Kurkukun ‘Kaddara Book 2 Middle Steps by Boss Bature

You might also like

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 416

~*BOSS LADIES WRITERS*~_

*_💋KURKUKUN ƘADDARA💋_*

_The Prisoners🔥💫_

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty._

*Episode 1*

Zaro ido su Parveen su ka yi bakunansu a sake, yayin da su ke kallon ƙofar, Wani


irin farin Ciki ne Mara misaltuwa ya bayyana akan fuskokinsu Har sun wage baki zasu
Fasa ihu Angel Tai saurin Dakatar da su ta hanyar cewa"Kun manta abunda na faɗa ma
ku? Komi za ku gani ku ja Baki ku yi shiru idan ba haka ba asirin mu zai tonu har
su gane abunda mu ke ƙoƙarin yi' Fuskokinsu Haris da alamun ruɗu donsu basu son kan
me ta ke magana ba, sun dai ga murfin ƙarfe jikin bango, bayan haka sunji batul
tace ƙofar da su ke nema.

Naufal ne yai ƙoƙarin buɗe baki Yace"Angel Kun bar mu a duhu, bamu san kan me ku ke
magana ba" ya ƙarasa maganar idanunshi akan fuskarta, har lokacin bata daina sakin
murmushi ba, Haka zalika su parveen Bakin su awashe ya ke Kamar Gonar audugu Ji su
ke kamar ma Har sun fuce daga Cikin kurkukun.

"Ki yi mana bayani mana, Wannan murfin ƙarfen na menene a jikin bango"? javed ne
yai maganar, sautin Muryoyin su daƙyar ya ke fita saboda rashin ƙarfin jikin su,
har ƙwara sauran mazan akan mubeen ko da su ka shigo toilet ɗin kan shi na asaman
Kafaɗar Hannah, Sam babu kuzari a jikin shi.

"Na ruɗe Angel Ki fada mana mun ƙosa Mu ji," acewar Gabriel.

duk wanda yai magana acikin su idanuwanta na akan la66ansa, Sai bin su ta ke yi da
kallo, farin Ciki Ya hana ta yi magana.

"Idan ba zata Iya yi mana Bayani Ba, Deeja Ku faɗa mana Meke faruwa ne'? Haris ne
yai maganar idon shi akan su Deeja dake a tsaitsaye Cirko Cirko.

Ganin sun fara fusata Yasa ta haɗiyi yawu tare da sauke nauyayyar Ajiyar zuciya,
Cikin sanyin murya ta soma kora masu jawabi sannu a hankali ta fayyace masu komai
dangane da ƙofar sai dai ta 6oye masu Game da tattaunawar da su ka yi Ita da
Salsabeel.

Tsabar mamaki yasa su ka dinga jefawa junansu kallo Lokaci ɗaya wani irin Annurin
farin Ciki Mara misaltuwa ya lullu6e zukatan su, Har basu san lokacin da suka
ƙarasa gaban Angel suka ɗago da ita daga zuƙunnan da take abakin Bango, gaba ɗaya
su ka rungumeta, Kamar zasu Karya ƙasusuwan Jikinta, Musamman Gabriel da ya fi kowa
burin son ku6uta daga kurkukun ƙaddara, zafafan hawaye ne su ka soma gangarowa ta
saman fuskarta, ta rasa gane hawayen menene? Shin na farin Cikin da ta ke yi ne ko
kuwa na baƙin Ciki? Ɗaya bayan ɗaya ta ke kallon su Bayan sun sake ta, Maganar da
ke yi mata yawo acikin kanta itace"kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku za ku Rayu!
wannan maganar ta yi matuƙar tsaya mata aranta, ta ta6a zuciyarta, fatan ta Allah
yasa Mutuwar kada ta rusƙe su agidan kurkukun ƙaddara, ba zata so wani daga Cikin
su ya ƙara rasa ran shi a wannan Ƙazamin Ginin ba, Duk idan ta tuna Matasan Yaran
da ta gani awannan ɗakin lokacin da ta dura taga taje ta gane ma idonta su Rataye
Saman igiyoyi kamar dabbobi sai ta ji duk jikin ta ya mutu, Haƙiƙa ta yi matuƙar
girgiza ganin yadda Suke feɗe Cikin mutun mai rai su kwashe sassan Jikin
shi........"

Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda Angel ta fashe da matsanancin kuka
tamkar ranta zai fita har wani jiri ta ke gani acikin idanuwanta, Daƙyar ta jingina
bayanta Jikim bango, taci gaba da riskar kukan ta Fuskarta jaga jaga da hawaye.

Murnar da su ke yi ce ta koma Ciki, Damuwa ta bayyana Akan faces ɗinsu, Har suna
haɗa baki wurin furta Sunanta
"Angel! Why are u shedding ur tears? Dan Allah kada kisa zuciyoyin mu su karaya,
Baki ji irin farin Cikin da mu ke yi ba, saboda Kin gano mana ƙofar da zamu bi, don
mu ku6uta daga kurkukun ƙaddarar, Gidan da aka ƙuntata rayuwar mu aka hana mu
sakat, Shekara da shekaru tun muna jarirai har zuwa lokacin da muka fara mallakar
hankalin mu, Angel dukkan mu nan babu wanda bai haura shekara sha wani abu ba a
gidan kurkukun Nan, Ta ya ya ba zamuyi farin Cikin Ganin ƙofar nan ba? muna so mu
tsira kodan Muga ya wajen kurkukun nan ya ke, Muna so muga hasken dake awajen shi,
koda da numfashin mu na ƙarshe ne, mu dai burin mu, shi ne mu ga mun ku6uta, Idan
ma kina tunanin ba zamu Iya tsira mu dukkan mu ba, Zamu roƙi Allah da ya ara mana
lokaci mu bar kurkukun nan wlh bamu fatan mu yi wulaƙantacciyar mutuwa acikin shi!
Mun fi so Mutuwar ta risƙe mu acan inda zamu je koma akan hanyar Guduwar mu
ne......." Kalamansu sun ƙara karya mata zuciya, kallon da take binsu da shi da
rinannun idanuwanta waɗanda suka canza launi kallo ne da ke nuni da tsantsar ƙaunar
su, tausayin su da ta ke ji, Ko ɗaya daga Cikin su ba ta son ta rasa, sai dai tasan
ba abune mai yiwuwa ba, Mutuwa dole ce!

Tsawon lokaci Suna ta shan kukansu musamman Batul da su Azeeza in ka cire mazan da
ke a cikinsu, hawaye ne kwance acikin fararen idanuwansu.

"Muna 6ata lokaci Angel, Ni zan fara jaraba 6alle ƙofar," Gabriel ne yai maganar,
Shi da ba ƙoshin lafiya ba. A haka ya nufi ƙofar ya zuƙunna yana tatta6a Jikinta.

"Nima zan ta ya ka" acewar Naufal, yai maganar tare da matsawa kusa da Gabriel Ya
zuƙunna, Atare suka dunga bugun ƙofar da niyar ta buɗe, sun haɗa uban gumi akan
fuskokin su, murfin ƙarfen ko motsi bai yi balle su sa ran zai buɗe.

Matsawa Haris yai kusa dasu Shima ya sanya hannun shi, Hada matan kowa Ya shiga
gwada ƙarfin shi akan ƙofar don ta buɗe, Duk wannan budurin da ake yi Jemimah Tana
acan cikin ɗakin su kwance saman gado, ta lullu6e kanta da bargo baccin ne bai ishe
ta ba.

Sun ɗauka cewa abun wasan yara ne shiyasa su ka dage akan sai sun buɗe ƙofar, Mayen
ƙarfe ne murfin da ke ajikinta Yana da ƙarko Shekara da shekaru wurin yana adatse
ta ya ya zasu iya buɗe shi? Yaran da ba lafiya gare su ba, Ganin yadda suke ta
gabzar ƙofar ko sautin bugun da su ke yi mata bai fita sun Dage sun nace akan dole
sai sun buɗe ta..

"Haris! Gabriel! Ku daina wahalar da kanku, Ƙofar ba zata ta6a buɗewa ba, saboda
babu babban mukullin da zamu Iya buɗe ta da shi,". Jin wannan maganar da Angel ta
yi ne yasa su ka mimmiƙe tsaye sai nishi suke fitarwa ta ko'ina sufa ke tsastsafo
masu a jikin su

Atare suka haɗa baki wurin faɗin"Makulli? A ina zamu same shi? Dan Allah ki faɗa
mana inda ya ke"
Zuciyarta ba ƙaramar karaya ta yi ba a yayin da su ke tambayarta ina makullin ,
wani abu da ta lura dashi gaba ɗaya hankalin su ba'a kwance ya ke ba, duk sun
furgice burinsu kawai su bar kurkukun.

"Angel kin yi shiru baki amsa mana ba" Jan numfashi ta yi tare da sanya tongue
ɗinta ta ɗan lashi lower lip ɗinta da ya bushe Cikin sanyi murya ta soma yi masu
magana

"Danish! Shine makullin Da zai Iya 6alle mana ƙofar, gashi baya atare damu Yana
acikin kurkuku, Yanzu dole sai mun nemo shi idan har muna son mu ku6uta ......." a
matuƙar ruɗe su ke jefa mata kallo, Dole su yi mamaki, Ta ya ya Danish da ya
kasance Ragon Namiji acikin su zai zama Makullin buɗe ƙofa? How that can be
possible? Ta ina Danish ya ke da ƙarfin yin hakan? ganin irin kallon da su ke binta
dashi yasa ta fahimci cewa Basu gasgata maganarta ba. Suna buƙatar ƙarin haske.

"Bazan Iya yi ma ku dogon bayani ba, because you won't understand me, but
definitely Danish is the key to open the door, just believe my words, he can open
it,"

Lamarin ya yi matuƙar ɗaure masu kai, Musamman Haris shi da yafi kowa sanin Danish,
mutumin da ko ƙwaro Tsoron shi ya ke ji yau shine Angel ta ke kira da makullin buɗe
ƙofa.

"Maganar ki gaskice! Ni shaida ne akan hakan! Danish ne kaɗai zai Iya buɗe ƙofar!
kusan atare suka ɗaura Idanuwansu akan fuskar Gabriel da yayi maganar.

"Nasan za ku yi mamaki, Dalilin da yasa nace haka, Saboda kokawar da muka ta6a yi
dashi, lokacin da Danish Ya shaƙi wuyana da hannun shi, Shaƙar da bana tunanin
cikakken mutunne yayi mini ita, Ni nasan mai naji a lokacin da har yaja na naushi
idonshi, ƙarfi ne dashi naban mamaki, tabbas shi zai iya buɗe ƙofar......" tunkan
ya ƙarasa rufe baki Haris yace"Kun rikita mini tunani na, Taya mutumin daya rasa
idon shi ɗaya zai Iya yin hakan? Bayan ni asani na Danish bashi da wani ƙarfi,"
Fuskar shi da alamun ruɗu yai maganar.

"Danish Ya rasa ido"! Batul ce ta ambaci hakan Idanuwanta azazzare hankalinta ba


ƙaramin tashi yai ba jin abunda Haris yace don ita bata san da zancen rasa ido da
Danish yai ba, sun6oye mata don karsu tayar mata da hankalinta.

"Danish bai rasa idonshi ba, Sun samu sa6ani da Gabriel ne, Har takaiga ya naushi
idon shi, wanda silar hakan Giant yazo ya tafi dashi, Na 6oye maki hakan ne saboda
bana son hankalin ki ya tashi, Kuma Ni da kaina Danish ya faɗa mini cewa Lafiyar
shi qalou ba abunda ya same shi, ' Angel ce ta kora mata jawabi, Hankalin batul
yaƙi kwanciya da kalamanta, jikin ta yayi sanyi, hawaye tuni sun soma yin sintiri
saman kuncin ta.

"Shikenan Yanzu ki faɗa mana Taya za'ae mu ga ɗan uwan mu Danish? Idan ma ta kama
Ni zan bi ki mu shiga prison ne don mu nemo shi" Gabriel ne yai maganar da ƙwarin
gwiwarsa, Har yanzu yana nan da rashin tsoronshi.

Girgiza kai Angel tayi"wannan aikina ne, Ni kaɗaice zan Iya dawo da Danish Cikin
mu, In sha Allah, "

"But how could you do that? Bayan babu wata ƙofa da zaki Iya shiga prison"? Har ta
buɗe baki da niyar Ta amsa Ma Naufal tambayar da yai mata, kwatsam! ba zato ba
tsammani Kunnuwanta su ka jiyo mata motsin buɗe ƙopar ɗakin su, hakan yasa tai
saurin Katse maganarta, Idanuwanta azazzare Take kallon su.

"Kamar buɗe ƙofar ɗakin Mu ake yi? Mun shiga uku, Asirin mu zai tonu, wlh mu gudu
daga Cikin toilet ɗin nan," Parveen ce tai maganar, hankalinsu idan yai dubu toh ya
tashi, Gaba ɗaya duk sun bi sun ruɗe, a sukwane Angel ta juya da gudu ta nufi Ƙofar
toilet ta buɗe ta, Fucewar ta keda wuya suma suka bi bayanta, garin gudu har suna
bangaje juna, Adai dai lokacin da suka faɗo tsakiyar ɗakin, kowannansu ya tsaya
da tafiya, Idanuwansu azazzare su ke bin benan da kallo, sai faman haki suke yi
babu mai sauran kwanciyar hankali acikin su, babban abunda su ke jima fargaba kada
ace Tsohuwa zafreen ce, Ilai ko hasashen su Ya zama gaskiya, ƙofar na ƙarasa buɗewa
kunnuwansu suka soma jiyo masu takun takalmanta Har wani sauti su ke badawa ƙwas
ƙwas! Jikinsu Ya hau kakarwa zufa ta dinga tsastsafo masu ta ko'ina a jikin su.

Cikin muryar raɗa Deeja tace"Mun shiga uku Angel mun manta bamu maida tukunyar
fulawar nan ba! Yanzu idan ta shiga toilet ɗin ya zamu yi?

Ƙasa ƙasa da murya Angel ta ce"In sha Allah ma ba zata shiga ba, Idan ma tai
yunƙurin yin hakan zan dakatar da ita," ita kanta da ta ke yin maganar a tsoroce ta
ke furtata, ƙarfin halin ne kawai.

Ahankali ta ke tunkaro in da suke atsaye Cikin shigarta ta jajayen kaya, Yau babu
mask a kan fuskarta, Daga bayanta Giants ne Guda Biyu masu ƙirar Samudawa, ko da ta
ƙaraso dab dasu saita dakata da yin tafiyar A tsanake ta ke binsu da kallo ɗaya
bayan ɗaya, Saboda tsabar ruɗu da kama kai, Jikin Angel na 6ari ta russinar da
kanta Ƙasa muryarta babu natsuwa ta furta"Ina kwana" Tun da tsohuwa zafreen ta kafe
ta da ido sam ta kasa motsawa, Lamarin ne ya ɗaure mata kai, Yadda Angel ta duƙa
mata wurin gaishe da ita.....
Da sauri su Haris suka russinar da kansu tare da gaishe da ita Cikin girmamawa.

Babu wanda ta amsamawa a cikinsu, Tsawon mintuna biyar kafin ta ɗan yi gyaran murya
tare da basu Umarnin su ɗago da kawunansu, bayan sun ɗago ta tsare fuskar angel da
blue eyes ɗinta, Suspicious looking ta ke binta dashi Hatta tsigar jikin Angel sai
da ta tashi haiƙam, Sam takasa yarda su haɗa ido da tsohuwa zafreen, ta dage tana
ta wasa da yatsun hannunta, ta harɗe su acikin na juna, Su ta ƙurawa ido.

Su Deeja duk sun sha jinin jikin su, ganin irin kallon da tsohuwa zafreen ke bin
Angel da shi, Kuskuren da Angel ta tafka shine gaishe da zafreen da ta yi, Mace
Dattijuwa irin zafreen wadda taga jiya taga yau, Taya zata Iya yi mata wayau?
Yarinyar da bata ta6a gaishe da ita ba, sai yau Hakan ya ƙara sanya mata zargin
wani abu na faruwa a ɗakin nasu, A hankali takawar da idanuwanta daga kan fuskar
Angel ta soma bin fuskokin su Batul da kallo, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi,
sam babu alamun gaskiya atattare dasu, duk wani motsinsu akan idonta.

Ba zato ba tsammani suka ga ta tuntsire da dariya mai sautin gaske hankalinsu ya


ƙara ɗugunzuma, a firgice su ke bin ta da kallo, Lokaci ɗaya ta dakata dayin
dariyar ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri.

"Meyasa ki ka yi gaggawar gaishe dani tun kafin in buƙaci hakan? Kamar daga sama
Angel taji ta jefa mata tambayar.

Yawu ta haɗiya kutt a maƙoshinta, Idanuwanta na kallon Ƙasa azazzare ta soma magana
Cikin rashin natsuwa

"Nagane kuskure na, kuma Na yi danasanin rashin kunyar da na yi maki a kwanakin


baya, inaso na gyara tsakanina dake ne saboda nasan ban kyauta ba.." tunkan ta kai
ƙarshen maganar tsohuwa zafreen ta soma sakin bazawarin murmushi, wanda silar hakan
yasa ta kasa ƙarasa zancen da ta kamo.

"Saboda meyasa kike son gyara tsakanina da ke"? Ras taji gabanta ya faɗi, Daƙyar ta
tattara natsuwarta kafin ta ci gaba da magana"Mahafina bai koyar dani rashin kunya
ba, Tunkafin rasuwar shi yana yawan yi mini nasiha akan girmama na gaba dani, amma
saboda rashin jin magana irin nawa ban bi abinda yake koya mini ba nayi
danasani........" Sosai ta fashe da kuka gaba ɗaya idonsu Hibba akanta, Tsabar
mamaki yasa suka saki bakunansu suna kallon Fuskarta, Ba ƙaramar ƴar drama bace.

Da buɗar bakin tsohuwa zafreen sai cewa tai"well done Unaisah! Dila sarkin wayau!
Da ace ke ƴar film ce tabbas zaki iya cin gasar wadda tafi kowa Iya wasan
kwaikwayo, Tun da nake ba ata6a rainin mini wayau irin na yau ba, Ƴar ƙaramar
yarinyar da na yi jika da ita...." maganar tsohuwa zafreen ba ƙaramin ƙara ɗaga
masu hankali ta yi ba, duk sun sha Jinin Jikin su.

"Ku faɗa min Me ku ke shiryawa ne" Shiru su ka yi ƙirjinsu na bugawa , Mirmushin


gefen fuska ta saki tare da cewa"Dama nasani ba za ku faɗa mini ba, Idan naso zan
iya yin anfani da sihirin da nake dashi wurin jin abunda zuciyarku ke saƙa maku, Ko
in sanya ku yi mini magana da kunan ku,'

Yanayin yadda suka zazzare Ƙwayar idanuwansu tamkar zata faɗo ƙasa, tsoro da
firgici ne tsantsa akan fuskokin su.

Ganin tana ƙoƙarin buga sandarta ƙasa Yasa Angel tai saurin cewa"Zan faɗa maki
gaskiya, " tsayar da ido zafreen tayi akan fuskarta.

"Tattaunawa mu ke yi akan yadda zamu ku6uta daga Cikin kurkukun nan saboda mun gaji
da rayuwar kulle, Muna so mu ma mu yi rayuwar ƴanci kamar yarda sauran mutane su ke
Yi"

Daƙyar ta kai ƙarshen maganar tana mai haɗiyar yawu, Su Batul duk suna sauraronsu
babu wani mai natsuwa a cikin su.

"Ban yarda da maganar ki ba, A iya sani na prisoners basu da hankalin Yin tunani
mai kyau irin wannan balle har su baki haɗin kai ku tattauna da junanku, Ke ce kika
tsara komai Unaisah, saboda kina son karkatar da hankalina don In yarda da maganar
ki, "

Tun kan ta ƙarasa maganar ta soma bin ɗakin nasu da kallo, Kamar sakarkaru haka
suka dinga binta da ido Cike da fargabatar karta faɗa sashen toilet ɗinsu asiri Ya
tonu, A hankali take tafiya tana ƙarewa ɗakin Kallo Kafin Ta Juyo a sukwane Ta tun
kari sashen toilet ɗin su, Tashin hankalin A matuƙar tsorace suke kallon bayanta,
Giants ɗin dake atare da ita basu motsa ba, suna atsaye Kamar gumaka

Su Angel Ido ya raina fata, Sai faman Cizon yatsa ta ke Yi, Ji take kamar ta watsa
aguje tasha gaban zafreen.

"Innalillahi Ya Allah ta makance kafin ta shiga, Ya Allah ka taimake mu! ya Allah


ka hanata gani" Acikin zuciyoyinsu suke furta hakan, Suna ganin ta shige Ciki, Zufa
ta soma wanke fuskokinsu, Azeeza tuni ta fara matse kwallo, sun san dole Taga
abunda suke aiwatarwa, Idan kuwa harta gano zasu ɗanɗani kuɗarsu ne, Kowa zaiji a
jikin shi, Babban abunda yafi damun Angel gargaɗin da Salsabeel ya yi mata akan su
yi takatsantsan Yanzu idan asiri ya tonu gaba ɗaya taja masu masifa da bala'e.

Runtse idanuwanta ta yi sosai, hawaye ta ko'ina suka shiga wanke fuskarta,


idanuwansu Deeja akanta, Tausayin kansu ne ya kama su, Har sun fara hasashen irin
Azabtarwar da za'ayi masu kafin akashe su, Sai bin Juna su ke yi da ido babu mai
magana saboda Giants ɗin da ke tsaye akansu.

Fitowa tsohuwa zafreen ta yi daga sashen toilet ɗinsu, Fuskarta ɗauke da shu'umin
murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa, girgiza mata kai su ka dinga yi ba tare da
sun iya furta komai ba, Sun riga da sunsan taga ƙofar nan shikenan ta faru da ta
ƙare, Watan Cin ubansu ya tsaya, sun kirawa kansu mutuwa tunkafin lokacin su yayi.

"Wallahi Allah!....' Azeeza ce ta yi su6ul da baka, da sauri Gabriel Ya toshe mata


bakinta da hannun shi, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwansu, duk sun ƙagara su
ji wani hukunci zata yanke masu tun da ta gano plan ɗinsu.

Walking magestically ta ƙaraso gabansu Tare da tsaida sandarta a ƙasa, Daya bayan
ɗaya ta ke kallon su tsawon mintuna Uku kafin ta soma magana atsanake

"Furennin da ku ka shufka sunyi kyau sosai, Wanene ke basu ruwa A cikin ku? Zaro
ido su ka yi akan fuskarta Mamaki Ya kamasu, Aransu suka shiga ayyana cewa" ko dai
bata ga ƙofar ba ne? Ko kuwa Allah ne yaji kokensu ya hanata ganin komai.

"Kun yi shiru baku bani amsa ba"? Yawu Angel ta haɗiya Muryarta Na rawa ta
ce"am..um..ni..nice..Ni nake bata ruwa, tare da ƴan uwana,"

Murmushi tsohuwa zafreen ta saki tare da cewa"Ku cigaba da bata ruwa inason
furenni, Nan da wani lokaci zan ɗauke tukunyar fulawar in mayar da ita ɗakina..."
tsabar zalama tunkan ta ƙarasa maganar Angel tai wuff wurin cewa"idan ma kinaso
Yanzu saina ɗauko maki ita ki tafi da ita, ai mu mun fi son duk wani abu da zai
faranta maki rai" kallonta tsohuwa zafreen ta yi da tsoffin idanuwanta"Kamar baki
da gaskiya? Ina magana kina katse ni"! A kausashe tayi maganar.

Sunnar dakai ƙasa Angel tayi a tsananin ruɗe Batul ta ɗaura da cewa"Ae tun lokacin
da aka canza mana abinci zuwa ganye, Angel ta soma Fita hayyacinta, sam babu
natsuwa atattare da ita, Hakanan zaki ga ta zauna tana sambatu ita kaɗai" ta ƙarasa
maganar hada murmushinta,

(Yara sun zama ƴan wasan kwaikwayo)

"Eyyah Hakane ashe, " jinjina kai Angel tayi"dama ni tun ina agida idan na ci
abincin da aka haɗa da ganye zaucewa nake yi, Bana son Cin ganye yana affecting
ɗina" Fuskarta amarairace ta yi maganar.

Shiru tsohuwa zafreen ta yi a yayin da ta ke ƙare masu kallo kamar tana son gano
wani abu da ke 6oye akan fuskokin su sai dai Allah bai bata ikon fahimtar komai ba,
Abun da ya ɗaure mata kai yadda su ke yi mata magana ba tare da jin shakkarta ba.

"Da za ki bamu dama Yau na rana ɗaya kawai, Ki zauna muyi fira da ke, A matsayin ki
na kakarmu....." gaba ɗaya sun ruɗar da ita, sai kallonsu take yi tana faman
jinjina kai kamar ƴar ƙadangaruwa

Sun kashe mata bakin magana, A hanzarce ta juya ta nufi bene Giants dake take mata
baya suka juyawa tare da bin bayanta, Suna jiyo sautin rufe ƙofar ɗakinsu, Gaba
ɗaya suka daka uban tsalle tare da rungume junansu fuskokinsu ɗauke da farin Cikin
nasarar da su ka yi akanta, yau sun kashe tsohuwa zafreen da mamaki

"Alhamdulillah Ya Allah, Mun gode da taimakon ka agare mu, " Angel ce ta furta
hakan.

"Mun ji jiki yau Allah, ba kiji yadda gaba na ke faɗuwa ba, tun da ta shigo
hankalina yaƙi kwanciya" acewar Yasmin, Hibba tace"Ae ba ke ka ɗai ba, ni kaina
ƙiris ya rage in saki fitsari a wando, matar can bala'e ce' Kowa yana tofa
albarkacin bakin shi

"Amma wai ya akai da ta shiga toilet din bata ga komai ba? Kuma har ta ga Tukunyar
fulawar"? Naufal nai yai tambayar mamaki ya ishe shi

"Ae Allah muka roƙo shine ya makantar da ita, shiyasa bata ga komai ba" Deeja ce
tai maganar,

"Pls kudaina maganar nan kada Suji mu tunda suna ganin mu, Inaso mu yi magana amma
dole mu jira zuwa anjima idan marece Ya nutsa, sai mu shiga sashen toilet dinmu
saboda idan su ka ga zaryar Tayi yawa zasu fahimci wani abu" Atare suka hada baki
wurin furta mata "Toh"

"Yanzu kowa yaje ya kwanta, Inaso ku huta, kafin zuwa anjima " ɗaya bayan ɗaya suka
nufi gadajen su tare da haye saman suka kwakkwanta, Mutun uku ya rage a tsaye,
Zuciyoyin A cunkushe suke da tunanin taya zasu Iya 6alle murfin ƙofar nan? Taya
zasu iya Gano Danish? Fatansu Allah yasa adawo masu da shi ba tare da sun sha
wahala ba, A tunanin su Haris kenan su da basu san komai game da zamanshi giant ba.

Mutun uku da suka rage atsaye Gabriel ne sai Batul tare da Angel, Sunƙi tafiya ga
dukkan alamu suna buƙatar jin wani bayani ne daga gare ta.

Kallon su ta ɗanyi kafin ta soma magana "Gabriel nasan me ka ke son ji, Ka ƙara
haƙuri zan yi maka bayanin komai" amsa mata yai da toh tare da juyawa ya nufi gadon
shi.

"bugun zuciyata me kike tunani ne"? Lumshe ido batul ta yi tare da ware su kan
fuskar Angel"har yanzu ban fahimci komai ba, dangane da abunda ya faru da ɗan uwana
Danish, hankalina bai kwanta da abunda kika faɗa mini ya faru dashi,"

Matsawa Angel tayi kusa da ita sosai har numfashinsu na kokawa dana juna

"Kin damu dashi"? Jinjina mata kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa"taya bazan damu
dashi ba Angel, bakisan yadda nake jin shi acikin zuciyata ba, da ace ina da hanyar
da zanbi inje gare shi nothing would stop me from going."

Angel ba ta yi mamakin jin abunda batul tace mata ba, saboda sanin irin shaƙuwar
dake a tsakaninsu, Hakan yasa ma taƙi sanar da ita cewa Ya zama Giant, gudun kada
ta sanya damuwa

Ruwan hawayen da ya taru acikin idonta ne yaci gaba da gangarowa

"Ki kwantar da hankalin ki bana son kina shedding tears din ki, Ko dan saboda farin
Cikin ki zan yi ƙoƙari wurin ganin Danish ya dawo gare mu," kwantar da kanta tayi
saman kafaɗar Angel taci gaba da yin shessheƙar kuka tana faɗin"Amma ai bashi da
lafiya, An cire mashi ido ɗaya, bansan awani hali yake ciki ba, "

"Ki daina kuka batul so kike hankalinsu Ya ƙara tashi? Nace ma ki lafiyar shi ƙalau
shi da kanshi Ya faɗa mini cewa babu abunda ya samu idonshi"

lallashinta Angel taci gaba dayi har saida ta samu ta lafa, Abun da yaɗaure ma
Angel kai, zazza6in da taji a jikin batul lokacin da ta kwantar da kanta saman
kafadarta, Jikinta zafi sosai.

Hannayenta biyu ta ɗaura saman shoulders ɗin batul, ta ɗago da kanta, Idanuwansu
acikin na juna,

"Baki da lafiya ne?naji jikin ki da zafi"? Muryarta adisashe ta ce"Lafiyata qalou,


idan ma bani da lafiya damuwar rashin Danish ne" shiru Angel tayi kamar an ɗauke
mata sautin muryarta, ta rasa tunanin me za ta yi, Ruƙo hannun batul tayi acikin
nata

Calmly tace "You need to take a bath, mu je in raka ki toilet, girgiza kai batul
tayi"A'a bana iya wanka, nafi so na kwanta zuwa anjima idan na tashi zanyi,"

Gyaɗa kai Angel tayi"shikenan muje mu kwanta da anjima nima zanyi wankan"
Atare suka nufi gadajen su, tafiya su ke yi kamar waɗanda aka zarewa laka, babu
kuzari a jikin kowaccensu, Ita dai Angel akwai wani abu dake damunta acan ƙasan
zuciyarta, Fatan ta Allah yasa hasashenta karya zama gaskiya don kuwa ba ƙaramar
matsala za'a samu ba.

Ta yi niyar ta kwanta asaman Gadon Danish ganin Jemimah kwance saman nata gadon,
sai dai kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta batul ta riga ta kwanciya saman
gadonshi, da ido ta bita da kallo ganin ta rungume pillow dinshi a ƙirjinta tare da
lumshe idanuwanta, Jiri Angel ta gani acikin idanuwanta kamar zata faɗi kasa
adaddafe ta nufi gadonta daƙyar ta haye gefen jemimah ta kwanta tana faman sauke
ajiyar zuciya, lokaci ɗaya ta ji yanayin jikinta ya canza zuwa zazza6i, hakan yasa
ta soma ambaton sunan Allah, sama sama ta fara jin bacci yana fisgarta har ya ci
nasara akanta sosai ta nutsa tana bacci...............

Ɗakin ya yi tsit babu mai magana a cikin su, kamar masu bacci alhalin kuwa likimo
su ka yi, sai da marece ya nutsa Angel ta umarce su akan su je su yi wanka saboda
wunin ranar jikin su baiga ruwa ba, ba tare da 6ata lokaci ba kowannansu Yayi
wanka, ta ɗauko masu sababbin uniform ɗinsu kowa ya zura nashi a jikin shi, tsaffin
kuma suka cire su Angel ta kar6esu ta ninke su ta ajiye saman table.

Lokacin da dare ya gabato, dubara su ka yi wurin kashe Floor lamps ɗin da ke a


ƙasan ɗakin su, Duhu Ya mamaye idanuwansu, saboda sabon da su ka yi da ɗakin yasa
su ke iya gane hanya ko a cikin duhu, Kamar yarda Angel ta tsara masu mutun Uku ne
zasu Haɗa masu kayan su A cikin akwatin da zasu gudu da shi, Rai da burin sufa
shirin matafiya su ke yi tun kafin su gano Makullin Buɗe ƙofa, Babu wanda yai bacci
acikin su Hatta Jemimah idonta biyu tun ɗazu da marece da ta farka Angel tayi mata
bayanin komai dangane da gano ƙofa da kuma shirin su na guduwa, abunda yasa tayi
mata bayani don kada ta basu matsala, da ya ke yarinyar tana da wayau ta fahimce
ta sosai, yanzu haka suna kwance saman gadon Angel ita da azeeza sun rungume juna
sunata saƙa wasiƙar jaki game da rayuwar da za su yi agidan daddyn Genie ɗinta.

Sauran Ƴan uwan nasu duk suna a zaune gefen gadajen su, duk wani motsin su Angel
akan kunnuwansu.

"Bamu san Girman ƙofar ba Angel Kada mu gaza wuce wa da akwatin kayan mu" Gabriel
ne yai maganar, Cikin duhu suke magana, zurfin tunani ta yi acikin kwakwalwarta, A
Labarin da Salsabeel ya bata Na mahaifin shi habibullah ya tabbatar mata da cewa
Ƙofar sai da rarrafe mutun zai Iya giftawa ta cikinta, mutun zai Iya rarrafawa ko
ya zauna, Amma babu zancen miƙewa tsaye, abun zai zo masu da sauƙi tun da basu da
girman jiki, yawancinsu dogaye ne amma babu ƙiba, haris ɗin ma da ke da jiki yanzu
ya zabge ya koma kamar su Javed.

"Ae akwatin zamu Iya kwantar dashi mu dinga tura shi ta cikin hanyar, Ni abunda
nake Jiye mana kada mu kwasa mu tafi zai Iya kasancewa ƙurmin daji ne bamusan ya
weather ɗin shi zai kasance ba, Zafi ko Sanyi, Zamu sha wahala akwai sanyin da ma
zai Iya kisa Haka zafi ma, Ni nafi so mu tafi da bargunan mu saboda tsaro, shiyasa
nake so mu ɗauki akwati ɗaya sai Backpack ɗin Unaiza dole mu tafi da ita saboda
gadon mu ce.

Duk maganganun da suke tattaunawa cikin duhu akan kunnan ƴan uwansu da ke zaune
gefen gado Sun natsu suna sauraron su.

"Mu fara ɗaukar uniform ɗin mu jera su ciki, " batul ce tai maganar, Angel tace"Ki
je toilet ki ɗauko mana fitila ɗaya amma ki fara kashe ta tun acan dan kada su gan
mu, a ɗakin tsohuwa tamira zamu aiwatar da komai" ta amsa mata da toh, kafin ta
nufi hanyar sashen toilet ɗinsu cikin duhu har ta samu ta cimma ƙofar makewayin
nasu, da hannu ta tura ƙofar ta kutsa kai ciki ta shiga ta ɗauko fitilar tare da
kashe ta, Kafin ta dawo ɗakin tunkan ta ƙaraso tace dasu gata nan tafe, Ruƙo
hannunta Angel tayi acikin nata ta kuma ruƙo hannun Gabriel da ɗayan hannun atare
suka shige ɗakin tsohuwa tamira,

"Ki kunna fitilar yanzu, Ni kuma zan shiga ɗaki In ɗauko Akwatin kayan mu da
backpack ɗin" ta amsa da toh, Batul na kunna fitilar Haske Ya gauraye ko'ina na
ɗakin tsohuwa Tamira, Zazzaro ido su ka yi ita da Gabriel da mamaki akan fuskokinsu
suke bin Bedroom ɗin da kallo, basu ta6a sanin haka ya ke ba, Yau ne rana ta farko
da batul ta fara shigowa ɗakin tsohuwa tamira. Kallon Juna su ka yi ita da Gabriel
Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu ba tare da sun yiwa juna magana ba.

Turo ƙofar ɗakin akayi da sauri suka kalli mai shigowa, Angel ce janye da akwati
ɗaya na kayansu, Ta goyo back pack ɗin Unaiza saman bayanta sai ta yi tamkar
Ɗalibar makaranta, A tsakiyar ɗakin tsohuwa tamira ta ajiye akwatin saman floor, ta
kwanto jakar bayanta ta ɗaura ta saman table.

"Angel Har yanzu ba ki yi mana bayanin ta ya ya akai kika gane inda ƙofar nan ta
ke? Waye ya faɗa maki kiyi amfani da ruwan zafi don shafen wurin ya tsage? after
that Mun yi mamakin yadda akai kika buɗe ɗakin tsohuwa Tamira ko dai itace duk ta
faɗa maki hakan"? Batul ce tayi mata tambayar a ƙagare da son jin amsarta.

"Zan baki amsar tambayarki amma kafin nan inaso ki kira mini su Haris su shigo ayi
komai agabansu" har ta juya zata fuce da fitilar hannunta da sauri Gabriel Ya cafko
damtsen hannunta tare da janyo ta baya yana fadin"So kike asirin mu ya tonu? Ina
zaki da fitila"? Murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Na shafa'a ne" kar6ar fitilar
yayi ita kuma ta fuce Jim kaɗan Su kaji an turo ƙofar Haris Ne agaba Deeja na
abayan shi dasu Hibba a jere suka shigo Hada azeeza Hannah ce ta ruƙo hannunta.

"Wa ya ce ku zo da Azeeza? Ba a kwance ta ke ba"? Gabriel ne yai maganar Yana


kallonta, Naufal yace"kasan halinta da rigima tafi son komai za'ayi ayi agabanta
mutun na fama da makantar dare,"

Ranta ne ya 6aci sosai jin abunda suke cewa, fusge hannunta ta yi daga ruƙon da
Hanna tayi mata, A ƙasa ta zuƙunna tana rera masu kuka.

Angel tace"Dan Allah ku rarrashe ta idan ba so ku ke ta tona mana asiri ba" Gabriel
ne ya nufi wurin da ta ke a zuƙunne ya kai hannu ɗaya ya ɗago da ita kamar jira ta
ke yi ta faɗa saman laps ɗinshi tana cigaba da kuka, Murmushi ya saki yana kallonta
har mamakin Ƙarantarta ya ke yi,
"Its ok Share hawayen ki My Azeeza, kinsan bana son zubar hawayenki, Ko so ki ke
Ajiyo sautin kukan ki asirin mu ya tonu"? Muryarta da shessheƙar kuka tace"A'a"
yace"okey wipe ur tears, zan Goya ki abayana don bana son kisha wahalar neman ɗan
jagora," yai maganar tare da miƙa ma Batul fitilar hannun shi, bayan ta kar6a ya
zuƙunna Azeeza ta haye bayan shi ta ƙanƙameshi sosai, Ya miƙe ɗauke da ita"

Angel na ƙoƙarin fara yi masu bayani muryar jemimah da suka bari ita kaɗai acikin
ɗaki ya karaɗe kunnuwansu ta kware baki Tana ƙwala mata kira"Genie! Genie! " da
sauri Angel ta nufi ƙopar ta buɗe ta fuce, Bayan fitarta Hankalinsu Ya koma kan
ɗakin da su ke a ciki na tsohuwa Tamira Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu su ke
yi, Parveen Acici Tana Hango Wannan Tea pot ɗin da ƴan kofuna biyu jiki na rawa ta
nufi table ɗin dake ɗauke dasu, ta zauna saman kujera tare da ɗaukar pot ɗin tana
jijjigata don taji idan akwai ruwan shayi aciki,

"Kada ki kuskura ki ce zaki sha, Kawai daga ganin abu bakisan tsawon lokacin daya
ɗauka a ajiye ba kin ɗauka zaki sha da ya ke ba ki da linzami indai akan abinci ne"
Deeja ce ke yi mata magana, Saboda kafiya irin ta parveen ko kallo bata isheta ba
hada cewa"dama kin daina wahalar da kanki wurin yi mini magana don wlh saina sha
tea ɗin nan" Tsawa haris ya daka mata"Zaki tashi ko saina 6ata maki rai"? Murguɗa
mashi ƙaramin bakinta ta yi"Wai ku ina ruwan ku dani ne? Cikina ne ko naku"? dafe
kai Hannah ta yi tare da cewa"ku ukun nan kunfi kowa jaraba dake da Azeeza sai
waccan ƴar jemimah, Ni inaga Idan mun tashi tafiya mu bar su a kurkukun domin kuwa
nan yafi da cewa dasu, in ba haka ba zasu ja mana ne" Jin maganar Hannah yasa
azeeza dake kwance bayan gabriel ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, saboda ance
za'a barsu a kurkuku

"Pls Hannah stop saying that, na samu na rarrasheta gashi yanzu kinsa ta kuma
fashewa da wani kukan" acewar Gabriel, ta6e baki hannah ta yi ba tare da ta tanka
mashi ba.

Daƙyar ya samu yashawo kan Azeeza ta daina yi mashi kuka, Parveen kuwa harta
Tsiyaya Shayin A cikin Cup hada lashe baki zata fara sha, Kamar daga sama taji an
damƙi wuyan rigarta daga baya, da sauri ta ɗago don taga wanene, dama saida ranta
ya bata cewar shi ne

Harara ta shiga jefa mashi tare da murguɗa mashi baki, Ya ɗaure fuskarshi sosai
babu annuri

"Tashi ki bar wurin" kaitsaye ya bata umarni, tasan halin shi sarai miƙewa ta yi
ranta a6ace, bata so ya hana ta shan tea din ba, ta ƙwallafa rai.

Acikin hannunshi ya ruƙe nata sosai don kada ta kufce mashi ta koma shan shayin,
Naufal kenan.

"Angel shiru bata dawowa ba, Tabar mu atsaitsaye cirko cirko, Ni bari ma in haye
saman gadon tsohuwa in kwanta"

Rubina ce ta yi maganar, bata kai ga zuwa ta hau gadon ba, Angel ta turo ƙofar
hannayenta biyu rungume da uniform dinsu, Jemimah na kwance saman bayanta, Ta
ƙanƙameta da hannayenta, abunda ya jawo har suka daɗe Jemimah ce ta buƙaci ta
rakata toilet zata zazzage cikinta, Shiyasa basu dawo da wuri ba, Sai da Angel ta
jira ta gama tukunna ta kamota suka dawo ɗakin.

Ataƙaice Cikin daren suka jera uniform ɗinsu acikin akwatin kayan, Hada barguna
Deeja ta ɗauko masu guda takwas daƙyar akwatin ya iya ɗauke su, Har saida suka rage
uniform din dake a ciki suka turasu cikin backpack ɗin Unaiza tukunna ya ishe su,
Bayan sun kammala sanya kayan suka datse shi, daga cikin abubuwan da suka dauka
bayan uniform da barguna hada cotton scarves dinsu da Hulunansu sai rigunan sanyi
da takalmansu, A cikin jakar unaiza suka saka Madubin da tsohuwa Tamira ta basu
kyauta, ba su bar cikin ɗakin ba saida Angel ta fayyace masu komai dangane da
tattaunawarsu da Salsabeel.Abu ɗayane bata fada masu ba komawar Danish Giant bata
so su sani gudun kada su tayar da hankulansu. Haƙiƙa tsohuwa tamira ta kafa tarihi
acikin zukatansu, A yau ta amsa sunanta na mahaifiyar su wadda ta raine su, basu
ta6a yarda cewa tana sonsu ba sai yau da Angel ta labarta masu komai dangane da
taimakon da ta yi masu, sun ji ƙaunarta sosai har suna fatan Allah ya haɗa su da
ita kafin subar kurkukun, sai da su ka kammala shirya komai tsaf na kayansu, Angel
ta kalle su ɗaya bayan ɗaya Azeeza tuni bacci ya ɗauke ta abayan Gabriel,
hankalinta kwance sai sharar bacci ta ke Yi, Jemimah kuwa Idonta biyu Sai faman
baza ido ta ke yi Hannunta na a ruƙe dana Angel.

"Me yakamata Mu yi yanzu don ganin An dawo mana da ɗan uwan mu Danish"! Haris ne
yai maganar

"I'll go and get him back tonight!" da ƙwarin gwiwa Angel ta yi maganar.

"Ta yaya hakan zai yiwu? Angel muna jin tsoron wani abu ya same ki, Me zai hana mu
tafi gaba ɗayan mu"! batul ce ta yi mata maganar fuskarta da alamun damuwa

"Zan bi ki Angel Mu tafi atare"! Gabriel ne Ya yi maganar" girgiza kai ta yi"Bana


so wani abu ya samu ɗaya daga Cikin ku, Bazan bari ka bini ba Gabriel ni kaɗa nake
so na jefa kaina cikin hatsari Zan roƙi Allah ya tsare ni....." muryarta na ɗan
rawa ta ambaci hakan kamar akwai rauni atattare dani, tabbas tana matuƙar fargabar
abu biyu, Na farko tafiyar da zata Yi tabar su da jimamin Awani hali take a ciki,
Na biyu Haɗuwarta da garkuwar kurkuku, Wani irin azababben tsoron shi ta ke ji tun
kafin ta yi tozali da shi.

"Genie Pls don't leave me Ki tafi dani..." cikin shessheƙar kuka Jemimah ta yi
maganar tana ƙara damƙe hannun Angel dake ruƙe da nata.

"Wlh Angel hankalin mu ba'a kwance ya ke ba, Gani mu ke kamar wani abu zai faru da
ke idan kika tafi kika barmu" Deeja ce ta yi maganar, ta fahimci kowannan su
atsorace ya ke da tafiyarta.

"Angel bazamu ta6a yafewa kan mu ba idan har wani abu ya faru dake ta silar
taimakon mu da ki ke ƙoƙarin Yi,"

Javed ne yai maganar, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskokin kowannan su, La66anta
sai kerma su ke yi sam ta kasa buɗe baki ta yi masu magana sai binsu ta ke yi da
ido, Zuciyarta ba ƙaramin karaya ta yi ba, Ita kanta tana ji a jikinta cewa wannan
karan zaiyi wuya ta dawo cikin su ba tare da wani mummunan abu ya faru da ita ba.

"Idan har muka ji kin daɗe baki dawo ba, Zamu biyo ki ne"! Hibba ce tai maganar
hawaye kwance saman kuncinta

Daƙyar Angel Ta iya tattara natsuwarta tare da cewa"Ku daina sanyawa ranku cewa
wani abu zai faru dani, idan ma ya faru dani to ku sani ƙaddarata ce wadda ban isa
in sauyata ba, Ni da Allah na dogara wani mutun ko Aljan ɗaya daga cikinsu bai isa
ya cutar dani ba face da izninsa, ƴan uwana addu'arku kawai nake buƙata akan Allah
ya bani Sa'a akan abunda zan je nema......." Sautin shessheƙar kukansu ne ya
gauraye Ɗakin tsohuwa.

Muryarta adisashe tace"Tunkafin ma na tafi kun fara kuka? Meyasa? Dan Allah ku
daina kamar fa kuna discouraging ɗina ne, Nafi so inga kuna ƙarfafa mini gwiwa,
ganin hawayenku da nake yi ba ƙaramin raunata mini zuciya ya ke yi ba.

"Ba zamu iya jurewa rashinki atare damu ba Angel, wlh muna ƙaunarki fiye da yarda
muke son kanmu, bamu son wani abu ya same ki, saboda mu kike ƙoƙarin jefa kan ki ga
halaka taya ba zamu yi kuka ba? Angel ke uwace agare mu, Kin fiye mana iyayenmu da
su ka yi watsi damu, Dan Allah Angel karki bari mu rasa ki" Sosai suka sanya mata
kuka

Itama ta fashe masu da matsanancin kuka mai cin rai tamkar ana zare ranta Cikin
muryar kuka take magana

"Shiga prison Ya zamar mun dole, Idan har ban je ba rayuwar mu tana a cikin haɗari,
sannan Alƙawari ne na ɗauka Dole na cika shi ku daina raunata mun zuciyata kada
kusa Na gaza......" Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin
zuciyarta.

Tsawon lokaci suna kallon kallo a tsakanin su kafin ta tsagaita da yin kukan tace
da batul"Ga amanar jemimah, Ki rungume mun ita a ƙirjin ki har sai ta yi bacci, da
zarar na dawo zan kar6i abuna" cikin sanyin murya batul ta amsa mata da cewa In
sha Allah zan bata kyakkyawar kulawa har ki dawo Angel, murmushin yaƙe ta ƙaƙaro
kan fuskarta tare da kallon su Parveen da ke atsaitsaye tace"Zan tafi ba za ku
rungume ni a jikin ku ba"? Jin haka yasa da sauri suka matso kusa da ita, Ɗaya
bayan ɗaya suka dinga rungumeta a ƙirjin su, kamar karsu sake ta, a ƙarshe Ta Soma
tafiya tana ja da baya tana kallon su idanuwansu akanta, Jiki amace ta juya tare da
buɗe ƙofar ɗakin tsohuwa tamira, Da gudun gaske Cikin duhu ta nufi sashen toilet
ɗinsu tana faɗowa Hasken sauran fitilun dake a cikin toilets Ya haskaka
idanuwanta, buɗe ƙofar toilet ɗin ta yi tare da shigewa Ciki. Yatsun hannunta na
kerma ta sanya jamlock ta datse ƙofa don kar su yi gigin cewa zasu bi bayanta, A
jikin ƙofar ta jingina bayanta sosai ta fashe da kuka gudun kada su ji sautin
kukanta yasa ta toshe bakinta da tafin hannunta, tsawon mintuna goma shabiyar tana
sharar ƙwalla kamar ruwan hawayenta zasu ƙare sai da tayi mai isarta kafin ta soma
tafiya tana tunkarar Tagar da zata dura, har zata gifta tukunyar fulawar nan ta ɗan
dakata da yin tafiya kafin a hankali ta kalli inda ta ke a jingine jikin bango, duk
da halin da take aciki na fargaba sai da tayi mamakin ganin an maida tukunyar a
mazauninta na asali, shiyasa ɗazu tsohuwa Zafreen bata samu damar ganin ƙofar ba
saboda an toshe ta, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe idunuwanta daga bisani
ware su sosai akan furen Danish da ganyayyakin shi su ka bubbuɗe gwanin ban
sha'awa, Kyakkyawar fuskarshi ta ke imagining acikin idanuwanta, aranta kuwa tana
ayyana koya Zata Ganshi a yanzu daya koma Giant? Da wannan tunanin Angel Ta ƙarasa
gaban glass window ɗin Ta janyo bokitin Ta haye sama A hankali ta 6a66ako glass ɗin
tare da curo shi ta dire shi ƙasa kafin ta daddage ta haura Saman tagar bakinta
ɗauke da Bismillah.

Zuƙunna tayi a jikin bangon da ta faɗo, wani irin Sanyi ne ya mamaye sassan
Jikinta, Ga tsoro daya mamaye zuciyarta, Biji biji take ƙarewa doguwar hanyar
kallo, duhu sosai babu haske sai dai da alamun haske a ƙarshen hanyar Inda Babban
filin nan ya ke.

miƙewa Tayi tsare tare da Sanya hannayenta Biyu ta ruƙo duguwar sumar kanta tare da
nannaɗeta ta jefar da ita saman gadon Bayanta, tunawa da addu'oin da ta karanta a
jiya da tayi fitar nan yasa a yanzu ma ta soma ambaton su acikin zuciyarta, A yayin
da take tafiya tana nufar cikin kurkukun........

*Boss Bature Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game neman ƙarin Bayani Ya tuntu6i Layina na whatsapp 08103884440 banda
Kira just message😊*

_~*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*~_

*KURKUKUN ƘADDARA*

_The Prisoners 2🔥💫_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

Bayin Allah su Batul zullumi da fargabar Halin da Angel zata shiga Ya hana su
runtsa a daren ranar, A ɗakin tsohuwa Tamira su ka zazzauna saman floor, zuciyarsu
na harbawa da faɗuwar gaba, Sun yi shiru kowa da a bun da ya ke saƙawa acikin
ranshi. Deeja ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan su yi mata addu’a. Su ka amsa mata
da toh, nan fa kowan nan su ya soma karanto addu’o’in da Angel ta koya ma su.

Dare ya nutsa sosai Azeeza tuni ta koma bacci, a saman ƙirjin Gabriel ta kwantar da
kanta, Hannun shi na dafe da bayanta kamar zai mai da ta cikin sa.

Jemimah tana a kwance saman cinyoyin Batul ta ƙi yin bacci, ba yadda ba su yi da


ita ba akan ta runtse idon ta ta yi bacci amma ta kafe akan sai Genie ɗinta ta
dawo, a ƙarshe ma da su ka matsa mata sai ta sanya masu kuka, Tsananin tausayinta
ne ya kama su, Haris yace ku bita a hankalin ni banga laifin ta ba, saboda ita
yarinya ce ta saba kwana rungume da Angel dole taji ba daɗi, Rarrashin ta ya kama
ta mu yi, Amsa mashi su ka yi da toh, atare su ka haɗu suna rarrashin jemimah
daƙyar su ka shawo kanta.

Parveen sai hammah ta ke yi Ga yunwa ga Bacci, Naufal da ke zaune a gefenta Yace da


ita Ki kwanta ki yi bacci mana, Kin ishe ni da hammah” harara ta ɗan jefa mashi
tare da cewa”in yi bacci fa ka ce? Sai kace bansan ciwon kaina ba, Ta ya zan iya
runtsawa bayan yan uwar mu tana acikin kurkuku....” ta6e la66ansa Yai”Naji daɗi da
ki ka yi Hankali” bata tanka mashi ba sai ma ɗaura kanta da ta yi asaman laps
ɗinshi.

“Batul mu tashi mu bi Genie mu ɗauko ta” Muryar Jemimah ce ta yi maganar Fuskar ta


ta yi sumtum saboda kukan da tasha, Lallashinta Batul ta yi” Ki yi haƙuri kin ji,
In sha Allah zata dawo Cikin Mu, Badajimawa ba,” Zumbura ba ki ta ɗanyi “Toh idan
ta dawo zamu gudu ko”? gaba ɗaya hankalinsu Haris ya dawo kanta

Murmushi Batul ta sakar mata”Eh mana da zarar ta dawo zamu gudu mubar kurkuku....”
tunkan ta kai ƙarshen maganar Jemimah ta katse ta da cewa”Zamu koma gidan daddyn
Genie Ko? In da zamu sakata mu wala mu yi rayuwar mu babu takura Allah yasa genie
ɗin mu ta dawo da wuri na ƙosa muje inga gidan daddyn ta”

farin cikin da su ka gani akan fuskar jemimah a yayin da ta ke yin maganar yai
matuƙar karya masu Zuciya, Har sai da suka ji hawaye sun cika idanuwansu, cikin
rauni na murya Deeja tace da ita

“Jemimah Pray for Her! Tana buƙatar addu’ar mu, mu dage da yi mata addu’a har sai
ta dawo Cikin mu” jinjina kai jemimah ta yi tare da cewa”tom zan mata addu’a” ta
ambaci hakan tare da lumshe idanuwanta, acikin zuciyarta tana ambaton Ya Allah ka
dawo min da Genie ɗita in dai kana son farin ciki na....”

“Gabriel Ka tada azeeza ta tashi Mu haɗu mu duka wurin yi mata addu’a ba yadda
za’ae muna acikin tashin hankalin nan ita tana bacci, ko dai jemimah da ta ke
ƙarama a cikin mu ta kasa runtsawa balle ita” Rubina ce ta yi maganar, Girgiza mata
kai Gabriel yai alamar Bazai tayar da ita ba

“I’m sorry to say I can’t wake her I don’t want to worry her, Just Let her sleep.”
ɗaure fuska Rubina ta yi jin a bun da yace, ita haushinta yadda suka tashi hankalin
su akan Angel amma ita Azeeza ta lafe jikin shi Hankalin ta kwance ta ke sharar
bacci.

“Akwai matsala fa! Dare Yana ƙara nutsawa babu alamun Angel zata dawo” Sarah ce ta
yi maganar tana daga zaune Ta jingina bayanta jikin bango, Ta saki dogayen
ƙafafuwanta ƙasa.

“Duka yaushe ta tafi da har za ki fara tunanin akwai matsala! Pls mu yi mata fatan
Alkhairi, Ni gajan haƙuri ke bana so” acewar Haris.

To jama’a abu fa kamar wasa A ƙalla Angel ta ɗauki tsawon awanni babu ita babu
alamarta, Idanuwansu sun kaɗa sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa ga zullumin rashin
ta atare da su, sun dage sai addu’a Su ke Yi mata, Ba zato ba tsammani Hasken Ɗakin
su ya gauraye ko’ina, ta jikin ƙofar ɗakin tsohuwa da bata ƙarasa datsewa ba su ka
hango hasken da ke kurɗaɗowa, Hankalinsu Ba ƙarami tashi yai ba, A kiɗime su ka
mimmiƙe tsaye hatta Azeeza da ke bacci sai da ta farka tana faman murza idanuwanta
da yatsun hannayenta.

kallon kallo suka shiga jefawa junansu fuskokinsu ɗauke da matsananciya damuwa
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un;’ shine kalmar da ta fara fitowa abakunansu
Deeja, Yayin da su ke a tsaitsaye cirko cirko, Bakomai ne ya tayar masu da hankali
ba face ganin Safiya ta yi ba tare da Angel ta dawo ba. Nan ta ke ransu ya basu
cewar wani abu ya faru da ƴar uwarsu.................

Shine meke Faruwane ata 6angaren Angel!?

Ai tun lokacin data watsa da gudu ta nufi Cikin kurkuku, Sautin kururuwa
Mai ƙaraji da gurnani ya cika kunnuwanta, ga wani azababben San yi da ya addabe ta,
kamar jaura ta gifta Cikin duhu ta ke gudu

Adai dai lokacin da ta ɗaura ƙafarta saman ground floor ɗin nan Inda ke kewaye da
dogayen benaye Ba zato Ba tsammani idanuwanta su ka sauka akan ƙafafuwan Tsohuwa
Zafreen Lamarin yai matuƙar gigitar da ita, sam Ba ta yi tsammanin Zata ci karo da
wani abu ba ita kawai ta sanyawa ranta cewa Danish ne kaɗai mutumin da zata haɗu da
shi.

Mummunar faɗuwa gabanta yai, ƙirjinta ya hau bugu da ƙarfi da ƙarfi A firgice ta
ɗago da idonta akan tsohuwa zafreen da ke a ruƙe da sanda, Kasancewar Filin Yana da
Fitilu masu haske can saman silin ya gauraye ko’ina, daga ƙasa har sama shigar
Jajayen kaya ne a jikinta kamar kullum Fuskarta na asanye da takuntumi.

“Ya Allah saida nayi addu’a kafin in fito but why na fara Cin karo da mummunar
tsohuwar nan Ina lillahi.....” acikin zuciyarta ta ambaci hakan, Kafin ta yi wani
yunƙuri tsohuwa Zafreen ta soma tunkarota sautin takalmanta ƙwas ƙwas har cikin
dodon kunnan Angel, Duk ta ku ɗaya idan ta yi sai gaban Angel Ya faɗi, tauraruwa
mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba.

Ko da ta ƙaraso gabanta, Bata tanka mata ba, Sai bin ta da tayi da wani matsiyacin
kallo irin na marasa imani, Shuɗayen idanuwanta sun Ciza launinsu.

“Ban yi mamakin Ganin ki ba Unaisah! Ina ji arai na ba yau ba ne rana ta farko da


kika fara ƙetare Iyakar Ki, Taurin kan ki da kafiyar ki da kuma rashin tsoron ki su
ne suka ƙarfafa maki gwiwar shigowa Cikin prison! Ko a tarihi ba a ta6a samun
prisoner ɗin da ya ta6a ƙetare Iyakar shi ba sai Akan Ki”!

Magana ta ke yi muryarta na fita da sauti mai amo.

yawu Angel ta haɗiya, tuni tasha Jinin jikinta, Ido ya raina fata sam ta kasa
magana, Zufa sai tsastsafo mata ta ke yi kan fuskarta har ɗiɗɗiga ta ke a ƙasa.

“Ko za ki Iya faɗa min menene Ya fito da ke? Kuma Ta yaya akai Kika tsaga bangon
ɗakin ku kika fito”? Muryar Angel na rawa ta soma magana”Tsautsayi ne da ƙaddara,
dan Allah kada ki cutar dani, Zan koma inda na fito, Kawai Inason ganin ɗan uwana
Danish ne shiyasa na fito neman shi.....” kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon
sautin Dariyar tsohuwa zafreen da ya tari numfashinta.

Tsagaitawa ta yi da yin dariyar, ta soma matsawa tana ƙara kusanta kanta da Angel,
A tsananin tsoroce Angel ta ke Ja da baya tana girgiza mata kai

“Tun jiya dana shigo ɗakin ku Raina ya bani cewar Wani abun ku ke shiryawa kuma ke
ce jagora a cikin tafiyar, Saboda prisoners basu da wayan da zasu Iya ta6uka wani
abu, Unaisah ke ce ƙwarin gwiwar su, Babban kuskuran da ki ka aikata shi ne ƙetare
Iyakarki! Hakan Ya sa6awa dokar Kurkuku! Na yi imanin babu mai Iya ƙwatarki daga
hannu na! Saina rushe duk wani sashe na Jikin Ki da ke da ƙarfi zuwa mai
rauni......” Zazzare ido Angel ta yi tamkar ƙwayar zata faɗo ƙasa Jikinta sai kerma
ya ke yi.

“Kin jama kan ki bala’i da masifa! Not only u! Hatta Ƴan uwan ki da Ki ka baro
ɗaki, suna cikin masifa, Zanje gare su Bayan na gama da ke, duk saina tarwatsa
farin Cikin da ku ke da shi” Muryarta a kausashe ta ke furta maganar.

Hawayen da su ka taru a cikin idonta ne suka soma gangarowa saman kuncinta da wani
irin rauni na murya ta furta”duk horon da za ki yi mani kada ki haɗa da ƴan uwana,
Ni ce mai laifi don haka Ni za ki hukunta”

Fuskar Tsohuwa Zafreen a murtuke ta jinjina kai tare da cewa “Umarni ki ke Bani? In
yi abunda kike so”? A ruɗe Angel ta girgiza kai ba tare da ta iya furta mata komai
ba.

“Zan jaraba Ki inga idan zaki Iya ceton Kanki, Nasan baki ta6a shaƙar ƙamshin
mutuwa ba amma yau zansa ki shaƙeta sosai, waɗannan Idanuwan naki launin ruwan toka
yau zansa su koma launin Ja, Hawayen da ke fito wa ta cikinsu zansa su janza launi
zuwa na Jini, La66an ki da su ka saba gaya wa Mutane magana Ayau ɗin nan zan canza
masu kamannin.....” Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi tarasa gane inda
kalaman tsohuwa Zafreen suka dosa.

Ja da baya tsohuwa zafreen ta soma Yi yayin da ta ke sakin Shu’umin Murmushin nan


nata na tantiran Ƴan duniya waɗanda su ka ga jiya su ka ga yau

Juyawa Baya ta yi tare da nuna ma Angel Third floor da sandar hannunta

“Ɗan Uwan ki da ki ke nema Yana a hawa Na Uku, Za ki Iya zuwa gare shi, Fatan
Nasara” Kalmar ƙarshe da ta furta mata kafin Ta buga sandar hannunta ƙasa, Nan ta
ke hayaki Mai kamar an watsa tiya gas Ya cika idanuwan Angel, bata Iya ganin komai
amma taji aranta cewa tsohuwa Zafreen ta 6ace daga wurin da ta ke a tsaye, a
hanzarce ta kamo sunan Allah taci gaba da ambaton duk wata addu’a da tazo bakinta,
Cikin ƙankanin lokaci ƙurar ta washe Idanuwan ta suka dawo dai dai. A lokacin ta
riga ta yanke shawarar komawa ɗakin su gurin ƴan uwanta saboda gudun kada tsohuwa
zafreen ta cutar mata dasu kamar yarda ta furta mata cewa zata je gare su, A
hautsine Ta juya da niyar tabi hanyar da ta 6ullo don ta koma ɗakin su, Rass gaban
yai mugun faɗuwa ganin babu corridor ɗin kwata kwata kamar ba’a ta6a yinta ba, Yawu
ta haɗiya zuciyarta na harbawa da sauri da sauri tamkar zata faso ƙirjin ta.

A fujajen ta mayar da dubanta ga dogayen benayen da tsohuwa Zafreen ta faɗa mata


cewa ɗan uwanta na anan A hankali ta ke tafiya tana tunkarar benan Yayin da ta ke
cigaba da karanta addu’o’in neman tsari a cikin bakinta, firgita ta yi sakamakon
Jin sautin shessheƙar kukan Su Azeeza a cikin kunnanta, ta ko’ina sautin kukansu ne
kamar zasu zautar da ita, Tunawa da barazanar da aka yi mata acan lokaci na farko
data ta6a shigowa prison yasa ta yardarwa kanta cewa ba kukan su bane Anayi ne don
a tsoratar da ita, hakan yasa ta samu ƙwarin gwiwa, Watsawa ta yi da gudu ta Haura
saman benan Har ta yi tsakiyarshi Taji ya soma motsawa Matakalarshi ta dinga komar
da ita baya kamar dai yadda ya faru a jiya, Gudu ta dinga yi tana haurawa, wata
uwar zufa ta wanke fuskarta, daƙyar ta samu ta haye saman Second floor.

Numfashi taja tare da fetsar dashi, sai faman yin haki ta ke yi, Tsawon mintuna
takwas kafin taci gaba da tafiya tana bin hanyar, wani abu daya ƙara rikitar da
ita, Ginin wurin ya dinga canza mata hanyar da take bi, Sai ta yi nisa taga an
dawo da ita Baya, hakan ba ƙaramin gigitar da ita yayi ba. Tarasa ina zata dosa,
Tamance ma hanyar da zata bi ta isar da ita hawa na Uku, tana Cikin yin tafiyar
kamar zautacciya ita kanta batasan inda ta ke jefa ƙafafuwanta ba, Cikin rashin
sa’a ta faɗo cikin wani ɗaki.

Idanuwanta basu sauka a ko’ina ba sai akan wasu tsoffin mata da ke agaban manyan
tukwanan girki, An ɗaura su saman murhu Wuta sai Ci ta ke, Hannuwansu ruƙe da
ludayi Suna Juya naman da ke a cikin Tukunyar girkinsu, Gabanta ne ya faɗi ganin
Naman mutun yatsun hannun da ta gani ne cikin romar miyarsu ya tabbata mata da cewa
Naman mutunne su ke yi. farfe sun shi.

Basu lura da ita ba sai da ta daddage ta kwatsa ƙara Mai sautin gaske silar hakan
Ya janyo hankulansu ga kallonta, zaro ido waje ta yi ganin sun ganta, a kiɗime ta
manne ma bango ɗakin, jikinta sae kerma ya ke yi Tamkar a mafar ki ta ke kallon su.

Halittarsu gwanin ban tsoro Munanan gaske, ga Uban tamoji tamojin akan fatar
fuskokin su, kamar jijiyoyin jikin bishiya ƴan rigunan da ke sanye a jikin su
launin Ja Kamar yar shara ta maza da su ke sanyawa, Ga uban gashi a hammatocinsu
sai ɗoyi suke Yi. a ƙalla sun kai su Shida, uban fason da ke a tafin ƙafafuwan su
kamar Kwanannar Fura da ta bushe ta tsastsage.

Kamar mahaukata haka suka fashe da dariya mai sautin gaske Muryoyinsu ne suka Cika
mata kannuwanta.

“Laah ga Unaiserh Ta kawo mana ziyara, yau zata sha farfesun Ƴan Ci ki, Zonan
Unaisah Yarinyar mu, Zo ki sha roman nama”

La66anta na kerma ta furta”Bazanci ba, Ni ba wurin ku nazo ba, Dan Allah Ku ƙyale
ni In tafi....” Tun kan ta ƙarasa maganar ɗa ya daga Cikin tsoffin ta ɗebo farfesun
a cikin ludayi hada Yatsun hannun mutun, tunkaro Angel ta yi tare da miƙa mata
Ludayi” Kar6i nan ƴata ki sha Roman Farfesun Mutun akwai daɗi” Tashin zuciya ne ya
farma mata, a matuƙar firgice ta juya tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu,
sai dai kash ƙofar ta ƙi buɗuwa.

Fashewa ta yi da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, da hannu ta dinga Bugun


ƙofar kamar zata 6alle ta ko motsi ƙofar ba ta yi ba har sai da tsoffin nan suka
cimmata, Ta ƙarfi Suka zaunar da ita tare da rurruƙe mata hannayenta da ƙafafuwanta
ta yadda ba za ta Iya ƙwatar kanta ba. Tsohuwar da ke a ruƙe da Ludayin ce ta
zuƙunna agabanta tare da tsoma hannayenta masu zaƙo zaƙon akaifa ta ɗebo Ƴan hanjin
Cikin sai tiri suke Yi, runtse ido Angel ta yi sosai ta guntse bakinta zucuyarta na
tashi kamar zata yi hauka, Bata ta6a ganin masifa ido da ido ba sai yau da Allah ya
haɗa ta da tsoffin nan, Duk yadda tazo ta kufce masu abun ya faskara kamar zata
haɗiyi zuciya ta mutu, Ta ƙarfi suka 6are bakinta har saida gefe ya dinga fitar da
jini, baiwar Allah taji raɗaɗin azaba, duk ta ciccije la66anta da tsiya su ka dunga
tura mata ƴan hanjin abakinta, don dole ta dinga haɗiyarshi da zafinshi harshenta
duk ya sale haka la66anta ma sun yi suntum.

Kamar zautacciya haka tsoffin nan su ka maida ta, Sai da su ka gama azabartar da
ita kafin suka saketa Anan ƙasa ta shiga kwarara amai suna kallonta suna dariya,
kaf saida ta amayar da ƴan hanjin da su ka bata, wani azababben ciwon kai ya
farmata, Ga jiri da ta ke gani acikin idanuwanta

“Lami ba ta ƙoshi da farfesun ba, A ƙaro mata wani” maganar su taji a cikin
kunnanta, a galabai ce ta miƙe jiki ba ƙwari ta dinga bugun ƙofar ɗakin har sai da
ta samu daƙyar ta buɗe ta, gudu ta ke yi jini na wanke rigar Jikinta saboda bakinta
da suka sanya ƙarfi wurin 6are shi gefe ya tsage bleeding ya ke kamar jinin jikinta
zai ƙare.

Baiwar Allah ga zazza6i mai zafi daya rufar mata, Jikinta sai kakarwa ya ke yi, ta
gama fita hayyacinta, Neman hanyar da zata koma cikin ƴan uwanta ta ke yi saboda ta
riga da ta sare da kurkukun, mutuwa ka ɗai ta ke gani acikin idanuwanta gashi ba ta
son ta mutu ba tare da ta yi bankwana da ƴan uwanta ba.

Tsabar raɗaɗin da bakin ta ke yi mata ne ya jaza mata rauni da rashin kuzari a


jikinta Ƙaffuwanta suka harɗe Gaba ɗaya ta kife saman floor, kanta ya daki ƙasa
sosai, runtse idanuwanta ta yi yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta miryarta
babu sauti take ambaton sunan ƴan uwanta tana neman taimakon su akan su zo su
taimake ta, kada ta mutu ba tare da sun gana da junan su ba, Babu alamun hankali
atattare da ita, sai sambatu ta ke yi ita kaɗai, Addu’o’in da ta ke ƙokarin yi
yanzu sun kufce mata......

Sautin tafiya ta soma Ji kamar motsi motsi saman jikinta, a daddafe ta miƙe tana
faman yin nishi, Ras taji gabanta Ya faɗi ganin wasu Girgizo kwafta kwafta a kewaye
da ita, Tashin hankalin da ta shiga ne yasa ta fasa ƙara tare da yunƙurawa ta miƙe
da gudun gaske ta miƙi hanya tana gudu tana waiwayon su gaba ɗaya sumar kanta mai
tarin yawa ta rufe mata idanuwanta, Cikin rashin sa’a Ta 6urma cikin wani ɗaki tare
da Jan ƙofa ta datse, ba tare da ta ankara da inda ta faɗo ba, Jikinta sai kerma ya
ke Yi.

“Barka da zuwa Ɗakin Fiɗa, Ga dukkan Alamu mun samu wata sabuwar ma’aikaciyar”
Muryar matashin saurayi taji acikin kunnanta, Tun kafin ta juya ta kalle su Jikinta
ya hau tsuma, A furgice ta waiwaya tare da sanya hannu ta nannaɗe sumar kanta da ta
rufe mata idanuwanta, Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un bakomai ne yasa ta
ambaton hakan ba face Matasan ƴan matan da ta gani kwance saman gadaje kalar na
marasa lafiya, zindir babu kaya a jikin su hada masu Ɗauke da juna Biyu, gwanin ban
tausayi, Giants ne tsaitsaye akansu Hannayensu ruƙe da kayan theater suna acikin
shigarsu ta baƙaƙen Kaya.

“Ƴar uwa dan Allah ki taimake ni, ki fitar dani daga wurin nan kada su kashe ni”
waro ido sosai Angel ta yi akan matar da ta yi mata magana, Ita ce mai ɗauke da
juna biyu Daga ganin cikinta tsoho ne Ya shiga wata na tara. Sun tu6e mata kaya
tsiraicinsu duk abayyane, Wannan wata irin masifa ce? Hasbunallahu wa’ni e mal
wakeel Lahaula wala ƙuwata Illa Billah, Allahumma ajirni fil musibati wa aklif ni
khairan min ha,’ adabarbarce Angel ta ke ambaton hakan. Matar sai kuka take yi tana
rokonta akan ta taimake ta ko dan saboda yaron da ke a cikinta, rushewa Angel ta yi
da kuka ba tare da ta Iya furta magana ba.

Ɗaya daga Cikin Giant ɗin dake a ɗakin tiyatar ne Ya tunkarota Hannun shi ruƙe da
wuƙa, Tunkan yai magana ta fahimci abinda ya ke nufi, aiko Jiki na 6ari ta juya
tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin don ta gudu, sai dai ina kafin ta yi hakan ta ji Ya
damƙi hannunta, ruƙo bana wasa ba, ta ƙarfi ya dinga janta har sai da ya kai ta
bakin gadon da matar nan me ciki take kwance.

Zura mata wuƙar ya yi a cikin hannunta Ya damƙe shi da nashi hannun, Ta ƙarfi ya
soma ƙoƙari sanyata farke cikin matar, Kamar zata zauce saboda tsabar kiɗima har
Allah ta dinga roƙo akan ya ɗauki ranta kafin faruwar hakan, Bata ta6a danasanin
zuwanta duniya ba sai yau, ta yi fatan ace bata ta6a wanzuwa acikinta ba, ta yi
kuka kamar ranta zai fita tayi haukan tayi borin duk abanza, ta ƙarfi giant din nan
ya ɗaura hannunta saman cikin matar nan da ke ta kuka tana roƙonta akan ta taimake
ta, Saboda rashin imani Ya yi amfani da hannun Angel wurin farke cikinta Kamar an
fasa pipe ɗin ruwa Haka jini yadinga tsastsafowa yana wanke fuskar Angel har ta
cikin bakinta ya dinga fallasa yana shiga.

Hatta jaririn da ke acikinta bai tsiri ba, Biyu suka raba shi da wuƙar, Allah
sarki Angel Gani ta yi kamar ita ta aikata kisan kan, Wata irin kururuwa ta saki da
iya ƙarfinta na karshe ta bangaje giant ɗin da ke a ruƙe da ta ita Amakance ta
dinga Tafiya tana neman Hanyar fita, muryarta da sautin kuka ta ke faɗin.

“Nashiga Uku na bani na lalace Inalillah wa’inna ilaihirraji’in Na aikata kisan


kai! na yi kisa da hannayena Shikanen Na mutu, nasan Allah ba zai ƙyale ni ba, Na
kashe mashi baiwarshi da bata ji ba bata gani ba, Wayyo Allah Na......”

Yatsun hannayenta ta ɗaura asaman kanta kamar Aljanna Jinin matar duk ya canza mata
kamanninta, duhu ya mamaye idanuwanta da zuciyarta.

Giants ɗin da ke Yin aikin fiɗar sai tiƙar dariya su ke Yi, Hankalinsu kwance su ke
Cigaba da gudanar da aikin su, yadda su ke farke cikin mutun kamar dabba babu imani
ko misƙala Zarratin.

Da wata irin raunatacciyar murya ta ke faɗin”Allah ba zai ta6a barin ku ba, Mugaye
Azzalumai, Tun agidan duniya za ku fara gir6ar abunda ku ka shuka ƴan iska fasiƙai
masu zuciya irin ta kafuran farko, In sha Allah Ni ce Ajalin ku, Sai kun ɗanɗani
kuɗar ku sai kun gane ba ku da wayau, kamar yarda kuka sa na zubar da hawaye na in
sha Allah kuma za ku zubar da naku hawayen Na jini ma, Yadda ku ka cutar dani ku ka
sa na aikata kisa kuma sai an yi maku mafiyin shi......” ƙululun baƙin Cikine ya
tokare maƙoshinta, silar hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar.

Hannayen ta biyu ta sanya saman wuyanta, ta shaƙe shi sosai cikin fitar hayyaci
kamar zata kashe kanta, tsabar raɗaɗin da ƙunar da zuciyarta ke yi mata ne yasa ta
ke ƙokarin aikata hakan, tana a cikin wannan mawuyacin halin taji An sunkuce ta
kamar Ɗiyar roba haka aka ɗauke ta sama, wani gabjejen giant ne yai mata wannan
ɗaukar, fucewa yai da ita daga Cikin ɗakin Ɗauke saman kafaɗarshi bai nufi ko’ina
da ita ba sai cikin wannan Ƙaton palourn Da taron matsafa su ke gudanar da Bautar
su, Wasu dogayen mutane masu sanye da jajayen kaya ko’ina na jikin su arufe ya ke,
sun kai su talatin, Agaban dodon tsafin su, Anan Ya sauke ta saman floor, a
durƙushe ta kife kasa saboda rashin ƙwarin Jikinta, Hatta numfashinta a hargitse
yake fita Jikinta yai zafi rau kamar wadda aka tsomo daga cikin wuta.

A lokacin ta kai maƙura bata iya ta6uka komai, motsin hannun mutun ta ji ajikinta,
saboda duhun da idanuwanta su ka yi mata yasa ta makance, bata ganin komai, kayan
Jikinta suka cire mata gaba ɗaya iya pant ɗin ta su ka bar mata, duk da bata acikin
hayyacinta sai da ta shiga matsanancin tashin hankali tunawa da robar ruwan zamzam
ɗin da ke a cikin wandonta, rarrafe ta dinga tana laluban suturarta don ta mayar
dasu a jikinta sai dai kash bata samu damar ganin inda aka jefa mata kayanta ba.
Kukan zuci ta dinga yi, duk wani motsinta akan idon matsafan, ita damuwarta ba akan
tsiraicinta da suke kallo ba, robar ruwan Zam zam ce damuwar ta, Ya za ta yi idan
ta rasa ta? Ita kaɗai ce damar da suke da ita.

Kunnuwata ne suka soma Jiyo mata Sautin muryoyinsu Marasa daɗin ji magana su ke yi
da yaren su na matsafa gur6ataccen yare mara daɗin ji, kamar zata haukace, Lallai
yau Angel ta shaida tana acikin kurkukun ƙaddara.

Ƙwaryoyin ne ruƙe a hannun matsafan masu ɗauke Da zallar Jinin mutane mai ƙarni,
Layi suka jera agabanta suka tsaya tare da Kwarara mata Jinin A saman kanta, Wa’iya
zubillah Numfashinta ya gauraye da Ƙarnin Jinin Nan ta ke Ta ƙara sa faɗuwa ƙasa
tana fitar da numfashi sama sama, basu ƙyale ta ba sai da su ka yi mata wankan
tsarki da jinin da ke a hannunsu, wani kalar Jini mai wari da ƙarni daga gani sun
tsuma shi sosai, ba ƙaramin zautar da ita su ka yi ba, Kwakwalwarta bazata Iya jure
abinda suke yi mata ba, Tana jin motsin hannayensu a jikinta saƙo da lungu su ke
cuccuɗata kamar suna yi mata wanka, Sun goga mata najasa a jikinta sun wulaƙanta
Martabar jikinta. Allah ne bai nufa Angel zata mutu ba da tuni ta jima da mutuwa
lokacinta ne bai yi ba, domin kuwa warin jinin da suka yi mata wanka dashi kaɗai ya
isa ya halakar da ɗan adam. Bayan sun kammala yi mata wankan tsarkin nasu na
matsafa, Giant ɗin da ya kawota Ya sanya hannu tare da tattareta kamar tsumma Ya
ɗauke ta, Ya fito da ita daga Cikin Falon Ya nufi Hawa Na uku da ita, ba tare da
sun mayar mata da uniform ɗin ta ba, ko yatsun hannunta bata Iya motsawa, Sautin
tafiyar shi ka ɗai ta ke iya ji acikin kunnuwanta, ƙofar Wani ɗaki Ya tura da
ƙafarshi Ya shigar da ita, Katafaren bedroom ne na zamani kamar ba’a cikin kurkukun
Ya ke ba, Da jinin jikinta da komai Ya jefar da ita saman gadon tare da Juyawa Ya
buɗe ƙofar Ya fuce.

Kaɗan daga Cikin Abunda ya faru da Angel kenan A cikin Daren ranar, Shin me kuke
Tunani zai biyo Baya? Bayan gaba ɗaya Shirinsu Ya tarwatse Babu alamun zata haɗu da
Danish, Ko da ta haɗu dashi daƙyar ma Ta iya gane shi saboda bata a cikin
hayyacinta babbar matsalar babu ruwan zamzam ɗin da zata Iya shawo kanshi, saboda
kwalbar tana a cikin aljihun uniform ɗinta, Ya salam!! Wannan wace irin mummunar
ƙaddarar rayuwace!!! Me zai faru da su Azeeza? Me tsohuwa zafreen zata yi masu🥺

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

*KURKUKUN ƘADDARA*

_The Prisoners E3🔥💫_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

A yayin da Angel ta ke A Cikin mawuyacin Hali Idan muka koma 6angaren ƴan uwanta da
ke ta tsammanin dawowarta, wani mummunan abu Ya faru dasu!! Tun lokacin da suka
fuskanci cewa gari ya waye bata dawo ba, Hankulan su su ka tashi matuƙa, Sun kasa
fitowa daga Cikin ɗakin tsohuwa Tamira, gudun kada asirin su Ya tonu, tun da ana
kallon duk wani motsinsu.

“Yanzu ya zamu Yi? Nifa ina tsoron mu fito daga ɗakin tsohuwa Agan mu dole su zargi
wani abu” Deeja ce tai maganar

Haris yace”Zaman mu kuma acikin ɗakin yafi komai haɗari, Idan Giant su ka zo kawo
mana abinci zasu ga babu mu aɗaki zasu Iya zargin mu”

Damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Kowa yana tofa albarkacin bakin shi, jemimah da ke
a ruke da hannun Batul idanuwanta sun kumbura suntum saboda rashin baccin da bata
samu damar yi ba adaren Jiya, jikinta hada zazza6i,
“Mun tsaya muna kallon juna, Yakamata Muyi wani abu akai,” eve ce ta yi maganar,
fuskokin su duk sun kumbura musamman idanuwanta saboda rashin baccin da ba su yi ba
a daren jiya.

Numfasawa Batul ta yi tare da cewa”mu fita kawai” ta ambaci hakan tare da ɗaukar
jemimah saman Jikinta, ƙofar fita ta nufa ta sanya hannu ta tura ta, Zura ƙafarta
ke da wuya Cikin ɗakinsu Ta yi arba da tsohuwa Zafreen A tsaye hannunta ruke da
sandarta fuskar nan ɗauke da murmushi, A gigice Batul ta koma Cikin ɗakin Zuciyarta
na bugun uku uku, Ganin yadda ta Faɗo masu yasa su ka haɗa ba ki wurin
tambayarta”Lafiya? Me yasa ta dawo”? Muryarta na ruwa ta ambaci sunan tsohuwa
Zafreen!

“Wlh ita ce naganta a cikin ɗakin mu, Wayyo Allah mun shiga uku”! Cikin shessheƙar
Kuka ta ƙarasa maganar, Kafin wani ya kuma cewa wani abu tsohuwa zafreen ta faɗo
cikin ɗakin da su ke a ciki, A firgice Azeeza ta 6oye bayan Gabriel Jikinta nata
kerma, Tashin hankali ne tsantsa akan fuskokinsu.

Ɗaya bayan ɗaya ta ke bin su da shu’umin kallon nan nata

“Halan Ƴar uwar ku ku ke Jira ta dawo”? Shiru su ka yi babu wanda Ya tanka mata,”
Idanuwan su azazzare jin ta gane me su ke jira, hakan ya tabbatar masu da cewa Sun
yi aran gama da Angel, Zuciyoyin su ba ƙaramin karaya su ka yi ba. Dama saida ransu
ya basu cewar fitar Angel ba alkhairi bace.

Tuntsirewa ta yi da dariya mai sautin gaske kamar zata fasa masu kunnuwan su, har
saida suka sanya tafin hannayen su wurin toshe kunnuwan su.

Lokaci ɗaya ta dakata da yin dariyar tare da ɗaure fuskarta tamau babu annuri ko
misƙala zarratin.

Wahalallan Yawu su ka haɗiya, Daƙyar Deeja ta samu damar buɗe baki Muryarta na
kakarwa ta soma magana”Dan Allah Ki yi haƙuri kada ki cutar mana da ƴar uwar mu,
duk abunda ta aikata ba laifinta bane, Laifin mu ne, ta yi ne saboda mu.....” bata
ƙarasa maganar ba, Haris yai saurin toshe mata bakinta gudun kada ta tona masu
asiri, A hasashen shi Tsohuwa zafreen bata san zancen shirin guduwar su ba, Iya
abunda ta sani shine Shigar Angel kurkuku.

Muryar jemimah Cikin shessheƙar kuka da 6acin rai tace”Wlh idan ki ka ta6a mini
Genie ɗina saina rama mata, bata ma ku komai ba ku ke cutar min.....” a hanzarce
Batul ta toshe mata bakinta da hannu, Hankalin su yai matuƙar tashi ganin irin
kallon da tsohuwa Zafreen ta ke bin Jemimah.

“Dan Allah Ki yi haƙuri da kalaman da ta yi maki, yarinya ce bata son komai ba,
kuma bata acikin hayyacin ta,” Atare suka haɗa baki suna bata haƙuri, da buɗar
bakin ta sai cewa ta yi”Sorry for ur self! Ku ya cancanta in ba haƙuri saboda kune
rayuwar ku ta ke acikin matsala, Ni bani da damuwa”

A matuƙar ruɗe suke binta da kallo

Cigaba da yin magana ta yi cikin shaƙiyanci da izgilanci”Na jima inason kasancewa


tare da ku ban samu damar Yin hakan ba sai yau, Ganin ku da nayi ahaka yayi matuƙar
tayar mini da tsohon tsumina, ya za’ai? Zaku bani haɗin kai ko kuwa zan ƙwaci
haƙkina ta karfi”? Ta yi tambayar tana ɗage masu gira.

Kallon kallo su ka soma jefa ma junan su, sam basu fahimci me ta ke nufi ba.

“Au Na manta kufa dabbobine ba ku san komai ba, dole sai ana yi ma ku magana da
yaren da zaku iya ganewa,” ta ambaci hakan tare da tunkarar su, bayin Allah sai ja
da baya baya suke Ke yi.

“Abunda na ke nufi shine zan kwanta da ku In biya buƙatata, idan ku ka bani haɗin
kai salin alin zamu rabu lafiya, har ma In bada umarnin akawo maku lafiyayyan
abinci, kuma daga rana irin ta yau za’a daina baku ganye kuna Ci”

Hankalinta akwance ta ke kora masu Bayani, Cikin shessheƙar kuka Deeja tace”Wlh ba
zamu ba ki haɗin kai ba” ta ambaci hakan tare da kallon su Hibba

“Kada ku yadda da ita so ta ke ta yi mana irin abunda akayiwa unaiza wanda yaja har
ta mutu tabar duniya......” Maganar da Deeja ta yi ne ya fargar dasu, sai yanzu su
ka fahimci abunda tsohuwa zafreen ta ke nufi. Ƴan matan cikin su tuni sun fashe da
kuka suna roƙonta akan karta ta6a su ta ƙyale su, Baiwar Allah Azeeza ta ƙanƙame
Gabriel kamar zasu koma mutun ɗaya. tsananin tausayin kansu ne ya kama su, don basu
ga alamun sassauci akan fuskarta ba.

Tsawa ta daka masu tare da nuna mazansu da sanadar hannunta”Maza ku fuce ku bani
wuri, ba da ku zanyi ba, Matan na ke kwaɗayin kasancewa dasu” kaitsaye ta basu
umarnin fita, kamar sakarkaru haka suka haura ƙafafuwan su su ka nufi ƙofar fita,
Azeeza da ke ruƙe da Gabriel tuni ya yi wurgi da ita ƙasa saboda basa acikin
hayyacin su, ta yi amfani da sihirine wurin basu umarni su fita, fucewar su ke da
wuya ƙofar ɗakin ta datse ta yadda ba zasu Iya tsere mata ba.

Jikin su sai kerma ya ke yi, da gudu Azeeza ta shige ƙarƙashin gadon tsohuwa
tamira, ganin ta yi hakan yasa Batul sauke Jemimah tare da turata ƙarƙashin gadon,
tace da azeeza ta rungumeta a jikinta, bayan ta ɗago ta jera da sauran ƴan uwanta
suka haɗu suna yi mata magiya akan ta ƙyale su kada ta cutar dasu.

Shu’umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, A hankali ta jefar da sandar


hannunta, Dama lafiyar ƙafarta lau, ruƙe sandar da ta ke yi na ado ne. Yatsun
hannayenta ta ɗaura kan doguwar rigar da ke a jikinta, Ta zame ta nan take
tsiracinta Ya bayyana babu kyan gani jikin ta duk tamoji tamoji kamar jikin
faskaran Icce, Undyn da ke a jikinta shara shara ya ke kamar net kana iya ganin
komai, uban gashin gabanta gwanin ban ƙyama, Tsayin shi ya kai na ciyawa, wani abun
tashin hankalin ma Halittar gabanta sak irin na Namiji ce hakan na nufin tsohuwa
zafreen Mata maza ce! Nonuwanta kamar silifas har saman Cikinta. Runtse idanuwansu
su ka yi don ba za su Iya jurar kallon tashin hankalin nan ba. Ajikin bango suka
ƙanƙame juna kamar zasu tsaga shi su shige ciki saboda tsabar yadda su ka manne
mashi.

Bayan ta kammala cire doguwar rigar ta jefar da ita ƙasa.

“Ku kwantar da hankulan ku Ni ba da ku zan fara ba, Na ƙarƙashin gadon su nafi


sha’awa” jin wannan maganar yasa suka bubbuɗe idanuwansu azazzare suke kallonta,
Kafin su ka kai idonsu kan gadon tsohuwa Tamira da ƙarfi Deeja ta furta sunan
Jemimah da Azeeza, Kafin su yi yunƙuri zuwa gare su tsohuwa zafreen ta cimma
ƙarƙashin gadon da hannu Ta janyo ƙafar azeeza da ta jamimah da ƙarfi ta fusgosu
waje kawunansu ba ƙaramin buguwa su ka Yi ba, A saman gado ta kwantar dasu Sai
faman lashe baki take tana ƙokarin cure masu kayan jikin su.

Kukan kura Su Batul su ka yi da gudu gaske suka haye saman gadon, Da iya ƙarfin su
na ƙarshe su ke kai mata naushi duk don ta ƙyale masu Ƴan uwansu, sai dai ina ko
kaɗan tsohuwa zafreen bata Ji bugun nasu ba, batasan ma su na yi ba don tuni ta
tsuduma cikin biyan buƙatarta dasu azeeza, ta raba su da kayan jikin su, sautin
kukansu Ya karaɗe Cikin ɗakin wani irin raɗaɗin azaba su ke ji a jikinsu, sai da ta
tabbatar ta lala masu rayuwa, tun numfashinsu na fita a wahalce har ta kai ga sun
daina motsi, gaban su sharkaf da jini, tukunna ta ƙyalesu ta koma kansu Batul da ke
bugun bayanta, wata irin wawura ta kai masu da hannayenta masu faɗi ta dinga
Rabasu da kayan jikinsu Zir ta yi masu Mutun biyu ta damƙa acikinsu Sarah da Yasmin
Ta kwantar dasu ƙasa ta hau kansu taci gaba da biyan buƙatarta, wa’iya zubullah
Tashin hankalin da suka fuskanta Bazai misaltu ba, basu ta6a ganin Masifa ido da
ido ba sai yau, Suna ji suna gani ta gama amfani dasu sarah ta koma kan su Rubina
ɗaya baya ɗaya ta ke kwantar dasu ƙasa ta hau kansu tana Biyan buƙatarta. sautin
koke kokensu da gurnanin tsohuwa zafreen Ya cika kunnuwansu Haris, waɗanda tuni sun
jima da haukacewa, Don tun bayan fitar su daga cikin ɗakin ƙofar ta datse,
Tunaninsu ya dawo, Sun yi kuka har sun gaji, yayin da su ke jiyo sautin muryoyin su
Deeja cikin mawuyacin hali su ke ƙwala masu kira donsu zo su cece rayuwar su sai
dai sun gaza yin hakan, basu da wata hanya da zasu iya taimakon su, ji su ke kamar
su haɗiyi zuciya su mutu, sun yi fatan ace mafarki ne ba gaske ba.

Mutun ɗaya ce ta rage A tsaye Fuskarta jaga jaga da hawaye ta rasa ya za ta yi don
tasan itama zata dawo kanta ne idon ta gama dasu Deeja gani ta ke kamar ƴan uwan su
sun mutu saboda wasu daga Cikinsu babu numfashi atattare dasu Musamman jemimah da
Azeza zaiyi wuya su rayu. zafreen ta gama kashe masu rayuwarsu ta wulakanta su
kamar dabbobi.

A haukace Batul ta nufi table ɗin da ke ɗauke da Tunkunyar shayin nan ta ɗaɗɗago
shi da hannu biyu, tana haki ta nufi tsohuwa zafreen da ta duƙufa asaman su
Rubina, ta daddage ta buga mata shi, Ko gizau batayi ba, Komawa ta yi tare da ɗauko
kujerar table ɗin ta dawo ta kuma buga mata ita saman kanta, still bata ɗago ba.

A fujajan ta koma cikin ɗakin tana neman abunda zata ƙwala mata, Duk ta bi ta
haukace sai waige waige ta ke yi fuskarta sharkaf da hawaye, har zata juya ta
wutsiyar idonta ta hango Rigar wuƙa da ke a so ke a tsakanin littattafan cikin Book
shelves ɗin ɗakin.

Tsohuwar ajiye ce wuƙar da tsohuwa Tamira ta ba Danish Kyautarta a lokacin da ya


buƙaci yana son datse sumar kan shi, ashe ya maida mata ita shiyasa ko lokacin da
Angel ta yi mashi magiya akan ya bata wuƙar Yaƙi bata saboda bata atare da shi, da
gudu Batul ta nufi book shelves din ta zura hannu ta ɗauko rigar wukar ta zaro ta
Jikinta har salƙi ya ke yi saboda tsabar kaifinta, wuƙar sihiri ce mai haɗarin
gaske, Cikin zafin nama ta watsa aguje bata nufi ko’ina ba sai kan Tsohuwa Zafreen
a lokacin ta gama da su Rubina juyowar da za ta yi ke da wuya Batul ta daddage ta
Luma mata wuƙar Cikin idonta, kafin ta yi wani yunƙurin yin amfani da sihirinta
Batul ta ja wuƙar Tun daga kan idonta har zuwa saman wuyanta ta tsartsarga mata
Jikinta, Wani irin ƙarfine yazo mata, Dama jinin ta akan akaifa ya ke, Zuciyar ta
bushe, Gaba ɗaya tsohuwa zafreen ta gigice saboda azabar zafin da taji na shigar
wuƙar, Ta yi ƙoƙarin Buge Batul sai dai Allah bai bata Ikon Yin hakan ba, ba
ƙaramin Illah Batul ta yi mata ba, Sai dai duk da haka wani abun mamaki babu ɗigon
Jini da ya fito daga idonta, duk inda Batul ta fasa mata da wuƙar kamar ana ɗinke
fatar wurin haka ta dinga haɗewa tamkar ba’a ta6a tsaga ta ba.

So ta ke ta lalubo sandar hannunta saboda ƙarfin sihirinta yana a jikin sandar,


Idan har babu ita Sauran sihirin da ke a jikinta ba lallai Ya iya yi mata tasiri
ba, Daƙyar ta samu ta yi wurgi da Batul gefe ɗaya gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya
daku, wuƙar hannunta ta kufce mata, yunƙurawa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye
Jikinta na kakarwa ta soma tafiya tana tunkararta, so ta ke kawai ta kashe ta har
Lahira, Cikin fitar hayyaci Batul ta miƙe zaune daga kwancen da ta ke a ƙasa, Ja da
baya ta dinga Yi har sai da ta ƙurewa bango.

Tuni tsohuwa zafreen ta cimmata, tafin ƙafarta ta ɗaura saman Yatsun hannun Batul
ta murjesu, tsabar raɗaɗin da Batul ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin ku ka na
fitar hayyaci, wata irin zufa ta soma tsasstafo mata

“Kafin ki kashe Ni, Ni zan fara kashe ki, Dabba kawai, Kin yi kuskure da ki ka soka
mini wuƙa A cikin idona, Angaya maki cewa Ni Mutunce da zan mutu farat ɗaya? Tana
huci ta yi tambayar, janye tafin ƙafarta tayi daga kan yatsun hannun Batul ta ɗaura
ƙafar saman jikinta da ƙarfi ta danna shi tare da murza ƙafar, Jini ne ya soma
gangarowa ta cikin bakin batul Nan ta ke Numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa.....

Ba zato ba tsammani tsohuwa Zafreen Taji an buge mata kanta da ƙarfi gaba ɗaya ta
kife ƙasa, ta baya aka shammace ta, A hanzar ce ta ɗago don ta ga wanene, a matuƙar
ruɗe ta ke kallon fuskarta, Ba kowa bace face TSOHUWA TAMIRA.

“Ban yi mamakin ganin ki ba Dama na jima da zargin cewa ba ki atare damu Tamira!”
zafreen ce tayi maganar muryarta akausashe, saboda tsabar 6acin rai facial musles
din tsohuwa tamira har kerma su ke yi, Hankalinta yai matuƙar tashi ganin yadda
zafreen ta lalata rayuwar Yaran da ta raina gaba ɗaya ta gama da rayuwarsu, ta yi
danasanin zuwan da ta yi amakare da duk hakan bata faru ba, idanuwanta sun yi jawur
dasu tamkar garwashin wuta, wani irin hu ci ta ke futarwa

Yunƙurawa tsohuwa zafreen ta yi tare da miƙewa tsaye, Ido cikin ido su ke kallon
juna babu sassauci akan fuskokin kowannan su.

“Ni dama ba ki ta6a burgeni ba, Muguwa azzaluma baƙar kafura, Ban ta6a ganin dabba
Jahila daƙiƙiya irin ki ba, Wai ke baki da hankali ne? Ke fa mutunce waɗannan yaran
da kika lalata rayuwar su mutanene fa ba dabbo bi ba, Laifin me su ka yi maki da
har su ka cancanci wannan hukuncin daga gare ki”? Rai amutuƙar 6ace ta jefa mata
tambayar.

Ɗaure fuska tsohuwa zafreen Ta yi, idanuwanta sun kaɗa jawur dasu, Babu ko alamun
imani akan fuskarta

Tana magana tana huci kamar mayun waciyar zakanya” Ni kike gayawa magana? Ka da ki
manta ke bakowa bace a gidan kurkukun nan face ƙasƙantacciya mai rainon Yara, dole
Ki yi mini biyayya saboda ni ke agaba da ke, Nafi ƙarfin ki Tamira nesa ba kusa ba,
Idan har kina son ki tsira da ranki to ki gaggauta barin wajen nan tunkafin In yi
maki mummunar Ill......”Bata kai ga ƙarasa maganar ba, tsohuwa Tamira ta daka mata
tsawa har saida ta furgita, karo na farko kenan da taga Rashin tsoro acikin idon
Tamira.

Nuna ta ta yi da yatsan hannunta”ko da can baya da na ke girmamaki ba dan ina jin


tsoron ki bane sai don Ƙudirin da na ke dashi na son Rushe Baƙin tarihin da kuka
kafa, Ajali ne ke kiran ki shiyasa har ki ka yi gigin shigowa cikin ɗakina, A yau
inaso in nuna maki ƙarfin ikon da na ke shi wanda na samu awurin rainon yaran da
nake yi, Zafreen Yau zaki yaba ma aya zaƙinta, Ko da zan rasa raina ne saina fara
ganin bayanki wulaƙantacciya kawai”a fusace ta ambaci hakan idonta akan fuskar
zafreen ga dukkan alamu mamaki da al’jabi ne ya hana ta mayarwa Tamira martanin
maganarta. bata ta6a tsammanin tsohuwa Tamira zata Iya yada mata magana ba tare da
jin shakkarta ba.

“Tsautsayi da ƙaddara ne suka jefo waɗannan Watsastsun ƙafafuwan naki cikin ɗaki
na, Kin ga babu mai kallon mu bare aji sautin mu, Yau zan huce haushina akan
ki....” Tunkan ta ƙarasa maganarta, tsohuwa Zafreen ta 6ace ma ganinta, Hankalin
tsohuwa Tamira Ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada ace ta
bar ɗakin, In kuwa haka ta faru zasu fuskanci azabtarwa domin kuwa za ta je ne ta
fallasa su.

Jin motsin mutun abayanta yasa ta yi saurin Juyawa, Har saida gabanta Ya ɗan faɗi
ganin tsohuwa Zafreen ta bayyana cikin shigar jajayen kayanta hannunta ruƙe da
sandarta, ashe 6acewar da ta yi don ta ɗauko sandar hannunta ne ta kuma mayar da
suturarta.

“Na yi tsammanin kin ji tsoro kin gudu ne”; acewar tsohuwa Tamira
Mahaukaciyar dariya zafreen Ta saki tare da cewa”Babu tsoro a cikin zuciyar tsohuwa
Zafreen! Tamira kin shiga Uku! Kin tsokanowa kanki Bala’e da masifar da ba za ki
Iya jurarsu ba, Zan kashe ki har lahira bayan na gama da ke zan ƙarasa kashe
waɗanda basu mutu ba a cikin Yaran can naki, Zan sha Jinin su In ci tsokar naman
su”

Tana kai ƙarshen maganar ta, ta yi kukan kura tare da Afkawa tsohuwa Tamira, gaba
da gabanta Aljani Ya taka wuta, Domin kuwa Zafreen tafi Tamira ƙarfin sihiri,
Faɗane ya kaure a tsakanin su kamar dawakai, ba ka iya jin komai sai sautin buge
bugen su da gurnaninsu uwa namun dawa, Ƙura ta karaɗe cikin ɗa ki, Kusan atare su
ka canza suffofin su, Tsohuwa Zafreen ta rikiɗa ta koma Damusa, Tamira ta koma
kura, Ko a namun dawa Damusa ba abokiyar karawar Kura bace, Faɗan nasu Ya canza
salo, kamar a filin daga su ka cigaba da kaima junan su Hari duk suka raunata
kawunan su.

*ANGEL*

Tsawon lokaci tana a sume saman Gadon da aka kwantar da ita, fatar jikinta jawur da
Jinin da su ka yi mata wanka dashi duk ya daskare mata, zai yi wuya yabar Jikinta,
saukar ruwan sanyin da ta ji ajikinta ne ya farkar da ita a firguce ta farka, sai
dai ta kasa buɗe idanuwanta saboda nauyin dasu ka yi mata, hatta bakinta Yaƙi
buɗuwa la66anta sun kumbura suntum wani irin zogin azaba su ke yi mata.

Ba zato ba tsammani kunnuwanta su ka jiyo mata muryar SALSABEEL.

“Meyasa ki ka yi gaggawa? Kin manta me na faɗa ma ki? Sai da nace ku yi


takatsantsan idan ba haka ba za ku ja ma kan ku ne damu kan mu....” Sam ta ƙasa
motsa bakinta, Idanuwanta kaɗai ta iya samun damar buɗe su akan jikin shi, Yana
atsaye Cikin shigar Giant ko’ina na jikin shi arufe kamar yarda ta ganshi a
shekaran Jiya. Ta yi mamaki sosai saboda a tattaunar da su ka yi da ita ya faɗa
mata cewa ba zata sa ke ganin shi ba, sai ga shi Ya dawo yau, hakan ya tabbatar
mata da cewa suna acikin haɗari gaba ɗayan su, taja masu bala’e.
Rushewa ta yi da matsancin kuka raunin da ke abakinta yaci gaba da fitar da jini

Tsananin tausayin ta ne Ya kama shi, ganin yadda suka raunata Jikinta sun gur6ata
mata tsaftatacciyar fatarta, tsabar takaici da danasanin gaggawar da ta yi ne yasa
ta yin kukan, tana so ta yi ma shi magana sai dai ta kasa saboda sautin muryar ta
yaƙi fita ko da tana yin kukan babu sauti.

“Ban faɗi hakan don na fama maki ciwon da ke acikin zuciyarki ba, Nasan kina yi ne
duk don ki cece rayuwan ƴan uwan ki, don kuma ki cika mana alƙawarin da ki ka
ɗaukar mana, sai dai kash gaggawar da ki ka yi ta yi silar jefa rayukan mu cikin
haɗari, Zai yi wuya mu tsira sai dai bazan bari Ki rasa ran ki ba, Zan yi maku
ƙoƙari Ayau ɗin nan ku fuce daga cikin kurkukun nan kafin Hankalin Matsafan ya dawo
kanku, Mun ci sa’a shuwagabannin kurkukun basu aciki, Sauran da suka rage Giant ne
masu haɗarin gaske, Ni kaina da na ke da sihiri a jikina bazan Iya ja dasu ba, A
yanzu haka da nake Yin magana da ke nayi ƙoƙarin Sarrafa ɗakin Da ke ɗauke da
madubin tsafin su shiyasa ba zasu Iya ganin mu ba, Nan da Awa ɗaya Zamu Aiwatar da
komai Idan har lokacin nan ya cika kuna acikin kurkukun nan mu dukan mu zamu Mutu
bayan azabtarwa da zasu Mana.”

Baiwar Allah duk da raɗaɗin da bakinta ke yi mata ahaka ta daure ta cije ta soma Yi
mashi magana muryarta araunace daƙyar sautin ma yake fita

“Sun cire min uniform ɗina, Ruwan zamzam din Yana a cikin aljihun wandona bansan Ya
zanyi ba” cikin ƙunar rai ta ambaci hakan
“Zanje na ɗauko maki Uniform ɗin ki, cikin minti ɗaya” Yana ambaton hakan ya 6ace
ma ganinta.

Yunƙurawa ta yi daƙyar ta miƙe zaune, Ƙarnin Jinin jikinta ya addabi hancinta,


bargon da ke shimfiɗe saman gadon ta janyo ta yafa ma jikinta, Zuciyarta acunkushe
take da damuwar halin da ƴan uwanta su ke a ciki, Ita ba ta damu da kanta ba, sune
damuwarta. Fatanta Allah yasa tsohuwa zafreen bata cutar dasu ba kamar yarda ta
faɗa mata.

Durowa Cikin ɗakin salsabeel Yayi hannu shi ruƙe da uniform ɗinta, Jar vest ɗinta
da wandon ta Ya miƙa mata su, yatsun hannayen ta na kerma ta kar6e su, Agaban shi
ta zura kayan bayan ta kammala sanya su ta zaro ƴar ƙaramar robar zamzam daga
cikin aljihun wandonta, Idanuwanta acike tab da ƙwala ta kalle shi tare da cewa”Ta
ya ya zan Iya ganin Danish har in bashi ruwan zam zam ɗin”?

“Bamu da isasshen lokaci, A saman bayana zan goya ki in kai ki inda Ya ke kuma zan
taimaka maki mu bashi ruwan, ya kai ƙarshen maganar tare da Juya mata baya ya
zuƙunna daga bakin gadon, matsowa ta yi tare da kama bayan shi ta haye, Ya yunƙura
Ya miƙe, Daga inda ya ke goye da ita Ya 6ace 6att....

Ba su dura a ko’ina ba sai A wani katafaren Ɗaki mai tsawo da faɗi komai na cikin
shi launin Ja ne, hatta dogayen labulayen da ke a kewaye dashi red colour ne. wani
irin sanyi ne ke ratsa sassan Jiki acikin ɗaki kamar sanyin A.c, daga gani special
room ne na kurkukun ƙaddara, Tsadaddun furniture ɗin da ke a cikin ɗakin kaɗai abun
kallo ne.

Jin shiru bata motsa daga saman bayan shi ba yasa shi yi mata magana muryarshi
cikin raɗa ya furta” Mun ƙaraso, Ki tashi ki ga ɗan uwanki” yanayin yadda ya yi
mata maganar ne yasa taji gabanta Faɗuwa shi kanshi Salsabeel ɗin A tsorace Ya ke
da abunda zai Biyo baya balle ita kuma da ta ke Ƴar ƙwaruwa wadda bata taka kara ta
karya ba. Tsoro ya hana ta ɗago ta kalli inda Danish ɗin Ya ke duk irin kewar shi
da ta yi, Sosai ta runtse idanuwanta Hannayenta ƙanƙame da Salsabeel.

“Na faɗa maki bamu da isasshen lokaci ki sauka mana” yai maganar tare da zuƙunnawa
don ta sauka, Kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai jiki na kerma ta sauko daga saman
bayanshi, sai lokacin ta samu damar Ware idanuwanta sosai Tana ƙarewa ɗakin kallo
tun daga kan labulayen dake a cikin shi har zuwa kan shimfiɗaɗen Carpet ɗin dake a
ƙasa Ga wani ƙayataccen table mai ɗauke da Dinner set, plate ta gani na tangaran
mai ɗauke da kayan marmari, ga wani apple da aka datsi saman shi, hada sawun
haƙoran mutun, Ga wani glass cup mai ɗauke da wani abu acikinsa ruwane amma launin
shi yayi bright red kamar an surkashi da wani abu. Duk fa wannan kalle kalle da ta
ke yi ba ta yi tozali da shi ba, saboda ta hana idonta kaiwa gare shi, Har sai da
Sabsabeel yai mata gyaran murya tukunna ta soma Juyar da ƙwayar idanuwanta a
hankali ta ɗaura su kan katafaren king sized bed ɗin da ke kafe a cikin ɗakin, Gado
ne irin na sarakuna launin shi Golden Colour an shimfiɗe shi da lallausan Bedsheet
launin Ja, slowly ta sauke idonta akan dogayen ƙafafuwanshi wa’iya zubilla tsabar
ruɗu yasa ta dabarbarce saboda ta kasa yadda cewa shine, Halittar Jikin shi gaba
ɗaya ta canza, Ya zama jibgegen ƙato, Samun Namiji mai irin ƙirar ƙarfin shi zaiyi
wuya, ƙira ce mai matuƙar tsoratarwa, rikitarwa da kuma jan hankali, Ga dukkan
alamu bacci ya ke yi a giant ɗin ma bai bar halin shi na yin bacci ba, Dogon
wandone Baƙi A jikin shi, Sai Jar t shirt ta matse jikin shi, ta bayyana ainihin
surar shi, musamman damtsen hannayen shi tamkar zasu fasa rigar saboda tsabar
ƙarfi.

Sun canza shi sosai Farar fatar wuyan shi hada zanen tattoo launin baƙi da Ja wanda
ya kasance Tambarin kurkukun ƙaddara ne duk wani Giant yana da Zanan a wuyan shi,
sun rage mashi tsayin sumar kanshi, Anyi mashi kitson zane guda shida, wutsiyar
kitson ta sauka har saman Broad-shoulders ɗin shi, Ya koma kamar ƴan iskan turawan
nan, waɗanda tun daga suffarsu zaka shaida cewa, ba bu Ɗigon Imani A zuciyar su.

Zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta a yayin da ta ke ƙare mashi kallo, Ta gaza


yarda da abunda idanuwanta su ke Nuna mata, Wai Danish ɗinta ne Ya koma haka?
Hankalin shi kwance ya ke sharar bacci babu alamun damuwa atattare da shi, duk irin
kewar shi da ta yi shi baisan ma da zaman ta ba balle sauran ƴan uwan shi, saboda
zalunci na mutanan nan sun rabasu da ɗan uwansu.

Cikin shessheƙar Kuka Ta furta Sunan shi”Da..Nish..” walking nervously ta nufi


bakin gadon ta zauna daga gefe tana ƙare mashi kallo, Ya yi wani irin haske mai
kyan gaske, tsabar kyan fuskarshi tamkar zai kashe mata ido, la66ansa sun yi jawur
dasu kamar na Jinjiri, Dogon hancin shi ya tafi tsaye ba lanƙwasa, kwarin idon shi
ta zuba ma ido, dogayen eye lashes dinshi masu kyau da tsari.

“Don’t waste Our time! Mintuna kaɗan suka rage mana,” Muryar Salsabeel ce ta fargar
da ita, Ji ta ke kamar ta faɗa mashi ta rungume shi a jikinta ko ta samu sassauci a
cikin zuciyarta.

Matsawa kusa da ita sabsabeel yai “Ki buɗe murfin robar, Ni zan hau saman gadon In
ruƙe shi gudun kada ya farka ya ham6are ki, naushin giant yana da haɗari sosai
Bugu ɗaya su ke Yiwa mutun ya mutu In ba wani iko na Allah ba’ Wannan maganar da ya
yi ta ɗaga mata hankali, ta ƙara jin tsoron shi.

Yatsun hannunta na kerma ta soma ƙoƙarin buɗe murfin, tana dab da zata Ƙarasa cire
shi, Kamar An ce ta kalli fuskarshi taga ƙwayar idon shi na motsi ta saman kwarin
idon shi, da ƙarfi ta furta”Ya farka”

Sautin miryarta ne ya daki dodon kunnanshi, Aiko kamar an zungure shi Ya ware
manyan idanuwanshi launin russet brown akan fuskarta, wani irin ƙwar jini yai mata
a furguce Ta miƙe daga gefen gadon Tana ja da baya, idanuwanta azazzare, Salsabeel
da ke yunƙurin ruƙe kafaɗun shi don Ya hana shi miƙewa A zafafe Yai wurgi dashi tun
daga saman gadon Ya ƙundumo ƙasa Ji ka ke tummm, Hankalin Angel fa ya ƙara tashi
ganin yarda ya jefar da babban mutun kamar Salsabeel yadda kasan kallon tamola haka
ya jefar dashi wanda a haife salsabeel zai Iya haifarshi, Durowa yai daga saman
gadon Yana huci Kamar mayunwacin zaki, breast ɗin shi har motsi su Ke yi, Wani
matsiyacin kallo da taga yana binta dashi yasa ta haɗiyi yawu mai zafin gaske,
kallon da Danish ke yi mata kamar ma baisan wace ce ita ba, Tunkararta Ya soma yi
Yana gurnani har wani jijjiga jikin shi ya ke yi, babban abunda ta ke ji ma tsoro
kada Ya rikiɗa Ya canza halitta don ta fahimci abinda ya ke shirin Yi kenan, Juyawa
ta yi da gudu tana neman inda zata 6oye kanta don kada ya cimmata, saida ta gama
shan wahalar kewaye ɗakin Kwatsam taga Ya bayyana agabanta. Ɗagowa ta yi a tsananin
tsorace ta ke kallon shi tana girgiza mashi kai haɗi da marairaice mashi fuska don
Yaji tausayin ta amma ina ai ko kallo arziƙi bata ishe shi ba, Muryar Salsabeel ce
ta karaɗe kunnuwanta a kausasace ya ke bata Umarnin ta gudu daga gabanshi kada ta
bari ya Damƙe ta.

kafin ta yi yunƙurin Canza hanya Cikin rashin sa’a ta ji Ya damƙi qugunta Kamar
ɗiyar roba Ya ɗaga ta sama Muddin kuwa Ya bugata da kasa sai qugunta Ya 6alle
saboda ƙarfin dake gare shi bana Mutun bane na baƙin shaiɗanin aljani ne, Yana
ƙoƙari makata Da ƙasa Salsabeel ya cimma shi Gaba ɗaya yai wurgi da ita ƙasa ta
kife robar zamzam ɗin da ke a hannunta tuni ta gangara ƙarƙashin table ɗin da ke a
ɗakin gashi murfinta ya fara zamewa zai cire saboda buɗeshin da ta fara Yi, ruwan
da bai wuce Kur6a ɗaya ba Ya kare idan ya zube shikenan sun rasa damar da su ke da
ita.

Faɗane ya kaure a tsakanin Salsabeel tsohon ƙashi da Danish garkuwar kurkuku, Yadda
Danish Ya ɗaga salsabeel Ya buga shi da kasa ba ƙaramin gigita Angel yai ba,
lamarin ya tsoratar da ita babban abunda take jima tsoro kada Ya kashe shi da bugu,
da ko ta shiga uku, ƙarfi ba ɗaya ba Danish ya zarce salsabeel Nesa ba kusa ba
saboda shi matsayin babban giant ke gare shi masu haɗarin gaske, Salsabeel Kuwa Ko
star ɗaya bai da ita a muƙamin Giant, ta inda Allah ya taimake shi ƙwarewar da ya
samu A fannin sarrafa tsafi, ba don haka ba da tuni Danish ya jima da karkarya
ƙasusuwan jikin shi, Bugun da ya ke yi mashi da ace Lafiyayyan mutun ya yi mashi
wanda baida sihiri a jikin shi da tun a bugun farkon, ga6o6in jikin shi zasu daina
aiki.

Ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji daɗi faɗansu ya yi matuƙar ta6a ƙwaƙwalwarta, Ku
ka ta dinga yi hannayenta daddafe da kanta, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya
farmata, muryar Salsabeel taji a raunace ya ke faɗa mata ta ɗauko zam zam ɗin, da
sauri ta rarrafa ta nufi table ɗin har ta kusa ƙarasawa Taji an Janyo ƙafarta da
ƙarfi Yai wurgi da ita gefe ɗaya har saida kanta ya bugu da bango tsabar raɗadi
Yasa nan ta ke ta sume. Sai faman huci ya ke yi yana gurnani, gaba ɗaya ya gama
naƙasa ƙwarin gwiwarsu , shi kanshi Salsabeel Yana durƙushe ƙasa kanshi Ya bugu
sosai ga6o6in jikinsa sun rauna, akan idon shi Danish Ya jefar da table ɗin da
ƙafarshi, Kayan marmarin da ke asaman shi duk su ka tarwatse ƙasa, Ashe yana sane
da robar Zam Zam ɗin hannunta, Kafarshi Ya ɗaga da niyar ya ta ke ta don ta fashe,
A kiɗime Salsabeel Ya fasa ƙara tare da Miƙewa Yana jan kafarshi Ya nufi Danish.

Shu’umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar shi hada juyowa ya kalli Fuskar
Salsabeel Ya ɗaga mashi gira muryarshi tamkar ta mashayin giya ya furta”What?”

“Kada ka fasa ta na roƙe ka ko dan saboda ƙaunar da ke a tsakanina da kai danish,


Nifa ne Ya yan ka, Yau da hannun ka ka ke buguna kamar zaka kashe ni? Sai ka ce
baka sanni ba? Laifin me muka aikata maka? Kalli kaga yadda ka Bugi ƴar uwarki
Angel kamanta irin ƙaunar da ke atsakaninka da ita”? Ta6e la66ansa yai”who is she”?
Tambayar daya jefa mashi kenan

Muryar Salsabeel tamkar zai fashe da ku ka Ya ce “Ka kalle ta da kyau yar uwarka ce
Angel, Ba ka yi kewarta ba? Idan bazan manta ba lokacin da ka ke rashin lafiya
saboda matsalar da idon ka ya samu sunanta ka ke faɗi acikin sambatun ka ko ka
manta ne”? Kwa6e fuskarshi yai Alamar bai tuna komai ba.

Salsabeel sai Jan hankalin shi ya ke yi da surutu A yayin da ya ke tunkararshi duk


don ya samu damar ɗauke robar zamzam ɗin da ya ke Yunƙurin fasawa.

“you’re trying to deceive me” Danish Na ambaton hakan Ya dire ƙafarshi saman robar,
kukan Kura Salsabeel Yai tare da cakumar Wuyan shi Da iya ƙarfin shi na ƙarshe Ya
daddage Ya janye Danish gefe ɗaya, A gaban robar Sabsabeel Ya zuƙunna Yana Kallon
Yadda ruwan Cikin ta ya tsiyaye ƙasa, Tsabar takai Ci yasa shi Fashewa da kuka
kamar ƙaramin Yaro, ƙululun baƙin ciki ne ya addabi zuciyar shi, Damar da su ke da
Ita ta ƙare, zaiyi wuya su tsira.

Jikin Salsabeel na tsuma Ya yunƙura tare da miƙewa Ya ɗaura idanuwanshi akan Bayan
Danish wanda ke ƙoƙarin Tunkarar Angel don Ya ƙarasa kasheta, A hankali ya ɗaura
yatsun hannun shi saman rigar jikin shi ta kakin Giant, For the fast time da yai
nufin bayyana ainihin suffar shi, Cire Rigar jikin shi yai tare da jefar da ita
ƙasa, Faffaɗan ƙirjine dashi Irin na sadaukan Ya ƙi, 6an6are mask ɗin da ke akan
fuskarshi Yai tare da jefar dashi saman rigarshi.

Namijin Duniya Kyakkyawan gaske, fatar jikin shi Jawur ta ke, Ya fito a baturen
shi, Idan ka kalli fuskar shi ba za ka ta6a yarda cewa shi jinin tsohuwa Tamira ne,
saboda ita mummunace tsufa Ya 6oye kyanta.

“Na bika ta lalama ka ƙi banin haɗin kai yan zu zan yi maka ta tsiya, Danish ko ni
ko kai A yau ɗin nan” Jin miryarshi yasa Danish dakatawa da yin tafiyar, cikin
Takun Qasaita Ya waiwayo yana kallon shi, ganin ya tu6e rigarshi yasa ya fahimci
shirin faɗa Ya yi, jijjiga jikin shi yai nan ta ke ya rikiɗa ya koma Jibgegen zaki
ƙosasshen gaske sai gurnani ya ke yi yana wage bakin shi.

Hankalin Salsabeel Yai matuƙar tashi ganin ya rikiɗa, saboda shi sihirin shi bai
kai ƙarfin da zai Iya rikiɗa ya canza halitta ba, ganin yadda ya ke tunkaro shi a
fusace Yasa shi ja da baya ya soma tunanin me yakamata yayi don Ya dakatar dashi,
idan ba haka ba A kashe zai kashe shi har lahira.

Waige waige ya dinga yi yana bin ɗakin da kallo har idon shi ya sauka akan Wuƙar
yanka kayan marmarin da ke yashe saman floor, Ba zai iya ɗaukarta ba don bai son Ya
cutar dashi, Lallashinshi ya soma yi yana faɗin”Am sorry Danish ni ba faɗa zanyi da
kai ba, Pls ka saurare ni Danish dan Allah ka canza halittarka zuwa ta mutane ina
son yin magana da kai.....” Magiya ya dinga yi mashi amma ɗan tahalikin nan yaƙi
sauraron shi, Juyawa yai da gudu ya nufi saman gadon ɗakin Ya daka Uban tsalle Ya
haye saman shi tare da sanya hannu ya rarumo bargon dake nannaɗe saman shi, dai dai
lokacin da Danish Yai kukan kura Ya daka tsalle da suffar Zaki Zai kai mashi hari
Yai saurin Rufe shi Da bargon Ya nannaɗe shi a ciki, Allah ne ya taimake shi Ya
bashi ƙarfin da shi kanshi yasan bana shi bane, a saman floor suka faɗo, Sosai Ya
matse Danish Acikin bargon, ruƙo bana wasa ba kamar zai kashe shi, tun yana jin
sautin gurnanin shi har ta kai ga yai shiru babu motsi alamar ya suma.

Tsabar farin Ciki yasa shi sakin dariya yayin da hawaye ke bin fuskarshi, tunawa
da lokacin su da ke shirin ƙarewa saura Mintuna 30 ya rage masu kacal, A hanzarce
Ya zame bargon da ya lullu6e shi a ciki, har ya koma suffar shi ta mutane a ƙasa ya
kwantar dashi, Miƙewa Salsabeel yai da sauri ya nufi robar zam zam ɗin da ya
tsiyaye, Ya ɗauko ta a tsakiyar tafin hannun shi ya dawo ya zuƙunna agaban Danish,
a hankali ya buɗe mashi ƙaramin bakin shi ya dinga matsar robar ta ƙarfi kamar
zaiyi hauka daƙyar ya samu ɗigon Ruwan Ya faɗa bakin shi, Ɗigo ɗaya kacal, Gani ya
ke kamar ba zai isa ya dawo hayyacin shi ba, hakan yasa shi cigaba da matsa robar
duk don ya samu ruwan ya ƙara ɗigowa a ƙarshe da ya gaji ya jefar da robar ƙasa, ya
dafe kanshi da hannu biyu zuciyar shi na harbawa da matsanancin sauri.

faɗuwar da gaban shi ke yi ya tabbatar mashi da cewa wani mummunan abu na faru da
wani nashi ko dai mahaifiyar shi, ko kuwa yaran da ya ke ƙoƙarin taimakon rayuwar
su, Miƙewa yai a zabure Jiki ba ƙwari ya nufi Angel da ke yashe ƙasa tun ɗazu da
Danish ya jefar da ita ta sume bata ƙara motsi ba, hannu biyu ya sanya tare da
ɗaukar ta, Ya dawo ita gefen Danish Ya kwantar da ita, kafin ya ƙara miƙewa Ya nufi
Kayan saman table da Danish Ya watsar dasu ƙasa, A cikinsu ya samu robar ruwa, ya
ɗaukota tare da dawo wa gaban su Ya zuƙunna yana faman fitar da huci Shi kanshi a
raunace ya ke daurewa kawai ya ke yi duk don ya samu ya ƙarasa taimakon su.

A Saman fuskar Angel Ya watsa ruwan a Firgice ta farka haɗi da miƙewa tsaye tana
Faman zazzare idanuwanta fuskarnan jawur ta kumbura suntum.

“Unaisah” Cikin sanyin murya Salsabeel ya ambaci sunanta ko da ta kalle shi a


tsoroce Ta furta”wanene kai”! Ras Ya ji gaban shi ya faɗi, Can kuma sai ya tuna da
fuskarshi daya cire, shiyasa bata gane shi ba.

“Salsabeel ne” kallon shi ta dinga yi kamar yau ta fara ganin shi, ita kanta ba
haka ta yi tsammanin zata ga fuskarshi ba.

“Ga ɗan uwan ki nan, Na yi ƙoƙarin ɗiga mashi ruwan zamzam ɗin sau ɗaya abakin shi
bansani ba ko zai farka acikin hayyacin shi ko kuwa akasin hakan, Ba zan Iya jiran
farfaɗowarshi ba, hankalina ba akwance yake ba, Ina tsoron wani abu ya sami
mahaifiyata Don haka zan tafi wurin ƴan uwanki nasan tana atare dasu” Angel na
ƙoƙarin buɗe ba ki tace mashi ya tafi da ita kada yabarta anan gudun kada Danish ya
farka a matsayin Giant ya kasheta sai dai kash kafin tayi maganar Salsabeel tuni ya
6ace ma ganin ta...
A 6angaren Su tsohuwa zafreen kuwa Dambe su ka yi bana wasa ba, Saboda tsabar
zalunci sai da ta cire mata kunnuwanta duka biyun ta cinye su, Jini duk ya wanke
jikin tsohuwa tamira, duk yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa saboda rashin ƙwarin
Jikinta, har sai da zafreen ta kwantar da ita ƙasa ta dinga buga kanta Ga ƙasa
tuntuna motsi har ta kai sumewa.

Mahaukaciyar dariya zafreen ta saki ganin ta yi nasara akanta, Faɗa da aljani ba


riba maganar da zafreen ta furta a yayin da take miƙewa ta nufi wuƙar da batul ta
yi amfani wurin yi mata Illah, Jinin da ke a jikin wuƙar ta lashe kafin ta juyo ta
dawo kan tsohuwa Tamira, Ta zuƙunna tana Shafa Jikinta da tsinin wuƙar”Na jiye maki
baƙin Ciki, domin kuwa ayanzu ɗin nan zar farke Cikin ki, In kwashe ƴan hanjin dake
a cikin ki In cinye su, idan kin isa Ki kwaci Kanki, ƙazamar banza har ni za ki
kalli idona Ki gaya mini magana kamar bakisan wacece ni ba.....” ta ambaci hakan
tana mai sakin murmushi

Yunƙurin caka mata wuƙar ta yi ba zato ba tsammani taji an buge kanta da wani abu
mai nauyin gaske tamkar dutse kafin ta yi yunƙurin juyawa don taga wanene taji an
ƙara buga mata shi akanta, nan ta ke kanta ya juye Ta kife ƙasa,.

Batul ce a tsaye Tana haki, Hannunta ruƙe da sandar Zafreen da ta jefar ƙasa,
ƙarfin sihirin da ke a jikin sandar ne yasa har ta yi nasarar kwaɗeta da ita,
daddagewa tayi da ƙarfi taci gaba da buga mata sandar, Jijiyoyin wuyan ta duk sun
furfuto waje saboda tsabar 6acin rai, babu sassauci atattare da ita tun tsohuwa
zafreen na motsi har ta kai ga idanuwanta sun Juye, Jefar da sandar Batul ta yi
ƙasa tare da ɗaukar wuƙar da zafreen ɗin ta jefar, Saman ruwan cikinta ta haye ta
daddage ta dinga luma mata wuƙar Jini yadin ga ambaliya kamar an kunna fanfo harta
saman fuskarta, Kacaca tayi mata sai da ta farketa, A ƙarshe dai Baful ta yi
nasarar kashe tsohuwa Zafreen ko shura wa ba ta yi ba nan ta ke rai yai halin shi,
harta mutu batul bata daina farke jikinta da wuƙar ba, saboda bata acikin
hayyacinta, kuka ta ke yi tamkar ana zare ranta.

Farfaɗowa tsohuwa Tamira ta yi a hankali ta buɗe idanuwanta da suka ruƙida su ka yi


jawur dasu, ta wurga su kan Batul da ke a zaune saman Zafreen tana aikin fiɗa.

Muryarta na rawa ta ambaci sunanta”Ba..tul..” Sai lokacin ta jefar da wuƙar


hannunta, jiki na rawa ta sauko daga saman jikin zafreen ta rarrafo Zuwa gaban
tsohuwa Tamira.

Fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, taci gaba da yin kuka tana faɗin”Ta
zalunce mu ba mu yi mata laifin komai ba, ta kashe mana ƴan uwan mu ta gama da
rayuwar mu.....”

Hannun tsohuwa na kerma ta ɗaura shi saman sumar kan Batul da ke a tarwatse daƙyar
take iya yi mata magana”Batul babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin
baku haƙuri akan irin jarabtar rayuwar da kuka fuskanta, Ku yi haƙuri kuyi haƙuri
Allah yana atare da ku.......” Da numfashinta na ƙarshe ta ƙarasa maganar nan ta ke
rai yai halin shi, A matuƙar kiɗime Batul ke Fuskarta.........

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E4🔥💫_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura
mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu kamar zasu
fasa fatarta, hatta saman fore head ɗinta jijiyoyin ne....

A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin ɗaki, tun suna kuka har sun fidda rai da ƴan
uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shessheƙar kukansu har ta kai ga yanzu
basu Iya jin komai, A bakin ƙofar ɗakin tsohuwa Tamira suka zuzzuƙuna, Zuciyoyin na
tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun ƙafe, Haka zalika Naufal da javed
babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba ƙoshin lafiya ce da
shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi,
Daƙyar ne yai tsawaicin kwana.

A firgice su ka ɗago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin ɗakin su, jiki na kerma
suka miƙe suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba
ƙaramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin
murya ya soma yi masu magana.

“Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima ɗan uwan ku ne nasan ba
ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira”! Duk da basa
acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi.

Cikin shessheƙar kuka Haris yace”ƴan..uwan mu suna a cikin ɗakin tsohuwa Tamira,
Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su
saboda ta datse ƙofar.....” tun kan ya kai ƙarshen maganar, Salsabeel Ya wuce da
wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ƙofar Nan ta ke ƙofar Ta buɗe.

A fujajen Ya faɗa Cikin Ɗakin Hankalin shi a matuƙar tashe Ya ke binsu da kallo
ɗaya bayan ɗaya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira
har izuwa kan su Parveen da ke a sume ƙasa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform ɗin su
yashe a kasa da ta Cire masu, Da ƙarfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa’inna
ilaihirraji”un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya
dunƙule, Tsabar ƙunar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa ƙirjin
shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu
haka ya ke Ji.
“Ya Allah ka ɗauki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne” Muryar Batul
ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa’iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi
ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar
tsohuwa Zafreen A can gefe ɗaya, tangal tangal yai kamar zai kife ƙasa Da sauri ya
tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai ɗumin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba
wlh da ɗaya daga cikinsu baƙin ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel ɗin har
su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka
fuskanta a wannan baƙar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta
zama mahaukaciyar ƙarfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya
zuƙunna cikin rauni na murya ya furta”ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki
mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni kaɗai a cikin
wannan Duniyar mai cike da ruɗani”? Daƙyar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na
murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma
magana Batul ta ɗago da runannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu ta ƙura su
akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a
ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi.

“Hada kai Aka kashe min Ƴan uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine”! ɗago wa yai
tare da kallonta, Kafin yai yunƙurin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman
jikinshi tare da dunƙule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko’ina tana faɗin
Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe
mana ƴan uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne....? bata ƙarasa maganar ba kuka
Yaci ƙarfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi
saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah
Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka
ɗaukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah
gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ƙai, Maganar su ta ƙarshe ya soma tariyo acikin
kanshi.

“Salsabeel ko bayan ba raina inason yaran nan su ku6uta daga KURKUKUN ƘADDARA! Ka
yi min alƙawarin nan, ka taimaka masu ko dan su isar da saƙon mu zuwa ga mutanan
duniya, Bana so acigaba da aikata zalunci agidan kurkukun nan Ina mai jin takaici
da baƙin Cikin ganin yadda ake tauye wa ƙananun yara haƙƙinsu na rayuwa, basu ji ba
basu gani ba, An hana su more rayuwar su ta duniya, Ana kashe masu rayuwa a
lalatasu A ƙasƙantar dasu kamar dabbo bi, sannan a kashe su, kuma su mutu a
wulaƙance! Ka faɗa min Laifin me suka aikata da su ka cancanci Yin irin wannan
rayuwar? Idan har kana so In yi alfahari da kai a matsayin ka na Jini na to ka cika
min burina, Bana so Ganin mutuwa ta yasa zuciyarka ta raunata nafi so a lokacin da
ka yi tozali da gawata ka ƙara Jin ƙwarin gwiwar aiwatar da umarnin da na baka,
idan mutuwa ta risƙe ni a gidan kurkukun nan bana so kabar gangar jikina a gidan
kurkukun ƙaddara Ka yi nesa dani kafin ka binne ni.........” lokacin da tsohuwa
Tamira ta yi mashi maganar sosai ya fashe mata da kuka yana faɗin zai yi duk abunda
take so amma tadaina maganar zata mutu, ya ta ke so ya yi da rayuwar shi? Bashi da
kowa a duniyar nan bayan ita, murmushi ta yi tare da ce mashi Kana da Allah sannan
bayan shi ga ƴan uwanka nan suma basu da gatan daya wuce Allah da kuma kai, Don
haka ka daina tunanin cewa sai da ni zaka Iya aiwatar da komai. Ni dai fatana Ku
tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, Azzaluman shuwagabannin da suka ƙirƙire shi ku
tabbatar tun agidan duniya sun ɗanɗani kuɗarsu kafin su koma ga mahaliccin su bana
so kubar hukuma ta hukunta su saboda duniyar nan acike take da marasa gaskiya idan
kunga ba zasu baku goyan baya ba ku yi amfani da ƙarfin ikon da ku ke dashi wurin
yi masu mummunan kisan da sai sun yi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin
duniyar nan, Kafin su mutu ku Azabtar dasu ta yadda zasu manta da duk wani jin daɗi
da su ka yi a duniya, Idan har ku ka yi min hakan to zan jin daɗi, zan yi kuma
alfahari da ku, Bayan ta yi mashi wannan maganar salsabeel yana kuka ya roƙe ta
alfarma ɗaya kafin faruwar duk waɗannan abubuwan yace mata yana so ta kar6i
musulunci akaro na biyu ta yi imani da Allah, Numfasawa tayi tare da ce mashi”Ba
zai yiwu ba saboda Allah ba zai ta6a kar6ar tubanta ba ko da ta musulunci saboda
ɗumbin zunubban da ta aikata sun yi muni sosai, Salsabeel ya yi ƙoƙarin fahimtar da
ita ta hanyar Yi mata nasiha ya nuna mata cewa shi Allah gafurirrahim ne yana son
bayinsa waɗanda su ka aikata zunubi suka gane kuskuran su kuma su ka tuba zuwa gare
shi, daƙyar ya samu tsohuwa Tamira ta sake kar6ar shahada maganarsu ta ƙarshe data
furta mashi”Zan je wurin Yaran can inaji araina wani abu yana faru a ɗakin su,
Kafin na isa wurin su inaso ka yi gaggawar zuwa Ɗakin Madubin sihiri Ka canza ganin
su ta yadda ba zasu fahimci abunda ke faruwa ba......wannan itace magana ta ƙarshe
da tsohuwa tamira ta furta mashi kafin tabar wurin shi, akan hanyar shi ta zuwa
ɗakin madubin sihiri Ya ga duk wani abu da ya faru da Angel kun ji yadda akai har
yaje gare ta.

Cakumar Batul ya yi da hannun shi tare da janyota ta dawo saman faffaɗan ƙirjin
shi, Rungumeta yayi da hannayenshi tamkar zai mayar da ita cikinshi, Hakan da yayi
mata ne yasa ta sassauta kukan nata......

Tsoro da fargaban abunda idanuwansu zasu nuna masu ya hana su shiga Cikin ɗakin,
Bayin Allah suna atsaitsaye Bakin ƙofar suna sauraron gunjin kukan da Batul ta ke
yi.

Idan mu ka koma 6angaren Angel kuwa tun bayan tafiyar Salsabeel tana zaune cikin
matsanancin tashin hankali, Da fargaban farfaɗowar Danish, Ba zato ba tsammani ta
ga yatsun ƙafarshi na motsi, A gigice ta yunkura da niyar ta miƙe Sai dai kash
ƙafarta ta ƙi bata haɗin kai, Wani irin tsami ta yi mata, a tsananin tsoroce take
ja da baya tana kallon shi jikinta nata 6ari

A hankali Ya ware kyawawan idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin na tsawon daƙiƙa
talatin kafin Ya yunƙura ya miƙe zaune.... Ta wutsiyar idon shi ya ke hango kamar
mutun na motsi, hakan yasa shi yin saurin kai idon shi gare ta, unexpected idanuwan
shi su ka sauka acikin nata, da wani irin kallo ya ke bin ta da shi, gani ta ke yi
kamar bai dawo hayyacin shi ba.

Ya kasa tantance wacece ita? Saboda daskararren jinin da ke a jikinta, ta koma


mashi kamar aljanna, ranta ne ya bata cewar ko dai ya dawo hayyacin shi? Wata’ƙil
saboda munin da ta yi ne yasa bai gane ta ba, Cikin jin shakkar shi muryarta na
kerma ta ambaci sunan shi”Da..nish..its me ur Angel” Ware fareren idanuwan shi yai
sosai akan fuskarta, jin muryar da ya daɗe yana mararinta, ba zai ta6a mantawa da
muryarta ba, A ruɗe ya motsa la66ansa tare da furta sunanta”Angel? Is that you”?
Ita kanta batasan ya akai ta iya miƙewa ba, Tsabar farin Ciki da gudu ta nufe shi
tana ƙarasawa gaban shi slowly ta zube saman gwiwowinta tare da faɗawa saman
faffaɗan ƙirjinshi sosai ta rungume shi tana ku ka, Bai damu da ƙarnin jinin da ke
a jikinta ba, sai dai zuciyar shi ta rikice ya shiga ruɗanin ganin canzawar da ta
yi, Jikinta duk raunuka ta yi muni kamar ba Angel ɗinsa ba, Tunawa da Ƴan uwanta da
kuma ƙurarren lokacin da ke gare su yasa tace mashi”Ka tashi mu tafi Danish ka
kaini ɗaki, na bar su Azeeza suna jiran mu” shiru bai motsawa ba saboda ya rasa
tunanin shi.

Bugun bayan shi ta dinga yi da hannunta Cikin shessheƙar ku ka ta ke faɗa mashi Ya


tashi ya ɗauke ta suje ɗaki ƴan uwan su na acikin haɗari, “ daƙyar ta samu Danish
Ya miƙe ɗauke da ita saman faffaɗar kafaɗar shi, daga ina ya ke a tsaye Ya 6ace bai
dura a ko’ina ba sai A cikin ɗakin su, Tunkan ya sauke ta ta riga zame jikinta, Su
Haris da ke a tsaye bakin ƙofar ɗakin tsohuwa, a ruɗe su ke kallon shi Musamman
Gabriel yasha ruwan mamakin ganin Danish da idon shi Garas.

Muryar Angel na rawa ta soma ambaton sunayen su”Ha..ris..Mubeen..Naufal..Javed..”!


akace labarin zuciya a tambayi fuska, Tun kan ma su yi mata bayanin abunda ya faru
da gudu ta faɗa cikin ɗakin tsohuwa Tamira da ke a buɗe, Idanuwanta Azazzare take
kallon Ƴan uwanta dake kwance ƙasa ba numfashi, Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki
ta fitar hayyaci wadda tayi silar faɗowar Danish dasu Haris cikin ɗakin sai lokacin
su ka ga mummunan abunda tsohuwa zafreen ta aikata ma ƴan uwan su. Silar ƙarar da
Angel ta fasa ne yasa Batul raba jikinta daga na salsabeel fuskarta jaga jaga da
hawaye ta ɗago idanuwanta, tana yin tozali da Angel da gudu ta nufota tare da
faɗawa saman ƙirjin ta suka ƙanƙame juna suna yin kukun zuci, Cikin shessheƙar kuka
Batul ta labarta mata duk abunda ya faru bayan tafiyarta, Tasha kuka kamar ba gobe,
ta yi fatan ace dukkan su ne suka mutu hada ita, gaba daya shirin su ya tarwatse
taya zasu iya barin kurkuku Bayan ƴan uwansu duk sun mutu, Alƙawarin data ɗaukar
masu bata samu cika shi ba, Ga danish ɗin ta ci nasarar dawo dashi sai da kash Ta
faru ta ƙare, ƙaddara ta riga fata, Cikin raunatacciyar murya ta wanda ya gama
sarewa da rayuwar duniya ta furta”Nashiga Uku na bani na lalace! Ya Allah zunubin
me muka aikata mu ke fuskantar irin wannan mummunar jarabawar daga gare ka? Idan ba
ka son mu, ka ɗauki ran mu mu huta, Mun gaji mun gaji Wayyo Allah na Na rasa
Azeeza na rasa jemimah na rasa Deeja da sauran Ƴan uwana, To ni zaman uban me zanyi
acikin duniyar nan wlh bazan rayu ba dole in kashe kaina......” Cikin fitar hayyaci
ta furta kalaman, kamar mahaukaciya, ta juya da niyar ta je nemo makamin da zata
halaka kanta dashi, Cikin zafin Nama Salsabeel Ya damƙi hannunta, tare da juyo da
ita ta yadda zata fuskance shi”Meye ribar ki idan kin kashe kan ki? Dama ba sai da
na faɗa maki Ba lallaine ku rayu ku dukan ku ba, Yanzu idan kika mutu Kinsan adadin
rayukan da za’a cigaba da 6arin jinin su a gidan kurkukun nan? Idan har bamu
lallashi zukatan mu ba mun kawo ƙarshen Azzaluman da suka cutar da ƴan uwan mu Duk
wani ƙoƙarin mu ya tashi abanza kenan! Ya ku ke so inyi da raina ne? saboda ku na
rasa mahaifiyata Ni kaina ashirye nake da in rasa raina in dai akan ku ne, Don haka
kada wanda Ya ƙara Yi mana kuka Ya isa haka !! Mutuwa dole ce ko muna so ko bamu
so, Kuma mutuwa sauƙi ce agare su saboda rayuwar duniyar bakomai bane acikinta face
ruɗani, cike take da ƙalubale iri iri, ni banga amfanin yin kuka don wani ya mutu a
cikinmu ba, Saboda Allahn daya halicce su wanda yafi mu sonsu shine ya kar6i
abunshi, Sai sunfi jin daɗi fiye da na duniyar nan......’ sosai Salsabeel ya yi
masu nasiha har saida yaga sun dawo hayyacin su tukunna Yace dasu babu isasshen
lokaci su wuce su tafi, Danish Zai buɗe masu ƙofa, shi zai kula da gawawwakin Ƴan
uwansu da suka mutu, Tun shigowar Danish ɗakin kusan suman tsaye yayi, saboda
tsabar Kiɗima da ganin halin da ƴan uwan shi su ke aciki, Ya rasa bakin magana, Ya
yi matuƙar girgiza da ganin yadda aka wulaƙanta rayuwar Ƴan uwan shi, Hankalin shi
yai mugun tashi, Zuciyar shi tamkar zata faso ƙirjin shi ta 6allo saboda tsabar
ƙunar da ta ke Yi mashi, Ya fusata Iya fusatuwa, ganin yadda yake huci ƙirjin shi
na motsi ga wata narkakkiyar zufa dake wanke mashi fuskarshi, yasa Salsabeel yin
saurin dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana”Danish ka sassauta fushinka idan ba
haka ba giant’s heart ɗin ka zata iya motsawa, pls ka ceci rayuwar su ku gudu daga
kurkukun nan, duk wani abu da ya toshe maka kai, Unaisah zata yi maka bayani idan
kun fita” daƙyar ya samu Danish ya iya sarrafa fushin sa.

Muryar Angel adisashe tace dashi”Ni bazan Iya tafiya in bar gawar su Azeeza acikin
wannan ƙazamin ginin ba, inaso na cika masu burin su duk da basa araye zan fitar da
gawarsu waje in yaso sai mu binne su a akan hanya, dan Allah ku taimaka min” Tana
magana hawaye Na wanke fuskarta.

“Unaisah bamu da isasshen lokaci pls ku tafi kawai ku barni dasu zan san inda zan
6oye gawarsu” fashe mashi ta yi da kuka kamar zata haɗiyi zuciyarta, Hankalin
Danish gaba ɗaya ya dawo kanta, tsananin tausayinsu duk ya kama shi.

“Bazai yiwu ku iya tafi da su ba! Kubar su a wurina zan tsaga ƙasa In binne su”
acewar Salsabeel

Ataƙaice zan yi bayanin yadda su ka gudu daga KURKUKUN ƘADDARA, Angel ce ta goya
Jemimah abayanta tare da sanya Mayafin kayan su da ta ɗauko acikin akwatin su,
Gabriel ya goya gawar Azeeza abayanshi ya ɗaureta da mayafi, Naufal ya goya Parveen
asaman bayanshi, Haris yaso ya goya Deeja abayanshi sai dai Salsabeel Ya hana shi
gudun kada su ja ma kansu wata wahalar, Iya waɗannan kaɗai su ka ɗauka sauran Sun
bar su awurin shi bayin Allah badan sun so ba, kusan mutun shida daga Ciki hada
Deeja, Sarah, Eve, Yasmin, Rubina da Hibba, Danish ya yi ƙoƙarin yin amfani da
sihirin shi wurin farfaɗo dasu, mutun ɗaya kaɗai ta samu damar tashi Hannah, a
ƙarshe ya tabbatar masu da cewa Heart attack ne Yai silar mutuwar su, zuciyar su ce
ta buga.

Ƙululun baƙin Ciki kamar su Zauce, Kafin tafiyar su Mubeen ma ya yanke jiki ya
faɗi, Don dole suka haƙura da shi, Lamarin ya yi matuƙar gigitar da su.

Salsabeel ya yi masu alƙawarin Zai yi nesa da gawarwakin Ƴan uwan su, tare da ta
mahaifiyarshi ba zai bari a wulaƙanta su ba, sun yi kukan rabuwa dashi, har magiya
Angel ta dinga yi mashi akan ya zo su tafi atare da shi, amma yace masu ba zai iya
bin su ba, su yi haƙuri su tafi idan Allah yasa yana da tsawaicin kwana zasu sake
haɗuwa ne duk da yasan abune mai wuya ya rayuwa ko dan saboda 6arnar da suka aikata
dole matsafan su azabtar da shi.

Rabuwar su ta yi matuƙar ta6a zuciyar kowannan su, a gurguje su ka nufi sashen


makewayin su, Tsabar tashin hankali yasa Gabriel mantawa da zancen Ƴar uwar shi
Gabriella da ke a cikin kurkuku, tun da ya ga mutuwar ƴan uwan shi prisoners, yasa
wa ranshi dangana.

Suna shiga Cikin Toilet ɗin, Danish Ya datse ƙofar da sihirin shi, ya Janye
tukunyar fulawar daga kan ƙofar, nan ta ke ta bayyana duk irin wahalar da suka sha
ta ƙi buɗewa shi Bugu ɗaya yayi mata gaba ɗaya ta 6alle murfin ƙarfen ya dare biyu,
Sun yi mamaki da al’ajabi yace da su”Ba zai bi su ba, zai tafi da Akwatin kayan su
tare da back pack ɗin su, za su tarar dashi a bakin ƙofar da zasu 6ula idan sun
ƙarasa” hankalin su bai kwanta da maganar shi ba, gani su ke yi kamar wani mummunan
abun zai faru da su idan baya atare da su, ganin sun toge sunƙi tafiya yasa shi
Kwantar masu da hankali, daƙyar ya samu su ka Zuƙunna ƙasa tare da kutsa kai ɗaya
bayan ɗaya su ke shiga cikin ƙofar da rarrafe, Bayin Allah ga yunwa ga ƙishin ruwa,
ga raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu, Ita kanta hanyar da suka biyo Wata uwar ƙura ga
yanar girgizo da ƙwari sai hawan masu jiki su ke yi, Amma saboda rashin kwanciyar
hankali yasa basu damu da su ba. Babu mai magana acikinsu saboda ƙunar da ran su ke
yi masu, Angel ce tai ƙoƙarin tunasar dasu akan suci gaba da ambaton addu’o’in data
koya masu ko sun samu sassaucin a wurin Allah, sun ɗau ki shawararta ahaka suka
Dinga tafiya da rarrafe babu ƙaƙƙautawa, idan suka gaji su kan ɗan zauna su huta
kafin su dasa da wata tafiyar, A ƙalla sun shafe tsawon awanni Takwas suna
rarrafawa ba tare da sun kawo ƙarshen Ƙofar ba, a takure su ke Bayin Allah sun ga
rayuwa gwiwowin ƙaffuwan su duk sun gurje sun sage, maƙoshinsu ya bushe ƙamas, tun
suna ambaton ƙishir ruwa suke ji har sun gaji sun yi shiru.........”😭

💔Prisoners💔

Sun ci baƙar wahala saboda tsohuwar hanyace da ta yi shekaru aru aru a datse ba
tare da an yi amfani da ita ba, Muggan ƙwarin da ke a ciki sai ɗallinsu su ke Yi,
amma saboda azabar raɗaɗin da zuciyar su ke yi masu yaci uban raɗaɗin harbin da
ƙwarin ke yi masu yasa ba su ji, A makance suke tafiya basu ji basa gani, ga wani
azababben zafi daya addabe su, kowan nan su ya haɗa uban gumi burin su kawai su
cimma ƙarshen ƙofar, wani ƙarin tashin hankalin fitilun da ke a hannun su Batul
hasken su ya fara ƙoƙarin ɗaukewa abunda basu ta6a yi masu ba, sun fuskanci
matsanancin tashin hankali har sai da suka fidda rai da fita saboda ganin tsawon
awannin da suka shafe ba tare da sun kawo ƙarshen ta ba, tun da suna rarrafawa
Hannah ke kuka tana faɗin ƙaiƙayi ta ke ji a jikin ta, duk da halin da su ke aciki
hakan bai hana su rarrashin ta ba akan ta yi haƙuri, a lokacin da ba su yi tsammani
ba kwatsam! hasken fitilun hannun su Ya ɗauke ɗuff Innalillahi wani irin duhu
baƙiƙƙirin ya mamaye idanuwan su, ko fuskokin su basa Iya gani, duk sunbi sun
firgice saboda hanyar ta 6ace masu, Sunan Danish su ke ta kira a bakunan su, sun
manta cewa baya atare da su.

“Danish ka taimaka mana, duhu bamu iya ganin komai, bamu san ya za mu yi ba,” abu
biyu ya haɗe masu ga fargabar kar a rutsa su ga kuma Rashin haske gani su ke kamar
Aljalinsu ne zai risƙe su awurin, Sautin koke koken su ne ya cika hanyar, sun kasa
jurewa tsananin tsoro suke ji, Danish ka yi mana magana pls Ya zamuyi? Kada a rutsa
damu, idan ba mafita ne ka faɗa mana.....” Cikin shessheƙar kuka Angel ta yi mashi
maganar, kamar zasu yi hauka, sun rasa gane me ke shirin faruwa dasu ne?

“Innalillahi wa’inna ilaihirra’un! ya Allah kawo mana ɗauki! Wai ina Danish ɗin ya
ke bai jin mu ne ko baya atare damu”! Naufal ne yai maganar, tsabar matsewar da su
ka yi yasa wani bai iya motsawa daga inda yake balle har su iya gano inda Danish
ɗin ya ke, Yadda kasan kifin gwangwani haka suka cunkushe, Bawan Allah Haris gaba
ɗaya baya acikin hayyacin shi, Damuwar shi Deejarshi da ya rasa, Yaji ƙuncin da har
abada bazai ta6a goge mashi ba, zuciyarshi ta yi mashi nauyi ga dukkan alamu wani
mummunan ciwon ne ke shirin kama shi.

“Nifa ina jin tsoro ace Danish Ya canza ra’ayin shi na taimakon mu, zai iya komawa
giant”! Gabriel ne yai maganar cikin rauni na murya
“Ni da ma na fidda rai da rayuwa, bansawa raina zan bar kurkukun nan araye ba.”
Javed ne yai maganar cikin rauni na murya.
Suna Cikin Jimamin rashin Jin motsin Danish da fargabar me zai Biyo Baya.

Ba zato ba tsammani suka soma hango haske Yana kurɗaɗowa ta Cikin wata ƙofa Yana
gauraye inda su ke zazzaune, Tsabar ruɗani Ya sanya su ka Waro idanuwan su waje
Kamar ƙwayar Zasu faɗo ƙasa Sun kasa gane hasken menene ke isowa gare su.

Ba kowa ba ne abakin Ƙofar fa ce Garkuwar kurkuku shine ya buɗe ƙofar Kogon


Bishiyar, Ashe ta inda zasu 6ullo Cikin kogon bishiya ne Mai girman gaske Wurin Ya
wawake........

Saboda rashin wadataccen haske basu Iya ganin shi da kyau, Cikin sanyayyiyar murya
ya furta masu “You ave reached the door. Today, you will finally leave the prison
of destiny, am happy for the first time that you will live a happy life. am ready
to be your shield, and I will not let you get hurt by the lows and difficulties of
life.”

Abun farin Ciki sai dai ba halin nuna shi saboda ba haka suka tsammaci zasu bar
kurkukun ba, Ƴan uwan su duk sun mutu, duk irin burin da suka ɗaukarwa kansu na son
Yin rayuwar Ƴanci gaba ɗaya ya tashi abanza, Cikin su goma sha takwas mutun goma
suka tsira, ahakan ma basu da tabbacin zasu ƙarasa da ran su da lafiyar su ba tare
da wani abun ya kuma faruwa da su ba, Kusan atare suka rushe da matsanancin kuka
tamkar ana zare rayukansu, Kukan baƙin Ciki da ƙunci da raɗaɗi, Kuka mai matuƙar
tsuma zuciya, Tsananin tsauyin su ne ya kama Danish A hankali ya ke ƙare masu
kallo, Cikin sanyin murya yace da su Idan nace Ku yi haƙuri Na cuce ku, I can’t
stop you from shedding your tears, except to encourage you to cry. It’s the only
thing that can ease the pain in your heart.”

Fuskar shi ɗauke da matsananciyar damuwa yai maganar, kamar ya ƙara tun zura su
aiko suka ƙara sautin kukan nasu, Idanuwansu duk sun kumbura Fuskokinsu sun yi
jawur. ganin basu da alamun motsawa yasa shi matsawa tare da ruƙo hannun Angel dake
goye da gawar jemimah abayanta, ya turo ta waje a hankali, Tana fitowa ta runtse
idanuwanta da ke tsastsafo da ƙwalla.

ƙurmin Daji ne mai nau’ikan tsirrai da dabbobi iri-iri. Manya manyan bishiyoyi masu
tsayi da faɗi suna da Dogayen rassa, Faɗaɗan Ganyayyakinsu Sun toshe hasken Farin
watan da ke a sararin samaniya kaɗan ne ke samun damar haskowa ta tsakankanin
Ganyayyakin, yau shekara Uku da watanni rabon da ta tsinci kanta A waje, Ina ga
sauran ƴan uwanta Prisoners waɗanda tun da uwar su Ta haife su basu ta6a tozali da
haske rana ba, Ɗaya bayan ɗaya Danish ya dinga janyo su kamar basu son fitowa, Kaf
ɗin su Ya fiddo da su, kafin Ya maida ƙofar kogon tamkar ba’a ta6a ratsa cikinta
ba.
Sai faman zazzare idanuwansu suke yi suna bin Dajin da kallo duhu Ya hana su ga
komai da kyau, Tsananin tsoro ne ya kamasu, Ga wani irin bala’intaccen san yi kamar
Jaura ta gifta, Haƙoran su sai kakarwa su ke yi, muryoyinsu Na rawa suka soma
ambaton sunan Danish Suna faɗin sanyi su ke Ji.

Da sauri Ya buɗe akwatin kayan su dama shi ne ya ɗauko shi Tare da back pack ɗin
Unaiza, Ya zaro masu bargunan su, A saman bayan su Ya lullu6a ma kowannansu bargo,
Tunani ya shiga yi ya zaiyi dasu? Ga dukkan alamu sun gaji basu Iya motsawa gashi
yana fargabar kada akawo masu hari yasan dole abiyo bayansu. Babu mai ƙoshin lafiya
acikinsu kowa takan shi ya ke yi shiyasa ko farin cikin fitowar ba su yi ba duk da
irin ɗaukin da suka dinga yi, su fa har yanzu basu yarda cewa sun fito daga
kurkukun ƙaddara ba, gani su ke yi kamar har yanzu suna aciki, saboda duhun daya
mamaye idanuwansu basu Iya gani dakyau hada ƙarin nauyin da idonsu yai masu
sakamakon kukan da suka sha, wasu ma daga cikin su ciwon ido suke fama dashi,
Danish ne kaɗai yake Iya ganin su da kyau.

Yanke shawarar ya yi da zuciyarshi nan take ya haifar masu da jin matsanancin


bacci, Asaman dogayen ciyayin da ke shimfiɗe masu cukowa, Kowan nan su Ya kwanta
hada masu goyan cikin su, Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa, Ya ɗauki bargo
ɗaya daga Cikin wanda Ya lullu6a masu Kamar walƙiya ya 6ace Bai dura a ko’ina ba
Sai acikin kogon dutse mai girman gaske, da sihirin shi ya kawar da duk wani abun
cutarwa Ya gyara wurin tsaf babu ko ƙura balle aje ga batun halittun da ke rayuwa a
cikinshi, Bayan ya tabbatar da babu abun cutarwa Ya shimfiɗa bargon dake a hannun
shi, Kafin Ya juya tare da 6acewa ya dawo wurin da yabarsu kakkwance suna bacci,
Cikin mintuna Biyar Yai aikin da acikin awa biyu mutun zai iya yin shi, Bai da
banbanci da Jinni, kamar walƙiya ya dinga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya yana kaisu saman
shimfidar da yayi masu a cikin kogon dutse bai bar kowa ba, Bayan ya kammala kwashe
su ya ɗauke masu akwatin kayansu da jakar ya shigo dasu Cikin kogon ya ajiye shi.
Komawa yai cikin dajin Ya haɗo itace dayawa ya shiga dasu ruƙe a hannun shi Cikin
kogon dutsen, Ya jera su a ƙasa nesa da inda su Angel su ke akwance, Ya tsinto
duwatsu guda Biyu ya gurzasu jikin juna nan take wuta takama Ya cinna ta a jikin
itace sosai Wutar ta ruru, a ƙalla ya sauke ajiyar zuciya yafi sau a ƙirga, ya hada
uban gumi shi kaɗai, jiki bai saba da wahala ba, fuskarshi sai naso ta ke yi kamar
an watsa mashi ruwa, Ya jima zuƙunne abakin wutar Yayin da idanuwanshi ke akan ƴan
uwanshi dake lullu6e cikin bargo suna bacci, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi
kamar an kora ruwan san yi, haƙika yayi danasanin duk wani abu da ya faru dasu, Ya
ji ƙunci sosai A cikin ran shi, miƙewa ya yi a hankali ya ke tafiya yana tunkararsu
a gaban shimfiɗar su Ya zuƙunna tare da miƙa yatsun hannayenshi Ya ruƙo bakin
bargon dake lullu6e dasu Ya yaye shi, Hasken wutar da ke cini ne Ya haskaka mashi
fuskokinsu, Idanuwanshi na akan Marasa ran cikin su, idan ka kalle su a yadda suke
kwance baka ta6a cewa gawawwaki ne, Tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur, Zuciyarshi ta
ƙara karaya tsananin tausayin rayuwar ƴan uwanshi ne ya kama shi, Ya rasa ya akai
duk waɗannan abubun su ka faru ba tare da sanin shi ba? Shin me ya faru da su bayan
An ɗauke shi daga Cikin su? tambayoyi ya shiga jefa ma kanshi. Ataƙaice Daren Ranar
Danish bai runtsa ba, Kwana yai a zaune yana gadin su.

*MIDDLE STEP THE PRISONERS BOOK TWO🔥💫*

*BIRNIN ABUJA🏙*

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank
3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E5🔥💫_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

*ANEELERH*

Kwance ta ke asaman katafaren gadon ta da ke acikin haɗaɗɗen bedroom ɗinta da ke a


sabon gidan su na Abuja mallakin Uncle ɗan Iya ɗaya daga Cikin ƙannan Abie ɗinta
mazaunin garin Abuja, Attajirin mai kuɗi ne mai yiwa ƴan siyasa hidima, Tun bayan
da Abie ya samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi aka yi mashi transfer zuwa ministry
of finance da ke anan Abuja, a ƙalla yau watan su bakwai da barin jihar jos, ba
ƙaramin canjin rayuwa su ka samu ba a gidan ɗan Iya, mutunne mai son jama’a ga iya
mu’amala da kyautatawa mutane, kusan halin shi ɗaya da matar shi Aishatu wadda ake
da Aunty Ummi.

“Aunty Aneelerh! Auntyna! Where are u? i’m back” can cikin bacci ta dinga jin ana
ƙwala mata kira, Sautin muryar matashiyar budurwa.

Nauyin bacci ya hana ta buɗe idanuwanta sai ma ƙara ƙudundune kanta da ta ke yi


acikin lallausar bargonta, faɗowa cikin ɗakin ta yi Tabarakallahu Zankaɗeɗiyar
budurwa jawur da ita, Jikinta na sanye da egyptian gown launin shuɗi, Ta yi
rolling veil akanta, Light make up ne akan fuskarta daga ganinta ba ƙaramar wayayyi
bace a jin farko, Takalman ƙafarta high hills ne launi ɗaya da Mayafinta white
colour, hannunta na dama na asanya da Tsadadden agogo silver colour. Ƙamshin
turaren Jikin ta mai matuƙar sanyaya zuciya, wayar da ke a ruƙe a hannunta ƙirar i
phone 15 pro ce.

Agogon bangon da ke a ɗakin ta kalla ƙarfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga ƙwayar


idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta ɗanyi fuskarta ɗauke
da ƙayataccen murmushi tace”Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini
ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki
aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje” da zolaya ta yi maganar
a yayin da take ƙarasa shigewa Cikin bedroom ɗin, Cikin sanɗa take tafiya tana
tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, ɗaukar shi ta yi saboda
mugunta ta ƙure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke
ƙara nannaɗe kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta
ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya
hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yunƙurin buɗe ido da sauri Zahra ta
rage sanyin a.c ta ajiye remove ɗin saman drawer, ta ruƙe qugu tana binta da kallo.

Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse,
Tunkan ta buɗe ido ta soma surfa masifa tana faɗin”junaid bana hana ka ƙara min
sanyin a.c ba? Saboda ka raina min wayau ko?wlh idan ka bari na damƙi hannun ka sai
ka gane ba ka da wayau, Sullu6iyo kawai......” Bata ƙarasa maganar ba ta soma Jin
sautin dariyar Zahra, hakan yasa ta yi saurin ware idanuwanta tare da wurga su kan
fuskarta.

Gwalo ta yi mata tare da ɗaga mata gira tace”Ba junaid bane yayar shi ce mai irin
halin shi, “ Harara Aneelerh ta shiga watsa mata kamar ƙwayar idon zata faɗo kasa.

Zahra tana dariya tace”Iya hararar ne kawai idan mutun ya isa ya sanya hannu ya
dake ni, kai da ka zo baƙunta gidan mutane ka ishe su da baccin lalaci.....” bata
samu damar ƙarasa maganarta ba, Aneelerh ta rarumi pillow a zafafe da duro daga
saman gadonta, zaro ido zahra ta yi kafin ta juya da gudu ta nufi ƙofa cikin rashin
sa’a ƙafarta ta jirkice ta fasa ƙara zata kife ƙasa da sauri Aneelerh ta janyota
zuwa jikinta, sosai ta ƙanƙameta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi ta firgita
sosai.

“Rasa kunya 6eran tanka, Yanzu ga ki a hannuna, mai ƙwatarki yau sai Allah” Kokoyi
su ka soma Yi kamar ƙananun yara, Zahra sai ƙwalawa Umminta kira ta ke yi tana
faɗin tazo ta cece ta daga hannun Aunty aneelerh zata kashe mata ƴarta, Aneeleh na
dariya tace”Nima ai ina da uwar sai in kirata tazo taga idon mara kunya” ta ambaci
hakan tare da ƙwalawa Maminta kira.

Sun shaƙe junansu sai nishi su ke yi gyalen Zahta tuni ya jima da zamewa saman
tiles, gashin kanta baƙi wulik anyi mata kitson kalaba ya sauko har kafaɗarta.

“Aunty Aneelerh Am sorry wlh na miƙa wuya, zan maki biyayya na tufa bazan ƙara ba”
Azabar zafin da taji ne yasa ta furta mata hakan donta ƙyale ta.

Sakinta Aneelerh ta yi don itama ta gaji da kokawar Sai haki ta ke yi, A nan ƙasa
suka zauna saman floor suna kallon juna.

“Ɗauko mun ruwa mai sanyi in sha” harara zahra ta ɗan jefa mata”Baki da hannu ne”?
Zaro ido Aneelerh ta yi tare da cewa”bugun da nayi maki bai ishe ki ba” Jin haka
yasa zahra yin saurin miƙewa hannunta ɗaya dafe da qugunta, Binta da kallo Aneelerh
tayi fuskarta ɗauke da murmushi fucewa tayi daga Cikin ɗakin, after some minutes ta
dawo hannunta ɗauke da glass ɗin ruwa me sanyi, ta miƙa ma Aneelerh hannu tasa ta
kar6a tare da kafa ruwan abakinta Kur6a uku tayi mashi ya ƙare, Janye shi tayi daga
bakinta tadan kalli zahra da ke tsaye tana gatsina mata hanci.

“Ki gama yi mini rashin kunyar ina nan ina jiran ki, in dai ni ce za ki zo roƙona
in faɗa maki ƙiyamil lailin da za ki yi don ki mallaki Zuciyar matashin saurayin
nan da ki ka ƙwallafa rai akan shi, meye ma sunan shi? tai tambayar tana kallon
Zahra, Dariya ta saki tare da kai hannu ta kar6i glass cup din hannun aneelerh,
Cikin kwarkwasa ta Juya ta nufi ƙofar fita daga ɗakin tana faɗin”Heart beat of
Obinna” Murmushi Aneelerh tasaki tare da cewa”Ehem shi nake nufi, zakiyi bayani ne”
bayan fitar zahra miƙewa Aneelerh ta yi tare da juyawa har ta kusa shiga toilet
Muryar zahra ta katse ta”Bafa tafiya nayi ba, taimakon nan dai da aka saba aunty
Aneelerh, “ Juyawa aneelerh ta yi tare da kallonta, Fuskarta ɗauke da murmushi.
Harara ta jefa mata”ƴar wahala wanka zan shiga idan na fito zamu tattauna” Zahra
tace”idan ma shekara za ki yi zan zauna in jira ki” ta6e mata baki Aneelerh ta yi a
yayin da ta ke shigewa cikin toilet taja ƙofa ta datse.

Daga gefen gadonta Zahra ta zauna tana jiran fitowarta, almost 15 mins Aneelerh ta
buɗe ƙofar toilet ta fito jikinta sanye da rigar wanka fara ƙyal, ganin yadda zahra
ta tsare ta da ido yasa ta murguɗa mata baki “Tubarkallah” Dariya Zahra ta sa ki
kafin ta tsagaita da yin dariyar tace”Masha Allah Iyayen mu sun Iya haihuwa”
girgiza kai Aneelerh ta ɗanyi”Allah ya shiryeki Zahra, Yanzu dai ta shi ki fuce zan
sanya sutura, Ki jira Ni a palour “ maƙe mata kafaɗa zarah tayi”Nifa ba ƙaramar
yarinya bace da zaki kore ni, Menene aciki don kin sanya kaya agabana, sai kace
wani gardin ƙato Nima fa macace kamar ke komai ki ke dashi ina da.....” Kafin ta
ƙarasa maganar Aneelerh ta nufeta da gudu Zarah ta bar Cikin ɗakin tana dariya.

Kaitsaye ta nufi Cikin Hadadden palourn gidan mai girman gaske. Tun kan ta ƙarasa
ta hango mami da ummi zaune saman sofa suna fira, kowaccen su na sanye da atampha
riga da zane ba ƙaramin kyau su ka yi ba.

“Gani nan tafe” kamar daga sama suka ji miryarta.

Atare suka ɗago suna kallonta, mami tace”yaushe kika dawo gidan”?

“Ban jima da shigowa ba, Na shiga ɗakin Aunty Aneelerh ne, Na same ta kwance Tana
bacci,” Tai maganar a yayin da ta ke zama saman sofa mai mazaunin mutun ɗaya.

“Nasan kin kwaso gajiya, Tun asuba sai yanzu aka kammala aikin decoration ɗin, Kin
ci abinci kuwa”? cikin Kulawa mami ta yi mata maganar, Fuskarta ɗauke da murmushi
tace”mun aikatu Mami, Uban aiki kamar zamu shekara muna Yi, kinsan hidima idan
akace maki ta Hamshaƙan attajiran masu kuɗine komai dagaske ake yin shi basu
ƙaramar harka, Mami zanso Kije Gidan nan zaki sha mamaki wlh, Haɗaɗɗiyar Daular
arziƙi ce....” tun kan Zahra ta rufe baki Ummi tace”Ae Obie estate Aljannar Duniya
ce Mai zaman kanta, Idan fa ki ka shiga gidan Sai ki rasa gane Awace ƙasa kike,
tsabar kayan alatun da ke a cikinsa, Yasin in mutun mai ƙaramin Imani na rayuwa
acikin tuni zai daina Sallah.....” Dariya mami ta saki Yayin da take sauraron su,
daga uwar har ɗiyar gwanaye ne wurin Iya bada Labari.

“Aunty duk yadda zan kwatanta maki Haɗuwar Kayan alatun dake acikin Estate ɗinsu Ba
zaki Fahimta ba, Gani da ido yafi abaka Labari, Obinna family duniyace mai zaman
Kanta, Ranar dana ta6a zura ƙafa ta cikin gidan wlh Sai da gabana ya faɗi, nace
Anya ko Mutane suna tunanin duniya? Yo abu kamar baza a mutu ba, wannan ae sai
mutun ya manta cewa da tur6aya aka halicce shi” Dariya sosai Mami ta ke yi tana
kallon Aunty Ummi da ke kora mata jawabi, Zahra ta ɗaura da cewa”Ni wlh Naso Daddy
ya sama mun Ko aikatau ne agidan su, tun ranar da naji Salary din masu aikin gidan
da dollar ake biyan su, Ci da sha da suturarsu duka A kyauta ake yi masu, ai duk
wanda Ya haɗa alaƙa Da ɗan familyn Obinna kakar shi ta yanke saƙa, Shi da talauci
sun raba Jaha....” in serious matter za’a ta ke magana, Ummi taci gaba da
cewa”Shiyasa naso mahaifin ki ya kutsa ki cikin danginsu tun da dama ɗan bangar
siyasa ne, Ni ko wannan Yaron ne *DR JAZZ* kisamu ki aure shi, ko mun samu muma mu
dangawali arziƙi” ta ƙarasa maganar tana dariya, tur6une fuska zahra tayi Jin
abunda Ummi tace”haba ummi, dr Jazz fa meye haka, Ni da na ke harin bugun zuciyar
Family ɗin gaba ɗaya, Taya zaki haɗa ni da yaron da har yau ba’asan waye ubanshi ba
acikin family ɗin” da mamaki akan fuskar Mami tace”kamar ya ba’asan Ubanshi ba”?
Zahra tace”ɗaya daga Cikin ma’aikatan gidan su ce tazo dashi aikatau, Matar ma
farar fata ce, ba ki ga yaron ba kyakkyawa ga son mutane, ni bazan Iya auran mara
asali ba, Ta ya Ummi zatai min fatan auranshi? Ga gwarazan samari a family din
kyawawan gaske masu kama da kakansu Obinna....” tana magana tana turo baki.

