tayi saurin sauke kanta tana
murmushi ta ce "I like your hair cut" ya ce "Thank u love, wane irin shiri kike na
biki?" Ta bude hannayenta alamun bata sani ba ta ce "Ni kawai i don't like any
event" ya dago fuskarta yana kallanta ya ce "To shikkenan, yadda kikeso haka za'ai"
ta danyi murmushi ta zame jikinta, ya ce "To saida safe naga kamar kinajin bacci"
ta ce "Ehh bacci nakeji sai anjima" ya ce "Alright i love u" daga haka ya bata
light kiss a forehead dinta.

*2 weeks ltr*
Yau ya kasance friday ranar daurin auren Rafi'ah da Jawad, kowa ka gani
yana cikin farinciki, gida ya cika sosai fiye da auranta na farko, Tana zaune a
daki ita da Ameera Anty Salma ta shigo, ta zauna bakin gado tana kallan Rafi'ah
dake zaune tayi shiru, Anty Salma ta bata side hug ta ce "Kiyita addu'a Fatima, ba
wanda ya isa ya miki abinda Allah bai kaddara zai sameki ba" rungume Anty Salma
tayi cikin kuka ta ce "Anty wallahi tsoro nakeji, gani nake kamar abinda ya faru
4years back zai sake faruwa" Anty Salma ta shiga rarrashinta ta ce "Ba haka bane
daughter, insha Allah gidan zamanki ne na har abada" ta daga mata kai a hankali ta
ce "I hope so Anty" Anty Salma ta shiga share mata idanta ta ce "Yanzu muka dawo
daga gidanki mun karasa gyara komai, the house was so masha Allah, ki godewa Allah"
dan murmushi tayi ta ce "Nagode masa Anty" tashi Anty Salma tayi ta ciro mata wani
kaya ta ce "Yanzu mai make up din zata karaso, sai ki canza kaya kafin 'yan daurin
aure su dawo" sauke kanta tayi kasa ta amsa da toh. Karfe 1 bayan an idar da sallan
juma'a dumbum mutane suka shaida daurin auren FATIMA MUHAMMAD da AHMAD MUHAMMAD
AHMAD, tinda Rafi"ah taji 'yan daurin aure sun dawo hankalinta ya kara tashi,
batasan lokacin data fashe da kuka ba ta kankame Ameera cikin rawar murya ta ce
"Ameera ina tsoro wallahi" Ameera ta ce "Bakiji abinda Anty tace ba kiyita addu'a
babu abinda zai faru insha Allah" kuka sosai take tana addu'a cikin ranta, dan gaba
daya ta girgiza da abinda ya faru da ita a baya. Da yamma liss aka shirya Amarya
shiri na alfarma akai ta hotuna duk da fuskarta babu walwala sosai amma tayi mungun
kyau, Khairiyya na gidan itama duk inda tayi Imaan na binta a baya, Mummy dai
wannan karan tana bangaren ango, dan tinda aka fara biki bata leko gidan ba, suna
caan suna nasu hidiman suma, karfe 7 aka kara shiryata cikin wani tsadadden lace da
yayi mungun mata kyau, sai kamshi take ta ko ina, duk da gyaran jikin na sati biyu
kawai akai amma sai sheki take, sosai da sosai Abba da Ummi suka mata fada, tana
kuka haka aka dagata zuwa mota, shima Abdul duk yadda yaso kar yayi kuka saida
hawaye ya xubo masa, hannunta ya kamo ya ce "Allah ya sanya alkhairi Anty" a
hankali ta ce "Ameen" sannan ta shiga motar, motoci masu yawa ne suka rakata gidan
Abi, ana parking a kofar gidan zuciyarta ya hau bugawa, aka fito da ita zuwa cikin
gidan, fada sosai da naseeha Mami da Mummy suka mata, daga haka ta daga veil din da
aka rife mata fuskarta dashi aka musu hotuna, Ikraam nata kallanta tana murmushi,
ita dai taki yarda ta hada ido da kowa, bayan an gama komai daga nan aka wuce da
ita gidanta, har dakinta Mummy ta kaita ba irin fadan data manta bata mata ba, tun
tana daurewa harta fashe da kuka, bayan 'yan kawo amarya sun watse ya rage saura
Ameera da Mummy sai Ikram da Anty Salma su suka kara gyara gidan yayi tass, bayan
sun gama Mummy tace su tafi, ita tayi driving dinsu suka bar gidan. Rafi'ah na
zaune taci kuka harta godewa Allah taji Karar shigowar message, jawo wayar tayi ta
duba text message din, message ne na fatan zaman lafiya da kuma addu'o'i a rayuwar
auranta a karshe ya mata fatan alkhairi, murmushi tayi ganin sunan Yusuf a karshe,
tayi reply da "Thank u so much Yaya Yusuf i appreciate, and i wish u same" ajiye
phone din tayi ta kifa kanta akan gwiwowinta, b jimawa taji an bude kofar dakin, ta
dago kanta da sauri suka hada ido, sauke kanta tayi kasa, Jawad ya danyi murmushi
ya zauna gefenta ya ce "I'm i not welcome wife?" Ta noke kafada hawaye na sakko
mata, rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta ya ce "You stop crying Sweetheart"
dago kanta tayi a hankali sai dai bata bari sun hada ido ba, ya ce "Kinajin yunwa
ko?" Ta daga masa kai, ya ce "To muje parlor muci abinci sai muyi sallah" har
lokacin jikinta rawa yake kuma ziciyarta na bugawa, dukawa yayi yana kallan jajayen
idanuwanta ya ce "Ko in goya ki" ta rufe fuskarta ta ce "Ni bance maka ba ai" ya
mike yana kallanta ya ce "To ki bari na daukeki" bai jira cewarta ba ya dauketa ya
sata a shoulder dinsa suka fita parlor, akan kujera ya sauketa tayi saurin kifa
kanta akan cushion ta ce "Ni banaso fa" ya ce "Ki bari sai anjima kice bakyaso" ta
dago kanta tana kallansa ya kashe mata ido daya ya ce "Yes", plate ya dauko ya juye
gasheshen kazar ya zuba fresh milk me sanyi cikin glass cup guda biyu ya ce "I want
to feed u today" daga haka ya gutsuro naman ya fara bata a baki tana kar6a, ganin
tana kunya yasa ya jawota jikinsa ya ce "Bari to na miki irin na babies" zame
jikinta take sonyi amma ta kasa saboda rikon daya mata, haka dai ta hakura ta
kwanta ajikinsa ya dinga bata, sosai taci kazar ta sha fresh milk dinta, ganin ta
koshi ya daga plate din yana kallanta ya ce "To dagani na kai kitchen" a hankali ta
sauka ajikinsa ta ce "Kai baka ciba" ya ce "Na koshi" daga haka ya wuce kitchen,
yana dawowa ya sameta zaune inda ya barta, ya kai hannu zai dagata ta danyi kara ta
ce "Nida kaina ne" ya ce "Ai banaso kisha wahala, let me just carry you" kin yarda
tayi ta kara nokewa, ya ce "Then let me hold ur hand" hannunta ta mika masa ta ce
"Sai dai na kama naka" ya ce "To gashi" ta danyi murmushi ta kama hannunsa suka
wuce daki. Brush sukai sannan sukai alwala suka fito, ya jasu sukai raka'ah biyu
sannan ya dinga musu addu'ar zaman kafiya har karshen rayuwarsu, tashi yayi ya ce
"Bari naje kasa na kulle kofa" daga haka ya fita a dakin, mikewa tayi ta cire
hijabin jikinta ta bude press dinta, night gown kala kala ta gani, ta dauko wata
doguwa sannan ta cire kayan jikinta ta daura towel, ta dauko rigar zata sa kenan
Jawad ya bude dakin, tayi saurin durkusawa ta ce "Wayyo Yaya ka fita na shirya
mana" ya danyi murmushi ya karaso cikin dakin ya ce "Let me help u" daga haka ya
dagota daga tsugunen da take, hannunsa yasa ya kashe switch din dakin, ta ce "Yaya
kace tayani za..." Shiru tayi jin bakinsa akan nata, tayi saurin rintse idanuwanta
zuciyarta na bugawa.