Ummi tace”Saboda nasan baza ki Iya samun wanda kike so ba, Haukan banza ki ke yi a
kan shi, ke kin sani Ruwa ba sa’an kwando bane, Babban Goro sai magogin ƙarfe,
Wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, In banda haɗama irin ta zahra taya zaki nace wa
mutumin da yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba? Shiyasa nace ƙwara Dr Jazz ɗin shine dai
dai da ke,” ɗaure fuska Zahra tayi jin abunda Umminta take faɗi, ta haɗe rai sosai,
Muryarta a ƙule tace”Mami kinga ni ko? Ita fa mahaifiyata ce amma bata min fatan
naci ka burina, Kullum sai dai tayi discouraging ɗina, meyasa ta ke yi min haka
ne”? a bun ka ga me saurin kuka tuni idonta sun ciko tab da ƙwalla.

Fuskar mami ɗauke da matashin murmushi ta soma magana a tsanake”kwantar da hankalin


ki zahra, Ai duk kyan takalmi ƙafa ce ke taka shi, kuma idan Allah ya ƙaddara cewa
shi Yaron wanda kikeso Mijin ki ne duk min muƙamin shi duk mun izzar shi da kyanshi
wlh da kanshi zai nemo ki a duk inda ki ke, Ai shi so bashi a matsayin mutun, mai
kuɗi ko talaka Zahra kuma ta haɗa komai da duk wani ɗa namiji zaiso zama da ita a
matsayin matarshi,...” Tunda mamin Aneelerh ta soma magana zahra ta washe baki tana
zabga uban murmushi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, Tsabar murna
batasan sa’adda ta sauko daga saman sofa ɗin da ta ke zaune ba, ta dawo ƙasa saman
carpet, Ta kafe mami ido tana kallonta kamar wadda ta samu Tashar Bolly wood, Hakan
ba ƙaramin dariya yaso ba Ummi ba, Ganin yadda zarah ta ke sakin murmushi jin ana
yabanta.

“Mami ni ba ina kushe Zahra bane, Just bana so ta ƙwallafa rai akan abunda ita
kanta tasan bazata ta6a mallakarshi ba, Yakamata ta runƙa tuna matsayinta,
Mahaifinta fa ɗan bangar siyasa ne ba wani shege ba, Ta ya ya ta ke tunanin zata
Mallakin Hamshaƙin mutun kamar *OWAIS SHARAFUDEEN OBINNA*!? Bazan iya lissafi ma
matan da su ka yi hauka akanshi ba, Daga cikin hada Ɗiyar Chancellor na ƙasar
Germany bayan ita akwai Ƴar sarkin saudi arab, Ga ɗiyar shugaban ƙasar
America.....” Lamarin ya ɗaure wa mami kai, Baki asake ta ke kallon Ummi sai da ta
kai ƙarshen maganar tukunna tace”Ni ko zanso In ga wanene wannan Namijin hurul
ainin, Farin Jini sai kace ɗan gwal yo wannan koda lu’u lu’u aka ƙera fatar Jikin
shi sai haka,” Dariya su ka saki gaba ɗayan su.

“Saboda Farin Jinin da Allah ya yi mashi kakan shi Ya toshe duk wata ƙofa da za’a
Iya ganin shi, Zaiyi wuya ki samu hoton shi a social media, shahararre ne sosai
babu inda ba asan shi ba, Da zarar kin ambaci sunan shi awuri sai an girgiza” Ummi
ce ta kora mata jawabi, Al’ajabi Ya kama Mami”Na ƙosa Inji tarihin Family ɗinsu,
Najima Ina jin zancensu abakin mutune da kuma labaransu a gidan radio, Nasan
fuskokin Ya’yanshi a tv sai dai bansan Komai dangane da su ba”

Gyara zama Ummi ta yi”Jinin Nasara shi ne sunan da akeyiwa family ɗinsu laƙabi da
shi saboda wadatar Arziƙin da Allah yayi masu, Suna ɗaya daga cikin Most richest
family in the world, shahararru ne na bugawa A jarida, shi Obinna da ki ka ji ana
faɗi Kakan su ne tsohon ɗan siyasa ne wanda yai gwagwarmaya ya ruƙe muƙamai da dama
tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje, Allah ya yi su da farin Jini, matan
shi biyu a yadda naji labari, amma dukansu basa araye yanzu, shi kaɗai ne ya rage,
ƴa’ƴan shi bakwai kaf ɗinsu suna ruƙe da manyan muƙamai, su ke ruƙe da ƙasar nan,
Manyan ƴa’ƴan shi ƴan Uku ne sune first born ɗin shi” numsafawa Ummi tayi kafin ta
soma zayyana mata sunayen su kamar haka.

“SENATE PRESIDENT LATEEF OBINNA, bayan shi akwai CHIEF OF ARMY STAFF SIR MUBARAK
OBINNA, cikon Na ukun su shine HIS EXCELLENCY ABDUL RAZAK Obinna Gomnan Jihar
Lagos, waɗannan sune yan ukun shi, bayan su akwai ƙannan su maza HIS EXCELLENCY
DEEN OBINNA Gomnan Jihar kaduna state, mai bi mashi PRIME MINISTER HATEEM OBINNA
Shugaban ƙasar Canada Shi ne ya ke auran Gimbiya mujeedat ƴar Sarkin Dubai.....”
Tun da Ummi ta soma bata labarin Mami ta baza kunne tana sauraronta, ga dukkan
alamu al’ajabi ya kamata duba da yadda ta saki baki tana kallonta

“Bayan Hateem sai mai bi mashi SHARAFUDEEN OBINNA Current president na ƙasar
Nigeria, Adalin shugaba hawan shi mulki da wata biyar kacal ba a ƙara jin ɗuriyar
Ƴan ta’adda ba” Fuskarta ɗauke da murmushi ta yi maganar”Kada ki ji Ina yabon shi
ya cancanta ne, matan shi biyu Uwar gidan shi ɗiyar Sarkin Yarbawan Jihar lagos ce,
Ta biyun kuma ƴar gidan Alhaji wada ce, Ƙanwar former Gomna na Jiharku Jos”
Murmusawa mami ta yi fuskarta da alamun mamaki tace”Wai Alhaji Ubaid ki ke nufi
surukin tajudden? Dama ƙanwarshi ke auran Sharafuddeen”? Dariya ummi tayi”haba dai
kada ki ce min ba ki da masaniya,” watsa hannu mami tayi”taya za’ae in sani? Ni da
ba shisshige masu na ke yi ba, In banda ma abun ki ae bani da alaƙa dasu da ya wuce
ƙawancen Benazir da Aneelerh, Makaranta ce ta haɗa kuma Yanzu sun rabu, amma duk da
haka Na yi mamaki,”

Ummi tace”Auran su shekara goma sha ɗaya kenan A lissafi na, kada ki yi tunanin ina
sanya masu ido ne, Kinsan in mutun nada Arziƙi da ɗaukaka a kyauta ake bin diddigin
shi....” ta ƙarasa maganar tana dariya Mamin ma dariyar ta ke yi.

“Nasan zakiyi mamaki Idan na faɗa maki cewa Duk irin wadatar Arziƙin dake gare su
da ɗaukakarsu Basu da yawa family ɗinsu, Jikokin Obinna Goma sha Biyar” A ɗan ruɗe
mami tace”kai! Wai dagaske”? Jinjina kai mami tayi”ƙwarai kuwa, Saratu Obinna ce
kaɗai ta ke da ƴa’ƴa Uku, twins zaid da zain sai autarsu Faryat Obinna, Na manta ma
ban faɗa maki ita a jerin ƴa’ƴan shi ba, Saratu obinna Itace Autarsu, tana ruƙe da
muƙamin Minister of health Mijinta Pravin Obinna ɗan ƙasar india ne silar zuwanta
karatun likitanci india Allah ya haɗa ta dashi.....” Ummi bata ƙarasa maganar ba,
Zahra tai saurin cewa”Cin Arziƙi ya kawo shi, tsabar son banza mami ya canza sunan
ubanshi ya maidashi na Obinna, Sai ki rasa gane ɗa ne ko suruki a gidan” tun da
suka fara magana sai Yanzu ta tsoma masu baki hannunta ruƙe da wayarta da alama
chatting ta ke yi.

“To ke ina ruwanki zahra? Na rasa meya tsone maki ido da mutumin nan, ya fa riga
daya zama ɗan gida, yafi ƙarfin a kira shi da suruki sai da ɗa” Ta6e baki zahra
tai”Haba Ummi haka ake surukuntaka, mutun ya tare a gidan surukai don kawai yana
auran yar shi, nifa Pravin sam baya burgeni mutun kamar ɗan ta’adda” mami sai
kallonta take yi, ta fahinci bata ƙaunar mutumin.

Ummi na ƙoƙarin buɗe baki don ta yi magana Muryar Baby Junaid ta katse masu firar
tasu.

Mommy! I’m back! I really missed u, Na maki tsaraba” Gaba ɗaya suka ɗago suna
kallon shi, shigowar shi kenan Cikin Falon Jikin shi sanye da suit Na yara Black
colour, Madarar kyau, Ya ƙara girma ayanzu yana acikin shekara ta biyar a duniya.
hannun shi na aruƙe da Farar leda ta shopping, ba shi kaɗai ya shigo palourn ba,
Yana atare da Mahboob Ƙanin Zahra, Kamar su sak kamar tagwaye shi da ita, Crazy
Jeans ne a jikin shi, daga sama Ya sanya farar t shirt, Sumar kanshi kwance luf
tasha gyara, Miƙewa zahra tayi da gudu ta nufi baby junaid tana ware mashi hannu
don yazo ta rungume shi, tunkan ta ƙaraso ya girgiza mata kai Yana faɗin”Na mommy
ne wlh, Wayo kike so ki min dan In ɗan maki tsarabata” Dariya suka saki, Zahra
tace”matsalata dakai kenan, Komai Mommy mommy, idan da kara nima ai uwarka ce,
Zonan dallah” ta ambaci hakan tare da janyo shi zuwa jikinta.

Ummi tana murmushi tace”Kada ka yarda Junaid, Aunty zahra wayau zata maka don ka
ɗan mata tsarabarka, “ ɗaure fuska zahra tayi”Ummi kada kisa ya raina ni fa” Ummi
tace”ƙarya nayi ne? Yaro yayiwa babarsa tsaraba ke kuma Uwar wayau kina son cinye
mashi abu” gatsina mata hanci zahra tayi tare da Wuce Bedroom ɗin Aneeleh ɗauke da
Junaid a hannunta, Ya ɗaure mata fuska duk don kada tace zata Ci mashi tsarabar
shi.

“Sannu da dawowa,” Mami ce tayi maganar tana kallon mahboob dake zaune saman Sofa,
Fuskarshi ɗauke da murmushi Ya ce”Yawwa mami fatan na same ku lafiya,” Suka amsa
mashi da lafiyalou

“Har an kammala registration ɗin”? Ummi ce ta yi mashi maganar, ɗaga mata kai yai
alamar eh Saura zuwa school Ya rage mashi On monday zai fara zuwa, Uniform ɗinshi
suna acikin mota nabarsu, wlh nagaji Ummi yunwa nake ji kamar in ci ƴan hancin
Cikina” yai maganar Yana yamutsa fuska,

Ummi tace”nayi zaton Kun biya restaurant Cin abinci” ɗan zaro ido yai kafin
yace”Tab, Ga abinci agidanmu sai in kwasa in tafi restaurant cin abinci saboda
almubazzaranci, “ dariya mami ta saki, Mahboob Ya iya tattalin kuɗin shi, Ya tsani
almuzarranci arayuwarshi. Yasan ciwon kuɗin shi.

“Tsokanar ka na ke yi don nasan halinka, Da shegen maƙo, Fatana Allah yasa ba ka


bar mana yaro da yunwa ba” ta6e la66ansa yai”Tun da muka baro school ɗin ya fara
yi min kukan yunwa, don dole na tsaya a wata plaza na siya mashi snack, shine fa
daya ci ya rage saura nace ya bani inci yace mommyn shi zai ma tsaraba, ni da na
sayi abu da kuɗina amma ya hanani ci, Sauƙin ma wurin jatumarshi zanje ta biyani
ƴan canji na,” tuntsirewa Mami tayi da dariya, ita kanta Ummin murmushi ne akan
fuskarta, Lamarin mahboob sai addu’a, Babu mutunci indai akan kuɗine
“Kai yanzu saboda rashin ta ido, Sai ka je wurin Aneelerh ka ce ta biya kuɗin daka
siyama yaronta snacks? Ɗanka ne fa” Hura hanci yai tare da cewa”Kusan fa dubu ɗaya
na kashe mashi, haba ummi, kinsan fa yadda nake wahalar neman kuɗi, Daddy fa ko
sisi baya bani sai in yaga dama kema kuma haka” Baki asake Mami ke kallon shi Ummi
tace”indai mahboob ne kaɗan kika gani, ae baida mutunci indai akan kuɗin shi ne,
Mara Kunya tashi ka bamu wuri, kuɗinka kuma Ka zo da anjima ka kar6a ni zan biya
ka,” har ya yunƙura zai miƙewa, Idon shi ya sauka akan Ana mai aikinsu Aneelerh,
Fitowa tayi daga Kitchen hannunta ruƙe da tray an jera kayan breakfast ɗinsu,
hankalinta kwance take tafiya jikinta na sanye da Skirt pensil baƙi yabi shape din
Jikinta, Daga sama ta sanya Riga launin green, Ƙura mata ido yai yana kallonta,
Idon su mami akanshi ganin yadda yake binta da ido.

Tsawa Ummi ta daka mashi a firgice ya waiwayo yana kallonta, fuskarta a ɗaure
tace”Uban me kake kallo”? Yamutsa fuska yai”Kayan abincin dake a hannunta nake
kallo ba wani abu ba,” yai maganar tare da wuce ya nufi dining table ɗin, da Ana
take jera masu kayan breakfast, Kujera yaja ya zauna Yana faɗin”Ya ki ke”? Murmushi
ta sakar mashi”lafiyalou, na gan ka ɗazu da safe zaku fita da baby junaid” 6ata
fuska yai”shine baki min magana ba mun gaisa”?

Hankalinsu mami gaba ɗaya akanshi, Ummi tace”Oh Ni ƴar ubansu, Yaro ya zama mayen
mata, In banda haɗama irinta Mahboob ina zai kai Ana”? Mami tace”tashen balaga ne
kawai, nan da wani lokaci zai dawo hayyacin shi,” dariya suka saki, Kafin suka miƙe
zuwa Dining ɗin domin suyi breakfast..

Lokacin da Zahra ta shigo ɗakin Aneelerh ɗauke da baby junaid, A zaune ta same ta
gefen gado hannunta ruƙe da hoton su, wanda su ka yi aranar birthday ɗin Angel, tun
da ta fito daga wanka, ta shirya kanta Cikin riga da skirt, kanta na ɗaure da
mayafi, jin motsin shigowar Zahra yasa tayi saurin ɗaura hoton hannunta saman
drawer, idanuwanta acike suke tab da ƙwalla.

“Aunty Aneelerh Ga Baby Junaid ɗinmu Ya dawo” cikin sanyin murya zahra tayi maganar
don ta fahimci yanayin da Aneelerh take aciki, taƙi ɗagowa su haɗa ido, saboda ba
ta san zahra taga hawayenta.

Sauke Junaid ta yi ƙasa, da gudu ya nufi Aneelerh ya haye saman Jikinta hannun shi
ruƙe da ledar tsarabarta”Mommy ba ki yi missing ɗina ba”? a hankali ta ɗago ta
kalle shi, wani irin farin ciki ya ratsa zuciyarta, duk halin da zata shiga idan
tayi tozali da fuskarshi sai ta ji sanyi aranta, Ɗaukarshi tayi tare da ɗaura shi
saman laps ɗinta sosai ta rungume abunta”Momy ga tsaraba ki ci” Zahra na atsaye
tana kallon fuskar Aneelerh, tsananin tausayinta ta ke ji.

“Thank U my baby Boy, Nayi kewarka kamar zan zauce, Ya school ɗin? Surutu ya soma
yi mata yana zayyana mata kyawun makarantarsu, yana magana ya buɗe ledar tsabar ya
curo guntun donut daya ajiye mata abaki Ya tura mata, taunar shi ta soma yi tana
murmushi, daga gefen su Zahra ta zauna still idonta akan fuskar Aneelerh, Sai
kakkauce mata take yi duk don kada su haɗa ido

“Mommy uniform ɗina suna acikin motar bro, hada sandals ɗina, kuma ya ce in faɗa
maki ba zai ƙara kaini school ba saboda fetur tsada yake yi, wai sai dai ke kina
kai ni” dariya Aneelerh tasaki jin abunda yace”kwantar da hankalin ka, nima ai ina
da mota, kuma zan fara zuwa aiki, Kamar yadda nake ɗawainiyar kai Angel makaranta
lokacin da tana araye, inje in ɗauko ta kaima haka zan dinga yi maka....” zahra ce
ta katse ta da cewa”nima ina da mota, kuma ashirye nake da in dinga ɗawainiyar
kaishi,” sai da tayi wannan maganar Aneelerh ta ɗago tare da kallonta, Hawayen da
take 6oye mata ne suke soma gangarowa saman kuncinta.

“Haba Aunty Aneeleeh i know it’s hard to let go of the past, but worrying about it
won’t change anything wlh bamu jin daɗi idan muna ganinki cikin damuwa” zahra na
rufe baki Baby junaid yace”sai da na mata faɗa ta daina kuka, ta ƙi jin maganana,
mommy bata jin magana zanje na faɗa wa mami kina kuka” yai maganar yana ƙoƙarin
sauka daga saman jikinta da sauri ta ƙanƙame shi”na daina babyna, tun da baka so,
ba sai ka faɗa ma mami ba kaji ko” amsa mata yai da toh amma idan ki ka ƙara saina
faɗa mata” murmushi Aneelerh ta saki idonta akan zahra dake kallonta.

“Idan ina kallon hotunansu ina tuna irin rayuwar farin cikin da mu ka yi, Shiyasa
ni ke zubda hawaye na, Allah na gani bazan Iya mantawa dasu acikin rayuwata ba,
waɗannan mutanan uku masu mahimmanci sun kafa tarihi acikin zuciyata, nayi imanin
har in koma ga mahaliccina bazan ta6a samun wanda zai maye min gurbinsu ba, Nafi
damuwa da Angel wlh ina son yarinyar nan naji takaicin rashinta naso ace sun rayu
tare da ɗan uwanta junaid, Angel abun tausayice ta rayu ba tare da mahaifiyarta ba,
Na rasa wata irin zuciya ce a ƙirjin benazir......” sosai Aneelerh ta fashe da
kuka, Jikin zahra duk yai sanyi, zagayo da hannunta tayi saman bayan Aneelerh ta
kwanto da kanta saman kafaɗarta”I feel ur pain Aunty Aneelerh, da inada halin da
zan iya yaye maki damuwarki da nayi sai dai babu, abu ɗayane nayi maki alƙawari zan
tayaki addu’a, ni a tunanina bai kamata ace anyi shiru da maganar nan ba, idan har
ba a yaɗa labarinsu taya za’asan in suna araye? Yakamata atada zancen labarin
6acewarsu a social media, inaso labarin ya zama sabo tamkar a yau ya faru in dai
har mu ka yi hakan in sha Allah indai suna araye zasu bayyana ne.......” tunda
zahra ta soma magana Aneelerh ta natsu tana sauraronta, ga dukkan alamu ta gamsu da
zancenta

Da sauri ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar zahra muryarta adisashe tace”Zahra
kina ganin idan muka yi hakan za’a dace” fuskar zahra ɗauke da murmushi tace ƙwarai
kuwa in sha Allah zamuyi nasara, Kibar komai a hannuna Idan Daddy ya dawo zamu yi
magana dashi, tunda kinga shi mutunne na jama’a zai tsara mana yadda za’a watsa
labarin 6acewarsu, so nake duniya ta ɗauka,” lumshe ido Aneelerh tayi har cikin
ranta take jin ƙwarin gwiwa.

“Samu Ƴar uwa kamarki zaiyi wuya Zahra, shiyasa nakeson ki ina matuƙar ƙaunarki, ke
ta dabance kina da kaifin basira, Ni ban ta6a tunanin tada zancen 6acewarsu
tajuddeen ba sai da ki ka bani shawara, Allah ya Biya maki buƙatunki na alkhairi”

“Ameen auntyna, ko dan saboda farin Cikin ki zanyi ƙoƙari inga an watsa labaransu
tare da hotunansu, “farin ciki ya cika Aneelerh, sosai ta rungume zahra, Baby
Junaid yayi lamo saman ƙirjinta, sai faman lumshe ido ya ke yi bacci ne ke shirin
ɗaukarshi

“Excuse ma’am” muryar Ana ce ta katse su, atare suka ɗago suna kallonta, tana daga
tsaye bakin ƙofar ɗakin, a mutunce suka gaisa kafin ta sanar dasu cewa Breakfast
yana jiransu a dining’ amsa mata su ka yi da toh, kusan atare suka miƙe, Aneeleh na
ɗauke da babyn junaid”
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E6🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

*JUSTICE DEMOCRATIC PARTY*

(JDP HQ)

Manyan mutanene dattawa da matasa zazzaune a babban ɗakin taro na jam’iyyar Justice
democratic party ɗaya daga cikin jam’iyun da su ka shara a ƙasar Nigeria,
zungureran table ne wanda ke kewaye da kujeru, daga saman teburin akwai microphones
na kowani member da zai yi magana, An tanadi kayan sha jere saman table, ɗakin
taron yai tsit babu mai magana a cikin su, fitinannan ƙamshin turaren jikinsu ya
gauraya da sanyin A.c na comference room ɗin da su ke a ciki.

Tsabar 6acin rai ne da fusata akan fuskokin su ga dukkan alamu suna fuskantar
tashin hankali a jam’iyarsu, musamman party leader ɗin su Alhaji bukar mai guduma
fuskarshi a murtuke ta ke babu annuri, baƙin shi ya nunku har shining ya ke yi, Ya
dunƙule tafin hannayensa da ya ɗaura su saman table din, Kowannan su ya ɗauki
wankar tsadaddiya shadda daga gani naira ta zauna masu, kuma gogaggun ƴan siyasa ne
waɗanda su ka jima a harkar suna gwagwarmaya, tsawon mintuna goma shabiyar, kafin
shugaban jam’iyar mai guduma ya sassauta fusatar fuskarshi idanuwanshi jawur ya
ɗago yana kallon mambobin su, tun daga jerin waɗanda ke a 6angaren damansa, Alhaji
ubaid wadata Alhaji musa wadata former president, Alhaji badamasi da sauran ƴa’ƴan
jam’iya, A hankali ya ɗauke idanuwan shi daga ta 6angaren dama ya mayar dasu kan
mambobin dake zaune 6angaren hagunsa, Jinjina kansa ya ɗanyi yayin da ya ke fitar
da huci ya soma magana tamkar mayunwacin zaki”Me ke shirin faruwane da jam’iyar mu?
Zamu zauna ne mu zuba ido kamar mazurai muna kallon su? Mun ɗaura shugaban ƙasa
dudu 4 yrs ya faɗi aza6e, mun kuma tsayar da sabon ɗan takararmu ubaid wadata an
kayar dashi aza6e, Ga dukkan alamu durƙushewar jam’iyarmu ce tazo, tayaya jam’iyar
da bata fi shekara biyar da kafuwa ba zata nemi ruguza tarihin tamu party din? A
zafafe ya kai ƙarshen maganar yana kallon kowan nan su, babu wanda yai yunƙurin
tanka mashi saboda sunsan halin shi idan ranshi ya 6aci, wani irin bauɗaɗɗan
mutunne,

Jinjina kan shi yai yayin da ya ke fitar da huci duk irin sanyin A.c da ke shawagi
a ɗakin hakan bai hanashi fitar da gumi ba.

“Babu irin tarihin da jam’iyar mu bata kafa fa, Ina ce shi kanshi dattijon arziƙin
rainon jamiyar jdp ce, daga baya ne ya sauya ra’ayin shi akan wata manufa tashi ta
daban wadda ba mu da masaniya akanta ya kafa tashi jam’iyar mai taken Progressive
action party (PAP) Yan zu ga shi cikin ƙanƙanin lokaci sun ƙwace ƙarfin ikon da mu
ke da shi a ƙasar nan, tsabar haɗama gaba ɗaya ƴa’ƴan shi ke juya ƙasar nan idan
har bamu ta6uka wani abu ba zamu tashi a tutar babu ne”! Ya ƙarasa maganar tare da
kai hannu Ya daki table din gaban shi, kowa yasha jinin jikin shi, damuwace ƙarara
akan fuskokin su.

Gyaran murya Alhaji Ubaid wadata yai kafin atsanake ya soma magana cikin dattako

“Allah ya huci zuciyar mai girma jagoran mu, Ni anawa ganin yakamata mu fito da
dabarun da za mu bi don ganin mun dawo da ƙarfin ikon da mu ke da shi ada, idan ma
ta kama mu bi tsarin da su ka ɗauko wanda yasa jama’a suke rububin tasu jam’iyar,
Idan har muna so mu farfaɗo da tamu jam’iyar” bayan Alhaji ubaid yai magana sauran
Ƴan jam’iyar kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, Idan ka cire mutun ɗaya wanda tun
da ya zauna meeting ɗin idanuwanshi su ke a lumshe daga gani yana da jiji da kai da
izza, ɗakin taron ya rikice da zafafan zantuttukan su kowa yana faɗin ta cikinsa,
rai amatuƙar amace Ya sanya hannu ya daki table ɗin gabanshi wanda silar hakan ya
janyo hankulansu ga dubanshi, Ƙaraminsu babbansu slowly ya buɗe idanuwanshi akan
faces ɗin su, sun kasa kunne suna jiran jin me zaice hatta shugaban jam’iyar tasu
ya natsu yana jiran jin bayani daga gare shi.

Cikin harshen turanshi Ya soma magana da kakkausar murya”Let’s take a step back and
focus on what we need to do right now. We need to come up with a strategy for the
next election, We need to come up with a plan to fight back. We need to show the
people that we are the party that can make a difference in their lives. We need to
show them that we are the party that cares about their needs. We need to show them
that we are the party that will fight for them, And We need to let them know that
we are the party that is on their side.” tun da Alhaji musa wadata ya soma magana
ƴa’ƴan jam’iyar su ke jinjina kansu ga dukkan alamu ya ɗauko magana mai ma’ana a
ƙarshe ya daki table din gabanshi ya furta”Sharafudden obinna ba zai haura 4 years
a mulki ba! Alƙawarine na ɗaukar wa kaina, duk yadda za’ae sai mun kayar dashi a
za6e na gaba, dole jam’iyar mu ce asama babu wani mahaluƙi da ya isa ya durƙusar da
jam’iyar mu, abokan hammaya ba za su ta6a cin galaba akan mu ba,” yana kai ƙarshen
maganar azafafe ya yunƙura ya miƙe yana gyara malunmalun ɗin jikin shi, Ko sallama
baiyi masu ba, Ya haura ƙafa yabar cikin ɗakin taron, yayin da su ke bin bayanshi
da ido, har saida ya 6ace ma ganinsu tukunna suka dawo da dubansu kan maiguduma.
tattaunarwar tasu ta ɗauki tsawon awa ɗaya kafin suka rufe taron da addu’a da kuma
fatan nasara ga jam’iyarsu, Ɗaya bayan ɗaya suke fitowa harabar headquater inda
jerin danƙara danƙaran motocinsu suke a killace. Bayan sun ƙara gaisawa da juna
kowa Ya nufi motarshi, Musa wadata Yana kishingiɗe a back seat na danƙareriyar
motarshi tsadaddar gaske, Ya lumshe idanuwanshi sanyin A.c ta ko’ina, gefen shi P.A
dinsa ne, security ɗin da ke jigilar tuƙa su yana zaune a driver seat yana jiran
jin umarninsa.

Ƙwanƙwasa glass ɗin motar da akayi ne yasa shi ware manyan idanuwanshi, muryar
Alhaji ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi”Ina son magana da kai” Iya abunda ya furta
mashi kenan, Muryarshi da izza ya amsa mashi da toh, daga haka yaba drivern nashi
iznin ya tada motar su nufi gida” A jere motocin su su ka nufi gate ɗin fita daga
cikin headquater ɗin su...

*JOS CITY*

Zaune ya ke saman darduma cikin shigar larabawa farare ƙal, kyakkyawan balarabe
daga ganin fuskarshi ba ƙaramin mutun bane ya ɗan fara manyanta, Arab turban ɗin da
ke nannaɗe akanshi, ya ƙara mashi kyau ga wani kwantaccen saje baƙi wulik mai
matuƙar jan hankali, lallausar sumar kanshi ta sauko har saman wuyanshi dark black.

Daddaɗan ƙamshin turararen jikin shi mai matuƙar sanyaya zuciyar mai shaƙar shi,
idanuwan shi suna a lumshe yayin da ya ke yin qira’ar Alqur’ani mai girma, Yatsun
hannunshi na dama na a asargafe da cazbaha, Qur’anin da ya ke karantawa yana
agabanshi saman wooden qur’anic stand dogayen eye lashes ɗinsa a jiƙe su ke sharkaf
da hawaye ga dukkan alamu ayar da ya ke karantawa ce ta sanya shi tsuma.

Sam bai ji takun tafiyar mutun acikin ɗakin shi ba, tafi ƙarfin mintuna talatin da
shigowa, idanuwanta akanshi ganin bai da niyar tsagaita karatun ƙur’anin nashi ne
yasa ta ambaci sunan shi

*”DR SHUREIM*”Nasan kana jin takun tafiyata don haka idan ka kai ƙarshen Aya ina
son magana da kai”! tamkar ta yi magana da bango ko kallo bata ishe shi ba, sai ma
ƙara sautin muryashi da ya yi” dogon tsoki taja tare da zuwa gaban dardumar ta shi
ta kai hannu ta rufe qur’anin da ya ke karantawa, a tsiyace ta ƙwace cazbagar dake
nannaɗe a hannun shi ta ɗaura ta saman qur’anin, don ta fahinci da gayya ya ke yin
karatun duk don kada ya saurari maganarta.

Tana huci ta ɗago tana kallon shi still bai buɗe idanuwanshi ba, kuma bai dakata da
yin karatun ƙur’anin ba domin kuwa haddace akanshi

“Ka da ka bari raina ya 6aci wlh zan yi maka abunda baka tsammani, na rasa uban me
na yi ma ka daka ɗaura mun karan tsana sai ka ce ba uwarka ba! Ko kana da wadda
tafi ni ne a duniyar nan”? Ta jefa mashi tambayar, Shiru bai ce uffan ba, gyaɗa kai
tayi”ilmin addinin na ka ya tashi abanza tunda ba ka san ka girmama iyayen ka ba,
tsawon shekara da shekaru kana nuna wariya tsakanina da mahaifinka laifin me namaka
Shureim”? Cikin jin ƙunar rai ta yi maganar, A hankali ya buɗe idanuwanshi farare
ƙyal da su ya ɗaura su akan fuskar Mahaifiyar tashi, ba kowa ba ce fa ce Layla
mahaifiyar Benazir, Doctor shureim shine babban ɗansu, Ya ya ne awurin Benazir
mahaifiyar Angel.

Daddaɗar muryar shi ce ta ratsa kunnuwanta”ba ki min laifin komai ba, har yanzu
kina nan a matsayinki na mahaifiyata, kawai bana buƙatar kusancin ki da ni”
Zagayawa ta yi zuwa gefen gadon shi ta zauna suna fuskantar Juna”Nasan dalilin
dayasa ka ke yin fushi dani, haba shureim tsawon shekaru nawa why za ka ruƙe abu
aranka yai ta damun ka? Yakamata mu manta da abunda ya wuce, kuskure ne an riga da
an ta6ka, kuma in sha Allahu hakan bazata ƙara faru wa ba” fuskarshi a ɗaure ta ke
babu walwala” tayi tsammanin zai tanka mata sai ji ta yi ya yi shiru bai ƙara
magana ba.

Ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, zuciyarta na ƙuna tace”na lura sam
faɗuwar mahaifinka bata dame ka ba, An ya kuwa shureim kana ƙaunar mu a matsayin mu
na iyayenka? Cos na fahimci baka son cigaban mu” murmushin takaici dr shureim ya
saki, da ido tabi shi da kallo ganin yana dariya har fararen haƙoran sa su ka
bayyana masu kyau da tsari.

“Mahaukaciya ka mai da ni? ina magana kana dariya” fuskarta a ɗaure tayi maganar,
Yunƙurawa yai tare da mikewa Ya fuskance ta kafin ya soma magana”Saboda ku ba iyaye
bane daya kamata a nuna damuwa akan ku! Daga ke har shi bakusan ciwon kan ku ba,
Gaba ɗaya hankalin ku na akan son abun duniya damuwar ku akan cigaban ku ne ba akan
mu ba! Ta ya ya zan damu don mahaifina ya faɗi a za6e? Aini abun farin cikine agare
ni, don na fahimci siyasarshi tafi komai mahimmanci awurinku! Saboda rashin sanin
ciwon ƴa’ƴa Yau tsawon shekara goma sha shidda Benazir bata a tare da ku, hankalin
ku a kwance ba ku iya ta6u ka komai ba, duniya kawai kuka sa agaba, Wlh na jima ina
danasanin kasancewar ku Iyayen mu! Na yi fatan ace mutun yana iya canza iyaye da
tuni na yi hakan, Nifa ba ku da amfani acikin rayuwata! Kun riga da kun yi min
abunda har abada zuciyata bazata ta6a mantawa da shi ba, kune silar duk wata masifa
dana tsinci kaina aciki.......” daƙyar ya ƙarasa maganar cikin jin ƙunar rai, a bun
ka ga farin mutun tuni fuskarshi ta canza launi zuwa ja, numfashi yaja muryarshi
adisashe yace”kun manta cewa ƴa ƴa amana ne agare ku? Ranar gobe ƙiyama Allah zai
tambaye ku game da amanar da ya ba ku, Rashin nasara yanzu ku ka fara gani, in sha
Allah ba zaku ta6a samun abunda ku ke so ba, har tsayuwar dare zanyi maku akan kada
Allah ya cika maku burinku na mallakar kujerar.....” bai ƙarasa maganar ba
sakamakon zazzafan marin da Layla ta sakar mashi, da sauri ya dafe kuncinsa da
tafin hannun shi na dama, Idanuwanshi sun rune zuwa ja.

Tana hu ci ta nuna shi da yatsa”don uban ka ka tattara kayan ka kabar gidan nan
tunkafin ranka ya 6aci, shashasha kawai wanda baisan ciwon kanshi ba,” Cikin sanyin
murya yace”zan tafi koda ace baki kore ni ba Mommy, dama ita gaskiya ɗaci gare ta,
kuma in sha Allah zanje na nemo ƴar uwata benazir aduk inda take, idan ku bakusan
ciwon kanta ba ni na sani....” tunkan ya kai ƙarshen maganar layla ta nufi ƙofar
fita ɗaki kamar zata tashi sama tsabar 6acin rai.

Zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa idanuwansa jawur hawaye na cigaba da gangarowa saman
kuncinsa, haƙiƙa mahaifiyarshi ta fama mashi mikin dake acikin zuciyarshi, matsawa
yai gaban gadon shi ya miƙa hannu ya ɗauki wayarshi yana duban hoton da ke a kan
wallpaper na wayarshi, lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su sosai akan
hoton da yake kallo, baya gajiya da kallon fuskarta A hankali ya furta

_ke ce silar tarwatsewar farin cikina kuma kece silar shiriyata! Ki yafe min nayi
kuskuren da bazan ta6a gyara shi ba, ina son ki sosai ina jin ki har cikin raina,
nasan haƙƙin ki ne ya ke bibiyar rayuwata_

kifa kansa yai saman mattress sosai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin
yaro.

Bayan fitar Layla kaitsaye ta nufi falon gidan, ranta ya 6aci sosai, kalaman Dr
shureim sun sosa mata zuciyarta, yau kusan shekara uku da dawowarsu Nigeria tun
bayan barin su Dubai, Layla taji takaicin faɗuwar Alhaji ubaid saboda tafi kowa
ƙwallafa rai akan hawan shi mulkin shugaban ƙasa don ta ji daɗin yin sharholiyarta
a matsayin first lady, sai dai Allah bai basu nasara ba, bugu ɗaya aka ƙundumo shi
ƙasa, tun farko sai da ya ji fargabar tsayawa takarar jin wanda za su kara da shi,
don kuwa yasan muddin Sharafudden Ya nemi takarar shugaban ƙasa zaiyi wuya ya iya
kada shi, sanin farin jinin da Allah ya yi mashi, Mutun ne na jama’a mai kyautatawa
al’umma.

“Hajiya..”muryar mai aikin gidan su ce a dabarbarce ta ambaci sunanta ganin yadda


ta bi ta da matsiyacin kallo”lafiya”?

Cikin harshen larabci ta ce “Mun yi baƙi ko da ya ke sun wuce baƙi”

“Saboda ƙannan uwata ne”? Ta jefa mata tambayar, Sunnar da kai ƙasa zainab ta ɗan
yi”Hajiya Aisha ce matar governor tare da....” bata kai ga ƙarasa maganar ba, layla
ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu”ni ban gayyaci uban kowa ba a gidana,
Matsiyatan banza gulmace ta kawo su wato an zo aga yadda na ƙare to ta Allah ba ta
su ba ƴan kutmar uba, jajen ne har yanzu bai ƙara ba abu an kusa rabin shekara da
faruwarshi saboda baƙin hali sunƙi su manta..” tun da ta fara sambatu zainab ta yi
kasaƙe tana kallon fuskarta ba ki asake, ta fahimci zallar baƙin ciki ne Azuciyar
uwar gidan ta ta, rashin nasarar su ya tsaya mata a zuciya nema ta ke ta zauce,
dama ya lafiyar gwiwa mutun mai ƙarancin imani.

Tsawa layla ta daka mata, firgigit! zainab ta ɗan zabura”Ki je ki sanar da su cewa
bana nan” muryarta na ɗan rawa tace”Ae an riga an faɗa masu cewa kina a cikin
gidan, yanzu haka anyi masu iso suna acikin main palour...” daƙyar zainab ta ƙarasa
maganar tana mai haɗiyar yawu ganin irin kallon da layla ta ke jefa mata tamkar
ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa, guntun tsoki taja”masu aikin gidana sun fara raina ni
saboda rashin nasarar mu dole na yi wani abu akai, su kuma waɗancan taron
magulmatan zanje gare su, bari na fara zuwa ɗaki in zuba gwalagwalai na don kar su
raina ni” acikin zuciyarta ta yi maganar tare da juyawa ta nufi sashen da ɗakinta
Ya ke.

Binta da ido zainab ta yi haɗi da ɗan girgiza kanta”Allah ya shirye ki layla” har
zata Juya idon ta ya sauka akan Dr shureim da ke shirin fitowa daga ɗakin shi
hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, tsananin tausayin shi ne ya kamata ganin yadda
ya canza, ta lura da damuwar da ke akan fuskarshi, a hankali yake tafiya yana
tunkaro inda take ga dukkan alamu bai lura da ita ba har sai da ɗan yi mashi gyaran
murya, tukunna ya ɗaura fararen idanuwanshi akanta, Sam babu walwala akan
fuskarshi, darajar da ta ke da shi a idon shi yasa shi nufarta, ya ɗauki zainab
taimkar auntynsa, Babbar macace mai hankali da natsuwa.

Yana ƙarasa gabanta ya duƙar da idon shi ƙasa ba tare da ya gaishe da ita ba

“Ko ba ka faɗamin ba dr shureim naga damuwa akan fuskarka, na ɗauke ka tamkar ɗan
ciki na, dan Allah shureim ka da ka bari damuwa ta canza ka, inaso ka sani komai ya
faru muƙaddari ne daga Allah, rubutacciyar ƙaddara ce wadda ba wanda ya isa ya
canza ta” cikin kwantar da murya ta ke lallashinsa, sai faman karkaɗa car key ɗin
hannunsa yake yi, tun da ta fara yi mashi nasiha bai tanka mata ba sai da ta kai
aya tukunna ya soma magana a tsanake “Aunty zainab na aikata babban zunubin da har
abada ni nasan Allah ba zai ta6a yafe min ba, Ni kaina nayi danasin mara
amfani....” duk yadda yaso ya jure ya kasa kamar ƙaramin yaro cikin muryar kuka
yaci gaba da cewa”Ina sonta aunty zainab sune silar komai, bazan ta6a yafe masu ba
na tsane su, Mu kuma tamu jarabtar ta iyaye ce, basu damu da mu ba, buƙatar su
itace agabansu, Yan zu haka da nake maki magana Mommy ce ta kore ni saboda na faɗa
mata gaskiya, ki yi haƙuri Aunty zainab kada ki ce za ki dakatar dani ƙwara na
tafi, zama atare dasu bai da amfani, zanje na nemo ƴar uwata Benazir In ruƙe ta a
hannuna waɗannan mutanan ina zargin sune silar tarwatsewar rayuwarta kamar yadda su
ka yi silar tarwatsewar tawa rayuwar......” yana magana hawaye na cigaba da wanke
fuskarsa, ita kanta zainab ɗin tuni idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, ruƙo
hannunshi tai a cikin nata, da sauri ya ɗaura kanshi saman kafaɗarta”Shureim Allah
ba azzalumin bawansa bane, duk wanda ya cuci wani Allah zai saka mashi, ko a
tsakanin ƴa’ƴa da iyayen su akwai hisabi, Na yi maka alƙawarin zan taimaka maka
akan komai, ashirye ni ke dana zama uwa agareka, Ae ɗa na kowa ne idan su basu so
to ni inaso, dama ban ta6a haihuwa ba” jin abinda tace ne yasa shi ɗago da
fuskarshi yana kallon ta, murmushi ya ƙaƙaro akan fuskarshi, haƙiƙa kalamanta sun
sanyaya masa zuciyar shi.

“Aunty zaina are u serious zaki taimaka min”? Jinjina mashi kai tayi alamar eh,
farin cikine ya bayyana akan fuskarshi’Aunty zainab akwai wani aiki da nake so mu
yi atare bana so kowa Ya sani....” bai kai ƙarshen maganar ba, Takun tafiyar
Mahaifiyarshi Ya dakatar dashi, muryar zainab na rawa tace mashi

“Ka tafi kawai zan kira ka awaya anjima sai mu yi magana” amsa mata yai da toh, Da
sauri Ya fuce ita kuma ta nufi hanyar kitchen.

Cikin takun izza ta ke tafiya, har ta canza kayan jikinta zuwa tsadadden leshi
wuyanta da hannyenta Zinari ne, ta buga uban ɗaurin kallabin nan ture kaga tsiya,
Takalman ƙafarta high hills ne, ta wanke jikinta da turare, tana tafiya tana hura
hanci

Tana dab da zata shiga palourn gidan muryoyin manyan matan da suka kawo mata ziyara
ta karaɗe kunnuwanta, da sauri ta la6e tana sauraron abunda su ke tattaunawa

“Ae ban ta6a ganin mutum mai haɗamar tsiya irin Alhaji ubaid ba, nifa tun lokacin
da ya sauka mulki yana fama da ciwon ƙafa raina ya bani cewar wani munafuncin suka
ƙulla ashe kujerar shugaban ƙasa yake so, yanzu gashi ba wan ba ƙanin duka sun
rasa” 6a66akewa su ka yi da dariya

“Ni dama tun da naji Sharafudeen Ya tsaya takarar shugaban ƙasa raina ya bani cewar
shi zaiyi nasara, sai gashi ta tabbata, wa zai Iya ja dasu? Ganganci ne ya kai
Alhaji ubaid, Ko da ya ke matar shi ce mai haɗamar a yadda na fahimta” hajiyar da
ta yi maganar ta ƙarasa tana dariya, wata ta ɗaura da cewa”ai ko sharafudeen bai
tsaya takara ba kinsan Allah ba wanda zai za6i ubaid, Mutanan da basu son darajar
ƴa’ƴan su ba taya zasu Iya ruƙe ƙasa irin nigeria mai cike da taron Talakawa? Ƴar
ta fa benazir tana ƙasar ture, ayadda naji labari karuwanci take yi kuma ana zargin
uwarce ta turata, Allah na tuba zato zunubi, duk da ni dai daga majiya mai ƙarfi
naji ...”Hankalin layla idan yai duba toh ya tashi, tseguminta da suke yi yayi
matuƙar gigitata, bata ta6a tunanin mutane zasu sanya masu ido game da rayuwarsu
ba, haƙiƙa ranta ya 6aci, Ta yi niyar ta shiga tayi masu korar kare amma saita
lallashi zuciyarta, Ta daidaita natsuwarta tare da yi masu sallama ta kutsa kai
cikin katafaren palourn jin motsin shigowar ta ne yasa su ka yi saurin dakatawa da
yin firar, ɗaya bayan ɗaya ta ke binsu da kallo, mata kenan abin a Jininsu ya
ke.......

*UNCLE ABDALLAH*

A ƙalla yau wata ɗaya da dawowarsu Nigeria, sun fara sauka a adamawa state wurin
dangin hajiya adama kafin dawowarsu gidansu da ke anan Jihar jos, zaune ta ke saman
sofa mai mazaunin mutun uku, Jikinta na sanye da riga bubu ta material ta yafa
mayafi akanta, Yayin da idonta ke asanye da farin glass, hutu yazauna mata ta ƙara
ƙiba abunta.

Ta natsu tana kallon portrait artist ɗin dake zuƙunne agaban Drawing board Yana
gudanar da aikinsa, daga ƙasa gefenshi Kayan zananshi ne, Hada hoton Angel da
hajiya adama ta miƙa mashi don Ya zana mata Ita, tana son ganin yadda zata koma a
shekarunta na yanzu don su samu sauƙin gane ta

“Ranki shi daɗe, Yarinyar zata kai shekara nawa Ayanzu”? Me zanan ne yai mata
tambayar.

“I think 15 to 16 years,” amsa mata yai da okey, Kafin yaci gaba da aikin zanan
shi,

“Mijina ya faɗa min cewa kai ƙwararre ne a 6angaren zana mutane, so please don’t
disappoint me” murmushi mutumin ya saki ba tare daya juyo ya kalle ta ba ya furta
mata”In sha Allah”

“Assalamu Alaikum”! Muryar Uncle abdallace ta janyo hankulansu ga dubanshi,


Shigowarshi kenan Jikinshi na a sanye da shadda launin maroon, idan ka kalli
fuskarshi Sak Uzair hatta duhun fatarsu iri ɗayane.

Cikin girmama mai zanan ya gaishe da uncle abdallah, Bayan ya amsa mashi da fara’a
ya ɗago ya kalli Hajiya adama”mu shiga ciki ina son magana da ke” amsa mashi tai da
toh, Yai gaba ta miƙe tabi bayanshi, A cikin bedroom ɗinsu su ka tsaya suna
fuskantar Juna

“Tun ɗazu nake jiran shigowarka, Inataso muyi maganar zuwan mu abuja, almost one
month da dawowarmu Nigeria banje naga jikana ba duk irin yadda na ƙwallafa raina
akan son ganinshi, “

“Duk yadda kika kaiga ƙagara da son ganinshi ba ki kaini ba,”

“Ni banga alamun hakan ba, pls idan munje mu tafo dashi, tunda ka ga bamu da wani
ɗa da zamu dinga kallo muna jin daɗi” fuskarta amarairaice tayi mashi maganar,
girgiza mata kai Uncle Abdallah yai”idan mukayi hakan bamuyiwa Mahaifiyarshi adalci
ba, ta rasa mijinta yanzu kuma sai mu tada zancen zamu kar6i yaro daga gurinta”?
Ɗaure fuska Hajiya adama tayi, ranta ya 6aci”Abdallah baka son farin cikina, Ni zan
koma palour wurin mai zanan can” Ta ambaci hakan tare da juyawa a fusace zata tafi,
Har takusa kaiwa bakin ƙofa muryarshi ta katse mata hanzarinta”ba zan ta6a manta
irin wahalar da nasha kafin na mallake ki a matsayin matata, ta ya ya kike tunanin
bana son farin cikin ki”? shiru bata Juyo ta kalle shi ba, idonshi na akan bayanta

“A yanzu haka da ni ke yi ma ki magana, na yi mana cuku cukun komawa can da zama,


na samu aiki a babban companyn sharafudeen saboda ba zan Iya raba uwa da ɗanta ba,
haka zalika bazan Iya raba kaka da jikanta ba, shiyasa na yanke shawarar komawarmu
can, Nasan hankalin ki zaifi kwanciya idan kina ganin shi akai akai” idanuwanta ne
suka cuko tab da ƙwallar farin ciki.

Fasa fita ta yi daga Cikin ɗakin, Jiki asanyaye ta nufe shi tare kwantar da kanta
saman ƙirjinshi, Hannun shi Ya ɗaura saman bayanta yana cigaba da gayamata daɗaɗan
kalamai masu kwantar mata da hankali, tsawon mintuna biyar kafin ta ɗago dakai Tana
kallon shi

“Inaso zanyiwa Aneelerh kyautar zanan fuskar Angel da akayi min a south korea,
Nasan za ta yi farin ciki saboda tana matuƙar ƙaunarta, kuma zatayi mamakin ganinta
a shekarunta na yanzu don inada tabbacin idan har Allah yasa ta bayyana zamu iya
ganinta da suffar da mai zanan ya zanata, kasan sun ƙware a iya zane” tana magana
Hannunta ruƙe da gaban rigarshi kamar tana gyara mashi ma6allinta

“Idan ki ka bata zanan ke fa? Almost dala dubu ɗari akayi maki shi fa”

murmushi ta ɗan saki”saboda haka yasa nace ka kiramin wani mai zanan ni sai na
ɗauke shi,” yace”mai zai hana ki bata sabon zanan da za’ayi ke sai ki ruƙe na
koriyan? Girgiza kai ta yi alamar “a’a, Nafison nayi kyauta da abunda yafi kyau da
tsada, Farin cikinta kawai nakeso,” yanayin fuskarshi ya nuna tamkar bayason taba
Aneelerh zanan fuskar Angel da akayi mata aƙasar korea, ba ta kawo komai aranta ba
saboda ta fahinci Son zanan ya ke yi ba don saboda tsadarshi ba.

“Hajiya an kammala” daga Cikin palour su ka jiyo sautin muryar me zanan, da sauri
Hajiya adama ta nufi falon uncle abdallah yabi bayanta, tunkan su ƙarasa shiga Ciki
idanuwansu suka soma hango masu Kyakkyawar fuskar Angel jikin allon zanan nashi,
Tsabar mamakin yadda suffarta ya fito ne yasa su sakin baki, Kamanninta sak dana
tajudden Hasken fatarne kaɗai na mahaifiyarta da kuma sumar kanta.

“Wow! Zanan sak kalar na south korewa nayi mamaki! Banbancin kawai tsadar kayan
aikin da akayi amfani wurin yin wancan zanan amma wlh yayi kyau over” hajiya
adamace take ta sambatun ganin zanan, Shi kanshi uncle abdallah Ya yi mamakin ganin
zanan, Suffar Angel sak sai dai an ƙara mata girmanta, takai dai dai age ɗinta na
yanzu 15 to 16 years,

Mai zanan yana atsaye yana kallonsu, sai sakin murmushi yake yi jin yadda suke
yabon aikinsa

“Ina fata Angel ta bayyana kamar yadda muka ganta a zananta, in har hakan ta faru
nayi maka alƙawarin zan ninka maka kuɗinka” fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar
tana kallon mai zanan, washe baki yai yana faɗin”In sha Allah ranki ya daɗe ƴar ki
zata bayyana kamar yadda na zana ta a hoton nan, kuma ina roƙon Allah yasa zanene
ya zama silar ganinta” atare suka amsa mashi da ameen, Kafin tafiyar mai zanan
saida suka haɗa mashi sha tara na arziƙi.

*EVIL FOREST*

*the Prisoners💔*

Kamar matattu haka su ka sha baccin su cikin kogon dutse, Allah kaɗai yasan awanni
da su ka kwashe suna sharar bacci, Bawan Allah Danish A zaune ya ke bacci, Wutar da
ya kunna masu tuni ta jima da mutuwa, Hasken rana ya kwalo daga sararin samaniya
duhun dajin ya ɗan washe, A hankali ta soma mutsun mutsun buɗe idanuwanta a yayin
da ta ke ambaton Sunan Allah, tsabar kumburan da idon nata yai daƙyar ta ke iya
buɗe shi, ga uwar kwamtsa cunkushe da idon, kaɗan ta ke iya buɗe shi tana kallon
Saman kogon dutsen, cikin rashin fahimtar ina ne? sam ta manta cewa sunbar kurkukun
ƙaddara, wani irin tsorone ya kamata muryarta sam babu wadataccen sauti ahaka take
ƙoƙarin ƙwalawa ƴan uwanta kira ɗaya bayan ɗaya, duk tabi ta furgice.

“Batool! Gabriel! Haris kuna ina ne? Duhu bana iya gani da kyau, Naufal wai Ba mai
ji na ne”? Shiru taji babu motsin mutun a kusa da ita, Jikinta yai mata tsami, ko
yatsanta ta gaza motsawa, ga dukkan alamu dannau ne ya danneta, kware muryar tayi
da ƙarfi ta furta Sunan Danish! Har cikin dodon kunnan shi ya ji sautin muryarta,
slowly ya ɗan ware kyawawan idanuwanshi akan fuskarta, bargon da ya lullu6a mata a
iya ƙirjinta ya tsaya hakan ya bashi damar kallon ta da kyau, duk da jinin da
matsafa su ka yi mata wanka dashi ya koma mata tamkar fenti tayi muni sosai, cikin
sanyin murya ya furta sunanta”My Angel” jin muryarshi yasa ta dakatawa da yin
sambatun nata, ƙoƙari take wurin ganin ta motsa jikinta don ta samu damar zuwa gare
shi, fahimtar hakan yasa shi matsawa dab da ita, kwanto da fuskarsa yai saitin
fuskarta yai mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, numfashinsu har yana kokawa dana
juna, kaɗan ta ke iya ganin fuskarshi, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta,
muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi”Da..Nish” fatanta Allah yasa ba mafarki
bane.

Dogayen yatsun hannun shi ya ɗaura a gefen fuskarta ya shafa a hankali da sauri ta
ɗaura nata hannun saman nashi dake akan face ɗinta, Sai yanzu ta samu damar motsa
jikinta, zafafan hawaye ne su ka soma wanke mata fuskarta, Ɗago da ita yai zuwa
saman ƙirjinshi Ya kwantar da ita, duka yatsun hannayen shi na acikin sumar kanta,
sosai ya ƙanƙameta, yanayin yadda su ka rungume junansu zai tabbatar maka da irin
kewar juna da su ka yi, ba ka jin komai sai sautin nunfashinsu, da bugun zuciyarsu
dake harbawa da sauri da sauri,

“I can’t explain how much I miss you. I’m sorry for what happened, it’s all my
fault. I’m sorry, Angel.”

Cikin rauni na murya yai maganar, Cikin shessheƙar kuka ta soma yi mashi magana”ba
laifinka bane Danish, ka daina faɗin hakan, ni abunda yafi damuna rashin ƴan uwan
mu da suka rasu, na yi takaici Danish, ban cika masu alƙawarin da na ɗaukar masu
ba, Jemimah da Azeeza sunci burin fita daga kurkuku don suje gidan daddyna, haka
parveen burinta ta ci abincin gidan daddyna, baiwar Allah deejah ga sauran ƴan uwan
mu da mu ka rasa” daƙyar ta ƙarasa maganar, zafin jikin su duk ya ɗumamasu, Yanayin
weather ɗin dajin San yi sosai, daga inda suke suna iya jiyo sautin kukan Namun
dawa.

Ɗaura tsinin hancinsa yai saman sumar kanta, shi kaɗai yasan raɗaɗin da ya ke ji
acikin zuciyarshi, Jin shiru bai tanka mata ba, yasa ta ɗago da kanta daga saman
ƙirjinshi ta ɗaura eye balls ɗinta akan fuskarshi, bacci ne bai ishe shi ba, sai
faman lumshe idanuwanshi yake yi, a tsanake su ke ƙarewa juna kallo tsawon mintuna
goma sha biyar, ‘

“Bana so su Gabriel su farka su taras da gawawwakin su azeeza, abun zai ƙara ta6a
zuciyarsu, ka taimaka min Danish mu binne su kafin farkawarsu,” shiru bai tanka
mata ba sai kallon ta ya ke yi kamar yau ya fara ganinta

“Danish! Am talking to u, bana jin daɗin jikina, maganar ma daƙyar nake iya
furtata” Still bai motsa la66ansa ba’ ta rasa meyasa ya ke kallonta yana lumshe ido
Ya ƙi tanka mata,” Gyaɗa kai tai”shikenan tun da bazaka taimaka min ba, Ni zan je
na rufe su” tana ƙoƙarin miƙewa sexy voice ɗin shi ta ratsa kunnuwanta”Kin ta6a
ganin an binne mutun da ranshi”!! ras taji gabanta ya faɗi a matuƙar ruɗe ta
zazzaro idanuwanta waje tana kallon shi........

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E7🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

“ka na nufin ba su mutu ba suna a raye”? A ƙagare ta jefa mashi tambayar, jinjina
mata kai yai ba tare da ya furta mata kalma ba, bugun zuciyarta ne ya qaru a
sukwane ta juya baya don ta samu damar ƙare masu kallo, bargunan da ya lullu6e su
da shi ya hana ta gan su da kyau, jikinta na 6ari ta ƙara sa gaban su ta zuƙunna
tare da kai hannu ta ɗage saman bargon, duk wani motsin ta akan idon Danish.

Wani irin farin ciki ne Ya lullu6eta haƙiƙa ta yi al’ajabin wannan iko na Allah,
kamar zautacciya haka ta dinga ɗaura kanta saman ƙirjinsu haɗi da jogana kunnanta
saitin zuciyar su don ta ji idan tana bugawa, daga kan Jamimah ta fara tana ɗosa
kunnanta bugun zuciyar jemimah ya daki dodon kunnan, nan ta ke ta fahimci cewa
bacci su ke yi, Tambayoyi ta shiga jefawa kanta, Ta ya ya akai haka ta faru? Dama
wanda ya mutu yana tashi? don ita dai a iya saninta idan an mutun ba adawowa, ɗaura
kunnanta ta yi saman ƙirjin Azeeza lumshe idanuwanta ta yi wani irin sanyi ne ya
ratsa zuciyarta, jin bugun zuciyar azeeza na har6awa, matsawa ta yi gaban Parveen
tunkan ta ɗaura kanta saman ƙirjinta idanuwanta su ka sauka akan ƙaramin bakinta
ganin yana motsi yasa ta fahimci tana araye, Lamarin yai matuƙar ɗaure mata kai, ta
ya akai su ka rayu! Kuma Danish da kanshi ya tabbatar masu cewa Heart attack ne yai
silar mutuwarsu, duk da bata da ƙoshin lafiya hakan bai hana smart brain ɗinta aiki
ba, Zurfin tunani ta shiga idan har su Jemaimah su ka iya jure abunda ya faru dasu
ya kenan ta 6angaren Sauran ƴan uwansu da su ka baro? Waro idanuwanta waje ta yi
yayin da zuciyarta ka harbawa da sauri da sauri, a fujajen ta zabura ta miƙe kamar
an zungure ta, ta juya ta nufi Danish dake a zaune Ya ɗan lumshe idanuwanshi,
ƙoƙari ya ke ya hana kanshi yin bacci gudun kada yaja masu matsala, zuƙunnawa tai
agabanshi

“Danish taya akai su Jamima su ka rayu? Bayan kai da kanka ne ka faɗa mana cewa
zuciyarsu ce ta buga” ware idanuwanshi yai akan fuskarta, tsananin tausayinta ne ya
kama shi, damuwarta akan ƴan uwanta, bata damu da kanta ba, ƙarantar shekarunta
yafi komai ɗaure mashi kai, yadda harta iya jure waɗannan wahalhalun rayuwar wanda
yayi imanin ko wani babban ba zai Iya jurarsu ba.

“Danish bana so ina magana kana share ni, ka faɗa min ta ya ya akai su ka rayu? A
iya sanina idan mutun ya mutu baya tashi, Sai gashi su Azeeza sun tashi, ko dai ka
yi amfani da sihirinka ne wurin dawo masu da rayuwarsu...”? A ruɗe tai maganar babu
kwanciyar hankali atattare da ita, a hankali ya ɗan motsa la66ansa.

“My Angel, u should stop talking about them, ba ki da lafiya u need a rest,” damƙar
wuyar best ɗin jikin tai sosai ta fashe mashi da kuka tana faɗin”Danish ka faɗa min
dama kasan suna araye shi ne ba ka bari mun goyo su Deeja mun taho da su ba? Me
yasa ka yi mana ƙaryar cewa zuciyarsu ce ta buga”? Tana magana tana ku ka, raunin
gefen bakin ta tuni ya fara tsastsafo da jini.

Ranta yai mugun 6aci zuciyarta ta harzuƙa, A haukace ta miƙe tana faɗin”Zan koma na
taho da su Deeeja, ban damu da in rasa raina ba,” a hanzarce ya miƙe jin abunda
tace, ido cikin ido su ke kallon juna”Am sorry Angel i don’t mean to hurt u, kinsan
bana ƙarya, sannan bani da amsar da zan baki that’s why nayi shiru, hatta su Azeeza
ban san suna araye ba, a daren jiya na yi ƙoƙarin binne su cos bana son ku farka ku
taras da gawawwakinsu, hakan zai fama ma ku ciwon da ke a cikin zuciyarku, nayi
amfani da sihirina wurin tsaga ƙasa har na fara sanyasu a ciki idona ya sauka akan
yatsun ƙafafuwansu dake motsi, i was shocked cos ban yi expecting din zasu rayu ba,
kin ji yadda akai nasan suna a raye”

kamar ta so ta fahimce shi sai dai wani sashe na zuciyarta yaƙi aminta dashi,
girgiza mashi kai tai”Ni dai zan koma kurkuku in ɗauko su Deeja, Saboda ina ji
araina cewa Suna araye”

Ya fahimci damuwace ke ƙoƙarin zautar da ita, Zaiyi wuya ta fahince shi, yasan
halin kayansa da rigima ga kafiya da taurin kai, juyawa ta yi tare da nufar ƙofar
fita daga kogon dutsen, da sauri Ya bi bayanta tare da ruƙo arm ɗinta ya janyota
zuwa jikinshi, sosai ya matseta.
“Angel daji ne fa, ba mu a kusa da kurkukun ƙaddara, ta zarar awanni ce, A daren
Jiya bayan mun fita ni ne na ɗauko ku na dawo da ku nan duk don na sauƙaƙa maku
wahala” daƙyar ya ke magana, damuwace ƙarara akan fuskarsa, ƙoƙarin raba Jikinta
tayi daga nashi.

Zuciyarta ce ke azalzalarta sam bata fahimtar kalamansa, idanuwanta sun makance

“Ka sake ni Danish, nasan ko nace kaje ka ɗauko min su Deeja ba za ka je ba, don
haka ni zanje, saboda ina ji araina ƴan uwana suna araye basu mutu ba gashi mun
baro su a hannun Azzaluman mutanancan.....” cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa
maganar, duk yadda yaso ya hanata tafiya taƙiya, har kwatanta mata haɗarin da dajin
gare shi amma ta kafe akan sai taje, sakinta yai idon shi akan bayanta, sam babu
kuzari a jikinta ahaka ta fuce daga cikin kogon dutsen, Hasken ranane ya galle mata
idonta da sauri ta lumshe su na ɗan sakanni kafin ta ware su tana ƙarewa ƙurmin
Dajin kallo, Daddaɗar iskar dajin ce ta ratsa sassan jikinta ni’imtacciyar gaske,
hatta sumar kanta sai kaɗawa take yi saboda ƙarfin iskar, saboda taurin kai irin
na Angel da kasada, Ahaka ta soma tafiya tana nufar cikin dajin ita ala dole saita
gano inda kurkukun ƙaddara ya ke, tun kan aje ko’ina ta fara tsorata da ganin
ƙananun halittun da ke yawo Saman bishiyoyi, duk da haka bata sare ba taci gaba da
tafiya hada ɗan saurinta da gudunta, ko takalma babu a ƙafarta.

Tun bayan fitarta Danish Ya fito daga cikin kogon dutsen, ya goya hannayenshi saman
faffaɗan ƙirjinshi Yana kallon bayanta, Ta yi matuƙar bashi mamaki, duk da ya
fahimci babu hankali atattare da ita, in ba haka ba ta ya ya wanda ya tsira yake
ƙoƙarin komawa ga halaka. Yarinta ce ke damunta da kuma son ƴan uwanta.

Tana cikin yin tafiyar nan, kukan namun dawa Ya dakatar da ita cak ta tsaya tana
ƙarewa wurin da take atsaye kallo, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan
Snake ɗin dake bin jikin bishiya yana ƙoƙarin saukowa ƙasa, zaro ido waje tai a
gigice ta fasa ƙara tare da juyawa da gudun gaske tamkar zata tashi sama, majicin
na ƙarasa saukowa yabi bayanta, tashin hankali duk ta bi ta rikice don ta fahimci
ita yake bi, tun da uwarta ta haife ta bata ta6a yin tozali da maciji ido da ido ba
sai yau da Allah ya haɗosu, Tarasa gane ta wace hanya zata bi ta koma cikin kogon
dutsen.

Danish ta dinga ƙwalawa kira kamar maƙoshinta zai 6allo, sai da ta gama galabaita
cikin rashin sa’a tai tuntu6e da dutse gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa, ƙiris ya
rage ta kife ƙasa a lokacin da ba ta yi tsammani ba taji Ya damƙo ta tare da
kwantar da ita saman chest ɗinsa.

ƙanƙameshi tayi sosai ta fashe mashi da kuka tana zazzaga mashi masifa akan me zai
barta ita kaɗai acikin daji? Idan ma don saboda ta yi mashi kafiya ne, bai ga ita
yarinya bace, tun da fara mashi faɗa bai tanka mata ba, hannayen shi biyu suna
tallabe da ita, sai da ta yi mai isarta, tukunna ta buɗe kumburarrun idanuwanta
akan fuskarshi, tun daga kan tausasan red lips ɗinsa ta soma bi da kallo har izuwa
ga dogon hancin sa kafin ta ɗauke idon nata ta ɗaura su kan sexy eyes ɗinshi masu
matuƙar jan hankali.

ƙoƙarin shagala su ke yi da kallon Juna, tunawa da ƴan uwansu da su ka baro a kogon


dutse ne yasa tayi saurin katse masu kallon ƙurullan da suke bin juna dashi”Danish
mu koma kada wani abu ya same su” girgiza mata kai yai in a smoky voice ya furta
mata”ba abunda zai same su, ina sane dasu, na rufe kogon dutsen babu wani abun
cutarwa da zai Iya tunkarar su”Sam hankalin bai kwanta da kalaman shi ba

“Danish ni dai mu koma,” ashagwa6e tayi mashi maganar, ita kanta batasan ta sanya
shagwa6a ba’

“Zamu koma, but before that, Inaso ki raka ni cikin Dajin in nemo mana abunda zamu
ci, ko kina so su farka suna Jin yunwa ne”?

Girgiza mashi kai tayi”a’a amma ni ba zan bi ka ba, Ka maida ni cikin kogon dutsen
in ya so kai sai ka je nema mana abunda zamuci” kafe ta da ido yai, hakan yasa ta
jefa mashi harara haɗi da murguɗa mashi baki, munin fuskarta bai hana shi ganin
kyanta ba, musamman da ta yi mashi abunda ke jan hankalin shi gareta, Harara da
murguɗe abun A jinin ta ya ke.

“Idan ba za ki bi ni ba, Ga hanya nan ki koma kogon dutsen ni kin ga tafiyana” yai
maganar tare da nufar Cikin dajin, da ido tabi bayanshi da kallo, ranta a 6ace
yasan ba zata iya kai kanta ba shiyasa yace ta koma, Tunawa da macijin da ya biyota
ne yasa ta zabura da gudu tabi bayanshi, Yana cikin tafiya yaji ta zura hannunta
cikin nashi, ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi.

Ta yi tsammanin Iya abincin da zasu ci ne zasu nemo, ba ta san plan Ya shirya mata
ba, Yanayin Iskar dajin ba ƙaramin ni’ima ta saukar masu ba, Suna tafiya suna
kallon Juna, wani irin Sanyi ne ke ratsa zukatan su, dakatawa tai dayin tafiyar ta
ɗan kalli fuskarshi”Na gaji Danish ƙafata ciwo ta ke yi min” ba tare da ya amsa
mata ba, ya juya mata bayan shi, ta gane me yake nufi, da sauri ta haye Saman bayan
Ya miƙe ɗauke da ita, ba ƙaramin daɗi taji ba, shin me yafi ranta gata ga garkuwar
kurkuku, ta ƙanƙameshi sosai, lumshe idanuwanta tayi sai faman shaƙar mashi fatar
wuyan shi take yi, bai sauke ta a ko’ina ba sai abakin wani tabkeken ruwa mai
gudana, Ta jikin dutse ruwan ya ke gangarowa tsaftatacce fari ƙal dashi.

“Mun ƙaraso,” Jin abunda yace ne yasa ta ɗago da kanta, tana ƙarewa wurin kallo,
nan ta ke ta ji tana sha’awar shan ruwan, Zuƙunnawa yai ta sauko daga saman bayan
nashi, a jere suka tsaya suna bin ruwan da kallo, ga dukkan alamu ya burgesu .

“Danish ƙishi na ke ji, nasan kaima kana ji, mu sha sai mu ɗebi wani mu kai ma su
Parveen ko”? Ba tare da ya juyo ya kalli fuskarta ba ya soma magana”Wanka nake so
nayi maki, saboda kinyi muni, jikin ki yayi datti”

Har saida gabanta ya faɗi jin abunda yace, juyowa yai da fuskarshi ya kalleta tare
da kashe mata ido ɗaya

“za ki iya cire kayan ko in taimaka maki ne”? gabanta ne ya dinga faɗuwa sai ta ga
kamar ya canza mata, babu alamun wasa akan fuskar shi yai maganar.

Ganin yana matsowa kusa da ita, yasa ta juya da niyar ta gudu, ko ta ku ɗaya bata
kai ga yi ba taji Ya damƙi ƙugunta, ƙarfi ba ɗaya ba, Duk yadda taso ta kubce mashi
ta kasa, matseta yai a ƙirjin shi, A hankali Yai amfani da hannun shi ɗaya wurin
zame rigar Jikin shi, tare da wandon kakinsa na Giant, ya rage daga shi sai short
fari, saman gungurumeman dutsen dake agefen ruwan, ya jefar da uniform ɗinshi.

kamar jinjira haka ya ɗauke ta, kaitsaye Ya nufi Cikin ruwan da ke gangarowa, ba
yadda ta iya dashi, Tana kuka tana fadin bataso ya ƙyale ya rabu da ita, ahaka yayi
mata wanka tass ya wanketa Kamar yayi amfani da sabulu ita kanta tayi mamikin yadda
Jinin jikinta ke fita, Farar fatarta sol ta dawo har wani salƙi takeyi da ɗaukar
ido, hatta uniform ɗin da ke ajikinta sun wanku sosai sun manne ma fatarta,

kwantar da kanta yai saman broad chest ɗinshi, Ya cusa yatsun hannunshi cikin sumar
kanta yana cuccuɗata da ruwa, Jinin da ya danƙare mata a cikin kan ya dinga fita,
gashin kanta ya dawo ainihin launin shi dark brown mai kyan gaske, ba ƙaramin
taimakonta yai ba da yayi mata wanka, Ita kanta tasan bazata iya wanke najasar dake
a jikinta ba, ƙanƙame jikinshi tayi sosai la66anta na kerma take faɗin”sanyi Danish
san yi ni ke ji, tamkar ana ƙara gudun ruwan sun jiƙe sharkaf acikinsa, sai da ya
kammala tsaftace mata jikinta tukunna ya ɗaukota saman kafaɗarshi ya dawo da ita
Gefen dutsen da ya ɗaura uniform ɗinshi.
Tun da ya sauke ta ta faɗa ma faffaɗan ƙirjinshi, ta zagayo da hannayenta saman
bayanshi, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, idanuwanta a lumshe, ita kaɗai
tasan daɗin da ta ke ji, da farko taji haushi da ya yi mata wanka, amma yanzu ta
fahimci Dalilin dayasa ya tursasa mata yin wanka, jikinta yayi mata daɗi wata irin
ni’ima ke sauka, tamkar an yaye mata damuwar dake acikin zuciyarta, sun natsu suna
sauraron bugun zuciyar junansu, irin yanayin da yafi son kasancewa tare da ita,
yana son Angel dinsa fiye da yadda yake son kanshi, a shirye yake daya sadaukar da
ranshi indai akanta ne”

Fatar wuyanta ya ƙurawa ido fara sol sai ƴan tabannin da ba arasa ba, na gurjewar
da tayi, ɗaura tafin hannayensa yai asaman bayan nata,

“My Angel!” a kasalance ya furta sunanta shiru bata amsa mashi ba

“Are you feeling sleepy?” kamar yayi magana da bango shiru taƙi buɗe ba ki ta yi
magana, ƙoƙarin rabata yayi daga ƙirjinsa, sai dai taƙi bari ya ɗago da ita, ta yi
tighting ɗin shi tamkar zata koma cikin shi, baiwar Allah, Dama abuƙace take da ta
samu inda zata sassauta raɗaɗin da ke acikin zuciyarta, abubuwan da suka faruwa a
rayuwarta ta soma tariyowa tun daga lokacin da ta mallaki hankalin ta, har zuwa
rayuwarta a hannun fulanin Daji da kuma faɗowarta gidan kurkukun ƙaddara, Zafafan
hawayene suka wanke fuskarta, jin shessheƙar kukanta ne yasa shi rikicewa ya shiga
ambaton sunanta adabarbarce, daƙyar ya iya 6an6arota daga ƙirjinshi, eyes dinshi
akan fuskarta ta runtse idonta

“My Angel I don’t want you to dwell on what happened before, I know it hurts you,
but please forget about the past. I don’t like to see you cry.

tun da ya soma lallashinta bata buɗe idanuwanta ba, tsawon mintuna kafin a hankali
ta ɗago da kanta tare da jingina bayanta jikin dutse.

Matsawa yayi jikin ƙaton dutsen ya miƙa hannu ya ruƙo uniform ɗin shi, A tsanake Ya
sanyasu a jikin shi

“Zaki Iya jirana anan”? girgiza mashi kai tayi”tsoro nake ji, ka maida ni cikin ƴan
uwana” yaso ta amince ko dan ya samu ya shiga cikin Dajin Ya nemo masu abunda zasu
ci, kwantar mata da hankalinta yai”Yanzu zan dawo, bana so ƴan uwanmu su tashi da
yunwa pls ki jirani anan, ba abunda zai same ki, kada kije ko’ina” bai jira amsarta
ba, ya 6ace ma ganinta.

Tunawa da cewa ita fa yanzu mai ƴanci ce yasa ta ɗan saki murmushi, har ta fara
tunanin irin mugun kisan da za ta yi ma waɗanda su ka sadaukar da su, badajimawa ba
ta soma Jin motsin tafiyar mutun a firgice ta buɗe idanuwanta lokaci ɗaya ta sauke
nauyayyiyar ajiyar zuciya ganin Danish ne ya dawo hannun shi a ruƙe da Zomayen Daji
da ya yo masu farautarsu, ya ruƙe ƙafafuwansu da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun
ke aruƙe da gorar ruwan, mamaki ne ya kamata ganin zomaye, miƙa mata gorar ruwan
yai da sauri tasa hannu ta kar6a, Acike take da ruwa, jera kafaɗa su ka yi suna
tafiya suna satar kallon juna, abunda ya ɗaure mata kai yadda Danish yasan komai
dangane da Daji mutumin da bai ta6a fita daga cikin kurkuku ba, Yanzu tadaina yi
mashi kallon solo6iyo, A Namijinsa ta ke kallon shi.

Lokacin da su ka ƙaraso Gaban Kogon dutsen, Atare su ka shiga Ciki, Ya ajiye


zomayen saman korayen ciyayin da ke shimfiɗe ƙasa, ya ɗago da ido ya kalle ta,
zanje na haɗo itace yanzu zan dawo, Ta amsa mashi da toh,’

Bayan tafiyarshi ta ajiye gorar ruwan ƙasa, kafin ta nufi shimfiɗar su, ba ta yi
mamakin ganin ba su farka ba saboda ta riga ta gane aikin Danishi, gaban akwatin
kayansu ta zuƙunna ta buɗe ta curo tsoffin uniform ɗinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta
canza na jikinta da suka jiƙe ta shanya su daga wajen dutsen, dawowa tayi cikin
kogon Agaban shimfiɗar ta zuƙunna tana ƙare masu kallo, idanuwanta akan Jemimah da
Azeeza, daɗi kamar zai kasheta, a ƙagare ta ke da su farka su ga wurin da Allah ya
kawosu tasan zasu sha mamaki da al’ajabi kuma zasu ji daɗin cika masu alƙawarin da
ta yi.

Sam ba ta ji motsin shigowarshi ba, har sai da yai mata gyaran murya tukunna ta
waiwayo su ka haɗa ido da shi

In zo in tayaka”? girgiza mata kai yai” a’a bana so ki wahala” miƙewa tayi tare da
zuwa gabanshi ta zuƙunna tana ƙare mashi kallo, hankalin shi ya koma akan itacen da
ya ke jerawa bayan ya kammala ya ɗauki duwatsun jiya da yai amfani wurin rura wuta,
duk wani motsin shi akan idonta har ce mata yai “kije ki huta mana, ba kince kina
jin sanyi ba? Ki ɗauko bargo” maƙe mashi kafaɗa tai alamar ba za ta je ba.

Bawan Allah shiya zauna zaman gasa masu naman, sai maiƙo yake yi kamar an soya shi
da mai, Kitsan jikin zomayen ne ke narkewa, bayan ya kammala ya ɗaura gasasshen
naman da ya tsira Jikin icce saman faffaɗan ganyan da ya shimfiɗa a ƙasa.

“Danish” ɗagowa yai tare da kallonta, bakomai ya gani acikin idanuwanta ba face
Tsantsar tausayin shi

“Kada ki damu kanki am ok, idan zan shekara inayi maku bauta ba zan gaji ba”
kalamanshi sun ƙara sanya mata ƙaunarshi acikin zuciyarta.
“A ina ka samu wannan gorar ruwa”? Tai maganar tana nuna ta da yatsa

“A cikin Daji ba abunda ba zaki Iya samu ba, Hada kan mutun” murmushin gefen fuska
ta saki, ga dukkan alamu zasu fara kafa nasu tarihin soyayyar tun acikin Daji.

Ɗagowa yai da lumsassun idanuwanshi ya ɗaura su kan fuskarta

“Can you eat by yourself? Or do I need to feed you?”

Girgiza mashi kai tai” ka wahala sosai, ni ya kamata in baka da hannuna” ya ji


daɗin maganarta har ya buɗe baki da niyar mayar mata da martanin maganarta,
kwatsam! muryar Jemimah ta katsesu da wani irin sautin mai amo take kwaɗawa Angel
kira amatuƙar gigice take fadin”Genie wayyo Allah Genie Zafi Jikina ƙaiƙayi nake
ji” Ahanzarce Danish da Angel suka miƙe da sauri suka nufi shimfiɗarsu atare suka
zuƙunna agabansu, Hannu biyu Angel ta sanya ta ɗauko ta zuwa saman jikinta, ta
ƙanƙameta, Duk tabi ta furgice sai kuka takeyi masu tana harba ƙafafuwanta, Sautin
kukanta ne ya farfaɗo da sauran ƴan uwan nasu, Batul ce ta fara miƙewa kamar
fatalwa idanuwanta luhu luhu sun kaɗa jawur, baiwar Allah har faɗawa tayi sai uban
haske, gashin kanta kuwa a hargitse yake, Buɗe idonta keda wuya ta sauke su akan na
Danish dake kallonta, Muryarshi na ɗan rawa ya furta sunanta”Ba..tul” ɗauke idonta
tayi daga kan fuskarshi ta mayar dasu Kan kogon dutsen da suke aciki saƙo da lungu
tabi da kallo, kukan farin cikine ya kubce mata, Da sauri Danish ya ruƙo hannunta
acikin nashi ya kwanto da kanta saman ƙirjinshi, sosai ta ƙanƙameshi tana cigaba da
yin kukan.

Farkawa Gabriel yai zumbur ya miƙe yana ambaton sunan Azeeza, da ita ya kwanta
acikin ranshi, sai tsuma yake yi yana fitar da huci, Cikin shessheƙar Kuka Angel
tace dashi”She’s still alive! Azeezar mu bata mutu ba, suna araye,”

Karaf maganarta ta sauka akan kunnan sauran ƴan uwan su da suka farka, a zazzaune
suka miƙe Tun daga kan Javed, Naufal da Hannah mutun uku ne basu motsa ba, parveen
Azeeza da Haris, ga dukkan alamu sun farka daga bacci sai dai sun kasa motsawa,
Jikinsu ba ƙoshin lafiya, ko yatsan su sun gaza ɗagawa.

Hankulansu gaba ɗaya ya koma kan su, kowan nan su fuskarshi akumbure take suntum,
babu walwala ko annuri, dagaske Azeezana bata mutu ba? Gabriel ne yai tambayar
yayin da idonshi ke fitar da hawaye, Danish ne ya bashi amsar tambayarshi, Tsabar
farin Cikine ya bayyana akan fuskarshi, Rumfa yai ma azeeza da ƙirjinshi motsa
la66anta da take yi ne ya tabbatar mashi da cewa tana araye sungumarta yai tare da
ɗaurata saman laps ɗinshi, Danish Ya miƙa mashi gorar ruwa don ya bata tasha,
Yatsun hannun shi na kerma ya kar6a ya kafa mata abaki, ruwan yana wucewa ta
maƙoshinta sai dai ta gaza buɗe idonta, Farin Ciki duk ya cikasu, Naufal ne ya
ɗauki Parveen Baiwar Allah anji jiki, miƙa mashi gorar ruwan Gabriel yai ya kar6a
yabawa parveen kamar zata haɗa da gorar duka ta shanye, Sai lokacin Danish Ya raba
jikin shi daga na Batul Ya rarrafa zuwa gaban Haris dake kwance kamar matacce ya
ɗaura hannayenshi biyu wurin ɗago dashi ya kwantar da kansa saman kafaɗarshi, Cikin
sanyin murya ya ke ambaton sunanshi”Haris! Haris!” shiru bai amsa mashi ba, jikin
shi yai zafi sosai babu alamun lafiya atattare dashi, ɗaura tafin hannun shi yai
saman ƙirjinshi bugun zuciyar haris a hargitse yake fita, hakan ba ƙaramin tada
mashi hankali yai ba, Yana fargabar wani abu ya same shi.
“Ɗan uwana Rabin raina nasan kana jin muryata pls kada ka bari damuwa tayi maka
illa, ina atare da kai” jin muryar Danish acikin kunnanshi yasa shi ƙoƙarin motsa
la66ansa sam sautin yaƙi fita, Fahimtar hakan yasa danish matsar da kunnanshi
saitin bakin Haris

“Deeja ta mutu! Na rasa Deeja Danish! Bazan iya rayuwa ba tare da ita ba, zuciyata
nauyi take yi min, ka taimaka ma rayuwata” a hargitse yake magana, tsananin
tausayin shi ne ya kama Danish, dama sai da ranshi ya bashi cewar akan Deeja ne ya
shiga mawuyacin halin nan.

“Haris ka kwantar da hankalin ka, ba mu da tabbacin suna araye ko sun mutu, tun da
har su Azeeza suka farka bayan munyi tunanin sun mutu ina saran suma za’a iya samun
masu rai acikin su” cikin jin ƙunar rai Haris ya furta”Danish idan har hakane
deejana tana araye azzuluman mutanancan zasu Iya kashe min ita, mun barsu fa a
kurkuku, Danish ka koma ka ɗauko min ita, idan baso kake na mutu ba’ sosai ya sanya
mashi kuka, Rarrashin shi ya dinga yi yana lalla6a shi duk don ya samu ciwon nashi
ya lafa.

Waɗanda suka fi jin jiki a cikinsu Jemimah ce da Azeeza sai Haris, Ita parveen
tunda taji ta ajikin Naufal ta wartsake, har tana iya ambaton yunwa take ji,
Jemimah kuwa taƙi daina yi masu kuka, Sautin kukanta ya karaɗe kogon dutsen kamar
ana zare ranta, Hankalin Angel duk yabi ya tashi, Ta rasa ya zatayi da ita, Cikin
muryar kuka take yiwa Danish magana akan yazo yataimaka mata, Har ƙwara Azeeza tun
da ta ƙanƙame Gabriel bata ƙara motsawa ba, ta lafe mashi idanuwanta arufe suke
gam.

Sun rasa ya za su yi dasu, kukan jamima ba ƙaramin tsuma zuciyarsu yake yi ba, taji
jiki baiwar Allah, Sunga ƙoƙarinta da har ta iya yin kukan, azabar raɗaɗin gabanta
ne ya addabeta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, fuskarta jaga jaga da
hawaye, yarinyar da bata wuci shekara goma da watanni ba, ta rasa budurcinta, su
kansu sunyi mamakin da ta iya rayuwa, lokacin mutuwarta ne baiyi ba, Tana kuka suna
kuka, Babu wanda bai zubar mata da ƙwalla ba in ka cire Danish, kwantar da Haris
yai saman shimfiɗar, jikinshi na tsuma ya nufi Angel Ya sanya hannu biyu ya kar6i
jemimah daga hannunta, fucewa yai da ita daga Cikin kogon dutsen basu san Inda ya
nufa da ita ba.

Tsawon mintuna sai gashi ya dawo rungume da ita a ƙirjinshi, ajiyar zuciya suka
sauke Jin tayi shiru tadaina kukan, Akwatin kayansu ya buɗe ya ɗauko mata rigar
sanyi, cikin waɗanɗa tsohuwa ta yi masu kyautarsu, Ya sanya mata a jikinta, ga
dukkan alamu wanka ya yi mata, bayan ya kammala sanya mata rigar, ya curo mata hula
ya zura mata akanta, ya kuma ɗauko Mayafin kayansu, Sai kallon shi suke yi, Danish
ya basu mamaki, Asaman bayanta ya yafa mata mayafin ya miƙe tsaye yana lallashinta
kamar yadda akeyi wa jarirai, jemimah ta natsu sai faman lumshe idanuwanta takeyi,
Jikinta ya lafa sosai ta daina jin raɗaɗi ciwo nata, juyowa yai tare da nufar Angel
ya miƙa mata jemimah,
“Zan tafi da Azeeza ki basu naman su fara ci” amsa mashi tayi da toh, ta kar6i
jemimah tare da rungume ta a ƙirjinta, bayan Ya ɗauki Azeeza Ya fuce da ita, janyo
masu naman tayi zuwa gabansu, duk da halin da suke aciki hakan bai hanasu Cin naman
ba, Saboda matsiyaciyar yunwar da suke ji, Mutun ɗayane ya kasa cin naman, ko da
Javed Ya tallabo shi ya zaunar dashi Yana tura mashi abaki, Amayar dashi ya dinga
Yi, ruwa kaɗai ya iya sha, sun damu da rashin lafiyar Haris Ya galabaita sosai,
Jemimah dai ta ɗanci naman Angel ce take bata abaki, har yanzu bata buɗe
idanuwanta ba, balle ta san a ina suke.

Shigowa cikin Kogon Danish yai Hannunshi ɗauke da Azeeza, Ya wanke ta tass jikinta
sai kakarwa yakeyi, tunkafin ya ƙaraso Gabriel Ya buɗe akwatin kayansu ya ɗauko
mata rigar sanyi tare da mayafi, Bayan Danish Ya miƙa mashi ita, Ya sanya mata
rigar asaman uniform ɗinta, Ya ɗaura mata mayafi saman kanta, kafin ya kwantar da
ita saman ƙirjin shi, Abaki ya dinga gutsuro namanta yana tura mata abaki daƙyar
take iya taune shi, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, duk fa wannan budurin da
sukeyi Azeeza da Jamimah da Parveen basu san cewa sun bar kurkukun ƙaddara ba,
Saboda basa acikin hayyacin su.

Danish bai samu damar cin nashi naman ba, Jira yai sai da suka kammala ɗaya bayan
ɗaya ya raka su zuwa bakin ruwan nan suna yin wanka, da taimakon shi Haris ya samu
yayi wanka jikin shi ya ɗanyi mashi daɗi, bayan sun kammala Ya ƙara haɗo wasu
itacen Ya kunna masu wuta Kogon dutsen ya ɗumama sosai Sanyin da su ke ji ya washe,
sun cinye namansu duka, Kaɗan Danish ya samu yaci, kamar masu zaman makoki haka su
ka zauna kewaye da wutar da ke ci, Suna kallon junan su kowa da abunda ya ke saƙawa
aran shi, jemimah tuni bacci ya ɗauketa kamar jinjira haka Angel ta matseta a
ƙirjinta, haka azeezama bacci ne ya ɗauke ta, tana kwance saman jikin gabriel,
Haris ya langwa6a kanshi saman kafaɗar Danish, Batul ta ɗaura kanta saman kafadar
Angel, Parveen tana a kwance saman ƙirjin naufal, da hannu biyu ya tallabeta, haka
zalika Hannah tana arungume jikin Javed, sun natsu suna sauraron kukan namun dawan
dake hargowa acikin Dajin, ba zaka ta6a fahimtar yanayin da su ke a ciki ba, kowa
da abunda yake saƙawa aranshi.

*OBIE STATE*

In Abuja🏙

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E8🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

*Obie Estate*Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi, Aljannar duniya da babu tamkarta a faɗin


nahiyar Africa, Hamshaƙin Estate Ne Da ya haɗa tanƙama tanƙaman luxury Villas, da
duk wani Ababen more rayuwa, Kayan alatun da ke a cikinsa kaɗai abun kallo ne,
dollar ta yi kuka awurin ƙera ginin, yana da 6angarori da dama, kama daga katafaren
Gate ɗin shiga Estate ɗin wanda Jami’ae ne ke tsaron shi Sojoji da ƴan sanda Ko
sauro bai isa Ya ƙetara ƙofar shiga gidan ba saboda tsaron da ke gare shi, ba iya
mutane ba hada na’urorin da ke sanya ido ga duk wani mai shige da fuce, kowace
kusurwa ta villas ɗin tana maƙale da na’urorin cctv camera, daga bakin faffaɗan
gate ɗin Santalelen titi ne zai isar da kai ga Interior ɗin daular, akwai Harabar
ajiye motocinsu, Gardens da swimming pools area, Ga zoo wurin da ake kiwata
dabbobin gidan. Kowani Villa na estate ɗin Yana da nashi kayan alatun na more
rayuwa, parts ɗin da ke a cikin kowani gida ya haɗa da Haɗaɗɗun falullukansu
waɗanda suka ji jigunannun furniture, Bedrooms, Dining rooms, Kitchens, Bathrooms,
Laundry rooms, da sauransu, akwai Ƙayatattun dogayen benaye zubin twin stairs da U-
shaped stairs, Idan ma mutun baida ra’ayin Hawa Benan Kowane Villa yana ɗauke da
residential elevator wadda aka fi sani da lifter, tun daga Hawa na farko zata ɗauki
mutun har izuwa hawa na Uku, dai dai da cokalin amfani na gidan babu wanda aka ƙera
a ƙasa Nigeria, kaf kayansu daga ƙasar waje ake shigo dasu, mai karfin imani ne
Kaɗai zai iya rayuwa acikin estate dinsu ba tare daya shagala daga yin ibadarshi
ba, sai dai ta inda masu rayuwa cikin gidajen zasu burge ka Allah ya hore masu
baiwar Ilmin duka na addini dana zamani, wayayyun mutanene masu daraja da ƙima a
idon duniya, Sun Iya takun su ba zaka ta6a Iya aibatasu ba, saboda kyawawan
ɗabi’unsu da halayansu, komai nasu is Extraordinary.

Tun da garin Allah ya waye masu aikin gidan su ke ta kai komo, kowaccensu ta yi
dressing cikin chef’s uniform launin farare, ƙwararru ne a 6angaren girke girke da
gyaran gida, basu wasa da aikin su, Suna ba lokacin mahimmancin sa, kuma suna
takatsantsan wurin kula da buƙatun mutanan gidan.

A tsastsaye su ke a Cikin Katafaren Kitchen ɗin gidan mai girman gaske, A shaƙe ya
ke da kayan Amfani, ko’ina a tsaftacensa ya ke tamkar ba amfani su ke yi da shi ba,
aiki su ke yi tuƙuri babu kama hannun yaro, Matasan Ƴan mata da manyan su, wasu
suna aikin wanke nama wasu suna yanke yanken kayan lambu agaban cutting board,
yayin da wasu su ke agaban manyan gass cooker suna kula da girkin da suka ɗaura,
akwai waɗanda ke a tsaye in front of kitchen microwave suna aiki.

Ƙamshin girkinsu ya karaɗe ko’ina tun daga cikin kitchen ɗin har izuwa Babban falon
gidan.
Babbar macace ta shigo kitchen ɗin domin duba masu aikin don ganin yadda komai ke
gudana, A ƙalla za ta kai shekara 40 a duniya, Ta kasance ɗaya daga cikin Masu yi
masu hidima a gidan, ita ce head maids shugaban ma’aikatan Cikin gidan, Macace mai
yawan fara’a ga son mutane, ma’abociya son Shigar fararen Kaya, A yanzu haka
pakistan ne a jikinta riga da wando farare ƙal anyi masu adon duwatsu launi daban
daban, ƙafarta na sanye cikin flat shoes, bakowa bace wannan face *DIVYA*
ba’indiyace amma sunfi kiranta da *HAJJATY* tun da ta shigo kitchen ɗin masu aikin
suka fahimci itace tazo dubasu nan fa suka ƙara dage damtse suna aiki duk don su
ku6uta daga faɗanta.

A hankali ta ke zagaye Kitchen ɗin, Hannayenta a goye saman ƙirjinta, ɗaya bayan
ɗaya take binsu da kallo, na ɗan wani lokaci kafin tayi masu gyaran murya, kusan
atare su ka ɗago suna kallonta, Hannu ta tafa masu

“Aikin ku yana kyau, You ladies Are doing a fantastic job, everything smells
delious, i’m sure ɗanɗanon girkin zaiyi daɗi kamar yadda ƙamshinsa ya ke da daɗin
shaƙa, Ina ƙara jinjina ma ku,” ta ƙarasa yi masu maganar tare da ɗaga masu babban
yatsan hannunta na dama alamar Jinjina.

Murmushi ne Ya bayyana akan fuskokin su, ba ƙaramin daɗi suke ji ba, Idan hajjati
ta yabe su, suna matuƙar sonta kuma suna girmamata saboda kyawun halayanta da
ɗabi’unta.

“Dame dame aka kammala ne”? ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu, Abla ce ta soma
Yi mata jawabi

“Kebab with chips, Beef shawarma, burger and pancakes,...” kusan abu goma ta
lissafa mata, Jinjina kai Hajjaty ta ɗanyi kafin ta ɗaura da cewa”Kada na katse
maku aikin ku, lokaci Yana ƙurewa, Ku hanzata ku kammala, “

“An aikawa Hajiya saratu Breakfast ɗinta!”? da sauri Safa tace”yanzu nake shirin
zuwa in kai mata, Nice nike duty part ɗinta” Gyaɗa kai Hajjaty ta yi.

“Okey, shirya min fresh fruit ki haɗa min da kakkauran tea,” Wadda aka kira da
Sarah ta amsa mata da toh, ba tare da 6ara lokaci ba ta shirya mata kayan marmari
a cikin ƙayataccen wooden tray, tare da cup of tea, ta miƙa mata hannu biyu tasa ta
kar6i tray din tare da juyawa ta fuce.

Bayan fitarta, Fira ta 6arke a tsakaninsu

“Safa ashe ke ce kike duty a part ɗin Aunty jarabatu zaki sha Masifa, “ Abla ce tai
mata maganar, murmushi suka saki, sophia tace”Ai hajiya saratu ba daga baya ba, In
dai wurin Iya masifane, Last time fa da naje kai mata abinci cewa ta yi wai na
gutsiri ƙafar kaza, hada cewa ita bata yarda damu ba, wama ya sani ko mun saka mata
guba acikin abinci donta ci ta mutu,” dariya suka saka

“Tana da wuyar sha’ani bata yarda da kowa ba, In ba wannan Mijin nata ba, Uban son
banza suruki da zaman gidan surukai Ko kunya babu” sophia ce tai maganar, Safa
tace”Ai koni na samu wurin zama agidan nan abunda zanyi kenan, waman taraka bati
siddan, shiyasa a kullum nake roƙon Allah ya bani bugun zuciyar family ɗin, Wlh
idan na Aure shi nadaina sakin baki ina bacci, nafilfili zanta yi akan Allah ya
dawwamar da auran mu don nasan maƙiya da mahassada ba zasu bar mu mu zauna lafiya
ba, Musamman Mahaifiyarshi uwar Ji da izza, kinga matar nan bata ɗaukar raini
batason Mu’amala da bare....” tun da ta fara zuba suke binta da kallon rainin wayau
saida takai aya tukunna Abla tace”you don’t ave sense, Dama najima da zargin
kwakwalwarki ba dai dai take aiki ba, Ko Jazz da muka raina wlh yafi ƙarfinki, Ni
kaina ba zance bana son Owais ba, amma ance abunda yafi ƙarfinka ka haɗa shi da
baka so” kwa6e fuska Safa tai”kiyi min fatan alkhairi kawai, Nima a hausa novels ni
ke jin irin hakan na faruwa, mafi yawanci zaki ga ƴar aiki ta auri ɗan masu gida,
wani sa’in ma mai gidan ta ke aurewa....” sautin dariyarsu ne Ya hana ta ƙarasa
maganar, suna fira suna aiki,

“Safa kina atare da wahala, in dai ko zaki cigaba da tunanin zaki samu abunda ki ke
so kamar yarda ki ke karantawa ahausa novels, Ni Bance baya faruwa ba amma Allah a
zamanin da mu ke ciki zaiyi wuya, mai kuɗi sai ƴar mai kuɗi, talaka sai ɗan talaka,
Ina jiye maki tsoron heart attack ya kama ki silar son wanda bai son Kina yi ba, a
ƙarshe ki ƙare a emergency room”

Dariya suka saki gaba ɗayan su, kwata kwata firar da suke yi bata ɗauke masu
hankali daga yin aikin su ba, manyan cikin su ne kadai basa magana sai dai idan sun
faɗi abunda ya basu dariya su ɗan murmusa.

“Ni takaici na magadan gidan nan basu da yawa, duk irin tarin dukiyar nan ace Iya
mutun goma sha biyar ne ke da gadonsu” Abla ce tai maganar.

Abla tace”Nikaina abun na damu na, Yana yi mun ciwo a zuciya, na rasa gane meyasa
basa son haihuwa, daga mai ƴa’ƴa biyu sai mai ƴa’ƴa uku, Allah ya hore masu wadatar
arziƙi sai ƴa’ƴa ne zasu gagare su? Abun na ƙona mun rai, komai nasu na rayuwar
turai, Mu da zasu taimaka su Aure mu, duk bayan ƴan watanni zamu dinga sakar masu
ƴa’ƴa tuni zamu cika famiy ɗin”

Maganar Abla ba ƙaramin dariya ta basu ba, Sofiya tace”Sannu kaza suma ai suna son
ƴa’ƴan, sannan bada son ransu bane ba su haihuwa, Ƙaddarar su ce ta zo masu ahaka,
naji labari a bakin Hajjaty saboda tafi mu daɗewa a gidan, Suna haihuwa amma ƴa’ƴan
basu zuwa da rai, A mace ake haihuwarsu yawanci da zarar sun yi haihuwar fari da ta
biyu zaiyi wuya kiga sauran sun rayu a matattu su ke haihuwarsu, Allah ni tausayi
suke bani, Musamman prime minister Hateem shifa Bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, shi
da matarshi Gimbiya mujeedat, ƴa’ƴa biyu duka mata, rashin haihuwarsu ba ƙaramin
gi6i yai masu ba arayuwarsu, Ki duba fa hateem shine yafi kowa arziƙi a family
ɗinsu daga shi sai sharafudeen,” mamakine akan fuskar Wasu daga cikinsu waɗanda
basu daɗe da fara aiki ba

“Abun da ɗaure kai, Kuma an duba lafiyarsu? Ko dai wata lalurar ce da suka gada tun
kaka da kakanni”?

“Ko ɗaya, Tun daga ƙasa Nigeria har zuwa ƙasashen waje an bincika lafiyar kowan nan
su, Ba su da wata matsala da ta shafi ƙwayoyin haihuwarsu, lafiyar su ƙalau, har
manyan malaman addini saida kakansu ya sanya don su bincika mashi meke faruwa a
zuri’arshi, Sakamakon ɗaya ne dana asibiti, basu da wata lalura,”

Jikin su duk yai sanyi, Basu ta6a sanin zancen haihuwar da matansu keyi yara suna
zuwa ba rai ba sai yau da sophia ta sanar da su.

“Allah mun tuba ka yafe mana, shiyasa akace zato zunibi koda ya kasance gaskiya,
Gulma ba ta yi rana ba, Mune kullum tsegumin mu akan suna yin irin rayuwar turai ba
su son haihuwa ashe ba laifin su bane, jarabtace daga Allah” murya asanyaye Safa
Tayi maganar.

Abla tace “Na tausaya masu, kuma In sha Allah zamu ta ya su da addu’a, akan Allah
ya yaye masu lalurar da ke damun su” shiru suka ɗanyi Na wani lokaci, daga bisani
Safa ta shirya Kayan breakfast ɗin Hajiya saratu A Babban tray ta jera mata su,
Bayan fitarta daga Cikin kitchen ɗin su ka ɗaura da wata firar, sam basa gajiya da
firar Familyn Obinna.

“Muna fa da gagarumin bikin ranar zagayowar Haihuwar Obie, Nasan za’ae shagali na
kece raini, za’a yi 6arin Dollar da pounds, Aranar zamu ga Zaratan ƴa’ƴan Obinna da
Jikokinshi waɗanda basa a ƙasar, Ina da tabbacin Owais ma zai halarta”

Fuskar Sophia ɗauke da farin Ciki tayi maganar, Abla tace”Anya ko Owais zai zo?
Kinsan fa halinshi, samun lokacin shi abune mai wuya”

“ai ko baiyi niya ba sai obinna Ya matsa mashi akan ya zo, Kinsan fa kaf cikin
jikokinsa yafi ƙaunar Owais, kowa yasan da wannan zancen, Kinga ko ba zai so ayi
shagalin nan ba tare da Owais Ya halatta ba,” acewar Abla

Murmushi Sopy tayi “Can’t wait to see Allah Ya nuna mana Lokacin, Dole naje ayi min
wankin ido, don na samu damar ƙare Mashi kallo”

“Da rabon kisha mari, Owais baya son Kallo Idan Yana magana mutun bai isa Ya ɗaga
ido ya kalle shi ba, Sannan ba’a katse shi, Sauƙin shi ɗaya Idan har kika karanci
halayanshi da ɗabi’unsa tsaf zaku zauna lafiya, mutunne mai sauƙin kai baida girman
kai, Yana da tausayi ga taimakon na ƙasa dashi.....” tun da ta fara jera masu
Kyawawan halayanshi bata tsagaita ba har saida Landline ɗin dake a bakin ƙofar fita
kitchen ɗin ta yi ringing tukunna ta dakata da yin magana, da sauri Sophia ta fuce
ta je ta ɗauki landline ɗin Ta ɗaga kiran daya shigo, Cikin girmamawa tayi sallama,
Jikinta sai 6ari yake yi.

“Cofee....” Iya abunda Taji an furta mata acikin wayar, jin yayi rejecting yasa ta
zame ta daga saman kunnanta ta ajiyeta saman table, Dawowa Cikin kitchren ɗin Tayi
Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta.

Har suna haɗa baki wurin tambayar ta “Wanene Ya kira” kwa6e fuska tayi tare da
cewa”Nakasa gane muryar wanene acikinsu, Zaid ne ko Zayn, Coffee su ke buƙata, wa
zai kai masu”? Ta yi tambayar tana kallon sauran. Shiru babu wanda yace zai kai,
saboda Mugun tsoron shiga part ɗinsu suke Yi, saboda masifarsu,”

“Kinga tun da ke kika ɗaga Kiran nan Ki lalla6a ki je kawai ki kai masu awuce
wajen” Acewar Abla, Yamutsa fuska marwa ta yi, Ba yadda ta Iya don dole ta haɗa
masu coffee acikin mugs guda biyu ta ɗaura saman Plate ta fuce daga cikin kitchen
ɗin.

Tun lokacin da Able ta fita hannunta ɗauke da tray Na breakfast ɗin Hajiya Saratu,
Kai tsaye ta nufi Part ɗinsu, Tun kan ta ƙara sa gaban ƙofar ɗakin ta daddaɗan
ƙamshin turarenta Ya daki hancinta, macace mai son ƙamshi ga iya ɗaukar Wanka, A
bakin door ɗin Ta tsaya tare da Yi mata sallama, daga cikin ɗakin tajiyo muryar
Hajiya saratu

“U can come in” A hankali ta tura ƙofar ta shiga, Hajiya saratu tana azaune
tsakiyar Katafaren gadonta, jikinta na asanye da jallabiya, Kanta babu Kallabi
Kitson zanene all back Wutsiyar gashin ta sauko har saman kafaɗarta, fararen
idanuwanta suna a manne da farin glass medicated, tana da duhun fata mai kyan
gaske, Hutu ya zauna mata, Hankalinta gaba ɗaya yana akan tsadaddar Apple Laptop
ɗin da ta ke yin operating, ga dukkan alamu aiki ta ke yi.

“Once you’re done looking at me, please put the food on the table and leave my
room.” Muryarta ce ta fargar da Safa daga kallon ƙurullan da ta ke bin ta da shi,
Adabarbace ta gaishe da ita”Ina kwana Hajiya,” Guntun tsoki taja ba tare da ta amsa
mata ba, ko kallo ba ta ishe ta ba, asaman front table din bakin gadon, Safa ta
ɗaura mata tray din

“ko akwai wani abu da ki ke buƙata “? cikin Jin shakkarta Safa ta yi mata tambayar
don tasan halinta, in har bata ba mutun iznin tafiya ba, yai yunƙurin Juyawa zai
tafi atsawace zata ce mashi da Iznin wa!

Safa har ta gaji da tsayuwa shiru bata tanka mata ba, tamkar bata san da mutun
awurin ba, Halinta ne share mutane, sai da ta mula ta sha iska tukunna ta ba ta
zinin tafiya, bayan fitar Safa daga ɗakin, Ta dakata da yin aikin laptop ɗin,
Yunƙurawa tayi tare da kai hannu ta damƙo Burger Ta soma turata abakinta tana ci,
Bata wasa da Cikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ta handameta, ta kuma janyo Chicken
wings tana ci, baya tagama ta ɗauki bowl ɗin dake shaƙe da plaintain chips hannu
baka hannu ƙurya kamar mai fama da cutar yunwa, Saida ta lamushe komai, a ƙarshe ta
kora da ruwan lemu mai sanyi.

“Daɗina dake bakya wasa da Cikin ki,” Jin muryar Mijin nata yasa ta ɗago da eye
balls ɗinta akan fuskar shi, Daga cikin toilet ya fito waist ɗinshi ɗaure da towel,
Ƙirarshi tamkar ɗan wrestling, Kakkarfan mutunne Jibgegen ƙato, Kyakkyawan
ba’indiye Sumar kanshi akwance luf saman kanshi, Ga wani kwantaccen saje gefe da
gefen doguwar fuskarshi, ‘ ta6e mashi baki Tayi”meye haka? Bana hanaka yawo da
towel a qugunka ba? Yanzu da ace mai aikin nan tana acikin ɗaki ka fito fa?
Fuskarta aɗaure tayi mashi maganar, Matsawa yai kusa da ita yaɗan ranƙwafa saitin
fuskarta”yaushe zaki daina kishina? Murga mashi baki tayi”Bansani ba, Ni dai na
faɗa maka, Karka kuskura ka ƙara fitowa ɗaure da guntun abu a qugunka bana son
ta6ara” Ido cikin ido suke kallon Juna.

“Ƴa’ƴan mu Uku, kowan nan su Ya mallaki hankalin shi, Na yi tsammanin zaki rage
kishi na da kike Yi” harara ta watsa mashi”pls Ka wuce ka je ka sanya suturarka,
bana son ganin ka ahaka” Hannu ya kai yana ƙoƙarin warware towel ɗin gabanshi da
sauri ta damƙi hannayenshi aɗan fadace tace”Pravin meye haka? Yarinta ce fa
wannan”? Kashe mata ido ɗaya yayi fuskarshi ɗauke da murmushi yace”indai ina atare
dake bazan ta6a girma ba, saboda tsantsar ƙaunar da kike nuna min” ta6e baki Saratu
Tayi”naji yanzu kaje ka sanya suturarka, Sannan me kake son Ci insa akawo maka”
Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”abunda kika ci shi nake sonci abar ƙaunata,
naga ma har kin kammala naki breakfast ɗin why ba ki bari na fito munci atare ba?”
Ɗaure mashi fuska tayi “Pravin mu fa ba ƙananun yara bane da zaka tsaya kana
gayamin kalaman Soyayya, ko da ya ke nafa tuna kufa indiyawan nan bautawa soyayya
kuke yi har ku tsufa kuna abu ɗaya” cikin Zolaya ta ƙarasa maganar, gyaɗa kanshi
yai”komi zaki ce bazanji haushin kalamanki ba, Amaryata kuma uwargidana, sannan
uwar ƴa’ƴana abun alfaharina,” lumshe ido ta ɗanyi idan zata biyewa pravin ba zai
barta taci gaba da yin aikinta ba, gwanine a fagen Iya soyayya da daɗin baki, Ya
ƙware wurin Iya jan hankalin mace.

“Romeo, now your Juliet is at work, I’m almost done, zansa a kawo maka breakfast
ɗin ka, Ni da kaina ma zan baka abincin abaki” Amsa mata yai da Okey, Daƙyar ta
lalla6a shi Ya miƙe ya nufi Cikin ɗakin Yana tafiya tana satar kallon Bayanshi, a
gaban closet ɗin kayanshi Ya tsaya tare da kai hannu ya buɗe

“My Juliet ba ki faɗa min kayan da ki ke so In sanya ma”! Murmushi ta saki”Yau babu
aiki, ka samu hutu don haka Nafi sha’awar ganinka Cikin shigarku ta al’ada, Ya gane
me take nufi, riga da wando Ya curo kalar na mazan Indiya ya sanya su ajikinshi,
sun bi shape din jikinshi yadda kasan matashin saurayi saboda haɗuwarshi.

Bayan ya kammala Shirya kanshi, Hajiya saratu tasa aka kawo mashi breakfast, Da
kanta take bashi abaki Yana ci, mugun son shi ta ke yi, ta mutu akan pravin, kamar
yadda shima yake ƙaunarta, Allah Ya hada jininsu. Babu mai cin moriyarta irin
Mijinta, komai nata mallakin shi ne.

Lokacin Da Sophia ta ƙarasa Bedroom ɗin twins dake acan Upstairs Second floor,
Jikinta na kakarwa ta yi knocking ƙofar, almost 3 times kafin tajiyo muryar ɗaya
daga Cikinsu “you can come in” Numfashi taja kafin ta tura ƙofar Haɗaɗɗen bedroom
ɗinsu, Sanyin A.c da ƙamshin Turarensu ne Ya daki hancinta har sai da ta lumshe
idanuwanta saboda tsabar yadda ƙamshin Ya kurɗaɗa ta ƙofofin Hancinta, tunkan ta
shiga ciki Ta hango Ɗaya daga Cikinsu A tsaye Gaban tanƙameman dressing mirror Daga
shi Sai short a jikinsa launin ja, Yayin da twin brother ɗin shi yake a kwance
saman gado rabin jikin shi lullu6e da duvet. Kyawun surarsu sak irin na mahaifinsu
Pravin, tamkar yayi kakinsu.

Muryarta na ɗan rawa tace”Barka da safiya yalla6ai, Ga coffee ɗin Ina zan aje’ ba
tare da ya juya ya kalle ta ba yace “On my head” tuni tasha jinin jikinta, Batasan
Ya zatayi ba, Zaid dake a kwance saman gadon Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya saman front
table ɗin gaban gadon.

“Is that how your parent taught you to enter a room without saying ‘Assalamu
Alaikum ? Ɗakin kafurai kika shigo”?

Muryarshi tamkar ta mashayin giya

“Afwan yalla6ai, kafin in shigo saida na fara yin sallama, wata’ƙil baka jini ba
ne” A sukwane Ya juya yana binta ɗan iskan kallo

“Am I deaf?” girgiza mashi kai tayi muryarta na kakarwa tace “That’s not what I
meant, sir...” bai bari takai ƙar ƙarshen maganarta ba, ya nuna mata ƙofar fita
Aɗan tsawace ya furta “Oya Go back ki sake yin wata sallamar”
fuskarshi a murtuke yayi maganar, Idanuwan sophia tuni sun ciko tab da ƙwalla,
Jiki asanyaye ta juya ta koma waje.

Kware Murya tayi”Assalamu alaikum” shiru bai amsa mata ba, shiga ciki tayi”Sir nayi
sallamar in shigo? Coffee ɗin Yana hucewa”

Kafin Ya bata amsa Zayn dake kwance saman gado ya furta “I didn’t hear it. Go back
and make another greeting”

Tayi mamakin Jin muryarshi duk a tunaninta bacci yake yi, ashe idonshi biyu, “
Maƙoshinta tamkar zai 6allo ta ƙara kware murya wurin Yi masu Sallama, Tun tana yi
da marmari har ta fara gajiya, idanuwanta sunyi luhu luhu, A ƙalla tayi masu
sallama kusan sau Goma sha biyar ba tare da sun bata iznin shiga ɗakin ba, Har
saida Coffeen hannunta Ya salafce, sai da suka tabbatar Ta jigata sosai tukunna
Zaid yace da ita ta shigo ciki, hawaye nabin kuncinta ta shigo.

Kishingiɗe ta samu zayn ya ɗaura kanshi saman pillow, Ko kallon arziƙi bata ishe
shi ba, jiki na 6ari ta nufi Table zata ɗaura plate ɗin, Kakkausar Murayar zayn ce
ta dakatar da ita

“Don’t you dare put that on the table! Ki koma ki canza wani coffee ɗin, wa zai sha
abu ya salafce” juyawa marwa tayi tana kuka ta fuce daga Cikin ɗakin, ko a jikinsu,
sun Iya rashin mutunci da mugunta idan suka so, duk rana ta Allah sai sun sanya
ɗaya daga cikin masu aikin gidansu zubar da hawaye.

“Bro, when are we going back to America?” Zaid ne yai maganar while sitting on the
dressing table chair.

Yatsina fuska Zayn yai “we have no way out, Zaid, seriously, naji takaicin tursasa
mana dawowa Nigeria da obie yai, Ya hana rayuwarmu sakat, mu kaɗai mu ka tsone
mashi ido, ga Owais can kamar tsuntsu Yana shawagi a ƙasashen waje sai mu da muka
tsone mashi ido, nifa na gaji da halin dattijon nan, na rasa zaman me yake yi
acikin duniyar nan, duk shekara sai na sayi sabon likafi da miski na mutuwarshi but
yaƙi tafiya” Ranshi a6ace yake magana

Zaid dake kallon ɗan uwan nashi yana murmushi yace” I know what you’re mad about”
Yatsina fuska yai”Kai ma ɗin itace damuwarka, Ummin america ce silar komai, “ Yana
magana a harzuƙe ga dukkan alamu an fama mashi raunin dake acikin zuciyarshi.

“Everything about her is different. From the first day I saw her, I knew she was a
classy woman with a magnetic personality that could captivate any man.” lumshe ido
zayn yayi, bakomai yake tariyowa ba face farkon haɗuwarsu da ita.

“Naso ace ta amince min, ba abunda zai hana in aureta, zan tattara dukiyata gaba
ɗaya data mahaifiyata, da ta Dattijon can duka In bada a matsayin sadakinta, sai
dai kash ta nuna bata buƙatar aure arayuwarta, Zaid ya zanyi da raina? Ta sanya min
jarabar da bazan Iya gogeta ba” cikin jin shauƙi yake magana.

Harara zaid ya watsa mashi”nifa ban gane ba, Taya zaka dinga yi min magana akan
macen da nake son in mallaka? Kasan dai haramun ne muyi sharing mace ɗaya a gidan
aure ko?, awaje ne muke da ikon yin hakan duk da shima yin hakan haramun ɗinne”
ta6e la66ansa yai”Zaid ni ba zan yi jayayya dakai ba, just Kada kamanta ni ne gidan
kuɗi, na gaban goshin mommy, mata kuma saida kuɗi”

Dariyar shaƙiyanci zaid ya sakin kafin yace “Nima ina da daddy, kada ka manta komai
na mommy mallakinsa ne” Sakin baki Zayn yai saida Zaid ya karasa maganar tukunna
yace”Daddy ai ɗan koren mommy ne, mutumin da ke zaune agidan surukansa? Mommy ce fa
silar arziƙinsa, tayaya zaka hada kan ka da Ni? baya kasan Mune ke da dukiyar Ku
kuma Bayin mu ne, Sai mun ɗan watsa maku hatsi tukunna kuke samun wanda zaku
tsastsaga.....” Kallon al’ajabi Zaid yake bin ɗan uwansa dashi, yadda yake magana
Yana kushe mahaifinsu yai matuƙar ɗaure mashi kai, da ace wani bare ne yai wannan
maganar, hada shi za’a haɗu wurin cin ubansa, don sun tsani gorin da akeyiwa
mahafinsu akan yana zaune gidan surukansu.

“Assalamu Alaikum” Muryar Sophia ce ta katse masu firar tasu, daga wajen bakin
ƙofar ta tsaya”Yalla6ai ga coffee din na canza wani” har suna haɗa baki wurin
furta”we don’t need it!” ranta ya 6aci, duk wahala da tasha a ƙarshe sunce basu
sha, gyaɗa kai ta yi tare da juyawa ta bar part ɗin nasu.

“Zayn ba ka da mutunci, daddyn namu ka ke yi wa gori? Yunƙurawa yai tare da mikewa


zaune A harzuƙe yace”ƙarya nayi ne?ni ban ta6a ganin Mutun mai matattar zuciya
irinta daddy ɗinmu ba, har yau in na tuna gorin da akeyi mana raina 6aci yake yi,
Allah ya hore mana komai na rayuwa amma daddynmu yaja mana abun magana” Jinjina kai
Zaid yai”Nima fa abun na ƙona min rai yana yi min ciwo a zuciya, amma ya zamuyi
dole mu rungumi ƙaddararmu” saukowa Zayn yai daga saman gado Ya nufi toilet ya
shige, ya rage saura Zaid a ɗakin ya tasa mirror gaba yana kallon fuskar shi,
bakomai yake tunanowa ba face fuskar *UMMIN AMERICA*.

*MIDDLE STEP💋*

Daga alkalamin Boss✍️

Kishingiɗe yake saman lallausar Darduma, a Cikin Haɗaɗɗen Garden ɗin gidansa,
jikinsa na asanye da Voile sky blue riga da wando, Kayan sun zauna mashi, Fari ne
Ba irin sosai ɗinnan ba, dukkan wasu alamun tsufa sun bayyana akan fuskarshi da
jikinshi, A ƙalla zai kai shakara tamanin a duniya, daga ganin fatarshi hutu ya
zauna mashi, kan shi babu hula, tsufanshi bai 6oye mashi Kyawun fuskarshi ba,
tsabar kyan Da Allah yayi mashi zaiyi wuya mutun yai mashi kallo ɗaya ya kauda kai,
saboda haɗuwarshi da iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara
hurhura duk ta lullu6e ainin launin gashin nasa, daga gaban goshin sa akwai siraran
hurhura, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau ta yi mashi ba,Yana da tsayin fuska,
da Manyan idanuwa, Launin gray mutunne shi ma’abocin son ƙamshi, tamkar Da ruwan
turare ya ke yin wanka saboda tsabar yadda jikin shi ke fitar da daddaɗan fragrance
mai kwantar da tarzoma, Dogon gemun shi fari fat ya sauko har saman ƙirjin shi,
Yana da yalwatacciyar suma.

Dattijon Arziƙi kuma gwarzon Namiji mai ɗauke da suffofin Jagoranci, waɗanda su ke
da Jan hankalin Jama’a, mutunne shi mai daraja, Wadatar Arziƙi, kaifin basira da
bajinta, Jajircewa, Mai cikar kamala, ga iya mu’amala Da mutane, kaifi ɗaya ne kuma
bai Sa6a alƙawari,Ta ko’ina Allah Ya hore mashi, Kuma duk mun tarin dukiyar da ya
mallaka Hakan bai gusar dashi daga Yin ibadarshi ba, Hakokin Ubangiji kama daga
fidda zakka, sadaka, Da kyautatawa al’umma, mutun ne mai jin ƙan talaka, Shi nashi
arziƙin bai ɗaura mashi Girman kai da maƙo ba, Da kuma ƙyamar Talaka, kowa Nashi
ne wannan kenan.

daga bayan shimfiɗar shi Sandar shi ce jingine da bishiya wadda aka ƙerata da
zallar Gold kuɗin ta kaɗai sun ishi bawa yai maganin talaucinsa, Yayin da iskar
Garden ɗin take ratsa sassan Jikin shi, A hankali ya ke ɗan lumshe idanuwanshi yana
buɗesu haɗi da ƙarewa ƙayatattun kayan alatun da ke a garden ɗin kallo, a duk
lokacin da kewar jikanshi ta addabe shi yakan ke6ance kanshi daga Cikin Jama’a, ba
tare da sanin kowa ba, ya ke shigowa garden shan iska, yasan muddin masu kula da
lafiyarshi suka gan shi shi kadai agarden sai sun kira ya’yanshi sun faɗa masu daga
nan su kuma zasu rasa kwanciyar hankalinsu, har sai sunzo sun duba shi, sun
tabbatar da lafiyarshi tukunna hankalinsu zai kwanta, shi kuma bayason ya katse
masu aiyukansu, saboda suna ƙoƙari wurin zuwa ganinshi akai akai, Suna matuƙar
ƙaunarshi, Babbar damuwarshi a yanzu Jikanshi daya mutu akan ƙaunarshi yayi nesa
dashi, ya kwallafa rai akan son shi, ko ƴa’ƴanshi da ya haifa baya yi masu irin son
da ya ke yi mashi, gaba ɗaya hankalin shi na akan, kyawawan furannin cikin garden
ɗin, Da Halittun dake yawo acikinsa irinsu ɗawisu da filfilo Yana matuƙar son ganin
su.

Shu’umin ƙamshin Humran Jikinta ne ya daki Hancinsa, tun kan ta ƙaraso Ya ɗago da
idanuwanshi Ya kalle ta kafin Ya kawar da idon shi gefe ɗaya sam babu walwala akan
fuskarshi

Ƙarasowa tayi daga gabanshi Ta ɗan russina ta gaishe shi cikin girmamawa, shiru bai
tanka mata ba, hakan da yai mata yasa ta fahimci babu lafiya, ba ta ta6a ganin
damuwa akan fuskar dattijon ba sai yau, cikin sanyin murya tace”Yalla6ai na duba
acikin gida baka nan shiyasa nazo duba ka a garden, fresh fruit ne na kawo maka”
tai maganar tare da ɗukawa ta ajiye mashi kayan marmarin.

Da buɗar bakinsa sai cewa yai”Owais Ya dawo gidan nan”! murmushin gefen fuska
Hajjaty tasaki”yalla6ai owais Ai baya a ƙasar Ko kamanta ne” yamutsa fuskarshi yai”
Oh toh na manta, “har zata miƙe ta kuma cewa”Ko kana buƙatar wani abun ne”? Girgiza
mata kai yai”bana son kowa yasan ina a garden”! amsa mashi tayi da toh kafin ta
kama hanyar fucewa Kaitsaye ta nufi Entry hall na shiga gidan, Zuciyarta a cunkushe
take da tunanin meke damun dattijon? Ta ya ya zata Iya sani? Duk ta damu kanta
akanshi saboda Kyautatawar da yake yi masu bazata so ta gan shi a irin wannan
yanayin ba.

Adai dai Ƙofar shiga Falon suka ci karo da matashin dake ƙoƙarin fitowa, Dogo
siriri bai da ƙiba ko misƙala zarratin, Fari sol dashi daga ganin shi farar fata ne
bai haɗa komai da jinsin baƙaƙe ba, Jikinshi na sanye da Kayan likitoci farin
wando, Farar shirt daga sama ya ɗaura Lapcoat, Fararen idanuwashi na manne da farin
glass, Masha Allah Kyakkyawan gaske, Sumar kanshi har saman wuyanshi,

“Jazz! “ yanayin yadda ta ambaci sunanshi ne yasa shi cin burki, Yana kallonta,
fuskar shi a ɗaure yace “Me kike buƙata? Allura ko tiyata”? Dariya ta ɗan saki har
fararen haƙoranta suka bayyana.

“Kinga sauri nakeyi Yanzu aka kirani awaya, Ina da patient” yai maganar yana
ƙokarin bi ta gefenta Zai je wuce, ruƙo Hannun shi da tayi ne yasa shi yamutsa
fuska Hada bubbuga ƙafarshi atakure Yake kallonta

Cikin sanyin murya ta soma magana”Jazz kana araye obinna ya ke6ence kanshi a
garden? Hankalina ya tashi ganin damuwa akan fuskarshi....” Tunkan ta ƙarasa
maganar Jazz Ya zame glass ɗin idon shi, Yanayin fuskarshi Ya canza sosai, ba tare
daya ce mata uffan Ba ya nufi garden ɗin gidan, bin bayanshi tai da kallo fuskarta
ɗauke da murmushi don tasan muddin Jazz yaje garden, damuwar obinna ta ƙare, Saboda
kaifin basirar dake gare shi Tsab zaiyi mashi solving matsalar shi.
Kamar yadda Hajjaty Tabar Obinna haka Jazz ya same shi a kishingiɗe saman darduma,
ya ɗan lumshe idanuwanshi, bai ta6a kayan marmarin da ta kawo mashi ba.

Sautin muryar Jazz ce ta daki kunnanshi”ina gwanin wani ga nawa!Kai ni fa bani da


tamkar dattijon nan aduniya, Akanshi zan iya faɗa da kowa, duk mutumin da bai
daraja gemunshi ba babu mutunci tsakanina dashi....” Cikin ɗaga murya ya ke yin
maganar.

Hakan ba ƙaramin faranta zuciyar obinna yai ba, a tsanake yake kallon shi,

Kashe mashi ido ɗaya Jazza yai”ku fa tsaffin nan sai ana lallashinku ana
tarairayarku, da zarar mutun ya haura shekara 70 a duniya sai kaga ya fara ɗabi’u
irin na Yara, haba Uban mu maganin kukan mu, Idan Yunwa kake ji ba sai kai magana
abaka abinci ba? Shine don rigima zaka ke6e kanka cikin garden salon ka jamana
bala’e ace bamu baka kulawa yadda ya dace”? fuskarshi a ɗaure yai maganar, still
murmushine akan fuskar obinna, A faɗace Jazz Ya nuna mashi hanya da yatsan hannun
shi”maza tashi ka koma gida idan ba so ka ke Kaji ɗanyar geza a jikin ka ba, “
Wannan maganar da yayi tayi matuƙar bashi dariya sosai Obinna ya tuntsire da dariya
yana kallon shi, jinjina kai Jazz yai hada ruƙe qugu yace”Na fahimci rashin mabugi
ne ke damun ka, “ yai maganar tare da juyawa yana neman bulalar da zai buge shi,
Dariya hada dafe ciki obie yake yi, Yayin da yake kallon shi,

“Mutun bai rasa ci da sha ba, Sutura Allah ya hore mashi, wadatar arziƙi da ta
ƴa’ƴa mai yafi wannan aduniyar nan”? A faɗace yai maganar, kamar wanda aka 6ata ma
rai, alhalin nan duk cikin zolayane, ganin yayi nasarar sanya shi farin ciki yasa
shi matsawa kusa dashi.

Hannayenshi ya ruƙe acikin nashi”haba sanyin idaniyata, Dan Allah kafaɗin menene
damuwarka? Ashirye nake dana sanyaka farin ciki,” fuskarshi amarairaice yai mashi
maganar,

Lumshe ido obie ya ɗanyi kafin a hankali ya waresu kan fuskar Jazz

“Shi ne damuwata, Kafi kowa sanin hakan, bansan ya zanyi ba, inason ganin shi, ban
ta6a tunanin zai ɗauki tsawon lokacin nan batare da yazo kawo min ziyara ba,” farin
ruwane kwance acikin idanuwanshi, Hankalin Jazz ba ƙaramin tashi yai ba.

“Kamar yadda ka damu dashi, shima haka ya damu dakai! Ayyuka ne suka yi mashi yawa,
pls ka yi mashi uziri....”

“Jazz Inaso Owais Ya halacci shagalin da za’ayi na murnar zagayowar ranar


haihuwata, Amma nasan abune mai wuya ya iya zuwa” shiru Jazz ya ɗanyi yana kallon
fuskarshi.

“Idan zaka Iya bani dama zan sa shi yazo, Nayi maka alƙawarin hakan,” Yai maganar
tare da kai hannu ya ɗauki 6arin kanka Cikin kayan marmarin da hajjaty ta kawo ma
Obinna, Abaki Ya tura yana sha.

“Na bar maka komai a hannunka, Indai zaka Iya cikamin burina na ganin Owais Ya
halacci taron nan,”

“Kada ka damu dattijo, ko babu mota ba abun hawa sai owais yazo kasar nan, “ yai
maganar tare dakai hannu zai ƙara ɗaukar Ayaba, Obie Ya ka6e mashi hannu

“Jazz ka raina girman gemuna, Kowa yana jin shakkar tunkarata amma kai Ko kaɗan ba
ka Jin kunyar kallona ido cikin ido, “ dariya yasaki tare da cewa’Suma don basu son
ainihin wanene kakana ba, shiyasa suke jin shakkarka, “

“Ba aiki zaka je bane”? zaro ido waje yai sai lokacin ya tuna da mara lafiyan da
zaije dubawa, da sauri ya mike yana faɗin”Rigimamman tsoho ni nayi nan Allah ya
ƙara lafiya da nisan kwana, ‘ har ya miƙi hanyar zai bar garden ɗin ya kuma dawowa
ya zuƙunna a gaban farantin kayan marmarin ya ɗibi mai uban Yawa Kafin ya mike yana
faɗin”Allah yaja da ran dattijon arziƙi tsoho mai ran ƙarfe, An buga dakai an
barka, Namijin zaki uban dawa”

Murmushi ne ɗauke akan fuskar shi, idanuwanshi akan bayan Dr jazz har saida ya 6ace
ma ganin shi tukunna ya ɗauke idon shi.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E9🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

Wuraren ƙarfe biyar da rabi na marece, Aneelerh ta fito daga cikin toilet bayanta a
goye da baby junaid tayi mashi wanka ta ɗaura mashi towel, A saman Gado ta kawantar
da shi fuskar shi ɗauke da murmushi, ɗan zaro mashi ido tayi”Why are u smilling at
me”?
“Mommy daɗi nake ji, Angel zata dawo” aɗan ruɗe ta bi shi da kallo”Junaid! Waya
faɗa maka Angel zata dawo”? Da yatsan hannun shi ya nuna mata saitin zuciyarshi,
murmushi ta saki haɗi da ɗan girgiza kanta”my baby boy nima ina ji araina ƴar
uwarka ta kusa bayyana in sha Allahu nan bada jimawa ba, in dai tana numfashi a
doron duniyar nan....”tunkan ta rufe baki yace”Mommy Angel tana sona? ɗaga mashi
kai ta yi alamar eh”Angel tana sonka junaid tun kafin zuwanka duniya ta ƙwalla fa
rai akan son ganin ka,”

Ta yi maganar tare da juyawa ta nufi gaban mirror ta ɗauko Mayukan shafawarshi, a


saman mattress ɗin ta ɗaura su, ta soma shafa mashi ajikinshi.

“Aunty Aneelerh,!” muryar zahra ce daga waje take kwaɗa mata kira, A hanzar ce
Junaid ya buge hannun Aneelerh data ruƙe shi, ya damƙi towel ɗinshi dake yashe
saman katifar, Lamarin yai matuƙar ɗaurewa Aneelerh kai, ganin yadda yake
kiciniyar ɗaure qugunshi, duk don saboda zahra kada ta gan shi babu kaya, Kafin
zahra ta faɗo ɗakin tuni ya kammala maida towel ɗinshi sai faman haki yake yi, ƙasa
ƙasa da murya tace”junaid ban kammala shafa maka man ba”, turo mata baki yai”Ni ae
bana sho Aunty zahra ta gane min abuna, idan ta tafi sai ki ƙarasa shafa
man....”kumshe dariya Aneelerh tayi abakinta.

“Aunty Aneelerh Abie da daddy suna son Yin magana dake, Na riga na faɗa masu komai
game da tada zancen 6acewar su tajuddeen, sun amince da yin hakan” Farin Ciki ne ya
bayyana akan fuskar Aneelerh”Zahra, zanje yanzu mu yi magana da su, Ga junaid nan
ki cigaba da shafa mashi...” kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon toshe mata baki da
Junaid yai da tafin hannun shi, Kallon fuskarshi tayi, 6acin rai ta gani akanta.

Ta6e baki zahra tayi idonta akan fuskar Baby junaid,”Kin ga Aunty Aneelerh Ki tashi
ki je suna a palour, bana so damar nan ta wuce mu, Ki barni dashi zan ƙarasa gyara
mashi jikin” amsa mata ta yi da toh, kafin ta sakko daga saman gadon ta nufi closet
ta buɗe ta curo mayafinta bayan fitarta ɗakin, Junaid ya takure kanshi jikin
headboard na gadon, lallashinshi ta soma yi”haba habibina meye na 6ata fuska nifa
ma mommyn ka ce, zo nan in gyaran maka jikin ka, Maƙe mata kafa ɗa yai”so ki ke ki
kalle mun abuna, ni banso, Zan jira mommy ta dawo”

ɗaure fuska tayi ganin zai 6ata mata lokaci yasa ta haye gadon ta cafko shi, ya
dinga kuka yana shure shuren ƙafa, daƙyar ta samu ta shafe mashi jikin tana
fadin”ɗan jakar uba, Jiki duk madara, da ace baka da kyau ko kallo baka ishe ni ba”
tur6une mata fuska yai hada jifarta da harara, Miƙewa tai daga saman gadon ta sauko
ta nufi closet din kayan su ta ɗauko mashi riga da wando, ta dawo ta zauna gefen
shi, a tsanake ta zura mashi a jikinsa, tunkan ta kammala Wayar Aneelerh ta soma
ringing
“Wayar mommy tana ringing” junaid ne ya sanar da ita

“Ni bana ɗaga wayar mutun idan bashi ya bani izni ba” gatsina mata hanci yai”Angel
ce ke kira aunty zahra dan Allah ki ɗaga, kada ta katse” kwantar da kanshi tai
saman ƙirjinta, faɗi yake ni ki sake ni, inje in ɗaga kiran Angel” taƙi barin shi
ya motsa, suman kanshi take shafawa da hannunta, shiyasa ya ke gudun zahra ta ɗauke
shi, kamar ta samu lallausan bready haka take daƙuna shi.

Bayan fitar Aneelerh A palour ta taras da Uncle ɗan Iya tare da abie hada Mommy da
Ummi zaune saman Sofa, cikin girmamawa ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe su, A
mutunce suka amsa mata, daga ƙasan sofa ɗin da mami da ummi ke azaune ta jingina
bayanta, tare da sunnar da kanta tana jiran jin me zasu ce.

Gyaran Murya uncle ɗan Iya ya yi, hakan yasa ta ɗago da ido ta kalle shi, ya ƙwama
farin Glass a fuskarshi Ya ɗan sauko har saman karan hancinsa, a halitta baƙi ne
wulik, kamar ba jinin Abie ba, yana da Manyan idanuwa hancin shi a wargaje yake,
Haka bakin shi manyan la66a ne dashi, wandon shadda ne a jikin shi Daga sama Malun
malun ce babi Ƴar Ciki, Ya ƙwama Hula Akanshi Ga uban sanƙo, a saman Kujera mai
mazaunin mutun uku suke zaune su Biyu, gyaran murya yai kafin ya soma magana”Zahra
ta faɗa min komai, a gaskiya kun kawo shawara mai kyau, Kunyi tunani na hankali”
yana magana yana watsa hannayenshi Ɗabi’arsa ce Yin hakan.
“bai kamata don abu ya haura shekaru da faruwa muja baki muyi shiru, tun da har
yanzu bamu da tabbacin suna araye ko sun mutu! Idan ko suna araye ba ƙaramin
ganganci mu kayi ba, Na watsar da zancen 6acewarsu, wata’ƙil Silar tada zancen
Allah Ya bayyanar mana dasu.....” tun da ya soma magana suka natsu suna
sauraronshi, Aneelerh ta duƙar Da kanta ƙasa Farin Ciki duk ya cikata, gani take
kamar ma har an riga an ganso su.

“In sha Allah zanyi magana da ziyad babban ɗan jarida ne muddin labarin nan ya je
gare shi ina mai tabbatar baki da cewa cikin ƙanƙanin Lokaci Duniya zata ɗauka
tamkar bai jima da faruwa ba, a manyan Kafafan sada zumunta za’a yaɗa labarinsu,
irin su BBc, CNN, and ONt, muma kuma zamu bada gudummuwar mu, wurin Yaɗa hotunansu
a social media”

Bayan Uncle ɗan Iya ya takaita da zancen nashi Abie ya ɗaura da cewa”kafin Gobe ki
tabbatar kin tattara duk wasu hotunansu Tajudden kin tura mashi, Sannan Adage da
addu’a duk danasan kina ƙoƙari wurin yi masu, Mamie ta fadamin kullum sai kin tashi
yin nafilfili dare, naji daɗin jin hakan sosai, Allah yayi maki albarka” amsa mashi
ta yi da ameen, Mamie tace”Ubangiji Allah ya bayyanar mana dasu, Allah yasa silar
tada zancen 6acewarsu da za’ayi su bayyana, mungode sosai” godiya suka hau yiwa
Uncle ɗan Iya, kafin daga Bisani Aneelerh ta miƙe tare da yi masu sallama ta Nufi
bedroom ɗinta tsabar zumuɗi kamar zata tashi sama, lokacin da ta shiga ɗakin, A
kwance ta samu zahra tana fuskantar ceilling hannunta a ruƙe da wayarta, ga dukkan
alamu Chatting take Yi, Baby junaid tuni ya jima dayin bacci yana kwance saman
ƙirjinta. Jin motsin shigowar Aneelerh Yasa ta ɗan kawar da kanta daga kallon wayar
ta take Yi ta kalli Aneelerh tunkan ta ƙarasa shigowa ciki Ta lura da tsantsar
farin Cikin dake akan fuskarta

“Yah aunty Aneelerh Ina fatan komai lafiya”tana murmushi tace”abie yace in tura ma
Uncle hotunansu tajuddeen wlh bakiji daɗin da naji ba,”Zahra na murmushi tace”Allah
yasa Adace sister, nima zan tayaku sharing a instagram page ɗin mu,” Godiya
Aneelerh ta yi mata, ringing ɗin wayarta ne Yaja hankalinta ga duban saman pillow,
Da sauri ta nufi wayar takai hannu ta dauke ta

“Bansan wanene ke kiranki ba, Tun ɗazu bayan kin fita wayar ke ta ringing ban daga
ba”

“Why ba ki ɗaga ba zahra, Surukata ce fa” ta6e baki zahra tayi”matar da ke son
ƙwace mana baby junaid ɗinmu ai ƙwara daban ɗaga ba” picking call ɗin Aneelerh tai
tare da kanga wayar a kunnanta.

Cikin girmamawa tayi mata sallama”Assalamu akaikum” on the other hand Hajiya adama
ta amsa mata da”Wa’alaikum salam daughter In law, ina kika shiga inata kira ba
aɗagawa”? aneelerh tamkar tana agabanta tace”Bana akusa da wayar ne bansan kun kira
ba” gaisawa sukayi kafin hajiya adama tace”guest what”? ɗan zaro ido Aneelerh ta
ɗanyi tana wurwurga eye balls ɗin ta can tace”kun dawo ƙasar”? Sautin dariyar
hajiyar adama ne yasa ta saki murmushin farin ciki.
“Mun dawo, in sha Allah end of this month zamu shigo Abuja, two days kin daina
kiran layina Why? Ko dan saboda kada na ƙwace maki Yaro”? Cikin Jin kunyar
maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, wlh ina ta zucci zuccin in kira ki
Allah ne bai nufa ba” Tai maganar a yayin da take kokarin zama saman stool, Ta gaji
da tsayuwar, Zahra ta kasa kunne tana sauraron Firarsu.

“Idan ma don saboda dashi ne to ki kwantar da hankalin ki, babu wanda zai raba ki
da ɗanki, Munyi magana da abdallah Ya fahimtar dani game da cutuwar da zakiyi idan
muka ce zamu raba ki da shi, Ni kaina bazanso Inyi silar sanya ki baƙin ciki
ba....” buɗe ido Aneelerh Tayi Wani irin farin cikine tsantsa akan fuskarta, Zahra
da ta tsareta da ido tana kallonta, sai faman yi mata mimi da baki takeyi donta
fada mata me Hajiya adama ke fada mata wanda yasa ta farin ciki

“Zan kira mamin naki mu yi magana, Sannan akwai wata gagarumar kyauta dana shirya
maki idan mun zo zaki gani” Hawayen farin Ciki ne su ka wanke fuskar Aneelerh, kasa
jurewa tayi batasan lokacin da kuka ya kubce mata ba. Muryar Hajiya adama a ɗan
ruɗe take fadin Aneelerh why? Kuka kuma? Meya faru? cikin shessheƙar kuka tace mata
kukan farin Cikine, taji daɗin ƙaunar da take nuna mata, tana alfahari da su, samun
surukai irinsu abune mai wuya, Hajiya adama taji daɗin daɗaɗan kalaman da Aneelerh
take faɗa mata, tsawon lokaci suna waya Kafin daga bisani Tayi mata sallama,
Idanuwanta acike tab da ƙwalla ta wurga su kan fuskar zahra tambayarta ta shiga me
suka tattauna da Hajiya adama? Nan Aneelerh ta sanar da ita komai, Fasa ihu zahra
Tayi tare da jefar da wayarta gefenta, ta sauke junaid daga saman jikinta a hankali
ta kwantar dashi, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi Aneelerh ta rungumeta
kamar zata maidata ciki, Farin Ciki duk Ya cikasu, Miƙewa Aneelerh tayi bayan ta
ajiye wayar gaban mirrror, Rawa suka soma takawa ita da zahra, hada ɗebo shoki suna
kifawa saman goshinsu, Yayin da suke sakin Dariyar murna.

*EVIL FOREST*

A ƙalla yau satin su ɗaya acikin kogon dutsen ba tare da sun motsa ba, saboda
marasa lafiyan cikinsu, jikinsu yai tsauri, duk da haka suna ƙoƙarin basu kulawa ta
musamman, Danish Ya haɗa masu garin maganin da su ke sha suna samun warakar raɗaɗin
ciwonsu, A cikin gorar ruwansu ya ke jiƙa masu maganin, Bayan haka duk in za su yi
tsarki da ruwan zafi su ke yin shi, danish ne yai masu dabarar yin hakan,
Alhamdulillam Jikinsu Azeeza yayi kyau sauƙi ya samu, ba su rasa ci da sha ba,
kullum ne sai sun ci abinci sau uku, Danish ne ke ƙoƙarin yi masu farautar abunda
zasu ci wani sa’in zoman daji yake kaso masu ko tsuntsaye hada kayan marmari ya ke
samo masu, saboda su ya ke hana idonshi bacci, A zaune yake kwana shi da Angel
dinsa, tana ɗebe mashi kewa, shaƙuwace mai ƙarfi a tsakaninsu.
Burinsu marasa lafiyar cikinsu su ƙarasa wartsakewa ko sun samu su cigaba da
tafiya.

Yau tun da sanyin safiya ta soma Jin hayaniya acikin kunnuwanta, ƙasa ƙasa take iya
jin maganganunsu, Tsantsar mamaki ne ya kamata Jin muryoyin su Batul, tamkar a
mafarki, a harzarce ta buɗe idanuwanta tare da miƙewa zaune tana ƙarewa Kogon
dutsen kallo, Haris ne kaɗai ya rage a kwance yana bacci, Ya ƙudundune kanshi cikin
bargo, ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya ta soma yi, da wata irin kasala ta miƙe
tsaye tare da yin hamma, abu biyu ya ɗaure mata kai da farko tayi tsammanin zata ga
su Azeeza sai dai bata kowa ba.
Hankalinta A matuƙar tashe ta fito tana ƙarewa Dajin kallo, Kamar daga sama tajiyo
muryar Jemimah tana ambaton Sunan da take kiranta dashi”Genie!’ ras taji gabanta Ya
faɗi, A ruɗe ta wurga ƙwayar idonta kansu, Gaba ɗayansu ne banda Haris, Yau wata
rana sun fito daga kogon dutse jiki yayi kyau, Sai wasa suke Yi suna tsalle tsalle,
Farin Ciki duk ya cikasu, Bakunansu awashe kamar gonar auduga, ba ta san lokacin da
hawaye suka soma wanke fuskarta ba, Nan ta ke ta zube saman gwiwowinta tare da kifa
kanta ƙasa ta yi sujjada tana godewa Allah da ya nuna mata wannan ranar, Haƙiƙa
tayi farin ciki mara misaltuwa, kafin ta ɗago daga sujjadar Jemimah ta watso da
gudu ta faɗo saman bayanta, sai tiƙar dariya ta ke yi tana fadin”Genie Daɗi kamar
zai kashe mu, Wlh daɗi muke ji, wannan wurin mai kyau bamu ta6a ganin irin shi ba,
Genie Yau zamuje gidan daddynki ko”? Kasa ɗagowa Angel tai, wani irin yanayi take
jin kanta.
Ƙarasowa Azeeza tayi Hannunta ruƙe cikin na Gabriel, Sauran Ƴan uwansu na abiye da
bayansu, agaban inda tayi sujjadar suka tsaitsaya suna kallon ta
“Angel muna son yin magana dake”muryar parveen ce ta ratsa kunnanta, daƙyar ta iya
haɗiye kukan da ke shirin kubce mata ta ɗago da kanta, tare da zagayo da hanneyenta
biyu ta ruƙe Jemimah gudun kada ta faɗo daga bayanta
Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, tun daga kan fuskar Azeeza dake ta sakin
murmushi, fatar jikinta tayi haske sosai dama ita can launin skin ɗinta na farar
fata ne, da launin gashinta, ta rame sosai ta ƙara komawa ƙarama. ɗauke idon ta
tayi daga fuskar Azeeza ta mayar dasu kan fuskar parveen, itama ta faɗa duk sunyi
haske kamar fatalwu, Murmushi ta ɗan saki tare da kallon Batul dake a tsaye tana
sakar mata murmushin ƙauna.

“Rabin rai kin tashi lafiya, Nasan kinyi mamakin ganin mu awaje muna shan iskar
duniya, Danish ne ya fito da mu waje kuma yace da zarar ya sama mana abinci mun ci
zamu kama hanya” lumshe ido Angel ta ɗanyi tare da ware su kan fuskar Hannah.

Muryar Gabriel ce ta janyo hankalinta ga kallon shi”Muna so muyi maki godiyane akan
irin ƙoƙarin da kikayi mana, Angel kin cancanci ayaba maki, babu wasu kalmomi da
zamu Iya yin amfani da su wurin yi maki godiya ke da Danish, Allah ne kaɗai zai Iya
biyanku” Cikin sanyin murya tace”Allah shine abun godiya Gabriel, Alhamdulillah ala
kullu halin, ina taya ku murnar Samun ƴanci arayuwarku, Kuma inayi mana fatan Allah
ya bamu sa’a adukkannin abunda muka sa agaba, Ubangiji Allah yasa ƙarshen wahalar
mu ce tazo....” addu’o’i ta dinga jera masu suna amsa mata da ameen, Sai da ta kai
ƙarshen maganarta, muryar jemimah ta katse ta”Genie ba zamu ƙara komawa kurkuku ba
ko?” Batul tace”har abada mu da kurkukun ƙaddara, Daga nan sai Gidan daddyn Genie,
ko kina son komawa ne”? Zaro ido tai tare da girgiza kanta”banso, Allah ya tsinema
su da tsohuwa zafreen, muguwa idan mu ka yi ƙarfi sai mun kashe su, damu da daddyn
Genie, zamu rugurguza kurkukun kowa ya huta, Kuma zamu ƙwato ƴan uwanmu da ke a
wurinsu” ranta a6ace ta ke yin magana, kumatunta sunyi jawur da su.
Angel tace”In sha Allah Jemimah mune zamu kawo ƙarshensu, Allah sai ya saka mata
cin zalunmu da su ka yi, haƙƙin mu ba zai ta6a barinsu ba, tun agidan duniya zasu
fara gir6an abunda suka shuka” tana magana hawaye nabin fuskarta.

“Angel Ba ki faɗa mana ina ne nan ba? Munga wasu abubuwa da su ka ɗaure mana kai
waɗanda bamu ta6a ganinsu ba ko a mafarki,” Javed ne yai mata maganar fuskarshi da
alamun ruɗu.
“Angel munga kalar ganyan da ake kawo mana muna ci a kurkuku,” still fuskarta da
murmushi ta yunƙura ta miƙe hannunta ruƙe da Jemimah, Gabriel ta kalla”meyasa baka
yi masu bayani ba”? Ta6e la66ansa yai”sun fi so suji daga bakin ki,” Ajiyar zuciya
ta sauke tare da cewa”Okey, Ku jira Danish Ya dawo, idan muka kammala cin abinci,
muka kama hanya zanyi maku bayanin komai” amsa mata su ka yi da toh. Kafin wani ya
ƙara cewa wani abu, Motsin tafiyar Danish ta janyo hankulansu ga dubanshi.

A tsanake ya ke yin tafiya yana tunkaro su, hannun shi ɗaya a ruƙe da kwandon da ya
haɗa masu saboda ajiyar kayan abincin su, tunkan ya ƙaraso Jemimah ta sauko daga
bayan Angel, da gudu suka nufe shi ita da Azeeza da parveen, atare suka faɗa mashi
tare da ƙanƙame shi suna sakin dariyar farin ciki.

Ganin shi suke yi tamkar mahaifinsu, saboda kyautatawar da ya ke yi masu wurin yin
jinyarsu, nufo wurin su Angel tayi tana faɗin”Sannu da dawowa My Man, Na farka ban
gan ka, meyasa baka tada ni mun tafi atare ba” ta yi maganar tare da kai hannu ta
ruƙo hannun Kwandon da ya ruƙo, sakar mata yai ta kar6a tana leƙa cikinsa Kayan
marmari ne ashaƙe cikin kwandon.

Da sauri ta ɗago suka haɗa ido da juna, murmushi ta sakar mashi”sannu da ƙoƙari,
duk namu ne wannan,” ɗaga mata gira yai alamar eh, “mun gode Danish, Allah ne kaɗai
zai Iya biyanka,” lumshe mata ido yai kafin ahankali ya ware su akan fuskarta.

Su Parveen sun ƙi sakin jikin shi tun da su ka rungume shi ba su ɗago ba, faffaɗan
tafin hannun shi ya ɗaura asaman kawunan su a hankali ya ke shafa sumarsu kan su,
sai ƙara ƙanƙame shi suke Yi, a hankali ya furta masu”Ya Jikin naku”? Jemimah da
Azeeza suka haɗa baki”Ai mun warke, Gidan daddyn Genie zamu je yau”
Ganin sunƙi sakin shi yasa Angel yi masu magana”ku sake shi mana, Ko mun samu muyi
sauri muci mu tafi, idan har ba barin Dajin nan mukayi ba Hankalina ba zai kwanta
ba” Jin maganarta yasa suka sake shi, Ya ruƙo hannun Azeeza dana Jemimah suka jera
atare suna tafiya, Cikin Kogon dutsen su ka koma gaba ɗayansu, suna shiga suka
tarar da Haris zaune shi kaɗai, bai jima da farkawa daga bacci ba, A ƙasa kowanansu
ya zauna, Angel ta curo kayan marmarin ta rarrabamasu, A tsanake suke sha suna
kallon Juna, bayan sun kammala sha, Suka fara shirin tafiya, Ba tare da 6ata lokaci
ba, Angel Ta goya jemimah abayanta da mayafi ta ɗaureta, Gabriel Ya goya Azeeza
abayanshi, sai daɗi suke ji an goyasu har gwalo suke Yima Parveen, Batul kuma ta
Goya Back pack ɗin Unaiza abayanta, Javed Ya ruƙe masu akwatin kayansu, basu bar
komai acikin kogon ba, Hatta Gorar ruwansu acikin kwandon kayan marmarinsu su ka
sanyata, Parveen ce ta ruƙe kwandon a hannun ta.

Matafiya sun shirya tsaf saura tafiya ta rage masu, kafin fitarsu daga kogon dutsen
saida Angel ta yi masu addu’o’i tabi kowan nan su ta tofe shi tun daga ƙasa har
sama ko da ta zo kan Danish sai ce wa yai me take yi haka? ta daina watsa mashi
yawu baiso, dariya tayi batare da tace mashi komai ba, Danish ne ke ruƙe da Haris
saboda rashin ƙwarin Jikin shi.
Suna tafiya suna fira a dokar dajin, Su parveen sunga abubuwan da suka ɗaure masu
kai, Komai suka gani sai sun tambayi Angel menene shi? Lokacin da rana ta ƙwalo
Kowannansu Ya zazzare idanuwanshi suna kallon Sararin samaniya inda rana ta hudo,
Angel sai ƙoƙarin hanasu takeyi akan su daina kallonta, gudun kada hasken ranar ya
kashe masu idanuwan su.

Bakomai yasa su yin hakan ba face tsantsar mamaki da al’ajabi, su fa duk ɗaukarsu
Fitila ce aka ajiye sama, kamar dai yadda ceiling ɗin ɗakin su na kurkuku Yake,
Parveen sarki kwa6a magana da ta gaza jurewa tace da Angel ta faɗa mata tayaya akai
har aka ɗaura fitilar sama? Ita bata ta6a ganin fitila mai hasken ta ba,” Dariya
Angel tasaki tare da cewa”Kai parveen Nafa ta6a faɗa maku saboda gudun haka, Rana
ce wannan da kuke Gani, Babu wanda ya ɗaurata Yana daga cikin halittar ubangijin mu
Allah, bayan ita akwai Wata da taurari suma duk Allah ne ya halicce su, Idan Dare
yayi zan nuna maku su, taci wahala wurin wayar masu da kai daƙyar ta samu suka
fahimce ta, kusan saida ta maimaita masu karatun data koya masu tukunna suka Iya
tunawa, A ƙalla sun shafe awanni suna kutsawa cikin Dajin babu alamun zasu shigo
cikin Garin, Wani irin kurman Dajine ta ko’ina acunkushe yake da tsirrai.
Gaba ɗaya sun gaji da tafiya, Dama jikinsu bai saba da wahala ba, Ga6o6in jikinsu
duk sun raunata, Mutun Biyune basu jikata ba, Jemimah da Azeezah, hankalinsu kwance
Har bacci ya ɗauke su a goye sai daga bisani suka farka,
“Wlh mun gaji Angel, Wai haka zamu dinga tafiya ba tsayawa? Ƙafafuwana duk sun
rurruƙe, Ga yunwa inaji” Parveen ce tayi maganar,
“Ya ki ke so muyi parveen dole muyi tafiya da da halima hada gudu, in ba haka ba
zamu ƙare acikin Dajin nan ne,” fuskar Angel ayamutse ta yi maganar,
Danish duk yana sauraronsu, hankalin shi na akan Haris daya ruƙe.
Parveen ta hanasu sakat, don dole Naufal Ya goyata abayanshi, Jemimah hada
tsokanarta”ƙatuwa dake dole sai an maki goya irin namu” Harara parveen ta watsa
mata. Ba tare da tace komai ba.
Zogin da ƙafafuwansu suka fara yi masu ne yasa suka yada zango agaban wata ƙatuwar
bishiya suka zazzauna suna faman yin haki, Gorar ruwa parveen ta curo masu, Bayan
tasha ta miƙa ma Naufal yasha ya miƙa ma Hannah, sai dakowa yasha ruwan, Sun natsu
suna faman lumshe idanuwansu,
“karfa kuyi mana bacci anan, bamu gama tafiya ba, naga kuna rufe ido,” Angel ce
tayi masu magana, Fuskar Parveen atur6une tace”kaɗan zamuyi, “ batul Ta natsu tana
kallon Bishiyoyin dake a kewaye dasu,

“Angel Su waɗannan basu gajiya da tsayuwa ne”!? Fuskar ta aɗaure tayi maganar babu
alamun wasa
“Su wa kike nufi” Angel ta tambaya tana kallon fuskar Batul, Da hannu ta nuna mata
Bishiyoyin dake fuskantarsu, Ɗan zaro ido Angel tayi tare da kallon Danish dake
kallon fuskarta, kiris ya rage ya saki murmushi jin wautar Batul. hankalinta a
kwance taci gaba da cewa”tun da muka taho suke ta tsayuwa babu motsawa, Itama rana
sai binmu takeyi da gudu duk inda mukayi sai na ganta, to wai su basu gajiya ne”?
Kalamanta sun rufe ma Angel baki ta kasa bata amsa, daƙyar ta iya cewa”Haka Allah
ya Halicce su Batul”

Gabriel da ya ƙumshe dariya abakin shi yace da ita”ke yanzu idan waɗannan
bishiyoyin suka motsa zaki tsaya? Har kina da bakin cewa Basu gajiya da tsayuwa”?
Sai lokacin ta ɗan saki murmushi ba tare data kalle shi, shiru su ka ɗanyi na wani
lokaci, Har bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukar su Jemimah ta fara ambaton fitsari take
ji, Ɗaukarta Angel tayi tare da miƙewa ta kalli Danish”Zanje nakaita tayi
fitsari,”lumshe mata ido yai tare da cewa”No, basai kunje nesa ba, Zata iya yi ko
abayan bishiya ne” Amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi bayan bishiyar da ita,
bayan sun dawone tace dasu su tashi suci gaba da tafiya kada dare yayi masu anan,
Miƙewa su kayi jiki duk ba ƙwari, Ta maida goyan Jemimah gabriel ma ya goya
azeezarshi suka dasa da tafiya.

Allah ya tsare su tunda suke tafiya babu wata muguwar dabbar da suka ci karo da
ita, Sai dai sautin koke kokensu da suke ji acan wani sashe na Dajin, Sunyi nisa da
tafiya kwatsam Ba zato ba tsammani Akuya ta faɗo wurinsu kamar an jehota, a matuƙar
figirce suka watsa da gudu cikin dajin duk su ka tarwatse saboda tsabar firgitar da
su ka yi.

Hankalinsu Danish ba ƙaramin tashi yai ba, babban abunda suke jima tsoro kada wata
dabbar ta handamesu, Mutun biyar ne suka watse waɗanda suka rage Danish ne sai
haris shima saboda Ya ruƙe shi ne ya kasa guduwa, Gabriel dake goye da azeeza sai
Jemimah da Angel, Basu ta6a ganin akuya ba sai yau, shiyasa Suka watse, mun shigo
uku Danish! Ya zamuyi? Angel ce ta ambaci hakan, Bai amsa mata ba ya kwantar da
Haris jikin bishiya da gudun gaske ya faɗa Cikin Dajin don Ya tattarosu.
Jemimah ta ƙanƙame angel sai satar kallon akuyar take Yi, ta yi tsaye tana Lasar
baki, Ciyawar dake awurin take Ci,
Ran Angel ya 6aci, Duwatsu ta tsinta a kasa ta dinga jifar akuyar, Da gudu Ta
watsa tana kuka, Sautin dariyar Jemimah ne ya karaɗe kunnuwansu
“Genie ashe ma matsorayaci ce, wai wannan abun su Batul suke ma gudu, ni sun bani
dariya, Ko kunya ma bata ji tana yawo zindir babu kaya a jikinta, ƴan nonuwanta
azube kamar na tsohuwa, Genie itama mutunce kamar mu ko”? shiru Angel bata tanka
mata, Damuwace ƙarara akan fuskarta, Hankalinta ba zai ta6a kwanciya ba idan har ba
adawo dasu Batul ba.
Azeeza tana a la6e saman bayan Gabriel, Muguwar matsoraciya tun da akuyar nan ta
faɗo wurinsu Ko yatsanta tagaza motsawa, Numfashinta ma a dabarbarce yake fita,
Jikinta sai kakarwa yake yi, ba dan Allah yasa tana a goye a bayan Gabriel ba kuma
ya ɗaureta da mayafi da kuwa Silar 6acewar azeeza kenan acikin Daji, Allah kaɗai
yasan inda zata kutsa kanta saboda tsoro.
“Shiru basu dawo ba Angel, Ni inaga zan bi bayan Danish ne” Gabriel yai maganar, da
sauri tace”A’a, Kada kaje ko’ina, Inaji araina zasu dawo atare, nasan duk inda suka
shiga Danish zai nemo su”

Haris dai Yana a langwa6e jikin bishiya, suna cikin jimamin rashin ƴan uwansu, suka
soma Jin takun tafiyarsu da sauri suka Juya baya suna kallon su, a jere su ke
tafiya suna tunkaro su, abun da zai baka mamaki Hada naufal da javed su da suke
maza, Batul na aruƙe da hannun Hannah, dana Parveen Sai haki sukeyi sun hada uban
gumi, Danish na abiye da bayansu, Tunkan su ƙaraso Angel ta fashe da dariya hada
dafe cikinta, Hatta Gabriel dariyar yake yi masu, hakan ba ƙaramin ƙona ransu yai
ba.

Ko da su ka ƙaraso zazzaga masu masifa Naufal ya shiga yi yana fadin meyasa basuyi
masu bayanin cewe akuyace ba, ae su basu son suffarta ba, iya namanta da suke ci ne
suka sani,’ Sai da yayi mai isarshi parveen ma ta ɗaura da nata faɗan akan dariyar
da suke yi masu, sauran dai basu ce komai ba, Ruƙo haris danish yai tare da taimaka
mashi ya miƙe tsaye. Zuciyarsu Naufal a jagule suka ci gaba da tafiya, Rayuwarsu ta
daji gwanin ban sha’awa, Ga cin dariyar kwa6ar su batul komai basu sani ba sai
Angel tayi masu bayani, idan dare ya tsala gefen bishiya Danish Yake yi masu
shimfiɗa, bayan sun kwanta Yabi su da barguna Ya lullu6e su, sannan ya shiga daji
Ya samo itace ya haɗa masu wuta saboda sanyin Dajin, Tun da suka fara tafiyar nan
Danish bai runtsa ba, Su kaɗai suke Yin baccinsu, Baya gajiya dayi masu hidima,
basu da matsalar komai Abinci har sai sun ture, Nama iri iri suke Ci na dabbobin da
yake yi masu farautarsu, Ga kayan marmari availabe cikin Dajin, wasa wasa kusan
Watansu ɗaya suna tafiya babu alamun zasu taddo cikin gari, Lamarin Ya ɗaga
hankulansu, A haka ma Danish yana taimakon su ba tare da sun sani ba, Duk idan dare
ya nutsa bacci ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya ya ke ɗaukar su Ya nutsa dasu Cikin
dajin ya yi tazarar tafiyar awanni dasu, basu ta6a lura da hakan ba, duk don ya
sauƙaƙa masu wahalar tafiyar, shiyasa ya ke yi masu hakan, don kuma su yi gaggawar
barin Dajin, Don ya fara Jin alamun wani baƙon Yanayin a jikin shi, fargabarshi
kada Giant’s heart ɗinshi ta motsa batare daya Nisantu daga dajin ba.

*PRISONERS💔*

Dare Ya nutsa sosai suna akwakkwance suna bacci, Hasken Wutar Dake Ci Ya haskaka
zagayen wurin da suke, yana a Zaune gaban wutar idanuwanshi akan shimfiɗarsu, Sai
faman lumshe idanuwanshi Yake yi, ga dukkan alamu baccine yake ƙoƙarin fuskarshi.

Angel da ke a kudundune cikin bargo taƙi runtsawa duk don saboda shi, ta kasa
samun natsuwa, Yaye bargon tayi tare da fitowa daga Ciki Ta miƙe tana miƙa ta nufi
inda yake zaune, Tunkan ta ƙarasa taga yana gyangyaɗi Ƙiris Ya rage ya kifa kanshi
Cikin wutar dake agabanshi da gudun gaske Ta ƙarasa tare da zubewa gefen shi saman
gwiwowinta, da hannyenta biyu ta tallabo fuskarshi tana bin shi da kallo, Sam ya
gaza buɗe idanuwanshi sunyi mashi nauyi, rungume kanshi tayi saman kirjinta,
idanuwanta suka ciko tab da ƙwalla, tsananin tausayinshi take ji.
“Danish muje mu kwanta,” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta mata”bazan iya bacci ba Angel
idan har ba barin Dajin nan mukayi ba, Ina jin fargabar wani abu ya same ku ta
silar rauni na” ƙara ƙanƙame shi tayi a jikinta”In sha Allah ba abunda zai same mu
Danish, Allah Yana atare damu, Kuma Inayi mana addu’a, Kada kaji komai kazo mu
kwanta, rashin yin baccin zai Iya ja maka wata matsalar da bana fata” A hankali ya
zagayo da hannayenshi saman waist ɗinta, kafin ya lumshe idanuwanshi. Jin shiru bai
ƙara motsi ba yasa tayi tunanin ko baccin ya ɗauke shi ne, Kiran sunanshi
tayi”Danish” amsa mata yai”Na’am” cikin kulawa tace dashi”nayi tsammanin ka fara
baccin ne, pls kayi bacci Danish, inaso ka huta, bana so kana wahala” daɗin murya
yake ji acikin kunnuwanshi, har baison intana magana tadaina, Yafi son taita yi
mashi surutu.
“Danish naji ka yi shiru baka ce komai ba”? Har saida ta fidda rai da zaiyi mata
magana tukunna taji yace”Angel ni wannan ba damuwata bace, i ave told u duk wahalar
da zanyi indai akan ku ne bana gajiya, ke ce ƙwarin gwiwar da nike da shi Angel “
murmushi tasaki idanuwanta akan Kitson zanan dake akanshi,
“Faɗamin me ka ke ji akaina? sannan Meyasa kake ƙaunata? Ta yi maganar tare da
Ɗaura yatsun hannunta saman kanshi, tuntuni ta ke son ta kwance mashi kitson da
akayi mashi a prison don bata son ganin shi da kitso kamar mace tafi son ta ganshi
a Namijin shi.

“Nikaina bansani ba” amsar daya bata kenan,


Ɗagowa yai da kanshi tsinin hancinsu Ya haɗe jikin na juna, Hasken wutar dake cine
ya haskaka fuskokinsu
Hakanan Taji gabanta na faɗuwa, ganin launin idonshi na canza mata, duk tabi tasha
jinin jikinta, ƙwarjini yayi mata da sauri ta kawar da idonta gefe ɗaya
“Abu ɗaya nake fargaba a duniyar nan! Shi ne ace za’a raba ni da ke!” Dawo da
dubanta tayi akan fuskarshi, jaddada mata maganar shi yai”Zan iya komai a wannan
lokacin,”
“Maganar raba ni da kai ma bata taso ba Danish, dani da kai tamkar anta da jini ne,
mutuwace kaɗai zata Iya raba ƙaunar dake a tsakanina dakai, Amma agidan duniya bani
da madadinka” kalamanta sun ɗan sanyaya zuciyarshi,
“Ina tsoron ranar da zaki Canza min, duk da bana kawo hakan araina, Angel wani zai
Iya ƙwace min ke, kinga ni bani da komai da zan iya faranta maki da ya wuce kaina”
Muryarshi araunace yai maganar.

Ɗaure mashi fuska ta yi “Danish zaka Iya bari wani ya ƙwace maka ni”? Girgiza mata
kai yai alamar a’a, ya ƙara da cewa”Sai inda ƙarfi na Ya ƙare, “

Lumshe ido ta ɗan yi calmly ta furta “Yadda muka sha wahala atare Danish, Haka nake
so Mu ji daɗi atare, Bani da abokin rayuwar daya wuce kai a faɗin duniyar nan,
Kaine mallakina, masoyi na har abada, ta ya ya kake tunanin zan iya canza ma ka?
Ai kaine nake tsoron Ka canza min idan mun shiga Cikin gari, saboda nasan mutane da
yawa zasu dinga rububinka saboda kyawun Da Allah yayi maka, Sannan bansan su wanene
Iyayenka ba, amma inaji araina ba ƙananun mutane bane yadda kake da kyan nan da
izza ɗabi’unka sak Irin na ƴa’ƴan Hamshaƙan masu kuɗi ne, Ni ko ka ga ba ƴar kowa
bace, Mahaifina ɗan Jarida ne kuma ya rasu ma, “ Idanuwanta acike tab da ƙwalla
tayi maganar, ƙwallar na gangarowa saman kuncinta yai saurin sanya tongue dinshi Ya
lasheta, nan ta ke ta ji yanayin jikinta ya fara canzawa.

“Ni bani da iyaye Angel, Ki daina yi min maganarsu bana son ji, ke ce uwata kuma
kece ubana, Kece gatan da nake dashi, Idan ina dake bani buƙatar kowa,” muryarshi a
kausashe yake yi mata magana, Ta fahimci bayason zancen Iyayen shi da take yi
mashi.

“Meyasa bakason Inayi maka maganar iyayenka? Danish Salsabeel ya faɗamin tun kana
jariri aka sadaukar dakai, Naji raɗaɗi jin hakan acikin zuciyata, sai dai Ni bazan
Iya yankewa iyayenka hukunci ba, Kada ka manta sadaukarwar kurkukun ƙaddara ba dole
sai iyayenka ba, zai iya yiwuwa ba sune suka sadaukar dakai ba, wata’ƙil ma basu
da masaniyar kana araye....” bai bari ta taƙarasa maganar ba yai saurin toshe mata
bakinta da tafin hannun shi”Is ok, Kije ki kwanta dare Yana ƙara yi,” maƙe mashi
kafaɗa tayi”Idan Kaga na kwanta toh muna atare da juna ne,”kafiya ta sanya mashi ya
rasa ya zaiyi da ita, A ƙarshe dole Ya haƙura Ya ƙyaleta, kwantar dakanshi yai
saman ƙirjinta, Taci gaba da kwance mashi kitson kanshi, Kafin bacci Ya ɗauke su
saida ta warware kitson duka, A manne da juna suke ta sharar baccin su, Karo na
farko da ya fara runtsawa Acikin Dajin❗❗❗

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E10🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

A Kwance ya ke saman shimfiɗeɗan gadonsa, Kamar kullum cikin shigar larabawa,


hannun shi a ruƙe da wayarshi, Ya ƙurawa Hoton wallpaper ɗin shi ido, ko ƙyaftawa
bai yi sam baya gajiya da kallon hotonta, Yanayin fuskarshi Ya nuna tsantsar
damuwa, a hankali ya ɗaura yatsun shi saman hoton kan wayar yana shafa fuskarta,
lumshe idanuwanshi Ya ɗanyi kafin a hankali ya ware su kan hoton, waƙar larabci ya
soma rairawa da daddaɗar muryarsa duk akan hoton wadda ya ke kallo, ya dage yana yi
mata waƙa mai nuni da ƙaunarta da yake yi, Tunawa da bata a raye yasa shi dakatawa
da raira waƙar, Ya jefar da wayarshi gefe ɗaya saman mattress ɗin, haɗi da kifa
kanshi saman pillow, kamar ƙaramin yaro ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, abun ne
yana damunshi ya hana rayuwarshi sakat.

“Shureim, Ka yi haƙuri Ka daina sanya damuwa aranka, I know it hurts you, but
worrying won’t make anything better, it’ll only make things worse kuma ka tuna
Allah yanasan bayinsa masu tuba, Kana fa da ilmin ka ba sai na tunasar da kai ba,”

bai tsammaci jin muryarta ba, A hankali Ya ɗago da idanuwanshi Waɗanda su ka kaɗa
jawur da su, ya ɗaura su kan fuskar Zainab.

Tana a tsaye cikin shiga ta riga da skirt, kanta sanye da hula, ga dukkan alamu
daga kitchen ta fito.

“Babu wanda yasan nashigo shureim, Satar hanya nayi don nasan idan hajiya layla ta
sani ba za ta bar ni in zo wurin ka ba.......” numfasawa ta ɗanyi kafin ta ɗaura da
cewa”Tuntuni na so mu samu lokaci muyi magana sai dai ban samu damar yin hakan ba
saboda baka nan, till today” har cikin zuciyarshi ba ƙaramin sanyi yaji ba,
yunƙurawa yai tare da miƙewa ya zauna ya jingina bayansa jikin headboard din gadon
Yana kallonta, Still hawaye basu daina wanke fuskarshi ba, Zainab ta damu dashi
sosai, har mamaki ta ke yi yadda wasu iyayen Allah ya basu damar haihuwar ƴa’ƴa
nagartattu amma suke watsi da su, basu damu da damuwar su ba, yayin da wasu neman
ƴa’ƴan su ke yi ruwa Ajallo, tana matuƙar jin takaicin haka.

“Aunt Zainab, Kin tabbata ba wanda yasan kin shigo? Ina mommy da daddy ne”
“Layla tana a palour, mahaifin ka kuma Yana a garden shi da kawunka Musa” Jin hakan
Yasa shi saukowa daga saman gadon shi Ya nufe ta, tsayawa yai suna fuskantar Juna.

“Ka faɗa min wani taimako ka ke so In yi maka? in sha Allahu babu abunda zai
gagara, a shirye nake da in share maka hawayen ka”
Hannayen ta biyu ya ruƙo a cikin nashi gabanta sai faɗuwa ya ke yi, tsoronta kada
wani daga cikin Iyayenshi ya faɗo ɗakin, muddin hakan ya faru zata ɗanɗani kuɗarta
ne.

“Aunt Zainab I feel in my heart that she’s still alive! Tun bayan da abun ya faru
I’ve never dreamed of her as dead, I’ve always seen her alive in my dreams.” tun
kafin ya ƙarasa maganar ta katse shi “How could that be possible, Shureim? Mutumin
da ya mutu ai baya dawowa and the dreams you’re having aren’t real Don’t believe
what you see in your dreams.”