*Firstly, my apology goes straight to TEAM YUSUF, u people shoul understand me here
pls, a rayuwa ba komaine kakeso kuma kake samu ba, wani abin kana sanshi amma baka
san ba shine alkhairi a tattare da kai ba, shiyasa akeso a kullum mutum idan yayi
addu'a yayi fatan wannan abin shine alkhairi a rayuwarsa idan ba alkhairi bane
Allah ya canza masa da mafi alkhairi, wannan shine fatanmu a koda yaushe Allah kuma
yasa mu dace 🤲🏻 so inaso ku gane Allah ya kaddara zaman Rafi'ah da Yusuf ya kare ta
dalilin wadannan mutunen, Allah kuma ya kaddara za'a haifi Imaan, furthermore
littafina na gina shine akan Jawad da kuma Rafi'ah 🥰, thank u for reading 🤗*

_08103810398_
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_24_

Slowly ta bude idanuwanta tana bin dakin da kallo, ta mike a hankali ta shiga
toilet, After few minutes ta fito daure da towel tana kallan agogon dake jikin
wall, dan zaro ido tayi ta nufi press dinta ta dauko doguwar riga ta saka sannan
tayi packing smooth hair dinta tasa hijab ta tada sallah, bayan ta idar ta jima
tana addu'a sannan ta kifa kanta akan gado tana tuno rayuwarta right from the
beginning till now, batasan lokacin da wasu hawaye masu zafi suka sakko mata ba,
jin an bude kofar tayi saurin goge idanta ta limshe idanuwanta, Jawad ya karaso
inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "How are u sweetheart?" ba tare data dago
kanta ba ta ce "Fine, good morning" ya danyi murmushi yana dora hannunsa a kanta ya
ce "Morning" dago kanta yayi yana kallan fuskarta ya ce "Open your eyes?" Ta noke
kafada, ya dan shafa beard dinsa yana kallanta ya ce "Kunyana kikeji?" ta girgiza
kai ta ce "No, just that..i'm not..feeling fine" yadda tayi maganar yasa ya danyi
shiru yana kallan cute face dinta, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Now tell me what's
wrong with you" sai lokacin ta bude idanuwanta suna hada ido ta sauke kanta kasa,
ya danyi murmushi ya kai bakinshi kunnenta yayi mata magana, daga masa kai tayi, ya
bata light hug yana murmushi ya ce "Just like your first experience?" ta daga masa
kai, ya rungumeta ya ce "I'm sorry, pardon me pls" ta zame jikinta a nashi ta mike
ta ce "I want to sleep" ya mike yana kallanta ya ce "Breakfast fa?" Ta dan turo
baki ta ce "I'm not hungry" ya zauna bakin gado yana kallanta ya ce "No u have to
eat ko kadan ma, kinga tin dazu na tashi nake ta faman hada maki breakfast" kanta a
kasa tana kallan dogayen yatsunsa dake kan kafarta, ya dan 6ata rai ya ce "So u
won't appreciate?" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ya tashi tsaye ya dagata
tayi saurin nokewa ta ce "Ai zan iya" ya ce "To naga kinaso na daukeki ne" ta dan
turo baki tana kallansa ta gefen ido, ya kafe ta da ido ya ce "Kuma aciremin himar
din nan" ta dan zaro ido ta ce "Yaaayaaahh" ya ce "Yes now, ni baza kimin yawo da
himar a gida ba" ta zauna bakin gado ta ce "Tona fasa yin breakfast din" zama yayi
gefenta ya ce "To naji tashi muje" mikewa tayi tana turo baki ta fita a dakin, ya
shafa gashin kansa yana murmushi yabi bayanta.
_3 weeks ltr_
Jawad ne zaune a parlor yana operating laptop, daga kansa yayi ya kalli
time sannan ya mike ya haura upstairs, dakinsa ya bude ya samu Rafi'ah na kwance
tana waya, suna hada ido ta turo baki tayi hanging call din ta juya masa baya, ya
danyi murmushi ya karasa kan gadon ya ce "U haven't eat dear, ya jikin ki?" a
hankali ta ce "Na koshi" ya dagota zua jikinshi ya ce "Are u still angry with me?"
Ta girgiza masa kai a hankali sai kuma ta kifa kanta a kirjinsa tana sharar hawaye,
cikin rarrashi ya ce "Ki bari next week sai muje i promise u this time around kinga
shekaranjiya da zazzabi kika kwana" cikin muryar kuka ta ce "Ni wallahi na gaji u
are always saying next week, 3 weeks banga Ummina ba banga Abba ba banga kowa ba
sai Abdul daya zo min sallama ya koma school, ko Imaan sau biyu Khairiyya ta
kawota" fashewa tayi da kuka ta kankameshi, shi dai kasa cewa komai yayi, caan ya
dan bubbuga bayanta ya ce "Tashi ki shirya na kaiki, u meet me downstairs" daga
haka ya janyeta a jikinsa ya dauki car key dinsa ya fita a dakin. Kwanciya tayi ta
dinga share hawayen idanta bata kuma tashi ta shirya ba, bayan 20 minutes ya shigo
dakin ya karasa inda take ya durkusa yana kallanta ya ce "Are u not going?" Ta dago
jajayen idanuwanta tana kallansa ta ce "Ba fishi kakemin ba" ya dan zaro ido ya ce
"Niiiii?" ta ce "Ehh" ya ce "A'a niba fishi nake maki ba, kawai rigimarki ne tayi
yawa, idan kinyi hkr ma na karasa da case din nan sai in kaiki gida harki kwana,
amma kince ke bakyaso, then sai muje na kaiki anjima na dauko ki" sakkowa tayi akan
gadon tana kallansa ta ce "Amma ba fishi kamin ba?" Ya daga mata kai yana kashe
mata ido daya ya ce "In the next 2 weeks zaki koma school ma ai" toilet ta shiga ya
bita da kallo yana dariya, fuskarta ta wanke tass sannan ta fito ta goge da clean
towel ta fita a dakin zuwa dakinta, press dinta ta bude ta dauko atampa doguwar
riga ta saka, sosai dinkin ya zauna mata tayi dauri me kyau tayi light make-up
sannan ta yafa veil ta fashe jikinta da turare, tana juyawa suka hada ido da Jawad
dake bakin kofa yayi folding hannayensa, ta sauke kanta kasa ta fara kwashe kayan
data cire ta shiga toilet tasa a washing machine, a hankali ta karaso kusa dashi ta
ce "Na gama" ya rungumeta yana limshe ido ya ce "U looks more beautiful wife" a
hankali ta ce "Thank u" sakinta yayi ya kama hannunta suka sauko downstairs sannan
yayi switching sockets suka fita ya rufo kofar, side hug ya bata suka karasa
parking lot ya ce "Yaushe zan dauko ki?" Ta ce "Da daddare" ya ce "No ban yarda ba"
ta ce "Allah Yaya zanyi hira da kowa sosai na dade fa bangansu ba" ya ce "After
Magrib zanzo" ta dan tsaya tana kallansa ta ce "Why not 9pm or 10pm Yaya?" Murmushi
yayi ya bude mata motar ya ce "Bismillah" bayan ta shiga ya rufe ya zagaya
mazauninsa.
Khairiyya ce kwance akan gadonta tana rokon Yusuf karya mata allura,
gaba daya fuskarta ya wanku da hawaye, injection din hannunsa ya ajiye a gafe yana
kallanta ya ce "It won't pain you lil sis, kinga jikinki yayi zafi" cikin kuka ta
ce "Ai Daddy yace magani zan sha" ya ce "To bakiji sauki ba kinga sai allura kenan,
bari na kira Ammi ta rike ki" sanin Ammi baza ta mata da dadi ba yasa ta danyi kara
ta ce "Wallahi zata min fada dan Allah karkamin me zafi zan tsaya" ya ce "A hankali
zan maki" daga haka ya dauki injection din ta juya jikinta na rawa, yana mata ta
saki kara ta kankame hannunsa, yasa mata cotton wool a wajen yana murmushi ya ce
"Allah ya baki lafiya" harara ta maka masa ta ce "Ba amin ba" ya fashe da dariya ya
ce "Ameen din dai, in kuma kikaiwa kanki addu'an haka ni kuma naita maki allura"
Ammi ne ta shigo dakin rike da cup ta ajiye a gefen gado ta ce "Anyi alluran?" Ya
ce "Ehh" ta ce "Ga tea idan zaki sha" daga haka ta fita a dakin. Zama yayi a gefen
gadon ya dauko tea din ya kai bakinta ya ce "Kar6i kisha" ta noke kafada tana
jujjuya ido ta ce "Nina koshi" ya ce "To haka zamuyi auran kina harara na" ta ce
"Aini ban harareka ba" ya ce "To kwanta kiyi bacci" a hankali ta zame jikinta ta
kwanta ta ce "Yau kace zaka kaini na kaima Imaan abinda ka siya mata" ya ce "Not
today, sai idan kin samu sauki" ta ce "Da yamma dan Allah" ya ce "Sai naga idan kin
samu sauki kafin nan".
Parking Jawad yayi a kofar gidan Abba yana kallan Rafi'ah ya ce "Mun
karaso" kafin ya rife bakinsa ta bude motar ta fito ta shige ciki da sauri, tana
bude kofar parlor ta dan ja baya ta wara ido ta ce "Saudat" Saudatu dake murmushi
ta ce "Anty Rafi'ah" Rafi'ah ta zauna gefenta ta ce "Long time, sai waya kawai, ya
mutanen garinku dasu mamanku, wannan babynki ce?" Rafi'ah ta dauki 'yar farar
yarinyar da batafi 3 months ba tana jujjuyata ta ce "Masha Allah, ta girma sosai,
me sunanta?" Saudatu na murmushi ta ce "Sunanku daya, nima wayana ne ya fadi banda
numberku" Rafi'ah ta rungumeta ta ce "Allah ya raya ta da Imani, shiyasa bama
saminki ashe?" fitowa Ummi tayi a kitchen Rafi'ah ta nufeta da sauri tayi hugging
dinta ta ce "I missed u Ummina, ina Abba?" Ummi ta ce "Abba ya fita dazu, bakimin
waya zaki zo ba, da yanzu zan sauke Saudatu a gidanki na wuce aiki" ta danyi
murmushi ta ce "Nima ina shigowa kawai na ganta, i was so surprise ashe zata kawo
mana ziyara" Saudatu dai ta danyi murmushi, Sakkowa Imaan tayi da gudu ta nufi
mahaifiyarta ta rungumeta, Rafi'ah tayi hugging dinta tana kallanta ta ce "Kinga na
samu wata babyn, do u like her?" Imaan ta daga mata kai, murmushi tayi ta koma kan
kujera ta zauna Imaan ta zauna a gefenta, jin knocking yasa ta dan zaro ido, Ummi
dake kallanta ta ce "Tare kuke ne?" Ta mike da sauri ta ce "Ehh" parlorn Abba Ummi
ta shiga sannan Rafi'ah ta bude masa kofar, ya shigo hade da sallama ya zauna akan
carpet, amsa gaisuwar da Saudat ke masa yayi, ya kalli Imaan dake kallansa ya ce
"Come to me daughter" ta karaso da sauri ta rungumeshi harda hawayenta wai ya gudu
ya barta, chocolate ya bata masu yawa hakan yasa ta hakura da mitan tayi shiru,
bayan few minutes Rafi'ah ta masa jagora yaje ya gaishe da Ummi sannan suka fito,
daga haka ya koma mota. Parlorn Abba Rafi'ah ta shiga ta zauna gefen Ummi ta ce
"Dafa yini nazo kuma kince zakije aiki" Ummi ta ce "Why didn't u call me and ask?
Test kuma zan musu, sai kije gidan Mummy ga Imaan nan, idan na gama zan biya na
dauketa" ta dan hade rai ta ce "To, wani satin saina dawo" Ummi dai bata ce mata
komai ba ta fita a parlorn, mikewa tayi itama ta fito a parlorn ta samu Saudatu na
goya Babynta suna sallama da Ummi, ta ce "Tafiya zakiyi ne" ta ce "Ehh wallahi
zanje gidan wata Innarmu anan zan kwana" Rafi'ah ta ce "To insha Allah zanzo miki
kafin ki koma" ta danyi murmushi ta ce "Ina nan kwana 3 zanyi" ta ce "To sai kin
ganni, ki gaishe da mutanen gida, bari na karba phone number ki" Saudatu ta ce
"Ameen" daga haka ta saka mata number, Ummi ta ce "To bari na saukeki" ta ce "To ba
komai" upstairs Rafi'ah ta nufa ta dauko kayan Imaan set biyu tasa a karamin jaka
sannan tayiwa Ummi sallama suka fita, tinda suka fito Jawad yake kallanta yana
murmushi, bayan sun shiga motar ya ce "Sai kyau kikeyi wife" ta dan turo baki ta ce
"Ummina zata fita yanzu dan girman Allah next week ka kawoni" ya ce "Angama Madam"
daga haka yaja motar suka tafi. Suna zuwa kofar gate dinsu yayi horn ya shiga yayi
parking, Imaan ta fito da gudu ta nufi cikin gida, ita dai Allah ya gani yanzu bata
wani sakewa idan tana tare da Mami, Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "U look
sick, ko har yanzu zazzabin ne" ta girgiza kai a hankali ta ce "Ni banajin komai
kuma" daga haka yaja hannunta suka nufi entrance din gidan, da sauri ta janye
hannunta ganin ba saketa zaiyi ba, ya juyo yana kallanta sai kuma yayi dariya ya
bude kofar, Dukkansu suna zaune a parlor Mummy na yiwa Ikram kitso, Mami kuma ta
dora Imaan a cinyarta tana fada mata tare da Daddy suka zo, da sallama suka shiga
parlorn, Rafi'ah tayi saurin sauke kanta kasa ta zauna akan carpet, zama yayi a
tsakiyar Mami da Mummy ya gaishesu, Ikram ta gaishesa sannan Rafi'ah ma ta gaishe
su, Ikram ta ce "Anty ina wuni" sauke kanta tayi kasa ta ce "Fine" Mummy ta ce "Har
yanzu zazza6in ne? Shekranjiya da mukai waya tace tana zazza6i" ya ce "Ehh amma
taji sauki, dama yini daya ne tayi, data sha magani shikkenan" Mummy ta ce "To
Allah ya sauwake, ya kuke ina babu komai" ya ce "Alhamdulilah ba komai" Tashi Ikram
tayi ta jera mata abinci a gabanta ta ce "Anty ga abinci" ta girgiza kai ta ce "Na
koshi Ikram, yanzu ai 10am ne, sai anjima" Ikram ta ce "To bari na tattara" da
hannu Jawad ya mata alamar ta barshi ya ce "Zataci, bata ci komai ba" Mummy ta ce
"To maiyasa Fatima, ko murnar zuwa gida ne?" Ta girgiza kai a hankali, Mummy ta ce
"To dauki abinci kici" daukar warmer Ikram tayi ta shiga parlornsu ta ce "Zaki fi
jin dadi anan, feel free pls" Mummy ta ce "To ki tashi ki bita" a hankali ta mike
tabi bayan Ikram, Mami dai na zaune sai murmushi take tana shafa bayan Imaan dake
kwance a jikinta. Zama Rafi'ah tayi akan carpet tana kallan Ikram ta ce "Pls i need
a cup of tea" Ikram tayi dariya ta ce "Laa dama yunwa kikeji shine kikai shiru"
murmushi tayi ta ce "Ba wani yunwa" Ikram ta fita tana dariya, bude babban warmern
tayi taga chips ne da soayyan kwai, ta bude dayan taga farfesun kayan ciki, kauda
kanta tayi gefe da sauri ta rife warmer ta fara jaa baya tana kokarin tashi, kafin
ta karasa tashi ta fara kwararo amai a wajen, dai dai lokacin Mami ta shigo Jawad
na biye da ita, yayi kanta da sauri yana dagata ya ce "What's wrong with u?" Magana
zatai amma ta kasa saboda wani aman daya taho mata, Ikram da shigowanta kenan ta
tsaya kallansu, Mami ta sauke Imaan ta karasa kusa dasu ta ce "Kace taji sauki?" ya
ce "Ehh but bansan kuma meke damunta ba" Mami ta ce "To dadin meyake daminta?" ya
dago yana kallanta sai kuma ya sauke kansa ya ce "It's malaria probably with
typhoid" kama hannun Rafi'ah Mami tayi tana masa wani kallo suka shiga daki, toilet
ta kaita ta wanke mata baki sannan ta kwantar da ita akan gado, tana bude kofa ta
ganshi tsaye yayi folding hannyensa, ta ce "Kasan tanada ciki ka fito da ita a
haka?" Ya dan shafa kansa ya ce "Mami ita ta takura saita fito, and i noticed she
was pregnant day before yesterday" wuce shi tayi ta jawo kofar dakin ta ce "Da kace
Malaria ne?" Ya ce "Uhm da farko haka Doctor yace min".