Fuskarshi a yamutse ya ke dubanta

“Amma ni inaji araina bata mutu ba!” kafe mata yai akan zancen shi
Ta fahimci ya fara zaucewa, Zaifi ta lalla6a shi don ta kwantar mashi da hankalin
shi”shureim, idan ma tana araye da buƙatar mu shirya plan don mu tabbatar da abunda
muke zargi,”

Jinjina mata kai yai alamar yana fahimtarta.

“Dole Ka bi duk a bun da zan faɗa maka,” amsa mata yai da in sha Allah, mu zauna
sai muyi magana” girgiza mashi kai tayi”a’a ina tsoron Mahaifiyarka ta faɗo dakin
nan, Just A tsaitsaye zan faɗa maka matakin da zaka ɗauka domin mu ci nasara akan
binciken da zamu yi” zame hannunta tayi daga cikin nashi da sauri ta nufi ƙofar
ɗakin ta leƙa tana duban ko’ina don kada wani ya faɗo masu, ganin bakowa yasa ta
gyara labulan ɗakin nashi, ta juyo da sauri ta nufe shi Yayin da take cigaba da yin
maganarta”mataki na farko shine Dole ka tanƙwashi zuciyarka, ka danne raɗaɗin da ka
ke ji ka daina sanya damuwa aranka”

“Mataki na Biyu Ka daina gudun Iyayen ka, Ina nufin Ka koma masu tamkar yadda ku ke
da su Ada, Biyayya sau da ƙafa, ka nemi yafiyarsu akan 6ata masu rai da ka ke
Yi.....” tun kan ta kai ƙarshen maganar ta lura da canzawar da yai, a marairaice
yace da ita”Aunty zainab taya zan iya yin hakan? Ni bana jin zan Iya sakar masu
fuska mu koma kamar yadda muke ada” murmushi ta ɗan saki kafin tace”Shureim kenan,
Nafi so ina magana kana fahimtata, ta wannan hanyarce kaɗai zamu Iya gano meke
wakana a tsakanin Iyayenka” jinjina mata kai yai alamar ya fahimta.

Har ya buɗe baki zai yi Magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa

“Me ka ke buƙata in kawo maka? nasan kana jin Yunwa”

A ruɗe ya ke kallonta da mamaki Akan fuskarshi, Me ya kawo zancen yunwa acikin


maganar su.

“Ko dai kana buƙatar chips in haɗo maka da shi”? Ta wutsiyar idon shi Ya hango
Layla A tsaye bakin ƙofar, Ta kifa ɗaurin ɗan kwalin atampa akanta, Riga da skirt
ne sun bi shape ɗin jikinta, duk da alamun manyantaka atattare da ita, hakan bai
6oye kyawun surarta ba.

Wahalallan Yawu ya haɗiya haɗi da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, aranshi ya ayyana
ko yaushe tazo bakin ƙofar! Sai yanzu ya fahinci dalilin canza maganar zainab, ita
tun kafin layla ta shigo tajiyo takun takalmanta saboda bata sanya takalmi idan ba
mai tsini ba, Ba don Allah yasa taji motsinta ba da ko ta yabawa aya zaƙin ta

“Aunty zainab wai meyasa ki ke son takurani akan dole sai naci abinci, nace maki
bana jin yunwa ki tafi kawai, Ni bana buƙatar ganin kowa akusa da ni, ana dole ne”
Ranshi a matuƙar 6ace yai maganar, tare da Juya mata baya, Ya ruƙe qugu da hannu
ɗaya, Zainab dake kallon bayanshi tace”Shureim zama da yunwa zai Iya haifa maka
wata matsalar, abunda bama fata, Ni bari naje na faɗawa mahaifiyar taka kaƙi cin
abinci wataƙil idan ita tayi maka magana ka ci” Har zata Juyawa shureim Ya juyo a
sukwane Ya daka mata tsawa”Karki Kuskura ki ce zaki haɗani da ita, Ko kin faɗa mata
abanza, matar da bata damu da ci na ko sha na ba.....” Sai da yai wannan maganar,
Layla ta kai hannu ta ɗan kwankwashi Jikin Ƙofar ɗakin nashi Don hankalinsu ya dawo
kanta, tamkar basu san da zamanta ba suka ɗago suna kallonta, Fuskarta tasha uban
make up, gashinta baki wulik har mid back ɗinta, Cikin takun izza da nuna isa Ta
nufo su tana magana”Zainab Nagode da kulawarki akan ɗana, ki ƙyale shi, shureim ya
daina jin maganar kowa a yanzu bansan laifin me mu ka yi mashi ba da yake gudun
mu,’ tun da ta fara magana Zainab take sauke ajiyar zuciya, jin bata gano me suke
tattaunawa ba, shureim ko sai ƙara ɗaure fuskarshi ya ke yi kamar zata fashe saboda
tsabar nuna fusatarshi.

Idanuwan mahaifiyarshi akan fuskarshi, Cikin girmamawa zainab tace”Shureim har


yanzu yaro ne, tun da yana a ƙarƙashin kulawarku, sai ana haƙuri dashi ana kuma
lallashin shi da jan shi a jiki ta hakanne zamu iya sanin meke damun shi” jikinta
na ɗan kerma tayi maganar, gyaɗa kai Layla tayi”is Okey, ba sai kin koyamin yadda
zan Kula da ɗana ba, Ni da na haife shi ni nasan kayana, Zaki Iya tafiya ki bamu
wuri” ta yi maganar tare da nuna mata ƙofa da hannu.

layla kenan Ita ba’a mata gwaninta, Jiki asanyaye zainab ta kama hanyar fita ɗakin
tana tafiya tana waiwayon shureim da ido take Yi mashi alamar Ya sake mata, kada ya
manta da shirinsu, Lumshe mata idon da yai ne yasa ta fahimci ya gane me take nufi,
Bayan fitar zainab, Layla ta tsare shi da idanuwanta

“me zan yi maka wanda zaisa Ka daina guduna? Haba Shureim saboda na kore ka cikin
fushi shine ka kama Hanya ka tafi egypt wurin Ammi, Kasa ta kirani awaya tana ta
zazzaga min masifa, ‘ ranta a6ace take yin maganar, har ya harzuƙa zai mayar mata
da martani kalaman zainab suka faɗo mashi arai da sauri ya danne fushinsa, abunda
ta tsana dashi tana magana Yana shareta, Wuyan farar jallabiyar jikinshi ta damƙa
da hannayenta waɗanda ke a sanye da awarwaro da zabba na zallar zinari, Jijjiga shi
tai”Shureim so kake baƙin cikin ka ya kashe ni? Na rasa benazir kaima kuma kana
neman ɗaura min hawan jini, so ka ke zuciyata ta buga in mutu shureim”? hankalin
shi ba ƙaramin tashi yai ba, ganin hawaye sun ciko idonta.

Duk da yasan ta yi hakanne don ta samu kanshi, sassauta muryarta tayi tare da
sakin Kwalar rigarshi”Kai kaɗai nake gani naji daɗi, Meyasa ba za ka manta da
abunda yawuce ba, ina magana kana share ni, kasan bana son hakan, Yana ƙona min
rai” baisan sa’adda hawaye suka cigaba da wanke fuskarshi ba, muryarshi na ɗan rawa
ya furta”?mommy saboda ni za ki zubar da hawayen ki”? Muryarta a kausashe
tace”Shureim, how many times have I cried for you? I understand that you’re trying
to drive me crazy,” Shureim ka daina ƙaunata” Tai maganar tana watsa hannayenta’
shiru Ya ɗanyi yana kallon fuskarta, tabbas ya ga 6acin rai acikinta.

“Astagfurillah” jin ya ambaci haka Yasa ta zaro idonta akan fuskarshi


“Mommy, I didn’t know you cared about me that much, I thought you’d stopped loving
me, amma yanzu mommy akaina kike zubar da hawayenki”?

Mamakin kalaman shi ne yasa ta kafe shi da ido ba ƙyaftawa, Hadisi Ya soma janyo
mata da ayoyin al’kur’ani mai girma waɗanda ke magana akan wanda Ya ƙuntatawa
iyayen shi.

“Shureim ka sani kuma kake take sani? Shine Ka rufe ido Kana ƙuntata min? Meyasa”?
Marairaice mata fuska yai”ya zanyi! Sharrin zuciyane da kuma sharrin shaiɗan, sune
suke azalzalar zuciyata akan abunda Ya faru, sunƙi bari na manta komai,” Dafa
kafaɗar shi tai da hannunta ɗaya”Ka yafe min shureim, nayi maka alƙawarin zan
tarairaye ka na baka kulawa kamar yadda muke ada, Sannan inaso kamanta da abunda ya
wuce, Ba laifin mu bane, mu ne sila, amma kaine ka aikata komai ba tare da ka yi
shawara damu ba, kai kasan ba yadda za’ai da hankalin mu da tunanin mu mu goyi
bayanka akan aikata hakan, a lokacin da ace ka yi shawara damu wlh shureim ba zamu
goyi bayan abunda ka aikata ba” har cikin zuciyarta ta ke magana, Shi kanshi Yaji
jikinshi yai sanyi, zuciyar shi ta karaya, tabbas maganar da ta faɗi gaskiya ne.

“ Mommy, ni ne ya kamata na nemi yafiyarki, akan gudun ku da nake Yi ke da Daddy,


Dan Allah ku yafe min, na gane kuskurena”

yai maganar yana ƙoƙarin zubewa saman gwiwowinsa da sauri ta ɗago da shi ta rungume
shi tana ɗan bubbuga bayanshi da yatsun hannayenta, Farin ciki duk Ya cikata, ta
manta when last ta ji ɗumin shureim a jikinta, saboda rashin jituwar dake a
tsakanin su.

Muryar shi da alamun karaya ya furta mata”Mommy, ana ‘uhibuk kathiran” Hawayen da
suka taru acikin idanuwanta ne suka soma gangarowa saman kuncin ta, still ba su
raba jikinsu daga na juna ba, martanin maganarshi ta mayar mashi”i love u too My
son, ba zan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Shureim ka faranta min rai,”
ta yi maganar tare da raba jikinsu daga na juna, fuskokin su ɗauke da murmushin
ƙauna

“Idan har dagaske mun shirya inaso daga yau ka goge duk wasu hotunanta dake a cikin
wayarka, kallonsu baida amfani shureim, saboda suke fama maka raunin dake a cikin
zuciyar ka”

Shiru yai yana kallon fuskarta, har sai da ta kai ƙarshen maganar, Har ga Allah bai
jin zai Iya goge hotonta a wayarshi, don ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba
aduk lokacin da ya kalle su, Allah ya jarabce shi da ƙaunarta, Yafi sonta akan kowa
na duniyar nan, duk da bata araye.

Gudun kada ta zarge shi, yasa shi yin saurin cewa”saboda farin Cikin ki mommy zan
yi deleting ɗinsu, ni kaina bana son abunda zai ƙara shiga tsakanina da ke,”

Gyaɗa kai ta yi “Shureim ka ɗauko wayar ka goge su agabana In gani” tuni yasha
jinin jikin shi, ba don yaso ba ya amsa mata da toh, slowly ya juya ya nufi gadon
shi ya ɗauko wayar, Kafin Ya kai mata, wayar ta hau ruri, hakan ba ƙaramin daɗi yai
mashi ba, Waiwayowa yai still tana a tsaye tana kallon shi”who’s calling u”? Ta
jefa mashi tambayar, Nuna mata screen ɗin wayar ya yi sunan Daddy ne Ya bayyana
akai” Umarni Ta bashi ya ɗaga kiran Ya kara wayar a kunanshi, Muryar Alhaji Ubaid
ce ta ratsa kunnuwanshi”Shureim Uncle ɗin ka na son ganin ka, gamu nan zamu shigo
cikin gidan” muryarshi A sanyaye ya amshi mashi da toh, takaicin shi ɗaya layla
taƙi tafiya, ta tsare shi da ido, adan dole sai ya goge hotunanta awayarshi.

A hankali ya zame wayar daga kunnan shi, matsawa yai kusa da ita, Bayan ya cire
password Na wayar Ya miƙa mata adai dai kan Gallery ɗinshi, Ta kar6i wayar tana
duba hotunan, Ta yi mamakin ganinsu kamar hauka, hada wanda ya ke a rungume da ita
saman ƙirjinshi, ta6e baki layla tayi, hankalin shureim ba ƙaramin tashi yai ba
ganin zata danna delete all, jikin shi har tsume ya ke yi.

“Assalamu alaikum”! Muryar zainab ce ta katse mata hanzarin ta, a sukwane ta juya
tana binta da kallo, a bakin ƙofa ta tsaya”Alhaji ne ya shigo tare da kawun
shureim, Shine yace nayi maki magana...” yatsina fuska layla tayi”Naji, ga ni nan
zuwa” Miƙa wa shureim wayar tayi”ka tabbatar ga goge su, sannan ka fito ku gaisa da
kawunka,” Amsa mata yai da toh, Bayan ya kar6i wayar, fitar ta keda wuya Ya cire
memory ɗin wayar, Ya 6oye shi a cikin rigar pillow, Ajiyar zuciya ya sauke Ba
ƙaramin daɗi yaji ba, don ji ya ke kamar za’a raba shi da ranshi idan akace ya goge
hotunanta.

Toilet ya shiga ya wanko fuskarshi, Ya futo Ya nufi dressing mirror, cikin jerin
turarurrukansa ya ɗauki ɗaya ya feshe shi a jikin shi, bayan ya ajiye ya fito daga
ɗakin Ya nufi babban palourn.
*GIDAN ƊAN IYA*

Tun da ta fito daga cikin toilet ta ke a tsaye bakin wardrobe, daga ita sai Towel
ɗaure a ƙirjinta, Ya sauko har saitin gwiwarta, a ƙalla Tafi ƙarfin mintuna goma,
ba tare da ta motsa ba, idanuwanta na akan Jerin suturarta da ke a ninke sun sha
guga, ba komai ne ya tsaida ta ba fa ce neman kayan da zasu dace da tarban Manyan
baƙin su da zasu Yau, Ruwan ido take yi, duk kayan da ta ɗauko sai taga kamar ba
zasu dace da ita ba, Wayarta dake a jiye saman drawer ce ta soma ringing, nan ta ke
taji gabanta ya faɗi fatanta Allah yasa basu bane suka ƙaraso, Da ɗan saurinta ta
nufi wayar tare da kai hannu ta ɗauketa, ko da ta duba screen ɗin wayar, babu sunan
wanda ya kira, Baƙuwar number ce, kokwanto ta shiga yi akan ta ɗaga ko karta ɗaga?
Don ita a tsarinta bata ɗaga baƙuwar number in dai ba wadda ta yi saving akan
wayarta ba ce, kusan sau uku kiran nashigowa Yana yin rejecting ba tare da ta ɗaga
shi ba, tayi kasaƙe kamar an dasa mata Aya,

Shigowa Cikin ɗakin Zahra ta yi, bakinta ɗauke da sallama, turkish gown ce a
jikinta launin pink ba ƙaramin kyau tayi mata ba, tayi rolling veil saman kanta.
Ganin Aneelerh a tsaye yasa tace”lafiya? Ya akai naga baki shirya ba? Ko kin manta
cewa suna a hanya? Sun fa kusa isowa, Na rasa meke damunki, Ko har yanzu kewar baby
junaid ɗin ce bata sake ki ba”? Harara Aneelerh ta ɗan jefa mata, Ba tare da tace
koma ba, ta ɗaura wayarta saman mattress, kafin ta juya ta nufi wardrobe din
Kayan da ta bari a buɗe.

“Zahra zo Ki tayani zabar kayan da zan sanya, Ruwan ido Ya hana ni ɗauka tun
ɗazu” murmushi zahra ta saki yayin da take tunkarar wardrobe ɗin”Aunty aneelerh,
shiga za ki yi ta mutunci, ta kece raini, Lace ko shadda su zasu fi dacewa, “ Ta yi
maganar tare da Kai hannu cikin wardrobe ɗin kayan ta janyo mata wani haɗaɗɗan lace
launin golden colour, ta miƙa ma Aneelerh, Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i
Kayan da zahra ta miƙa mata”na yadda ke ƙwararriyace a6angaren iya zabar kayan da
zasu dace da mutun, nafi karfin 15 mins ina neman wanda zasu dace dani na kasa, sai
da ki ka zo” Zahra tace”kada ki manta aikina ne, burina kiyi kyau auntyna,
surukanki su ganki a mutuncenki, bari naje na ɗauko maki sarƙar da zata dace da
kayan, ‘ amsa mata Aneelerh tayi da toh, Wuce wa zahra tayi agaban drawer chest Ta
zuƙunna ta dauko mata jewelry box dinta, Ta buɗe ta lalubo mata necklace da
earrings launin Lace ɗinta, maida box dinta tayi kafin ta miƙe ta daura mata su
gaban mirror.

“Aunty aneelerh, Ga su nan saman mirror, Pls Ki shirya da wuri, Ni zan je na taya
su mami shirya masu abincin”

Amsa mata ta yi da toh ta ƙara da yi mata godiya, Bayan fitar zahra, Aneelerh ta
shirya tsaf cikin Lace ɗinta, riga da skirt, sun yi bala’in yi mata kyau, sun ɗan
kama jikinta, shape ɗinta ya fito sosai, Kamar a jikinta aka ɗinka kayan, a gaban
mirror ta zauna tana yin make up, lip gloss ta shafa ma la66anta, Ta ɗan shafa
hoda, ta ɗauki brush tana gyara jagirarta, ‘ Sumar kanta Ta sauko har saman
bayanta, ƙarar Shigowar text a wayarta ne yasa ta ɗan kalli 6angaren da wayar take
ajiye saman gado, sai lokacin ta tuna da baƙuwar number da ake ta kiranta ɗazu, sai
da ta fara Ɗaura dan kwalin leshin Kafin ta miƙe ta nufi wayar ta ɗauke ta, Da
yatsan hannunta ta janyo sakon A hankali ya buɗe, Ta yi mamakin ganin Sunanta da
aka rubuta da manyan haruffa, menene ma’anar sakon? Just Aneelerh? Wanene wannan?
Kiran number ta soma ƙoƙarin Yi sai dai taƙi shiga, A ƙarshe ta hakura ta daurata
saman pillow, Gaban Mirror ta koma ta ɗauki jerin turarurruka tana feshe jikin ta
da su, tunawa da baby junaid ɗinta yasa ta ɗan saki murmushi, tayi missing ɗinshi
sosai, yau tun da safe Mahboob Yaje kai shi school, Bayan ta haɗa da shi da kuɗin
fetur, kusan sati biyu da fara zuwanshi makarantar, kullum da fara’a yake tafiya,
yana zumuɗi, da zarar an kaishi Ya ke saka masu rigima sai sun dawo dashi gida, Har
atashi daga school ɗin Yana yin kuka, Fuskarshi jawur ake dawo mata da shi. Malaman
makarantar har sun canza mashi suna daga Junaid zuwa babyn mommy, saboda sunanta da
yake yawan kira masu.

Daga waje tajiyo muryar Zahra tana kwaɗa mata kira”Aunty Aneelerh! “ girgiza kai
tayi aranta tace”Ko yaushe ne zahra zata daina Yi min irin wannan kiran talaucin
kamar zata ƙararmin da sunana”

Zahra na shigowa ɗakin ta Waro ido waje tana fadin”Wow!!! Tabarakallahu Ahsanul
khaliqin Aunty aneelern kinga yadda ki kai kyau? Kamar wadda zata shiga gasar miss
world,” harara Aneelerh ta jefa mata fuskarta asake tace”Naji na gode Da yabo, ni
dai yanzu faɗa min Kiran menene kike yi min”? Watsa hannu Zahra Tayi”dama ummi ne
ta aiko ni zaki ci abinci yanzu ko sai anjima idan sunzo”?
“Yunwa nake Ji zahra, ba zan Iya jira sai sun zo ba, ki samu plate ki zuba min
dambun shinkafa, Ki haɗo min da lemu mai sanyi, “
“Toh, Amma kafin nan mu ɗanyi selfy mana” ta yi maganar tare da Kunna camera din
iphone nata, ta ɗaga Wayar Tare da ɗaura kanta saman kafaɗar Aneelerh, gaba ɗaya
suka saki murmushi, ‘ kusan hotuna Biyar tayi masu atsaye kafin Ta nufi hanyar fita
ɗakin tana faɗin”Idan surukan naki sunzo zamu ƙara yin wasu hotunan tare, Hakan
Yana ƙara danƙon zumunci,” fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi ta ke bin Bayan Zahra
da kallo, gefen gadon ta zauna tana Jiran dawowarta.

*EVIL FOREST*

Tun da garin Allah Ya waye Masu a cikin ƙurmin dajin, Kowan nan su Ya farka, Da
wata irin matsiyaciyar yunwa, suna zazzaune abakin bishiya sun jingina bayan su,
Sai hamma suke Yi, Jiya basu ci abinci da yawa ba kafin Kwanta, sauran Kayan
marmarin da suka rage ne su ka sha, dan ma suna da jumurin yunwa, Hankalin su ba
akwance Yake ba, Danish Yaƙi farkawa daga bacci, tsawon awanni tun daren Jiya da
Angel ta sanya shi yin bacci yake ta yi, Ko motsi Ba ya yi numfashinsa ne kaɗai ke
fita, tun suna sa ran zai farka har sun fara tunanin Anya kuwa Lafiya? Baccin ya
wuce na hankali, domin kuwa tuni safiya ta jima da wuce wa sun shiga tsakar rana.
Sun tsare shi da ido suna kallon shi, A saman shimfiɗar da Angel ta yi mashi, ya ke
a kwance sun ƙudundune shi da bargo, tuntuni su ka so su tada shi daga bacci amma
Angel ta hana su, ita aganinta bai kamata su takura mashi ba, tsawon wata ɗaya baya
runtsawa kullum shine yin gadinsu, Na yau kawai Ya samu ya runtsa ai bai kamata su
katse mashi hutun shi ba.

“Angel Yunwa mu ke Ji” Parveen ce Ta yi maganar, Fuskarta A kumbure ga miyan bacci


a gefe da gefen bakinta, sumar kanta A haukace take babu gyara kamar Ƴar
mahaukaciya, Angel da ke Fuskantar su tana zaune daga gefen shimfiɗar Danish,
fuskarta sam babu walwala, abun ya fara damunta ganin yaƙi farkawa fatanta Allah
yasa baccin lafiya ne ya ke yi.
“Genie we are feeling hungry, pls cikina kukan Yunwa yake mini” Jemimah ce tayi
maganar, tamkar zata fashe da kuka, idon Angel akan fuskokinsu, Batul sai hamma
take Yi, tana faman yamutsa fuskarta.

“Ki jaraba Tada shi mana, wata’ƙil Ya farka, Tun da kinga mu bamu san kan dajin nan
ba, balle mu ce zamu shiga ciki mu nemo abinci” Naufal ne yai maganar muryarshi da
kasala.

“Ni zan Iya zuwa na nemo mana abincin sai mu ci” Gabriel Ne yai maganar, hannunshi
ɗaya asaman sumar kan Azeeza da ke kwance saman ƙirjin shi.

Girgiza kai Angel ta yi”A’a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne kaɗai zai Iya shiga
dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba,” bubbuga ƙafa jemimah tayi
cikin shessheƙar kuka tace”wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki
tada shi ki tada shi Kin ƙiya so kike mu mutu ko”?

Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel faɗa, ita kanta Angel
kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar
fusata.
“Angel ku tada shi mana” Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro
kurkuku, baya magana daga Eh sai a’a, su kaɗai ne abunda Yake iya furtawa, amma yau
sai gashi yayi masu magana, sun ɗanyi mamaki kuma sunji daɗi ga dukkan alamu sauƙi
ya samu
Saboda maganar Haris yasa ta kai hannu ta bubbugi kafadar Danish, Muryar ta ƙasa
ƙasa take furta sunanshi”Danish wake up! Ka tashi suna jin yunwa,” shiru bai motsa
ba, Kusan sau biyar tana yi mashi magana har acikin kunnanshi takai bakinta

Nan fa gabanta ya fara faɗuwa, Parveen tace”ki buge shi mana wata’ƙil ya farka” Ba
tare da ta kalli parveen ba tace”bazan Iya ba” ta ambaci hakan tare da cigaba da
kwala mashi kira.

“Angel nauyin bacci ne da shi, Ba haka yakamata Ki tayar dashi ba, let me help u,
“ Gabriel ne ya ambaci Hakan, Sai da ya fara janye azeeza daga jikinshi, tukunna Ya
matsa gaban shimfiɗar Danish, bubbuga kafadarshi ya yi Da ƙarfi haɗi da ambaton
Sunanshi”Danish! Danish!” yadda yake kware murya hatta su kansu sautin Ya cikasu,
amma wani iko na Allah Danish ko girgiza Bai yi ba, Zuciyar Angel a jagule ta ɗaura
Kunnanta saitin ƙirjinshi Bayan ta yaye mashi bargon, jin heart beat ɗinsa yasa ta
ɗan sauke ajiyar zuciya sai dai ta yi mamakin dalilin rashin farkawarshi, Hankalin
sauran ƴan uwan Yaƙi kwanciya, Gaba ɗaya suka dawo kewaye da shimfidarshi Kowa Ya
zuƙunna
Su Azeeza har sun fara shessheƙar kuka suna faɗin Wayyo Allah Danish ɗinmu meke
damunka, dan Allah ka farka ka yi mana magana ko hankalin mu ya kwanta, Mu mun
haƙura ma da abinci kai kawai muke so ka tashi.

“Ko dai suma ya yi ne? Ku duba cikin gorar ruwan mu idan akwai sauran ruwa ku ɗauko
Mu yayyafa mashi” Gabriel ne yai maganar cikin rashin kwanciyar hankali, Angel
tace”a’a kada ku watsa mashi ruwa, Zuciyarshi fa tana bugawa, bacci ya ke yi,
kunsan Danish da nauyin bacci, Balle kuma da ya ɗauki tsawon kwanaki bai runtsa
ba,’ ɗaya bayan ɗaya suke jogana kunnansu saman kirjinshi don su ji idan zuciyarshi
na bugawa, Hankalinsu Ya ɗan kwanta da jin sautin heart beat din nashi.
“Nasan nan bada jimawa ba zai farka, Mu ɗan ƙara haƙuri” Miƙewa Jemimah tayi tare
da bubbuga ƙafarta, abunka ga yaro ba haƙuri, Yunwa ce ta addabeta, Juyawa tayi
gaba ɗaya suka bi bayanta da kallo, agaban korayen ciyayen dake shimfiɗe a wurin ta
tsugunna, ta soma tsigowa tana turawa abaki tana ci, hakan da tayi ne ya tuna masu
da Ganyen da ake basu a prison, aiko da sauri batul da Parveen da azeeza suka
mimmiƙe agaban jamimah su ka zuƙunna kamar akuyoyi haka suke cizgar ciyawa suna ci,
tsawa Angel da daka masu”Meye haka dan Allah? Kunsan wani irin ganye ne ku ke ci?
Ku daina” a tsawace ta ƙarasa maganar, ta mike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana kwace
ciyawar da suka damƙa a hannun su, Fashe mata da kuka Parveen da jemimah su ka yi
Nan take taji zuciyarta ta karya, cikin shessheƙar kuka suke faɗin ba za su iya
jurewa ba, yunwa ce ta addabe su, ta taimaka tabar su su ci ganyen, suna jin daɗin
shi ahaka.
Idanuwanta acike tab da ƙwalla tace”Is ok, Bari na shiga cikin dajin in nemo mana
abincin da zamu ci,” miƙewa Gabriel yai”Zan bi ki Angel” girgiza mashi kai tai”A’a
gabriel, Ka zauna ka kula da su Azeeza, Yanzu zan dawo” ba don yaso ba ya amsa mata
da toh, Kallon sauran Ƴan uwan nasu tayi”Javed Naufal, Ku kula da su Azeeza, Yanzu
zanje na dawo,” Naufal yace”meyasa zaki tafi ke kaɗai, bayan kin faɗa mana mu yi
takatsantsan da dajin nan akwai mugayen halittun da zasu Iya cutar damu, why angel?
Gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ke kaɗai ba, sai dai mu tafi mu duka,” Yai
maganar tare da miƙewa, Javed ma Ya miƙe, haris ne kaɗai Ya rage a zaune yana
sauraronsu.
Ita kanta gabanta faɗuwa yake yi gani ta ke yi kamar wani mugun abun zai iya
faruwa da ita
Murmushi ta ƙaƙalo akan fuskarta duk don ta kwantar masu da hankulan su yasa
tace”Bawani abu fa, da zarar nayi addu’a Allah zai tsare ni har inje in dawo
lafiya, ku kwantar da hankalinku” girgiza kai Gabriel yai”bazai yiwu ba Angel, bana
so wani abu ya same ki ta silar mu, idan har ba zaki bari mu bi ki ba, To ki bari
Danish Ya farka Ya je da kanshi ya samo mana abincin....” tunkan ya ƙarasa maganar
Angel tai saurin katse shi da cewa”su Azeeza yunwa su ke Ji, Na yadda Gabriel Ka
raka ni mu tafi, ku kuma ku zauna yanzu zamu dawo” Hankalinsu ya ɗan kwanta, Atare
da Gabriel Suka nufi Cikin dajin, Hannunta ruƙe da ƙaramin kwandon su, komawa su
azeeza su ka yi abakin bishiya suna zaman jiran dawowarsu.

Cikin dajin suka kutsa suna tafiya suna dan tattauna fira a tsakaninsu, ta ko’ina
bishiyoyine masu tsayi Da faɗi, Rassansu sun lullu6e wurin da inuwar su.

“Hankalinka ya kwanta ka biyo ni, ni ban san ma ina zamu dosa ba, Ka ta6a shiga
daji”? Ta jefa mashi tambaya, girgiza mata kai yai alamar a’a”bazan Iya tunawa ba
Angel, na manta da komai na rayuwata, amma inaji araina koda ace ban ta6a shigowa
daji ba, zai iya yiwuwa na ta6a kallon shi a waya, Ni yanzu burina mu fita daga
Cikin Dajin nan, Ko mun samu mu tona asirin zaluncin da ake yi a cikin kurkukun
ƙaddara, Angel na damu da rashin ƴar uwata, ina tsoron kafin mu yi nasara su kashe
min ita” yayin da yake yin maganar yanayin fuskarshi ne Ya canza, abun ba ƙaramin
ta6a zuciyarshi yake yi ba duk in ya tuna da ƴar uwarshi Gabriellah.
Cikin nuna jin tausayin shi angel tace”ka kwantar da hankalin ka, Idan Allah yasa
mai tsawaicin kwanace zamu ganta, in kuma ta riga mu gidan gaskiya, Allah Ya
jiƙanta, yana daga cikin ƙaddarar bawa, ba dole ya rayu da abunda ya ke so ba, wata
rana ma kowa zai mutu ba wanda za’a bari gadin duniyar.......” fira ta yi daɗi sai
nutsawa suke Yi, cikin Dajin ba tare da sunsan inda zasu dosa ba, Ga wata iska mai
daɗi da ta ke kaɗawa, wasa wasa Ƙarfin iskar sai ƙaruwa ya ke Yi, ta cika masu
idanuwansu daƙyar suke buɗe su.

Yayin da su Angel suka tafi nemo masu abinci, Sun yi zazzaune zaman jiran tsammani,
Har sun fara lumshe idanuwan su saboda iskar dake kaɗa masu ba ƙaramin kasala take
haifar masu ba, kwatsam! Ba zato ba tsammani kunnuwansu suka soma Jiyo masu wani
irin sautin gurnani mai matuƙar rikitarwa da razanarwa, A firgice suka ware
idanuwansu, Yayin da zuciyarsu ke buguwa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zata 6allo ƙirjin
su, tsananin tsorone Ya kamasu sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansu suke Yi, a
ƙoƙarinsu na su gano ta inda sautin gurnani ke fitowa, sai dai sun kasa sani kuma
sun kasa ta6uka komai, Azeeza tuni ta shige ma Batul kamar zata koma Cikinta, Jikin
su sai faman yin kakarwa yake yi saboda gurnanin ya cika kunnuwansu, Haris dake
azaune gaban shimfiɗar Danish muryar shi adabarbarce ya ke ambaton
sunanshi”da..da..nish ka tashi, pls ka tashi danish, Wani abu yana tunkaro mu’ Da
rarrafe su batul suka ƙarasa gaban shimfiɗar Danish, Cikin fitar hayyaci suke bugun
Jikinshi don ya farka ya ceci rayuwarsu, duk sun bi sun ruɗe tsigar Jikinsu ta
tashi haiƙam, Har suna haɗa baki wurin ambaton sunanshi”Danish mun shiga uku, dan
Allah ka farka, Wannan wani irin sauti ne haka babu daɗin ji, ga Angel bata nan sun
tafi tare da Gabriel, Ni dama nasan zai yi wuya mu bar dajin nan da ran mu’ cikin
shessheƙar ku ka suke magana hawaye na bin fuskokinsu, Jemimah da azeeza tuni sun
rushe da kuka mai sautin gaske, tunkafin ma suga menene ke tunkarosu, sautin
kukansu Jemimah shiya ƙara Janyo hankalin Abunda ke nufo su, basu san sune suke
Janyo shi ba, babu wanda yai hankalin Ya tsawatar da su akan su daina Yin kukan
suyi shiru, ba su yi tunanin yin hakan ba, lokacin da sautin gurnani ya ƙarfafa
hatta ganyayyakin dake a wurin Girgixa suke yi, nan take idanuwansu suka tsaya cak
akan wurin da suke zargin zai 6ullo, Kamar An Jeho suka faɗo ƙasan wurin, wasu
irin Mugayen Halittun namun dawa, masu gashi gashi a jikinsu babu kyan gani gwanin
ban ƙyama, Suffarsu tamkar ta majici sai dai sun gurmi maciji a halitta tsaf zasu
Iya haɗiye mutun su nannade shi a cikin bakunansu, Tashin hankalin da ba’a sama shi
Date, Wata irin gigitacciyar ƙara suka fasa, Ganin Yadda halittun suke Kurɗaɗowa
saƙo da lungu masu Yawan gaske gasu manya manya, Gadan gadan suke tunkarosu Harwani
nannaɗe Jikinsu suke yi suna harɗewa, tsabar firgi da tsoro ne yasa suka Watsa da
gudun gaske kamar zasu Tashi sama, Gudu su ke yi na fitar hayyaci, gudun ceton rai,
su kan su basu son Inda zasu dosa ba, wani ƙarin tashin hankalin Halittun da gudu
suke binsu, Ga sauri da Allah yai masu, sun fuskanci matsanancin tashin hankali
mara misaltuwa, musamman ƙananun cikinsu Azeeza da jemimah duk sun tarwatse kowa Da
inda nufa, dan bala’i, Halittun suna lura da kowace kusurwa suka faɗa, Yadda suka
raba kawunansu haka suma halittun su ka karkasa kawunansu wurin binsu, Haris da ba
ƙoshin lafiya gare shi ba, tuni Numfashin shi ya soma sarƙewa, bakinshi ya soma
fitar da jini, Gashi kowa Ya watse sun barshi, Yana ji yana gani halittar nan Ta ta
taɗiye ƙafarshi gaba ɗaya ya kife ƙasa, tana gurnani ta wage bakinta masu haƙora a
jere babu kyan gani, ta Zurma ƙafafuwanshi.....Innalillah

A 6angaren Azeeza da ke ruƙe da jemimah suna tiƙar gudu, hada tuntu6e sun rasa ina
zasu dosa, Jemimah sai kuka take yi tana ambaton sunan Genie, Cikin rashin sanya
Wasu muggan ƙayoyi suka Sargaho ƙafafuwansu kusan atare suka rubza ƙasa kansu ya
daku.

A 6angaren Batul da parveen da Hannah da suka nufi Hanya ɗaya, Halittun nan sai
binsu suke yi, sun rasa ina zasu dosa, suna gudu Sumar kansu Na rufe Masu
idanuwansu, ba zato ba tsammani ƙafafuwansu suka zurma a cikin wani rami da ca6ali
ya cika shi, gaba ɗaya su ka nutse cikin shi, Ko numfashi basu Iya fitarwa.

Idan muka Koma 6angaren Angel da Gabriel, lokacin da suka ƙaraso bakin wata
bishiyar Mangaro sun tsaya suna tunanin hawa saman bishiyar don su tsigo su, atare
suka haye suna aikin tsinkar magaro, sai da suka gama ɗibarshi a cikin kwando,
Gabriel na yunƙurin zura ƙafarshi Ya sauko ƙasa kwatsam idanuwanshi suka sauka
akan kurar dake ƙasan bishiyar tana cin wani namun dawa data kamo, wahalallan yawu
ya haɗiya tare da kallon Angel, ita sam bata lura da abunda ya hango ba,
“Gabriel mu sauko mana, Suna jiran mu” Muryarshi Na kakarwa yace”Angel mun shiga
uku, wlh kura ce a ƙasa take cin nama,” Sai lokacin ta wurga Idanuwanta ƙasan
bishiyar, Gabanta yai mugun bugu, muryarta da tashin hankali ta furta Innalillahi
wa’inna ilaihirraji’un! Kafin Gabriel ya furta wani abu daga can cikin Dajin ihun
muryar Naufal Ta karaɗe kunnuwan su, Kallon Juna su ka yi nan ta ke su ka fahimci
babu lafiya a wurin Ƴan uwan su, zufa tuni ta wanke fuskarsu, ganin tana yunƙurin
sauka yasa gabriel damƙo hannunta, muryarshi a hargitse yace”Kada ki sauka angel
kashe ki za ta yi” Girgiza mashi kai tayi idanuwanta sun rikiɗa jawur dasu
tace”ƙwara ta cinye ni, wlh sai naje wurin ƴan uwana, Baka ji ihun naufal ba, Allah
kaɗai yasan meke faruwa dasu” kokawa suka soma yi da Gabriel a saman bishiyar, ya
hana ta saukowa sai kiciniyar kwace kanta ta ke yi, aiko Suna cikin Yin kokawar nan
Gaba ɗayansu suka ƙundumo ƙasa agaban kurar nan, Bakin ta ca6a ca6a da jini, Kafin
ta ɗago da ido ta kallesu, Da iya ƙarfinsu na ƙarshe suka yunƙura suka miƙe a guje
suka watsa, da gudu itama kurar tabisu tana gurnani, babu wanda bai fita hayyacin
shi ba, lokacin da suka faɗo wurin da suka bar su azeeza hankalinsu ba ƙaramin
tashi yai ba, gabin babu kowa ga kuma Danish a kwance yana ta sharar baccin shi.
Kafin Angel tayi yunƙurin zuwa wuri shi kurar nan ta dako uban tsalle ta faɗo masu,
Da ƙarfi gabriel Ya fusgi hannunta tana kuka tana ambaton sunan danish Tana miƙa
hannu yaja ta da gudu, wani iko na Allah kurar ta tsalle Danish tabisu da gudu, su
kawai ta ke hari, kurɗaɗawa suka yi cikin dajin suna gudun famfalaki Kura ta zamar
masu masifa ta hanasu sakat.........”

*Boss Bature✍️*

Tun bayan da dr shureim ya fito daga bedroom ɗinshi ya nufi Palour, A zazzaune ya
samu Alhaji ubaid tare da Uncle musa zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Layla
tana a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, Idon shi na akan Uncle ɗin nashi,
Ya ɗauki wankan tsadaddiyar shadda mai ɗaukar ido, ƙamshin turaren shi Ya cika
palourn, idanuwanshi suna a lumshe, hannun shi na dama haɗaɗɗiyar agogon diamond ce
wadda a ƙalla price ɗinta ya kai 300m, mutunne mai ji da naira, hutu ya zauna mashi
ko Alhaji ubaid ba zai nuna mashi tarin dukiya ba, ko a muƙami bai kai shi matsayi
ba, Alhaji musa ƙanine ga Alhaji ubaid uwa ɗaya uba ɗaya, kuma shine former
president, akwai tazarar shekaru a tsakaninsu, A kyawun halitta Musa ya zarce
Alhaji ubaid, Yana da hasken fata yayin da Alhaji ubaid yake da duhun fata, Sannan
yana da Yalwatacciyar sumar kai tasha gyara ga sajen gefe da gefen fuskarshi baƙi
wulik, Kamar matashin saurayi. Ya iya ɗaukar wanka ga aji ga kuma ji da kai.
Daga ƙasan carpet dr Shureim ya zauna cikin girmamawa ya gaishe dasu, Alhaji ubaid
ne kaɗai ya amsa mashi, kawun nashi kuwa ko arziƙin kallo bai samu ba, har sai da
hajiya layla tace mashi”baka ji shureim yana gashe ka ba”? Ba tare daya buɗe idon
shi ba yace”Naji,” sanin halin shi yasa Shureim bai damu ba, Layla dai ce ranta ya
6aci dama ita bata iya 6oye fushin ta, Alhaji ubaid ko murmushi ne akan fuskarshi,
Har yau mamakin Halin Ƙanin nashi Yake yi.

“Shureim, kasan shi fa mutumin turaine ba haka yake son ka gaishe shi ba, Ka
matsa kusa dashi yaji ɗumin ɗanshi a jikin shi” acewar Alhaji ubaid,

Yatsina fuska layla tayi, aranta kuma ji take kamar ta shaƙe wuyan Alhaji musa,
jin kanshi na matuƙar ƙona mata rai, miƙewa shureim yai tare da nufar sofa ɗin da
musa ya ke a hakimce, ya zauna daga ƙasa,
“Uncle sannu da zuwa, Ya gajiyar tafiya” sai lokacin ya ɗan ware idanuwanshi tare
da kallon shureim na tsawon mintuna, sai da ya mula ya sha iska tukunna ya soma
magana
“Babu gajiya atare da ni, kai zanyiwa sannu, ni banzo da niyar in ganka ba, banma
yi tunanin kana a ƙasar ba, sai da Ya ya ya ke faɗamin, shureim kafi ƙarfin ka tako
kazo gidana ne? Laifin hada ni ya shafa kenan”? Tun da ya soma magana, hajiya layla
take jifar shi da harara a fakaice batare da ta bari Alhaji ubaid ya gani ba, ita
sam baya burgeta, haushin nuna isar da yake yi take ji,
“Ay min afwa Uncle, bani da kwanciyar hankali ne shiyasa bana samun damar zuwa,
amma kuna araina,”
Ta6e baki Alhaji musa yai ba tare da ya furta kalma ba

Hajiya layla tace”To ai kaima ɗin baka damu dashi ba, Ba ka neman shi taya zai yi
tunanin kana buƙatar ganin shi a gidan ka......” bata ƙarasa maganar ba, da sauri
ta dakata ganin irin kallon da Alhaji ubaid ya ke jefa mata, sam baya son tana
shiga tsakanin shureim da ƙanin shi, saboda mugun son shi ya ke yi baya son 6acin
ranshi.

“Kare shi za ki yi”? Alhaji musa ne yai maganar sautin muryar shi a kausashe,
Shiru tayi bata tanka mashi ba,
“Kada ki shiga tsakanin Uba da ɗansa, Kija baki kiyi shiru” Alhaji ubaid ne yai
maganar, Ta6e baki tayi tana faman hura hanci.
“Ae da kabarta yaya ta ƙarasa maganarta,” yai maganar fuskarshi ɗauke da murmushi.
Kafin ya kawar da idonshi daga kallonta.

“Shureim, Idan na tashi tafiya abuja atare da kai zamu tafi, bazan barka a gidan
nan ba, don Na fahimci akwai masu takura maka, Shiyasa duk ka rame kayi duhu,”
Cikin kulawa yake yi mashi maganar, hannun shi ɗaya asaman kafaɗar dr shureim ɗin,
Layla ta yi mamakin jin abunda yace, mutumin da ko ƴa’ƴan shi bai sakar masu fuska
shine ya ke zancen zai tafi da shureim, kwa6e fuska ta yi don ta fahimci so ya ke
ya ƙuntata mata.

Alhaji ubaid yana murmushi yace”naji dadin jin hakan, wata’ƙil idan kuka je can
yafi sakewa, don na fahimci shureim baya son zama gida...” kafin ya ƙarasa maganar,
layla ta katse shi da cewa ‘’ae sai ku tsaya kuji ra’ayin shi ko? Idan ya ce yana
son zuwa can ɗin,” Tana rufe baki Alhaji musa yace”ai ba shawara nake nema dashi
ba, Umarni ne” Cikin isa Ya furta hakan, Kafin ya kalli dr shureim, ka shirya komai
naka idan muka tashi tafiya atare zamu tafi”

Lamarin ya ɗaure mata kai, shi dai Dr shureim yai shiru bai tanka masu ba, Girgiza
kai Hajiya layla tayi’bazai yiwuwa ba, haba dan Allah duka yaushe muka samu shureim
ɗin ya dawo wurin mu, Sannan kuma yanzu kace zaka tafi dashi? Aɗan bari ya huta
mana, Shi kaɗai fa nake gani inji daɗi,” rai a6ace take magana, Sun natsu suna
sauraronta, sai da takai ƙarshen Aya tukunna Alhaji ubaid yace da ita”meye na tada
jijiyoyin wuya? Guduwa zai yi dashi ne? Bafa raba ki zaiyi dashi ba, Yana so ya
zauna gidan shi na ɗan wani lokaci,” fuskar Alhaji musa aɗaure yace”idan na ga dama
zaici gaba da zama awurina ne kuma ke baki isa ki hana shi ba” murmushin fuskar
Alhaji ubaid bai washe ba yace”ba girmanku bane ku tsaya kuna sa’insa akan Shureim
sai kace wani ƙaramin yaro, ko da ya ke laifin ka ne shureim tuntuni nake baka
shawarar kayi aure ka ƙi yi, da ace kana da Iyali babu wanda ya isa yai iko da kai”
da zolaya yayi maganar, Shureim dai ya natsu yana jinsu, Ya jima yana jin takaici
yadda rayuwa ta canza mashi, Ya koma tamkar ƙaramin yaro a idon kowa, saboda raunin
zuciyarshi.

daƙyar Alhaji ubaid ya samu Ya maida sa’in sar tasu Wasa, dama can basu jituwa
tsakanin Layla da ƙanin shi tunfil azal.
“Yakamata mu tashi muje muci abinci, zainab ta shirya mana a dining” layla ce tayi
maganar, Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe tare da nufar Dining room.

*Kaɗan daga Cikin Na sati mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya*

*Evil forest*

Sautin Ƙarar Danƙararen Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk
mallakin Sojin Ƙasar america ne Ya karaɗe ko’ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta
rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza suke yi saboda ƙarfin iskar fankar
Jirgin, Shawagi jirgin yake yi a saman Iska Yana kewaye ko’ina na tsawon mintuna
talatin, Yayin da Hot soldiers din dake a tsaye saman jirgin cikin shigarsu Ta ka
ki sun ɗaura ɗamarar Yaki, Sai dai ga dukkan alamu Sun kammala gudanar da abunda Ya
kawo su Cikin Dajin, Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar helicopter
ɗin Hannun shi ruƙe da tactic phone Wayar da sojoji suke yin amfani da ita wurin
yin sadarwa ga Manyansu dake acan Headquater, Cikin Harshen turancin Yake Yin
magana muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

“We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S.
with the eleven children we found in the forest.”

Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya
fito......, Nima kuma na ajiye alƙalamina.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E11🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

Gaba ɗaya Haris ya fidda rai da rayuwa, tun da halittar nan ta zura ƙafafuwansa
cikin wawakeken bakinta, tsabar tsoro da firgici sun hana shi motsawa jini duk ya
wanke bakinsa har saman rigar sa, jikinsa yai wani irin mahaukacin zafi na fitar
hayyaci, Bawan Allah sai sambatu ya ke yi yana ambaton Sunan Danish dana sauran ƴan
uwan su don su kawo mashi agaji.

Ba zato ba tsammani ya ji Sautin dirar wani abu daram! tamkar zai fasa kunnansa,
tsabar firgitar da yai ne yasa nan take ya sume saman koraren ciyayin.

Wani Gabjejen Bature ne A tsaye cika shigar Kaya na tatattun Ƴan ta’adda babu ɗigon
Imani akan fuskarsa, Hannunsa ɗaya ya ruƙe da Bindigar da yai amfani da ita wurin
harbin Halittar da ta nannaɗe Jikin Haris, yayin da ɗayan hannun ya ke ruƙe da
cigarette.

Hankalin shi a kwance ya ke zuƙar Tabar Cikin ƙwarewa Har ta hanci Hayaƙin Ya ke
fita, kwarkwararrun idanuwanshi na akan Haris dake kwance Ya sume, Tuntsirewa
Baturen Ya yi da dariya hada ɗan girgiza kanshi, da ƙarƙarfan muryar sa ta Mashaya
giya cikin harshen turanci ya ke faɗin

“wani irin ganganci ne ya kawo ka ƙurmin daji da ƙananun shekarun ka, ba ka da


hankali ne? Matashi da kai kake son ƙare rayuwarka abanza? Ina iyayen ka su ke”?

kamar zautacce Shi kaɗai ya ke yin maganar shi, sam bai fahimci Yaron Ya sume ba,
Sai da Ya gama Magana kafin ya matsa inda Haris yake a kwance, Ya zuƙunna Bayan Ya
soke pistol ɗin a qugunsa, Ya sanya hannayensa Biyu Da ƙarfi Yake jan jikin
halittar, Har sai da yai nasarar zaro ƙafafuwan Haris daga bakinta, Allah yaso ba
ta kai ga Gatsa haƙoranta akan legs ɗinsa ba, da ko ta yi mashi babbar illa, Bayan
Ya zame jikin Halittar da karfi Ya jefar da ita gefe ɗaya, yunƙurawa yai ya miƙe
tsaye yana kakka6e tafin Hannayensa, Zuƙar Tabar sa Ya ƙara Yi”Bani da zuciyar
Imanin da zan Iya taimakon ka, ka gode wa Allah da na raba ka da dabbar nan, da ko
yau Ka rasa ƙafar zuwa gidan Iyayen ka” Yana magana yana sakin dariya idanuwansa
akan fuskar Haris.

Sautin kururuwar neman a gajin da ya Ji ce Tasa shi Kan ga kunnansa ga iska Don Ya
ji da kyau, Muryar Naufal ce Ya ke faman Fasa Ihu, Da gudu Baturen Ya kutsa Cikin
Dajin Yana Tunkarar inda sautin Ƙarar ke fitowa, ta wutsiyar idon shi ya hango
gifcin mutune sanye da Jajayen kaya, Ta tsakantsakin jibga jibgan Bishiyoyin dake a
kewaye da wurin da yake, Cikin Zafin Nama Ya daka uban tsalle ta tsakiyar wasu
bishiyoyi, Kamar an jeho shi Ya faɗo Tsakar wurin da Su Naufal su ke, Gaba ɗaya sun
fita hayyacin su, Halittun sun kewaye su sai gurnani su ke yi, Naufal da javed sun
ƙanƙame Juna, Kuka hada majina fuskokin su jaga jaga da hawaye, wandunansu a jiƙe
sharkaf da ruwan fitsarin da suka saki, Ɗan iskan murmushi dangerous terrorist Ya
saki kafin Ya zaro bingidar da ke soke a qugunshi, Ya saita Jikin Halittun ɗaya
bayan ɗaya yake sakar masu alburushi, duk wadda ya harba nan take Tsakiyar Cikinta
yake tarwatsewa Ƴan hanji su fito waje, Sautin harbin bindigar da basu ta6a ji bane
Yasa su rikicewa Kusan atare suke yanke jiki saman koraren Ciyayin suka faɗa a
sume, Tuntsirewa Baturen yai da dariyar shaƙiyanci Yana faɗin

“Yaran nan kuna da ban dariya, Sai ka ce ba maza ba? Kun iya shiga daji amma ba ku
Iya faɗa ba? Zaman gida da sanya buje zaifi da cewa da ku, In yaso kun cigaba da
taya iyayen ku shiga kitchen yin girki” acikin harshen turanci ya ke yin maganar.

Gabanshi Ne yai mugun faɗuwa Jin ƙarar Jirgi A cikin kunnuwansa, Da sauri Ya kai
idanuwansa saitin rassan bishiyoyin da suka lullu6e sararin samaniya, nan ta ke
yanayin fuskar shi Ya canza daga annuri zuwa tsantsar baƙin ciki, fargaba da tashin
hankali, Juyawa yai da gudun gaske tamkar zai tashi sama Haka ya dinga buga uban
tsalle Yana gudun Ceton, ga dukkan alamu bai da gaskiya shiyasa ya ƙe ƙoƙarin
gujewa waɗanda suka kawo mashi Hari, tuni Ya jima da jefar da tabar hannun sa,
kwata kwata Baya a cikin Hayyacinsa, shi kansa baisan in da ya ke wurga
ƙafafuwanshi ba, saboda tabar firgicin da ya shiga, ko ma su wanene su ka biyo shi
sun shammace shi bai yi tsammanin za’a gano inda ya 6uya ba.

Sautin Ƙarar danƙareran Helicopter mai saukar angulu Ƙirar UH-60 Black Hawk
mallakin Sojin Ƙasar amurka ne Ya karaɗe ko’ina Na Cikin Dajin Evil forest Hatta
rassan bishiyoyin da ke a cikin dajin girgiza su ke yi saboda ƙarfin iskar fankar
Jirgin, har wani jijjiga ya ke yi tamkar zai fasa dodon kunnan mutun, Shawagi ya ke
yi a saman Iska Yana kewaye ko’ina.

Hot soldiers din da ke a tsaye baƙin ƙofar jirgin zafafan gaske fusatattun sojoji
masu ji da ƙarfi, cikin shigarsu Ta ka ki sun ɗaura ɗamarar Ya ki, Ɗaya daga cikin
su Hannayen sa biyu Na ruƙe da Telescope abun hangen nesa, Ya kanga shi saitin
idanuwansa, Sojan da ke a gefen shi Yana Ruƙe da Tactical phone wayar da sojoji ke
Yin amfani da ita wurin yin sadarwa da Manyansu dake acan headquater, Cikin Harshen
turanci Ya ke Sanar da su cewa Sun ƙaraso Dajin ayanzu hake suna kewaye shi domin
gano Location ɗin da ɗan Ta’addan Ya 6uya a dajin.

Me ruƙe da abun Hangen nesan ne Ya soma magana Yana ɗaga murya ya ke faɗin A samu
wuri a sauke Jirgin Yana zargin me laifin Yana a yankin da su ke, Jin maganar Shi
Yasa sojojin dake sarrafa Jirgin su ka Soma ƙoƙarin Samun wurin Da zasu Sauka, A
hankali helicopter ɗin Ya ke yin ƙasa tunkafin ya ƙarasa direwa, Sojojin suka soma
diddirowa ƙasa Sautin Army boots ɗin dake a kafarsu Yana bugun ƙasa kamar zasu dare
ta, Hannayensu ruƙe da Jibga jibgan bindigu, Haka zalika qugunansu na soke da
pistols ƙananun bindugu, Sun rufe kawunansu da helmet (hular kwano) Hatta faces ɗin
su ba ka Iya gani, Iya idanuwansu ne kaɗai a bayyane, Kusan su shidda ne su ka
sauko daga jirgin, Da hannu Commender ɗin su ya rarraba su zuwa gida Uku, kafin ya
basu Umarnin shiga Dajin, Da gudun gaske Su ka faɗa cikin zafin nama su ke
kurɗaɗawa Cikin ƙurmin Dajin, Babu tsoro ko fargaba suna da ƙwarin gwiwa akan aikin
su da ƙwarewar su, kuma suna da tabbacin za su yi nasarar Yin aikin da aka turo su,
saboda duhun dajin Da fitilu masu haske su ke yin amfani wurin haska gabansu.

Gaba ɗaya sun Yi matuƙar galabaita, tun suna tiƙar gudu Hancin Angel Ya soma
bleeding zufa duk ta wanke fuskokinsu da jikinsu, Maƙoshinsu ya bushe ƙamas sai
azabar raɗaɗi da ƙaiƙayin da ya ke yi masu

ƙafafuwan su Zogin azaba su ke yi masu, Sun rasa ina zasu tsoma ransu su ji daɗi,
Suna a tsaka mai wuya tsakanin mutuwa da rayuwa, Kurar dake a biye dasu Tana gab da
zata cimmasu, Wani irin uban tsalla ta daka tana Gurnani Ta takaiwa Ƙafar Angel
Cafka da haƙoranta, wata irin gigitacciyar ƙara ta fasa ita da Gabriel a matuƙar
razane.

Kurar na ƙoƙarin Gutsire ƙafar Ba zato ba tsammani, Sautin dirar bullet Ya ratsa
kunnuwan su, Basu san daga Ina aka harbo bullet ɗin ba, Gaba ɗaya ya tarwatse Kan
kurar, Nan take ta saki ƙafar Angel Ta faɗi ƙasa tana birgima, wata irin nauyayyar
ajiyar zuciya Gabriel Ya sauke Yayin da zufa ke cigaba da wanke fuskarshi, angel
kuwa Tsabar firgice ne Yasa ta yanke Jiki Ta faɗi ƙasa a sume tamkar matatta.

Hankalin Gabriel Ba ƙaramin tashi yai ba, Ganin yadda Angel ta zube, Cikin
shessheƙar kuka ta wanda ya gama galabaita muryarsa na kakarwa ya furta sunan ta da
ƙarfin”Angel! no!No! Don’t die Angel, Na shiga Uku, Pls Angel ki tashi Ina zansa
rai na!”

Fuskarsa sharkaf da hawaye yake yin maganar, Zuciyar shi a karye Ya zube saman
gwiwowinsa agaban Angel, Ya dinga kuka yana jijjiga jikinta Da hannayenshi, Sam
baya acikin hayyacin sa, shiyasa ma bai yi tunanin Su wanene suka kashe Kurar ba,
duk a tunanin shi Angel ta mutu ne, duk yabi ya zauce ya rasa madafa.

Jin Takun Tafiyar Mutanan da ke tunkaro shi ne yasa shi saurin wurga eye balls
ɗinsa da suka kaɗa jawur Yana duban su, Sojoji ne Su biyu Hannayen su Ruƙe da
Bindugu, duk da baya acikin hayyacinsa saida Ya zabura yana neman guduwa a zaton
shi Gianta ne na gidan kurkukun ƙaddara.

Kakkausar Muryar Sojan ce ta ratsa kunnuwanshi”Don’t Move or else i will shoot ur


head wit My gun”

Wannan maganar da ya yi ce tasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar ba tare da ya juyo


ya kalle su ba, ya soma magana cikin rawar murya

“Just kill me so that I can finally rest, Na rasa ƴan uwana, bani da burin cigaba
da yin rayuwa a duniyar nan, ku kashe ni kawai idan ba haka ba ni zan kashe kai na”
Yana magana zufa na tsastsafowa ta jikin fatar shi.

Muryar Sojan ce ta kara ratsa kunnanshi cikin harshen turanci yace

“ba zamu kashe ka ba, rayuwarka tana da mahimmanci a wurin mu, Aikin mu shi ne mu
shiga tsakanin ku da mugun da ya yi garkuwa da ku Ya kawo ku cikin Dajin nan, Idan
ka bamu haɗin kai zamu mai da ku ƙasar ku” tun da Sojan Ya soma Yi mashi magana
Cikin kwantar da murya, sai ya ji natsuwarshi ta fara daidaita, kuma ya fahimci ba
jami’an kurkukun ƙaddara ba ne.

Da sauri Gabriel Ya waiwayo baya yana dubansu, a jere suke tsaye su biyu, Yawu ya
haɗiya Muryarshi still adabarbarce ya furta”idan har dagaske kuna son taimakona,
akwai ƴan uwana da suke a cikin dajin, muna acikin mayuwacin hali, wasu mugayen
halittune suka biyo mu, ina tsoron su kashe min su” Jin wannan Maganar Yasa ɗaya
daga cikin sojojin ya tasa ƙeyar gabriel Gaba, Zuwa Cikin dajin.

Yayin da ɗayan Sojan da su ka bari a tsaye gaban Angel ya soma magana ta hanyar yin
amfani da tactical phone ɗin hannun shi, Ya sanar da commender game da yaran da
suka tsinta a dajin, suna zargin ɗan ta’addan ƙasarsu ne ya gudo dasu cikin dajin
yai garkuwa da su don ya kare kanshi daga farmakin da zasu kawo mashi.

Commender ɗin ya ba da Umarnin A tattaro yaran dukansu, a lokacin har sunyi nasarar
Cafke ɗan ta’ addan da su ka zo kamawa, Mugun ɗauri suka yi mashi duka jikinshi
suka nannaɗe da igiya suka ɗaure shi tamau bayan sun yi mashi allurar kashe ƙwarin
Jiki gudun kada ya kubce masu saboda sanin shi da su ka yi, mugun ɗan ta’adda ne
mai hatsarin gaske, A cikin jirgin suka wurga shi.
A saman Kafaɗa Sojan Ya ɗaura Angel Ya nufi wurin da suka sauke helicopter ɗinsu, A
ciki ya shigar da ita ya kwantar, Bada jimawa ba, sai ga wasu sojojin su biyu ɗauke
da Nufal da Javed saman kafaɗin su. bayan sun shigar dasu Cikin jirgin sai ga kira
daga Ɗayan Sojan daya tafi da Gabriel gaba ɗaya suna jin muryarshi ta cikin
wayarsu, sanar da su yai akwai sauran yaran da zasu nemo acikin Dajin, Yana buƙatar
a turo Wasu sojojin da zasu ɗauke su, Umarni commender yaba sauran sojojin da suka
dawo akan su je su zaƙulo sauran yaran, Da gudu suka kutsa cikin Dajin.

Gabriel da sojan da ya taso ƙeyar sa suna cikin Tafiya sai faman wurwuga ido
gabriel yake yi a ƙoƙarin shi na ya gano inda su Batul su ke, Gabanshi sai faɗuwa
ya ke yi tsoron sa kada ace halittar nan ta hanɗame su, Har zasu gifta kwatsam ta
wutsiyar ido Soja Ya hango launin jajayen kaya ƙuɗundune cikin koraren ciyayi da
sauri ya furta”wait” hakan yasa Gabriel dakatawa da yin tafiyar, Reverse sojan yai
tare da juyar da kanshi Ya wurga ƙwayar idanuwanshi saitin wurin da ya hango jan
uniform ɗin, Gabriel na yin tozali da su da ƙarfi ya furta sunan Azeeza, da gudu ya
nufi wurin da suke maƙale da juna babu numfashi, Sojan na ganin Ya tunkari wurin
shima yabi bayanshi, agabansu Gabriel ya zube saman gwiwonsa Yana Ambaton sunayen
su cikin karyayyiyar murya ta wanda ya Sare, kafin sojan Ya motsa Sai ga sauran
Sojojin da commender ya turo sun kutsa ta wurin da suke. suna ƙarasowa ba tare da
6ata lokaci ba suka ciccire ƙayoyin da suka sargafe ƙafafuwan Azeeza da jemimah,
Kafin su ka ɗauke su saman kafaɗunsu, da hanzari suka juya dasu zuwa cikin jirgin.
Bayan tafiyar su Sojan Ya ce da Gabriel Za su Iya tafiya yanzu? Da sauri ya
girzgiza kai, cikin disasshiyar murya ya faɗa mashi”Akwai sauran mutun uku da babu
acikin su” Sojan Yace ya tashi su shiga neman su, Ba su buƙatar 6ata lokaci, Akwai
Iya adadin da aka basu, Idan har ya cika zasu tafi ne” jin haka yasa Gabriel Miƙewa
shi kansa ba ƙoshin lafiya ne dashi ba, ƙarfin haline kawai.
A ƙalla sun shafe tsawin mintuna goma shabiyar suna neman Su Batul, Sai kurɗaɗawa
suke Yi cikin dajin babu su babu alamarsu, ganin zasu 6ata lokaci yasa sojan ce
mashi”Su tafi kawai, Zai iya yiwuwa sun rasa rayukansu ne” kamar ƙaramin yaro haka
Gabriel ya fashe mashi da kuka tare da zubewa saman gwiwowinsa Ya ruƙe ƙafafuwan
Sojan Ya dinga kuka Yana roƙonshi akan kada su tafi su bar ƴan uwan shi a dajin,
Shi yana ji aranshi suna araye wata’ƙil sun faɗa wani wurin ne sakamakon muggan
halittun da suka tsoratar dasu,’ Tsawa Sojan Ya daka mashi a harzuƙe Ya hambare
Gabriel da ya ruƙe mashi ƙafa.

Muryarshi a kausashe yace “Get up and let’s go. Otherwise, we’ll leave you here in
the forest.” Hawaye na bin kuncin Gabriel, Ya girgiza mashi kai yana faɗin”bazan
Iya tafiya nabar su ba, Atare muka sha wahala, bai kamata mu tsira mu ƙyale su ba,
ni banga gawarwakinsu ba, Tayaya zan yadda sun mutu,” numfashi yaja kafin ya ɗaura
da cewa”Zaku iya tafiya da waɗanda kuka ɗauka, Ni ku barni anan zanje na nemo ƴan
uwana ko da ace zan rasa raina ne” Juyawa Sojan Yai a fusace Ya soma tafiya, Sai da
yai nisa zuciyarshi ta soma tariyo masa kalaman Gabriel, Dakatawa ya ɗanyi yana
wani tunani, ga dukkan alamu kalaman sun ta6a zuciyarshi, A hankali ya ɗan waigo
Baya yana dubanshi, Bawan Allah Ya kifa kansa saman ciyayi, Sai kuka yake yi kamar
ranshi zai fita, takaicine ya ishe shi ga samu ga rashi, Yasan muddin sojojin suka
tafi shida barin dajin har bada, a ƙarshe ma ya rasa ranshi, sai dai baya jin zai
Iya binsu alhalin sauran ƴan uwanshi da suka sha wahala suna acikin dajin! ya
zasuji idan suka dawo hayyacinsu suka taras babu su? Me zai biyo baya?

A lokacin da Gabriel baiyi tsammani ba, muryar Sojan Ta ratsa kunnanshi

“Yaro ka ci albarkacin sarƙar cross ɗin da ke a wuyan ka, A karo na biyu zan
Taimake ka, mu gano sauran Ƴan uwan naka” wani irin farin Cikine ya lullu6e Gabriel
Jiki na rawa ya yunƙura Ya miƙe, kafin su fara tafiya sai ga sauran Sojojin da su
ka je kai su Azeeza hada ƙarin wasu kusan su shidda suka nufi Dajin neman sauran
Yaran, Marece ya nutsa abun da sojojin suke gudu dare ya yi masu a dajin saboda
Sanin hatsarin dake gare shi, Daƙyar Gabriel Ya samu Ya gano masu hanyar wurin da
suka yi shimfiɗarsu, da gudu Ya nufi Danish da ke a kwance yana sharar baccin shi.

Tun kafin sojojin su ƙarasa Gabansu yai wani irin faɗuwa saboda razanar da su ka
yi da ganin shi, Wani abu ya ɗaure masu kai, har saida su ka kalli junansu da
alamun ruɗu akan fuskokin su, Ba Iya kyawun Fuskar Danish bane Ya girgiza su,
Zazzafar surar Jikinshi Ta yi matuƙar rikitar dasu, Kaf a cikinsu babu mai kalar
ƙirar ƙarfin shi, Hakan ba ƙaramin kokwanto Ya saka masu ba acikin zuciyoyin su,
har sun fara kokwanton Anya kuwa ɗan ta’addan da suka Biyo ne yai garkuwa da yaran?
Ta ya ya za’ai ɗan ta’addan Ya iya sato wannan jibgegen ƙaton mai ƙirar sadaukan
Yaƙi, a ganin su ko shi ɗan ta’addan bai kama ƙafar Matashin yaron ba wurin zubin
halittarshi.

Muryar Gabriel da sassarfa yake Ambaton sunan danish Hannayenshi duka biyu akan
jikinsa sai jijjigashi yake yi yana faɗin”Danish ka tashi, mun samu taimako za’a
fidda mu daga cikin daji, Har ma an tafi dasu Angel, pls ka tashi, Bana so mu tafi
mu bar ka”

Ko motsi Danish bai yi ba, ganin haka yasa shi juyawa yana kallon Sojojin, Sun
ƙame a tsaye suna kallon Abun al’ajabi kusan suman tsaye sukayi yayin da suke
kallon Danish
“Dan Allah ku taimake ni, ɗan uwanmu ne, haka Allah ya halicce idan Yana yin bacci
yakan ɗauki tsawon awanni bai farka ba,” a ruɗe yake kora masu bayani, duk don ya
samu su tafi da Danish kada suce zasu barshi anan, don ya fahinci tashin shi ba
yanzu ba

Daƙyar ɗaya daga cikin sojojin ya iya shanye mamakin shi ya sarrafa kanshi wurin
furta” bai da lafiya ne? Ko ya suma ne”?

“A’a, bacci ya ke yi, kuma ba zai Iya farkawa yanzu ba, ....”tun kan ya ƙarasa
maganar ɗaya daga cikin soldiers ɗin Ya zaro penlight ya zuƙunna agaban
shimfidarsa, da yatsun hannayensa yai amfani wurin gwale idanuwan Danish ya haskasu
ya tabbatar da yana araye ga numfahi na fita a tsanake, Kallon sauran sojoji
yai”he’s alive” jin haka yasa suka gasgata maganar Gabriel, mutun Biyu suka
ranƙwafa tare da ɗaura hannayensu da nufin su cuccu6i Danish sai dai wani abun
ɗaure kai ko motsi baiyi ba, saboda tsabar nauyin sa duk irin ƙarfin da Allah ya yi
ma sojojin na halitta da kuma na horon aikin da suka samu baisa sun Iya cuccu6ar
Danish ba, A ƙarshe suka Yanke shawarar zuwa ɗauko stretcher domin ɗaukar shi,
zaifi Yi masu sauƙi, abun ɗaukar Majinyatane da ake amfani dashi, Yana da maruƙi a
jikin sa, saman shi faɗine dashi kamar allo, bayan sun ɗauko stretcher ɗin Saida
suka haɗa ƙarfi su huɗu tukunna su ka iya cuccu6ar Danish tare da ɗaura shi saman
abun ɗaukar, su ka ɗaga shi har zuwa Bakin helicopter din kafin suka samu damar
shigar dashi ciki, Bayan sun tafi da danish Ɗaya daga Cikin Sojoji biyu da suka
rage Ya ɗauki Back pack ɗinsu da ya gani a jikin bishiya, don suna buƙatar duk wasu
shaidu da za su zamar masu hujja.

da hannu ɗaya ya ruƙo jakar ɗayan hannun kuma ya ruƙe hannun akwatin kayansu Yaja
shi zuwa Bakin jirgin.

A can Cikin Dajin Gabriel ne Ya rage tare da Sojan nan, Suka kuma kutsawa cikin
dajin Don ya sanar mashi akwai sauran Ƴan uwanshi, Abun dai ya ɗaurewa Sojan kai,
Su fa duk a tsammaninsu ɗan ta’addanne ya yi garkuwa da su daga ƙasar su america
Ya shigo da su Dajin, Saboda Yaran sunyi kama da mutanan ƙasarsu, Hasken fatarsu da
Doguwar sumar kawunansu, a hasashensu kenan, sai dai duk da haka sun ɗanyi mamakin
wasu abubuwa da suka sanyasu yin al’ajabi, tayaya har ɗan ta’addan ya iya guduwa
dasu bayan ƙasarsu tana da mugun tsaron da babu wani shege da ya isa Ya ƙetare ta
cikin Salama, Abu na biyu Ta ya ya Ɗan ta’addan Ya iya ɗaukar mutun mai mugun Nauyi
irin matashin saurayin da suka gaza ɗagawa? Abu na uku da ya ɗaure masu kai Uniform
ɗin Jikin yaran masu ɗauke da numbobi sunyi mamakin hakan.

Suna Cikin yin tafiya, Zuciyar Gabriel na dakan uku uku tamkar zata faso
kirjinshi ga kishirwa da ya ke ji, babban tashin hankalin shi Ina Su Batul suka
kutsane a cikin Dajin? Ga dare yana shirin yi masu adajin, fargabansa kada sojojin
su ce zasu tafi.

“Kana tunanin ƴan uwanka zamu same su? Lokaci Yana ƙure mana” Sojan ne yai
mashi maganar, gabriel bai samu damar amsa mashi ba saboda tashin hankalin da ya ke
aciki, Sai faman wurwurga ƙwayar idanuwansa ya ke yi akan bishiyoyin dake a kewaye
dasu, Suna Cikin yin tafiya suka ƙaraso gaban wannan ramin mai ɗauke da ta6o, har
zasu gifta shi Kwatsam Sojan Yaji ya taka wani abu, Da sauri Ya ɗage ƙafarshi yana
kallon Warin Slipper ɗin dake asaman ciyayin, Gabriel na ganin takalmin Ya zuƙunna
tare da kai hannu ya ɗauke shi, Gabansa ne ya faɗi A gigice ya kalli sojan tare da
furta”Takalman Ƴar uwata ne!” Ya gane slippers ɗinsu ne Da tsohuwa Tamira tai masu
kyautarsu, dama tunda suka shigo Dajin da takalmansu suke yawo a ƙafafuwansu,
shiyasa ko ƙaya ba ta ta6a shigarsu ba.
“Dan Allah ka taimaka mun, wlh takalmansu Batul ne ƴan uwana” Muryarshi na rawa
yake maganar, cikin ƙagara.
Waige-waige Sojan ya ke yi yana bin ko’ina Na dajin da kallo, Kafin ya sauke
idonshi akan Ramin ta6on, kasancewar Sojoji suna da ƙwarewa wurin sanin takan Daji,
Nan take ranshi ya bashi cewar Ta6on da ke a wurin Ramine, mutun zai Iya rubzawa
cikinsa, musamman wanda ke gudu cikin fitar hayyaci.

Matsawa yai gaban ramin, Bayan ya soke bingidar hannun shi a ƙugun shi, Ya ɗan
zuƙunna saman ƙafarshi, a tsanake Ya tura hannun shi Cikin ramin ta6o, Cikin sa’a
Ya damƙo gashin ɗaya daga Cikin su, matsar da hannun shi yai ya ruƙo Hannunta, Ya
ɗago da ita gaba ɗaya jikinta ya 6aci kaca kaca da ta6on baka Iya ganin komai na
fuskarta, hatta Gabriel bai gane wacece a cikin su ba, A ƙasa sojan ya kwantar da
ita tare da ƙara zura hannun shi Ya ƙara cafko hannun wata ya curo ta, bayan ya
kammala zaraso duka ukun Gabriel Yace mashi suke nan babu saura, Jin haka yasa
Sojan Zaro wayarshi Ya sanar ma sojojin dake a bakin helicopter din cewa sun ƙara
samu Yara Uku azo da stretcher a ɗauke su, Cikin ƙanƙanin Lokaci sai ga sojoji
sunzo da abun ɗaukar, duka ukun suka ɗaurasu saman shi kamar tsummokarai haka suka
nannaɗe.

Sojoji biyu ne suka tafi dasu zuwa Inda jirgin ya ke, Hankalin Gabriel Ya ɗan
kwanta sam ya manta da Haris saida suka kamo Hanya zasu Nufi jirgin ba zato ba
tsammani su ka ci karo da haris a sume, Ba tare da 6ata lokaci ba, Sojan da suke
atare Ya sa6e shi saman kafaɗa, suka nufi Jirgin Bayan sun Shiga su dukansu.
Matuƙar jirgin suka Tada shi, Da wata irin jijjiga tayoyin jirgin su ka soma
motsawa suna yin tafiya sannu a hankali, Gabriel da ya kasance shi kaɗai idon shi
biyu, farin Ciki duk ya cika shi, sam baiyi tunanin wace ƙasa za’a kaisu ba,
hankalin shi bai kai nan ba, fatan shi su bar dajin Cikin ƙoshin lafiya.

Bayan tashin jirgin sama Ɗaya daga Cikin sojojin dake a tsaye bakin ƙofar
helicopter ɗin ne Ya kanga Tactical phone ɗin hannunsa jikin kunnansa Yana magana
Cikin Harshen turancin muryarshi na fita da amon murya saboda ƙarfin iskar Dajin

“We successfully apprehended the criminal. We are now on our way back to the U.S.
with the eleven children we found in the forest.” (Munyi nasarar cafke mai laifin,
yanzu muna akan hanyar mu ta dawowa U.s, tare da yara goma sha ɗaya da mu ka samu
a dajin)
Da wani irin speed jirgin ya karya kwana ya miƙi hanyar komawa ƙasar da ya fito.

*Alhamdulillah Finally Ex-prisoners sun Bar Evil forest Fatan Nasara*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E12🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

*GIDAN ƊAN IYA*

Gaba ɗayan su sun Hallara a bakin Entry hall na shiga palourn gidan, Mommy da Mami
sun yi matuƙar yin kyau cikin shigar Lace, Zahra da Aneelerh sai Abie da Uncle ɗan
Iya sun yi shiga ta alfarma, Bakomai ne yasa su fitowa ba fa ce tarbar Su Hajiya
adama, A ƙagare su ke da ganin baƙin nasu, badajimawa ba su ka kira Aneelerh awaya
su ka sanar da ita cewa sun shigo garin abuja, har ta tura masu da addrress ɗin
gidan.

Ƙarar Horn ɗin motarsu ne Yasa kowan nan su Sakin fuskarshi, da sauri mai gadi Ya
fito daga ɗan ɗakin sa, Ya je ya buɗe masu gate.

A hankali Danƙareriyar Motar uncle abdallah ƙirar Kia optima ta kunna kai cikin
gidan kai tsaye ya nufi wurin Ajiye motocin su, bayan yai parking ɗin motar, Ya
fito daga ciki fuskar nan ɗauke da annuri, ya ɗauki wankan shadda gezna,
ƙafafuwanshi na asanye da patent leather shoes launin Shaddar shi, ƙamshi ta
ko’ina.

Zagayawa yai ta other side ɗin motar ya buɗe ma Hajiya adama ƙofa, ƙafar ta ta
fara zurowa nan take Zahra ta ɗan zaro ido tare da kallon Aneelerh, murmushi gefen
fuska Aneelerh ta sakar mata don ta fahimci abunda ya sa zahra mamaki, wato tsadar
High hills ɗin dake ƙafar Hajiya adama.

Zahra ta ƙware wurin sanin farashin Kaya, A kunne ta yi ma Aneelerh whispering

“Surukar ki Ta ji naira yasin, Takalman ƙafarta kalar na saratu obinna ne” girgiza
kai Aneelerh ta yi ba tare data tanka mata ba.

Lokacin da Hajiya Adama ta ƙara sa fitowa daga Cikin Motar ba ƙaramin tafiya ta yi
da imaninsu ba, saboda tsabar wankan kece rainin da ta ɗauka na tsadadaddan Swiss
cord lace launin brown mixed wit yellow, Riga da zani ne ta daura, kanta yasha
ɗaurin ɗan kwali, sarƙar wuyanta da awarwaron hannun ta, da zabbanta duk na zinari
ne, ta yarfa mayafin kayan saman kafaɗarta, babu make up a saman fuskarta zallar
kyan da Allah ya yi mata ne, Hajiya adama akwai kyau ga diri.

Kallon abdallah ta yi fuskarta ɗauke da murmushi, da hannu yai mata nuni da


surukansu da ke a tsaye suna fuskantar su

“mu je ko?” Sai lokacin ta lura da su, tafiya suka soma Yi a jere tunkan su ƙaraso
Zahra take ta faman ingiza kafaɗar aneelerh

“ki je ki tarbo su,”

kunya ta hana Aneelerh zuwa, har saida suka ƙaraso, Abie Yana dariya Ya ruƙe
hannun Abdalla suka fara yin gaisuwarsu ta manya”Marhaban marhaban lale surukai na
gari, Sassannun ku, kun sha hanya, ku ƙaraso ciki” Ya ja hannun abdallah, Mamie da
hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su ɗauke da murmushi, bayan sun
raba jikinsu, Ummi ta miƙe mata hannu suka gaisa a mutunce”Sannu da zuwa Hajiya, mu
shiga daga Ciki” ta yi maganar, tare da jan hannun hajiya adama wadda idonta ke
akan Aneelerh, sai faman noƙe kai ta ke yi,
“Kunya kamar bafullatana, Ni kaina da nake bafullatana Bani da kalar kunyarki,” da
zolaya hajiya adama ta yi maganar, Yayin da su ke shiga cikin babban falourn gidan,
daddaɗan ƙamshin turarensu ya gauraya da sanyin A.c.
A saman soma mai mazaunin mutum uku Mami da ummi da hajiya adama su ka zauna, Abie
da Uncle ɗan iya su ka zazzauna saman 2 sita, Aneelerh tana zaune saman one sita,
Yayin da zahra ta ɗan zauna saman hannun sofa ɗin da Aneelerh ke zaune, sai faman
sakarwa juna murmushi suke Yi, Gaisuwa ta musamman suka ƙara yiwa junan su cikin
girmama juna da mutuntaka.

Uncle ɗan Iya Yana faman washe baki Yace”Abdallah Kai ne ka koma haka?gaskiya mun
daɗe bamu haɗu ba, tun lokacin da ka fito daga cikin mota, idanuwana su ka yi
tozali da kai sai da gabana ya faɗi araina nace ina muka samu baƙin Bature,
Abdallah hutu ya zauna maka daga kai har Hajiyar taka kun yada zumunci ko in ce mun
yada zumunci Allah dai ya shiryemu” dariya suka saki gaba ɗayan su.

Ummi tace”Ya gajiyar tafiya? Nasan Kun jigata sosai, tafiya daga jos zuwa abuja ba
abune mai sauƙi ba, kun ma yi ƙoƙari dana ganku da kuzarin ku”

mami ta ɗaura da cewa”Alhamdulillah mun gode ma Allah da ya kare mana ku ya tsare


mana ku har ku ka ƙaraso Lafiya, wannan abun farin ciki ne agare mu, gamu ga
surukanmu, mutane masu ƙima da daraja, muna ƙara yi maku barka da zuwa” Maganar
Mami ta yi matuƙar faranta zuciyoyinsu.

Musamman Hajiya adama har saida ta ɗan saki murmushin da ya bayyana jerarrun
fararen haƙoranta.

A tsanake tace “A gaskiya ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba, ni
dama tun da muka fito daga cikin mota raina Ya bani munzo gidan mutunci da karamci
musamman da naji gidan Uncle ɗan Iya ne Masha Allah, Fatan mun same ku lafiya”
atare suka haɗa baki”Lafiya lou Alhamdulillah”

Uncle abdallah ne ya soma yin magana cikin dattako da halin girma


“Mun jin daɗin samun ku cikin ƙoshin Lafiya, Abun farin cikine wannan kuma muna
godiya da irin tarbar da muka samu, Ina yi mana fatan kamar yadda muka haɗu anan,
Ubangiji Allah Ya haɗamu A gidan aljanna alfarmar Annabi muhammad SAW, kusan atare
suka haɗu wurin furta kalmar SAW

“Yakamata mu fara yiwa annabi Salati” Abie ne yai maganar, tare suka ɗaga
hannuwansu bayan sunyi salati ya ci gaba da jero masu addu’o’i Suna amsawa da ameen
ameen Bayan ya kammala, Uncle ɗan Iya ya wurga idon shi kan Aneelerh da ke ta faman
sakin murmushi tana noƙe kai
Jin Muryarshi tasa ta ɗago da ido tana kallon shi
Daƙuwa ya sakar mata”Ungo nan, jira ki ke sai mun ce ki je ki gaishe da surukan
naki? yarinya sai ka ce jinin fulani” Tsuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayansu,
Yadda yai magana yai matuƙar basu dariya hada Aneelerh, Da sauri ta miƙe daga saman
sofa ta nufi Hajiya adama daga ƙasa saman carpet ta zauna gefen ƙafar Hajiya adama,
muryarta ƙasa ƙasa ta furta”Sannunku da zuwa, Ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro
mutanan can” ɗaura hannu hajiya adama tayi saman kafaɗar Aneelerh

“Lafiyalou daughter in-law Fatan na same ki Lafiya”


Aneelerh ta amsa da lafiyalou, kafin ta matsa gefen uncle abdallah Ta gaishe da
shi, da fara’a ya amsa mata

Bayan sun gama gaisawa da aneelerh, Zahra ta gaishe dasu, suka amsa mata
Kafin daga bisani, Mami tace”bismilla mu shiga ciki, Ku huta kada mu Cika ku da
surutu, “ ta faɗi hakan ne don tasan yanayi na matafiya yafi buƙatar hutu, Miƙewa
su ka yi Mami da Abie na agaba Hajiya adama da uncle abdallah suna abiye dasu,
wuce abie yai da uncle abdallah zuwa ɗakinsa, Itama mami ta wuce nata ɗakin tare da
hajiya adama bayan tafiyar su.

Fira ta 6arke tsakanin Zahra da Ummi, a lokacin Uncle ɗan Iya ya fita waje domin
amsa kiran da akayi mashi a waya

“Wlh ummi takalman ƙafarta kalar na saratu obinna ne, kinsan ko kuɗinsu yakai dubu
talatin” Ɗan zaro ido Ummi ta yi” Tab Aneelerh ashe surukan ki Attajiran masu kuɗi
ne, ai naga sarƙar wuyanta da awarwaron hannunta duk na zanari ne, gaskiya kin taki
sa’a, Yarinya mai ƙashin arziƙi,”

kwa6a fuska Zahra ta yi”ni kuma mai ƙashin tsiya ko”? ummi na dariya tace”Ni dai
bance ba, kema ina maki fatan miji na gari da surukai na gari” yatsina fuska ta yi
ƙasa ƙasa da murya ta furta”Suruki na gari kamar Owais, surukai na gari hamshaƙan
masu kuɗi irin hajiya sarauta” Aneelerh dake zaune saman carpet ta miƙe ta koma
saman sofa ta zauna
Ummi ta kalleta”nasan zasu buƙaci ganin jikansu, gashi ya tafi school till 6 na
marece za’a tado su saboda lesson na Islamiya da ake Yi masu, “ zahra tace”Zan kira
mahboob A waya ya je ya ɗauko shi, Ni fa dama can banso aka sanya shi hada
islamiyyar ba, ace kullum sai ƙarfe shidda zai dawo gida, in banda weekend,”

Harara ummi ta ɗan watsa mata”Sannu Uwarsa, islamiyarce ke ba ki so ya yi kenan sai


dai na bokon” Girgiza kai zahra tayi”Ba haka nake nufi ba ummi, Yaron ya yi ƙaranta
brain ɗinsa ma ƙarama ce ta ya ya ki ke tunanin zai Iya ɗauke duk abunda aka koya
masa”

Tun da suka fara magana aneelerh ta yi shiru tana kallonsu, acan ƙasan zuciyarta
kewar baby junaid ce ta addabeta, maganar zahra tasa duk ta ji ba daɗi ita kanta ba
ta son Yana kaiwa har ƙarfe shidda sai dai ba yadda za ta yi ita kanta tana so
yaronta ya saba da karatun boko dana addini.

Tsawon lokaci suna fira a tsakanin su jefi jefi har aka fara kiran sallah, Abie da
Uncle abdallah suka fito da haramar zuwa masallaci, a harabar gidan suka yi arba da
uncle ɗan Iya zaune saman Kujera Yana danna waya, Abie ya ce da shi Ya tashi su je
masallaci, A nan suka jira shi ya shiga gidan ya ɗauro alwala kafin ya dawo suka
ɗunguma zuwa masallacin dake a kusa da gidansu

Acan Cikin Gidan kowa ya koma ɗaki domin yin sallar magrib, hankalin Aneelerh
Yaƙi kwanciya, Jin shiru mahboob bai dawo mata da yaronta ba, Gashi har an kira
sallah. A zaune ta ke saman darduma hannayenta Biyu sama tana jera addu’o’i tasha
dogon hijabinta.
Ba zato ba tsammani ta ji saukar mutun saman Bayanta, Ya ƙanƙameta Yana tiƙar
dariya”babyn mommy is back” Gabanta harya faɗi sai da taji muryarshi tukunna ta
sauke ajiyar zuciya, haɗi da ɗan sakin murmushi jin ya kirata da sunan da
malamansu suke kiranshi wato babyn mommy, bayan ta shafa addu’ar, ta zagayo da
hannunta ta ruƙo damtsen shi ta zagayo da shi tare da zaunar da shi saman laps
ɗinta, Kamar kullum fuskarshi duk jirwayen hawaye, uniform ɗin jikin shi riga ce
fara sai wando red colour, daga saman rigar akwai ƴar coat launin Ja, kafin ya ta
fi school saida ta gyara mashi sumar kanshi amma yanzu da ta kalli sumar kan nashi
A hargitse ta ke.
Idanuwanshi luhu luhu ya furta”Mommy, kin ga banyi kuka ba yau ko? Ai kince in
daina” smiling softly tace”jirwayen menene akan fuskarka” tai maganar tana nuna
hawayen da indext finger dinta, kwa6e mata fuska yai”mommy ai ni bake nayi ma kuka
ba, uncle mahboob ne da safe da zamu school, Ya cinye min chocolate ɗina da kika
saka min a basket”

idanuwanshi cike tab da ƙwalla yai mata maganar, ranshi ya 6aci.

Ɗaure fuska aneelerh tayi”Na rasa gane me ke damun mahboob, shi bai siya maka ba
sai dai ya cinye maka? Tir wlh andai ji kunya”

“Mommy don’t worry, Ni ma ai na rama”


“Dame ka rama” da mamaki ta yi mashi tambayar, hannu taga ya zura cikin aljihun
wandonsa, ya zaro ɗan ƙaramin box mai kyan gaske Ya nuna mata
“Menene wannan”? Shu’umin murmushi babyn mommy ya saki”pls mommy kada ki yi min
faɗa, inaso yadda ya sani zubar da hawayena shima ya yi kuka, A motar shi na samu
wannan, buɗe ki gani abun da ke a ciki” yai maganar yana miƙa mata box din, bayan
ta kar6a ta buɗe akwatin, haɗaɗɗen zoben azurfa ne, na mata mai kyan gaske stone
ɗin jikin shi har ƙyalƙyali Ya ke yi,
Jinjina kai aneelerh tayi”Lallai Mahboob Ya iya kashe na ƴan mata kuɗi amma bai
Iya kashe ma ƴan uwan shi ba, dama irinsu babu mai cin moriyarsu sai mata, kowace
mai sa’ar ce wannan Ya siyama zobe kuma daga gani mai tsada ne”
“Mommy daga ni sai ke, kada ki faɗa mashi ni na ɗauka, Mubar shi yai ta wahalar
nema shima Ya ji idan akwai daɗi” Cikin 6acin rai ya ke yin maganar.
“Babyn mommy, ai ni farin cikinka shine nawa, don haka kar6i box ɗin nan ka 6oye
mana shi cikin rigar pillow,” kar6ar zoben junaid yai da gudu ya nufi gado ya
haye tare da ruƙo pillow ya zuge zip ɗinshi Ya tura box ɗin, abun mugunta ya samu
sai faman sakin murmushi yake yi kamar gonar auduga

Miƙewa ta yi daga saman sallayar, bayan ta cire hijab din jikinta ta tura a
wardrobe, Baby junaid ta ɗauka ta nufi toilet dashi, Wanka tayi mashi bayan sun
fito ta ɗauko mashi riga da wando na shadda, ta zura mashi kayan ajikin shi, ta
feshe ko’ina na jikin shi da turare bayan ta kammala gyara mashi sumar kansa ta
ɗauke sa suka nufi Palour, kafin su ƙarasa sai da ta yi mashi huɗuba akan ya natsu
ya gaishe da kakanninsa kada ya bata kunya, ya amsa mata da toh, Lokacin da suka
ƙarasa palourn babu kowa duk suna a dining area sun hallara domin Cin abincin da
aka shirya masu, dukkansu Ne a zazzaune saman dining chairs, zahra da Ana ke yin
aikin zuba masu abinci.

Farin Ciki a wurin Hajiya adama baya misaltuwa, shima Uncle abdallah sai murmushi
yake saki ganin jikan nashi, Yayi matuƙar tafiya da hankulansu, tun daga kan yadda
ya zuƙunna kamar wani babban mutun ya gaishe da su, Hajiya adama ta ɗauke shi Tana
shafa sumar kanshi tace”Masha Allah, Yaro kamar rainon turai, Jawur dashi” atare
suka ci abinci, tana ci tana bashi abaki, Junaid an samu jikin Granny, Ya ƙanƙameta
yana zuba mata shagwa6a shi ala dole ga jikallen Hajiya adama da uncle abdallah.

Bayan sun kammala Cin abincin, aka fara kirayen kirayen sallar isha’i, Mazan suka
tashi domin zuwa masallaci.
Shigowa cikin kitchen Mahboob yai fuskarshi a ɗaure babu annuri, Ana dake a
tsaye bakin sink tana wanke kwanukan da aka 6ata, Jin motsin mutun yasa ta waiwayo
don ganin wanene, ganin mahboob ne atsaye sai ta saki fuska tana faɗin”mahboob
sannu da dawowa ashe kaine banji motsin shigowarka ba” Yamutsa fuska yai muryarsa
agajiye ya furta”kin ban mamaki Ana, Yanzu hada ke aka haɗa baki wurin yin
almubazzaranci? Sai ka ce gidan Obinna abinci har kala Biyar? Ina laifin ko
shinkafa da wake ne adafa masu In yaso sai a yayyanka masu kayan lambu asama”
ranshi a matuƙar 6ace yake yin maganar, Fuskar Ana da alamun ruɗu take kallon shi
“Mahboob me kake nufi”? Hura mata hanci yai”magana nake akan almubazzarancin girka
abinci da ku ka yi saboda surukan Aneelerh” dafe kai tai da hannu ɗaya

“Pls mahboob ka daina magana kada wani daga Cikin su Ya faɗo kitchen ɗin ba tare da
sanin mu ba, bansan meke damunka ba, menene damuwarka idan an girka masu abinci
kala Biyar? Ko sisin ka babu acikin kuɗin girkin” harara ya wurga mata tamkar
ƙwayar idon zata faɗo kasa, rai a6ace ya ce”Abar zancen, Zuba min abinci yunwa nake
ji”

girgiza kai Ana ta yi kafin ta nufi dish rack ta ɗauko plate ta zubo mashi dambun
shimkafa, Ta miƙa mashi, Matsiyacan kallo yabita da shi

“Shi kaɗai aka girka? da mamaki akan fuskarta tace”yanzu ka gama zazzaga min
masifar almubazzaranci na girka abinci Kala Biyar, yanzu kuma ka ke tambayata shi
kaɗai aka girka? Dalla ni kar6i plate if not shima zaka rasa ne”

fuskarta a ɗaure ta yi mashi maganar, hakan ba ƙaramin kayar mashi da gaba yayi
ba, sassauta muryarshi yai”nifa wasa nake yi maki, dan Allah ki zuba min komai da
aka girka yunwa nake ji, idan na gama cin abincin akwai wata kyauta da zanyi maki”
magiya ya dinga yi mata daƙyar ya samu Ana ta zuba mashi abinci kala Biyar ta ɗaura
masa saman dinner table na kitchen Yana ci yana santi, Musamman da ya zo kan
Farfesun ganda, duk ya bi ya susuce hada siɗar hannu kamar ɗan maroƙi.

Bayan kammala sallar isha’i tun akan hanyar dawowa daga masallaci Uncle abdallah
yace da abie Yana so zasu wuce idan sun koma, abie yace ba zai yiwu ba, dama ba
kwana zasuyi ba? uncle ɗan Iya da ke atare da su Yace”Yaya ka ƙyale shi, sai mu ga
ta ƙofar da zai fita, Dama Hajiyar shi na cikin gidan dole shima Ya shiga, Haba
Abdallah yanzu ku kwaso uwargajiya sannan ka ce zaku tafi? A wani masauki zaku
sauka ne da yafi namu? Uncle abdallah yace”A hotel ne zamu sauka” ya 6oye masu cewa
sunyi gida a abuja, Uncle ɗan Iya na jin haka yace”ai da kuɗin hotel ɗin da zaka
bayar ƙwara ka dunƙule su ka bani sai ku kwana a gidanmu dan na fahimci kuɗin ne su
ka yi maka yawa” dariya suka saki gaba ɗayansu suna tafiya suna Yin fira gwanin ban
sha’awa, Bayan komawarsu gidan uncle adallah da abie suka nufi ɗaki atare.

Hajiya adama na akwance saman gadonta, Har ta canza kayan jikinta daga Lace zuwa
Rigar bacci, da har ta yi shirin tafiya tana jiran uncle abdallah ya dawo su tafi,
sai ga mami ta shigo ɗakin, ganin tana shirye shiryen tafiya yasa ta ce da ita ina
zuwa tace ae zasu sauka a hotel ne, girgiza kai mami ta yi ki ma daina faɗin hakan
don ba zai yiwu ba, ga gida kuma sai ku ce zaku kwana a hotel? Hajiya adama
tace”bamu son mu ɗaura maku nauyi ne, mami tace”babu wani nauyi wlh, idan ma kina
tunanin ko dan saboda gidan ƙaninsa ne, to ki kwantar da hankalin ki, gidansu ne su
biyu, kusan ma rabi da kwata na abunda aka kashe a ginin da kuɗin abie ne, Allah ne
bai nufa zamu dawo nan ɗin ba, sai daga Baya da ya samu ƙarin matsayi awurin aiki
kin ji yadda akai muke zaune agidan, na faɗa maki ne don ki kwantar da hankalin ki,
idan da kara ae gidan surukai gidan ƴan uwana ne tun da anzama ɗaya, Ga ɗan jikanmu
junaid ya ƙara mana danƙon zumunci”

maganar Mami ce tasa hajiya adama fasa shirin tafiyar, mami bata jima da fita daga
ɗakin ba Kiran uncle abdallah Ya shigo wayarta, ko da ta ɗaga kiran sanar da ita
yai game da fasa tafiyar su sai zuwa gobe, hankalin ta ya ƙara kwanciya, ba tare da
6ata lokaci ba ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, tana shirin kwanciya, muryar
Aneelerh daga waje ta katse ta, sallama tayi mata, hajiya adama ta amsa mata da
wa’alaikum salam, Suruka ta gari shigo ciki mana’

cikin Jin kunya Aneelerh ta turo ƙofar ɗakin hannunta ɗauke da baby junaid, saukowa
yai daga jikinta da gudu ya nufi hajiya adama tana dariya ta ɗauke shi kafin ta
zauna gefen gadon tana shafa sumar kanshi, ganin Aneelerh na ƙoƙarin zama daga ƙasa
yasa ta katse ta da cewa”ki Zaune gefe na, Muyi fira” komawa gefen gadon aneelerh
tayi
“Mommy barka da dare, Ya gajiyar tafiya”?

Hajiya adama tace”ai Gajiya tabi jiki tun da na ga jikana” shiru suka ɗanyi kafin
Hajiya adama ta ce”Ya haƙurin rashin da mu ka yi”? Duƙar da kai Aneelerh ta ɗanyi,
a duk lokacin da aka yi mata maganar 6acewar su tajudden tamkar an fama mata mikin
dake acikin zuciyarta ne, nan take hawaye suka cika idonta, Muryarta na ɗan uwa ta
furta”Haƙuri an gode Allah, muna ta binsu da addu’a,”
“Ko akwai wani abu da ku ke shiryawa ne game da 6acewarsu”? Jinjina kai Aneelerh
tayi”Eh mommy, dama na jira ne sai kun huta mu yi magana.....” gaba ɗaya Aneelerh
ta kwashe komai dangane da tada zancen 6acewar su Uzair ta labarta mata, annurin da
ta gani akan fuskar Hajiya adama ne Ya tabbatar mata da zata samu goyon bayanta,
“Kunyi tunani mai kyau surukata, Naji daɗin shawarar da zahra ta baki, Yarinyar
tana da hankali, duk cikinmu babu wanda yai tunanin tada zancen, idan har akaci
nasara silar shawarar da ta bada, Na yi mata alƙawarin kyauta ta musamman” Ba
ƙaramin daɗi Aneelerh ta ji ba, Mommy adama ta ɗaura da cewa”In sha Allah zamuyi
magana dashi abdallahn dangane da tada zancen, sannan zamu bada tamu gudummuwar,
fatana Allah ya dafa mana, Ya dube mu da idon Rahma, Ya bayyanar mana da su idan
suna a raye, ko da basa a raye da buƙatar muji meya faru da su”! Cikin girmamawa
aneeleeh tace”In sha Allah zamuyi nasara mommy, saboda bana son in rasa surukai na
gari irin ku” Sam batasan Ta furta hakan ba, Dariya Hajiya adama ta yi”Nima ai bana
so na rasa suruka ta gari irin ki Aneelerh, domin kuwa zai yi wuya asamu tamkar
ki,” cikin jin kunya aneelerh ta miƙe tana faɗin”Bari na kawo maki abun sha” bata
jira amsarta ba, ta yi saurin Juyawa ta fuce daga ɗakin, Bayan fitarta Hajiya adama
ta dubi Baby junaid dake kwance saman ƙirjinta, Ya tsareta da ido, tun da suka fara
magana bai tanka masu ba, ya kasa kunne yana sauraronsu, sai yanzu ya samu damar yi
mata magana

“Granny kinsan Angel” jinjina mashi kai tayi”nasanta mana, Inason Angel sosai”
marairaice mata fuska yai tamkar zaiyi kuka”baiwar Allah Angela ɗina, Mommy ta faɗa
min da ita da daddynta da daddyna sun 6ace, ni tsorona ma kada ace 6era ne ya cinye
su ba....” Zaro ido Hajiya adama tayi can kuma sai ta tuntsire da dariya
“Granny, mommyna kusan kullum sai ta yi kuka saboda su angel, ƴar baiwar Allah,
mami ta hanata Yin kuka amma bata Jin maganarta, sai da nayi mata faɗa, na nuna
mata raina ya 6aci tukunna ta daina” sosai hajiya adama ke yin dariya, Sambatu iri
iri junaid ke yi mata ba ƙaramin nishaɗi ya ke sanyata ba,
“Gobe akwai school junaid, mu kwanta mu yi bacci” maƙe mata kafaɗa yai”Ina
tsaraba na”?
“Nayi maka amma sai gobe zan baka, nafi so ka huta yanzu muyi bacci” amsa mata yai
da toh mu jira mommy ta kawo mana abun sha ko? in mun sha sai mu kwanta,
Turo ƙofar ɗakin Aneelerh tayi hannunta ɗauke da cup of coffee asaman table ta
ajiye mata shi, Godiya hajiya adama tayi mata, daga nan su ka yi sallama da junansu
Aneelerh ta fuce,
Atare da junaid suka sha coffee ɗin Bayan sun kammala, Hajiya adama Ta kwantar
dashi ta tottofe shi da addu’a, sauka tai daga saman gadon ta nufi switch ta kashe
hasken ɗakin, kafin ta dawo ta hau gadon ta rungume jikallanta aƙirji, ahaka bacci
ya ɗauke su

****JOS CITY MUN WAYI GARI LAFIYA AGIDAN ALHAJI UBAID*******

zazzaune suke a saman dining suna Yin breakfast A tsanake shiru baka jin sautin
komai saina cokulansu, kwas kwakwas kamar zasu fasa plates ɗin, sun natsu suna tura
abinci a cukunnansu, Alhaji ubaid na sanye da Jallabiya Hajiya Laila dake agefensa
arab gown ce a jikinta launin royal blue ansha uban make up, Alhaji musa ya ɗauki
wankan tsadaddun suit sun zauna mashi, mutumin fa akwai kyau kamar shi ya tsara
kanshi ya iya ɗaukar wanka ga aji, daga gefen shi Dr shureim ne cikin shigarshi ta
gado wato Kayan larabawa, daddaɗan ƙamshin turarensu mai daɗin shaƙa, musamman
turaren Alhaji musa fragrance ɗinsa na dabanne. A hankali ya ɗan ɗago yana duban
shureim ya lura ba abincin ya ke ci ba, tun da suka zauna yake ta faman jujjuya
spoon ɗin hannun shi acikin plate ɗin gabanshi, gyaran muryar da Alhaji musa yai
mashi ce tasa shi ɗagowa ya kalle shi
Cikin kulawa ya ke yi mashi magana”meyasa bakasan cin abinci shureim? Na lura tun
shekaran Jiya da nazo gidan nan baka ci wani abun kirki ba” Hajiya Laila ta ɗan
dakata da cin abincin fuskarta a yamutse take kallon alhaji musa aranta tace”ji
wani ikon Allah ko’ina ruwanshi da cin shi da shan shi? Ni narasa gane shisshigin
nan da yake yiwa shureim, mutumin da bai damu da shi ba, sai yanzu ne yasan da
zaman shi’
Cikin sanyin murya shureim ya kalli uncle ɗin nashi”ina ci mana, kawai ni nafi
sha’awar abincin hausawa ne wannan baya min daɗi abaki” Alhajin ubaid yace”Meyasa
tuntuni baka yiwa zainab magana ta girka maka ba? Kamar ba ka da bakin magana,
komai naka ya zama na shiririta shureim so ka ke ka koma yaro”? shiru shureim yai
shi kanshi haushin rashin ƙwarin gwiwarshi yake ji, ya koma kamar wani sakarai
komai sai yadda akayi da shi.
“Kada ka damu Yayana, da zarar mun koma abuja zai dawo asalin Dr shureim ɗin da
ka sani ne, Kasan matata ta iya bada tarbiya zata gyara maka ɗanka ya zama namijin
gaske”

Wannan maganar ta Alhaji musa tayi matuƙar ƙona ran Hajiya layla, har dai tagaza
jurewa
“Me kake nufi? Ni ban iya bada tarbiya ba kome”? Ko kallo bata ishe shi ba saima
Ya ɗauki glass ɗin lemu mai sanyi yakai baki Yana kur6a.
“Haba layla, meyasa bakya iya 6oye fushin ki ne? Laifine don ya yabi matarshi?
Harara ta wurgawa Alhaji ubaid tamkar ƙwayar idon zata faɗo kasa
“bansan meyasa kake goya mashi baya ba, idonka ya rufe kwata kwata baka ganin
laifin shi, wannan ba adalci bane” rai a6ace ta ƙarasa maganar tare da buga table
din, A fusace ta miƙe tabar dining ɗin
Miƙewa shureim yai da niyar yabi bayanta da sauri Alhaji ubaid ya dakatar
dashi”dawo ka zauna” komawa yai ya zauna
“daddy bana jin daɗin hakan, kasan halina tunfil azal bana so inga ran wani daga
cikin ku ya 6aci” Shureim ne yai maganar
“ka kwantar da hankalinka, In sha Allah zan sasanta tsakaninsu, Yanzu zan shiga
wurinta in lallasheta” Yai maganar tare da miƙewa yabar dining din bayan tafiyar
Ubaid Alhaji musa ya ɗago ya kalli shureim

“You should start preparing, Ƙarfe shabiyu zamu bar jos, already nayi magana da
pilot ɗina, bana buƙatar ka tafi da komai naka, Duk wani abu da za ka buƙata za’ayi
maka acan” murmushin yaƙe dr shureim ya ɗan saki
“in sha Allah Uncle yanzu zan shiga ciki In ƙara shiryawa” amsa mashi Yai da toh,
Kafin miƙewar Dr shurem P.a Ɗin Alhaji musa yai sallama daga wajen palourn, Hakan
yasa shi saurin miƙewa cikin takun izza ya nufi ƙofar fita daga palourn
Ajiyar zuciya dr shureim ya sauke, shi kanshi shakkar Alhaji musa yake ji,
mutumin babu wasa a harkarshi.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank
3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E13🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

Juyawa yai da sauri ya nufi kitchen maimakon ɗakin shi, Yana shiga ya ci karo da
zainab tana goge tiles da floor wiper sam bata lura dashi ba, har saida yai mata
sallama tukunna ta ɗago suka haɗa ido
Fara’a ta sakar mashi”shuraim tun jiya na ke son yin magana da kai, fargaban
Iyayenka ta hanani tunkarar ka” ƙarasa shiga kitchem ɗin yai

“Aunty zainab Ya zamuyi? Uncle musa ya matsa min akan saina bishi abuja, ƙarfe
sha biyu zamu bar jos, “ dafe kai ta yi da hannu ɗaya

“Naji takaicin jin haka shureim, Duk plan ɗin da muka shirya ya tashi abanza kenan”

Girgiza mata kai yai”in sha Allah komai zai tafi dai dai aunty zainab, ko da ace
bana nan that will not change anything”

Damuwa ce cunkushe akan fuskarta

“How ka ke tunanin komai zai tafi dai dai bayan bamu a wuri ɗaya”?

murmushin gefen fuska ya sakar mata har dimples ɗinsa suka lotsa.

“Kin manta da waya? Ina da ita kina da ita, zamu dinga yin communicating da
junanmu, hakan ma zai fi ba tare da wani ya zarge mu ba” ƙayataccen murmushi zainab
ta saki

“Allah ya yi maka albarka shureim ni sam na manta da waya, amma fa zan yi missing
ɗinka sosai mutumina
Murmushin fuskarshi bai washe ba yace”Ni kaina zanyi missing ɗin auntyna mai
share min hawayena, amma in sha Allah zamu dinga yin waya akai akai, Inaso komai da
ke faruwa a gidan nan kidinga sanya min ido, da zarar an samu update ki kirani
awaya ki sanar dani, amma fa sai kinyi takatsantsan kinsan Iyayen nawa ba ƙananun
mutane bane”

jinjina kai Zainab ta yi don ta gamsu da bayanin shi

“In sha Allah zan kiyaye shureim, kaima ka kula min da kanka, “ idanuwansu duk sun
ciko da ƙwalla, don ba ƙaramin ƙaunar juna su ke yi ba, tana jinshi tamkar Ɗanta,
shima Yana jinta tamkar mahaifiyarsa, sun jima a kitchen ɗin sunayin magana kafin
daga bisani yai mata sallah.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Dr shureim Ya fara shirye shiryen tafiya abuja, bai
canza komai na suturar jikinsa ba, Iya turarurrukansa kaɗai ya feshe jikinsa,
sannan ya warware Ɗaurin larabawan dake akanshi, Ya sharce lallausar sumar kanshi
Ya gyarata tsaf yabi da mayukansa ya shafe ta, Kafin barinsa ɗakin saida yai Nafila
Ya roƙi Allah da ya tsare shi ya kare shi daga sharrin mutun sharrin zuciya da duk
wani abun cutarwa, ya kuma roƙi Allah da ya sa silar komawarshi gidan uncle din shi
abuja rayuwar shi ta canza ya dawo kamar yadda yake ada, addu’o’i sosai shureim
yayiwa kanshi, Bayan ya kammala ya zaro memory ɗinshi da ya 6oye a cikin rigar
pillow ya zaura shi awayarsa, Hankalin sa Ya ɗan kwanta zai samu natsuwar cigaba
da kallon hotunan Abar ƙaunarsa awayarsa.

A gefen gadon shi ya zauna yana daddana wayar shi, Lokaci ya ke jira ya cika.

**DAULAR OBIE ESTATE**

A Hankali Jigunannun Motocinsu su ke kunno kai saman shantalelen titin obie estete,
gaba da baya Sojoji ne ke tafiya akan ƙafafuwansu, Hannayensu ruƙe da bindigu,
Motar farko mallakin Sir mubarak ce, motar dake a biye da ita zungureriya ƙirar
Navigator limousine wadda cikinta tamkar bedroom ya ke saboda tsabar haɗuwarta,
Dattijon arziƙi ne hakimce acikin motar tare da Jikokinsu tagawaye zain da zaid sai
Dr Jazz shalelensa, Motar da ke abiye da tasu Danƙareriyar gaske mai numfashi
mallakin Senate president Lateef Obinna ce, Yayin da motar ƙarshe Ta pravin Obinna
ce, gayu mutanan Allah su kansu motocin da dattaku ake yin driving ɗinsu a tsanake
cikin ƙwarewa, sautin karatun kur’ani mai girma ne ya karaɗe ko’ina, Ƙirar Ahmad
suleiman mai matuƙar ratsa sassan jiki, daga motar dattijon arziƙi ƙirar ke fitowa,
ƙa’ida ne a lokacin da suka fito zasu tafi masallaci sai yasa an kunna masa ƙirar
Ahmed suleima haka zalika idan zasu dawo daga masallaci sai an kunna masu karatun
wani sa’in Idan ƙirar takai mashi karo har bi yake yi yana lumshe ido, A yanzu haka
dawowarsu kenan daga masallacin Juma’a.

Sannu A hankali su ke tunkarar Moto park ɗinsu, kusan atare motocin suka Yi parking
at same time, Da azama sojoji su ke bubbuɗe masu mota, A hankali Obie Ya sauko
ƙafarshi dake sanye cikin takalma kalar na sarakuna, Jikinsa Jallabiya ce daga sama
Ya ɗaura alkebba haɗaɗɗar gaske sai ƙyalli ta ke Yi, ɗaya bayan ɗaya su ke fito
daga Cikin motocin, gaba ɗayansu haɗaɗɗun Jallabiyoyi ne a jikin su daga Iyayen Har
ƴa’ƴan.

“Mu shiga ciki ko”? Obie ne Yai masu maganar, Zaid da zayn Sai faman sunnar dakai
ƙasa suke yi kamar marasa gaskiya, mamakin hakan yasa Mahaifinsu pravin tanka masu

“Lafiya”? Kafin su yi yunƙurin bashi amsa Sir Mubarak ya tari numfashin su

“Zaku ci ƙaniyarku ne, ƙananun Ƴan iska masu kwana da wando, har ni zaku dinga
kakkaucema wa? Kun raina ni ko”? Fuskar shi a ɗaure ya ke yi masu magana, sir
mubarak mutunne mai fusatacciyar zuciya abu kaɗan ke hasala shi sai da ta wani
6angaren yana da sauƙin kai.

Dr jazz Yana ruƙe da hannun Obie dariya ce ƙumshe abakinsa, ya ƙi bari ta kubce
masa gudun kada Ya ji saukar mari daga Sir mubarak, Twins kuwa Duk sun sha jinin
jikinsu sai faman noƙe kai suke yi haɗi da sosa ƙeyarsu.

A fusace Ya daka masu tsawa har saida suka ɗan razana atare su ka ɗago da fararen
idanuwansu akan fuskarshi” Ina magana kuna kallona? Saboda tsabar fitsara”? Da
sauri suka sunnar da kawunansu ƙasa, Alkunyace ta hana Pravin sanya baki, Gyaran
murya senate Lateef Ya yi ma ɗan uwan nashi, Ya juya yana duban shi, cikin muryan
Manyantaka Ya soma magana
“Aymasu afwa, Yarane su har yanzu, basu mallaki hankalin su ba, Sai ana haƙuri da
su”

girgiza kai Sir mubarak yai”Pls ka daina wannan maganar, Yara sun balaga kana faɗin
basu mallaki hankalinsu ba”? Juyawa yai tare da kallon su twins muryarshi a
kausashe yace”Dagaske baku mallaki hankulan ku ba”? Har suna haɗa baki wurin
furta”wlh mun mallaki hankalinmu, pls Ka yi haƙuri Uncle mun gane kuskurenmu zamu
gyara in sha Allah, Dan Allah daddy ka bashi haƙuri wlh ba zamu ƙara ba” A
marairaice suke kallon Mahaifin nasu pravin, Shi dai Obie bai tanka masu ba,
murmushi ne ɗauke akan fuskarshi.

“Za ku Yi bayanine, muddin Owais ya dawo ƙasar nan zan sanya shi Ya ba ku horon
isod, Ni dama can ban Goyi bayan aikin Company da ku ke zuwa yi ba, saboda ba ku
iya komai ba” Zaro ido waje su ka yi jin abunda yace Hankalinsu ya tashi matuƙa,
saboda suna mugun tsoron training ɗin Isod har ƙwara abasu horon aikin Soja, tuni
sun raina kansu, Muryoyinsu tamkar zasu fashe da kuka su ke kallon Kakansu obinna
don ya sa baki akan maganar
Pravin na murmushi yace”dama kun daina wahalar da kan ku, kunsan wanene Kawun na
ku mubarak, Idan ya yanke hukunci babu wanda Ya isa ya dakatar dashi, Ni ma kuma na
goyi bayan hukuncin da ya yanke”

Ransu ya 6aci jin abunda daddyn su Yace, juyawa su ka yi afusace suka nufi gidan.

Girgiza Kai Sir mubarak yai”kun ga irinta ko? Ana magana sun juya sun tafi saboda
rashin ganin girman nagaba da su, duk izzar Owais ba ka ta6a yi mashi magana Ya
juya maka ƙeya duk mun rashin daɗinta, natsuwa ya ke yi ya saurareta, Ai duk
laifinka ne Pravin da kai da Saratun Kun sangartasu duk cikin Ƴa’ƴanmu babu
sangartattu irin twins, Zanyi maganinsu ne” Maganar Sir mubarak ta ta6a zuciyar
Pravin, yana ɗaya daga Cikin abunda ya tsana, ya ji an kushe ƴa’ƴan shi an yabi na
wasu, Musamman owais, gani yake kamar don saboda Shi ba Jinin family ɗin bane
Shiyasa suke nuna ma ƴa’ƴan shi wariya.

Tuni yanayin fuskarsa ya canza sam babu annuri, Ba tare da ya kalli fuskokinsu ba
Ya furta”Ni zan Shiga ciki Sai kun ƙaraso” Yana faɗin hakan Ya zura hannayenshi
cikin aljihun jallabiyar shi ya nufi gidan.

Gaba ɗaya sun fahimci canzawar da yai, Senate Lateef ya girgiza kai Yana bin
bayan pravin da kallo

“Narasa gane kan mutumin can, ƙaranci Hankali nadamun shi, meye aciki don Anyi
maganar ƴa’ƴan shi sangartattune? Ƙarya aka yi ne”? ran sir mubarak Yafi na kowa
6aci”Ka barni dashi, zan koya mashi hankaline, Maganar horon Isod da za’a ba ƴa’ƴan
shi ba fashi ko da zuciyarshi zata buga ne ɗan rainin wayau”

gyaran murya Obie Yai masu hakan Ya janyo hankulansu ga kallon shi, ya ɗan jingina
bayan shi jikin motarshi su kaɗai suka rage a harabar ajiye motocin, tun bayan
isowar su gidan sojojin da ke take masu baya suka watse zuwa 6angaren da suke kula
da shi na gidan.
“Sai kuna Yi mashi uziri, Pravin yana da raunin zuciya, ga shi dai a ido kamar
Namiji sai dai a zuciya baida mararraba da mace, shima auta ne kamar saratun, mijin
auta ai auta ne shima inda kara”

ƙumshe dariya Dr jazz yai jin sharrin da Obinna ke yiwa Pravin

Fuskar senate Lateef ɗauke da murmushi yace”A’a, baba ai ko saratun dakakkiyar


zuciyace da ita, kaima ka sani gaba ɗayanmu Jinin ka muka Biyo, babu ragwantaka
atare damu, shi dai ne macen Mijin tace, ita kanta saratun Juya shi take yi son
ranta, Ina ji ran nan mun shigo gidan tana yi mashi masifa akan Ya zari kuɗi a
account ɗinta ba tare da ya nemi iznin ta ba, sai lalla6ata ya ke yi kamar zai yi
mata sujjada”

Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, daga obinna har shi Sir mubarak ɗin.

Dr Jazz ya saki baki yana tiƙar dariya kamar wani babba ya shige cikinsu, sai da
suka kammala Yin dariyar, Sir mubarak Ya lura dashi, sam ya manta da dr Jazz a
cikinsu, Ɗaure fuska Yai”kai! Me ka ke wa dariya? Akwai tsaranka ne acikin mu”? Da
sauri Dr jazz Ya shanye dariyarshi, Hada la6ewa bayan Obinna.

Senate lateef yace”Ni zan wuce gida Baba, In sha Allah zan samu lokaci in shigo
ciki mu ƙara gaisawa” obie yace”kada ka ta kura kanka, Ai kuna ƙoƙari ma, Ko awaya
ne munyi magana, Idan ka shiga gidan ka gaishe min da hajiyar taka, Ina nan ina
jiranta ta zo ta same ni agida mu gaisa”

Amsa mashi yai da toh, kafin Ya kalli ɗan uwan nashi”Ni zan wuce Mubarak agaishe
min da Turai,” amsa mashi yai da toh”Nima a isar min da saƙon gaisuwa zuwa ga madam
ɗin taka” A mutunce sukayiwa junansu sallama,

“Baba nima zan shiga ciki, amma kafin nan zan raba ka da wannan mata mazan” yai
maganar yana ƙoƙarin damƙo hannun Dr jazz, Ƙanƙame obie yai, Sir mubarak yace” So
ka ke ka karyamana Uban namu, Fito nan, Ni ba wani abu zanyi maka ba, Inaso ne mu
shiga ciki, ka gaida mahaifiyar taka, nasan saboda ni ya sa ka daina leƙowa
wurinta, tsakaninka da sai kira awaya sai kuma idan ta shigo gaida baba”

Jin abunda yace ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin jin shakkar Uncle
mubarak ya ke yi ba, ruƙo hannun shi mubarak Yai

“Zaka rabani da sanyin idaniyata” acewar dattijon arziƙi.

Dr jazz yace”kada ka damu kakana, Ba zan jima ba, zan shigo gidan, pls Ka kwanta
ka huta,” lumshe ido obie yai idonshi akansu har saida suka 6ace ma ganinshi,
tukunna Ya ruƙe sandarshi Ya nufi cikin gidan.

Hajiya saratu ce zaune gefen gadonta cikin shiga ta bubu gown anyi mata kaftan
style, kanta babu mayafi, Ta natsu tana kallon screen ɗin laptop ɗinta dake ajiye a
gabanta saman round table, fuskarta ɗauke da murmushi, Video call ta ke Yi da ƴar
autarta Faryat dake zaune gidan Yayanta Hateem na ƙasar canada

Matashiyar budurwace launin fatarta kalar na mahafiyarta ne, tana a zaune saman
wasu haɗaɗɗun kujeru dake a kewaye da table, agaban tafkeken swimming pool, gefen
laptop ɗinta Cup ɗin coffee ne ajiye, ta ɗauki wankan short gown ajikinta launin
pink tabi shape ɗin jikinta.

“Yaushe zaki dawo gida ne? Na yi missing ɗin ki daughter”


Fuskar Faryat ta cika screen ɗin laptop ɗinta, faɗaɗa murmushin fuskar ta tayi da
zazzaƙar muryarta ta furta
“I’ll come home as soon as we have a school break because I can’t wait to see you,
my first love.”

“Canada ta kar6e ki daughter, kinyi haske kinyi kyau abunki, faɗamin dame dame ki
ke yi a lokacin da ba ki yin komai”?

Farfari Faryat tayi mata da ido kafin ta soma jera mata

“Going to the movies, beach, club, playing games... “

tunkan ta ƙarasa maganar Hajiya saratu ta dakatar da ita, Fuskarta a ɗaure


tace”Faryat! Kina zuwa club? Da beach..? waro ido Faryat tayi batasan tayi su6ul
da baka ba, da sauri ta toshe bakinta da tafin hannuwanta

“Mom, I was just joking. You know Uncle Hateem would never let me go to those
places. Also Yazrin and Nazli keep an eye on me, even when there’s no school, they
keep me company. I’m too busy to waste time.”
Hankalin saratu har ya ɗan kwanta

“Dama nasan ƙarya kike yi min, Na yadda da yayana Hateem nasan duk wani shige da
fucen ki Yana a tafin hannun shi, duk da yana busy hakan bazai hana shi sanya
jami’an da zasu dinga kula da motsinki ba, shiyasa tun farko na tura ki can don su
gyaramin natsuwarki, kuma Alhamdulillah naga canji” Dariya Faryat ta saki jin
abunda mommyn nata tace, Tsawon mintuna talatin sunayin wayar kafin daga bisani
sukayi sallama da juna.

Layin Landline na kitchen Hajiya sarah ta kira Safa ce ta ɗaga kiran.

“Assalamu alaikum” Sarah ce tai sallama, Hajiya sarah bata tsaya amsa sallamarma
ta ce”Jira ake sai nace akawo min abinci? Ko so ake in taƙo da ƙafafuwana in zo
kitchen ɗin in ɗiba”? Muryar safa adabarbace ta furta”Ba haka bane Hajiya, duk
laifin abla ne, itace take da aiki apart dinki, amma in sha Allah yanzu zata
ƙaraso” yatsina fuska Hajiya saratu tayi fuskar ta babu annuri ko misƙala zarratin

“Okey, ina buƙatar dambun nama, A haɗo mun da fresh fruit, kada amanta da
farfesu...” a ƙalla ta lissafa kusan abu takwas da za’a kawota don tayi
breakfast....tunkafin Ta yi rejecting kiran muryar Pravin ta ratsa kunnata

Ranshi a6ace ya shigo yana zazzaga masifa”wannan wani irin wulakanci da cin fusk
ne, Nifa nagaji da aibata ƴa’ƴana da ake Yi” yana huci ya ƙarasa maganar tare da
goya hannayensa saman ƙirjinsa, idon saratu akanshi bayan ta katse kiran ta ɗaura
wayar saman nightstand
A tsanake ta soma yin magana”wanene ya ta6a min romeo ɗin nawa”? ko sallama babu
ka shigo kana ta zazzaga masifa? Tell me meya faru”? Aƙagare tayi maganar, tare da
yunƙurawa ta miƙe tana fuskantar shi
Zuciyarshi A harzuƙe ya furta”Yayyanki mana, Akan me zasu dinga kushe ƴa’ƴana
suna yabon nasu? sai yaushe ne zasu daina nuna min wariyar launin fata? Saboda
kawai ni bani da alaƙa daku shine zasu dinga kushe min ƴa’ƴana”? Idan da kara
ƴa’ƴana ai nasu ne’ Tsabar fusata yana magana facial muscles ɗinsa na kerma.
Matsawa tayi kusa dashi, fuskarta a ɗaure ta furta”what? Wanenen acikinsu yai
maganar”? Da alama ranta ya 6aci hakan ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba

“Lateef ne da Mubarak, Agaban obie da sangartaccen Yaron nan dr jazz suke kushe
Twins, har faɗi sukeyi wai sangartattune basu Iya komai ba irin na maza, zaifi kyau
su ajiye aikin da sukeyi na company su koma ɗaura zani” Baki asake saratu ke kallon
shi hada ruƙe qugu, muryarta akausashe tace”Pravin dagaske sune suka furta hakan?
Kuma agaban Baba shine bai tsawatar masu ba”? Kwa6e fuska pravin yai”ae abunda zai
baki haushi, baisanya baki amaganar ba, saima murmushi da yake saki, hada wannan
munafukin Yaron, Shi da ba ɗan kowa ba agidan face ɗan mai aikin, wama ya sani ko
shege ne, dani da uwarshi duk ɗaya muke ai, yadda bani da alaƙa da ku, itama haka
har ƙwarani mun samu ƙaruwa ta ƴa’ƴa har uku”

Ran Hajiya saratu ya 6aci matuƙa, sai faman jinjina kai take yi tana fadin”bari
naje wurin baban, yanzu har takai ga ƴa’ƴana aka kushewa agaban sakaran yaron nan
jazz? suma waɗanda suka yi maganar zasu fuskanci 6acin raina wlh, zasu san dani
suke magana” takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana neman mayafin da zata yafa,
Pravin hada saurin rigata ƙarasawa gaban closet ɗin kayansu Ya buɗe ya ɗauko mata
mayafi da kanshi ya ɗaura mata shi asaman kanta, A fujajen ta fuce daga cikin
ɗakin, fitarta keda wuya pravin ya soma sakin shu’umin murmushi, ba tun yau ba ya
saba haɗata faɗa da ƴan uwanta, mugun munafuki ne na bugawa a jarida, A zubin
halitta idan ka kalle shi tamkar Namiji.

Bayan fitar Hajiya saratu da ƴan mintuna, ya sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin zame
jallabiyar jikin shi da niyar canza kaya, Sallamar Abla ta ratsa kunnuwanshi, Jimm
ya ɗanyi kamar bazai amsa mata ba, daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta”shigo daga
Ciki” a hankali ta turo ƙofar, Hannunta biyu ruƙe da faffaɗan tray na Kayan
breakfast ɗin Hajiya saratu.

Ganin Pravin shi kaɗai a ɗakin Yasa ta ɗanji faɗuwar gaba, miryarta na rawa ta
furta”umm..amm dama Kayan breakfast ne na kawoma Aunty saratu” lumshe idon shi Ya
ɗanyi, tare da tunkarota Ya ruƙe tray din hannuta”bari na ƙarasa shigar maki da shi
ciki,” kar6a yai tare da juyawa ya ɗaura tray ɗin saman table, kafin Ya juya ta yi
saurin kai hannu zata tura ƙofar ɗakin saboda sanin halin shi, sai dai kafin ta
kaiga ƙarasawa ga ƙofar yai saurin damƙota ya janyota zuwa jikinshi, Hankalin abla
Ba ƙaramin tashi yai ba tsananin tsorone da fargaba duk ya cikata, ƙamshin
turarensa ya addabi hancinsa, cikin shessheƙar murya take faɗin”pls ka sake ni dan
Allah, na roƙe ka kada kaja min bala’e,” kwantar da kanshi yai saman kafaɗarta
dogon hancin shi na gogar fatar wuyanta, yayin da hannayensa ke asaman ƙirjinta
ahankali yake matsasu, kamar zatayi hauka ƙoƙarin kwace kanta take yi saida ya
hanata yin haka saboda ƙarfine dashi kamar doki, fashewa tayi da matsanancin kuka
tana yakushin hannunshi da akaifun hannunta kamar zatayi hauka.
“Nashiga uku, Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Ya Allah ka kawo min ɗauki,”
hankalin shi kwance yake cigaba da ƙoƙarin tura hannayenshi cikin rigarta

“Daddy!” muryar Zayn ce tasa shi saurin sakin Abla, ɗaure mata fuska yai

“Don’t you dare tell anyone what happened. Wipe ur tears off your face right now.”
Jinjina mashi kai tayi da sauri ta sanya ƙasan rigarta ta share hawayenta, shu’umin
murmushi pravin ya saki’Good zaki Iya tafiya sai mun haɗu wani lokacin” wani irin
ɗaci taji acikin zuciyarta, Tana buɗe ƙofar ɗakin taci karo da twins, ko kallonsu
batayi ba da sauri tabi ta gefensu ta wuce, awata ƴar corner ta la6e ita kaɗai ta
zuƙunna tana cigaba da yin kuka haƙika pravin ba ƙaramin cin zarafinsu yake yi ba,
shiyasa suke gudun zuwa su tarar da shi a ɗakin Hajiya saratu musamman idan bata
nan, Romancing ɗinsu yake yi tamkar zai kashesu, halinshi ne bunsuranci, har ƙwara
Ƴa’ƴan shi twins duk iskancinsu babu ruwansu da masu aikin gidan, amma shi uban
nasu baya iya kauda idonshi akansu, Ya maidasu kayan biyan buƙatar shi, Kuma ba su
isa su ce zasu hana shi ba, saboda barazanar da yake yi masu, hakan yasa suke mugun
jin shakkar fallasa shi awurin masu gidan, kuma hada ƙarin basu son yayi masu silar
barinsu aiki gidan, ba don kudin da ake biyansu da dollar ba, sai don sabon da
sukayi da mutanan gidan sannan da yawansu Iyayensu masu ƙaramin hali ne, wasu ma
babu Iyayen neman na kansu suke yi don su rufawa kansu asiri.

Ex-prisoners Meya hwaru Bayan jirginsu Ya ɗaga daga Cikin Dajin Evil forest shin
sun sauka lafiya ko kuwa akasin hakan”?

*SAN ANTONIO-TEXAS🏙*
*UNITED STATES OF AMERICA*

San antonio texas babban birni ne da ke a cikin jihar Texas ta america Yana ɗaya
daga cikin jigunannun manyan biranan America Masu matuƙar ƙayatarwa Manya manyan
gine gine na tarihi dana zamani, abubuwan more rayuwa masu ban sha’awa na musamman
da kuma wadatar arziki, Hadaddiyar daula ce a U.s tsayawa suffanta kyawun birnin
6ata baki ne, balle ni da nake da abunyi.

*San Antonio International Airport🛫*

Katafaren Airport ne na tashi da safkar jirage dake a cikin birnin san antonio,
ƙayataccen gaske, sanarwa ce ta soma fitowa daga muryar na’urar computer (PA
announcement) Kunnuwan Ma’aitakan Airport ɗin da fasinjojin dake zirga zirga a
cikinsa gaba daya sun natsu suna sauraron sanarwar kwamfutar

“Attention, passengers. A UH-60 Black Hawk helicopter is scheduled to land at San


Antonio International Airport in approximately 10 minutes. We appreciate your
patience and understanding.” (“Amaida hankali, fasinjoji. Jirgin sama mai saukar
ungulu na UH-60 Black Hawk yana shirin sauka a filin jirgin saman San Antonio a
cikin kusan mintuna 10. Muna godiya da haƙuri da fahimtar ku.”)

Tunkafin ƙarasowar Helicopter ɗin nasu tuni Daga can headquater na sojoji an kira
Emmergency Number ta Asibitin University Hospital Domin zuwa ɗaukar Marasa lafiyan
da Jami’an su suka ɗauko, Da wata irin jiniya Jibga jibgan Ambulances din suke zuba
uban gudu saman titin da dai sadaka da airpot din, jiniyarsu ta karaɗe ko’ina duk
inda suka bi darewa akeyi abasu Hanya tunkafin su ƙaraso saboda sanin aikinsu na
agaji, kowace ambulance tana ɗauke da tambarin sunan asibitin UHS which means
(University Health System) daga gefen rubutun Zanan white cross ne backround dinsa
launin Ja,Kusan su uku ne Motocin suka jera, a Airport helipad ambulances ɗin suka
Yi parking, helipad yanki ne na musamman da aka tanada domin safka da tashin
helicopter.

Mintuna goma na cika cuf cuf A gogon birnin San antonio ya buga ƙarfe 5 na safe,
adai dai Wannan lokacin sautin Danƙareran Jirgin Da ke shawagi Saman iska Ya karaɗe
kunnuwan kowa dake a yankin airport ɗin ga dukkan alamu Matafiya sun ƙaraso 🛫.

Sannu Ahankali Helicoptern Ya sauke tayoyin shi yayin da ya ke yin ƙasa ƙasa,
Slowly yake tafiya har yakai ga inda zai dakata a filin helipad, Sojoji ne Kewaye
da Jirgin waɗanɗa suka zo tarbarsu daga headquater, Motocinsu na ajere dana ɗaukar
marasa lafiyan.
Buɗe Bayan Ambulances ɗin akayi at same time, Ma’aikan Jinyane waɗanda ake kira
EMTs (emergency medical technicians) suka soma diddirowa daga bayan motar, mata da
maza turawa cikin shigar fararen kaya masu ɗauke da tambarin Lafiya Hannayensu da
ƙafafuwansu duk safunane haka zalika Sun toshe rabin fuskokinsu da face mask.

Saukowa Sojojin helicopter ɗin suka soma Yi daga cikin shi, Biyu daga cikinsu
ruƙe da ɗan ta’addan da su ka damƙo a evil forest, Kaitsaye suka nufi motar ƴan
uwansu sojoji da suka zo daga headquater, Abayan Kanta suka wurga shi tare da datse
ƙofar,
Dawowa su ka yi wurin ƴan uwansu, nan fa aka fara rungume juna, ƴan uwan nasu
nayi masu jinjina ta ban girma, akan Nasarar cafke ɗan ta’addan da su ka yi.
Ba tare da 6ata lokaci ba, Emts suka Curo stretcher daga motarsu kusan guda
Takwas, agaban Helicopter ɗin suka ƙarasa da shi ɗauke a hannunsu, Da taimakon
sojoji suka dinga Jigilar ɗaukar su Angel suna miƙa su cikin motar, da aka zo kan
Danish Sai dai sojojin suka kar6i stretcher ɗin suka shigar dashi ambulance ɗin,
Bayan sun kammala kwasarsu, Motar sojoji gaba da baya a yayin da motocin Ambulances
ɗin ke a tsakiya, da wata irin Jiniya suka haura saman titi da gudun gaske, sauran
sojojin dake acikin motar da ɗan ta’addar yake tuni sun raba hanya sun nufi
headquater ɗinsu da shi.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E14🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop


of betrayal and cruelty💔._

*Universal Hospital*

Ba sai na tsaya misalta kyawun asibitin ba, tun da akace america zance Ya ƙare just
imagining ɗinsa zakuyi, lokacin da motocin suka ƙaraso entry way na shiga asibitin
ɗuff suka ɗaukar jiniyar bayan shigarsu A parking space motocin suka dakata da yin
tafiyar, Cikin ƙanƙanin lokaci Emts Suka kammala jigilar shigar dasu cikin asibitin
duk wani motsinsu akan idon sojojin Bayan kammala Shigar da su asibitin, Likitoci
da nurses suka duƙufa domin duba lafiyar jikinsu, tuni sun canza masu kayan jikinsu
daga Uniform ɗinsu Jajaye zuwa Patient’s uniform launin Light blue, hatta waɗanda
suka 6aci da ta6o sun wanke su tass tamkar basu ta6a faɗawa cikin ca6ali ba.

gaba ɗayan su a Amenity ward aka kwantar dasu, sashe na musamman da ake kwantar da
sarakuna da hamshakan masu kuɗi, duk mutun ɗaya ɗaki ɗaya, tsabar haɗuwar ɗakunan
tamkar bana jinya ba, anzuba ababen more rayuwa, kama daga haɗaɗɗen gado, ga A’c
hada tv da frigde komai na jin daɗi, tuntuni sun farfarɗo daga suman sai dai gaba
ɗayansu they were in a state of unconsciousness sakamakon firgici da tsoron da ya
rikitar da su, razana suke yi haɗi da yin sambatu hakan yasa likitoci su ka yi masu
allurar kashe ƙwarin jiki don su samu damar duba lafiyar jikin su, the first thing
da doctors su ka fara yi masu is general checkup wanda ya haɗa da sauraran bugun
zuciyar su duba hunhunsu, fatarsu da idanuwansu daga bisani suka fara yi masu
gwaje-gwaje da su ka shafi blood test, chest X-ray, da sauran gwaje gwajen hotunan
wasu 6angarori na ga6o6in su, domin duba raunukan da suka ji da cututtukan da ke
damunsu, Cikin ƙwarewa likitocin su ke gudanar da binciken nasu, ɗaya daga cikin
abunda suka gano wanda ya ɗaure masu kai, duka yaran akwai depression atattare da
su (ciwon baƙin ciki da damuwa) Mutun ɗaya ne ke fama da Ciwon Zuciya (stress-
induced cardiomyopathy, agaggauce su ka fara bashi taimakon gaggawa, Ga ƙarancin
Jini da ya ke fama da shi, tuni sun fara yi mashi Blood transfusion.

A ƙalla likitoci sun shafe tsawon awanni akansu, wani abu da yai mugun ɗaurewa
Likitocin kai Ƙoshin Lafiyar Danish da kyawun surar shi! Tun da Allah ya halicce su
basu ta6a ganin mutun mai rai da lafiya irin shi ba, gashi yaƙi farfaɗowa sun rasa
gane wani kalar bacci ne ya ke yi, kuma sam babu wata lalura da ke gare shi, bacci
ne kawai yake ta shara abin shi, Duk sun ƙagara da su ji bayani daga Gare su, Amma
sun bari sai Yaran sun ji sauƙi tukunna su ji daga bakinsu menene ya haddasa masu
depression? Da ƙananun shekarun su, mutun ɗaya da Sojojin su ke tsammanin Jin
bayanai daga gare shi, Tun acikin jirgi da suka yi mashi allurar bacci bai ƙara
farfaɗowa ba, Yanzu haka Yana akwance saman gado sai sharar baccinsa Ya ke yi.

Till Wuraren ƙarfe 12 Na rana, Gabriel ya soma mutsun mutsun farkawa daga bacci,
Dama jiran shi suke Yi ya tashi, Kasancewar akwai na’urorin cctv a kowace kusurwa
na medical rooms ɗin ta hanyar su likitocin su ka san da tashin sa.

Slowly ya buɗe idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin, Tamkar a mafarki Ya ke kallon
shi, tsantsar mamaki ne da al’ajabi akan fuskarshi, Tambayar kanshi ya soma yi
cikin ruɗanin zuciya, Ina ne nan? Wanene ya kawo ni? Anya ba mafarki nake Yi ba”?
da wata irin kasala Gabriel ya miƙe zaune Yana faman wurwurga ƙwayar idanuwansa
akan haɗaɗɗen room ɗin da ya ke a ciki, Lamarin ya ɗaure mashi kai, Daddafe kanshi
yai da hannayenshi biyu tamkar zai fasa ƙara, abunda ya ƙara rikitar da shi Uniform
ɗin da aka canza mashi, daga jajaye zuwa light blue Riga da wando, Ƙasa ƙasa da
murya yake ambaton sunayen ƴan uwan shi

“Azeeza! Angel! Danish! Batul! Naufal! Javed! Par.....” bai ƙarasa maganar ba
sakamakon Jin motsin buɗe ƙofa, A firgice ya zazzare idanuwanshi akan masu shigowa.

Uku daga Cikinsu asanye suke da scrub suit, Kayan Likitoci, biyun da ke biye da su
cikin kakin Sojoji masu ruƙe da muƙaman Major da Captain wakilai ne da aka turo
daga can headquater, likitocin uku dake atare dasu Turawa sun haɗa da md (medical
director) Dr. mark Johnson, bayan shi sai Hospital Ceo Dr. laura Davis babbar
macace fara jawur, na ƙarshen su health records technician ne Dr. Danial Brown
hannun shi ruƙe da Apple ipad.

A gaban gadon shi su ka tsaya suna dubanshi

Cikin harshen turanci suke Yin magana


“Fatan ka farka Lafiya? Ya jikin naka”? Dr Brown ne yai mashi maganar, cikin
kulawa,.Muryarshi adabarbarce ya furta”Ina ƴan uwana suke”? Tambayar farko da ya
fara jefa masu.

“Did you forget that we found you in the forest? (Kamanta a daji muka tsince ku”?)
Major ne Yai mashi maganar, Gabriel was silent as he tried to remember what had
happened. They could see that he was confused and would need time to sort out his
memories.
Nuna mashi screen ɗin Ipad dr bown yai, hotunansu Angel ne a jere da suka ɗauka
yayi saving ɗinsu akan wayar, ƙura ido gabriel yai akan screen ɗin, a tsanake ya ke
ƙare masu kallo, nan take ya zaro ido wani irin farin Cikine Ya lullu6e shi, hada
murmushin sa.

“Do you remember everything now”? Major ne yai maganar, Jinjina mashi kai yai
alamar eh, janye wayar dr.bown yai tare da kallon abokan aikin nasa da sojojin

“He needs some food and a cold drink” Jinjina kai su ka Yi, A waya Md Ya kira
nurse Ya isar da saƙon abunda za’a kawo masu, cikin ƙanƙanin Lokaci Nurse ta shigo
hannunta biyu ruƙe da round tray saman shi plate ne shaƙe da abinci sai bottles
biyu na ruwa dana lemu mai sanyi, A saman table ɗin gaban gadon gabriel ta sauke
tray ɗin kafin ta juya ta fuce, Zama suka yi saman sofa ɗin dake a ɗakin suna jiran
shi Ya kammala ci.

Kafin ya fara cin abinci sai da ya fara ɗagowa ya kalle su”Ni zan ci”? murmushi
suka sakar mashi Jin tambayar da yai masu

Md yace”’It’s all yours. Eat until you are satisfied. We need to talk to you when
you’re done.”

A kan idonsu Gabriel Ke cin abincin sai da ya ci ya ƙoshi Ya kora da ruwan sanyi,
tukunna ya dawo da duban shi gare su.

“Zamu iya farawa yanzu” ɗaga masu kai yai alamar eh

Major ne Ya fara yi mashi magana


“Zaka Iya fadamin alaƙar dake a tsakaninka da sauran yaran? Jinjina kai Gabriel
yai”Eh, Ƴan uwana ne”

“Menene sunayenku da shekarunku”?


Duk wata kalma da Gabriel ya furta a rubuce dr. Brown ya ke shigar da bayanan
cikin ipad ɗin hannunsa.

“Muna zargin Ɗan ta’addan da muka je kamawa A dajine yai garkuwa da ku don
gujewa farmakin da zamu kai mashi Shin dagaske ne”? Ras Gaban Gabriel Ya faɗi, tuni
yanayin fuskarshi ya canza baisan amsar da zai basu ba, jin shiru yasa Major
ambaton sunanshi”Gabriel amsar ka mu ke jira, muna so mu tabbatar da hasashen mu
ne”

idanuwanshi sunyi wuƙi wuƙi akan fuskokinsu, duk sun ƙagara da son jin amsar da
zai basu, abunda yasa ya shiga ruɗani kokwantone yake yi Akan ya faɗa masu gaskiya
ko kuwa ya 6oyeta gudun kada su ƙara jefa rayuwarsu cikin hatsari, Yana tsoron
abunda harshenshi zai furta, Tunawa da Angel yasa shi saurin cewa

“I have forgotten everything, but my sister Angel knows everything.” ya faɗi


hakanne don su ƙyale shi, don kuma su tuntu6eta don yasan tafi shi wayau ita kaɗai
tasan yadda za ta yi ta fidda su.

Numfasawa Kowan nan su yai, sun fahimci har yanzu babu kwanciyar hankali
atattare da shi

“Gabriel, please calm down and explain to us what happened. We’re medical
professionals, and we have the right to examine your health and help you get
better. And those soldiers you see are the ones who saved your life in the forest.
If you cooperate with us, we’ll help you and reunite you with your family.” cikin
kwantar da murya dr laura ta yi mashi magana.
wahalalln Yawu gabriel ya haɗiya muryarshi na rawa ya furta”Angel tasan komai, duk
wani bayani da kuke son ji daga bakina ita zata faɗa maku,”

“Can you identify your sister from these photos? Wacece Angel a cikinsu”?
Dr.brown ne yai maganar tare da nuna mashi hotunansu ta cikin ipad’s gallery din
hannunsa

Ƙura ido gabriel yai akan fuskarta ya ɗaura yatsan shi”Itace”

Dr. mark ne ya soma yin magana

“muna son jin bayani dangane da abunda ke damunku”? Ya yi mashi tambayar ne saboda
abun da ya ɗaure masu kai, na farko Depression dake damunsu da ƙananun shekarun su,
na biyu dangane da matashin saurayin nan da ya tsone masu ido wato Danish da ya ƙi
farkawa daga bacci.

“Babu” amsar daya basu kenan


Captaim yace”ka natsu kayi mana bayani, ba cutar dakai zamuyi ba, idan har baka
bamu amsa ba zamu maida ku inda muka ɗauko ku ne” jin haka yasa Gabriel zazzare
mashi ido, da sauri ya girgiza kai yana faɗin”Ni ai bansan komai ba Angel ce ta
sani,” kansu ya ɗaure jin yanata ambaton sunan Angel

“We should wait until your sister wakes up and see if she can provide any
information that might help us.” acewar dr. brown

Gaba ɗaya sunyi amanna da hakan, Miƙewa Sojojin sukayi tare da likitocin Bayan
sunce mashi ya koma ya kwanta suka fuce daga ɗakin, A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya
suna tattaunawa a tsakaninsu, Hankalinsu yaƙi kwanciya da yaran, sun fara kokwanton
Anya kuwa Jinsin su ne? Ko dai sun yi kuskure wurin ɗauko su a matsayin
ɗan’ta’addan ƙasar su ne yai garkuwa da su, Kyawun yaran yafi komai tafiya da
hankalin su, sun rasa da wani jinsi zasu danganta su, Saboda Kyawun prisoners Ya
banbanta dana sauran mutane su ɗin na dabanne.

Bayan kammala tattaunawar su, Sojojin sun bar asibitin da niyar idan sauran Yaran
suka farfaɗo daga bacci Ayi hanzarin kiransu da gaggawa don suna buƙatar ganawa da
su.

Nauyayyar ajiyar zuciya Gabriel ya sauke tun bayan fitarsu yake ta sakin murmushi
baƙin shi yaƙi rufuwa, tuni hawayen farin ciki sun wanke fuskarshi bakomai yake
tunawa ba fa ce twin sister ɗinsa da sauran ƴan uwansu da suka rasa rayukan su a
kurkuku, Ya ji raɗaɗin Rasa su da su ka yi da yanzu duk atare zasu ji daɗin
rayuwarsu, don yana ji aranshi ƙarshen wahalar su ce tazo, babban burin shi a yanzu
sauran ƴan uwansu su farfaɗo, Yasan zasuyi farin ciki Mara misaltuwa, fatan shi
Allah yasa Idan Angel ta farfaɗo Ta yi ƙoƙari wurin yin magana da sojojin cikin
hikma yadda zata yi masu hanyar komawa gidan daddynta ko dan saboda azeezarshi da
ta ƙwallafa rai da son zuwa can.

Yayin da ya ke yin tunanin, hawaye basu daina yin sintiri akan fuskarsa ba, a saman
pillow ya ɗaura kansa, ga sanyin A.c dake ratsa jikinsa.

Motsin buɗe ƙofa ya ji da sauri ya ɗan yunƙura ya miƙe zaune yana kallon mai
shigowa ciki, Matashiyar Nurse ɗin da ta kawo masa abinci ce ɗazu, Fuskarta ɗauke
da murmushi agaban gadon ta tsaya tare da goya hannayenta saman ƙirjinta

Fuskarta da murmushi ta soma magana

“Hello, I’m Sister Rebecca, May I know your name?”


Daƙyar ya iya buɗe baki ya furta suna shi “Gabriel” jinjina kai nurse rebecca
tayi a wayance tace “It’s wonderful to meet you, Gabriel. How is your body? I hope
you’re feeling better now,”
Rashin sabo ya hana ya saki jiki da ita, cikin rashin natsuwa yake amsa mata.

Ganin yadda take sakar masa fuska yasa shima sakin tashi fuskar

“Is there any part of your body that’s hurting?” cikin kulawa ta yi mashi
tambayar.
Girgiza mata kai yai”A’a lafiyata ƙalau”

“Okay, is there anything you need?” again ta ƙara tambayar shi.

Ƙasa ƙasa da murya ya furta “No, thank you.”

“Okey, ko akwai wani abu da kake buƙata”? Shiru ya ɗanyi yana faman wurwurga eye
balls dinsa ɗakin Ya ke bi da kallo
Ganin kamar tv yake kallo yasa tace” “Would you like to watch some TV?”

Numfasawa yai tare da mayar da idon shi akanta

“I wanna see my brothers, I want to know how they’re doing.”

“Please, don’t worry, Your relatives are in good health and we expect them to wake
up soon.” da sauri ya tari numfashin ta
“Can you help me go to their room to see them?” A ƙagare yai mata maganar

“Don’t worry I’ll take you to see them but first you need to rest. You’ve
traveled for hours, and you must be tired. I’ll turn on the TV so you can relax,
and if you need anything, you can use the phone to call me.” ta yi maganar tana
nuna mashi wayar dake ajiye saman table na gefen gadonshi

“Ga kuma ƙofar shiga toilet idan kana buƙata” duk abunda ta yi mashi bayani saita
nuna mashi da hannu

Bayan ta kammala, Taje gaban plasma tv dake manne jikin bango ta kunna mashi
tashar da ake wasan ƙwallon, don tasan mafi akasin maza sunfi sha’awar kallon wasan
ƙwallo,

A ƙirji ya rungume pillow yana kallon tv ɗin, fuskar nan ɗauke da annuri banza ta
samu an samu ƴanci, Yadda nurse ɗin ke tarairayarshi kamar wani ƙaramin yaro da bai
wuci shekara goma ba.
Kafin barinta ɗakin saida ta ɗauki Kayan abincin da ta kawo mashi ta fuce da su
robar lemun da bai sha ba kaɗai ta bar mashi, Hannu ya miƙa ya ɗauke ta, Yana sha
Yana kallo Hankalin shi kwance gwanin ban sha’awa

*The prisoners Middle step❤*

Wuraren ƙarfe ɗaya na rana agogon birnin san antonio ta buga, adai dai wannan
lokacin sambatun muryar Angel ya cika ɗakin da aka kwantar da ita, tana akwance
saman haɗaɗɗen gadon, patient’s gown ce a jikinta launin ligh blue, drip ɗin da aka
sanya mata tuni ya jima da ƙarewa, zazza6in jikinta ya sauka temperature ɗinta ya
dai dai ta.
Muryarta na kakarwa take ambaton sunan danish, Shi ya tsaya mata arai shiyasa
take sambatun ambaton sunansa, duk da sanyin A.c na ɗakin hakan bai hana zufa
tsastsafo mata ba, zucyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi
“Danish ɗina kura ta cinye min shi, wayyo Allah Danish ɗina na shigo uku munbar
Danish Gabriel kura Zata kashe min shi.....” tuntana sambtun a hankali har takaiga
ƙware murya da wata irin firgita Ta ware Gray eyes dinta ta zazzare su akan
haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakin, Sam bata acikin Hayyacinta, bakomai take gani acikin
idanuwanta ba face Fuskar Kurar da ta biyo su A daji tana gurnani, gizo take yi
mata, A gigice ta zabura har batasan ta fisge iv line ɗin dake hannunta ba, durowa
daga saman gadon tayi Hannayenta bibbiyu daddafe da kanta, Tsantsar tashin hankali
ne akan fuskarta, duk tabi ta furgice, doguwar sumar kanta har saitin gwiwarta gaba
ɗaya ta hautsine gashin kan tamkar na mahaukaciya, Sam bata acikin hayyacinta
batasan A ina take ba? Daji kawai take gani a idonta

Sosai ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, idanuwanta sun makance,,

Da gudun gaske Likitoci suka faɗo ɗakin da take a ciki, Dama jiran farkawarta suke
yi, wasu daga cikin Ƴan uwanta sun farka acan inda aka kwantar dasu, Sun rasa gane
kan Yaran tsabar tsoro da firgici Jikin su sai kerma ya ke yi sunga mutanan da basu
saba gani ba, duk wanda yai yunƙurin tunkararsu ƙara suke fasawa tamkar ana zare
ran su, Kalma ɗaya su ke iya ambato abakunansu Sunan Angel wannan yasa Likitocin su
ka ƙara da ta farka, don sun fahimci ita kaɗaice zata Iya sarrafa su.

Sam bata ji motsin shigowarsu ba, Sai dai ta ji muryoyinsu akanta, Nan fa hankalin
Ta ya ƙara tashi, A firgice ta waiwayo tana binsu da kallo tun daga ƙasa har sama,
Waro idanuwanta waje tayi tamkar ƙwayar zata faɗo kasa, jijiyoyin wuyanta sun fito
ruɗu ruɗu, tsantsar tashin hankaline akan fuskarta da ruɗani, sai lokacin ta soma
tunanin wai ma A ina take ne? Ya akai ta tsinci kanta a wurin nan? Wanene Ya
kawota? ina ƴan uwanta suke? Su wanene waɗannan masu fararen Kayan kamar likitoci
ne”? Wahalallan Yawu ta haɗiya, zufa duk ta wanke fuskarta da jikinta, yadda kasan
wadda ta yi tozali da aljanu, ganin komai take yi tamkar a mafarki

Cikin kwantar da murya su ke yi mata magana don sun fahimci arikice take babu
natsuwa atattare da ita
“Ki kwantar da hankalin ki, Dukanmu nan da kike gani likitoci ne, mune masu kula
da lafiyarki, Sannan anan inda kike Asibitine.....” Ras taji gabanta ya faɗi Cikin
sarƙewar murya ta soma motsa small lips ɗinta
“Ban...ban..gane ba wanene ya kawo ni nan? Su wanene ku kuma Ina ƴan uwana su
ke”? Kallon tuhuma take binsu da shi gani take yi kamar mugaye ne.
“Ƴan uwanki suna nan Cikin ƙoshin Lafiya, idan kika natsu zamu Nuna maki su,
wata’ƙil hankalinki ya kwanta” maƙe mashi kafaɗa tayi”wlh bazan yarda daku ba, so
kuke ku cutar dani, Ni ku faɗamun Ina danish ɗina yake da sauran ƴan uwana.....”
cikin disasshiyar murya tayi maganar hawayen nabin fuskarta, ganin suna matsowa
kusa da ita aiko da sauri ta dinga ja da baya tana girgiza masu kai, haɗi da
zazzare masu ido don karsu ta6ata

Hakan yasa suka dakata da yin tafiyar, turo ƙofar da akayi ne yasa gaba ɗayansu
suka juya don ganin wanene

Nurse rebecca ce Ta shigo ɗakin hannunta ruƙe dana Gabriel, Wani irin farin
Cikine Ya lullu6e shi ganin Angel, Ita ko ta runtse ido, Masifa kawai take Ji, da
ƙarfi Ya ambaci sunanta”ANGEL!!” Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnanta, Kamar an
tsunkuleta Ta buɗe ido Tana faman zazzaresu Akan fuskokinsu, da gudu gabriel Ya
ƙarasa gabanta, Gaba ɗaya ya rungumeta Yana dariya, A ƙalla ta sauke ajiyar zuciya
yafi a ƙirgita, ƙanƙame shi tayi tamkar zasu koma mutun ɗaya.
Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirkon suna kallonsu, murmushine ya bayyana
akan fuskokinsu, tamkar sun samu tv.
Raba Jikinta Tayi daga na Gabriel Muryarta na rawa take faɗin”Gabriel wanene ya
kawo mu nan? Pls ka faɗamin Aruɗe nake bangane komai ba, Ina danish dina da sauran
Ƴan uwana?

Ruƙo Hannayenta yai acikin nashi”Angel mun tsira! Mun ku6uta daga kurkukun
ƙaddara da Evil forest.......” a tsanake Gabriel Ya kwashe komai Ya sanar da ita,
Cikin harshen hausa, hakan yasa Doctors din basuji me yake faɗa mata ba.
Maimakon tayi dariya Sai gani suka yi ta rushe da matsanancin kuka, abunda da ya
ɗaure masu kai, tana kuka tana dariya a lokaci ɗaya, slowly ta zube saman
gwiwowinta, tare da ɗaura goshinta saman tiles, Sujjada tayi domin nuna godiyarta
ga Allah daya nuna mata wannan ranar da suka daɗe suna Jiranta!

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

_The Prisoners E15🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

~Middle step~

Lokacin da ta ɗago daga sujjadar fuskarta jaga jaga da hawayen, Tafin Hannayenta ta
ɗaga sama ta soma ambaton sunan Allah tana Yi mashi kirari, Hakan Ba ƙaramin ruɗar
da likitocin yai ba, shi dai Gabriel sai murmushi yake saki yana dubanta, Bayin
Allah su kaɗai suka san Wahalar rayuwar da suka fuskanta Dole suji daɗin wannan
Ranar, Ta jima tana addu’a,

Sam takasa miƙewa daga zaunan da take, Hawayen fuskarta tamkar zasu ƙare Sai
sintiri suke yi saman kuncinta

“Angel pls stop shedding ur tears” Gabriel ne Yai mata maganar, Cikin shessheƙar
kuka ta ɗago ta Kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kada jawur da su

“Gabriel dole in yi kukan farin Ciki, kai ka sani irin wahalar da muka sha, munyi
rayuwar kulle tamkar dabbobi har ƙwara ni akan sauran ƴan uwana tun suna jarirai,
wannan ne karo na farko da zasu ɗanɗani rayuwar ƴanci acikin ƴan uwansu mutane, Iya
cuta an cuci rayuwarsu mun tsira amma raunin dake acikin zukatanmu na har abada ne,
saboda akwai abubuwan da muka rasa wanda nayi imanin baza su ta6a gogewa a tarihin
rayuwarmu ba”

Hankalin likitocin ba ƙaramin tashi yai ba ganin yadda take kuka tana surutu gashi
ba su fahimtar abunda take cewa, sai dai sun gane akwai abunda ke damun su wanda
yai silar haifar masu da ciwon damuwa da baƙin ciki

Gabriel da ke a tsaye tuni shima ya fara zubar da hawaye.

Gabanta ne Ya ɗan faɗi Jin kukan Jemimah, Nan take shessheƙar kukan da ta ke yi
ya dakata, Dr. Laura ce ta shigo Ɗakin hannunta ɗauke da Jemimah Tsabar jaraba ta
runtse idanuwanta sun yi suntum saboda kuka, Sunan Genie kaɗai Take furtawa, jikin
Angel na rawa Ta yunkura ta miƙe da sauri ta nufi dr. laura Hannu biyu tasa ta
kar6eta sosai ta rungumeta a ƙirjinta, hannunta hada cannula da aka sanya mata.

“Angel” Muryar Batul ce ta ratsa kunnuwanta, da sauri ta ɗago tana kallonsu, A


jere su ke shigo ɗakin kowan nan su Yasha kuka Idanuwa sunyi luhu luhu, doguwar
suman kawu nan su A hargitse kamar waɗanda aka koro daga gidan mahaukata.

Kowan nan su Na sanye da light blue uniform da aka sanya masu, hannayensu sanye da
cannula na drip da aka sanya masu.

Batul ce ta farko, Bayanta Parveen ce da hannah, Sai mazan Javed da Naufal, da


gudum gaske suka ƙarasa shiga ɗakin gaba ɗaya suka ƙanƙame Angel kamar zasu kada
ita ƙasa.

Al’ajabi Ya hana Likitocin cewa komai, Sun saki baki galala suna kallon Ikon Allah,
Aransu suna Mamakin ƙaunar da suke yi ma ƙaramar Yarinyar da su ke kira da Suna
Angel.

Farin Ciki kamar zai kasheta, Daɗi take ji tarasa ina zata tsoma ranta, Sun
lullu6eta suna yi mata kuka, ko numfashi daƙyar take Iya fitarwa

“Angel ina ne nan? Wanene Ya kawo mu? Wlh tsoro muke ji, munga wasu mutane da
bamu saba gani ba, kada su cutar damu Angel, sai kallon mu suke yi kamar zasu lashe
mu” Su parveen ne ke kora mata jawabi
“Ko dai mafarki muke Yi ne? Mu dake acikin Daji Ya akai muka tsinci kanmu a
wannan wurin tare da wasu mutane masu fararen Kaya, Angel ko dai Aljannace da kike
bamu labari? Idan mun mutu zamu shiga” Maganar Batul tayi matuƙar bata dariya,
Daƙyar ta samu suka saketa, Ga jemimah ta ƙanƙameta Jikinta sai kerma Yake yi.

Azeeza tana maƙale da Gabriel Sarkin tsoro, Ta kasa ɗauke idanuwanta daga kan
faces ɗin Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirko suna kallonsu.

“Angel mun shiga ku, Sai kallon mu suke yi,” Hanna ce ta yi maganar
Muryar dr. Laura ce ta katse masu Hanzarinsu cikin harshen turanci ta ke yin
maganar

“Ku kwantar da hankalinku, babu wanda zai cutar daku, Anan inda kuke Asibiti ne, mu
kuma da kuke gani likitoci ne da nurses haƙƙinmu ne kula da Lafiyarku, Za mu
taimaka maku don ganin kun warware daga lalurar dake damunku, Muna so ku ɗauke mu
tamkar Ƴan uwanku, idan ku ka yi hakan munyi maku alƙawarin zamu share maku
hawayenku, Zamu gatanta ku mu baku kyakkyawan kulawa har izuwa lokacin da zamu miƙa
ku ga Iyayen ku.

Tun da tafara Yi masu magana kowannansu Ya natsu yana sauraronta, da alama sun
fara fahimtarta

Matsowa Kusa Dr Brown Yai daga gefenta Ya tsaya”duk wani abu da kuke buƙata zamu
yi maku shi, ku ɗauka tamkar kuna a gidan Iyayenku ne, burin mu shine ku bamu haɗin
kai, Ku daina Jin tsoron mu”
Muryar Dr Jack Ce Ta janyo hankulansu ga dubanshi
“Mun haɗa ku wuri ɗaya ne saboda mun fahimci ba za ku ta6a sakewa damu ba, idan
har ba Kuna atare da Ƴar uwarku Angel ba, Muna fata Yanzu hankalinku zai kwanta, ga
ku ga Mamanku Angel” Da zolaya yayi masu maganar, murmushi Angel ta saki tana
kallonsu, daga gani suna da mutunci.

“Masoyiya Angel faɗa min me ki ke yi wa Yaran nan naki ne? Don na lura ba ƙaramin
ƙaunar ki su ke Yi ba” Dr Brown ne yai magana haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, Sunnar
da kanta ƙasa Tayi dariya takeso tayi sai da takasa.

“Yaushe kika haife su ne? Sannan Ina Mijin naki”? Kunyace ta rufe Angel da sauri
ta ɗaura Kanta saman sumar kan Jemimah dake ruƙe a hannunta.

Dariya Dr. laura ta saki”Wow Kunya take ji, To ko dai Matashin saurayin nan mai
bacci ne mijinki? Wannan kyakkyawan don naji kamar kina ambaton sunanshi” gaba ɗaya
sun sanyata jin Kunya ji take kamar ta nutse ga farin Ciki da ya lullu6eta.

Da biyu likitocin suke zolayarta, Yana daga cikin aikinsu kwantar da hankalin
Mara lafiya musamman su da suke son su saki jiki da su, Ta hakanne zasu samu
bayanan da suke so daga gareta.

“Mun fahimci Masoyiya Angel bakinta ya mutu, saboda An sosa mata inda ke yi mata
ƙaiƙayi, Yanzu faɗa min me kikeson Ci ke da Ƴan uwan naki mu kawo maku” Cikin
kulawa Dr. laura ke yi mata magana.

Kallon sauran Ƴan uwan nata tayi

“Ko ba ku jin yunwa ne”? Shiru suka yi ba wanda Ya bata amsa, idonsu akan Angel,
Dariya doctors ɗin suka saki
“Oh Baku Iya magana sai da izninta, to ke masoyiya Angel Faɗa mana me kikeso
akawo maki keda Ƴa’ƴan naki don bama son barinku da Yunwa”

Cikin Jin kunyarsu Angel ta furta”komai muka samu zamu ci” Jinjina kai Dr Laura
Tayi kafin ta juya ta kalli Sister rebecca”A shirya masu lafiyayyan abinci da Kayan
sha” amsa mata Tayi da toh da sauri ta juya ta fuce.

Dawo da dubanta tayi akan fuskokinsu


“Yanzu zamu tafi mu baku wuri Pls Idan an kawo maku abincin Ku tabbatar Kun cinye
min shi duka kaf, zanji daɗin hakan,’ dr Laura davis Na rufe Maki Dr Mark Yace”Zamu
dawo Da Anjima, Kyawawan ƴan mata, dole in za6i ɗaya daga cikin ku, irin wannan
Kyau haka”
Dr Bown Yace”ai ba kai kaɗai ba mutumina, Ni ruwan ido ma ya hanani zabar ɗaya,
ta ko’ina Kyau nake gani musamman Masoyiya Angel ta tafi da ni” Dariya ce ta
kubcewa Angel da Gabriel
Harara Dr Laura davis Ta watsa mashi”bazaiyiwu ba, Duk na riga ku, Nima nayiwa
ƴa’ƴana kamun matan aure a Cikin su’ Nishaɗi sosai suka sanya su.
“Zamu tafi Masoyiya Angel, Amma kafin nan Ki kula mana da ƴa’ƴanki, Ki lallashesu
su daina mana kuka dake kanki bama so kuna zubda tsadaddun hawayenku” Cikin sanyin
murya Angel ta amsa mata da toh, Sallama suka Yi masu atare suka fuce daga ɗakin
suna masu santin Kyawun Yaran acikin ransu.
Fitarsu keda Wuya Ange Ta fada saman Gadon rungume da jamimah tana tiƙar dariyar
Farin Ciki tana faɗin”ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN”

“Kuyi Farin Ciki mana, Ina Tayamu murna Mun ku6uta daga Kurkukun ƙaddara, Mun
zama masu ƴanci” Su Batul sunƙi sakin jiki har yanzu basu fahimci Ta ya ya akai
suka tsinci kansu a wannan wurin ba.
Gabriel ne yai ƙoƙarin fahimtar da su abunda Ya faru zuwan Sojoji Dajin.
Wayyo Allah daɗi Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskokinsu,
Bakunansu sun kasa rufuwa Fararen haƙoransu tamkar Gonar auduga
“Gabriel kana nufin Yanzu mun bar kurkuku da daji? Muna acikin Mutanan duniya”
Fuskar Gabriel da murmushi Ya amsa masu”ƙwarai kuwa, Babu ku babu zubar da hawaye
baƙin ciki da kunci sun ƙare” Tsabar Farin Ciki Suna kuka suna dariya, gaba ɗaya
suka Haye saman Gadon Angel, suka kwanta a jere da ita sai daɗi suke ji saman
ceilling ɗin ɗakin suka ƙurawa ido kowa Yana tariyo abubuwan da suka faru a
rayuwarshi jin shessheƙar kukansu ta cika ɗakinne Yasa ta soma yi masu magana cikin
lallashi
“Dan Allah ku daina, Yanzu lokacin farin ciki ne, Godiya yakamata Muyiwa Allah, a
koda yaushe shi mahaƙurci mawadaci ne, yau gashi dai mun shaida hakan Allah ya
kar6i kokenmu yaji ƙanmu ya raba mu da ƙangin rayuwar da muke aciki, A yau mu masu
ƴan ci ne zamu shaƙi Iskar duniya son ranmu batare da wani yayi mana Iyaka da ita
ba” Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu
Cikin shessheƙar Kuka Azeeza ta soma magana tana fadin”Ni ƴan uwanmu nake
tunanawo waɗanda muka rasa acikinmu, tare da Salsabeel da ya taimaki rayuwar mu,
nasan dole su kashe shi idan suka kama shi Yana acan kurkuku Suna azabtar dashi”

Naufal ya ɗaura da cewa”babu Deeja! Babu Mubeen Akan idonmu ya yanke jiki Ya
faɗi, a lokacin muna aga6ar barin kurkuku.....” Kasa ƙarasa maganar Yayi saboda
kukan da ya ciyo shi.

Javed ya dasa daga Inda ya tsaya”Mun rasa tsohuwa tamira! Mun rasa Eve da Yasmin
sannan mun rasa Hibba da Rubina, da Sarah! “ tunkan Ya rufe Baki Angel ta ɗaura da
cewa”Allah Sarki Unaiza Ƴar gidan daddy, da Majnoon Bayin Allah ban ta6a tunanin
zamu tsira ba tare dasu, Muna ƙaunar ƴan uwanmu sosai, Sai dai mutuwa tayi mana
Yankan ƙauna, Ta raba mu da su, In sha Allah zamu haɗu da su agidan Aljanna inda
babu kurkukun ƙaddara babu duk wani mugu, Allah sarki tsohuwa tamira da Salsabeel
waɗannan bayin Allahn Har duniya ta naɗe bazamu ta6a mantawa dasu ba, saboda Sun
kafa tarihi acikin zukatanmu In sha Allah a koda yaushe zamu dinga binsu da addu’a,
sannan zamu Cika masu burin su na ruguza tarihin KURUKUKUN ƘADDARA.

Abubuwa da dama suke tariyowa na rayuwarsu na baƙin Ciki da farin Ciki


“Angel Danish fa har yanzu bai farfaɗo ba, Haris kuma Bashi da ƙoshin lafiya nurse
ta faɗa min abunda ke damun shi ni nasan silar deeja ne, Amma tace Ciwon nashi
bazai jima ba, Zaiji sauki”
Jin wannan maganar yasa gabanta faɗuwa, A hanzarce ta miƙe zaune saman mattress
ɗin, su Batul ma suka mimmiƙe suna kallonta, sun sha kuka fuskokinsu sunyi jawur
dasu abunka ga farare, Ita dai Jemimah tunda ta lafe ma angel hankalinta kwance
bata da sauran damuwa.

Ƙasa ƙasa da murya ta ambaci kalmar Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Gabriel


Akwai matsala! Wai ni wace ƙasa ce wannan”? A matuƙar ruɗe ta jefa mashi Tambayar,
duk budurin da akeyi bata lura da fararen fata bane sai da yayi mata zancen Danish.

“Ni kaina Angel bansani ba” Dafe kai tayi da hannu ɗaya, Yayin da take bin ko’ina
na room ɗin da kallo, karaf idonta ya sauka akan wani hoto dake manne jikin bango,
a jikin shi an rubuta

SAN ANTONIO TEXAS United states of America

zazzare idanuwanta waje tayi wuƙi wuƙi Muryarta Na kakarwa ta soma maimaita Sunan
America, tun da take arayuwarta bata ta6a taka kafadarta a ƙasar waje ba, Iya
Nigeria ne, Yau ƙaddara Ta jefo su America a maimakon Nigeria! Hankalinta idan yai
dubu toh ya tashi, ta ya ya zasu Koma Nigeria har su samu damar ɗauko ruwan zamzam
da zasu ba Danish? Don tana Ji aranta Baccin da yake yi bana lafiya bane zaiyi wuya
ya farka batare da giant’s heart ɗinsa ta motsa ba, Muryoyinsu Aruɗe su ke ambaci
sunanta”Angel menene? Bamu tsira ba ko? Wani abu zai faru damu”? Girgiza masu kai
tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Wlh ba Nigeria bace wannan ba ƙasa ta
bace, America ce ƙasar turawa, taya akai haka ta faru!? Nauyayyar ajiyar zuciya
suka sauke, don su basu san abunda take gujemawa ba, Lamarin ya girgizata har
tafara tunanin dama kurkukun ƙaddarar ba A nigeria ya ke ba? Akwai gagarumar
matsala dole su nemi mafita.

“Angel ae zamu Iya zuwa can ko”? Da sauri Gabriel ya amsa masu da cewa”Eh mana ba
wani abu, kada ku damu kanku, Sojoji sunce idan muka basu haɗin kai zasu damƙa mu
wurin Iyayenmu, Idan suka tambayemu sai mu faɗa masu cewa Mu ƴan nigeria ne”

Kafin wani Ya ƙara magana acikinsu, Nurse rebecca Ta turo ƙofar ɗakin Hannunta
ruƙe da faffaɗan tray na kayan abinci da aka jera masu, A saman table ta ɗaura
masu, kafin ta ɗago tana dubansu fuskarta ɗauke da murmushi tace”Idan kuna buƙatar
wani abu zaku Iya kira awaya ku sanar dani” Ta yi maganar tana nuna masu wayar dake
ajiye saman table, al’ajabi ne ya kama su wai yau sune ake tarairaya? har
tambayarsu ake yi in suna buƙatar wani abu? Wannan wani irin abun farin ciki ne!