_08103810398_

*Thank u all for your calls and messages i appreciate, Allah ya kara mana lafiya,
wadanda basu da lafiya Allah ya basu lafiya 🥰 thanks for ur concern nagode sosai da
sosai 💃🏻💃🏻*
*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

_25_

Zama yayi akan kujera ya zaro wayarsa a pocket yana dialing phone din Aliyu, Mummy
da shigowanta kenan ta wuce dakin Mami tana fadin "Ni dama tin dana ganta nasan
akwai karamin ciki a jikinta" yayi saurin sunkuyar da kansa ya sake dialing phone
din Aliyu, fitowa Mummy tayi tana kallansa ta ce "Wai tin yaushe ta fara laulayin
me?" ba tare daya kalleta ba ya ce "Shekaranjiya ne" ta ce "To Allah ya raba
lafiya, Allah kuma yasa kar tayi irin laulayin cikin Imaan" shidai baice komai ba
yana zaune, gaba daya jikinsa yayi sanyi sosai, kallan Ikram dake gyaran wajen aman
yayi ya ce "Sadeeq yana gida ne?" Ta ce "A'a" mikewa yayi ya wuce dakin Mami ya
sameta tana canzawa Imaan kaya, a bakin gado ya zauna kansa a kasa ta ce "Wani
taimako aka bata ne?" Ya ce "Nothing" ta dago kanta tana kallansa ta ce "Why?
Bakuje asibiti bane?" Ya ce "Aliyu ne ya dubata a gida kuma na kirashi bai dauka ba
yanzu" Mami ta ce "Allah ya bata lafiya" a hankali ya ce "Ameen" mikewa yayi zai
fita a dakin ta ce "Ka kyaleta ta kwanta" a takaice ya ce "I'm not going to her"
daga haka ya fita a dakin.
Karfe 12 Rafi'ah ta farka daga nauyayyen baccin daya dauketa, ta bude idanuwanta a
hankali tana bin dakin da kallo, jin an bude kofar yasa tayi saurin runtse
idanuwanta dan tinaninta Mami ce, Jawad ya hau kan gadon ya daga blanket din
jikinta yana kallanta, bude idanuwanta tayi suka hada ido, ya rungumeta lightly as
if he don't want to, ya ce "How are u feeling now?" A hankali ta ce "Fine" ya bata
kiss a forehead dinta ya ce "Me kikeji yanzu?" Ta ce "Nothing, kawai kaina ke dan
min ciwo" ya kara rungumeta ya limshe idanuwansa ya ce "Quick recovery wife". Kusan
minti 3 tana kwance a jikinsa kafin ta dago kanta a hankali ta ce "Pls Yaya i'm i
pregnant?" Idanuwansa ya bude yana kallanta ya ce "Of course, are u not happy?" ta
girgiza masa kai hawaye ya taru a idanta ta ce "No just that" shiru tayi ta kwanta
ajikinsa tana sheshekar kuka, ya fara patting bayanta a hankali ya ce "What Baby?"
Cikin kuka ta ce "Zan sha wahala" sosai ya jawota jikinshi ya ce "No, insha Allah
baza musha wahala ba, God knows best ai kowani ciki da yadda yake ba lallai ya zama
daya da wancen ba" a hankali ta ce "I hope so, banasan na tina wahalan dana sha
last" ya shafa kanta ya ce "Ba komai, just keep on praying" kankameshi tayi ta fara
sauke ajiyar zuciya, sai taji dadi yadda yake karfafa mata gwiwa, ya shafa bayanta
ya ce "Are u still afraid?" Ta ce "No" ya rungumeta sosai a hankali ya ce "I love u
wife, and i will still love u till my last breathe, Allah ya bamu cute babies kamar
ke" murmushi tayi a hankali ta ce "Kamar kai dai" ya ce "Ehh zaki haifa duka, sai
kin haifi 22" batasan lokacin data fashe da dariya ba, ya ce "Dariya na baki
kenan?" Ta ce "I swear" bakinshi ya dora akan lips dinta tayi saurin juyawa ta ce
"Yaya idan wani yazo fa?" Ya ce "Duk da kike kwance ajikina baki yi tinanin hakan
ba?" zame jikinta ta farayi ya kankameta ya ce "Bazaki tashi ba" ta ce "Dan Allah
kar Mami tazo" ya ce "And so" daga haka ya kashe mata one eye, ta fara kwace
jikinta da karfi tana "Ni dai inada kunya wallahi bazan yar..." Shiru tayi jin an
bude kofar dakin, Jawad ya dago kansa a hankali suka hada ido da Mummy, ta ce "To
ka tashi dama ka dauki matarka ku bar mana gida, ai taji sauki Allah ya kara
karewa" tana kai nan ta juya ta fita a dakin. Ajiyar zuciya Rafi'ah ta sauke jin
muryar Mummy, ta mike a hankali ta sauko akan gadon ta dauka dankwalinta ta daura
sannan ta juya tana kallan Jawad dake gaban mirror yana sa hula, ta kalli kan gadon
ta ce "Yaya ka 6atawa Ikram gadon ta" ya ce "Zata gyara ai, danma bamu 6ata yadda
naso ba" harara ta dan dalla masa yayi kanta zai kamota ta fita da sauri, parlor ta
leka taga ba kowa ta dauka veil dinta ta yafa, rungumeta taji yayi ta baya, tayi
saurin juyawa ta ce "Yayaaahh" ya ce "Muje dakin Mami muyi mata sallama" ta ce "To
ka sakeni nikam" sakinta yayi ya kama hannunta ya ce "Muje to" ta tsaya tana
kallansa ta fara hade rai, ya ce "Ha'a i'm i holding u?" Ta ce "But u are holding
my hand" sake hannunta yayi ya wuce gaba ya ce "Zamuje gida ai" ta dan turo baki
tabi bayansa zuwa dakin, suna zaune akan gado ita da Imaan, Jawad ya zauna bakin
gadon Rafi'ah ta zauna a kasa ta ce "Zamu tafi Mami" Mami ta ce "To ko a yimiki
kunu?" Kanta ta girgiza a hankali ta ce "Na koshi Mami" Jawad ya mike yana kallan
Imaan ya ce "Sai anjima" Mami ta ce "Allah ya kaimu, Allah kuma ya sauwake" ya ce
"Ameen" hannu Imaan ta daga musu, Rafi'ah dai mikewa tayi ta fita a dakin, Jawad ya
daga mata hannu ya ce "Bye sweetheart". A kitchen suka sami Mummy da Ikram suna
yiwa Abi tuwo, Rafi'ah ta dan tsaya a bakin kofa ta ce "Sai anjima" Mummy ta ce "Mu
jima da yawa, Allah ya kiyaye" shidai Jawad murmushi kawai yake ya ce "Ameen" Ikram
ta fito tana kallan Rafi'ah ta ce "Allah ya kiyaye Anty, sai nazo" ta ce "To sai
kinzo Ikee" daga haka suka fita.
Daren ranar Rafi'ah na kwance a iikin Jawad kiran Ummi ya shigo mata,
tayi picking ta kai kunne hade da sallama, Ummi ta ce "Ya jikinki, Anty Halima tace
baki da lafiya?" A hankali ta ce "Ehh amma naji sauki, Munyi waya da Abba dazu nace
masa nazo ban ganshi ba" Ummi ta ce "To kin kyauta, sai anjima" tana hanging call
din kiran Mummy ya shigo mata, ta dauka tana yatsine fuska ta ce "Ba koranmu kikai
dazu a gidanki ba?" Mummy ta ce "Ba wannan ba kinji Ikleemah bata da lafiya ko?"
Mikewa tayi a jikinshi ta ce "Meya sameta ni ban sani ba, yanzu fa muka gama waya
da Ummina" Mummy ta ce "Mijin dai ya saketa wai ta samu ciki shi bayasan haihuwa,
ya mata duka cikin ya zube, tana caaan tana kuka ga uwa da kanwar uwa a kurkuku,
abundai abin tausayi jikinta duk duka ya farfashe" ita dai kasa cewa komai tayi ta
ce "Allah ya kyauta" daga haka sukai sallama.

*_Sorry for d short update, i'm very busy that's why_ 🙏🏻*

*_...‫شريك حياتي‬..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
_[Part 2]_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

✍🏻
_By FATIMA _

Washegari Rafi'ah na kwance a daki tana kallo a laptop Jawad ya shigo, ta juya
tana kallansa ta ce "Wallahi Yaya naci abinci" hawa kan gadon yayi ya danna stop ya
ce "Tashi muje kisha tea" ta dan zaro ido ta ce "Nafa sha" ya ce "Bangani ba"
daukanta yayi kamar 'yar Baby suka fita a dakin zuwa parlor, ya ce "Oya show me the
cup?" ta ce "I have washed it" daki ya koma da ita ya daurata akan gado ya ce
"Let's fulfill our deal" ta zaro ido ta ce "Not now pls" ya rungumeta ya ce "Why
Baby, i'm in need of u" shagwa6e masa fuska tayi ta narke ajikinsa ta ce "Let me
finish watching my film plsss" bakinshi ya dora akan lips dinta in a low voice ya
ce "Pls dear" ta fara shamba kafafuwa tana kuka a hankali, sosai ya kara hugging
dinta ya fara bata hot kisses all over.
Haka rayuwar Rafi'ah yaci gaba da tafiya gwanin dadi da kuma sha'awa, ba abinda ta
nema ta rasa a wajen mijinta, kulawa na musamman yake bata ko nan da caan tare suke
zuwa, yadda yake makalata a jikinsa sai kace cikinsa zai maidata, office ma idan
yaje da wuri yake dawowa, sai dai kuma idan yana da case, shima kansa har kiba yayi
ya kara kyau sosai, ko makaranta taje hankalinta baya kwanciya idan baizo da wuri
ba, ta dinga turo baki tana masa shagwa6a saiya lalla6ata take saukowa. Bangaren
Yusuf kuwa soyayya suke da Khairiyya na gani na fada, ko kadan bayasan abinda zai
takura mata, kullum yana cikin frinciki musamman idan yana tare da Imaan dan
yawanci zamanta ya dawo wajen Ammi ko kuma wajen Mami, bai kara shiga tashin
hankali me tsananiba sai lokacin da aka kirashi Jiddah ta haihu amma yaron ya koma,
sosai da sosai Khairiyya taji tausayinsa, Jiddah dai ba wai kukan rasuwar yaron
kadai takeyi ba, kuka take saboda yanzu zamanta da Yusuf ya kare, dama da abin
cikinta ya zauna shine zatai tinanin ko zai maidata, amma yanzu da babu d'an tasan
kashinta ya bushe, ranar da akai sadakan uku ba irin kukan da Jiddah batai ba, ta
rirrike Ammi wai dan Allah tasa baki, ita dai bata iya tace komai ba saboda tasan
Yusuf bazai ta6a mayar da ita.