Har ta juya zata fuce, Muryar Angel ta dakatar da ita “Sister, which country are
we in?” ? ta tambaye ta ne don ta ƙara tabbatarwa
Juyowa Nurse rebecce tayi fuskarta da fara’a ta furta”San antonio texas” idanuwan
angel luhu luhu ta ce”Thank u”
Hankalin Angel Yaƙi kwanciya, sam bata lura Sun fara Cin abincin ba, gaba ɗayansu
sun dawo bakin gadon, Su parveen banza ta samu, soyayyar kaza mai maiƙo ta damƙa
tana turawa abaki atsiyace take cizgar Naman kazar, Jemimah ta sungumi tsiran nama
ita da azeeza, Batul kuwa Soyayyan ƙwai ta ɗauka tana Ci har wani nannaɗe shi take
yi kafin ta tura abaki, Hannah ko warmer ta ɗauka shaƙe da Chips tana ci, Ba baka
sai kunne, Su naufal an dahi Chicken shawarma, Javed ko Kayan marmari ya damƙa yana
sha, kamar kwancen Yunwa Sun zaƙe suna ci suna Korawa da lemu me sanyi kala kala
aka kawo masu, basu san akwai cctv ba a ɗakin, Duk wani motsinsu ana kallonsu😂
Ita kanta Angel data dubesu saida gabanta ya faɗi, Ganin yadda suke cunkusa
abinci abakunansu Kamar kuraye, Muryarta na rawa take faɗin’pls ku bi a hankali
kada ku shaƙe” tamkar kurame babu wanda ya dubeta bama su san akan me take magana
ba, a dole ta ƙyalesu ta zura hannu ta ɗauki burger tana ci...........

*BARI MU LEƘA GIDA NIGERIA*

*A DAULAR OBIE ESTATE*

A Zaune take dirshan acikin Katafaren Bedroom ɗin Obinna, wa’iya zubilla kai kace
ɗakin matashin saurayine saboda tsabar haɗuwarshi, An kashe dukiya a furniture ɗin
ɗakin komai na cikinsa launin Red and golden ne, Ko sarki Albarka, Tanƙamemen
gadonsa Royal state bed irin gadon da ko mutun baijin bacci ya hau sai Ya runtsa,
Ga wasu matassan kai launin red da golden jere a gaban headboard ɗin, Dogayen
labulaye ne a kewaye da ɗakin, ga wasu bedside drawers masu ɗauke da lamp, daga
saman ceilling ɗin ɗakin Haɗaɗɗen Chandeliar ne dake bada hasken ɗakin ga wata
zungureriyar Sofa Bayan ita akwai arm chairs masu ɗan banzan kyau, Ga wani
ƙayataccen table dake ɗauke da Kayan Ado na ɗaki. Daga jikin bangon ɗakin
haɗaɗɗiyar wallpaper ce mai zanan flowers masu matuƙar ƙayatarwa da jan hakalin me
kallonsu, floor ɗin ɗakin tamkar mirrored tiles ne Kana Iya ganin fuskarka a
cikinsa tamkar madubi, ga wani Jigunannan Dressing mirror Tafkekan gaske Jerin
tsadaddun turarurrukane ne asaman shi da sauran kayan gyaran jiki, idan nace zan
cigaba da zayyana haɗuwar Ɗakin dattijon arziki tabbas zamu ƙare takun tsakiya
wurin fasalta Kyawunshi.

Yana daga kishingiɗe saman lallausar mattress ɗin gadon, Apple laptop ce agaban
shi, Da alama Video call Ya ke yi da wani, ɗabi’arsa ce yana magana yana shafa
gemun shi wani sa’in har Jan shi ya ke yi.

Hajiya saratu tayi zaman cin tuwo saman lallausan carpet ɗin gaban gadon shi, tana
jiran Ya kammala Yin wayar, ta tsare shi da ido babu annuri akan fuskarta, Hankalin
shi gaba ɗaya yana akan fuskarta, Nazarin yanayinta ya ke yi, kamar daga sama ta
tsinkayi muryar shi akanta
“Saratu kin wuni lafiya”? Ƙara tamke fuskarta tayi”lafiyalou baba, fatan na same
ku lafiya” murmushin gefen fuska ya sakar mata”Alhamdulillah, in ce ko lafiya? Naga
yanayin fuskarki da 6acin rai, Waye ya ta6amin autata ne yanzu in ɗaura ɗamarar yin
yaƙi da shi” murmushin Yaƙe ta ƙaƙalo, har ta buɗe baki zatayi magana yai saurin
tarar numfashinta”nasan kinzo gaishe da baban nakine kamar yadda kika saba, Naji
daɗi sosai mamana, Bari na kira hajjaty A waya ta kawo mana dinner mu ci atare ni
da autana” tur6une fuska Hajiya saratu tayi”ba yunwa nake ji ba, Zuwa nayi mu yi
magana, kafin barina ɗaki sai da nayi magana da masu aiki nasan sun kai min a
ɗakina”
“Ai nasan ba yunwa kike ji ba, Ni nake ra’ayin cin abinci tare da ke, idan mun
kammala sai mu yi magana” aruɗe take kallonshi, ƙiri ƙiri Ya hana tayi magana.
Ba tare da ya jira amsarta ba, Ya ɗauki waya dake saman bedside drawer, Ya kira
landline na kitchen, bugu uku aka ɗaga kiran, muryar sophia ce ta ratsa kunnansa
cikin girmamawa ta gaishe da shi.

“Ina buƙatar Dinner ɗina a shigo min da shi ɗaki yanzu” amsa mashi tayi da toh
kafin yai rejecting call ɗin, idanuwanshi akan saratu da ta haɗe rai, kasa jurewa
tayi don baƙaramin takura tayi ba hakan yasa ta soma magana ba tare da ta jiran
umarninsa ba.

“Baba ni gaskiya ba a kyautamin agidan nan, akan me za’a dinga kushe min ƴa’ƴana
ana yabon na wasu, abun yana ƙona min rai bana jin daɗi, haba dan Allah wannan ba
adalci bane, kuma ba girman Yaya Lateef bane da yaya mubarak su zauna suna faɗan
maganganun marasa daɗi akan ƴa’ƴana, ni kaɗai ke ba’ason ya’ya na a family din nan
ko dan saboda ban auri jinsin mu bane” Rai a6ace take yin maganar, tun da ta fara
magana bai dakatar da ita ba, ya natsu yana sauraronta idonshi akan fuskarta, dama
tun kafin ta fara yin maganar yasan meya kawo ta, Yana mamakin Halin saratu, ko
irin alkunyar nan babu, idonta ya rufe akan ƴa’ƴa da miji, abu ɗayane take jin
nauyin yi wato idan tana zazzaga masifa bata bari su haɗa ido dashi, murmushine
akan tausasan la66ansa
“Kin gama maganar ko akwai saura” bata ɗago ta kalle shi ba idonta na akan carpet
ɗin da take a zaune dirshan
“Hateem Faɗa min menene sunan macan da take ɗaukar zigar miji”? ras taji gabanta
yai mugun faɗuwa, A ruɗe ta ɗago da ido tana kallon fuskar obinna, ƙayataccen
murmushine akan fuskarshi, Ji take tamkar ta yunƙura ta miƙe ta zuba da gudu don ta
fahimci Video call yake yi da Yayanta hateem na ƙasar Canada, Hakan na nufin duk
wata magana da ta ke faɗama babansu akan kunnanshi, Hankalinta ya tashi don ba
ƙaramin jin shakkar shi ta ke Yi ba, duk acikin yayunta tafi fargabar sharafudden
da hateem.

A hankali Obie Ya juya mata Lapton ɗin gabanshi don suyi magana da Yayanta, sunnar
dakai ƙasa tayi sam ta kasa ɗagowa ta kalli screen ɗin laptop nasa
Daddaɗar muryar prime minister Hateem ce ta ratsa kunnuwanta
“Ji ra kike in gaishe ki”? Girgiza kai tayi tamkar tana agabanshi, cikin girmamawa
ta soma gaishe da shi
“Ina wuni Yayana, Ya aiki Ya iyali”
“Ki ɗago da ido ki kalle ni Saratu”! Da kakkausar Murya ya furta hakan, Yawu ta
haɗiya kafin A hankali kamar maijin tsoro ta saci kallon screen ɗin.

Tabarakallahu ahsanun khalikin!! Ni kaina da nake rubutawa sai da alƙalamina ya


girgiza da ganin Kyakkyawar surar nan mai cikar kamala, gwarzon namiji jajirtacce,
kallon ɗaya zaka Yiwa fuskarshi ka shaida Jinin Obinna ne, Yana ɗaya daga Cikin
waɗanda su ke kama da babansu, basu baro komai nashi ba, Kyanshi, ɗabi’unsa da
halayansa, Fatarshi kaɗai abun kallo ce, yadda kasan da ruwan madara ake mulketa
saboda tsabar kyau, skin colour ɗinshi launin na mahafinshi ne, A zaune yake Cikin
Katafaren Office ɗinsa dake a Presidential residence Na ƙasar Canada, tsayawa
zayyana kyawun Office ɗin da dukiyar da aka kashe masa wurin zuba kayan cikinsa
abune da hankali ba zai ɗauka ba, wata’ƙil zamu ƙare Takun tsakiyane wurin zayyana
shi, wasu hadaddun tailored suit ne a jikinsa sunbi shape ɗin jikinsa, mutumin
akwai ƙira.

“Bai kamata kiji kunyar haɗa ido dani ba Saratu, tunda har kika iya tako
ƙafafuwanki kika zo ɗakin baba don kiyi mashi masifa, Ke ko kunya bakya ji? Ki
zauna Miji Yana ziga ki Kan ƴan uwanki? Sara Ba haka nasanki ba, Ni ba haka ƙanwata
take ba, jarumar macace mai hankali da tunani, why kike son bani Kunya”? Maganar
Hateem tayi matuƙar sanyata jin kunya, duk sai ta ji haushin kanta ya kamata, tayi
danasanin zuwa ɗakin obinna, saboda tana matuƙar jin nauyin Hateem, da ace tasan da
shi suke yin video call da batayi gigin zuwa kawo ƙorafi ba.
“Kiyiwa kanki faɗa saratu, Ba girmanki bane, Ƴa’ƴanki ai namu ne, babu wani
banbanci, nasan abunda Yaya mubarak da Yaya lafeef zasu faɗi bazai wuci akan
Cigaban Ƴa’ƴanki bane, maisonka shike faɗa maka gaskiya duk min ɗacin ta, Maƙiyinka
kuwa sai dai Ya 6oye maka yakamata Kiyi tunani ƙanwata” Cikin kwantar da murya yake
yi mata nasiha, shi kanshi Obinna har lumshe ido yake yi saboda jin daɗin nasihar
da Hateem Yake yiwa ƙanwarshi, kuma ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi sosai
Muryarta tamkar zata fashe da kuka ta soma magana”In sha Allah yaya zan kiyaye,
bazan ƙara biye mashi ba, zuciya ce ta ɗibe ni, Ni kaina nasani kuna son ƴa’ƴana
shiyasa kuke yi masu faɗa don su gyara, duk wanda ya rasa faɗi a duniya yai asara,
ina jin daɗin ƙoƙarinku akaina da ƴa’ƴana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku”
idanuwanta har sun cicciko da ƙwalla
“Kada ki bari hawayen nan su zuba, Kinsan banaso ko”? Ɗaga mashi kai tayi
alamar eh”Okey yi min murmushin nan naki in gani” Dariyace ta kubce mata, da sauri
ta ɗaura kanta saman manyan laps ɗinta
“Ya aikin naki? Fatan komai na tafiya lafiya” amsa mashi tayi da”lafiyalou”

Jinjina kai Hateem yai”Allah ya taimaka” sallama sukayi da ita Obie Ya juya laptop
ɗin, idon shi akan Hateem
“Shiyasa nake Ƙaunarku, Saboda ku ɗin na dabanne, ƴa’ƴana abun alfaharina, Allah
Yabar munku, ubangiji Allah ya tsare mun ku Ya kare munku daga sharrin maƙiya da
mahassada......”addu’o’i obinna yadinga jero mashi, Yana masa mashi da ameen ameen
hada saratu wurin amsawa daga bisani Suka yi sallama dashi
Rufe laptop ɗin yai tare da miƙe ma saratu, Yunƙurawa tayi tare da matsawa gaban
gadon ta kar6i laptop ɗin ta nufi saman desk ɗinta ta ɗaurata.

“Assalamu akaikum” muryar Hajjaty ce ta ratsa kunnuwan su, atare suka amsa mata
da wa’alaikum salam shigo daga Ciki, Tura ƙofar tayi kamar kullum fararen Kayane a
jikinta, Tasha uban ado kamar amarya, sam bata gaji da ca6a ado, Hannayenta sun
sha ƙunshi na jan lalle.
Hajiya saratu dake a tsaye tana kallonta, Haushin Matar take ji, ta tsani taga
ƴar aiki tana ɗaukar wanka kamar yar masu gida, zuciya da saƙe saƙe, sai ta dinga
ganin kamar obinna bin jikinta yake yi da kallo, fargabanta kada wata rana
dattijonsu ya ƙyasa, Ƙarasawa Hajjaty tayi cikin ɗakin Asaman Carpet ta ɗaura tray
ɗin, sai faman sakar mashi murmushi take yi shima ɗin mayar mata da martanin
murmushin yake yi, Hankalin Hajiya saratu yaƙi kwanciya Tana a tsaye ta ruke
qugunta
“Yalla6ai fatan ka wuni lafiya, tun ɗazu nake jiran shigowarka gidan bansan kun
dawo daga masallaci ba, ae da tuni na jima da kawo maka abinci” Yanayin yadda take
magana muryarta tamkar ana busa sarewa, ƙamshin turarenta Ya addabi hancin hajiya
saratu
Lumshe ido yai kafin ya amsa mata da”lafiyalou Alhamdulillah, nagode da kulawarki
agareni, Kina ji da dattijon nan naki sosai nima na yaba da hakan”

Fuskar Hajiya saratu a ɗaure ta furta”ke! Tashi kibar ɗakin nan tunda kin kawo
mashi abincin,ya gode sai anjima” miƙewa Hajjaty tayi tare da jiyawa ta kalleta”Ina
wuni hajiya”
“Da ban wuni ba kin ganni, Ƴar rainin wayau sai yanzu kikasan dani aɗakin, dallah
ni zo ki fuce waje” jikin Hajjaty yai sanyi duk sai ta ji ba daɗi
“Inaso zan zuba mashi abincin....” tunkan ta ƙarasa Hajiya saratu ta daka mata
tsawa”Nace ki fita ko”? Matsawa tayi tare da fusgo hannun Hajjaty taja ta waje,
Obinna dake a kishingiɗe saman gadon ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, lamarin
saratu sai addu’a ya fahimci kishin mahaifin nata takeyi.

Bayan fitarsu daga ɗakin, a bakin ƙofar suka tsaya da tafiya, Hajiya saratu na
faman ciccije le6e ta furta”Ni ban yadda dake ba, akan me zaki dinga zuwa ɗakin
Ubanmu, balallaga dake Ina laifin Ki turo matasan ƴan matan masu aikin su dinga yi
mashi hidima”? Idanuwan hajjaty tuni sun cicciko tab da ƙwalla, ta tsani faɗan
hajiya saratu, a shekaru kusan tsaran junane amma ta tasata gaba tanayi mata faɗa
kamar wata ƙanwarta
“Ai shine ya za6eni bani nake kawo kaina ba, Yafi so ina yi mashi hidima, kuma ki
tambaye shi zai fada maki hakan” Harara Hajiya saratu ta watsa mata”ae dole ya za6e
ki, tun da kin riga kin asirce shi da wannan munafukin turaren naki, mace sai kace
karuwa, Kin bi jiki duk kin feshe da turare Bakisan haramin bane mace ta fesa
turare mai ƙarfi ba? Ina laifin wanda zaki ɗan matsa a hammata!” yawu hajjaty ta
haɗiya batare da tace mata komai ba
“Idiot, daga yau karki kuskura In ƙara ganin Kin a ɗaki babanmu, tun fil azal ni
baki kwanta min araina ba, Ina raga maki ne saboda mijina ba dan haka ba wlh da
tuni na jima da korarki can ƙauyanku na can india, A tsawace takai ƙarshen
maganar tare da ingiza hajjaty, tai taga taga zata faɗi daƙyar ta samu ta dafe
bango, dogon tsoki Hajiya saratu ta buga kafin Ta juya ta koma ɗakin obinna.

Jiki asanyaye hajjaty ke tafiya yayin da hawaye ke bin fuskarta, Da mayafin


hannunta take share ƙwallar dake sintiri saman kuncinta, Kalaman Hajiya saratu sun
ƙona mata rai.

Tun fitar Hajiya saratu daga ɗakinta, Pravin Yana zaune gefen gadon shi, Shi da
Tagwayensa zayn da zayn, suna zaune saman sofa, ransu ya 6aci matuƙa babu annuri
akan fuskokinsu

“Yanzu me kuke so ayi”! ya jefa masu tambaya yana mai kallon fuskokinsu
“Ka sama mana hanyar da zamu bar ƙasar nan, saboda mun gaji da zaman gidan nan, a
takure muke kowa baya son mu kusan kullum ne sai anyi mana Gori” murmushin gefen
fuska Pravin ya ɗan saki Yana duban ya’yan nashi cikin so da ƙauna
“Kun bani Kunya wlh, Why maganar mutane zata dame ku? Har wani ya isa yasa kubar
Danginku? Kenan wata rana zaku Iya kashe kanku saboda wani ya 6ata maku rai eye”!
ɗaure mashi fuska suka yi don sun fahimci uban nasu babu zuciya a ƙirjinsa, shiyasa
bai ganin illar abunda ake yi masu, yafi so su zama masu matattar zuciya irin shi
“Daddy pls, ka fahimce mu, bama jin daɗin zama gidan nan, america muke son komawa
da zama” girgiza kai pravin yai”bazaiyiwu ba, ai baku keda kanku ba, Nima ina
buƙatar ku atare dani, Ku faɗi wani abun na daban da kuke so zan iya yi maku shi”
magiya suka dinga yi mashi akan ya amince masu su koma america,
“Daddy bafa da kuɗinka xaka ɗauki ɗawainiyarmu ba, munsan komai kakeso mommy zata
yi maka taimakonmu kawai zakayi mu samu ta amince mana”
Ɗaure fuskarshi yai”saboda ni bani da arziƙin da zan Iya ɗaukar nauyinku”?
Girgiza kai sukayi atare
Ta6e la66ansa yai”bansan me kuka ɗauke ni ba, Ita kanta mahaifiyar taku A yanzu
bata kama ƙafata wurin arziƙi ba,” kallon Juna su ka yi da mamaki akan fuskokinsu
Miƙewa yai daga gefen gadon Ya nufi gaban drawer chest, Ya buɗe ya zaro atm card,
dawowa yai ya zauna yana fuskantarsu
“Banyi maku Iyaka da kuɗin dake acikin acct bank ɗina ba, don nasan har abada
bazaku Iya ƙarar da su ba, a duk lokacin da kukeso zaku Iya cirar kuɗi ku biya
buƙatunku, sannan kuje ƙasar da kuke so, Farin Cikinku shine nawa”
Kallon da suke yi mashi kamar basu yarda da maganarshi ba, saboda sun raina
arziƙinsa,
Still murmushine akan fuskarshi yace”baku yadda da mahaifinku ba ko”? Shiru basu
tanka mashi ba, Aransu suna ayyana may be babu ko sisi a atm ɗin, idan ma akwai
kudi to Na mommynsu ne tunda ita ke da kuɗi.
Miƙa hannu pravin yai tare da ruƙo wayarshi dake a gefenshi, kamar sakarkaru haka
suka tsare shi da ido suna kallon shi, Daddana wayar yayi kafin Ya miƙa masu da
sauri Zayn ya kar6i wayar Suka haɗa ido suna kallon screen ɗin wayar, Total balance
ne na kudin dake a acct bank dinsa, tsabar firgita har saida suka ɗan zabura ganin
millions of dollars, wanda a kuɗin nigeria Billions ne.
Aruɗe suka haɗa baki wurin furta”Daddy Numbobi ne waɗannan ko kuwa kuɗin ne
dagaske” dariya ya sakar masu
“Abunda idanuwanku suka nuna maku, Just ku ɗauki atm ɗin zan tura maku pin ɗinsa
ta text message,” lamarin yai mugun ɗaure masu kai,
Girgiza kai Zayn yai”a’a daddy kuɗin sunyi mana yawa, ni tsorona ma kada ace Na
mommy ne” Miƙa mashi wayar yai
“Idan har kuka bari na kar6i atm ɗin nan kada ku ta6a tsammanin zan taimaka
maku!” Kallon Juna sukayi zuciya na azalzalarsu akan su kar6i atm din suyi
sharholiyarsu
“Zayn mu kar6a ko”? Girgiza kai zayn yai”A’a zaid kuɗin mommyne fa, idan muka
ta6a zata gane ni dai ban goyi bayan hakan ba”
“Pls zayn tun da daddy ne ya bamu just mu kar6a kawai”
“No zaid, kuɗin sunyi yawa zasu sa mu shagala mu daina yin sallah ne” Pravin dake
kallonsu ba ƙaramin dariya suka bashi ba.
“Har yanzu akwai ƙuruciya atattare daku, kuɗin kuke gudu? Ai nayi tunanin idan na
baku jiki na rawa zaku kar6a, ban ta6a tunanin kuna da zuciyar Imani akan kuɗi ba,
Sam baku da haɗama, Ga dama ta samu amma kuna ƙoƙarin yin watsi da ita”!
Muryar zayn na rawa ya furta”Daddy zamuyi shawara tsakaninmu, ka ajiye mana atm
ɗin zamu kar6a” jiki na rawa ya ruƙo hannun Zaid suka fuce daga ɗakin.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa Ya maida atm ɗin inda ya ɗaukosa, komawa
yai gefen gadon ya zauna yana cin abincin Da abla ta kawoma Hajiya saratu

*Dr.Jazz*

Tun zuwa shi gidan Mommynsa ta ke ta faman tarairayarsa tamkar ƙaramin yaro, Yana
daga kishingiɗine saman doguwar sofa ya ɗaura kanshi saman laps ɗinsa, Sai zuba
mata shagwa6a yake yi, yatsun Hannayenta na acikin sumar kanshi Tana yi mashi susa
Mahaifiyar Dr.Jazz Baturiyar ƙasar England ce, sunanta na asali Harriet, Silar
zuwanta aikatau gidan ta musulunta suka canza mata suna zuwa khadija amma sunfi
kiranta da Turai, Farace jawur tana da jiki bata da tsayi launin idonta green ne,
sumar kanta launin blonde, A yanzu ba matsayin mai aiki take ba, Matace awurin Sir
mubarak, Ya daɗe da auranta tun Bayan rasuwar matarshi Hajiya naja’at, Ƴa’ƴan shi
biyu da uwar gidansa gaba ɗayansu ba mazauna Nigeria bane, Suna a ƙasar canada suna
kula da Babban companynsu tare da sauran ƴan uwansu dake zaune agidan Hateem.
Turkish dress ne a jikinta, Riga da wando launin red colour, Ta ɗaura satin
scarve asaman wuyanta, ta zubo da gashin kanta har gadon baya, Allah yayita da
ruwan kyau.
“Jazz sai nake ganin kamar baka yi kewata ba, Meyasa bakasan zuwa ganina? kullum
Sai in ni na shiga gida nake samun damar ganinka idan naci sa’a baka tafi aiki ba.
Fararen idanuwanshi ya daura akan fuskarta,
“Mommy ba haka bane, Ni just banason haɗuwa da daddyne, ya cika faɗa, kuma sharri
yake yi min yana cewa wai ni mata maza ne, Fisabilillah”
“Ya faɗi hakanne donka Gyara rayuwarka, ni kaina ina mamakin shagwa6arka sai kace
wani yaron goye, komai naka irin na mata”

Ɗaure mata fuska yai”mommy kina goyan bayansa kenan, yaci gaba da kira na mata
maza”? Girgiza mashi kai tai”A’a, Ai nafi kowa jin haushin inji ya kiraka da hakan,
Yana ta6a min zuciyana, donni nasan namiji na haifa ba maca ba” murmushi Jazz Ya
saki”to kice mashi ya daina”
“Zan buga mashi warning, kada ka damuwa” maƙe mata kafadai yai”Allah mommy ni
nasani wasa kikeyi, saboda ke kanki shakkarshi kike ji ba zaki Iya buɗe baki ki yi
mashi magana akan ya daina ba”
Jan kumatunshi tayi da hannunta In jiwa ya faɗa maka! Ni bana jin tsoronshi awaja
ne mutane ke jin shakkarshi, da zarar ya shigo nake juya shi son raina, Har girki
yana yi min” Baki asake Jazz ke kallonta
“Uncle mubarak ɗin”! Jinjina masa kai ta yi”ƙwarai kuwa, ae dukkan Namiji bawan
matane,
Har ya buɗe baki zai ƙara magana, Wayar Aljihun wandonshi ta soma ruri, miƙewa
yai da sauri ya curo wayar, bayan ya duba sunan mai kiran nashi ya ɗago tare da
kallon mommynsa, Wanene ya kira”?

Bai amsa mata ba sai dai ya sakar mata murmushi, da sauri Ya fito daga falon
gidan, Kamar wani munafuki duk faɗin gidan bai isheshi ba sai da ya shiga garden
tukunna ya dakata da yin tafiyar, Yai picking call ɗin jiki na rawa ya kara ta akan
kunnansa, Kirari ya soma yiwa wanda ya kira shi wayar tamkar maroƙi,
“Yalla6ai Kajin nan suna nan cikin ƙoshin Lafiya, Suna samun kyakkyawar kulawa
yadda ya dace,” dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana sauraron muryar mai magana,
“Ana basu hatsi yalla6ai mai rai da lafiya, Yanzu haka idan nagama magana da mama
zan tafi gidan gona domin duba lafiyarsu,” sai faman sakin murmushi yake yi,
aladabce yake yin maganar
‘kasan kajin turawa saida hatsi mai kyau, Gaskiya basu da matsala yalla6ai, biyu
daga cikinsu ne kaɗai suke neman gazawa, shi zakaran ciwon nashi Ya lafa, sauran
Kajin muna nan muna basu kyakkyawar kulawa, in sha Allah zasu samu lafiya harma
asamu nayin farfesun sallah”

Tuntsirewa dr Jazz yai da dariya hada dafe ciki.


duk wannan surutun da ya ke yi acikin waya baisan Sir Mubarak na tsaye abayanshi
ba, daga shi sai gajeran wando, Da singlet fara, hannunshi ɗaya ruƙe da Cup na
coffee

Mamaki ne ƙarara akan fuskarshi Jin dr jazz na Zancan kajin turawa awaya

“Okey toh, Zuwa anjima idan nashiga gidan Gonar zan Kiraka Awaya” Daga haka
sukayi sallama, Juyawar da zaiyi karaf suka haɗa ido da sir mubarak, tuni yasha
jinin jikinsa, Duƙar da kai ƙasa yai ido ya raina fata
“Jazz! Dawa kake magana a waya? Kajin menene naji ana magana akai? Ni dai A iya
sanina likitan mutane ne kai bana dabbobi ba” sosa ƙeya jazz yai, mirya dabarbarce
yake faɗin”am...umm..dama “ Ya rasa ta ina zai taro zancen,
Kallon tuhuma Sir mubarak ke jafa mashi hakan yasashi yin saurin fauzewa
“daddy, Ni da abokina ne dr fawan muka buɗe gidan gona, kajin turawa ne muke
kiwo, wasu ne babu lafiya shine ya kira muna tattaunawa game da yadda zamu shawo
kan matsalar”
Ajiyar zuciya Sir Mubarak Ya sauke”Okey, mu shiga gidan” yai maganar tare da miƙa
mashi Cup din hannunsa, da sauri jazz Ya kar6a Yana sha atare suka nufi gidan sai
faman sauke ajiyar zuciya yake yi.

*GIDAN ƊAN IYA*

Mahboob ne ke ta faman zuba sauri Yana tunkarar harabar ajiye motocin su, ya ɗauki
wankan shadda, tunkan Ya ƙarasa idonshi ya sauka akan motar Uncle abdallah, ƙura
ido yai yana kallon bayan motar sunanta Ya karanta, Aranshi Ya ayyana lallai
mutanan nan ba ƙananun shaggu bane wannan mota haka mai tsada! saboda
almubazzaranci da rashin sanin ciwon kuɗi, Ina laifin ko ƴar ƙaramar honda mutun ya
saya ya wadatar, mutane sun ɗaurewa ƙaryar arziƙi wurin zama, Allah dai ya shirya
mu, ae ni wlh ko nayi arziƙi ban Iya fidda kuɗina in sayi mota, na ƙwammace duk
inda zanje in taka da ƙafata, idan ma da nisa ne ƙwara in biya kuɗi In hau motar
Haya, Ita ma wannan motar da nake amfani da ita ba don babansu abokina ne ya bani
kyautarta ba kuma ina ganin mutuncin shi saboda ya ji tausayina ya siyamin ganin
ina hawa motar haya yasin da tuni na jima da siyar da ita’ Shi kaɗai ya ke yin
sambatunsa, Har ya ƙarasa gaban motarshi Ya buɗe front seat Ya shiga Ciki Yana ƴan
dube dube, da alama wani abu yake nema, saƙo da lungu na motar yake ta bincikawa,
har ƙarkashin seat, tuni ya haɗa uban gumi.
“Ina na ajiye zoben nan Jiya? Ko dai ban shigo da shi mota bane? fuskarshi a
hautsine Ya jefawa kanshi tambayar, zurfin tunani ya shiga yi still bai tunano inda
ya ajiye shi ba, A ƙarshe Ya soma tunanin kodai Ya shigar da shi ɗaki ne,

Fitowa yai daga cikin motar Ya datse murfin, Jiki na 6ari ya nufi cikin gidan.

Abie da Uncle ɗan Iya ne zaune a saman sofas na palourn tare da Uncle abdallah,
Sun nutsa suna tattaunawa dangane da 6acewarsu tajuddeen, Mahboob Ya faɗo falon Ko
kallo basu ishe shi ba hankalin shi na akan zoben shi da bai gani ba.

“Wancan ba mahboob bane? Kamar naso na wayi fuskarshi” Uncle abdalla ne yai
maganar,

Girgiza kai uncle ɗan Iya yayi Yayin da yake bin bayan mahboob dake ƙoƙarin karya
kwana zai nufi sashen ɗakinsa
“Shine, halan bai gaishe ka ba”?

Murmushi ɗauke akan fuskar Uncle Abdalla yace”Tun da muka zo ban yi tozali da shi
ba, sai dai naji labarin shi awurin junaid”

Cikin nuna 6acin rai Ɗan Iya yace”baida wayau ne ai ni bansan baizo ya gaishe ka
ba, bari ya fito daga ɗakin ɗan rainin wayau, Zahra tafi shi hankali”

Abie yace”Ƙuruciyace ke damunshi, Zahra kuma ae tafi shi shekaru baza a haɗata da
shi ba”
Ɗan Iya yace”babu wata ƙuruciya atare da shi, Sarai yasan me yake yi sai girman
jiki ba wayau” da alama Ranshi ya 6aci da rashin gaishe da uncle abdallah da baiyi
ba.

Kafin wani daga cikinsu ya ƙara yin magana Hajiya adama ta fito daga ɗaki
hannunta ɗauke da baby junaid, tun da ya dawo daga school a wurinta ya wuni ya
hanata sakat duk inda za ta je ƙafarta kafarshi toilet ne kaɗai yake bari ta shiga,
Ta canza Kayan jikinta zuwa atampa riga da skirt, Ta yafa mayafi akanta, kafin ta
ƙarasa shiga palourn Mamie ta fito daga ɗakin Ummi su biyu ganinta yasa suka nufi
wurinta fuskokin kowannansu da fara’a suka soma gaisawa da junansu

Atare suka ƙarasa shiga palourn, Kowa ya samu wuri ya zauna, Kafin suka fara
gaishe da Mazajensu, miƙa ma junaid hannu uncle abdallah yai”zonan kyakkyawan
Jikana mu gaisa,” da sauri Junaid ya sauko daga saman laps din Hajiya adama ya nufi
sofa ɗin da uncle abdalla yake azaune Ya haye saman jikinshi yana faman sakar mashi
murmushi, shafa fuskarshi yai da tafin hannunshi”Masha Allah mutumina, Ka tashi
lafiya? Fadamin meyasa baka je school ba yau? Sannan baka bi mu zuwa masallacin
Juma’a ba” Zaro ido Junaid yai haɗi da ɗan girgiza kanshi muryarshi da shagwa6e
yace”nafa je, ae yau da wuri ake tada mu duk ranar juma’a, kuma ni ai ban isa zuwa
masallaci ba inji mommy” maganarshi ba ƙaramin ƙayatar da su take yi ba, musamman
In ya haɗa da shagwa6a,

“Junaid kaji tsoron Allah, Aneelerh ce ta faɗa maka haka? Faɗamin gaskiya ka dai
san me ƙarya ɗan wuta ne” jin haka yasa shi saurin sanya tafukan hannayenshi biyu
ya toshe fuskarshi Yana tiƙar dariya” muryarshi ƙasa ƙasa ya furta”ba ita bane, ae
malaminmu ne yace mu ƙananu ne bamu isa ɗaukar zunubi ba” gaba ɗaya suka saki
dariya, bayan sun tsagaita da yin dariyar ne, Uncle ɗan Iya yai masu gyaran murya
hakan yasa suka dawo da dubansu gare shi.

“Dama yanzu nake shirin aikawa a kira mun ku, don mu haɗu duka muyi magana, Kafin
mu shiga cikin zancen Ina ƙara yiwa baƙinmu barka da zuwa fatan kun wayi gari
lafiya” da fara’a Hajiya adama ta amsa mashi a mutunce
Mami tace”tun ɗazu da safe take son yin magana mun fara sai nace ta bari idan kuka
dawo daga masallacin juma’a zaifi mu haɗu mu duka mu tattauna tunda abune daya
shafi kowannanmu da buƙatar aji shawara daga bakin kowa”

Jinjina kai Abie yai”hakane, Yanzu Ina aneelerhn take”?

“Tana a ɗakin zahra, Bari na shiga na kirata” kafin ta mike muryar junaid ta
katse mata hanzarinta.
“Ni zan Kirata” Bai jira amsarta ba, Ya sauko da gudu Ya nufi Ɗakinsu, uncle
abdallah ne ya ɗan ɗaga murya yana yi mashi faɗan ya daina gudu kada ya faɗi yaji
ciwo, Jin haka yasa shi dakatawa da yin gudun ya soma yin tafiya a tsanake

A lokacin Aneelerh da Zahra suna zaune saman gado kowa ya dafi waya suna fira suna
chatting, sun ɗauki wankan dogayen riguna
“Ba zaki leƙa wurin surukar taki ba? Kin barta a ɗaki ita kaɗai” acewar zahra
“Ɗazu da safe na shiga na gaishe ta, har ma na tarar da mami zaune suna tattaunawa
shiyasa ban tsaya ba,”
“Gaskiya aneelerh ki godewa Allah, surukarki tana da mutunci ta iya magana ga
faran faran da jama’a, Ni wlh ba ƙaramin burgeni take yi ba, Inasonta sosai, da ace
tana da wani ɗan Bayan Yaya uzair Allah dana aure shi” har cikin zuciyarta take yin
maganar,
Aneelerh na murmushi tace”Chief Owais din fa? Ko kin fasa”! farfari Zahra Tayi
mata da ido
“shi wannan na dabanne, idan ana maganar ƙarauƙarau ba a maganar Zinari, My dream
man inaji araina ma ya kusa dawowa ƙasar jiya har mafarkinsa nayi”
Murmushin gefen fuska Aneelerh ta saki
“Allah Ya cika maki burinki zahra, Ni na ƙosa inga fuskar Owais ɗin nan, har
tambayarki nayi hotonsa kinƙi ki nuna min, bansani ba ko rowa kike yi min” dariya
Zahra tayi”Ina jin fargabar zuciyarki ta buga silar ganin kyakkyawar fuskarshi,
kuma kinga ke matar aure ce bana son ki kalli haramun” Sakin baki aneelerh tayi
yayin da take kallonta, tama rasa bakin magana
“Fuskarshi tsadane da ita, idan har zaki Iya biyan farashi sai muyi ciniki in
nuna maki” fashewa da dariya aneeleeh tayi jin wani zancen abakin zahra.
Faɗowa Ɗakin Junaid yai tun abakin ƙofa yake faman ƙwala mata kira”Mommy!mommy!”
a hanzarce ta kai idonta ga ƙofar
“Babyn mommy lafiya kake ta ƙwalamun kira” tai maganar tare da sakowa daga saman
gadon ta nufe shi, hannu biyi tasa ta ɗauke shi tana kallon fuskarshi
“Mommy ana kiranki, ki zo inji su abie”
“Sune sukace ka kira ni”? Ɗaga mta kai yai alamar eh ya ƙara da cewa”ke kaɗai
banda Zahra”
Harara zahra Ta wurga mashi”aiko sai naje ɗan baƙin ciki, so kake kayi mun buƙulu
wata’ƙil ƙudi ne za’a raba mana,
Saukowa tai daga saman gadon ta ɗauko masu mayafi a closet ita da Aneelerh ta
yafa mata akanta, atare suka fuce daga ɗakin zuwa palour

Hankalin Mahboob Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin babu zoben a ɗaki, duk yabi ya
birkice ɗakin, ya tarwatsa komai, Hatta zanin gadon shi da fululluka duka yayi
wurgar dasu saman tiles, ya zazzago da jerin ninkakkun kayansa na cikin wardrobe
kaf dinsu Ya bazasu saman gadonshi, zufa ta ko’ina, Bawan Allah shine har ƙarkashin
gado neman zobe, Cikin drawer chest, da laundry basket, kanshi harya fara yi mashi
ciwo, ya tsani asara a rayuwarshi, a haukace ya tura ƙofar toilet dinsa ya shiga
ciki Yana neman zoben, gaba ɗaya ya fara zaucewa, ganin babu zoben a toilet ɗin ya
dawo ɗakin, yana haki zufa sai tsastsafo mashi take Yi, Idanuwanshi sunyi jawur
dasu luhu luhu yakai maƙura tamkar zai rushe da kuka, jiri ne ya fara ɗibarshi a
hanzarce ya koma gefen gadon shi ya zauna tare da sanya hannayenshi biyu ya tarbe
kanshi Takaicin duniya ya ishe shi, bakomai yake tunawa ba face kuɗin da Aka sayi
zoben, har zazza6i yai daya miƙa su dubu goma sha biyar. Ahakama kuɗin bada guminsa
ya same su ba, Abokin shi ne ya siya mashi zoben saboda ya nuna yana so kuma baida
kuɗi.
*Boss Bature✍️ Mu haɗu monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E16🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Kusan a tare Aneelerh da zahra su ka shigo palourn, a saman carpet kowan nan su yai
zaman cin tuwo Junaid na azaune gefenta, tun da su ka zauna idanuwan su Mami da
Abie na akan su, at same time suka haɗa baki wurin gaishe dasu cikin girmamawa,
fuskokinsu Uncle abdallah da fara’a suka amsa masu.

Bayan kowan nan su Ya natsu, Hajiya adama ta soma magana cikin nutsastsiyar murya
“Dama jiyane Aneelerh ta ke faɗamin dangane da tada zancen 6acewarsu tajuddeen da
za’ayi, a gaskiya naji daɗin jin hakan sosai, Kuma na yabama zahra da ta kawo
wannan shawarar ta yi tunani mai kyau” Tun da ta fara magana sun natsu suna
sauraronta, Zahra sai faman washe baki take yi jin anyabi shawararta, tana matuƙar
son taga An yabeta.

Bayan Hajiya adama ta ƙare magana Uncle abdallah Ya ɗaura da cewa”yanzu haka abun
da mu ke tattaunawa akai kenan, Ni kaina Naji daɗin tunanin nan da akayi abune mai
kyau da buƙatar atada zancen 6acewar su ya dawo sabo, wata’ƙil ta silar hakan Allah
ya agaza mana Muji ɗuriyarsu duk da bamu da tabbacin ko suna araye don ni har yau
bana ji araina cewa babu su a doron duniyar nan!”

Numfasawa Abie Yai Kafin ya ɗaura da nashi jawabin”In sha Allahu muna sa ran wannan
Karan zamuci nasara, dama dalilin taruwar mu anan don kowa Ya bada tashi shawarar”
Bayan Kammala Maganar abie, Uncle ɗan Iya Ya soma magana
“Na riga nayi magana da Ziyad babban ɗan jarida ne, Tun ranar da muka Yi magana
da Aneelerh, ta turo min hotunansu already na tura mashi su, da duk wasu bayanai da
za’a buƙata, Ya ce min in sha Allah cikin weekend da zamu shiga komai za’a fara
yaɗa labarinsu” Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu da alama sun ji daɗin Jin
hakan
Uncle abdalla yace”Wai kana Nufin Ziyad ɗan Gidan senate Lateef”?

Jinjina kai Uncle ɗan Iya yayi”ƙwarai kuwa, Ziyad yanzu ae shi ke jan Ragamar
Companynsu Na jarida mai suna Obinna News Network (ONT) Yaron Akwai hazaƙa Kullum
ne saina bibiyi Labaransu a shafinsu, ƙwararrune a 6angaren Aikin Jarida, duk wani
labari da zaiyi trending a social media Sune na farko da zasu fara buga shi a
shafinsu”

Uncle abdalla Yace”Allah sarki, Uzair Da tajuddeen Sunci burin yin Aiki a
companynsu, suna son Yin aiki tare da Ziyad Allah bai nufa ba” cikin karyayyiyar
Murya Uncle abdallah ya ƙarasa maganar, jikin kowan nan su Yai sanyi

“Nima a bakin uzair na ta6a jin labarin Ziyad ɗin nan shahararran ɗan Jarida, “
Acewar Hajiya adama

Uncle ɗan Iya na murmushi yace”Allah sarki, ae muna mutunci da Iyayensu, lokacin
da ace nasan suna da burin yin aiki da shi ai dana haɗasu, Yadda Taj da uzair suke
da hazaƙa a 6angaren Jarida tabbas da suna atare ba ƙaramin Cigaba za’a samu a
ƙasar nan ba, don shima Ziyad ɗin Akwai ƙwalwa Bashi da tsoro gaskiya tsirararta
yake faɗin ta” murmushi kowannan su Ya saki.

“Yakamata ka gayyato mana shi agidan nan, tunda kowa nasan ganin shi, Ko da ya ke
nasan zaiyi wuya ya iya samun lokacin zuwa sai dai mu muje inda Yake” Abie ne yai
maganar

“In dai ziyad ne baku da matsala, mutunne mai sauƙin kai, zan Gayyace zuwa gidan
nan”

Tun da suka fara magana sai Yanzu ummi tasa baki”kaga daga nan Idan Yazo sai mu
bashi auran zahra....” tunkan ta ƙarasa magana zahra dake chatting da wayarta A
sukwane ta ɗago Girarta a haɗe tana kallon fuskar mami.

Hakan da ta yi ba ƙaramin dariya ya basu ba, Uncle ɗan Iya yace”kin kawo shawara
mai kyau, Ni kaina nayi tunanin hakan don yaron akwai farin Jinin ƴan mata ita
kanta zahra nasan zata ƙyasa” Kifa kai zahra tayi saman cinyoyinta, takaicin Duniya
ya isheta, ita da ta ke da burin mallakar Uban gayyar family ɗin su kuma suna yi
mata zancen Ziyad.

“Akwai Kyauta ta musamman da zan ba Aneelerh, nasan Itama zata taimaka mana sosai”
Hajiya adama ce ta yi maganar idonta Akan uncle abdallah.

“Na baro ta a mota, jiya na manta ban shigo da ita gidan ba, Bari naje na ɗauko”
yai maganar yana yunƙurin miƙewa Sai ga Mahboob Kamar an wurgoshi Rai a6ace yake
Tafiya Fuskar shi a haɗe babu mutunci.

“Ka koma ka zauna Ga mahboob nan, ka bashi key ɗin motar ya ɗauko maka” Karaf
acikin kunnanshi Maganar ta sauka, Har ƙara sauri yake yi don yabar falon
Ɗaga murya Uncle ɗan Iya yai”Kai Mahboob zonan” Cak Ya tsaya da yin tafiyar
fuskarshi A murtuke ya Juyo Ya nufi inda suke zazzaune saman sofa.

Zuƙunnawa Yai ƙasa Ya ɗago da fuska Yana kallon Abie ɗin nasu

Rai a6ace yace dashi”Mahboob ba ka ga munyi baƙi bane a gidan namu”?


Hannu yasa ya ɗan sosa ƙeyarshi Muryarshi ƙasa ƙasa Ya furta

“Bana Jin ɗaɗi jiya shiyasa ban samu damar zuwa ganin su ba,”

Wani kallo Da Ummi ke wurga mashi daga inda take zaune saman Sofa kamar zata kifa
masa mari, Hakan yasa shi yin sauri kallon Uncle Abdallah Ya furta”sannunku da
zuwa, ya gajiyar tafiya, ya kuma aka baro mutanan can”

fuskar uncle abdalla asake ya amsa mashi”lafiyalou Mahboob, ya school ko an


kammala” fuskar shi ba yabo ba fallasa ya ce”diploma ce na kammala”

Ganin yanayin fuskarshi babu walwala Uncle abdalla yace “Ko dai har yanzu ba
lafiyane? Naga kamar baka acikin natsuwarka”

Sai lokacin Ya ɗan sakin murmushin yaƙe “Bakomai, ai naji sauƙi” Iya abunda ya
furta kenan, Baby Junaid ya tsareshi da ido, Dariya ce ƙumshe a cikin bakinshi don
ya fahimci damuwar rashin zoban shi ce ta sanya shi shiga wannan halin, Cikin kunne
yai ma Aneelerh raɗa”Mommy zoben yake nema, kalli idonshi ki gani sunyi jawur,
Allah bani bashi mommy sai ya zubar da hawayensa”

Ƙiris ya rage Aneelerh ta saki dariya yayin da take sauraron muryar junaid, ita
kanta ta lura da 6acin ran da ke akan fuskar Mahboob.

“zai baka Key ɗin mota, saƙo zaka ɗauko mashi” Fuska a ɗaure uncle ɗan Iya yai
mashi maganar, tare da kallon uncle Abdalla

“Bashi key ɗin motar,” acewar ɗan Iya, ciro key ɗin uncle abdallah yayi kafin ya
miƙa ma Mahboob, Ya sanya hannu biyu ya kar6a.

Yunƙurawa yai ya miƙe ya fuce daga ɗakin yana ƙunƙuni.

Kafin dawowar Mahboob Junaid Ya miƙe da sauri Ya nufi ɗakin Mommyn shi don Ya duba
zoben da su ka 6oye.

Yana shiga ɗakin Ringing wayar Aneelerh Ya daki dodon kunnan shi, Da sauri ya nufi
wayar dake Ajiye saman pillow Ya haye gadon ya janyo ta.
Jikinshi har kerma yake yi wurin yin Picking call ɗin ya kara wayar a kunnanshi.

Da ƙarfi Ya furta”Wanene”? Shiru ba”a tanka masa ba.

Hakan baisa ya fasa yin maganar shi ba

“Mommy bata nan tana a palour suna magana da su Abie, I’m the only one in the
room.” still ba’a tanka mashi ba, Surutu Yaci gaba da Yi

“Angel ce ke kira”? Shiru ba amsa”Sister Angel, say something! It’s your brother,
Baby Junaid. I miss you so much”

Da shagwa6a ya yi maganar, Sai lokacin Muryar mutumin da ya kira a wayar ta bayyana


da sauti mai matuƙar Ratsa zuciya.

“Where is the owner of the phone?” ta6e baki Junaid yai”ai na faɗa maka tana a
palour”
“Okey ina son yin magana da ita, ko zaka Iya kai mata wayar” Tuntsirewa Junaid
Yai da dariya yana faɗin”a’a Sai dai ka yi magana dani, sai in faɗa mata”
“Pls ka kai mata wayar, “ maƙe kafaɗa Junaid Yai kamar yana agabanshi”ni dai a’a,
Ka faɗamin sai in faɗa mata saƙon”
“Shekarunka nawa”? Ga dukkan alamu wanda ya kira wayar ya fahimci ƙaramin yaron
ne ya ɗaga tun daga kan voice ɗinsa.

“Huɗu Biyar shidda” Sautin dariyar mutumince ta ratsa kunnan junaid.

“No wonder ashe babban mutun ne kai, zamu iya zama abokai” maƙe kafaɗa junaid
yai”to aini yarone kai kuma babba”.
“Okey yanzu faɗamin Ina yayarka Angel”? Kwa6e fuska junaid yai cikin muryar
shagwa6a yace”ta 6ace 6era ya cinyeta ita da daddynta da daddyna sun mutu nima
mommyna ta faɗa min” sosai mutumin Ya fashe da dariya, jin wautar Junaid

“Ka hana Ni Yin magana da mommynka, gashi kanata cinye min kati”
“Ae nace ka faɗamin saƙon sai In gaya mata” mutumin yace”Okey, ka faɗa mata
DADDYN UNAISAH NE ya Kira”!

“To zan faɗa mata Sai anjima” Yana kai ƙarshen magana Yai rejecting call ɗin
tunkafin mutumin yai mashi sallama, Pillow Ya janyo ya zuge zip ɗin Ya curo ring
box ɗin Yana Kallon zoben
“Na Angel ne wannan, Bazan bashi ba Allah tun da ya cinye min chocolate ɗina”
Yana magana yana ta6e la66ansa.

Shigowa Mahboob Yai cikin palourn Hannun shi ruƙe da Kyautar wani abu Mai faɗi an
rufe shi da wrap sheet mai Ƙyalƙyali, Karasowa Yai agaban sofas din da Uncle
Abdallah Yake zaune Ya sauke gift ɗin kafin ya miƙa mashi key ɗin motar, Kar6a
Uncle Abdalla yai”nagode sannu da ƙoƙari” muryarshi ƙasa ƙasa Ya amsa da”yawwa”
Juyawa yai da sauri Ya nufi Sashen kitchen ganin Ana na zarya kai abinci a dining.

Tunkafin a buɗe Kyautar kowa Ya ƙagara da son ganinta, musamman zahra ta ƙura
idanuwanta kamar na mazuru.
Ummi na murmushi tace”masha Allah wannan kyauta tunkafin abuɗe mun fara zumuɗin
ganinta” Mami tace”ni kaina a ƙagare nake Allah”
A hankali Uncle Abdallah Yake warware wrapping sheet ɗin, slowly Kyawawan
idanuwanta dara dara suka Fara Bayyana, da mamaki su ke Kallon juna cikin rashin
fahimtar wacece wannan Kyakkyawar Matashiyar.

Lokacin da ya warwaro wrapping sheet ɗin dai dai Saitin hancinta ya ƙarasa
6an6are ledar gaba ɗayanta, adai dai time ɗin Mahboob da Ana sun fito daga kitchen
Hannun shi ruƙe da glass Na lemu Karaf Idanuwanshi suka sauka akan Hoton zanan
fuskar Angel, Nan take ya saki glass ɗin hannunshi gaba ɗaya ya tarwatse ruwan
lemun dake acikinsa ya tsiyaye saman tiles.

Tsabar Al’ajabi da mamakine Yasa Aneelerh da mami Yunƙurawa a sukwane suka miƙe
tsaye Suna ƙare ma Zanan Kallo Yasha fenti kamar horonta aka ɗauka.

Gaba ɗaya sun Rasa bakin magana, zanan yayi bala’en Yin kyau, fuskar Angel ta
fito raɗau Kyakkyawar matashiyar balarabiya bugu da ƙari buzuwa a 6angaren
Mahaifinta” Zahra Ko sai faman Yarfa hannu take yi tana ambaton Wow wow
Tabarakallahu ahsanul khalikin! Gaskiya koma wanene portrait artist ɗin da ya zana
hoton nan ba ƙaramin ƙwararre bane ya baje basira”

Ummi tace”Masha Allah, Yarinyar ba ƙaramar kyakkyawa bace, kamar tajuddeen Ya yi


kakinta, Kamanninta sak Kalar nashi, Hasken fatarne ta ɗauko Na mahaifiyarta
benazir”

Lamarin ya ɗaurewa Ana kai Ganin yadda Mahboob Ya fasa glass cup ko ajikin shi,
Hankalin sam baya atare dashi, Zanan Fuskar Angel Ya tafi da Imaninsa, dama can tun
fil azal Mahboob Mayen mata ne.
“Mahboob Meke damunka ne? Baka ga 6arnar da ka yi ba ne’?

Ba tare da ya kalli fuskar Ana ba Ya furta”dama akwai matan Hurul aini A duniya”?

Girgiza kai Ana ta yi Fuskarta ɗauke da murmushi ta nufi dinning, don ta jera
kayan tray din hannunta.

Farin Ciki Ya hana Aneeleeh furta kalma, agaban zanan da ke a jingine jikin
hannun sofa, ta zuƙunna saman gwiwowinta, yatsun hannayenta na kerma ta ɗaura su
saman fuskar Angel, Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka ta kifa kanta saman
zanan

“Haba Aneelerh menene abun kuka? Ke da za ki yi farin Ciki”? Mami ce tayi maganar

Hajiya adama ta miƙe ta nufi Aneelerh ta ɗan ranƙwafa ta ɗaura hannunta saman
kafaɗarta.

“Share hawayen ki Aneelerh, banaso pls, Ni ban Kawo maki zanan nan don ki yi kuka
ba, saboda farin Cikin ki yasa Nasa aka yi min shi, nasan zaki ji daɗi sosai” Abie
yace”in dai ko bazaki daina kukan nan ba, zansa su koma da zanan” sai lokacin ta
ɗago da rinannun idanuwanta da suka kaɗa jawur ta kalli fuskokinsu cikin shessheƙar
kuka tace”Nadaina, wlh kukan farin cikine Ya kubce min, Inason Angel sosai, na kasa
jurewa ne, da na ga zanan nan sai naji na ƙara ƙagara da son ganinta a shekarunta
Na yanzu” Mayar da idanuwanta ta yi a kan hoton

“Allah sarki my Angel, ɗiyata ƙanwata kuma ƙawata abokiyar firana, Na yi missing
ɗinki sosai bazan ta6a mantawa dake ba har abada” Kifa kanta tayi saman hoton
Hawaye suka cigaba da wanke fuskarta, ta yi matuƙar karya masu zuciya.

*Middle step A gidan Alhaji ubaid*

Tun lokacin da Dr. shureim Ya kammala kimtsawa ya zauna gefen gadon shi ya natsu
yana kallon hotunan abar ƙaunarsa, Ƙarfe Goma sha Biyu Na bugawa, Kiran Alhaji musa
Ya shigo wayarsa.

Da sauri Yai picking call ɗin Ya kara a kunnanshi

“Shureim Ina Jiran ka a palour!”

Abun da Ya furta mashi kenan, Ajiyar zuciya ya sauke Tare da miƙewa Ya fito daga
Bedroom ɗinsa, Yana mai jin kewar ɗakin nashi, tafiya yake yi tamkar bayason Taka
ƙasa, Ji yake kamar In yabar gidan zai ƙara nisanta kanshi da ita ne, duk irin
yadda yake zumuɗin barin gidan hakan bai hana wani sashe na zuciyarshi ƙin amince
masa ba, Saboda acikin gidan ne, abar ƙaunarsa ta kafa tarihi acikin zuciyarshi.

Lokacin da ya ƙaraso palourn, A zaune ya samu Alhaji musa da Uncle ubaid, Sai
Mahaifiyarshi laila Da Mai aikin gidansu zainab, Hannunta ruƙe da shopping bag.

Yanayin fuskokin su Ya nuna alamun rashin jin daɗin tafiyar shi, musamman mai
aikin gidansu zainab da kuma Mahaifiyarshi Layla, tana a tsaye ta ruƙe qugu
fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin zallar 6acin raine.

Shi ko Alhaji ubaid sai faman sakin fara’a ya ke yi babu alamun zaiyi kewar ɗan
nashi idan ya tafi.

Idanuwan dr. Shureim akan na mahaifiyarsa, da sauri ya nufi inda take atsaye,
hannu biyu ta sanya ta rungumo shi a ƙirjinta, hakan da tayi mashine yasa shi jin
hawaye sun cicciko idanuwanshi.

Bubbuga bayanshi take yi a hankali tana faɗin”Shureim ɗina, zanyi missing ɗinka
sosai, naji takaicin tafiyar nan duk da ba wani wuri zakaje me nisa ba, sai dai sam
hankalina bai kwanta da tafiyarka ba, Naci burin In gatantaka In baka kulawa ta
musamman tuntuni, sai dai rashin zamanka agida da kuma gudunmu da ka ke yi, shi
yasa ban samu damar yin hakan ba, Yanzu kuma na samu na shawo kanka, an nuna anfini
iko da kai za’a rabani da kai,’ tun da ta fara magana Alhaji musa Ya haɗe rai
fuskarshi a tamke ba annuri, don yasan dashi take magana.

“Mommy ki samin albarka ita nake buƙata daga gare ki, Sannan ki kwantar da
hankalinki, Ni musulmine kuma nayi imani da Allah dashi na dogara, aduk inda zan
kasance Allah yana atare dani, ballanta kuma agidan Uncle ɗina ne ba nisa zanyi ba,
nasan za ku dinga zuwa akai akai kuna ganina, Nima kuma zan dinga zuwa gida”
Maganar Dr. shureim ta yi matuƙar karya mata zuciya, Allah na gani tana son ɗanta
sosai, Muryar Alhaji musa ce ta katse su”shureim bamu da isashen lokaci, ka wuce mu
tafi”

Ɗagowa Yai daga jikin mahaifiyarshi ido cikin ido suke kallon Juna, Canza harshe
ta yi zuwa larabci kafin taci gaba da magana

“Shurem hankalina bai kwanta da kawunka ba, Ni ban yarda dashi ba, Bai ta6a nuna
damuwa akanka ba, tun lokacin da ƙaddarar nan ta risƙe ka har ka fara shaye shaye a
ƙarshe ma kabar ƙasar gaba ɗaya, musa bai ta6a bibiyar rayuwarka ba, babu ruwanshi
dakai Ƴa’ƴanshi kaɗai Ya sani, Ta ya ya hankalina zai kwanta da zuwan ka gidan shi?
Allah kaɗai yasan mugun nufin shi akan ka” Tana magana tana shafa sumar kanshi da
ta sauko saman wuyanshi, babu wanda Yasan me ta ke cewa, dama da biyu ta yi mashi
maganar da larabci don saboda tasan basa Jin Yaren, mai aikinsu kaɗaice ta ke ji
saboda itama balarabiyace, jikin zainab duk yai sanyi da jin maganar Hajiya layla,
baiwar Allah duk ta damu da Shureim gani ta ke yi kamar idan ya tafi wani abu zai
faru dashi.

Muryarshi araunace Ya soma magana da harshen larabci”Mommy kidaina wannan tunanin


dan Allah bana so, ki kwantar da hankalin ki, Uncle musa bazai Ta6a cutar dani ba,
duk da bai damu dani ba a lokacin baya, yanzu ya nuna yana ƙaunata zai Iya yiwuwa
ko dan saboda tausayin halin da nake aciki ne, Nafi so ki yi mashi kyakkyawan zato
mommy”

Gyaɗa kai ta yi “Shikenan shureim zan cigaba da yi maka addu’a akan Allah ya kare
mun kai ya tsaremun kai daga sharrin duk wani abun cutarwa” Cikin harshen labaraci
ta dinga jero addu’o’i tana tottafa masa Yana amsawa da ameen.

Bayan ta kammala ya ɗago da ido Ya kalli zainab, idanuwanta sun cicciko tab da
kwalla.

Matsawa ya yi kusa da ita, fuskarshi ɗauke da murmushi yace”auntyna zan tafi


asanyamin albarka” yai maganar tare da duƙar da kanshi, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi
mata ba, Ƴan hawayen da ta ke matsewa tuni sun soma shararowa saman kuncinta.

Tafin hannunta ta ɗaura saman arab turban ɗin dake naɗe akanshi, a tsanake take
jero addu’o’i tana tottofa masa a ƙarshe ta ƙara da cewa”Allah yasa Silar komawarka
can ka samu farin Ciki na har abada” Ya amsa mata da ameen ameen”Allah ya saukeku
lafiya shureim” ya ƙara amsa mata da ameen

Daga Haka Ya juya ya nufi Mahaifinshi Alhaji Ubaid.

Fuskarshi ɗauke da murmushi yake duban shureim”daddyna, asanya min albarka”

Da buɗar bakin Alhaji ubaid sai cewa yai “Shureim sai ka ce zaka Bar ƙasar, irin
wannan bankwana haka! Na lura Jikinka duk Yai sanyi, Ko kamanta Abuja ne zaka je
gidan ƙanina”? Harara Hajiya layla ta jefa ma Alhaji ubaid a fakaice.

“Lokacin da ka ke ƴan guje gujenka ba tare da sanin kowa ba, Ka ke barin ƙasar
nan sai yau don zaka tafi gidan uncle ɗinka kake Neman albarkarmu”?

Da mamaki akan fuskar Dr Shureim ya ke kallon Alhaji ubaid, Ran Hajiya layla ya
6aci A harzuƙe tace”Dan Allah Ya isa haka! Me yakawo wannan maganar? Saboda kawai
yace ka sanya mashi albarka? Idan baza ka sanya mashi ba sai ka ƙyale shi Ya tafi,
dama albarkar uwa aka fi buƙata, bata uba ba”

Runtse ido shureim Yai, Maganar daddynsa ta ta6a mashi zuciyarshi tuni ƙwalla sun
Ciko idonshi, Hatta zainab ta ji ɗacin maganar Alhaji ubaid ji take kamar ta
kikkifa mashi maruka a kuncinsa.

Still da murmushi akan fuskar Alhaji ubaid ya ke dubanta, kafin ya maida


dubanshi ga shureim.

“Ka ji abunda Mommynka tace, babu buƙatar albarka ta, Don haka zaka Iya tafiya”
cikin jin ƙunar rai Yace”daddy na roƙe ka, Ka sanya min albarka ina buƙatar taka”!
hawaye tuni sun wanke fuskarshi, Jinjina kai Alhaji Ubaid Yai, Kafin Ya janyo Dr
shureim Ya rungume shi, Yana tofa mashi albarka, Hankalin shi ba ƙaramin kwanciya
ya yi ba.

Miƙewa Alhaji musa yai daga saman sofa ɗin da ya ke azaune, ko kallo basu ishe shi
ba, Cikin takun nan nashi na izza, ya juya ya fuce daga falon don shi arayuwarshi
Ya tsani 6ata lokaci.

Tsoki Hajiya layla taja aranta tace”abanza, Uban Ji da kai, ai ni da za ka


burgeni, ka kama Hanya ka yi tafiyarka, kabarmin ɗana”

Ruƙo Hannun dr shureim Alhaji ubaid Yai, Yaja shi suka nufi Hanyar fita falon,
Da sauri Zainab Tabi su Hajiya layla kam zama tayi dirshan saman sofa tana faman
cije le6e.

Abakin Engry hall na gidan, Zungureriyar motar da zata ɗauki Alhaji musa zuwa
airport tayi parking, Hamshaƙiyar gaske Ƴar ubansu mota mai numfashi.

Yana daga kishingiɗe a ɗaya daga cikin back seat na motar, tamkar yana acikin
bedroon ɗinsa saboda tsabar haɗuwarta, slowly murfin motar ke zugewa Dr shureim na
ƙoƙarin shiga ciki, Muryar Zainab ta katse masa hanzarinsa.

“Namanta da wannan, kai na haɗamawa” juyowa yai tare da kallonta, Ledar hannunta ta
miƙa masa, fuskar shi ɗauke da murmushi ya kar6a Yana yi mata godiya, kafin daga
bisani yayi masu sallama, yasa kai cikin motar, daddaɗan Sanyin a.c ya ra6i sassan
jikinsa shi kanshi Ya yi al’ajabin haɗuwar motar.

Mutun Biyune agaban motar, Driver ɗinsa da kuma p.a ɗinsa wani gabjejen mutun mai
ƙirar Ƙarfi daga gani yana gym saboda ko’ina na jikinsa a murɗe Yake, wankan suit
ne a jikinsa Baƙi wulik baida fara’a a fuska.

Kaitsaye Airport Suka nufa, already An shirya mashi privet jet dinsa, Bayan
shigarsu cikin jirgin wanda Tsayawa zayyana Haɗuwarshi 6ata lokaci ne, abune da
hankali bazai ɗauka ba, saboda an kashe dukiya kamar ba asan zafin nemanta ba, Kai
kace saman bishiya ake tsinko kuɗin ana amfani da su. (😂)

Dr. shureim Yaga aljannar duniya, Bayan tashin jirgin Cikin mintuna da basu wuci
arba’in ba Suka ƙaraso Airport ɗin Abuja, Tun kafin jet ɗinsa ya ƙaraso airport ɗin
tuni Escords ɗinsa sun hallara abakin motocin su cikin shiga ta baƙaƙen suits domin
tarbarsu da kuma basu tsaro.

*EX-PRISONERS❤*

Tun Bayan da suka kammala Cin abinci kowan nan su yai kulu wash rabu hani’an, Nurse
ta shigo ɗakin ta kwashe kayan abincin da suka ci ta fuce da su waje.

Gaba ɗayansu suna A saman gadon zazzaune Sai Yanzu su ka samu damar ƙarewa ɗakin
kallo.

“Angel menene wancan”? Parveen ce ta yi maganar tana nuna mata plasma tv dake
manne a jikin bango.

“Tv ce da ita ake yin kallo”


“To ki kunna mana mu gani mu ma” girgiza kai Angel ta yi”a’a Parveen ku bari sai
munje gidan daddyna tukunna”

ta faɗi hakanne don tasan muddin ta kunna masu kallo zasu birkice mata ne, a ƙarshe
ay abun kunya, tun da basu ta6a gani ba.

Tambayoyi suka dinga jera mata kamar ƴan jarida, komai na ɗakin sai sun tambayeta
menene shi ya akeyin amfani da shi, ita kanta ba komai ta sani ba saboda ba kalar
ɗakinsu na gida bane, Iya abunda ta sani take amsa masu.

“Zan shigo toilet” Batul ce ta yi maganar, saukowa ta yi daga saman gadon ta


nufi ƙofar da take tunanin ta toilet ce ta tura da hannu ta shiga, tun da ta shiga
take bin ko’ina da kallo sauƙin ma toilet ɗin su na prison na zamani ne, da ko anga
ƙauyanci sai dai da banbanci sosai, don wannan akwai sink da bathtub hada shower ga
mirror da sauran Kayan amfani.

Agaban madubi Batul ta tsaya tana kallon fuskarta, bata ta6a ganin Kyanta irin na
yau ba yatsun hannunta ta tura cikin Curly hair ɗinta tana cakuɗa shi.

Acan bedroom ɗin Bayan shigarta toilet, zuciya da saƙe saƙe Angel sai ta dinga
ayyanawa aranta ga Batul can ta kunna Ruwan zafi amaimakon na sanyi” Jiki Na rawa
ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, ko neman excuse babu ta shigo toilet
din kamar an jeho ta.

Jin motsin shigowar mutun yasa Batul Juyowa a firgice don ganin wanene. Kusan atare
suka sauke Ajiyar zuciya

“Dama ba wani abu za ki yi a toilet ɗin ba”?


Murmushi Batul ta sakar mata”Inaso ne in ƙare ma ko’ina kallo,”

“In dai wannan ne kada ki damu zan yi maku bayanin komai, amma Yanzu ki fito mu
koma ɗaki” Amsa mata ta yi da toh ta juya ta nufi Angel ta ruƙo hannunta suka fito,
shugowarsu ɗakin ke da Wuya Aka buɗe ƙofar, Dr Daniel brown ne tare da Nurse
rebecca.

Fuskokinsu ɗauke da murmushi, cikin harshen turanci ya soma yi mata magana.

‘Masoyiya Angel da ƴa’ƴanta, fatan na same ku Lafiya” Amsa mashi sukayi da


lafiyalou
“Ya jikin naku? Ko akwai inda ke yi maku ciwo “? Atare suka girgiza mashi kai

“Okey, Starting tomorrow, you’ll be receiving injections for three days, and
you’ll also be taking regular medication to improve your health.” cikin kulawa dr
brown ke yi masu magana idonshi akan fuskar Angel.
Murmushi ta sakar mashi”mun gode sosai da kulawarku agare mu, Allah ne kaɗai zai
Iya biyanku”

“Kada ki damu, aikin mu ne, Ko akwai wani abu da kuke buƙata”?

Cikin raɗa Batul ta yi ma Angel magana a kunne”muna son ganin Haris da Danish”

“Doctor, can we see our brothers?” kamar mai jin shakkar shi ta yi maganar.

Jinjina mata kai Yai alamar eh, Kafin ya ɗaura idonsa akan Nurse rebecca” Ki kai su
ɗakin Ƴan uwansu”
“Okey sir” Mayar da idonshi yai kan Angel” pls muna so ki samu natsuwa sosai, ki
kwantar da hankalinki dana ƴan uwanki, akwai magana da zamuyi dake tare da sojojin
da suke ceci Rayuwarku, sunce da zarar kin farka a sanar da su, Ni kuma na bari sai
zuwa gobe idan kin ƙara wartsake wa duk da naga jikin naki da ƙwari”

shiru Angel ta yi tana faman zazzare mashi gray eyes ɗinta aranta ta ayyana
komai suke son sani? fatanta Allah ya bata ikon amsa masu tambayoyin da zasu Yi
mata

“Haɗin kanki mu ke buƙata Masoyiya Angel” murmushin yaƙe ta sakar mashi wanda bai
kai zuci ba.

Bayan fitar shi daga ɗakin, Nurse ta kalli faces ɗinsu”zamu Iya tafiya” A
hanzarce suka sassauko daga saman gadon suka bi bayanta, tun da suka fito daga
ɗakin gabansu ke faɗuwa ganin haɗaɗɗen wurin da suka tsinci kansu a cikinsa,
Asibitin Har ya gaji da haɗuwa, babu tazara a tsakanin ɗakunansu da inda aka
kwantar da su Haris duk acikin amenity ward ne.

Abakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Haris suka tsaya, sai da nurse ɗin ta fara
tura ƙofar ta shiga tukunna Ɗaya bayan ɗaya su ka soma shiga cikin ɗakin cike da
zumuɗin son ganin ɗan uwansu, tun kan su ƙarasa suka hango Haris kwance magashiyan
saman medical bed an sanya mashi robar oxygen a hancin sa.

Da sauri suka ƙarasa gaban gadonshi, gida biyu suka raba kansu, gefen dama
Gabriel ne da Javed sai Naufal da Parveen ta 6angaren hagu Angel ce da Batul,
Jamimah da azeeza sai Hannah, tsananin tausayin Haris ne Ya kamasu, tuni idanuwansu
sun cicciko tab da ƙwalla.

Cikin shessheƙar kuka Angel ta ambaci sunansa”Haris!” har cikin dodon kunnanshi
Kiran Ya isar mashi, sambatu ya soma yi masu Yana ambaton sunan Deeja yana faɗin”mu
koma ku ɗauko ta, Deeja na tana araye suna can suna azabtar min da ita, dan Allah
ku taimakamin ku cece rayuwata ku ɗauko min deeja na” tuni Hawaye sun wanke
fuskokinsu, Hatta nurse rebecce Dake atsaye jikinta yai sanyi ganin hawayen su, Duk
da bata iya jin abunda ɗan uwan nasu ke cewa

“Haris”! Muryar Angel ce ta ƙara ratsa kunnan su, A hankali Ya soma ƙoƙarin buɗe
idanuwansa da suka kumbura jawur ya ɗaura su akan fuskarta, Ware su yai sosai,
Ganin Yana ƙoƙarin miƙewa yasa Nurse ɗin Yin saurin matsawa bakin gadon ta rankwafa
ta zame mashi roban oxygen din daga hancinsa, ta taimaka mashi Ya miƙe zaune Bayan
ta sanya mashi pillow a tsakankanin bayan shi da headboard na gadon.

Sun natsu suna kallon shi, azabar ciwo tasa shi canza kamanni, fatarshi ta yi
haske Ya rame sosai, hakan ba ƙaramin Kyau ya fiddo mashi ba, sumar kan shi a
cukurkuɗe kamar mahaukaci sabon kamu, ɗaya bayan ɗaya ya ke binsu da kallo Yana
ambaton sunansu da raunatacciyar muryarsa
“Angel, Batul, Azeeza, Jamimah, Hannah, Javed, Naufal, Gabriel..” Numfashi Yaja
Kafin ya furta sunan Deeja”Ya akai banganta ba? Ina aka kaimin deejana? Baku zo da
ita ba”? Idanuwanshi acike tab da hawaye yai masu maganar

Cikin sanyin murya Angel tace”Haris pls ka daina sanya damuwa aranka, dubi kaga
yadda ka rame, tamkar ba Haris ɗin mu ba, duk kabi ka zauce, Why pls? Bama Jin
daɗin canzawar da ka yi, gashi baka da ƙoshin lafiya”

daƙyar sautin muryarshi ke fita”Bazan Iya jurewa bane Angel, inason deejana ina jin
tsoron ace narasa ta, donni inaji araina tana araye tun da har su azeeza basu mutu
ba, Itama sumane tayi”

“Haris idan har baka kwantar da hankalin ba, Ta ya ya zamu Iya samun ƙwarin
gwiwar fallasa asirin masu kurkukun ƙaddarar har muci nasarar ɗauko sauran ƴan
uwanmu da suke acan idan basu mutu ba? Dole fa sai ka bamu haɗin kai ka danne
damuwar dake aranka tukunna zamu Iya Cin galaba akan su”! Angel ce ke yi mashi
magana cikin kwantar da murya

Gabriel ya ɗaura da cewa”Kin faɗi gaskiya Angel, Haris pls ka taimaka ma kanka
muma kuma ka taimake mu sannan ka taimaki rayuwar su Deeja Rashin lafiyarka shi zai
tarwatsa mana shirin mu, Nurse ta faɗamin abunda ke damun ka, Ciwon zuciyane Haris
kuma nasan bakomai ne ya jawo hakan ba face Deeja!! kaga yanzu mun ku6uta daga Daji
muna acikin mutanan duniya, Nan inda muke asibiti ne Inda ake duba marasa Lafiya
sune suka bincika lafiyarka kuma suka tabbatar mana da cewa damuwace ta silar wani
abu daka ƙwallafa rai akan son shi, pls Haris Ka taimaka mana! Idan har ba ka ji
sauƙi ba Likitocin nan bazasu ta6a bari mu koma Nigeria ba gidan daddyn Angel”
tunda Gabriel Ya fara magana Haris Yake bin ɗakin da suke da kallo, sai lokacin Ya
gane ba adaji suke ba, shifa gaba ɗaya baya acikin hayyacinsa baisan ma a ina yake
ba, idanuwanshi sun makance.

Azeeza sarkin tausayi tun da ta tsareshi da ido, Hawaye ke bin fuskarta.


Cikin shessheƙar kuka tace”Dan Allah haris ka yi haƙuri, In sha Allah deejan mu
bata mutu ba da sauran ƴan uwanmu Zamuje mu ɗauko su”

Batul tace”kwanciyar hankalinka kawai muke buƙata Haris, idan ba haka ba kaga
zaka mutune kafin muyi nasarar dawo da su deeja, me kake tsammani idan Ka mutu muka
gano deeja araye ya za ta ji? Ka mutu saboda ita? Kaima ka sani yadda take ƙaunarka
itama mutuwa zatayi tabi ka”

lumshe idanuwanshi yai, ƴan uwanshi ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba, sai
kwantar mashi da hankali suke yi duk don su samu ya wartsake

“Ina ɗan uwana”? yai tambayar yana kallom faces dinsu


“Danish bai farka ba Haris Har yanzu, bacci yake yi, “ Angel ce ta bashi amsa,
damuwace ƙarara akan fuskarshi
“Angel wani irin bacci ne wannan Har yanzu bai farka ba? Ina jin tsoro wani abu
yasame shi” girgiza kai Angel tayi”a’a Hairs ba abunda zai same shi, Ni inaji
araina Lafiyar danish qalou, Bacci ne kawai ya ke yi kasan ya ɗauki tsawon lokaci
bai runtsa ba shiyasa bai farka ba”

Gyaɗa kai yai”Allah yasa hakane,”


. “Haris ka ci abinci ko kana jin yunwa”? Kallon parveen yai”bana Jin yunwa
parveen, Naji daɗin kulawarku agare ni, sannan Ina tayamu murnar barin kurkukun
ƙaddara” murmushi kowan nan su Ya saki, shima ya ƙalalo murmushi akan fuskarshi

Muryar Jemimah da shagwa6a tace”Idan ka ji sauƙi, zamu ga deeja ma har kuci


abinci atare da ita, kana bata abaki itama tana baka abaki, agidan daddyn genie
ɗita” gaba ɗayansu suka sanya dariya, Nurse rebecca dake tsaye tuni ta zauna saman
chair tana dubansu sam bata gajiya da kallon Yaran burgeta suke Yi kamar ta sace su
take ji.
Haris Ya ji daɗin maganar Jemimah har saida yaɗan murmusa
“Sannan Haris zai dinga wanke ma deeja gashin kanta yana sharce mata shi,” Batul
ce tayi maganar, tsabar daɗin maganarta har saida fararen haƙoransa suka bayyana.

“Bayan haka zai dinga goyata a saman bayanshi Suna yawo” acewar Hannah sosai
Haris ya fashe da dariya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri akan fuskarsa,
Lamarin ya ɗaurewa rebecca kai, mamakinta yadda yaran suke matuƙar ƙaunar junansu,
wani abu da ya ƙara burgeta yadda suke ta sanya shi dariya tabbas su ka ɗai suke
Iya sarrafa junansu.

“In sha Allah Haris our dream will come true” lumshe idanuwanshi yai tare da
buɗe su akan fuskokinsu sai ya dinga ganin tamkar Deejar sa ce zaune a tsakiyar
gadon tana sakar mashi murmushi, hakan yasashi sakin murmushi kamar wani zautacce

“Haris ka kwanta ka huta, kada mu cika ka da surutu, zamuje ɗakin Danish mu duba
shi”

“Nima inaso naganshi Angel, muje atare”

Kallon Nurse ɗin tayi”pls sister zamu Iya tafiya da shi ɗakin ɗan uwanmu”?
Smilling gently, nurse rebecca tace”badamuwa, zamu Iya tafiya da shi” ta yi
maganar tare da miƙewa Ta nufi gaban gadon, da taimakonta Haris ya sauko daga saman
gadon tace mashi ya dafa shoulder ɗinta don ya samu damar yin tafiya, Rurruƙeta yai
da hannayenshi a haka suke Yin tafiyar, Su Angel suna abayansu har suka ƙaraso
ɗakin da aka kwantar da garkuwa, Jikin Angel har 6ari yake yi saboda tsabar zumuɗi,
tun kafin su ƙarasa shiga ɗakin suka hango Danish Baje saman gadon, kamar matacce,
lallausar sumar kanshi ta tarwatse saman mattress ɗin gadon, da sauri Angel ta nufi
gadon Ta haye daga gefe Idonta akan Kyakkyawar fuskarshi, Har kullum kamar ana ƙara
ninka mashi kyawunshi, fatarshi tayi smooth fara sol Ko tabo babu, Sun canza mashi
uniform ɗinshi wanda ke a jikin sa Yanzu kalar nasu ne Riga da wando light blue,
rigar tayi tighting ɗinsa, gajeran hannu ne da ita Hakan ya bayyana ƙaƙƙarfan
Damtsen hannun shi, Likitoci sun sha wahala wurin canza mashi kayan Jikinshi saida
suka haɗa ƙarfi tukunna su ka samu damar raba shi da su.

A hankali take bin Shi da kallon so da ƙauna tun daga saman sumar kanshi har i
zuwa kan Long eye lashes ɗinsa, dogon hancin nan nashi yayi sam6al babu lanƙwasa,
full lips ɗinsa sun ciza launinsu, slowly ta sauke idonta akan Zanan tattoo dake a
gefen dogon wuyanshi Yayi bala’in yi mashi kyau
A gefe da gefen gadonshi kowannansu Ya samu wuri ya zauna hada haris da nurse ta
zaunar dashi, natsuwa su ka yi a yayin da su ke kallon ɗan uwansu, daɗi kamar zai
kashe su
Angel ta shagala da kallonsa ji ta ke kamar ta faɗa saman chest ɗinsa ta ƙanƙame
shi ko ta samu sassaucin kewarsa da ta ke yi, Muryar Haris ce ta fargar da ita.

“Angel zuciyarshi tana bugawa”?

A hanzarce ta kwantar da kunnanta saman chest ɗinsa saitin heart ɗinsa nan take
taji bugun zuciyarshi na harbawa a tsanake
Ɗagowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace dasu”zuciyarshi tana bugawa, bacci ne
yake yi”

Jin haka yasa Kowan nan su Ya matsa kusa da shi, ɗaya bayan ɗaya suke ɗaura
kunnuwansu saitin zuciyarshi, nurse rebecca dake a tsaye murmushine ɗauke akan
fuskarta

hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, jin zuciyarshi na bugawa

“Sai yaushe zai farka? Baccin yayi yawa” Javed ne yai maganar, Naufal yace”may be
saiya ɗauki adadin kwanakin da yayi bai runtsa ba tukunna zai farka” zaro ido Angel
tayi haɗi da girgiza kanta”in sha Allah ba zai kai wannan lokacin ba zai farka.

Ta ƙare maganar tare da ruƙo zira ziran yatsun hannun Danish na dama acikin nata,
sosai ta runtse su (nima kuma na runtse alƙalamina)

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E17🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

A ƙalla sun shafe kusan 30 minutes a ɗakin Danish, Ji suke kamar abarsu su kwanta
a ɗaki ɗaya saboda haka su ka saba kwana a kurkuku, daga bisani Nurse tace dasu
zasu tafi zuwa gobe zasu Iya zuwa su ƙara duba shi’ jiki asanyaye suka miƙe suna
tafiya suna waiwayon shi musamman Angel ji ta ke yi kamar ta koma ta rungume shi.

Bayan fitar su daga ɗakin, Nurse Ta raka kowan nan su room da aka kwantar da shi,
ba su so aka raba su ba, har yanzu tsoron mutanan su ke ji, ba dan Angel ta lalla6a
su ba da ko babu inda zasu je, a ɗakinta zasu kwana, musamman Azeeza da jemimah
ɗaƙyar Angel ta lallashesu ta lalla6asu don ta fahimci dokar asibitin ce haka ba’a
haɗa mutun fiye da ɗaya a ɗaki, wata’ƙil sai idan ya kama dole, sauƙin ma kowan nan
su akwai nurse ɗaya da ke kula da ɗakin shi, duk wani abu da zasu buƙata zasu yi
masu, hatta toilet suna raka mutun In ya buƙaci hakan musamman gasu da basu san
yadda zasuyi amfani da wasu abubuwan ba.

A daren ranar sun yi kwanan farin ciki basu da wata damuwa.


*Daular Alhaji Musa wadata*

idan nace zan tsaya zayyana maku zunzurutun Kayan alatun da ke a gidan Alhaji musa
daga ni har ku zamu koma Yin Mafarkinsa ne, wato Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce,
Katafaren Villa ne Wanda Idan ka zura ƙafarka acikinsa tamkar ka Bar Nigeria ka
shiga Dubai ne, Aljannar duniyace ƴar ubansu, A ƙalla security din dake tsaron
Kafcecen Gate ɗin shiga gidan sunkai su goma shabiyar, Wasu gabza gabzan Garada
Masu Ƙirar sadaukan Yaƙi, Babu wasa akan fuskokin su, Bana tunanin ko aljani zai
Iya gifta gate din gidan salin alin ba tare da sun cafke shi ba, Shantalelen titi
ne zai sadaka da Cikin gidan kai tsaye daga bakin babban gate ɗin, yadda kasan da
zallar goal aka ƙera ginin saboda ɗaukar idon gilassan Ƙofofin da Windows, ko gidan
shugaban ƙasa albarka, Babu ce kaɗai ke babu agidan Alhaji musa, komai na gidanshi
babu made in Nigeria, an zabga almubazzarancin dollar wurin ƙera ginin, don hatta
sample dinsa da ƙwararrun da suka ginasa kaf aikin turawa ne.

Mamaki da al’ajabin dukiyar Uncle din nasa Ya hana shi Kwantar da hankalinsa, Tun
Bayan da escords suka ɗauko su daga airport, Motocin suka shigo gidan gabanshi ke
ta faɗuwa, saboda sabon gini ne baya a ƙasar Uncle ɗin nasa Ya mallake shi, shiyasa
komai yake ɗaure masa kai, Kafin shigarsu gidan Saida shureim Ya dinga jero
addu’o’i acikin zuciyarshi Yana neman tsari akan Allah ya kare shi daga shagalar
duniya, Idan har zaman shi gidan ba alkhairi bane, Ya roƙi Allah da ya yi mashi
silar barin shi cikin sauƙi ba tare daya sha Wahala ba.

Tun da suka shiga gidan Kamar wani baƙauye Haka ya dinga bin ko’ina da kallo, wasu
matsiyatan Chandeliers saman ceilling Masu ƙyalƙyali tamkar zasu rubzowa mutun
saman kanshi, Ga wasu Haɗaɗɗun twins stairs, masu ɗauke da Glass Elevator a
gefensu. Idan ka shiga cikinta Kana iya hangen mutanan dake zarya a palourn Yayin
da take Yin sama dakai ko take dawowa dakai ƙasa.

A katafaren Palourn gidan kuwa Wasu Jigunannun Royal Sofas set ne Ƴan ubansu masu
numfashi Ga Arm chairs kalar Na sarakuna, A gefe da gefen kujerun Sofa table ne,
Tiles din palourn baida banbanci da Mirrored tiles Kana kallon Fuskarka acikinsa
Idan kana Tafiya, zallar haɗuwa, An zuba komai na more rayuwa, Idan nace zan tsaya
zayyana haɗuwar Komai dake acikin Gidan Tabbas zamu ƙare middle step da last step
acikin gidan Alhaji musa (🤣)

Babu wanda Yasan da zuwansu, Hatta Iyalinsa Ba su san da dawowar shi a yau ba, yana
ɗaya daga Cikin Halayan Alhaji musa, Idan zai yi tafiya babu wanda ke sani Matar
shi ko ƴa’ƴanshi, Haka zalika Idan Zai dawo sai dai su ganshi, saboda zuwan ba zata
Ya ke yi masu.

A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta ƙudundune kanta
acikinsa, daga gaban dardumar Qur’anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon
gaba da ita a yayin da take Yin karatun al’ƙur ani mai girma.

“Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin
ta ɗago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare ƙal
launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji
musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya ɗare na
mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde
har saman fore head ɗinta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da
ƙaramin baki launin pink, Ba ta da ƙiba ko misƙala zarratin siririya ce, abu ɗayane
ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon.

“Zeenat! Bacci ki ke Yi”? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta


zabura ta miƙe tare da wurga ƙwayar idanuwanta kan Mai shigowa ɗakin, babbar macace
mai cikar kamala, Ta ɗauki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan
fuskarta, baturiyace Siririya bata da ƙiba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar
budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah
Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta ɗaure kanta da kallabi, hakan bai 6oye
doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace ɗin wuyanta da earrings
ɗinta na zallar diamond ne sai ƙyalƙyali suke Yi da ɗaukar ido.

Muryarta Adisashe ta amsa mata”mommy karatun ƙur’ani nike Yi bacci ya ɗauke ni


bansani ba” ta yi maganar tana Yin miƙa haɗi da yin hamma

“Ba ki ji dirar motoci ba ne”? Ras Taji gabanta Ya faɗi, Muryarta na rawa ta
furta”dad... daddy is he back “?

Ta6e baki Hajiya Sarah tayi”ya dawo tun ɗazu, yanzu haka yana a ɗakinsa, yace baya
son takura, kinsan halinsa”

Hankalin Zeenat Ba ƙaramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko
baƙin Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda
rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so
da ƙauna.

Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa”ya naga
kamar baki farin Ciki da dawowarshi”? A hanzare ta girgiza kai” “I’m so happy he’s
back, na yi murna ai shi ɗinne baya son takura”

Murmushi tasakar mata”Albishirinki”!


Da mamaki ta tsayar da eye balls ɗinta kan face din momyn nata
“Goro”!
“Fari ko ja”
“Fari”
Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin raɗa ta furta mata”Ba shi kaɗai ya dawo ba,
Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom ɗin da aka ware masa” Tun
kafin Hajiya sarah ta ƙarasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da ɗaura
goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta

“Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada” ɗagowa Zeenat
Tayi, tare da miƙewa tsaye Hijab ɗin jikinta sai Ja da ƙasa Yake yi.

“Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa” tsantsar
farin cikine akan fuskarta

“No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai
ki je ki kai mashi a ɗakinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci
hausawa”

Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta ƙagara don a kwaɗaice take da
son ganinsa
“Na faɗa maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya
dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko ɗan gyalene ki yafa a kafaɗa,” turo
baki zeenat tayi da ƴar shagwa6a tace”Mommy ae shima Yaya shureim ɗin yafi son mace
mai sanya dogon hijabi”

“To ai bance bayaso ba, tun da acikin gidane ki samu gyale ki yafa” ta ƙare
maganar da zolaya ta furta”Muslimatun matar limam” Dariya Zeenat ta sanya tana
kallon mommyn nata.

“Zan koma kitchen, Ki tabbatar kin shirya da wuri”

Amasa mata tayi da toh


Bayan fitarta, da sauri Zeenat ta cire hijab ɗin jikinta, ta nufi toilet ta
shige, cikin Ƴan mintuna ta fito Sanye da bathrobe (rigar wanka) fara Ƙyal a
jikinta, hannunta ruƙe da short towel tana tsane sumar kanta, Bayan ta kammala
tsane gashin, a gaban tafkeken dressing mirror ta zauna saman chair tana Gyara
Jikinta, Hair dryer ta kunna Ta busar da sumar kanta, Bayan ta gama ta soma shafa
tsadaddun Mayukan shafawarta dake a jere gaban madubin.

Zeenatu muguwar sangartacciyace ta saba tun tana ƴar ƙarama duk In za ta yi make up
ko zata sanya sutura masu aikin gidansu ne ke taimaka mata, saboda ba ta Iya komai
na aikin wahala ba, hatta sanya ɗan kunne bata Iyaba wahala take sha, Yau saboda
zumuɗin zuwan ya ya shureim bata bari wani ya taimaka mata wurin sanya sutura ba,
tun tana agaban mirror mai aiki ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta ta nemi zinin shigowa,
ta tambayeta Ko tana Buƙatar wani abu, tace mata a’a taje kawai za ta yi komai da
kanta, ashe da rabon tasha wahala.

Gaba ɗaya saida ta faffasa kayan kwalliyar gaban mirror, bata da natsuwa ko
misƙila zarratin tana da rawar kai da zumuɗi, tun daga kan Hoda da ta ɗauko zata
shafa, Ta sil6e daga hannunta gaba ɗaya ta tarwatse a saman tiles, garin hodar ya
zube, Ta kuma janyo janbaki a tsiyace take murza ma la66anta nan take ya gutsire
guntulan Ya faɗi ƙasa ta jefar da shi, duk kwalbar turaren data ɗauka sai ya sil6e
ƙasa Ya daki tiles kwalbar ta fashe ruwan Ciki Ya tsiyaye, hakan bai dame ta ba,
don ta yi asararsu.

Bayan Ta kammala ƴan shafe shafenta, bata bi takan kayan da ta faffasa ba,
tsallake su ta yi ta nufi tafkekiyar glass wardrobe ɗinta, daga wajen glass ɗin
kana Iya ganin jerin suturar sanyawarta ashaƙe tamkar a company, Abayas, shadda
atampa leshi, material, english wears, Pakistans, ga jerin Kayan baccinta, komai fa
anzuba mata su, shalelen daddy musa

Da hannu ta zuge glass wardrobe ɗin, Ta ƙura ido tana tunanin suturar da zata
sanya don ta burge Yayanta shureim, idanuwanta ne su ka sauka akan haɗaɗɗiyar
atampa, yatsun hannunta na kerma ta cafko ta, tana kiciniyar ciro atamfar ai ko
gaba ɗayan jerin Kayan da ke a gidan tsakiya suka zazzago saman tiles, ko ajikinta,
saida ta 6arar da kayan wardrobe ɗin wurin neman sutura ɗaya kacal da zata sanya a
jikinta, Ga abu a fili ta ɗauka tasa shine bazata Iya ba, tafi so saita haukata
komai na ɗakin tukunna a ƙarshe tabar masu aiki da wahalar gyara mata su.

Tamkar zata fashe da kuka, ruwan ido Ya hanata ɗaukar Kayan da zata sanya don ta
burge Yayanta.

“Assalamu alaikum” Muryar ɗaya daga Cikin masu aikin gidan ce babbar mace wadda
suke Kira da Tani.

Da sauri Zeenat ta juyo tana kallonta,


“Yawwa Tani, shigo ciki ki taimaka min narasa wasu Kaya zasu dace dani, Inaso ne
na burge yaya shureim”

Baki asake Tani take bin ɗakin da kallo, Sam ba ta yi mamakin ganin yadda Zeenatu
ta faffasa Kayan Kwalliyarta da turarurrukanta ba, Halinta ne yin 6arna kamar 6era.

“Haba zeenat, Dubi yadda kika zazzago da ninkakkun Kayan Cikin wardrobe ɗinki
ƙasa, sannan kinbi kayan kwalliyarki da kwalaban turare duk kin faffasa su why pls?
Harfa larai na turo donta taimaka maki ki shirya a tsanake amma sai ki ka ce mata
ta tafi za ki yi da kanki, yanzu kin kyauta abun da ki ka yi”? Cikin kwantar da
murya take Yi mata magana.

Zumbura mata Baki Zeenat tayi”Nifa bana son faɗa, Idan ma na faffasa su ai daddy
zai canza min wasu, kuma ai bada gangan nayi ba ko”
Girgiza kai Lami tayi haɗi da sakin murmushin takaici “Oh, Saboda kinsan daddynki
zai siya maki wasu shiyasa kika faffasa su? Ke Baki damu da asarar dukiyar da
za’ayi ba kenan”?

Bubbuga ƙafafuwa Zeenatu tayi fuskarta a tur6une tace”Ni ki daina Yi min faɗa,
Nace maki ba laifina bane kuma in sha Allah zan gyara, pls ki taimaka min In gyara
komai kada mommy tazo taga ban shirya ba”

Gyaɗa kai Tani tayi”ai dole kam in tayaki gyarawa, idan ba haka ba hada ni zata
shafa”

Ƙarasa shiga ɗakin Tani tayi, cikin ƙanƙanin Lokaci ta ɗauko Parker ta tattara
Kayan kwalliyar da zeenatu ta faffasa ta zubar a trash can na ɗakin, Ta koma bakin
wadrobe din ta soma ninke mata kayan da ta zubar a kasa ta jera mata su a cikin
wardrobe, duk tana a tsaye ta ruƙe qugu tana kallon tani.

Wani haɗaɗɗan Cord lace ta ɗauko mata Red colour anyi mashi adon flower yellow.

“Zeenat wannan zaiyi maki kyau sosai, Red and yellow, kalar farare ce sannan kuma
kyawawa irinki”

Washe fararen Haƙoranta tayi Jiki na rawa ta sanya hannu ta kar6i kayan da Tani ta
miƙo mata, Sai da Tani ta taimaka mata wurin ɗaura zani da ɗaura ɗan kwali don ba
ta iya ba, masha Allah Lace ɗin Yayi bala’en Yi mata kyau.

“Bari na ɗauko maki Takalman da zaki sanya” Tani ta yi maganar tare da nufar Shoe
rack din ɗakin, Inda jerin takalman Zeenatu suke na gayu masu tsini da flat, ta
ɗauko mata yellow kalar head ɗinta.

Ta dawo ta ajiye mata su agabanta, ta koma ta ɗauko Jewelry box dinta, ta ɗauko
mata sarƙar diamond da earrings, Bayan ta kammala sanya mata su, sai da ta gyara
mata make up ɗin fuskarta.

Ita kanta Tani Kyawun Zeenatu ya tafi da imaninta, Inaga wanda Akayi adon domin
shi.

“Kinyi kyau sosai shalelen daddy musa, Muje kitchen ɗin in shirya maki dinner
dinsa ki kai mashi”

Ta amsa mata da “Toh”

Daƙyar take yin tafiya da high hills din ƙafarta, Bawai don bata saba sanya
takalmi mai tsini ba, sai don rashin natsuwarta.

Bedroom ɗinta a second floor Yake, Ƙa’ida ne idan zata sauko down stairs sai dai
Ta hau elevator saboda a wurinta wahala ne taka bene.
Atare da Tani suka Hau elevator ɗin ta sauko dasu down, da kwarkwasa take yin
tafiya tana taka tiles sautin na bada kwas kwas kwakwas.

Kaitsaye kitchen suka nufa, tun daga Cikin Katafaren palourn gidan kana Iya hangen
Masu aikin dake safa da marwa acikin kitchen, a tsakiyar falon ta dakata da yin
tafiya.

Tani tace “Bari na ɗauko maki Kayan abincin” ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta
nufi kitchen, badajimawa ta fito hannun ta ruƙe da wooden tray faffaɗan gaske, daga
saman shi wasu haɗaɗɗun Warmers ne da flatware da sauran kayan abinci”

“Anya kuwa zeenatu zaki Iya ruƙe tray din nan? Naji da nauyi, ko dai In raka ƙi
ɗakin nashi”?
Girgiza mata Kai tayi”a’a Zan Iya ki bani kawai” miƙa mata tray din tani tayi,
Ta rurruƙe shi da hannu Biyu, tana tafiya tana rangwaɗa, Tani dake a tsaye ta
ƙurawa bayanta ido, ita tasan daƙyar zata Iya kai shi ɗakin ba tare da ta 6arar
dashi ba.

Ɗakin da aka warema Dr shureim a gidan baida banbanci dana sarki saboda luxury
furniture dake a cikinsa, sam ta manta ba ta tambayi Tani a wani room ya sauka ba,
sai faman wurwurga eye balls ɗinta take yi a ƙoƙarinta nata gano masaukinsa, Cikin
sa’a ta hango ɗaya daga cikin ɗakunan dake a rufe ƙofar shi ta buɗe hakan na nufin
anan aka saukar da shi.

A lokacin Yana a kwance saman katafaren gadon ɗakin, Ya cire Jallabiyar jikinsa,
Iya short ne fari, ya zame arab turban din kansa, Kwantacciyar sumar kanshi baƙa
wulik, ya sanya singlet tabi shape ɗin ƙirjinsa.

Bacci ne ya ɗauke shi gefen shi wayarshi ce ajiye yana cikin kallon hotunan abar
ƙaunarsa bacci yai awon gaba da shi.

“Yaya shureim ɗina” Muryar Zeenatu ce ke ƙwala mashi kira, tun kafin ta ƙarasa
bedroom ɗin.

“Ya ya shureim am coming” kasancewar tana da zaƙin murya mai tsiwa har cikin
kunnanshi yake jin muryarta.

“Yaya shureim” firgigit! ya farka daga baccin haɗi da miƙewa zaune la66ansa na
ambaton sunan Allah, idanuwanshi har sun canza launi saboda bacci.

ɗakin Yabi da kallo a ƙoƙarin shi na ya gano ta inda zata 6ullo, sautin takun
tafiyarta ne Yaja hankalin shi ga kallon ƙofar ɗakin.

Daƙyar ta ke tafiya, sai faman zabga murmushi take yi akan fuskarta, tun da ta
shigo ɗaki ta tsayar da blue eyes ɗinta akan fuskarshi, da ƙarfi ta furta hubby na”
kamar a mafarki shureim ke kallon zeenatu, kamar yau ya fara ganinta sam ya kasa
motsawa daga zaunan da yake saman gadon.

Ganin yadda take yin tafiya babu natsuwa yasa shi yin saurin furta”bari nazo na
taimaka maki” maimakon ta dakata da yin tafiyar tun da yace zai taimaka mata, sai
ma ta ƙara saurin tafiyar da take yi, a hanzarce dr shureim ya haura ƙafafuwanshi
ya sauko daga saman gadon sai dai kafin yai saurin zuwa gareta, Cikin rashin sa’a
takalmin ƙafarta ya karkace ai ko Gaba ɗaya Ta saki tray ɗin hannunta Ya kife saman
tiles kayan abincin ciki duk suka tarwatse, Nan take zanin da aka ɗaura mata Ya
warware Ya zame ƙasa, Daga Ita sai ɗan pant ɗinta.

Runtse ido dr shureim yai, ba arziƙi ya dakata da yin tafiyar.

Jikinta sai kerma yake yi, Kunya duk ta isheta muryarta na rawa ta soma
magana”wayyo Allah na, Am sorry yaya shureim wlh duk zumuɗin ganinka ne bansan ya
akai zanin ya warware ba, gashi na zubda maka kayan abincin” ta yi maganar tana
faman yarfa hannayenta, Kunyar duniya ta ishe shi

“Yaya shureim bari na koma Tani ta gyara min ɗaurin zanin, yanzu zan dawo maka da
wani abincin tun da wannan Ya 6are” saboda tsabar ruɗu Anan tabar mashi zanin da
kallabinta da ya warware, da takalmanta, da gudu ta juya ta fuce daga ɗakin

A hankali dr shurem ya buɗe idanuwanshi Yana kallon 6arnar da Zeenatu tayi mashi,
rashin natsuwar yarinyar ba ƙaramin burge shi yake yi ba, Saboda yana samun nishaɗi
sosai, tsabar shiririta ita da tace za taje a gyara mata zani ta tafi tabar zanan a
ƙasa.

Yaushe rabon da ya yi dariya irinta yau harya manta, Hada dafe cikinsa tun da
zeenatu tabar ɗakin bata ƙara dawowa ba saboda Kunya gare ta, kamar ba jinsin turai
ba, Tani ce tazo ɗakin ta bashi hakuri game da 6arnar da zeenatu tayi mashi yace
mata bakomai ai yarinyace yana yi mata uziri, Bayan tani ta kwashe kayan da ta
6arar mashi, Ta koma kitchen ta canzo mashi wani abincin ta dawo ta kawo mashi,
kafin Tani tabar ɗakin sai da ta tattara kayan zeenatu da ta bar masa zaninta da
ɗan kwalinta da takalman duka ta kwashe ta fuce da su, dr shureim yaso ta dawo suyi
fira sai dai yasan abune mai wuya ta bari su ƙara haɗuwa yau sai dai zuwa gobe idan
kunyar ta sake ta.

*PRISONERS MIDDLE STEP💋❤*

Ƙarfe 7 na safe agogan San antonio ta buga, adai dai lokacin Sojojin sun zo duba
marasa lafiyansu daga headquater, mutun uku ne Commender, Major, tare da Captain
sun zo cikin shigarsu ta kaki, A office ɗin dr. Laura davis suka fara zama domin
tattaunawa.

A6angare Angel tana ƙudundune cikin bargo tasha baccinta, sai mutsu mutsu take
yi duk ta yamutsa bedsheet ɗin ga dukkan alamu mafarki take Yi, A firgice tafarka
Haɗi da yakice bargon ta wurgar da shi gefe ɗaya, hannayenta biyu saman fuskarta,
cikin shaƙaƙƙar murya take ambaton sunan Danish, Mummuna mafarki tayi akanshi Ya
farka Ya rikiɗa ya zama dodo Yana shan Jinin mutane, Hankalinta duk yabi ya tashi
haiƙam gani take kamar mafarkinta zai iya zama gaskiya.

Ta yi zurfi acikin tunaninta muryar Nurse ta Fargar da ita


“Barka da safiya Masoyiya Angel, fatan kin wuni Lafiya” da sauri ta ɗaura idonta
kan fuskar nurse ɗin

In a cool voice ta amsa mata Lafiyalou

“How are you feeling today? Are you experiencing any pain?” girgiza kai Angel
tayi”A’a”
“Okey, nasan zaki buƙaci shiga toilet, ki gyara fuskarki, akwai sojoji da suka
zo suna son ganawa dake, Amma kafin nan Zan kawo maki breakfast ɗinki ko kina da
za6i na abunda kike son ci”?

Girgiza kai Angel tayi”a’a”


Okey daga haka Nurse ɗin ta juya ta fuce, Saukowa tayi daga saman gadon abakin
ƙofar shiga toilet ta zura slippers dake ajiye saman carpet, kafin ta tura door din
ta shige ciki.

A hankali take tafiya tana bin ko’ina na toilet ɗin da kallo A tsaftace yake
fari ƙyal Kamar ba’a ta6a amfani da kayan Cikinsa ba.

Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da


murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples ɗinta biyu suka lotsa, yatsun
Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta
ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba ƙaramin kyau za su yi ba,
fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke
fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha’awar son Yin alwala, nan take ta canza
ra’ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na
daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet ɗin
tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? Buɗe ƙofar da akayine
yasa ta ɗago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ruƙe da tray na
kayan breakfast ɗin Angel asaman table ta ɗaura mata shi.

Ɗagowa tayi suka hada ido da juna”Is there anything you need?”
Da sauri tace”Hijabi da abun sallah inaso zanyi”
Da murmushi akan fuskar nurse ɗin tace”are u muslim”? Ɗaga mata kai Angel ta yi
alamar eh, nurse ɗin tace”Okey, ki jira ni yanzu zan dawo”

Fuce wa tayi daga ɗakin, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙare ma ɗakin kallo,
shigowa nurse ɗin tayi hannunta ruƙe da hijab da Prayer mat ta miƙa mata, Farin
Ciki a wurin Allah bakinta yaƙi rufuwa.
“Thank u so much” nurse ɗin na murmushi tace da ita”never mind” ita kanta batasan
Ina ne alƙibla ba, sai da ta tambayi nurse ɗin tayi amfani da wayar hannunta wurin
yi mata bincike ta gano mata Alƙiblar da zata fuskanta tukunna ta shimfiɗa carpet
ɗin, a tsanake ta kabbara sallah, saman chair nurse din ta zauna tana jiranta,
Raka’a Biyu Angel tayi kafin ta sallame sallar, wani irin daɗi take ji yau tayi
sallah, bakinta yaƙi rufuwa, tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tana karanto
addu’o’ kirari tafara yi ma Allah kafin tayi ma ƴan uwanta da suka rasu addu’a, da
su kansu a ƙarshe ta roƙi Allah akan Ya haɗa ta da ƴan uwanta ba tare da ta sha
wahala ba, Allah yasa daddynta Yana araye, da auntynta Aneelerh. bayan ta kammala
Yin addu’ar, Ta shafa a fuska, ta yunƙura ta mike, ta nannaɗe prayer mat ɗin da
hijabin ta dubi nurse ɗin

“Kin gama” ɗaga mata kai Angel tayi alamar eh, Miƙewa tayi tare da zuwa gaban
angel ta kar6i carpet din da hijabin juyawa tayi ta nufi closet ɗin ɗakin ta buɗe
ta sanyasu aciki.

“Aduk lokacin da kika buƙaci yin ibadarki zaki iya ɗauka ki yi” godiya Angel tayi
mata, daga bisani ta zauna zaman Cin breakfast, lafiyayyan kalaci aka haɗa mata,
tana ci tana tunane tunane sam tamanta da sojojin dake jiranta.

Sai da ta kamalla cin abincin ta ƙoshi, Nurse ɗin ta tattara komai ta fuce dashi,
Zama tayi gefen gadon idonta akan ceilling ta ƙurawa haɗaɗɗen kwan ɗakin ido, Yayin
da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru.

Ba zato ba tsammani ta tsinkayi muryoyinsu a yayin da suke shigowa ɗakin, A


hanzarce ta miƙe tana faman zazzare gray eyes ɗinta akansu, sojojinne tare da
likitocin, saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna a jere suna fuskarta, Dr Laura
davis ta zauna gefenta, Kamar wata mara gaskiya duk ta kama kanta, Hankalinta ba
ƙaramin tashi yai ba.

“Masoyiya Allah fatan Kin wayi gari lafiya? Ya jikin naki” muryarta adabarbarce
tace”da sauƙi sosai” cikin kulawa suke Yi mata magana da harshen turanci

Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana”mun nemi jin bayani daga bakin ɗan
uwanki Gabriel sai dai bai bamu haɗin kai ba, Yace duk abunda muke son sani ke ce
zaki amsa mana.

Jin wannan maganar yasa hankalinta ƙara ɗugunzuma.

Fahimtar yanayin ta ne yasa dr mark cewa” Ki kwantar da hankalin ki, Bamu zo da


niyar mu takura maki ba, Ƴan tambayoyi ne zamuyi maki da zarar kin amsa mana zamu
tafi, munfiso ki natsu kiyi nazari kafin ki amsa mana”

“Kin shirya”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, duk tabi tasha jinin jikinta.
“Da farko zamu so ki fada mana Ya akai kuka tsinci kanku A daji? Waye ya kai ku
can? Sojojin kasar mu suna hasashen ɗan Ta’addan daya gudu zuwa canne Yai garkuwa
daku don ya kare kanshi daga farmaki da suka kai mashi, shin dagaske ne ko kuwa?
Ƙura masu ido ta yi ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu, tsabar fargaba ƴan
hanjin cikinta sai kaɗawa suke Yi, Tarasa Tayaya zata fara basu amsar tambayarsu?
sam ba ta jin zata Iya faɗa masu ainihin Abunda Ya faru da rayuwarsu, ita aganinta
kamar idan suka ji zasu guje su ne, musamman idan Danish Ya farka a matsayin giant
ba ƙaramar masifa zaija masu ba, Zaiyi wuya su yarda da abunda zata faɗa masu,
saboda Labarin baƙar izayar da suka sha a prison ba kowane zai gasgata kalamanta
ba, zama su Iya tunanin ƙarya take yi masu, bayan haka tana tsoron ta fada masu, su
kuma su tara Ƴan jarida su sanar dasu a ɗauki hotunansu ayi share da labarin prison
tabbas yin hakan zai jaza masu babbar matsalar da zata Iya ja su rasa rayukansu don
tasan dole Shuwagabannin kurkukun ƙaddara su bibiyi rayuwarsu ko dan saboda abu
biyun nan na farko Garkuwar kurkukun da su ka gudu da shi, Na biyu don kada su tona
masu asiri.

duk da sanyin A.c dake ratsa fatar jikinta hakan bai hanata zubar da zufa ba, ta
ko’ina take tsastsafo mata, Hakan ba ƙaramin ɗaure masu kai yai ba, farat ɗaya suka
fahimci akwai wani gagarumin al’amari atattare da yarinyar sai dai zaiyi wuya ta
iya sanar da su gaskitar zance.

Gyaran murya Commender yai mata, A hargitse ta wurga eye balls ɗinta akan
fuskarshi

“Kin yi shiru baki ce komai ba meyasa”?

Dafa kafaɗarta dr laura tayi da hannu ɗaya”Ki kwantar da hankalin ki my daughter,


Ki natsu ki bamu amsa, a shirye mu ke da mu taimaki yaruwarku, haɗin kanki kaɗai
muke buƙata, kuma muna tabbacin zaki Amsa mana tambayoyin mu”

gaba ɗaya ta ruɗe saboda saƙe saƙen da zuciyarta ke yi mata, wani sashe Yana jan
kunnanta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata faɗa masu abunda ya faru a
rayuwarsu, Yayin da wani sashe na zuciyarta ke Jan hankalinta akan ta faɗa masu
wata’ƙil su taimaka masu wurin kawo ƙarshen Azzaluman kurkukun ƙaddara, Yanzu idan
ta 6oye masu taƙi faɗa masu gaskiya kwatsam wani abin da ba’a fata ya zo ya same su
har su rasa rayukansu shikenan tarihin kurkukun ƙaddara zai cigaba da wanzuwa ne.

Sun tasata gaba kamar sun sami tv, duk sun ƙagara da su ji amsarta, gashi taƙi
buɗe baki tayi magana.

“Idan har baki bamu amsar tambayoyinmu ba, zamu maida ku Dajin da muka ɗauko
ku”! Acewar Major

Ras Taji gabanta ya faɗi, Lokaci ɗaya ta fashe masu da matsanancin kuka mai ratsa
zuciya Cikin shessheƙar kuka take faɗin”Ni bansan komai ba, Bazan Iya tunawa ba,
Namanta komai, ɗan uwana danish shi ya sani”

Ta ƙara rikita masu lissafi, Captain yace”kun haɗa baki ne? Mun tambayi ɗan
uwanki Gabriel ya faɗa mana cewa ke kaɗaice kika san komai, Yanzu kuma mun
tambayeki kince kema bakisan komai ba A tambayi Danish! Why kuke son Yi mana yawo
da hankali....? Da alama Ya Hasala ne dan muryarshi a kausashe yake mata magana.

Da sauri dr laura ta katse shi”Sir, bata da ƙoshin Lafiya, Ni a ganina bai kamata
mu tsareta da tambayoyi ba a yanzu, ƙaramar yarinya ce sai ana lalla6ata”

Sassauta fushin fuskarshi Yai, Cikin kwantar da murya yaci gaba da cewa”Okey,
Share hawayenki, ki daina yi mana kuka bama so” Muryarta Na rawa ta amsa mashi da
toh.

Miƙewa Dr laura ta yi ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauko mata fanta me sanyi, ta


haɗo mata da tissue, Ta dawo gefen gadon ta zauna tare da miƙe mata tissue ɗin,
Hannayenta na kerma ta kar6a ta soma goge ƙwallarta da hancinta, Bayan ta gama
share hawayen dr laura ta miƙa mata lemun kar6a tayi tare da yi mata godiya.

kamar tasan Mayyar fanta ce, Buɗe wa tayi agaban su ta kur6i ruwan lemun kusan sau
uku tana sha, Sun tsareta da ido suna kallonta, hakan ba ƙaramin rikitar da ita
yake yi ba.

“Pls Masoyiya Angel, Ki taimake mu ki taimaki rayuwarki da ta sauran ƴan uwanki,


Ki faɗa mana gaskiyar abunda Ya faru a rayuwarku wanda yai silar haifar maku da
ciwon damuwa, Idan har baso kikeyi mu maida ku daji ba” acewar Captain.

“Abunda mukeson sani shine Ya akai kuka tsinci kanku a ƙurmin dajin Evil forest?
saboda ɗan ta’addan ƙasarmu da muke hasashen shine Ya kai ku can mun titsaye shi
akan ya faɗa mana menene alaƙar shi da ku, Ya faɗa mana cewa Baisan komai dangane
da ku ba, Ya taimaki wasu daga Cikin ƴan uwanku ne, Munyi dogon nazari akanku, da
farko munyi tunani ƴan ƙasarmu ne ku, sai kuma muka ji kuna magana da wani harshe
wanda bana nahiyarmu ba! Mun rasa gane daga wani Jinsi ku ke? sannan menene
maƙasudin haddasa maku ciwon damuwa da baƙin ciki? lamarin ya ɗaure mana kai da
ƙananun shekarunku? hada me fama da ciwon zuciya! Wani abun al’ajabin ɗaya daga
cikin Ƴan uwanku yaƙi farkawa daga bacci mun rasa gane meke damun shi......” tun da
major ya soma yi mata magana a tsanake ta tsare shi da ido tana kallon la66ansa har
ya ƙare maganarsa, tukunna ta fara magana
“Gaskiya ne abunda ɗan ta’addan ya faɗi, bashi ne yakaimu daji ba, Mun jima Acan
kusan zance tun kafin mu mallaki Hankalin mu, bazan Iya tuna abunda Ya faru
arayuwar mu ba, kome yakai mu Dajin, abunda na sani shine Munci baƙar wahalar
rayuwa dani da ƴan uwana, wanda silar hakan yajaza mana depression....”
Kallon Juna su ka yi, still sun fahimci bazata faɗa masu abunda suke son ji ba,
sam bata son su sani babu alamun zata yarda da su.

Murmushin gefen fuska Major ya sakar mata”Ni dama tunda naga idanuwanki da
ƙaramin bakin nan Naki raina ya bani kina da wayau sosai,” duƙar da idonta ƙasa Ta
yi zuciyarta na bugun uku uku.

Dr. Laura sam ba ta so suka matsa mata da tambayoyi ba, tuntuni ta basu shawarar
su bari Yaran su saba da su tukunna amma da yake Sojoji ne Yana ɗaya daga cikin
Halayansu, Idan suna son jin bayani daga bakin mutun ba wani uziri da suke Yi mashi
dolenshi ya amsa masu.

“Yaren da ku ke yin magana da shi na wace ƙasa ne”? Captain ne Ya jefa mata
tambayar.

Muryarta na ɗan rawa ta furta”Ni.. geria” Tsabar mamaki ne yasa su kallon Juna.

“Kina nufin daga Nigeria ku ke? Tayaya hakan zai yiwu? Dama Nigeria suna da farar
fata ne acikin su? a iya sanina baƙar fatane mutanan Nigeria, Sannan matansu kuma
basu da dogon gashi, kuma Launin idonki Kalar na mutanan ƙasarmu ne”
Dr. Mark jockson ne Yai maganar da alamun mamaki akan face ɗinsa
Dr. Laura na murmushi ta dube sa”kada ka bani kunya mana, ko mu a ƙasarmu ai akwai
black americans, zai Iya yiwuwa suma suna da alaƙa da fararen fata ne ina nufin
half cast”

“Dagaske Ku ɗin Ƴan Nigeria ne? Jinjina masa kai tayi”Eh, ai yaren da muke yin
magana dashi hausa ne na nigeria, zaku Iya bincikawa”
Ba ƙaramin mamaki suka yi ba, Hatta turancin da yaran suke magana da shi sak
Na america ne bana Nigeria ba.

“Yanzu dai bazaki faɗa mana gaskiyar abunda ya faru da ku ba ko! To Shi ɗan uwan
naki da kika ce yasan komai tayaya zamu Iya farkar da shi daga bacci”! Anzo dai dai
wurin da tafi so, marairaice masu fuska ta yi”maganinshi Yana a nigeria, dan Allah
ku taimaka ku maida mu ƙasarmu, idan ba haka ba ɗan uwanmu zai Iya mutuwa” hada
ƙwallarta
“Meke damun shi ne” Dr Brown ne yai mata tambayar, batare da ta yanke shawara da
zuciyarta ba tace”nima bansani ba, Idan yafara bacci yana ɗaukar tsawon lokaci bai
farka ba, to akwai maganin shi kuma yana acan ƙasar”
Murmushi kowannansu ya saki, hakan yasa tasha jinin jikinta, Commender yace”Kin
Iya acting, da farko kince bazaki Iya tuna komai daya faru a rayuwarku ba, amma
ayanzu kin faɗi inda za’a samu maganin ɗan uwanki hakan na nufin tunaninki yana nan
baki manta komai ba ko”? ɗaure mata fuska yai “Zaki faɗa mana gaskiya ne? Ko kuwa
kunfi so mu je dake can headquater Ki amsa mana tambayoyinmu ta tsiya” tashin
hankalin da ba’a sanya mashi date
Maganar commender tayi matuƙar tsoratar da ita Jikinta Ya hau yin kakarwa duk
tabi ta rikice, A ƙarshe data ga dagaske zasu titsayeta saita amsa masu tambayoyi
ko su tafi da ita headquater, aiko da ƙarfi tasa wata irin gigitacciyar ƙara data
firgitar dasu, Hannayenta Biyu ta sanya ta daddafe kanta tana faɗin”Nace maku ni
bansan komai ba! Dan Allah ku maidamu ƙasarmu Nigeria, ɗan uwana zai Iya rasa
ranshi, Na roƙe ku idan har dagaske zaku taimaki rayuwarmu to ku maidamu Nigeria
wurin danginmu,” kamar mahaukaciya haka tadinga nanata masu akan su maidasu
Nigeria.

Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda Ƙwayar idanuwanta suka burkice
Launin Ciki Ya 6ace sai zallar farin idon, Jijiyoyin wuyanta dana Gaban goshinta
shatunsu ya fito ruɗu ruɗu, Jefar da robar fanta hannunta ƙasa ta yi, a zafafe Ta
miƙe saman gadon kamar ƴar daba, ta dunƙule hannayenta, taci gaba da ambaton Ku
rabu dani ku ƙyaleni, Ku maida mu ƙasar mu Nigeria nace ku kaimu ƙasar mu, can muke
son zuwa”

Har suna haɗa baki wurin lallashinta”sorry ki kwantar da hankalin ki, zamu tafi
yanzu, Ki daina kuka ki kwantar da hankali, Ki koma ki kwanta, babu wanda zai Ƙara
tambayarki wani abu” sun firgita da ganin haukan Angel.

Dr laura duk tabi ta ruɗe Sun rasa gane kanta.

Kallon Sojojin ta yi”Pls, Ku ƙyale yarinyar nan, Muje office muyi magana, idan ba
haka ba za’a Iya samun matsala” gyɗa kai sukayi ba don sunso ba suka Juya tare da
fucewa daga ɗakin tare da Likitocin, Ya rage da ita sai Dr laura.

“Pls My daughter kukan Ya isa haka, Ki koma ki zauna muyi magana kinji”?
Lallashinta tashiga yi, Daƙyar Angel ke iya kallonta sumar kanta duk ta rufe mata
fuska, dagangan ta ƙirƙirarma kanta Ciwon hauka.

Marairaice mata fuska Angel tayi”dan Allah ki taimaka mana, su maida mu ƙasarmu,
banaso mu rasa ɗan uwanmu zai Iya mutuwa, maganinsa yana can, Nayi maki alƙawarin
idan ya farfaɗo zan fada maku duk wani abu da ku ke son ji dangane da mu”

saukowa Angel tayi daga saman gadon, A sukwane ta zube saman gwiwowinta agaban Dr
laura, Idanuwanta sun cicciko tab da hawaye take faɗin”Na roƙe ki Ki taimaka mana,
kamar yarda Allah Ya taimake ki, Kice ma sojojin can sumaida mu Nigeria, Idan ba
haka ba Ɗan uwana danish zai mutune, ba zaku Iya sarrafa shi ba, maganinsa yana
acan, Ni na yarda ku sanya jami’an ku, su bimu can kasar don su shaida abunda na
faɗa masu su sanya mana ido’ Muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar.
Tsananin tausayintane Ya kama dr. Laura har cikin ranta ta aminta da yarinyar,
Miƙa mata hannu tayi”miƙe tsaye” da sauri Angel ta ɗaura hannayenta asaman na dr
laura, ta yunƙura ta miƙe, ba zato ba tsammani taji ta rungumeta a kirjinta,
ƙamshin turarenta Ya daki hancin Angel sosai ta ƙankameta tana faman sauke ajiyar
zuciya.

Shafa sumar kanta dr laura tayi a hankali take yi mata magana


“Ni tun farko banso suka tsareki da tambayoyinsu ba, sunyi gaggawar yin hakan,
But Inaso ki kwantar da hankalin ki, Zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin sun
maida ku ƙasar ku, idan har kikayi min alƙawarin zaku faɗa mana abunda ya faru da
ku bayan ɗan uwan naki ya farfaɗo kamar yadda kika ce”
Cikin sanyin murya Angel tace”Nayi maki alƙawari shiyasa ma nace su sanya jami’an
da zasu bibiyi rayuwarmu” ta ƙare maganar tare da raba Jikinta daga na Dr laura
Shafa fuskarta tayi”is ok, Zanje muyi magana da su yanzu ki koma ki kwanta ki
huta”

Amsa mata Angel tayi da toh, Bayan fitar dr laura, Daɗi kamar zai kasheta, don
tana ji aranta zasu amince masu su koma Nigeria, juyawa tayi tana neman robar
fantar data jefar a ƙasan tiles can ta hangota gefen nightstand zuwa tai ta ɗauko
lemun ta koma gefen gadon Hankali kwance taci gaba da shan lemun fatanta Allah yasa
su amince masu.

Gaba ɗayansu sun Hallara a katafaren ofishin dr laura, Kowan nan su Ya samu wuri ya
zauna saman haɗaɗɗun kujeru, table ne Ya ratsa tsakaninta da su,.

“Shawarar da zan bada shine bai kamata mu takura masu da tambayoyi ba, duba da
Yanayin yaran akwai ciwon damuwa atattare da su, tursasa masu zai Iya haddasa masu
wata matsalar da bama fata” Dr laura ce ta kora jawabin idonta akan faces din
sojojin
Commender yace”Ya zamuyi kenan? Menene Mafita don muna buƙatar son Jin ainihin
abunda ya faru da su a dajin nan”
Numfasawa dr laura tayi”Munyi magana da yarinyar, tabbas bata manta komai ba,
tasan abunda ya faru da rayuwarsu sai dai rashin yarda da tsoron fargabar abunda
zai biyu baya idan ta faɗa mana sun Hana ta sanar damu, abun duba anan shine Babu
yarda za’ae su saki jiki damu don ta yanzu, saboda basu sanmu ba bugu da ƙari kuma
ba ƴan kasar mu bane, donni na yarda da maganarta, Idan har munaso muci nasara
akansu dole sai mun yi masu abunda su ke so, ta hakanne zasu saki jiki damu har su
faɗa mana gaskiyar abunda mu ke son ji daga gare su, sannan suna buƙatar wadda zata
Kula da rayuwarsu tamkar mahaifiyarsu, Ta hakanne zasu saki jiki da ita har su Iya
faɗa mata damuwarsu, abu na biyu shine Muyi masu abunda suke so! Musamman ita Angel
din ta roke ni akan mu maida su ƙasarsu, Akan idonku kunga haukan da tayi mana
tabbas akwai ƙamshin gaskiya a maganarta, tace maganin ɗan uwansu yana acan, kuma
tace zamu Iya sanya jami’ae su bi su har can kasar sannan tayi alƙawarin idan harya
farfaɗo zata faɗa mana duk abunda muke son ji.

Shiru suka ɗanyi na wani lokaci kowan nan su Yana nazarin maganar dr laura.

Numfasawa Major yai kafin ya soma magana”Me zai hana mu damƙa Case ɗinsu ya koma
hannun Hukumar Isod? (Intelligence Special Operations Division) Tun da shugabansu
Ɗan ƙasar Nigeria, su kaɗaine zasu Iya bincikar Ainihin abunda Ke faruwa da yaran,
saboda suna da ƙwarewa a 6angaren.

Jinjina kai Commender yai da alama ya gamsu da jawabin Major

“Hakane ka kawo shawara mai kyau, case ɗin yafi dacewa dasu, Tunda Aikinsu ne Yin
binciken sirri Harma da fafatawa idan ta kama kuma duk muna atare dasu banbancin
kaɗan ne mu ba jami’an sirri bane su kuma duka sun Haɗa sunayin aiki a matsayin
sojoji sannan kuma jami’an sirri”

Captain Yace”Nima na goyi bayan hakan, amma fa zaiyi wuya mu iya samun chief ɗin
nasu a waya, So the best way to contact him is through email, We need to start
making our request for the case through their email, If they show interest in the
case, we will turn everything over to them.”

Commender yace”shugaban nasu ai Yana a Washington (babban birnin america) kuma


naji raɗe raɗen kamar cikin weekend da zamu shiga zai bar ƙasar ya koma Nigeria,
duk da bani da tabbaci kunsan aikin nasu na sirri ne babu mai sanin shiga da fucen
su, Idan har muka samu ya nuna interest akan case ɗinsu komai zai zo mana da sauƙi,
In yaso sai mu damƙa mashi Yaran ya tafi da su can, mu kuma zamu dinga bibiyarsu
don jin ya ake ciki”

Murmushi Dr laura tasaki, Har cikin ranta ba ƙaramin daɗi taji ba, Fatanta Allah
yasa Chief ɗin Isod Ya amince da case ɗin Yaran, ko dan saboda Yarinyar da ta roƙe
ta akan amaida su ƙasarsu”

“Doctor, how long do you think it will take for the children to be discharged”?
captain ne yai mata tambayar,

Dr. Laura ta bashi amsa da cewa “After the three-day injection course is completed,
we will be able to discharge them, Shima Ɗayan Yaron mai fama da ciwon zuciya Zamu
Iya sallamar shi idan har aka Kiyaye sharuɗɗan da zamu rubuta na bashi kulawa ta
musamman, “ ta ƙara da cewa”zasu Iya zama a asibitin namu har zuwa lokacin da shi
chief ɗin zai Amsa mana buƙatar mu”

Commender yace”dole ne mu sama masu wadda zata Iya kula da su tamkar ƴa’ƴanta
kamar yarda kika bada shawara, wadda zata Iya tarairayarsu ta basu kulawar da zasu
Saki Jiki sosai,” Yai maganar yana kallon fuskar dr laura
Major yace”why not bazamu damƙa amanar kula da yaran a hannun UMMIN AMERICA ba?
Tun da itama Ƴar Asalin ƙasar Nigeria ce, hatta yaren da naji Yaran suna magana da
shi itama tana jin shi sosai” Jin Major Ya ambaci sunan Ummin america yasa Dr Mark
da dr brown Kallon Juna ga dukkan alamu sun girgiza da jin an ambaci sunanta, Dr
laura ta zaro ido tana faɗin” The Baddest mistress? There’s no way we can leave the
children in her care, She’s a dangerous woman. How could she possibly know how to
take care of them?” hankalinta bai kwanta da zancen miƙa yaran ga Ummin america ba
saboda sanin wacece Ita.

Bayan ta ƙare magana Major yace”Ai ba yau tafara Yi mana aiki ba, tana taimaka mana
sosai akan irin case ɗin nan, Ina da tabbacin zata Iya! Fiye da yadda baki
tsammani”Kwa6e fuska Dr laura Tayi don ita har aranta Fargabar Ummin americe take
ji, Kowa yasanta sananna ce a 6angare Iya karuwanci tantiriyar ƴar bariki ce, tayi
ƙaurin suna america shiyasa su ke yi mata laƙabi da Ummin america, tsabar Iya
shaiɗancinta har award ake bata akan Iya Karuwanci.

“Mu zatayi ma aiki, bai shafi sana’arta ba, Kawai munaso Yaran su kace a
hannunta amatsayin guardian ɗinsu, Kafin Mu damƙa mata su zamu yi yarjejeniya da
ita idan har ta amince to lafiyalou ba zamu samu matsala da ita ba” ta6e baki dr
Laura tayi”amma dai ba’a asibitin mu za’a gayyato mana ita ba, Don ina jin fargabar
ta rikitar mana da ma’aikatan mu da surar jikinta”

Gaba ɗaya suka sanya dariya jin abunda tace, ta faɗi hakanne don tasan Ummin
America kamar maganaɗisu take awurin Iya jan hankalin mutun da surar Jikinta,
Dirine da ita na bala’e’
Sunjima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani Commender yace

“Dr mun gode sosai da shawarar ki, Zamu koma bakin aiki Yanzu, Idan har Chief
din isod Ya amince da buƙatar mu zamu tuntube ku”

Daga haka Sojojin sukayi Ma Dr laura sallama, Har bakin parking space na asibitin
ta rakosu, Bayan tafiyar sojojin suka dawo Cikin asibitin.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank
3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E18🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

*DAULAR OBIE ESTATE*

A katafaren ɗakin Hajjaty head maids ta gidan obinna, tsabar haɗuwarsa tamakar bana
ƴar aiki ba.

fitowar kenan daga bathroom, ga dukkan alamu wanka tayi, ta ɗaure ƙirjinta da
towel fari, iya gwiwar ƙafafuwanta ya tsaya mata, fatarta da lemar ruwan wankan da
ta yo, a gaban mirror ta tsaya tana kallon kyakkyawan fuskarta har yanzu akwai
sauran make-up ɗin jiya da ta yi jan bakin bai goge ba, don ita bata rabo da
kwalliya a fuskarta.

Har ta miƙa hannu zata ɗauki man shafawarta cikin jerin mayukanta, ba zato ba
tsammani muryarshi ta ratsa kunnanta”My heart beat” ras taji gabanta ya faɗi, sam
bata ji shigowarshi ba, A hargitse ta yi saurin wurga idonta kan fuskarshi

Yana daga kishingiɗe saman gadonta, farar singlet ce a jikinsa da short.

Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, muryata na rawa ta furta sunan shi”PRAVIN”!

Dafe kai tayi da hannu ɗaya, tsananin fargaba ne ya kamata.

“Nashiga uku, why Pravin meyasa zaka yi min haka! Kana so ne kaja min bala’e?
Yanzu idan wani ya faɗo ɗakin nan me kake tunanin zai biyo baya”? A ruɗe ta ke yi
mashi magana tana faman zazzare dara daran idanuwanta,

“Haba pravin baka min adalci ka riga da kasan ko’ina na kusurwar gidan nan cctv ne
za’a iya ganin duk motsin ka”

Tun da ta fara magana, Pravin ya tsareta da manyan idanuwanshi, har sai da takai
Aya, tukunna Ya sauko daga saman gadon ya nufe ta kamar wani zaki, dab da ita Ya
tsaya ƙamshin turaren jikinsa ba ƙaramin Illa Ya ke yi mata ba tuni ta fara shiga
yanayi.

“My honey, ni ban zo donna 6ata maki rai ba, haƙƙina nake so, Nakasa jurewa ina
buƙatarki, kinsan bani da haƙuri in dai akan buƙatar kaina ce, sannan ki kwantar da
hankalin ki, babu wanda yasan na shigo ɗakin ki, daga ni sai ke”

Ya ƙare maganar yana faman sakar mata shu’umin murmushin nan nashi, Idanuwanshi
akan ƙirjinta da suka tsone mashi ido.

Jikinta sai kerma yake yi kamar wadda sanyi ya kama, tana matuƙar jin tsoron wani
ya faɗo masu a ɗakin, ita kanta a buƙace ta ke da shi tana son kasancewa da shi sai
dai tana tsoron wani ya gansu.

Still sautin muryarta adabarbarce take furta”Pravin ni ina fargaban wani ya


gan....” bata kai ga ƙarasa maganar ba, yai saurin zura harshen shi acikin ƙaramin
bakinta, hannayenshi biyu ya ɗaura saman manyan mazannanta ya ci gaba da murzasu,
nan take numfashinsu ya fara hauhawa yana fita da sauri sauri alamun sun fara hawa
kan network, ko’ina na jikinta ya ke bi yana matsawa da hannunsa, Sosai yake
kissing ɗin ta tamkar zai cire mata la66anta, Zame tongue ɗinsa yai daga bakinta,
tun daga kan wuyanta ya fara manna mata hot kiss har izuwa ƙirjinta, ya warware
towel ɗin da tayi ɗaurin gaba dashi gefe ɗaya ya jefar da shi, gaba ɗaya ya ɗauketa
ya jefar saman gado, doguwar sumar kanta tuni ta tarwatse saman mattress, Ya sanya
hannu ya zame Singlet ɗin jikin shi Ya haye saman gadon Yaja bargo Ya ƙudundune
su, To jama’a nidai bansan me sukeyi a cikin bargon ba, na dai ji sautin gurnaninsu
tamkar namun nawa na fafatawa. Bargon da suka lullu6a dashi sai yamutsewa yake yi
yana motsi kamar ana dambe a cikinsa, ba yau bane karo na farko da ya fara biyan
buƙatarshi da ita ba, sam basa gajiya da juna pravin da divya wato hajjaty, Babu
wanda yasan suna harƙalla atsakaninsu.

(To fa, akwai gwarama yasin Ana wani abu agidan Obinna, Ko ina hajiya saratu
taje? Ana nan za’a 6ata mata tarbiyar Miji🤣)

A hankali danƙareriyar Motar Hajiya saratu ta kunna kai Cikin Villa dinsu adai dai
parking space security ɗin da ke driving nata yai parking na motar, Da sauri Ya
fito daga driver seat Ya zagaya Ya buɗe mata ƙofa, ta zura ƙafarta dake sanye cikin
High hills, dawowarta kenan daga meeting da suka yi a ministry of Health tare da
manyan ministocin Kiwon lafiya da suka kawo masu ziyara daga Who (world health
organization) don inganta Lafiya.

Tsadadden leshi ne fari a jikinta, riga da zani daga sama ta ɗaura lap coat,
fararen idanuwanta na amanne da glass fari matar fa akwai Iya ɗaukar wanka, ta
ko’ina Jikinta ƙamshi yake fitarwa.

Saukowa ta yi daga Cikin motar, da sauri ta nufi cikin gidan hannunta ruƙe da
hand bag ɗinta, duk inda ta gifta masu aiki ne ke safa da marwa, cikin girmamawa su
ke gaishe da ita, idan ta gama dama ta amsa idan bata ga dama ba sharesu take yi.

A katafaren Main palour na gidan ta shigo, Tafkeken gaske A ƙalla Yana ɗauke da
Royal sofas two set saboda faɗinsa.

“Sannu da dawowa Hajiya” muryar Safa ce ta dakatar da ita daga Yin tafiyar,
Fuskarta babu annuri a ɗaure take tamau kamar wadda aka 6ata ma rai”Pravin Ya dawo
ne”? Tambayar da ta jefa mata kenan.

“Bani da masaniya, da ya ke mu na yin aiki a kitchen ne bansan ko ya dawo ba”


Gyaɗa kai Hajiya saratu ta yi”Okey, zan shiga ɗakin baba, kafin in dawo ki
tabbatar kin kai min lunch ɗina a ɗaki, bana son 6ata lokaci” amsa mata tayi da toh
hajiya.

Da sauri safa ta nufi kitchen don ta shirya mata abincin.

Kaitsaye hajiya saratu ta nufi sashen obinna.

Tana gab da zata shiga ɗakin Dr jazz ya fito Yana sanye da suit black colour. Ko
da suka haɗa ido da ita gabansa ba ƙaramin faɗuwa yai ba.

Muryarshi asanyaye ya furta”ina wuni mommy” harara ta wurga mashi

“Kai bana ce kar na kuskura na ƙara ganinka acikin gidan nan ba? wannan wata
irin mayuntaka ce? Meye haɗinka da babanmu”? Tafa Hannu ta yi haɗi da ruƙe ha6a.

Muryarshi adabarbarce ya furta”ai ba anan nake zaune ba tun lokacin da ki ka ce


bakison ganina, na koma gidan daddy da zama...” daƙyar ya ida maganar ganin irin
ƙasƙantaccen kallon da take wurga mashi.

“Uban waye daddyn naka? In banda yaudarar kai yaushe Yaya mubarak ya zama uban
ka? Kai fa ba ɗan kowa bane a family ɗin nan, ka daina ɗaukar kanka wani shege, ai
tun ranar da aka faɗamin cewa hada kai ake tsegumin ƴa’ƴana, naji na ƙara tsanar ka
matsiyacin banza, in banda zaƙewa da shisshigi da kutsu da samun wuri irin na ɗan
talaka ina kai ina haɗa kafaɗa da masu asali a dangi eyeh? A faɗace take yi mashi
magana tamkar zata rufe shi da bugu, Bawan Allah dr jazz tuni hawaye sun cicciko
idon shi.

Ta6e baki tayi”dallah jibarka, sai uban tsawo kamar fal waya ba ƙiba, duk irin
arziƙin da ku ke ci a ƙarƙashin inuwar mu har yau baka ƙara komai ba, Sai Iya gulma
da munafunci shashasha kawai, dallah ni bani wuri in wuce kar na ham6are ka” jiki
na rawa ya matsa mata hanya, ta shiga ɗakin obinna.

Idanuwanshi sun kaɗa jawur, babu mai yi mashi gori irin hajiya saratu ƙiri ƙiri
take nuna ta tsane shi, sam ya kasa motsawa saboda jirin da ke shirin ɗibarshi, a
hanzarce ya dafe bango da hannu ɗaya, Ƴar ƙwallar da yake 6oyewa tuni ta gangaro
saman kuncinsa, a hankali yake cizon pink lips ɗinsa haɗi da lumshe idanuwanshi.

“JAZZ”! Ras Ya ji gabanshi ya faɗi sam bai ji takun tafiyarsu ba, a fakaice Ya
zaro hanky daga trouser pocket ɗinsa Ya share ƙwallarsa, Kafin ya ɗago yana
kallonsu.

Turai ce mahaifiyarshi tare da Sir mubarak sun shigo gaida baba, jallabiya ce a
jikinta ta yafa mayafi akanta, Sir mubarak yana sanye shima da jallabiya ta maza.

Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba ganin damuwa akan fuskarshi

“Jazz lafiya naga kamar idonka ya canza launi”?

Girgiza mata kai yai”bakomai mommy am ok, idona ne ke yi min ciwo, yanzu nike
shirin zuwa gida.....” Sir mubarak ne ya katse mashi hanzarinshi.

“Jazz meke damunka ne? Sai kace wani ƙaramin yaro? Idan ba ka da lafiya baka san
Hanyar zuwa asibiti bane? Ba za ka je aduba maka idon naka ba”?

Cikin sanyin murya yace”zanje in sha Allah, nagode da kulawar ka daddyna.


Hankalin turai bai kwanta da abunda ɗan nata ya faɗa mata ba, Matsawa tayi kusa
dashi, ta ruƙo hannunshi acikin nata

“My Son, ka je gida ka kwanta ka huta, idan muka dawo zamuyi magana” cikin kulawa
take yi mashi magana

Amsa mata yai da toh mommy, bayan yayi masu sallama ya kama hanyar fita daga
gidan.

Hajiya saratu na zaune saman carpet, sir mubarak yai sallama hannun shi ruƙe dana
matarshi, daƙyar ta amsa masu sallamar, A saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna,
hakan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ganin ita ta zauna saman carpet su kuma
sun Haye saman sofa.

“Yaya mubarak Ina wuni, Ya iyali”


“Lafiyalou saratu, Ya naki aikin ya kuma Iyali”Alhamdulillah” ta amsa mashi

Sir mubarak yace”baba baya nan”? Yai maganar yana bin ɗakin da kallo
Hajiya saratu tace”ya shiga toilet ne, shine yace min Injira shi” sir mubarak Ya
furta Okey, ina mijin naki na shigo gidan ban gan shi ba, Ko ya tafi office ne” yai
tambayar ne don yasan aikin nasu na Companynsu har Saturday suna zuwa banda sunday
and Friday.

“Tun da safe muka rabu da shi, yana shirin tafiya office, bai dawo ba ne”

Ran turai ba ƙaramin 6aci rai ba, ganin hajiya saratu da tayi a ɗakin obinna ya
tabbatar mata da cewa Itace silar halin da Jazz ya shiga, batun yau ba tasa ba yi
mashi gori.

“Saratu Baki gaishe da Auntyn taki ba” kamar yayi magana da bango, Ta haɗe fuska
ba annuri
Da ɗan tsawa Sir mubarak Yace”Saratu baki Ji ina magana bane” sai da ta mula
tasha iska tukunna tace”yaya ai bani ya dace in fara gaishe da ita ba, saboda ni ce
agaba da ita,” Ran Sir mubarak ya 6aci, zuciyarshi ta motsa, Tsawa ya daka mata har
sai da turai ta zabura saboda firgitar da tayi.

“Kada ki kuskura ki bari in sake nanata maki! Nace ki gaishe da ita tunkafin na
6ata maki rai” sanin halinshi yasa ta wurga ma turai harara kafin tace”Ina wuni
matar yaya”
Cikin sanyin murya ta amsa mata Lafiyalou.

Fitowa Dattijon arziƙi yai daga toilet, jikinsa sanye da jallabiya, dogon gemunsa
kamar ana ƙara mashi tsawo fari fat, fuskarshi ɗauke da murmushi yake binsu da
kallo

“Gayu mutanan Allah, wa nake gani kamar turai? Rufe fuska turai tayi da mayafin
jikinta, Sir mubarak na murmushi yace”yau surukar taka tazo gaidaka, tun ɗazu da
safe tasa naci akan saita shigo, nace tabari mu zo atare”

“Amma nayi farin ciki, ni nasan ɗiyata tana son zuwa duba babanta, kaine dai ka
hanata zuwa mubarak, Allah ya kamaka, dama Ana kawo min tseguminka, akan ƙuntata
mata da ka ke yi kana yi mata kulle agida”

Ƴar dariya Sir mubarak yai yana faɗin”gaskiya kowaye ya faɗa maka haka baba to ka
bincike shi, Ni nasan ma baya wuce Jazz ne, Aiko inda shine yau a headquater zai
kwana”

Dariya suka sanya banda hajiya saratu data ɗaure fuska, muryarta aƙula ta soma
magana
“Baba dama na shigo ne don in gaishe ka, inaso zan wuce” Ganin tana yunƙurin
miƙewa sir mubarak yai saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Koma ki zauna
sarkin fushi, indai saboda mune kike ta 6ata fuska yanzu zamu koma gidanmu,” ya
ƙarasa maganar tare da kallon Baban nasu, hankalin shi na akan fuskar saratu

“Zamu wuce baba”

“Ban gaji da ganinku ba, ku zauna muyi fira mana” acewar Obinna

“Auta Ya meeting ɗin naku?

Yamutsa fuska tayi”lafiyalou, baƙin har sun tafi, shiyasa na dawo gida”

“Masha Allah,” ya ambaci hakan tare da shafa gemunshi

“Ya shirye shiryen tarbar baƙinmu na gida da zasu zo? Ko kun manta da shagalin da
zamuyi ne”?

Sai lokacin Saratu ta sassauta fushin fuskarta jin anzo inda tafi so”A’a baba
taya zamu manta da rana mafi mahimmanci agaremu ranar da mahaifinmu abun
al’faharinmu yazo duniya,” Kalaman saratu sun faranta mashi ranshi.

Sir mubarak yace”Ai nafi kowa zumuɗin ranar tazo baba, naso ace ni aka ba damar
ɗaukar ɗawainiyar duk wani abu da za’ayi a ranar, sai dai kash Hateem yai min
kutse, gaskiya ban ji daɗi ba, Haka last time Sharafuddeen ne ya ɗauki nauyin
gudanar da shagalin”

Da murmushi akan fuskar obinna yace”ai ba wani abu, dakai da su din duk abu
ɗayane awurina, ina matuƙar alfahari da ku, kuma Inajin daɗin yadda kuke nuna mini
ƙauna”

Ya ƙare maganar tare da kallo Turai, da zolaya yace”Surukar wannan karon wani
kalar wanka zaki ɗauka”? Duƙar da kai ƙasa tayi fuskarta ɗauke da murmushi.

Hajiya saratu tace”anko ne zamu fidda ae, zanyi magana da zahra ɗaya daga cikin
matasan Yaran da suka yi mana decoration lokacin birthday din twins, ta ƙware wurin
iya tsara anko in yaso ma sai su yi mana decoration ɗin”

Jinjina kai Obie yai’naji daɗin jin haka, nima na yaba da aikinsu, yarinyar da
kike magana akanta ai na ganeta ƴar gidan ɗan Iya ce, suna da mutunci mutanan kuma
mahaifinta yana yi mana hidima sosai, Yakamata ayi masu magana da wuri, tun da mun
shiga watan”

“Insha Allah idan na koma ɗaki zan Kira zahran awaya in sanar da ita, amma baba
kowa da kowa zai hallara ko? Dan banason inga babu wani adanginmu”
Sir mubarak yace”dolensu ma su zo ai, ƙwan su da kwarkwatarsu, babu wanda zamu
yi ma uziri acikinsu, da na gida nigeria da na ƙasar wajen kowa zai zo, Inyaso
mutun zai Iya komawa aranar da yazo don wlh bamu raga ma kowa, just rana ɗaya kacal
zamu taya mahaifinmu birthday, banga dalilin da zai hana mutun zuwa ba” a tsanake
obinna ke kallonshi, yana matuƙar jin daɗin girmama shi da su ke Yi.

“Ku kwantar da hankalinku, in sha Allah kowan nan su zai zo, munyi waya da
lateef da abdul razak duk sun tabbatarmin da zuwansu, dama ni banida matsala dasu,
Mutun ukun nanne suka fi shiga busy, sharafuddeen da Hateem inayi masu uziri sosai
saboda yanayin aikinsu, to su dinma dai Alhamdulillah sun tabbatarmin da zasu samu
damar halatta, hada sauran jikokina owais dai ne bani da tabbacin zai zo ko kuwa,
har yau dai bansamu wayarshi ba,” muryarshi da rauni ya ƙarasa maganar.
ta6e la66a hajiya saratu ta yi aranta tace”sai kace wani ɗan gwal duk yabi ya dami
kanshi akan owais, kamar shi kaɗai ne jikanshi”

Muryar sir mubarak ce ta fargar da ita daga yin zancen zucin”indai owais ne yana
sane da wannan ranar mai muhimmanci, duk mun busy din da zai shiga bazai manta da
ranar nan ba, saboda ƙaunar da yake yi maka, don haka ka kwantar da halinka baba,
In sha Allah Jikanka zaizo.

Nauyayyar ajiyar zuciya obinna ya sauke, zallar farin ciki ne kwance akan
fuskarshi har ya ƙosa ranar ta ƙaraso ko dan yaga Jikanshi daya daɗe yana
mamarinsa.

“Baba Ni zan wuce ciki” hajiya saratu ce tayi maganar a yayin da take miƙewa
tsaye tana gyara mayafinta.

“Har mun gama magana”? Ya jefa mata tambayar, murmushin yaƙe ta ɗan saki”inaso ne
in shiga ciki, namanta na sanya mai aiki ta kaimin abinci, idan naci na huta zan
Kira zahran awaya duk yadda muka tattauna da ita zanzo na sanar maka”

Gyaɗa kai obie yai”nima nafi so ki huta autana, ki ci abinci ki ƙoshi idan
takama ki kwanta kiyi bacci” dariya ta dan saki tana kallon baban nasu, maganar shi
ta tuna mata ƙuruciyarta, shi dai burinshi saratu taci abinci ta kwanta ta huta
idan ta dawo daga makaranta, bayason tana aikin wahala.

“Nagode da kulawarka akaina baba, Allah yabar mana kai abun alfaharin mu”

Amasa mata yai da amin, Juyawa tayi ta kalli Sir mubarak da turai

“Ni zan wuce yayana, a huta lafiya” bata jira amsarsu ba, da sauri ta fuce daga
ɗakin.

Bayan fitarta, tattaunawa suka cigaba da yi game da yadda za’a tsara komai na
shagalin da za su yi.

Tun da ta shigo ɗakin, komai na ciki agyare ta same shi, Safa ta kawo mata lunch
ɗinta yana asaman table ta ɗaura mata shi.

Cire lapcoat din jikinta tayi a saman Hanger ta sagala ta, shaf shaf ta canza
kayan jikinta zuwa, rigar shan iska, daga bisani ta koma gefen gadon ta, ta zauna
domin cin abinci, farawa da bismilla ta kai hannu ta damƙi haɗaɗɗan cup na cofee ta
kur6e shi, bayan ta gama ta soma shan farfesun naman kaza da zafi zafinshi, cikin
ƙanƙanin lokaci ta shanye shi ta kuma damƙar Chips ta cinye ta cakumi cheese burger
ta tura abaki hankalinta kwance take cin abincinta.

Ringing ɗin wayarta ne ya janyo hankalinta ga duban hand bag dinta dake ajiye
saman pillow.

Ba ta yi niyar ɗaga kiran ba, don ita a ƙa’ida bata picking call idan tana cin
abinci saita kammala, hakanan dai tayi ra’ayin duba me kiranta, tissue ta yaga ta
goge bakinta, kafin ta yunkura ta ruko handbag din, duba sunan me kiran nata tayi
sunan ya fito 6aro 6aro asaman screen ɗin iphone ɗinta

*Princess Mujeedat* murmushi hajiya saratu ta saki da zumuɗi ta ɗaga kiran cikin
harshen turanci ta soma yi mata kirari

“Uwargidan shugaban ƙasar Kanada, Gimbiya mai jiran gado ta Haɗaɗɗiyar Daular
Larabawa! Sarauniya ɗaya tilo da ke mulkin zuciyar Yaya Hateem, Wuu hu huu! ina
gwanar wata ga tawa, Uwar gida sarautar mata daga ke babu ƙari mun kulle ƙofa”
sautin ƙayataccen murmushin gimbiya mujeedat ne ya karaɗe kunnuwan saratu, da alama
taji daɗin yabon da saratu ke yi mata.

bayan ta gama yi mata kirarin ta ɗaura da cewa”Habawa auntyna nayi fushi Allah, sai
yau aka tuna dani, ai amana batace haka ba fisabilillah, daga ke har Yaya hateem
ɗin baku tunawa da mutane sai wanda ya taka yaje inda ku ke” (idan kaga hajiya
saratu na magana da mutun fuskarta asake to koma wanene ba ƙaramin mutun bane,
babban gorone magogin ƙarfe dai dai da ita koma fiye da ita, zaranne yai dai dai da
kalar yadin🤣)

Ni kaina da naji muryar mai magana saida naji shock, kai daga jin voice ɗinta
zaka shaida jinin sarauta ce, gaba da baya, Jinin arziƙi waɗanda suka gaji abun, da
izza da dattako ta ke yin magana tamkar bata son furtata.

“Ba abun da ki ke tunani bane ƙanwata, ban manta dake ba kina araina shiyasa ma
na kira don mu gaisa” itama da turancin ta mayar mata da amsa don ba ta jin hausa.

“Duk da haka ban sauko daga fushin ba, gaskiya idan kinason mu shirya ki biyo
yaya hateem kuzo Nigeria taya murnar birthday din baba, nasan halinki bakison taka
ƙasarmu” fuskar hajiya saratu awashe take yi mata magana.

“Naji daɗin kirarin da ki ka yi mini, shiyasa a kullum nike ƙara godewa Allah
daya bani surukai nagari irinku, wannan abun alfaharine, haƙika ban ta6a danasanin
auran hateem da nayi ba, saboda tunda muka kasance a ƙarƙashin inuwa ɗaya har Allah
ya azurtamu da samun zuri’a ban ta6a samun matsala da shi ko dangin shi ba, Kuna
nuna min ƙauna sosai nima Ina sonku”

Hajiya saratu baki yaƙi rufuwa, sauran burger din dake abakinta tuni ta ƙarasa
haɗiye ta, dadi take ji yau gimbiya mujeedat ta kirata awaya.

“Me kike ci ne? Naji bakinki acunkushe da wani abu, wato har yanzu ƙanwata baki
daina ciye ciye ba ko”? Tuntsirewa hajiya saratu tayi da dariya annurin fuskarta
sai ƙara nunkuwa yake yi. Mamaki takeyi yarda Gimbiya mujeedat keyi mata magana
matar da saboda izzarta idan ka kirata awaya bata picking sai ka fara tura mata
text message ka nemin iznin yin magana da ita, idan taga dama zata baka reply akan
ka kirata a lokaci kaza, amma muddin mutun ya kira layin mujeedat batare da ya fara
neman izni ba to bata ɗaga kiran nashi.

*A GIDAN ƊAN IYA*

Idan muka koma 6angaren su Aneeleeh tun ajiya Hajiya adama da Uncle abdallah suka
sanar da su game da zancan komawarsu gida, Abie yace bazai yiwuwa ba su ɗan ƙara
kwanaki mana, Anan uncle abdallah Yake sanar dasu cewa Ai sun samu gidan da zasu
zauna a abuja ya 6oye ne bai sanar dasu, harma ya samu aiki a companyn
sharufuddeen, ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba sun tayashi murna sosai, musamman
da suka ji cewa bazasu raba Aneelerh da junaid ba ko da yakai shekarun da zasu Iya
kar6ar shi ne, Zasu haƙura ne har Allah ya bayyanar masu da su Uzair, dama rashin
ɗan nasu ne yaja har suke son kar6ar shi, Aneelerh hada kukan farin Ciki, Ta ƙara
jin son surukan nata, ba ita kaɗai ba hatta su mami sun ji dadin ziyarar da suka
kawo masu sun kuma jinjina ma ƙoƙarinsu na barma Aneelerh ɗanta, su kansu sun
fahimci ba ƙarami so suke yima yaron ba tun da gashi ta dalilinsa sun dawo abuja da
zama, ba su kai ga barin gidan ba, abie ne ya dakatar da su yace su ɗan jira akwai
malaman da zai sanya su yi masu safkar alƙur’ani a sabon gidan su, hakan ba ƙaramin
daɗi yai masu ba, don su basuyi tunanin yin hakan ba.

Hankalin Mahboob yaƙi kwanciya tun da yayi tozali da hoton Angel, a daren ranar
daƙyar Ya iya runtsawa, saboda fuskarta da ke yi mashi gizo, ya kwana da mamakin
baiwar Kyan da Allah Yayi ma yarinyar, bai ta6a ganinta ido da ido ba sai dai ahoto
yasanta tun tana ƴar ƙaramarta, Aneelerh take ɗaukar ta hoto da video tana sanyawa
a status dinta to anan yasanta, a ƙarshe daya gaza haƙara bayan sun dawo daga
sallar asubahi, ya lalla6a yaje ɗakin aneelerh, tsabar Iya fadanci hada Kiranta da
aunty, bai ta6a kiranta hakan ba sai yau da Allah ya jarabe shi da son sanin komai
dangane da Angel.

Tambayoyi ya tsare Aneelerh da su akan ta fada mashi dagaske yarinyar mutunce


bata haɗa jinsi da aljanu ba? Don shi gaskiya bai yarda da kyanta ba, Ya zarce na
jinsin mutane, tun da yake kallon indian film, da korean drama bai ta6a ganin
jarumar da ta kama ƙafar Yarinyar a kyau ba.

Aneelerh taci dariyar wautar Mahboob, har tambayar shi ta yi ko dai sonta ka ke
yi ne? Naji kanata zuzuta kyawunta, “ da sauri ya dafe ƙirjinshi da hannu Yana
faɗin”Sai kace dai bani da hankali aunty Aneelerh? Ae rijiya ba wurin gaɗar makaho
bane, Nasan ciwon kaina ban shirya yin jinya a gadon asibiti ba, ni kawai kyanta ne
ya ruɗe ni ba wani abu ba, tsakani da Allah yarinyar ba matar yaku bayi bace, ko
makaho ya shafa fuskarta zai shaida hakan tafi dacewa da Manyan ƴa’ƴan masu kuɗi
waɗanda suka jiƙe da naira, ni yanzu idan nace zanso ta, ko zan aureta, Aunty
Aneelerh ina zan samu kuɗin ɗaukar ɗawainiyarta? Kuɗin man shafawarta dana zuwa
saloon kaɗai sun isa su takaita jarin mutun balle ni da ba kuɗi gare ni ba”

tsabar dariya Aneelerh hada hawaye, shiko fuskarshi a daure yayi mata maganar bada
wasa ba, ya ƙara da cewa”ƙwara na auri ƴar talaka wadda ba ta da tsayin gashi, sai
yafi min sauki, in manna mata ƴar naira ɗari biyar taje gidan kitso ayi mata, man
shafawa a jiki kuma Ko vaseline na siya mata ya wadatar, Iya kuɗin ka iya shagalin
ka, Amma wannan Ifritun yarinyar wlh aunty Aneelerh duk talakan da ya aureta ya
cuci rayuwarta, yasin ni har kotu zan Iya kai ƙarar shi, ita kanta idan ta auri
talaka batayiwa kanta adalci ba fisabilillahi.

Lamarin mahboob sai addu’a, Haka ya dinga santin kyan Angel, Har faɗi yake shi ya
kosa A gano su, in sha Allah zai tayasu da addu’a akan Allah ya bayyanar dasu,
burinshi idan Allah yasa ta dawo gidansu da zama zai zama na hannun damanta saboda
idan ta auri basarake ko wani mai ji da naira, ya dinga samun ƴan canjin kashewa.

Saboda Angel Ya manta da zancen neman zoben shi, gaba ɗaya ya ɗaura burin duniya
akan Angel, harya fara ƙiyasta kuɗin da zai tatsa wurin Mijin da zata aura.

Daƙyar Aneeleerh ta samu mahboob Ya fita daga ɗakinta, ya addabeta da zancan


kyawun Angel.

Alhamdulillah, a yau labarin 6acewarsu Angel ya dawo tamkar sabo a shafukan sada
zumunta, ta ko’ina buga labaransu Akeyi tare da hotunansu, tun da Ont suka fara
yaɗa labarin nan take sauran gidajen jaridu suka bubbuga labaran da gidan radio. Ta
ko’ina zancen su akeyi kamar yau abun ya faru, labari ya dawo sabo, Yanzu shine Top
story dake trending a social media, mafi yawan mutane Kyawun Angel ke ruɗarsu har
su kaiga ɗaukar labarin su karanta sannan suyi share ɗinshi don ataimaka a gano su.

Fuskar Aneelerh tun safe da annuri akanta, Mutane sai kiranta sukeyi awaya
sunayi mata jaje haɗi da tambayarta wasu bayanai da suka danganci Angel, a ƙarshe
sunayi mata fatan Alkhairi, Numbobinsu ne akan labaran da akayi share nasu shiyasa
mutane ke ta kiransu suna yi masu jaje.

Ta natsu saman mirror chair, turkish gown ce a jikinta launin maroon tayi bala’en
yi mata kyau, babu mayafi akanta zallar sumar kantace
Hannunta na aruke da wayarta, tun ɗazu take maimaita karanta labarin su Angel da
akayi posting ɗinsa a shafin Ont na insta

“Mommy” muryar junaid ce ta janyo hankalinta ga kallonshi, ta cikin mirror,


Hajiya adama tayi mashi gayu don yau ma a ɗakinta Ya wuni, ita tayi mashi wanka,
tasa Aneelerh ta kawo mata kayan shi ta santa mashi jeans da shirt fara, sumar
kanshi tasha gyara.
Ƙarasawa yai gaban kujerar da take a zaune, ya daura kanshi saman laps ɗinta,
ƙamshin turaren jikinsa na Hajiya adama ne da ta shafa masa
‘Wow my baby boy, kayi min kyau sosai, lallai granny ɗin nan taka tana matuƙar
sonka irin wannan gayu haka da tayi maka”

Ɗaura wayar tayi gaban mirror, ta sanya hannu biyu ta ɗago da junaid ta ɗaura
shi saman laps ɗinta, langwa6ar da kanshi yai saman kirjinta

“Mommy namanta ban faɗa maki ba, jiya wani mutun ya kira awaya har yace wai in
faɗa maki....” katse shi tayi”yaushe aka kirani? Bana son ƙarya fa”
Muryarshi da shagwa6a ya ce “mai ƙarya fa ɗan wuta mommy, ni dai Allah ba ƙarya
nake maki ba” miƙa hannu Aneelerh tayi ta ɗauki wayar, tana shiga call logs tayi
arba da New number da aka kira kuma an ɗaga kiran.
“Junaid bana hanaka ɗaga min kira ba”?
Zumbura mata maki yai’to ai nayi tunanin Angel ce ke kira, kuma baki a ɗakin
shine na ɗaga, kuma yace in kai maki wayar ku yi magana ni kuma naƙiya nace sai dai
ya faɗamin in gaya maki” tun da ya fara magana ta ƙura mashi ido tana kallon shi,
komai nashi burgeta yake yi, musamman in yasanya shagwa6a a maganar shi.

“Meyasa baka kawomin wayar ba”?


Ƙura mata ido yai ba tare daya furta kalma ba
Sam hankalinta bai kwanta da baƙuwar number da ake yawan kiranta da ita, tuntuni
take ganin missed calls daga Number taƙi yarda ta ɗaga kiran don har yanzu bata
daina fargabar mutanan nan da suka ɗauketa da sunan jami’an sirri.

“Junaid, daga yau karka kuskura ka ƙara ɗaga min kira kaji ko”? Ɗaga mata kai Yai
alamar eh, tace”yanzu zan sanya number ɗin a black list, hankalina zaifi kwanciya’
ta yi maganar a yayin da take cigaba da daddana wayar hannunta, blocking number din
tayi saida ta kammala baby junaid yace
“Mommy namanta ban gaya maki ba yace wai in faɗa maki daddyn um am....” natsuwa
ta yi tana kallon shi,
“What”? Shine yace min wai ince maki daddyn ummm...” sam ya kasa tuna sunan duk
ta ƙagara da sonjin ƙarashen sunan
“Kai nake sauraro ka fadamin mana”
“Wai ma daddyn.....” girgiza kai ya ɗanyi”mommy kaina ya cunkushe na manta, idan
na tuna zan gaya maki”

Murmushine shimfiɗe saman la66anta, Idanuwanta akan face dinsa

“Shikenan My baby boy, yanzu faɗa mun Ina ka 6oye zoben Mahboob? Na duba cikin
rigar pillow ban ganshi ba, yakamata mu maida mashi abunsa kada ayi mana kallon
6arayi”

Gatsina mata hanci junaid yai haɗi da murmura idanuwanshi yace”tab ae Allah
bani bashi, Na angel ne na 6oye shi wani wuri inda ba wanda ya sani, Allah Angel
zan baimawa shi, kuma kada ki fada ma kowa in baki so mu 6ata dake,”

Dariyace ƙumshe abakinta”kai junaid babu kyau fa, da guminsa ya sayi zoben taya
zaka ce ba za ka bashi ba? Kana so Angel ɗinka ta sanya abun sata? Kayan haram da
ba mallakin ka ba?
Girgiza mata kai yai”a’a mommy, to ai bani da kuɗin da zan siya mata wani”

Shafa sumar kanshi tayi”mommynka tana da kuɗi, zan siya maka wani but pls ka
maida ma mahboob zoben shi kaji my boy”

Ɗaga mata kai yai”Toh zan maida mashi badan halinshi ba, kuma Allah idan ya ƙara
cinye min chocolate ɗina saina sanya shi kuka” fashewa Aneelerh tayi da dariya, ba
ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.
*DAULAR ALHAJI MUSA*

Ya kasa fita ko da ƙofar ɗakinsa ne, tun jiya da ya zo gidan baƙunta yake yi masu,
fitowa yai daga Cikin bathroom jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, ya ɗaure
igiyarta a tsakiyar cikinsa daga can ciki akwai short da ya sanya, sumar kansa ta
manne ma fatarsa saboda lemar ruwan wankan daya jiƙata, Dr shureim ba dai kyau ba,
ta ko’ina sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikinsa, ya ji daɗin dawowarshi gidan uncle
ɗinsa baida wata damuwa, musamman tarbar da ya samu awurin Hajiya sarah, ta nuna
farin cikin ganinshi kamar ɗan cikinta haka take tarairayarsa.

Walking slowly ya nufi dressing mirror Don Ya kimtsa kanshi

Gyaran muryar da aka yi mashi ne yasa shi yin saurin juyo wa baya don ganin
wanene

Lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya yana kallon uncle ɗin nasa
Yana daga tsaye bakin ƙofa, kayan gym ne a jikinsa, short da riga sun ɗame
jikinsa, mutumin akwai ƙira kamar ɗan wrestling.

Da fara’a akan fuskar shureim ya furta”My Uncle” yai maganar yayin da yake
tunkarar shi, gabanshi sai faɗuwa yake yi ya rasa gane dalilin dayasa a duk lokacin
da ya yi tozali da uncle din nashi sai yaji faduwar gaba.

Kyakkyawar fuskar Alhaji musa, mai ɗauke da ƙayataccen saje, ba murmushi sai dai
yaɗan sakar mashi fuska.

“Fushi nakeyi da kai shureim baka iya takowa kazo ɗakina ka gaishe ni, ko dama
jira kake inzo room ɗinka”? Cike da izza da nuna isa yake yin maganarsa.

Yawu shureim ya haɗiya”ba haka bane uncle, yanzu nake ƙoƙarin zuwa part ɗin naka”

Yamutsa fuska Yai”okey, nima na fadi ne kawai ba don wani abu ba, ko akwai abun
da ka ke buƙata”?

Girgiza kai shureim yai”a’a aini ka gama min komai kawuna, nagode sosai da
kulawarka agareni, Allah yabarmun kai” matsawa Alhaji musa yai dab dashi, Ya
janyoshi a jikinshi yai hugging nashi tightly, in a whisper ya furta”idan akwai
abun da kake buƙata ka sanar dani, idan ma baka Iya fadamin ka tura min ta text
message, sannan akwai saƙo da za’a kawo maka zuwa anjima, ya ƙarasa maganar tare da
raba jikinsu daga na juna.

Still face din Uncle musa ba fara’a, haka Allah ya halicce shi baida sakin fuska.

“Nagode sosai uncle, tun jiya da nazo gidan nan akayi min kyakkyawar tarba naji
daɗin Hakan sosai”

“Shureim ba’ayi min godiya, next time kada ka ƙara” fuskarsa a ɗaure yai
maganar
Cikin jin shakkar shi shureim ya furta”in sha Allah” ya ƙara da cewa”burina ka
canza rayuwarka shureim, banason ganinka acikin damuwa, kaman ta duk wani abun da
ya faru a rayuwarka, shiyasa na dawo dakai gidana saboda nasan zaka fi samun
kwanciyar hankali, sannan Inaso naji ra’ayinka, bance ka bani amsa yanzu ba, nafi
so sai ka natsu kayi nazari tukunna.

Jinjina kai shureim yai, idanuwanshi na kallon ƙasa, saboda ƙwarjinin alhaji musa
bai iya jurar kallon fuskarsa.

“Bazan hana Ka Yin duk wani abu da za ka yi don jin daɗin rayuwarka ba, sai dai
ban goyi bayan zamanka a cikin gida ba aiki ba, abu na biyu kuma Aure, kasan shi
sunnah ce ta manzon Allah SAW, Aure yana ɗaga darajar mutun yazamto mai cikar
kamala da natsuwa, rayuwarka zata canza idan ka yi aure, Na gaji da ganinka a
matsayin tazuru” Yai maganar yana ɗaga mashi gira, da zolaya akan fuskarshi,
kunyace ta hana shureim furta komai, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, Yana jin
nauyin uncle din nasa.

“Da ace kayi aure da wuri da yanzu mun samu ƙaruwar babies” da sauri shureim Ya
juya mashi ƙeya ya rasa ina zai tsoma ranshi, hakan da yai ba ƙaramin nishaɗi yaba
kawun nashi ba
“Zeenatu ta shigo kun gaisa”? Muryarshi ƙasa ƙasa ya amsa mashi da”eh jiya tazo”

“Okey, pls, shureim inaso kana taimaka mata, Kuna fita yawo atare, still ƙanwar
taka bata canza ba, sam bata da natsuwa, ni ban ta6a ganin mahaddaciyar ƙur’ani
mara natsuwa irinta ba, zaka ga duk min rashin natsuwar mutun indai yana yawan
karanta al’ƙur’ani natsuwa na shigarshi amma ita kullum abun nata ƙara gaba yake
yi”

A hankali shureim Ya juyo ya kalle sa, mamakine ƙarara akan fuskar Shureim wai
yau shine kawu musa keyi ma magana har haka? Mutumin da bai Iya surutu ba.

“In sha Allah uncle, zanyi ƙoƙari wurin ganin na taimaka mata, “ gyaɗa kai
yai”haka nakeson Ji, Ni zan shiga Ciki, idan ka yanke shawara game da abunda na
faɗa maka, ka same ni a ɗaki ka sanar dani ko kuma ka kirani awaya”

Amsa mashi yai da toh, sallama Uncle musa yai mashi kafin ya fuce daga dakin

Ajiyar zuciya shureim ya sauke, hannun shi ɗaya dafe da ƙirjin sa.

Lokaci ɗaya zuciyarshi ta fara tariyo mashi haukan zeenatu na Jiya, murmushin
gefe fuska ya saki, aranshi ya ayyana ko ta na ina yanzu, yasan zai yi wuya ta jure
rashin ganinshi.

Ai tun Jiya data bar ɗakinshi Cikin sanɗa ta nufi ɗaki akan hanya suka ci karo
da Tani, Abunka game saurin kuka nan take ta ƙware mata baki tana kuka ta faɗa mata
abunda ya faru

Lallashinta tani tayi tana fadin to menene aciki, Ki kwantar da hankalinki dr


shureim dai ɗan uwanki ne ba wani bare ba, yanzu bari na baki mayafi na ki ɗaura a
qugunki, ni kuma zanje ɗakin nashi in ɗauko maki zanin, Ai mantawa nayi ban baki
undy kin sanya ba jiya, ke kuma baki tuna min ba,”

Cikin shessheƙar kuka take faɗin Na tsani kaina Tani, bani da hankali, sai yaushe
ne zan daina hauka, sam bani da natsuwa, meyasa na kasance haka”? Cikin kwantar da
murya tani tace”karna kuskura na ƙara ji kince haka, in banda abunki ma, meye na
damuwa?, Haka Allah ke son ganinki, don haka ki share hawayenki, ai ni wlh ba
ƙaramin burgeni kikeyi ba saboda kina da hankali, dayawa wasu ƴa’ƴan masu kuɗin
basa girmama ƴan aikinsu amma ke kin ɗauke mun tamkar iyayenki, shiyasa nake ƙara
ƙaunarki”

“Tani ba zaki gane ba, ni duk ba wannan ba, Yaya shureim bazai ta6a ɗauka na a
matsayin mace ba, idan har ban daina wannan haukan ba” tsabar kukan da takeyi make
up din fuskarta ya ca6e mata, jan bakin har saman kumatuntu.

Ɗaura mata Mayafi Tani tayi asaman waist dinta, tace”ki koma ɗaki, zan shigo muyi
magana” ta amsa mata da toh, ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
A daren ranar daƙyar Tani ta lallasheta, ta kwantar mata da hankalinta akan
tadaina cewa ta tsani kanta saboda yarda Allah ya halicce, kowa da irin tashi
ƙaddarar, bawa bai ta6a zama 100% batare da an samu naƙasu atare da shi ba. Sannan
Idan saboda yayanta shureim ne takeyin kuka waya fada mata rashin natsuwarta zai
hana shi sonta? Wata’ƙil ma haukan nata ne zai ƙara mashi ƙaunarta, don shi so babu
ruwan shi da yanayin mutun abu ƙalilan ke haifar dashi indai mutun ya kasance
ƙaddararka.

Kafin Tani tabar ɗakin sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali tukunna ta
fuce, tsakar dare Zeenatu ta farka, ta shige toilet ta ɗauro alwala kamar yarda ta
sama tashi yin nafilfilin dare, yawanci addu’arta duk akan Allah ya bata natsuwa
take yinta, abun yana damunta.

(Abunda Ya faru a daren Jiya kenan bayan zeenatu ta baro ɗakin Dr shureim)

Tun safe baiwar Allah taƙi fitowa daga ɗaki, tarasa ya zatayi, kunyar duniya ta
ishe ta, aƙarshe ta janyo al’ƙur’ani ta cigaba da karantawa, har rana ta fito
tukunna Ta ajiye shi ta shiga bathroom tayo wanka, ta fito ta sanya doguwar riga ta
zura hijabi maroon har kasa, ko make batayi ba, cikin sanɗa ta fito daga ɗaki tana
tafiya tana waige waige kamar wata munafuka, a haka ta ƙaraso part din daddynta.

A lokacin bai jima da fitowa daga wanka ba, tun bayan da ya baro room din
shureim, Ya dawo nasa ɗakin, Jallabiyace a jikinsa launin milk mai kyan gaske, Yana
daga kishingiɗe saman doguwar sofa ta cikin katafaren ɗakisa, tsayawa zayyana
kyawunsa 6ata baki ne hankali ma bazai ɗauka ba.
Ya ɗaura kansa saman pillow, Yayin da apple laptop ɗinsa ke a saman flat tommy
ɗinsa.

Idanuwanshi suna a lumshe ya natsu yana kallon wani abu a laptop din nasa, ga
dukkan alamu video call ya ke yi, sautin muryarshi baya fita yayi low sosai, yana
magana eyes dinshi suna lumshewa.

Kusan sau Uku zeenatu tana ƙwala mashi sallama baiji ba, saboda hankalin shi
baya atare da shi.

Tasan baison ashigar mashi room batare da an nemi izininsa ba.


Jin shiru bai amsa mata ba, Yasa ta haura ƙafa ta shiga ɗakin tana tafiya babu
natsuwa sai faman zumbula sauri take yi burinta kawai ta ƙasa gare shi, duk da
fargabar shi da take ji.

Cikin rashin sa’a, garin sauri hijab ɗin ta da ke ja da ƙasa Ta harɗe ƙafarta
ɗaya, wani irin sul6i ne ya kwashe ta, gaba daya ta rubza saman Sofa table din
gabanshi, wanda ke ɗauke da Cup na coffee mai zafi da aka ajiye mashi, gaba ɗaya
Cup din Yai tsalle Ya fada mashi ruwan ya wanke Laptop dinsa da gaban
jallabiyarshi, zeenatu kuwa tunda ta kife saman sofa table din bata ɗago ba,
jikinta sai kakarwa yake yi hankalinta idan yai dubu to ya tashi, zufa ta ko’ina
take tsastsafo mata, duk da sanyin A.c ɗin ɗakin. ko gizau baiyi ba idonshi akan
keyboad ɗin laptop nashi da ruwan coffee ya jiƙa, Tashin hankalin da ba’a sama shi
data🤣

*Boss Bature✍️ Mu haɗu gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

~Middle step~

_The Prisoners E19🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

In a smoky voice ya furta”I’ll call you later.” da mutumin da su ke yin video call
ɗin da shi ya ke magana. Tun kafin ta ɗago da kanta cikin shessheƙar kuka ta ke
faɗin”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Am sorry daddy, nayi kuskure bani da
hankali, dan Allah ka yi haƙuri wlh bazan ƙara ba” lumshe idonshi ya ɗan yi kafin
gently ya sauko da ƙafafuwanshi ƙasa, Hannun shi tallabe da laptop ɗinsa, ko kaɗan
bai ji zafin ruwan da ya hau saman jikinsa ba.

Zeenatu ba ta dai na yi mashi magiya akan ya yi hakuri ba, hankalin ta duk yabi ya
tashi saboda mugun tsoran daddyn nata ta ke ji.

“Daddy na tuba bazan ƙara ba, Ka yafe min nagane kuskure na” tsoro Ya hana ta
ɗago su haɗa ido.

Miƙewa yai daga saman sofa ɗin ya juya ya nufi cikin Katafaren room ɗin nasa,
After some minutes sai gashi Ya dawo babu laptop din a hannunsa, Ya canza
jallabiyar jikinsa, ɗaura idanuwansa yai akan bayan zeenatu, dogayen yatsun
hannunta sai kerma suke Yi.

Agaban Sofa table ɗin Ya dakata da yin tafiya, da kakkausar murya yace”Ke! Miƙe
tsaye tun kafin ran ki ya 6aci” Jikinta na kerma ta ɗago da kanta hawaye sun wanke
fuskarta sharkaf, abunka ga farar fata face ɗin ta yi jawur, Blue eye balls dinta
sun ciza launin su idon nata ya rune, small pink lips ɗinta tsabar ƙarantarsu
tamkar na jariri.

Cikin rashin natsuwa ta zube saman gwiwowinta, Idanuwanta na kallon tiles ɗin
ɗakin
“Dad...am sorry bazan ƙara ba, nasan bana jin magana bani da natsuwa amma ka yafe
min, kada ka hukun......”

Gigitacciyar tsawar da ya daka mata ce tasa ta yin saurin toshe kunnuwanta da tafin
hands dinta

A razane take faɗin “Na shiga uku daddy, nace maka bazan ƙara ba, Nagane kuskure
na”

Muryarshi a kausashe Ya furta sunanta”Zeenatu? Sau nawa ina gargaɗin ki akan ki


daina faɗo min ɗaki ba tare kin nemi izni na ba? Waya baki iznin shigowa ciki”?

Wahalallan yawu ta haɗiya, idanuwanta sunyi luhu luhu sai faman wurwurga eye
balls ta ke Yi kamar ƙwayar zata faɗo ƙasa.

“Am sorry dad...” katse ta ya yi”Kin Iya tsallan kwaɗi?” tun da ya fara magana
bata bari ta ɗago sun haɗa ido ba sai Yanzu da ta ji yace Tsallan kwaɗi

A hargitse ta zare mashi manyan idanuwanta


A matukar ruɗe take girgiza mashi kai”daddy bazan Iya ba, Ni bansan yarda
akeyi ba, ai nace ka yi haƙuri bazan ƙara ba”

Gyaɗa kai Yai”Tashi ki fuce ki bani wuri shashasha, daga yau karki kuskura ki
ƙara faɗo min ɗaki”

Zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, duk sai ta ji ba daɗi, ba ƙaramin kewar daddyn
nata tayi ba, maimakon Ya nuna farin Cikin ganinta saima korar ta da yayi.

Ganin yarda ta tsare shi da ido taƙi motsawa ne Yasa shi daka mata tsawa”nace ki
tashi ki fuce min daga ɗaki tun kafin In yi ball dake” fuskarshi a haɗe Yai maganar
ba annuri.

A gurguje Zeenatu ta miƙe ta juya tana tafiya Jikinta na kakarwa har Ta kai bakin
ƙofar fita ɗakin, ta ji ba za ta iya jure fushin daddynta ba, tasan duk akan
kuskuren da ta yi mashi ne.

Yana atsaye ya goya hannayenshi saman faffaɗan kirjinshi Ya natsu Yana kallon
Bayanta, Har ta kusa fucewa daga ɗakin A lokacin Ya juya zai shige ciki ba zato ba
tsammani ya ji an rungumeshi ta baya, ƙanƙameshi ta yi tana faɗin”wlh daddy ba in
da zan je, ai na faɗa maka kuskure ne bada sani na na 6arar maka da coffee,
yakamata ka yi haƙuri ka yafe min, Ni banason kana fushi dani saboda kai mahaifina
ne, kuma inason ka sosai bazan Iya jurar fushin ka ba”

Har cikin zuciyar shi ba ƙaramin sanyi ya ji ba, kalaman zeenatu sunyi matuƙar
kashe mashi jiki, Ba tun yau ba duk idan ta 6ata mashi rai ko ya kore ta daga
ɗakinsa ba ta tafiya shiyasa yai mata hakan don ta ga ne kuskuren ta yasan dole ta
dawo ta bashi haƙuri.

Da hannu ɗaya ya ruƙo hijabin jikinta Ya janyota zuwa gabanshi, Ya kwantar da


kanta saman chest ɗinshi, A hankali ya ke ɗan bubbuga bayanta da hannayenshi cikin
sigar lallashi, hakan da yai mata ba ƙaramin kwantar mata da hankali yai ba, harta
fara samun natsuwa.

Tsawon mintuna kafin ya raba Jikinshi daga nata, fuskarta jawur idanuwanta har
sun ɗan kumbura.

“Kin 6ata min riga da hawaye” tana faman zazzare ido ta furta”am sorry”

“Is okey, kinsan banason ganin hawayenki, meyasa kike min kuka”?

“Daddy ai kai ne ka sani yin kuka, Ina baka haƙuri kaƙi ka saurareni”

“Zeenatu ɗago ki kalli Cikin idona” daƙar ta Iya ɗagowa ta sanya idonta cikin
nashi gabanta Ba ƙaramin faɗuwa yai ba saboda ƙwarjinin da yai mata.

“Bansan meyasa ki ke jin tsorona ba, Nifa daddynki ne, saboda kawai kin 6arar min
da coffee shine duk kika ɗaga hankalin ki? Ni shine abunda Ya 6ata min” fuskarshi a
ɗaure tamau yai mata maganar.

Muryarta na ɗan rawa ta furta”dad..dy ai kai ne baka dariya ko murmushi ba ka yi


min kullum fuskarka a ɗaure, kuma baka son ina zuwa kusa da kai, nasan saboda
rashin natsuwata ne amma in sha Allah daddy zan daina, ina yin addu’a ma har tsakar
dare Akan Allah ya yaye min...” Yatsan Hannun shi ya daura saman lips ɗinta

“Ya isa haka, Karki kuskura na ƙara ji kin ce bana son kina zuwa kusa dani, kinji
ko? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh

Mayar da ita Yai saman chest ɗinsa, Yaci gaba da shafa bayanta Yana ƙara
lallashinta.

A haka Hajiya sarah ta riskesu, a bakin ƙofar shiga room ɗin nashi taci burki,
farar mace alkebbar mata doguwar riga ce a jikinta fitted gown ta lace, Kusan rabin
ƙirjinta awaje Yake, Tubarkallah na shanunta atsaitsaye su ke, tamkar bata ta6a
haihuwa ba, light make up ne akan fuskarta, Ƙafafuwanta na sanye cikin High hills,
sun ƙara mata tsayinta. Babu mayafi akanta zallar sumar kantace tasha ado tsabar
haɗuwarta tamkar budurwa.

“May I come in”? Muryarta har cikin kunnuwansu, Alhaji musa ne ya bata Iznin
shigowa ciki, ɗagowa zeenatu ta yi daga kan chest ɗinsa, Muryarta na ɗan rawa ta
furta”daddy zan tafi”

“Da iznin wa”? Ya jefa mata tambaya, shiru ta yi tana ƴan kame kame, Sam ba ta son
mommynta ta shigo ɗakin daddynta idan tana aciki.

Ƙarasowa Ciki Hajiya saratu tayi, kaitsaye ta nufi Alhaji musa, fuskarta ɗauke
da ƙayataccen murmushi take duban su shi da zeenatu.

“Masha Allah, Uba da ƴarsa kunyi kyau fatan ban takura maku ba”

Zeenatu ce tai saurin cewa”Mommy, na shigo gaida daddy ne dama, yanzu zan tafi”
kallon da Alhaji musa Yai mata ne yasa ta yin saurin canza magana”A’a ba yanzu zan
tafi ba, sai daddy ya bani iznin tafiya”

Ta yi maganar tare da samun wuri saman sofa ta zauna, Jikinta nata yin kerma acan
cikin zuciyarta addu’o’i take karantowa.

Matsawa Hajiya sarah Ta yi dab da shi, duk da shakkarshi da ta ke ji hakan bai


hanata nunawa mijin nata soyayya, tarairayarshi ta ke yi kamar sabon jinjiri ta
haka ta ke iya samun damar Iya sarrafa shi.

Hannayenta ta ɗaura saman waist dinsa, Daddaɗan ƙamshin turarenta tuni ya fara
Kashe mashi jiki.

“Baby, jiya ka hana kowa yazo kusa da kai, kuma ina buƙatar ka, Na kwana da son
kasancewa atare da kai” cikin harshen turanci ta ke yi mashi magana, gogan naka
babu fara’a akan face ɗinsa ya ƙame a tsaye kamar soja.

“Zeenatu, ta shi ki je ɗakin Yayanki shureim, Tani ta faɗa mini tun safe ba ki ci
abinci ba, nayi mata magana ta shirya mashi abincin aɗakinsa, Za ki Iya zuwa can
kuci atare da shi”

Kamar Jira ta ke yi mommyn ta yi mata magana, da sauri ta miƙe ta nufi hanyar fita
daga ɗakin Har Allah Allah take aranta, saboda bata son ganin Iyayen ta suna yin
romancing din junansu agabanta Kunya take ji kuma hakan Yana jefata wani hali.

Baya fitar Zeenatu ta dawo da dubanta akan fuskar shi.

Muryarshi a kausashe Ya furta “Baki da kunya? Baki ga me kika ruƙe min ba ne”

Kashe mashi ido ɗaya tayi muryarta da kwarkwasa ta furta”kaine ka koyamin rashin
Kunyar,” hakan da tayi mashi ba ƙaramin jefa shi yanayi tayi ba, dama Shi mutunne
da baya wasa da duk wani abu da jikinshi ke buƙata.

“Yanzu ina da aikin da zanyi, Da anjima zan neme ki” marairaice mashi fuska
tayi”A’a baby, yanzu nake buƙatarka ni, kusan 3 days baka atare dani, bazan iya
jurewa ba.”

Yamutsa fuskarshi Yai, Kafin Yai yunƙurin ƙara furta wata kalma, tayi saurin zame
wuyan rigar jikinta, Ba ƙaramin shammatarshi tayi ba, gaba ɗaya ya rasa sukuni,
Baisan ya akai ba ya tsinci kanshi asaman gado sun tsunduma suna Korar shaiɗanu,
Suturar jikinsu A saman floor na tsince su bansan ina zan kaisu ba, Laundry ko
toilet? (🤣 wato duk izzar namiji sai in bai haɗu da mace ba)

Tuni Dr shureim Ya kammala shiryawa, Ya canza suturar jikinshi, still Arab


dress ne, kayanshi na gado, Yana daga zaune gefen gadon shi, Hannun shi ruƙe da
Wayarshi Yana kallon hoton abar ƙaunarsa da ya buɗo a gallery.

Ba zato ba tsammani Yaji Muryar matashin saurayi Yana Kwaɗa sallama daga bakin
ƙofar ɗakinsa, slowly ya ɗago da ido yaɗan Juya yana kallon Saurayin dake sanye
cikin black suit, dogo kuma faffaɗa, Hannun shi ruƙe da Ƙatuwar shopping back mai
ɗauke da sunan *Obinna tech*

A sukwane Dr shureim ya ɗaura wayarsa saman mattress Ya yunƙura ya miƙe Still


idonshi akan mutumin.

“Dr shureim Barka da warhaka”


Muryarshi babu natsuwa ya furta”yawwa barka dai” duk yasha jinin jikinshi saboda
mutumin babu fara’a akan fuskarshi kamar wanda aka ɗaurawa aure da mutuwa.

“Saƙo ne daga Uncle ɗinka” nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tunawa da saƙon da
uncle musa Yace za’a kawo mashi.

A hanzarce ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, Ya miƙa hannu biyu ya kar6i kayan daga
hannun mutumin haɗi da yi mashi godiya.

Fuskar shurem ɗauke da murmushi ya nufo cikin ɗakin, A saman gado Ya ɗaura
shopping back ɗin, Bayan yayi bismilla, Ya buɗe ta tare da zura hannu Ya zaro kayan
dake aciki, har saida gabanshi Ya ɗan faɗi.

Apple laptop ce, tare da Apple watch, abu na ƙarshe da ya gani Unexpected
Danƙareran Key ɗin Mota, Zubewa yai saman gwiwowinsa agaban Kayan Yana duban su, A
tsanake Ya ke ƙare masu kallo, haƙiƙa Yayi farin Cikin Kyautar nan da uncle musa
yai mashi ya ji daɗi sosai, ɗaga Hannayenshi sama Yai, Ya soma jera addu’o’i Yana
yiwa kawunsa bisa irin farin cikin daya Sanya shi ayau, Ya faranta mashi sosai.

Bai gama shan mamakin Kayan ba, Muryar mutumin da ya kawo Kayan ta katse mashi
addu’o’in da ya ke yi.

“Dr shureim Zan iya shigowa Ci ki?


Da sauri Ya miƙe tsaye Yana kallon shi.
Manyan Akwatuna ne guda Biyu a hannun shi ya ruƙe handle ɗinsu Yana Jansu irin
masu tayoyin nan.

“Bismillah” yai mashi nuni daya shigo Ciki, Bayan ya shiga Cikin ɗakin agaban
tafkekiyar Glass wardrobe ɗin ɗakin mai faɗi Ta mamaye bangon da take a jikinsa,
Anan mutumin Ya dakata da yin tafiya ya buɗe akwatunan, Farin Ciki Ya hana dr.
shureim Rufe bakinsa.

Arab dress ne kala kala Na maza, Kalar waɗanda Yafi so, A ƙalla sunkai kala
Hamsin sababbi fitigil dasu shaƙe cikin akwatin, Hada Arab turban ɗin da Yake
naɗawa akanshi.

Atare da mutumin suka soma jera kayan acikin wardrobe ɗinsa, Bayan sun kammala
jera kayan, Man ɗin Ya buɗe ɗayan akwatin Wa’iya zubilla Uncle musa Ya gwangwaje
ɗan nasa da Haɗaɗɗun leather shoes da tsadaddun turarurruka Na Larabawa, Da suran
Kayayyakin amfani na gyaran Jiki, a gaban mirror suka jera Kayan, Bayan mutumin Ya
kammala, Dr. shureim yai mashi godiya suka Yi sallama da shi.

Yana atsaye idonshi akan sabbin Kayanshi sai binsu ya ke yi da kallo, daɗi kamar
wanda akayiwa albishir da gidan Aljanna.

Muryar Tani ce Ta janyo hankalin shi ga dubanta.

A yayin da ta ke shigowa ɗakin nashi

“Dr shureim barka da rana, Fatan Ka wuni Lafiya? Ya kwanan gidan uncle ɗin naka”

Hannunta biyu ruƙe da Faffaɗan wooden tray, daga saman shi jerin lunch ɗinsa ne.

Da fara’a akan face dinsa Ya soma Amsa mata gaisuwar”Alhamdulillah, Fatan kema
Kina Lafiya ya aiki”?

“Lafiyalou, ai Munji daɗin zuwanka gidan nan, Ko ba komai zaka ɗebe ma Zeenatu
kewa, Baiwar Allah jiya tayi murnar zuwanka, Tana matuƙar son yayanta” Fuskarta
awashe Ta yi maganar, adai dai takai gaban table ta ɗaura mashi tray ɗin.

Murmushin gefen fuska Yasaki tare da faɗin”Allah sarki, Tun Jiya bata ƙara
dawowa ɗakina ba, Idan ba damuwa ki kira min ita idan kin fita, nasan saboda Kunyar
abunda Ya faru Jiya ne Yasa ta kasa zuwa gaishe ni da safe”

“Wlh kamar ka sani, abunda ya hanata zuwa kenan, ai zeenatu akwai kunya,
Yarinyar kuma tana da mutunci ga kamun kai, Ga ilmi, ita dai taji daɗin rayuwarta,
Gaskiya ba ƙaramin mai sa’a bane zai mallaki Zeenatu” tun da Tani ta fara Yi mashi
sambatun Kyawawan halayar zeenatu Ya natsu Yana sauraranta haɗi da kallonta, Ya
fahimci so ta ke Yi, Ta yi mata gyaran hanya awurin shi. Dama tun Jiya da yazo
matar take ta yi mashi sambatu akan zeenatu.

“Idan badamuwa, inason Ganinta” washe baki Tani ta yi”Toh, yanzun nan zaka
ganta,” Da sauri Ta juya ta fuce daga ɗakin.

Tattara Kayan saman gadonshi yai, acikin Shopping bag ɗin Ya tura su.

Ajiyar zuciya ya sauke Ya koma gefen gadon shi ya zauna yana jiran ƙarasowar
Zeenatu.

Akan Hanya Tani taci karo da zeenatu tana tafiya kamar munafuka, sam babu natsuwa
atattare da ita, sai ƴan waige waige take Yi, har sai da suka bangaji juna da Tani
tukunna ta zabura ta kalleta suka haɗa ido
“Ina kika shiga ne?”

“Ɗakin daddy” ta bata amsa


“Hawayen menene akan fuskarki! Waya ta6amin ke” zumbura mata Baki Ta yi ba tare da
ta bata amsa ba.

Ruƙo hannunta Tani tayi”Muje ɗaki ki gyara fuskarki, dr shureim ne yace in kira
mashi ke” waro ido waje tayi jin ance Yaya shureim ke kiranta.

Jiki na rawa Tabi Tani suka nufi falo abakin stairs suka hau elevator takai su
Second floor, Bayan sun fito da sauri suka nufi ɗakin zeenatu, sai da Tani ta jira
tayo wanka tukunna ta taimaka mata wurin canza Kayan jikinta, Pakistan ta sanya
riga launin blush pink har gwiwa, Tare da burgujejan wando Fari anyi mashi adon
stones, Tani ta ɗaura mata Mayafi akanta, Babu makeup Iya kyawun fuskarta ne.

Flat shoes Ta zura a ƙafarta, Atare da Tani suka baro ɗakin Bayan sun sauko down,
sai da Tani taja mata kunne akan ta natsu kada Tayi mashi hauka, ta amsa mata da
toh.

A hankali take Yin tafiya tana nufar sashen room ɗinsa, a bakin ƙofar ɗakinshi ta
la6e tana leƙensa Yana zaune idonshi akan screen ɗin wayarshi, Ya natsu Yana kallo
ko motsi bai yi, Kunyace ta kama ta, muryarta
Ƙasa ƙasa take ambaton sunanshi”yayana rabin raina” shiru dr a
Shureim bai amsa mata ba

“Hubbyna” still shiru, da alama bai ji sautin muryarta ba.

Tunani ta soma yi ko menene ya ke kallon acikin wayarshi wanda yai silar ɗauke
hankalinshi! Ras taji gabanta Ya faɗi sakamakon amsar da zuciyarta ta bata na cewa
wata’ƙil hoton girl friend dinshi yake kallo.

Cikin sanɗa ta ke yin tafiya cikin ɗakin nashi duk don ta gano abunda Yake kallo,
daga 6angare hannun dama na gadonshi ta zagaya tana yi mashi dogon wuya, ƙamshin
turarenta ne Ya tona mata asiri, lumshe idonshi yai yana tunanin a ina aka samu
fragrance me daɗin shaƙa a ɗakinsa, ɗagowar da zai yi keda wuya idonshi ya sauka
akan zeenatu dake leƙan wayarshi, da sauri ya danna power button hasken phone ɗin
ya ɗauke screen yai duhu.

Duƙar da kanta ƙasa ta yi, yanayin fuskarta ya canza”yaya shureim ɗina, ka wuni
lafiya? Am sorry Jiya ban dawo mun gaisa ba” A hankali Ya miƙe ya zagayo ta Inda
take atsaye dab da ita ya tsaya yana ƙare mata kallo.

Baisan ya akai ya tsinci kanshi da kallon wankan pakistan ɗin da ta ɗauka ajikin
ta, ta yi bala’en yi mashi kyau, Yarinyar kamar Fure haka take da ɗaukar ido.

Tabbas Idan yaci gaba da kallonta zai shagala ne

Acikin zuciyarsa Ya ambaci

“A’uzubillahi minasshaiɗanirrajim”

A fili kuma Yace”Zeenatu, kada ki damu bakomai, ay nayi maki uziri kece kika
takura kanki”

Muryarta da shagwa6a tace “Mommy ne tace inzo muci abinci atare, tun Jiya dana bar
ɗakinka banci komai ba” Ya rasa gane wani irin yanayi yake ji atare dashi, tana yin
magana blue eye balls ɗinta na jujjuyawa, Yatsun hannunta sai kerma sukeyi saboda
rashi natsuwarta.
Abu mafi jan hankali a jikinta ƙirjinta kamar zasu tsonewa mutun ido
“Ki jirani awaje”! Abunda Ya furta mata kenan
“Yaya shureim ba abinci zamuci atare ba”?
“Eh, amma ba’a cikin ɗakina ba, kinsan babu kyau mace da namiji su ke6e a ɗaki
ko”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh

“Bari na ɗauko mana kayan abincin sai mu koma dining room” tuna abunda ya faru
Jiyane yasa shi yin saurin cewa”No! Ni zan ɗauka,” amsa mashi tayi toh” Ya zagaya
other side ya ɗauko tray din Kayan abincin da hannu biyu ya ruƙo shi, yana agaba
tana bayanshi, a Haka suka ƙarasa cikin Haɗaɗɗen ɗakin Cin abincin gidan, Dining
tables har kala Uku, Kowanne a kewaye da chairs, a saman table Ya ɗaura masu tray
ɗin, suka zaune suna fuskantar juna, Hankalin shi ba ƙaramin kwanciya yai ba, A
inda suke Masu aiki Na iya hangensu daga main palour.

Sai faman sakar mashi murmushi take Yi

“Yaya shureim, zamu dinga fita yawo atare ko? Kaga kullum ina agida daddy baya
barina zuwa yawo, tun da na kammala secondry school kullum Ina agida” ta ƙarasa
maganar tare dakai hannu ta ɗauki serving spoon ta buɗe warmer ta Fried rice ta
zuba masu a plate Biyu, ta sanya masu spoons aciki.

Suna ci suna Yin fira ga lemunsu me sanyi a glass.

“Kada Ki damu, Munyi magana da daddynki, Yace yanason ina taimaka maki da wasu
abubuwan”

Washe baki Tayi”yaya shureim zamu fara fita shan ice cream da zuwa cinema? And
shopping ko”? Ɗaga mata gira yai alamar eh, cizon pink lips dinta tayi”Yaya shureim
Amma ka ta6a yin soyayya”? Ƙiris ya rage ya shake saboda surutun zeenatu, girgiza
mata kai yai”ban ta6a ba ke fa”?
“Maza dayawa suna haukan sona, Ni kuma nafison auran miskilin namiji, mai ilmin
addini dana zamani kuma Yana amfani da su, sannan me Koyi da sunnar Annabi Muhammad
SAW”

Tunda ta fara lissafa kalar namijin da takeso, dr shureim ya dakata da cin


abincinsa, Ya natsu yana kallon pink lips ɗinta, taƙi tsayar da idonta wuri ɗaya
Sai faman ƙeƙƙeftasu takeyi kamar babie.

“Yaya shureim kai fa watakalar mata ka ke son Aure” baisan sa’adda Ya


furta”ra’yinmu ɗaya” zare mashi ido tayi

“What”? Girgiza mashi kai tayi”amma yaya shurem idan ra’ayinmu ɗaya kenan bakason
mace me surutu? Mara natsuwa mai rawar kai haka”? Murmushi ya sakar mata har
dimples dinsa suka lotsa.
“Nidai nace Ra’ayinmu ɗaya” ya sake nanata mata maganarsa, murmushin gefen
fuska tasakar masa”indai dagaske Ra’ayinmu ɗaya da kai, Toni inason Namiji mai
surutu mara natsuwa mai rawar kai, kaga kenan Kaima kana son mace irin haka”

dariya ce ta kubce mashi, Harya shaƙe da abinci Da sauri ta miƙa mashi lemu Ya
kar6a Yana kur6a, Gwanin ban sha’awa haka suka cigaba da cin abinci tana Janshi da
surutu.

*DAULAR OBIE ESTATE*

A ɗakin Hajjaty, Kwance suke asaman gadon sun mannewa juna, Babu sutura a jikinsu
zufa duk ta wanke jikinsu tamkar A.cn ɗakin Bata aiki, tsawon awanni da suka gama
sharholiyarsu baccine Ya ɗauke su, Faɗaɗan tafukan hannayenshi ya cikasu da boobs
ɗinta, ƙafarshi ɗaya tana a tsakankanin cinyoyinta sosai Ya shigeta, Ahaka bacci
yai awon gaban dasu.
Sautin ringing ɗin wayarshi ne Yai silar farkawarshi, Idanuwanshi sunyi jawur
dasu, kasala duk Ta baibaye shi, daƙyar Ya Iya zame jikinsa daga nata, wani irin
mayataccen kallo yake binta dashi, ji yake kamar ya ƙara second round don Baya
gajiya da ita, matsawa yai saitin face dinta, ya kama lips dinta yai sucking dinsu,
kafin A hankali Ya zame tongue ɗin ya mayar saman nipples dinta sosai yai sucking
dinsu kamar zai karar dasu.

wayarshi sai ringing ta ke Yi yaƙi mayar da hankali kanta.

Jin Zafin abun da Yake yi mata ne Yai silar farkawarta, idanuwanta sunYi mata
nauyi muryarta a disashe ta furta sunansa”Pravin pls ya isa haka, Yakamata Ka tafi,
marece har Yayi, Nasan Hajiya saratu zata neme ka,”

ɗagowa yai da idonshi Ya kalli face dinta


“Kin gaji dani ne”? Girgiza mashi kai tayi”kaima ka sani bani gajiya da kai
pravin, da ace zan gaji da kai da tuni na rabu da kai” daƙyar take yin magana
idanuwanta na lumshewa har yanzu mayen shi ta ke Yi.

“Pls ka tafi pravin na roƙe ka”


Da kasalalliyar muryarshi yake yi mata magana”zanyi kewarki nasan idan Owais ya
dawo gidan nan ba ƙaramin takura zan yi ba, amma duk da hakan zanyi ƙoƙari ina
satar hanya ba tare da kowa ya sani ba zan dinga zuwa ɗakin ki kina rage min zafi’
harara hajjaty ta ɗan jefa masa”matarka fa? har mamaki nakeyi irin yarda kake liƙe
min bayan matarka tafi ni komai”

Ta6e lips dinsa yai’kada ki ce haka, arziƙi kawai zata nuna maki bayan haka bana
tunanin akwai wani abu da zata Iya finki dashi, sai dai ma ki fita.

“Amma kafi sonta akaina? Saboda Ta haifa maka ƴa’ƴa”

“Waya faɗa maki? Kema ai na samu ƙaruwa dake, sai dai Allah bai nufa zai yi
tsawaicin kwana ba, Ya rasu amma zamu sake haifar wasu idan kina so”

Tamkar ya fama mata raunin dake acikin zuciyarta, kifa kanta tayi saman
pillow, Hannu ɗaya ya ɗaura saman sumar kanta yaci gaba da shafa lallausan gashin
kanta.

“Its ok, kada Ki yi min kuka kinsan banaso My honey, “

Cikin shessheƙar Kuka take faɗin”Pravin na gaji da irin rayuwar nan, bana jin
daɗin kasancewata a matsayin ƴar aiki agidan nan saboda matarka saratu, ta tsane ni
bata sona, har Gori ta ke Yi min tana kirana da sunan karuwa, wai ina shisshigema
babansu wai ni pravin...’ sautin kukanta ba ƙaramin ta6a mashi zuciya yai ba

Lallashinta ya soma Yi”am sorry nasan ba daɗi but ki yi haƙuri, in sha Allah zan
nema maki mafita, idan bakya son zama gidan zan siya maki wani ki koma ki zauna can
Hakan Yayi maki”?

Ya yi tambayar yana leƙen fuskarta

Ba tare da ta ɗago da kanta daga saman pillow ba tace”A’a, ai ni bana son inyi
nesa da kai, Idan ka siya min gida na koma zaka Yi min wuyar gani, amma idan anan
ne zan dinga ganinka akai akai, koda ba za mu yi magana ba idan ka gifta ina jin
sanyi araina.

Lumshe ido yai, muryarta na ƙara jefa shi cikin Yanayi na jin shauƙinta.

“Shiyasa nake ƙara sonki My heart beat, kin fiye min kowace mace a duniya divya,
kinyi haƙuri dani da daɗi da ba daɗi kin zauna dani, Inason ki sosai, kema kin
sani, saratu bata fiye min ke ba, zan Iya rabuwa da ita amma ke bazan Iya rabuwa
dake ba saboda ke Jinina Ce kuma amanace ke agare ni.

Kalaman pravin sun sanyaya mata zuciyarta sosai, bata ta6a kokwanto akan abunda
yake faɗa mata ba.
Idanuwanta jawur take duban fuskarshi

“I love u so much, My life partner,” murmushi ya sakar mata.

“Idan akwai abunda kike buƙata Ki sanar dani zanyi maki shi”

Girgiza mashi kai tayi”a’a ai ni ka gama min komai pravin, ka haɗani da mutanen
kirki waɗanda har yau ina alfaharin kasancewa ta acikin su, sun ɗauki nauyin komai
na rayuwata ci na shana da suturar sanyawata, kaine sila pravin, bayan Albashi da
nake samu awurinsu kaima kana turamin kuɗi duk ƙarshen wata masu yawan gaske,
bansan ina zan kaisu ba, Tun da bani da buƙatarsu da ace Yaronmu yana araye kaga
sai mu dinga siya mashi abubuwan wasan Yara, da sutura masu kyau .....”da rawar
murya takai ƙarshen maganar, sosai ta sanya mashi kuka.
Cikin shessheƙar Kuka tace”Pravin bazan 6oye maka ba, Inason na haihu ko dan na
samu madadin shi”
“Ki kwantar da hankalinki, Zanyi shawara akan hakan” jinjina mashi kai Tayi
Yunƙurawa yai tare da miƙewa Ya sanya hannu Biyu ya cuccu6eta duk girman jikinta
baya jin nauyin ɗaukarta, Saukowa yai daga saman gadon Ya nufi toilet da ita,
wayarshi da ya bari acikin aljihun short dinsa dake yashe ƙasa sai ringing take Yi,
da zarar kiran ya katse wani ke shigowa.

****************❤

A ƙalla ta shafe sama da mintuna 30 tana zarya A cikin ɗakinta, Hannunta ruƙe da I
phone dinta, Yayin da idanuwanta ke kallon Haɗaɗɗiyar agogan bangon ɗakinta Ƙarfe 6
na marece, Lamarin Ya ɗaure mata kai, damuwa ce ƙarara akan fuskarta, Tun ɗazu da
ta kammala Yin waya da Gimbiya mujeedat, Hankalinta ya dawo kan Mijinta, Ganin time
ɗin dawowarshi daga aiki har Ya zarce babu shi babu alamar shi, saboda damuwar
rashinsa ta manta da zancen Kiran Zahra, Hatta P.A dinsa Ta kira awaya ta tambaye
shi ina pravin? Yace mata ai shi tun wuraren ƙarfe sha Biyu na safe rabon shi da
pravin, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, hakan na nufin ko aiki baiyi a office
ba, to ina Ya shiga? Tun ɗazu take kiran layin shi ba’a picking, abun duniya ya
isheta, saboda ta damu da pravin tayi kewarshi sosai, bata tunanin ko abincin zata
Iya ci idan bai dawo ba.

Guntun tsoki taja A fili ta furta”ya Salam, Ya Allah ga bawanka nan, Ka tsare min
shi a duk Inda Yake, “ ta ambaci hakan tare da jefa wayarta saman Gado, da sauri ta
nufi tafkeken closet na kayansu ta buɗe ta ɗauki Mayafi ta Yafa a kafaɗa, tsabar
sauri takalman da ta zura a ƙafarta daban daban, adai dai baƙin ƙofar fita daga
ɗakin Suka yi kicibus da Twins Bakunansu ɗauke da sallama, Wankan suit ne a
jikinsu, sun bi shape ɗinsu, Masha Allah, wrist watch dinsu mai Kyan gaske, Wani
irin daddaɗan ƙamshi ke fita daga Jikinsu.

Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba ganin mommyn nasu fuskarta babu walwala.

Har suna haɗa baki wurin furta”Mom Lafiya? Meke damunki ne” girgiza kai
Tayi”inafa lafiya, daddynku tun ƙarfe shabiyu yabar office, har yanzu bai dawo ba,
Na kira Layin shi wayar tana ringing ba’a ɗayawa.

Atare suka kalli juna, babu alamun damuwa akan fuskokinsu.


Kwantar mata da hankali suka soma Yi”mommy ki kwantar da hankalinki, daddy fa ba
wani ƙaramin yaro bane da zaki tashi hankali akanshi, Yasan inda Yaje kuma zai dawo
ne in sha Allah”
Fuskarta babu walwala take dubansu”pls ku bani Hanya in wuce inaso Naje na faɗa
ma baba” har suna haɗa baki wurin furta sunan baba

“Haba Mommy, Akan wani dalili zaki je ki faɗa mashi? So kike ki tashi hankalin
shi, Gaskiya a’a ki koma ki zauna, zamuje mu nemo daddy duk In da ya shiga”

Ruƙo Hannunta Zayn yai, Suka koma Cikin ɗakin, Gefen gado ya zaunar da ita,

“Zayn pls, Ku duba daddynku, Ni damuwata kada ace wani abunne ya same shi dama
jiya ya faɗamin baya jin daɗin jikinshi” muryarta tamkar zata fashe da kuka ta yi
masu maganar.

Zaid Yace”in sha Allah ba abunda ya same shi mommy, yanzu zamuje mu nemo shi” ya
ambaci hakan Tare da ruƙo hannun ɗan uwansa suka fuce daga ɗakin.

Ransu ya 6aci matuƙa, daga gaban ƙofar ɗakin suka tsaya suna kallon juna
“Mutumin nan ɗan rainin wayau ne, wlh Zaid zan tona mashi asiri awurin mommy, Ta
ya ya zai bar mahaifiyarmu cikin damuwa, Yana can Yana sharholiyar shi, dama zuba
mashi ido nakeyi ina tara shi....” duk yadda zaid yaso ya dakatar da Zayn Akan Yai
shiru yaƙi rufe baki saida Yakai ƙarshen Aya

“Ka daina ɗaga murya bro, Ni bawai ina goyan bayan abunda yake yi ba ne, just ka
yi tunani mana, muddin ka tona ma daddy asiri wlh mu zaka ja ma bala’e, Kana ganin
irin gorin da ake yi mana a family, akan mahaifinmu yana zama gidan surukansu Yanzu
idan ka faɗama Mommy cewa daddy Yana bin matan banza me kake tunanin zai Biyo
baya”?

Sassauta fushin fuskarshi Yai”Hakane Zaid amma abun Yana ƙona min rai, why ya ke
son ja mana baƙin jini? Dame mommy ta rage shi da har yagaza kama mutuncin kansa,
wai shi so yake dole saiya 6ata mana suna” tuni idanuwanshi sun cicciko tab da
ƙwalla

Ya ci gaba da cewa”Shine silar komai dake faruwa arayuwarmu, Zaid Ina kishin
mahaifiyata sosai, Ina jin takaici da ƙululun baƙin Cikin mutumin nan, wlh duk
ranar da mommy taji labarin abunda Yake aikatawa tabbas zuciyarta zata Iya bugawa
saboda tana da kishi kuma Tana son daddy, ni har kokwanto nakeyi anya daddy yana
son mommy kuwa? Ko dai Abunda mutane suke hasashe akanshi gaskiya ne? ya aureta
saboda dukiyar family dinmu’ yana magana hawaye naci gaba da taruwa acikin
idanuwanshi.

Dafa kafaɗarshi Zaid Yai”duk abunda ka ke ji zayn nima inajin shi, Amma Ya
zamuyi? Mu tamu ƙaddarar ahaka tazo mana, Muyi haƙuri wata rana sai labari Sannan
Yakamata muna tayashi da addu’a akan Allah ya shirye shi, saboda shi mahaifinmu ne
duk inda za’aje adawo mu jininsa ne kuma ba zamu so mutuncinsa ya zube a idon
jama’a ba.

Lallashin junansu su ka yi, Hannunsu ruƙe cikin na juna suka Nufi Babban falon
gidan, masu aikine keta kai komo.

Suna dab da zasu fuce daga falon, Kwatsam Pravin Ya faɗo Sai faman zumbula sauri
Yake Yi, Jikinshi sanye da Suit dinsa light brown, ƙiris Ya rage su ban gaji juna
da shi, duk da faɗin ƙofar kasancewar Kowan nan su Hankalinshi ba a kwance yake ba
Har zasu gifta shi, suka ci wani uban burki agabanshi, Tun daga Kan Yarda suke
jefa mashi kallo yasa shi kame kanshi.

“Har kun dawo daga aikin”? Tambayar daya jefa masu kenan.

Zayn tamkar ya shaƙe baban nasu haka Yake ji, takaici Ya hana su yi magana.
“Lafiya? Baku ji ina magana ba”?
Saida suka taushi zuciyoyinsu tukunna suka Iya yi mashi magana,

Zaid yace”Sannu da dawowa daddy, Ya office din? Naga yau ka yi marece ko duk Aikin
ne ya ruƙe ka”?

Basarwa Yai tare da cewa”Eh, “ daga haka bai ƙara tanka masu ba, Sai bi da yai ta
gefen su Ya wuce, kamar sakarkaru haka suka Bi bayanshi da kallo, Sam baisan cewa
sun san abunda yake aikatawa ba.

Kusan atare suka girgiza kawunan su.

“Zayn tunda Ya dawo mu koma ɗaki, dama Ni agajiye nake wlh, inaso na ɗan kwanta
In huta”
Juyawa sukayi Atare suka nufi part dinsu.

Hajiya saratu na zaune gefe gadonta, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta Hannu
biyu ta zabga uban tagumi, gabanta sai faɗuwa yake yi gani take yi kamar wani
abunne Ya faru da mijinta, Kasa samun natsuwa tayi zumbur ta miƙe kamar an
zungureta da sanda, safa da marwa taci gaba da yi acikin ɗakin tana ƙarewa agogon
bango kallo.

Ba zato ba tsammani muryar Pravin ta ratsa kunnuwanta”Assalamu alaikum” tunkafin Ta


juyo ta kalleshi ta soma sauke nauyayyar ajiyar zuciya, tsabar farin ciki da sauri
ta nufeshi, hannu biyu ya rungumeta a ƙirjinsa.

Sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, yayin da take ƙara shaƙar ƙamashin turaren
jikinsa.

“Am sorry My wife, nasan ban kyauta maki ba....”tunkan Ya ƙarasa maganar, Hajiya
saratu ta dago da fuskarta, babu annuri ko misƙala zarratin tuni yasha jinin
jikinshi.

Da kakkausar Murya ta furta”PRAVIN DAGA INA KAKE”!? Rass Yaji gabanshi Ya faɗi
“Na kira p.A dinka Awaya ya sanar dani cewa tun ƙarfe 12 kabar office, Inason Jin
ya akai kabar office ina kuma kaje”? Rai a6ace take Yi mashi magana, Hannunta ruƙe
da qugunta.
Ya tsareta da Ido batare daya furta kalma ba, hakan ba ƙaramin Ƙona mata rai ba,
Tsawa ta daka mashi kamar mahaukaciya Ta cakumi Gaban rigarshi.

“Nace ka faɗamin Ina kaje pravin? Saboda ka maidani shashasha ban da amfani
awurinka shine zaka kama Hanya kabar office tun ƙarfe sha Biyu baka kirani awaya ka
sanar dani ba, Kasa duk nabi na tashin hankalina akanka, ni na ɗaukama wani abunne
ya same ka sai gashi ka dawomun lafiyarka qalou”

Ƴan hanjin cikinsa tuni sun soma kaɗawa, Abunka ga shu’umin namijin wanda yasan
takan mace, runtse idonshi yai tare da kai hannu ya dafe gefen cikinsa.

Nan take Hankalinta yai matuƙar tashi la66anta na rawa take faɗin”pr...pravin?
Lafiya? Meke damunka”
Da wata irin kasalalliyar murya ya furta”My stomach, bana jin daɗi ai tun Jiya
na faɗa maki,” ya ƙarasa maganar yana faman cizon la66ansa, lokaci ɗaya fushin
fuskarta ya sassauto, tsananin tausayin shine Ya kamata, ganin yana tangal tangal
kamar zai faɗi yasa tayi saurin talla6e waist ɗinsa, da taimakon ta suka ƙarasa
gaban Gado Ya hau Ya kanta Yana fuskantar ceilling, daga gefen gadon ta zauna daga
gefenshi tana kallon shi
“Pravin am sorry nayi maka faɗa bansan baka da lafiya ba, kaine kaƙi Yi min
magana, why pravin kasan baka da lafiya meyasa baka kira awaya ka sanar dani ba?
Cikin kulawa take yi mashi magana, har ta manta da zancen tambayarshi Ina yaje.

Wahalallan Yawu ya haɗiya, Cikin mawuyacin Hali Ya furta”wayar bata a hannuna ne


a mota nabarta, Ina Cikin Yin draving zan dawo gida, Ciwon ciki Ya takura min,
draving dinma na gagara Yi, shine na wuce gidan abokina dake anan kusa, to acan
bacci ya kwashe ni,

“Pravin why baka je asibitin Gida ba? ai da komai yazo maka da sauki, yanzu ka
tashi ka shirya In kaika asibiti da kaina inyaso sai in dubaka acan”

Tana Ƙoƙarin miƙewa yai saurin fusgo hannunta, gaba ɗaya ta faɗa saman jikinsa,
Ƙanƙame ta yai da hannayenshi biyu

Yana faman cizon le6e ya furta”rashin lafiyata bata asibiti bace, My wife kece
kike damuna saboda rashin bani haƙƙina da bakya yi akai akai, shiyasa nake fama da
ciwon cikin nan, ko da yaushe Aikinki ne agabanki, idan dare yai nayi maki magana
kina danna laptop sai kice min In jira ki kammala daga nan har bacci ya ɗauke ni
baki gama ba......”

Pravin Ya kashe mata Jiki da kalamansa, ta yarda da abunda ya faɗa mata saboda
tasan bata kyauta mashi ta 6angaren nan mafi yawan time idan Ya matsa mata tana Yin
aiki bata kula shi saita kammala.

“Am sorry dear, indai nice zan gyara, kayi haƙuri nayi kuskure but bazan ƙara
Ba, tun da abun Yana affecting dinka”. Lumshe ido Yai, har cikin zuciyarshi ba
ƙaramin daɗi Yaji ba, ganin yai nasara akanta.

“Yanzu ka faɗamin me kakeso? Za ka yi wanka in taimaka? Ko zaka fara Cin abinci


ne”

Yana faman sakin nishi Ya furta”nafi buƙatar wankan, amma idan kin amince muyi
atare”
Murmushi tasakar mashi”is Okey, shine kaɗai abunda kakeso”? Ɗaga mata Gira yai
alamar eh, A hankali ta ɗaura yatsun hannayenta saman coat din jikinsa Ta cire
mashi ita, kafin ta zame mashi belt din wandonsa, yunƙura yai tare da miƙewa ya
sauko daga saman gadon Ya ƙarasa zame wandon ya rage daga shi sai short da singlet
dinsa, Yaja hannunta suka nufi toilet, da gudu nabi bayansu sai dai kafin in ƙarasa
Pravin Ya kulle ƙofa.

*EX-PRISONERS❤*

Idan muka koma 6angaren Prisoners, sai dai muce Alhamdulillah, tun bayan da Dr
laura davis ta tattauna da Sojoji bata ƙara Ji daga gare su ba, An dai samu damar
Kammala Yi masu injections ɗinsu kuma kullum sai sunsha magani na safe daban na
rana daban na dare daban, injection ɗin duk mutun ɗaya uku suke Yi mashi arana,
Likitoci sun ci kwakwa Wurin ma Matan allura, Musamman Azeeza da Jamimah, mugun
tsoron Allura su ke ji, idan za’ayi masu sai an kira Angel ta ruƙesu, tukunna ake
samun sauƙin yi masu allurar, Mazan dai da sauki basu tsoron Allura tamkar basu son
ana tsira masu ita a jikinsu ba, cikin kwanaki huɗu da su ka Yi a Texas Rayuwarsu
ta fara canzawa, saboda kyakkyawar kulawar da suke samu tarairayarsu ake Yi kamar
new born babies, abinci sau uku ake basu, Breakfast, lunch and dinner, Lafiyayyan
abinci mai gina jiki, sau ɗaya ake sanyasu yin wanka, su canza Kayan Jikin su, Su
Angel an dage da yin sallah da addu’a, har tsakar dare tana tashi yin night
prayers, yawanci addu’o’inta akan Danish ne, ta roƙi Allah da ya kare mata shi,
idan farkawarshi Alkhairi ce Allah Yasa ya tashi cikin amince, idan kuma
farkawarshi ba Alkhairi bace Allah yasa yaita sharar baccina har zuwa su koma
Nigeria zaifi masu sauƙin su Yi control dinshi, duk da yanzu ta fara fargaban kada
su zo Nigeria A nemi Ruwan zam zam arasa tabbas ba ƙaramar matsala za’a samu ba,
damuwarta yanzu akan Sojojin ce shiru basu dawo ba, Kuma bata Ji daga bakin dr
laura Ya ake ciki ba, Shin za’a maidasu ƙasarsu ne ko kuwa a’a, Ta dai zubawa
sarautar Allah Ido 👀

Sam ta kasa runtsawa, tun wuraren ƙarfe tara na dare ta farka, saboda mugun bugun
da ƙirjinta ke yi mata, tabbas tana ji aranta wani abun ne ke shirin faruwa.
Miƙewa Tayi zaune saman gadonta, ta jingina Bayanta Jikin pillow, idanuwanta suna
a lumshe, sanyin A.c sai ratsa fatar jikinta Yake yi wata irin kasala take Ji da
matsanancin faɗuwae gaba.
“Masoyiya Angel, Lafiya kika farka daga bacci? Na lura kamar wani abu ke
damunki”
Muryar Nurse Jessica ce ta fargar da ita, har saida ta ɗan zabura don bata yi
tsammanin jin Muryar mutun a kusa da ita ba.
Slowly ta wurga eye balls ɗinta akan fuskar nurse ɗin, tana daga zaune saman
chair ta kusa da gadonta, hannunta ruƙe da wayarta, fara ce sol, uniform ɗin
jikinta light blue ne kalar nasu, ta ɗaure jar sumar kanta da ribbom.
Nauyayyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa”sister, nagode da kulawarki
agareni, nakasa runtsawane saboda inason ganin yan uwana ko zaki Iya taimaka min”?
Smiling gently nurse jessica tace”Na lura kina son ƴan uwan nan naki, cos tun
ranar dana fara kula da ke, sau uku kike zuwa room ɗinsu Kina duba su, faɗamin ko
dai akwai damuwane? Ko tsoro kike ji kada mu sace maki su”? Da zolaya nurce jessica
tayi mata maganar
Cikin jin kunya Angel takama ƴan kame kame tana faɗin”am.... Ba haka bane just
inason su sosai, mun shaƙu da juna, shiyasa bana samun natsuwa idan ban gansu akai
akai ba”

Nurse jessice tace”Kuna burgeni sosai, inaso Inga ƴan uwan masu son junansu,
masu haɗin kai, ta hakanne ake cin ribar zaman duniya, idan har kana da ɗan uwa mai
share maka hawayenka, mai nuna maka ƙauna wanda baya gajiya dakai tabbas ka gode ma
Allah, zai yi wuya ka rasa madafa a duniyar nan, babu wanda zai yi gigin cutar
dakai muddin kuna da haɗin kai a tsakaninku, amma idan Ya kasance kuna ƴan uwa baku
da haɗin kai, danasani zai biyo baya cos dayawa rashin kulawa keja har damuwa tayi
ma ɗan uwanka Illa, ya akaita abunda zakuyi danasani gaba dayanku”

Angel ta natsu Tana sauraron Kalaman Nurse Jessica, Haƙika kalamanta sun ta6a
mata zuciya, sai taji ta ƙara ƙaunar ƴan uwanta, ta ɗanyi mamakin yarda nurse ɗin
take sakar mata fuska suke Yin fira, saboda ta ta6a Jin ana faɗin turawa sun tsani
baƙar fata suna nuna masu wariyar launin fata, sai dai tayi tunanin ba duka aka
taru aka zama ɗaya ba, sannan kuma su basu da banbanci dasu, hasken fata, launin
ido da kuma sumar kai, shiyasa suka zama ɗaya.

“Ki tashi muje in raka Ki ɗakunan ƴan uwan naki, Nima Inason ganin su, musamman
twins ɗin nan” murmushine Ya bayyana akan fuskar Angel jin abunda nurse ɗin tace,
tuntuni ta faɗa mata, ba twins bane Jamimah da azeeza ɗaya ta girma ɗaya amma taƙi
yarda, ba ita kaɗai ba hatta sauran nurses ɗin da likitocin kallon twins suke Yi
masu acewarsu Basu da banbanci, Komai nasu kala ɗaya.

da zumuɗi Angel ta sauko daga saman gadon, light blue uniform ɗinta ne a jikinta,
sai da ta fara zuwa gaban closet ɗin ɗakin ta buɗe ta ɗauko Hijabin da aka bata
Nayin sallah ta zura a jikinta.

Hannunsu ruƙe cikin na juna ita da nurse ɗin suka fito daga ɗakin, hasken
electric bulbs Ya haskaka Asibitin tamar da rana, a tsanake suke Yin tafiya suna
tattaunawa a tsakaninsu, ɗakin Gabriel suka Fara shiga, tayi mamakin ganinshi idon
shi biyu Shida nurse rebecca, ta kunna masu kallo sun natsu abunsu.

Jin motsin shigowar Mutun yasa suka kai eyes dinsu ga ƙofar, murmushi ne ya
bayyana akan faces dinsu
Mayar masu da martanin murmushin nasu Angel tayi”ɗan uwana, Baka Yi bacci ba?
Fadamin meya hana ka Yin bacci”!
Kafin Ya bata amsa nurse rebecca tace”Ni na hana shi, Ko bakisan mun fara soyayya
bane, Gabriel baka faɗa mata ba”? Gaba daya suka sanya dariya, jessica tace”har
kinyi kamu kenan” ɗaga mata gira tayi”yap, taya zan bari damar nan ta wuce ni”?
Firarsu ba ƙaramin nishaɗi take sanyasu ba, Angel tuni ta haye saman gadon gabriel,
Ruƙo hannunshi tayi acikin nata,
“My sister, meya hana Ki yin bacci”? Ƙasa ƙasa da murya ta furta”Danish,
Hankalina Yaƙi kwanciya da rashin farkawarshi, Yaufa kusan One week kenan a
lissafina, Gabriel bansan ya zanyi ba, Ni nafi so Mu koma nigeria....”katse mata
maganar yai da cewa”ai kin faɗamin dr laura tace zata taimaka mana mu koma can ko?

Ɗaga mashi kai Tayi”eh, amma har yau shiru, banji daga gareta ba, Kuma kaga
sojojin basu ƙara dawowa ba”

Ganin kamar duk ta damu yasa shi kwantar mata da hankali”Wani jinkirin alkhairi
ne Angel, wata’ƙil ki ga gobe anzo mana da kyakkyawan labari, don haka Mu ƙara
haƙuri kada mu damu kanmu komai zai tafi dai dai My lovely sister” Yai magabar Tare
da jan kumatunta da hannunshi, Hakan ba ƙaramin dariya Ya bata ba.

“Masoyiya Angel, zamu Iya tafiya “? Muryar nurse Jessica ce ta katse masu
tattaunawar tasu.

Peck tayi mashi saman cheek dinsa”ka kwanta ka huta,” ta ambaci hakan tare da
saukowa daga saman gadonshi ta nufi nurse jessice taja hannunta suke fuce bayan
sunyi masu sallama.

Room ɗin Batul suka shiga, A kwance suka same ta saman gado, ta ƙudundune da
bargo, da alama tayi zurfi abaccinta, Basu shiga ɗakin ba suka wuce ɗakin Jemimah,
Itama baccin take Yi, ta wawware ƙafafuwanta ta saki baki da hanci, nurse din dake
kula da ita, Tana acikin ɗakin har gaisawa sukayi da ita kafin suka nufi ɗakin
Azeeza, Kamar yarda suka samu jemimah haka suka sameta a kwance bacci yai daɗi,
murmushi Angel tasaki kafin suka ƙara gaba zuwa ɗakin Parveen, Hallau dai mai hali
Baya ta6a canzawa, bata Yi mamakin ganinta a zaune gefen gado ta tasa abinci saici
take Yi, An kunna mata tv tana kallon mbc channel Suna Yin cartoon tom and jerry,
Sai tiƙar dariya take Yi kamar zata kifa kanta saman table din gaban gadon, babu
alamun bacci a idonta, sam bata ji motsin shigowarsu ba, plate ɗaya ne agabanta
shaƙe da chicken wings, gefen plate ɗin kuma Apple juice ne, Duniya Ta yi mata
daɗi, Gyaran muryar da Angel Tayi mata ne yai silar Jawo Hankalinta ga dubansu,
bakinta cunkushe da nama ta furta “Angel”

Nurse ɗin da suka zo atare da ita sai murmushi take saki, Da alama parveen ta
burgeta, ba tun Yau ba, duk in tazo dubata sai ta sameta tana Cin abinci, da wuya
ka same ta bakinta babu abun taunawa.

Farin Cikine Ya bayyana akan fuskarta, Da sauri ta ƙarasa suka rungume juna ita
da Angel.

Shafa sumar kanta Tayi”Parveen kowa Yai bacci banda ke, kina nan kinata cin
abinci Ko gajiya bakya yi, so kike ki karya masu jari ko”? Da zolaya tayi maganar,
bayan ta raba jikinta daga na Angel, Just 4days Har kumatu ta ƙara.
“Ai nurse ɗinne Yace min duk in ina buƙatar wani abu Inyi mashi magana...” zaro
ido Angel Tayi hada ruƙe ha6a tace”Eyehh! Wato saboda yace maki haka shine kuma ko
da wani lokaci sai kince mashi zaki ci abinci, Angaya maki nan Restaurant ne?
You’re a patient bai kamata aga kina cunkushe cunkushen abinci, kamar me fama da
cutar Yunwa” sam Sun manta da nurse din da ke abayansu, Da turancin Angel Keyin
maganar, hakan Yasa ta fahimtaci abunda suke tattaunawa, sai faman sakin murmushi
take Yi tana binsu da kallo.
“Angel ai su ba ruwansu, komai mutun yake so suna yi mashi, baki ga yarda nurse
din Ya ke ji dani ba, Shine ma Ya kunna mun abun nan ba ƙaramin Daɗi naji ba” ta yi
magana tana nuna mata plasma tv

Watsa Hannu Angel Tayi”Okey, Koma Ki cigaba da cin abincinki, pls Ki samu ki
kwanta ki huta, ki kula mun da kanki” murmushi parveen ta sakar mata

“Thank u sis, Allah yabar mana Angel ɗinmu” Nurse jessica ta tsaresu da ido,
gwanin ban sha’awa take kallon su
Sallama sukayi Ma parveen bayan sun fito daga ɗakin suka nufi ɗakin Hannah,
Yarinya ƴar madara, hankalinta kwance take sharar baccinta, Rabin jikinta duvet ne.

Bayan sun ƙara gaba ɗakin Naufal su ka shiga da ɗakin Javed, Kowan nan su bacci
Yake Yi, daga ɗakin Javed suka nufi ɗakin Haris, Bawan Allah ba laifi Jiki Yai
kyau, yana samun kulawa fiye da sauran ƴan uwanshi saboda lalurar shi.

Sunyi tunanin bacci yake yi ganin shi kwance ya rufe idanuwanshi, Har sun Juya
zasu fuce muryar shi ta katse masu hanzarinsu

“Angel!” Atare suka Juyo suna kallonshi, Ya buɗe idanuwanshi da suke a lumshe,
farin Cikine Ya lullu6e Angel, da sauri ta nufi gadon shi daga gefe ta haye,
taimaka mashi tayi ya mike zaune, ta rungume shi a chest ɗinta, hannunta asaman
bayanshi tana shafashi

“Haris ɗina Ya jiki naka da sauƙi ko”? Muryar shi, ƙasa ƙasa Ya masa mata”da
sauƙi Angel, bana jin ciwo a jikina sai dai har yanzu ina yin mafarki akan
Deejana, ina ganinta a prison suna azabtarmin da ita, tana kuka tana roƙona akan in
taimaki rayuwarta’ cikin rauni na murya yai maganar

“Ka kwantar da hankalinka haris, Mafarki ba gaskiya bane, sau dayawa mafarki
Shaidanne yake assasa shi, wani daga Allah ne wani mafarkin kuma ya danganta daga
Yarda ka ƙwallafa abu aranka, shiyasa nace ka dage da yin addu’a, in sha Allah
haris in dai Deeja tana araye zaku haɗu ne,”

Nurse ɗin ta zuba masu ido tana kallon su, bata san me suke tattaunawa ba a
tsakaninsu, saboda sunyi amfani da harshen hausa.

Still Haris bai ɗago kanshi daga saman chest ɗinta ba ji yake kamar deejanshi ce

“Wlh Angel inason deejana, Kuma inayi mata addu’a, Ko yanzu da kika sameni na
rufe idanuwana, addu’a nakeyi mata, Ni bazan ta6a gajiya dayima deeja addu’a ba,
Har nunfashina na ƙarshe”

Tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, (Ƙaunar dake a tsakanin haris da
Deeja, daga Allah ne, irin son da ake kira true love, Inason ka kana so na badan
wani abu ba❤ Allah Ya bamu masu sonmu tsakani da Allah🙏)

Shafa sumar kanshi Angel Ta yi da hannunta, Jin shessheƙar kukan shi Ba ƙaramin
Karya mata zuciya yai ba

“Haris pls don’t cry, kasan bana son jin kukan ka, ko ba danni ba, nurse da ke
kula dakai bazata Ji daɗi ba, Suna iyakar bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun sanyaka
farin ciki duk don ka rabu da ciwon zuciyar dake damunka” a hankali ya ɗago da
kanshi Idanuwanshi sun ɗan kumbura.

“Angel, nadaina bazan ƙara ba” tafin hannunta ta ɗaura saman fuskarshi tana
share mashi hawayenshi
“Zan tafi Yanzu nurse tana Jirana, Amma kafin nan kayi min murmushi mana” daƙyar
ya ƙaƙaro murmushi kan fuskarshi, Hakanan taji gabanta Ya faɗi ƙura ido tayi akan
face dinshi kamar tana son gano wani abu sai dai ta kasa gane menene shi.

Ganin yadda take kallonshi yasa yace mata Lafiya Angel’? Girgiza mashi kai Tayi
bakomai, ka kula mun dakanka, Sai Allah Yakaimu” daga haka ta sauko daga sama
gadon, suka fice daga ɗakin shi ita da nurse jessica.
Last room da suka Nufa ɗakin Garkuwa, tunkafin su ƙarasa take Jin faɗuwar gabanta
na ƙaruwa, ji take yi kamar idan ta shiga ɗakin wani abu zai faru, Da bismillah
abakinta ta kutsa kai dakin nurse jessica tabi Bayanta, kamar matacce haka suka
same shi kamar kullum Sai sharar baccin shi Ya ke yi, Lamarin Danish ba ƙaramin
ɗaurewa likitoci kai Yai ba, tsawon kwanaki mutun Yana yin bacci yaƙi tashi? Tun
abun na damunsu har sun haƙura sun zubawa sarautar Allah ido.

Saman chair nurse ta zauna idonta akan face din Danish

A hankali Angel ta zauna gefenshi Tana ƙare mashi kallo, Ji take yi tamkar ta
fasa ihu acikin kunnuwanshi wata’ƙil idan Yaji zai farka, sai da tasan ko Tayi
abanza, Allah shine shaidarta, ta matsu a ƙagare take da son farkawarshi kamar ta
yi hauka
Sam ta manta da nurse dake a ɗakin, ta natsu tana kallon shi kamar zata Haɗiye
shi, A hankali Ta ɗaura small pink lips ɗinta farar fatar cheek dinsa ta manna ma
kiss.

Murmushin gefen fuska nurse jessy ta dan saki, abun ba ƙaramin ƙayatar da ita yai
ba, kamar ta samu tv haka take kallonsu.

A hankali Angel ta kwantar da kanta saman faffaɗan chest dinshi ta kasa kunne
tana sauraran heart beat dinsa

Muryarta cikin raɗa take Yin magana”My man pls wake up, nayi kewarka kamar zan
zauce, dan Allah ka taimaki rayuwana ka farka danish, a matse nake duk na takura da
rashinka, pls idan kana Jina Ka amsa min” hauka ta soma yi mashi asaman jikinsa
tabi duk ta hayeshi, shessheƙar kuka tadinga yi mashi duk don ya farka sam babu
hawaye akan face dinta, ɗagowa tayi da kanta, gray eyes dinta akan fine face nasa,
eyes lashes dinsa ta ƙurawa ido masu kyau da tsari.

Bakomai take tunawa ba face Farkon haɗuwarsu a prison, a karo na farko da Ta yi


tozali dashi saida gabanta Ya faɗi saboda zazzafan Kyanshi, Murmushi tasaki tunawa
da maganar farko data fara haɗasu lokacin da tana zazzaga masu masifa akan afaɗa
mata ubanwa ya kawota prison
Muryarshi ta ratsa kunnanta, tamkar ana busa sarewa
“Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki
kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da
mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta,
don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u
understand me!” a lokacin takai maƙura A zafafe Ta juyo ta kalle shi tsabar mamaki
tamkar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, duk da bugun da zuciyarta tayi mata na
ganin kyanshi hakan bai hanata zazzaga mashi masifa ba.

“Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you
are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona
ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!”

Batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, Rayuwa kenan, Idan mutun ya kasance
ƙaddararka baka isa ka canza shi ba, bata ta6a tunanin zasu sasanta tsakaninsu ba,
saboda rashin jituwarsu sai gashi a yanzu sun shaƙu da junansu ita da sauran ƴan
uwanta prisoners.
Nurse Jessica Har tafara Gajiya da zama bacci na shirin kwasarta a saman
kujera, sam batason ta katse Angel donta fahimci ba ƙaramin so take Yiwa ɗan uwan
nata ba, duba da yadda ta haye saman jikinshi tana sambatu hada murmushi da dariya.

Soft lips ɗinsa ta ƙurawa ido tamkar anyi mixing din launinsu da pink

“Masoyiya Angel Yakamata mu koma ɗaki ko”? Muryar Nurse jessica ce ta fargar da
ita, Amsa mata Tayi da toh Kafin ta miƙe ta ɗan dukar da kanta saitin fuskarshi
sumar kanta ta yi mashi rumfa, A hankali ta ɗaura small mouth ɗinta saman Forehead
dinsa Da Niyar ta manna mashi peck ba zato ba tsammani taji ya damƙi waist dinsa
ruƙo bana wasa ba, Agigice Take kallon face dinsa wani abun mamaki bai farka daga
baccin ba, tashin hankalin da ba’a sama shi data, Nan take Jikinta Ya hau Yin
kakarwa ido Ya raina fata, wata irin zuface ta soma tsastsafo mata ta cikin hudar
gashin jikinta.......

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number
dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

_The Prisoners E20🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Hankalinta a matuƙar tashe take kallon fuskarshi, Numfashinta na hauhawa zuciyarta


na bugawa da sauti mai ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjinta, tsabar tsoratar da
ta yi, Nurse Jessica da ke a zaune ta rasa gane meke faruwa ne? taga dai tun da
Angel ta yi mashi rumfa taƙi motsawa, kamar an daskarar da ita, idanuwanta ba su
hango mata hannun Danish da ya damƙi Qugun Angel da shi, sakamakon Sumar Kanta da
Hijabin jikinta sun lullu6e shi.

“masoyiya Angel, Ke nake Jira, kusan ƙarfe goma na dare, Yakamata Muje ki kwanta
ki kwanta ki huta” Cikin Kulawa ta yi mata maganar Tana leƙen fuskarta sai dai bata
samu damar ganinta ba, saboda wuyan Hijabinta Ya zame tuntuni sumar kanta ta
zazzago gefe da gefen fuskarta, ta rufe su.

Yunƙurin kubcewa tayi daga ruƙon nashi sai dai ko gizau wannan bai yi ba, kuma
bai motsa ba, Ya matseta A jikinshi, tamkar an ɗaureta da igiyoyi, duk da sanyin
A.c na room din hakan bai hana ta zubda gumi ba, zufar dake wanko fuskarta kaitsaye
take sauka saman fatar face nasa, idanuwanta azazzare, yayin da acan cikin
zuciyarta ta ke ta ambaton”INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJI’UN”! Ba ƙaƙƙautawa.

Muyar Nurse Jessica ce ta ƙara fargar da ita”Lafiya kuwa Angel? Ya akai naji
Kinyi shiru? Ko kinyi bacci ne a jikin shi” ta ƙare maganar tare da yunƙurawa ta
miƙe daga saman chair ɗin ta nufi gaban gadon ta tsaya tana ci gaba da yi mata
magana, tsabar yadda la66anta ke yin kerma ta kasa buɗe baki ta faɗa mata Halin da
take a ciki.

Miƙa Hannu nurse jessica ta yi da niyar ta ɗago da Angel, saboda ta yi tsammanin


bacci ne Yai awon gaba da ita, Sai dai Kafin ta ruƙo ta, Angel Ta yi ƙoƙarin Yin
magana Muryarta A hargitsa ba natsuwa ta furta”ɗan Uwana Ya farka! Shine Ya ruƙe
Ni”

Mamaki Ne Yasa Nurse jessica Zaro Ido haɗi da buɗe Baki, Ta Furta” Are u serious
Ya farka?

“Ya farka, but he didn’t open his eyes. He held me so tightly that I couldn’t
separate myself from him” cikin shessheƙar Kuka Angel ta furta maganar.

Jin haka Yasa Nurse jessica faɗin”Bari Na taimaka maki ki miƙe”

Hannu Biyu ta sanya ta ruƙe Angel ta soma kiciniyar 6an6arota daga Jikin Danish
da Iya ƙarfin ta na ƙarshe sai dai takasa ta6uka komai, Mugun ruƙo Yai mata, Hatta
dogayen nails ɗinsa sun yi mata shatu saman bayanta, Lamarin ya ɗaurewa Nurse
Jessica kai, ganin ta sanya Iya ƙarfinta na ƙarshe Amma abanza, hakan ba ƙaramin
ruɗar da ita yai ba, Muryarta na rawa ta furta”Bari naje na kira doctor”

Da sauri ta fuce daga Cikin ɗakin hada ɗan gudunta

A lokacin da bata Yi tsammani ba, Sexy voice ɗinsa ta ratsa kunnuwanta muryar
da ta daɗe tana mararin Jinta

“My Angel” Iya abunda ya furta mata kenan.

nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ya ambaci sunanta, hakan na nufin Yana acikin
Hayyacinsa, ƙura ma fuskarshi ido tayi ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi,
sannu A hankali yake ƙoƙarin ware su, sunyi mashi nauyi saboda baccin da yai na
tsawon kwanaki, Ta yi matuƙar ƙagara da son Yin tozali da kyawawan Reddish-brown
eyes ɗinsa, kaɗan Ya buɗe su bai ƙarasa ware su ba, sun ciza launinsu, hakan ba
ƙaramin kyau suka ƙara ma shi ba, Tsabar farin ciki batasan sa’adda ta fashe mashi
da kuka mai tsuma zuciya, tana haɗawa da dariyar farin Ciki, ya natsu yana kallonta
da wata irin kasala a jikinshi, sam bai san a ina suke ba Iya fuskarta Yake Iya
gani.

Cikin shessheƙar kuka haɗi da shagwa6a take faɗin”Nayi missing ɗinka My man, sai
yau zaka farka? Kabarmu da kewarka da fargabar a wani hali zaka tashi, sannan kuma
ka tsoratar dani sosai....” lumshe idanuwanshi ya ɗanyi tare da ware su saman
fuskarta, Hawayenta sai jiƙa masa face dinshi suke Yi, har cikin bakinsa, hakan bai
dame shi ba, tamkar ya samu ruwan sha, haka ya ke yin swallowing dinsu.

Kallon da ya ke yi mata kallo ne dake nuni da tsantsar ƙaunarta da kewarta da


yayi, hucin numfashinsu sai gaurayewa yake yi dana juna, hakan bai sha masu kai ba.

Idanuwanta sharkaf da hawaye sun rune jawur taci gaba da cewa”dan Allah ka faɗamin
ba abunda ke damunka? Naga kanata kallona kaƙi kula ni” ta ƙare maganar still da
shagwa6a, yamutsa fuskarshi yaɗanyi haɗi da motsa tausasan la66ansa calmly ya furta

“ke ce damuwata, kinsan bana son zubar hawayenki, ki daina yi min ku ka or else
I’ll go back to sleep

yai maganar yana ƙoƙarin lumshe idanuwanshi da zolaya yai mata hakan aiko da sauri
ta shanye kukanta, tana faɗin”na daina My man, kaine ka ƙi kwantar min da hankali
na” ba zato ba tsammani taji ya manna mata peck saman fore head dinta, farin ciki
duk ya cikata.

Muyarta har shaƙewa ta ke yi saboda kukan da tasha”ka sake ni, Ka matse ni” tayi
maganar tana ƙoƙarin kubcewa daga ruƙon da yai mata, so ta ke yi ta nuna mashi
sabon wurin da suke acikin shi, ƙanƙameta Ya ƙara yi yana faɗin

“Ki jira, zan sake ki, ina samun natsuwa atare da ke”

ƙayataccen murmushi ta saki, ta ɗan dakata suna kallon cikin idon junansu, lokaci
ɗaya taga Ya haɗe face dinsa.

“Lafiya”? Tai tambayar tana cigaba da kallon shi

“Namanta, ban sama maku abincin da zaku ci ba, Na bar ku da Yunwa”

Murmushin gefen fuska ta sakar mashi”Ka kwantar da hankalin ka, Muna cin
Lafiyayyan abinci har sai mun ture, shiyasa nace ka sake ni inason nuna maka wani
abu” slowly ya zame hannunsa daga ruƙon Da yai Mata, Light bulb ɗin ɗakin Ya haske
mashi ido, saukowa tayi daga saman gadon ta fuskanci gabas Ta duƙa tayi sujjada
tana godewa Allah daya farkar mata dashi cikin ƙoshin Lafiya ba tare da wani abu ya
same shi ba.

Alhamdulillahi Ala kulli Halin.

Ya yi matuƙar Yin mamakin ganin room ɗin da ya ke aciki, a kasalance ya yunƙura


Ya miƙe zaune yana ƙarewa ko’ina Kallo, tunani ya shiga yi Ina ne nan? Waye ya kawo
su? Fuskarshi da alamun ruɗani ya Tura yatsun hannunshi cikin yalwatacciyar sumar
kanshi yaci gaba da cakuɗata tamkar yana sosata, saukowa ya yi da ga saman gadon.

Jikinshi yayi mashi nauyi daƙyar yake taka ƙafarshi, yayin da yake ƙarewa ɗakin
Kallo, Angel tana a duƙe tun da tayi sujjada bata ɗago ba, addu’o’i take tayi masu.

Yana ƙoƙarin buɗe baki da niyar ya yi mata magana, Sai ga doctors da nurses sun
shigo ɗakin da saurin su, Kusan atare su ka ci uban burki suna kallon kallon a
tsakanin su da shi, Mutumin da suka daɗe suna mararin ganin Ya farka, sai yau Allah
ya nufa zai tashi, Sun yi matuƙar girgiza da ganin Shi a tsaye kan ƙafafun shi,
kyan fasalin shi Ya yi masu ƙwarjini.

Da hannu Yai masu Alamar su wanene su? Sai Ƴan kame kame suke Yi An rasa me Iya
buɗe Baki Yayi mashi magana.

Juyawa yai da sauri Yaje gaban Angel da ta yi sujjada, Da hannu ɗaya ya ruƙo
damtsen ta, Ya ɗago da ita tsaye kamar wata ƴar baby, nuna mata likitocin Ya yi da
hannun shi

“Who are they, and where are we?”

daƙyar ta samu natsuwar Fayyace mashi komai tun daga kan Yadda aka tsunto su a
daji aka zo da su asibitin kamar yadda Gabriel Ya sanar da ita.

Bayan ta gama kora mashi jawabi ta kalli fuskokin likitocin tace “ku ta ya ni
murna ɗan uwan mu Danish Ya farka”

murmushi kowan nan su Ya saki Nurses din dake a cikinsu kamar sun samu tv haka suke
Binshi da mayataccen kallo, ba mazan ba ba matan ba.

“Muna ta ya ki Murna masoyiya Angel, munga brother ɗinki Ya farka cikin koshin
Lafiya” nurse jessica ce Tayi maganar

Daƙyar wani dr ya iya buɗe baki yace”Danish Fatan Ka tashi Lafiya, tsawon lokaci
muna jiran ranar da zaka buɗe idanuwanka, Sai yau muka samu damar ganin ka, Mun ji
daɗi sosai” yai maganar tare da miƙa mashi hannu don su gaisa, Man ɗin fa bai yarda
da su ba, dama yana da wuyar sha’ani ga ƙiwuya kamar ƙaramin Yaro.

“Danish Ka miƙa mashi hannu ku gaisa” Angel ce tayi mashi magana, goya
hannayenshi yai saman broad chest dinsa, Alamar ba zai miƙa mashi hannun ba”

murmusi yaƙe ta ɗan saki”ku yi haƙuri, Danish baisan ku ba, Har yanzu baccin bai
sake shi ba, nasan kafin zuwa gobe zai Warware’

Nurse rebecca tace “badamuwa, Dama mu fatan mu Ya farka da ranshi da lafiyarshi,


Hakan ma ya wadatar”

Dr. Anthony Yace”Calm down, Danish. No one will bother you. We are doctors, and
we have the right to check your health until you feel better.” still bai tanka masu
ba.

Dr harry yace”ni dama tun kafin Ya farfaɗo raina Ya bani zai yi wuyar sha’ani,
sai gashi maganata ta tabbata, mutane masu irin Kyanshi bakowa suke kulawa ba” da
zolaya yai maganar, Ya ƙara da cewa “mu dai yakamata asaki jiki damu tunda malaman
lafiya ne, muna so ka bamu dama mu ƙara bincika Lafiyarka” tun da suka fara Magana
bai tanka masu ba sai kallo da yake binsu dashi kamar yaga wasu halittu daba na
mutane ba.

“Ko akwai Inda ke yi maka ciwo yanzu”? Dr anthony ne yai mashi maganar, Angel
sai ƙoƙarin ingiza hannunshi take Yi don yayi masu magana amma Yaƙiya, Nurse
jessica tace”ga dukkam alamu rowar muryarsa yake yi mana, Ni inaga Mu ƙyale shi
zuwa gobe nasan zai warware kuma zai saki jiki da mu”

Kamar za su yi hauka wurin yi mashi magiya don yayi masu magana yayi shiru
abunshi, har so sukayi su bincika lafiyarshi amma Ya hana, duk wanda yai gigin
matsowa kusa dashi, zazzare masu ido yake yi alamar zaiyi fighting dinsu, lamarin
ya ɗaure masu kai, ganin sun sanya naci akan sai sun duba shi, Angel ta roƙe su
akan su ƙyale shi zuwa gobe, fargabanta kada su hayaƙa shi azo asamu matsala, tunda
harya fara zare masu ido yana ɗaure masu fuska. Ba don sun so ba, su ka yi masu
sallama da niyar gobe zasu dawo, kusan atare suka fuce waje, aransu suna Ayyana
irin kyawun fuskarshi da surarshi, sai santin shi suke Yi musamman nurses din cikin
su.

Su Uku Suka rage a ɗakin, Nurse Jessica ta dubi Angel”na lura brother ɗin nan
naki, ke kaɗai yake jin maganarki, Inaso ki tambayar min shi ko akwai abunda yake
buƙatar ci”? Kallon shi Angel Tayi, idonshi na akan plasma tv ta ɗakin, sai ƴan
kalle kalle yake yi.

“My man kana jin Yunwa”? Da budar bakinsa sai cewa yai”Ina haris da su Batul?
Inason ganinsu”

Kallon Nurse din Tayi”yace yana son ganin ƴan uwanmu” gyaɗa kai tayi”badamuwa
Zamu Iya zuwa”

Ruƙo Hannunshi tayi acikin nata”muje in nuna maka su” nurse jessica tana agaba
suna abayanta, tun da suka fito daga ɗakin Yake ƙarewa ko’ina kallo, agogo kaɗai
mutun zai kalla ya gane cewa dare ne amma donta hasken light bulbs na asibitin ba
za ka ta6a gane dare bane.

Nurses ɗin dake yin zarya da doctors sai satar kallon shi suke yi, hada masu yin
tuntu6e.

Ɗakin Haris suka Shiga, tun bayan fitar Angel bacci ya ɗauke shi.

Rabin jikinshi lullu6e da bargo, da sauri Danish ya ƙarasa daga gefen gadonshi
Ya zauna Yana kallon shi, nurse da Angel suna a tsaye suna dubanshi.

“Bacci ya ke yi Danish, ko zamu bari sai gobe idan Ya farka mu dawo” ɗaga mata
kai Yai alamar eh, dama burinshi ya gansu hankalinshi sai yafi kwanciya, ɗaura
hannunshi yai saman sumar kan Haris ya shafata a hankali, tsantsar farin Cikine
akan face dinsa’ mintuna Biyar kafin Ya miƙe, suka nufi ɗakin Batul, ko da suka
shiga, basu sameta a saman gadonta ba, nan fa hankalin Angel Ya tashi, “ina batul
taje” nurse jessica harta buɗe baki zata bata amsa, suka ji motsin fitowarta daga
toilet, Kamar a mafarki take kallonsu kafin ta tsayar da idonta kan Danish, da
ƙarfi ta ambaci sunanshi, da gudun gaske fa ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan
ƙirjinshi, ɗaura Hannayenshi yai saman bayanta sosai ya yi tighting ɗinta, daɗi
kamar zai kasheta, annurin fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake yi, da alama yaji daɗin
canjin rayuwar da suka samu.

Ɗagowa tayi da kanta daga saman chest dinsa, ido cikin ido suke kallon juna, tuni
hawaye sun cika idonta muryarta na rawa ta soma yin magana

“Ɗan uwana rabin raina, kaga canjin rayuwar da muka samu ko? Nasan Angel ta faɗa
maka komai, Danish ba zamu Iya misalta kewarka da mu ka yi ba, wlh naji daɗin
farkawarka nayi farin cikin ganinka” a tsanake ya furta mata”nima nayi farin ciki
Batul, Ina taya mu murna, ina yi mana fatan wannan ya kasance ƙarshen wahalarmu”
Angel da nurse jessica sai murmushi suke saki yayin da suke kallonsu.

“Danish nasan za ka ji wani iri, nan ba kamar prison ba, inda aka ƙuntata
rayuwarmu, tun muna Yara wannan ne karo na farko da muka fara tsintar kanmu awajen
prison cikin mutanan duniya, Iskar da muke shaƙa a yanzu ta ƴanci ce bata kurkukun
ƙaddara ba” kalamai masu daɗi take faɗa mashi

“Muna samun kyakkyawar kulawa awurin mutanan nan” tayi maganar tana nuna mashi
nurse jessica”sun bincika Lafiyarmu, kuma sun taimaka mana wurin samun sauƙi,
sannan muna samun Cin abinci har sau uku arana, komai muke so sunayi mana, Ina fata
kaima zaka saki jikinka da su sannan ka ba su haɗin kai donsu duba lafiyarka, idan
akwai wani abu dake damunka zasu taimaka maka wurin samun sauƙi in sha Allah,
sannan idan kana Jin yunwa ka yi masu magana zasu baka abinci, ba sai kasha wahalar
neman abunda zaka Ci ba...” muryarta na rawa ta ƙarasa maganar, hawaye tuni sun
cigaba da wanke face dinta

Ɗaura tafin hannunsa yai saman face nata, share mata hawayen fuskarta ya soma Yi
Calmly ya furta”its ok, stop shedding ur tears, ngde da shawararki, zan basu haɗin
kai,”

“Danish babu wasu kalmomi da zan Iya yin amfani da su wurin yi maku godiya kai da
Angel, Allah ne kaɗai zai Iya biyan ku, haƙiƙa kun taimaki Rayuwarmu kun gatanta
mu, kun yi mana silar barin mu kurkukun ƙaddara, duk wani cigaba da zamu samu a
duniyar nan kune sila, ba zamu ta6a mantawa da halaccin ku agare mu ba, kun fiye
mana iyayenmu sau dubu, matsayin da suka rasa awurinmu kune kuke ruƙe da shi....”
sosai ta fashe masu da kuka, Janyota yai zuwa saman chest dinsa ya ƙara yin hugging
dinta yana lallashinta.

Daƙyar ya samu Batul ta dakata da yin kukan, bayan ya raba ta da jikinsa, ta


rungume Angel sosai suka ƙanƙame juna, tsawon mintuna kafin suka raba jikinsu.

“Allah yabar Mana ke, Our Super star, Allah ya cika maki burikanki dake da
Danishi ɗinmu” murmushi kowan nan su ya saki, sun ɗan jima a ɗakin Batul kafin suka
Yi mata sallama, Sauran ɗaku nan su Azeeza suka shiga kowan nan su bacci ya ke yi,
Ya haƙura sai zuwa gobe zai gaisa da su.

Komawa ɗakinshi su ka Yi, nurse jessica tace da Angel, zata kawo mashi Abinci,
kafin ta dawo ta taimaka mashi Ya shiga toilet ya gyara jikin shi, amsa mata tayi
da toh, Bayan fitar nurse ɗin, Taja hannun Danish suka shiga toilet, tun da suka
shiga yake bin ko’ina da kallo, Karaf Ya ɗaura Idonshi Kan madubin toilet din A
firgice taga Ya Juya mashi Baya.

“Danish meya faru”? Hankali atashe tayi mashi Tambayar

“Bana son ganin shi,” ba ta yi mamakin jin abunda yace mata ba, tunawa da ranar
da tsohuwa tamira ta basu kyautar madubi, kowa ya duba fuskarshi, amma shi Yaƙi
Yarda ya kalle shi.

Dubara tayi wurin Cire Hijabin jikinta, taje gaban mirror ɗin ta lullu6e shi.

“Nayi maganin matsalar Juyo ka gani” a hankali Ya juya yana kallon mirror din nan
take ya sauke ajiyar zuciya, ganin ta rufe madubin.

“My Man, Ka fara Yin wankan, almost one week jikin ka bai ga ruwa ba, I’ll wait
for you outside.” Akan idon shi ta fuce, a bakin ƙofar toilet din ta jingina
Bayanta tana jiran fitowarshi, ta kasa kunne tana sauraron motsinshi, daɗi take ji
kamar wadda akayiwa albishiri da gidan Aljanna, a ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi
a ƙirga fatanta Allah yasa subar america batare da sun samu wata matsala ba.
Gaba ɗaya hankalinta baya atare da ita, gangar jikin ce kaɗai, ruhin Yana atare
da Danish dake acikin toilet, har Nurse jessica ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da
food trolley, ta gunguro shi zuwa gaban table, murmushi tasaki tana kallon Angel
dake maƙale jikin toilet door, aranta ta ayyana ko dai soyayya ce a tsakaninsu, don
wannan shaƙuwar tasu tafi ƙarfin a kirata da abokantaka.

Bayan ta ƙaraso gaban table din, ta soma jera kayan abincin saman shi, har ta
gama jera su, ta juya da food trolley din duk Angel bata lura da ita ba, Har ta
fuce daga ɗakin.

Jin motsin buɗe ƙofarshi, Yasa tayi saurin komawa gefen gado ta zauna tana
faman sakin murmushi kamar wata zautacciya.

Zuro ƙafarshi yai saman carpet dake gaban ƙofar shiga toilet ɗin, Kafin ya ƙarasa
fitowa, jikinsa da danshin ruwan wanka da yai, Ya maida uniform dinsa da aka sanya
mashi.

Tun ya fito idonshi na akanta, ya lura da tsantsar farin cikin dake akan
fuskarta, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba.

Gefenta Ya zauna yana ƙare mata kallo

“Na fito” sai da ya ambaci hakan tukunna ta ɗago suka haɗa ido wani irin
asirtaccen kallo suke jefa ma junansu kamar zasu haɗiye kawunansu tsabar ƙauna.

Lokaci ɗaya ta samu kanta da jin kunyar shi, Muryarta adabarbarce ta


furta”am..um.. Ga abincinka da nurse ta kawo nasan kana jin yunwa” ta yi maganar
haɗi da nuna mashi table din, ɗaura idonshi yai akan kayan abincin kafin ya dawo da
dubanshi gareta”baki jin bacci? Naga sauran ƴan uwanmu suna yin bacci, ta hakan na
fahimci dare ya nutsa”

Maƙe mashi kafaɗa tayi”bana jin bacci, inaso na zauna a kusa dakai, don na
taimaka maka da wasu abubuwan, tun da yau ka farka ba ka san komai dangane da wurin
nan ba, bana so in tafi in barka kai kaɗai a room” natsuwa yai yana kallonta, har
ta ƙare maganar tukunna ya furta mata”nagode da kulawarki agareni, kuma nagode da
nuna damurki akaina” still murmushin fuskarta bai washe ba
“Zamu ci abincin atare? Ko kin ci naki”? Yai tambayar yana duban fuskarta, Yafi
son tana kallon Cikin idonshi idan suna magana.

“Bana jin yunwa, amma Zan Iya taimaka maka ka ci naka” amsa mata yai da”okey, “
miƙa hannu tayi tana buɗe plates din, lafiyayyan abinci aka haɗa mashi Grilled
chicken with roasted vegetables, and black bean burger with sweet potatoes fries,
hada Green tea a mug.

“My Man, komi da ka gani a saman table ɗin nan duka sai ka cinye shi, yadda
kasha baccin nan na tsawon kwanaki nasan cikin ka babu komai ko ruwa ma babu, yanzu
faɗamin me ka ke son fara ci? Cikin kulawa take yi mashi magana.

“Ki za6a min” murmushi ta sakar mashi, Mug din ta miƙa mashi, Yasa hannu biyu ya
kar6a, a tsanake yake kur6anshi da zafi zafinshi, idonshi na akan face dinta, ta
ƙurawa adam’s apple dinsa ido.

Batasan Ya janye cup din ba sai dai taji muryarshi acikin kunnanta”me kike
kallo”? Yamutsa fuska ta ɗanyi”bakomai, tun da ka gama shan tea din, zaka Sha ruwa?
Ko lemu”? Girgiza mata kai yai”a’a, tea din ya ishe ni, sai dai wani abun”
Kamar wani ƙaramin yaro haka take tarairayarshi, da hannu ta dinga bashi grilled
chicken din yana ci, Idan ka kallesu a yadda suke zaune sai ka sha mamaki saboda
girman da yai ma Angel, Bata wuci Ya lullu6eta da faffaɗan kirjinshi ba, amma
saboda sabo da juna, da kuma shaƙuwa da ƙaunar dake a tsakaninsu bata ganin girman
shi.

Ɗaya daga cikin abunda ke burgeta, idan ta tura mashi abincin abaki yadda yake
motsa tattausan full lips nasa da kuma motsin Adam’s apple dinsa, komai nashi
ƙayatar da ita yake yi kamar yarda itama ta ke burge shi, a ƙarshe sai suka koma
suna feeding din junansu tana bashi abaki, Shima yana bata abaki.

Abunda basu sani ba, Har safiya tayi gari ya ware babu wanda Ya lura a cikinsu,
tuni sun kammala cin abincin, sun shagala suna kallon juna.

*ABUJA NIGERIA A GIDAN ƊAN IYA*

A round ƙarfe 10 na safe agogon Nigeria, tun bayan kammala sallar Asubahi da ta
koma bacci bata farkaba ba saboda Jiya sun sha fira da Aneelerh sun kusa raba dare
kamar ƴa’ƴan Aljanu, shiyasa yau take ta sharar baccinta kamar matatta, ta wawware
ƙafafuwanta saman mattress, ta saki baki da hanci, sai jan minshari ta ke yi kamar
ragon sallah, daɗin bacci hada yawu a gefen bakinta, Gajeran wandone a jikinta sai
ƴar farar half vest data zura, sumar kanta babu kitso zallar gashinta a hargitse ba
gyara.

Tayi zurfi acikin baccinta, Wayarta dake ajiye saman side drawer ta buga uban
ringing, Babu alamun zata farka har kiran ya katse, wani ya kuma shigowa, sautin ya
cika ko’ina banda kunnan zahra dake yin bacci.

Shigowa cikin ɗakin Aneelerh Tayi, jikinta asanye da doguwar riga, ta yi rolling
mayafi akanta, kaitsaye ta nufi drawer din ta miƙa hannu ta ɗauki wayar tana
faɗin”Allah ya shirya zahra, wannan bacci haka kamar matatta, ana ta kiran mutun
awaya wama ya sani ko arziƙi ne ke kiranta...” Waro ido waje aneeleeh tayi ganin
sunan mutumin dake kiran Aneelerh, Ya fito 6aro 6aro saman screen din, bakowa bace
face Hajiya Saratu Obinna, Jiki na rawa ta haye saman gadon takai hannu tana
bubbuga ƙafar zahra”banza, ki tashi arziƙine ke kiran ki, zahra ki tashi kada muyi
asara” yamutsa fuska zahra tayi muryarta kamar ta mashayin giya ta furta”dallah
wanene ke takuramin, ni a ƙyaleni inyi bacci na, ba dama mutun ya ɗan kwanta ya
runtsa sai an samu wani uban anacin ya tada shi’

cikin magagin bacci take yin sambatun. kiran har yayi rejecting, zuƙunnawa Aneeleeh
tayi saitin kunnan ta da karfi ta furta”Shashasha Hajiya saratu obinna ce ke Kira”
A haukace Zahra ta zabura Ta miƙe tana faman mutsustsuke ido, A fujajen take
fadin”Wai dagaske? Ina wayar? Gaba ɗaya tabi ta ruɗe jin an ambaci sunan Hajiya
saratu obinna, sai faman zazzare ido take yi.

Miƙa mata wayar Aneelerh ta yi “yo har yayi rejecting, Tun ɗazu nake ta ƙoƙarin
tada ki, Kinƙi ki farka gashi yanzu kin ja mana asara....” bubbuga katifa zahra
tayi da hannu tsabar takaici hada hawaye akan fuskarta”Aunty aneelerh, kin karyamin
jari, meyasa da kika tada ni naƙi tashi baki shiga toilet kin ciko bokiti da ruwa
kin watsa mun ba”?

Babu wasa akan face dinta ta yi maganar, Sakin Baki aneeleeh tayi tana kallonta

Zahra ta ci gaba da yin kuka tana faɗin “Nashiga uku, wayyo Allahna, ni wlh bakiyi
min adalci ba, wama ya sani ko kujerar Hajji za’a raba mana,” sosai ta fashe ma
Aneelerh da kuka. Lamarin ya ɗaure mata kai, ta rasa ina zahra da mahboob suka gado
shegen son kuɗi, sai dai tafi tunanin ta 6angaren mahaifinsu ne.
Lallashinta ta soma yi”Kiyi hakuri sister kukan Ya isa haka, wata’kil ta ƙara
Kiran ki,” cikin shessheƙar kuka tace”taya za’ae ta sake kira na, bakisan halin
masu kuɗin nan ba, basu ɗaukar raini, za ta yi tsammanin dagangan naƙi ɗaga
kiranta, Wayyo Allahna aunty Aneelerh, nayi wa arziki ƙulli, har ƙiyamil laili nayi
akan Allah ya bude mun kofofin samu, da kuma miji nagari a sabuwar shekarar da zamu
shiga...” dariyace kumshe abakin Aneelerh.

Dafa kafaɗarta tayi”Sorry My lovely sis, Yanzu abunda za’ae, Ki kira Layinta mu
gani ko zata ɗaga” kar6ar wayar tayi daga hannun Aneelerh, Yatsun hannunta har
kerma sukeyi sam babu natsuwa, kiran layin ta soma Yi, tamkar zata fashe da kuka ta
kalli Aneelerh”line busy, dama ni nasani, wlh basa ɗaga kira, idan ba su suka kira
mutun ba”

Aneelerh tace”mu ɗan ƙara haƙuri, zuwa anjima sai mu ƙara jaraba kiran layinta,
yanzu ki tashi ki shiga toilet ki ki gyara jikin ki, zan Jiraki anan,” cikin
shessheƙar kuka ta amsa da toh, kafin ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ta
shige.

Bayan shigarta da mintuna biyar Aneeleeh tana zaune tsakiyar gadon tana jiran
fitowarta, zuciyarta acunkushe take da tunanin baby junaid ɗinta tayi kewarshi, tun
shekaran Jiya Uncle abdallah da hajiya adama suka koma gidansu, anyi rabuwar
mutunci sun nemi alfarma Junaid ya zauna wurinsu na tsawon 2 weeks, zai dawo gida,
sannan duk weekend za’a dinga kai masu shi, yanzu haka yana acan gidan nasu, tsawon
kwana uku da yayi acan kullum ne sai ya matsa masu akan su kira mashi Mommyn nasa,
wani lokacin tun kafin ta farka daga bacci kiran su ke shigowa wayarta saboda
jarabar junaid.

Tayi zurfi cikin tunaninta, Wayar Zahra ta soma yin ringing, Kafin ta wurga
idonta kan inda zahra ta ajiye wayar saman drawer, da ƙarfi taji sautin buɗe ƙofar
toilet, Ras taji gabanta Ya fadi ganin zahra ta watso aguje, jikinta duk kumfa daga
ita sai gajeran towel tayi ɗaurin gaba da shi, hatta fuskarta kumfar sabulu ce,
miƙa hannu tayi ta rurumi wayar, tsabar zumuɗin ganin wanene ke kiranta, fatanta
Allah yasa hajiya saratu obinna ce, cikin sa’a idonta yai mata nuni da sunanta akan
screen, sai ƙoƙarin ɗaga kiran takeyi kumfar hannunta ta hana touching din yin
aiki, kamar zata fashe da kuka, sai da aneelerh ta taimaka mata wurin answer mata
call din tukunna ta samu natsuwa, a Hands free ta sanya kiran don suji me zata je
Cikin girmamawa zahra tayi mata sallama”Assalamu alaikum” kamar tana agabanta.
On the other hand sautin muryar hajiya saratu ya karaɗe kunnuwansu
“Wa’alaikum salam”
“Ina kwana hajiya, fatan kun tashi Lafiya, wlh bana a kusa da wayar ne, kunata
kira bansamu damar ɗagawa ba, da yake na ɗan shiga toilet ne”

Aneeleeh dake zaune saman gado, dariyace ta kubce mata da sauri ta cakumi pillow
ta toshe fuskarta dashi don kada sautin Ya fita, bakomai ne ya sanyata yin dariya
ba face yadda zahara keyin waya kamar ƴar maroƙa, ga kumfa a jikinta.

“Bawani abu ai, nayi maki uziri, dalilin dayasa na kira layin ki, last time da
kukayi mana decoration aikin ku ya yi mana kyau, muna so za’a ƙara Yi mana wani
next week, sannan muna so za’a fidda mana anko wanda zai dace damu”

Da sauri zahra ta kar6e da cewa”in sha Allah hajiya komai kuke so za’ayi yadda ya
dace, hada ƙunshi da kitso idan akwai mai buƙata”

Hajiya saratu tace”okey, You can send me the list of your services and I’ll add
what I want to the list, through text message zaki tura min”

“Toh hajiya in sha Allah, Mun gode sosai, da kiranmu da ku kayi, kuma in sha
Allah zaku same mu masu biyayya ga duk abunda kuke so,” bayan sunyi sallama da
Hajiya saratu, Zahra ta sauke nauyayyar Ajiyar zuciya, Ta fasa ihu Tana
faɗin”Alhamdulillah! lokacin Yin arziki na Yayi, wai yau ni ce Aunty saratu ta kira
awaya? nayi mamaki wlh, matar tana burgeni bata ɗaukar raini, akwai harkar arziƙi.

Ta saki baki sai sambatu take yi, Kumfar Jikinta duk ta bushe har ƙasan tiles
ruwan ke zuba, sautin dariyar Aneelerh ne Ya fargar da ita, da sauri ta jefa wayar
saman mattress din, ta ruga da gudu ta faɗa toilet tana dariya.

Daƙyar Aneeleeh ta samu ta tsagaita da yin dariyar. Ta ɗago da kanta daga jikin
pillow ta jingina bayan jikin head board.
“Aneelerh” muryar Mamie ce ta ratsa kunnanta, zumbur ta sauko daga saman gadon
ta nufi kofar ɗakin, shigowa ɗakin Mamie Ta yi suka ci karo da ita”oh dama kina
anan? Inata kiranki na duba ko’ina ban ganki ba” Aneelerh na murmushi tace”mamie
kema kinsan bani da wurin zuwa a gidan nan inba ɗakin Ƴar uwata zahra ba”
“Okey, ina zahran”?

“Ta shiga toilet yin wanka, amma takusa fitowa

Mamie tace”Okey, idan ta fito, muna jiran ku a dining, ku zo muci abinci”

Ta amsa mata da toh, bayan fitar mami ɗakin, komawa ta yi gefen gadon zahra ta
zauna, bada jimawa ba zahra ta fito chest dinta daure da towel, da zolaya Aneelerh
tace”Lashe money an fito lafiya”? Tuntsirewa zahra tayi da dariya tana fadin”aunty
aneelerh kuɗi duniyane, Dole inso kuɗi, saboda sune maganin talauci, maganin
ƙasƙanci da wulaƙanci, idan kina da kuɗi kin fi ƙarfin raini wlh, girmama ki za’a
dinga yi kamar wata basarakiya, taya mutum bazai so kuɗi ba? Yanzu fa ko a dangi
masu kuɗi sune masu faɗa aji, idan baka da kuɗi toh baka da banbanci da Allon
bango”

Fashewa Aneeleeh tayi da dariya, zahra ta zaƙe sai kora mata jawabi ta ke yi
dangane da kuɗi.

“Zahra wasu kuɗinfa ba alkhairi bane, suna kai mutun ga shagalar duniya har ya
halaka”

“Aunty Aneelerh, nima ai bana roƙon Allah yabani kuɗi kaitsaye batare da nace
Allah yabani masu albarka ba, kuma ni burina inyi arziƙi don al’umar annabi su
amfana da ni, Ina kwaɗayin inga na taimaki marasa ƙarfi....”.

“Zahra Allah ya dubi kyakkyawar niyarki, inayi maki fatan Alkhairi”


“Ameen auntyna”

Shaf shaf ta kammala shiryawa, cikin riga da skirt, ta dawo gefen Aneeleerh ta
zauna bayan ta ɗauki wayarta

“Ki tashi muje muci abinci, su mamie suna jiran mu a dining”


“Inaso ne in fara turama aunty saratu list na abunda mukeyi, zaki Iya zuwa kada
su ji mu shiru” miƙewa Aneelerh tayi daga gefen gadon ta fuce daga ɗakin.

Through text message ta tura mata saƙon kamar haka

Here’s a list of services that “Zahra’s World of Beauty” could offer:

- Bridal makeup and hairstyling


- Event planning and decoration
- Haircuts, color, and styling
- Manicures and pedicures
- Facials and skin care treatments
- Massage and body treatments
- Waxing and other hair removal services.

Bayan ta kammala rubuta sakon a ƙalla saida ta maimaita shi yayi sau ashirin
gudun kada ace tayi kuskure kafin ta tura mata, fuskarta ɗauke da murmushi ta ajiye
wayar saman pillow, ta miƙe ta nufi falo domin Yin breakfast, fatanta Allah yasa
Hajiya saratu ta mayar mata da martanin saƙon da wuri, taci buri sosai akan zuwa
estate dinsu, ko dan ta haɗu da Owais idan Allah yasa lokacin ya dawo ƙasar.

*KURKUKUN ƘADDARA*

*AN YANKA TA TASHI*

Babban ɗakin tarone mai girman gaske, wanda akeyiwa laƙabi da fadar matsafa,
Mallakin shuwagabannin kurkukun ƙaddara, ta ko’ina manya manyan matsafane maƙil
acikin fadar, zazzaune saman kujeru dake a jere tsakiyar fadar, kowannansu yana
sanye cikin shiga ta baƙaƙen dogayen riguna masu huluna, sunyi 6adda kama ta yadda
mutun bazai ta6a Iya ganin koda ziririn gashin kansu bane, Hannayensu da
ƙafafuwansu baƙaƙen safunane, Yayin da fuskokinsu sun sanya masu mask me suffar
ƙwarangwal gwanin ban tsoro, saƙo da lungu ta fadar, Wasu Gabza gabzan giants ne
daga masu ƙaramin miƙami har izuwa manyansu masu star uku a gaban kakinsu, wata
irin ƙira garesu mai matuƙar ruɗarwa, rikitarwa da razanarwa da kuma tsoratarwa,
kallonsu kaɗai zai Iyasa zuciyar mutun ta buga, Ga tsawo da Allah yayi masu tun
daga kan tsayuwarsu zaka tabbatar babu ɗigon imani akansu.

Daga can saman karagar fadar, wasu jigunannun arm chairs ne guda shidda ƴan ubansu,
mutane shiddan dake zaune saman kujerun dogayen rigunane launin jajaye na maza a
jikinsu masu huluna, baka ta6a Iya tantance suffarsu saboda sun 6oye ko’ina na
jikinsu, hannyensu na ruƙe da Sanda wadda aka ƙerata da zallar zinari, daga gabansu
zungureran teburi ne, samanshi maƙil Yake da kayan ciye ciye dana shaye shaye daga
ciki hada Jinin mutun da farfesun naman mutun ga zungura zunguran kwalaban giya, da
Kayan marmari nau’i kala kala, da gasasshen nama na dabbobi daban daban.

Komai na fadar matsafan tun daga kan ƙofofi da tagogi da fentinta da jan carpet din
dake shimfiɗe ƙasanta, gaba ɗaya Launin baƙi da Ja ne, saman rufin fadar wasu
haɗaɗɗun fitilune masu haskaka cikinta.

Zanunnukan dake a jikin bangon fadar, na kan ƙwarangwal ne, da yatsun hannun
shaiɗanu masu akaifu zaƙo zaƙo da sauran zanunnuka masu ban tsoro.

Daga gefe ɗaya tacan 6angaren da Arm chairs din nan suke Tanƙameman madubine wanda
suke Kira da Allon tsafi, gaba ɗaya Hankalin matsafan yana akan Allon tsafin nasu,
fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, ga dukkan alamu wani abu suke kallo wanda
yai silar ɗauke masu hankulansu..........

(Nima kuma na ɗauke alƙalamina)

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin
yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct
number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

_The Prisoners E21🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

A ƙalla sun shafe mintuna suna kallon Allon tsafin, ga dukkan alamu sun girgiza da
ganin abun da idanuwan su ke gane masu, Hankulan su sun yi matuƙar tashi, abun ya
yi mugun ɗaure masu kai, bakomai bane suke kallo acikin Allon tsafin face Garkuwar
kurkuku tare da Angel, duk wani motsinsu akan idonsu tamkar video haka suke
ganinsu, lokaci ɗaya Allon tsafin yayi duhu hoton fuskokin su ya 6ace.

Kowan nan su ya sauke Ajiyar zuciya, sun natsu suna jiran jin bayani daga bakunan
shuwagaban nin su.

Ɗaya daga cikinsu ne yai gyaran murya, da wata irin kakkausar murya mai sautin
gaske tamkar bata mutun ba, ya soma Yin magana Cikin harshen su na shahararrun
matsafa ni kuma ina fassara maku.

“Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu
miƙe tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za’ayi nasara akan mu, Ko a
tarihi ba’a ta6a samun prisoners ɗin da suka tsira daga kurkukun ƙaddara ba, su ne
na farko kuma sune na ƙarshe, da farko sunyi nasarar ƙetare kurkuku da taimakon
Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani
mahaluƙin da ya isa ya iya ƙetare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare
da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba
akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar
data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja
har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya ɗauke shi munyi nasarar yi mashi
abunda ya dawo gare mu sai dai wani abun al’ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma
ma gangar jikin shi, kamar yadda kuka gani a allon tsafin mu, shin me ya jawo
hakan”? Yai tambayar yayin da yake gyaran zaman shi.

Mutumin dake a gefenshi, Ya ɗaura da cewa”Yarinyar da ke atare da shi itace


silar komai, kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, Cewa itace za ta yi silar
tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, gangancin da mu ka yi shine Haɗa su wuri ɗaya da
garkuwar mu, sakamakon shaƙuwar da sukayi a tsakanin su, taja shi ga faɗawa tarkon
sonta, mu kan mu bamu ta6a tsammanin Garkuwar prison zai Iya kamuwa da matsanancin
so irin haka ba” dakatawa yai da yin maganar yana motsa yatsun hannunsa, kafin ya
cigaba da cewa

“Sai dai har yanzu bamu rasa power ɗinmu ba, Garkuwa namu ne har abada, mu ke
ruƙe da masarrafin da zamu Iya sarrafa linzamin shi, mu kaɗai ne mu ke da iko da
shi, ba zamu ta6a yin danasanin Ɗaura shi amatsayin magajin kurkukun ƙaddara ba,
kuskure ɗaya da muka tabka shine sakacin da mu ka yi da har ya samu nasarar guduwa
daga kurkuku, Ni ban damu da sauran Yaran da suka ku6uta ba, saboda basu da amfani
a wurinmu, mun ci moriyar su, mutun ukun ne sune rauninmu, Na farko Garkuwarmu dole
sai da shi za’a Iya Cin galaba akanmu, Na biyu ƙaddarar kurkuku, yarinyar ta fi
sauran hatsari tun da har ta Iya Jan hankalin garkuwarmu, wanda nayi imanin da ace
babu ƙauna a tsakanin shi da yarinyar ba zai ta6a taimakon sauran ƴan uwan shi don
su gudu daga tarkon mu,” Ya faɗa yana mai jan dogon numfashi Ya fetsar da shi, ya
cigaba da faɗin “Itace silar komai, kuma itace kaɗai zata Iya sarrafa shi bayan mu,
idan kuwa hakan Ya faru zai Iya fallasa mana sirrin mu ya kuma taimaka wurin ruguza
kurkukun ƙaddara”! Da ƙarfi Ya ambaci hakan Yana mai nuna fusatar shi.

“Yarinya ta ƙarshe itace bugun zuciyar kurkukun ƙaddara, kamar yadda ya zo mana a
allon tsafin mu, idan har muka samu nasarar Cire Zuciyarta daga ƙirjinta zamu samu
ƙarfin Iko fiye da wanda muke da shi a yanzu, Ita kuma ƙaddarar kurkuku dole mu
dawo da ita cikin mu idan har muna son ta zamar mana ƙaddara mai kyau, barin ta
awaje shi zaisa ta zamto mummunar ƙaddara agare mu” Tamkar mayunwacin zaki haka
yake kora masu jawabi yana fitar da huci.

Bayan ya rufe baki Na gefen shi ya soma magana da wata irin murya ta dattawa
waɗanda suka Shahara a fagen zalunci.

“Tun fil azal, Banso Muka damƙa amanar mu ga tsohuwa tamira ba, dama tun lokacin
Sai da na musa akan hakan, Ni dama nasani Jinin Habibullah ba zasu ta6a zama
amintattun mu ba, sai gashi sun yaudaremu sunci amanar kurkuku, sun kashe mana
Zafreen ɗaya daga cikin shuwagabannin mu, babu wanda ya ta6a tsammanin zasu Ci
amanar mu ita da ɗanta Salsabeel, sai da suka bari mun basu yarda mu su kuma suka
butulce mana, haƙiƙa Nayi takaicin rasa gangar jikin tamira, da ba abun da zai hana
mu azabtar da ita, mu sa6ule naman jikinta sannan muyi farfesun shi muba ma Karnuka
su shanye roman, amma duk da haka bamu makaro ba, Zamu huce haushin mu akan ɗanta
Salsabeel” mutumin da yayi maganar babu ɗigon imani akansa.

Bayan ya dasa aya a maganar shi, wani daga cikin shuwagabannin Ya numfasa tare da
cewa”Garkuwa ya yi mana mummunar 6arnar da ba zamu Iya gyarata ba, bamu ta6a
tsammanin zai Iya yi mana haka ba, sai dai ba zamu Iya hukunta shi ba, saboda shi
jinin mu ne, abu ɗaya da zamu Iya yi mashi shine mu hana shi jin daɗin rayuwarshi
da Yarinyar, mu shiga tsakaninsu, horon da zamu bashi kenan, sannan zamu ci gaba da
sarrafa shi wurin azabtar da mutane, kafin muyi nasarar dawo da su Cikin mu, hikmar
yin hakan mutane zasu fara tsoranshi suna nuna mashi ƙyamata, zai ji duk duniya
kamar ba’a sonshi ne, kunga anan zai yi tunanin mu kaɗaine gatanshi, kurkukune
kaɗai inda zai zauna yayi rayuwarshi ba tare da ƙuntata ba, daga lokacin daya fara
wannan tunanin mu kuma zamu samu damar kwashesu su ukun mu dawo da su cikin mu”! Ya
kai ƙarshen maganar tare da buga hannun arm chair ɗin da yake a zaune, gaba ɗaya
matsafan suka fashe da dariya mai sautin gaske tamkar ana bubbuga ganga, jikinsu
har jijjiga ya ke yi saboda tsabar yadda suke yin dariyar kamar dokuna.

“Mun Fi ƙarfin mutun, Ko mutuwa tsoron tunkararmu take Yi, shiyasa muka daɗe
muna sheƙe ayarmu, shan jinin mutune da cin tsokar naman su yanzu muka fara, Rainon
Yara ba zamu fasa ba, zamu cigaba da tarasu a cikin kurkukun ƙaddara muna biyan
buƙatarmu dasu domin samun ƙarfin ikonmu” Ihu suka dinga Yi sunayin shewa sautin
muryoyinsu tamkar zasu fasa bangon Fadar, kusan atare matsafan suke miƙe tsaye suna
taka rawarsu ta matsafa, kowan nan su, ya ɗauki abunda yake ra’ayin ci asaman table
wasu giya, wasu farfesun naman mutun wasu jini wasu kuma naman dabbobi suke ci,
Yayin da wasun su a tsaye suke saduwa da junansu kamar dabbobi wa’iya zubillah.

*DAULAR OBIE ESTATE*

*Dr. jazz❤*

Ƙudundune yake acikin bargo, saman katafaren gadonshi na gidan Sir mubarak, cikin
muryar raɗa yake yin magana a wayar shi.

“I’m not working today, I’m at home. yanzu haka da ni ke yi maka magana Ina
akwance saman gadona” shiru ya ɗanyi yana sauraron mutumin da suke yin wayarshi,
can yaci gaba da cewa”Boss Man kasan bana wasa da aikin ka, idan ka bani umarni
jiki na rawa nike yin shi, ko jiya na shiga gidan gonar na duba lafiyar kajin, sai
dai muce Alhamdulillah, Jikin su yayi kyau baka ga yadda suke tafiya ba tsokar
jikinsu har girgiza take yi saboda ƙoshin lafiyar dake gare su” ya ƙare maganar
muryarshi da sautin dariya

“My Boss Man, Amma dani da kai zamu ɗubi na azumi ko? Ko zamu bari sai sallah Ayi
layya da su”? Tuntsirewa yayi da dariya jin amsar da mutumin ya bashi muryarshi
cikin harshen turanci yake yi mashi magana.

“Amma ai kasan nayi ƙoƙari, tun da na fara kiwon kajin nan wlh ko ɗaya ban ta6a
gigin kamawa don in yanka ba, kuma miyau na ya biya fa” da shagwa6a ya ƙare
maganar.

Abun da bai sani ba, tun da ya fara yin wayar, Sir mubarak Ya shigo ɗakin jikinshi
sanye da kakin sojoji, Hannunsa biyu ruƙe da faffaɗan plate, daga saman shi an jera
Chocolate raspberry cupcakes.

Ya shigo ɗakin ne da niyar ya faranta mashi, tun lokacin da turai ta faɗa mashi
game da gorin da Hajiya saratu ke yi mashi akan cewa shi ba mahaifin shi bane sai
yaji ya ƙara ƙaunar yaron yana matuƙar sonshi.

Lamarin Ya ɗaure mashi kai, ba tun yau ba, Ya jima yana mamakin wayar da dr jazz
ke yi akan Kajin gidan gona, cikin tafiyar sanɗa Sir mubarak Ya ƙarasa shiga ɗakin
ya zauna gefen gadon shi hannun shi ruƙe da plate din, Ya kasa kunne Yana sauraron
tattaunawar jazz da Boss man din shi.

Jin shiru Jazz bai ƙara yin magana ba yai tunanin ko ya kammala yin wayar ne,
Gyaran murya ya yi mashi.

Jazz da ke ƙudundune cikin bargo yai lamo jikinshi ya kama yin kerma jin muryar Sir
mubarak Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba.

“Jazz nasan idonka Biyu Ka tashi inason magana dakai” A hankali Ya zame bargon,
Ƴar singlet ce ajikinshi tare da Gajeran wando, sumar kanshi duk ta hargitse.

Yana faman mutsustsuke ido da hannu ya saci kallon Sir mubarak


Muryarshi da kasala Ya furta
“Daddy ina kwana, ka tashi lafiya, ya mommy’ adabarbarce ya ambaci hakan sam bai
lura da plate din hannunsa ba.

Babu alamun zai amsa mashi gaisuwar tashi, wani irin kallon tuhuma Yake jefa
mashi, Ƴan kame kame jazz ya kama Yi, don Ya fahimci dadyn nasa yaji komai da ya ke
faɗi a wayarshi.

“Jazz, da wa ka ke yin magana a waya? muryar shi a kausashe Ya jefa mashi


tambayar.
Cikin rawar murya Jazz yace”daddy abokina ne dr fawan ai na faɗa maka tare da shi
muka buɗe gidan kaji muna yin kiwon su’ yaƙi yarda su haɗa ido da uncle mubarak.

Gyaɗa kai yai”Jazz zan ƙara jan kunnanka akan Ka kiyaye mutanan da za ka yi
mu’amala dasu! Bana son kayi abunda zaka Yi danasani, Ni bana zargin ka da wani
abu, Ina yi maka kyakkyawan zato My son, Nasihar da zanyi maka shine Kaji tsoron
Allah komi za ka yi a duniyar nan kada ka manta Allah Yana ganin ka, kuma zaka koma
gare shi ne, jin daɗin duniyar nan ƙalilan nan komai da muka samu anan zamu barshi,
a kowani yanayi na rayuwa mutawa zata Iya riskar mutun, me yakamata muyi? Mu
kasance muna aikata aikin Alkhairi akoda yaushe, sannan duk runtsi duk wuya kada ka
ta6a karya zuciyar wanda ya aminta dakai.....” cikin kwantar da murya Sir mubarak
Yake yi mashi nasiha, jikinshi duk yai sanyi, idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla
Ya ɗago Yana kallon fuskar Sir mubarak, Har Ila yau yana mamakin Halin Sir mubarak
da Obinna suna da mutunci da daraja ɗan adam, duk da kasancewar shi ɗan mai aikin
gidansu sun maida shi tamkar jinin su, tun kafin Ya mallaki hankalinshi suke yin
ɗawainiya dashi, cin shi shan shi suturarshi da karatun shi sune suka ɗauki nauyin
komai na rayuwarshi.

Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar sir mubarak ta katse shi”Ina magana ka
tsareni da ido” da sauri Ya sunnar da kanshi ƙasa, Ƙwallar da suka taru cikin
idonshi tuni sun soma gangarowa saman kuncinsa.

“Jazz Why are you crying”? Ya faɗa yana duban face dinsa.

cikin shessheƙar kuka ya soma magana”nagode sosai daddyna, ina matuƙar alfahari
dakai, saboda ƙaunar da kuke nuna mun kai da baba, ban ta6a danasanin kasancewata
acikin family dinku ba, Ina jin daɗin nasihar da ka ke yi min daddy, ka maidani
tamkar ɗanka komai na rayuwa kana Yi min...” murmushin gefe fuska sir mubarak yaɗan
saki.

“My son ya isa Haka, share hawayenka, Ni dai fatana Ka ruƙe mutuncinka Jazz, Kada
ka bani Kunya, inaso ka zama abunda duniya zata yi alfahari dakai”

Jinjina kai yai tare da ɗago da kai Ya ɗaura rinannun idanuwanshi akan fuskar Sir
Mubarak “In sha Allah, Nayi maka alƙawarin hakan, Zan kama mutuncina kuma bazan
ta6a baka kunya ba”

Miƙa mashi plate din hannun shi yayi

“Your mother made this for you. I know how much you love cupcakes.” fuskarshi ɗauke
da ƙayataccen murmushi Yake dubanshi, Hannun Dr Jazz Har kerma Yake yi wurin kar6ar
Plate din
“Kayi brush kuwa? Naga kamar yanzu ka farka daga bacci,”

Girgiza kai yai”ban kaiga Yi ba, Yanzu zan shiga toilet din’
“Okey, Ka ajiye plate din idan ka fito sai kaci” ƙaƙaro murmushi yai akan face
dinsa”Okay, Dad, I appreciate your care.”
Miƙewa sir mubarak Yai”Ni zan wuce Office, ka kula mun da kanka”

“Daddy Allah Ya dawo min dakai Lafiya, Allah ya tsare mun ya kare mun kai
daddyna”

Yaji daɗin maganar Jazz, har saida ya dan juyo ya kalle shi kafin Ya fuce daga
ɗakin”
Nauyayyar Ajiyar zuciya Jazz ya sauke, kalaman Sir mubarak sun tsaya mashi
aranshi, Cikin sanyin murya ya furta”Am sorry My daddy, Na riga dana jefa kaina
Cikin Tarkon da bazan Iya fidda kaina ba, addu’arka kawai nake buƙata Allah Ya bani
ikon cinye jarabawar nan”!! Ya ƙare maganar tare da saukowa daga saman gadon ya
ɗaura plate din hannun shi saman Table Ya nufi toilet Ya shige.

*Hajjaty the head maids💋*

A tsanake Take Yin tafiya tana nufar haɗaɗɗen garden din gidan, ta ɗauki wankan
Sari Launin Ja, Hannunta biyu ruƙe da Tray na Kayan Marmari tare da mugs biyu na
black tea, ta ko’ina ƙamshin turare ne ke fita a jikinta, tasha uban ado na sarƙar
wuya da awarwaro, make up din fuskarta Ya ƙara mata Kyau.

Tun kafin ta ƙarasa shiga garden din idanuwanta suka hango mata, Obinna tare da
babban amininsa daya kawo mashi ziyara, kallo ɗaya zaka yi mashi ka gane Inyamuri
ne, fari ne fat sumar kanshi da jagirarshi dukkansu hurhurace, hatta dogon Gemunshi
fari ne fat kalar na Obinna, sunyi shigar Manyan Kaya na hausawa, zaman hular
kanshi zai ƙara tabbatar maka da ƙabilar shi, suna a zaune saman shimdiɗar da
Hajjaty tayi masu ta alfarma, kowan nan su ya tada kanshi saman tuntun kalar na
sarakuna.

Tun kafin ta ƙaraso gabansu, ƙamshin turarenta Ya daki hancinan su, abokin obinna
Ya furta”masha Allah” Ya kafe ta da ido yana faman Jan gemunshi.

Zuƙunnawa tayi agabansu Ta sauke tray din, cikin girmamawa ta gaishe da


abokin”sannu da zuwa, ina wuni Ya iyali” lumshe idonshi yai tare da ware su kan
fuskarta, Obinna dake kallonshi ya fahimci kamar baya a hayyacinsa, hajjaty ta tafi
da imaninsa, har Ya gaza buɗe baki Ya amsa mata gaisuwarta, Sai faman bin jikinta
yake yi da kallon ƙurulla duk tabi ta tsargu.

“Ba ka ji tana gaishe ka ba ne”? Sai da obinna Ya ambaci hakan tukunna Ya iya
motsa la66ansa wurin furta”Lafiyalou madam, fatan na same ku lafiya”? Muryarta na
rawa ta furta lafiya lou

“Obie, dama matarnan tana agidan nan har yanzu? Yayi tambayar ne saboda lokacin
da tazo yi masu shimfiɗa bai kaiga zuwa gidan ba.

Harara obinna ya ɗan watsa mashi a fakaice, kafin ya bashi amsar tambayar shi sai
da ya fara kallon hajjaty yace”tashi ki tafi, mun gode” miƙewa ta yi tare da juya
ta nufi hanyar fita garden din tsabar sauri kamar zatayi tuntube.

Bayan tafiyarta obinna ya dubi aminin nasa”shegen bisa, faɗamin waya koya maka
kallon mata? Ni dai ya iya sanina dakai mace bata agabanka, sai gashi yau kana
neman zauce wa saboda kaga Mace” da zolaya ya yi mashi maganar.

Tuntsirewa Inyamurin yai da dariya yana faɗin”Don kawai na gani na yaba, matar ce
ba ƙaramin burgeni take yi ba, inason mace mai tsafta da iya ado, sannan kasan Ni
ma’aboci son ƙamshine, gaskiya ta tafi da imanina, ka taimaka min inaso na mallake
ta, dagaske nake ba wasa ba”

Da mamaki akan fuskar obinna ya ɗan zaro idona yana kallon shi, yayi mamakin jin
abun da ya furta, kuma ga dukkan alamu dagaske yake har cikin ranshi.

“Amma dai zolaya ce wannan ko”?


Jan gemun shi yai tare da cewa”na ta6a yi maka zolaya akan irin wannan maganar”?
Girgiza kai Obie yai” Bamu ta6a ba, sai dai nayi mamakin kalamanka, tun da muka
taso baka ta6a nuna kana buƙatar mace ba, ka haramtawa kanka tara Iyali, gaba daya
rayuwarka akan kasuwancinka ta ƙare”

Fuskar Inyamurin da fara’a ya yace”wannan karan dagaske nake, Inasonta da aure


mutumina, ka yi min hanyar da zan samu shiga wurinta, don bana son abun ya ɗau
lokaci” farin cikine tsantsa akan fuskar obinna abunda yajima yana yi mashi fata
“In sha Allah, zanyi maka ƙoƙarin yin hakan, nima nayi maka sha’awar auranta,
Matar tana da hankali da natsuwa”

Cigaba da tattaunawa sukayi a tsakaninsu.

A 6angaren Hajjaty kuwa, Jikinta duk yai sanyi tun da ta baro garden din gabanta ke
faɗuwa, tsigar jikinta na tashi, duk akan kallon da abokin obinna yayi mata.

Gaba ɗaya hankalin ta baya atare da ita, tafiya ta ke yi Zuciyarta nayi mata saƙe
saƙe, har ta ƙaraso entry hall tana ƙoƙarin bi ta ƙofar palourn Cikin rashin sani
suka bangaji juna ita da Hajiya saratu da ke ƙoƙarin fitowa daga falon, Ta kimtsa
cikin shiga ta alfarma, da alama wurin aiki zataje.

Da sauri Hajjaty ta ɗago su ka yi tozali da Hajiya saratu, Rass taji gabanta Ya


faɗi, Muryarta na kerma ta furta”kiyi haƙuri ban lura dake ba...” daƙyar ta ƙare
maganar ganin irin ƙasƙantaccen kallon da Hajiya saratu ke watsa mata.

Tana huci ta furta”baki da hankaline? Ko makauniya ce ke? Wato tsabar nuna isa
har kin kai matsayin da zaki iya haɗa kafaɗa ni ko”! Fuskarta a ɗaure tamau tayi
maganar.

Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata lura da pravin dake abayan
Hajiya saratu ba, Ya shirya cikin black suit, hannunshi ruƙe da wayarshi daya kara
a kunnanshi, Waya yake yi amma hankinsa na akan Hajjaty da hajiya saratu

“Bada sanina na bangaje ki ba, hankalina baya atare dani”

Harara Hajiya Saratu ta watsa mata tamkar ƙwayar idonta zata faɗo ƙasa”Ƴar
rainin wayau, wai bana hanaki shafa mahaukacin turaren nan a jikinki ba? Ke baki da
hankaline? an gaya maki Zawarci haukane” Rai a6ace ta faɗi hakan tare da ruƙo
Mayafin Sarin Hajjaty da hannunta.

Idanuwanta tuni sun ciko tab da ƙwalla.

“Wlh daga rana irin ta yau idan na kuskura na ƙara jin ƙamshin turaren ƴan borin
nan naki saina sauke maki kwandon rashin mutunci akanki,”

Azafafe ta ƙare maganar, tare da ingiza hajjaty tayi taga taga zata faɗi, Pravin
harya Yunƙura zai tarbeta, da sauri Ya fasa ganin matsiyacin kallon da Hajiya
saratu ta watsa mashi

“Wuce muje” cike da isa ta ba shi umarni, da sauri Yabi bayanta suka nufi parking
space.

Da ido hajjaty tabi su da kallo, hawaye tuni sun wanke fuskarta, jikinta na rawa
ta nufi cikin gidan, masu aikine ke ta kai komo acikin babban palourn.

Ba tare data bari sunyi tozali da wani ba, tayi saurin nufar bedroom dinta,
harta kusa shiga taci karo da twins sunyi shirin zuwa office.

Atare suka ɗago suna kallonta, muryarta na rawa ta furta”ina kwananku kun tashi
lafiya”
Harara Zayn ya watsa mata”ji wata tambayar rainin wayau nan, taya zaki tambayi mun
tashi lafiya? Bayan gamu kin gan mu a tsaye kan ƙafafunmu”

Zaid yace”Zayn, please watch your tongue Hajjaty tamkar uwa take agare mu,” a
harzuƙe yace”what! ƴar aikin ce zata zama uwar mu? oh Ko dan saboda tana ƴar india?
To ai mu ba indiyawa bane ubanmu ne ɗan can, Nifa baki burgeni saboda ban yadda
dake ba, ina zargin hada ke ake cin amanar mahaifiyar mu”
Afirgice Hajjaty ta zazzare ido tana duban fuskar zayn da yayi mata, tuni zufa ta
soma tsastsafo mata.

“Pls zayn ya isa haka, idan ba zaka girmamata ba, bai kamata kana gaya mata
magana akan idonta ba” yai maganar tare da jan hannun Zayn suka nufi hanyar fita
palourn.

Ba zata Iya jure wulaƙancinsu ba, da sauri ta nufi bedroom dinta, tana shiga ta
faɗa saman gado ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita.

Hajiya saratu tuni ta shige cikin mota, pravin na atsaye ya ruƙe murfin
motar”Lafiya? Ba zaka shigo bane”? Tayi maganar tana dubanshi ganin yaƙi motsawa Ya
kafe ta da ido.

“Bana so na 6ata maki lokaci, Ki tafi kawai Ni zanje a motata” da mamaki akan
fuskarta tace”saboda me”?

“Cikina ne Ya 6aci ina buƙatar shiga toilet, “ yai maganar yana shafa flat
stomach dinsa
Ta6e baki tai sam bata kawo komai aranta ba tace”Okey, saina dawo” duƙowa ya yi
saitin fuskarta ya manna mata peck a fore head dinta”Ki kulamin da kanki My wife,
zanyi missing dinki, Ni kona minti ɗaya banaso kiyi nesa dani” kwa6e fuska tayi

“kalaman ka ba zasu hanani tafiya office ba, sai dai su 6ata min lokacina, pls ka
kula min da kanka,” murmushin yaƙe ya sakar mata, Aranshi bai ji daɗin maganarta
ba, halinta ne bata Iya kalaman soyayyaba kuma ba ta cika son yana yi mata ba.

“please take care of ur self, ayi aiki lafiya”ya ƙare maganar tare da tura murfin
motar ya rufe mata ita.

Security din dake zaune a driver seat na motar yaja ta suka nufi shantalelen
titin da zai fiddasu daga estate din.

Shu’umin murmushine Ya bayyana akan fuskar Pravin, Jiki na rawa Ya juya ya nufi
entry hall, adai dai lokacin twins sun fito hannunsu ruƙe cikin na juna suka ci
karo da shi.

Gaba daya suka tsareshi da ido suna kallon shi


Fuskarshi da fara’a ya furta”Kyawawan samarina har Kun kammala Shiryawa za’a
tafi office,” zaid ne yai ƙoƙarin faɗin”daddy, ina kwana ka tashi Lafiya” Ya amsa
mashi da lafiyalou My son, kafin ya maida dubanshi ga Zayn da ya haɗe rai.

“Lafiya zayn ka tsare ni da ido? Ko ba ka da lafiya ne”? Basarwa yai”lafiyata


qalou daddy, just nayi missing dinka ne, amma ya akai daddy naga ka dawo gida? Ba
aiki zakaje ba”?

“Key ɗin mota ɗina na bari a ɗaki, shi zanje na ɗauko” zayn yace”bari na ɗauko
maka key din” yai maganar yana ƙoƙarin juyawa a hanzarce pravin ya damƙi
hannunsa”bana so ku makara yakamata ku wuce ku tafi office, zanje na ɗauko da
kaina, Ku kulamin da kanku,’ bai jira amsar su ba, yabi ta gefensu ya nufi cikin
falon.

“Zaid sai da na faɗa maka matarcan baƙar munafuka ce, saboda ita daddy yayi mana
ƙaryar zai je ya ɗauko car key a ɗaki” Yana huci yayi maganar
Zaid yace”please bro, ka yi mashi kyakkyawan zato, bai kamata kana zarginsu ba”

Tsoki Zayn yaja”wlh duk ranar dana gano ainihin abunda suke aiwatarwa saina tona
masu asiri awurin mommy, ita kuma matar can saina koreta daga gidanmu ta koma can
ƙauyansu na Indiya,” ya ƙare maganar tare da jan hannun zaid suka nufi motarsu.

Hajjaty na akwance cikin mawuyacin hali, idanuwanta sunyi luhu luhu sun rune zuwa
Ja, sai faman shessheƙar kuka take yi, Har ya shigo ɗakin bata sani ba, Haye wa yai
saman gadon ya zauna daga gefenta, Cikin sanyin murya Ya furta”My heart beat” har
cikin kunnanta ta ji muryarshi, sai dai takasa ɗagowa ta kalle shi, hakan Ya
tabbatar mashi da ranta Ya 6aci.

“kiyi hakuri, banji daɗin kalaman da saratu ta furta maki ba, ba yadda zanyi ne
shiyasa ban dakatar da ita ba, nasan ranki ya 6aci but pls ki daure,”

Cikin shessheƙar Kuka tace”bazan iya jurewa ba, nagaji nagaji nagaji da irin
wulaƙacin da suke Yi mini, sun tsaneni basu ƙaunar ganina, ita da zayn shima yaci
mutuncina, zaid ne kaɗai ke ƙaunata”

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, Kafin Yace”pls Ki ɗago muyi magana”
“Ai bana son kallonka, raina ƙara 6aci yake yi” lumshe idonshi yai haɗi da ware su
saman Bayanta.

“Ban ji zafin kalamanki ba, saboda laifina ne, Ni ne silar komai, “ sai da yai
wannan furucin ta ɗago da kanta, tana fuskantar ceilling, taƙi Yarda su haɗa ido.
Ba zato ba tsammani taji Ya kwanto da kanshi saitin fuskarta, ƙamshin turarensu
ya addabi hancinansu.

“Ki faɗamin me kikeso nayi maki wanda zai kwantar maki da hankalinki”
Harara ta watsa mashi muryarta da shagwa6e ta furta”pls ka tashi ka tafi office,
ka zauna kana 6ata lokaci akaina”
“Saboda kin cancanta ne, lokacina nakine, har aikin sai in fasa zuwa idan
kinaso” Yai maganar Yana kashe mata ido.

Batasan ya akai ta tsinci kanta da sakar mashi murmushi.


“Inaso na faranta maki, don haka ki shirya dama kin faɗamin kinason haihuwa”
zare mashi ido tayi’acikin gidan nan? Salon aganni da ciki a tuhumeni” da zolaya
yace”sai kice na Obinna ne, kinga shikenan kin kashe bakin magana’ fashewa sukayi
da dariya cike da nishadi.

“Idan hakan ta faru ko kowa zai ƙyaleni, Hajiya saratu saita kasheni” jan
kumtunta yai da hannunshi”Ai ko dana kasheta nima,” lumshe ido tayi”pravin ka tashi
ka tafi office aiki na jiranka.

‘Waya faɗa maki Ina yin aiki ni? Nifa salary kaɗai nake kwasa, bana yin Aikin
komai ko naje office din, P.a dina ke taimaka min,” ya ƙare maganar tare da ɗaura
tafin hannunsa ɗaya saman chest dinta, a hankali yaci gaba da yin squeezing dinsu,
numfashintane ya soma canzawa ta soma cizon la66anta.

“Faɗamin Ina kika je”? Cikin yanayi najin shauƙi ta amsa mashi da cewa”Garden
naje kaima Obinna da amininsa Kayan marmari” ganin ya ɗaure fuskarshi yasa
tace”lafiya’
“Mutumin bai kwantamin araina ba! Bana son kina zuwa wurin obinna idan abokanansa
suka zo, dattawan nan shegen son mata garesu, musamman irinki babu namijin da zai
ganki ya kawar da idon shi”

Ta6e la66anta tayi yayin da suke kallon juna “Are you jealous of me?Meyasa shi
obinna baka kishi da shi sai abokanan...” kasa ƙarasa maganar ta yi jin ya mannata
da ƙirjinshi”saboda shi na yarda dashi, bazai ta6a nuna kwaɗayi akanki ba, dattijon
yana da kamun kai, kuma baida burin ƙara aure tun da matanshi suka rasu, shi ko
amininsa Jan kunne tsaf zai Iya cewa yana sonki”
“Idan hakan Ya faru mai za ka yi mashi” tayi maganar tana shafa Wuyanshi da
yatsun hannunta.
Kashe mata ido ɗaya yai kafin Ya bata amsa da cewa
“Gemun shi zan tsige” dariya suka saki, da sauri Ya haɗe bakinshi da nata,
Hannayenshi Biyu tallabe da kanta tamkar zasu cinye harsunan junasu.

*San Antonio Texas*

*Army headquarter*

Babbar headquater ce mallakin sojojin san antonio, Haɗaɗɗen gini mai girma da faɗi,
launin fentin head quater din army green ne, Tun daga bakin entry way na shiga
headquater din zaka fara cin karo da Giant soldiars Cikin ta da wajenta maƙil Yake
da Gwarazan sojoji sadaukan Gaske masu ƙirar zakuna, kowan nan su Ya kimtsa cikin
shiga ta Kakinsu, ƙafafuwansu sanye da army boots, sun ruƙe Jibga jibgan bindigu a
hannuwansu, haka zaika ƙugunansu a soke suke da pistols, babu wasa akan fuskarsu
cikin taku na majiya ƙarfi suke kewage ko’ina na Gate din shiga headquater din.

Danƙareriyar motace Haɗaɗɗiyar gaske mai numfashi ƴar ubansu ƙirar Mercedes-benz S-
class launin black ta sharoro da matsakaicin gudu kaitsaye ta nufi Bakin Hq din,
tunkafin ta ƙaraso sojojin suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen ne wannan
ɗan kasada mai shirin zuwa lahira yake yi masu tuƙin ganganci a saman titin su.

Sai da mai motar yakusa zuwa gabansu, Ya rage gudun motar, tamkar na cikin motar
baisan da sojojin dake tsaron headquater dinba, Ya soma ƙoƙarin kutsawa zai ƙetare
gate din, aiko kamar mayunwatan zakuna suka tunkari motar, Wasu fusatattu daga
cikinsu tuni sun saita motar da bindigar hannusu, da kakkausar murya suke faɗin

“Hey! Stop the car! Otherwise we’ll attack you”!

Gaba ɗaya sun kewaye motar, Da ƙarfi wani baturen Soja Ya daki gaban motar da tafin
hannunsa tamkar zai 6alle ta, A harzuƙe ya furta

“Ka sauke glass ɗin motar, Idan ba haka ba zaka fuskanci horo mai tsanani daga gare
mu”

duk wannan suratan da sukeyi na cikin motar yaƙi fitowa babu alamun zai buɗe
murfinta, Hakan ba ƙaramin hayaƙa su yayi ba”

“You’re running out of time. I want you to come out of the car now! If you don’t,
I won’t hesitate to shoot! This isn’t a game, I’m serious. you have five seconds!”
baturen sojan da ya dafe motar da tafin hannunsa ne Ya furta hakan, Sai da suka
gama harzuƙa Zuciyarsu a maƙogaro, a lokacin da basuyi tsammani ba, mamallakin
motar Ya tura murfin Ya buɗe, Rai 6ace suka ƙura ido suna jiran ganin wani isasshen
ne wannan uban Ji da kan.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya
don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura
ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

_The Prisoners E22🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

_UMMIN AMERICA🔥🔥🔥_

A hankali ta zuro ƙafarta ɗaya daga cikin motar wow, high hills ne launin army
green sanye a ƙafarta, sunyi bala’en yi mata kyau, Launin fatar ƙafarta ka ɗai abun
kallo ce, kai kace hasken rana bai ta6a shafarta ba, tsabar kyan fatar da salƙinta.

Tun kafin ta ƙarasa fitowa sojojin suka sassauta fushin fuskarsu, Jikin kowan
nan su yai la’asar ƙamshin shu’umin turaren jikinta ya daki hancinansu har cikin
maƙoshin su fragrance din ya ratsa, Tabarakallahu ahsanul khaliƙin, gaba ɗaya ta
tafi da imanin su, basu san sa’adda Bindugun hannunsu suka faɗi ƙasa ba, Ta yi
matuƙar tafiya da hankalinsu, wani irin mayataccen kallo suke bin surar jikinta da
shi kamar zasu kai mata hari.

Black american ce, A zubin halitta tana da tsayi da jiki, Launin fatarta Chocolate
colour ne, Bodycon ce a jikinta, long sleeved gown dai dai gwiwa rigar ta tsaya
mata launin Army green, daga ganin ta kaga ƴar duniya hayaƙin taba, baƙar a shana
ƙona gari, Irin Ruƙaƙƙun karuwan nan ne Waɗanda suka amsa sunansu A harkar
Bariki,Wannan da kuke gani bakowa bace face UMMIN AMERICA, hamshaƙiyar macace mai
zaman kanta, Idanuwanta A tsaitsaye suke, Bata da mutunci, kuma bata da kunya ko
misƙala zarratin,Tun daga kan shigarta zaka shaida fitsararta, Gaba ɗaya rigar ta
bayyana tsiraicinta, boobs ɗinta sun cika faffaɗan kirjinta, tamkar zasu fasa rigar
su fito waje don atakure suke an matsesu.

Flat tommy ɗinta tamkar ba’a saka abincin acikinsa tsabar ɗamewarsa, ga Uban qugu
dake gareta tamkar ɗaura mata shi akayi saboda faɗinsa, ko kofi aka ɗaura a tudun
mazaunanta tsaf zai zauna batare da ya faɗo ba.

Wani irin daddaɗan ƙamshine ke fita saƙo da lungu na Jikinta.


Round face gare ta,Tasha Uban make up, tamkar an zanata don kyau, Ga eye lashes da
akayi mata fixing masu tsayi, dogon hancinta Na manne da Nose ring mai kyan gaske,
Haka yatsun hannunta na dama na sanye da knuckle ring, long nails din yatsun
hannunta fixing dinsu akayi.

Sumar kanta tasha gyara, sai dai daga gani hair wing ne ta daura ba asalin sumar
kanta ba, amma zai wuya mutun Ya iya ganewa.

Hankalin maza fa ya tashi haiƙam, gaba daya sun rasa natsuwar su, sai faman
haɗiyar yawu suke yi kamar zash lashe ta.

Muryarta tamkar ana busa sarewa ta furta”Zan Iya shiga Ciki”? Har suna haɗa
baki wurin bata amsa da cewa”You’re welcome”

shu’umin murmushi ta sakar masu, har dimple din gefen fuskarta Ya lotsa, juyawar da
za ta yi, mazaunanta suka girgiza gaba daya sojoji suka zabura tamkar zasu tallabe
mata shi.

Komawa Cikin motar tayi, kafin ta rufe motar, wani daga cikin sojojin yai saurin
datse mata murfin, A tsanake taci gaba da yin driving ta nufi cikin head quarter
din.

Ta tafi tabar su da jarabar kallon surar jikinta da su ka yi, ba zasu iya jurewa
ba ai ko da sauri suka nufi cikin head quarter din donsu samu damar ƙare mata kallo
ko sun rage raɗaɗin da zuciyarsu ke yi masu.

Bayan tayi parking ɗin motar, ta fito hannunta ruƙe da i phone dinta, Hankulan
sojojin dake Zarya a headquarter din gaba ɗaya ya dawo kanta, kamar sun samu
talabijin, Matarce akwai Iya jan hankalin maza da surar jikinta, duk idan Tayi taku
ɗaya jikinta sai ya girgiza hakan ba ƙaramin hayaƙa maza yake yi ba.

All eyes on her, Sojojin Tamkar zasu kai mata hari, sai dai ba damar Yin
hakan,Wani irin ƙwarjini gareta, A fuska bata da wasa, Zazzafa ce, Me zaman Kanta.

Ta wutsiyar ido take kallon masu ɗago mata hannu da masu yi mata alamar suna son
yin magana da ita.

Ko kallo basu ishe ta ba, jefi jefi takan ɗan wurga eye balls dinta akansu, da
gangan take kashe masu ido ɗaya ko ta ciji lower lip dinta da harshe, ɗabi’arta ce
Yin hakan, duk don ta ƙara hayaƙa su.

Kaitsaye ta nufi hanyar da zata sada ta da office din commender domin amsa kiran da
yayi mata, tasan ko’ina na headquarter din, don ba baƙuwarta bace, Ba yau bane rana
tafarko da ta fara shigarta.

Tun kafin ƙarasowar ta, tuni Anyi mata iso wurinshi, jiranta kawai Yake yi, yana
daga zaune saman chair, acikin katafaren office dinsa, komai na cikinsa army green
ne, hatta desk din gabanshi, dake dauke da computer dinsa, da wayar hannunsa tare
da flag and map, daga jikin bangon office din akwai book shelf, da jerin hotunansa
da awards dinsa, bashi kaɗai bane a office din hada Major.

Shigowarta office din, Tuni sanyin Iskar A.c ɗin cikinsa ta gauraya da ƙamshin
shu’umin turarenta.

Har saida suka shaƙe shi sosai a hancinansu.

Da kwarkwarsa ta ƙarasa gaban desk dinsa, kamar yadda ta saba yi mashi duk in
tazo office dinsa haka yau ma tayi mashi, Ta buga ƙafa tare da sara mashi, hakan ba
ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, har sai da suka saki murmushi, tun kafin Ya bata
iznin zama, ta zauna saman chair din dake facing dinsa, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa
ɗaya, murmushi ta sakar mashi haɗi da ɗaga mashi gira ɗaya ta kashe mashi ido.

A wayance ta soma yin magana cikin harshen turanci”fatan na same ku lafiya”


lumshe ido commender yai tare da kai hannu ya gyara zaman wuyan rigar kakinsa.

“Lafiyalou ummi, I’m glad to see u, Ina fata kiran da mukayi maki bai taƙura maki
ba”?

Ɗaga mashi gira tayi alamar eh ba tare da ta furta ba, a mutunce suka gaisa da
junansu. Bayan kowan nan su ya natsu, Major Ya miƙe ya bi ta ƙofa ya fuce waje jim
kaɗan ya dawo hannayen shi ruƙe da mugs na coffee guda biyu ya ɗaura su saman desk,
ya ɗago da ido Ya kalli Ummi”zaki Iya sha” ta furta okey, kafin takai hannu ta
dauki mug din ta soma kur6an coffee din, da alama ya yi mata dadi kusan sau uku
tasha kafin ta ajiye mug din, ta dawo da dubanta ga commender”am all eyes”

“Dalilin da yasa na kira ki ummi, Magana ce mai muhimmanci muke san yi da ke, Ina
fata za ki bamu haɗin kai kamar yadda kika saba taimakon mu” cikin harshen turanci
commender yayi maganar a tsanake.

Hankalin major na akan ƙirjinta har wani ƙara leƙensu yake yi kamar zai zura kanshi
cikin rigarta.

Kallon da Commender ya watsa mashine yasa shi saurin kawar da idonshi ya kame
mutuncin kansa

“Babu takura, ko da yaushe ina maraba da ku, zaka Iya faɗin komai ka ke so kai
tsaye”

ta ƙare maganar tana shafa saman boobs dinta da yatsun hannunta.

Yawu commender Ya haɗiya Kutt throat dinsa Ya bada sauti, shi kanshi daurewa yake
yi, surar ummin America na neman kwance mashi masarrafinsa.

“Ina so ki natsu ki fahimce ni kafin ki bani amsa” amsa mashi tayi da toh
Bayani ya soma yi mata dalla dalla tun daga farkon tsintarsu Angel da su ka yi a
Daji, har izuwa kawosu asibiti, da kuma abun da su ke buƙata daga gare ta, tunda
commender ya fara labarta mata, ta natsu tana sauraronshi.

“Muna so ki bamu haɗin kai wurin Kula da yaran ki ruƙe su tamkar ƴa’ƴanki, munsan
zaki Iyane shiyasa muka za6e ki, tun da ba yau kika fara yi mana aiki ba, mun yarda
dake ummi, burinmu ki tarairayesu ta yadda yaran zasu yarda dake har su Iya
faɗamaki ainihin abun da ya faru arayuwarsu’ ya ƙarasa maganar idonshi akan
fuskarta.
Lumshe ido ta ɗanyi kafin ta waresu akan fuskarshi

“ta ya ya zaku yi tunanin damƙa amanar yara har goma sha ɗaya a hannuna? Bayan
kunsan wacece ni, Ban ta6a haihuwa ba, kuma ni banason Rainon ƴa’ƴa, ban ta6a
sha’awar haihuwarsu ba, balle har in iya kula da yaran wasu, Ina mai baka haƙurin
Cewa Ni bazan Iya wannan aikin ba! zaifi ku samu macen da tasan zafin haihuwa mai
kamun kai ku bata rainon su” tana magana jikinta na jijjiga, major duk yabi ya
susuce ya rasa natsuwarshi, ba dan commender na akusa ba da ba abun da zai hana ya
damƙeta ko da zai sha mari ne.

“Ummi, Ki sassauta kalamanki, Kina yi min magana da tsiwa, Ko kin manta a ina
kike ne? Ki duba da kyau ki gani, nan ba club ba ne, ba kuma gidan karuwai bane,
sannan ba ga6ar taku bane, Head quarter din sojoji ce” Ya yi maganar tare da zaro
bindiga daga cikin drawer chest na desk din gabanshi Ya daurata saman desk din.

Tuntsirewa Tayi da dariyar rainin wayau

“Kai ma ka sani, Ummin america bata tsoron bingida, ni da ni ke yin mu’amala da


masu ruƙeta, yanzu haka da nake yi maka magana shigowa ta head quarter din nan gaba
ɗaya na tada masu jarabarsu, suna can waje, wandunan su sunyi masu nauyi’ cike da
shaƙiyanci tayi maganar, ta riga ta gama raina su bata jin tsoron su ko kaɗan.

Cikin kwantar da murya commender yace”is ok, kibar yi min wasa, Muyi magana ta
hankali, ki taimaka ki kar6i buƙatarmu, kome kikeso zamuyi maki, sannan ɗawainiyar
yaran da komai nasu mune zamu bada tallafin da za’a cigaba da kula da rayuwarsu,
tun daga cinsu shansu, suturarsu, da karatunsu, Iya taimakon da muke so kiyi mana
kija su a jiki ki zama tamkar mahafiyarsu” yamutsa fuska tayi tana faman wurwurga
eye balls dinta tace”Kana nufin wai a gidana zasu zauna? Ka san gidana gidan
mazane, a koda wani lokaci Ina busy wurin biya masu buƙatarsu, how ka ke tunanin
zasu Iya samun kulawar data dace? Kuma naji kace yaran suna fama da depression hada
me ciwon ciwo, gaskiga ba ƙaramar ɗawainiya bace kula da su, bazan Iya ba
commender, kada ka tursasamin, kasan ina girmamaka saboda halaccinka agareni”

Kallon major commender yayi, hakan ya bashi damar Yi mata magana

“Ba zamu takura maki ba, amma kafin ki tafi Inaso zan nuna maki hotunan Yaran Ki
gansu”

Miƙewa Major yai daga saman kujerar da yake a zaune Ya zagaya ta 6angaren Commender
Ya juyo mata da laptop din saitin fuskarta.

Operating ɗinta Ya soma Yi, hotunansu Angel Ya buɗo, daga kan hotonta Ya fara
Nuna ma Ummin america
“Sunanta Angel” Ya ambaci hakan yana kallonta, da alamun mamaki akan fuskarta ta
furta “wow she’s beautiful sai dai daga ganin bakinta za ta yi tsiwa, ni kuma bana
sha’awar Yara masu masifa” ta faɗa haɗi da yamutsa fuska, still murmushi ne akan
fuskar major da commender.

Hoton Batul ya nuna mata, sai da ta ta6e la66anta kafin tace “tana da kyau,
sai dai daga ganin fuskarta bata da masifa, wannan ko yatsa aka sanya mata abaki
bazata Iya cizon shi ba” ta kare maganar tana hura hanci.

Hoto na gaba fuskar Hanna ce, Ummin america tace”har ƙwara Yarinyar daka wuce
akan wannan, taci ka sanyi daga gani babu kuzari a jikinta” yadda take fayyace
ɗabi’unsu kamar ta ta6a ganinsu.

Ko da akazo kan Hoton Parveen Ya cika screen din laptop din.

Da buɗar bakin Ummi sai cewa tayi”yarinyar nan daga ganin kumatuntu mayyar abinci
ce, zai yi wuya idan ba asame ta da shegen ci ba, Ni bana so mutun mai ciye ciye”
murmushin fuskar Major da commender sai ƙara faɗada yake yi, don ba ƙaramin nishaɗi
take basu ba.

Hoton Jamimah Ya nuno mata, waro ido waje tayi hada sanya Hannu ta dafe saman
ƙirjinta.

“Major, ruƙon wannan Yarinyar ai sai likitan mahauka, shi kaɗai ne zai Iya
sarrafa ta, ba dai ni ba, Ni ina zan Iya kula da ita, daga ganin bakinta zatayi
tsiwa” Major yayi dariya tare da nuno hoton Azeeza, shiru tayi tana ƙare mata
kallo, kafin ta ɗago da ido ta kalli Major”sai naga kamar ƴan biyu ne ita da
Yarinyar da ka nuna min kafin ita, sunyi kama” Major yace”haka muke tsammani, sai
dai muna hasashen azeeza tafi Jemimah shekaru kamar yadda ɗan uwansu ya faɗa mana”
Yamutsa fuska Ummin america tayi”tana da kyau sai dai daga ganinta matsoraciya
ce, wannan ko tsawa na daka mata zata Iya sakin fitsari a wando, gani da tsiwa
bansan ya zamu ƙare da ita ba” ta fada tana ta6a baki tace”wai Iya matane Yaran”?
Ta yi tambayar tana kallon Fuskar Major

“akwai maza” ya bata amsa, a dai dai kan hoton Haris Ya buɗe mata shi.

“Sunan shi Haris, shine yaron da commender Ya faɗa maki cewa Yana fama da
ciwon zuciya”

Ta6e baki tayi”nifa banason namiji mai raunin zuciya, daga gani baya da hayaniya
ba laifi yana da kyan fata” ta faɗi hakanne saboda kasancewarta baƙar fata, tana
son mutun me duhun fata.

Wuce hoton Haris yai adai dai kan hoton Javed ya dakata Yana dubanta

“Amma dai wannan Yaron ɗan south korea ne ko?

Major yace”bamu da tabbacin ɗan Ina ne, duka yaran bamu san wani jinsi bane, sai
dai sun faɗa mana cewa Ƴan Nigeria ne” da sauri ummin america ta girga kai tana
fadin”Impossible, babu kalan waɗannan a nigeria, may be sun yi loosing memory ɗin
su ne shiyasa su ka faɗi hakan”

Hoton Naufal Ya budo mata, lumshe ido ta ɗanyi tare da waresu akan kyakkyawan
fuskarshi
“Wow, kaga Namiji, sumar kanshi ta burge ni, Yayi min kyau” ta yi maganar tana
hura mashi kiss.

“Yaro ne” Commender ne yace haka,


Ummi tace”Ai shi namiji baya kaɗan, especially idan abunsa ya ruƙa, a wurina
wannan ba yaro bane Namiji ne” murmushi suka saki, basu damu da abun da tace ba
saboda sun san halinta, bata mu’amala da matasan samari, Sai mazan da su ke da aure
waɗanda tasan idan ta bibiyesu za’ayi bala’i idan matansu suka kamata.

Bayan Ya wuce hoton Naufal Ya buɗe mata hoton Gabriel, tunda ta kafe shi da
ido bata ƙyaftaba sai faman jinjina kanta take Yi alamar mamaki

Can dai ta numfasa tare da cewa”Allah Ya yayi halitta, gaskiya idan aka bani
rainon yaran nan tamkar kun ba kura ajiyar nama ne, major idan akwai wani hoton
nuna mini na ƙosa na ƙarasa ganinsu”

Lokacin da Major Ya hasko mata hoton Danish daga zaune ta zabura ta miƙe tsaye
tana duban fuskarsa data cika screen na laptop din, duk suna akwance akayi masu
hotunan idanuwansu arufe.

Muryarta tamkar tame Yin raɗa ta furta “Speechless! Major Ina kuka samun
Kyakkyawar matashin nan mai kama da ɗan sarkin aljanu? Anya Cikakken mutunne? Ko
dai A cikin Dajin da kuka tsintosu Aljana ta haife shi Ta yada” dariya kowan nan su
ya saki jin sambatun ummi dama sai da ransu ya basu zata ruɗe idan taga hoton shi.

Major yace”sai ma kin ganshi a zahiri, ba ƙaramin kyaune da shi ba”

Ko da ta koma ta zauna, sam takasa ɗauke idonta daga kan fuskar Danish, Yayi
matuƙar tafiya da imaninta, aranta har ta fara Ayyana koya surar shi zata kasance a
zarihi?
Muryar Commender ce ta fargar da ita ga dubanshi”dukansu ne muka nuna maki, shin
kin canza ra’ayinka akan kula da su ko kuwa har yanzu kina akan bakanki”

Shiru ta ɗanyi tana yanke shawara da zuciyarta, duk sun ƙagara da son jin
amsarta.

“Yanzu haka case din Yaran mun miƙa shi hannun shugaban isod, shine zai cigaba
da jan ragamar bincike akansu, jiya muka samu amincewarshi na kar6ar case din nasu,
sai dai ya nuna baya buƙatar 6ata lokaci yanason ya tafi tare da yaran can nigeria
a jet dinsa, a satin da zamu shiga”

Lokaci ɗaya ummin america ta canza fuskarta zuwa 6acin rai, da farko tayi murnar
jin cewa Case din Yana a hannun chief na Isod, daga bisani daya furta komawa
Nigeria ne taji komai ya fita aranta.

“Naji kin yi shiru, baki ce komai ba”


Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta soma magana ranta a6ace”Idan har kuna so in ruƙe
Yaran a hannuna, they should stay in America. I will not follow them to Nigeria,”

Commender yace”amma meyasa? Ke kanki fa ƴar ƙasar Nigeria ce why baki son zuwa
ƙasar Ki”

Girgiza kai Tayi still fuskarta da 6acin rai ta furta”Ni ba ƴar nigeria ba ce,
asalina ne acan, amma Ni black american ce, tun da nace banaso mubar maganar kawai,
Ni zan koma gidan idan ka gama maganar ka”

Yanayin fuskarta Ya canza sosai, 6acin raine tsantsa, sun fahimci kamar akwai
wani abu daya ta6a faruwa da ita wanda har yajawo silar barinta ƙasar, kuma batason
Anayi mata maganar komawa can”

Ganin yadda ta haɗe rai babu annuri ko miskala zarratin akan fuskarta, Yasa
Commender cewa”Shikenan ki kwantar da hankalin ki, ba zamu takura maki ba, Zaki Iya
tafiya” ba don yaso ba ya ambaci hakan, duk basu ji daɗin canzawarta ba, muryarta a
disashe ta furta”thank u” ta yunƙura ta miƙe ta nufi ƙofar fita daga office din,
Har ta kusa ficewa Muryar Commender ta katse mata hanzarinta”duk da bansan abunda
ya faru dake a ƙasarki ba da har yasa kika tsani jin an ambaci sunanta, da akwai
wani abu da nike so in faɗa maki ummi” yayi maganar tare da miƙewa hannun shi ruƙe
da mug na coffee, Ya kur6a kafin ya ɗaure da cewa”wannan dama ce agare ki, da zaki
koma ƙasarki a karo na farko ki nuna ma waɗanda sukayi silar barinki ƙasar cewa
Kina araye kuma kinsamu cigaba a rayuwarki ba kamar yadda sukayi tsammani ba, inaso
ki basu mamaki ummi, sannan zuwanki Nigeri bana dundun bane na ɗan lokacine zaki
dawo nan da zarar Mun samu nasara akan binciken Yaran, zamu dawo dake nan, saboda
mu kanmu ba zamu so mu rasa nagartacciyar mace irinki ba, ke kanki kin sani muna
ƙaunarki kuma muna daraja ƙimarki a idanuwan mu, ba zamu so abunda zai 6ata maki
rai ba ummi, kina da damar da zaki Iya zuwa gida ki zauna ki yi tunani akan
maganata kafin ki yanke shawara.

Kalaman shi sun ɗan ta6ata, tuni zuciyarta ta fara sassautowa, ita kanta zataso
wannan damar ta zuwa Nigeria ko dan taba waɗanda sukayi silar barinta mamaki.

Numfasawa ta ɗanyi kafin a hankali ta juya tana kallon commender dake tsaye
abayanta, kamar bata son furta maganar tace”babu buƙatar yanke shawara, Na amince
Zan bi su zuwa Nigeria, Kuma nagode da karramawarku agareni, da zarar na gama
aikin, zan dawo ƙasata”

Murmushi major da commender suka saki, Jin abunda tace, har yanzu bata yadda ta
kira Nigeria da sunan ƙasarta ba.

Sun ji daɗin amincewarta, ba tare da 6ata lokaci ba, Commender ya dauko mata
kundun dake ɗauke da bayanansu Angel, duka takardun akwai Signature dinsu a jiki,
saura sanya hannunta suke buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci su ka Ƙulla Yarjejeniya ta
(guardianship agreement)atsakanin su da ita, sai da ta natsu ta karanta sharuɗɗansu
dalla dalla akan irin rainon da suke so tayima yaran kafin ta sanya hannu a
takardun, bayan ta kammala sun bata wasu takaddun yarjejeniyar da zata ruƙe a
hannunta.

Bayan tayi masu sallama, Ta fito daga office din, tana tafiya Sojoji Na binta da
kallo, Yayin da ita kuma hankalinta na akan takaddun dake a hannunta, Fatanta Allah
yasa Ruƙon Yaran da za ta yi da kuma zuwan ta Nigeria Ya zama alkhairi agare ta.

Tun kafin ta ƙarasa gaban motarta da ta bari a harabar ajiye motocinsu, ta hango
sojoji dadda6e sun kewaye motar suna jiranta, murmushin gefe fuska tasaki har
dimple dinta Ya lotsa, ta fahimci tunda ta shiga office din commender suke ta jiran
fitowarta don su yi mata magana, bata tsaya sauraron su ba, daƙyar ta samu suka
ƙyaleta ta shiga mota, a tsanake ta tada motar, Ta juya sitiyarin da gudu ta fuce
daga head quarter din.

*EX-PRISONERS❤*

Tun ɗazu da safe kowan nan su Ya farka daga bacci, sun wayi gari da jin kyakkyawan
labarin farkawar Danish, saboda zumuɗin zuwa ganin shi babu wanda ya nemi breakfast
acikinsu, gaba ɗaya sun Hallara a room dinsa, tun daga kan Haris, Javed, Naufal,
Gabriel, Batul, Hannah, Jamimah, Azeeza, ƙwansu da kwarkwatarsu sun yi tsaitsaye
cirko cirkon suna kallon shi, fuskokinsu ɗauke da Annurin farin Ciki, Ɗaya bayan
ɗaya Danish Yabisu ya rungume su a ƙirjinshi, kamar sunyi shekara basu atare da
juna, Haris hada kukanshi saboda murnar ganin Danish Ya farka.

Sun tasa shi gaba suna kallonshi kamar zasu lashe shi, Musamman Azeeza da
Jemimah, daɗi suke Ji Danish ɗinsu Ya farka.

Muryar jamimah da shagwa6a tace”munyi fushi ma sai yau zaka farka, kullum sai
munyi kukan rashin ka, ko bacci bamu Iya yi abincin ma ba mu ci” Harara Azeeza ta
watsa mata”wlh ƙarya take yi Danish kullum sai taci abinci sau uku, kuma tana Yin
bacci” Murmushi ya saki yana binsu da kallo, Haris dake zaune gefen gadon Danish ya
ruƙe hannunshi a Cikin nashi ji yake kamar za a kwace mashi ɗan uwanshi.

“Meyasa Angel Jiya daya farka baki tada mu daga bacci ba? Bayan kinsan irin
ƙagarar da muka Yi na son ganin shi” Hanna ce tayi maganar, Gabriel Yace”Ni dai ba
abunda zance sai godiya, saboda ba zamu Iya misalta farin Cikin da muke aciki ba,
Yau babbar rana ce agaremu ɗan uwanmu abun alfarinmu Ya farka da ranshi da
lafiyarshi” yana daga tsaye yake yin maganar Ya goye hannayenshi saman ƙirjinshi.

“Allah sarki Rayuwa kenan, Har na tuna kokawar da Ku ka yi kaida Danish akan
nace zan dire taga” gaba ɗayansu suka sanya dariya.

Batul tace”ai mu bamusan abunda ya haɗa su faɗa ba”

Parveen dake tsaye gefen Naufal hannunta ruƙe da Ayaba sai ci take Yi,
Kunnuwanta akansu ta natsu tana sauraransu.

Labari Angel ta basu na abunda ya faru lokacin da zata dire taga, ba ƙaramin
nishaɗi su ka yi ba.

Azeeza tace”munyi kuka lokacin sosai, Munyi tsammanin Danish ɗinmu zai rasa
idonshi ɗaya, sai gashi Allah ya dawo mana dashi da ranshi da Lafiyarshi, gaskiya
munji daɗi” da farin ciki akan fuskarta ta ƙare maganar, idanuwan Danish akan faces
dinsu, ita da Jemamah.
Parveen tace”ni banaso muna tuna baya, nafi so inji muna magana akan abunda zai
faru agaba”

Jemimah tace”Genie yaushe zamuje gidan daddyn naki? Ni na ƙosa mu koma can,
waɗannan mutanan masu jan kumatun, kullum sai sun tsira mana allura a ɗuwawun mu”
ta yi maganar tare da nuna ass dinta da indext finger dinta, gaba ɗaya suka
tuntsire da dariya, Azeeza tace”Kai jamimah ki ji tsoron Allah, Jiya fa ba ayi mana
allura ba, nurse ta faɗamin an gama yi mana ita, sai dai magani da zamu dinga sha
na tsawon one month” turo mata baki Jemimah tayi
Javed yace”Kufa baku gajiya da abun magana, Kun Cika ɗan uwanmu da surutu, Ko
so kuke yi ya koma baccin” atare suka zaro ido haɗi da ɗan buɗe baki”A’a wlh bamu
so Ya koma bacci,”

“Alhamdulillah, Tun da yanzu mun haɗu mu dukanmu, Yakamata Muyi wa Allah


godiya” Angel Ce tayi maganar, Tare da Ɗaga tafin hannayenta sama, Da sauri suma
suka ɗaga nasu zasu yi addu’a, Mutun ɗaya ne bai ɗaga nashi hannun ba, Hatta
Gabriel da ya ke Christian sai da ya ɗaga hannunshi don su yi addu’ar atare, Don
shi a yanzu baida za6in addini, yafi ƙarfi ta 6angaren musulunci saboda Angel.

Kallon fuskarshi Angel tayi”danish zamuyi addu’a, ba zaka ɗaga hannu ba”
Girgiza mata kai Yayi alamar a’a, ɗaure mashi fuska tayi sai yayi tamkar baisan
tana Yi ba
Cikin sanyin murya Haris yace”Danish meyasa har yanzu baka goyan bayan addinin
musulunci”?

Shiru danish bai yi magana ba, Kuma babu alamun zaiyi ta.
Damuwace ƙarar akan fuskokinsu
“Pls danish just for today ka ɗaga hannu Muyi addu’a” Muyar Angel tamkar zata
fashe mashi da kuka Tayi maganar.

Marairaice mashi fuska Azeeza da jemimah sukayi”Bro pls, let pray together,”

Runtse idanuwanshi Yai, ba tare daya buɗe su ba Ya furta”I can’t, ku daina yi


mini magana akan Inyi, bana so”

Sai lokacin Batul ta sanya baki”tun da ya nuna bayaso mu ƙyaleshi, damu da shi
duk abu ɗayane, ko da ace baiyi ba mu zamu yi mashi, hakan ma ya wadatar” Angel
bata ji daɗi ƙin Yin addu’a da yai ba, addu’oi’ ta soma karanto masu suna amsa mata
da ameen ameen, idanuwanta sun cicciko tab da ƙwalla, bayan sun Kammala kowan nan
su Ya shafa saman fuskarshi, banda Angel maimakon ta shafa addu’ar da tayi saman
fuskarta, sai ta shafa ma danish saman sumar kanshi, a hankali ya ɗago da
idanuwanshi yana duban fuskarta, harara ta watsa mashi tare da murguɗa mashi baki,
hakan da tayi ba ƙaramin ƙayatar da shi yai ba, muryarshi ƙasa ƙasa ya furta
mata”thank u” ta6e mashi baki tayi”kada ka yi tunanin na damu dakai,” ƙayataccen
murmushin gefen fuska yasakar mata, Su Batul sun natsu suna kallonsu.

Muryar Dr. laura ce ta katse masu hanzarinsu”Congratulation! My lovely Children


Ina tayaku murnar farkawar ɗan uwan ku daga bacci, banjima da shigowa asibitin ba,
dr Harry ke faɗamin cewa ɗan uwanku Danish Ya farka, wannan abun farin Ciki ne” ta
ƙarasa maganar, a yayin da take ƙarasowa Gaban gadon Danish. Fararen idanuwanta
dake asanye cikin farin glass ta ɗaura su kan face dinshi.

“An sanar dani cewa Baya kula kowa sai ƴan uwanshi, dagaske ne masoyiya Angel?
Tayi tambayar tare da kallon Angel

Da fara’a akan fuskar Angel ta amsa mata da cewa “Jiya ne amma yau ya saki jiki,
zai Iya magana da kowa”

Dr laura tace”Anya kuwa? Naga ko kallona baisan Yi, danish Ya jikin naka? Ko akwai
inda ke yi maka ciwo a jikin ka”? Tayi tambayar cikin ƙagara da son jin muryarshi
Cikin raɗa Angel ta furta mashi”danish pls kayi mata magana, sun taimake mu,
kuma suna da mutunci” kamar wanda akayi ma dole daƙyar ya iya motsa lips dinsa ya
furta”da sauƙi babu inda keyi mini ciwo,”

Dr Laura taji daɗin maganarshi”ina fata kaci abinci babu yunwa atare dakai”? Ɗaga
mata kai yai alamar eh
Ta furta”okey, amma meyasa jiya baka ba likitoci damar duba lafiyarka ba”?
A takure yake yi mata magana”saboda lafiyata ƙalau, bana buƙatar a duba ni,”
Jinjina kai ta ɗanyi tayi mamakin Halinshi, basu ta6a samun patient irin shi ba.

Muryar Angel ce ta janyo hankalinta ga dubanta”Aunty, mun gode sosai da


kulawarku agaremu, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku,” tayi mata maganar ne don ta
mantar da ita zancen yi ma Danish maganar duba Lafiyar Jikinshi.

“kada ki damu masoyiya Angel, aikin mun e kula da lafiyarku kuma Alhamdulillah,
Naga Jiki yayi kyau Allah ya ƙara Lafiya,” ta ƙare maganar tare da kallon Azeeza da
jemimah”My twins, Ya jikin naku” atare suka haɗa baki” da sauƙi” kafin ta ɗaura
idonta kan Parveen da sauri ta 6oye Ayabar dake a hannunta, dariya dr laura ta ɗan
saki”hmm ai na gani dama kin daina wahalar 6oye mini” duƙar da kai Parveen tayi
fuskarta ɗauke da murmushi.

Kallonsu Gabriel Tayi”Ƴan samari, Jiki yayi kyau, badan sister dinku ta matsa
akan son komawarku Nigeria ba, da a gidana zan killace ku, In cigaba da rainonku,”
murmushi kowan nan su ya saki.

“Zan Koma Office, Ku kula mun da kanku” har ta juya zata fuce Angel tayi saurin
cewa”Aunty, har yanzu sojojin basu kira ba naji su shiru basu zo sun duba mu ba”

Dr. Laura na niyar juyowa don ta bata amsa, ba zato ba tsammani, Suka hango Dr.
Mark tare da dr. brown sun nufo ƙofar ɗakin, Kusan a tare suka shigo.

Gaisawa suka Yi da dr laura, Cikin girmamawa su Angel suka gaishe da su, Bayan
sun amsa masu, suka tayasu murnar farkawar ɗan uwansu

Kafin daga bisani Dr Mark Ya soma Yin magana”Dr. Ke muke nema, Sojojin nan sun
Kira Awaya, idan ba damuwa zamu Iya zuwa office muyi magana”

Amsa mashi tayi da toh, ba tare da 6ata lokaci ba suka fuce daga ɗakin.

Hankalin Angel yaƙi kwanciya burinta taji me zasu tattauna, fatanta Allah yasa su
amince da maganar maidasu Nigeria.

Bayan fitarsu ɗakin kaitsaye office din dr Laura suka nufa, kowan nan su ya samu
wuri saman kujera Ya zauna suna fuskantar Juna da ita

“Ina sauraronku, me sojojin suke ce ne”? A ƙagare ta tambayesu


Dr mark Ne ya soma kora mata jawabi”Commender dinsu ne Ya kirani awaya, Ya sanar
dani cewa Chief na Isod Ya Amince zai kar6i case din Yaran....” tunkan Ya ƙarasa
maganar, dr laura tasaki murmushin farin ciki

“Bayan haka, sun ƙulla Yarjejeniya tsakanin ita ummin american da su sojojin,
zuwa Anjima zasu zo asibitin domin shirya yaran, zasu ɗauke su zuwa gidanta, sai
dai zamuyi kewarsu saboda Commender din ya faɗamin next week chief na isod zai bar
ƙasar tare da yaran” ya ƙarasa maganar idonshi Akan dr laura, mood din fuskarta ya
canza zuwa damuwa, ba ta yi tsammanin zasu bar ƙasar da wuri ba, zaman da su ka yi
da su na kwana huɗu ba ƙaramin sabo su ka yi da juna ba, sai dai ta wani 6angaren
taji daɗi kodan saboda Angel da ta roƙe ta akan ta taimaka masu su koma ƙasarsu.
“Dr lafiya? Naga kamar yanayin fuskarki Ya canza? Ko baki ji daɗin maganar bane”?
dr. Mark ne yayi maganar ganin ta haɗe fuska, Murmushin yaƙe tasakar mashi
“No ba haka bane, Na saba da yaran ne, banaso su yi nesa dani, banyi tsammanin
zasu bar ƙasar da wuri ba, inaso zan nemi alfarma abar mana su ko da one month ne
su yi anan kafin su tafi”

Dr brown yace”ba zai yiwu ba dr, da ace case dinsu a hannun sojojin yake zamu
Iya neman alfarmar abar mana yaran su zauna a wurinmu, sai dai kash sun riga da sun
damƙa case din hannun chief na isod, kuma kinsan shi ba ɗan ƙasar nan bane, A ƙasar
shi yake zaune Aiki ne mai muhimmanci ya kawoshi america, tun cikin weekend daya
wuce yaso barin ƙasar, saboda case din Yaran Ya fasa tafiya, yanzu haka da nakeyi
maki magana, yana shirye shiryen barin Washinton zai shigo garin mu saboda ya haɗa
kan yaran ya tafi dasu, mutumin babu wasa a aikinsa, Baison 6ata lokaci.