Zaune suke akan gado ta mimmike kafanta yana mata massage, jin yana bata
labari yaji tayi shiru yasa ya dago kansa yana kallanta, kar6e handout din hannunta
yayi ya ce "Wai yanzu kam baki da lokacina ko Fatima?" Dan zaro ido tayi ta mike
tana kallansa ta ce "Allah sarki Yayana, wallahi ba haka bane kaga final exams
zanyi ga babynka kullum yayita damuna" ta karashe maganar tana turo baki, rungumeta
yayi sosai yana shafa cikin ya ce "Soon zaku rabu Baby, 2 months ya rage mana" ta
danyi murmushi ta ce "I hope so, ranar dana haihu zanyita bacci ko sweetheart?" Ya
bata light kiss ya ce "Exactly Babynah" dan zabura tayi ta ce "Wait!! Honey did
anyone came today?" Ya ce "Wa kenan?" Ta ce "Sadeeq tailor, yace zai kawomin
dinkuna na" ya girgiza kai yana murmushi ya ce "Bai kawo ba, nidai ya kirani yace
in baki hakuri" wayarta ta jawo akan bed side drawer yayi saurin kwacewa ya
rungumeta ya ce "Me zakiyi?" A fusace ta ce "I want to call him, bayan shi yayi
alkawari zai kawomin har gida, wallahi idan bai gama..." Bakinshi da taji a cikin
nata ne yasa tayi shiru, ya fara bata hot and romantic French kiss, kusan 3 minutes
suna a haka kafin ya zare bakinshi a hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce
"Ya kawo yana dakina" ta danyi murmushi ta rungumeshi ta ce "Da gaske Yayana" ya
daga mata kai, ta sake sakin wani kyakkyawan murmushi ta ce "Dama ya za ai ina
yayar Amare kanwar ango ace ba'a kawomin dinkuna na ba" dariya ya danyi ya ce "Kin
dai girmi Khairiyya amma Ikram tafi ki" ta dan turo baki ta ce "Amma ai Yayanta
nake aure sabida haka i'm her Aunt" collapsing tayi a jikinsa ta ce "Yaya Ikram
dinmu zata sha girki, ance fa Ya Sameer baya awa daya baici abinci ba, he eats
alot" shi dai murmushi kawai yayi hannunsa na kan cikinta ya ce "Da zaki zama
kamarsa dana fi kowa jin dadi" ta zaro ido ta ce "Ni din" ya ce "Eh mana, nafiso
kiyita cin abinci ki kara kiba" a hankali ta ce " To zan dinga ci" daga haka ta
mike da kyar ta sauka akan gadon ta ce "Bari na dauko dinkin" ta fita ya bita da
kallo, duk sai yaji tausayinta sosai ganin yadda cikin ya mata nauyi, ya sauke
ajiyar zuciya yana addu'ar Allah ya rabata dashi lafiya.
Washegari ya kama Saturday ba school, da sassafe Rafi'ah ta tashi ta
musu breakfast sannan ta koma dakinta tayi wanka, sosai tayi wani sanyayyen kyau ga
cikinta dan dass lol, tana cikin daura dankwali aka bude kofar dakin, ta juya da
sauri jin kamshin turarensa, suna hada ido ta ce "Wooow, Yayana kayi kyau" ya
karaso inda take yana murmushi ya durkusa dai dai cikinta ya bashi kiss ya ce "Good
morning Baby" ya dora hannunsa akai, dan 6ata rai tayi ta juya kanta a hankali, ya
mike ya rungumeta ya ce "How was your night" kamar batasan yin magana ta ce "It
wasn't nice" ya dago yana kallanta da sauri ya ce "What makes it boring sweetheart"
turo baki tayi bata ce komai ba, ya danyi murmushi ya ce "Ni dai ban yarda ba,
ninasan yesterday night was so nice and sweet, ko in tuna maki" daga haka ya kai
bakinshi saitin kunnenta yana magana yana murmushi, dan tura shi tayi ta ce "Ni dai
banaso" ya ce "Then how are u?" Ta kara turo baki ta ce "I'm not fine" bakinshi ya
kai saitin nata ya bata light kiss ya ce "Laifi na miki ne?" Kamar zatai kuka ta ce
"Ba saida ka kula unborn dinka ba sannan ka kulani" ta karashe maganar idanta tap
da hawaye, wani serious and tidy hug ya bata yana murmushi ya ce "I'm sorry
sweetheart, ina sanki fiye da komai nawa, bama kece silar zuwansa duniya ba? I love
u more than u think" ta danyi murmushi itama ta rungumeshi ta ce "I love u so much
my Barrister" hannunta ya kama suka fita a dakin sukai breakfast, bayan sun gama ta
dauko veil dinta da side bag tana kallansa ta ce "Let's go" ya ce "Nifa banasan a
kallan min ke" ta kalli jikinta ta ce "Yaya to ai ba'a ganina" mikewa yayi ya gyara
mata veil din ya ce "Cover my property" ya karashe maganar yana kashe mata ido
daya, ta danyi murmushi ta kama hannunsa suka fita, key yasa a kofar sannan suka
wuce parking lot, ya bude mata mota ta shiga ya zagaya nasa mazaunin ya kunna
motar.
Suna hawa bakin titi ya kamo hannunta ya ce "What gift do u want for ur
convocation?" ta juyo tana kallansa ta ce "Saura 5 weeks fa Yaya" ya ce "I know, so
nake na sani da wuri" ta danyi murmushi ta ce "Just anything sweety, i will
appreciate what ever u give me" ya ce "Kin bani za6i kenan?" Ta daga masa kai, ya
ce "Ohk angama". Few minutes ya kaisu gida, yayi parking ta fito tana kallansa ta
ce "Sai dai ka bini a baya" ya danyi murmushi ya bi bayanta bayan ya rife motar, a
balcony ta tsaya jin hayaniya a parlorn, bayan Jawad ya karaso ta kamo hannunsa ta
ce "Kamar sunyi baki" shidai bai saketa ba kuma baice komai ba, ya murda handle din
kofar, Khairiyya ce da Ikram sai Sadeeq suna buga uban musu, suna ganinsa duk sukai
shiru sai Sadeeq dake dariya yana fadin "Baku da wayo ai, ku yarane" shigowa Jawad
yayi yana rike da hannun Rafi'ah, ganin su Khairiyya ne yasa ta saki murmushi, suka
taso da sauri suka rungumeta, Jawad dake kallansu ya ce "Ku kyaleta ta xauna" suka
saketa kowaccensu na murmushi suka gaishe shi, a takaice ya amsa yana kallan Sadeeq
ya ce "Kaima dai ka nemo mata aure zan maka" Sadeeq ya kwashe dariya ya ce "Allah
ko Yaya" Jawad ya ce "Uhm" daga haka ya shiga part din Mami, Rafi'ah ta kalli Ikram
dake zuba mata zance ta ce "Ku rakani wajen su Mami" hannunta Ikram ta kama suka
shiga part dinsu, Mami na zaune ita da Mummy da uban kaya gabansu suna hadawa cikin
akwati, duk kuma dinkakku ne, Rafi'ah ta zauna kanta a kasa ta gaishe su, Mami ta
ce "Ya jiki kuma" a hankali ta ce "Da sauki" Ikram dake kallan Khairiyya ta ce
"Kinga wai su Mummy suma harda anko, jiya sun cika wani akwati yau ma sun cika
wani" ita dai Khairiyya murmushi kawai tayi, Mummy ta dalla mata harara ta ce "To
kar muyi anko, kijimin iskanci banda bikinki sai kuma na Sadeeq idan yana da niyya,
saboda haka gara muyi yadda muka ga dama" dariya sukayi Mummy ta ce "Ai gaskiya ne,
idan kuwa Sadeeq yayi aure sai bayan shekaru kafin Abdul shima yayi, lokacin dai
karfinmu ya kusan karewa, sai kuma na Imaan idan da kwanan mu" Jawad ya ce "Ni baza
a yiwa yarinya na auren wuri ba" Mummy ta kama ha6a ta ce "Ikon Allah, ita wannan
figigiyar matarta ka shekaranta 17 tayi auran farko, kaima kuma a shekara 21 ka
aureta idan auran wuri ne ai bakayi magana ba" ya dan ta6e baki ya mike yana kallan
Imaan dake bacci a kan kujera. Mikewa Rafi'ah tayi suka shiga dakin Ikram, bayan
sun zauna Ikram ta ce "Anty ankawo mana dinkinmu bari kigani" Ikram ta jawo wani
babban akwati ta ce "Sauran suna dakin Mami, anko zamu dingayi har a gama bikin"
ita dai Khairiyya tayi shiru, dan harga Allah kunya take idan ta tuna wai Yusuf
zata aura musamman a gaban Rafi'ah,,,, kaya kala kala duk bibbiyu iri daya Ikram
taita fito dasu tana nunawa Rafi'ah, sunyi mungun kyau sosai, Rafi'ah ta ce "Masha
Allah, Allah ya kaimu nan da 2 weeks din nan musha biki" daga haka ta kalli
Khairiyya dake boye fuskarta a jikin gado, kamo hannunta Rafi'ah tayi ta ce "Zo
muyi magana Khairi na" Khairiyya ta matsa kusa da ita a hankali ta ce "Gani Anty"
Rafi'ah tayi murmushi ta bata side hug ta ce "Ki daina kunyana dan Allah, idan ba
haka ba zan kira Yaya Yusuf na gaya masa kuma zance ko magana bakya min" ta dan
zaro ido tana murmushi, Rafi'ah ta saukar murya caan kasa ta ce "Ko baki aureshi ba
dole watarana zaiyi aure, kuma nima ba gashi nayi aure naba, ki saki jikinki ni ki
daina kunyana haka nan, i pray ma in the next 1 year Imaan nada kanwa" tayi saurin
runtse idanta tana murmushi, Ikram ta ce "Anty wallahi ke kadai takewa kunya, kinga
wayar data dinga yi jiya da daddare" Rafi'ah ta ce "Na sani ai, yaushe suka zo?" Ta
ce "Kwanan su uku yau, nima idan zasu tafi zan bisu nayi kwana biyu" Rafi'ah ta ce
"Ina din?" Ikram ta ce "Gidan Ammi" Rafi'ah ta ce "Ehh lallai baki da kunya, kuma
duk ana kallanki sai a barki kije" Ikram ta danyi baya sannan ta ce "Ehh mana, kema
fa Anty da kina kwana a gidan nan, kuma ai abinda kuke keda Yaya yafi wanda nayi"
pillow Rafi'ah ta jefa mata ta ce "Banasan sharri kuma, aini akwai yayar mamana a
gidan, ke kuma wajen wa zakiji?" a hankali ta ce "Ya Sameer" sakin baki Rafi'ah
tayi tana kallanta, ita dai Khairiyya sai babbaka dariya take tana daga kwance,
Ikram ta dan harareta ta ce "To Khairiyya ma ta ban shawara, suyi hiransu muma muyi
namu" ta6e baki Rafi'ah tayi ta mike da kyar ta ce "Ni bazan iya muku ba, bari naje
parlor" Ikram ta ce "Ai kuwa duk inda kikai binki zamuyi" bude kofar dakin akai
Imaan ta shigo da gudu ta rungume Rafi'ah, sosai ta kankame yarinyar tana bata kiss
ta ce "I missed u daughter" Imaan ta ce "I missed u too Momma", daga haka ta dauko
sabon Tablet dinta akan gado tana nunawa Rafi'ah ta ce "Papana ya siyamin sabo,
harda laptop" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Masha Allah, kince kin gode ko" ta
daga mata kai tana kallan Khairiyya ta ce "Ko Antyna?" Khairiyya ta ce "Ehh kin
fada" kama hannun Imaan Rafi'ah tayi ta ce "Ko ruwa baku bani ba kun tsareni da
surutu" mikewa sukai suka bi bayanta Khairiyya ta ce "Sorry Anty" daga haka suka
fita a dakin.
Abinci kala biyu suka jera mata a parlor taci tasha sannan suka ci gaba da hira,
kuma duk hiran akan yadda bikinsu zai kasance ne, karfe 3 da rabi Jawad ya dawo
gidan shida Yusuf da Aliyu, suna zaune a parlor suka shigo, Ikram ta mike tana
kallan Khairiyya ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Yauwa sannu, ina fatan baku
sata surutu da yawa ba" murmushi sukai gaba daya, bayan sun zauna Rafi'ah ta ce
"Ina wuni Ya Yusuf" ya ce "Lafiya kalau our future Barrister" ta danyi murmushi
kanta a kasa, sai boye cikinta take da hijabi, Jawad ya ce "Ba Ya Yusuf zakice ba
ango zakice" ita dai murmushi tayi ta mike tana kallan Aliyu ta ce "Ina yini" ya ce
"Alhamdulilah madam, ya gida" ta ce "Lafiya kalau" daga haka ta nufi part din
Mummy, Khairiyya dai da kyar ta gaishesu dan kunyan Jawad take, ko yana waje bata
fiye magana ba, itama kuma Ikram haka ne, tsoransa take gani take kamar zai iya
dukanta idan tayi shirme. Hannun Khairiyya Ikram ta kama suka shiga part din
Mummy, suna zaune a parlor ita da Rafi'ah suka shigo, Mummy ta ce "To kun kai musu
abin sha?" Ikram ta dan ta6e baki ta ce "Khairiyya ki kai musu" wani kallo
Khairiyya ta mata ta ce "Wallahi ke zaki kai" kasa kasa Ikram ta ce" Ai naga ba azo
da Yaya Sameer ba" Khairiyya ta dan turo baki ta ce "Mummy kinji abinda tace ko"
Mummy ta ce "Cewa nayi fa kuje ku kai musu abin sha, kuyiwa Mami magana nima yanzu
zanje mu gaisa" daga haka ta mike, Rafi'ah ta ce "Mami tayi bacci ita da Imaan,
bansan yanzu ko sun tashi ba naji an kira sallan la'asar" Mummy ta ce "Imaan ta
koya mata baccin rana, da dai batayi" Rafi'ah ta danyi murmushi kawai, hijabi Mummy
tasa ta fita a dakin, Rafi'ah ta kalli Ikram ta ce "Karku kai musu komai idan kunga
dama mu yanzu zamu tafi" Ikram ta danyi murmushi ta ce "Allah sarki Antyn mu insha
Allah a gidanki zamu ringa kwana da biki" mikewa Rafi'ah tayi ta dauki veil dinta
ta shiga daki, ba jimawa ta fito sai tayi kyau sabida ta shafa powder da lipstick,
Khairiyya ta kamo hannunta ta ce "Safe journey Anty, sai munzo next week" ta ce "To
Allah ya kaimu, Ikee bye bye" hannu duk suka daga mata sannan suka fita tare, part
din Mami ta shiga ta mata sallama sannan ta fito suka fita parking lot, Yusuf na
shirin fita suka fito, Rafi'ah ta daga musu hannu ta ce "Safe Ya Yusuf" ya ce
"Alright sis" daga haka ya kashewa Khairiyya ido yaja motar suka fita, da sauri ta
dauke kai Ikram nata dariya. Bude hannaye Jawad yayi yana kallan Rafi'ah, ta karaso
a hankali ta shige jikinsa, ya rungumeta, kallan su Ikram yayi ya ce "To mungode
bye bye" kansu duk a kasa suka juya, Ikram ta dan ta6o Khairiyya kasa kasa ta ce
"Yayanmu yanzu baya kunya" Khairiyya ta danyi dariya ta ce "Ya kai Yaya Sameer?"
Duka ta kai mata tayi saurin kaucewa ta shige gida.