Jikin dr. laura ba ƙaramin sanyi yai ba, tana son su Angel, ganin duk ta damune
yasa Dr mark kwantar mata hankali”Tafiyarsu ba yana nufin mun rabu da su ba, Kada
Ki manta Sojojin ƙasarmu ne suka tsince su, bayanan su da komai Yana a hannunsu,
kuma zasu cigaba da bibiyar rayuwar yaran, wannan dalilinne ma yasa suka haɗasu da
Ummin america.

Gyaɗa kai Dr Laura Tayi”Ni damuwata depression din dake damun yaran, da kuma
Yaron dake fama da ciwon zuciya, Hankalina bai kwanta da Ummin america ba, Shin
zata Iya bamu su kulawar da zata sanya su manta da damuwarsu? nafa santa bata da
mutunci macace mai izza kuma ta shahara wurin Iya karuwanci.....” Damuwace ƙarara
kan fuskar dr laura, idanuwanta tuni sun ciko tab da kwalla.

“Yaran sunfi buƙatar kulawar mace wadda tasan ciwon haihuwa, bawai karuwa ba!
Wadda ta saba ƙwacewa matan aure mazajensu tana fasiƙanci da su! Yakamata Kuyi
tunani akan hakan, Ni zanyima Commender din nasu magana, akan su canza masu wadda
zata raine su, Yara fa har goma sha ɗaya za’a damka ma karuwa, gaskiya basuyi
tunani mai kyau ba, zata Iya 6ata su” ranta amuƙar 6ace take Yin maganar.

Cikin kwantar da murya Dr mark yace”ina baki shawara dr, kada kice zaki shiga
maganar nan! Tun ranar da major ya kawo shawarar abata kulawar yaran, Kin nuna
kuskuren yin hakan, amma sai basu damu ba, saboda sunsan halinta, kuma sunsan zata
Iya ne, kamar yadda yace ta saba yi masu aiki, so bai kamata ki damu ba”

Dr brown ya ɗaura da cewa”sunfi mu sanin wacece Ita, Mu sanin da mukayi mata na


karuwa ne, su kuma a matsayin ma’aikaciyarsu suke kallonta, ba zasu ta6a damƙa mata
amanar yaran ba tare da sun aminta da ita ba”

Gyaɗa kai Dr Laura Tayi”Shikenan na haƙura, bazan yi masu magana ba, amma inaso
zan ba Masoyiya Angel Kyautar waya, saboda inaso mudinga Yin magana da ita akai
kai”

“Na fahimci kina son yaran sosai, Ni kaina na kamu da ƙaunarsu, Har na fara jin
kewarsu” acewar dr. Mark

Dr brown yace”aini har ƙasarsu zan Iya zuwa ganinsu idan naso, don haka banda
damuwa, muna atare da su”

Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani, Kowa ya koma bakin
aikinsa.

*DAULAR ALHAJI MUSA*

*Dr Shureim❤*
Ƴan kwanakin da yayi a gidan Uncle ɗin nasa Rayuwarshi ta fara canzawa, a yanzu dr.
Shureim baida matsalar komai, ta kowani 6angare yana samun kyakkyawar kulawa,
kullum yana acikin gida, idan ya gaji da zaman ɗaki yakan fito ya zagaye gidan tare
da zeenatu, yana matuƙar jin daɗin kulawar da take bashi, sun shaƙu da juna kamar
sunyi shekara atare, hatta abincin atare suke cin shi, sai dai akwai wani abu da ya
fara damun zeenatu, hoton da yake yawan kallo awayar shi, abun yabi mashi jiki
kamar ibada, Idan ya fara kallon hoton baya so kowa yazo kusa da shi, kuma baya son
kowa yasan hoton menene yake kallo, duk idan ta faɗo ɗakin shi yana cikin kallon
hoton da sauri yake danna power button na wayar ya kashe ta, ta rasa gane wacece
yake yawon kallo? Don ta fahimci ba ƙaramin so yake yi mata ba, gashi ita kuma
Allah ya jarabceta da masifaffan kishi, ba ta son ganin yana kallon hoton, Har kuka
take yi a 6oye ba tare sanin kowa ba.

A Kishingiɗe yake saman katafaren gadonshi, tun safe bai fita ko’ina ba, ko ƙofar
bedroom dinsa bai leƙa ba, farin short ne ajikinsa, babu riga, gaba ɗaya hankalinsa
na akan screen din apple laptop dinsa dake ajiye saitin kanshi daya ɗaura saman
pillow,

Sam bai ji takun tafiyarta ba, saboda hankalinshi baya atare da shi, wankan swiss
lace ne a jikinta, launin ash colour riga da skirt sunbi shape din jikinta, kamar a
jikinta aka ɗinka kayan, duk da bata ƙiba kayan sunyi bala’en Yi mata Kyau, Tani da
Lami ne sukayi mata Make up, hatta ɗaurin ɗan kwalin kanta sune suka ɗaura mata
shi, ziririyar sarƙar wuyanta ta diamond ce, stone din jikinta sai ƙyalli Yake Yi,
ta yafa gyale a saman kafadarta, hannunta ruƙe da handbag, fragrance din turaren
jikinta mai daɗin shaƙa ahanci.

Hankalinta ba akwance yake ba, tun kafin ta shigo ɗakin tayi mashi sallama bai
amsa bata ba, har ta gaji da yin sallamar shiyasa ta yanke shawarar shigowa don ta
ga ko bacci yake yi ne
Tun kafin ta ƙaraso gaban gadonshi blue eye balls dinta suka sauka akan screen
din Laptop nasa

Ras taji gabanta yai mugun faɗuwa, zuciyarta tamkar zata faso ƙirjinta saboda
zafin da take yi mata, zeenatu tana da saukin kai sai dai tana da zuciya idan ta
hasala, ranta ya 6aci sosai ganin abunda yake kallo, hoton da ta tsana a duniyar
nan duk da batasan hoton menene yake kallo ba, ranta ya bata cewar budurwarsa ce
yake kallo.

Idanuwanta sun makance, bakomai suke hango mata ba face dr shureim ɗinta rungume da
mace a kirjinsa.

Runtse ido tayi da karfi ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara wadda tayi silar
firgitar da shi, da sauri Ya miƙe tare da wurga idonshi Kanta, tuni ta saki jakar
hannunta ƙasa, Zafafan hawayene suka wanke fuskarta.

Hankalinshi ba ƙaramin tashi yai ba, a hanzarce ya sauko daga saman gadon ya
nufeta fuskarshi da alamun ruɗu ya furta”zeenatu! Lafiya? Meya faru?

Girgiza mashi kai tadinga yi tana faɗin”kada ka matso kusa dani yaya shureim,
inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” gaba ɗaya ta gama rikitar dashi”zeenatu ki
natsu kiyi min bayani meya faru dake? Ko wani abu ne ya tsoratar da ke?

Cikin shessheƙar kuka tace”yaya shureim bazan Iya jurewaba, zuciyata zata Iya
bugawa, tun ɗazu mukayi magana dakai akan zamu fita yawo atare, kace min inje in
shirya kafin in dawo kaima za ka shiga wanka ka kimtsa, ashe baka yi komai ba, ko
wankan ma bakayi ba, ka zauna kana kallon hotonta saboda tafi ni mahimmanci
awurinka, ba tun yau ba kullum ne saina ganka kana kallonta, wai wacece wannan ne?
Dame tafi ni? Numfashinta na fita da hucin zafi ta ƙarasa maganar, tare da juyawa
da gudu ta fuce daga ɗakin nashi.

Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba, idonshi akan bayanta harta 6ace ma ganin
shi.

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya, har cikin ranshi baiji daɗin kalamanta ba, baiso
yai silar 6ata mata rai ba, duk da bai fahimci inda maganganunta su ka dosa ba,
lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin ya ware su a hankali, yayin da zuciyarshi ke
tariyo mashi furucin da tayi mashi, yasan bai kyauta mata ba, ta ƙwalla fa rai akan
son su fita tun Jiya shi da kanshi yai mata alƙawarin yau zai ɗauke ta a sabuwar
motarshi su fita yawo.

Cikin sanyin murya ya furta”am sorry my zeenat, “ da sauri Ya nufi toilet don yai
wanka.

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don
jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta
acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

‫❤🤍❤سجن القدر‬

_THE PRISONERS E23🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Confusion of the heart💫

Sir mubarak ne zaune Cikin Motarshi, da su ka yi parking dinta a harabar ajiye


motoci na asibitin Obinna,Tanƙameman asibiti ne Ya haɗu tamkar ba wurin Jinyar
marasa lafiya ba, An zuba dukiya wurin gininsa, suna da ƙwararrun ma’aikata na gida
Nigeria dana ƙasar waje.
Su biyu ne acikin motar, Shi yana a back seat na motar Ya zauna a hakimce, A
yayin da Driver-operator dake driving dinsa Yana zaune saman driver’s seat kowan
nan su na sanye ciki kakinsa na sojoji, sun yi shiru, Sanyin A.c din motar na ratsa
fatar jikinsu, ga dukkan alamu wani muhimmin abu ne ya kawo su asibitin, akwai
wanda suke Jira Ya ƙaraso, tsawon mintuna Biyar, wani kyakkyawan matashin likita Ya
nufo motar da saurin shi kamar zai yi tuntu6e.

A gaban motar su ya dakata da yin tafiyar, ya kai hannu yai knocking glass din
motar, turo ƙofar da a kayi ne Yasa shi yin saurin gyara natsuwar shi, Sam hankalin
shi ba a kwance ya ke ba, tun da sir mubarak ya kira shi awaya ya sanar da shi game
da zuwan shi asibitin gaba ɗaya ya rasa natsuwar shi, saboda sanin matsayin shi a
ƙasar.

“Dr fawan, shigo ciki mana “ muryar Sir mubarak ce ta fargar da shi, Jiki na rawa
ya shiga motar, ya zauna yana faman zazzare idonshi yace”daddy, ina wuni Ya gida ya
Iyali” sir mubarak yace”lafiya lou fawan, Ya aiki ya fama da marasa lafiya” tun da
ya fara magana bai ɗago Ya daura idonshi akan fuskar fawan ba, Hankalin shi na akan
Wayar hannun shi da yake daddanawa.

Still muryarshi na rawa ya furta”Lafiya lou daddy, sai ga kiranka, Na ɗanyi


mamaki” sai da ya ambaci hakan sir mubarak Ya ɗago da ido ya kalli fuskar fawan,
duk da sanyin A c na motar, abun mamaki zufa ce ke tsastsafo mashi, kallon tuhuma
sir mubarak yake jefa mashi, saboda zufar daya gani a saman goshin shi.

“Ya akai naga kana zubar da gumi? Ko baka da lafiya ne”? Yawu fawan Ya haɗiya
tare da cewa”babu komai, Lafiya ta ƙalau”

Ta6e baki Sir mubarak Yai”Okey, Inaso ka kaini gidan kajin da kuke kiwo kai da
Jazz,” da alamun ruɗu akan fuskar dr Fawan yace”Gidan kaji? Daddy ban fahimci
abunda kake nufi ba, waye ya buɗe gidan kaji” yanayin yadda ya furta maganar, babu
alamun yasan da zancen.

Fuskar sir mubarak a ɗaure tamau yace”You know who I am. I don’t need to explain
this to you, Don haka kada ka 6oye min gaskiya, wani gidan kaji ne kuka buɗe kai da
jazz? Da kanshi ya faɗa mini cewa kun zuba jari don kuyi kiwon kaji, kusan kullum
ne saina kama shi yana yin waya akan gidan kiwon kajin ku”

Hankalin dr fawan ba ƙaramin tashi yai fa, Muyarshi na rawa ya furta”`wallahi


thumma tallahi daddy bansan da zancen gidan kaji ba, sai dai ko ƙarya dr jazz yayi
maka, ka ji na rantse maka da Allah...” Lamarin ya ɗaurewa Sir mubarak kai, Sojan
dake zaune a driver seat Ya natsu Yana sauraron su, ta cikin ear-view mirror din
motar Yake kallonsu.

“Fawan, Ka faɗamin gaskiya, ni nasan Jazz ba zai ta6a yi mini ƙarya ba, na lura
gaba ɗaya baka acikin hayyacin ka, idan ma saboda ni ne to ka kwantar da hankalin
ka, babu abun da zan yi maka, ni dai buri na shine ka kai ni gidan Kajin ku, inaso
in gansu, nayi maka alƙawarin idan ka rakani na gansu zan ƙara maku jari”

cikin ruɗu dr fawan ya girgiza kai yana fadin”bazan yi maka ƙarya ba daddy, ina
ganin ka tamkar uba agareni saboda ƙaunar dake a tsakanina da Jazz, wlh Daddy ni
bamu ta6a yin maganar buɗe gidan kaji da dr jazz ba”

Da kakkausar murya Sojan dake a gaban motar yace”Sir, this boy isn’t telling us
the truth. Why don’t we take him to the headquarter? Maybe if we do, he’ll tell us
the truth.”(yalla6ai Yaron nan bazai fada mana gaskiya ba, Me zai hana Mu shiga
dashi headquarter Wata’ƙil idan mu ka je can Ya faɗa mana gaskiya)
Zaro ido waje dr fawan yai, jin ance za’aje dashi headquarter, sir mubarak
yace”kada ka damu ai basai munje headquarter ba, akwai bindiga a ƙuguna, “yai
maganar tare da sanya hannu ya zaro bindigar Ya ɗaurata saman laps dinshi, tsabar
tashin hankali ne tsantsa akan fuskar fawan.

Sir mubarak yace”idan na kashe ka na kashe banza, sai dai idan munje lahira ayi
mana hisabi, don haka ka faɗa min gasiya, idan ba haka ba zan tarwatsa kanka da
bindigar hannuna” bawan Allah dr fawan duk sun tsoratar dashi da barazanar su, ƴan
hanjin cikin shi sun kaɗa.

Hawaye tuni sun soma wanke fuskarshi, cikin sanyin murya yace”ko da zaka kashe ni
daddy, bazan fasa faɗa maka gaskiyata ba, wlh rantsuwar ɗan musulmi bani da
masaniya akan maganar gidan kaji, daddy banyi niyar fada maka ba, amma don in kare
kaina zan sanar dakai wani abu da baka sani ba” Hankalinsu gaba ɗaya yana akan
fuskarshi.

Numfasawa yayi kafin ya ɗaura da cewa “Daddy, jazz baya zuwa aiki, yau kusan wata
ɗaya da sati, bansani ba ko kunsan da hakan, Ni kaina na damu da canzawarshi,”.
Zuciyar Sir mubarak a hautsine Ya furta”idan kuwa har hakane Dr fawan baka kyauta
mini ba! Meyasa tuntuni baka kira awaya ka sanar dani cewa baya zuwa aiki ba? Kusan
kullum sai na ganshi ya shirya zai je asibiti, hakan na nufin ba aiki yake zuwaba
wani wurin daban ya ke tafiya? Ya jefa mashi tambayar yana mai jin ɗaci acikin
zuciyarshi.

“Ka yi hakuri daddy, Bana son in shiga tsakaninka da shi, sannan ni bansan baku
da masaniya akan hakan ba”

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!” Sir mubarak ne ya furta hakan, zuciyarshi


tayi matuƙar karaya da jin cewa jazz baya zuwa aiki, Ya fara zargin shi akan
ƙarairakin da ya ke yi mashi, bai ta6a tunanin Jazz zai yi mashi haka ba, duk da
irin ƙaunar da yake nuna mashi.

Idanuwan shi tuni sun kaɗa jawur, zuciyarshi ta motsa.

“Bana so Jazz ya san cewa nazo asibitin nan! Ko nayi magana dakai! Kaja baki kayi
shiru,” dr fawan ya amsa mashi da toh daddy, in sha Allah bazan faɗa mashi ba.

“Ka share hawayen ka,” da sauri dr fawan ya zaro hanky ya soma goge fuskarshi.

“Dr fawan, Na yarda da jazz sai dai a yanzu na fara zargin shi, wallahi If I find
out that he’s doing something wrong, sai ya ɗanɗani kuɗar shi,” rai a6ace ya furta
maganar, ya ƙara da cewa “dr fawan nagoda da bayanan da ka bani, zaka iya komawa
bakin aikin ka” jiki na rawa dr fawan ya fito daga cikin motar, Bayan yayi masu
sallama Ya nufi cikin asibitin yana faman sauke ajiyar zuciya.

Shiru su ka yi babu wanda ya ƙara magana acikin motar, Lamarin ya ɗaurewa Sir
mubarak Kai, Mamakin shi ƙaryar da jazz yai mashi na cewa Sun buɗe gidan kaji, da
kuma zuwa aikin da yake yi ashe duk ƙarya ne.

Driver-operator, Ya fahimci halin da sir mubarak ya shiga na damuwa, cikin


kwantar da murya yace”Sir, pls kada hakan ya dame ka, nasan ba daɗi mutumin daka
yarda dashi ya sa6aka, sai dai fa har yanzu bamu da tabbacin abun da dr jazz ya ke
yi, mu kyautata mashi zato, sannan shawarar da na ke so in baka yalla6ai, me zai
hana mu fidda rana ɗaya, Mubi bayan shi ba tare da sanin shi ba, a lokacin da ya
shirya zai tafi aiki,”

Ta cikin mirror din motar Yake duban sir mubarak, nauyayyar ajiyar zuciya ya
sauke tare da kallon drivern yace “Ka kawo shawara mai kyau, tabbas inason sanin me
jazz yake aikatawa, nagode da shawararka, zamu Iya tafiya”

Cikin girmamawa Ya amsa mashi da toh, sannan ya tada motar Ya fito da ita daga
cikin harabar ajiye motocin, atsanake ya ke yin driving har suka haura saman titi,
sir mubarak bai dai na cizon yatsanshi ba, saboda Ya damu da jazz, Ƙaunar da ya ke
yi ma mahaifiyar shi ce ta shafe shi, ko ƴa’ƴan shi da ya haifa bai jin su kamar
yadda yake jin jazz, hankalin shi ba zai ta6a kwanciya ba idan har bai gano abun da
ya ke aikatawa ba, ya jima yana danne zuciyarshi akan ƙin amincewa da zargin yaron
da ta ke yi, abun da ya jawo shi ga bincikar shi a yanzu ya fahimci aduk lokacin
daya kama jazz yanayin waya da zarar Yaganshi yake rasa natsuwarshi, Jikinshi ya
hau kerma, shiyasa ya fara suspecting dinsa.

❤ANEELERH❤

Tun kafin ta sallame sallar azahar wayar ta dake ajiye saman drawer take ta buga
ringing, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa, sai da ta kammala sallar ta ɗaga
hannu tayi addu’a ta shafa a fuska, kafin ta miƙe da sauri ta nufi drawer ta ɗauki
wayar, murmushi ta saki ganin sunan surukar arziƙi ya bayyana akan screen din
wayar, aranta ta ayyana halan baby junaid ne ya matsa a kirani awaya.

Bayan ta ɗaga kiran ta manna wayar a kunnanta, kafin ta furta sallama muryar
junaid ta katse mata hanzarin ta.

“Mommy, baby junaid ne, ni ne na kira ki awayar granny,” har sai da ta ji gabanta
Ya ɗan faɗi, da mamaki tace”junaid da gaske kai ka kirani? Ina mommy adama? Ko dai
itace ta baka wayar don ka yi mini magana”

muryarshi da shagwa6a yace”mommy ai bata nan, suna a falo, Ni kaɗai ne a ɗakin...”


tun kan ya ƙarasa maganar tace”Junaid bana hana ka ɗaukarwa mutane waya ba? Faɗamin
ya akai ka iya buɗe mata waya”?

“Mommy wasa nake maki, itane ta bani wayar, ta fita falo, ni kaɗai ne a ɗakin”

A faɗa ce tace”ƙarya ka ke yi mini junaid, ba ita bace ta baka wayar, kaine ka


ɗauka ka kira ni, maza ka aje mata wayarta tun kan na 6ata maka rai,” ta yi maganar
tamkar ranta ya 6aci sai dai azahiri ta yarda bashi wayar akayi, kawai tana son ta
hayaƙa shi ne.

Sautin kukan shi ne ya cika mata kunnuwanta.

“Mommy ba ki yi missing dina ba, shiyasa kike yi mini faɗa, Kin barni ni kaɗai
agidan su, ni wlh gida zan dawo, ko dai kizo ki ɗauke ni ko kuma in gudu in 6ace
kamar Angel” maganarshi tayi matuƙar bata dariya, cikin sigar lallashi tace”am
sorry my baby boy, wlh nayi kewarka kamar zan zauce, yanzu dai ka yi haƙuri kadaina
kuka, Mommyn ka bata son zubar hawayen ka”

Cikin shessheƙar kuka yace”ni dai kizo ki ɗauke ni mommy, ko in gudu” hankalinta
ya dan tashi, zuciya da saƙe saƙe saita dinga tunanin ko dai wani abu akayi mashi
ne wanda ya 6ata mashi rai har yake neman dawowa gida.

“Junaid, faɗamin meya faru? Basa baka abinci ne? Ko ba ayi maka wanka ne? Ko
wani ya buge ka ne”! A jere ta furta hakan.

“Ni ba su yi min komai, ina cin abinci kuma mommy adama tana min wanka har sau
biyu safe da dare, ni kawai ke nakeso kizo ki dauke ni, ko in gudu” ajiyar zuciya
ta sauke, hankalinta har ya ɗan kwanta.

“My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, zasu dawo mun da kai nan bada jimawa
ba,’
Rigima ya sanya mata”Allah in baki zo ba saina gudu” dariya ce ta kubce mata, jin
sautin dariyarta ba ƙaramin 6ata mashi rai ba.

“Mommy dariya kike mini ko! Shikenan zan kashe wayar” da sauri tace”sorry
nadaina, pls kada ka kashe min waya, Ina jin daɗin yin magana dakai, Yanzu faɗa min
a kwance kake ko a tsaye”

“Saman gado” ya bata amsa atakaice, har ta buɗe baki zatayi magana ya katse ta da
cewa”Mommy, na tuna sunan mutumin nan da ya kira ki a waya, ran nan, amma ba zan
fada maki ba, In kina son ji kizo nan”

“Am sorry my baby boy, yakamata ka fahimce ni, babu yadda za’ai inzo, Zasu yi
tsammanin ban yarda ɗazu bane shiyasa na biyo ka, dan Allah ka faɗa min sunan shi,
ka ji yaron kirki”

cikin ƙagara da sonji tayi mashi maganar.


“Toh mommy, zan faɗa maki amma bana so kowa yaji har zahra” muryarshi da
shagwa6a yake magana.

“Junaid, Ni kaɗaice a ɗakin, Zahra bata nan taje wurin aiki, Mahboob ma baya
acikin gida, Abie da Uncle basu dawo gida ba, mami da ummi ne kuma basa a ɗakin,
suna a can palour suna fira”

“To zan faɗa maki, amma kada ki faɗa ma zahra da mahboob” ta rasa ya za ta yi da
shi, Yaƙi faɗa mata sai jan maganar yake yi kamar baya son fadi.

Kukan ƙarya ta soma yi mashi tana fadin”dan Allah baby junaid dina ka faɗamin,
zuciyata zata iya bugawa idan ban ji ba” tuntsirewa yayi da dariya yana fadin”mommy
wasa kike ba wani kuka ai na ganoki” gajiya tayi da tsayuwar, ta koma gefen gado ta
zauna, tamkar tana agabanshi ta marairaice mashi fuska tana fadin”pls my baby boy,
ka faɗa min, komi ka ke so zan yi maka”

“Zoben Angel, da ki ka ce zaki siya mini in bata tun da na maida ba mahboob


nashi”

“Kada ka damu, kafin ka dawo gida zan siya maka zoben, Nayi maka alƙawari,
Yanzu faɗa min toh”

Sai da ya mula ya ishe iska tukunna Ya furta”wai ma...waima daddyn Unaisah, haka
yace min fa” shiru tayi jimm tana tunanin sunan daya furta mata daddyn unaisa?
Wanene daddyn unaisa? Ita kanta unaisan wacece ita!, sunan ya shige mata, jin tayi
shiru yasa Baby junaid ambaton sunanta”mommy kin yi shiru baki ce komai ba”

“Junaid, na ruɗe ne, na kasa gane wanene daddyn unaysa, amma shi mutumin Iya abun
da ya faɗa maka kenan”?

“Eh, bai faɗa min komai ba, Mommy ki kira shi ki ji toh wanene shi, ko daddyn
Angel dina ne?”

lokaci ɗaya taji gabanta Ya faɗi Jin Ya ambaci ƙila daddyn Angel ne, nan take
ƙwaƙwalwarta ta tunano mata sunan wacece Unaisa, a sukwane ta mike tsaye Tana faman
zare idanuwanta, zurfi tunani ta shiga duk duniyar nan mutun ɗaya ta sani mai sunan
daddyn unaisa, wato Tajuddeen, ta gaza yarda da abinda zuciyarta ke faɗa mata.

La66anta na kerma ta furta”ka tabbata haka sunan yake? Ko dai abakina ka ta6a jin
na ambaci sunan daddyn Unaisa?

“Mommy wlh dagaske nike maki haka yace min wai in faɗa maki daddyn unaisa ne,
mommy zan kashe wayar, ga mommy adama nan zata shigo dakin” kafin ta yi mashi
magana yai rejecting kiran.

Hakanan tadinga jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, jiki asanyaye ta koma gefen
gadon ta zauna, tsawon mintuna zuciyarta nayi mata kokwanton maganar da junaid Ya
faɗa mata, har dai a ƙarshe ta yanke shawarar cire nombar daga black list, don ta
kira ta ji wanene mutumin da junaid ya fada mata cewa daddyn Unaisa ne, fatanta
Allah yasa Dagaske ne hasashenta.

Yatsun hannunta har kerma suke Yi wurin daddana wayar, bayan ta cire number daga
black list, ta danna call cikin sa’a Kiran Ya shiga, wayar ta fara ringing, tsabar
zumuɗi jikinta har kerma yake yi, Har kiran yayi rejecting ba’a ɗaga ba, Miƙewa
tayi tsaye ta zame dogon hijabin jikinta ta jefar saman mattress, safa da marwa ta
cigaba da yi a tsakar ɗakin, ta ruƙe wayarta a hannunta, a Ƙalla Ta Kira layin
kusan sau biyar Yana ringing ba’a ɗaga ba, Hankalinta yaƙi kwanciya burinta taji
wanene mutumin nan daya kira kanshi da sunan daddyn Unaisah.

Har ta fidda rai da za’a ɗaga Kiran, Unexpected A kira Na shida data yi mashi sai
gashi Anyi picking call din.

Cikin rashin natsuwa ta furta”Assalamu alaikuma” maimakon ta ji muryar Namiji sai


taji muryar matashiyar mace tana yi mata magana da wani yare.

“Baiwar Allah, bana jin harshen da kike yi mini magana dashi, Idan kina jin hausa
mu yi magana da shi”

Ko da Aneelerh ta ambaci hakan, matashiyar sai ta canza harshenta zuwa Yaren


hausa ta ƴan koyo tace”wanene ke magana”? A ƙagare Aneelerh tace”sunana Aneelerh,
dalilin dayasa na kira Layin, kwanakin baya ana yawan kirana dashi, Ina tunanin ko
wani ne ke nema, pls ina neman me wayar” ta faɗi hakan ne don junaid ya fada mata
cewa Namiji ne Ya daga kiran lokacin da aka kira.

Matashiyar budurwar tace”Ni ce me wayar, wato irin kune ku ke bibiyar mazajen mu


don ku ƙwace mana su ko”? Sakin baki Aneelerh tayi jin abun da matar tace.

“Kiyi haƙuri, Nima matar aure ce kamar ke, kawai inason nasan ainihin wanene me
wayar, ki taimaka min a ƙagare nake da son ji” da alama matashiyar Yarinyar Akwai
ƙuruciya atattare da ita, tun daga kan kalamanta zaka shaida hakan.

“Nace maki ni ce me wayar,” atsawace ta furta hakan, Aneelerh tace”ba wayar ki


bace, saboda ke da kanki ki ka ce irina ne masu bibiyar mazajan mutane don mu kwace
masu miji, hakan na nufin ba wayarki bace wayar mijin ki ce” sautin dariyar
matashiyar ne ya cika mata kunnuwanta, lamarin ya ɗaure ma Aneelerh kai, gashi duk
ta ƙagara a matse take da son jin wanene.

“Ke dai zan faɗa maki gaskiya, tun da kin gano ni, ba wayata bace, wayar mijina
ce, kuma baya nan Ya fita ni ka ɗai ce agidan”

“Okey, pls Ko zan Iya sanin sunan mijin naki”?

“A’a gaskiya, salon ki je ki kai ma boka sunan shi ayi maki asiri ki mallake shi”
duk yadda Aneelerh ta kai ga jurewa saida ta fashe da dariya jin abun da Yarinyar
tace, daƙyar ta sassauta da yin dariyar tace”wlh ni bana bin boka, Ko hanyar zuwa
wurin shi bansani ba, Yar uwata ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ni bana ɗaya
daga cikin matan dake zuwa wurin boka, saboda na dogara da Allah shi kadaine zai
Iya biyamun buƙatuna”

matashiyar tace”Ni ban yarda dake ba, mata dayawa suna son ƙwace mini mijina
saboda kyakkyawa ne kuma yana da ƙarfi”
Aneelerh tace”baiwar Allah na faɗa maki nima matar aurece, da mijina akan me zan
nemi mijin ki”!

“Oho nima bansani ba, idan kin gama magana zan kashe wayar” amsar data ba
aneelerh kenan” Shiru aneelerh ta ɗanyi tana tunanin hanyar da zata 6ullo mata, ta
fahimci Yarinyar bata da cikakken Ilmi da wayau sai a hankali. Dabara ce ta faɗo
mata.

Dariya ta fara saki, Matashiyar tace me kike yi ma dariya Aneeleh tace”Ai dole
inyi dariya, ke yanzu baki gane muryata ba ne? Aneelerh fa ce matar abokin mijin ki
Shu’aibu”

Da buɗar bakin budurwar sai cewa tayi”ƙarya kike yi aini mijina basu nan shi
shu’aib ba, TAJ ne sunan shi, Kina son ki yi mini wayau ne”

Jin ta ambaci sunan Taj Yasa Aneelerh Tsayawa cak ta dakata da yin tafiya, yayin da
bugun zuciyarta ya ƙaru, Muryarta na ɗan rawa ta furta”ƙarya kike yi, ba sunan
mijin ki tajuddeen ba, so kike in yadda don kada ki faɗa min ainihin sunanshi, ai
ni nasani Shu’aibu ne sunan shi”

Matashiyar budurwar tace”To kada Allah yasa ki yadda ma, kuma wlh ma ƙarya kike
yi mini cewa wai ke matar abokinsa ne baki da gaskiya,” da alama ranta ya 6aci ta
fara harzuƙa.

Sassauta murya Aneelerh tayi”Ki yi haƙuri, ba yadda ki ke tsammani bane, Dan


Allah ki faɗamin ina mijin naki yake inason yin magana dashi”

Dogon tsoki matashiyar Taja, kafin ta furta”ba kin ce ke matar abokinsa bane? To
ki ce ma shu’aibun Ya kawo ki gidan mu,” kafin Aneelerh ta furta wani abu,
Matashiyar ta katse kiran!”

Hankalin ta Yaƙi kwanciya, Jiri ta soma gani acikin idanuwanta, a daddafe ta nufi
gado, Ta haye ta kwanta, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta ta
shiga ruɗani, tun da Matashiyar ta ambaci sunan tajuddeen, natsuwarta tabar
jikinta, taso ace tayi waya da shi don ta tabbatar da abun da take hasashe.

Har ƙara jaraba kiran layin tayi amma matar taƙi ɗagawa.

Dubara ce ta faɗo mata aranta, da sauri ta rubuta mashi saƙo cikin harshen
turanci.

_Idan ka karanta saƙona, dan Allah ka kira ni, Inason Yin magana da kai, saƙo
daga Aneelerh muhammad falgore_

Ajiyar zuciya ta sauke Bayan ta kammala rubuta mashi sakon, Ta ɗaura wayar saman
side drawer, A gogon ɗakin ta kalla ƙarfe Uku na rana, kwanciya tayi saman gadon
tana jiran tsammanin Kiran me wayar.

❤ZEENATU❤

A 6angaren zeenatu kuwa tun da ta fito da gudu daga ɗakin Dr. Shureim ta koma
ɗakinta, ta fada saman gado taci gaba dayin kuka tamkar ranta zai fita, cikin
muryar kuka take fadin”yaya shureim ba sona yake yi ba, wata yake so daban, dama
nasani babu namijin da zai yarda yaso ni saboda rashin natsuwata,”

Idanuwanta sun kaɗa jawur, miƙewa tayi zaune ta soma cire lace jikinta a saman
floor, ta watsar da kayan hada ribbon din da aka daure mata gashin kanta, iya undy
ta bari a jikinta, ta jashi saman ƙirjinta, tana huci yayin hawaye ke cigaba da
wanke mata fuskarta, saukowa tayi daga saman gadon ta nufi gaban dressing mirror
dinta, cikin 6acin rai ta sanya hannu ta watsar da jerin turarurrukanta komai sai
da ta wurgo shi ƙasa, bayan ta gama ta koma gaban wardrobe dinta, ɗaya bayan ɗaya
sai da ta wurga da suturar saman floor, hankalinta bai kwanta ba har saida ta maida
ɗakin kamar na mahaukata, tukunna ta koma saman gadon ta haye tare da jan bargo ta
lullu6e zuciyarta na ta farfasa.

Bayan Dr. Shureim ya fito daga wankan, kimtsa kanshi yai ciki shiga ta larabawa Ya
feshe jikinsa da turare,
Ya ruƙo wayar shi a hannun shi, tare da car key dinsa, walking quickly ya fito
daga bedroom dinsa, Ya nufi ɗakin zeenatu, duk inda Ya gifta a paloun masu aiki ne
suke Yin aikace aikacen su cikin girmamawa suke gaishe da shi.

“Yalla6ai barka da fitowa” muryar Tani ce ta katse mashi hanzarinsa, dakatawa


yai da yin tafiyar ya juya ya dubeta

“Yawwa barkanki, Ya aiki” fuskarta da fara’a ta amsa mashi”Lafiyalou


Alhamdulillah,”

Har zai wuce ta Ya kuma tsayawa ya kalle ta”Ɗakin zeenatu nake nema” Da rawar
Jiki ta ce”Yana a second floor, muje in nuna maka ɗakin” ta faɗa tare da yin gaba
Yabi bayanta, Yayi matuƙar ƙagara da son ganinta, duk don Ya lallasheta akan laifin
da yayi mata.

Bayan sun hau elevator ta sauke su a second floor, Tani ta nuna mashi ƙofar
ɗakinta.

“ki shiga ki faɗa mata inason magana da ita”


Tani ta amsa da toh, tana zura ƙafarta ɗakin zeenatu, gabanta Ya faɗi ganin
irin 6arnar da tayi, hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, jiki na rawa ta nufi
gefen gadonta.

“Zeenatu! Lafiya meke damunki ne? Meyasa kika hargitsa suturar ki”?

Shiru zeenatu bata tanka mata ba, saima ƙara ƙudundune kanta da take yi cikin
bargo.

“Dan Allah zeenatu kiyi mini magana, nasan 6ata maki rai akayi ki fada mini
wanene”

Jin tayi shiru ba ta yi mata magana ba yasa tace”ba zan takura maki ba, Yanzu ki
tashi Yayan ki shureim Yana a ƙofar ɗakin ki, shine yace in yi maki magana yana son
ganinki”

Kamar jira ta ke yi Tani ta ambaci sunan shureim, Cikin shessheƙar kuka


tace”Tani, I don’t want to see him. Please tell him I won’t come. Yaya Shureim
doesn’t love me wata yake so daban, tun jiya yayi min alƙawarin zamu fita yawo
atare, yau kuma da kanshi yace min inje in shirya kafin in dawo zai yi wanka ya
shirya, Tani da naje ɗakin shi babu abunda yayi, yana akwance saman gado yana
kallon hoton girl friend dinsa a laptop....” daƙyar ta ƙare maganar.

Jikin Tani yai sanyi, duk sai taji ba daɗi, sai yanzu ta gane dalilin dayasa ta
shiga halin da take aciki.

“Kiyi haƙuri zeenatu, ki tashi ki gyara jikinki, Yace yana son magana dake nasan
yazo ne don ya baki haƙuri, kuma naga ya shirya hada key din mota a hannunshi....”
Katse ta Zeenatu tayi”Na fasa zuwa ki faɗa mishi bazan je ba, tun da bayaso na”
Cikin muryar raɗa Tani tace”yana fa jin ki, bai kamata kina ɗaga murya ba, sannan
ke in banda abunki waya fada maki budurwashi ce yake kallo awayar?

“Ai naga hoton da yake kallo, Yana a kwance saman gado ya rungumeta a kirjinsa”
ta fada tana jan numfashi taƙi fitowa daga bargon.

“Zeenatu, kiyi mashi kyakkyawan zato, yaya shureim yana sonki fiye da yadda kike
son shi, Ni shawarar da zan baki shine kada ki bari ya gane kina son shi, idan kika
kwantar da hankalin ki da kan shi zai furta maki kalmar so”

Sassauta muryarta tayi”Tani, zan iya jure wannan amma bazan Iya jure kallon
hoton budurwarshi da Yake Yi ba,”

Dafe kai Tani tayi da hannu ɗaya”zeenatu baki da tabbacin budurwashi ce, pls kibi
komai a sannu zamu gano ainihin wacece Yake kallo awayarshi, Yanzu Ki tashi muje
Yana awaje yana jiranki’

“Tani ki daina wahalar da kanki, Nifa ba inda zanje, Ki fada mashi bana Jin daɗi
bacci Nike Yi”

Duk yadda Tani taso ta lallashe ta akan ta tashi ta je gare shi taƙiya, a dole ta
ƙyaleta ta juya ta fuce daga ɗakin.

A tsaye ta same shi Ya jingina bayanshi jikin bango.

Harya fara Gajiya da tsayuwa


“Ka yi haƙuri, Zeenatu tayi fushi bansan meya haɗa ta dakai ba, nayi ƙoƙarin In
lallasheta amma taƙi amincewa ta amsa kiran ka, ban ji daɗi ba shureim, duk da
bansan meya haɗa ka da ita ba, amma bai kamata tun yanzu afara samun rashin jituwa
a tsakaninka da ƙanwarka, zeenatu tana da haƙuri sai dai tana da zuciya idan aka
6ata mata rai’

Tun da ta fara magana Ya natsu yana sauraronta, sai da ta kai karshen maganar
tukunna yace”Inaso zan shiga ciki”

bai jira amsar da Tani zata bashi ba yai saurin haura ƙafarshi cikin ɗakin zeenatu.

Dafe kai tayi da hannu ɗaya tunawa da 6arnar da zeenatu tayi a ɗakin, gashi kuma
Ya shiga hake zai je ya same shi kamar bola, can kuma ta ayyana aranta cewa ɗan
uwanta ne, daga haka ta ƙara gaba.

A tsanake Yake bin ko’ina na ɗakin da kallo, yayi mamakin ganin yadda ta hargitse
komai, ta rikita mashi tunanin shi, Ya rasa gane fushin menene take yi da shi? Don
shi a tunanin duk akan fitar da yace za su yi ne.

Sam bai lura da lace din data cire ta jefar saman floor, idanuwanshi na akan
gadonta, bargon da ta lullu6e dashi sai kerma yake kamar wadda sanyi ya kama.

daddaɗan ƙamshin turarensa ne Ya daki hancinta, Nan take ta fahimci Ya shigo


ɗakin nata.

Gefen gadonta ya zauna Yana dubanta, calmly ya furta”Zeenat ina son yin magana
dake
Shiru tayi bata tanka mashi ba, tayi tunanin Tani ta fada mashi cewa bacci take
yi kamar yadda tace ta gaya mashi.

“Nasan Kina Jina zeenatu, Ki amsa mini, nazo ne don in baki haƙuri, nasan ban
kyauta maki ba, Yanzu haka da nike yi maki magana na kammala shiryawa ke nake jira
mu tafi”

Cikin disasshiyar murya tace”yaya shureim bana jin daɗin jikina, bazan iya
fita ba, sai dai zuwa gobe”

“am sorry zeenatu, fushi kike yi da yayan naki? Ba za ki yi mini uziri ba?

“Yaya shureim ni ba fushi nike yi dakai ba, fitarce na fasa, Bana jin daɗi”

Ya rasa ya zai yi ya shawo kanta don ta amince su fita.

Yanke shawarar Yaye Bargon Jikinta yai don ya samu damar lallashinta dakyau.

Tsautsayine Yakai hannun shi saman bargonta, Ya ruƙo shi tare da jan shi, Ras
yaji gabanshi ya faɗi da sauri Ya maida mata bargon a jikinta, Yana faman jan
numfashi da ƙarfi da ƙarfi, miƙewa yai da wani irin Yanayi ya nufi ƙofar fita daga
ɗakin Yayin da la66ansa ke ambaton sunan Allah, Har ya kusa kaiwa ƙofar ɗakin
Muryar zeenatu ta katse mashi hanzarin shi.

“Yaya shureim kai da kanka ka faɗa mini cewa baka ta6a yin soyayya ba, amma
meyasa kake kallon hoton wata awayarka”

Ta gaza haƙura har saida ta amayar masa da abunda ke cikinta, shi kuwa Man din duk
ya rasa natsuwarshi, tunda Yaja bargonta Yayi arba da undy din jikinta shara shara
Hakan ba ƙaramin tada mashi hankalin shi yai ba, ga dukkan alamu ita batasan ma ya
buɗe bargon ba saboda ta ƙudundune kanta, idanuwanta suna arufe.

“Zeenatu, abun da na faɗa maki da gaske ne, banyi maki ƙarya ba, Ni ban ta6a yin
soyayya ba” A hankali Ya ɗan Juyo yana dubanta, a lokacin ta fiddo da kanta daga
Cikin bargon, Yalwatacciyar sumar kanta, ta rufe mata gefen fuskarta, Jan bakin
data shafa ya dame fuskar saboda kukan da tasha, har saman kumatunta jan bakin ne,
duk da kwalliyar fuskarta ta 6aci ba ƙaramin kyau tayi mashi ba.

Muryarta da shagwa6a tace”ka faɗamin wacece ka ke kallo awayarka? Idan ba


budurwar ka bace.

Ƙayataccen murmushine Ya bayyana akan fuskarshi, sai yanzu ya gane dalilin


dayasa take haukan nan, wato kishin shi take Yi saboda yana kallon hoton wata
wayarshi, aranshi ya ayyana da ace tasan hoton wacece yake kallo da batayi haukan
nan ba.

“Zeenatu, dama saboda hoton wayata kike kuka”? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh.
“Okey, Ki kwantar da hankalin ki, ba budurwata ba ce,” maƙe mashi kafaɗa tayi”ni
ban yadda ba yaya shureim, idan har dagaske kake yi min ba budurwan ka bace to ka
nuna min hoton in gani”

Lumshe idonshi ya ɗanyi tare da waresu kan fuskarka, duk da tazarar dake a
tsakanin su, ba ƙaramin Kyau take yi mashi ba musamman yanzu daya fahimci irin
zazzafan son da take yi mashi.

Ganin ya tsareta da ido, ba tare daya furta komai ba yasa tace”Yaya shureim
magana fa nake yi maka, kayi shiru baka ce komai ba, Ni dama nasani baza ka nuna
min hoton in gani ba”

Yadda take yin maganar tana jujjuya eyes balls dinta ne suka ƙara rikitar da shi.

Gyaran murya ya ɗanyi kafin yace”Idan har Ki ka amince zaki shirya mu fita, Ni
kuma zan nuna maki wacece nake kallo awayata,” zum6ura mashi baki tayi”toh, amma ka
fara yi min alƙawari,”
“Nayi maki alƙawari”

“Yanzu zan shirya yaya shureim,” ganin tana ƙoƙarin miƙewa tsaye yai saurin fuce wa
daga ɗakin gudun kada Ya ƙara ganin abunda zai hana shi Runtsawa.

Fitowa ya yi daga cikin gidan Ya nufi harabar ajiye motocin su, Wasu danƙara
danƙaran motoci ne na Alhaji musa a killace a ƙalla sun haura goma shabiyar, kuma
dukansu babu motar ƙasa da miliyan talatin, Manya manyan motocine tsadaddun gaske
masu numfashi.

Motarshi Ya buɗe Ya shige Ciki Ya zauna a driver seat haɗi da ɗaura kanshi jikin
headrest, bakomai Yake tunawa ba face maganar da Alhaji musa ya faɗa mashi akan
Aiki da kuma aure, A yanzu ya fara tunanin ta yadda zai 6ullo mashi da zancen auran
zeenatu, yafi buƙatar auren akan komai, saboda yanason ya samu natsuwar cigaba da
gudanar da rayuwarshi, zeenatu ta kwanta mashi aranshi ɗari bisa ɗari, kuma yana da
tabbacin zeenatu zata maye mashi gurbin abunda ya rasa.

Almost 15 mins, ƙamshin turarenta Ya doki hancinsa, Nan take ya fahimci


ƙarasowarta, buɗe motar Tayi tare da samun wuri ta zauna gefenshi” ɗaura idonshi
yayi akan face dinta, babu make up, zallar kyan da Allah yayi matane, ta canza
kayan jikinta zuwa turkish gown launin black gray, Ta yafa mayafi akanta,
Idanuwanta sun kumbura saboda kukan da tasha.

Kallon Juna suka somayi kamar zasu haɗiye kawu nan su, Ko ƙyaftawa basa yi,
kunyar shi ce ta kama ta, da sauri ta daura kanta saman laps dinta.

“Zamu Iya tafiya” da shagwa6a tace”a’a yaya shureim, nafi so ka fara nuna mini
hoton in gani”

Zaro wayarshi yai daga cikin aljahu Ya daddanata, Kafin Ya miƙe mata wayar”kar6i
ki ganta, Kyakkyawa ce tafi ki kyau, ita nike da burin aure”

Gabanta na faɗuwa ta ɗago, tare da sanya yatsun hannunta dake kerma ta kar6i wayar
da ya miƙo mata, idanuwanta rufe tabarsu, Gudun kada taga abun da zai hanata
kwanciyar hankali.

Dr. Shureim dake kallonta, murmushine ɗauke akan fuskarshi

“Meyasa ki ka rufe idonki”? Muryarta na rawa ta furta”bana son inga abunda zai
hanani bacci”

“In sha Allah ba zai hanaki yin bacci ba, sai daima ya sanyaki yin bacci cikin
kwanciyar hankali, now Open your eyes slowly and look at the picture,”

She took a deep breath and tried to slowly open her eyes kamar yadda ya bata
umarnin ta bude su a hankali.....”

(Kaɗan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya🤣 sai dai
Allah yakaimu zamu gani, Very soon In sha Allah Zamu shiga Takun ƙarshe na labarin
kurkukun ƙaddara)

*Boss Bature✍️ Mu haɗu Monday In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya
don jin yadda zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura
ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

‫❤🤍❤سجن القدر‬

_THE PRISONERS E24🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Confusion of the heart💫

lokacin da ta ware idanuwanta akan screen din wayar wani irin sanyine ya ratsa
zuciyarta ganin fuskarta, hotonta ne tun tana ƴar shekara goma sha ɗaya a duniya,
tsabar farin ciki Ya hanata rufe baki, hada hawayenta saboda farin cikin ganin
hotonta ne yaya shureim yake kallo, bata kawo komai aranta ba saboda ta yarda da
shi.

Ɗagowa tayi idonta acikin nashi ta furta”yaya shureim dama hotona kake kallo”?
Ɗaga mata gira yai alamar eh, ta kuma cewa”yaya shureim wannan ai tsohon hotona ne
a ina ka same shi”

Fuskarshi ɗauke da murmushi yace”nima tsohuwar ajiyace a cikin memory dina, saboda
inason hoton bana so na rasa shi, bama shi kaɗai ba akwai sauran hotunanki a
gallery ɗin wayar zaki Iya dubawa ki gani”

Yatsun hannunta na kerma ta bubbuɗe sauran hotunan tana kallonsu hada wanda tun
tana jaririya akayi mata shi, abunda ya ɗaure mata kai gaba daya gallery na wayarsa
hoton mutun biyune acikinsa daga hotonta saina ƙanwarshi benazir.

“Yaya shureim tun yaushe kake kallon hotuna na”? ta faɗa da mamaki akan fuskarta.

Muryarshi ƙasa ƙasa tamkar tame yin raɗa ya furta mata”tun lokacin dana fahimci
kece ƙaddarata” wurga mashi blue eye balls dinta tayi akan face dinsa.

“Ƙaddararka? Kamar yaya kenan”? Cikin rashin fahimtar kalaman shi ta ambaci hakan.

“Lokaci zai ƙure mana zeenatu, ki bari idan muka dawo gida zan fahimtar dake
abunda nake nufi” amsa mashi tayi da toh, haɗi da miƙa mashi wayarshi Ya sanya
hannu ya kar6a, ya turata a aljhu, har cikin ranshi ba ƙaramin daɗi yaji ba, ganin
bata kawo komai aranta ba, Duk da ya 6oye mata ainihin hoton da yake kallo.

“Allah sarki aunty benazir, nayi missing dinta Yaya shureim, tsawon lokaci babu
ita, Allah dai yasa aganta da ranta da lafiyarta” cikin sanyin murya zeenatu ta yi
maganar, ya amsa mata da ameen.

Yana ƙoƙarin tada motar, ba zato ba tsammani yaji zeenatu ta kwantar da kanta
saman kafaɗarshi, wata irin kasalace ta soma baibaye shi sakamakon ƙamshin
turarenta dake kashe mashi jiki.

A hankali motarsu ta miƙi Hanyar babban gate din gidan, Gate security officers
ɗin dake tsaron gidan suna ganin motarshi gaba ɗaya suka yunƙuro suka nufo motarsu,
hannunsu ruƙe da jibga jibgan bindigu, ba arziƙi dr. shureim Yaci burki, Jin ya
dakata da yin driving din yasa zeenatu ɗago da kanta daga saman kafadarshi ta dube
shi.

“Yaya shureim meyasa ka dakata da yin driving din”

“Masu tsaron gidan nan ne suke tunkaro mota ta,” ya bata amsa a takaice.

Dafe kai tayi da hannu ɗaya”Namanta ban faɗa ma daddy ba, Ni nasan daƙyar zasu
bari mu fita, idan har bai basu umarnin su ƙyale mu ba, gashi baya agidan, Mommy ma
har yanzu bata dawo daga office ba” ta faɗa tana faman zare ido.

“Yaya shureim ka kira daddy awaya ka sanar dashi” a tsoroce take yi masa maganar
don ita kanta mugun jin shakkar masu tsaron gidan nasu take ji, ƙirar jikinsu kaɗai
abun tsoratarwa ne, sannan basa wasa da aikinsu, gashi babu annurin akan
fuskokinsu.

Kafin dr shureim Ya zaro wayarshi tuni sun cimma masu, ƙawanya su ka yi mata
motarshi.

Ɗaya daga cikin su ne yai knocking glass motar, da kakkausar murya yake ya ce
“wanene acikin motar? Muna baka umarnin ka zuge glass din motar ka”

zeenatu ce ta sauke glass din, Ya zuƙunno Yana dubansu A tsanake miryarta na rawa
tace”yanzu zai kira daddy awaya, yayana ne shureim zamu fita yawo ne”

Security guard ɗin yace”oh, meyasa baki faɗa mashi ba’a fita dake waje ba tare da
iznin daddyn ki ba”?

Still muryarta arude ta furta”ai mantawa nayi ban fada mashi ba” jinjina kai
mutumin yai”okey, Muna jiran umarninsa”

Kusan Sau uku dr shureim yana jaraba kiran layin Alhaji musa bai ɗaga ba, zeenatu
tace dashi”ka jaraba kiran Layin mommy, idan tayi masu magana zasu barmu mu fita”
kiran Layin Hajiya sarah yayi ringing biyu ta ɗaga, bayan sun gaisa ya sanar da ita
halin da suke aciki, tace dashi yaba ma Security guard din waya suyi magana da shi.

Miƙa masu wayar yai, bayan sun kar6a ya dubi zeenatu, yayi mamakin ganin zufa na
wanke fuskarta duk da sanyin A.c na motarshi, ya fahimci tsoron su take ji.

“Ki kwantar da hankalinki zeenatu kina atare dani”

cikin sanyin murya ya ambaci hakan, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”yaya
shuriem ni bana son tashin hankali, duk laifin daddyne ni banga amfanin ajiye
waɗannan ƙattan ba acikin gidanmu, ai Allah ne ke tsare bawansa bawai mutun ba” da
shagwa6a ta ƙare maganar, ruƙo hannunta yai acikin nashi, da sauri ta mayar da
kanta saman kafaɗarshi tare da lumshe idanuwanta tana faman sauke ajiyar zuciya.

Miƙo mashi wayar Security guard ɗin yai”an baku iznin fita, amma bisa sharaɗin
zaku koma mazaunin baya na motar, Ni zanyi driving dinku duk inda zaku je” zeenatu
tamkar zata fashe da kuka tsabar jin takaicin jin abunda Security guard din ya
fadi.

Dr shureim yace “ba damuwa mun gode da kulawa,” ya faɗa yana buɗe murfin motar,
fitowa su ka yi daga front seat suka koma back seat na motar suka zauna,” security
guard din ya shiga ciki Ya zauna a driver’s seat, Ya tada motar Ya fuce dasu daga
cikin gidan lokacin da suka haura saman titi, security guard din ya tambaye su ina
zasu je ne, zeenatu ce ta zayyana mashi wuraren shaƙatawar da zasu je, kafin
dawowarsu gida sai da suka mori lokacinsu, kamar karsu dawo gida.

*EX-PRISONERS❤*

After two days (bayan kwana biyu)

Idan muka koma 6angaren prisoners sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tafiya ta
kankama, tun bayan da sojoji suka ƙulla yarjejeniya da ummin america, A ranar
wuraren ƙarfe shidda na marece, sojojin suka zo kawo masu ziyara domin duba
lafiyarsu, a ɗakin hutawar dr Laura, suka tattarasu gaba ɗayansu, sunyi matuƙar jin
daɗin ganin Yaran sun samu sauƙi musamman Danish da suka barshi Yana ta faman
sharar bacci, dama sun ƙwallafa rai akan son ganin ya farka, duk da bai sakar masu
fuska ba sai da suka ja shi ajiki, kafin tafiyar sojojin sai da dr laura ta nemi
izni akan tana so abata dama ta ɗauki Yaran zuwa gidanta na tsawon kwana uku,
saboda tana so gobe zata kai su saloon agyara masu jikinsu da sumar kansu, sannan
tana so zata siya masu suturar da zasu sanya, sojojin basu amince da buƙatarta ba,
saboda chief na Isod Ya hana a fita da yaran ko’ina, yace kada a kuskura a fitarsu
daga asibiti sai Airport idan zasu tafi, Sun bata haƙuri akan ƙin amincewa da
buƙatarta sun kuma nuna mata illar yin hakan tun da su Yaran suna hasashen cutar da
su akayi kuma dole asamu masu bibiyarsu, ba dan taso ba ta haƙura, sai dai kamar
yarda tace zata siya masu suturar sanyawa tayi ƙoƙarin yin hakan duk da Commender
yace kada ta wahalar da kanta, Chief na isod Ya ɗauki ɗawainiyar yaran duk wani abu
da zasu buƙata a duniyar nan shi zaiyi masu, dr laura tace taji amma dole ta siya
masu wani abun da zasu dinga tunawa da ita akai akai, commender yace mata ba
damuwa, bayan tafiyar sojojin, tsabar farin Ciki awurin Angel kamar zata zuba ruwa
ƙasa tasha, dr laura ce ta faɗa masu komai dangane da tafiyarsu Nigeria, da kuma
damƙa case ɗinsu a hannun Chief of Isod, daren ranar da aka faɗa masu ko bacci bata
yi ba, kwana tayi tana yin Nafilfili, har sai da idanuwanta suka kumbura saboda
hawayen dake fita acikinsu, ƙafafuwanta suka fara yi mata zogin azaba, tukunna ta
dakata dayin sallar asaman prayer mat bacci ya ɗauke ta.

Tsawon kwana Biyu Kacal, a tsakani Shugaban Isod, Ya shigo birnin San Antonio
Texas, Ya kama Yau kenan Monday, Kuma A yau din zasu Bar America, Da zarar ya fito
daga meeting din da suka shiga ahead quarter tare da Chief of army staff, da
commender da sauran sojojin dake da alhaki akan Tsintar Yaran A daji, tattaunawa ce
ta musamman da zata dauki tsawon awa nni suna Yinta.

*UNAISERH ANGEL💋*

Mutuniyar tun da ta farka, bakinta awashe kamar wadda akayima Albishir da gidan
Aljanna, sai faman zarya take Yi a ɗakin ta kasa zama, jefi jefi ta kan wurga eye
balls dinta kan wall clock dake a ɗakin don ganin lokaci idan yana tafiya, ta ƙosa
su kammala meeting din azo a ɗauke su, don ita a takure take da zama america.

Ta zuba hannayenta biyu acikin aljihun wandonta, bakomai take tunawa ba face Aunty
Aneelerh da daddynta, ta sanyawa ranta cewa idan suka koma Nigeria, zata ganshi a
gidansu.

Zame hannayenta tayi daga cikin aljihun wandonta, ta goya su saman ƙirjinta,
abun nayine.

“Masoyiya Angel,” muryar dr Laura ce ta fargar da ita ga kallonta, har batasan


lokacin da ta furta”Sun gama meeting din”? Fuskar dr Laura dauke da murmushi ta
ƙaraso ciki, hannunta ruƙe da ƙatuwar shopping bag.

A gefen gado ta ɗaura jakar kayan, tare da miƙa hannu ta rungumo Angel a
jikinta.

“Zanyi missing dinki masoyiya Angel, sai dai na lura kamar ke ba za kiyi kewata
ba ko”? Ta fada tana raba jikinta daga na Angel.

Duƙar dakai Angel tayi cikin jin kunyarta tace”Idan nace bazan yi missing dinki
ba, Nayi ƙarya, ba ma ke kaɗai ba, duka nurses da likitocin da suka taimaka mana
wurin samun lafiyarmu, zamuyi kewarku sosai”

Shafa gefen fuskarta dr. laura tayi da tafin hannunta.

Cikin karyayyar murya ta furta”masoyiya Angel, saura mintuna ƙalilan suka rage
maku a asibitin nan, Ƴan uwanki duk sun shirya cikin sabbin Kayan da na Siya masu,
Kema ga naki nan” ta faɗa tana nuna mata jakar kayan data ajiye mata saman
mattress.

“Sannan akwai Waya dana siya maki, na yi maki Saving phone number dina tare dana
Dr brown dana dr mark, da duk numbers na nurses da suka kula da ku, idan kin sanya
layi akan wayar ki kira mu pls” Daƙyar ta karasa maganar, idanuwanta sun cicciko
tab da ƙwalla, Jikin Angel duk yai sanyi, zuciyarta ta karaya.

Cikin murya tamkar tame Yin raɗa, dr laura taci gaba da cewa”Abu ɗaya da ban
faɗa maku ba, dama na yanke shawarar Sai mun ke6e dake in sanar da ke, saboda Na
yaba da hankalin ki da kuma kaifin basirarki da wayon ki,’ Angel ta natsu tana
sauraronta.

“Matar da sojoji suka damƙa amanarku a hannunta, Mistress ce,” kai tsaye sunan Ya
daki dodon kunnan Angel, cikin rashin fahimtar ma’anar hakan ta maimaita kalmar
mistress.

Jinjina kai Dr Laura Tayi”tantiriyar ƴar bariki ce mai zaman kanta, shaidaniyace
a fagen iya karuwanci, ta shahara sosai, babu wanda baisanta ba, tayi ƙaurin suna a
America, maca ce mai haɗarin gaske, Namiji baya Iya ganinta Ya kawar da idonshi,
saboda kyawun surar dake gareta, Nayi ƙoƙarin Fahimtar da sojojin Akan illar damƙa
amanarku a hannunta amma sunƙi su amince min Angel, ni nasan da wuya ta Iya baku
kulawar daya ce, in ma bata gur6ata maku rayuwarku ba, Musamman Ƴan uwanki
maza........” Hankalin Angel Ba ƙaramin tashi yai ba, duk da Sanyin A.c na ɗakin
zufa ce ke tsastsafo mata saman goshinta, idanuwanta azazzare take kallon fuskar dr
Laura dake kora mata jawabi.

“Ni damuwata depression din dake damunku, da kuma ɗan uwanku mai fama da ciwon
zuciya, idan har aka cigaba da ƙuntata maku zaku Iya rasa rayukanku, shiyasa banso
suka damƙa amanarku a hannun karuwa ba, donni a sanina da matar masifaffiyace tana
da girman kai, bata ta6a yin aure ba, kuma bata san ciwon haihuwa ba, abunda ta
sani shine ƙwacewa matan aure mazajensu tayi fasiƙanci da su, matar ta zama tamkar
annoba, ta raba aure da dama saboda hatsabibancinta” dakatawa tayi da yin jawabin
idonta akan Angel, tsantsar tashin hankali take gani acikin ƙwayar idonta, Jikin Ta
ƙaura Yai la’asar, An gudu ba’a tsira ba.
Muryarta Na rawa ta furta”Aunty, amma meyasa suka damƙa amanar mu a hannunta?
Babu wata ne sai ita? Kuma ai mu bamu buƙatar wadda zata kula damu, idan ma akwai
abunda zamu buƙata bai wuce jami’an da su bamu tsaro ba....” bata ƙarasa maganar ba
dr laura ta katse ta da cewa”dalilin dayasa suka damƙa amanarku a hannun ummin
america, kamar yarda major ya sanar dani, matar tamkar ma’aikaciyarsu take, ta saba
yi masu aiki wurin jan hankalin tantiran ƴan ta’addan da suka gagara a ƙasa, suna
yin amfani da ummi wurin ɗana masu tarkon da zasu kamasu, kuma suna cin nasara,
Masoyiya Angel ban faɗa maki hakan donna tada maki hankali ba face don ki dage
damtse wurin Yin yaƙi da ita akan ƴan uwanki, kada ki kuskura ki bari ta ke6e da
ɗaya daga cikin Samarin dake a jikinku, Idan ba haka ba za’a Iya samun matsala,
saboda bata da linzami matar, duk da A yanzu ina kyautata mata zo, tun da har
sojojin suka aminta da ita suka damƙa mata amanar ku, hakan na nufin sun san zata
Iya ne, Bayan haka sun ƙulla yarjejeniya da ita akan baku kula ta musamman da kuma
gujewa duk wani abu da zai 6ata maku rai, kamar yarda na gani dai dai da tsawa tayi
maku babban laifine, don haka Zan tura maki sharuddan da sojojin suka gindaya mata
akanku ta whatsapp, saboda inaso kiyi amfani da su wurin ja mata kunne idan ta sa6a
maku,” jinjina kai Angel tayi alamar toh ta ƙara da cewa “bansan da wasu kalmomi
zanyi amfani ba wurin yi maki godiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanki, saboda
kyautatawar da kukayi mana, gashi kun ɗauke mu tamkar ƴaƴan ku, “

Shafa sumar kanta dr Laura tayi”Kada ki damu yana daga cikin aikin mu!, Yanzu ki
shiga kiyi wanka, Mintuna ƙalilan suka rage maku,” amsa mata tayi da toh, Bayan
fitar dr Laura, Angel ta nufi Jakar Kayan, zuciyarta a hautsine ta girgiza da jin
wacece matar da aka damƙa ma amanarsu, ita babban abunda ta ke jima fargaba
garkuwarsu, tunawa da lokacin da aka kawo masu unaiza a kurkuku, yarinyar ta ruɗe
shi da big boobs dinta, balle kuma matar da taji ance tana tafiya da imanin namiji
saboda dirin jikinta, tashin hankalin da ba’a sanya mashi date. (🤣)

Har ta fara Imagining abun da zai faru, a gidan da zasu zaune atare da ita, tayi
tunanin sun samu sauƙine komawarsu Nigeria ashe akwai sauran rina akaba.

A hankali ta ruko hannun jakar Kayan, ta zaro kayan dake acikinta, wata
haɗaɗɗiyar A-line gown ce launin red colour mai round neck ƴar ubansu awurin
haɗuwa, Rigar tayi mata kyau a ido, sai faman jujjuyata take yi, aranta tana ayyana
yau wata rana zata sanya kaya na mutunci wanda ba uniform din prison ba, wannan
abun farin ciki ne agare ta.

Bayan ta gama kallon rigar, ta ɗaurata saman mattress, ta zaro kwalin takalman dake
a cikin jakar tare da kwalin sabuwar wayar da dr laura ta siya mata, ƙirar iphone
15 pro, Takalman kuma Ankle strap ne masu tsini launin black, hada face mask da
mayafi aka basu wanda bakowa bane Ya tsara hakan face chief na Isod, Lokacin da dr
laura ta bukaci zata siya masu kaya Sai da aka nemi izininshi, yace ya amince bisa
sharaɗin idan zasu sanya kayan a haɗa masu da Niƙab ko face mask da zasu rufe
fuskokinsu, a ƙalla ta shafe tsawon mintuna biyar tana kallon kayan, bakomai yafi
burgeta ba face wayar da aka bata kyauta, tunawa da lokaci yasa tayi saurin nufar
toilet ta shige ciki, shaf shaf tayi wanka kafin fitowarta, Nurse jessica ta shigo
ɗakin hannunta ruƙe da gift kit ƙaramin akwati na kayan shafa, ta ɗaura shi gefen
gadon Angel, ta zauna saman kujera tana Jiran fiowarta, bayan ta fito daga wankan,
suka gaisa da nurse din cikin girmamawa, daga bisani tayi mata bayani game da care
kit din data kawo mata donta gyara jikinta, godiya Angel tayi mata bayan ta ɗauki
kayan shafar da rigar ta juya ta nufi toilet dasu saboda jin kunyar kada aganta
tana sanya kaya, murmushi nurse jessica tayi yayin da take binta da kallo.

Bayan ta shafe ko’ina na jikinta da body oil mai tsadar gaske, skin dinta har
glowing take yi, rigar tayi bala’en yi mata kyau, duk da bata da jiki tana da
tsawo, white in red abun ba’a magana, lokacin da ta fito daga cikin toilet ɗin, ita
kanta nurse din sai santin kyan Angel take Yi, daga saman rigar ta tsuke daga
ƙasanta bazace daga ta jujjuya rigar take bubbuɗewa kamar ana hura mata iska, bayan
ta kammala shiryawa nurse ta feshe mata jikinta da turaren desired destiny,
fragrance din turaren mai daɗin shaƙa a hanci.

Face mask din da ta sanya black colour ne launin takalmanta, har saman karan
hancinta mask din ya haura, Gray eyes dinta ne kaɗai suka Bayyana.

Ɗaura Mayafin rigar tayi asaman kanta tayi rolling dinsa, gyalen yana da tsayi ba
laifi, Har saman gwiwar hannayenta yakai mata, shima launin takalmanta ne.

“Kin yi kyau masoyiya Angel, sai ki ka yi mini kama da Cinderella saboda rashin
ƙibarki,” Ƙayataccen murmushine kwance saman fuskarta,

“Na lura kin ƙosa ki bar ƙasar nan, Ni kuma gashi bana son ki tafi, saboda na
saba da ke masoyiya Angel,” cikin sanyin murya Nurse jessy tayi maganar tana duban
fuskarta.

“Dr. laura ta bani kyautar waya, kuma ta faɗa min akwai phone numbers din ku
aciki, zan dinga kiranku akai akai muna gaisawa saboda ni kaina bana son mu rabu
don ya zamar mana dole ne mu tafi” Sai da tayi maganar Nurse jessica ta wurga eye
balls dinta kan kwalin wayar, zaro ido ta ɗanyi haɗi da cewa”wow, gaskiya dr. Laura
tana Ji da ke shalelenta, wannan waya haka mai kyau da tsada, Ina taya ki murna
masoyiya Angel, Kuma naji dadi da ta baki wayar, Kinga zamu dinga kiran juna muna
gaisawa, harma muyi video call” fuskarta dauke da matsanancin farin ciki, ta nufi
gefen gadon ta ɗauki kwalin wayar a hannunta, tana ƙare mashi kallo, Angel dai sai
murmushi take saki, bakinta yaƙi rufuwa kamar ta fasa ihu Haka take ji tsabar
murnar yau zasu Bar america zuwa ƙasarta ta gado.

“Yakamata mu tafi masoyiya Angel, Ƴan uwanki suna Jiranki a waje” cike da ƙagara
Angel ta amsa mata da toh, shaf shaf ta zura takalman a ƙafarta masha Allah, wankan
Angel yabi jiki.

A hannu ta ruƙe wayar bayan ta curo ta daga kwalin, atare suka fito daga ɗakin.

Tun kafin ta ɗago da idonta, Muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta”Genie gamu
nan ki dube mu da kyau, mun yi kyau” Da sauri ta wurga idonta kansu, masha Allah
har saida gabanta Ya faɗi tsabar kiɗima da ganin Kyawun da suka Yi acikin sabbin
kayansu, jemimah da azeeza launin gown dinsu Royal blue ne, hannah da parveen
launin punch pink, Ita kuma Batul launi ɗayane dana Angel, red colour, kowaccensu
akwai Face mask a fuskarta, Anyi masu rolling Veil a saman kawunansu, takalman
kafarsu flat ne ba kalar nata ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallon mamakin
Kyawun da suka Yi, mutun ɗaya ne ke babu a cikinsu, Mazan su huɗune, kowannansu ya
kimtsa cikin shiga ta mutunci ta kece raini wato shigar hadaddun Slim fit suit, sun
manna mask a fuskokinsu, kwantacciyar sumar kawunansu ta kwanta luf, ƙafafuwansu na
sanye cikin tsadaddun takalman fata, ta ko’ina ƙamshin turarensu ne ya karaɗe ward
din da suke.

Ganin tayi tsaye tana kallonsu bata motsa ba, yasa kowan nan su sanya hannu a
lokaci ɗaya suka Zame mask din dake a saman fuskokin su, sai faman washe mata baki
suke yi, wani irin farin ciki ne Mara misaltuwa ya kamata, tun daga kan yadda suke
shaƙar iskar ƴan ci zaka tabbatar da kwanciyar hankali da natsuwa atattare da su,
su kansu sun yaba da kyawunsu, sai faman shafa kayan jikinsu suke Kamar zasu
lashesu.

Jemimah ce ta ruƙo hannun Azeeza suka watso da gudu zuwa gabanta, Atare suka fada
saman jikinta, Hugging dinta su ka yi suna tiƙar dariyar murna, tuni idanuwanta
suka cicciko tab da ƙwalla, ko a mafarki bata ta6a tsammanin zata ga wannan ranar
ba, yau gata ga ƴan uwanta cikin shiga ta alfarma ba uniform din kurkuku ƙaddara
ba.
A hankali Batul da sauran ƴan uwan nasu suka nufo wurin Angel, ɗaya bayan daya
take rungumo su saman chest dinta, suna matuƙar ƙaunar junansu, nurses da likitocin
dake tsaitsaye cirko curko sai kallonsu suke yi gwanin ban sha’awa.

“Angel, Kinga yadda ki kayi kyau? Rigar nan tayi maki kyau, wlh duk munyi kyau,”
Batul ce tayi maganar tana shafa gaban rigarta da hannunta.

“Nayi tunanin abinci kaɗaine abu mafi kyau a duniyar nan, ashe sutura ma abu ne
mai ƙayatarwa, gaskiya bazan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Daɗi Nake
ji kamar In buga tsalle sama in dira ƙasa,” Parveen ce tayi maganar, sautin
dariyarsu yacika ko’ina, kasancewar suna Yin firar cikin harshen hausa babu wanda
ya fahimci abunda suke tattaunawa a tsakaninsu, sai dai Abi la66ansu da kallo.

“Ban ta6a ganin kalar kayan nan ba, Mun saba da Uniform kala daya na prison, Yau
sai gashi mun tsinci kanmu acikin sutura mai kyan gaske, godiya ta tabbata ga
Allah, domin kuwa shine silar komai, dama kin ta6a fada mana cewa mahaƙurci
mawadaci, sannan duk tsanani Yana tare da sauƙi, kuma babu yanayi na rayuwa da yake
kasancewa Na dundundun, Yau mun shaida hakan Angel” tun da Haris Ya fara magana
Suka natsu suna kallonshi, tamkar ba mara lafiyan nan ba, Jikinshi Yayi kyau ɗan
black beauty da shi, Kalamanshi sun tunama Angel deeja, Yarinyar akwai tawakkali
duk da bata da zurfin ilmin addinin musulci tayi imani da Allah, fiye da wani
musulmin daya taso acikin musulunci, tunawa da deeja ne yasa ƙwallar idonta suka
soma gangarowa saman kuncinta, a fakaice ta sanya hannu ta share su, haƙiƙa taji
zafin mutuwarsu, ga salsabeel daya tsaya mata aranta, bawan Allah ko awani hali
yake ayanzu? Ya rayu ko ya mutu? Allah masani!.

“Angel, Ina fata Yanzu hankalinki ya kwanta, babu sauran damuwa tun da yau zamu
koma Nigeria” Gabriel ne yai mata maganar Haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, hakan ba
ƙaramin dariya yaso ya bata ba, Javed yace”ni fa duk atakure nake jin kaina,
mutanan nan sai kallon mu suke Yi,”

Naufal Yace”ka gode ma Allah tun da ba Giants din kurkukun ƙaddara bane suke
kallon ka,” gaba daya suka sanya dariya cikin nishaɗi.

Gabriel yace “kyau suke kallo, wankan da muka ɗauka ne Ya burgesu, mu kanmu mun
burge kanmu balle kuma su”
Hanna tace”Wannan abun da aka sanya mana a fuska yafi komai 6ata min rai, Duk ya
toshe mun ƙofofin hancina, wai ba yadda za’ai mu tafi batare da mun sanya shi ba”?
Tana faman yamutsa fuska tayi tambayar tana kallon Fuskar Angel.

Kafin tayi yunƙurin bata amsa Gabriel ya riga ta cewa”saboda tsaro, shiyasa aka
bamu shi don mu sanya, sunanshi face mask,” Javed Yace”ai na gane shi, kalar wanda
tsohuwa zafreen take sanyawa ne” harara parveen ta ɗan jefa mashi”Ni bana so kuna
maganar matar nan, na tsaneta kamar mutuwa ta”

“Ina danish yake ne? Shi bai fito ba ne”? Angel tayi tambayar tana leƙen ƙofar
room dinsa.

Haris yace”Suna can ɗakin shi suna ta fama dashi akan ya sanya kayanshi yaƙiya,
kinsan mutumin da taurin kai kamar ƙashin nama, bansan Ya suka ƙare da shi ba, Har
lalla6a shi nayi na nuna mashi kayan dake a jikina amma yasa kafiya akan bazai
sanya ba”

Mai hali bazai ta6a canzawa ba, aranta ta ayyana hakan, Kallon su azeeza
tayi”our twins ku sakar min rigata, zanje ɗakin danish”
Azeeza tace”toh, mu tafi atare zamu biki” Ruƙo hannayensu tayi a cikin nata, suka
nufi ɗakin Danish, Su Haris ma suka bi Bayansu, har sun kusa shiga Muryar dr laura
ta katse masu hanzarinsu.
Cikin harshen turanci take yi masu magana “Duk inda na kalla kyawawan ƴan mata ne
da samari nake gani, kunyi kyau sosai, Kamar in sace ku” gaba ɗaya suka sanya
dariya, Miƙa ma Haris hannu tayi”zonan My baby boy, Ya jikin naka”? Zuwa yai
gabanta ta sanya hannu biyu ta rungume shi a ƙirjinta kamar yaron cikinta

“Allah ya ƙara maka lafiya Haris, zamu yi kewarku sosai, Ku kula mana da kanku,
zamu dinga kira akai akai don mu gaisa da ku” cikin karyayyar murya ta ƙare
maganar, tare da raba shi daga jikinta, idanuwansu duk sun ciko da ƙwalla.

Voice dinshi na rawa ya furta”mun gode sosai da kulawarku agare mu, Kune mutune na
farko da kuka fara jan mu a jiki kuka bamu kulawa ta musamman, akanku muka fara
yarda cewa akwai mutanan kirki a duniya ba duka aka taru aka zama ɗaya ba” murmushi
tasakar mashi tare da kai hannu ta shafa sumar kanshi”nayi magana da Angel, Nasan
zata baka kulawar daya dace, duk wani abu da kakeso kayi mata magana” amsa mata yai
da toh.

Angel da su jemimah duk suna a tsaye da sauran nurses da doctors dake kallonsu.

Miƙa ma Su hannu tayi”ku zonan my twins, Inason jin ɗuminku a jikina, gaskiya
zanyi kewarku” da sauri jemimah da Azeeza suka isa gareta hannu biyu ta sanya ta
rungume su tighly.

Bayan ta raba jikinta daga nasu ta kalli parveen da zolaya tace “Oh, Ji ra kike
saina ce kizo ki rungumeni? Ko dan baki ga abinci a hannu na ba”?

Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayansu da gudu parveen ta ƙarasa ta rungumeta,


shafa kanta dr laura tayi’ki kula mun da kanki, a duk lokacin da kika ji yunwa,
kiyi ma Angel magana zata baki abinci, kada ki zauna da yunwa” lumshe ido parveen
tayi ji take kamar karsu rabu da juna, don ba ƙaramun so suke Yima matar ba.
“Pure heart, my beautiful daughter zo ki rungume mommynki” ta faɗa tana kallon
Batul, da ɗan sauri ta je gabanta ta faɗa saman chest dinta sosai ta rungumeta.

“Ki kula mun da kanki, Allah ya tsare mun ku, zanyi kewarku” Batul tace”muma
zamuyi kewarku, idan muka samu dama zamu dinga zuwa muna ganin ku,”dr laura
tace”kada ki damu basai kunzo ba, muma zamu Iya zuwa dubaku har ƙasar taku” Batul
taji dadin kalamanta, ɗaya bayan ɗaya sai da tabisu ta rungumesu tana mai ƙara
jaddada masu akan su kula dakan su.

Lokacin da tazo kan Angel, Har ta miƙa hannu zata rungumota, Ba zato ba tsammani
Garkuwa Ya fito daga room dinsa, adai dai lokacin Jami’an Isod sun shigo ward din,
Cikin shiga ta black suits, Hannayensu da ƙafafuwansu sanye cikin baƙaƙen safuna,
takalman ƙafarsu leather shoes ne fuskokinsu duk sun sanya face mask, ƙirar su bata
da banbanci data jami’an kurkukun ƙaddara, Giants ne wani irin faffaɗan kirjine
dasu, na ban mamaki, suna tafiya cikin taku na ƙasaita, kai daga ganinsu zaka
shaida ƙarfin da suke dashi damtsen hannunsu tamkar zai fasa rigar jikinsu a
murmurɗe suke, azafafe suke yin takunsu tamkar zakuna, Suna tafiya tsokokin jikinsu
na motsawa da ƙaƙƙarfan kuzari na majiya ƙarfi.

Lokaci ɗaya ward din Yai tsit tamkar mutuwa ta gifta, bakomai ne Ya jawo hakan ba
face fitowar Danish daga room dinsa, tare da dr brown da dr. Mark jackson,
Tabarakallahu ahsanul khalikin, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da mutumin da
sutura ta raina kanta a jikinsa ba irin Danish !

Wankan daya ɗauka na slim fit suit dinsa sunyi bala’en yi mashi kyau, ya fito a
garkuwarsa, Garzon namiji mai jini ajika, sannan kuma mai ji da kyau da ƙarfi,
haɗaɗdar sumar kanshi dark brown curly sun gyara mashi ita, sunyi cutting dinta sun
ɗaure mashi ita, ta sauko saman dogon wuyan shi, takalman ƙafarsa leather shoe ne
launin black suit dinsa.
Fuskarshi tamkar anyi mashi make up tsabar haɗuwa, ga wani irin zazzafan ƙamshin
turare dake kurɗaɗowa saƙo da lungu na jikinsa kamar wanda aka tsamo daga cikin
kogon turare, Agogon hannunsa silver ce sai ɗaukar ido take Yi, wani abu da zai
baka mamaki duk irin haɗuwar da yai acikin kayan babu annuri akan fuskarshi ko
misƙala zarratin Ya haɗe rai kamar wanda aka ɗaura ma aure da mutuwa, Yana tafiya a
bubbuɗe kamar wanda zai Yi dambe, Kyawun surar danish yayi matuƙar tafiya da Imanin
Nurses din dake a kewaye da wurin da likitoci, all eyes on him ba matan ba mazan
ba, kowa kallonshi yake yi kamar zasu haɗiye shi, kai hatta Jami’an isod sai da
gabansu ya faɗi sunyi matuƙar girgiza da ganin shi, har dai wani daga cikin su ya
gaza jurewa muryarshi ƙasa ƙasa cikin harshen turanci Ya furta”Nayi tsammanin daga
Chief din mu angama halittar Namiji mai kyan fuska da sura, ashe ba haka bane nayi
kuskure, a yau naci karo da namijin duniya kamar garzonmu OWAIS, wannan Yaron Bai
da mararraba da shi, banbancinsu Launin fata”

*💋ABBAN SOJOJI💋*
*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da
kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da
ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala,
ga wadda za’a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message
from Boss Bature*

*✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct
number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

‫❤🤍❤سجن القدر‬

_THE PRISONERS E25🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*


Confusion of the heart💫

Jami’in dake gefen wanda yai maganar ne ya daura da cewa”Ni kaina na girgiza da
ganin matashin saurayin nan, Gaba ɗaya ma na rikice, na tabbata ko shi Boss Owais
din Yai arba da wannan Yaron sai yayi mamakin shi.

Amenity Ward Ya ruɗe da sambatun mutane akan kyawun Garkuwa, shi ko Dan tahalikin
Duk yabi ya rikice A rayuwarshi ya tsani kallo saboda Yana affecting din
natsuwarsa, Yana Hayaƙa shi, idanuwanshi sun makance neman Angel Yake yi, Gata
akusa dashi amma ya kasa ganewa, sai ƴan waige waige yake yi a ƙoƙarinsa naya gano
ta, An rasa me Iya buɗe baki yayi mashi magana acikin ƴan uwan nashi, baisan cewa
shine ya ruɗe su ba, Ya canza masu sosai cikin sabuwar shigarshi.

Sai da Haris Ya ɗaga murya Ya furta”Danish gamu anan” tukunna ya wurga


reddish eye balls dinsa akan fuskokinsu, cikin takun sauri Ya nufe su yana ƙarasawa
ba yi ƙasa a gwiwa ba Ya rungume Angel a saman broad chest dinsa, Ya cusa fuskarshi
saman kafaɗarta Yana faman sauke ajiyar zuciya, lumshe idanuwanta tayi lokacin da
ƙamshin turarensa Ya daki hancinta, gaba ɗaya taji ta a wata duniya tacan sama
jannati, in a throaty voice ya furta mata”bana son kallo, Ki faɗa masu su daina
kallo na, suna cutar dani”

Sam takasa yin magana, saboda yayi tighting dinta a kirjinshi, ya zagayo da arms
dinsa saman bayanta, mutanan dake awurin sai faman sakin murmushi suke yi kamar
zautattu, bakomai ne ya burgesu ba face hugging din da Danish yai ma Angel, sunyi
tamkar ma’aurata, kayan jikinsu sun yi fitting dinsu black and red, kamar furanni.

Gyaran Murya ɗaya daga cikin Jami’an isod Yai masu, muryarshi a bubbuɗe ya
furta”Zamu Iya tafiya, amma kafin nan Shi wannan Yaron Ina face mask dinsa Yake”?
Ya yi tambayar Yana nuna Danish da indext finger.

Da sauri Dr Mark, ya tura hannu cikin front pocket din coat dinsa, Ya zaro face
mask, Ya nufi Danish, yana fadin

“Handsome man, namanta ban sanya maka mask dinka ba, Kar6i ka sanya” kamar yayi
magana da gunki, Ko motsi Baiyi ba, tunda ya ƙanƙame Angel dinsa yayi shiru kamar
maiyin bacci.

Numfasawa dr laura tayi sai lokacin ta samu damar buɗe baki tace”Danish yana yi
maka magana, kaga sauran ƴan uwanka duk sun sanya nasu face mask din, Kaima ya
kamata ka kar6a ka sanya, jami’an isod suna jiran ku zasu ɗauke ku zuwa Airport ne”

Lamarin Ya ɗaure masu kai, Babu alamun zai motsa, Ga Angel tana so ta raba jikinta
daga nashi don ta lallashe shi, yaƙi bari tayi hakan saboda matsetan da yayi a
chest dinsa, hatta numfashinta daƙyar take Iya fitar dashi”

Cikin ƙagara Haris Yace”dan Allah Danish ka sake ta, Ka kar6i abun fuskar kai ma
ka sanya ko mun samu mu tafi”

Magiya suka dinga yi mashi akan ya saki Angel Amma Yaƙiya ko kallo basu ishe shi
ba”

Ɗaya daga Cikin Jami’an Isod Ne yai nazari akan Yaron, kasancewar suna da kaifin
basira, nan take Ya fahimci wani abu dangane da shi, ɗaya bayan ɗaya ya kalli
nurses din dake a ward din da likitocin da suka tsaya suna kallon su, Muryarshi a
kausashe Ya furta”Idan ba damuwa kowa Ya koma bakin aikinsa”!

Jin hakan yasa kowan nan su Juyawa suna tafiya suna waiwayon prisoners, Mutun
Biyar ne suka rage, dr laura da mark da brown sai nurse jessica da nurse rebecca.

Tun kafin Jami’in Ya tambayi lafiya su basu tafi ba? Dr laura tace”Muna so muyi
masu rakiya har zuwa airport, nasan suma Yaran zasu so hakan”

Jinjina kai yai tare da ɗaura eye balls dinsa kan Bayan Danish.

“Danish, likitocin da suka duba lafiyar ku ne su ka rage sai kuma mu jam’an da


muka zo domin tafiya da ku, babu kowa bayan mu, muna jiranka please kada ka 6ata
mana lokaci”! Cikin kwantar da murya yai mashi magana.

Sai da Ya ambaci hakan tukunna daƙyar Ya raba jikinshi daga na Angel, numfashinta
da sauri sauri Yake fita, hada tarinta saboda mugun shaƙar da tayima turarensa ya
sarƙeta.

Dr mark ne Ya sanya mashi mask din saman fuskarshi, da zolaya jami’in yace”ka
tabbatar ka rufe mashi hada idonshi, don wannan idan mutane suna kallon shi tsab
zai haɗa mana traffic jam a saman titi”

Gaba ɗayan su suka sanya dariya, ban da Danish, sam babu kwanciyar hankali atattare
da shi, Hakanan Yake jin haushin mutane babu gaira babu dalili, ji yake kamar ya
rufe su da bugu har sai sun mutu. Su Batul kuwa duk sun sha jinin jikin su, ganin
Jami’an Isod suke Yi tamkar mutanan prison, tun da suka shigo ko motsin kirki sun
gaza yi, Sai faman binsu da ido suke yi, ko magana jami’an su ka yi sai sun razana
babu wanda Ya lura da hakan.

Bayan Dr. mark ya kammala sanya mashi mask din, ya juya ya ruƙo hannun Angel
acikin nashi, a jere suka nufi Hanyar fita daga ward din Yayin da dr laura da mark
da brown suke Abayansu, su kuma jami’in Isod suna a kewaye da su, domin basu tsaro,
duk inda suka gifta a sibitin ido na akansu, ba marasa lafiyan ba, ba ƴan zuwa
dubiyan ba, ba Ma’aikatan cikinsu ba, kowa hankalin shi na akan su, Danish sai ƙara
matse mata hannunta yake yi a cikin nashi, hankalin ta ba akwance ya ke ba don ta
fahimci akwai wani abu dake damun shi.

Kaitsaye suka nufi parking space na asibitin, wasu danƙara danƙaran motoci ne
masu numfashi jigunannun gaske, a killace a harabar, da su akazo ɗaukarsu, hankalin
su Batul Ba ƙaramin tashi yai ba, Basu ta6a ganin abu irin wannan ba, Motocin dake
a killace aharabar suke ta faman bi da ido, Angel ce tayi amfani da harshen hausa
wurin yi masu magana akan su natsu kada su tsorata, abun hawa ne da akeyin anfani
dasu wurin tafiya mai tsayi wadda ƙafa bazata Iya yinta ba, sai da tayi masu bayani
cikin kwantar da murya tukunna suka fara sakin jikinsu.

Kafin su shiga motar sai da aka fara sanya kayan su a boot, akwatuna ne da
duffle bags kusan guda biyar, Suturar da dr laura ta siya masu ce, tare da
Takalmansu da magungunan da zasu dinga sha, da sauran care product da zasu yi
amfani da su. Bayan an kammala shigar da kayan cikin motocin ɗaya bayan ɗaya
jami’an suka bude masu car doors din, motar farko Danish ne da Angel sai Batul suka
zauna a mazaunin Baya, Mota ta biyu Gabriel ne tare da Haris da Hanna, Mota ta uku
Naufal ne da parveen sai Javed.

Dr. laura ta nemi alfarmar jami’an akan tana son su bata damar ɗaukar jemimah da
Azeeza a motarta, Jami’an suka ce mata zata Iya ɗaukarsu ba wani abu, A back seat
na motarta, Azeeza da Jemimah suka shiga, Ita kuma ta zauna A driver seat domin Yin
driving dinsu, Dr mark da dr bown suma hada su za a tafi kaisu airpot din, A cikin
motocinsu zasu tafi tare da Nurse jessica da rebecca.

Tun da prisoners suka shiga cikin mota, suke ta ƴan kalle kalle wa yaga baƙauye
yazo birni, duk sun sha jinin jikinsu, Fargaba suke Yi kada a cutar dasu, badan
Angel ta kwantar masu da hankalinsu ba, da kuwa Anga hauka, kusan A lokaci ɗaya
masu tuƙa motocin suka tada su, Jemimah ta rungume Azeeza jin sautin tashin
motarsu, Jikin su ya hau yin kerma kamar waɗanda sanyi ya kama, Dr laura dake
kallonsu ta madubin motar, fuskarta ɗauke da murmushi ganin yadda suka ƙanƙame tace
masu su kwantar da hankalin su, babu abunda zai same su.

A motar su Parveen Ta ƙanƙame naufal saboda tsoron da taji, hada javed sun haɗu
sun mannewa juna kamar kifayen gwangwani.

A motar su Gabriel kuwa, Hannah da Haris sun ƙanƙame shi, sai faman tiƙar dariya
yake yi, shi dama wayayye ne bakomai ne Ya manta na memory dinsa ba, Hannayen shi
biyu ya sanya saman bayansu Ya ƙara tighting dinsu ajikinshi yana kwantar masu da
hankalinsu.

Danish kuwa tun da suka shiga motar, ya kwantar da kanshi saman kafaɗar Angel, ko
motsi baiyi, Yana zaunea left hand dinta, yayin da Batul take a zaune saman seat
din dake a right hand dinta, Ganin yadda Batul ta ruɗe jin tashin mota, Hannayenta
biyu ta ɗaura saman kanta, kamar zata fasa ihu da sauri Angel ta damƙo hannunta
tare kwantar mata da kanta saman laps dinta, ƙanƙameta tayi sosai tana faman sauke
ajiyar zuciya, abun ne yazo masu wani iri basu saba ba.

Slowly motocin suka nufi hanyar babban gate din asibitin, gaba da bayansu motocin
Jami’an isod ne, Sun sanya motocin da aka ɗauko su dana su dr. laura a tsakiyar
nasu motocin domin basu tsaro.

Da matsakaicin gudu motocin suka haura saman titi, prisoners sun ga abunda yafi
ƙarfin idanuwansu, Ta glass din window su ke Hangen danƙara danƙara gine ginen
birnin san antoni, masu ƙayatarwa, ga wuraren shaƙawata da kuma mutanan dake zarya
ta ko’ina, sun natsu suna kallon ikon Allah abun ya ɗaure masu kai.

“My man, bacci zaka yi”? angel ce tayi mashi magana tana duban fuskarshi, tayi
mamakin ganin zufa na tsastsafo mashi saman forehead dinsa, duk da sanyayyan Sanyin
A.c na motar, Batool tuni ta miƙe daga saman laps din Angel, ta koma bakin windown
motar tana kallon Ikon Allah.
In a low voice ya furta mata”Am not feeling well, ina jin wani iri a jikina kamar
wani abu zai faru dani” shafa sumar kanshi tayi da hannunta”In sha Allah ba abunda
zai faru da kai My Man, Ina atare dakai, so ka kwantar da hankalin ka, bari nayi
maka addu’a” ta faɗa haɗi da manna la66anta saman lallausar sumar kanshi, addu’o’i
ta soma karantowa tana tottafa mashi asaman kanshi.

Muryar Batul ce ta katse mata hanzarinta”Angel wai su mutanan duniya dama haka
suke da gudu kamar zasu tashi sama”?
Dariya ce ta kubcewa Angel, ta wurga idonta kan batul data mannewa glass din
tagar motar, ta ƙura ido tana kallon al’amurra.

“Batul ba mutane bane suke Yin gudu, Abun hawan da muka hau ne ya ke yin gudu
damu”

Ba tare da batul ta juyo ta kalle ta ba tace”Oh, yanzu na fahimta” daga haka bata
ƙara cewa komai ba.

*UMMIN AMERICA💋*
A hankali motar su take tafiya saman shantalelen titi, tana a zaune saman front
seat, ta ɗauki wankan pant suit sunyi bala’en yi mata kyau, dogon wandone fari da
sexy vest fara ta matse ta kirjinta Ya fito sosai, don ma ta ɗaura Blue coat daga
sama, ta canza launin sumar kanta zuwa blue, light make up ne asaman face dinta ,
fararen idanuwanta suna a manne da farin glass hakan ba ƙaramin ƙara mata kyau ba,
Matar dake driving dinta, ƙawarta ce *NATASHA* baturiyar England, Aminnan junane,
sai dai daga ganinta babu digon imani a zuciyarta, fitsararrace ta bugawa a jariga.
Kayan dake a jikinta da su da babu duk ɗayane, doguwar rigarta tamkar net take
shara shara kana Iya hangen inners din ta, A yayin da take zaune saman driver’s
seat, Cigrette ce a hannunta na hagu, ɗayan hannun kuma da shi take juya sitiyarin
motar daga gani ta ƙware a iya driving, Tsabar Iya shan taba harta hanci ta baki
take huro hayakinta.

fira suke ɗan ta6awa a tsakaninsu cikin harshen turanci.

“Zanyi kewarki ummi, yanzu idan kika tafi yaushe zaki dawo? Natasha ce ta jefa
mata tambayar.

Numfasawa tayi kafin calmy ta furta “bazan daɗe ba, temporary guardianship ne ba
permanent ba, da zarar na kammala yi masu aiki zan dawo America”

Dariyar shaƙiyanci Natasha ta saki, tana mai cigaba da hura hayakin tabarta.

“idan ki ka yi wata ɗaya baki dawo ba, zan biyoki Nigeria don bazan Iya jure
rashin ki ba” ta fada tana duban fuskar Ummi.

“Zaki tafi ki barni da mutananki, don nasan ba zasu ƙyaleni ba, da zarar sunji ki
shiru ni zasu tuntu6a,” Ummi tace”Zaifi ki canza layin wayar ki, kafin in dawo, don
bana so kowa yasan da zancen barina ƙasar nan ko kuma inda zanje, Yana daga cikin
sharuɗɗan da sojoji suka gindaya mini.”

“Ai nayi mamaki da kika amince zaki kar6i jagorancin kula da yara har goma sha
ɗaya, idan nice bazan Iya ba, kema nasan ba hakanan kika kar6i aikin ba. akwai wata
manufa a ƙasa” ta ƙare maganar tana dariya.

Ummi tace”kamar kin shiga zuciyata, tabbas inaso naje Nigeria ne don karan kaina
bawai don aikin da sojoji suka bani ba, nima akwai abun da zai kai ni, da ba don
haka babu abun da zai sa in bar America.

Natasha tace”yayi kyau mutuniyata, ina fata zaki cigaba da sheƙe ayarki, bana so
silar zuwan ki ƙasarki ki shiryu nafison ki ƙara lalacewa ki 6ata masu mazajen
auransu,” dariya suka sanya gaba ɗayansu.

Ummi tace”Yaran fa da aka bani in jagoranta kyawawane fa akwai wani zazzafan Yaro
acikinsu, yana da kyawun sura” lumshe ido natasha tayi muryarta tamkar ta mashayin
giya tace”kice yaron babbar harka ne, tun kafin ma in ganshi na ƙyasa”

Ummi na dariya tace”yadda kike shaiɗaniyar nan nayi imanin idan kika ganshi
daƙyar zaki Iya runtsawa, kallon shi kaɗai zai tada maki da maitarki, Natasha nayi
mu’amala da maza kala daban daban amma shi wannan Yaron na musamman ne, Kamar dai
Chief Owais, kinsan shima Yana da zazzafar sura.

Natasha tace”Har yau ban daina kallon hotonshi ba saboda bana gajiya, aduk lokacin
dana rasa abokin harka hoton shi nake kallo in rage zafi, gayen ya haɗu duniyace
shi” cikin jin shauƙi Tayi maganar”

Ta ƙara da cewa”ƙawata zan baki shawara, matasan Yaran da za’a baki rainon su, kada
ki raga masu, idan jarabarki ta motsa kibiya buƙatarki da su, ai ke wannan Aikin da
sojoji suka baki gaba ta kai ki, in banda abunsu sun ta6a ganin inda aka ba kura
ajiyar nama”? Da shaƙiyanci ta faɗa tana sakin shu’umin murmushi na tantiran ƴan
duniya.

Ummi ta ɗan zaro ido haɗi da cewa”ba zai yiwu ba natasha, ke kin san wanene Chief
owais, yafi bomb bala’i, akan shi na fara jin tsoron namiji a duniyar nan, Mutumin
bai da fara’a Yana da kamun kai, sannan bai da imani idan ya damƙi Mara gaskiya,
idan har na kuskura na ƙetare Iyakata akan Yaran wlh tsaf zai Iya kasheni har
lahira, ni ko dai ban shirya mutuwa ba, akwai sauran bururrukan da nakeson cimmawa.

Fashewa Natasha tayi da dariya fararen haƙoranta a jere kamar gonar auduga, sam
firar su bata ɗauke mata hankali ga yin driving din da take Yi ba, har ta zuƙe
tabar hannun ta duka.

“Dole kiyi mini dariya ƴar rainin wayau” ta fada tana hararar ta.

Tsagaitawa Natasha tayi da yin dariyar ta dubi fuskar Ummin america”mutuniyata,


Kina ta zumuɗin zuwa Nigeria, banji kina maganar mutumin ki ba” cikin rashin
fahimtar kalamanta ta furta”Wa? Kashe mata ido ɗaya Natasha tayi”Boss Man, ko kina
nufin har kin manta da shi? ta faɗa tana duban hanya.

Yamutsa fuska Ummin america tayi”Allah ya raba ni da alaƙaƙai, bana fata wani abu
ya ƙara hada ni dashi, jarababbe kawai”

Natasha na dariya tace”haba ummi, mutumin fa ya mutu akan ƙaunarki, nayi ƙoƙarin
ganin na maye gurbinki acikin zuciyarshi sai dai Ya nuna mun cewa ke kaɗai ce za ki
Iya sarrafa shi yadda ki ke so, kuma yana nan akan bakansa na cewa ba zai ta6a
barinki ba har abada ke tashi ce”

Mood din fuskarta ne ya canza zuwa 6acin rai.


“Natasha, I don’t even want to hear his name, bawai don bana son shi ba, kawai ni
bana son mutumin da zai nuna ƙarfin iko akaina, kamar wani ubana, yaushe rabona da
shi tun lokacin dana ɗauki cikinsa na zubar ba tare da saninshi ba, muka samu
sa6ani dashi ban ƙara ganin ƙeyarsa ba, Kin san fa mutumin akwai zuciya ga girman
kai, nasan zai neme ni ne tun da baya gajiya dani”

Natasha tace”kina wasa da damarki ummi, da Ace nice na samu matsayin da kika samu
acikin zuciyarshi, bana tunanin zan iya bijire mashi, biyayya zanyi mashi sau da
ƙafa””

Ta6e baki ummi tayi”nima ba gudunshi nake yi ba, Ciki ke bana so, saboda zai 6ata
min shape din jikina, kuma ni tun kafin mu ƙulla alaƙa dashi sai da na faɗa mashi
sharuɗɗana, nace mashi bana ra’ayin yin aure kuma bana son ciki, ban damuwa ba idan
zamu shekara munayin sharholiyarmu da shi in dai zaiyi min biyayya”

Murmushin gefe fuska Natasha tasaki”Ummi kenan, Yanzu mu ajiye zacenshi a gefe,
ni dai shawarar da zan baki shine idan kika koma ƙasarku, kada ki kuskura ki kula
ƙasƙantattun mutanan da su ka yi silar barin ki Nigeria, bana so ki nuna kin san
su, inaso ki nuna masu cewa kwandon shara yafi su mahimmanci a awurin ki”

Maganar Natasha ta ta6a zuciyarta ummi, tuni ta ɗaure fuskarta, tunawa da wani abu
da ya faru a rayuwarta.

“Please, stop talking about them, i don’t wanna hear it” rai a6ace ta furta hakan,
jinjina kai Natasha tayi”shikenan nadaina mutuniyar saboda bana son 6acin ranki”
mood din fuskar Ummi Ya canza sosai, abubuwan da suka faru arayuwarta take
tariyowa, masu daɗi da marasa daɗi.

“Mutum biyu masu mahimmanci arayuwata, ina fata na sake haɗuwa da su, Yarinyar
dana bari inason na ganta duk da bani da tabbacin tana araye ko ta mutu, ba dan
bana son ta ba, na tafi na barta, tun tana jaririya, shi kaɗai ne danasanin da
zanyi arayuwata”

A cikin zuciyarta ta furta hakan ba tare da sautin muryarta ya fita ba, tuni
idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla. Afakaice ta zaro hanky daga hand bag dinta
ta share ƙwallar idonta.

Sun jima suna tattaunawa da ƙawarta Natasha, A lokaci ɗaya motar su, da motocin
jami’an da suka ɗauko su Angel suka ƙaraso katafaren Airport din, slowly Ummi ta
zuge glass din motar don ta samu damar ƙare ma Yaran kallo ita da Natasha, kafin
fitowarsu daga mota, suka soma Jin jiniyar motar sojoji, kusan guda uku suka nufi
wurin da sukayi parking din nasu motocin, bayan sunyi parking din motocinsu,
Commender ya fito daga motarshi, tare da Major da captain da sauran sojojin da su
ka zo da su. kowan nan su yana sanye cikin kakinsa, ga dukkan alamu sunzo Yi masu
bankwana ne.

Jami’in dake tuƙa motarsu Angel ne ya fito da sauri Ya zagaya Ya buɗe masu kofa,
Angel ce ta fito hannunta ruƙe dana Danish, duk da face mask din dake akan
fuskokinsu hakan bai 6oye tsantsar kyawun idanuwansu ba, Hankalin Natasha ba
ƙaramin tashi yai ba lokacin da idanuwanta su ka yi tozli da kyakkyawar surar
Danish, tun kan ummi ta faɗa mata wanene shi tayi saurin cewa”kamar Yaron da kika
faɗa min ko”? Ummi na murmushin shaƙiyanci tace”may be shine, ai ni fuskar shi na
gani a hoto, naga wannan ya sanya face mask, amma dai ina da tabbacin shi ɗin ne,
masha Allah ƙaramin mutum da babbar harka, Ni ma ban ta6a ganin shi ido da ido ba
sai yau, Nayi tsammanin jin shi yafi ganinshi, ashe ganin shi yafi jinshi,” lashe
baki Natasha tayi da harshenta kamar wata mayya tace”Ya tafi da imanina, Ya za’ai
ummi? Anya bazan biyo ku Nigeria ba? Kinga ke sai ki dinga rainon su ni kuma Ina
biyan buƙatata da su”

Ummi tace”bismillah zaki Iya bin mu amma ki sani komai ya faru dake kada ki nemi
ni, Chief owais sai yayi jajjagen namanki, idan kika ta6a mashi ƴa’ƴanshi”

Har ta ƙarasa maganar, Natasha batasan me take cewa ba, idonta akan Danish, Bayan
fitowarshi da Angel, Batul ta fito, Sauran Jami’an suka fito tare da bubbuɗe masu
motocin. Gabriel ya fito tare da Haris da hannah, Naufal ya fito da parveen da
javeed, dr laura ta fito daga motarta, ta bude masu Azeeza, suka fito suma, Nurses
din dake atare da su da dr mark da brown kowan nan su Ya fito waje. Prisoners sun
baza ido suna kallon inda suke, tun kafin su shiga cikin Airport din.

Ummi America da natasha sun tsaresu da ido


“Yaran Fa akwai kyau, Yanzu ummi har kina Iya zama wuri ɗaya dasu ba tare da kin
rage zafi ba”? Shiru ummi tayi mata ba tare data tanka mata ba, hankalinta na akan
prisoners, ta ƙura masu ido, hakanan ta dinga jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, ba
tare da sanin dalilin daya haifar mata da hakan ba, jikinta yai wani irin sanyi,
ɗaya bayan ɗaya take bin su da kallo, yayin da suke gaisawa da sojojin cikin raha
suke amsa masu.

Sai daga bisani Ummin America ta buɗe murfin motarsu, atare suka fito ita da
Natasha, Hankalin su Angel Ya dawo kansu, Kallo ɗaya tayi mata sai da gabanta ya
faɗi, kuma nan take ta gane wacece ita, tun da taga uban hips dinta da boobs dinta
da suka cika ƙirjinta, ranta ya bata cewar tabbas itace matar da aka damƙa ma
amanarsu, tun da ta fito hankalin kowa ya dawo kanta, taku ɗaya girgiza goma,
wankan suit din jikinta ya tafi da imanin kowa dake awurin.

Kallon kallo suka soma bin juna da shi, tsakanin prisoners da ummin america, da
kuma dr. Laura, da jami’an isod, da sojojin da suka halarta, sama sama suka soma
gaisawa da ita, Dr laura ta haɗe rai kamar yadda itama ummin american ta ɗaure mata
fuska, bayan sun gama gaisawa da juna, jami’an suka buɗe boot na motocin da suka zo
da su suka ɗauko suitcases dinsu tare da jakunkunan kayansu, gaba ɗayansu suka
ɗunguma zuwa cikin departure gate din Airport, ta inda suka samu sauƙi, Jirgin da
zai ɗauke su privet jet ne mallakin Jami’an isod, babu buƙatar jira ko wasu shaidu,
An riga An shirya masu komai su kawai ake jira domin tafiya, duk inda suka bi
darewa akeyi abasu hanya saboda sojojin dake atare da su, prisoners sai ƴan kalle
kalle suke Yi, sunga wuri mai kyan gaske ga mutane launi daban daban suna ta yin
zarya acikin wurin, Yankin da jirginsu zai tashi fili ne na musamman aka ware shi
domin tashi da safkar jirage masu zaman kansu.

Tanƙamemen Privet jet ne Aka tanadar masu, Mallakin Chief of isod, Aljannar
duniyace ƴar ubansu a wurin haɗuwa, tun daga wajen jirgin zaka fara cin karo da
sunan ISOD da aka rubuta da manyan haruffa ajikinsa.

Idan ka shiga cikin jirgin kamar ka shiga haɗaɗɗen villa ne saboda haɗuwar kayan
alatun dake acikin sa, akwai Falour wanda yaji hadaddun leather seats masu
numfashi, tare da ƙayatattun tables, ga fine carpet shimfiɗe saman floor na jirgin,
bayan shi akwai large flat-screen TV, ga Conference table domin yin meeting, a
kewaye yake da kujeru, ga kitchen da bathroom, and privet bedroom da kuma dining
area, Komai fa akwai shi acikin jirgin babu ce kaɗai ke babu, ta ko’ina sanyin A.c
ka ratsa cikinsa.

Bayan sun sauka abakin jirgin, Hankalin su Batul Yaƙi kwanciya tun da su ka yi
arba da jibgegen jirgin dake agabansu, ko a mafarki basu ta6a yin tozali da abu
kamar wannan ba, duk sun bi sun rude, sai faman zazzare idanuwa suke yi, badan
Angel na atare da su ba, da tuni wasu daga cikinsu sun zauce saboda tsabar kiɗima,
bankwana suka somayi da sojojin da suka rako su, Dr laura hada hawayenta na rabuwa
da su, ɗaya bayan ɗaya saida ta rungume su, tana yi masu fatan alkhairi, Jemimah da
Azeeza sunji ɗacin rabuwa da ita, sun sha kuka hawaye duk Ya 6ata fuskokinsu,
lallashinsu ta dinga yi tana kwantar masu da hankali, tace kada su damu zata iya
zuwa har Nigeria tagan su, babu wanda bai ji kewar rabuwa da su ba, Dr mark da
brown suma sun matse ƙwallarsu, hatta nurse jessica da Rebecce sai da su kayi kukan
rabuwa da su, musamman masoyiya Angel kowa ya saba da ita, suna sonta sosai, ummin
america tuni tayi sallama da ƙawarta Natasha, bayan sun gama ƴan rungume rungume,
sojojin da ke atare dasu sunyi masu fatan sauka lafiya, lokacin da zasu hau
matakalar jirgin daƙyar suke taka staircases din, har dai suka samu damar shiga
ciki, al’ajabi ya kama su ganin haɗuwar jirgin, kowan nan su Ya samu wuri saman
tausasan leather seats din suka zazzauna, tun da suka shiga jirgin ummin america
bata tanka masu ba, sai dai kallon kallon da suke Yi a tsakanin su, ita dai Angel
damuwarta Danish ɗinta, Ya ƙanƙameta, babu alamun lafiya atattare da shi, jikin shi
yai zafi rau.

Lokacin da jirgin Ya soma tafiya Yana bin hanya kafin Ya ɗaga sama, Hankalinsu
Azeeza ba ƙaramin tashi yai ba, jami’an Sunyi ƙoƙarin kwantar masu da hankali,
ganin yadda su ka ruɗe jikin su ya hau yin kerma, sun fahimci mugun tsoro ne da su,
Angel ce ta tunasar dasu akan suyi addu’a, aiko atare suka hada baki suna karanta
addu’o’in data koya masu.

Cikin ƙanƙanin lokacin jirgin Ya ɗaga sama Ya keta hazo can cikin sararin
samaniya, Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke kamar an yaye masu tsoron da suke Ji,
hankalin kowan nan su ya kwanta tun da aka kunna masu kallo a tv, ban da na Angel,
Yanayin fuskarta ya canza, sakamakon maganganun da taji Danish yana furta mata
acikin kunnanta, muryarshi arauna ce yake fadin baya son mutane, haushin su yake
ji, yana ji kamar ya kashe su, jinin su yake sha” ƴan hanjin cikin ta ba ƙaramin
kaɗawa su ka yi ba, sai faman zazzare ido take yi, babu wanda ya lura da halin da
take a ciki, sauƙin ma acikin kunne yake yi mata raɗa, sautin muryar baya fita,
kuma akwai tazara tsakanin seats dinsu dana sauran ƴan uwansu, ɗaya daga cikin
jami’an isod ne Ya ɗauko mashi eye mask ya miƙa ma Angel don ta sanya mashi a
tunanin shi hasken jirgin ke bayaso shiyasa ya cusa kanshi saman kafadar Angel may
be ko yana son ya runtsa ne.
Tun da ta sanya mashi eye mask taji yayi shiru ya daina magana alamar bacci ya
dauke shi, a ƙalla ta sauke ajiyar zuciya yafi a ƙirga, addu’o’i taci gaba da
karanto mashi tana tottofa mashi saman sumar kanshi, fatanta Allah yasa ba wani
mugun abun bane zai faru da shi, gashi ta manta bata nemi takardar dake ɗauke da
address din gidansu salsabeel, duk da bata tunanin ma ko sunje zasu samu abunda
suke so.

A Kishingiɗe yake saman shimfiɗeɗan full-sized bed dinsa dake acikin privet room na
jirgin, ya ɗaura kansa saman tattausan pillow, Shin wanene wannan kyakkyawan
matashin saurayin? A jin farko afagen kyau da ƙasaita, Namijin duniya, A halitta
madai-dai ci ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a buɗe yake, ga wannan six pack din
nasa baro baro, Vest din jikinsa tayi tighting dinsa, kana iya ganin zanen
ƙirjinsa, Ko ɗan wrestling bazai nuna mashi ƙirar ƙarfi ba, in ka kalli damtsen
hannunsa sai ka tsorata, mutun ne mai ji da ƙarfi, Allah yabasa kyawawan idanuwa
farare tass ga su so sexy, masu ɗauke da launin ƙwayar ido reddish brown, har
shining suke yi, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa
tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage
jagirarsa su haɗe da juna saboda Yana da yalwatacciyar suma, lallausar sumar kanshi
tasha gyara anyi mashi Military haircut yayi bala’en yi mashi kyau, abun da yafi
komai jan hankali a jikin shi tsadaddiyar launin fatar shi, chocolate colour, har
wani glowing take yi, hutu ya zauna mashi, jikinshi ya wanku da dollar, duk inda
namiji yakai to ya zarce nan, komai nashi na kece raini ne ba wasa a tattare dashi,
kuma burin kowace ƴa mace ne shi, a 6angaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka
ba, su kan su kuɗin raina kansu suke yi agabanshi, duk da tarin dukiyarsa baida
girman girka, mutum ne shi da bai ɗauki duniya da zafi ba, Allah ya bashi kaifin
basira, Yana da ilmin addini dana zamani, ta ko’ina Allah ya hore mashi, yana
matuƙar jin ƙan talaka, Yana da tausayi ga son taimako, shi sam abun hannunshi bai
rufe mashi ido ba, kyawawan halayansa da ɗabi’unsa abun burgewa ne, shiyasa ya fita
daban ko acikin jikokin family ɗinsu, ya shahara aduniya sosai, babu inda ba’a
sanshi ba, mutane basa gajiya da yabon shi, burin kowane ya yi tozali da shi,
babban abunda ya tsana a duniyar nan shi ne yaga mugun mutun mara imani acikin
mutane Yana zalunci, In kuwa ya damƙi irin su, mai ƙwatar su sai Allah, shiyasa
mutane masu irin halin suke mugun jin shakkar shi, dai dai da sunan shi aka fada
sai gabansu ya fadi, don baya yi masu da kyau, ni nasan bazan Iya misalta
ƙasaitaccen Namijin nan ba, Kaɗan ne na Iya faɗa maku sauran ku biyo ni acikin
labarin, Yanzu ne wasan Ya fara.

Tun da ya ɗaura lumsassun idanuwanshi akan tsadaddar laptop din gabanshi ƙirar
Apple macbook pro bai ƙyafta idon shi ba, Hannun shi na dama na sanye da wrist
watch ƙirar Rolex submariner haɗaɗɗar gaske, ya tattara dukkan natsuwar shi akan
abun da yake kallo, duk wani motsin prisoners dake acikin jirgin yana kallon su ta
cikin laptop dinsa, Ƙayataccen table din dake agaban gadon shi ɗauke ya ke da Mug
na cofee ga fresh fruit da aka ajiye mashi, daga gefen shi saman mattress, suit
jacket dinsa ce daya cire launin Navy blue, trouser din ta ne a jikin shi, hankali
a kwance bai da wata damuwa.

Awanni da suka ɗauka acikin jirgin ba ƙaramin daɗi suka ji ba, saboda an gatanta
su, sunci abinci har sau biyu, sun yi bacci sun tashi, komai suke so yi masu ake
yi, Danish ne kaɗai baici komai ba, tun da bacci ya ɗauke shi bai farka ba.

*💋ABBAN SOJOJI💋*
*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Assalamu alaikum, fatan mun wuni lpy, ga masu son abban sojoji complete 400 da
kuma kurkukun ƙaddara wanda nake cikin rubutawa, ga number da zasuyi mini magana da
ita, new number ce wadda nake da ita me 08103884440 whatsapp din ya samu matsala,
ga wadda za’a same ni da ita (08134387050) ayi mini magana ta whatsapp, message
from Boss Bature*

*✍️ Mu haɗu Gobe In sha Allah Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda
zata Kaya, Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct
number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*

First bank

3196407426,

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina
08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

_~*BossLadiesWriters*~_

_*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*_

~Middle step~

‫❤🤍❤سجن القدر‬

_THE PRISONERS E26🔥💫_

*Daga alƙalamin Boss Bature*

Confusion of the heart💫

Tun da Aneelerh ta turawa numbar saƙo har yau ba’a tuntu6eta ba, abun ya dame ta,
ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kullum ne sai ta ƙara jaraba kiran layin ko
za’aci sa’a mamallakin wayar ya ɗaga amma wani iko na Allah a kashe take samun
layin duk ta damu da son jin wanene.

Fitowa ta yi daga cikin ɗakinta hannunta ruƙe da wayarta, ɗakin zahra ta nufa da
niyar ta faɗa mata halin da take ciki wata’kil ta bata shawara akan abun da ke
damunta.

A bakin ƙofar ɗakin ta fara yin sallama, shiru ba’a amsa mata ba, kusan sau uku
tana kwaɗa sallama zahra bata amsa ba, tunani ta soma yi ko dai ta koma wurin aiki
ne? Ko kuwa baccin lalacin da ta saba yi ne, wata’ƙil kuma wanka ta shiga.

Haura ƙafa ta yi ta shiga ɗakin zahra, tun abakin ƙofar room din ta fara cin karo
da takalmanta da jakarta da mayafin ta gaba ɗaya ta watso su saman floor, nan take
hankalin Aneelerh ya tashi da sauri ta ɗago da ido tana kallon gadonta, duvet dinta
da pillow dinta duk ta watso su ƙasa, Komai na ɗakin ta tarwatsa shi.

Aneelerh ta fahimci babu lafiya wani abu ya faru da ita, Zahra da ta sani Mai
tsafta dagangan dai bazata ta6a barin ɗakinta a hargitse ba.

Cikin tashin hankali ta soma ƙwala mata kira”Zahra! zahra!!” shiru babu amsa,
ranta ne Ya bata cewar ko dai bata agidan ne ko kuma ta shiga ɗakin ummi, da sauri
Aneelerh ta fuce daga ɗakin, Har zata gifta ta falo ta wutsiyar ido ta hango Mami
da ummi zaune suna fira, juyawa tayi da sauri ta nufe su, babu wanda Ya lura da ita
acikinsu har saida ta furta”ummi mami Ina zahra” kusan atare suka ɗago suna
kallonta, gaba daya sun fahimci babu kwanciyar hankali atattare da ita.

Ummi tace”kin duba ɗakinta baki ganta ba”?


Kafin ta bata amsa mami tace”Aneelerh wai lafiya? Ya akai naga kamar bakya acikin
natsuwarki”
Muryarta na ɗan rawa ta furta”bakomai, na duba ɗakin zahra ne ban ganta ba”

Mami tace”shine duk kika ɗaga hankalin ki? Sai kace yau ta fara fita daga gidan,
kema kinsan zahra idan har ba wurin aiki taje ba toh tana acikin gida”

Ummi tace”tun ɗazu fa ta dawo, ki kwantar da hankalin ki, bata wuce cikin
ɗakinta, Ki koma ki sake dubawa”

Juyawa tayi da sauri ta nufi ɗakin donta ƙara dubawa.

Bayan tafiyarta ummi ta dubi mami”ƙawancen Aneelerh da zahra ba ƙaramin burgeni


ya ke yi ba, har mamaki nake yi idan naga yadda Aneelerh take jan zahra a jiki, duk
da ta girme ta”

Mami na murmushi tace”ai shi ƙawance ba a shekaru yake ba, indai mutum Ya mallaki
hankalin shi ko da ya girme ka zaka Iya ƙawance da shi, Ni kaina ba ƙaramin burgeni
suke Yi ba, Allah dai Ya bar zumunci”

Ummi tace Ameen ameen.


Daga haka su ka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.

Afujajen Aneelerh ta faɗo ɗakin zahra tana faman Yin haki, ta kware murya tana
ambaton sunanta”Zahra! zahra! Nasan kina jina, Dan Allah kiyi mini magana”

Still babu alamar za’a tanka mata, ranta ne ya bata cewar wata’ƙil ta fita ne ba
tare da sanin kowa ba, Har ta juya zata fuce daga ɗakin ba zato ba tsammani ta soma
jin shessheƙar kukan zahra, da sauri Aneelerh taci burki, a sukwane Ta juya tana
bin ko’ina na ɗakin da kallo, a ƙoƙarinta nata gano inda zahra ta 6uya, hankalinta
yafi karkata akan toilet din ɗakin, da sauri ta ƙarasa bakin kofar ta kara
kunnanta, sosai take jin kukan zahra mai matuƙar tsuma zuciya.
Muryarta na rawa ta furta”Zahra meya faru dake? Wanene ya ta6a min ke? Dan Allah
ki faɗamin zahra, ashe kina jina shine kika ƙi tanka mun ko?” cikin shessheƙar kuka
zahra tace”...Aunty Aneelerh babu abun da ke damuna, kawai bana son kowa ne a kusa
dani”

“Ki fito daga cikin toilet din muyi magana zahra, ni bana so inganki acikin
damuwa, kema kin sani har farin cikina zan Iya sadaukarwa saboda ke, don haka ki
fito muyi magana” cikin kwantar da murya Aneelerh take yi mata magana.

“Zahra ke nake jira ki fito muyi magana, wlh idan kika bari na haura ƙafa ta daga
cikin ɗakin nan to kada ki yi tsammanin zan waiwaye ki, haba dan Allah, ina amfanin
irin hakan? Ashe dama baki ɗauke ni kamar yadda na ɗauke ki ba? Har zaki Iya ke6e
kanki cikin damuwa ba tare da kin neme ni ba”?
A faɗace Aneelerh ta ambaci hakan, duk don ta samu zahra ta buɗe ƙofar toilet
din.

Bugun ƙofar tayi da hannunta”kada Allah yasa ki buɗe ƴar rainin wayau” ta faɗa
tare da juyawa ta nufi ƙofar fucewa daga dakin, Buɗe ƙofar toilet din zahra tayi,
Fuskarta sharkaf da hawaye idanuwanta har sun kumbura, kumatunta sunyi jawur dasu,
Short ne a jikinta tare da farar vest, Sumar kanta kamar ta mahaukaci sabon kamu.

Da gudun gaske ta nufi Aneelerh dake ƙoƙarin fita daga ɗakin, Gaba ɗaya ta faɗa
saman bayanta ta rungume tana cigaba da yin shessheƙar kuka.

Ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, tare da kai hannu ta ruƙo damtsen zahra ta
zagayo da ita, har saida gabanta ya faɗi ganin yadda hawaye suka wanke mata
fuskarta tamkar ba zahra ba, damuwace ƙarara akan fuskarta, kwantar da kanta
Aneelerh tayi saman kirjinta, a hankali take shafa sumar kan zahra da yatsun
hannayenta.

“Ya isa zahra, ki daina kuka bana son ganin hawayenki,’ cikin murya kuka
tace”Aunty Aneelerh ba zaki gane ba, Ni kaɗai nasan halin da nake aciki, Allah ji
nake kamar in haɗiyi zuciya in mutu kowa ya huta”

Kalaman zahra sun ƙara ɗaga mata hankali, tabbas akwai gagarumar matsala,
Yarinyar da koda yaushe fuskarta dauke da murmushi komai zaka yiwa zahra a duniyar
nan baka isa ka 6ata mata ranta ba, sai gashi a yau itace take Yin kuka har tana
faɗin kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu.

“Kiyi haƙuri zahra, bai kamata kina yin wannan furucin ba, Idan ma wani abune ke
damunki meyasa ba zaki kai kukan ki ga Allah ba? sai kawai ki kulle kanki a toilet
kina kuka? Hakan ya dace? Kina tunanin shine mafita a gare ki? Ga ummi ga mami, ga
mahboob, ga abie da uncle uwa uba ga kuma ni meyasa ba zaki tuntu6i ɗaya daga cikin
mu ki faɗa masa damuwarki ba? Kin tsaya kina yin zurfi ciki a ƙarshe ki yi wa kanki
illa amma faɗamana da zakiyi shi zaisa ki samu maslaha na abunda ke damunki, ko da
ace bamu da abun da zamu taimaka maki wurin yaye damuwarki zahra zamu Iya baki
shawara ko mutayaki da addu’a akan Allah ya yaye maki”

Faɗa Aneelerh tayi mata, sai faman sauke ajiyar zuciya take Yi, ruƙo hannunta
Aneeleeh tayi”wuce ki shiga toilet ki wanke fuskarki Ina jiranki” ta faɗa tare da
sakin hannun zahra, baiwarAllah jikinta duk ba ƙwari tana tafiya tana waiwayon
Aneelerh, yayin da hawaye ke cigaba da fita a idonta.

Kafin fitowarta Aneelerh ta bar ɗakin ta nufi falo, fridge ta buɗe ta dauko mata
ruwa me sanyi.

Cikin tafiyar sauri ta nufi ɗakin.

“Aneelerh kinga zahran ne”? Muryar mami ce ta katse mata hanzarinta, ba tare da ta
juya ta kallesu ba ta bata amsa da cewa”Eh mami, ashe toilet ta shiga”
Bayan ta shiga ɗakin, ta daura ruwan a gaban mirror, ta koma bakin door din ɗakin
ta soma tattara kayan da zahra ta watsar ta maida su a ma’ajiyarsu.

Ba ta jima da zama a gefen gadon ba, Zahra ta fito daga toilet, ta wanke fuskarta
kamar mara gaskiya ko haɗa ido da Aneelerh bata son yi, saman mirror chair ta zauna
tana fuskanta Aneelerh, sai dai ta taƙi ɗagowa su haɗa ido da ita.

“Ga ruwan nan ki sha” ta faɗa tana nuna mata robar ruwan, data ajiye mata, Yatsun
hannunta na kerma ta ɗauki bottle water din ta cire murfin ta soma ɗaɗɗakar ruwan
kamar zata haɗa da robar duka ta shanye, bayan ta gama sha ta maida murfin robar ta
daurata gaban mirror.

“Zahra ina sauraronki, Ki natsu ki fadamin meya faru dake? Da har yaja kika kulle
kanki a toilet, bana so ki furta mun kalmar babu komai! Ranki zai Iya 6aci”
fuskarta a ɗaure tamau tayi mata maganar.

Zahra na faman sunnar dakai, idanuwanta akan yatsun hannunta muryarta adabarbarce
ta soma magana.

“Aunty aneelerh zan faɗa maki amma kada ki faɗa ma kowa dan Allah,” jinjina kai
Aneelerh tayi”in sha Allah”

Cigaba da yin magana tayi”dama akan decorating company dinmu ne, ban ta6a faɗa
maki cewa banawa bane, mallakin mamansu ƙawata ne, Ni a lokacin dana kammala karatu
ina neman aiki bansamu ba, Nayi ma daddy magana akan ya taimaka mini in buɗe Beauty
saloon nawa nakaina, amma sai yace min shi baida halin da zai Iya taimaka mani,
bayan ni nasan yana da arziƙin shi kawai baison bani ne kusan halin shi ɗaya da
mahboob in dai wurin maƙone ko mami fama take yi dashi, dawowar ku gidan nan ne ma
ya fara sakin hannunshi gudun kada ku gane halin shi,’ Aneelerh ta natsu tana
sauraranta.

Numfasawa zahra tayi kafin taci gaba da cewa”akwai wata rana da naje gidansu
ƙawartawa, muna zaune a falo muna fira akan yadda zamu buɗe beauty saloon da zamu
gudanar da kasuwancin su, har take ce min mommynta tana da kuɗi sai dai itama
maƙone da ita ba ta Iya fidda kuɗi ta bata hakanan idan ba abun da ya shafi
karatunta bane, amma da zata amince mana ko da bashine ta bamu idan muka samu kuɗi
tun da kusuwancin ana samu sosai indai mutun ya samu kar6uwa awurin mutane, sai na
zaro ido nace mata a’a ni bana so muci bashi muzo mu kasa biya, na faɗi hakanne
saboda sanin halin mahaifiyarta masifaffiyace bata da mutunci in dai akan kuɗin ta
ne, Aunty Aneeleh fatima ta matsa mini akan muje muyiwa mommynta magana tasan idan
na sanya baki zata bamu tallafin da zamu buɗe, saboda muna mutunci da ita, duk
cikin ƙawayen fatima tafi sakewa dani har idan nayi kwana biyu banzo gidan su ba
takan tambayi fatima ina ƙawarnan taki mai dimple da yake haka take kira na, sai
tace mata zata kira ni idan tana son ganina, Aunty aneelerh tsautsayi ne ya kai ni
ga amincewa da maganar fatima, muka kwasa muka je wurin mommynta, muka fada mata
dangane da beauty salon din da muke so za mu buɗe gashi bamu da kuɗi, matar nan
tayi dariya tace mana ai ba wani abu, ta ji daɗi da mu ka yi tunani mai kyau, ita
tana son mutun me burin ya nemi na kansa, don haka zata buɗe mana company da zamu
dinga gudanar da kasuwancin mu harma mu zuba ma’aikata acikin sa da zasu dinga taya
mu aiki, idan yaso zamu dinga raba riba da ita, a lokacin munyi mamakin jin zata
buɗe mana company mu da muke maganar buɗe ƙaramin beauty saloon, ni bansan da wata
manufa a ƙasa ba, Ni da fatima munyi murna muka dinga yi mata godiya da addu’o’i,
tun da ta buɗe mana companyn bata ta6a kar6ar ribar da muke rabawa ba, duk in muka
kai mata kasonta sai tace mana mu ruƙe a hannun mu zata nema yanzu bata buƙatar
kuɗi, Aunty Aneelerh tun muna tara mata kuɗin har dai fatima tace min mu kashe
kudin ai mommynta bata buƙatarsu shiyasa bata kar6a ba, in yaso daga baya in muka
tara wasu kuɗin sai mu biyata, zuciya ta ɗebeni muka haɗu ni da fatima mu ka kashe
kuɗin, acikin su na cika da nawa kuɗin na sayi mota, Na canza wayata na sayi iphone
15, wayar da kika ga ina ruƙewa a hannuna, Na ciri dubu ɗari uku naba ummin mu nace
gashi nan tasa mun albarka kasuwanci yayi kyau, ummi taji daɗin kuɗin nan, dama
tana buƙatarsu daddy baya bata kuɗin da zatayi hidindimu dasu, duk nice fa nake
taimaka masu idan na samu kudi, shi kawai ta 6angaren abinci ne yake yi mana
ƙoƙari, sai kuma kayan sallah idan tazo amma inba sallaba babu abunda daddy yake yi
mana, kudin shi sai dai muga wasu suna ci, acikin kuɗin naba mahboob dubu hamsin
shima yai ta yi mini godiya hada ƴar ƙwallar shi saboda daɗin da yaji....’ dakatawa
ta ɗanyi da yin maganar hawaye nabin fuskarta, tun kafin ta ƙarasa jikin Aneelerh
yai sanyi don tasan ƙarshen zancen bamai daɗi bane.

Jinjina kai zahra ta ɗanyi kafin ta daura da cewa”Aunty aneelerh saida na


tabbatar kuɗin sun ƙare tukunna hankalina Ya kwanta, sai kwanan nan da Hajiya
saratu ta kira awaya suna buƙatar ayi masu decoration da kitso da ƙunshi, lokacin
dana duba asusun mu, ba mu da isassun kuɗin da zamuyi order na kayan da za’ayi masu
amfani, dama dai ita hajiya falmata itace take yi mana hanyar da ake shigo mana
kayan adon daga dubai, muka zauna nida fatima mukayi shawara sai tace min zatayi ma
mom dinta magana, bayan sunyi magana da ita, sai ga fatima tazo wurin aikin mu
idanuwanta jawur dasu, hankalina atashe na tambayeta lafiya meya faru da ita, cikin
shessheƙar kuka tace min mominta tace idan har muna so tayi mana order din kaya mu
fara tura mata ribar da muka tara mata a hannun mu, tana buƙatar kuɗin da gaggawa,
tun anan fatima tace mata ai babu kudin nan mun kashe su, tsabar 6acin rai ta
zazzaga mata masifa tamkar ba ƴar ta ba, hada mari ta kwasa mata a fuska, ko
lokacin da tayi mini magana fuskarta da sahun yatsun hannun mahaifiyarta, Hankalina
ba ƙaramin tashi yai ba, saboda ni bansan inda zan samu kuɗi na biyata ba, daga ni
har fatiman bamu da kuɗin a hannun mu, Aunty Aneelerh nasan bamu kyauta ba tunda ba
kyauta ta bamu ba, amma muka ta6a mata kudinta bayan yarjejeniyace muka ƙulla da
ita akan duk in aka samu riba zamu raba kaso uku, matsalar da aka samu kuɗin data
bar mana a hannun mu taƙi kar6arsu har saida tsautsayi yasa muka ta6a su....”
fashewa tayi da kuka Aneelerh ta natsu tana dubanta.

“Nayi ƙoƙarin Na saida motata don na samu na biyata kuɗinta sai dai bansamu wanda
zai siya ba, Jiya ina kwance saman gado na gama shan kuka na sai ga kiran fatima
awaya, na ɗaga muka gaisa da ita, tace min mominta tana son Yin magana dani inzo in
same ta agida, hankalina ya dan tashi don tunda muƙe nuƙu nuƙu akan yadda zamu
biyata kudin bata ta6a yin maganar dani ba, tsakaninta ne da fatiman, nace mata
zuwa gobe zanzo gidan nasu, jiya ko bacci banyi ba, da sassafe na shirya babu wanda
ya san na fita daga gidan nan naja mota naje gidansu fatima babu kowa afalon gidan
saida mai aikin gidan ta fito daga kitchen muka gaisa take ce min ai hajiya ta faɗa
mata game da zuwana in shiga ɗaki tana jirana, da sauri na juya na nufi ɗakinta
gabana na faɗuwa abakin kofar ɗakin nayi mata sallama, muryarta ƙasa ƙasa tace min
wanene? nace mata zahra ce ƙawar fatima mai dimple, tace in shigo ciki.....”
dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana faman ƙyafƙyafta ƙwayar idanuwanta.

Cikin ƙagara da sonjin ƙarashen zancen Aneelerh tace”naji kinyi shiru? Me tace
maki ne”! Yawu zahra ta hadiya muryarta na ɗan rawa ta ɗaura da cewa”Ina shiga
ɗakin na same ta kwance saman gado daga ita sai ɗan undy shara shara ajikinta,
arude na juya zan fuce da sauri ta kira sunana zahra zonan, cak na tsaya ba tare
dana juya na dube ta ba, ta sauko daga saman gadon ta nufo inda nake a tsaye ta
tsaya daga bayana ta soma yi min magana .

Ya maganar kuɗina da zaku bani? Nayi magana da fatima tace min atare kuka kashe
kudin meyasa zahra? Ban ta6a tunanin za ku yi mini haka ba, Na yadda daku na damƙa
maku amana amma kuna nema kuyi mini wasa da dukiyata, ko dan ba ku san zafin nema
bane”? faɗa sosai tayi mini bansan lokacin dana fashe mata da kuka ba ina roƙonta
akan tayi hakuri nayi mata alƙawarin zan biyata kuɗin ta cikin satin nan, Aunty
Aneelerh ba zato ba tsammani naji ta sanya hannu ta ruƙo hannuna, ta juyo dani ta
rungumeni a ƙirjinta, ban ɗauka da wata manufa ba sai da naji tana matse ni a
kirjinta gabana yaci gaba da faɗuwa, cikin dabara ta miƙa hannu ta bayana ta datse
ƙofar ɗakinta da jamlock, ba tare da sanina ba....” ganin yadda Aneelerh ta zaro
ido waje yasa zahra ta dakata da yin maganar la66anta na kerma.

Aneelerh tace”zahra ke nake sauraro uban me tayi maki” a kausashe Aneeleeh ta


furta mata hakan, cikin ruɗu zahra tace”nayi ƙokarin raba jikina da nata amma saita
ƙara tighting dina, ta zame mayafin dake akaina, ta sanya hannu tana shafa sumar
kaina cikin raɗa take furta min”meyasa nake yi mata kuka? Ko dan saboda tayi mini
faɗa akan kuɗinta ne, muryata na kerma nace mata ta yi haƙuri zan biyata kudinta,
tace min in kwantar da hankalina ai ba dole saida kuɗi zan Iya biyanta ba, A jikina
ma ina da abun da suka fi kuɗi daraja, idan na amince na bata haɗin kai zata yafe
mana bashin harma ta yi mana order na kayan decoration din da muke so, cikin rashin
fahimtar maganarta nace mata ni ban gane me kike nufi ba? Menene yafi kuɗi daraja a
jikina? Kuma wani irin hadin kai kikeso in baki”? Har lokacin bata raba ni da
jikinta ba, saima nishi da naji tana saki, tace min tana buƙatata jikina kawai
takeso, zatayi amfani dani.

Saboda yarda da nayi da matar saina dauka wasa take yi mini, Cikin sanyin murya
nace mata mommy amma dai zolayata kikeyi ko”? Na fada ina kokarin raba jikina daga
nata saidai taƙi bari inyi hakan, kamar zata maidani cikinta.

Babu alamun wasa a kalamanta tace min” Zahra na ta6a yi miki wasa irin wannan?
Nace mata a’a, tace min toh dagaske take, dama ta jima tana kwaɗayin son kasancewa
tare dani bata samu damar yin hakan ba don ta lura kamun kaine dani kuma ni ba ƴar
harka bace, shiyasa ta yi dabarar amincewa da buƙatarmu ta buɗe mata company kuma
taƙi kar6ar kuɗin ribarta dake a hannun mu, Ashe maƙarƙashiya ta shirya mini saboda
tasan zamu iya ta6a kuɗin, Ni ban ta6a tunanin matar zatayi mini haka ba.

Aunty Aneelerh data faɗamin hakan tsigar jikina ta tashi, na rasa uwar ubana,
na soma kiciniyar ƙwace kaina daga ruƙon da tayi min ina fadin ni ki sake ni in
tafi gida, wlh kin ban mamaki na dauke ki tamkar mahaifiyata saboda ƙaunar dake a
tsakanina da fatima ashe nayi babban kuskure, Ni bazan ta6a baki haɗin kai don mu
aikata sa6on Allah ba, kema inayi maki fatan Allah ya shiryeki,’ sai da nasha
wahalar bangajeta, da gudu na damƙi ƙofa zan buɗe naji ta a garƙame kafin in zare
jamlock din Naji ta damƙeni ta wurgar dani saman gado tana fadin”baki isa ki
kubcemun ba zahra, dama nasan zakiyi min taurin kai shiyasa na biyo maki ta wannan
hanyar, wlh idan har kika bijirema buƙatata zan saki dole ki biyani kuɗina a yau
ɗin nan idan ba haka ba zan damƙa ku hannun lawyer dina, sannan zan rufe
companynku,”

Ina kuka nace mata naji ta bani lokacin da take son kuɗinta In sha Allah zan
biyata amma ni kada ta kuskura tace zata ta6a jikina, ta jira taga idan ban biyata
ba sai ta yi mini duk abun da ta ga dama, tana faman sakin shu’umin murmushi tace
min bataso inyi danasani, don tasan banda arziƙin da zan Iya biyanta, tasan wanene
mahaifina karen ƴan siyasane sai yayi masu wahala suke watsa mashi hatsin da zai
samu ya tsastsaga harma ya ɗan mana, raina ya 6acin sosai jin irin wulaƙancin da
take yi mini nasan nina ja ma kaina, dama ance kwaɗayi mabuɗin wahala, sannan idan
har kace zaka dogara da wani kana tare da wahala, sai dai ba yadda zanyi ne tun
farko da nasan wacece ita wlh daban amince ta buɗe mana company ba, daƙyar na samu
ta ƙyale ni abisa sharadin gobe da safe ƙarfe 7 tana jiran alert na kuɗinta, wlh
idan daddy yaji maganar nan sai ya kusa kasheni, ni bansan ya zanyi ba”

Zuciyar Aneelerh tayi matuƙar karaya, tayi mamakin Hajiyarsu zahra me halin
bunsuranci.

“har nawa ne kudin”?


Zahra na matsar ƙwalla tace”kusan fa miliyan shidda muka raba ni da fatima”

Zaro ido waje Aneelerh tayi tana mai jinjina kai tace”tabɗijancan, ashe da rabon
zahra ki kwana a cell, don kuwa babu abunda zai hanaki zuwa gidan Yari, Ni har na
hangoki cikin uniform dinsu” fashewa zahra tayi da kuka jin abunda aneeelerh take
faɗi.

Cikin shessheƙar kuka tace”Aunty aneelerh kidaina banso, bakisan halin da nake
aciki bane shiyasa kike zolayata, wlh saboda tashin hankalin da nake aciki tun safe
ko ruwa ban sha ba”

Tsananin tausayinta ne Ya kama


Aneelerh, idanuwanta sunyi jawur dasu kamar an watsa mata barkono, muryarta na
rawa tace”Aunty aneelerh ko zaki taimaka mini mu je mu nemo wanda zai sayi motata
da wayata kafin lokacin Ya cika” Jikinta na kerma tayi magana.
“Lokacin da ku ka yi yarjejeniyar buɗe companyn kinyi shawara da wani? Ina nufin
Uncle ko Ummi akwai wanda kika faɗa mawa”?!

Girgiza kai zahra tayi”Ni ban faɗa ma kowa ba, babu wanda ya sani, kawai dai na
faɗa masu na samu aiki a company, sun tayani murna kuma sun yi min fatan akhairi,
ummi ma ta ta6a tambayana ya akai companyn yaci sunana? Kamar nawa, sai nace mata
banawa bane, Yarinyar me companyn ce takwarata shiyasa aka sanya mashi Sunan Zahra
world of beauty”

Jinjina kai Aneelerh tayi”Kinyi babban kuskure Zahra, Matar nan Tayi maki wayau,
Nafi ganin laifin ki, ke fa da kanki kikace kinsan halinta masifaffiyace amma ahaka
kika biyewa fatima ku ka kashe kuɗi har miliyan shidda bayan kinsan ba gadon ɗan
iya bane, Idan ita yarinyar bata da wayau ai ke da hankalin ki, kuma ita dukiyar
mahaifiyarta ce, ke kuma fa? Baki haɗa komai da ita ba,Yanzu ai gashinan taja maki
bala’e, ko dai ki biyata kuɗinta ko ta maka ki kotu, Ni dai shawarar da zan baki
shine kije ki yi mata abun da take so!” hankali akwance aneeelerh tayi mata magana,
tayi tsammanin zata taimaka mata ne donsu nemi mafita amma sai taji tana fadin
hakan, zuciyarta ta karaya sosai, har batasan sa’adda ta fashe da kuka ba, ta sauko
daga saman kujerar ta zube saman gwiwowinta Cikin shessheƙar kuka take fadin”Na
shiga uku aunty aneelerh, amma dai wasa kikeyi mini ko? Ni nasan bazaki ta6a bani
shawarar in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, wallahi ina tsoron Allah, Ina
tsoron ranar da zan koma gare shi”

Ɗaure mata fuska Aneelerh tayi”Idan har baki amince mata ba zahra tayaya kike
tunanin zaki Iya biyanta? Kinsan halin mahaifinki bazai ta6a biya maki kudin nan
ba, Ummi kuma bata da kuɗi, zahra ƙwara ki bata haɗin kai, nayi maki alƙawarin babu
wanda zai ji abunda ya faru, daga ni sai ke, kinga tace zata ƙara maku wasu kudin
harma tasa ayi maku order na kayan da zaku yi amfani da su daga dubai, wallahi
zahra ki amince mata idan ma don baki saba bane zaki saba a Hankali, Allah kuma
gafurirrahim ne, zaki iya tuba ko daga baya ne in ta gama amfani dake”

Zazzare ido waje zahra tayi yayin da take kallon Aneelerh, cikin matsanancin
tashin hankali da ruɗani, Muryarta na rawa ta furta”Aunty Aneelerh dagaske kike? In
bata hadin kai”? Murmushi Aneelerh ta sakar mata hadi da ɗaga mata gira alamar eh,
girgiza kai zahra tayi idanuwanta cike tab da ƙwalla tace”wallahi aunty Aneelerh
bazan Iyaba, koda kuwa duniya zata mallaka mini don in biya mata buƙatarta bazan
ta6a amincewa ba, da in sa6ama Allah na ƙwammace in rasa komai dana mallaka don In
biyata kuɗin ta, ina tsoron Allah kuma ina jin tsoron ranar da zan koma gare shi,
yanzu idan na mutu kafin in tuba fa”? ta faɗa yayin da hawaye ke cigaba da wanke
fuskarta, kallon da take bin Aneelerh da shi, kallone na mamaki da al’ajabin
shawarar da ta bata, har ta fara kokwanton Anya kuwa Aneelerh ce wannan? Ko dai
Aljanu sun shige ta ne?

Gyaɗa kai Zahra tayi cikin rauni na murya ta furta “Aunty Aneelerh ki daina wannan
maganar kina rikita mini tunanina, idan har ba zaki taimaka mini mu nemi mafita ba
bai kamata kina tunzurani akan in aikata zunubi mai girma irin wannan ba, har kin
sa nafara kokwanto akanki duk da nasan wacece Auntyna”

Ta6e baki aneelerh tayi haɗi da watsa hannayenta tace” Zahra, we don’t have any
other solution besides this, ina ƙara jaddada maki, ki hanzarta zuwa ki biya mata
buƙatarta, idan ba haka ba zata kai ƙarar ki kotune sannan ta rufe maku companyn
ku, amma idan kika bata hadin kai, kinga zaki ci riba biyu da farko zata yafe maki
bashin da take bin ki, na biyu kuma zata yi maku order na kayan amfani daga dubai,
wannan fa babbar dama ce agare ki!!!” da sauti mai ƙarfi ta ƙarasa maganar,
fuskarta babu annuri, ta yunƙura ta miƙe tsaye, Zahra ta saki baki tana kallon ta
da rinannun idanuwanta.
“Ni kinga tafiyata, Idan kin canza ra’ayin ki kina iya zuwa ɗaki ki same Ni, zan
taimaka maki da mayukan da zaki gyara mata jikin ki” ta hankaɗe kafaɗa ta juya ta
nufi kofar fucewa daga ɗakin.
Kamar sakarya haka zahra tabi bayan Aneelerh da kallo har ta 6ace ma ganinta,
hannu biyu ta ɗaura saman kanta, tana faman ambaton kalmar Inna lillahi wa’inna
ilaihirraji”un”

Tsantsar tashin hankaline akan fuskarta, wani irin azababben zazza6ine ya


lullu6eta, saman floor ta kwanta, idanuwanta na fuskarta ceilling, yau Aunty
aneelerh ta bata mamaki, ta karya mata zuciya, duk da har yanzu ta kasa yarda da
abunda zuciyarta ke faɗa mata dangane da ita, batasan ya zatayi ba? Don ita har ga
Allah bata jin zata amince da shawarar Aneelerh ta ƙwammace ta tattara duk wani abu
data mallaka taje ta biyata kuɗinta zaifi mata kwanciyar hankali akan ta sa6a ma
Allah, tazo tana danasani mara amfani, babban abunda take jima takaici asarar da
zatayi na zuwa gidan Obinna, On friday na satin da suke ciki Za’ayi shagalin
birthday na babansu, already sun fidda masu anko, decoration ne da kitso suke
buƙatar ayi masu jibi, tasan tarasa wannan damar, Hajiya falmata baza ta bari ta
cigaba da yin aiki a companynsu ba muddin bata amince da buƙatarta ba, gashi ita
bata da komai, dole ta haƙura tama riga da ta fidda rai, shawarwari ta shiga
yankewa da zuciyarta, a karshe ta yanke shawarar Zata yi magana da mahboob watakil
ko cikin abokanan sa asamu wanda zai sayi motarta da wayarta, da wannan tunanin
baccin wahala ya ɗauke ta, babu ci babu sha tun safe baiwar Allah.

*DAULAR OBIE ESTATE*

Zayn ne kwance saman shimfiɗeɗen gadonsu, daga shi sai short a jikinshi, tun da
suka dawo daga office yake ta sharar baccin shi kamar matacce, toilet door din
ɗakin aka buɗe Zaid ne Ya fito waist dinshi ɗaure da towel, jikin shi da alamun
danshin ruwan wankan da yayo, tun kafin ya ƙarasa gaban gadon ya soma ambaton sunan
zayn.

“Bro, get up, I want to have an important talk with you, please,” ya faɗa ayayin
da yake ƙokarin zama gefen gadon, hannu yakai yana bubbuga ƙafarshi”pls ka tashi
zayn, baccin ya isa haka sai kace mai sleeping sickness, tun da muka dawo daga
office kake ta sharar bacci ko dai ka sha ƙwaya ne”? Ya faɗa yana cunkulin kafar
zayn da mugunta, dogon tsoki Zayn yaja, yana faman yamutsa fuska ya furta”

“Zain, I don’t want to be stressed, please, let me rest, I’m tired,”

Rai a6ace yai maganar ba tare daya buɗe idanuwanshi ba.


Zain na murmushi yace”Haba babyn mommy, you should wake up, you’ve had enough
sleep. I know it’s not just work tiredness that made you sleep, because your
secretary told me that you’re not doing anything other than gathering girls in your
office. Ko nayi ƙarya?” He spoke jokingly, looking at Zayn’s face, tamkar bai ji me
yace ba, Ya haɗe fuska babu annuri.

“Dole kayi shiru, tun da baka da abun cewa, adai dinga jin tsoron Allah,
taƙamarka kana da kyan fasali shiyasa kake maƙure Ƴan matasan mata a office kana
zare masu ido, don kasan dole suyi maka biyayya tunda suna aiki a ƙarƙashin
ikon ......” bai ƙarasa maganar ba, sakamakon zaburar da zayn yai ya miƙe tare da
damƙar pillow, ya buga mashi akai, Ya janyo wani pillow ya dinga bugunshi ta
ko’ina, Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yake fadin”zaid ka takura ma rayuwata,
kai ma ka sani wallahi nafi ƙarfin in maƙure ƴa’ƴan mutane a office, Ni bana yima
mace dole in ba ita ta nuna tana buƙatana ba, kai ne dai bunsuru da baka Iya gani
ka kauda idonka, Ni da aji na matane suke kawo kansu wurina bani nake kiran su ba”
ya faɗa yana hararansa”shashasha kawai mai kama da daddy” Ya ƙare maganar Yana haki
kamar wanda yasha gudu, idanuwanshi sun kaɗa jawur saboda baccin da bai ishe shi
ba.

“Zayn? Ni ne bunsuru? Kuma mai kama da daddy? Kana nufin shima daddyn mu
bunsurun ne”? Fuskarshi a ɗaure yayi maganar.
Ɗaga mashi gira zayn yai”ƙarya nayi ne? Babyn daddy, Nifa ba ina nufin bunzuru na
dabba ba, No, just ina kwantanta Namiji mai bin mata ne da sunan bunsuru, kasan
shima bunsurun haka ɗabi’unsa suke, duk inda yaga mace sai ya bita, shiko namijin
da mata suke kawo kansu gare shi bazai yiwu ba a kirashi da bunsuru, sannan Ni
bance hada daddy ba, kai kaɗai na ce” a fusace zaid yace”kada ka manta, dani dakai
bamu da banbanci ko a murya, idan ina kama da daddy then you look like him too, and
you’re a he-goat as well.

gwalo zayn yai mashi”Oho dai, ai kwanan nan zanje ayi mini surgery amaida mun
kamannin fuskata irin na mommyna, donni bana son abunda zai haɗa ni da ku” da
zolaya yake yi mashi magana, amma shi zaid sai yake ganin kamar baison shi ne,
ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa zayn saurin cewa” wasa fa nake yi maka, kaima ka
sani ni da kai abu ɗayane, na fadi hakanne don in 6ata maka rai kamar yarda ka
tada ni daga bacci”
Yamutsa fuska Zaid Yai”naji, yanzu dai mu ajiye wannan gefe, Ya maganar zuwanmu
america”? Yai tambayar yana duban fuskar Zayn
“Bamu da isassun kuɗi a account, Ni dai na hakura, ƙwara kaima ka haƙura kawai
muyi zaman mu a ƙasar mu ta gado,”
Girgiza kai Zaid yai”bazai yiwuwa ba, zayn bakasan yadda naci burin haɗuwa da
Ummi ba, Jiya har mafarkin ta nayi, na kasa gogeta acikin zuciyata”

Ta6e baki zayn yai”faɗamin acikin mafarkin me kuka aikata”


“Bamu aikata komai ba, kawai dai mun hadu a jabi lake mall, har nake tambayarta
yaushe ta shigo ƙasar? Kafin ta bani amsa ka katse mini bacci ka tada ni kana fadin
lokacin sallar asuba yayi”

Murmushi Zayn ya sakar mashi”kace nayi maka buƙulu, wata’kil da har kiss ta manna
maka da hug”
Harara zaid ya jefa mashi atakure yace”ya zamuyi ni dai? Ko dai mu kar6i Atm din
daddy daya ce zai bamu”? da sauri zayn ya girgiza kai Yana fadin”No, ba zamu kar6a
ba” zaid yace”why? Ni bansan meyasa baka son mu kar6i Atm dinsa ba, maƙudan kuɗi ne
fa zayn zasu ishe mu muje duk inda muke so, wai kai kafi son muyita wahalar jiran
salary”?

“Eh, ƙwara mu jira salary, akan mu kar6i kudin da ba mu san inda aka same su ba,
ka yi amfani da hankalin ka mana, ina daddy yake da arziƙin tara waɗannan millions
of dollars din? Abun da baka sani ba, Dana zauna na lissafa dukiyar mommy ko rabin
tashi bata kai ba, ita da ta gaji arziƙin kenan, da farko nayi tsammanin ko kuɗinta
ne ta bashi ajiya amma daga bisani na zauna nayi nazari sosai na gane cewa kuɗin
nan fa bana mommy bane, kuma ba albashin daddy bane suka tara mashi su, Ni tsorona
kada mu je mu kar6i kudin sai mun gama sharholiyarmu asiri ya tonu agano daddynmu
yana aikata wani abun, duk da ina kyautata mashi zato, amma gaskiya ni zaid ban
yarda da kuɗin nan ba, bada guminsa ya tara su ba, akwai dai wani abun a ƙasa”

Damuwace ƙarara akan fuskar zaid sam babu alamun Ya fahimci zancen twin bro
dinsa.

“Na lura zayn baka son daddy, baka ƙaunar shi, kafi son mommy, sai kace bashi
bane ya haife ka, na tabbata da ace mommyne ta baka atm dinta jiki na rawa zaka
kar6a ka yi amfani da kuɗin amma da yake na daddy ne shine kake neman yi mashi
ƙazafi, wallahi kaji tsoron Allah zayn, mahaifin mu babu abunda yake aikatawa da
guminsa Ya tara kuɗin shi, wata’kil dama can me arzikine Ya dai 6oyene don baison
agani, amma nidai ina kyautata mashi zato, kuma atm daya bamu don yaga muna buƙara
kuɗine Yana so ne Ya faranta mana” Zayn ya natsu yana kallon dan uwan nashi ya
haƙiƙance Yana yi mashi magana, sai da yakai ƙarshen Aya tukunna zayn yace”baka
amfani da ƙwaƙwalwa, ta inda muka banbanta kenan, Zaid ka faɗa min wani ubane zai
ɗauki maƙudan kuɗi irin wadannan yaba ƴa’ƴanshi don suyi sharholiya? Ba tare daya
tambayi me zasu yi da kuɗin ba? uba na gari bazai ta6a aikata hakan ba, Ni bani ke
bansan daddy ba, shine baison mu zaid! Saboda tun da muke dashi bai ta6a zaunar
damu a matsayin shi na mahaifinmu yayi mana nasiha akan rayuwar duniya ba, ko
lahirarmu, komai mu ka yi dai dai ne a wurin shi, Mommy ce kaɗai take tsawatar mana
idan mu ka yi ba dai dai ba......”

Tun da Zayn ya fara magana muryarshi a kausashe, idanuwanshi sun kaɗa sun ciko da
ƙwalla, zaid dake sauraron shi, Yayi shiru yana kallon shi, Jikin shi ya fara yin
sanyi, dakatawa ya ɗanyi yana faman fitar da huci, kafin ya ɗaura da cewa”idan har
dagaske kuɗin shi ne meyasa be yi amfani da su ya gina mana gida na kanmu ba? bayan
yasan duk irin gorin da ake yi mashi, hmmm kawai baison asan Yana da kudin ne don
yasan za’a tuhume shi ina ya same su, shine kawai,” shiru su kayi ɗakin Yayi tsit
na ɗan wani lokaci,

“Kaina harya fara ciwo, Inaso in kwanta In huta” Zaid ne ya ambaci hakan tare da
miƙewa Ya nufi closet din Kayansu dake acan cikin ɗakin,
Kwantawa zayn yai saman mattress yayin da idanuwanshi suke fuskantar ceilling,
abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yake yi ba, Yana matuƙar jin ɗacin irin rayuwar da
mahaifinsu yake yi.

*Hajiya Saratu ❤*

A tsaye take gaban mirror, jikinta sanye da Jallabiya, babu mayafi akanta, hakan ya
bayyana kitson zanan dake akanta, hannunta ruƙe da wayarta ta karata a kunnanta,
fuskarta da fara’a, ga dukkan alamu magana take yi da wani awaya.

“Nayi mamakin ganin kiranki, Allah dai yasa lafiya, don nasan hakanan baki nema
na, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba”

On the other hand matar da suke yin waya ta soma magana, Daga jin muyarta babbar
macace mai ji da qasaita.

“Oh, saboda kada na fara yi maki ƙorafin baki kirana shine kika rigani yin
magana”?

Hajiya saratu na dariya tace”wallahi ba haka bane Hajiyata, abubuwane suka yi min
yawa, amma duk da haka ai ina ƙoƙarin tura maki saƙon barka da juma’a, ke dai ce
baki nemana, amma nayi maki uziri saboda hidindimun al’umma da kuke fama da su,
nasan sune suka sanyaki busy”

“Hakane, amma kada ki damu, dama dalilin dayasa na kira ki, game da zuwanmu
gidane, Naga saƙon ankon da kika tura mini nagode, so abunda nikeson kiyi mini,
Inaso ki fada min me baba yafi so”? murmushi saratu tasaki, Har cikin ranta taji
dadin tambayar da tayi mata.

“Gift ne zaki shirya mashi na birthday dinshi”?

“Eh, na tambayi yayanki akan ya faɗa min me yafi so, kinsan halin shi, cewa yai
shi baisani ba, Duk abunda yayi mini in siya mashi, Ni kuma nafi son abun zai burge
shi sosai”

Dariya hajiya saratu tayi tana fadin” Gaskiya baba ni kaina bazan Iya cewa ga
abunda yafi so ba, amma kwanakin baya naji yana magana da abokinshi akan yana son
suturar su na al’adar inyamurai, tun lokacin dai banji sun ƙara magana ba, kuma ba
akawo kayan ba, idan har kika shirya mashi su a matsayin gift dinsa, Nasan zai yi
farin ciki sosai kuma zaiyi mamaki”

“Okey, Send me his measurements through WhatsApp, and please don’t let anyone
know. I want to surprise him.” ta amsa mata da toh nima agaida mun da yayan nawa,
ko na kira shi sai yaga dama yake ɗagawa, Ina nan ina jiran shi zamu haɗu ne”
sautin dariyar hajiyarne ya cika kunnanta da ba’a tace”Ai kin fi kowa sanin yayan
naki, sai dai ki ba wani labari” Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi
sallama, Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin zama gefen gadonta, Muryar Hajjaty ta
katse mata hanzarinta, tayi mamakin jin sallamarta, don koda gigin wasa bata ta6a
tako ƙafarta zuwa ɗakinta ba, Jim ta ɗanyi kafin ta furta”Wacece” ta fada tamkar
bata gane me magana ba”

“Hajjaty ce” jinjina kai Hajiya saratu tayi tuni mood din fuskarta Ya canza, jim
ta ɗanyi kafin tace”zaki Iya shigowa”

A hankali ta turo ƙofa ta shigo ɗakin, tun daga ƙasa hajiya saratu ta soma binta
da wani matsiyacin kallo, pakistan ne ajikinta farare, ta ca6a uban ado, sai dai
babu ƙamshin turaren nan, sai ka matsa kusa tukunna zaka Iya jin shi, hannunta biyu
ruƙe da wooden tray, kayan abincine shaƙe asaman shi.

Lamarin ya ɗaurewa Hajiya saratu kai, tayi sototo tana kallon ta


Muryarta na ɗan rawa ta furta”Ina wuni” yamutsa fuska tai”da ban wani ba kin
ganni, shin wai ma me ya akawo ki room dina? Makuwa ki kayi ne”? Fuska adaure ta
mata maganar.
Duk tasha jinin jikinta, adabarbarce ta furfa”am..umm...dama abincine na kawo
maki, Ni na girka shi da kaina abincin ƙasar mu ne...” daƙyar ta ƙare maganar a
tsananin tsoroce.

Murmushin yaƙe hajiya saratu ta sakar mata”dama ke ce kike kawo min abinci? Ina
masu aikin gidan ne? Ko sunyi yaji ne”

“Suna a kitchen suna aiki, kawai nayi ra’ayin in kawo maki ne da kaina, nasan
zaki ji daɗin girkin tun da baki saba cin kalar shi ba” hankalin ba akwance ba take
yin maganar,
Ruƙe ha6a hajiya saratu tayi tana faman jinjina kai tace”To fa, sabon salo, tanan
kika biyo? An gaya maki bani da hankali ne da zanci abincin da kika girka da hannun
ki? Wato bokan ki ya haɗo ki da maganin barbaɗe kin zuba min aciki shine ki kawo
mun don inci in mutu saboda kinsan abinci ne lago na ko”?

Hankalin Hajjaty ba ƙaramin tashi yai ba, cikin sanyin murya tace”Allah shine
shaidata, tun da nake arayuwata ban ta6a takawa naje wurin boka ba, kuma ni banzo
da niyar in cutar dake ba, abincine kawai na kawo maki, dan Allah ki kar6a ki
ci......” Kafin ta ƙarasa maganar, Hajiya saratu ta dakata mata tsawar data
firgitar da ita, jikinta ya kama kakarwa, nuna mata hanyar fita tayi daga
ɗakin”Fuce min daga ɗaki tunkafin Inyi ƙwallo da tray din hannun ki, Ƴar rainin
wayau, wallahi na fi ƙarfinki ba za ki ta6a cin galaba akaina ba, tunda can baki
ta6a girka abinci kin kawo min don inci ba sai yau da kika shirya kashe Ni”?

Tuni idanuwan Hajjaty sun cicciko tab da ƙwalla, cikin shessheƙar kuka tace”meyasa
kika tsaneni? Laifin me nayi maki? Duk cikin masu aikin gidan nan ni kaɗaice ke
bakiso, idan laifi nayi maki ki faɗa min sai in gyara”

A tsawace Hajiya saratu tace”wai ke baki da hankali Ne? Kin manta wacece ni acikin
gidan nan? Ko kin fara shaye shaye ne? Ni narasa gane wani tsautsayin ne ya kawo ki
cikin ɗakina, I don’t know where you get the nerve to talk to me face to face, ke
ga ta6ararra dallah fuce ki ban wuri”

Juyawa Hajjaty tayi da sauri ta fuce daga ɗakin, Kamar zatayi tuntu6e, gutun tsoki
Hajiya saratu taja tare da samun wuri ta zauna gefen gado, tana mai mamakin ƙarfin
hali irin na Hajjaty.

_~*✊💋BossLadiesWriters💋✊*~_
~The return of Benazir~

‫❤🤍❤سجن القدر‬

Bayan fitar Hajjaty daga ɗakin Hajiya saratu, zafafan hawaye ne su ka wanke
fuskarta, taji ɗacin maganganun da saratu ta faɗa mata, ita har ga Allah bada nufin
komai taje kai mata abincin ba, dama Pravin ne ya bata shawarar ta rinƙa kyautata
mata, wata’ƙil ta fara ƙaunarta, saboda ta faɗa mashi tana son su dinga shiri da
matarshi.

Kafin tabar ƙofar ɗakin sai da ta ajiye tray din ƙasa, ta share ƙwallar fuskarta,
tukunna ta ɗauka ta nufi ɗakin twins da niyar ta kai masu abincin wata’kil su ci.

A lokacin Zayn yana zaune saman gado Ya tasa laptop dinsa agaba Yana operating
dinta, zaid kuma Yana a kwance gefenshi hannun shi ruƙe da Wayar shi Yana daddanna
ta.

Sallamar hajjaty ce ta janyo hankulan su ga duban ƙofar ɗakin.

Zayn tamkar bai ji ba yai shiru yaƙi amsawa sai zaid Ne ya amsa mata tare da
bata Iznin shigowa ciki, A hankali ta shigo da tray muryarta asanyaya tace”barkan
ku da hutawa, fatan kun wuni lafiya” da fara’a akan fuskar zaid ya ce”lafiya lou
auntyn mu, yau ke ce da kan ki ki ka zo kawo mana abinci”? Ya yi maganar tare da
ajiye wayar shi ya sauko daga saman gadon Ya nufe ta, zayn ko kallo bata ishe shi
ba, baiwar Allah taji daɗin sakar fuska da zaid ya yi har cikin ranta taji ta ƙara
ƙaunar shi.

“Abincin ƙasar mu ne, ni na girka shi da kaina, na kawo maku ne don ku ɗanɗana”
hannu biyu zaid yasa ya kar6i tray din Daga hannunta yana fadin”gaskiya kina ji da
ƴa’ƴan nan naki, wallahi munji daɗi, kamar kinsan kuwa yunwa muke ji, Yanzu nake
shirin kira akawo mana abinci mu ci”

Asaman table ya ɗaura tray din, sai faman sakin murmushi take Yi yayin da take
kallon fuskar zaid, buɗe warmer ya fara yi, ƙamshin Abincin ya daki hancinsa,
Jinjina kai yai tare da ɗago da ido Ya kalle ta”Aunty, Ya sunan wannan haɗin”?

“Chicken tikka masala” ta faɗa still da murmushi kan face dinta.

“Daga jin ƙamshin abincin zai yi daɗi, balle ma daya kasance hannu mai albarkane
Ya girka sa” ya fada yana nade hannun rigarsa.

“Zaid! Kada ka kuskura ka ci abincin nan! Kai baka da hankaline”? Ras taji
gabanta ya fadi jin abun da zayn yace.
Fuskar zaid a ɗaure ya dube shi”kaga bana son zancen banza, babu ruwanka dani,
Kaja baki kayi shiru idan bazaka ci ba”

Ya ƙare maganar tare da maida dubansa ga hajjaty “mun gode Aunty, Idan nagama cin
abincin zaki ji feed back dina” jiki asanyaye ta amsa mashi da toh, da sauri ta
fuce daga ɗakin tana faman sauke ajiyar zuciya.

Ƙamshin Abincin da Zaid ke ci duk Ya cika mashi hanci da maƙoshi, dauriya ce


kawai Yake yi, Yana danna laptop Haɗi da satar kallon Zaid, da gangan yake cuko
spoon da abincin Yana turawa abaki, hada sambatun shi”wannan abinci kamar a aljanna
aka dafa shi? Kai ka ji wani ɗanɗano mai daɗi, gaskiya duk wanda baici abincin nan
ba an barshi a baya” Harara Zayn ya watsa mashi sam bai lura ba, saboda Ya bashi
Baya.

Ajiye spoon din ya yi cikin abincin, ya tsiyaya lemu mai sanyi acikin glass, Ya
ɗauka Yasha rabi, Ya ajiye.

“bari na ɗan shiga toilet” ya faɗa hadi da miƙewa da sauri Ya nufi toilet door ya
shige, shigar shi ke da wuya Zayn ya janye laptop dinsa, cikin sanɗa Ya rarrafa
saman mattress din zuwa gaban table din, Yana faman yamutsa fuska Ya ɗauki spoon Ya
zura a plate din abincin aranshi yana fadin ba lallai ma abincin yai daɗi ba,
mutuminka tun da yayi one spoon abaki, Tsabar daɗi kunnanshi har motsi suke yi,
Yana ci yana satar kallon ƙofar toilet gudun kada Zaid Ya riske shi Yana cin
abincin Hajjaty, a ƙarshe Ya ajiye spoon din Ya duma hannu ya ɗauko cinyar kaza
Yadinga cizga Yana ci, Kusan Rabin abincin plate din ya cinye, ya ɗauki lemu Ya
kur6a, Jin motsin za’a buɗe ƙofar toilet Yasa shi yin saurin sauke glass din lemun
saman table, ko hannun shi bai goge ba, Da sauri Ya koma can saman gadon Ya jingina
bayanshi jikin headboard ya ɗauki laptop dinsa Ya cigaba da operating dinta.

Fitowa zaid Yai daga toilet, Yana faman yarfa hannun shi, Satar kallon fuskar
zayn yayi, mutumin Ya haɗe rai babu annuri, Sai dai Ya manta bai goge bakinshi ba,
yayi dama dama da maiƙon abincin da ya ci.

Ƙayataccen murmushi zaid ya saki aranshi ya ayyana”babyn mommy ai nasan zaka


aika, shiyasa na shiga toilet don na baka damar ka ci, ɗan rainin wayau anaso ana
kaiwa kasuwa” Ya faɗa Yana zama bakin gadon, da zolaya yace”Zayn ya akai naga
abincin dana rage an ci shi”?

Muryar zayn ba wasa yace”ka tambayi wanda kaba ajiya, Ni meye ruwana aciki”?
Gumtse dariya Zaid yai”amma dai da kunya wallahi, Ni dai nasan babu 6era agidan
nan” rai a6ace zayn yace”ban san iya shege zaid, Uban waye 6eran”?

“Ai ni ban kama suna ba, kawai nayi maganata ne” dogon tsoki Zayn yaja yana faman
hura hanci, Aranshi ya ayyana Ina ma zaid Ya rage abincin da kuwa ya cinye shi
duka, don ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba.

*SIR MUBARAK🤍*

A Hankali Yake tafiya Yana tunkarar ɗakin Dr. Jazz, Daga shi sai short A jikin shi
da singlet, Tura ƙofar Yayi baiga kowa a ɗakin Ba, shiga Ciki Yai Yana bin ko’ina
da Kallo zanin gadonshi a hargitse Takalman shi Yashe saman floor, tunani ya shiga
yi aranshi ko ina ya shiga? Ko dai yana a toilet ne Ko ya shiga Garden, Yanke
shawarar zuwa garden ɗin ya yi don Ya dubo shi, Ahanzar ce Ya juya da niyar ya fuce
kwatsam Muryar Jazz ta katse mashi hanzarin shi.

“Oh tsayawa za ka yi Kana kallonta? Babu abun da zaka Iya yi mata? Sai kace ba
ka san Hanyar da zaka kashe ta ba idan haukanta Ya motsa”! wani irin bugu zuciyar
Sir Mubarak Tayi Jin Kalmar Kisa, A firgice ya juya baya Yana bin toilet door ɗin
ɗakin da kallo, don Ya fahimci acikin toilet yake Yin wayar, Cikin tafiyar sanɗa
Sir Mubarak Ya nufi ƙofar toilet Ɗin Ya kanga kunnan shi Yana sauraron shi.

“Ai ba dole Saina zo ba, Kaima zaka Iya sarrafata, Idan taƙiya Kawai ka bi Hanyar
da nace maka, ka kashe ta kowa Ya huta,” shiru Ya ɗanyi can kuma yaji yaci gaba da
cewa”ba yadda za’ai inzo, Ina tsoron asirina Ya toni, hmm bakasan halin da nake
aciki ba, ko jiya saida na kamo Hanya zanzo gidan, ganin ana bin motata yasa na
karya kwana na nufi asibiti, saboda raina ya bani akwai wanda ke bin diddigina dole
Inyi takatsantsan”

Hankalin Sir Mubarak Ba ƙaramin tashi yai ba, sai faman jinjina kanshi yake Yi,
Bai ta6a tsammanin Jazz Yana da wayau ba sai Yau, Har yasan Ana bibiyarshi wato
shine Ya canza Hanya, Hakan ya ƙara tabbatar mashi da zargin shi akanshi.

“What are you doing here, baby?”

Muryar Turai ce ta ratsa kunnanshi, Hatta dr Jazz dake a toilet, Sai da Ya ji


sautin muryar mutun a ɗakin shi, a yayin da yake atsaye gaban sink, wandon crazy
jeans ne da shirt a jikin shi, da sauri Yai rejecting call din Ya tura wayar cikin
aljihun wandon shi, Jikinshi Ya hau Yin kerma, Tsananin fargabane Ya kama shi, A
hankali Yake tafiya yana nufar ƙofar fita, Kafin fitowarshi da sauri Sir Mubarak
Yai wuff Ya nufi Turai dake kallonshi da mamaki akan face dinta ganin Yadda ya ke
yima Jazz la6e a ɗaki, Harta buɗe baki zata ƙara yin magana ya yi saurin sanya
faffaɗan tafin hannunsa Ya toshe mata bakinta, tare da janta zuwa wajen ɗakin.