_2 weeks ltr_

Su Ikram ne zaune a daki da friends dinsu suna ta pictures, sunyi kyau sosai cikin
kayansu iri daya, bude dakin akai Rafi'ah ta shigo da warmer a hannunta, sosai tayi
wani mungun kyau sai sheki take, ga cikinta ya fito sosai cikin gown din jikinta,
juyawa Khairiyya tayi tana kallanta ta ce "Wooow Antyn mu u look so cute" Rafi'ah
ta danyi murmushi tana amsa gaisuwar da friends dinsu ke mata ta ce "Ai kune da
kyau Khairi, Amare irinku haka kyawawa" dariya suka danyi Ikram ta ce "Pls Anty
Yaya ya fita ne?" Rafi'ah ta ce "Yana daki, is anything wrong" kamar zatai kuka ta
ce "Dama zamuje Saloon ne kuma naji dazu yace baxamu sake fita ba sai za'aje kamu"
murmushi ta danyi ta ce "Zan mishi magana, sai drivernsa ya kaiku, ga abinci nan
kuci" daga haka ta juya ta fita, daya daga cikin friends dinsu ta ce "Woow Antynku
ta birgeni Ikram, kyakkyawa ce" Ikram ta danyi murmushi ta ce "To ko zaki dawo ku
zauna tare" dariya sukai sosai sannan Khairiyya ta jawo warmer da plate ta fara
zuba musu abincin.
Tana bude dakin ta sameshi gaban mirror yaci Ash shadda yana saisaita hular kansa
ya juyo suka hada ido, ta danyi murmushi ta karasa gabansa ta ce "Masha Allah
Yayana me kyau" rungumeta yayi yana shakan kamshin jikinta ya ce "I love u wife,
inasan kullum in dinga jinki a jikina, i don't want to miss u even for a seconds"
daga haka ya shiga kissing dinta passionately, bayan seconds ta zame jikinta tana
dariya ta ce "Naki yawan" ya ce "Pls" juyawa tayi ta koma bakin kofa ta ce "No pls,
Yaya su Ikram zasuje Saloon" ya ce "Let them, amma daga nan su dawo" ta ce "To,
bakamin fishi bako?" Ya ce "Uhm" juyawa tayi tana murmushi ta fita a dakin, kasa
kasa ya ce "I will caught u".
Karfe 5 na yamma aka shirya amare tsaf cikin kayansu iri daya aka tafi wajen kamu,
kowa da kowa ya tafi amma banda Rafi'ah dake hannun Jawad, tana zaune bakin mirror
daure da towel tana turo baki ya fito a toilet, ta dauke kanta taci gaba da abinda
take, kusanta ya karasa ya rungumeta ta baya ya ce "I'm sorry wife" kin kulashi
tayi sai dai hawaye ya taru tap a idanta, ta zame jikinta a hankali zata tashi ya
ce "Won't u pardon me Baby, yau fa throughout baki kula dani ba" kafin tayi magana
hawayen idanta ya shiga sakkowa, ya rungumeta sosai yana jijjigata ya ce "Kiyi hkr
dan Allah, bari na tayaki ki shirya mu tafi" ba musu ta zauna ya fara mata drying
kanta yana mata combing dinsa, bayan sun gama ya dauko kayanta dake kan gado ya ce
"Should i help?" Ta daga masa kai, daga haka ya tayata ta shirya, gaban mirror ta
zauna ta fara make up shi kuma ya fita zua dakinsa, within few minutes ta gama
make~up dinta me kyau, ta dora dankwalinta sannan ta feshe jikinta da turare ta
dauka veil dinta ta shafa, woow masha Allah tayi wani sanyayyen kyau, side bag
dinta ta dauka ta lankaya sannan ta fita a dakin, tsayawa tayi tana kallansa ganin
yadda yayi kyau, ya sakar mata murmushi ya ce "Masha Allah, zamu haifa cute babies
insha Allah" murmushi ta danyi ta dauko wayarta a jaka tana kallan screen din, ya
ce "Who's calling?" A hankali ta ce "Ameera" daga haka ta dauka wayar, Ameera ta ce
"Ban ganki ba" ta ce "Ina hanya Amarya" daga haka ta danyi murmushi tayi hanging
call din, Jawad ya ce "Ta kusa aure ne?" Ta ce "In the next 1 month zatai aure" ya
ce "Allah ya sanya alkhairi" ta ce "Ameen" daga haka ya bata side hug suka fita.
Suna shiga wajen kallo ya dawo kansu saboda yadda sukai kyau, ta dan
zame hannunta a cikin nasa ta nufi inda Ameera ke zaune, Imaan ta taso da gudu ta
rungumeta ta ce "Look at Papa" ta nuna mata Yusuf dake gefen Khairiyya a high
table, ta daga musu hannu tana murmushi sannan ta zauna tasa Imaan a cinyarta,
Ameera ta ce "Kuma kika bar Ogan a gefe" juyawa tayi taga yana zaune gefen Aliyu
suna hira, ta juyo sannan ta ce "Gashi ga abokinsa nan, ina Ogan naki ke?" Ameera
ta ce "Ya tafi Kaduna kuma yayi niyyar zuwa wallahi" Rafi'ah ta ce "Allah ya dawo
dashi lafiya" ta ce "Ameen, wai yaushe zaki haihu musha suna?" Rafi'ah ta ce "bayan
auranki da wata 1" Ameera ta ce "Kina nufin sauran wata 2" ta ce "Insha Allah"
Sosai da sosai akaci akasha sannan akai hotuna kowa ya watse. Washegari ya kama
Saturday karfe 1 aka daura auren Yusuf da Khairiyya da Sameer da Ikram, bayan 'yan
daurin aure sun dawo akai hotuna sosai. Da Daddare kuwa bayan Isha aka fara shirye
shiryen kai Amare, gida daya aka kaisu kowa da nata part din, gidan yayi mungun
haduwa, suna kuka haka aka barsu kowa ya watse, Rafi'ah ta musu nasiha sosai sannan
ta basu misalai kala kala ciki kuwa harda abinda ya faru da ita, sanda ta tashi
tafiya saida suka sata kuka itama, da kyar ta daure ta karasa mota ta shiga, Jawad
dake zaune yana jiranta ya ce "Allah ya basu zaman lafiya, muma muje muci namu
amarcin" harara ta dan 6alla masa ta turo baki ta maida kanta gefe, yayi murmushi
yana shafa beard dinsa yaja motar suka tafi.