Lokacin da Jazz ya fito daga toilet din zufa na bin fuskarshi, ya dubi ko’ina
baiga mutun ba, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, har wajen ɗakin Ya leƙa bai ga
kowa ba, Hakan yasa shi kokwanton wata’ƙil Kunnuwanshi ne suka jiyo mashi ba dai
dai ba, hankalinshi ya kwanta, komawa ya yi cikin ɗakin Ya kwanta saman gadonshi,
yayin da idanuwanshi ke fuskantar ceilling, ga dukkan alamu wani abu yake tunanowa
wanda yasa shi fitar da ƙwalla a idon shi.

A bedroom Sir mubarak Ya shigar da turai suna tsaye suna kallon juna, kallon tuhuma
take bin shi da shi.

“Nayi mamakin ganinka a ɗakin Jazz kana yi mashi la6e, meyasa”?

Fuskarshi a murtuke babu annuri yace”laifi ne don uba ya shiga ɗakin ɗanshi”?
Aruɗe tace”ba laifi bane, amma meyasa kake yi mashi la6e”? Shiru ya yi yana duban
fuskarta, A yadda suke atsaye suna fuskantar juna, Ko kafaɗarshi bata kai ba,
saboda ƙarantarta, doguwar rigace a jikinta ta shan iska, ta tufke blonde hair
dinta da ribbom.

“Ka tsare ni da ido kana kallona, Baka bani amsar Tambayata ba”! a ƙagare ta
faɗa, Ya rasa ya zaiyi ya kawar da hankalinta daga tambayar da take yi masa.

Dubara ce ta faɗo masa, da sauri Ya sanya Hannu biyu ya ruƙe waist dinta, sama ya
ɗaga ta kamar ɗiyar roba Ya kwantar da ita saman gadon shi Rumfa ya yi mata da
faffaɗan kirjin shi, tuni tasha jinin jikinta.

“Kin tsareni da tambaya ke ga mai ɗa ko? Ni da ke waye yafi wani iko da shi? Yawu
ta haɗiya muryarta na ɗan rawa ta furta”kai”

“Kinsan da hakan shine kike yi min tambayoyi kamar ƴar jarida”? Shiru tayi mashi
tana faman zazzare green eyes dinta.
“Jibarki ƴar mitsila dake kamar in matseki nake ji” dariya ce ta kubce mata,
natsuwa yai yana kallon fararen haƙoranta.

“Yanzu dai faɗamin me kike shiryawa a birthday din Baba? Ba za kiyi kitso da
ƙunshi ba”?

“Idan zaka kai ni inda za’ai min kitson da ƙunshin inaso, sai dai anko din da zasu
sanya nasan hajiya saratu bazata barni in shiga cikinsu ba ko da na siya” a
marairaice ta ƙare mashi maganar.

Jan hancin ta ya yi da hannun shi”Ina ruwanki da ita? Ai ba dole sai kin shiga
cikinsu ba, babban tarone fa za’ayi akwai manyan baƙi da zasu zo, kema zaki samu
ƙawaye acikin su”

Da shagwa6e ta furta”baby ba zaka gane ba, hajiya saratu bata son ganina, ita fa
haryan zu kallon ƴar aiki take Yi mini, hada faɗa min wai ba ata6a canzawa tuwo
suna, ni dai inajin fargabar ta disgani acikin su, ƙwara Inyi zamana acikin gida
zai fiye min kwanciyar hankali” daƙyar ta ƙare maganar ganin yadda ya tsare ta da
ido, kallon so da ƙauna ya ke yi mata.

“Meyasa kike kira na baby? Ko kunya bakya ji? Nayi maki kama da ƙaramin Yaro ne?”
fuskar shi a ɗaure yai mata maganar.
Kashe mashi ido ɗaya tayi”I call you baby because you’re like a baby to me, and I
still take care of you kuma ina feeding dinka” ɗan zaro mata ido ya yi da sauri ta
rufe baki tana faman zazzare mashi ido.

Da zolaya ya furta”raini ya fara shiga tsakanina dake, saboda ina tu6e kaya
agabanki ko”? Runtse mashi ido tayi tana faman tiƙar dariya.

Jinjina kanshi yai”ki saurare dakyau, daga yanzu idan saratu ta faɗa maki magana
ki dinga mayar mata da martani, ki daina nuna kina jin tsoronta shiyasa ta rainaki,
Kina jina ko”? Tana faman zumbura mashi pink lips dinta tace”ni bazan Iyaba, saboda
ta girmeni ko a shekaru kuma ƙanwarka ce,”

“Umarni nake baki ba shawara ba, kada na kuskura na ƙara ganin kin dawo gidan nan
kinayi min jan ido akan saratu tayi maki wani abu, idan ba haka ba zaki kar6i horo
mai tsanani daga gareni,” muryar shi a kausace yake yi mata maganar
Kama kunnanta ya yi da yatsan hannun shi”Idan kunne Ya tsira”? Da sauri ta ƙarasa
mashi karin maganar”Jiki Ya tsira My baby” murmushi yasaki tare da manna mata kiss
saman soft lips dinta.

*GIDAN ƊAN IYA*

Zahra ce zaune saman prayer mat, ta zumbula dogon Hijabi, fuskarta sharkaf da
hawaye, tun da ta kammala sallar Magrib bata motsa ba, hannunta ruƙe da cazba sai
faman janta take Yi, damuwar duniya ta isheta, tun ɗazu data farka daga bacci ta
kasa Yin wanka ko abinci bata ci ba, babu kuma wanda yai tunanin ya leƙo ta, tayi
trying kiran layin mahboob yaƙi picking call din, har yanzu bai leƙo cikin gidan
ba, ga lokaci yana ta tafiya gani take yi kamar ana ƙara gudun agogon ɗakinta,
hannayenta biyu ta ɗaga sama tana jera addu’o’i akan Allah Ya kawo mata mafita.

Muryar Aneelerh ce ta ratsa kunnanta”Yar uwata rabin raina, tun safe baki ci
komai ba, Ga abinci na kawo maki” Shafa tafin hannunta tayi saman fuskarta, Rai
amatuƙar 6ace ta yunƙura ta mike haɗi da fuskantar Aneelerh, dake tunkarota,
hannunta ruƙe da madaidaicin tray, mai ɗauke da plate din shinkara da ƙaramar
warmer ta miya, tare da lemu mai sanyi.

Kafin ta ƙaraso zahra ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana”Aunty Aneeleeh


idan kin kawo abincin nan domin in ci ne to ki maida shi kitchen! Bana buƙata” a
faɗace ta furta.

“Haba zahra, kashe kanki ki ke so Ki yi ne? Tun safe baki ci komai ba, Ni kaɗai
na damu dake, dan Allah ki kar6a ki ci”

Harara zahra ta wurga mata cikin 6acin rai tace”Ai ni kingama zubda girmanki a
idona, tun da har kika iya bani shawarar In amince wurin aikata sa6on Allah, Kin
ban mamaki aunty aneelerh, bansan haka kike ba” tana magana tana jan majina.

Jinjina kai Aneelerh tayi”Laifina ne zahra, Ni da na damu dake shiyasa kike gaya
min magana son ranki, daga taimako? Daga yau ka da ki kuma tsammanin zan ƙara baki
shawara idan har baki kar6i abincin nan ba” wani ɗan iskan kallo Zahra ta watsa
mata, har saida ta dasa aya amaganarta tukunna zahra ta ruƙe qugu kamar ana
tunzurata tace”Idan har kin damu dani, meyasa ba zaki taimaka mu nemi mafita atare?
Saima ƙoƙarin da ki ka yi don ganin kin sanya ni a gur6atacciyar hanyar da zan
lalata duniyata da lahirata, ke ba mai ƙaunata bace aunty Aneeleeh, bana sonki kuma
bana son ganin ki!, Yakamata ki nisanta kan ki dani, Idan ba haka ba zan yi maki
rashin mutuncin da baki ta6a tsammani ba!!”

A kausashe Ta furta maganar tana nuna Aneelerh da cazbahar hannunta kamar zata rufe
ta da bugu.

Gyaɗa kai Aneelerh tayi tama rasa bakin magana, kalaman zahra sun bata mamaki,
bata ta6a tunanin zahra zata Ya furta mata su ba.

Juyawa ta yi da sauri ta nufi ƙofar fita, adai dai lokacin Mahboob yana ƙoƙarin
shigowa ɗakin suka ci karo da Aneelerh, har gaishe ta ya yi amma ko kallon shi ba
ta yi ba, hakan yasa shi tsammanin ko wani abu Ya faru ne.

Zahra na jin sallamar shi da sauri ta sanya hannu biyu ta share hawayen dake akan
fuskarta, komawa tayi daga gefen gadonta ta zauna tana dubanshi.

Riga da wandon shadda ne ajikinshi, hannun shi ruƙe da key din motar shi.

“Zahra Lafiya ki ke yi mini kiran talauci? Ina akan hanyar dawowa gida naga miss
calls dinki, Allah dai yasa lafiya”

Cikin sanyin murya tace da shi”ka zauna mahboob mu yi magana” zama yai da ɗan
mamaki akan face dinsa yace”meyasa ki kuka? Naga idanuwanki sun kumbura wanene Ya
ta6a ki? Ko ke da aunty Aneelerh ne”?

A hanzarce ta girgiza mashi kai tana faɗin”bakomai, banajin daɗi ne kaina ke ciwo”

“Kin sha magani” cikin kulawa yake yi mata magana, ɗaga mashi kai tayi alamar eh
ta ƙara da cewa”Aunty Aneelerh ce ta bani maganin”

Gyaɗa kai yai”okey, Allah ya sawaƙe sister yanzu dai faɗamin me kike buƙata ne
Kin dai san ban da ko sisi”

Murmushin takaici tasa kar mashi jin abinda yace

“Mahboob ba kuɗi zan roƙe ka ba, taimako nakeso kayi min dan Allah, bana son ka
tambayeni dalili kawai ka yi abun da nace maka, kuma bana son kowa Ya sani daga ni
sai kai”

“Kada ki damu, Ina jin ki” a ƙagare Ya furta mata hakan


“Inason zan siyar da motata ne da wayata, saboda ina buƙatar kuɗi ko akwai wanda
ka sani da zai Iya siya a yau din nan’? Ta jefa mashi tambayar tana duban
fuskarshi.

Mamakine ƙarara akan fuskarshi, Har saida Yaɗan saki baki da ido Yana dubanta
Kafin yace”ke kuwa me zai ja ki siyar da motarki da wayarki? Runtse ido ta dan yi
hawaye na ƙoƙarin cin ƙarfinta tace dashi”Mahboob banason tambaya! Kawai ka taimaka
mun in zaka Iya in kuma ba za ka yi ba to ka tashi ka tafi kaban wuri”

“Shikenan Naji, nayi shirun, amma dai kinsan kowa zai saye su sai kin faɗi ko? Ba
lallai asamu wanda zai siya da mutunci ba”

Ɗaga mashi kai tayi”Ni wannan ba damuwata bace, indai kuɗin zasu kai 4m Ya
wadatar”

“Okey, amma ni shawarar da zan baki mai zai hana ki bada motar da wayar taki
jingina? Idan kika samu halin biyan kuɗin sai ki Kar6o Kayan ki, zahra kinsan babu
mai siya maki su idan kika rasa na hannunki kuma ni bazan juri ara maki motata ba”
Ya faɗa Yana yamutsa fuskarsa, Harara ta watsa mashi da rinannun idanuwanta”kai fa
banza ne wlh, Ni ina ruwana da motarka? Koda zan rasa abun hawa mahboob bazan ta6a
aron kayanka ba”

Murmushi ya ɗan saki tare da miƙewa yace”to Aunty zahra, Ni zan tafi, in sha Allah
zan samu wanda zai siya, amma ki sani zamu kasa kuɗin gida uku, Ki kwashi kaso biyu
ni kuma ɗaya....”

Tunkan ya ƙare maganar zahra ta rarumi pillow aguje tabi shi da gudu ya fuce daga
ɗakin Yana tiƙar dariya muryarta ashaƙe take fadin”wallahi mahboob ka fita idona,
Ni ba tsarar wasanka bace, kuɗin nan da gumina na tarasu bada gumin wani ba’ rai
a6ace take yin maganar, bayan ta gama zazzaga mashi masifar ta juya ta koma cikin
ɗakinta tana faman tallabe cikinta dake yi mata kukan yunwa.

Safa da marwa ta soma Yi A tsakar dakin duk ta ƙagara da jiran kiran mahboob,
Fatanta Allah yasa asamu wanda zai sayi motar.

Wuraren ƙarfe 8 na dare, Kiran mahboob Ya shigo wayarta jiki na rawa ta ɗaga ta
kara a kunnanta, Anan yake sanar da ita cewa abokinsa Ya ce yana so harma sunyi
cinikin motar akan miliyan uku da rabi zai siyeta, ita kuma wayar zai siyeta dubu
ɗari biyar idan ta bari ahakan zuwa gobe da safe zai kai mashi Motar da wayar, daga
nan zai tura mashi kuɗin, tsabar farin Ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, duk
da tayi asara ba kaɗan, saboda an karya kuɗin motar da wayar, amma hakan bai
dameta, burinta ta sauke nauyin dake akanta, Bayan sun gama wayar, ta zuƙunna takai
goshi ƙasa tana godiya da Allah, daga bisani ta mike tana tiƙar rawa, da gudu ta
fito daga ɗaki ta nufi kitchen, ta ciko plate da abinci, ta buɗe frigde ta dauko
lemu mai sanyi kafin ta dawo ɗakinta, ita kadai ta zauna tsakiyar gado tana ci tana
sakin murmushi, baƙin cikinta ɗaya ta rasa damar da take da ita na zuwa Obie
estate, tunawa da wannan yasata rushewa da kuka ga abinci cike abakinta.

*JOS CITY*

Dare ya tsala sosai, Gari yayi duhu, a lokacin da kowani mahaluƙi yake a
makwancinsa domin runtsawa, baka jin sautin komai saina kukan tsuntsaye dana
karnukan Layi dake Hargowa.

A hankali take tafiya Hannunta ruƙe da trolley, doguwa ce a halitta, siririya


bata da ƙiba sai dai tana da hips, doguwar jallabiyace a jikinta, ta sanya niƙab ta
rufe fuskarta, abun da zai baka mamaki ita kaɗai take Bin santar babu alamun tsoro
atattare da ita, da taimakon street light ta ke samun damar ganin ko’ina, Har Allah
Ya nuna mata gidan da take nema, Katafaren Villa ne Mai gingirimeman gate.

da sassarfa ta nufi gate din, tana zuwa gabanshi, Takai hannu ta soma ƙwanƙwasa
ƙofar, tun tana yi a hankali har takai ga tsunto dutse ta cigaba da bugun ƙofar da
shi kamar zata 6alle gate din’

Security officers din dake tsaron gidan guda Biyu ne cikin kakinsu suka fito daga
ɗakunansu jiki na rawa suka ƙara so gaban gate din, da alamun mamaki akan
fuskokinsu suka haɗa bakin wurin furta Wanene ke buga mana ƙofa a dai dai irin
wannan lokacin”! Da fargaba suka furta maganar.

Cikin shessheƙar kuka da muryarta mai tsiwa ta furta”BENAZIR CE”

kallon Juna Officers din suka Yi, ɗaya yace”Wanene kuma haka? Mutun ko aljan? Wa
ki ka zo nema agidan ko dai kin yi 6atan Hanya ne”

Tamkar zata fashe da kuka tace”dan Allah ku buɗe mun gate in shigo, ni ce
benazir ɗiyar Alhaji ubaid”!

Ba ƙaramin ɗaure masu kai lamarin yayi ba, kasancewar su tsoffin masu gadin
gidan, sunsan wacece benazir Yarinyar uban gidansu data 6ace tsawon shekara goma
sha shidda, kokwanto suka soma Yi anya kuwa itace?

Officer mai gemu yace”kai, Da wuya ya zama gaskiya yarinyar da babu tabbacin tana
araye kota mutu”!

Ɗayan kuma yace”Ai ni banma yarda ba gaskiya, Kusan shekara goma sha shidda da
6atanta sai Yau ƙarfe sha biyu na dare zata dawo! anya kuwa ba tarko bane aka ɗana
mana”?

Mai gemu yace”amma kuma muryarta sak kalarta hajiya layla, Har tsiwar iri ɗaya da
tayi maganar”

Jin sunƙi buɗe mata kofa yasa ta rushe masu da kuka mai sautin gaske a faɗa ce ta
ke fadin”wai baza ku buɗe mun gate ba, na gaji da tsayuwa wallahi idan baku buɗe ba
na shigo cikin gidan saina Sa an kore ku”

Yawu suka haɗiya atare mai gemu yace”Ke baiwar Allah, ba yadda za’ai mu buɗe maki
gate ba tare da mun sanar da masu gidan ba, dan haka ki ƙara haƙuri mu faɗa masu”

Kafin suyi yunƙurin zuwa cikin gidan su sanar masu, ba zato ba tsammani suka ji ta
bangaje ƙofar jikin gate din dake a kulle, nan take ƙofar ta buɗe, hankalin su ba
ƙaramin tashi Yai ba, A firgice suke dubanta yayin da take shigowa ciki da
akwatinta, Ko kallo basu isheta ba, da sauri ta nufi cikin gidan.

Kasa motsi suka yi Kamar an dasa masu Aya, tuni zufa ta wanke fuskokinsu, Mamakin
su Taya akai ta Iya bugun ƙofa da ƙarfi Har jamlock mai ƙarko Ya zame kanshi!
Tabbas suna hasashen ba mutun bace aljana ce, tuni suka sha jinin jikinsu.

Tana tafiya tana bin ko’ina na gidan da kallo, abubuwa da dama sun canza mata
ba kamar yadda ta tafi tabarshi ba.

Adai dai lokacin Zainab mai aikin gidan tana a palour hannunta ruƙe da floor
wiper tana goge tiles, ta saba ba tun Yau idan bata son aiki Yayi mata yawa takan
fito har tsakar dare Tana aikace aikacen ta don ta rage wasu ayyukan na safe duk
idan taji ƙarfi a jikinta.

Tamkar da rana saboda hasken Ƙaton kwan dake a falon Ya gauraye ko’ina,
Hankalinta kwance ta duƙufa tana gudanar da aikinta ba zato ba tsammani taji an
banko ƙofar falon.

A firgice Zainab ta ɗago tana kallon matar da ta fado cikin falon afujajen,
tsabar firgitar da ta yi har batasan sa’adda ta jefar da wiper din hannun ta ba,
tun daga ƙasa har sama take kallonta, Hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tsananin
tsoro Ya kamata, Jikinta ya hau yin kerma, Muryarta na rawa ta furta”baiwar Allah
wacece ke? taya ya akai kika shigo gidan nan? Ƙarfe sha biyu na dare”? Aruɗe take
jefa mata tambayar.

Shessheƙar Kukan matar ne Ya ƙara firgitar da ita, ta soma Ja da baya tana


ƙoƙarin guduwa cikin gidan don ta faɗo ma Hajiya layla abun da ke faruwa sai dai
kafin Ta juya muryar Matar ya ratsa kunnanta cikin harshen larabcin take faɗin.

“AUNTY ZAINAB NI CE BENAZIR!! INA ABBANA! INA UMMI NA! INA MIJINA DA ƳA TA!!! A
jere ta jefa mata tambayoyin.

Har abada ba zata ta6a mantawa da muryar nan ba, koda kuwa amafarkine Ta jita
tabbas zata shaida mamallakiyarta.

A hargitse Ta juya Tana dubanta, A hankali benazir ta ɗaura ziraran yatsun


hannun ta farare tas ta ruƙo ƙasan niƙab ɗin fuskarta ta ɗage shi sama” tsabar
kiɗima da ganin fuskar da tayi kimanin shekaru sha shidda ba ta yi tozali da ita
bane yasa Jikinta ya hau yin kerma, tsantsar mamaki da al’ajabi ne akan fuskarta,
ta zazzare idonta akan kyakkyawar fuskar benazir, sam takasa yarda da abun da
idanuwanta ke nuna mana gani take yi tamkar mafarki ne take Yi!!

Tayi wani irin haske Kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Fuskarta sharkaf take da hawaye ta
ko’ina, ga zufa dake tsastsafo mata sam babu kwanciyar hankali atattare da ita.

Tsantsar tashi hankaline Akan fuskar zainab, Muryarta adabarbarce ta


furta”be..be..nazir! Dagaske ke ce ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai
ba”?

Da ƙarfi ta furta”Ni ce Aunty zainab! Ki amsa min tambayoyin da nayi maki”!

Tana faɗin hakan Nan take Ta yanke jiki Ta faɗi ƙasa a sume, akwatin hannunta ya
kife saman floor.

Juyawa Zainab tayi da gudun gaske ta nufi ɗakin hajiya layla, Hada yin tuntu6e
tsabar sauri, tunkafin ta ƙarasa ta soma ƙwala mata kira na fitar hayyaci tamkar
maƙoshin ta zai 6allo waje.

“Hajiya layla! hajiya layla”

Kaitsaye kiran ya daki dodon kunnuwan su daga ita har Alhaji ubaid dake kwance
saman katafaren gadonsu, A firgice suka farka a lokaci ɗaya suka miƙe zaune suna
ambaton Sunan zainab.

Doguwar jallabiya ce a jikin alhaji ubaid wuyan rigar ya karkace, Hajiya layla
kuwa Rigar Bacci ce a jikinta, da sauri Alhaji ubaid ya kunna bedside lamp din
ɗakin.

Sam babu kwanciyar hankali atattare da su, duk sun ƙura ido suna jiran ganin ta
inda zainab zata 6ullo.

Kamar daga sama suka ji ta banko ƙofar ɗakin tana faman Yin haki.
Da mamaki Akan fuskar Layla tace”Zainab baki da hankali ne? Ko kin makance ne?
Taya zaki faɗo mana ɗaki a irin wannan lokacin ba tare da kin nemi iznin shigowa
ciki ba”!

Kafin zainab ta bata amsa Alhaji ubaid Ya katse mata hanzarinta da cewa”Zainab
Lafiya kike ƙwala mana kifa? Kowani abun ne Ya faru”?
Cikin rawar murya ta furta”dan Allah kuyi haƙuri ku yafe ni, bana acikin
kwanciyar hankalina ne shiyasa na faɗo maku ɗaki ba sallama nasan bai dace ba”
dogon tsoki Layla Taja”Ba dogon bayani na tambaye ki ba, Ki faɗi min uban mi Ya
kawo ki ɗakin mu?

Bata kai ga ƙarasa maganar ba, Alhaji ubaid Yai saurin katse ta da cewa”Ya isa
haka, Haba kin cikata da faɗa, Kin ƙi bari tayi mana bayani dangane da abunda ke
faruwa” tsuke fuska Layla Tayi.

Cikin sanyin murya zainab tace”dama BENAZIR ce ta dawo!”

Kallon juna Alhaji ubaid da layla suka Yi lokaci ɗaya, kafin suka dawo da dubansu
ga zainab, Har suna haɗa baki wurin tambayar wacece Benazir!! Tsabar ruɗanin da
suka shiga
Zainab tace”benazir ƙanwar dr shureim Ƴar wurinku itace ta dawo, Yanzu haka tana
acikin palour ta yanke jiki ta faɗi a sume.

Girgiza kai layla tayi haɗi da cewa”baki da hankali zainab, dama na fara zargin
kin fara shan ƙwaya, In ba haka ba, ta ya ya benazir da ta gudu da ƙafafuwanta zata
dawo gida! bazai yiwu ba.

Alhaji ubaid Yace”ko dai mafarki ki ka yi ne zainab? Girgiza mashi kai tayi hada
hawaye akan fuskarta tace”wallahi dagaske nake yi zaku Iya zuwa palourn ku duba
benazir ce da kanta ta dawo”

Kusan atare suka sauko daga saman gadon, da sauri zainab ta basu hanya suka fuce
har suna bange juna tsabar sauri.

Tunkafin su ƙarasa falon suka soma hango mutun kwance saman floor da baƙaƙen Kaya
ga trolley dinta a gefe ɗaya, kasancewar ta yaye niqab din fuskarta hakan ya basu
damar ganin fuskarta, wani irin mahaukacin bugu zuciyarsu tayi A matuƙar gigice
suka furta sunanta”BENAZIR” adai dai lokacin gate security officers din gidan suka
shigo falon da sallama sam babu kwanciyar hankali akan fuskokinsu ganin Yanayin
mutanan gidan yasa suma suka ƙame suna faman zare ido.

Muryar Hajiya layla Na rawa ta furta”wallahi itace Benazir ɗina ce, Yarinya tace
data 6ata, itace ta dawo da kanta” ta ƙare maganar jiki na 6ari ta nufi gaban
Benazir dake kwance ta zube saman gwiwowinta tare da kai hannu ta ruƙo niƙab din
fuskarta ta ƙarasa cire mata shi, Kowa dake a falon saida yai matuƙar Al’ajabin
ganin Benazir, yalwataccen gashin kanta har gadon bayanta Ya nannaɗe kamar taliyar
indomie, babu alamun wahala atare da ita, sai ma hutun dake kwance saman farar
fatarta, wani iko na Allah, gaba ɗaya Jikinta Ya jiƙe da ruwan zufar dake tsastsafo
mata, hatta baƙar jallabiyar jikinta ta manne ma fatarta saboda zufar data wanketa,
ga wata zufar dake kurɗaɗowa ta cikin sumar kanta ta jiƙe sharkaf duk da sanyin A.c
din falon.

Rushewa da kuka Hajiya layla tayi haɗi da ɗaura Hannayenta biyu saman kanta tana
fadin”Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un! Dan Allah kuyi wani abu akai mana kun
tsaya kuna kallonta, sai kace baku gane ta ba, ɗiyata ce benazir Allah Ya dawo mun
da ita da ranta” Sautin kukan ta ya cika ɗakin, Zainab ma tuni ta fashe da kukan
farin ciki, security officers dake tsaye Jikinsu ya yi mugun yin sanyi, da farko
sunyi tsammanin ba mutun bace amma daga bisani Bayan ta shigo cikin gidan suka
dudduba ƙofar donsu tabbatar mutun ce ba aljana ba, ashe Jamlock ɗin ƙofar gate
dinne basu kulle shi ba sun manta, shiyasa har ta samu damar sanya ƙarfi ta bangaje
ƙofar ta shigo ciki.

Mamaki da al’jabi sun Hana Alhaji ubaid motsawa Ya kafe fuskar Ƴar tashi da ido
Yana kallonta, ruwan hawaye ne kwance acikin idanuwanshi haƙiƙa ya yi farin ciki
mara misaltuwa kusan shekara goma sha shidda Yau rana ɗaya Allah Ya kaɗo masu da
hankalinta ta dawo wurinsu, Allah ne kaɗai Yasan uwa duniyar data shiga.

Cikin shessheƙar kuka zainab tace”yakamata muyi wani abu akai, Benazir tana
buƙatar taimakon gaggawa, ga dukkan alamu wani abunne Ya faru da ita wanda Ya
haifar mata da fitar da gumi a jikinta”

Da sauri Alhaji Ubaid Ya sanya Hannayenshi biyu, Ya cuccu6eta Ya juya ya nufi


sofa mai mazaunin mutun uku Ya kwantar da ita, kallon zainab yai”je ki ɗauko min
wayata a ɗaki” ta amsa mashi da toh, da ɗan gudunta ta nufi bedroom dinsu.

Jiki amace layla ta miƙe ta koma saman sofa hand din da benazir ke akwance ta
zauna tana duban fuskar ƴartata Kamar Ta haɗiyeta haka take ji.

“Alhaji kun tabbata benazir ɗinmu ce ta dawo”! Mai gemu ne Yai mashi Maganar,
Jinjina masu kai Yai”babu shakka itace Allah ya dawo mana da ita” Ajiyar zuciya
kowan nan su Ya sauke tsantsar farin ciki Ne Ya kamasu.

“Muna tayaku murna, ita kuma muna yi mata fatan Allah Ya bata lafiya, Ubangiji
Allah yasa ƙarshen wahalarta kenan, sannan Alhaji Muna baku shawarar a kira malamin
da zai dubata don yanayinta dana gani a matsayina na wanda yake da sani a 6angaren
sihiri, Yarinyar ka ba likita take buƙata ba, Malami take buƙata saboda duk wasu
alamomi na jikinta sun nuna kamar sihirine daya daɗe a jikinta ya kwance !!! A
firgice Alhaji Ubaid Da Hajiya layla suka ɗago suna duban mai gemu da yayi maganar,
jinjina masu kai yayi”ba yau na fara ganin irin hakan ba, ina da tabbacin Yarinyar
nan kurciya aka yi mata, amma idan kunaso ku gasgata zance na ku kira babban
malamin da zai dubata” sam sun kasa magana sai bin shi da kallo da su ke Yi.

Daƙyar Hajiya layla Ta iya buɗe bakinta la66anta na kerma tace”amma benazir da
ƙafafuwanta ta gudu tabar gidan tajudden Bayan ta haihu tabar mashi jinjira a cikin
kwamin wanka, tayaya hakan zai yiwu? Wanene zai yi mana hakan?

Girgiza kai mai gemu yai”haka zakuyi tunani saboda bakusan dalilin tafiyarta ba,
amma abun duba anan tayaya Uwa zata gudu tabar jinjirin ɗan da ta haifa ta hanyar
raya sunna!! Duk irin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗanta? Sannan idan har dagaske
benazir ta gudu don son ranta tsawon shekara goma sha ɗaya meyasa zata dawo da
ƙafafuwanta ba’a cikin Hayyacin ta? Ga zufa duk ta wanke suturar jikinta, Nidai
shawarar da zan baku shine a tuntu6i malamin da zai dubata”

Jinjina kai Alhaji ubaid ya yi shi kanshi jikin shi ya yi sanyi da zancen Mai
gemu, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalamanshi.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruke da wayar Alhaji ubaid Ta miƙa mashi, Yasa
hannu Ya kar6a.

“Dare Yayi yanzu, kada mu katse ma wani baccin shi, shawarar da zan bada shine a
ɗebo ruwa a yayyafa mata in sha Allah zata farka, zuwa asuba sai a kira malamin da
zai dubata” mai gemu ne Yayi maganar, muryar Alhaji ubaid a sanyaye yace”Inaso zan
kira Dr shureim ne, saboda a irin wannan lokacin baya runtsawa Idonshi biyu Yana
tashi domin Yin nafilfilin dare” ya ambaci hakan tare da Danna wayar hannunshi ya
buga ma dr shureim Kira ta soma ringing.

Kallon zainab Hajiya layla tayi idanuwanta sun kaɗa jawur tace”ɗauko mun ruwa a
fridge “ amsa mata zainab tayi da toh, da sauri ta nufi hanyar kitchen.

Dafe kai Hajiya layla tayi da hannu ɗaya, Sumar kanta duk ta tarwatse saman
bayanta, ta manta da yanayin jikinta, don ma babu wanda ke acikin natsuwar shi,
hankalinsu na akan Benazir.
Bayan zainab ta dawo, hannunta ruƙe da bottle water me sanyi ta buɗe murfin ta
miƙa ma Hajiya layla, Yayyafa mata tayi saman fuskarta, nan take ta sauke nannauyar
ajiyar zuciyata muryarta da tsiwa take fadin”ina mahaifiyata Ina mahaifina! Ina
mijina da ƴata Ina yayana shureim, suna ina ! Na shiga uku na bani na lalace Na
rasa kowa nawa, wayyo Allahna na shiga Uku wallahi gida zan koma Nabar Yarinyata
cikin Jini, tajuddeen kai na bama amanar ɗiyata nasan bazaka bari rayuwarta ta
wulaƙanta ba. Dan Allah ka bani Ƴata ita nake son gani’

tunda ta fara sambatun nan zainab da hajiya layla suka fashe da kuka suna kallonta,
ta runtse idanuwanta sai faman ciccije le6enta take Yi da haƙoranta tuni suka soma
faffashewa, jini Ya soma tsastsafowa, dunƙule hannu tayi tana buge buge, da sauri
zainab da hajiya layla suke rurruƙeta sosai suna ambaton sunanta

*DR.SHUREIM❤*

Lokacin da Kiran Alhaji Ubaid ya shigo wayarshi, Yana a zaune saman darduma cikin
shiga ta larabawa, Yayi nisa acikin karatun qur’nin dayake yi Kiran Ya daki dodon
kunnanshi, Hakanan yaji gabanshi Na faduwa, aranshi ya ayyana kowa ne ne ke
kiranshi a tsakar daren na! ya salam, Sai da yakai ƙarshen Aya tukunna Ya zabura Ya
miƙe Ya nufi wayar dake ajiye saman side drawer ya ɗauke ta yana duban Screen din,
Hankalin shi ba ƙaramin tashi yai ba ganin sunan Abie dinsa Ya bayyana, kafin Ya
ɗaga kiran saida Ya fara kallon agogon bango ƙarfe ɗaya da rabi na dare, picking
call ɗin ya yi muryarshi na rawa ya furta”Assalamu alaikum Daddy!!!” muryar Alhaji
ubaid Babu natsuwa Ya furta mashi”shureim Ƴar uwarka ta dawo gida daren nan cikin
mawuyacin hali”! Da alamun ruɗu akan fuskar dr shureim Yace”bangane wa kake nufi ba
daddy” muryar shi da sauti mai ƙarfi Yace”BENAZIR!! nake nufi ta dawo gida cikin
daren Nan, Gatanan kwance tana buge buge zufa duk ta wanke jikinta, mun rasa ya
zamuyi da ita”

Zafafan Hawaye ne suka wanke fuskar dr. shureim, tsabar farin ciki baisan sa’adda
Ya zube saman gwiwowinsa Yayi sujjada, sosai ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma
zuciya, Alhaji Ubaid Yana jiyo sautin kukan dr shureim Kamar ƙaramin Yaro.

“Shureim ba kuka yakamata kayi ba, dan Allah ka natsu muyi magana, hankalin mu
ba’a kwance Yake ba, Ƴar uwarka bata acikin Hayyacinta, Mai gemu ya tabbatar min da
cewa Kurciya ne akayi mata, saboda alamomin dake a jikinta na fitar sihirine”

Jin wannan maganar ta Mahaifin nasa ne yasa shi saurin ɗagowa daga sujjadar, arab
turban dinsa tuni ya warware Yabar saman kanshi.

Manna wayar yai saman kunnanshi da alamun kiɗima ya furta”Sihiri kuma!!


Alhaji ubaid Yace”to haka dai mai gemu Ya faɗa mana, baka ga yadda jikinta ke
fitar da gumi ba kamar wadda aka tsamo daga kogon ruwa, bari na kanga maka wayar
kaji haukan da take Yi mana” on the other hand Alhaji Ubaid Ya matsa gaban benazir
Ya saita wayar abakinta.

Muryarya ce ta ratsa kunnuwan dr shureim”Ni ku sake ni, Ku ƙyaleni ku daina ruƙe


mun hannuna, wurin Mijina zanje nabar mashi ƴata a gida ita nake son gani, wallahi
ku rabu dani dole in tafi” Jikin taƙaura yai la’asar, a sukwane Dr shureim ya miƙe
tsaye da waya kare a kunnanshi.

Muryarshi na rawa Ya furta”daddy najima ina zargin hakan, innalillahi wa’inna


ilaihirraji’un, wallahi da ina da halin da zan Iya zuwa Jos acikin daren nan da
babu abun da zai hana inzo don in cece rayuwar ƴar uwata, amma duk da haka daga nan
ɗin ma zan Iya taimakawa, Daddy Idan Aunty zainab tana akusa ka miƙa mata wayar!”

Jikin Alhaji ubaid na 6ari ya miƙa ma zainab Wayar yace ta kar6a dr shureim ne ke
son Yin magana da ita, da sauri ta sanya hannu ta kar6i wayar tana fadin”dr shureim
kaga wani ikon Allah ko? Tsawon shekara goma sha shidda Yau benazir ta dawo gida,
wlh tsabar farin ciki bansan inda zan tsoma kaina ba, sai dai na damu da yanayin da
take aciki”

Numfasawa dr shureim Yai tare da cewa a tsanake”Aunty zainab, yanzu bani da


natsuwa, zuwa gobe da sassafe zan shigo Jos din, amma kafin nan ki duba ɗakina a
cikin drawer chest na bedside drawer gida na uku, akwai robobin ruwan zam zam da
wani malamin mu na ƙasar egyp ya bamu su don mu dinga yin amfani da su muna
taimakon mutanan da suke fama da matsalar sihiri, ki ɗauki ɗaya Kije ki buɗe bakin
benazir Ki matsa mata shi ki tabbar ta shanye shi duka in sha Allah, sauran sihirin
dake ajikinta zai barta ne kafin goben mu ƙaraso” amsa mashi tayi da toh, yace ta
miƙa ma mahaifiyarshi wayar da sauri ta miƙa mata, yatsun hannun layla na kerma ta
kar6i wayar.

Cikin shessheƙar kuka tace”shureim benazir ɗinmu ta dawo gida, sai dai kamar bata
acikin hayyacinta, duk ta faffasa la66anta da haƙoranta.

Cikin kwantar da murya dr shureim Yace”Ki sanya handsfree Inason daddy yaji
maganar da zanyi” da sauri layla ta mayar da wayar handsfree, zainab tuni ta shige
ɗakin dr shureim neman ruwan zam zam.

“Mommy daddy, dan Allah ku kwantar da hankalinku, wallahi Allah ne ya taimaki


rayuwar baiwar Allah nan Ya Karya sihirin dake a jikinta, kuma ya dawo mana da ita
da ranta, wani mugun aka samu mara imani mai zuciya irin ta kafuran farko Yai silar
rabata da danginta tsawon shekara goma sha shidda, wallahi tun lokacin dana ji
yanayin da benazir ta gudu tabar gida raina ya bani cewar wani abunne Ya faru da
ita, haƙiƙa munyi sakaci wurin kula da ita, gaba ɗaya mun ɗaura mata lafin
guduwarta babu wanda ya ta6a yi mata kyakkyawan zato akan meyasa ta gudu tabar
jinjira acikin kwamin wanka, Kuma bata nemi kowa ba ta kama hanya tayi tafiyarta,
anyi amfani da halayanta na rashin jin magana da rashin Kunya da take dashi anyi
mata abun da yasa tabar mu saboda ansan kowa zai yi tsammanin ita ta gudu dakanta
tunda dama bata jin magana, da ya ke Allah ba azzulumin bawansa bane sai gashi ya
dawo mana da ita a lokacin da bamuyi tsammanin ganin ta ba” gaba ɗaya sun natsu
suna sauraron muryar dr.shureim, hatta security officers din gidan duk suna
sauraron shi ga dukkan alamu suna gamsuwa da bayananshi duba da yadda suke gyaɗa
kawunansu.

“Banaso wani daga cikinku Ya tambayeta meyasa ta tafi, ko kuce zakuyi mata faɗa
dan Allah kada kuyi mata hakan, Kuma kada ku faɗa mata abun da ya faru da mijinta
da ƴarta, naji tana ambaton sunansu, ku sanar da ita cewa suna nan kuma zaku haɗata
da su idan ta kwantar da hankalinta, idan ba haka ba zata Iya zaucewa idan taji
cewa babu su”

Kamar malami da ɗalibansa haka shureim keyi masu magana suna amsa mashi da toh.

“Zuwa da safe kafin mu ƙaraso, a kira likitan gidanmu Ya duba lafiyarta,” suka
amsa mashi da toh.

“Mommy idan zainab ta bata ruwan zam zam din, in dai bacci bai ɗauke ta ba, ki
taimaka mata tayi wanka taci abinci, idan kuma tayi bacci ku ƙyale ta kada ku
takura mata” layla ta amsa mashi da toh.

Shigowa falon Zainab tayi hannunta ruƙe da robar zam zam ta ƙara so gaban sofa
din da benazir ke akwance tana sambatu, muryarta harta disashe fuskarta ta kumbura
suntum.

Zuƙunnawa tayi agaban sofa din, ta cizge murfin robar, da sauri Alhaji ubaid ya
rurruƙe mata hannuwan Benazir, daƙyar ta Iya buɗe bakinta ta kafa mata ruwan zam
zam din ya dinga shiga cikin ƙaramin bakinta, gaba ɗaya ta shanye ruwan, ko mintuna
biyar ba’ayi ba da bata ruwan bacci mai nauyi ya ɗauketa, sai faman sauke ajiyar
zuciya take yi, zufar jikinta tuni ta soma daskarewa, addu’o’i zainab ta dinga
karantowa cikin harshen larabci tana tottofa mata saman fuskarta da jikinta, hakan
ba ƙaramin daɗi yayi ma iyayenta ba, tuni layla tayi sallama da dr shureim ta miƙa
ma Alhaji ubaid wayarshi ya sanya hannu Ya kar6a ya tura a aljihun jallabiyarshi,
security office din dake atsaye bakin ƙofar falon suka yi masu sallama da niyar
gobe da safe zasu dawo duba jikin benazir, Alhaji ubaid yai masu godiya kafin suka
fice daga falon.

Hajiya layla ta dubi zainab kije ki kwanta mun gode sosai, dan Allah gobe da a
suba ki shirya mata lafiyayyan breakfast din da zata ci” amsa mata tayi da toh, ta
mike ta nufi room dinta, ya rage saura Alhaji ubaid da Hajiya layla a falon, kallon
juna sukayi lamarin Ya girgiza su, abun daya ɗaure masu kai wanene yayi masu wannan
muguwar aika aikar!!!
Atare suka ɗaura idanuwansu kan benazir tsantsar sonta da ƙaunarta ne Ya kamasu,
Har cikin zuciyarsu basu ji daɗin ƙaddarar data afka mata ba, tayi matuƙar basu
tausayi ganin irin mayuwacin halin da take aciki, fatansu Allah Ya toni asirin
baƙin azzulim daya yi silar barinta gida!!! yadda suka ga Rana haka suka ga dare,
babu wanda Ya runtsa acikin zukatan nan guda huɗu, Hajiya layla da Alhaji ubaid, Dr
shureim da Zainab, akan kunnuwansu aka fara kiran sallar asubahi!!!!

Dr.shureim Tun bayan daya dawo daga sallar asuba Yake ta faman shirye shiryen
tafiya jos, tuni Yayi wanka ya kimtsa cikin shigar shi ta larabawa Yabi ko’ina na
jikin shi Ya feshe da turare, Hannun shi ɗaya ruke da wayar shi ɗayan hannun Yana
ruƙe da car key dinsa, takalmasa Ya zura a ƙafa Jiki Na rawa ya nufi ƙofar fita
daga ɗakin bayan ya fito bai nifo ko’ina ba sai part din Alhaji musa don Ya sanar
mashi da zancen bayyanar benazir da kuma tafiyar da zaiyi zuwa jos, abakin ƙofar
ɗakin ya dai daita natsuwarshi, ya ɗaga murya yayi mashi Sallama, kusan sau uku
kafin muryar Alhaji musa ta amsa mashi
“Wa’alaikum salam shureim shigo ciki mana” ajiyar zuciya ya sauke, tare da sanya
hannu Ya ture ƙofar ta buɗe, baiyi tsammanin zai ganshi tare da wani ba, ashe bashi
kaɗai bane, su biyune shi da Hajiya Sarah suna zaune saman Sofa ɗin ɗakinshi, An
jera masu kayan breakfast a saman sofa table din gabansu, mutumin babu annuri akan
fuskarshi, Jallabiyace a jikin shi hajiyar tashi kuwa ta ca6a uban adon lace a
jikinta, ta kashe ɗaurin kallabinta, wutsiyar gashin kanta ya sauka har saman
wuyanta
Fuskarta da fara’a take kallon shureim”barka da safiya My son, fatan ka wayi gari
lafiya” shureim na murmushi yace”yawwa mommy, ina kwananku’ ta amsa mashi da Lafiya
lou, tare da nuna mashi wuri saman armchair ta ɗakin tace”bismillah ka zauna mana”
tun da ya shigo Alhaji musa bai ɗago Ya kalli fuskarshi ba, Hankalin shi na akan
abincin da Yake ci, plate ne agabanshi shaƙe da farfesun nama Yaji ƙayan hadi sai
ƙamshi Yake Yi, a tsanake Yake cin abun shi.
Kasa zama shureim yayi idanuwanshi akan fuskar Alhaji musa Yace”uncle barka da
safiya” kamar bazai amsa mashi ba ya furta”lafiya” da ido Hajiya sarah tayi alamar
yayi haƙuri da halin uncle din nashi, murmushi shureim ya sakar mata yaɗan jinjina
mata kai
“Ko zaka Bari idan Ya gama cin abinci sai ku yi magana, don bai cika son yana cin
abinci ana yi mashi magana ba” hajiya sarah ce ta fada,
Kafin dr shureim ya bata amsa muryar Alhaji musa ta katse mashi
hanzarinshi”Shureim ina jin ka, faɗi abunda ya kawo ka”
Ba ƙaramin daɗi Yaji ba, da fara’arshi ya fara magana”uncle bansani ba, ko
daddy ya kira ka awaya ya sanar dakai abun farin cikin daya faru a daren Jiya” sai
da ya ambacin hakan tukunna alhaji musa Ya ɗago da ido yana dubanshi alamar yana
son jin ƙarashen zancen
“Ƴar uwata Benazir ta dawo gida a daren Jiya ƙarfe goma sha biyu na dare!!!”
Tsantsar mamaki da al’ajabi ne Ya bayyana akan fuskar alhaji musa, sai dai babu
alamun zai furta magana sai faman jinjina kanshi yake yi.
Hajiya sarah kuwa Tsabar farin ciki mikewa tayi tsaye tare da ɗaga hannyenta sama
tana ambaton”ALHAMDULILLAH!! wayyo Allah shureim Allah Yasa ba wasa kake Yi min,
dagaske Benazir ta dawo gida da ƙafafuwanta ko kawota akayi”?
Shureim na murmushi yace”da kanta ta dawo gida, kuma abun mamaki tana ta sambatu
tana ambaton sunan daddy da mommy da mijinta da ƴarta, kuma muna hasashen kurciya
ne akayi mata da har ta gudu tsawon shekaru bata dawo gida ba, shiyasa nake so inje
jos din Yanzu.......”
Hawayene suka wanke fuskar Hajiya sarah, Muryarta na rawa ta furta”shureim nima
zan bika muje jos din, nasan shima uncle din naka zai je sai mu tafi atare...”
kafin ta ƙare maganar Alhaji musa ya dakatar da ita ta hanyar cewa”Ya isa haka?
Kinsan bana son shouting” shiru suka yi gaba ɗayansu, duk suka sha jinin jikinsu.
Kallon shureim yayi”ina zaka je da safen nan, naga ka shirya ga key din mota a
hannu”?
Cikin sanyin murya yace”jos zan tafi, Inason ganin benazir”

Ta6e baki Alhaji musa yayi, tsawon mintuna ɗakin yai tsita, saida ya mula yasha
iska tukunna yace”zanyi waya da yaya ubaid din, basai kaje jos din ba, zansa su zo
nan abuja...” har saida gaban shureim Ya faɗi jin abinda Yace, bashi ba hatta
Hajiya sarah arude take duban fuskarshi, kallon mara hankali take binshi da shi don
wanna Yafi ƙarfin a kira shi da izzah, Tayaya zai nuna ƙarfin iko akan Yayanshi?
Waye ya dace yazo gidan wani? Almost 16years yarinya ta 6ace sai Jiya ta dawo ƙarfe
sha biyu na dare ko kaɗan bai nuna danuwarshi ba, kuma babu alamun zai je ya taya
yayanshi murnar ganin yarsu da suka yi?
Muryarta na rawa ta furta”am..amma hakan bai dace ba, nayi mamaki daka furta
wannan maganar, kodai baka ji abunda shureim Yake faɗi bane? Ƴar wurin Yayanka
benazir ce data 6ace tsawon shekaru ta dawo gida a daren jiya ƙarfe goma sha biyu
na dare Yakama ka tashi ka shirya mu tafi” da buɗar bakinshi sai cewa yai”Umarni
kike bani”? Da ƙarfin hali Ta furta”A’a kawai ina ƙoƙarin faɗa maka abunda Ya dace
ne” tamkar zaki Haka ya yunƙura ya miƙe Ya dubi fuskar shureim da mamaki Ya gama
kamashi
“Nace bazaka je jos ba, ka koma ɗaki ka zauna, zansa Iyayen naka su zo tare da
ƴar uwar taka abuja” gyaɗa kai dr shureim yayi jiki amace yace”toh uncle, na
hakura, zan jira su zo ɗin” ƙwalla ce ta ciko idanuwanshi da sauri Ya juya ya fuce
daga dakin.
Bayan fitarshi Alhaji musa Ya nuna Hajiya sarah da Yatsan hannunshi”koda gigin
wasa kada ki kuskura ki ƙara shiga tsakanina da shureim idan muna magana, abune da
ya shafeni da dangina banaki ba, don haka ki kiyaye” yana gama fadin hakan a fusace
yakai hannu ya yago tissue ya goge bakinsa ya nufi cikin dakin.
Jiki asanyaye hajiya sarah ta zauna saman sofa din, lamarin Ya ɗaure mata kai,
wannan rashin adalcin har ina? Meyasa zai dinga iko da yayanshi? Ko dan Yana da
dukiya ne? girgiza kai tayi ahankali ta furta”wannan ba adalci bane” ta faɗa haɗi
da miƙewa ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Bawan Allah dr shureim abun duniya ya isheshi, Uncle musa Ya bashi mamaki, bai
ta6a jin haushinshi ba sai yau daya nuna ƙarfin iko akan iyayenshi, Ya fahimci ma
bai damu da dawowar benazir ba saboda babu annuri akan fuskarshi duk da yasan halin
shi ne hakan, amma yaji ɗaci aranshi, don me zai dinga juya mahaifinshi son ranshi
bayan shine agaba dashi, ko a shekaru Alhaji ubaid Ya zarce Alhaji musa nesa ba
kusa ba saboda shi ba wasu shekaru gare shi ba, shiyasa ko a jam’iyarsu ake
kiranshi da ƙaraminsu babbansu. Abun ya ɗaurewa Dr. Shureim kai, har ya fara tunani
kodan Yana da dukiyane shiyasa yake sarrafa kowa yadda yake so? In banda rashin ta
ido har zai Iya buɗe baki yace zai kira iyayan nashi suzo abuja maimakon shi ya
tattara iyalansa suje can jos din su tayasu murnar dawowar ƴar su, Anya kuwa Uncle
musa bai fara shan ƙwaya ba”? Saƙe saƙe zuciyar shureim take Yi mashi hakanan ya
samu kanshi da kokwanton uncle din nasa.
“Shureim dan Allah ka yi hakuri da abunda uncle dinka Ya faɗa maka, wallahi banji
daɗi ba, bai kyauta ba, wannan ai ba adalci bane, bansan meyasa yake yin haka ba”
Muryar Hajiya sarah ce ta katse mashi zancen zucin nashi, har ya kusa shiga ɗakin
shi Ya ci burki tare da Juyowa baya yana dubanta
Damuwace ƙarara akan fuskarta, kamar yadda shima tashi fuskar damuwarce
Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi da karyayyar murya ya furta”kada hakan ya
dame ki mommy, da ace bansan halin uncle din nawa bane, amma nasani, shiyasa nake
yi mashi uziri, bakomai zan jira su zo din kamar yadda ya fada”
Gyaɗa kai hajiya sarah tayi har cikin ranta bataji daɗin abin daya faru ba
“Bari na kira maka zeenatu, nasan zata ɗebe maka kewa, kafin isowarsu” still da
murmushi akan fuskarshi Yace toh, zan jirata
Bayan tafiyarta, Ya shiga dakin shi, asaman gado ya jefar da key din hannun shi,
Ya tu6e arab tur6an dinsa Ya jefar saman gado, Ya zauna daga gefe hannu bibbiyu ya
zabga uban ta gumi takaici Ya ishe shi, mahaifinshi Yafi 6ata mashi rai saboda
shine silar komai, da ace tun farko bai bari uncle musa ya raina shi ba da duk
hakan bata faru ba.
Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar Zeenatu ta katse shi
“Yaya shureim ɗina” a hanzarce ya ɗago da ido yana dubanta, ta zumbula dogon
hajibi har ƙasa Yake ja, ta ruƙo round plate mai ɗauke da mug, sai faman sakar
mashi murmushi take yi, kwata kwata babu natsuwa atattare da ita, kafin shigowarta
ɗakin mommynta ta faɗa mata xancen ganin benazir shiyasa take ta yin farin ciki,
ita fa tun da take bata ta6a ganin benazir ba a hoto kaɗai tasanta saboda kafin
guduwar benazir tana ƴar jinjirarta.
Ganin yadda take tafiya babu natsuwa yasa shin saurin motsa la66ansa da niyar ya
dakata da ita, sai dai ina kafin yai yunƙurin yin hakan tuni tayi tuntu6e da
takalmanshi daya cire a tsakar ɗakin, Mugs din data dauko yai tsalle sama Ya dira
daman ƙafarta ruwan coffee mai zafi Ya ɗalli ƙafarta, zafin da tajine yasa ta jefar
da plate din hannunta, ta duƙe saman floor tana kuka, da sauri Ya miƙe ya ƙarasa
gabanta, ya zuƙunna tare da kai hannu ya damƙi ƙafafuwanta Ya soma tottofe su da
addu’o’i, ta dage sai kuka take yi mashi, abunka ga farar fata wurin da ruwan
coffeen Ya ta6a yayi jawur kamar zai fashe.
Kukanta duk Ya cika mashi kunnuwanshi, a hankali ya ɗago Yana dubanta, hawaye sun
wanke fuskarta, lokaci ɗaya ya soma tariyo sambatun benazir tuni yaji jikinshi yai
sanyi, haƙiƙa Yana matuƙar tausayin rayuwar ƴa mace, fuskar benazir ce ta dinga yi
mashi gizo akan fuskar zeenatu, har baisan sa’adda Ya rungume ta a kirjinshi Ya
zagoya da hannanyeshi saman bayanta, Yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi,
ƙanƙameshi zeenatu tayi kamar zata koma cikin cikinsa, daddaɗan ƙamshin turarenshi
ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba, tuni ta haɗiye kukan da take yi, tayi kwance
abunta sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, dr. Shureim sam ya manta dawa ya
rungume a jikinshi, kewar benazir duk ta addabe shi, Ya jefa zeenatu cikin yanayi
najin shauƙin shi, yayin da shi hankalinshi nacan wani wurin daban...............

Idan muka koma 6angaren zahra, tun wuraren ƙarfe shidda Mahboob Ya shigo mata da
jakar kuɗin motarta da wayar da aka saida mata, shaf shaf ta shirya cikin jallabiya
ta yafa mayafi akanta, tace da mahboob ya taimaka ya kaita gidan Hajiya falmata,
yace zai kaita amma bisa sharadin zata bashi nashi kason, tunda ai yayi mata
ƙokari, a lokacin taƙagara da taje tace mashi ta amince su tafi kawai, kafin su bar
gidan saida ta fara cire miliyan ɗaya ta ajiye su cikin drawer, ya rage saura 3m
dai dai kuɗin da zata bata.
Tana zaune a back seat na motar mahboob, yayin da shi kuma yake zaune a mazaunin
driver, a tsanake yake yin driving har Allah Ya kawo su gidan Hajiya falmata.
A parking space mahboob yai parking din motar yace da ita ta shiga yana jiranta,
ta amsa mashi da toh, ta buɗe motar ta fito ta nufi ƙofar shiga babban falon gidan”
Murmushin gefen fuska Mahboob ya dan saki yayin da yake bin Bayan zahra da
kallo, ya zuro ƙafarshi daga cikin motar daya bar murfinta abuɗe
Wayarshi ce tayi ringing daga cikin aljihu da sauri Ya zura hannu ya duba mai
kiranshi sunan Aunty Aneelerh ne Ya bayyana
Picking call din yai ya kara wayar a kunne”Babbar yayanmu, mun karaso gidan fa,
Yau zahra zata sha mamaki, wallahi bakiga yadda take ta zubda uban gumi ba, kamar
wadda tayi ma sarki ƙarya fadawa suka kamo ta” tuntsirewa yayi da dariya,
Muryar Aneelerh da sautin dariya tace”baiwar Allah, ina fata yau hankalinta zai
kwanta, naji daɗi da nasarar da muka samu, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mata ita”
ya amsa mata da ameen

Ta kuma cewa”Idan kuka dawo gida, ka faɗa mata cewa motarta da wayarta jingina ka
bada su, idan tanaso ta baka kuɗin za’a dawo mata da su, sannan please bana so
tasan cewa jiya munje gidan hajiya falmata, ya amsa mata da toh, daga haka sukayi
sallamar.

Tun da zahra ta shiga gidan, takasa zama, tana a tsaye tana jiran fitowar hajiya
falmata don ta miƙa mata kuɗinta, mai aikin gidan ce ta fito daga part din dakin
nata ta dubi zahra”ki zauna mana gatanan fitowa” galla mata harara zahra tayi’ba
zama nazo yi ba” murmushi mai aikin tasaki kafin ta wuce ta nufi kitchen
Jim kaɗan, Hajiya falmata ta sauko down stairs, sleeping dress ne a jikinta riga
da wando ta yafa mayafi akanta.
Fuskarta babu walwala ta dubi zahra”zauna mana” tayi maganar tana nuna mata sofa
Harara zahra ta watsa mata”ba zama nazo yi ba, kuɗinki na kawo maki” tayi maganar
a fadace ta ajiye mata jakar gaban kujerar da take a zaune
Har ta juya zata fita muryar hajiya falmata ta katse mata hanzarinta
“Zahra! Dan Allah ki zauna inaso muyi magana badan halina ba”
Batayi mata gardama ba tace”dan kin haɗani da Allah, shiyasa zan zauna badan haka
ba wallahi ko kallo baki ishe ni ba” murmushi hajiya falmata tasaki.
Bayan zahra ta zauna tana faman haɗe rai tace”ina sauraronki sauri nake yi in
tafi”
“Nasan zakiyi mamaki zahra, kuma ba lallai ki yarda da abunda zan faɗa maki ba,
abunda Ya faru a tsakanina dake badagaske bane, jarabaki nayi saboda wani dalili
nawa....” da mamaki zahra take dubanta, jinjina kai hajiya falmata tayi”tabbas ba
halina bane, nayi ƙoƙarin jan ra’ayinki ne don insan dawa ƴata take tarayya”
Tunkan ta kare maganar zahra tasaki dariyar rainin wayau tana fadin”dallah malama
dakata! Banason zancen banza, harni zaki raina ma wayau? Ki gama zubda mutuncinki
agabana kuma ki dawo kina fadin jarabani kikayi akan me kenan? A tsiwace ta furta
hakan
Numfasawa hajiya falmata tayi”zahra dalilin dayasa nayi maki hakan, Mun samu
sabani nida wata aminiyata hajiya naja’at akan ƴarta dake bin mata, ta laƙafa mun
sharrin cewa ƴata fatima ce ta koya mata, saboda ita kaɗaice suke tarayya, sannan
ita taba yarta tarbiya tasan bazata ta6a aikata hakan ba, faɗa sosai mukayi da ita,
ta zageni taci mutuncina, damuwar duniya ta isheni, lokacin dana dawo gida narasa
ya zanyi in tuhumi fatima saboda nima ina tsoron ace ƴata tana aikata kalar abunda
Yarinyar aminiyartawa take yi, nasan zaiyi wuya fatima ta faɗa min gaskiya, kinji
dalilin dayasa na yanke shawarar yi maki hakan saboda nasan ke kaɗaice aminiyar
fatima, duk wani abu da zatayi saida shawararki, atare kuke yin komai, Ni a
tunanina ta hanyar dana 6ullo maki zan samu abunda nake nema na gano abunda ƴata
take aikawata ashe ba haka bane nayi babban kuskure zahra, dan Allah Ki yafe min”
fashewa tayi da kuka hawaye nabin fuskarta, baiwar Allah zahra tuni zuciyarta ta
karya, sam bata kawo komai aranta ba, ta yadda da kalaman hajiya falmata, cikin
shessheƙar kuka tace”Amma meyasa zaki yi jarabawar dani? Kin hanani bacci kin
hanani cin abinci, kin jefa rayuwata cikin matsanancin tashin hankali, babban abun
takaicina shine karya min zuciya da kikayi saboda na ɗauke ki tamkar mahaifiyata
ina ganin girmanki, ashe dama duk plan ne kika shirya min”?
Hajiya falmata na matsar ƙwalla tace”kiyi hakuri zahra nasan ban kyauta maki ba,
dan Allah ki rufe min asiri kada kowa Yaji maganar nan, saboda banaso ayi tsammanin
nima ina aikatawa ne sannan, maganar kuɗin da nake binku ni tuntuni na yafe maku,
wallahi na bar maku su babu abunda zanyi dasu, sannan maganar yin order na kaya
daga dubai in sha Allah gobe zasu iso Nigeria, inaso kuci gaba da gudanar da
aikinku a companyna ke da fatima, don bazanso in rasa mace mai nagarta da tawakkali
irinki ba, komai kuke so zanyi maku zahra, ni dai fatana ki manta da duk wani abu
daya faru a tsakanina dake, Ki cigaba da daukata tamkar mahaifiyarki”
Rushewa zahra tayi da kuka, kamar ranta zai fita, bata ta6a tsammanin komai zai
zo mata da sauƙi ba, harta fidda ran cigaba da aiki a companynsu da kuma damar zuwa
obie estate ashe da rabon mafarkin ta ya zama gaskiya.
Cikin shessheƙar kuka tace”In sha Allah mommy babu wanda zaiji maganar nan,
komai Ya wuce amma dan Allah kada ki ƙara yi min wasan nan, ni kaɗai nasan raɗaɗin
da naji acikin zuciyata”
Jinjina kai hajiya falmata tayi da karyayyar murya tace”bazan ƙaraba zahra, nima
nayi danasani, dan Allah ki tsaya mu yi breakfast atare kada kice zaki tafiya”
Zahra tace”sauri nake yi wata rana zan dawo, Ina fatima take”? Hajiya falmata
tace”bata nan, jiya ta tafi gidan uncle dinta amma yau zata dawo saboda aikin da
zakuyi tare” murmushin farin cikine Ya bayyana akan fuskar Zahra, sai faman washe
bake takeyi harta fara tunanin irin rashin mutuncin da zatayi ma Aneelerh idan ta
koma gida,
Godiya sosai hajiya falmata tayi mata, itama zahra tayi mata godiya da fara’a
suka rabu.
Ta ruƙo jakar kuɗinta a hannu, tana fitowa daga falon da gudu ta nufi motar
mahboob tana dariya haɗi da yin rawa tana jujjuya,
Mahboob tamkar baisan komai yace”zahra kin haukace ne? Lafiya kike dariya kamar
wadda ta zauce ga hawaye akan fuskarki” da sauri ta share hawayen da gyalen
jallabiyarta
Tace dashi”bro ka tayani murna yau ina cikin farin ciki, amma fa kada ka tambayeni
meyasani shiga yanayin nan”
Mahboob na murmushi yace”shakuruminki aini ba ɗan jarida bane da zan tsareki da
tambaya, Yanzu dai shiga mota muje gida muyi magana akan haƙƙina,”
Da farin ciki tace”ai mahboob kamar yadda Allah Ya rufa min asiri kaima zan rufa
maka asiri, kai dai muje gidan” ta faɗa haɗi da shiga motar, ya tada suka nufi
Hanyar komawa gida.

*EX-PRISONERS🥳*

*At abuja Nigeria🛬*

Alhamdulillah Matafiya sun samu damar sauka Lafiya basu wayi gari ba sai acikin
Katafaren Luxury Villa Mallakin Chief Owais sharafuddeen Obinna! haɗaɗɗiyar Daular
arzƙi ce wadda zamu Iya kiranta da Aljannar duniya saboda Kayan alatun dake acikin
ta, Katafaren gini ne mai girman gaske ta 6angaren tsayi da faɗi Yana ɗauke da
Sassa Uku acikinsa, a ɗaya daga cikin Part din gidan aka yima Prisoners masaukinsu,
A hankali nake bin ginin da kallo domin in ƙarasa ga cikinsa, ta ko’ina na kalla
ƙyalƙyalin gilassai ne suke kashe min idona da kyawunsu, wasu irin haɗaɗɗun floor-
to-ceiling Glass windows ne masu mamaye bango, daga ƙasa har sama glass ne, Kana
Iya hangen Katafaren Main falo din dake acikin sashen ta glass windows din, Ga wasu
sliding doors ƙofofi masu zuge kansu da zarar sun gama tantance mutun saboda gidan
Yana da mugun tsaro ba iya mutane ba hada na’urori ke sarrafa shi, ba za ka ta6a
Iya ƙetare Gingirimeman entry way din gidan ba tare da An tantance ka ba, daga ƙasa
har sama, bana tunanin ko aljani zai Iya shiga salin alin ba tare da na’ura ta
haska shi ba, salon kuma ace nayi karya (😂)

Dafa ƙofar glass din Nayi da hannuna ɗaya, Na’ura ta tantance ni aka bani iznin
shiga ciki, Slowly glass din Ya soma zugewa, Na baza ido ina kallon tsaruwar Falon
da kallon shi kaɗai zai Iya faranta zuciya, launukan painting cikinsa black, gold
and white, An ƙawata shi da manya manyan sectional Chersterfield sofas, saiti biyu
ne a palourn, Ƴan ubansu masu numfashi masu tafshi da daɗin zama ga jerin Throw
pillows launuka daban daban saman kowace sofa, daga tsakiyar Katafaren falon wani
faffaɗan Glass table ne daga saman shi an ɗaura flowers Vase, Furannin har ƙyalli
suke Yi masu launi daban daban, bayan haka a kowani sofa hand din akwai Round glass
table, mai dauke da kayan ƙyale-ƙyale na ado, daga saman jigunan ceilling din falon
wasu ƙayatattun Crystal chandeliers ne masu girman gaske, An ƙawatasu da ado, kusan
guda Uku ne a saman silin din, Haskensu Ya mamaye ko’ina tamkar da rana, Idan ka
kalle su sai ka yi tsammanin zasu rubzo maka saman kai, sobada girman su, ga wata
faskekiyar flat screen tv wadda idan kana kallo da ita sai ka yi tsammanin mutanan
ciki zasu fito waje saboda girmanta, Bayan sofas din falon akwai hamshaƙan
armchairs har guda biyu, hatta saman floor din falon Kayan adone aka ɗaura samansu,
sparkling floor lamps ne ajiye a kasa suna bada nasu hasken mai ƙyalƙyali, akwai
Kayan jin sauti, Ga Dogayen labulaye dake kewaye da falon an zuge su, A ƙalla Part
din Yana ɗauke da Faluka sun kai Uku, bayan wanda na zayyana ma ku, daga cikin
falon farko kana Iya hangen furniture din da ke a cikin falo na biyu ta hanyar
Glass window, komai zaka Iya gani, Gidan fa Ya haɗu Ga glass elevator gefen twins
stairs din dake a falon, ta ko’ina sanyayyan sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikin
bil’adama mai ni’imar gaske, bayan haka ta cikin glass din falon zaka Iya hango
Sashen da tanƙameman swimming pool din gidan Yake, ruwan dake acikinsa launin sky
blue ne, da wasu kujerun shaƙatawa a gefenshi, da sauran ababen more rayuwa, Idan
muka koma Dining room wato ɗakin cin abincin gidan abun ba’a magana, shima a kewaye
yake da floor-to-ceilling glass windows, kana Iya hangen abubuwan dake wakana daga
wajen ɗakin cin abincin, An ƙawata shi da haɗaɗɗun dining tables, na farko
zungureren table ne mai mazaunin mutun goma sha biyu, da me mazaunin mutun shidda,
da kuma tabur mai mazaunin mutun uku, kowan nan su saman shi an ƙerashi da zallar
glass, ƙafafuwansu kuma wooden legs ne, wasu haɗaɗun gujerune kewaye da tables din,
daga saman ceilling din ɗakin cin abincin ƙaton kwan fitila ne ke haskaka cikinsa,
ga kuma Zungureriyar floor lamp, Itama nata hasken Daban Yake, agurguje zamu leƙa
Cikin Bedrooms din dake a part din, A ƙalla ɗakunan kwanan dake a cikin part din
sun kai goma sha biyar, Just for one part, ƙofar shigar kowani ɗaki ta glass ce sai
dai baka Iya hangen abunda ke ciki idan har na cikin ɗakin ya zuge curtain dinsa
ba, ƙofar da kanta take zugewa da zarar mutun Ya kusance ta take sliding a hankali,
Idan ka shiga ɗakin idanuwanka zasu fara Yin Arba da wallpaper ta bango mai matuƙar
jan hankali, kowani room Yana ɗauke da hamshaƙan king-side beds masu tausasan
Katifu kalar wanda ko mutun bai jin bacci idan Ya hau su sai dai aji sautin
minsharin shi, saman gadon shimfiɗe yake da tausasan bedsheet, da jibgegen bargon
lullu6a kafi mage laushi, ga jerin matassan kai daga gaban gadon.

Gefe da gefen gadon nightstands ne, wadanda ke ɗauke da bedside lamps, daga bakin
gadon faffaɗan wooden table ne mai ɗauke da drawer chest a jikin shi, ga wani
haɗaɗɗen rag carpet shimfiɗe ƙasa mai dumbujejen gashi gashi ajikinshi tsaf mutun
zai Iya kwanciya saman shi saboda laushinshi, ga wani ƙayataccen dressing mirror
gabanshi haɗaɗɗiyar kujerace, daga can cikin ɗakin akwai dressing room, aljannar
duniya kamar ka shiga company saboda haɗuwar Large walk in closet din daya mamaye
kowani bango na dakin sanya suturar, suturun sanyawa ne an jera su, daga waje zaka
Iya ganin kayan dake a cikin closet din, 6angaren Kayan bacci, dana Dogayen riguna,
6angaren english wears dana atamfofi ga laces, da jerin coat, ga 6angaren takalma
kala kala, dana jakkuna, kai komai fa an zuba shi babu ce kaɗai ke babu, shima
ɗakin Yana da nashi dressing table, mai ɗauke da oval-shaped mirror, Mai Kyan
gaske.

Ataƙaice Idan fa nace zan tsaya zayyana daular Owais sharafudden tabbas zamu ƙare
littafin akan bayyana kyawunsa, sai dai mun shiga cikin labarin sannu a hankali zan
ƙarasa zayyana maku haɗuwar wasu 6angarorin na gidan.

*CHIEF OWAIS✊*

Gajiyar tafiya ta hana shi ta6uka komai, ga6o6in jikinsa sunyi mashi nauyi, tun da
ya fito daga bathroom yake a kwance saman katafaren king bed dinsa, ya lullu6e
surar jikinshi da Cashmere robe launin dark navy, Iya gwiwarsa rigar ta tsaya
mashi, ya ɗaure igiyarta daga saiting flat waist dinsa, mutumin fa akwai ƙirar
ƙarfi, Kyawawan idanuwanshi A lumshe suke tamkar maiyin bacci, Yalwatattun eye
lashes dinsa sun kwanta luf, a hankali Yake motsa soft thin lips dinsa tausasa
launin pink, dogon hancinsa Yayi tsaye babu lanƙwasa Yayin da yake fitar da
numfashi cikin kwanciyar hankali, ya zagayo da hannun shi ɗaya ta saman
yalwatacciyar sumar kanshi, ba za ka ta6a gane a wani yanayi yake aciki ba, ya tada
kansa asaman tattausan pillow.

Alert ne ya shigo wayarshi, tamkar baisan motsawa A hankali ya miƙa ziraran yatsun
hannunsa na dama ya janyo wayar dake ajiye saman nightstand, daƙyar yake iya buɗe
eyes dinshi akan screen din wayar, Doorbell alert ya gani alamar wani yana son
shigowa room dinsa, unclock button ya danna, a hankali ƙofar room ɗin ta zuge,
mutun biyu ne sanye cikin kakinsu, baƙaƙen kaya, dogon wando tare da black shirt,
daga sama sun ɗaura long coat, kowannansu ya 6oye fuskarshi da face mask,
idanuwansu ne kaɗai zaka Iya gani, suna da faffaɗan ƙirji, agaban gadon shi suka
dakata da yin tafiya, cikin girmamawa suka haɗa baki wurin furta

“Barka da safiya Yalla6ai, fatan ka tashi lafiya, Ya gajiyar tafiya” tun da suka
fara magana basu ɗago da ido sun kalle shi ba, saboda a ƙa’ida shi ba’ayi mashi
magana ana kallon cikin idon shi, hakan babban laifi ne.

Bai da niyar yi masu magana, bai kuma buɗe idanuwanshi ba tun da ya lumshe su,
aran su su ka ayyana yau qasaitar tashi ce ta motsa, kamar gumaka Ya shanyasu a
tsaye suna jiran amsar shi, sai da ya mula yasha iska kamar baison motsa la66ansa
Ya furta”Lafiya” muryarshi tamkar ana busa sarewa.

Big Guy yace”Sir, is there anything you need?” ya tambaye shi ne don shi a
ƙa’ida ba’ayi mashi abun da bai ce yana so ba, ko da kuwa abinci ne ka kawo mashi
duk mun yunwar da yake ji in dai bashi yace yana so ba to zai ce maka ka koma dashi
inda ka ɗauko shi sai in yaga dama ya ke kar6ar shi”

Jin yayi shiru yasa Big Guy kuma cewa”yalla6ai zamu Iya yin magana ta waya”? Sai
lokacin Ya ɗaga mashi kai alamar eh, ajiyar zuciya Big Guy ya sauke tare da kallon
mutumin dake a gefen shi wanda suke kira Boss Man, murmushi su ka sakar ma junan
su, sun ƙwammace su yi magana dashi ta text message saboda wahala yake basu in dai
a baki zai furta masu magana.

Slowly ya ware reddish brown eyes dinsa akan screen din iphone dinsa, a tsanake
yake yin typing.

Jin ƙarar shigowar message ta wayar Big Guy ne yasa shi yin saurin curo wayar
daga cikin aljihun coat dinsa Ya duba abun da Chief ya rubuta mashi

_I need My breakfast right now_

cikin girmamawa big guy yace “I’ll bring it to you immediately,”

Ya faɗa tare da Juyawa ya fuce daga ɗakin, Boss Man daya ya rage a tsaye ya natsu
yana jiran jin me zai ce.

A lokacin da bai yi tsammani ba, muryar Chief ta katse shi”Have a seat” wuri ya
samu saman doguwar sofa din ɗakin Ya zauna
“Check your phone, I sent you a message.”
Ya bashi umarni.
Da sauri Boss Man Ya zaro wayarshi daga aljihu ya soma karanta saƙon chief din
nasu.

“Ya kake fatan ka tashi lafiya” murmushi ya saki har saida ya ɗago dakai Ya kalli
fuskarshi, Yana matuƙar yin mamakin girmama shi da yake yi duk cikin waɗanda ke
aiki a ƙarƙashinsa shi kaɗai Owais Yake gatantawa, suna mutunci da juna.

“Lafiyalou Alhamdulillah, Ina fata kaima lafiya, don na lura kamar gajiyar
tafiya bata sake ka ba” abaki Ya furta mashi maganar, shi kuma Ya bashi amsa ta
text message.

“Nagaji sosai, amma alhamdulillah, lafiyata ƙalou, Ina fata ka leƙa wurin Ƴar
taka, “
Still fuskar Boss man da murmushi yace”ban kaiga zuwa ba, Yanzu nake shirin shiga
na duba ta”

Text ya rubuta mashi”Make sure you give her a big hug. I know you’ve missed her
for a long time.”

Idanuwan shi ne suka cicciko tab da ƙwalla, tuni jikinshi yai sanyi, cikin sanyin
murya ya furta”in sha Allah, zanyi hakan, daren jiya ko runtsawa banyi ba saboda
jiran ƙarasowarku Nigeria, duk don saboda Inyi tozali da ita, sai dai ban samu
damar Yin hakan ba, saboda Bayan nayi sallar asubahi a masallaci bacci Ya dauke ni,
saida na shigo gida nake jin labarin ƙarasowar ku......” dakatawa ya ɗanyin da yin
maganar, ganin text din da owais Ya tura mashi.

“Don’t let the tears fall from your eyes, Otherwise, I won’t let you see your
daughter.” fashewa yayi da dariya jin abunda yace mishi, har saida ya ɗago ya dubi
fuskar Owais, Hankali kwance sam idanuwanshi basa akan fuskar Boss Man ɗin.

“Kana da mutunci, shiyasa muke ƙaunarka, wallahi tunda nake arayuwata ban ta6a
ganin matashin saurayi mai wadatar arziƙi, da kyau da asali, mara girman kai irinka
ba, saboda kowa naka ne, babu ruwanka ka ji daɗin rayuwarka, bazan ta6a mantawa da
alheran da kayi mun ba, nasan bazan Iya biyanka ba amma ina fata Allah Ya wadatani
da abunda zan faranta maka da shi”

Tunda ya fara magana Chief owais Ya natsu yana sauraron shi, idanuwanshi akan
screen din wayarshi.

Tambaya ya jefa mashi”What’s her full name?”

cikin girmamawa Boss Man yace”UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN” lumshe idanuwanshi yayi,
ƙamshin turaren jikinsa yana ƙara daɗaɗa hancinsa.

“She looks like you” dariya Boss Man ya saki yana duban fuskarshi Yace”tayaya
akai ka sani? Kaida baka kallon mutane, Ni nasan baku haɗu da ita ba”

Kafin Owais Ya furta magana, alert Ya shigo wayar shi, unclock button ya danna,
door room din ta zuge, Big Guy ne ya shigo da food trolley, Ya gunguro shi zuwa
gaban wooden table din gadon Owais, a saman shi Ya jera mashi kayan Lafiyayyan
breakfast dinsa, Bayan ya gama da zolaya Boss man yace”Big Guy, mutumin fa yau baya
iya cin abinci da kanshi, ko zaka mashi abaki”? Big Guy na murmushi yace”If he
gives me the opportunity to do that, I’ll do it har wanka zan dinga yi
mashi....”daƙyar Ya ƙare maganar ganin yadda Chief owais Ya ɗago da sexy eyes dinsa
akan fuskarshi, cikin jin kunyar maganar daya furta ya sunnar dakai ƙasa Yana
faɗin”afwan Sir, su6ul da baka nayi”

Fuskarshi a ɗaure Ya furta”If you ever repeat this mistake, you’ll spend the rest
of your life in prison.” Dariya Boss Man yayi jin abunda chief yace, Big Guy na
murmushi aranshi Yana fadin”Ai bazan ma ƙaraba, Yanzun ma albarkacin boss man naci”

Ajiye wayarshi yayi saman nightstand, Ya yunƙura Ya miƙe Yana faman Yamutsa
fuskarshi, Big guy dake satar kallon damtsen hannun shi sai faman jinjina kanshi
Yake Yi, dawowa yayi end bed din Ya zaune gaban glass table din dake shaƙe da
abinci.

Serving dinshi big guy Ya fara Yi, Ya miƙa mashi mug na coffee, Kafin Ya fara sha
sai da Ya fara fadin”Boss bismillah” Man na murmushi Yace”A’a yalla6ai, Ni ina na
isa In haɗa Kafaɗa dakai wurin cin abinci, kaima ka sani bamai yiwuwa bane, sannan
Ni a ƙoshe nake, Madam ta girka min abinci na cika ciki na”

Ta6e baki Chief Owais Yai, ba tare daya ƙara furta komai ba.
“Yaran fa har Yanzu bacci suke Yi yalla6ai, na lura ba ƙaramin gajiya suka yi ba,
musamman Kyakkyawan matashin nan dake acikinsu, mai kama dakai,’ yamutsa fuska
owais Yai jin ance mai kama da shi.

Fresh fruit ya soma ɗauka Yan sha, duk wani motsin shi akan idon Boss Man,
Yaron ba ƙaramin burgeshi Yake Yi ba, ƙaramin mutun da halin girma, Idan kaji
shekarun chief owais zaka sha mamaki, girman jikine kawai dashi da kuma babban
matsayi da Allah Ya bashi, uwa uba Ya iya dattako.

Boss man Yace”An kammala shirya masu breakfast dinsu, masu aiki suna can suna
aikin jera masu, Yanzu su kaɗai muke jira su farka don su ci” ya faɗa yana duban
fuskar chief, Jinjina kanshi ya ɗanyi batare daya ɗago da idona ba ya furta”hakan
Yayi kyau”

Miƙewa Boss Man Yayi”Ni zan shiga Cikin gidan, Ka ci abinci Lafiya our chief” Ya
ambaci hakan tare da Juyawa Ya fuce daga ɗakin, Ya rage saura Big guy dake saving
dinshi.

*🤍EX-PRISONERS❤*

Kwance take saman katafaren gadon ɗakin Danish, tun daren Jiya da suka ƙaraso
kowannansu aka ware mashi ɗakin shi, mutun biyu ɗaki ɗaya, Danish ne kaɗai Aka
mallaka mashi bedroom ɗaya saboda shine babbansu, Angel da Batul ɗakinsu daban,
Azeeza da jamima ɗaki ɗaya, Parveen da Hanna suma nasu daban, Gabriel da Naufal
room ɗaya, Javed da haris a ɗaki ɗaya.

Saboda Rashin lafiyar danish yasa ta gudo daga ɗakinsu ta dawo nashi tana matuƙar
jin tausayinshi batasan wani abu ya same shi, gani take kamar idan tayi nesa dashi
wani abu zai faru da shi, gown din Jiyace a jikinta red colour, tayi uban
squeezing, hatta sumar kanta a haukece take babu gyara sunsha bacci kamar ba za su
farka ba, daɗin lumbutsetsiyar katifar gadonne Ya sanya suka shagala, daga ita har
shi garkuwan, ya cire suit jacket din jikinshi Iya farar shirt dince Ya bari, da
gajeran wando fararen laps dinshi kamar ka ta6a jini ya ɗago tsabar hasken fatar,
ya ɗaura kanshi saman wuyanta, yayin da hannayenshi biyu ke a ruƙe da waist dinta,
zafin jikinshi ya daidaita bakamar da suna acikin jirgi ba zazza6i ya lullu6e shi,
Yanzu ya samu sauƙi numfashinshi na fita cikin kwanciyar hankali, Sanyin A.c din
dakin ya ƙara masu ƙaimi wurin Yin baccin nasu kamar matattu.

Mutsu mutsu ya soma yi alamar zai farka, wata irin matsiyaciyar yunwace ta
addabe shi, tun Jiya baici ko mai ba, ko ruwa bai gifta maƙoshin shi ba, Dogon
numfashi yaja idanuwanshi sunyi mashi nauyi Ya gaza buɗe su, da wata irin
kasalalliyar murya ya soma ambaton sunanta”My Angel! My Angel” badan la66ansa na
akusa da wuyanta ba da kuwa zaiyi wuya ta iya jin muryarshi.

Kamar an zungureta, a firgice ta farka tana faman zare gray eyes dinta haɗi da
ambaton sunanshi”Danish are u okey? Ko jikin ne”?

Daƙyar Ya iya janye head dinsa daga saman wuyanta Ya daura shi saman tattausan
pillow, a hanzarce ta yunƙura Ta miƙe zaune tana faman mutsistsike idanuwanta da
hannunta donta samu damar ƙare mashi kallo.

“My man, yunwa ko”? Tun kafin ma ya faɗa mata abunda Yake Ji ta riga shi faɗi.
Ɗaga mata gira yai alamar eh, murmushi ta ɗan sakar mashi har dimple dinta Ya
lotsa”Danish banga ka yaba kyan ɗakinka ba, ko da yake baka acikin hayyacinka,
saboda kana Jin Yunwa, bari naje naga ko zan samo maka abunda zaka ci, kafin in
dawo ka shiga toilet kayi wanka, sai ka canza kayan jikinka” kamar ƙaramin yaro
haka takeyi mashi magana.
Wurga eye balls dinshi yayi akan katafaren ɗakin nashi, kamar na ɗan shugaban
ƙasa tsabar haɗuwarshi.

Saukowa Angel tayi daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon shi, daɗi kamar ya
kashe ta, haƙika taji daɗin canjin rayuwar da suka samu, har ta fara tsara masu
irin rayuwar jin daɗin da zasuyi, sai dai ta ɗan shafa’a da zancen kurkukun
ƙaddara.

Tun da ta fito daga ɗakin take faman ƙwala ido tana kallon haɗuwar katafaren falon,
Cikin sanɗa take Yin tafiya kamar 6arauniya, fararen ƙafafuwanta babu takalma, bata
nufi ko’ina ba sai ɗakin su Azeeza a hankali ta zuge ƙofar ta faɗa cikinsa, tayi
mamakin ganinsu a tsaitsaye saman bed mattress kowacce ta ruƙe pillow a hannunta,
sai tsalle suke Yi suna fadin”gamu agidan daddyn Genie” dariyace ta kusa kubce mata
da sauri ta toshe bakinta da tafin hannunta, wato su duk a tunaninsu gidan daddyn
Genie ne aka kawo. yara sun zama ƴan hutu. Fitowa tayi daga ɗakinsu ta nufi ɗakin
Parveen tana shiga ta sameta a zaune tsakiyar gado, bacci yaƙi sakinta ga yunwa
tana ji sai faman yin hamma take Yi, sumar kanta kamar ta mahaukaciya duk ta
yamutsata, ta gimtse eyes dinta, hannah na akwance gefenta sai sharar baccinta take
Yi.

Ƙumshe dariya Angel tayi da sauri ta fito ta nufi ɗakin su Haris don ta duba su,
lokacin data shiga ɗakin gaba ɗayansu bacci suke yi daga shi har javed duk sun cire
suit jacket dinsu sunbar shirt da gajeran wando.

Fitowa tayi dakinsu ta nufi, ɗakinsu Naufal, adai dai lokacin Gabriel Ya fito daga
wanka, daga shi sai short, Ya ruƙe short toilet Yana tsane sumar kanshi, Naufal
kuma yana zaune saman mirror chair Ya ƙura ma madubin ido da alama gabriel din Yake
jira ya fito daga wankan shima Ya shiga.

Gaba ɗaya basu lura da Angel ba, da zolaya gabriel Yace”mutumin kyau kake kallo a
madubi naga tun ɗazu ka tasa shi agaba ko ƙyafta ido baka Yi”

Ba tare daya juyo ya dube shi ba yace”Kai nake jira ka fito daga toilet din nima
wankan nake son Yi”

Gabriel Yace”amma dai kasan toilet din nan ba kalar na prison bane, akwai ruwan
zafi dana sanyi kada kaje ka ƙona fatarka, kazo in nuna maka Yadda zakayi amfani da
shi”

Harara Naufal Ya watsa mashi”bana buƙata, nima zan Iya dakai na” gabriel na
dariya yace”bana so ka yi danasani” miƙewa naufal yai ya nufi toilet din Ya shige,
shigar shi ko minti ɗaya ba ai ba sai gashi ya fito Yana haɗe rai Ya kalli
gabriel”nifa bangane komai ba” dariya ce ta kufce ma Angel gaba ɗaya suka juya suna
kallonta, har ta juya zata gudu Gabriel Yai saurin zuwa ya ruƙo hannunta”Sister
yaushe kika shigo? Ba sallama?
“6atan Hanya nayi, ni banma san na faɗo ɗakinku ba”

Naufal Yace”kindai shigone yi mana leƙen asiri, kuma kinga abunda kikeson gani,
gashi har kina dariya” girgiza kai tayi”wallahi ni ba abunda nashigo gani, ba ri ma
in tafi” ta faɗa tare da Juyawa da sauri ta fuce daga ɗakin,

Kallon Naufal Yai”muje ko” sai da ya fara murguɗa mashi baki, kafin Ya Juya suka
nufi toilet din, Ya nuna mashi yadda zaiyi amfani da komai, kafin Ya baro shi a
cikin toilet din.

Tana cikin tafiya Muryar Batul ta katse mata hanzarinta”Angel”a firgice ta Juya
tana kallonta, buɗe baki tayi haɗi da zare idonta, ganin Batul ta fito tana faman
Yin hamma haɗi da Yin miƙa duk a lokaci ɗaya
“Yaushe kika tashi”?
“Yanzu, na duba ɗakin banganki ba ashe kina anan” tunda ta fara magana idonta ba
akan Angel Yake ba, Katafaram Falon take ƙarema kallo, kamar maijin tsoron shi, sai
faman ƙyafƙyafta idanuwanta take Yi, bakinta hada Miyan bacci, kwata kwata babu
natsuwa atare da ita, musamman sumar kanta tafi komai haukacewa.

Miƙa mata hannu Angel tayi”idan zaki bini taho mu tafi, Nima kitchen nake nema,
danish ne Yake jin yunwa” da sauri batul ta ƙarasa ta nufeta ruƙo hannunta tayi
acikin nata, Har sun ɗaga ƙafa zasu motsa kwatsam muryar Ummin america ta katse
masu hanzarin su”Where are you all going? Wa ya Baku iznin fitowa daga ɗaki”? Har
saida gabansu Ya faɗi, duk suka sha jinin jikinsu, A hankali take saukowa down
stairs, kimono robe ce a jikinta har ƙasa rigar takai mata, Tabi shape din jikinta,
takalman ƙafarta high hills ne, hair wing din dake akanta launin black ne.

Tana tafiya Hips dinta na jujjuyawa kamar ana kaɗasu, agabansu ta tsaya haɗi da
Goya hannayenta saman tudun kirjinta tana kallonsu, idan ta kalli Angel sai ta
kalli Batul, kamar wasu munafukai sunyi wuƙi wuƙi da ido, musamman Batul duk tasha
jinin jikinta, saboda mugun jin shakkarta take ji, har ƙwara Angel ashirye take da
tayi mata rashin kunya idan har ta ƙetare iyakarta.

“Ke! Meye sunanki”! Ta jefa ma batul tambayar, muryarta na rawa ta furta”BATUL”!


ta6e baki ummi tayi tare da daura idonta kan Angel”ke fa”?
Ɗaure mata fuska Angel tayi kamar bazata tanka mata ba tace”UNAISAH”
“Me kuke nema ne”?

Angel ce tayi ƙarfin halin bata amsa da cewa”ɗan uwana ke jin yunwa, shine na fito
don in sama mashi abun da zai ci”
Ta6e la66a ummi tayi”An shirya maku breakfast din ku a dining, dama ku nake jira
ku farka” ta faɗa tana nuna masu dining room da hannunta, atare su ka kai idonsu
ita da batul suka kalli ɗakin.

“Ku koma ku tada sauran ƴan uwan naku, su fito mu yi breakfast, idan mun kammala
inaso zanyi magana da ku”

Amsa mata su ka yi da toh, da sauri suka juya suka nufi bedrooms din ƴan uwansu,
tana a tsaye tana bin bayansu da kallo, bakomai yafi bata mamaki da yaran ba face
doguwar sumar kansu data lullu6e bayansu kamar hijabi, aranta ta ayyana ɗawainiya
da yaran nan ba abune mai sauƙi ba, gyaran gashin kansu kaɗai wata wahalar ce mai
zaman kanta, gashi an faɗa mata babu shige babu fuce balle tace zata kai su saloon,
kuma babu damar a gayyato masu yi din suyi masu, dole sai dai ita ce za ta gyara
su.

Daya bayan ɗaya suka bi ɗakunan yan uwansu suka shiga domin tada wadanda basu farka
daga bacci ba, saida suka taimaka ma Azeeza da jamimah suka wanke fuskokinsu da
bakunansu, tukunna suka fito daga ɗakin, Kayan jiya ne a jikinsu sai mayafin da
suka yafa akansu, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, musamman azeeza tun da tayi
tozali da ƙwan fitilun falo jikinta Ya hau yin kerma, duk ta firgice, Parveen kuwa
baki yaƙi rufuwa kamar lefen sakarai sai faman zazzare idanuwa suke Yi, saboda
yanzu ne suka samu damar ganin ko’ina na cikin gidan dakyau, Hanna kuwa daƙyar take
taka tiles din floor, da takalmi ta fito amma saboda tsabar ruɗu a hannu ta ruƙe
takalman ta rungumesu a ƙirjinta, gani take kamar in ta taka ƙasan da takalman zai
fashe, Naufal da Javed har tuntu6e suke yi garin yin kalle kalle gidan yayi matuƙar
ruɗar dasu, shi ko Haris jiki sai kerma yake yi basa ban ban, shima crystal
Chandelier din ceilling ne Ya ruɗar da shi ga sanyin A.c da yayi mashi yawa, hatta
gabriel dake da wayewa yau dai an ƙure shi, sai faman jinjina kai Yake yi yayin da
yake bin katafaren falon da kallo, abunda zai baka mamaki jamimah hankalinta kwance
babu abunda ya ruɗe ta koya tsoratar da ita, sai faman washe baki take Yi komai ta
kalla saita nuna shi da yatsa tace”menene wancan” ta ishe su da tambaya kamar
rainon ɗan jarida, Ummin america dake a tsaye bakin ƙofar shiga dining room din,
lamarin ya ɗaure mata kai, tayi matuƙar yin mamakin ƙauyancin su, gasu dai a
halitta kamar ƴa’ƴan masu kuɗi, tafiya suke yi tamkar suna jin tsoron taka floor,
sunƙi maida hankali su shigo su ci abinci, sai faman ƴan kalle kalle suke Yi kamar
wuyansu zai cire.

Mutum ɗaya ce babu acikinsu, Angel da ta tafi bedroom ɗin Danish, Batul dai tana
atare da su Haris.

Gyaran muryar da ummi tayi masu ne ya janyo hankalinsu ga kallonta.


Da hannu ta nuna masu ƙofar shiga”ku zo ku shiga” ba tare da sun tanka mata
ba, suka nufi ɗakin cin abincin, koda suka shiga sai suka koma suna bin ko’ina da
kallo, Parveen ce ta furta”La’ha’ilah! Wannan duk namune”? Ta jefa tambayar tana
nuna kayan breakfast din dake a jere saman zungureran table.

Ummi ce ta bata amsa da cewa”naku ne, kowa ya samu wuri ya zauna” su parveen anga
banza, tuni taja kujera ta zauna, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya samu wuri ya zauna,
sai faman baza ido suke Yi suna bin komai da kallo, jamimah tana jinjina kai
tace”Yau zamu ci daɗi, wallahi munji daɗi muma mun zama ƴan gayu, gidan daddyn
genie akwai abinci da kayan wasa”

Azeeza taƙi ɗagowa dakai, ta ƙanƙame jikinta saman kujera, ita kwan fitila ne
damuwarta, na ɗakinsu bai kai na falo dana dining room girma ba, sun hanata sakat,
Gabriel dake kallonta cikin muryar raɗa ya ambaci sunanta”My azeeza” ɗagowa tayi da
ido tana kallon shi sai faman yamutsa fuska take Yi
“Meke damun ki”?
Da index finger ta nuna mashi saman ceilling ba tare da ta kalla ba, muryarta ƙasa
ƙasa tace”zai Iya faɗowa saman kanmu”

Murmushi ya sakar mata”ki kwantar da hankalin ki, ba zai ta6a faɗowa ba, idan ma
zai faɗo sai na tare maki shi, hakan yayi maki”? Sai lokacin ta ɗan saki murmushi
jin abun da yace ta jinjina mashi kai alamar eh.

Parveen sai faman haɗiyar yawu take yi ta ƙosa su fara ci, sai dai sun gaza sanya
hannu ganin yadda Ummin america ta tsare su da ido ko kyaftawa ba tayi, tana daga
tsaye bakin glass door din dakin, ta lura basu cika ba shiyasa ta tsaya tana jiran
sauran su ƙaraso don su fara ci.

“Menene wannan abun” jamimah ce tayi tambaya tana nuna wata roba
Kallon robar Gabriel yai a jikinta an rubuta Honey.

“Zuma ce a ciki, kin ta6a sha”? Girgiza mashi kai tayi alamar a’a, ta kuma nuna
dafaffan ƙwai tace”wannan luluyayyan abun fa”? Harara ya dan jefa mata”Ƙwai ne, pls
ki daina yi min tambaya baki ga ana kallon mu ba”? Ta6e mashi baki tayi”to aini
inason in sani ne ko,” har tayi shiru can kuma kamar an cikare ta tace”Gabriel kace
ƙwai ne, to shima kamar ƙwan fitila mai bada haske Yake”shiru yayi yana kallonta ba
tare daya furta komai ba,

(abun da yasa take tambayarshi saboda bakomai ne suka sani dangane da nau’ikan
abinci, ko a kurkuku snacks da nama suke ci da kayan marmari, haka zalika a asibiti
da suka zauna bakomai ne suka sani ba yawanci duk kalar abunda suke ci a prison ne,
yau sunci karo da wasu nau’ikan abincin dana sha wanda basu ta6a yin tozali da su,
shiyasa jemimah ta tsare shi da tambayoyi kamar ƴar jarida)

Batul dai sai satar kallon ummi take yi ita kanta ummin ta lura da kallon ƙurullan
da Batul take Yi mata, shiyasa ta tsaida idonta akanta, tunda tayi hakan batul ta
saddar da kanta ƙasa cikin jin kunyarta.

Abun da Ya faru, Lokacin da suka kammala tada ƴan uwansu Angel ta nufi ɗakin
Danish, shigarta keda wuya ta taras dashi atsaye gaban mirror Yana faman yin haki
Ya dunƙule tafukan hannayensa kamar wanda zai yi dambe, Kafin ta buɗe baki ta
tambaye shi lafiya, idanuwanta suka sauka akan madubin daya fasa, ƙwaƙƙwaran naushi
ya kai mashi gaba ɗaya ya zube ƙasa ya tarwatse.

Rass taji gabanta Ya faɗi, a tsananin tsoroce ta furta”Na shiga uku! danish
meyasa zaka fasa masu madubi? Kasan kuwa tsadar dake gare shi? Wai meke damunka ne?
So kake kaja mana bala’i daga zuwa gidan mutane har ka fara yi masu 6arna”
hankalinta atashe tayi maganar tana duban bayanshi.

A hankali Ya jiyo yana kallon cikin sanyin murya ya furta”mutun na gani aciki
Yana kallona, shiyasa na naushe shi” Zaro ido waje tayi can kuma ta tuntsire da
dariya hada dafe ciki, ɗaure mata fuska yai ganin tana yi mashi dariya.

Nuna shi tayi da yatsa tana fadin”mutumin da ka gani acikin madubin kaine ba wani
ba, ai saida naso in nuna maka kanka a mirror amma kaƙiya, ka nuna baka son kallon
shi gashi nan Yanzu ka fasa masu madubi mai tsada, Ni dai ba ruwana” ta faɗa
fuskarta da murmushi.

Kallon rashin fahimta yake binta da shi, ya rasa gane me take nufi, kamar bata
fahimci abunda ya faɗa mata ba.

Gudun kada wani ya shigo ya taras da 6arnar da Danish yayi yasa tayi saurin
juyawa tana yan dube dube cen idonta ya sauka kan wani abu yayi mata yanayi da
tsintsiya da sauri ta ɗauko ta tattara broken glass din ta turasu kasan gadon shi
dan bataga dust bin a dakin ba ajiyar zuciya ta sauke

Kafin ta ɗago tana dubanshi”kai kaɗai muke jira, zamu yi break fast, ka shiga
toilet ka wanke face dinka da bakinka, idan mun gama cin abincin sai kayi wankan”
toilet door Ya nufa, har ya kusa kaiwa ƙofar ta tuna da madubin toilet, da karfi ta
furta”dakata danish” cak ya tsaya da tafiya, da sauri ta nufi ƙofar toilet din ta
buɗe ta shige ciki, towel ta ɗauko ta rufe madubi, saboda tsaro tasan zai Iya Fasa
shi kamar yadda ya fasa na room dinsa.

Fitowa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya ta dubi fuskarshi”nasan idan ka shiga
ciki zakaga towel na lullu6e wani abu dashi, kada ka buɗe shi, madubi ne bana so ka
fasa shi kamar yadda ka fasa na ɗakin ka, Idan ba haka ba zasu ce saika biya su ne
kuma kaga bamu da kuɗi, kai ba kama san menene kuɗi ba, Ni zaka bari da aikin
biyansu” ta faɗa tana yamutsa mashi fuska, bawan Allah yayi tsaye yana kallonta.

“Ina jiran ka, kada ka daɗe ka yi sauri ka fito suna jiran mu”

Amsa mata yai da toh, kafin ya bude kofar ya shiga, Ƴan mintuna ya fito daga
ciki, har yayi brushing teeth dinsa, daga kasa har sama take bin shi da kallo, a
ganinta basai ya tsaya sanya kaya ba tun da ba wanka yayi ba, Ruƙo hannun shi tayi
acikin nata kamar wani ƙaninta”muje ko”? Ta faɗa tana ƙoƙarin janshi.

Adai dai lokacin da suka sauko falon, ƙofar shigowa cikinsa ta zuge a hankali,
atare Angel da Danish suka juya baya jin takun tafiyar mutun.

Basu san wanene ba, amma saida taji gabanta Ya faɗi, ganin kakin dake a
jikinshi na baƙaƙen Kaya, kuma ya rufe fuskarshi da face mask, 6oyewa tayi bayan
Danish ta ƙanƙame shi tana leƙen mutumin da ke tunkaro su.

Bugun zuciyarta na ƙaruwa kamar zai fasa ƙirjinta.


Miƙa ma Danish hannu yai da niyar su gaisa, Danish Yaƙi bashi hannu saboda rashin
yardar da shi, gyaran murya ya ɗanyi kafin ya soma magana a tsanake”zaku Iya kira
na da Boss man, ina ɗaya daga cikin masu kula da ku,” ya faɗi hakan ne don su saki
jiki da shi.

Ajiyar zuciya Angel ta sauke, jin muryarshi ta kamilallun mutane.

Dawowa tayi daga gaban shi ta tsaya tana dubanshi, ido cikin ido suke kallon juna
ba tare da ƙyaftawa ba.

Tsawon mintuna kafin ta furta”Ina kwana,” ya amsa mata”lafiyalou Angel, kin tashi
lafiya? Ya kuma gajiyar tafiya”
Tace”lafiyalou, gajiya tabi jiki, mun gode da kulawa” da alamun jin daɗin
maganarta ya furta”Naji daɗin ganinki da ranki da lafiyarki, ina fata baki da wata
damuwa” maganarshi taɗan so ta ruɗar da ita, amma sai ta basar tace”nima haka” da
ƙyar ta furta ganin irin kallon da yake binta dashi, duk saita sha jinin jikinta,
ta rasa gane kallon menene yake yi mata, dauriyace kawai yake yi, yaso ace zai iya
bayyana mata kanshi a yanzu sai dai bazai yiwu ba.

“Ciki zamu shiga Ni da Danish, suna jiranmu a dining” ta fada don ta samu damar
guduwa daga kallon da mutumin yake binta da shi.

Ɗagowa yai da ido ya dubi fuskar danish, har saida yaɗan ji gabanshi ya faɗi
ganin yadda ya ɗaureta tamau babu annuri, dama tunda ya shigo falon yake mamakin
kyawunshi da body structure dinshi don shi sai yanzu ya samu damar ganin shi,
abakin abokan aikinsa yaji suna zuzuta kyan yaran da kamanninsu da Chief dinsu.

“Ɗan uwan naki bai magana ne? Yaƙi bani hannu mu gaisa” murmushin yaƙe tasakar
mashi”rashin sabone, Yana da wuyar sha’ani amma idan kuka saba zai saki jiki da
kai”

Jinjina kai boss man yai”okey, mu shiga ciki, Nima can zanje” a fakaice ta
yamutsa fuska, aranta ta ayyana wannan mutumin zai takura mata ga shi da kallon
tsiya kamar zai lashe mutun” a fili kuma taja hannun dashi suka nufi dining room
din, Boss man na abiye da bayansu, kwata kwata babu alamun ƙauyanci atattare da
Danish, sai dai jefi jefi yake satar kallon kayan alatun dake acikin katafaren
falon.

Lokacin da suka shiga dining room din da sallama abakunansu, gaba ɗaya hankulansu
Baful Ya dawo kansu, Ummin america tuni ta samu wuri ta zauna, ganin Angel da suka
yi da danish nan fa suka fara sakin murmushi kamar wasu zautattu, kujera taja ma
danish ya zauna Yana fuskantar ummi, ita kuma Angel ta zauna daga gefen shi, Sai
daga bisani su Gabriel suka lura da Boss man daya shigo, kallon juna suka yi da
alama sun ɗan tsorata da ganinshi saboda dressing din jikin shi yayi shige dana
Giants din kurkukun ƙaddara.

Sai da Angel tace”ku gaishe shi, sunan shi Boss man, Yana ɗaya daga cikin waɗanda
zasu dinga kula da mu” har suna haɗa baki wurin furta mashi gaisuwa, a mutunce ya
amsa masu yaji daɗi yadda Angel tayi masu bayanin wanene shi.

Ummi ta dube shi awayance tace”barka” ya amsa mata da”yawwa ya kike fatan kin
wayi gari lafiya” a yayin da yake ƙokarin zama gefen kujerar dake a kusa da ita,
wadda ke fuskantar Angel, don yaji daɗin kallonta.

Ummi tace “Lafiyalou,” daga haka ta miƙe ta soma yin serving dinsu, a plates ta
zuzzuba ma kowannansu abinci, ta dauki cups ta tsirara masu tea dake acikin flask,
Bayan ta gama ta koma ta zauna”

Yatsun hannun parveen har karma suke yi wurin ɗaukar cup din tea, duka ta kur6e
shi, ta soma cin wainar kwai hannu baka hannu ƙurya.

Batul kuwa wani sabon salon ƙauyanci, tunda ta dafi plate din noodles tasha
romo da kayan haɗi, da hannu take ɗaukar indomie din tana Jujjuyata kafin ta turata
abaki, ɗaya bayan ɗaya Angel ke kallonsu, Kunya duk ta kamata, koda ta daura
idonta kan Jamimah robar zuma ta ɗauka ta dinga matsata a tafin hannunta ta sanya
harshe tana lasa hada tanɗar baki, Angel ji take kamar ta fasa ihu.

Ummin america da boss man duk suna kallonsu sai faman sakin murmushi suke Yi.

Gyaran murya ya yi masu jamimah ta dago tana kallon shi yace”kidaina shan zumar
ita kadai, ga mahaɗinta nan ki zuba asama sai ki ci” ya faɗa yana nuna mata plate
din pancakes da robar yougurt’ washe mashi baki tayi tana fadin”wallahi zaƙi
gareta, kunnuwana har motsi suke yi” gaba daya suka sanya dariya, Ummi kamar zata
shaƙe tsabar dariya, Angel dai abin duniya ya isheta, ita ala dole mai aji kada a
zubda mata mutunci su kuwa ba ruwansu bayin Allah basu san ma menene ƙauyancin ba.

“Malama, ki dauki spork da shi zakiyi amfani ki ci noodles din ba hannu ba” ummi
ce tayi maganar tana nuna batul da spoon din hannunta, bata Iya cin abinci da
cokali ba cos sunfi sabawa da hannu, jiki asanyaye batul ta ke faman ƴan kame kame
ta rasa ina zata ɗauki cokali, Angel ce ta ɗauko shi ta miƙa mata, ta kar6a ta
tsoma shi cikin indomie din batasan yadda zata kwasota ba, ganin yadda ummi take yi
masu dariyar shaƙiyanci yasa ran Angel ya 6aci ta haɗe rai, muryarta aƙula tace da
batul”idan bazaki Iya ci da shi ba, Ki ajiye shi ba dole” kallonta ummi tayi aikuwa
ta galla mata harara, mamaki ya kama ummi ganin abun da Angel tayi mata.

Batul kuwa ta ajiye cokalin taci gaba da ci da hannunta,


Maganar Angel ta burge boss man, sai ƙara dubanta yake yi, abinci yake ci amma
hankalin shi na akanta.

Haris dai tun da ya dafi chips babu maijin motsinshi, sai idan anyi magana ya
ɗago da ido Ya dube su.
Mutun ɗayane baya cin abinci, Ya rasa sukuninsa, saboda mutun biyu dake zaune
acikinsu, bayason baƙuwar fuska, uwa uba ummi dake ta kallon shi jefi jefi take bin
shi da kallo kamar zata haɗiye shi.

Sam Angel bata lura da yanayin da yake aciki ba, sai da Boss Man ya furta”meyasa
baka cin abinci ne”? Tukunna ta ɗago ta dubi Danish don ta gane dashi yake magana.

“Bakomai yake iya ci ba, danish me kake son ci”? Ta jefa mashi tambayar, shiru
bai bata amsa ba, kamar tayi magana da kurma.
Ummi tana yamutsa fuska tace”ai na lura kamar mune muka takura mashi, ƙwarama ka
saki jikin ka, saboda atare zamu cigaba da rayuwa acikin gidan nan”

Boss man yace”baya son baƙin fuska ne, amma tunda naga yafi sakewa da shi, Ki
jaraba bashi wannan muga idan zaici” yai maganar tare da ruƙo plate din farfesu ya
miƙa mata, bayan ta kar6a ta furta mashi”thank u” ta tura plate din agaban Danish.

Cikin muryar raɗa tace”pls ka saki jiki ka ci, tunda gani atare dakai, banason
kana damuwa” jinjina mata kai yai alamar toh, duk don ya saki jikin shi yasa ta
sanya hannu a plate din ta soma ci shima ya sanya hannun shi suka cigaba da ci
atare.
Sun dauki lokaci suna cin abincin, sunyi kulu wash rabu hani’an kafin daga bisani
ɗaya bayan ɗaya suka fara miƙewa,

Masu aikin gidanne suka tattara kayan abinci, bayan sun kwashe komai suka gyara
dining room din tamkar ba’a ta6a 6ata shi ba.

Falo suka koma, kowannansu ya zamu wuri saman sofa ya zauna, kamar yadda Man Ya
basu Umarni, yana daga zaune shida ummi suna fuskantar su, sanyin A.c sai ratsa
fatar jikin su ya ke.

Sun natsu suna jiran jin me zaice”da farko dai Ina yi maku barka da zuwa gidan
nan, ina fata kunji daɗin kasancewa acikin shi” ya faɗa yana dubansu.
Amsa mashi suka yi da eh, yace “good, ina fata zaku bamu haɗin kai, mu zauna
peacefully babu faɗa babu cacar baki,” ɗaga mashi kai sukayi alamar eh.

Ya ƙara da cewa”na fahimci bakomai ne kuka sani ba, to duk abunda baku gane ba
kada kuce zakuyi gamon kanku, hakan zai iya haifa maku matsalar da bama fata, idan
kunga abu kunaso kuyi amfani dashi baku san yarda akeyi ba, Ga auntyn ku nan yai
maganar yana nuna ummi dake zaune saman sofa ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya.

“Ku tambayeta zata koya maku, kada kuji shakkar komai, ku ɗauke mu tamkar iyayenku
ko yayyanku, ina fata kuna jina”? Jinjina mashi kai su ka yi, Angel tayi shiru tana
kallonshi, muryarshi ta tsaya mata aranta, ji take kamar tasan me irin muryar sai
dai takasa gano komai.

“Zaku Iya tambayar Ƴar uwarku Angel itama, don na fahimci kamar tafi ku sanin
wasu abubuwan” amsa mashi su ka yi da toh.

“Sannan duk abunda kuke buƙata ta 6angaren aike ni zaku yi ma magana, in sha Allah
zanyi maku shi, Idan time din sallah yayi zanzo in tafi da mazan dake acikin ku
muyi sallah akwai wurin da muke yin ibada acikin gidan nan, ina fata gaba ɗayan ku
musulmai ne” ya faɗa yana dubansu
Parveen tai karaf tace”banda Danish da Gabriel sunƙi kar6ar shahada” zaro ido ya
ɗanyi yana duban fuskar Danish daya haɗe rai babu annuri.

Gabriel Yace”nifa ƙarya take yi min, Nima musulmin ne”

Da zolaya boss man yace”idan har dagaske kai musulmi ne to ya akai naji sunanka
bana musulmai ba”?sunnar dakai ƙasa Yai yana faman sakin murmushi.

Angel tace”nice namanta ban biya mashi shahada ba, ya faɗamin yana so ya musulunta
shima” jinjina kai boss man yai, ya dawo da dubanshi gareta”shifa danish? Wani
addini yake yi”?

“Bashi da addini” dafe kai boss man yai”Eyyah banji daɗin jin hakan ba, kuma bashi
da ra’ayin ya musulunta kamar Gabriel”? Girgiza mashi kai Angel tayi”bayasoma anayi
mashi maganar ai, ranshi 6aci yake yi, shiyasa muka ƙyale shi”

“Okey, kada hakan ya dameku, in sha Allah asannu zamuja ra’ayin shi” ta6e baki
Danish yai jin abunda boss man yace.

“Gabriel na dawo gareka, tunda kana so ka musulunta, babu buƙatar 6ata lokaci,
Zan biya maka kalmar shahada saika maimaita da kyakkyawar niya” murmushi gabriel
yasaki bashi ba hatta sauran ƴan uwanshi sunji daɗi, ba tare da 6ata lokaci ba, Ya
biya mashi kalamar shahada, wani irin daɗine ya lullu6e su Angel, shima Gabriel din
daɗin yake ji sai faman washe baki yake yi.

“Ina taya ka murnar shiga addininmu, ko kana buƙatar na canza maka suna? tun kafin
gabriel ya bashi amsa su Batul su ka yi saurin cewa”Eh wallahi acanza mashi, sunan
shi wahalar faɗi yake yi mana,” dariya boss man yasaki jin abunda suka ce.
“Okey, daga yau zamu dinga kiranshi da.....”bai ƙarasa sunan ba yai shiru yana
kallon fuskar Gabriel duk sun ƙagara da suji wani suna za’a sanya mashi.

“SAJEED” wani irin ihun farin ciki suka saki, Sunan yayi bala’en yi masu daɗi
musamman Azeeza.
“Ina fata sunan yayi maka”? Jinjina mashi kai Gabriel yai”eh, nagode sosai”
Boss man yace”okey, daga yanzu sunan da zaku dinga kiran shi da shi kenan wato
Sajeed, Kefa Angel meye asalin sunanki” farfari tayi mashi da ido kafin ta bashi
amsa da cewa”Unaisah”
Tamkar baisan sunan ba yace”wow suna mai daɗi, mai zai hana kema mu dinga kiranki
da asalin sunanki” zumbura mashi baki tayi ba tare data furta komai ba, tana son
asalin sunanta sai dai tafi son sunan Angel saboda daddynta ne ya za6a mata shi.

“Dan Allah Angel ki amince mu dinga kiranki da Unaisah Yafi daɗi Allah” Batul ce
tayi maganar, Hannah tace”nima nafison Unaisah din yana da daɗi”
Haris ma yace”nima shine za6ina, Unaisah”
Ta6e baki Angel tayi tare da kallon fuskar Danish don taji me zaice, batasan boss
man na kallon ta ba, Ya fahimci tafi ƙaunar Danish akan sauran ƴan uwanta, saboda
yadda take bashi muhimmanci.

Da ido tayi mashi alamar ta amince da sunan ko kuwa”? Ɗaga mata gira yai alamar
eh.
Dawo da dubanta tayi akan fuskar Boss man”shikenan na amince, adinga kirana da
Unaisah”
Murmushi ya saki ba tare da sun gani ba saboda mask din fuskarshi.
Javed ne yace “um sallah ma Angel ta koya mana amma bamu taba yi ba dama tace in
muka zo zamu rinqa sallah da karatu”

Jinjina kai yayi tare da fadin “karku damu zamu rinƙa karatu tare in sha Allah
komai zaku iya wanda ya shafi addinin muslunci” Da alama sunji dadin maganar
Jemimahh tace”wai kai ba zaka cire abun fuskarka ba”?
Girgiza mata kai yai”a’a” tace “to meyasa baka son mu ganka? Ko dai mummuna ne
kai baka da kyau”? Dariya ce ta kubce mashi.

Azeeza tace”bakya jin magana jemimah ina ruwanki da shi? Ke komai sai kin nuna
zaƙewa” harara jemimah ta watsa mata”Ni ki ƙyale ni,” ta faɗa tana duban shi”dan
Allah ka cire muga fuskarka”
Javed yace”nima inason naganka, tun da kace atare zamu rayu agidan nan, please ka
cire mu ga fuskar ka.

Girga mashi kai yai”Ku yi haƙuri ba yanzu ba, tunda muna atare wata rana zaku
ganni”
Angel tace”babu komai, Allah ya nuna mana lokacin, Ni sai na ke jima kamar nasan
muryarka don dai kace ba yanzu zaka buɗe fuskarka ba ni kuma da saina gane wanene
kai” hakanan ta faɗa bada wata manufa ba, tasan batasan shi ba.

Murmushi yai ba tare daya tanka mata ba, kallon Ummi yai, tun da ta zauna tana
sauraron su bata ce komai ba
“Ba abunda zaki faɗa masu ne”?
Yamutsa fuska tayi kamar bata son furta magana tace”naso yau in taimaka masu su
gyara kansu, amma nabari sai zuwa gobe ko jibi, idan na ƙara hutawa”

Yace”okey, ku tashi mu tafi inaso zan nuna maku ko’ina na cikin part dinku, duk
abunda kuka gani wanda kuke neman ƙarin bayani akanshi Ni zaku tambaya” suka amsa
mashi da toh.
Miƙewa sukayi Ummi ma ta miƙe don tana son itama ta ƙarema ko’ina na part din
kallo, cikinsa da wajensa.
Yinin Ranar sunsha yawo, Sunga abubuwan ban mamaki dana Al’ajabi, ido ya samu
abinci, kamar karsu dawo cikin gidan, Boss man yasha tambayoyi kamar ƴan jarida,
duk abunda basu gane ba sai sun tambayeshi ba ƙaramar wahala yasha ba, itama ummi
tana taimaka mashi wurin amsa masu tambayarsu, duk yawon da suka sha basu leƙa
wajen gidan ba, kuma basu shiga sauran part din ba.

*JOS CITY*
Idan muka koma 6angaren Alhaji ubaid, tunda garin Allah Ya waye da sassafe Benazir
ta farka tana sambatu akan mijinta da ƴarta, Alhaji ubaid Ya jira kiran Dr.shureim
sai dai shiru, har kiran layin wayarshi yai amma bai ɗaga ba, ya kira Alhaji musa
akaci sa’a kiran ya shiga kusan sau goma tana ringing ba’ayi picking ba, gashi
lokaci yana ta tafiya babu alamun zuwan Shureim, daga bisani suka kira likita domin
duba lafiyar benazir, bayan ya duddubata ya faɗa masu cewa lafiyarta ƙalau, sai dai
akwai abun da ta ƙwallafa rai akanshi yaji tana fadin mijinta da ƴarta yace to kada
su kuskura suce zasu faɗa mata zancen babu su, don a halin da take aciki yanzu
bazata Iya jurewa ba, zata Iya samun ta6in hankali, zaifi suja baki suyi shiru,
sannan suci gaba da kwantar mata da hankali har zuwa lokacin da zata samu natsuwa
sosai, tukunna su faɗa mata, sunji dadin shawarwarin da likitan ya basu, bayan
tafiyarshi cikin ikon Allah, Benazir ta dawo hayyacinta a lokacin da basu yi
tsammani ba, ganin Iyayenta a gefe da gefen gadon da take akwance yasa ta rushe da
kukan farin ciki tana ambaton sunayensu haɗi da roƙon yafiyarsu akan babban laifin
da ta aikata na guduwar da tayi ba tare da sanin su ba, tayi mamakin jin suna
kwantar mata da hankalinta, sukace su basu ruƙeta aransu ba, sun yafe mata, ta
daina kuka komai ya riga daya wuce, tuna baya baida amfani tun da ya riga da ya
faru, ƙaddarace da babu wanda ya isa ya canza ta, haƙiƙa taji daɗin kyakkyawar
tarbar da ta samu awurinsu tayi tsammanin zasu koreta ne idan sun ganta, saima suka
koma suna lallashinta haɗi da tarairayarta, abinci ma abaki hajiya layla ta bata
shi, duk bayan ƴan mintuna sai ta tambayesu ina mijinta da jinjirar data bari a
cikin kwamin wanka? tana son tagansu, idan suna agida dan Allah su taimaka su kaita
wurin su, hajiya layla ta bata haƙuri da cewa sunyi tafiya basa a ƙasar amma tana
da tabbacin sun kusa dawowa, sai lokacin tace toh ita yarinyar ta rayu? Waye ya
rene ta harta girma? Kuma ya sunanta”?
Hajiya layla tace”ta rayu mana, kyakkyawar budurwa ta ɗauko hasken fatarki,
kamannin fuskarta ne dai ta ɗauko na daddynta, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi
ba, tana ta faman sauke ajiyar zuciya tace”baki faɗa min sunanta ba? Kuma tasan ni?
An faɗa mata sunan mahaifiyarta? Kuma Kuna nuna mata hotona”? Shiru hajiya layla
tayi don batasan amsar da zata bata ba, ita kanta ba zumunci take yi da tajuddeen
ba, saboda bada son ranta ya auri Benazir ba, shiyasa ko zuwa gidan bata ta6a yi
ba, tun lokacin da suka koma dubai da zama, a hotone ma ta ta6a ganin Angel din,
taji nauyin amsar da zata ba benazir, daƙyar ta Iya furta mata sunanta Angel, tana
faman murmushin yaƙe tace ai tasanki ya za’ai mu ƙi nuna mata hotonki, duk in
tajudden ya kawota gidan nan sai mun nuna mata hotunanki, Yarinyar tana sonki
sosai, kullum maganarta ina mamanta take? Yaushe zata dawo? Meyasa kika tafi baki
waiwaye ta ba’ jin hakan yasa benazir ta fashe da kuka, Hajiya layla duk tasha
jinin jikinta, fargabarta ranar da Allah zai haɗa benazir da ƴarta idan har tana
araye tabbas zaiyi wuya yarinyar ta amince da ita, ga kuma ƙaryar data faɗa mata.

Cikin shessheƙar kuka benazir tace”amma dai baku fada mata a yanayin da na tafi
nabarta ba ko”? Hajiya layla tace eh bamu faɗa mata ba, mun dai ce mata kin 6ace ne
ba’asan inda kika tafi ba, to dayake yarinyar tana da tawakkali kuma tana samun
kulawar tajo da kuma kulawar da muke bata hakan bai dameta sosai ba”
baiwar Allah benazir jikinta duk yai sanyi, tace Ina aneelerh da mijinta”?
Hajiya layla tace ai mijin aneelerh baya nan shima tare suka yi tafiyar, ta matsa
lamba akan tana son akaita gidansu Aneelerh don taganta, Alhaji ubaid ya sanar da
ita cewa ai basa garin jos sun koma abuja da zama, badan taso ba ta haƙura, damuwar
hajiyar laila ɗaya kada tace su nuna mata hoton ƴarta saboda babu maishi acikinsu,
har ƙwara Alhaji ubaid wata’ƙil asamu hutunanta na yarinyata saboda yana son
yarinyar, cikin ikon Allah benazir bata tambayesu game da hoton Angel ba, saboda
halin damuwar data shiga gani take kamar bazata ta6a ganin mijinta da ƴarta ba, duk
da mommynta ta kwantar mata da hankalinta.
Masu gadin gidan kusan sau uku suna shigowa cikin gidan domin duba lafiyar benazir,
duk sun damu da ita, haka zalika zainab takasa samun sukuni duk bayan ƴan mintuna
saita leƙo ta dubata, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba ganin yadda kowa ya damu
da ita.
Tana akwance saman gadonta, hajiya layla tana a gefenta, a lokacin Alhaji ubaid
Ya koma dakinshi, damuwar duniya ta ishe shi, tun da ya jaraba kiran layin shureim
dana Alhaji ubaid basu ɗaga ba, ya rasa sukuni, sai faman yin zarya yake yi acikin
ɗakin shi, kaf family dinsu babu wanda yasan da dawowar benazir, saboda bai sanar
da su ba, hatta mutanan da suke zumunci da su bai faɗamawa ba, saboda mai gemu ya
basu shawarar su dan jinkirta tunda ba’asan wanene yai silar yi mata asirin ba,
zasu Iya ƙara cutar da ita idan suka ji cewa tana araye kuma ta dawo gida, da ace
Iyayensu na araye da kuwa sune mutun na farko da zai fara sanarmawa donsu taya shi
murna sai dai babu su, mutum biyu ne yafi yarda dasu ƙanin shi Alhaji musa sai
ƙanwarsu autar gidansu Hajiya Laurat, second wife din mai girma sharafuddeen
obinna, itama ya jaraba kiran layin wayarta bata yi picking ba, abun duniya duk ya
ishe shi.

tunda tayi wanka ta canza kayan jikinta zuwa rigar shan iska bata ƙara saukowa
daga saman gado ba, ta tsare hajiya layla da tambayoyi
“Mommy shifa yaya shureim ko baya kasar ne”?
“Yana agidan uncle dinki”
“Baku faɗa mashi na dawo ba ne?
“Mun faɗa masa tun jiya da daddare shima yayi farin ciki hada kukanshi, yace ma yau
zaizo saboda ke’ murmushi tasaki”naji dadi Allah ya kawo shi lafiya, nayi missing
din yayana”
Hajiya layla ta amsa mata da ameen.
Kafin benazir ta ƙara furta wani abu, Alhaji ubaid ya shigo da sallama abakinshi,
atare suka ɗago suna kallon shi, da sauri benazir ta miƙe zaune tana ambaton
sunanshi
Murmushin yasakar mata kafin ya zauna daga gefen gadon yana dubansu yace”Bansan
meya faru ba, Ina ta kiran layin shureim dana musa babu wanda ya ɗaga acikinsu, Har
laurat na jaraba kira itama bata ɗaga ba” kafin wani ya furta magana acikin su ba
zato ba tsammani, sautin ringing din wayarshi ya daki kunnuwansu, hajiya layla
tace”wata’ƙil wani daga cikin su ne yake kiranki” da sauri ya ciro wayar daga
aljihun shi ya duba sunan me kira, murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi
“Wanene”? Layla ce ta tambaya ganin yadda ya saki fuska
“Musa ne Ke kira” ya faɗa tare da picking call din Ya kara a kunnan shi
Saboda ji da kai na Alhaji musa sai da Ubaid Ya fara yi mashi sallama tukunna ya
amsa mashi da cewa”wa’alaikum salam, ina kwana yayana fatan kun wayi gari lafiya”
Alhaji ubaid na faman washe baki yace”lafiyalou, ya iyalin naka”?
“Suna lafiya” atakaice ya amsa mashi, tun da ubaid ya fara waya, layla da benazir
suka zuba mashi ido suna kallon shi duk da basa Iya jin me alhaji musa yake fadi
“Shureim bai faɗa maka zancen dawowar benazir ba”? Ya tambaya ne don yaji baya da
niyar yi mashi maganar
Da gadara Ya furta”ya faɗa min, tun ɗazu da safe, na tayamu murna, Ina fata tana
lafiya”
Alhaji ubaid yace ai gatanan ma zaune kusa dani, Ko in bata wayar kuyi magana ne”?
Da sauri yace”No need, basai munyi magana da ita a waya ba, dama dalilin da yasa
na kira naga missed call dinka ne, ɗazu da safe shureim ya shirya zai taho nan jos,
Ni na hana shi, nace mashi ya bari zanyi maka magana kuzo nan abujan gidana” da
mamaki Alhaji ubaid yace”amma dai wasa kake yi min ko? Tayaya zakace min in kwaso
iyalina inzo gidan ka? Ni dakai waye ya dace yazo gidan wani? ai nayi tunanin idan
na fada maka dawowar benazir jiki na rawa zaka kwaso iyalinka kuzo nan domin tayani
murna sai kuma naji akasin hakan”
Alhaji musa yace”bazan Iya zuwa jos din bane, saboda Ina da ayyuka dayawa da
zanyi, shiyasa nace kuzo nan ɗin,”
Mamaki da al’ajabi ne akan fuskar hajiya layla, don taji martanin da alhaji ubaid
Ya bashi.
“Baikamata kace min haka ba, yanzu ayyukanka har sunfi ganin ƴata da za ka yi
muhimmanci?
Babu alamun damuwa a muryarshi yace”yaya kasan banason jan magana, meye aciki don
nace kazo gida na? Laifine? Alfarma nake nema bawani abuba, idan ba zaka yi min ba
zan aje waya”
Gyaɗa kai alhaji ubaid yai”shikenan, zamu fidda lokaci mu shigo abujan”
Ya amsa da yawwa, sannan bana buƙatar ku zo a mota, Ni zan shirya maku komai na
tafiyarku” amsa mashi yai da toh, daga haka Alhaji ubaid yayi rejecting call din,
yana mai mamakin Halin Alhaji musa.
“Me ku ka tattauna ne”? Layla ce ta jefa mashi tambaya
Muryarshi a raunace ya furta”yace bazai samu damar zuwa nan ba, shine ma ya hana
shureim zuwa saboda yafi son muje can gidan shi”
Ta6e baki hajiya layla tayi”shine kai kuma sai ka ce mashi zamu samu lokaci muje
can din ko?
Jinjina mata kai yai alamar eh, masifa ta soma zazzaga mashi”kasan Allah babu inda
zamuje sai dai kai daya gama asirce ka kama hanya ka tafi,Ni ban ta6a ganin mutun
mara kunya irin shi ba, yarinyar ta 6ace tsawon shakaru sai jiya tsakar dare ƙarfe
shabiyu tadawo bata ahayyacinta shine zaice mu kwasa mu tafi gidansa saboda muke
son yaganta? Kwata kwata bashi da tunani kuma baida hankali, kaida kakeyi mashi
biyayya gayanan shi bai damu da ƴarka ba,
...” tun da tafara faɗa, jikin benazir yai sanyi duk sai taji ba daɗi, Cikin sanyin
murya tace”mommy dan Allah ki yi haƙuri, kada hakan ya dame ki, Ni banga laifin shi
ba saboda ai ni na gudu da kaina ba korata akayi ba, wata’kil Yana jin haushin
abunda na aikata shiyasa yace muje can....”
Katseta hajiya layla tayi”benazir ba abunda kike tunani bane, mutumin nan baya
ƙaunarki, saboda bai damu dake ba, tun lokacin da kika 6ace bai ta6a magana akanki
ba, Mune kaɗai muka damu dake munyi nemanki har mungaji mun fidda rai da kina
araye, amma musa bai ta6a sanya baki akan maganar 6atanki balle har ya taimaka
wurin bada gudummuwar mu nemo ki.....” Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mata
maganarta”kidaina faɗa mata wannan maganar, bai dace ba, taya zakice kawunta ƙanin
mahaifinta bai sonta? Akan wani dalili? Shiya furta maki da bakin shi”
Harara layla ta watsa mashi”alama nagani shiyasa nace haka”
Idanuwan benazir ne suka cicciko tab da ƙwalla, cikin sanyin murya tace”Ni ban
damu ba, koda ace baya sona, tun da Iyayena suna sona Alhamdulillah, soyayyarku
kaɗai ta ishe ni sai kuma ta mijina da ƴata, da kuma Yayana, sannan Ni na amince
zanje abujan bawai don saboda shi ba, saboda inason ganin Aneelerh”
Girgiza kai layla tayi”bafa zan ta6a bari ki je gidan mutumin nan ba, Saboda Ni
ban yarda da shi ba, Idan kuma kika takura akan kinason zuwan bazan hanaki ba sai
dai ki sani bazan biku ba” babu alamun wasa akan fuskarta tayi maganar.
Magiya benazir ta dinga yi mata akan ta amince suje da ita, don ita batason suyi
nesa da juna, daƙyar layla ta amince zata bisu abujan, da wata manufa a ƙasan
zuciyarta don taci alwashin idan sukaje gidan Alhaji musa saita fada mashi baƙaƙen
maganganun da zasu hana shi sukuni, yanzu dai sun tsaida magana zuwa jibi zasu yi
tafiyar.
Aranar shureim ya samu damar kiran Alhaji ubaid ya fada mashi uzirin daya hana
shi ɗaga kiran shi, bayan sun gama magana, har benazir yace abata waya su gaisa,
sun jima suna waya da ita kusan awanni suka kwashe, kafin daga bisani yayi masu
sallama.

Idan muka koma 6angaren zahra tun bayan da ta koma gida, babu mutunci a tsakaninta
da Aneelerh ko gaisuwar arziki bata haɗa su, ta canza mata bata sakar mata fuska ba
kamar yarda suke ada ba, aranar mahboob yai mata maganar motar ta da wayarta yace
dama jingina yabada su, idan tana so zata bada kuɗin adawo mata dasu, farin ciki
kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha dama bada Son ranta ta bada su ba, ta haɗa mashi
kudin ta bashi, a daren ranar ya dawo mata da su, tuni ta fara amfani da wayarta
bayan ta mayar da sim dinta.
A washe garin ranar laraba suka fara shirye shiryen fara aiki a Obie estate tare
da sauran Interior designers dake aiki a ƙarƙashin company dinsu, tuni kaya sun iso
daga dubai, Hankalin zahra ya kwanta bata da sauran damuwa yanzu, ta ƙagara gobe
tayi don suje su fara gudanar da aikinsu saboda gagarumin taro ne zasuyi idan obie
zai yi birthday kamar shagalin biki saboda dukiyar da suke kashewa wurin ƙawata
gidan, shiyasa zasu fara yi masu aiki tun alhamis kafin Juma’a da za’a gudanar da
shagalin
❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤🤍❤

❤ANEELERH❤

A zaune take saman mirror chair, bata jima da fitowa daga wanka ba, ta zauna ne
domin gyara jikinta, ƴar rigar wanka ce a jikinta, ta kasa ta6uka komai hannunta na
a ruƙe da wayarta layin hajiya adama take dannawa kira, phone din na fara ringing
taji sanyi ya ratsa zuciyarta, bayan hajiya adama tai picking call din Aneelerh ta
yi mata sallama, on the other hand muryar Hajiya adama ta bayyana da alamun kasalar
bacci”wa’alaikum salam daugher in-low, ya ki ke ya gidan yasu mami da ummi”

Da fara akan fuskar Aneelerh tace”Lafiya lou mommy, yasu daddy fatan duk kuna
lafiya”
“Alhamdulillah Aneelerh, halan kin ji ni shiru yau ban neme ki ba shiyasa kika
kira”
Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace”haka ne dama nakira ne don mu gaisa” da
zolaya Hajiya adama tace”kodai kin kira ne don ki faɗa min jibi zaki zo ɗaukar baby
junaid tun da time ya cika”

Ƙumshe dariya Aneelerh tayi kamar tana agabanta sai faman noƙe kai take yi, jin
tayi shiru yasa Hajiya adama cewa”dama nasan ba zaki faɗamin ba, to ki kwantar da
hankalinki, in sha Allah friday zanzo dashi gidan naku”

Abeelerh taji dadin maganarta”nagode mommy, Allah yakaimu lafiya.


“Nima ngde ki kulamin da kanki, ki kuma gaishe min da su mami, junaid din bacci
yake yi zuwa anjima idan ya farka zan kira ki video call ku gaisa, dama yanata
sambatu yana ambon shi wurin mommy zaije”
Murmushi Aneelerh tadan saki kamar tana agabanta”zasuji nima agaishe da daddy, “
daga nan suka yi sallama da juna.

❤A washe garin ranar Alhamis❤

Wuraren sallar Asuba Unaisah tana zaune saman darduma ta zumbula hijabi, Batul tana
akwance agefenta saman dardumar, tun jiya da suka fara sallah da zarar sun gama sai
ta kwanta wahala take ji idan tana yin sallah hada ƙarin rashin sabo har ƙwara
ita akan su azeeza masu yin kalle kalle in suna yin sallah, mazan cikinsu sunfi
natsuwa shi kanshi Boss man yayi mamakin yadda suka Iya sallah da karatunta ya ƙara
jinjinama Unaisah akan ƙoƙarinta, yanzu karatun addinine zasu ƙara koya masu dana
boko kafin asanyasu makaranta bayan kammala bincike akansu.

Tafin hannayenta biyu ta ɗaga sama tanayin addu’a muryarta abuɗe take fadin

“Ya Allah ka jiƙan ƴan uwanmu da suka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah kakai rahama
ƙabarinsu, Ya Allah kabamu ikon cinye jarabawarka, Ya Allah ka bamu haƙuri da
juriyar rungumar duk wata ƙaddara da zata riske mu mai kyau ko mara kyau, Ya Allah
ka tsare min sauran ƴan uwana da nake atare dasu da sauran al’ummar musulmai, ya
Allah ka bamu nasara akan burinmu da muke son cimmawa na ganin mun kawo ƙarshen
azzaluman mutanan da suka ƙasƙantar da rayuwarmu suka cutar damu Allah kada ka basu
nasarar cigaba da aiwatar da zalunci..........” cikin shessheƙar kuka ta ƙare
maganar, hawaye tuni sun wanke fuskarta tunawa da rayuwar sauran ƴan uwansu ƙananun
yara da ake cutarwa a cikin kurkukun ƙaddara, tasan ba zasu fasa cin zarafinsu ba
suna lalata rayuwarsu kamar yadda su ka yi silar mutuwar ƴar uwar su Unaiza ƴar
gidan daddy da Majnoon yaran da ba suji ba basu gani ba.
Sautin kukan Unaisah ya karaɗe cikin ɗakin, batul ko motsi batayi ba, tunda ta
kifa kanta saman darduma bacci mai dadine yai awon gaba da ita ko addu’a bata samu
damar yi ba.

“Bazan ta6a mantawa da wasiƙar da kika bani ba, kuma bazan manta sunan mugun
mahaifinki ba, In sha Allah zan ɗaukar maki fansa koda kuwa zan jefa rayuwata ne
cikin haɗarin da zaiyi silar mutuwata ne.....” cikin karyayyar murya take furta
kalaman masu ta6a zuciya, idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur, hawaye sun kwanta saman
fatar fuskarta har zuwa gaban hijabin dake a jikinta.

“Ya Allah ka bayyana min daddyna idan yana araye, Inason nasake ganinshi shi
kaɗaine nake da burin haɗuwa dashi a duniyar nan”

Tunda ta fara karanta addu’o’i, yana la6e bakin ƙofar dakinsu Yana sauraronta, basu
jima da dawowa daga sallar asuba ba, ya rakosu Sajeed ne tuni sun nufi bedroom
dinsu.

Zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta, abubuwa dayawa sun so su rikitar dashi,


kamar yarda take zubar hawaye haka shima yake zubar da su saman fuskarshi, farar
jallabiyace a jikin shi ya sanya mask akan fuskarshi, Ji yake kamar ya faɗa ɗakin
Ya rungumota a jikinshi, duk a tunaninshi Unaisah ta manta dashi ashe ba haka bane
yana aranta har addu’a tana yi mashi, haƙiƙa yayi farin ciki mara misaltuwa, cikin
sanɗa Ya juya zaibar ƙofar ɗakinsu kwatsam muryar Jemimah ta tona mashi asiri da
ƙarfi ta furta”BOSS MAN!!!” cak Ya dakata da tafiya, hatta Unaisah dake a ɗaki
saida taji sautin sunanshi da jemaimah ta ambata, aiko da sauri ta miƙe ta nufi
kofar fitowa daga ɗakin.

A hankali Ya waiwaya baya yana duban jemimah, tasha dogon hijabi ajikinta kamar
zatayi tuntube da gudu ta nufo shi, Azeeza ma ta fito tabiyo bayanta itama hijabin
ne a jikinta.

Kallon da yake binsu dashi tamkar kallon da uba yake yiwa ƴa’ƴanshi ne, saboda
yana matuƙar ƙaunar yaran ya dauke su kamar jininsa, musamman yadda suka fara nuna
mashi yarda, Jiya izuwa yau sun saki jiki dashi, duk in zai gifta sai sun ambaci
sunanshi kamar su suka raɗa mashi.

Jemimah na ƙarasowa ya sanya hannu biyu ya ɗagata sama, ta kama tiƙar dariya tana
fadin”dan Allah kada ka sauke ni ƙasa”

Fuskarshi dauke da murmushi yace”raini ya fara shiga tsakanina dake ko? Tun jiya
badama kiga na gifta sai kin ƙwala min kira kamar wani tsaran wasanki, bakisan ni
baba ba ne”?

Tace”to aini daɗin sunan nake ji, Boss man shiyasa nake kira,” tana magana yana
kallon jajayen kumatunta bakomai yake tunawa ba face Angel ɗinsa, lokacin
ƙuruciyarta yaci wuyarta yakuma ji dadin shiriritarta.

“Jemimah Ina fata yau kinyi sallah ta hankali, don jiya Azeeza ta faɗa min abun
kunyar da kika yi” ya faɗa yana sauketa ƙasa, duban Azeeza yai har ya miƙa hannu
zai ɗauke ta ganin ta tsare shi da ido yayi tunani ko itama so takeyi ya daga ta
sama, da sauri ta maƙe mashi kafaɗa tana fadin”ai ni ba ƙarama bace, Na girmeta da
shekaru” dariyace ta kubce ma Boss man.

“Oh saboda kin girmeta shine bakyaso in ɗauke ki? To aini a wurina jinjira nake
kallonki” ya faɗa tare da ɗaukarta ya ruƙeta a hannunshi, Kunyar duniya ta cika
Azeeza sai faman noƙe mashi kai take Yi.

“Kasan Allah Boss man itama Azeeza bata Iya sallaba, ko karatun sallah ma bata
iyaba, idan nayi ƙarya kace ta maimaita maka Rabbighfir li” tuntsirewa yai da
dariya.

Ran Azeeza ya 6aci tace”wallahi ƙarya take yi min, ai acikin zuciya nake yin
karatun sallah tayaya har tasan abunda nake faɗi acikin zuciyata” gwalo jemimah
tayi mata”oho dai, ni dai duk rashin Iya sallana nasan yadda ake karatun sallah”

Idanuwan Azeeza tuni sun cicciko da ƙwalla, boss man yace”badai kuka zakiyi min
ba”? Cikin shessheƙar kuka tace”wallahi ƙarya take yi min na iya karatun sallah,
kaji na rantse maka, idan ma kanaso sai in faɗa maka kaji, itace fa bata Iya komai
ba, jiya muna sallar isha’i tana buga min dundu abayana, kuma ban rama ba”

Kwantar da kanta yai saman kafaɗar shi haɗi da daura hannun shi saman kanta Yana
lallashinta.

Idanuwanshi akan jemimah dake ta dariya, dama tun jiya da yayi tozali da fuskarta
ranshi ya bashi daƙyar in bata iya rashin ji ba, kamar dai Angel dinsa da tana
ƙarama .

Lallashinta yai”yi hakuri my daughter, kuruciya ke damunta dama kince min kin
girmeta don haka inaso ki ruƙe girmanki kada ki biye mata, idan tayi ba dai dai ba
kiyi mata nasiha a matsayinki na babba mai hankali da tunani, in sha Allah wata
rana zata daina ne” tunda ya fara magana Azeeza take amsa mashi da toh, jemimah
kuwa sai faman ta6e mashi baki take yi hada ruƙe qugu, tana fadin”tab ita ɗin zata
min nasiha, Allah ya kiyaye, ai ni bana jin maganar kowa idan bata Unaisa ba”

Mamaki jemimah take bashi gata ƴar ƙarama idan tana magana sai kayi tsammanin ta
ɗare shekarunta.

Sauke Azeeza yai saman floor, yace da ita”ki ruke hannun ƴar uwarki ku tafi ɗaki,
da anjima idan nashigo zamuyi magana” ta amsa mashi da toh nagode, kafin ta ruƙo
hannun jemimah tuni ta watsa da gudu ta nufi hanyar komawa ɗakinsu duk don kada
azeeza ta ruƙe hannunta.

Murmushi ya saki yayin da yake bin bayansu da kallo, Har ya ɗaga ƙafa zai nufi
hanyar fita ɗakin, Muryar Unaisah ta dakatar dashi”Boss” A hankali ya juya baya
yana dubanta tun ɗazu tana tsaye tana kallon su, sai da ta bari su Azeeza sun tafi
tukunna ta yanke shawarar yi mashi magana.

Ta wanke hawayen fuskarta, tana tafiya hijabinta na ja da ƙasa, har gabanshi ta


ƙarasa ta tsaya, tsananin tausayinta ne Ya kamashi, ji yake kamar ya rungumeta koya
rage radadin da yake ji acikin zuciyarshi, sai dai ba halin yin hakan yasan yadda
take da masifa idan Ya kuskura yai hugging dinta tsaf zata mare shi tunda batasan
wanene shi ba.

Ido cikin ido suke kallon juna, tsawon mintuna kafin ta numfasa tace”ina kwana?
Ka tashi lafiya? ya fama da mu”
Cikin sanyin murya yace”lafiyalou Unaisah, ya akai naga idanuwanki sun canza
launi, ko baki da lafiya ne”?

Girgiza mashi kai tai, cikin disasshiyar murya ta furta”lafiyata qalou, kasalar
bacci ce,”

Jinjina kanshi ya ɗanyi, ji take kamar tace mashi ya cire face mask dinshi sai dai
bata son ta takura mashi don ta fuskanci bayason su san wanene shi.

“Kin tsare ni da ido kina kallona ko akwai wani abu da kike son fada min ne”?

Murmushin gefen fuska ta saki, Har dimples dinta suka lotsa,


“Dan Allah taimako nakeso kayi min sai dai bani da ko sisi a hannuna”
“Kada kiji komai ki faɗi koma menene zanyi maki shi in sha Allah”

Tana faman noƙe kai tace”um dama waya ce da Aunty laura ta bani kyauta ɗaya daga
cikin likitocin da suka kula da lafiyarmu a america, to wayar babu sim aciki gashi
inason in fara amfani da ita”

ta faɗa tana duban fuskarshi, ya natsu yana sauraronta idan tana magana
kuruciyarta yake tunawa, yarinyar data sanya shi ciwon kai da zazza6i, cikin ikon
Allah yanzu ta ƙara girma ta zama kamilar mace ta mallakin hankalinta.

“Sim kaɗai kike buƙata”? Girgiza mashi kai tayi”a’a, da Allah kada kace na takura
maka, “ aranshi ya ayyana takura kuma ta nawa My Angel, nida nayi jinya gadon
asibiti saboda ke”

“Cikin Kayan da aka tsunto mu da su a daji, akwai backpack ɗina inason jakar,
gadonmu ce bansani ba ko sojoji sun haɗo mana da su” ta tambaya tana dubanshi.

“Duk wani abu naku yana atare damu, saboda muna buƙatar abubuwan da zasu taimaka
mana wurin yin bincike tamkar shaidune agare mu, amma kada ki damu zan ɗauko maki
backpack din, da anjima zan shigo maki da ita tare da sim din da zaki sama wayar”
wani irin farin cikine Ya lullu6e Unaisah, godiya tadinga yi mashi, yace mata yaji
daɗin ganin farin cikinta, juyawa tayi da niyar ta koma ɗaki, hijab din jikinta
dake jan ƙasa ta harɗe ƙasan takalmin ƙafarta, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da
zafin nama Boss man Ya ruƙo damtse hannunta Ya janyota ta faɗa saman kirjinsa, har
saida taji gabanta ya fadi, ƙanƙameta yayi da hannayensa biyu daya zagayo dasu ta
bayanta, Jikinta yai wani irin sanyi kamar wadda aka zare ma laka, bawan Allah
tunda ya rungumeta yai tighting dinta kamar karya saketa, ita kanta takasa raba
jikinta daga nashi, saima hannayenta data zagayo dasu saman bayanshi, ta
ƙankameshi, Jini ɗaya ba wasa ba, sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi at same
time, batasan ya akai ba ta tsinci kanta da jin hawaye sun cicciko idonta, shi kuwa
tuni sun wanke face mask dinshi.A hankali yake ɗan bubbuga bayanta kamar yana
lallashinta, tsawon shekaru rabon daya ji ɗumin jikinta anashi, bazai ta6a manta
ƙaddarar data afka masu ba, wadda tayi silar rabuwarsu, bazai ta6a manta sautin
shesshekar kukanta da muryarta a lokacin da yake gudu dasu cikin mota tana daddy
hancina jini, haka zalika bazai ta6a manta lokacin da ya jefar da ita cikin ruwa ba
duk don ya ceci rayuwarta Sai gashi cikin ikon Allah ta rayu Allah ya tsare mashi
ita, Allah kaɗai yasan irin wahalhalun rayuwan data fuskanta da ƙananun
shekarunta.....

Kamar yadda yake tariyo rayuwarsu haka itama take tunano daddynta, ji take kamar
shine ya rungumeta, shiyasa ta ƙara narke mashi tayi lamo saman wide chest
dinshi......

Gaba ɗayansu sun shiga yanayi mara misaltuwa, ba zato ba tsammani Boss Man yaji
dirar wani abu saman bayanshi, da sauri ya ɗago da kanshi idanuwan shi sun canza
launi sun kada jawur kamar mai fama da ciwon ido, yayi mamakin ganin pillow da aka
jefo mashi ya fadi ƙasa, da sauri ya ɗaga ido sama don ganin wanene ya wurgo mashi
pillow saman bayanshi, karaf idanuwan shi suka sauka akan Danish dake tsaye can
second floor, hannun shi ruƙe da wani pillown Yana niyar ƙara jeho mashi, fitowar
shi kenan daga ɗaki idanuwanshi suka hango mashi Angel ɗinsa rungume da wani ƙato,
shine fa yaje ɗaki ya ɗauko fululluka har biyu Ya jeho mashi ɗaya.

Ya haɗe fuska babu annuri, kayan bacci ne ajikinshi riga da wando launin pink
sunyi bala’en yi mashi kyau.

Harara ya watsa ma boss man, ganin Angel taki barin ƙirjin mutumin yasa shi ƙara
daddagewa ya wurgo mata pillow, da sauri boss man Ya tarbe pillown a hannun shi,
Lamarin ya ɗaure mashi kai, sai yanzu ya gane dalilin dayasa yaron yaƙi sakar mashi
fuska tun jiya yake daure mashi fuska, ashe kishi ne ke damun shi.

“Unaisah”! Jin boss man ya ambaci sunanta yasa ta ɗago da kanta tana kallon shi,
mamaki ne ya kamata ganin pillow a hannun shi, da ido yai mata nuna da bayanta, da
sauri ta juya don ganin wanene, a tsaye ta hango shi ya ruƙe qugu yana aiko masu da
harara.

Batasan sa’adda ta tuntsire da dariya hada dafe ciki,


da zolaya boss man yace”kishine ya addabe shi shiyasa yake jifar mu da pillow,
faɗa min meke a tsakaninki dashi.

Tana dariya tace”babu komai, shaƙuwace a tsakaninmu, baya son yaganni tare da
wani idan ba ƴan uwanmu ba, haushi yake ji”

“Kice ƙwara in lalla6a in gudu, tunkan ya sauko don wannan har buguna zai Iyayi,
“ ya fada tare da damƙa mata pillow din hannun shi, Ya juya da sauri ya nufi ƙofar
fita Yana faman sakin murmushi, bai ta6a ganin namiji mai kishi ba irin Danish.

Zukunnawa tayi ƙasa ta ɗauki ɗayan pillow, ta haɗa dana hannunta, ta nufi
upstairs, Har tsoron tunkarar shi take Ji, saboda yadda ya kumbura fuska, soft red
lips dinsa sunyi suntum da su”
Koda ta haye up din, taga Ya dunƙule hannu kamar zai nausheta, wurga mashi
pillows din tayi saman faffadan kirjinshi, da gudu ta sauko down tana tiƙar dariya,
akan idonta ya tattara pillows din ya nufi dakinshi ya shige.

Yau da wuri suka yi breakfast dinsu, saboda gyaran jikin da ummi zatayi masu.

A Katafaren Home beauty station ɗin dake a cikin part dinsu, saboda su aka tadani
komai na cikinsa, ɗakin Ya haɗu, bangon dakin beauty shelf ne An jera Kayan gyaran
jiki kala kala, dana gyaran gashi acikin kowani shelf, hada foot care product and
skin care product, Ga wani faskeken mirror a jikin bango, daga gabanshi wasu
hadaddun kujerune kusan guda takwas, A saman kujerun kowa Ya samu wuri Ya zauna su
shidda ne matan dake acikinsu, banda mazan tun bayan da suka kammala yin breakfast
suka tafi ɗaukar karatu a inda suke Yin sallah. Suma matan acan za’a dinga yi masu
karatu.

Kowaccensu tana sanye da bathrobe a jikinta, Ummi ce ta basu rigunan, saboda da


taji daɗin gyara masu sumar kansu.

Kujerar farko Unaisah ce zaune asamanta, ta biyu batul ce akusa da ita, sai Parveen
itama ta hakimce saman tata kujerar, daga gefenta Jemimah da Azeeza ne saman nasu
kujerun bayan su sai Hannah.

sun natsu suna kallon faces dinsu ta cikin madubi sai faman sakar ma juna murmushi
suke yi kamar wasu zautattu, daɗi suke ji za’a gyara masu sumar kansu, har sun fara
imaginning din kyawun da zasuyi

babu mai magana acikin su, saboda ummi tana acikin dakin ta hanasu surutu

tana a sanye da dogon wando ƴar rigar data sanya daƙyar ta rufe cibinta, babu
mayafi akanta.

“Dawa zamu fara” ta faɗa tana dubansu, har suna haɗa baki wurin furta Ni,
“bari in za6a da kaina” ta fada tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a ƙarshe ta
tsayar da idonta Kan Unaisah da Batul, daku zan fara, saboda yawan sumar kanku”
saukowa su ka yi daga saman kujerun, ta juya ta nufi Corner din da Sink Yake, gefen
shi beauty cabinet ne mai ɗauke da jerin shampoo da conditioner da suran mayukan
gyaran gashi.
Taci baƙar wahala wurin gyara masu gashi, musamman mutun biyun nan Unaisah da
Batul, saboda yawan gashinsu ga tsawo, da ruwan zafi ta jika sumar bayan ta jiƙu ta
shafa shampoo ta cuccuɗa ko’ina na gashin, bayan ta wanke shampoo din ta sanya
conditioner na tsawon mintuna kafin ta wanketa, tayi masu amfani da Hair dryer ta
busar masu da sumar kansu, ta fara shafa masu smoothing serum ta ɗauki comb taci
gaba da sharce gashin, tunkafin ta kammala take santin kyawun sumar kansu, bayan ta
gama sharce gashin ta kwarara masu hair oils kala daban daban saman sumar taci gaba
da cuɗasu da hannuwanta, tuni gashin ya ciza launin shi dark brown sai ƙyalli yake
yi da ɗaukar ido, ƙamshin hair oils din data shafa masu Ya cika hancinansu.

Lokacin da suka kalli sumar kansu ta cikin madubi, Ihun farin ciki suka saki suna
faman yi mata godiya tace su koma zu zauna, bata gama gyara masu ba, su Azeeza
sunyi zuru suna jiran suma ayi masu, sai faman santin su Unaisah da Batul suke Yi
har suna fadin suma kalar nasu za’ayi masu.

Ummi tayi ƙoƙari wurin gyara su, Yara kamar ƴa’ƴan wani shege maiji da raina,
saida tayi amfani da almakashi ta datse sumar kansu ta rage tsayinta ta dawo dai
dai tsakiyar bayansu, hair style din da tayima Batul da Unaisah Triple twist half
up ne, Bayan ta gama dasu ta bi sauran ɗaya bayan ɗaya ta wanke masu sumar kansu
kamar yadda tayi masu Unaisah haka suma tayi masu banbancin wurin hair style ne,
saida ta miƙar masu da gashinsu ta hanyar yin amfani da Straightener, kafin ta
ɗaure ma Azeeza da Jemimah gashinsu da ribbom guda biyu gefe da gefe wutsiyar
gashin ta sauko har saman kafaɗunsu.

Duk wannan gayun da akayi masu, Jemimah bata gode ba, ta sanya rigima akan sai an
maida launin gashinta kalar nasu Batul, Ummi taci dariya, bata ta6a tsammanin zata
ji ƙaunar yaran ba sai yau, su kansu sunyi mamakin yadda ta dage damtse wurin Yi
masu hidima, Abu kamar wasa Jemimah ta fashe masu da kuka, ita damuwarta launin
gashinsu Yafi nasu kyau, da ita da azeeza sumar kansu blonde ne kalar na turawa,
ita Azeeza bata damu ba sai murna take yi an gyara mata gashi, jemimah daice ta
matsa lamba, ummi harta fara tunanin ta canza mata launin gashin da yake suna da
Hair dye cikin jerin Kayan gyaran gashin su, Unaisah ce tace abar mata launin
gashin kanta, saboda yana dakyau ba lallaima idan aka maida mata kalar nasu yayi
kyau ba,” daƙyar suka lallashi Jamimah tadaina yi masu kuka.

Tsawon lokaci kafin Ummi ta kammala Gyara su, hatta skin dinsu da akaifunsu da
tafukan ƙafafuwansu duk saida ta gyara masu, ko’ina ka kalla na jikinsu saiya
burgeka, kamar basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, tun bayan da aka gama kowannansu
Ya koma bedroom dinshi, bacci mai nauyi ya dauke su, duk don saboda gyaran gashin
da akayi masu kada Ya 6ace yasa suka kwanta ta rubda ciki.

*OBIE ESTATE*

Danƙara danƙara motocine masu numfashi suke ta kurɗaɗowa ta cikin babban gate din
Obie Estate a ƙalla sunkai goma sha wani abu gaba da bayansu motocin fusatattun
sojoji ne sun mimmiƙe tsaitsaye hannayensu ruƙe da manyan bindigu, jiniyar motocin
jami’an ta karaɗe ko’ina na yankin, da matsakaicin gudu suka haura saman titin da
zai sada da su da Airport, Motar farko zungureriya tana ɗauke da dattijon arziƙi
tare da Dr.Jaz, mota ta biyu sanate president lateef ne zaune a mazaunin baya shi
da Iyalansa Hajiya madina da ya’yan ta biyu Ziyad da zuhra, Mota ta uku Hajiya
saratu ce a cikinta tare da twins zayn da zaid, da shi kanshi pravin din, Motar
bayansu Sir mubarak ne tare da Hajiya Turai, daga motarsu sai ta sauran ƴan uwa da
abokanan arziki da suka hallara domin zuwa tarban babban baƙonsu, kowan nan su yayi
shiga ta alfarma, mazan cikinsu shaddojine ajikinsu, matan kuma wankan abaya suka
ɗauka, har sun kusa isa Airport din ba zato ba tsammani suka soma hango wasu
hamshaƙan motocin daban sun biyo ta titin da zai jagorance ka zuwa Aso Villa,
Ƙarshen Haɗuwa ta glass din motocinsu suke hangen su, tunkafin suga su wanene
acikin motocin ransu ya basu Mr.president ne tare da muƙarrabansa shima yazo tarban
ɗan uwan nashi, abun yayi matuƙar ƙayatar dasu, basu yi tsammani zai halacci zuwa
Airport din ba, zuwan bazata yai masu, Motocin shugaban ƙasa na ƙarasowa suka haɗe
da nasu motocin Yawan adadin motocin suka ƙaru, hankalin kowannansu akwance yake
sun ci burin haɗuwa da babban baƙon nasu, duk sun ƙagara su ƙarasa Airport din.

“Ziyad Ina fata baka faɗa ma Ƴan uwanka ƴan jarida ba ko”? Sanate lateef ne yai
maganar a yayin da yake zaune gefen Hajiya madina a back seat na motarsu.

Ziyad na murmushi yace”ai daddy tuni na sanar dasu ku jura zuwansu kawai”
Buɗe baki sanate yai”amma dai wasa kake min ko? Kadai san Kawun naka bai san
taron ƴan jarida,”

Ziyad na sakin murmushin shaƙiyanci ya zuge mashi glass din motarsu, har sai da
gaban Senate yadan buga ganin motocin ƴan jarida birjik sai faman sharara gudu suke
yi har sunfi nasu motocin sauri duk dan su ƙarasa su dauki rahoto.
Dafe kai Senate yai”ziyad kana da matsala, yanzu menene na gayyatar waɗannan
mutanan ina amfanin yin hakan”?

Sai lokacin Hajiya madina ta sanya masu baki a maganarsu”ai indai ziyad ne dama ka
daina damun kanka, ka riga da kasan halinshi, jikin shi har 6ari yake yi idan ya
samu abun daukar rahoto”

Dariya ziyad yai jin abunda mommyn shi tace, shi dai senate lamarin ya ɗaure mashi
kai.

Kusan atare motocin suka yi parking a wurin da aka tadana domin ajiye motoci,
jami’an suka diddiro daga saman motocinsu suka soma bubbuɗe masu murfin motocin,
ɗaya bayan ɗaya suke fitowa, Ƴan jaridan ma suka fito Hannayensu ruƙe da Cameras,
wasu a wuya suka rataya cameran su, wasu kuma sun ruƙe welcome sign a hannun su duk
da akwai tazara a tsakanin su saboda mugun tsaron dake wurin dan ma yan jarida ne
masu naci da ba wanda ya isa ya tsaya a wurin.

Lokacin da Sharafudden Ya fito daga cikin Motarshi gaba ɗaya ido Ya dawo kanshi,
mutumin babu wasa a fuskarshi, kamanninshi sak da mahaifinshi Obinna, launin
fatarsu ne ba ɗayaba, Yana da hasken fata sai dai bai kai na Obie ba, nashi yadan
yi duhu, fatarshi taji hutu, babban mutunne mai cikar kamala, ya iya dattako ga
wadatar arziƙi, kusan duka halayan Owais shiya ɗauko babu abunda ya bari mashi,
hatta kyawun fuskarshi na mahaifinshi ne, Yana da tsawo da fadin ƙirji, wankan suit
ne a jikinshi, ya manna farin glass a idonshi, security detail din dake take mashi
baya sunyi mashi rumfa, Cikin takun ƙasaita Ya nufi mahaifinshi dake ta faman aiko
mashi da sakon murmushi, rungume juna sukayi, ƴan jarida kamar jira suke yi nan fa
suka fara daukarsu hotuna, bubbuga bayanshi obie yai da hannun shi yana fadin”Nayi
kewarka son, tsawon lokaci ka hanani ganinka sai yau, da yake ɗan uwanka zaizo
yanzu zan dinga ganinka akai akai”dagowa yai da kanshi daƙyar yake murmushi kamar
yana yi mashi wahala ya motsa baki ya furta”aymin afwa baba, kana araina koba dan
shi ba, nayi niyar shigowa gidan yau saboda nayi kewarka” obie yaji dadin
kalamanshi, da hannu ya nuna mashi sauran ƴan uwanshi, Jiki na rawa dr jazz da
twins suka ƙaraso suna gaishe shi cikin girmamawa, ɗaya bayan ɗaya yake amsa masu,
bayan sun kammala ƴan gaishe gaishen nasu, suka ɗunguma gaba ɗayansu suka shiga
Arrival area din, duk Inda suka gifta ma’aikatan airport din sara masu suke yi, sau
da ƙafa suke Yi masu biyayya, a katafaren waiting area kowannansu Ya samu wuri Ya
zauna sun natsu suna jiran ƙarasowar jirgin baƙon nasu.

Jami’an suna a kewaye da su, Ƴan jaridan ma suna a tsaitsaye acen baya suna jiran
Ya ƙaraso don su fara ɗaukar rahoto.

Vip Area din Ya cika maƙil da ɗaruruwan mutane wasu ma daga baya suka zo, Ko’ina ka
kalla kawunan Bil’adama ne, kowanene wannan Babban baƙon daya tara dubban jama’a
dake cike da ɗaukin ganinshi? lallai ba ƙaramin mai farin jini bane, shi ɗin na
musamman ne.
Agogon bangon Nigeria Yana bugawa ƙarfe goma shabiyu adai dai wannan lokacin sautin
katafaren jirgin shugaban ƙasar dake shawagi bisa sararin samaniya Ya karaɗe
Kunnuwan mutane, gaba ɗaya ransu ya basu cewar jirginshi ne Hakan yasa su ka fara
sakin murmushin farin ciki,

A katafaren Filin tashi da safkar jirage masu zaman kansu, Jet din ya sauka a
hankali Yake bin runway har Ya ƙaraso dai dai Inda zai dakata, tsawon mintuna kafin
ƙofar Jirgin ta buɗe matattakalar shi ta sauko ƙasa, hadadden red carpet,
ma’aikatan airport din suka shimfiɗa mashi tun daga bakin stair din har izuwa entry
din Vip area, mutanan dake aciki tuni sun mimmiƙe suna atsaitsaye curko curko suna
jiran ƙarasowarshi.

Musamman Ƙungiyar masu daukar hoto da ‘yan jarida sun Harzuƙa Jira suke kawai Ya
duro da ƙafarshi waje don su fara haska shi da kyamarorinsu kowa burinshi ya
kasance mutun na farko da zai fara ƙyalla mashi camera,

Jami’an sun kewaye Jirgin saboda su bashi tsaro, Maimakon mutumin da suke tsammani
Ya fara saukowa sai suka ga Security detail dinshi Royal Canadian Mounted Polices
suna fitowa daga cikin jirgin, zaratan Maza Ƙarfafa Masu Ƙira Irinta zakuna, Sanye
Cikin kakinsu, Qugunansu a soke da bindigu Pistols, A bakin stairs ɗin Suka Tsaya
sun haɗe da sojojin Nigeria dake a bakin jirgin.

Lokacin da Ya zuro ƙafarshi dake sanye cikin wasu hadaddun leather shoe Hankalin
kowa ya dawo kanshi, tabarakallahu ahsanul khalikin, ƴan jarida har goga kafada
suke Yi garin yin saurin haska shi da camera, A hankali Ya ƙarasa fitowa, Babban
mutunne ya fito sanye Cikin tailored suit, sun zauna mashi, Sunbi shape ɗin
Jikinshi, Fari ne Ba irin sosai ɗinnan ba, daga ganin fatarshi hutu ya zauna mashi,
kanshi babu hula, Sai ka rantse da Allah matashin saurayi ne, saboda haɗuwarshi da
iya ɗaukar wankanshi, sumar kanshi akwance take tasha gyara, tsakiyar gashin kan
nashi akwai siraran hurhurar gado, da akayi gayu da ita, ba ƙaramin kyau tayi mashi
ba,Yana da tsayin fuska, Manyan idanuwa, ga dogon hanci, bakowa bane wannan face
PRIME MINISTER HATEEM OBINNA! namijin zaki uban dawa, ɗaya tamkar da dubu, gwarzon
Namiji mai ɗauke da suffofin jagwaranci, mutun mai daraja da ƙima a idon al’umma.
yana da farin jini ba Iya kasarshi ba a ƙasashe da dama rububin shi suke Yi saboda
kyawawan ɗabi’unshi da halayanshi, mutumin maƙurane a 6angaren Kyau, ilmin addini
dana zamani, uwa uba Ya fito daga babban Gida, kallo ɗaya zakayi mashi ka shaida
ruwa biyune, gashi Hamshaƙin Mai kuɗi Ya shahara Aduniya.

Cikin dattako Yake taka matakalar benan, All eyes on him mutanen dake can nesa
suna hangenshi kamar zasu ƙetare Iyakarsu su faɗo gabanshi donsu Tarbe shi,
Fitowarshi Keda Wuya Uwar Gidan shi Gimbiya Mujeedat ta sauko daga cikin jirgin,
nan fa kallo Ya koma Kanta, Hankalin maza ya tashi, Ko mace ta kalleta saita
girgiza balle Namiji, ahaka ma ta sanya Arab gown launin fara ajikinta, Ta rufe
fuskarta da Niqab, dirin Jikinta Yafi komai jan hankali, da kuma kyawawan
idanuwanta da suka bayyana sun sha uban ado farare ƙyal, price din takalman ƙafarta
kaɗai sun ishi wani talakan jari, hatta hannayanta Safa ce ta sanya, Mijinta yana
matuƙar jin kishinta shiyasa duk inda zasuje da niƙab a fuskarta, bayan ta fito,
matasan ƴa’ƴansu biyu suka fito tare da Faryat ƴar gidan saratu, sunyi shiga kala
ɗaya data mahaifiyarsu dukansu matane, dogaye masu kyan sura, atare dasu akwai
advisors dinsa, manyan mutane masu bashi shawara, sun hada da chief of staff,
national security advisor, Fararen turawa sun ɗauki wankan black suit, kowan nan su
ya manna sunglases a idanuwanshi, ajere suke taka shimfiɗaɗɗan red carpet din da
zai jagorance su zuwa Vip arrival area, lokacin da suka karasa jama’a kamar zasu
haɗiyesu tsabar murnan ganinsu, Bawan Allah bai nufi kowa ba sai Mahaifinshi
Obinna, Hannu bibbiyu ya rungume shi ajikinshi, tsawon shekara basu ganaba sai yau
da Allah Ya nufa zai samu damar zuwa Nigeria, Wata irin runguma yayi ma Obinna,
gaba daya mutane suka sanya ihu suna tafa masu, Ƴan jarida Sun dage sai daukarsu
hoto suke Yi, sautin ƙarar kyamarorinsu ya cika airport din ji kake kyat kyat,
Gimbiya Mujeedat, da fara’a akan fuskarta ta rungume Hajiya saratu, kamar ƴan uwan
juna, Faryat kuwa da gudu ta faɗa jikin Zayn tana dariya, bayan ta rungume shi ta
kuma rungume Zaid, sai daɗi take ji taga ƴan uwanta, Nazli da Yazrin kuwa kamar
basu son ganin mutane, dama suna da wuyar sha’ani har ƙwara Yazrin tafi sakin fuska
akan Ƴar uwarta nazli, daƙyar suke rungumar ƴan uwan mahaifinsu, izzace ta bala’e
suke fama da ita, su ala dole ga jinin sarautar daular larabawa, Bayan prime
minister Ya saki mahaifinshi, Ya rungume ya’yanshi sharafudden kamar zasu koma
mutun ɗaya tsabar yadda suka hade jikinsu. Tuni ƙwalla ta cicciko tab a idanuwansu,
daƙyar suke yima juna magana, ɗaya bayan daya saida yabi ƴan uwanshi ya rungumesu,
kafin ya soma gaisawa da sauran manyan mutanan da suka zo tarbarshi, yaji dadin
ganin daruruwan al’ummar da suka taru domin shi, wannan abun farin ciki ne, Obie ne
yai mashi magana akan Yan jaridan da ke son yin magana da shi, A hankali yake bin
welcome sign din dake a ruƙe a hannunsu.

Rubutun dake ajiki ya soma karantawa acikin zuciyarshi kamar haka

_The entire country of Nigeria, welcomes Prime Minister Obinna with open arms!_

_A very special welcome to Prime Minister Hateem Obinna, on behalf of the entire
nation!_

_- Prime Minister Hateem Obinna, we are delighted to have you in our country!_

_We’re happy to extend a sincere and heartfelt welcome to Prime Minister Hateem
Obinna!_

Ƙayataccen murmushine ya bayyana akan fuskarshi, ƙwallar da yake 6oyewa baisan


sa’adda ta soma gangarowa saman kuncinsa, farin cikine Ya cikashi, yaji dadin
kyakkyawar tarbar daya samu, mintuna ƙalilan yayi jawabi ma ƴan jarida yayi masu
godiya da irin tarbar da suka yi mashi

Daga bisani Jami’an dake bashi tsaro suka yi mashi ƙawanya da iyalinshi zuwa wurin
da aka tanadar masu da jigunannun motocin da zasu yi jigila da su, bayan kowan nan
su ya shiga cikin mota, kusan atare drivers din dake tukasu suka tada su, A hankali
suke driving dinsu zuwa hanyar komawa Obie estate.

Duk inda suka gifta Jiniyar motocinsu ya karaɗe ko’ina, cikin ƙanƙanin lokaci
suka ƙaraso Cikin estate din, a harabar ajiye motocinsu suka yi parking, gaba ɗaya
kowa ya futo suka dunguma zuwa cikin katafaren falon gidan, Jami’an da yazo dasu
tuni an ware masu part din da zasu zauna a babban masaukin baƙin gidan, haka zalika
advisors dinshi suma An basu nasu Yankin da zasu zauna, bajimawa zasuyi a kasar ba,
Ƴan kwanaki ne zasuyi kafin su koma Canada, masu aikin gidan sai safa da marwa
suke Yi wurin kai masu kayan abincin da aka shirya masu, idan zasu gaisa da mutane
harshen turanci suke Yi, har yaren french suna jin shi sosai, Gimbiya mujeedat kuma
Tafi jin larabci da turanci, haka ƴa’ƴanta ma hausa wahala take yi masu, faryat dai
ce ta ƙware wurin yin hausa sai turanci, Prime minster ma Yana jin harshen hausa
amma yafi ƙwarewa wurin Iya yaren mahaifiyarshi turanci da faransanci, sai spanish.

Yinin Ranar gidan Ya cika maƙil da jami’ae, sojoji da ƴan sanda, sun kewaye ko’ina
na sashen Estate din, tsaron gidan Ya ƙaru, Kafin mutun ya samu damar shiga estate
din sai sun tantance shi da na’ura daga kasa har sama zasu bincike shi kafin ya
samu damar ƙarasawa ciki, babu mahalukin daya isa Ya shiga gidan koya fita lami
lafiya batare da jami’ae sun cacike shi ba, tun karfe ɗaya na rana Ƴan uwa da
abokanan arziki suke ta taruwa domin Yima baki barka da zuwa.

Wuraren ƙarfe huɗu Na marece, Lokacin mutane sun ɗan ragu, motocin ma’aikan
Companyn su Zahra suka ƙaraso Estete din, basu ta6a ganin tashin hankali irin na
yau ba, sun girgiza da ganin jami’ae a kewaye da estate din, Zahra Sarkin tsoro duk
tasha jinin Jikinta, Kafin abasu damar shiga estate ɗin saida jami’ae suka basu
umarnin su fito daga cikin motocinsu, ɗaya bayan ɗaya suka firfito matasan ƴan mata
Ansha gayu, daga ƙasa har sama jami’an suka bincikesu hatta kayan decoration din da
suka zo da su a mota. Saida suka duddubasu suka tabbatar babu makami ko wani abun
cutarwa tukunna suka basu iznin shiga cikin gidan.

Da taimakon Hajiya saratu suka ƙarasa 6angaren da zasu fara aikin nasu, saida aka
fara tarbarsu da lafiyayyan abinci suka cika cikunansu tukunna suka fara aikin
tsara decoration din, acikin wani katafaren ɗakin taro dake acikin gidan suka
hallara gaba ɗayansu interior designers din, Zahra da fatima sune gwanaye basu aiki
sai dai su nuna ma sauran matasan ƴan matan yadda zasu tsara kayan adon suyi kyau,
kasancewarsu ƙwararru a fagen Iya decoration tuni wurin Ya fara ɗaukar ido Ko’ina
ka kalla kayan adone ke kyalkyali da walƙiya kamar zasu kashe idon bil’adama.