*4 YEARS LATER*

Yara ne guda biyu a compound din gidan suna wasa akan keke, kana kallansu kaga
twins ne saboda kamar da suke, fitowa Rafi'ah tayi tana kallansu ta ce "Oya you two
should come in" macen dake kallanta ta ce "Momma we are not hungry" Rafi'ah ta dan
harareta ta ce "I'm not talking of food, Oya Aisar carry your bike it's cloudy"
sauka yayi akan keken yana kallan Aira dake turo baki ya ce "Wai kuka zakiyi?"
Rafi'ah ta kalli cute girl dinta ta ce "What again daughter?" Kamar zatai kuka ta
ce "I want to see my Papa" dan tsaki taja a hankali ta ce "He will soon come back"
daga haka ta kama hannunsu suka shiga ciki. Suna zaune a parlor sunyi pillow da
cinyar Rafi'ah sukaji horn, a tare suka mike suka fita da gudu ta danyi murmushi ta
bisu da kallo. Parking lot suka nufa da gudu, suna tsaye suna ta tsalle har Jawad
yayi parking, ya fito yana kallan Imaan dake faman turo baki ya ce "U close the car
idan kin gama fishin" daga haka ya jefa mata key din motar ya nufi wajen kids, da
gudu suka dale jikinsa suna dariya, ya ce "How are u my twins?" Suka amsa da "Fine"
daga haka ya sauke su ya kama hannunsu, Aisar ya ce "Papa Anty Imaan bata sauko ba"
ya ce "She will come in" daga haka suka nufi cikin gida, Rafi'ah na tsaye bakin
kofa tayi wani mungun kyau, ya bata light hug sannan ya zauna ya ce "Sannu da gida"
ta ce "Sannu da dawowa, ina Imaan?" Ya ce "Tana mota, fishi takemin na hanata zuwa
birthday gobe" Rafi'ah ta dan ta6e baki ta ce "Ta gayamin dazu nace saita
tambayeka" ya ce "Just forget, banasan fita yawo daga yanzu, duk da kaita za'ai but
i don't want her to be going out anyhow" ta danyi murmushi ta ce "Allah ya kyauta,
Mami na gaisheka" ya ce "Ke kika daukosu a school ne?" Ta ce " Dazu dana tashi a
aiki naje na daukesu, Mummy tace a kaisu weekend" ya ce "Allah ya kaimu" ta ce
"Abinci fa?" Ya ce "Let me bath first" daga haka ya mike, dai dai nan Imaan ta
shigo rike da school bag dinta, fuskarta ko walwala babu tana ta faman turo baki
ta nufi upstairs, kama hannun Rafi'ah Jawad yayi ya ce "Imaan kamar ke a da, saam
halayanki ta dauko" ta danyi murmushi tabi bayansa suka haura stairs, dakinsa suka
shiga ya juyo yana kallanta ya ce "Zaki tayani ko?" Ta dan zaro ido ta ce "Me din?"
Ya ce "Wanka" ya karashe maganar yana kashe mata ido daya, ta ce "Noo, na bar kids
dina downstairs" ya ce "Ba cartoon suke kalla ba, just let them" ta dan noke kafada
ta ce "No, sai ka fito sweetheart" daga haka ta jawo masa kofarsa tana dariya,
dakin Imaan ta shiga ta sameta zaune bakin gado tana danna laptop, Rafi'ah ta zauna
a gefenta ta ce "Meyasa bakyaji Imaan, do u mind kiyi tasa Daddynki magana ne" ta
dan girgiza kai a hankali ta ce "Ai dama cewa yayi na tambayi Papa kuma shima yace
bazanje ba, Momma she's a good friend of mine fa" Rafi'ah ta kamo hannunta ta ce
"That doesn't mean kiyi musu fishi, ki kira Daddy ki bashi hkr sannan ki samu Papa
a daki anjima, be a good daughter pls" dan murmushi tayi ta rungumeta ta ce "Thank
u Mum, and i love u" Rafi'ah ta dan bubbuga bayanta sannan ta mike ta fita. Da
daddare Jawad na zaune a bakin gado yana aiki a laptop Rafi'ah ta fito a wanka, ya
ce "Yanzu Imaan ta shigo" ta juyo tana kallansa ta ce "Meya faru?" Ya ce "She
apologize, banda abin Imaan ma nawa suke da har zataje birthday, she's just 9 years
fa" Rafi'ah ta ce "Ahaaa ai sun zama 'yammata, nan da few years zaka fara siyan
gado" ya dan harareta ya ce "Karatu zatai" bata ce komai tana ta murmushi tasa
night gown dinta, gefensa ta zauna ta dora kanta akan kafadarsa ta ce "Sweetheart
Awara xanci" ya dan zaro ido ya ce "Awara Fatima?" Ta ce "Yes" rungumeta yayi ya
rife laptop din ya ce "Ko dai mun sake samun twins ne?" Ta dan harareshi ta ce "Not
now" ya hade bakinsu yana kissing dinta tayi saurin mikewa tana dariya ta nufi kofa
ta ce "Good night Yaya i'm spending my night in the other room" daga haka ta masa
gwalo, ya mike yabi bayanta ta juya da gudu kafin ta kai kofa ya rukota tana ta
dariya ta ce "Wait wait let me close the door" yana dan saketa ta kara sauri ya
kara rikota ya rungumeta, silently ya ce "I so much love u wife"

_Alhamdulilah anan na kawo karshen littafina me suna *SHARIK HAYATY*, ina rokon
Allah ya yafemin kuskuren da nayi 🙏🏻 abinda na rubuta daidai Allah yasa ya amfani
al'umma._

*_My dear Ilham, Khadijah (KK) 😘 i luv u with full of respect sisters, wallah
words only can't express how much i love u, u have been supporting me right from
the beginning, wallah i luv u 🥰_*

*_Our Sajeeda i luv u also 😊 And again Lubabatu Kaseem and Zarah can't forget with
u people thanks for d gift sisters 😍 Finallay the members of FSM grp and LIFE
PARTNER FANS grp, I so much appreciate with ur comment Fans, can't mention u oll,
ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke, da wanda na sani dama wanda ban sani ba,,
ni kaina i don't want to miss u, kusani a duk inda kuke FATIMA ZARAH na yinku over
and over, oneluv* 💕 *💃🏻💃🏻 sanku na daban ne ina Kaunarku sisters, thanks for the
support and comments 😘 can't mention u but i know u oll, Teemarh na sanku bila
adadin 💗_*

_08103810398_

You might also like