*CHIEF OWAIS✊❤*

Wuraren ƙarfe takwas na dare, Ya fito daga bedroom dinsa, har yayi shirin kwanciya
bacci, sleeping dress ne a jikinshi launin sky blue, rigar tabi shape din broad
chest dinsa, ta bayyana strong arms dinsa, walking gently ya nufi bakin handrail,
Ya ɗaura faffaɗan tafin hannunsa asaman shi, A hankali yake buɗe kyawawan
idanuwanshi Yana ƙare ma ko’ina na downstairs da kallo, tun da ya diro nigeria har
Yau bai leƙa cikin estate dinsu ba, kuma babu wanda yasan da zuwanshi,
ni’imtacciyar iskar wurin Ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya take yi ba, abubuwa da
dama sunayi mashi yawo acikin kanshi.

“Barka da fitowa yalla6ai” muryar Big guy ce ta katse mashi tunanin shi, Yana
daga tsaye gefen shi,
Ba tare daya juya ya kalle shi ba, Ya amsa mashi da yawwa.
Cikin girmamawa yace”yalla6ai ina fata kana lafiya” ya tambaya ne don ganin
yanayin daya fito daga daki cikin shiga ta kayan bacci.

“I need coffee” abunda ya furta mashi kenan maimakon amsar tambayar da yai mashi.

Da sauri big guy ya juya domin ya kawo mashi abunda yake buƙata.

Badajimawa ba sai gashi ya dawo hannunshi ruke da Mug sai tiriri coffeee din Yake
yi, Ya miƙa mashi bayan ya kar6a, sai da ya ɗauki lokacin kafin Ya fara kur6ar shi.

“Yalla6ai yaushe zamu shiga cikin gida ne”?


Tamkar bazai amsa mashi ba Ya furta”tomorrow”Jinjina kai Big guy yai kafin ya
kuma cewa”Yau kawunka na ƙasar kanada ya shigo ƙasar bansani ba ko ka gani a
labarai”
Yamutsa fuska yai da alama surutun big guy ya fara takura shi, daƙyar ya
furta”Nasani”

Gyaɗa kai big guy yai”bari nabarka ka huta yalla6ai, mu kwana lafiya” ya amsa
mashi da okey.
Juyawa yai da sauri Ya nufi down stairs.
Yana cikin shan coffee dinshi, yayin da yake bin ko’ina da kallo, Karaf
idanuwanshi suka sauka Akan Danish dake ƙoƙarin fitowa daga ɗakin shi, Ya zuba
hannayenshi cikin short pockets dinsa, damuwar duniya ta isheshi, Ya kasa runtsawa,
saboda rashin ganin unaisah, tun ɗazu yake jiran zuwanta bata leƙo ɗakinsa ba, shi
kuma bai Iya takawa yaje ɗakinsu, Kamar anyi mashi Iyaka da shiga, ko falo bai Iya
zuwa idan ba Angel ta janyo shi ba, rashin sabone ke damunshi, kasancewar suna
fuskantar juna hakan ya bashi damar ganin shi da kyau, duk da akwai tazara a
tsakaninsu, dukansu suna a second floor na bene.

Kamar yadda Owais Ya jingina da handrail haka shima Danish ya ɗaura gwiwowin
hannunsa saman handrail, da farko bai lura da shi ba, sai da ya wurga eye balls
dinsa saitin inda yake fuskanta tukunna suka yi tozali da juna, ɗaure fuska danish
yai, tunkafin ma yasan wanene shi yaji baiyi mashi ba saboda shi baya ƙaunar yaga
Namiji idan har ba cikin ƴan uwansu maza ba, duk don saboda Babe Unaisah dinshi,
yaji haushi ɗazu da asuba dayaga wani ƙato Ya rungumeta, har zazza6i saida ya
lullu6e shi, ko abincin dinner dinshi baici ba, yaso ace Ya damƙeta da babu abun da
zai hana ta yabama aya zaƙinta.

Chief Ya natsu yana kallon shi, abun da ya ɗan bashi mamaki Da yaron girman
jikinshi, saboda yasan shekarunshi da sojoji suka faɗa mashi a bayanin da Gabriel
Ya basu, bai wuci 20 years ba.

Tsawon mintuna suna kallon kallo a tsakaninsu, kafin daga bisani chief Ya juya
mashi baya ya nufi bedroom dinsa ya shige, saukowa down Yai cikin sanɗa yake yin
tafiya yana neman room dinsu Unaisah, ya rasa ta wace hanya zaibi ya gano ɗakinsu.

Firgita yai sakamakon Jin hannun mutun saman Bayanshi, abunka ga mai ji da ƙarfi,
yayi tunanin wani ne zai cutar dashi, aiko ya damƙo hannun mutumin da niyar ya
wurgo shi ƙasa sai kuma Ya fasa, Ya juya a hankali don ganin wanene, Boss man ne
atsaye hannunshi ruƙe da Backpack din unaisa, Da mamaki akan fuskarshi yace”Sannu
Iliya ɗan mai karfi, au da buguna zakayi daga kawai na dafa kafaɗarka? Haka ɗazu da
safe ka dinga jifana da pillow saboda na rungume ƴar uwarka ko”? Cikin jin kunyar
maganarshi Danish ya sadda kanshi ƙasa, ba tare daya furta komai na.

Murmushi boss man ya saki tare da miƙa mashi backpack din hannun shi”kar6i nan,
ka kaima Masoyiyar taka Unaisah kace inji boss man, ta duba cikin aljihun jakar
zata ga sabon sim dana sanya mata”

Hannu yasa ya kar6i backpack din, daƙyar ya iya furta mashi thank, kafin ya juya
yanufi inda yake tunanin zai samu ɗakinsu.

Boss Man yana atsaye yana bin bayanshi da kallo, Har ya 6ace ma ganin shi kafin
Ya juya ya nufi ƙofar fita.

Yayin da Danish keta faman neman ɗakinsu Angel, tana acan cikin toilet gaban
madubi, daga zuwa Yin uziri taci karo da abun arziƙi a kirjinta, Duk tabi ta ruɗe
ta rasa ina zata tsoma ranta don farin ciki, batasan yaushe breast suka fara fito
mata ba, bata ta6a lura ba sai yau data tsaya gaban madubi tana bin jikinta da
kallon ƙurulla, guntuwar rigar bacci ce a jikinta, Daƙyar ta rufe gwiwarta, sai
faman ɗaɗɗage rigar take Yi tana ƙara leƙensu, sunyi ƙananu dasu basu fara nuna ba,
kamar wadda akayi ma albishiri da gidan Aljanna sai faman sakin murmushi take Yi,
itama yau irin abin ƴar gidan daddy sun fara fito mata, taci alwashin bazata bari
Danish yagansu ba, sai sun ƙara girma sunkai kamar na unaiza tukunna, da gudu ta
fito daga toilet ta nufi closet dinsu ta buɗe ta dauko ƙaramin mayafi ta koma cikin
toilet, ta tu6e wuyan rigar, ta ɗaure kirjinta tamau da mayafin kafin ta maida
wuyan rigar tana faɗin”Allah na gode maka, nan bada jimawa ba nima zan zama
budurwa”

Duk wannan haukan da takeyi, batul tana akwance saman gadonsu, tayi nisa acikin
baccinta,
Adai dai lokacin zata fito daga toilet din tana zuro ƙafarta, tayi arba da danish
tsaye bakin ƙofar dakin, Hannun shi ruƙe da backpack, Sai faman baza ido Yake yi
don ya ganota, daƙyar ya samu ya gane dakin nasu,
Jin motsin mutun yasa shi yin saurin ɗaura idonshi akan fuskarta, ido cikin ido
suke kallon juna, wani abu daya ɗaure mashi kai, shu’umin murmushin daya gani
kwance saman la66anta, hada ruƙe qugu da hannu ɗaya.
❤EX-PRISONERS❤

Sam ya kasa ƙarasawa gare ta, slowly yake bin jikinta da kallo, tun daga kan
fararen ƙafafuwanta har izuwa saman gwiwowinta da suka kasance jawur da su kamar
bata ta6a yin rarrafe ba, ɗagowa yai da eye balls dinsa zuwa saman Waist dinta da
ya faɗaɗa, ganin irin mayataccen kallon da yake binta dashi ne yasa ta juya da gudu
ta nufi can cikin dakin wurin closet dinsu, har sai da yaji gabanshi yaɗan faɗi
lokacin data watsa da gudun mazannanta suka girgiza rigar ta bayyana shape dinsu,
yawu ya haɗiya adam’s apple dinsa Ya motsa sama da ƙasa.

Yaɗan ji shock ganin baƙon al’amari ajikin Babe unaisah dinshi, bai ta6a ganin
girmanta ba sai yau da yai tozali da ita cikin short gown, Kayan arzuƙa sun fara
ha66aka.

Cikin sanɗa take tafiya tana tunkaroshi, idanuwanshi akan fuskarta, still
shu’umin murmushin nan take sakar mashi, hatta Yanayin tafiyarta ya canza, dogon
wandon bacci ta zura a jikinta duk don Ya daina kallon mata jikinta.
Dab dashi ta tsaya tana duban backpack din hannunshi, har cikin ranta taji dadin
ganin jakar, daɗi kamar zai kasheta, haɗa ido sukayi da shi, mutumin duk ya susuce
kamar wanda aka zare ma laka, sam babu kuzari a jikinshi tunda yai arba da hips
dinta.

Harara ta jefa mashi haɗi da murguɗa mashi soft pink lips dinta, muryarta da
shagwa6a tace”kallon ya isa haka, bani jakar nagode” ta faɗa tana ƙoƙarin ruƙo
hannun backpack din, da sauri ya ƙanƙameta a wide chest dinshi, alamar bazai bata
ba, ɗaure mashi fuska tai”wai meye haka? Baka ga dare yayi ba, yakamata kaje ka
kwanta, ni bansan ma ya akai boss man ya baka back pack din ba, ai daya sani shiya
kawo min da kanshi” bada wata manufa ta furta maganar ba, amma da yake jarabar
kishi ce dashi, sai yaji kamar tana nufin tafi son ganin boss man akanshi shiyasa
tace haka, aikuwa nan take Ya haɗe rai, babu annuri ko misƙala zarratin, ganin ya
fusata yasa tace”meye faru my man”? Wurgar mata da jakar Yai ƙasa, da sauri Ya juya
Ya nufi ƙofar fita kamar zaiyi tuntu6e, Jiki na rawa tabi bayanshi tana ambaton
sunanshi”My man! Dan Allah ka tsaya muyi magana, Ni ce na bata maka rai ko? Pls am
sorry bazan ƙara ba, Ka yafe ni pls, bazan Iya bacci kana fushi dani ba”

Har ya kusa fucewa daga ɗakin, Can kuma sai ya dakata kamar mai tunanin wani abu,
Ba zato ba tsammani taga ya juyo a sukwane, ƙiris Ya rage ta hade kirjinta da
nashi, gadan gadan Ya tunkarota hakan da yai ba ƙaramin tsoro yaso ya bata ba, Juya
tayi da niyar ta faɗa toilet, ta 6oye sai dai kafin ta kai ga shiga taji Ya damƙi
waist dinta da ƙarfi Ya ɗaga ta sama kamar ɗiyar roba, tadinga ihu tana fadin Am
sorry my man dan Allah kada ka 6alla ni”

Batul dake a kwance tana sharar bacci, koke koken Angel ya fara takura mata sai
faman mutsu mutsu take Yi alamar zata farka.

ya tsareta da reddish eyes dinsa da launinsu Ya ciza tamar zallar red, da


kakkausar murya ya furta”meyasa kike son 6ata min rai”? Ya fada batare daya sauke
ta ƙasa ba,
Jikinta na kerma tana faman wutsil Wutsil da ƴan ƙafafuwanta tace”danish dan Allah
ka ƙyaleni, kaga Batul dake bacci tafara takura da surutunmu, kuma ni bansan laifin
me nayi maka ba, amma ina baka haƙuri ka tafi ɗaki ka kwanta”

Ta6e la66ansa Yai alamar bai damu ba, kafin ya sassauto da Voice dinsa”Kin hana
zuciyata sakat, tunda safe da kika rungume ƙaton nan Hankalina ba akwance yake ba,
nakasa samun sukuni, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nake ji, ke ko ajikinki, baki
leƙo dakina kin duba halin da nake aciki ba,saboda ke banci dinner dina ba, baki
damu dani ba, ko nema na bakiyi ba, saboda kin samu wanda yafi ni ko”

Runtse idanuwanta taɗanyi, hadi da dafe kai da hannu ɗaya, dama saida ranta ya
bata bazai ƙyaleta ba, saboda jarabar kishinshi, shiyasa yau ta hana shi ganinta,
duk dan ta tsira daga fushin shi.

Shirun da tayi mashine Ya ƙara 6ata mashi rai, Baisan sa’adda Yai zazzafan taku
Ya nufi Saman shimfidedan gadonsu, Ya jefar da ita Ta faɗa saman lallusar mattress
din, da sauri ta juyar da jikinta tai kwanciyar rubda ciki, gudun kada Gyaran
gashin da akayi mata ya tarwatse, Cikin shessheƙar kukan ƙarya Take Fadin”Nifa bada
son raina ya rungume ni ba, Hijab din jikina ce ta taɗiyoni na tafi zan kife ƙasa
shine Ya tarbeni na faɗa chest dinsa, kaima ka sani bani marmarin kasancewa da wani
ɗa namiji idan bakai ba, dan Allah kadaina tayar da hankalinka akaina, saboda Ni
taka ce kai kaɗai, shi mutumin ma da kake Yin kishi akanshi babbane ba matashi ba,
Ya isa ya haifemu nida kai”

Tun da ta fara yin magana, Ya rasa sukunin shi, Gyaran gashinta Yai matuƙar jan
hankalin shi, kamar princess, twisting din da akayi mata guda biyu saman gashin ya
ƙara mata kyau, sam bata ji motsinshi ba, ta dage sai haƙuri Take bashi, jin hucin
numfashinsa a jikinta Yasa tai wuff Ta juyo Tana fuskantar shi, har saida gabanta
Yaɗan fadi ganin Yadda yai mata rumfa, tuni tasha jinin jikinta, muryarta na rawa
ta furta”meye haka”
Lumshe mata ido yai tare da waresu saman fuskarta, abun ya ɗaure mata kai, Yana
neman ya rikitar da ita.
Ganin dagaske kamar wani abu yake so yai matane yasa ta fara canza mashi fuska,
zuwa ainihin true colour dinta, runtse ido tai da masifa tace”danish ka tashi ka
tafi ɗaki, wallahi kada ka bari na buɗe ido na ganka ranka zai Iya 6aci” saida ta
gama zazzaga mashi faɗan ta buɗe ido a hankali don taga idan ya tafi, ko gizau
baiyi ba yana nan yadda yake, Cikin zafin nama ta daddage ta ɗaura hannayenta saman
ƙirjinshi da niyar ta ingije shi, sai dai takasa yin hakan sakamakon wani abu daya
tayar mata hankali, a ruɗe take kallon shi ayayin da take kokarin mikewa zaune ta
jingina bayanta jikin headboard na gadon, Cikin sanyin murya ta furta sunanshi”My
man”

Idanuwanshi tuni sun fara canza launi, numfashinshi na fita da huci hucin zafi.

“Faɗamin meke damunka? Baka da lafiyane? Meyasa naji zafi ajikinka”?


Da wata irin kasala Ya kwantar da kanshi saman mattress dinsu, kasancewar Gadon
Yana da fadi Batul tana daga can 6angare guda.
“Kayi shiru baka bani amsa ba, kasan bana so Ina magana kana shareni,”
Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta”am sorry idan na 6ata maki rai, yanzu zan tafi
na kwanta” ya ambaci hakan tare da miƙewa ya sauko daga saman gadon, da sauri ta
biyo bayanshi tana ƙwala mashi kira, sai dai kafin ta isa gare shi, tuni Ya fuce
daga ɗakin, ƙofar tayi locking, kwantar da kanta tayi saman glass door Din, Jikinta
yai mugun yin sanyi, hankalinta Ya tashi ssai, ta girgiza da jin zafin jikinshi
tamkar hucin garwashin huta, taya zata iya runtsawa bayan bata da masaniya akan
halin da yake aciki? Gashi ya faɗa mata baici dinner ba duk don saboda da ita!
Ruwan hawaye ne suka taru acikin idonta, da sauri ta juya tana duban hadaddiyar
wall clock din dakin ƙarfe 10 na dare, badan taso ba ta haƙura da bin bayanshi amma
taci alwashin da asuba zata je ta dubashi, kamar yadda taga rana haka taga dare,
bacci ya ƙaurace ma idanuwanta, sai faman juyi take Yi saman gadonsu, duk ta takura
kanta ta hana zuciyarta sakat.

*FRIDAY MORNING🥳💃💃💃*

Bayan tasowa daga sallar asuba, dattijon arziƙi Ya nufi Sashen da bedroom dinsa
Yake hannun shi ruƙe da sanda, Farar Jallabiyace a jikinshi, lokacin daya ƙarasa
bedroom dinshi, da sandar hannun shi Ya tura ƙofar shigar shi keda Wuya kafin
ƙyaftawar ido Hasken ɗakin Ya ɗauke, duhu Ya mamaye idanuwanshi, Abunka ga tsoho
duk Yabi ya ruɗe, muryarshi Adabarbace yake fadin”subhanallah, Waye ya kashe min
hasken ɗaki? jazz bana son shaƙiyanci nasan kai kaɗaine zaka Iya min haka? Wai jazz
baka ji Ina magana” ya fada Yana cigaba da yin tafiya cikin duhu, Ya daura hannu
ɗaya jikin bango Yana laluban Switch don Ya kunna hasken dakin, Cikin 6acin rai
Yake Fadin”Jazz wallahi kada ka bari in kunna hasken ɗakin nan, ranka zai 6acine,
wato raini Ya fara shiga tsakanina dakai shiyasa har kake Yi min shegantaka ko”?

Daƙyar Ya samu Ya shafo switch din, a harzuƙe Ya danna button din, A hankali
Hasken ɗakin Ya soma gauraye ko’ina, tamkar da rana, Juyawar da zaiyi unexpected
Yaga abunda Ya bashi mamaki da al’ajabi, wato gaba ɗaya furannine launin ja da
yellow tun daga saman head boad har izuwa saman zanin gadonshi, An ƙawatasu masu
kyan gaske har ƙyalli suke Yi, tamkar a mafarki Yake kallon ikon Allah, A hankali
yake dogara sandarshi Yana tunkarar gadon tamkar maijin tsoronshi, saida Ya matso
kusa Ya ƙura ido Yana so ya gane rubutun me akayi da furannin, karantawa yai

*”HAPPY 80TH BIRTHDAY TO OUR BACKBONE”*

Lokaci daya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, Farin ciki mara misaltuwa ya
lullu6e shi, Sai faman sakin murmushi yake yi kamar wani zautacce, daga end bed din
Ya zauna, Yana ƙarewa furannin kallo, ranshi yana bashi cewar ƴa’ƴanshine suka
shirya mashi furannin, tabbas sune, Yayi mamaki babu wanda ya sanar dashi zasuyi
mashi hakan, Kuma atare dasu ya dawo daga masallaci, tun a babban falon gidan suka
rabu da juna kowa ya kama hanyar part dinsa.

Yayin da yake bin adon furannin da kallo, cikin sa’a idanuwanshi suka yi mashi
tozali da birthday cards birjik aka ajiye mashi don Ya karanta, kusan guda bakwai
daga saman kowani card an ɗaura fure, hayewa yai saman gadon har zuwa gaban cards
din Ya ɗago dasu a hannunshi kowanne yana da tittle dinsa da kuma sunan
mamallakinsa, Card din farko Sunan senate lateef ne, buɗewa yai ya soma karantawa
kamar haka.

_”To my dear father, thank you for always being there for me, guiding me, and
making me the person I am today. Your support, love, and encouragement have made me
who I am, and I’m so grateful for that”_

tuni idanuwanshi sun cicciko da ƙwallar farin ciki, Ajiye card din lateef yai, ya
buɗe card na biyu mallakin Sir mubarak Yana duban sakon cikin shi

_”From the bottom of my heart, I want to wish you a very happy birthday, Dad!
Your wisdom, kindness, and sense of humor have always brightened my days” annurin
fuskarshi sai ƙara nunkuwa yake Yi, haƙiƙa sunyi matuƙar faranta mashi da daɗaɗan
kalamansu, Yana matuƙar ƙaunar ƴa’ƴanshi.

Ajiye card din sir mubarak Yai, ya buɗe Na Sharafuddeen calmly ya ke reading
dinsa
“Happy birthday, Dad! You are the best father in the world and we are so lucky
to have you. May your day be filled with happiness and love.” hawayen da suka taru
acikin idanuwanshi tuni sun jiƙa fuskarshi, sumbatar card din Yai, kafin Ya daura
shi saman wadanda ya karanta, Ya duba sakon Prime minister

_”I’m so glad to have a father like you, who has been a rock of support through
the ups and downs of life. You’ve always encouraged me to be the best I can be, and
that means the world to me. On this special day, I just want to say thank you for
everything you’ve done for me. Happy birthday Baba tsoho much love”_

Dariya ya saki har fararen haƙoranshi suka Bayyana, Kalmar ƙarshe ta saƙon Hateem
ne Ya bashi dariya daya ce baba tsoho.
Lumshe idanuwanshi yaɗanyi yayin hawaye ke cigaba da wanke fuskarshi, abu ɗaya ne
yake fargaba a duniyar nan ranar da zai barta saboda ƴa’ƴanshi, bai sani ba
tsakanin shi da su wanene gawar fari, bai fata ma Wani daga cikinsu Ya riga shi
tafiya, bazai Iya jurar rashinsu ba, Ya ƙwammace mutuwa tafara Yin awon gaba dashi.

Sumbatar card din Hateem Yai, kafin Ya buɗe na saratu

- On this special day, I want to let you know how much I appreciate everything
you’ve done for me, Dad. You’ve always been my biggest fan and supporter, and I
can’t thank you enough for that. Wishing you a very happy birthday, with lots of
love My Baba, Allah yabarmun kai, madubin dubawata” manna ma card din kiss Yai
kafin Ya duba na sauran ƴa’ƴan nashi, waɗanda basu kaiga ƙarasowa Gidan ba, suma
sun bada saƙon da aka rubuta masu a cards dinsu.

Farin cikin duniya ya cika Obie, kwanciya yai saman furannin idanuwanshi na
fuskantar ceilling.
Ba zato ba tsammani Yajiyo sautin muryoyinsu acikin kunnuwanshi, Suna faɗin”Happy
Birthday To You, Happy birthday to You, Happy birthday to our Baba” zumbur Obinna
Ya yunƙura ya miƙe daga saman gadon Yana duban ƙofar room dinshi.
Dr. jazz ne Ya fara shigowa hannunshi ruƙe da madaidaicin Cake mai hawa huɗu daga
saman shi an jera candle, ga cake knife gefe ɗaya.

Shigowar dr.jazz ke da Wuya, Manyan ƴa’ƴan shi suke shigo ajere kowannansu sanye
da hadaddun jallabiyoyi, Mutun Na farko Sir mubarak ne daga bayanshi Senate lafeef
ne, wanda ke abiye dashi His excellency Abdul Razak ne Gomnan Jihar lagos, baisan
Yaushe Suka shigo garin abuja ba, Yayi mamakin ganinsu, zuwan bazata suka yi mashi,
ga kuma His excellency Deen Obinna Na jihar kaduna state, Daga bayanshi mai girma
sharafudden Obinna ne, Hannun shi ruƙe dana ɗan uwanshi Prime minister hateem
obinna, abun gwanin ban sha’awa, bayansu sai Saratu data shigo itama jallabiyarce a
jikinta ta yafa mayafi akanta, Fuskar kowannansu ɗauke da annurin farin ciki,
maimakon Ya taso Ya karaso garesu, sai kawai su ka ga ya fashe da kuka, haɗi da
sanya tafukan hannayenshi biyu Ya rufe fuskarshi.

Jikinsu duk Yai sanyi, duk da ransu yana basu cewar kukan farin Cikine Ya ke yi,
gefe da gefen gadon kowan nan su ya zauna kamar masu neman gafara, Senate lateef Ne
Ya fara magana
“Baba meyasa ka yin kuka? Dan Allah kada ka karya mana zuciyoyin mu, munci burin
mu faranta maka a wannan ranar mai albarka rana mafi daraja agaremu, ranar da abun
alfaharinmu Yazo duniya” ta tsakankanin yatsun hannunshi Yake satar kallonsu,
Muryar saratu da shagwa6a tace”baba please kadaina wallahi bamu jin daɗin ganin
hawayenka masu tsada suna zuba ƙasa”
“Baba idan baka daina kukan nan ba, muma zamu fara” acewar Sir mubarak
Mr.president sharafudden Yace”Daddy ka bamu dama mu share maka hawayenka da
hannayenmu please”
His excellency Deen Ya kar6e da cewa”daddy saboda kai, muka kamo hanya tunda duku
duku muka shigo abuja, saboda muhimmancinka agare mu, dan Allah ka buɗe fuskarka ko
mun samu damar ganinka, munyi kewar mahaifinmu” kalamansu ba ƙaramin karya mashi
zuciya suke Yi ba, sai dai yakasa cire takufan hannayenshi daga saman fuskarshi,
Allahu akhbar, wato Iyaye dabanne, duk mun muƙamin mutun shi bakomai bane agaban
Iyayenshi, gaba ɗayansu nan manyan mutanene masu ruƙe da manyan muƙaman ƙasa, masu
ƙima da daraja a idon duniya, Yau gasu zazzaune gefen gadon mahaifinsu, sun tasa
shi agaba suna lallashinshi, abun da yake ƙara haddasa mashi jin ƙaunarsu Biyayyar
da suke yi mashi, tun suna ƙanana har zuwa girmansu bai ta6a danasanin kasancewarsu
a matsayin ƴa’ƴanshi ba, basu ta6a sanyashi ciwon kai ba, samun ƴa’ƴa nagartattu
irinsu abune mai wuya a zamanin nan, damuwarshi tasu ce, suna matuƙar ji dashi suna
gatanta shi suna kyautata mashi shiyasa suke damun cigaba arayuwarsu saboda
albarkar dayake sanya masu.
Muryar His excellency deen Ce Ta katse mashi tunaninshi
“Baba munji kayi shuru baka ce komai ba, Idan akwai abunda ke damunka please Ka
faɗa mana, baka da tamkar mu a duniyar nan, ashirye muke da mu share maka
hawayenka”
da zolaya Sir mubarak Ya dubi jazz”faɗamin gaskiya kodai kaine ka 6ata mashi
rai”?
Jazz na murmushi yace”wallahi bani bane...” daƙyar ya ƙare maganar ganin irin
kallon tsiyar da hajiya saratu take watsa mashi, Muryarta a kausashe tace”tunda ka
kawo cake din miƙo min shi ka fuce kabamu wuri,” Jiki asanyaye Jazz Ya nufeta Ya
miƙa mata tray din, Tasa hannu ta ƙarba tana faman jifarshi da harara, sam bayason
barin Ɗakin, idan Yana atare da su ji yake kamar Yana acikin danginshi mantawa yake
yi da shi bakowa bane a family dinsu.
Har Ya juya zai fuce Muryar Hateem ta dakatar dashi”Zonan jazz” dakatawa yai dayin
tafiyar da sauri Ya koma gaban gadon, Hateem Ya sanya hannu ya kar6i cake din
hannun saratu Ya miƙa mashi”kamar yadda ka kawo shi kai nake so ka fara bashi”
ɗaure fuska hajiya saratu tayi badan tana jin shakkar Yaya hateem ba da kuwa babu
abunda zaisa ta bashi cake din, bawan Allah Jazz sai faman sakin murmushi yake yi,
ya kar6a Yana fadin”nagode daddy hateem,” jinjina mashi kai Yai batare daya ƙara
furta komai ba.
Baba, zamu tafi bamusan ko mune ke bakason gani ba, His excellency abdul razak ne
Ya furta hakan, Sai lokacin Dattijon arziƙi Ya zame tafukan hannayenshi daga saman
fuskarshi, tsufanshi Ya ƙara bayyana sosai, tamoji tamoji duk Ya kame fatarshi,
Zaro hanky Sir mubarak Yai daga cikin aljihun shi, Ya soma share mashi hawayenshi,
Bayan Ya kammala yasoma dubansu ɗaya bayan ɗaya, bi da bi, gaba ɗaya kamannin
fuskarshi suka ɗauko, Musamman sharuffudeen da hateem tamkar yai kakinsu, hatta
hasken fatarsu kalar nashi ne, launin idanuwansu ne dai kalar na mahaifiyarsu
reddish brown.

Ganin yadda duk suka damu ya sanya shi sakar masu fuska, cikin sanyin murya
yace”kai nifa ba wani abu ke damuna ba, Farin Cikin ganinku ne ya sanya ni kuka,
don haka ku kwantar da hankulanku, Jazz miƙo min cake din nan” Ya faɗa Yana ƙoƙarin
saukowa daga saman gadonshi, mimmiƙewa sukayi tsaitsaye suka kewaye shi, Tuni
damuwar fuskarsu ta washe
Miƙa mashi cake din Jazz Yai, sai da suka fara kirga mashi one two three kafin Ya
hura Iska Candles din jiki suka mutu, tafa mashi hannu sukai, sai faman sakin
murmushi yake Yi,
“Wazai fara bani cake din” ya fada yana dubansu,
Matsa ma jazz hanya sukayi Ya matso kusa dashi, Hajiya saratu ji take kamar ta
ingiza ƙeyarshi taji haushin kasancewarshi acikinsu, aganinta bashi ya dace Ya
shigo cikinsu ba, Ina laifin su twins suda su ke jikokinshi.

Shikuwa Hannunshi Har kerma yake yi wurin daukar wuƙa, Ya gutsiro cake din Ya
miƙa mashi abaki, Ya soma ci atsanake Yana duban Jazz hada ɗaga mashi gira Ya
furta”Waye ya haɗa min wannan? Yai min daɗi”
Jazz yace”mommyna ce ta haɗa maka shi” jinjina kai yai”amma ta iya na jinjina
mata” daɗi jazz yaji An yabi cake din mahaifiyarshi, saratu kuwa takaicin duniya ya
isheta.
Daya bayan ɗaya suka soma bashi cake din Yana ci, Kafin shima Ya kar6a Ya bi
kowannansu Ya bashi abaki, Bayan sun kammala ci, Ya daura cake din saman table,
Rungumarsu Ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana bubbuga bayansu da hannayenshi kamar
yadda ya saba yi masu tun suna Yara.
Saman gadonshi Ya koma ya zauna yace masu duk su zazzauna yana son yaita kallonsu,
hakan ba ƙaramin daɗi yai masu ba, kamar yadda ya basu umarni haka suka samu wuri
saman mattress din suka kewaye shi.

Banda jazz wanda tuni Yajima da komawa ƙofar ɗakin, ganin irin kallon barazanar
da hajiya saratu take Yi mashi kamar zata shaƙe shi.

Tun wuraren ƙarfe goma sha biyu na safe, Hamshakan motoci keta kurɗaɗowa cikin
gidan tunkafin lokacin da za’a fara gudanar da shagalin Ya gabato, sun Cika gidan,
kasancewar Baba Obie mutunne mai tarin jama’a, wasu ma ba a ƙasar suke zaune ba,
amma aranar sai gasu sun shigo Nigeria duk don saboda su halacci taron taya murnar
ranar haihuwarshi, Masu aikin gidan sai zarya suke Yi wurin Kaima baƙi abinci dana
sha, kitchen ya zama Dandalin magulmata, Bakunansu ko gajiya ba su yi da surutu.

“Yau zamu ba idanuwanmu abinci har su ƙoshi” Safa ce tai maganar,


Sophia tace”Hmm, aini yin aiki agidan nan gaba ta kai ni gobarar titi ajos, waiku
kunga haɗuwar Prime minister Hateem da matarshi! Wow masha Allah, Allah Yayi
halitta”
Marwa tace”shi kaɗai kika gani kenan, baki ga Mai girma sharafudden ba, ai
hadashi jiya cikin waɗanda sukaje airport tarbo prime minister, wallahi mutumin ba
ƙaramin burgeni yake Yi ba, dashi da ɗan uwanshi hateem, mutanan badai aji ba,
komai nasu da dattako suke Yin shi.

Abla tace”yau zamuci uwar sabada, zamu tashe mu watse, Mu raƙarƙashe don nasan
dole agayyaci mawaƙa da makaɗa, Ni nama rasa wani kaya zan sanya wallahi”

da zolaya safa tace”kalar dangi, Uban wa kike tunanin zai barki ki shiga hall din
taron? Ke kin isama? Sannu isassa mai walkin sa, ai kawai ki tsaya a iya
matsayinki, Ta ina zaki nemi haɗa kafaɗa da Manya manyan hamshaƙan attajiran masu
kuɗi, ai idan kin ganki a hall din can to amatsayin mai raba abinci zaki je” dariya
suka saki.

Abla tace”Nima fa da wasa nake wallahi, Ai ni tsoronma shiga zan ji, jiya izuwa
yau bani da kwanciyar hankali saboda jami’an sojojin da suka kewaye estate din ciki
da waje, nasan duk zuwan hateem ne yasa aka ƙara tsaro har haka”

Marwa tace”niko inaso na tambaya, abun yaɗan tsaya min araina,” har suna haɗa
baki wurin tambayarta menena,
Numfasawa tayi kafin ta soma magana”kunsan ni ban jima da fara aiki acikin gidan
nan ba, abun da yaɗan ɗaure mun kaina, taya akai hateem da yake ɗan kasar Nageria
Yake mulkar ƙasar turawa mai girma kamar canada, dama hakan yana iya yiwuwa? Ta
tambaya tana duban fuskokinsu,
Safa ce tafara Kora mata jawabi”bazai yiwu ba sai dai idan ya kasance, shima ɗan
kasarne, Misali kamar idan acan canada aka haife shi, kinga yana da ƴancin da zai
Iyayin duk wani abu da ɗan kasar zai yi, ko kuma idan mutun ya zauna a wata ƙasa
wadda ba tushen shi ba, har na tsawon adadin shekarun da zai iya cika duk wasu
sharudda daya cancanta ya zama ɗan kasar shima yana da right da zai Iya aiwatar da
duk wani abu da ɗan ƙasar zaiyi, shi kuma Hateem da kika gani asaline dasu a kasar
canada, tushen mahaifiyarsu ne, Allah yajiƙanta, ta fito daga babban family daya
shahara a ƙasar canada, bakomai nasani dangane da tarihinsu ba nima hajjaty ce
tafara bani, kinsan mahaifinsu yayi yawon duniya sosai, kuma yana da farin jinin
al’umma, duk inda ya shiga saiya samu kyakkyawar tarba, Ya zauna a kasashe daban
daban tunkafin Ya auri matarshi ta farko, mariganya Hajiya kudirat, Allah yakai
rahama ƙabarinta, itace ta haifa mashi Yan ukun shi, Senate lateef, sir mubarak da
abdul razak na lagos, bayanshi sai Deen obinna, da kuma saratu autarta, Hajiya
kudirat jinin sarauta ce, ta fito daga tsatson sarkin yarbawan jihar lagos, marwa
tace”Ikon Allah shiyasa hajiya saratu take da jinkai, Ashe suma Izzar sarautace a
jininsu” murmushi kowannansu ya saki, Safa ta numfasa kafin ta ɗaura da
cewa”sharafuddeen kuma da Hateem uwa ɗaya uba ɗaya suke, Idan kika lura sunfi
kamanceceniya da juna, duk da gaba ɗaya ya’yan obie dashi suke kama, babu wanda ya
ɗauko mahaifiyarshi, har ƙwara Saratu ta ɗauko kama da Hajiya kudirat, bari in baki
amsar tambayarki, Hateem dai a hannun dangin mahaifiyarshi can ƙasar canada Ya taso
acan aka haife shi, kuma acan aka raineshi, mahaifiyarsu bata ta6a zama a kasar
nigeria ba, Idan kinga tazo to zamane na ɗan lokaci, sai dai shi obie din ya taka
yaje inda take tare da ahlinsa, shiyasama har family house garesu a ƙasar canada,
shi kuma sharafudden da kika ga Ya taka matsayin shugaban ƙasa a nigeria bayan
mahaifiyarsu ta haifeshi a canada, to shi ba a kasar aka raine shi ba, Ya zauna a
hannun dangin mahaifinshine anan nigeria tun Yarintarshi har zuwa girmanshi, Idan
kina neman ƙarin bayani game da hateem, Ki binciki tarihin Barack obama tsohon
shugaban ƙasar america Kusan tafiyarsu ɗaya kinsan shima mahaifinshi ba ɗan kasar
america bane, tushen mahaifinshi daga africa ne” murmushi kowannansu Yasaki, Marwa
tace”ai basaima na bincika ba, Na gamsu da bayaninki sosai, Kin wayar min dakaina,
Da ina kokwanton taya haka zata yiwu ɗan nigeria ya mulki wata ƙasa, amma yanzu kin
goge min kokwantona, gaskiya abun Ya ƙayatar dani, balle shi hateem ma da ba Iya
haihuwarshi acan akayi ba, Tushen mahaifiyarshi ne”

firar da sukeyi bata dauke masu hankali Ga yin aikinsu ba, kasancewar sunada
yawa, akwai wadanda ke zaryar kai abinci, ba iya su kadai bane.
“Ni dai fatana Allah yasa uban Ƴan ji da izzar nan yazo yau” sophia ce tai
maganar,
Abla tace”Ai ga ƴar uwarshi nan uwar ji da Izza, Itama ta duro gidan, zanso inga
haduwarsu”
Safa tace”Kina nufin Nazli”? Jinjina kai Able tai”ita nake nufi, Yarinyar badai
Ji da kai ba, ta Iya haɗe fuska bata da fara’a, Har ƙwara Yazrin tafi sakewa da
mutane duk da itama bakowa take hulda dashi ba”
Marwa tace”ke kuwa ai dole suyi izza, jinin sarautar dubai, Jikokin sarkin
sarakai, Ga uba shugaban ƙasa sukutun da guda, uwa uba ga kyau kamar su suka tsara
halittarsu, Ni wallahi burgeni suke Yi, takun tafiyarsu kadai abun kallone”
Safa tace”ga kuma Hindu, nasan itama yau zata shigo gidan, itada mahaifiyarta
Hajiya sarauta, mace mai ji da izza”
Ta6e baki Sophia tayi”Um, nifa mutun ɗayace bana son ganinta, Hajiya laurat
saboda bata da mutunci matar, ƙyamar talaka gareta”
Dariya Abla tasaki tana fadin”kin kuwa san dole ta halacci taron nan, zata haɗu da
ƴar uwarta Aunty masifatu, mu kuma mun shiga uku” dariya suka sanya gaba ɗayansu
kafin suka maida hankalinsu akan aikin dake gabansu.

*HAJJATY❤*

A kwance suke saman gado, manne da juna, yahanata sakat tun ɗazu take son leƙawa
kitchen pravin Ya hanata motsawa, ga tarin ayyuka dake jiranta, tun asuba ya shigo
ɗakin.

Muryarta da kasala take ambaton sunanshi”Pravin pls ka tashi ka tafi ɗakin


matarka, baccin Ya isa haka, Ina da ayyukan da zanyi kada aji ni shiru a matsayina
na babba acikin masu aikin gidan nan”

A hankali Ya buɗe idanuwanshi da suka kaɗa jawur yana dubanta dasu.

Sai faman lumshe su yake yi, don ba ƙaramin nauyi suka yi mashi ba, Short ne
ajikinshi babu riga jallabiyar shi tana a saman mattress din, Ita kuma Iya undy ne
tayi daurin gaba dashi, shara shara kana Iya ganin tsiraicinta.
Kamar baisan furta maganar yace”dan Allah ki ƙyaleni, bana jin daɗin jikina ne,
ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai damu don baki aiki”
Ya faɗa haɗi da ɗaura hannunshi saman sumar kanta dake akwance saman bayanta, a
hankali yake shafa gashin
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Na roƙe ka, ka tashi ka tafi dan Allah,
Matarka zata Iya nemanka”
“Meye damuwarki aciki, duk kin wani ɗaga hankalinki”

Murguɗa mashi baki tai”Pls my baby boy, kasan yau babbar ranace agaremu, yakamata
mu shiga cikin dangi ai hidima tare damu”
Jinjina mata kai yayi’okey, naji zan tafi but before that, Inaso zan gargadeki,
kinga yau akwai manyan mutanan da zasu halacci taron nan, banason inga gifcinki
awurinsu, don na lura ba ƙaramin jan hankalinsu kike yi ba”

Farfari tayi mashi da ido”idan kaga banje wurinsu ba to bana numfashine, hakanan
kawai kake min baƙin ciki, don kada in samu mijin aure, kai kayi aure ni kuma ka
hanani sakat” da zolaya tayi mashi maganar.
Lumshe mata ido yai, ya tsare kirjinta da kallo kamar ba yanzu ya gama tsotsarsu
ba.

“Nidai na faɗa miki kuma na ƙare maganata, idan kika ƙara yi min irin wannan
maganar zanyi maganinki ne”
“Ashirye nake dana kar6i kowani irin hukunci da zakayi min, nasan dai bazaka Iya
cutar dani ba” ta faɗa tana tura mashi kirjinta, aiko da karfi Yakai masu cafka, ta
fasa ihu tana dariya, kutsa kanshi yai cikin undy dinta Ya cigaba da wasa da
jikinta, tsawon mintuna kafin ya fito da kanshi ya haɗa uban gumi, sai faman sakin
nishi take Yi tana haki kamar wadda tasha gudu
“Ki rakani toilet muyi wanka, jikina ya 6aci sosai” harara ta jefa mashi”ni bazan
bika ba, kaje wurin hajiya saratu tayi maka wanka” zaro ido yayi”ahaka ɗin” ɗaga
mashi gira tai alamar eh.
‘Idan ta tambaye ni waye yai silar jefa ni yanayin Nan me kikaso in fada mata”
Da shagwa6a tace”saika fada mata nice” da karfin hali ta furta hakan
Dariya pravin yai”aiko da wa’adin aikin ki agidannan Ya ƙare, har kashe ki zata
Iyayi, don ba ƙaramin kishine da ita ba, daga ni harke zata yi mana korar kare”

“Kaga sai mu koma ƙauyanmu na indiya mucigaba da yin bautar shanu” dariya suka
sanya gaba dayansu
Bayan sun lafa ya sanya hannu biyu ya cuccu6eta Ya nufi bathroom da ita, Jim kadan
Ya fito da ita ya ɗaurota saman kafadarshi, asaman gado ya kwantar da ita Yasanya
mata bargo ya lullu6eta yana fadin”ki kwanta ki huta pls, bana son kina aikin
wahala, inyaso da anjima saiki shiga cikin gidan” amsa mashi tayi da toh badan taji
maganarshi ba.
Shaf shaf Ya zura jallabiyarshi Yai mata sallama kafin ya fuce daga Cikin ɗakin,
Fitarshi keda wuya wayar shi daya manta saman bedside drawer ta soma yin ringing,
Ba tare data futo daga cikin bargon ba, Ta mika hannu tana laluban wayar har tayi
nasarar Cafkota, ta fiddo da kanta tana duban screen din
A tsanake ta furta sunan daya bayyana da manyan haruffa.

*Jan le6e* ta6e baki ta ɗanyi aranta ta ayyana kowane ne wannan mai suna jan
le6en? Sunan ma dariya yaso ya bata wai jan le6e, bazata Iya picking call dinba
saboda Ya hanata ɗaga mashi phone idan aka kira, ko wayar bai bari ta ta6a ba, Sau
ɗaya kiran ya shigo tai rejecting ba’a ƙara kira ba.

Ajiye mashi wayar tayi saman drawer, ta dan lumshe idanuwanta yayin da
zuciyarta ke tariyo mata fuskar kyakkyawan ɗansu da suka rasa, taji baƙin cikin
mutuwarshi har yau idan ta tuna shi sai hawaye sun cika idanuwanta, tana matuƙar
ƙaunar yaron, tsawon mintuna kafin ta yunƙura ta sauko daga saman gadon, donta
kimtsa ta nufi kitchen.

Idan muka koma 6angaren Unaisah, tun bayan kammala sallar asuba, ta nufi ɗakin
danish ba tare da sanin kowaba, tana shiga ta same shi kwance saman lallausar
carpet din dakinshi amaimakon saman gadonshi, dogon hijabi ne a jikinta launin
maroon, zuciyarta duk ba daɗi, daga gefenshi ta zauna tana duban kyakkyawar
fuskarshi, lokaci ɗaya taji gabanta na faɗuwa, sakamakon ganin yadda yake firgita
acikin baccin shi, da sauri ta ɗaura Hannayenta saman ƙirjinshi Nan fa hankalinta
Ya ƙara tashi Jin temperature dinshi, kamar na daren jiya, lamarin Ya ɗaure mata
kai, Ga sanyin A.c har yayi yawa amma shi zafi ne a jikinshi, babu sassauci,
Muryarta na rawa ta soma ambaton sunanshi”Danish! my Man? Wake up! Meke damunka?
Why nake jin jikinka da zafi” can cikin baccinshi yake jin miryarta.

“Dan Allah ka tashi kayi min magana meke damunka? Baka da lafiyane”?
Daƙyar ya samu damar ware idanuwanshi Akan fuskarta,
A daddafe ya samu Ya miƙe zauna yana dubanta, Short din Jiyane a jikinshi da
singlet.
Yaji dadin ganinta a room dinshi, Jiya yai zaman jiranta yai tunanin zata zo
gare shi har bacci yai awon gaba da shi bata leƙo ba, till now.
“Kayi shiru baka ce min komai ba, danish zafin jikin ka yai yawa, kodai inje in
faɗa ma Boss Man Yazo Ya duba ka”? Girgiza mata kai yai, kafin ya motsa la66ansa Ya
furta”babu abunda ke damuna, Lafiyata qalou, kece kika 6ata min rai”
Hankalinta bai kwanta da kalamanshi ba, aɗan ruɗe ta furta”ba haka bane danish,
dole akwai abunda ke damunka ba Iya 6ata maka rai da nayi bane, cos babu yadda
za’ai Jikinka yadau zafi rau batare da dalili ba, Please ka faɗamin idan ba haka ba
hankalina bazai kwanta ba, sannan kayi hakuri dan Allah, abunda ya faru Jiya wanda
ya 6ata maka rai, In sha Allah bazan ƙara bari Hakan Ya faru ba”
Cikin kulawa take Yi mashi magana, Jinjina mata kai yai”kiyi min alƙawarin ba zaki
ƙara rungumar wani ƙato a jikinki ba, idan bani ba koda su Naufal ne” kiris ya rage
ta saki dariya jin abunda yace
Jinjina mashi kai tayi”in sha Allah My man kai kaɗai kawai,” ajiyar zuciya ya
sauke Ya samu sassaucin radadin da zuciyar shi ke yi mashi
“Tunda naga yanzu hankalin ka ya kwanta fada min meke damunka? Menene ya haddasa
maka zafin jikinka”? Ta faɗa tana duban ƙwayar idonshi, la66ansa duk sun bushe
ƙamas.
“Dagaske nake Yi maki babu abunda ke damuna, Nima bansan ya akai jikina ya ɗauki
zafi ba”
“Nidai hankalina bai kwanta ba, ka ba ni dama inje in faɗa ma boss man halin da
kake aciki,” haɗe mata fuska yai jin ta ambaci sunan boss man, sam bayason ji.
“Bana buƙatar kowa ya dubani, ki kwantar da hankalin ki, zafin jikina baiyi min
illa ba, don haka kija baki kiyi shiru”
Jinjina mashi kai tay”maganar abinci fa? Jiya kace min ba ka ci dinner dinka ba,
ni sam Na shafa’a”
Yamutsa mata fuska Yai, hada jifarta da harara, murmushi tasakar mashi
“Bari naje na duba dining, idan an shirya mana abincin breakfast dinmu, zan shigo
maka da naka a ɗaki tunda baka son fita” ɗaga mata gira yai alamar okey.
Miƙewa tayi da sauri ta fice daga dakin ta sauko down stairs, koda ta duba ɗakin
cin abincin ba a jera masu komai ba, saboda time din da suke zama Yin breakfast bai
cika ba” yanke shawarar neman ɗakin Ummi tayi don ta fada mata game da ɗan uwansu
dake jin yunwa, wata’ƙil ta sama mashi abunda zaici kafin a shirya masu abincinsu.
Batasan ina zata nemo room din ummi ba, tadaisan acan upstairs Yake, cos ta ta6a
ganin tana saukowa saman bene, da sauri ta nufi stairs din tana tafiya Hijabin
Jikinta naja da ƙasa, babu kowa a palourn duk suna adaki.
A hankali take taka stair cases din Har ta samu ta haura can sama, Ta rasa wace
hanya zata bi wadda zata sada ta da bedroom din Ummin america, Tafiya taci daga
dayi tana bin ko’ina da kallo, aranta tana ƙara jinjina haɗuwar ginin, tana ta ƴan
kalle kalle kamar baƙauya harta zagayo ta 6angaren Hagu batare data gano hanyar da
zatabi ba, Ƙofar wani katafaren room Ta dakata da yin tafiyar, aranta ta tace”idan
kuwa wannan ne ɗakin aunty ummi duk Yafi namu kyau” Ta cikin glass din ƙofar take
hangen zallar haɗuwar kayan alatun cikinsa, kifa kanta tayi jikin ƙofar har ta
danna madannin Jikinta batare data an kare ba, da alama mamallakin ɗakin Yayi
recieving alert na neman iznin shigowa shiyasa ƙofar tafara ƙoƙarin zugewa slowly
take sliding, da sauri Unaisa Ta saki glass din Jin yana motsi, abunka game
karanbani, ganin ƙofar ta wage, sai kawai ta haura ƙafarta ciki, yau ta ga maƙurar
aljannar duniya a ɗakin data faɗo, wuyanta kamar zai 6alle, tana tafiya tana ƴan
waige waige kamar zatayi tuntube, tayi mamakin dukiyar da aka narka wurin tsara
Kayan furniture din dakin, Yana da fadi da tsayi, ga wannan floor to ceilling
window din a left hand din bangon ɗakin, Ta jikin glass din zaka Iya hangen wajen
ginin Harma da manya manyan gine ginen dake acikin burnin abuja, bayan haka daga
cikin bedroom ɗin zaka Iya hangen komai na cikin bathroom ta glass din ƙofar, sai
dai da alama ba haka akeyin wanka acikinshi ba, da akwai hanyar da ake rufe glass
din yai duhu idan mutun zaiyi using dashi.

Sai faman jinjina kai Unaisah take Yi, tajima tana mamakin wanene mamallakin
daular nan da suke acikinta, bata ta6a yin tozali da shi ba, tadai ta6a jin sunan
Chief of isod abakin Dr Laura.
Tabbas Da ace tasan ɗakin wanene da batayi gigin shigarshi ba, ta zaƙe sai
kurɗaɗawa take Yi can ciki ta shige kamar ɗakin baba tajo, shi kanshi bedroom din
Yana da katafaren falonshi Har yaci uban na down stair haɗuwa, tana ƙoƙarin giftawa
ta wata ƙofa dake a ɗakin, kwatsam kunnuwanta suka soma Jiyo mata sautin daddaɗan
kiɗa Yana tashi, na taken waƙar satisfya

Wani irin daddaɗan ƙamshi Ya ratsa hancinta sosai ta shaƙeshi, a hanzarce ta


ɗaura idonta saman kofar ɗakin rubutun sama ta karanta kamar haka
*Gym room” nan take ta fahinci dakin menene, wato wurin motsa jiki ne” aranta ta
ayyana bari ta dan leƙa taga wanene Ya kunna sautin kiɗa.
Kasancewar ƙofar abuɗe take, Unaisah ta zura kai kamar 6arauniya tana bin ko’ina
da kallo, an ƙawata room din da injinan motsa jiki, kala kala, ga kayan jin sauti,
sam bata lura da shi ba, kamar yadda shima bai lura da mutun ba, Yadaisan akwai
wanda ya shigo dakinshi saboda alert din da yai recieving awayarshi, saida Ya bada
iznin shigo ciki tukunna ƙofar ta buɗe.

Sai faman wurwurga eye balls dinta take tana bin ko’ina da kallo, lokacin da tayi
arba dashi wani irin mugun bugu ƙirjinta Yai, har saida ta dafe shi da hannu, tayi
matuƙar firgita da ganin shi, Ya tattara hankalinshi gaba ɗaya akan Punching bag
din da yake kaima naushi da hannayensa waɗanda ke sanye cikin boxing gloves, Cikin
zafin nama yake motsa jikinshi, Ya haɗa uban gumi, zufa ta ko’ina take tsattsafo
mashi, ƙirar ƙarfinshi Ta bayyana ga wannan sick pack din ƙirjinshi ruɗu ruɗu,
Damtsen hannayenshi sun murmurɗe, Yana naushin jakar motsa jikin Breast muscles
dinshi na shaking, babu riga ajikinshi, black short ne kaɗai Ya sanya wanda Ya
tsaya mashi dai dai gwiwarshi, bata samun damar ganin fuskarshi dakyau ba, saboda
ba ita Yake fuskanta ba.
Ta natsu tana kallonshi, Ko idonta bata ƙyaftawa, ba zato ba tsammani taji an
damƙi wuyanta ta baya, harta buɗe baki zata fasa Ƙara taji anyi saurin toshe mata
baki, tsoro Ya kamata jikinta ya hauyin kerma, ɗungurugum taji an dagata sama
Anjata zuwa cikin bedroom din, sai faman wuntsila ƙafafuwanta take Yi a ƙoƙarinta
nata kwace kanta daga hannun mutumin daya dauketa, har ƙofar ɗakin Ya fito da ita
Ya direta ƙasa, A firgice take dubanshi, bakomai bane face Big guy, kayan kakinsu
ne a jikinshi, ya sanya face mask a saman fuskarshi, idanuwanshi na akan fuskarta,
La66anta na kerma ta furta”wa..wa.. Wanene kai? Meyasa ka daukoni? Idanma saboda
nashiga ɗakinne aini bansan ya akai na shiga ba, rashin sanine, ɗakin aunty ummi
nake nema, danish ne Yake jin yunwa jiya baici dinner din shi ba kuma na duba
dining ba’a shirya mana abinci ba” tsabar ruɗune yasa take yi mashi zuba har abunda
bai tambayeta ba, taƙi barima Yai mata magana
Sai da ta dasa aya tukunna Ya soma yi mata magana cikin muryar raɗa”kinsan ɗakin
wanene kika shiga”? Girgiza mashi kai tayi alamar a”a gyaɗa kai yai”kada ki kuskura
ki ƙara yunƙuri shiga ciki, Idan ba haka ba jikin kine zai gaya maki, Ni nayi
mamakin ma taya akai kika samu damar shiga bayan ita kanta ƙofar sarrafata akeyi,
Kodai ba mutun bace ke”? Ya fada haɗi da ɗage mata gira alamar yana jiran amsarta.
Duk tabi tasha jinin jikinta, sai faman zare mashi gray eyes dinta take Yi,
daƙyar Ta iya fadin”nifa bansan komai ba, ai na fada maka dakin aunty ummi nake
nema” ta ƙare maganar tana murguɗa mashi baki.
Har murmushi yasakar mata batare data gani ba saboda mask din fuskarshi, dama Yaji
labarin rashin jin maganarta, gashi yanzu ya tabbatar dahakan”
“Okey, ki koma ɗaki, yanzu zanzo in kawo maki abunda shi ɗan uwan naki zaici,
kafin Ashirya maku naku abincin” amsa mashi tayi da toh, jikinta har rawa yake Yi
wurin yin saurin haura ƙafa ta kama hanyar komawa ɗakin danish, tana tafiya haɗi da
waiwayan big guy, Yana atsaye yana kallonta har saida ta 6ace ma ganin shi, tukunna
ya kawar da idonshi daga gareta.
Tun da ta koma ɗakin danish bata daina tariyo suffar mutumin da tayi tozali dashi
a gym room ba, Ya tsaya mata aranta, taso ace sunyi ido biyu da shi, don ta samu
damar ƙare ma fuskarshi kallo, shin wanene shi? Tabbas tanaso ta sani!
Bada jimawa ba, Big guy yai sallama dakin danish, hannunshi ruƙe da tray din
Kayan abinci ashake, bayan ta kar6a tayi mashi godiya, asaman carpet suka zauna ita
da danish, ta dinga bashi abaki Yana ci, suna kallon juna yayin da acan ƙasan
zuciyarta tunanin ɗan ta halikin nan take Yi, shi kanshi danish Ya lura da
canzawarta, saboda tsabar tunani har a hanci tai ƙoƙarin cusa mashi abinci, saida
ya damƙo hannunta tukunna ta ankara, yace mata me take tunanine tace mashi bakomai,
badan ya yarda ba ya ƙyaleta, A ɗakinshi ta zauna duk don ta faranta mashi, sai da
tasanyashi yai wanka ya canza kayan jikinshi tukunna hankalinta ya kwanta,
damuwarta ɗaya yanzu zafin jikinshi sai ƙara ninkuwa yake Yi.

*Obie Estate*

Wuraren ƙarfe huɗu da rabi Estate din Ya cika maƙil da mutane babu masaka tsinke,
manya mutane masu faɗa aji duk sun hallara, kama daga Ƴa’ƴan jam’iyarsu ta Action
progressive party ministoci, sanatoci, gomnoni, da sauransu, Kowannansu Ya ɗauki
wankan expensive shadda ta kece raini na shiga tsara, jikokin Obinna Na ƙasa
nigeria da wadanda ma basa ƙasar saboda shagalin nan sun dawo Nigeria A yau din
nan, daga cikinsu akwai ya’yan sir mubarak mazauna kasar canada, zaratan samari
Zaki shine babban ɗanshi mai bi mashi Ibad, bayansu sai ƴa’ƴan His excellency abdul
razak, babban danshi Yasir, tare da ƙanwarshi Yusra, sunzo ne tare da mahaifiyarsu
Her excellency hajiya muhibbat, bayan su sai Ya’yan his excellency Deen, babban
ɗanshi Justice Nadeem mai bi mashi Dr. nawaz tare da mahaifiyarsu suka zo Her
excellency hajiya Jamila, bayansu kuma sai ƴar gidan mai girma sharafudden Hindu
ƙanwar Chief Owais, tare da matayanshi suka zo Hajiya Malikat sarauta uwar gidanshi
da kishiyarta Hajiya laurat, da kuma ƴar wurin Lateef zulaihat kanwar ziyad, gaba
ɗayansu dai kowa Ya hallara ga yan matan hateem Nazli and Yazrin, gaba ɗaya matan
sun ɗauki wankan Swiss cord lace yayi bala’en Yi masu kyau, A babban hall din dake
acikin gidan aka gudanar da shagalin, An ƙawata cikinsa da kayan alatu, ko’ina ka
kalla furannine da ƙyalƙyalin sparkling chandeliers, ga Banquet chairs da aka
tanada domin baki su zauna, kowani table saman shi an ɗaura bouquet of flowers,
tare da Crystal glasses and silverware, da sauransu, floor din hall din kuwa an
shimfiɗe shi da ƙayataccen red carpet, daga can gaban hall din Gingirimeman Cake
stand ne an ƙawata shi sosai, Mawaƙa da makaɗa hada maroƙa sun hallara, domin suma
su kwashi rabonsu, an shirya kayan abinci saman zungureran table kala daban
daban, sai mutun Ya za6a ya darje, duk haɗuwar taron nan mutun ɗayane bai
hallaraba, Hakan ba ƙaramin ta6a zuciyar obie yai na, Yaci buri akan zuwanshi amma
shiru babu shi babu alamarshi, mutane sai tambayar shi suke Yi, ya akai basu ganshi
ba? Iyayenshi sun rasa amsar dazasu basu, sai dai suka dinga cewa bai kaiga zuwa
ƙasar ba, farin jini gare shi shiyasa duk wanda yazo sai ya tambayi ina owais Yake,
Taro Yayi albarka, Anci ansha anyi kullu wash rabu hani’an, Anyi harka ta arziƙi ta
kece raini, daruruwan mutanan dasuka kawo mashi kyauta taban mamaki basu ƙirgiwa,
baba obie Ya mori lokacin shi, Yayi farin cikin dabazai Iya misalta shi ba, Ƴan uwa
da abokanan arziƙi sun faranta mashi rai, sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban
mamaki, Sun taka rawar girma, sai dai muce Alhamdulillah taro Ya tashi Lafiya, gab
da magrib baƙi suka ragu waɗanda suka rage ƴan uwane na jini, da kuma mutanan
Hateem.

*WAIWAYE ADON TAFIYA💫*

(Abunda ya faru bayan zahra ta faɗa ma Aneelerh halin da take aciki, Na kuɗi da
hajiya falmata take binta bashi, bayan ta koma ɗaki damuwa ta isheta, tayi ƙarfin
haline kawai wurin bata shawara akan ta amince da buƙatar hajiya falmata saboda
tana son ta jaraba zahra ne don taga idan tana da hankali, tunani ta soma yi ta
wace hanya zata Iya taimakonta? Nan take zuciyarta ta bata shawarar tayi amfani da
sauran kuɗin nan da jami’an sirri suka bata, har yau bata ƙarar dasu ba, tamkar
tana jin tsoron ta6a su, tun dai data siya ma baby junaid kayan wasa bata ƙara
cirar ko naira biyar ba.

Ba tare da sanin kowa ba Aneelerh ta tuntu6i mahboob, a ɗakin shi ta same shi, ta
tambaye shi koya san gidan hajiya falmata mahaifiyar ƙawar zahra? Yace mata eh
yasan gidan, sun ta6a zuwa tare da zahran ma, tace toh so nake ka rakani gidan, da
mamaki akan fuskarshi yace amma me zakiyi acan din kinsan ta ne? girgiza mashi kai
tay alamar a’a, kawai inaso ka rakani muje, idan mun fita zan faɗa maka komai, amma
kafin muje gidan zaka fara rakani banki, akwai wasu kuɗi da nakeson in cira, Jin ta
ambaci kuɗi yasa mahboob saurin amincewa zai kaita gidan, a cikin motarshi ya dauki
aneeleeh saida suka fara biyawa banki ta ciri kuɗin kafin suka nufi gidan hajiya
falmata.

Lokacin da suka karasa gidan, A parking space mahboob Ya tsayar da motar,


Aneelerh tace dashi ya jirata anan, ya amsa mata da toh, da sallama abakinta ta
shiga palourn gidan, adai dai lokacin mai aikin gidan ta fito daga kitchen ta yi
arba da aneelerh, fuskarta da fara’a suka gaisa tace mata wurin hajiya falmata
tazo, Allah yasa tana nan, Mai aikin tace bata jima da dawowa daga office ba, ki
zauna bari naje in sanar da ita, da sauri mai aikin taje ta fado mata, jim kadan ta
dawo ta sanar da aneelerh sakon hajiya tace ta jirata gata nan zuwa, aneelerh ta
amsa mata da toh, kusan mintuna biyar Aneelerh tana a tsaye ta ruƙe qugu tana jiran
fitowarta, cikin jin fargabar ganin matar, sai faman bin palourn take yi da kallo.

Sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin Aneeleerh ga kallonta, A hankali take


saukowa down stair, ta ɗauki wankan tsadaddan leshi, kanta yasha ɗaurin ɗan kwali,
ta manna farin glass a idonta, Babbar macace tana da jiki, tana tafiya tsokokin
jikinta na motsawa, Fatar jikinta tasha hutu har ta gaji, daga ganin fuskarta
masifaffiyace, idanuwanta mitsi mitsi da su kamar na mutanan Yankin china, hancinta
kuwa abaje yake, ga big mouth dinta yasha man baki.

Ta6e baki Aneeleerh tayi aranta ta furta jibarta dan Allah, ƙatuwar banza da ita
kamar buhun masara, a haka take lalata rayuwar matasan ƴan mata, Allah dai ya
shirya, wasu mutanan sunyi asarar rayuwarsu.

Lokacin da hajiya falmata ta ƙarasa saukowa daga saman benan, idanuwanta suka Yi
mata tozali da kyakkyawar fuskar Aneelerh nan take taji ta burgeta, tayi mamakin
ganin baƙuwar fuska agidanta, bakomai yafi tafiya da imaninta ba face Kyawun surar
Aneelerh.

Ganin Yadda Ta tsareta da idone Yasa Aneelerh tayi saurin gyara mayafinta ta
rurrufe jikinta, Aranta ta furta A’uzubillahi minasshaidanirrajin, Aniyarki ta biki
baƙar mayya”
Saman sofa din dake fuskantar Aneelerh Hajiya ta zauna, tana dubanta da wani irin
mayataccen kallo.

Yamutsa fuska Aneelerh tayi fuskarta ba wasa tace”barka da Yamma”


Hajiya falmata ta amsa mata da”barka dai, bismillah ki zauna mana”

Ɗaure fuska Aneela tayi”bana zama agidan da ake aikata sa6on Allah, saboda ni
tsarkakakkiya ce, bai kamata in goga ma jikina najasa ba”!! Mamakine Ya kama hajiya
falmata, a hankali ta sauke glass din dake saman fuskarta don ta samu damar ƙarewa
Aneelerh kallo.

“Bansan wacece ke ba, sai dai na fahimci haukan talauci ne ke damunki shiyasa
kika kwaso ƙafa kika zo gidana don in taimaka maki”

Dariyar rainin wayau Aneelarh Tayi kafin tace”ki kalleni daga ƙasa har sama, kema
kinsan nafi ƙarfin ki kira ni da talauci, Ni banzo don nayi cece kuce dake ba
saboda bani da lokacinki, Maganar kudin zahra da kike bin ta bashi ne”
Shu’umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar Hajiya falmata da shaƙiyanci ta
furta”oh, kinzo ne ki fanshe ta, shiyasa kika kawo min kanki? Donni banga alamun
zaki Iya biyan kuɗin ba”
Girgiza kai Aneelerh tayi ranta a6ace tace”wato shi dai jaki duk yadda akai dashi
sai yaci kara, idan kina tunanin na kawo maki kaina ne don in fanshi zarah to ki
daina, domin kuwa nafi ƙarfin ƙasƙantacciyar mace ballagaza jahila kuma daƙiƙiya
irinki, Mace mara tsoron Allah, me yin amfani da dukiyarta don lalata rayuwar
matasan ƴan mata masu neman nakansu, Wlh kinji haushin rayuwar......” gigitacciyar
tsawa Hajiya falmata ta daka ma Aneelerh, tamkar damusa ta yunƙura ta miƙe tsaye
tana duban Aneelerh da mummunar fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin ta nuna
mata Hanyar fita da yatsan hannunta”Ke Fuce kibar min gidana, tunkafin ranki Ya
6aci, matsiyaciyar banza masu ƙashin tsiya”

Aneelerh da ƙarfin Hali tace”idan kinga na fita gidan nan to nagama faɗin ta
cikina ne, Kuma wallahi koda gigin wasa kika ce zaki ta6a lafiyar jikina saina
naƙasa ki bakisan wacece Ni ba” ta faɗa tana jefa mata harara, lamarin Ya ɗaurewa
Hajiya falmata kai, ganin karfin hali na Yarinyar nan data zo gidanta tana Yi mata
rashin Kunya.
Goya hannayenta tayi saman ƙirjinta”ina sauraronki, Me ya kawo ki gidana!”
Gyaɗa Kai Aneelerh Tayi”zuwa nayi don Inyi maki nasiha, don na fahimci Wadda
iyayenki suka yi maki tuni shaiɗan Ya hure maki kunne, dan Allah Jibarki cikin
shiga ta mutunci kamar wata mutuniyar arziƙi, al’halin nan kuwa fuska biyuce ke, A
fili musa a zuciya fir’auna, Haba baiwar Allah, Da hankalinki da tunaninki da
shekarunki kika za6i ki sa6awa Allah don kawai ki ji daɗin duniya? Kin manta da
Allah yana ganinki kuma zaki mutu ki koma gareshi, a ko’wani yanayi mutuwa tana iya
riskarki, idan taƙamarki kuɗine ki tuna Allah ne Ya baki Arziƙin bake kikayi ma
kanki ba, Idan yaso zai Iya ƙwace wa, kuɗi da kike gani wallahi masifane Idan baka
tafiyar dasu ta hanyar da ta dace ba, Ita kuma rayuwar duniya jin daɗinta ƙalilan
nan bata da tabbas, bakisan yaushe zaki mutu ba, kin sanya mugunta aranki saboda
Allah Ya azurtaki, Kina cutar matasan Ƴan mata, waɗanda Iyayen su suka sha wahalar
basu tarbiya ke kuma kina gur6ata masu rayuwarsu, Allah kaɗai yasan adadin Ƴan
matan da kika 6ata, kin goga masu jarabar da bazasu Iya gogeta ba, Kin cutar da
rayuwarsu mutane suna kuka da su saboda sun addabi rayuwar al’umma kuma ire-iren ku
ne ku ka yi silar lalacewarsu, wallahi kiji tsoron Allah kamar yarda ba zaki so ayi
da ƴar ki ba to kema kada Kiyi da ɗan wani, duk da naji irinku Harda ƴa’ƴan naku
kuke Yi, saboda shafewar basira da neman duniya kun makance bakwaji bakwa gani ku
ala dole saikun siyama kanku tikitin shiga wuta”? Tun da Aneelerh ta soma Yi mata
magana da faɗa haɗi da tsiwa take ta faman zare ido tana binta da kallo, tun da
take arayuwarta wani ɗan adam bai ta6a gigin tunkararta Ya faɗa mata magana game da
abunda Take aikatawa ba sai Yau da Allah Ya haɗa ta da Auntyn Zahra mai dimple,
Ayoyin kur’ani aneelerh ta soma karanto mata tana fassara mata, kamar an rufe mata
baki takasa dakatar da ita duk irin masifar da take da ita yau an kashe mata
bakinta
“Allah Yana son bayinshi waɗanda suka aikata 6arna suka tu6a saboda tsoronshi suka
koma gareshi, dan Haka ina baki shawarar tunkafin lokaci Ya qure maki Hajiya
falmata ki Gyara Halayanki, Ni bance zan sanyaki ki shiryu ba don nasan irinku
taurin kaine daku kamar kwakwa, ko malamai sunyi maku nasiha bakwaji bakwa gani sai
ranar da Allah Ya damƙe ku tukunna zaku gane kurenku, Ni in banda ma shafewar
basira, wai ku bakwa tuna mutuwa da kwanciyar ƙabari ne? Baku tuna duk abunda kuka
mallaka zai ƙare, daga kai sai halinka za’a binne ka a ƙabarin ka fa? Ke yanzu kin
za6i ki mutu kina aikata mummunan zunubi na bin Ƴan uwanki mata? Ga hakkin Iyayen
da kika sanyasu zubar da hawayensu ta silar lalata masu rayuwar ƴa’ƴa da ki ka yi
ga kuma Matasan ƴan matan da kika gur6ata ma rayuwa, wannan fa zunubine mai cigaba
da yaɗuwa ko bayan kin mutu zaki cigaba da samun kamasho acikin shi, saboda kinbar
tarin ƴan matan da kika gur6ata agari suna aikata fasadi, wallahi kiji tsoron Allah
tunkafin lokaci Ya qure maki, Ina ƙara jan hankalinki ki tuba ki koma ga Allah
tunkan mutuwa ta risƙe ki don ita bata kwankwasama mutun ƙofa balle Yace zai shirya
mata”

Wata irin zuface ta soma wanke goshin Hajiya falmata, Haƙiƙa kalaman Aneelerh sun
fara karya mata zuciya, sai faman zare ido take Yi, batasan ya akai ta tsinci kanta
da jin maganar Aneeleerh ba, Yarinyar tayi matuƙar burgeta kuma ta bata mamaki da
har ta iya yi mata nasiha batare da jin shakkarta ba, saboda mutane dayawa basa Iya
yin magana agabanta, amma Ita wannan ido cikin ido take furta mata magana .
“hajiya falmata, duk runtsi duk wuya kada ki Karya zuciyar wanda Ya aminta dake!
Ina magana akan zahra da ta dauke ki tamkar mahaifiyarta saboda ƙaunar dake a
tsakaninta da ƴarki fatima, Kin karya mata zuciya, naji daci lokacin da na sameta
ta kulle kanta acikin toilet tana Yin kuka babu ci babu sha ita kaɗai batare da
kowa ya sani ba, Kin hanata runtsawa saboda taƙi baki haɗin kai ku aikata sa6on
Allah, haba baiwar Allah, idan kece akayima yarki haka zakiji daɗi! Don kawai mutun
Na buƙatar agazawarka sai kayi anfani da dukiyarka donka cutar dashi? Babu wanda
yafi ƙarfin ya nemi taimako a duniyar nan, koda ba a wurin mutun ɗan uwansa ba, zai
nema awurin Allah Idan har baka agazama bawansa ba tayaya kake tunanin zai agaza
maka?

Jinjina kai Aneelerh tayi, Tuni zafafan hawaye sun wanke fuskarta cikin muryar kuka
taci gaba da cewa”Kin ƙona mata rai, zahra ta yarda dake fiye da tsammaninki, tana
kuka tana fadamin yadda ta aminta dake amma kika karya mata zuciya, Zahra da kike
gani tafi ki Hankali, Yarinyar tana da tawakkali, tana jin tsoron Allah, Na
jarabata don inga ko tana da wayon jure ƙaddara idan ta sameta, Ni dakaina nabata
shawarar ta baki haɗin kai, da buɗar bakinta sai ce mun tayi ita ko duniya za’a
mallaka mata bazata ta6a amincewa ta sa6ama Allah ba, saboda tana jin tsoron shi
kuma tana jin tsoron ranar da zata koma gare shi, Hajiya falmata kin ta6a tunanin
hakan? A matsayinki na babbar mace wadda ta haura shekara arba’in da ɗuriya a
duniya? Shekaru sunja amma baki tsoron mahaliccin ki? Kina amfani da dukiyarki
wurin Gur6ata duniyarki da lahirarki, maimakon kiyi amfani da su wurin taimakon
bayin Allah marasa ƙarfi wadanda zasuyi alfahari dake ko bayan ba ranki kuma ki
samu lada awurin Allah, Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar da kika daukarwa
kanki”!?

Ƙafafuwanta ne suka gaza ruƙeta, Jiri Ta soma gani a cikin idanuwanta, adaddafe
ta nufi sofa ta zauna tana faman fitar da numfashi.

Hankaɗe Kafaɗa Aneeleerh Tayi”Alhamdulillah nagama faɗar ta cikina, duk wanda


yayi da kyau don kanshi, akwai mutuwa akwai hisabi, maganar kuɗi Kuma nazo maki da
su miliyan Uku Cuf, Idan ma kina son ƙari zan ƙara maki, saboda inaso kisan muba
jinin faƙirai bane idan arziƙine muma mun gaje shi gaba da Baya”

Ɗaga murya Aneelerh Tayi da ƙarfi ta furta sunan Mahboob, shigowa ɗakin Yayi hannun
shi ruƙe da jaka baƙa, tunkan ya ƙarasa yake bin ko’ina da kallo, ganin haɗuwar
falon gidan aranshi Ya ayyana Lallai hajiyar nan ta tara shiyasa take tsula
tsiyarta son ranta saboda tana da arziƙi.

“Zoka ajiye mata tsiyarta,” Aneelerh ta faɗa tana nuna mashi gaban Hajiya
falmata, Ta zabga uban tagumi da hannu biyu, da alamun nadama atattare da ita.

Koda mahboob Yayi arba da fuskarta saida yasha jinin jikin shi ganin yadda ta haɗe
rai, ga gumi na fita a goshinta.

Kamar mai jin tsoronta Haka Ya ajiye mata jakar agabanta.

Aneelerh ta ruƙo hannun shi acikin nata, har sun ɗaga ƙafa zasu bar falon muryar
Hajiya falmata ta dakatar da su
“Dan Allah Ku tsaya”!! Kusan atare zuciyarsu ta buga, a sukwane suka waiwayo suna
dubanta, Gabansu ba ƙaramin faɗuwa yayi ba ganin ta fashe da kuka, miƙewa tayi daga
saman sofa din ta nufe su tana fadin”wallahi nayi nadama, dan Allah kuyi haƙuri da
abun kunyar dana aikata, Nima ba halina bane ƙawayene suka tunzurani har na faɗa
harkar” zubewa tayi saman gwiwowinta agaban aneelerh tana kuka tace”Tun da nake a
rayuwata wani ɗan adam bai ta6a yi mini nasihar data ratsa zuciyata ba sai akanki,
bansan wacece ke ba, amma nayi sha’awar In yi koyi da kyawawan halayanki, duk naji
na tsani kaina, na zubda mutuncina da girmana a idon zahra, wallahi naji kunyar da
ban ta6a jin taba, Naji ƙuncin Halin dana jefa zahra, saboda ni tagaza runtsawa Na
hana baiwar Allah yin bacci na hanata cin abinci, na jefa rayuwarta cikin ƙunci
batare da nayi tunanin raɗaɗin da zataji acikin Zuciyarta ba, wallahi nayi nadama
koda ace bazaku yarda dani ba, Na tuba kuma in sha Allah bazan ƙara aikata zunubin
nan ba, angama bi’iznilillahi, saboda inaso Inyi kyakkyawan ƙarshe kuma inaso in
tsira ranar gobe ƙiyama, In sha Allah daga yanzu nagama yin amfani da dukiyata don
in sa6awa Allah, da kuma gur6ata tarbiyar ya’yan mutane.....”daƙyar ta ƙare maganar
tana faman jan magina.

Ba Aneelerh ba hatta Mahboob Yayi mamakin wannan Ikon Allahn, sun yi sototo suna
kallonta kamar sakarkaru duk ta zama abun tausayi tsoron Allah ya shigeta, wata’ƙil
dama itace silar shiriyarta shiyasa Allah Ya haɗasu da ita.

Muryar Hajiya falmata na rawa tace”Ku taimaka mun dan Allah, inason in wanke
kaina awurin zahra, saboda inason taci gaba da kallona kamar yarda tasanni ada,
Nayi alƙawarin zan taimakamata, kuɗin da ku ka zo dasu na yafe mata ku ɗauka ku
maida mata su, Sannan inaso taci gaba da yin aiki a company dina, Kayan da suke son
ayi masu order A dubai gobe in sha Allah zasu iso Nigeria”

Kallon juna mahboob da Aneelerh suka ƙara Yi, Atare suka furta Alhamdulillah,
Aneelerh tace”nagode ma Allah daya bani baiwar Iya tsara kalamin da har suka ja
hankalinki, Naji daɗi dana zama silar shiriyarki, Ina fata zaki canza rayuwarki
daga Yau ki koma ta gari, wadda kowa zaiyi alfahari da ita”

Jinjina kai Hajiya falmata tayi Cikin sanyin murya tace”in sha Allah,” ruƙo
hannayenta aneelerh tayi acikin nata, miƙewa tayi tsaye suna fuskantar juna
“Ki godema Allah, saboda Yana son ki da shiriya shiyasa Ya baki damar gyara
rayuwarki tun da sauran numfashinki,”

Jinina Kai Hajiya falmata tayi.


Aneeleerh ta ƙara da cewa”sai dai kiyi haƙuri, ba zamu maida kuɗinba, nariga dana
kawo maki dasu, Ki ruƙe su a hannunki, zahra kuma bazata ƙara Yin aiki a companynku
ba, zan nema mata aiki awani wurin”!!

Magiya hajiya falmata tadinga yi mata akan tayi haƙuri su koma da kuɗin, ta yafe
masu, amma Aneelerh taƙi yarda, mahboob ne yace ta jira zasu yanke shawara a
tsakaninsu, ruƙo hannun Aneelerh yai acikin nashi yajata zuwa gefe ɗaya akwai
tazara tsakaninsu da hajiya falmata, tayi kasake tana kallonsu
“Aunty aneelerh tunda tace ta yafe kuɗin mu koma dasu kawai, ai ba roƙonta mukayi
ba”
Girgiza kai aneelerh tayi”nidai hankalina bai kwanta da matar ba, wallahi irinsu
shaiɗanune Mahboob, inajin tsoron ace wani tuggun zata kitsa mana shiyasa tace ta
yafe kuɗin, ƙwara mu maida mata aniyarta”
Yamutsa fuska mahboob yai”aunty aneelerh just ki gane, ni dai na yarda da ita,
sau dayawa zaki ga mutun yana aikata ba daidai ba idan Allah yaso shi da rahama
saiki ga ya shiryu cikin sauƙi batare da ansha wahala ba, Yanzu ki duba matar can,
hada fa kukanta kuma har zuƙunnawa tayi saman gwiwowinta tana roƙonmu, why bazamu
yafe mata ba? Komai ya wuce, ita kanta zahran ba ƙaramin daɗi zataji ba saboda tana
son fatima ƴarta aminnan junane tun tuni, sannan taci burin zuwa obie estate, bayan
haka aikin nan da take Yi a companyn su ba ƙaramin ƙaruwa take Yi ba, ita kanta
tana faɗi da bakinta irin alheran da take samu ta silar aikin da suke Yima mutane,
idan ma da wata manufa tace hakan to mu barta da Allah, In sha Allah babu abunda
zata Iya yi mata,” gyaɗa kai Aneelerh tayi”shikenan na amince da buƙatarta, mu koma
mu faɗa mata” komawa sukayi cikin falon, bayan sun sanar da ita shawarar da suka
Yanke ta dinga yi masu godiya farin ciki duk Ya cikata, kafin tafiyarsu saida ta
roƙe su alfarma akan su taimaka mata, tana so zahra taci gaba da ganinta a matsayin
mahafiyarta, tasan ayanzu bata da sauran mutunci a idonta.
Aneelerh ce tabata shawarar yadda zata tsara ma zahra, duk don ta amince da cewa
ba halinta bane, sun jima agidan kafin daga bisani sukayi mata sallama, sunyi
rabuwar mutunci da hajiya falmata, har musayar number sukayi da Aneelerh saboda
acigaba da zumunci.

( kunji abun da Ya faru, kafin washe garin ranar da zahra taje kaima Hajiya
falmata kuɗinta)

Wuraren ƙarfe takwas na dare, motar drivern da yaje dauko su Alhaji ubaid daga
airport ta kunno kai gate din gidan, tunkafin ƙarasowarsu, Dr Shureim da zeenatu
suna atsaye bakin Entry hall din falo, hannunsu ruke cikin na juna, daga ita har
shi jallabiyace ajikinsu, ta yafa mayafi akanta, tsantsar farin cikine akan
fuskokinsu, sunyi matuƙar ƙagara da son ganinsu.
Zeenatu sai faman washe baki take Yi, tunda tayi tozali da motar dake shigowa tana
tunkaro bakin entry hall din
Da zamudi tace”ya shureim kana ganin aunty benazir zata Iya gane ni kuwa? Saboda
mommy ta fadamin tun ina jaririya ta 6ace ba’a ganta ba”
Fuskarshi dauke da murmushi yace”idan ma bata gane ki ba, da zarar anyi mata
bayani zata shaidaki, zan faɗa mata cewa zeenatu ce ɗiyar uncle musa, and my wife
to be” tuntsirewa tayi da dariya taji daɗin maganarshi, muryarta da shagwa6a
tace”amma ya shureim ai ni banaso ka faɗa mata, wallahi kunya nake ji, ko mommy
layla ma kada ka fada mata please da daddyn ku” ta faɗa tana duban face dinshi.
“Ai ni nafiso suji My zeenatu, saboda a fara shirye shiryen shafa fatihar
auranmu” zaro mashi blue eyes dinta tai kafin tai saurin sanya tafukan hannayenta
biyu ta rufe fuskarta cikin jin kunyar maganarshi ta furta”dan Allah yaya shureim
dina kada ka fada masu yanzu, nidai kunya nake ji”

“Kunya kamar bafullatana, kin manta mommynki baturiya ce, daddy musa kuma Hausa
fulanine, kakarmu bafullatana ce kakan mu namiji kuma bahaushe ne, Ni bansan inda
kika gado Kunyar nan taki ba, a haka zamuyi aure kina jin kunyata”?

Kafin ta bashi amsa, motarsu Alhaji ubaid ta ƙaraso gab dasu, bayan drivern yai
parking, da sauri Dr shureim Yaja hannun zeenatu suka ƙarasa bakin motar, yakai
hannu ya buɗe masu murfin back seat, a hankali ta zuro da ƙafarta dake sanye cikin
takalma, ƙarasa fitowa tayi tun daga ƙasa dr shureim yake binta da kallo, wankan
atamfa ne a jikinta riga da skirt, ta kashe daurin dankwalinta, yalwatacciyar sumar
kanta ta sauka gadon bayanta, gyalen asaman kafaɗa ta yafa shi, idan kaganta ahaka
bazaka ta6a ce wa ta ta6a yin aure ba, kamar budurwa saboda babu abunda ya canza a
jikinta, dama bata ta6a shayarwa ba.

Wani irin kallon so da ƙaunar ƴan uwantaka suke jefa ma juna tsakanin ta da
shureim, idanuwan kowannansu ya ciko tab da ƙwalla, La66anshi na kerma ya furta
sunan ta”be.. Nazir! Yar uwata rabin raina, Jinin jikina Dagaske ke ce idanuwana
suke nuna min? Fashewa tayi da matsanancin kuka, gaba ɗaya ta faɗa saman chest
dinshi, ya zagayo da hannayenshi biyu ya rungumeta tamkar zai mayar da ita cikin
cikinshi, Zeenatu dake tsaye tana kallonsu hawaye tuni sun wanke fuskarta, tsananin
tausayin benazir ne Ya kamata, Fitowa Alhaji ubaid yai daga cikin motar shida
Hajiya layla, ya dauki wankan shadda, itama layla Atamfar ce ta sanya sunyi anko da
benazir hatta daurin dan kwalinsu da mayafin da ta daura a kafaɗa iri dayane dana
benazir, idanuwansu na akan dr shureim da benazir, sun ƙanƙame juna sai kuka sukeyi
kamar waɗanda suka rasa mafaɗi a duniya, zagayawa zeeenatu tayi ta 6angaren da su
hajiya layla suke koda sukayi arba da ita, Hajiya layla ta buɗe mata hannu da
fara’a akan fuskarta take fadin”Zonan My daughter zeenatu” kamar jira take yi da
sauri ta ƙarasa ta faɗa jikin Layla, rungumeta tayi sosai, tana dan bubbuga bayanta
ta furta”kin ƙara girma daughter, tsawon lokaci bamu haɗu ba, Daddynki Ya hanaki
zumunci da ƴan uwanki, baison kina taka wajen mu, gashi mu kuma muna ƙaunarki” ta
faɗa tana raba jikinta da na zeenatu, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki,
kallon Alhaji ubaid tai”sannunku da zuwa daddy” miƙa mata hannu yai da sauri ta
ƙarasa gare shi, Yai hugging dinta yana fadin”fatan mun same ku lafiya,” ɗagowa tai
da kanta tana fadin”Lafiya lou daddy mu shiga daga ciki”
Drivern daya daukosu Yana daga tsaye ya jingina bayanshi jikin motar,
Yace”yalla6ai ku ƙarasa shiga gidan, za’a shigo maku da kayan naku” amsa mashi
sukayi da toh, layla tace da su shureim ayi haƙuri adaina kukan ya isa haka mu
shiga cikin gidan inyaso kun ƙare kukan naku acan” Alhaji ubaid na murmushi yace”ke
ko kibarsu mana, An daɗe ba’a haɗu ba, Jini ɗaya ba wasa ba, mundai godema Allah
daya bayyana mana ita da ranta da lafiyarta ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita,
layla da zeenatu suka amsa mashi da ameen,
Gaba suka fara Yi, Ya rage saura zeenatu data ƙura ma benazir da shureim ido.

Ta kwantar da kanta saman kafadarshi, yayin da hawaye masu ɗumi suke cigaba da
wanke fuskarta, cikin muryar kuka take fadin”yaya shureim nayi danasanin duk wani
abu daya faru arayuwata, wallahi nayi danasani mara amfani, bansan meke damunaba,
hakanan na tafi nabar dangina nabar mijina, babban takaicina ƴar jinjirar dana bari
cikin jini, na haura ƙafa na tafi nabarta saboda rashin hankali irin nawa, bansan
meyasa na aikata hakan ba” cikin jin ƙunar rai ta ƙare maganar.
Ɗaura hannunshi yai saman bayanta cikin rauni na murya ya soma magana”kiyi haƙuri
benazir, wallahi ba laifinki bane, ni nasan duk rashin jin maganarki bazaki ta6a
iya aikata hakan ba, Ina yi maki kyakkyawar zato, ki kwantar da hankalinki My
sister” cikin kwantar da murya yake lallashinta
Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya janyo hankalinsu ga kallonta, idanuwanta sunyi luhu
luhu, da mamaki akan fuskar benazir ta furta”yaya shureim a ina muka samu
kyakkyawar matashiyar baturiya”?
Fuskarshi dauke da murmushi yace”zeenatu ce, nasan ba lallai kisanta ba, saboda
ba’ajima da haihuwarta ba ki ka tafi, ɗiyar uncle dinmu ce, ki kalli fuskarta
dakyau”

Farin cikine Ya lullu6e benazir, Yarinyar ta burgeta, Gata ƴar kyakkyawa da ita,
miƙa mata hannu tai zonan ƴar uwata, Ina fata an fada maki wacece ni, idan ma ba’a
sanar dake ba toh nidai sunana benazir, Ƙanwar dr.shureim” fashewa Zeenatu tayi da
dariyar farin ciki, Hawaye nabin fuskarta.
“zonan In rungumeki ajikina, Nima yau inji ɗumin ƴar uwata” jiki Na rawa zeenatu ta
nufi benazir suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya
Cikin shessheƙar kuka Zeenatu take fadin”Aunty benazir munyi kewarki sosai,
Mommyna tana bani labarinki, najima ina son ganinki arayuwata, duk da bamu ta6a
haɗuwa ba amma kullum idan nayi sallah sai nayi maki addu’a Akan Allah Ya bayyanar
mana dake idan kina araye, Idan bakya araye Allah Yajiƙanki yakai rahama agareki,
ashe da rabon zamu haɗu....”dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya cimmata, daga
ita har benazir din kukan sukeyi, Kalaman zeenatu sunyi matuƙar ta6a mata zuciyata,
tayi mamakin irin ƙaunar da take Yi mata, ita da bata ta6a ganinta ba, labarinta
kaɗai aka bata, haƙika taji dadi mara misaltuwa, kaunar zeenatu ta shigeta, tayi
fatan Ace itama ƴarta data bari tana yi mata addu’a.

“Aunty benazir dan Allah kada ki ƙara tafiya kibarmu, wallahi muna kaunarki nida
mommyna” sosai benazir ta fashe da kuka tana fadin”in sha Allah bazan ƙara
tafiyaba, nadawo kenan zeenatu, naji dadin kalamanki agareni, ƴar uwata rabin
raina”
Dr.shureim Ya natsu yana kallonsu, idanuwanshi sun kaɗa jawur, hawayen dake
gangarowa saman kuncinshi sai ƙara ninkuwa sukeyi.
Cikin sanyin murya yace dasu’Mu shiga cikin gidan” amsa mashi sukayi da toh,
hannun benazir acikin na zeenatu suka dunguma zuwa babban falon gidan.
Lokacin da suka ƙarasa ciki, Alhaji ubaid da Hajiya layla suna a zaune saman sofa
mai mazaunin mutun biyu, a yayin da Hajiya sarah ta zauna saman 3 sita, Alhaji musa
yana daga zaune gefenta, kamar kullum fuskarshi babu annuri, kamar wanda akayiwa
albishir da ranar mutuwarshi, shaddar jikinshi ta zauna mashi launin blue sky,
daddadan kamshin turarenshi Ya karade hancin kowa, Hajiya sarah Lace ne ta sanya
kalar shaddarshi, head dinta kalar takalman ƙafarta, sunyi kyau abunsu kamar sabbin
ma’aurata

Jin takun tafiyarsu yasa hajiya sarah ta ɗago tana dubansu, wani irin farin
cikine ya lullu6eta ganin benazir, Jiki na rawa ta miƙe tana faman sakin fara’a
fararen hakoranta tarr dasu ta nufi benazir tana fadin”ashe rai kanga rai? Benazir
dagaske kece idanuwana suke nuna min? Wayyo Allahna, Idan ma mafarki nake Yi toh
kada atadani abarni in tayi dan Allah” Rungume juna sukayi, Benazir ta fashe da
wani sabon kukan bata ta6a tsammanin zata samu kyakkyawar tarba a wurin ahalinta
ba, Tabbas sun bata mamaki tayi tunanin kamar yadda ta gudu babu wanda zai
saurareta donta dawo gare su.
Hajiya layla sai faman sakin murmushi take Yi ita da Alhaji ubaid hankalinsu na
akan Hajiya sarah data rungume benazir, Shi kuwa Alhaji musa ko kallo bata ishe shi
ba, tamkar baisan sun shigo falon ba.

“Allah sarki benazir, Ashe da rabon zamu sake ganawa a duniyar nan! Tsawon
shekaru sai yau Allah Ya nufa zan ƙara Yin tozali dake” ta fada tana duban benazir
da hawaye suka gama wanke fuskarta
Cikin shessheƙar kuka tace”Aunty Sarah nayi danasani, naji haushin kaina, naji na
tsani kaina saboda komai ya faru arayuwana laifina ne, tunda nida kaina na gudu na
tafi batare da nayi shawara da kowa ba, Dan Allah ku yafe min, nasan na 6ata maku
rai”
Idanuwan hajiya sarah tuni sun cicciko tab da ƙwalla, kasancewarta mace mai
tausayi.
Cikin karyayyar murya ta furta”dan Allah ki daina fadin hakan, Komai ya riga daya
faru kuma ya wuce”

Kafin benazir ta kuma yin magana muryar Alhaji musa ta katse masu hanzarinsu
“Idan kun gama jimamin, ku ƙaraso ku zauna” cikin isa Ya furta hakan, sai lokacin
Benazir ta ɗago da ido tana dubanshi, Ya haɗe rai babu annuri sam a fuskarshi, gani
take kamar baiyi farin ciki da dawowarta ba.
Ruƙo hannunta Hajiya sara tayi acikin nata, suka ƙarasa tare da samun wuri
kowannansu ya zauna, zeenatu da dr shureim suna zaune saman lallausan carpet,
Benazir kuma tana agefen hajiya sarah, ta ƙankame hannunta.
A tsanake Alhaji musa Yasoma yin magana batare daya ɗago da ido ba
“Da farko, Inayi maku barka da zuwa, yayana da kuma hajiya layla,’ kwa6e fuska
layla tayi aranta tace”dallah jibarshi ɗan rainin wayau”
Numfasawa yai tamkar bayason buɗe baki Ya furta”benazir,” amsa mashi tayi da
na’am.
Dawo nan ki zauna” yai maganar yana Nuna saman carpet daga gefen hannun sofa din
da yake zaune, jiki asanyaye ta miƙe ta dawo inda ya bata umarni ta zauna.
Kowa ya natsu yana jiran jin me Alhaji musa zaice da ita.
“Meyasa kika gudu daga gidan auranki har na tsawon shekaru baki nemi kowa ba”?
Kafin benazir ta bashi amsa hajiya layla tayi saurin cewa”Bai kamata kayi mata
wannan tambayar ba, kodai mu da muke Iyayenta bamu tambayeta komai ba, duba da
halin da tadawo gidan”
Ranshi a matuƙar 6ace ya dago da ido Yana binta da matsiyacin kallo batare daya
furta komai ba
Sai Alhaji ubaid ne yace”wannan maganar bata shafeki ba, tsakaninshi da ɗiyarshine
don haka ki daina sanya masu baki” harara ta wurga ma Alhaji ubaid”kaima ka sani
bazan ta6a rufe baki na ba, akan me zai tambayeta meyasa ta tafi? Lokacin da ta
gudun ya nuna damuwane akanta? Ko kuwa ya bada gudummuwar da za’a nemota ne eye?
Daga zuwanmu gidanshi zai tsareta da tambaya? Dama ya kira mune don Ya tuhumi ƴar
mu badan Ya tayamu murnar ganinta ba” tunda tafara zazzaga masifa hankalin hajiya
sarah dana zeenatu ya tashi haiƙam, shi kanshi shureim jikinshi yai sanyi laƙwas,
benazir dai ta saddar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da wanke fuskarta.

Lallashinta Alhaji ubaid Ya soma Yi, Alhaji musa kuwa sai faman jinjina kanshi
yake Yi, Yama rasa bakin magana

Hajiya sarah na faman yarfa hannu tace”dan Allah kiyi haƙuri aunty, idan ranki ya
6aci, nasan ba’a kyauta ba, Ni tun farko banso yace kuzo nan ba, har magana nayi
mashi akan mu yakamata mu taka muje tayaku murna amma ya hanamu zuwa....” daƙyar ta
ƙare maganar ganin irin kallon da Alhaji musa ke binta dashi, ba arziƙi taja baki
tayi shiru
Jinjina kai yaɗanyi kafin ya ɗaura da cewa”Allah Ya huci zuciyarki Hajiya layla,
Naji bazan ƙara tambayarta ba,” tayi mamakin jin abunda yace, har saida ta kalli
cikin idonshi, murmushin gefen fuska yasakar mata afakaice, kafin Ya maida dubanshi
ga benazir”ina yi maki barka da zuwa My daughter, naji daɗi da kika yi tunanin
dawowa gida, ki kwantar da hankalinki, kuma ki share hawayenki, abunda ya faru ya
riga daya wuce”
Ajiyar zuciya benazir tadan sauke, cikin sanyin murya ta soma magana”nagode uncle,
sannan idan na 6ata maka rai, kayi hakuri, nasan komai ya faru laifinane, dana kama
hanya na tafi”
Lumshe idanuwanshi yadanyi kafin ya waresu akan fuskarta”kada ki damu ni ban ruƙe
ki araina ba, kawai dai banji dadin guduwar da kikayi bane na tsawon shekaru batare
da kin tuntu6emu ba, amma yanzu tunda kin dawo da ranki da lafiyarki falillahil
hamdu, sai dai fatan Allah ya kyauta gaba, In sha Allah zanyi ƙoƙari dan ganin na
inganta maki rayuwarki, duk wani abu da kike buƙata ki sanar dani zanyi maki shi,
kada ki ƙara yunƙurin guduwa saboda muna buƙatarki, zaifi ki sanar damu idan ma
wani abune ya 6ata maki rai a tsakaninmu zamu Iya sama maki solution, Ina fata kina
jina”
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, lamarin Alhaji musa ya ɗaurewa hajiya layla kai,
bata ta6a tsammanin ya iya tsara kalami irin haka ba, hatta Alhaji ubaid yai
mamakin yadda ya sakar ma benazir fuska yana yi mata magana cikin lallami, aranshi
ya ayyana wata’ƙil tsananin tausayinta ne Ya kamashi, yaji dadin hakan, hankalin
hajiya sarah ya kwanta dana zeenatu, sai faman sakin murmushi suke Yi, haka zalika
dr.shureim shima murmushi ne akan fuskarshi.
“In sha Allah uncle bazan ƙara yunkurin guduwa ba, duk runtsi duk wuya zan zauna
atare daku, nima nayi danasanin abunda na aikata,
Gyaɗa kanshi yai,
Hajiya sara tace”tun ɗazu fa na sanya masu aiki sun shirya maku lafiyayyan abinci,
yakamata muje muci kada ya huce” da fara”a akan face dinta ta furta hakan,
Miƙewa sukayi atare suka dunguma zuwa dining room, benazir ta girgiza da ganin
daular uncle musa, Gidan Ya tafi da imaninta.
Saman dining chairs suka zazzauna, ga kayan abinci an jera masu saman table,”
Tani da lami ne suka zo domin yin serving dinsu, Bayan sun gaishe da alhaji ubaid
da hajiya layla, suka soma zuzzuba ma kowannansu abunda yake ra’ayin ci, hankalinsu
kwance suke ci baka jin sautin komai saina ƙarar cokulansu.
Jefi jefi zeenatu take satar kallon benazir da zarar sun haɗa ido sai ta sakar
mata murmushi, Ta fahimci yarinyar ba ƙaramin so take Yi mata ba, Dr shureim na
kallonsu, shima murmushine akan fuskarshi, Hajiya layla dai taƙi sakewa, itafa har
yau har gobe bazata ta6a yadda da alhaji musa ba, gani take yi kamar akwai wata
manufa atare dashi, abincin ma daƙyar take cin shi”

Bayan sun kammala cin abinci, Hajiya sarah ta rakasu zuwa masaukinsu da zasu zauna,
Hadaddun bedrooms aka ware masu, Zeenatu ta hana benazir sakat, tsabar Iyayi hada
ɗauko bargonta da pillow ta dawo down stair dakin benazir donsu dinga kwana atare,
Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,

*SIR MUBARAK✊*

Yana acikin dangi suna ta yin firar yaushe rabo tare da Ƴan uwanshi, Wayarshi dake
acikin aljihunshi ta soma Yin ruri, kusan sau uku kiran na shigowa yana yin
rejecting batare daya ankare ba, saboda hayaniyar ƴan uwan shi da suke Yin fira a
tsakaninsu, a babban katafaren falon gidan, a kira na huɗune, Senate lateef dake
zaune gefenshi ya ankarar dashi ta hanyar yi mashi magana ka duba wayarka tun dazu
nake jin sautin ringing ɗinta, amsa mashi yai da toh, sai da ya fara curo wayar ya
duba sunan mai kiran nashi tukunna ya mike yai masu sallama Ya nufi ƙofar fita daga
babban falon, bayan ya fitone Ya dakata da yin tafiya, Yabi kiran da aka yi mashi,
bugu ɗaya aka ɗaga kiran
“Major, ince dai lafiya? Naga miss call dinkane”
On the other hand major yace”yalla6ai yaron nan na wurinka jazz Ya fita daga gida
Yanzu haka da nakeyi maka magana munbiyo bayanshine muna asaman titi,”
Cikin saurin murya sir mubarak yace”gani nan zuwa, kubi a hankali kada ku bari
yaganku yaron wayau ne dashi, yanzu zamu biyo diddiginku” tunkafin maijor ya amsa
mashi yai saurin yin rejecting call din, Ya dannawa driver dinshi Kira bugu ɗaya ya
daga”Ina jiranka abakin entry hall na gidan baba, kazo da mota ka daukeni”
Ya ƙare maganar tare da kashe kiran, Jikin shi har tsuma yake yi fatan shi Allah
ya basu nasarar kama jazz don ganin menene yake aikatawa,
Badajimawa ba baƙar mota ƙirar Range rover ta shararo da matsakaicin gudu bata
nufi ko’ina ba sai bakin entry hall adai dai nan Tiger Yai parking dinta, Jiki na
rawa sir mubarak Ya buɗe front seat na motar ya shige tare da bashi umarnin su
tafi, reverse yai kafin ya karya kwana Ya nufi tanƙameman gate din fita daga estate
din dake a kewaye da jami’ai, tunda suka hango sir mubarak ta tagar motar basu yi
gigin dakatar dasu ba, kaitsaye motarsu ta haura saman titi, da gudun gaske tiger
yake driving dinsu tamkar zasu tashi sama, sir mubarak yai amfani da phone dinsa
wurin bin diddigin su major, cikin sa’a suka samo location din da suke, dare ne
tamkar da rana saboda hasken street light daya gauraye ko’ina, hanyar da suka biyo
kwata kwata babu mutane, sababbin gine gine ne a unguwar, wani ginin ma ba’a
kammala shi.

Rage gudun motar tiger yai ta hanyar glass din motarsu suka hango motar major
tana tafiya a hankali ga dukkan alamu sun ƙaraso inda dr jazz Yake shiyasa suka
rage speed din motar, bayan major yai parking din motarsu, kusan atare suka fito
shida wani matashin saurayi dukansu suna asanye cikin kakinsu na sojoji, daga bayan
motarsu Tiger yai parking din tasu motar, fitowa sukayi atare shida Sir mubarak,
koda su Major sukayi arba dashi a hanzarce suka buga ƙafa tare da sara mashi,
Jinjina masu kai Yai yayin da yake bin gine ginen da kallo Ya ce”ina ku ka ga jazz
din Ya shiga”? Ya jefa masu tambayar cikin ƙagara da sonjin amsarsu.

Major yace”Wancan gidan mai jan gate Ciki Ya shiga” yai maganar yana nuna wani
katafaren gida, Da sauri Sir mubarak Ya nufi gate din, Major da Army din da suke
atare kowannansu Ya zaro bindigarshi, shima Tiger Ya curo tashi pistol din, gefe da
gefen sir mubarak Suka Jera sun saita bindugunsu saboda tsaro gudun kada akawo masu
hari tunda basusan adadin miyagun da yake mu’amala da su ba, Cikin sanɗa suke
tafiya suna bin ko’ina da kallo, ta ƙofar jikin gate din da aka bari abuɗe suka
shiga, babu kowa abakin gate din tamkar anyi shara, Sir mubarak yace”Anya major
akwai mutane acikin ginin nan? Naji shiru babu motsin komai, kodai kunyi
kuskurene”? Girgiza kai major yai”Yalla6ai tabbas cikin ginin nan ya shigo, ba mu
yi kuskure ba, akan idonmu ya fito daga cikin motarshi Ya buɗe gate kafin Ya koma
ciki Yajata zuwa cikin gida”
Gyaɗa kai sir mubarak Yai”okey mu ƙarasa ciki” kaitsaye suka nufi katafaren ginin
da suke tsammanin zasu samu hanyar shiga cikin gidan, adai dai bakin wata ƙofa,
suka dakata A hankali Major Ya turo ƙofar cikin sa’a suka sameta abuɗe, ɗaya bayan
ɗaya suke shiga, Hadadden palour ne An ƙawata shi da furniture, ga sanyin A.c ta
ko’ina mai ratsa fatar jikin mutun.
Sunyi mamakin ganin babu kowa a palourn, ko motsin mutun babu, daga cikin falon
akwai bene da zai kai mutun up stair, yanke shawarar haurawa saman benan sukayi,
Cikin sanɗa suke tafiya kowa ya saita bindigarshi saboda tsaro, a second floor suka
dakata da yin tafiyar suna bin ko’ina da kallo, ƙofofin ɗakunane ta ko’ina, Sam sun
kasa motsawa saboda sunfara kokwanton anya akwai mutane agidan
Tiger yace”shirun yayi yawa, kada fa ace tarkone aka ɗana mana don mu afka”
Major yace”ai shi soja da kasada akasanshi, Idanma tarkon ne suka shirya mana to
bamu bane zamu rufza aciki ba, sune zasu afka, wata’kil watan tonuwar asirin su ne
Ya kama”

Sir mubarak Ya natsu Yana sauraronsu, ya rasa madafa sam bayason suyi kuskuren
shiga gidan mutane, don ya fara kokwanto.
Army yace”yakamata mu fara dudduba ɗakunan nan wata’ƙil mu same shi aciki” Ya
furta hakan tare dakai hannu Ya buɗe ƙofar ɗaki Ɗaya, karaf idanuwanshi suka sauka
akan matasan Ƴan matan dake akwance saman bedmattress, cikin shiga ta kayan bacci”a
matuƙar ruɗe ya juya yana kallon Sir mubarak Ya furta”yalla6ai ƴan matane kwance
saman gado, Anya kuwa bamuyi kuskure ba”! Matsawa sukayi zuwa bakin ƙofar da Army
yake a tsaye, kowan nan su Ya leƙa Sun yi mamakin ganin kyawawan ƴan mata kwance
suna sharar baccinsu farare tass dasu kamar jinsin larabawa.
Rai amatuƙar 6ace sir mubarak ya dubi Major”kace min nan jazz ya shigo to yana
ina? Waɗannan ƴan matan alamace dake nuna cewa Gidan wani ne muka faɗo”
Tuni major yasha jinin jikinshi, Muryarshi adabarbarce ya furta”yalla6ai wallahi
da idona naganshi Ya shigo gidan nan, Ga army nan ka tambaye shi, ai tare dashi
muka shigo, kuma shima yaga jazz din” Yai maganar yana nuna army da hannun shi
Kallon Army sir Mubarak Yai, da kakkausar murya ya furta”idan har kukasa naji
kunya wallahi zakuji ajikin ku ne” hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, Jin abunda
yace masu, Guntun tsoki Yaja tare da juyawa da niyar Ya fuce daga gidan, kwatsam ba
zato ba tsammani, kunnuwansu suka soma Jiyo masu shessheƙar Kukan mace cikin murya
mai ƙaraji take fasa ƙara tana fadin”Bana so! Ka ƙyaleni Nace maka banaso, Ni ka
ƙyaleni, ka sake ni ka rabu dani....” sautin gigitacciyar ƙarar data fasa gaba ɗaya
Ya cika ginin, Kallon juna sojojin sukayi kafin da gudun gaske suka nufi Hanyar da
suke jiyo sautin kukan Yarinyar, Sir mubarak kamar zai yi tuntube, cikin zafin nama
suka haɗa ƙarfi wurin bangaje ƙofar ɗakin, A tsiyace ƙofar ta bude, Hankalin sir
mubarak Idan yai dubu to ya tashi, A matuƙar gigice sojojin suke kallon abun da ke
faruwa, Lamarin yai matuƙar ɗaga hankulansu, musamman Sir mubarak Ya gaza yadda da
abunda idanuwanshi suke nuna mashi, Tuni zufa ta soma wanke fuskarshi,
Sam baiji motsin shigowar mutane ɗakin Ba, Ya duƙufa akan abunda Yake aikatawa,
Rigar shaddar shi da wandonshi gaba daya suna asaman floor, Singlet ce kaɗai a
jikinshi sai gajeran wando Fari, Ya haɗa uban gumi, matashiyar yarinyar daya danne
saman gado sai kuka take Yi, tana bugun bayanshi da hannayenta, A wahalce take
harba ƙafafuwanta cikin fitar hayyaci kamar ranta zai fita, ta gama galabaita,
tuntana kukan neman agaji har muryarta tafara disashewa, wani irin kukan kura sir
mubarak Yai cikin zazzafan taku Ya kutsa kai Cikin ɗaki, da hannayenshi biyu ya
damƙo wuyar singlet din Jazz da ƙarfin gaske Ya wurgar dashi kasa gaba ɗaya ya kife
kanshi ya daki tiles, Jiki na kerma ya ɗago yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya
tsayar da idanuwanshi akan fuskar Sir mubarak dake tsaye kanshi tamkar mayunwacin
zaki, hankalinshi yai matuƙar tashi da ganinsu duk yabi ya ruɗe ya susuce, jikinshi
ya hauyin kerma, sai faman zazzare idanuwanshi yake Yi, Muryarshi na kakarwa ya
furta”daddy....” bai ƙarasa maganar da zaiyi ba, Sir mubarak Ya damƙo wuyanshi ya
ɗago dashi tsaye cikin rauni na murya ta wanda ya karaya yake fadin”Jazz ka
kasheni, Ka cuceni, dama abunda kake aikawata kenan? Ƴan mata kuke tarawa acikin
gida, donku lalata rayuwarsu sannan ku kashe su? Nasha kama ka kanayin waya kana
fadin kaji ashe mutanene kajin, Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” cikin jin
ƙunar rai yace”Wallahi baka isa ka ɗaura min hawan jini baa, Kafin ka kasheni ni
zan fara kasheka don ubanka, Mugu azzalumi fasiƙi, Jazz ka bani mamaki, ka cuce ni
kuma ka cuci mahaifiyarka,’ Cikin shessheƙar kuka Sir mubarak Yake furta maganar,
Ya shaƙe wuyan Jazz sai faman mutsu mutsu yake Yi, don ya ƙwaci kansa.

Yayin da sojojin suke a kewaye da gadon da yarinyar take, duk tabi ta tsorata
jikinta sai kerma yake Yi, short gown ce a jikinta, yalwatacciyar baƙar sumar kanta
duk ta rufe gefe da gefen fuskarta, tamkar wadda tasha gudu sai faman yin haki take
Yi.
Sautin ƙarar da jazz Ya fasane Ya janyo hankulansu ga duban shi, wani irin
radadin azabane Ya ziyarce shi sakamakon buga kanshi da sir mubarak Yai jikin
Mirror din dakin, gaba ɗaya madubin Ya zube, Jini Ya wanke fuskar Jazz hatta gaban
farar shirt din jikinshi Yayi ca6a ca6a da jinin shi, daddafe kanshi yai da hannu
bibbiyu cikin mawuyacin hali Yake sambatu “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!
Daddy ka kashe ni, Na shiga uku na bani na lalace, daddy ka rabani da rayuwata”
Yarinyar dake zaune saman gadon, ganin yadda suka raunata shi yasa ta fasa ƙara
da ƙarfi ta furta”yaya Jazz, Wayyo Allah na kun kashe min shi, mugaye azzumai baiyi
maku laifin komai ba amma kuna cutar min dashi” Da gudun gaske ta duro daga saman
gadon ta kife ƙasa, sam babu natsuwa atare da ita, da rarrafe ta ƙarasa gabanshi,
Ta sanya hannu biyu ta ɗago dakanshi ta daura saman laps dinta, Cikin shessheƙar
kuka take fadin”Wallahi Allah bazai barku ba, Ku baku da burin daya wuce ku cutar
da rayuwar waɗanda basu ji ba basu gani ba, Sai Allah ya saka mashi, ku dukanku sai
kun shiga wuta” ta fada tana nuna su da yatsan hannunta, kallon juna sojojin
sukayi, sunyi matuƙar girgiza da jin kalaman Yarinyar, sun fara kokwanton Anya kuwa
Zargin da sukeyi mashi gaskiya ne? Tayaya yarinyar da ake cutar da rayuwarta, kuma
take fada don an ta6a mutumin dake ƙoƙarin rabata da mutuncinta!! Fashewa tayi da
kuka Hannayenta tuni sun 6aci da jinin dr jazz tana kuka tana ambaton sunanshi”yaya
jaz dan Allah kada ka mutu kabarmu, wallahi idan ka mutu nima saina kashe kaina”
Zuciyar sir mubarak ce ta soma harbawa da ƙarfin gaske, Jiri ya soma ƙoƙarin
kwasarshi, Gaba ɗaya ya gama rikicewa, Hankalinshi atashe Yake kallon Kwalaben
alluran dake ajiye saman bedside drawer tare da sirinji, hada magunguna, Adaddafe
Ya nufi drawer din da niyar Ya duba kwalaban don ganin na menene, sautin ringin
wayar Jazz ne Ya dakatar da shi, da sauri ya daura rinannun idanuwanshi inda yake
jiyo sautin daga cikin aljihun wandon shaddarshine, Major ne yai saurin daukar
wandon Ya binciko wayar cikin aljihun, Ya miƙa ma sir mubarak, yatsun hannun shi na
kerma ya ruƙe wayar, batare daya duba sunan mai kira ba Yai picking call din Ya
sanya kiran handsfree.

Sautin muryar mutumin dayaji tayi matuƙar gigitar dashi, har baisan sa’adda Ya
saki wayar jazz ta fadi saman floor, sojojin dake atare dashi duk sun sha jinin
jikinsu, kallon kallo suka soma Yi a tsakaninsu, cikin matsanancin tashin hankali,
sautin shessheƙar kukan matashiyar ya cika dakin, dr jazz tuni Ya jima da sumewa.

*EX-PRISONERS💔*

Gaba ɗayansu sun hallara a dining room, domin cin abincin Dinner dinsu, mutun ɗaya
ne ke babu acikinsu, Yana can dakin shi, mazan suna fuskantar matan, sunyi shiga
kala ɗaya wandon jeans da farar shirt,matan kuma dogayen rigunane a jikinsu, Aunty
ummi ce kaɗai ta banbanta dasu, riga da skirt ne ajikinta sun matseta, shape din
jikinta Ya bayyana muraran, babu mayafi akanta, sa6anin su Batul da sukayi rolling
veils.

tunda suka zauna Unaisah ta kasa samun sukuni, yanayinta tamkar na mara lafiya, sai
faman jujjuya spoon take Yi acikin plate din gabanta, da ke shaƙe da abinci,
damuwar duniya ta isheta, sam babu sukuni akan fuskarta, A hankali ta ɗago da ido
tana duban fuskokin Ƴan uwanta, tun daga kan Sajeed dake fuskantar Azeeza, suna cin
abinci suna kallon juna, har zuwa kan Haris dake fuskantar Hannah, kafin ta kawar
da idonta daga kansu ta maida su kan fuskar Naufal da javed, sun natsu suna cin
abincinsu, hasken musulunci ya fara shigarsu, komai nasu cikin natsuwa suke yin
shi, mayar da idanuwanta tayi akan face din jamimah, bakinta duk ya 6aci da maiƙo,
ta samu cinyar kaza saici take Yi kamar tsohuwar mayya, ta cinye tsokar naman,
Ƙashin take gwaigwaya kamar babu sauran naman alhalin gashinan saman tray guda aka
jera masu chicken legs, girgiza kai tayi kafin ta mayar da dubanta kan Batul dake
gefenta, ita dai duniya babu abunda ke burgeta irin taliyar indomie, tun ranar
farko data fara cinta, kullum ne in zasu ci abinci saita ci ta, sam bata gajiya, da
hannu take nannaɗota kafin ta tura abaki, rantane ya raya mata ana kallonta, dai
dai time dinda ta tura taliyar abaki ta ɗago da ido suka kalli juna ita da Angel,
da sauri ta haɗiya taliyar, cikin muryar raɗa ta tambayeta lafiya take kallonta? Ko
tayi ƙauyancine”? Girgiza kai Angel tayi babu komai kawai burgeni kikeyi idan kina
cin noodles da hannu”
Gyaran murya ummi tayi masu atare suka ɗago suna kallonta.
“Unaisa tun ɗazu na lura kamar bakya jin daɗi, meke damunki ne”? Murmushin yaƙe ta
sakar mata”babu komai aunty ummi, ko kinga wani abu ne” ɗaga mata gira tai”ƙwarai
kuwa, tun da gashinan kin kasa cin abincinki”
Kafin unaisa ta ƙara furta wani abu, Muryar Haris ta katse su
“Kodai Danish bashi da lafiyane? Tun jiya da rana ban ƙara ganin ya leƙo waje ba,
naso naje na duba shi sai dai karatu Ya mantar da nayi yin hakan”
Cikin nuna damuwa Sajeed yace”wallahi yana araina, tun ɗazu da muna awurin kar6ar
karatu nake ta tunaninshi, bansan dalilin dayasa baya son zuwa cikin mu cin abinci
ba, naga dazu da rana ke kika kai mashi lunch dinshi a dakin shi” ya faɗa yana nuna
Unaisah da spoon din hannunshi.
Naufal Yace”to me zai hana mu tashi muje ɗakin nashi mu duba su? Ni abunda ke
damuna da danish baya son sakewa cikin mutane” Yai maganar fuskarshi dauke da
damuwa.
Javed yace”ai halinshine tun fil azal, kaima kasan Danish bai cika son zama cikin
mutane ba, baison surutu kuma baison ana kallon shi”
Gyaran murya Ummi tai masu, Hankalinsu Ya dawo kanta sun natsu suna jiran jin me
zatace
“Koda ace halinshi ne hakan bai kamata ku ƙyale shi ba, cos barinshi acikin ɗaki
zai Iya haifar mashi da wata damuwar, duk da naga Unaisah tana ƙoƙarin dubashi,
amma a ƙalla yakamata kuma kuna zuwa wurinshi kodan ku dinga ɗebe mashi kewa, kafin
zuwa lokacin da zai saki jikinshi, nasan rashin sabone ke damun shi”
Jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da bayaninta, Sajeed yace”ku tashi muje
dakinshi Inyaso sai mu tafi da kayan abincin mu ƙarasa ci acan” Yai maganar tare da
miƙewa, da sauri Unaisa tace”a’a basai mun tafi mu duka ba, Ku zauna ni zanje in
taho da shi” amsa mata sukayi da toh, da sauri ta miƙe ta nufi ƙofar fita daga
dining room din
Miƙewa Batul tayi Ummi tace Ina zuwa? Cikin sanyin murya tace ina so zanbi Unaisah
ne”
“Ki koma ki zauna, ai tace zasu dawo atare dashi ko”? Amsa mata tai da toh jiki
asanyaye ta koma ta zauna.
Shiru suka ɗanyi, abincinma sun dakata da cin shi, hakanan suke jin zuciyoyinsu
na bugawa, Jemimah kadaice ke cin abinci ta cika masu kunnuwa da sautin taunar
abincinta, da gangan take yi duk don ayi mata magana.
Harara Azeeza ta watsa mata”dan Allah ya isa haka, ba zaki Iya ci a hankali
bane”? Hanna tace”ki daina wahalar da bakinki, dagangan take yi duk don ayi mata
magana” tuntsirewa tayi da dariya tana fadin”Eh din kuma gashi kunyi min maganar
ba” girgiza kai ummi tayi fuskarta dauke da murmushi take dubanta, hankalinta
kwance take yin magana. Kallon da naufal ya jefa matane yasa tai shiru tana ƴan
ƙunƙuni.
“Kuna burgeni, gaba ɗayanku” ta fada tana nuna su da spoon din hannunta.
Batul tace”aunty ummi, kina nufin kina sonmu”? Jinjina mata kai tayi”haka nake
nufi,” murmushi su naufal suka saki jin abunda tace,
Parveen na faman siɗar hannu tace”Aunty ummi ke baki haifi ƴa’ƴa bane, kamar
yadda daddyn unaisah ya haife ta? Ko kuwa ita mace bata haihuwane sai maza”? Da
mamaki Ummi ta dan zaro ido tana kallon parveen da tayi maganar, sam babu wasa akan
fuskarta ita bilhakki take Yin maganarta.
“Amma baki da hankali parveen, Kin manta labarin da unaisa ta ta6a faɗa mana ne?
Macace take haihuwa ba namiji ba, itama Mommyntane ta haifeta ta jefar da ita cikin
wannan abun kalar na toilet din gidan nan, namanta sunanshi” Batul ce tai maganar,
Azeeza tace”eh kuwa hakane, Macace ta haifi unaisa ba namiji ba, to aunty ummi ke
kin ta6a haihuwa”? tayi tambayar tana kallon ummin america wadda mamaki da al’ajabi
suka cikata, sai kallonsu take Yi ɗaya bayan ɗaya, sajeed Ya duƙar da kanshi ƙasa
sai faman sakin murmushi yake Yi jin wautar parveen.
“Aunty ummi kinyi shiru baki ce komai ba, kina ta kallonmu” Hanna ce ta jefa mata
tambayar, ta ƙura masu ido tana binsu da kallon mamaki,
“wai kuna nufin bakusan komai ba, game da zamantakewar aure?
Atare suka haɗa baki wurin furta”Aure kuma”? Gudun kada suyi wata 6aran 6aramar
yasa Sajeed yin saurin cewa”aunty Ummi, Yakamata mu maida hankali akan abunda muke
Yi yanzu,” Ta6e baki taɗanyi kafin ta furta”okey, “ ta fahimci baison maganar dama
ta lura yafi su hankali shida Unaisah, bata ta6a ƙagara da sonjin labarinsu ba sai
yau, tabbas tana son tasan tarihin rayuwarsu! Ya akai har suka kai wannan shekarun
basusan komai dangane da zamantakewar aure ba? batun Yauba ta lura da ƙarancin
wayewarsu, kamar babu ƙwalwa akansu, basu iya komai ba, In banda cin abinci da
kwanciya bacci sunfi ƙwarewa a 6angaren nan.

_(Ummin america batasan su wanene prisoners ba, Mutanan da suka juri rayuwar kulle
tun suna jarirai, basu ta6a ganin hasken rana ba, dare da rana basu da abunyi daya
wuce idan ankawo masu abinci sau ɗaya suci sai kuma idan lokacin baccin su Yayi su
kwanta, badan Allah Ya ƙaddara zuwan unaisah kurkukun ƙaddara ba, da kuwa abunda
zasu aikata sai yafi hakan saboda su din tamkar baƙine a duniyar mutane, basusan
komai ba, unaisah itace ta wayar masu da kansu dangane da mutanan duniya da wasu
abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan adam shiyasa ma har suke Iya sakin jiki suyi
rayuwa acikinsu)_

Shin meya faru bayan Unaisah ta fita daga Dining room?

Cikin sauri ta nufi upstair, tunkafin ta ƙarasa ƙofar ɗakin danish ta dinga jin
faɗuwar gaba, tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, jiki na rawa ta nufi ƙofar room
dinshi, zura ƙafarta keda wuya cikin ɗakin, taga babu kowa wayam har saman gadonshi
babu mutun, sai faman baza ido take Yi tana faman ambaton sunanshi tamkar
makoshinta zai 6allo”Danish! danish! my Man! Kana ina”? Shiru babu alamun zai amsa
mata, ƙofar toilet dinshi ta tunkara lokaci ɗaya taji sautin gurnaninshi mai
matuƙar firgitarwa ya cika ɗakin, cikin jin faɗuwar gaba ta sanya hannayenta biyu
da ƙarfi ta ingiza ƙofar ta buɗe, tun daga bakin ƙofar toilet din ta ci karo da
singlet dinshi, A hankali take bin ko’ina da kallo har tayi nasarar cin karo dashi
kwance acikin kwamin wanka, wanda ke akewaye da glass, ya ƙunshe kanshi cikin
kwamin, jikinshi sai kerma yake yi, faɗawa cikin toilet din tayi, Cikin sanyin
murya take fadin”My man meke damunka? Meyasa kake yin gurnani? Baka da lafiyane”
idanuwanshi dake a lumshe ya buɗesu sun kaɗa jawur dasu tamkar an wanke ƙwayar a
cikin jini, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata damu da yanayin da zata
riske shi ba, Jiki amace ta shiga inda kwamin yake ta zuƙunna agabanshi tana
dubanshi, fatarshi tayi wani irin haske naban mamaki, Ya cika kwamin da ruwa mai
sanyi, amma saboda tsabar zafin jikinshi yasa ruwan ya koma na zafi.

Idanuwanta tuni sun cicciko da ƙwalla muryarta na rawa ta furta”My man dan Allah
kayi min magana meke damunka? Meyasa ka shigo toilet ka kwanta cikin bathtub”? Ta
faɗi hakan ne donta fahimci ba wani uziri bane ya shigo dashi toilet dinba, saboda
bai cire short dinshi ba, Ahaka ya shiga cikin ruwan duk don ya sassauta zafin da
jikinshi yai mashi.
Da wata irin kakkausar murya ya furta”Kiyi nesa dani, zan iya cutar dake, bani
bane, Ki tafi ki ƙyaleni, bana so in ta6a lafiyar jikinki” zazzare idanuwanta tayi
waje tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, muryarta adabarbarce ta
furta”me..meyasa kace haka danish? Idan bakai bane to wanene? Nashiga ukuna! dan
Allah kadaina furta waɗannan kalaman, Ni nasan bazaka Iya cutar.....” kasa ƙarasa
maganar tayi sakamakon ganin sa6ar macijin dake tsastsafo mashi saman fatar wuyan
shi, Kafin ƙyaftawar ido danish ya rikiɗa ya zama Giant snake fari sol, Jikinsa
yana da tsayi da kauri, mai santsi, Ya nannaɗe kanshi cikin kwamin wankan, Wani
irin narkeken maciji danƙareran gaske yana da doguwar jela da siraran harshe,
tsabar firgici da ruɗanin ganin abunda bata ta6a ganiba Ya hanata motsawa, jikinta
ya hauyin kerma zufa ta wanke fuskarta, ko amafarki bata ta6a ganin mutun ya rikiɗa
ba sai yau da Allah Ya nuna mata Danish ɗinta Ya canza halittarshi zuwa maciji,
girgiza jikinshi yai nan take kwamin wankan da yake acikin shi Ya tsastsage Ya
tarwatse, Ya faɗo ƙasa, aikuwa da gudun gaske Unaisah ta fito daga dakin, ta fasa
razananniyar ƙara, tana gudu haɗi da yin tuntu6e, a matuƙar gigice ta fado saman
bene, Mayafin kanta tuni yajima da barin jikinta, Sumar kanta duk ta rufe fuskarta,
cikin tashin hankali take tattaka matakalar benan, tana kuka haɗi da ambaton sunan
ƴan uwanta
Adai dai lokacin Chief Owais Yana saukowa down ta cikin glass elevator, ya kimtsa
cikin Dark jeans, daga sama ya sanya button-down shirt, yayin da ƙafafuwanshi ke
asanye cikin patent leather shoe, gefenshi Big guy ne hannunshi ruƙe da car key,
karaf idanuwan big guy suka sauka akan unaisah dake Faman zumbula gudu tana tunkaro
down, ta cikin glass elevator din yake kallonta, kafin yai yunƙurin buɗe baki Yai
magana, unexpected danƙareran macijin Ya kunno kai daga ɗakin ya daka tsalle Ya
haura ta saman handrail din benan Ya rigata saukowa ƙasa, da buɗar bakinshi sai
cewa yai”yalla6ai anya ban fara samun matsalar gani ba kuwa? Kodai tsufane Ya fara
kamani”?
THE GIANT SNAKE😳🔥

Tamkar Chief Owais bai ji me big guy yace ba, Hankalinshi baya akanshi, har saida
Ya furta”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! yalla6ai maciji nake gani, gashi can
Yana tafiya”a matuƙar ruɗe big guy yai maganar, sai lokacin Chief owais Ya ɗaura
idanuwanshi kan narkeken macijin dake ta faman jan jiki yana bin floor, Lamarin yai
matuƙar ɗaga mashi hankali, tsantsar mamaki da al’jabi ne suka kama shi, Fitowa
sukayi daga cikin elevator din tamkar a mafarki suke kallonshi sun gaza motsawa,
tsabar ruɗi Yasa Unaisah ta rasa inda zata tsoma kanta, Hannayenta bibbiyu ta ɗaura
saman kanta ta ƙware murya da ƙarfi ta furta”wayyo Allah na, nashiga ukuna! danish
dina ya koma maciji, dan Allah ku taimaka min” sautin muryarta ya karaɗe ko’ina,
hatta su Ummi dake a dining saida suka Jiyota, aiko Da gudun gaske suka soma fitowa
daga dining room din, Hankalinsu a matuƙar tashe suka ɗaura idanuwansu akan
fuskarta kafin wani yai yunkurin tambayarta lafiya meya faru, Giant snake din Ya
daka uban Tsalle Ya haura ta ƙarafunan jikin bene Ya kurɗaɗa hawa Na uku Yabi jikin
bango yaci gaba da tafiya ga dukkan alamu hanya yake nema.

Tsabar firgici da tsorone Ya kama su Batul, Azeeza tuni tajima da silalewa ƙasa
ta sume, Ummin america jikinta sai kerma yake Yi, tamkar wadda sanyi ya kama, batul
kuwa zufa ce ta soma tsastsafo mata, Parveen tuni ta saki fitsari a cikin wando,
Jikin jemimah na kakarwa ta ƙanƙame naufal ta fashe da kuka tana fadin”mun shiga
uku, wannan katon abun menene, Hankalin kowa ya tashi, da rarrafe Hannah ta lalla6a
ta 6oye ƙarkashin dining table.

Unaisah dake atsaye Jiki ba ƙwari sai kuka take Yi tamkar ranta zai fita, Cikin
zafin rai take Fadin”Danish ne ya zama maciji dan Allah ku taimaka min banaso wani
abu ya same shi, za’a iya cutar dashi nasan bakowa bane zai yarda cewa mutum ne Ya
rikiɗa”

Girgiza kai Gabriel Yai, Iduwanshi akan macijin La66ansa na kerma ya furta”taya
haka zai yiwu? Danish ya zama maciji? Ko a tarihi ban ta6a ji ba”!
Fashe masu tayi da matsanancin kuka”wallahi shine akan idona Ya canza
halittarshi, ina maku magana kunƙi ku fahimceni, yakamata muyi wani abu akai danish
zai Iya komawa prison” tana magana Hawaye nabin fuskarta, shatun Jijiyoyin wuyanta
sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta,gana saman goshinta.

Chief Owais yayi tsaye a yayin da yake bin macijin da kallo, babu alamun tsorata
ko firgita atare dashi, sai dai tsantsar mamaki da al’ajabi da ruɗanin da suka
kamashi, big guy Har ya yunƙura zai zaro bindigar daya soke a waist dinshi Chief
Yai saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu, A hankali Ya furta”Don’t shoot
him! Can’t you hear what she’s saying?

Zufa nabin fuskarshi yace”yalla6ai zai iya cutar damu, Maciji ne fa kodai baka
ganshi bane”?
Batare daya dube shi ba yace”naganshi”

Gaban sune yai mugun faɗuwar ganin yadda macijin Ya haura saman taga ya faffasata
Gaba ɗaya glass din Jikinta Ya zazzago ƙasa, Jami’in dake kula da cctv footage din
gidan ne suka watso da gudun gaske Cikin shiga ta kakinsu, hannunsu ruƙe da manyan
bindigu, kafin owais yai yunƙuri dakatar dasu tuni sun Haura upstairs, sai dai
kafin suyi yunƙurin kai mashi hari, Ya daka uban tsalle Ya fado saman floor na down
stairs Yabarsu atsaye can saman third floor kamar sakarkaru, Hankalin Unaisa Idan
yai dubu toh Ya tashi, Agigice ta fasa ƙara tana fadin”kada ku harbeshi! Ba maciji
bane mutunne! Ɗan uwanmu ne danish, dan Allah na roƙe ku kada ku kashe mana ɗan
uwanmu, wayyo Allah na Ya Allah ka kawo mana dauki”

Chief Ya kasa buɗe baki Ya dakatar dasu daga yunƙurin harbin shi da suke Niyar yi,
Tuni sun saita shi, Kusa atare suka fara Sakar mashi alburishi, tamkar baisan
sunayi ba, saima nannaɗe kanshi da yai a tsakiyar falon, Jikin ummi na rawa ta
dinga ingaza su batul cikin dining room, da gudu sajeed dasu naufal dukansu suka
koma dining din, har zata rufe ƙofa Sajeed Yai saurin furta Azeeza tana awaje,
fitowa yai jiki na 6ari ya cuccu6i azeeza ya shigar da ita dining room din, Ummi
taja kofa ta datse, duk da haka hankalinta bai kwanta ba, zufa duk ta wanke
fuskokinsu, parveen kusan sau uku tana sakin fitsari awando, ta jiƙe sharkaf,
bakinta cike da donut data tura takasa ƙarasa haɗiyeshi, kowa fa yasha jinin
jikinshi.

Da kakkausar murya ɗaya daga cikin jami’an isod dake acan third floor Ya daka ma
Unaisah tsawa haɗi da furta”ki matsa daga nan, Ki koma cikin ƴan uwanki” Fashewa
unaisa tayi da kuka tana fadin”wallahi babu inda zanje, saidai ku haɗa dani ku
kashe, Nace maku ɗan uwan mu ne ya rikiɗa ba yin kan shi ba ne”

Muryarta adisashe ta ƙarasa maganar, sam bata lura da chief Owais ba saboda bata
acikin hayyacinta, tayi tsaye tana faman yin shessheƙar kuka,
Umarni Chief Yaba big guy”ka kawar da ita daga gabanshi” cikin jin faɗuwar gaba Big
guy ya nufi wurin Unaisah, kafin ya ƙarasa macijin Ya warware jikinshi daga
nannaɗewar da yai, da wani irin sauri yake jan jiki Yana nufar ƙarshen falon inda
glass door din nan take, fasa ƙara unaisa tayi har ta yunƙura zata bishi big guy
yai saurin cafkota, aiko ta daddage ta gartsa mashi cizo a hannunshi azabar zafin
da yaji ce tasa shi sakinta, a lokacin jami’an isod Sun watso da gudu sun sauko
down Sai faman harba mashi bullets suke Yi, tsabar mamakine Yasa suka koma
kokwanton macijin, da zarar harsashin ya daki fatarshi Yake faɗuwa ƙasa batare daya
huɗa fatarshi ba, hakan ba ƙaramin tayar masu da hankali yai ba.

Wani irin bahagon tsalle ya daka saman glass din Ƙofar, Ya faffasa shi Yabi ta
ƙatuwar huɗar daya 6ula Ya dira tacan Bayan gini, da gudun gaske unaisah tabi
bayanshi, tamkar zata tashi sama, sam bata acikin hayyacinta, ba ta ji bata gani ta
makance, gani take kamar hanyar komawa kurkukun ƙaddara yake nema.

Gaba ɗaya jami’an sunbi bayanshi aguje, Sai dai sun kasa cimmashi, unaisa tana
gudu haɗi dayin tuntu6e har tafi jami’an sauri, duk inda ya nufa tana abiye dashi,
sai faman ƙwala mashi kira take Yi tamkar ranta zaifita.........

Moving quickly Chief Owais Ya fito daga part din, Big guy yana abiye dashi,
hankulan kowannansu Ya tashi, kaitsaye suka nufi Harabar ajiye motoci na gidan,
wata dankareriyar mota suka nufa, Big guy ya buɗe mashi kofar ya shiga ya zauna
shima Ya zauna, yai ma motar key, sai da yakusan ƙure speed din motar tamkar zasu
tashi sama tsabar yadda take yin gudu direction din da macijin yabi suka
nufa.............

*OBIE ESTATE🏙*

*HAJIYA SARATU❤*

A tsaye take gaban Dressing mirror, bata kaiga cire Swiss cord lace din Jikinta ba,
babu mayafi akanta, hakan ya bayyana kitson zanan da akayi mata, fitowa pravin yai
daga toilet jikinshi sanye da bathrobe fara ƙyal, da alama wanka Yai, sam bata lura
dashi ba ta dai ji motsin mutun abayanta, amma dayake hankalinta ba akanshi yake ba
shiyasa bata samu damar waigowa ta kalle shi ba, A hankali Yake ƙarema bayanta
kallo, Kayan sun ɗanyi tighting dinta sun bayyana dirin jikinta, musamman faska
faskan hips dinta.

Ba zato ba tsammani taji ya kwanto da kanshi saman wuyanta, ta baya ya rungumota,


ya zagayo da hannayenshi saman flat stomach dinta.
muryarta tamkar tame jin bacci ta murya”pravin meye haka”?
Manna mata kiss Yai saman wuyanta,
“Ba tambayata yakamata kiyi ba, ɗazu ina kallonki cikin taro, Kin saki jiki sai
tiƙar rawa kikeyi Alhazawan nan masu dogon gemu sun tsareki da mazuran idanuwansu
sunata kallon jikinki”

Ɗaure fuskarta tayi tamau, tare da sanya hannayenta biyu ta damƙi hannunshi
dayake ƙoƙarin ɗaurawa saman ƙirjinta.

“Kaga Bana son surutu, Yanzu na dawo cikin gidan nagaji ina buƙatar in huta,”
yaƙi bari ta ƙwace kanta daga ruƙon da yai mata.

“Bansan meyasa kike Yi min haka ba! Sam baki darajani a matsayina na mijinki,
bakya jin shakkar fadamin kin fita ba tare da iznina ba” a faɗace ta fusge kanta
daga jikinshi ta juya tana dubanshi.

“Oh gidan Yaya hateem din ne saina nemi izinin ka zan shiga? Sai kace na tafi
wata uwa duniya, ko kamanta ne? Acikin estate din nan gidanshi yake, na shiga wurin
matarshi ne don mu ƙara gaisawa, shi kenan komai zanyi dole saina faɗa maka”? Ta
faɗa tana jifarshi da harara, bawan Allah Ya tsare ta da ido yana kallonta, Idan
tana yi mashi magana tamkar zata rufe shi da bugu

Guntun tsoki taja”ka daina kallona, ka wani tsareni da ido kamar zaka lasheni, ni
bansan meyasa kake son zama ɗaki ba kamar wani munafuki, gasu baba can a falo ka
shiga wurinsu ka zauna ayi fira dakai”

Shiru yai bai tanka mata ba, babu alamun zai daina kallon nata.
Ta6e baki tayi”Idan baka da abunyi ni inada shi, don haka bani wuri In wuce”

ta faɗa tana ƙoƙarin bi ta gefenshi da niyar ta tafi, ba zato ba tsammani taji ya


damƙi damtsen hannunta, ruƙo bana wasa ba, har saida ta ɗago idanuwanta azare take
dubanshi.

“Kidaina yi min faɗa, bafa tsoronki nake ji ba, Ina raga miki ne saboda ƙaunar da
ke atsakanina dake” har saida taɗanji gabanta ya faɗi rass, ganin yadda ya haɗe
fuskarshi, kwata kwata babu annuri tamkar bai ta6a dariya ba.

“Ke komai baki Iya ba dangane da zamantakewar aure? Sai kace ba mace ba? Baki Iya
soyayya ba sannan baki da lokacina sai idan kinga dama zaki bani hakki na? Abu
kaɗan saiki rufeni da faɗa kamar ɗan cikinki? Ko kin manta matsayina awajenki? Idan
kin manta bari na tuna maki, Ni mijinki ne a ƙarƙashin ikona kike, Nafi kowa Iko
dake hatta mahaifinki, Aljannarki tana a ƙarƙashin ƙafata idan har bakiyi min
biyayya ba tayaya kike tunanin zaki sameta”? cikin jin ƙunar rai Ya furta hakan,
maimaikon yaga nadama akan fuskarta sai gani yai ta tuntsire da dariya har fararen
hakoranta suka bayyana, fisge hannunta tayi daga ruƙon da yai mata.

Ta ruƙe qugu ta matsa dab dashi kafin ta soma magana”Naji abunda kace babyn baby,
sai dai akwai gyara a kalamanka, bani ce nake a ƙarƙashin ikonka ba, Kaine kake a
ƙarƙashin ikona, ko kamantane, agidanmu kake zaune, cin ka shan ka suturarka dama
komai nice nake kula dasu, baka da wata power pravin, babu yadda za’ai nayi maka
biyayya sai dai kai kayi min saboda nina cancanci hakan, Nice hula kaine ɗan
kwalin, aljanna kuma ta mai rabo ce” da wulaƙanci take furta maganar, lamarin ya
ɗaure mashi kai, a iya saninshi saratu tana da ilimin addini amma idan tayi wasu
kalaman ba ƙaramin mamaki take bashi ba, Ƙululun bakin ciki Ya hana ya furta mata
magana, idanuwanshi sun kaɗa jawur dasu, Ranshi Ya 6aci sosai a fusace Ya juya ya
fuce daga ɗakin, ta6e baki tayi aranta ta ayyana”matsalarka ce koda yake laifina ne
dana auri dangin kirishna, masu bautawa soyayya” ta faɗa tana dariya.

❤🤍❤

A Zazzaune suke saman tattausan carpet, ɗan ubansu zubin kafi mage Laushi dake A
cikin katafaren falon gidan baba obie, daga tsakiyar Royal sofa set din falon
carpet din Yake a shimfiɗe hadadden gaske, tamkar shimfiɗar sarakuna, an kewaye
bakin carpet din da tuntun, asaman su dattijon arziƙi Ya ɗaura kanshi, Prime
minister Hateem Yana a kishingiɗe shima ya ɗaura kan nashi saman tuntun, Basu kaɗai
bane saman carpet din akwai senate lateef tare da his excellency deen da kuma His
excellency abdul Razak duk sun kishingiɗa kansu saman tuntun, kowan nan su
jabbiyace a jikinshi, ta obie data hateem launi ɗayane ruwan toka, hateem ya manna
farin glass a idanuwanshi hannunshi na dama hadaddiyar Agogon azurface mai kyan
gaske, zobenta ne a yatsun hannun shi.
Jallabiyar sharafuddeen data his excellency deen launin brown ce, yayin data
Senate lateef ta kasance milk colour, hankalinsu kwance suke shan firarsu, sun baro
iyalansu a makwancinsu, yayin da su kuma suka haɗa majalissarsu afalo.

Babban tray ne aka ajiye masu kan carpet din, Saman shi Tea pot ce mai ɗauke da
green tea, ga jerin kofuna, suna fira suna shan abunsu
“Baba mun cika ka da surutu ko”? Senate lateef ne Yai maganar yana duban
fuskarshi.

Ɗaura hannu yai saman gemunshi tamkar yana kitsa shi Yace”Ni ai banƙi kuyita
surutu ba daga yau har gobe, wallahi bana gajiya da sauraronku, Ina jin daɗin ganin
ku atare dani, nayi kewarku sosai”

Murmushi kowan nan su Ya saki, In ka cire hateem daya lumshe idanuwanshi ga


dukkan alamu bacci yake ji.
“Kamar yadda baka gajiya da sauraronmu muma haka bama gajiya da faranta maka,”
acewar his excellency deen
lumshe idanuwanshi yadanyi hadi da jinjina kanshi
His excellency abdul razak Yace”baba, akwai wata magana mai mahimmanci da nakeson
Yi dakai, tunda yanzu duk mun haɗu agaban ka, Inaga Yakamata muyi anan idan ka bani
dama”!

Mayar da hankali obie Yai akan abdul razak”ina sauraronka”

“Dangane da matasan family dinmu, bai kamata mu zuba masu ido muna kallonsu ba,
yakamata kowan nan su ya fidda matar da zai aura”

His excellency Deen Yace”Ni kaina abun yana damuna, wani abin ɗaure kanma Yaran
tamkar basu da ra’ayin ajiye Iyali, kaga Justice namu da dr nawaz sam basu son Inyi
masu zancen aure”

Murmushi obie Yasaki yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Senate yace”har ƙwara Ziyad, idan nayi mashi maganar aure sai kaji yace inada
wannan burin baba in sha Allah nan bada jimawa ba zan fidda matar da zan aura ka
tayani da addu’a Allah ya bani mace ta gari”

Mai girma sharafuddeen dake sauraron yayyan nashi, hannun shi ruƙe da mug na tea
da yake kur6a, da alama yana jin dadin tattaunawarsu.

Deen yace”su kuwa waɗannan ba’a maganar ƴa’ƴansu, dama ance magaji mafiyi, akansu
na fara shaidar hakan” yai maganar Yana nuna Sharafuddeen da Hateem.
Gyaran murya sharafudden yai kafin ya soma magana atsanake”lamarin Owais namu
sai addu’a, Ni bana gane kanshi, mace bata agabanshi, na ta6a yi mashi zancen aure
sau ɗaya sai ce min yai baya son ya ɗaurawa kanshi nauyin da bazai Iya sauke shi
ba”

Murmushi kowan nan su ya saki, Obie yace”kada ku takura kanku akansu, lokacin yin
auran nasu ne baiyi ba, da zarar time yayi babu wanda zan saurara acikinsu sai dai
kawai suji sanarwar ɗaurin auransu a masallaci”

Jinjina kai sanate Yai”baba ka kawo shawara mai kyau, mu haɗa kowan nan su da
abokiyar rayuwarshi, tunda muna da ƴan mata a family namu”
His Excellency abdul razak Yace”wai Ina ɗan uwa mubarak Yaje ne”?
Senate lateef Ya bashi amsa da cewa”ɗazu dai muna zaune naji wayar shi na ruri har
nace mashi ya dubata ana kiranshi, tun da ya fita har yanzu shiru bai dawo ba,
wataƙil ya wuce gidanshi”
“Mu ma yakamata muje mu kwanta, mu huta” acewar deen.
Daura ido obie yai akan fuskar Hateem babu alamun Yana sauraronsu.
Gyaran murya yai mashi haɗi da zungurin kafaɗarshi da hannu, firgigit Ya ware
idanuwanshi Yana faman yamutsa fuska”Idan bacci kake Ji yakamata kaje ka kwanta”
girgiza kai yai”a’a ba bacci nake ji ba, Ina sauraronku”

da zolaya senate lateef yace”Oh, mu ka maida shashashu mun saki baki munata
surutu ka kasa kunne kana sauraronmu, Wato kafi ƙarfin ka tanka mana”

Mai girma sharafudeen Yace”bacci yake ji fa, ba sauraronmu yake yi ba, tun ɗazu na
lura dashi, baba ne Ya farkar da shi,” ya faɗa yana duban hateem”malam ka tashi
kaje wurin Iyalinka ka kwanta ka huta”
Yamutsa fuska Hateem yai”Na faɗa maka ba bacci nake ji ba, idona biyu” ya faɗa
yana zare mashi manyan idanuwanshi, dariya suka saki gaba ɗayansu.

Kafin wani Ya kuma furta kalma, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka Jiyo
masu sautin fashewar glass, Baba obie Yace”kuna jin abunda nake ji kuwa? Ko dai
kunnuwana ne suka jiyo mun badai dai ba”

Senate yace”kamar fashewar glass, bari in duba” ya faɗa yana mikewa tsaye, karaf
idanuwanshi suka sauka akan Giant snake din dake ƙoƙarin faɗowa ta ƙofar glass din
wani ɗaki dake acan upstair hawa na Uku, ras yaji gabanshi Yai mugun faɗuwa,
Muryarshi na rawa ya furta”inna lillahi wa’inna ilaihirraji’in!” Jin ya zabga
salati yasa Sauran ƴan uwan nashi sukayi saurin miƙewa, tare da daura idanuwansu
saitin inda senate Yake kallo, tashin hankalin da ba’a sanya mashi date, sunyi
matuƙar firgita da ganin danƙareran macijin dake bin jikin bene Yana ƙoƙarin
saukowa down, jikin baba obie Ya hau yin kerma abunka ga tsoho, Ido Ya raina fata,
lamarin ya ɗaure masu kai, Deen yace”maciji kuma? Tayaya akai ya shigo gidan nan?
ina jami’an dake tsaronshi? Wannan wani irin ganganci ne”?

Kafin wani ya bashi amsa, kwatsam suka jiyo takun tafiyar jami’an isod, da gudun
gaske suke shigowa cikin falon, hannayensu ruƙe da bindigu, atare suka hada baki
wurin furta”yalla6ai ku kwantar da hankalinku, zamu kawar maku dashi,” A matuƙar
ruɗe baba obie yace”baku da hankali, taya akai kuka bari maciji Ya shigo gidana? A
haka kuke fadin mu kwantar da hankalinmu? Kun makance ne baku ganin girman shi?
tayaya zaku Iya kamashi”! Da sauri Senate ya tari nunfashinshi”baba kayi haƙuri,
zasu fitar dashi, mubarsu suyi aikinsu”

Daya daga cikin jami’an yace”kayi hakuri yalla6ai ba laifinmu bane, mu kanmu
bamusan tayaya akai Ya faɗo cikin estate din nan ba, babu wanda yasan daga ina
Yake”

da hannu deen Ya nuna masu hanya”ku shiga kuyi aikinku” da sauri suka nufi benan.
Adaidai lokacin Unaisah dake ta faman gudu ta shigo cikin falon tana haki, duk ta
fita hayyacinta, kusan atare suka ɗaura idanuwansu akanta, da mamaki akan
fuskokinsu suke dubanta, kafin wani yai yunkurin yi mata magana, Chief owais Ya
faɗo falon tare da big guy, sunyi mamakin ganinshi babu wanda yasan yana a ƙasar,
tsabar firgici da tsoro Ya hana Obie furta sunanshi sai faman binshi Yake Yi da
kallo.

Umarni yaba big guy akan ya dauki Unaisah ya maidata gida, jin ya furta hakan yasa
ta watsa da gudu cikin falon bata nufi ko’ina ba sai saman benan da zai sadata da
macijin, da gudu big guy yabi bayanta, cikin shessheƙar kuka take fadin”dan Allah
kada ku kashe shi, wallahi ba maciji bane, ɗan uwanane danish”

damƙo hannunta big guy yai, tadinga kiciniyar ƙwace kanta ranta amtuƙar 6ace ta
soma zazzaga masu masifa tana fadin”wallahi babu inda zanje, nace maku dan uwanane,
ku ƙyale shi ku daina harbinshi tunda bai cutar da kowaba, wayyo Allah na danish
ɗina”

Sautin koke kokenta Ya cika gidan, hatta sauran mazauna gidan baba obie saida suka
jiyota, ɗaya bayan ɗaya masu aikin gidan suke fitowa daga makwancinsu, Pravin bai
jima da shiga ɗakin hajjaty ba ya jiyo sautin Kukan mutun agidan, sai gashi ya fito
hajjaty na abiye dashi, Hajiya saratu kuwa jin sautin kukan Yasa ta fito daga ɗaki
ta shigo falon, koda tayi arba da unaisa ga jami’ae da kuma shirgegen macijin dake
bin bango, hannayenta biyu ta ɗaura akai tana ambaton Inna lillahi wa’inna
ilaihirraji’un! Maciji acikin gidan nan? Wacece wancan Yarinyar? Ya akai ya shigo?
Aruɗe ta furta hakan
Kowa Ya shiga ruɗani, Jami’an sun dage sai antaya mashi Harsashi suke Yi, Ganin
suna ƙoƙarin yi mashi illa yasa Unaisa tayi wani irin kukan kura, ta bangaje big
guy da iya ƙarfinta na ƙarshe, ta haura sama da gudun gaske, duk yadda suka so su
kawar da ita sun gaza yin hakan har saida tayi nasarar ƙarasawa inda yake, tsawa
suka dinga dakata mata suna korarta daga gabanshi amma taƙi matsawa, macijin yabi
ya nannaɗe kanshi Ya dunƙule waje guda saman floor, lullu6e shi tayi da bazar
rigarta, tana kuka tana fadin”danish dan Allah ka saurareni, ka taimaki rayuwata,
bana so na rasa ka, ka canza halittarka ka tabbatar masu da cewa kai mutunne ba
maciji ba, idan ba haka ba zasu Iya kashe mun kai” cikin jin ƙunar rai take Furta
maganar, ta ƙanƙameshi kamar zata maida shi jikinta, jami’an sun natsu suna kallon
ikon Allah, Hajiya saratu sarkin tsoro sai faman baza idanuwanta take Yi, baba obie
Yana la6e bayan Mai girma sharafuddeen, Senate Ya ruƙo hannunshi dake tayin kerma,
A hankali Hateem Ya zare farin glass din dake asaman fuskarshi Ya ruƙe ahannunshi,
komai ke faruwa akan idanuwanshi, tamkar amafarki suke kallon lamarin, an rasa
wanda zai janyeta daga jikinshi. Abunda ya ɗaure masu kai babu alamun macijin zai
cutar da ita.

Duk da baya iya furta mata magana, ranta yana bata cewar yana son ya rikiɗa ya
koma mutun sai dai ya kasa yin hakan, jikinshi ya ɗau zafi sosai, cikin sanyin
murya ta soma yin magana, hawaye naci gaba da wanke fuskarta
“Ɗan uwana rabin raina, dan Allah ka canza halittarka, idan ba haka ba babu wanda
zai yarda cewa kai mutunne zasu ci gaba da cutar min dakai” ta faɗa tana ƙara
kankameshi a Jikinta.
umarni Owais Ya ba jami’an akan su daina yunƙurin harbinshi, amsa mashi sukayi
datoh, ya fadi hakanne saboda ya fara kokwanton mutunne kamar yarda ta faɗi, a
faɗace hajiya saratu tace”akan me zaka basu umarnin su daina harbinshi? idan ya
cutar da wani fa”? Ko kallo bata ishe shi ba, muryar baba obie Na rawa ya furta”Ku
kashe macijin nan, bana son ganinshi, ku kawar mana da shi”

“Baba ka kwantar da hankalinka, Ni na yarda da maganar yarinyar ba maciji bane


mutunne” mai girma sharafudden ne yai maganar.

A harzuƙe Obie Yace”tayaya mutun zai zama maciji? hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Ni
bazan ta6a yarda ba, ku kawar mana dashi kawai, idan baso kuke zuciyata ta buga ba,
Ita kuma waccan Yarintar mai kasada ƴar wacece? Ku ɗauke ta mana daga Jikinshi kada
ya sare ta”yai maganar yana nuna Unaisah da sandar hannunshi.

Duk yabi ya furgice masu, big guy ne ya kutsa ta cikin jami’an Ya nufeta,
muryarshi ƙasa ƙasa tamkar tame Yin raɗa ya furta”Unaisah, ki tashi mu tafi gida,
za’a dawo maki dashi” maƙe mashi kafaɗa tayi, la66anta duk sun bushe sun faffashe.

“Babu inda zanje, Ina atare dashi, Idan nayi nesa dashi, ba zaku Iya sarrafashi
ba, zai Iya guduwa ya nufi wani wajen” magiya ya dinga yi mata akan ta miƙe amma
taƙi tashi, hakan Yasa Chief owais motsawa ya haura saman benan Ya nufe su, Darewa
jami’an suka dinga yi suna bashi hanya har ya kaiga ƙarasawa inda suke, faffaɗan
tafukan hannaye shi ya ɗaura saman unaisa ya ɗaɗɗagota tare da ɗaurata saman broad
shoulder dinshi, juyawar da zaiyi da niyar ya tafi da ita, giant snake din Yai wata
irin girgiza da gudun gaske yabi bayan owais daya ɗauketa.

Jami’an suka saita shi da bindiga owais Ya hana su harbeshi yace masu su barshi
akwai dalilin dayasa yayi hakan, Yana tafiya macijin Yana bin bayanshi, kasancewar
ya ɗaurata saman kafadarshi tana Iya kallon giant snake din daketa ta faman jan
ciki Yana nufosu, hawayenta tamkar zasu ƙare muryarta shaƙe take ambaton sunan
Danish.

Ganin macijin zai sauko down yasa Hajiya saratu ta watsa da gudu zaninta har yana
kwancewa ta ruƙo shi ta nufi hanyar part dinsu aguje ta shiga ɗaki ta datse kofa,
tabi tagogi duk ta rufesu, a karshe cikin toilet ta shige tayi locking kanta.

Hankalin baba obie yai matuƙar tashi sai ƙara ƙankame jallabiyar mai girma
sharafuddeen yake yi, Hateem kuwa ko kadan baiji tsoron macijin ba, tsabar mamakine
Ya hana su furta magana, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah, duk inda owais
yai da ita sai macijin yabisu, fucewa yai daga falon Ya nufi motarsu da su ka yi
parking dinta abakin entry hall, Ya buɗeta Ya shigar da unaisah aback seat na
motar, ya buɗe front seat a mazaunin driver Ya zauna yai mata key, da gudun gaske
Ya fusgi motar, ta cikin glass din motar take kallon macijin daketa binsu da ƙarfi
Ya daka uban tsalle Ya haura saman motar Yai kwanciyarshi.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin yana atare dasu, bai nufi ko’ina ba sai sashen da
gidansu yake, ta gate din Baya ya shigar dasu a bakin entry hall chief Yai parking
din motar, Ya fito Ya buɗe back seat din Ya cuccu6i unaisah Ya ɗaurata saman
kafaɗarshi Ya nufi Babban falo da ita, hankalin shi kwance tamkar baisan da zaman
macijin ba, saukowa yai daga saman motar yabi bayansu da gudun gaske yake jan
jiki.

Cikin takun sauri Owais Ya haura upstairs da ita, kafin Ya ƙarasa second floor,
macijin Ya riga shi isa, wani wawan tsalle ya daka Yabi ta jikin bene Ya faɗo
tagabansu, ƙoƙari yake ya nannaɗe ƙafafuwan owais sai dai yakasa yin hakan saboda
owais bai bashi damar ruƙe mashi ƙafa ba, sai kakkauce mashi yake Yi, a haka ya
ƙarasa bedroom din Danish Ya shiga daga ciki, Ya kwantar da ita saman gado, Shigowa
ɗakin macijin Yai yana faman huci kamar zai kai mashi hari, saman gadon Ya haye
Yana faman bin mattress din. Owais dake a tsaye ya goya hannayenshi saman wide
chest dinsa, Ya natsu yana kallonsu.

Giant snake din Ya nannaɗe jikinshi agaban unaisah ya ɗago da kanshi Yana kallon
owais, duk a tunaninshi wani abu zaiyima unaisah shiyasa Yabiyosu, shi kuma owais
daya fahinci Baya iya cutar da ita shiyasa yai dabarar daukota sai gashi yaci
nasara akanshi”

Fitowa yai daga ɗakin Yaja ƙofar Yai locking dinta, Yabarsu su biyu adakin Ya
nufi down.
Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi, tsananin
tsorone Ya kamata, amma saboda ƙaunar da take yi mashi takasa motsawa, duk tasha
jinin jikinta, muryarta na rawa ta furta sunan shi”danish ɗina” juyowa macijin yai
da kanshi Yana dubanta, jikinta na kerma saboda ƙarfin hali ahaka ta miƙa mashi
hannunta, jan jiki ya somayi yana nufarta, saman kirjinta ya nannaɗe kanshi, wani
irin sanyi taji ya ratsata, lokaci ɗaya tadaina jin bugun da ƙirjinta keyi mata,
asaman fatar shi ta ɗaura hannunta, a hankali take shafashi duk don ta kwantar
mashi da hankalinshi, ita kaɗaice zata Iya fahimtarshi a halin da yake ciki.

Walking quickly chief Ya nufi Ƙofar fita daga part din, Kafin Ya ƙarasa Muryar Boss
man ta katse mashi hanzarinshi”yalla6ai” cak Ya tsaya da tafiya ya waiwayo yana
dubansu, su biyune suka fara shigowa shida big guy, daga bayansu sauran jami’an
isod ne da suka Biyosu, hankalinsu duk ba a kwance yake ba, musamman Boss man da
yaji labarin abakin big guy shigowar shi kenan gidan duk wannan budurin da akeyi
baida masaniya yana a part dinsa.

Fuskar chief owais ta canza zuwa yanayi na damuwa.


“Yalla6ai Ina macijin yake”? Big guy ne ya jefa mashi tambayar.
Daƙyar Ya iya buɗe baki Ya furta”yana adakin shi, tare da yarinyar na kullesu”
waro ido waje sukayi suna kallon shi
Muryar boss man na rawa ya furta”kana nufin tare da Angel ka rufe su aɗaki? Idan
ya cutar da ita fa”? Gaba ɗaya yabi ya ruɗe.

Big guy yace”ka kwantar da hankalinka, Ni na fahimci hikimar yin hakan, da ace bai
daukota ba macijin bazai dawo gidan ba, bamusan inda zai shiga ba, amma yanzu kaga
mun kulleshi aɗaki ta dalilinta”

Cikin rashin fahimtar kalaman big guy Boss man yace”bazai yiwu ba, Ƴata fa aka
kulle aɗaki ɗaya da maciji, Idan ya kashe min itafa” dafa kafaɗarshi Owais Yai da
hannu ɗaya”kadaina kiranshi maciji, mutunne, bazan iya yin abunda zai cutar maka da
ƴarka ba, Kamar yarda kake jinta nima haka nake jinta, fatan ka fahimce ni” gyada
kai Yai still hankalinshi bai kwanta ba.
“A wani daki ka kulle su”?
Atakaice owais Ya furta”A dakin shi” jiki na rawa boss man Ya watsa da gudu ya nufi
upstair.
Chief owais Ya maida dubanshi ga Big guy, “Things are starting to get out of
control, and I don’t know what to do now. But I want to see his brother, maybe he
can control him. kaje ka zo dashi” ya faɗa in a cool voice, amsa mashi yai da toh,
da sauri Ya juya ya fuce daga ɗakin, Kallon sauran jami’an yai”ku koma bakin aikin
ku, ku tabbatar kun kula sosai” Cikin girmamawa suka amsa mashi da toh, juyawa
sukayi da sauri kowa Ya nufi hanyar komawa bakin aikinsa.
Shafa sumar kanshi yai da tafin hannun shi nadama, yanke shawarar komawa gidan
obie yayi, yasan suna can hankali duk Ya tashi, ba lallai su iya runtsawa ba.
Cikin takun sauri Ya fita daga part din, Ya nufi ɗaya daga cikin motocinsu, wani
jami’i ne Ya nufeshi da sauri Ya buɗe mashi motar ya shiga a mazaunin baya, shi
kuma ya zauna a driver’s seat, yai ma motar key ya tashe ta, suka nufi cikin Obie
estate......

Unaisa tana akwance idanuwanta sun kumbura suntum, kumatuntu sunyi jawur saboda
kukan da tasha, busassun hawayene saman fuskarta, ta lumshe idanuwanta akan giant
snake din daya ɗaura kanshi saman kirjinta, karatun qur’ani take raira mashi cikin
disasshiyar muryarta daƙyar sautin ke fita, macijin Yayi lamo sai ƙara narke mata
yake Yi, ga dukkan alamu yana sauraronta.
Da karfi tajiyo muryar boss man Yana kwaɗa mata kira daga waje Unaisah,
Unaisah!!.
A hankali tasoma ƙokarin raba jikinta daga na macijin, ta lalla6a ta sauko daga
saman gadon tana cigaba da yin ƙira’ar al’qur’anin, agogon bangon ɗakin ta kalla
almost 10 na dare.
A jikin glass door din Boss man Ya jingina yana leƙensu.
Ƙarasowa tayi gaban ƙofa suna fuskantar juna, batasan sa’adda ta fashe mashi da
kuka ba, Cikin shessheƙar murya take fadin”kaga irin ƙaddarar da ta sami ɗan uwana
ko? Nayi ƙoƙarin na fahintar dasu cewa mutunne amma sunƙi su gane, sai harbinshi
suke Yi da bindiga”

Tsananin tausayine ya kamashi ganin yadda ta canza saboda damuwa.


Cikin kwantar da murya yace”Yana ina “?
Matsawa tayi daga bakin ƙofar, karaf idanuwanshi suka sauka akan giant snake din
dake nannaɗe saman gadon kamar bacci yake yi.
“Unaisa bai cutar dake ba”? Tambayar daya jefa mata kenan, Girgiza mashi kai
tayi”a’a baiyi min komai ba, dan Allah ka taimaka mashi, nasan kai kaɗaine zaka Iya
fahimtana,”

Jinjina kanshi yaɗanyi”okey, Ki kwantar da hankalin ki, kidaina kuka bana son
ganinki cikin damuwa”
Fuska amarairaice tace”dole in damu boss man, rayuwar ɗan uwana abun tausayice,
bazasu ta6a ƙyale shi ba, tun yana jariri suke cutar dashi har izuwa girmanshi
sunƙi su ƙyale bawan Allahn nan, mugaye in sha Allah bazasu ta6a yin nasara akanshi
ba”
Idanuwanshi tuni sun cicciko tab da ƙwalla
“Dan Allah ka taimaka mashi, akwai ruwan zamzam da ake bashi na addu’a ina da
tabbacin idan yasha zai dawo dai dai”
Cikin sanyin murya yace”A ina za’a same shi”?
“Ɗan uwanmune Ya bani address din gidan da zamu ɗauko, namanta takardar acikin
aljihun uniform dina, ai kace min kayan suna a hannunku, idan ka duba zaka ga
wandona launin baƙi, mu uku keda kalar kayan dani da batul saina danish, pls ka
bincika ka dauko ta, Allah yasa bata faɗi ba, nasan ma zaiyi wuya asamu zam zam din
koda an samu takardar adreshin”
“In sha Allah za’a nemo zam zam din, ki koma ki zauna amma pls kada ki bari ya
cutar min dake” amsa mashi tayi da toh” ajiyar zuciya ya sauke, tamkar karya tafi
yabarta haka yake ji, duk da Ya yarda Yaron bazai Iya cutar da ita ba, tunda gashi
ya same su asaman gado ɗaya batare daya sare ta ba, shi tausayin yaron ma yake Ji.

Juyawa yai da sauri Ya nufi down stair.


Komawa tayi saman gadon ta haye, ta kwanta daga gefenshi taci gaba da yi mashi
karatun qur’ani.

Da matsakaicin gudu motar chief ta ƙaraso bakin entry hall na shiga babban falon
gidan baba Obie, dasauri jami’en Ya fito daga motar Ya zagaya other side Ya buɗe
mashi murfin car din, Ya zuro kafarshi Ya nufi Cikin gidan da sauri, Kamar yadda
yabarsu haka ya same su a tsaitsaye cirko cirko , damuwace ƙarara akan fuskokinsu,
hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba idan har ba gawar macijin suka gani ba.

“Owais”! Obie ne ya ambaci sunan shi da mamaki akan fuskarshi.


Dagowa yai da kyawawan idanuwanshi ya daurasu akan faces dinsu, kamar yadda yake
kallonsu haka suma suke binshi da kallo, Kamar yaune rana ta farko da suka fara
ganin juna”
“Owais Ina macijin”? hateem ne ya jefa mashi tambayar.
Calmly ya furta”mun fitar dashi daga gidan” ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke,
Senate lateef Yace”Wacece yarinyar dake atare dashi? Munji tana kuka tana fadin ɗan
uwanta ba maciji bane shin dagaske ne”!
Jinjina kanshi yai alamar eh, ya ƙara da cewa”Ƴar uwarshi ce, ba maciji bane
mutunne kamar kowa, ƙaddara ce ta afka mashi”
“Wai kana nufin ɗan mutunne ya rikiɗa ya koma maciji”? His excellency deen ne Ya
jefa mashi tambayar, gaba dayansu sun ruɗe da jin maganar,
Abdul razak Yace”bazai yiwu ba, owais kodai ka fara shaye shaye ne? In bahaka ba ta
ina mutun zai Iya komawa dabba kamar maciji? Ai sai dai idan ya kasance ba mutun
bane shi”
Obie duk Yafi su firgita jikinshi yaƙi daina yin kerma
“Owais bana son ganin macijin nan, ku tabbatar kun fitar dashi daga gidan nan,
Idan ba haka ba zai Iya cutar da rayuwar ahalina”
“Baba ka kwantar da hankalinka, zuwa gobe in sha Allah zan shigo muyi magana,
nasan yanzu ko nayi maku bayani ba lallaibane ku fahimceni ba, ni kaina hankalina
ba a kwance yake ba”
Girgiza kai obie yai”owais idan kaga na kwantar da hankalina to macijin nan baya
acikin gidan nan, Ni ban ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, wai yaushema ka
dawo kasar? Ita yarinyar dake tare da macijin ƴar wacece? A ina take zaune”?
Shiru yai yana duban face dinshi, sam bayason yawan surutu, abu kadan ke hasala
shi, baisan amsar da zai basu ba, don ya fahimci hankulansu ba akwance suke ba.
Gyaran murya mai girma sharafudden Yai, hankalin owais ya dawo kan
mahaifinshi”kada ka damu, ka koma bakin aikin ka My son, Ni na fahimce ka, kaje
kawai zuwa gobe zamu nemaka donka zo ka warware mana rudanin da muke aciki” lumshe
ido owais yai haƙika yaji dadin maganar mahaifinshi, dama yasan shi kadaine zai Iya
fahimtar halin da yake aciki
Kafin Ya juya saida ya fara kallon Obie, wanda tuni idanuwanshi sun kaɗa jawur,
tausayin tsohon ne Ya kama shi, yayi matuƙar yin kewar kakanshi.
Matsawa yai kusa dashi Ya rungume shi saman faffadan ƙirjinshi, baba Obie Ya
kankame owais tamkar zasu koma mutun ɗaya.
Cikin sigar lallashi yake yi mashi magana”nayi kewarka baba, kana araina, nasan
ban kyauta maka ba, amma in sha Allah idan komai Ya lafa zuwa gobe zan shigo gidan”
cikin sanyin murya obie Ya amsa mashi da toh, ji yake tamkar karya tafi yabarshi,
yana matuƙar ƙaunar jikannan nashi.
Iyayenshi dake kallonsu, murmushi ne saman fuskokinsu.
Raba jikinshi yai daga na baba obie, yakai hannu Ya shafi dogon gemun shi, da
zolaya ya furta”kakana nakaina, nifa da jarumta nasanka, kai ɗin Namijin duniya ne,
dan Allah kada ka bani kunya, kada ganin macijin nan ya hanaka rintsawa adaren yau,
kayi bacci ka huta gobe jikanka zaizo gareka, sabon cake zamu yanka atare”
Farin ciki Ya cika obinna, yayin da yake duban owais, yana dariya yace”ka wahalar
dani, bakasan irin kewarka da nayi ba, Na ƙwallafa raina akan son ganinka, ka manta
dani owais, gobe idan kazo har tsallan kwaɗi zan sanyaka” dariya Iyayenshi suka
sanya, Owais yace”kowani horo zakayi min bazan musa ba, Na cancanci fiye da hakan,
Ni zan tafi, ku kulamin da kakana, Make sure he sleeps peacefully tonight.” ya faɗa
yana duban iyayenshi, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, owais ba ƙaramin
burgesu yake Yi ba, saboda yana son mahaifinsu.
Juyawa yai da sauri ya nufi ƙofar fita daga falon, idanuwan kowan nansu akan
bayanshi, Harya ɗaga kafa zai fuce, muryar prime minister ta dakatar dashi
“Owais! ina son yin magana dakai” a hankali Ya juya yana dubanshi, da sauri
Hateem Ya nife shi, babu mai Iya jin abunda suke cewa saboda sunyi nesa da sauran
mutanan.
Dafa kafadarshi yai da hannu ɗaya, tunkafin hateem yai magana owais ya riga shi
furta”uncle sai kunyi hakuri dani, ka zo kasar bansamu lokaci nazo gaishe ka ba”
murmushin gefen fuska yasakar mashi”ni wannan ba damuwata bace, nayi maka uziri
saboda nasan yanayin aikin ku,’ ya faɗa yana dubanshi kafin yaci gaba da magana.
“Inaso ka faɗamin dagaskene macijin nan mutunne”?

Jinjina kai owais yai”dagaske ne mutunne ya rikida, matashin saurayi”


Shiru hateem yaɗanyi kafin ya kuma cewa”Ya sunanshi”?

“Danish” ataƙaice ya bashi amsa.

“Duk da bansan abunda ke damunshi ba, amma idan har mutunne ya rikida hakan na
nufin aljanune atare dashi ko”?
Ɗaga mashi kai owais Yai”haka muke tsammani”
Hateem Ya numfasa kafin Yace”Inason ganinshi idan yadawo suffarshi ta ainahi,
sannan Yakamata a kira sheikh imam ya duba shi, ina da tabbacin zai Iya taimaka
mashi”
Amsa mashi yai da toh, daga haka sukayi sallama owais ya fuce daga falon.
Bayan tafiyar owais, su Hateem suka raka baba obie bedroom dinshi, babu yadda
basuyi dashi ba akan ya kwanta ya runtsa amma Yaƙiya gani yake tamkar macijin zai
faɗo ɗakinshi, duk yabi ya firgice, adole mutun biyu suka tayashi kwana,
Sharafudden da senate lateef, sauran kowa Ya nufi masaukin shi.
Hankalin Hateem Yaƙi kwanciya, Macijin Ya tsaya mashi aranshi, ya ƙwalla fa rai
akan son ganin yaron, ko bayan daya koma Gidanshi dake a estate din, a ɗaki ya
tarar da gimbiya mujeedat, tana faman yin zarya, ta kasa kwanciya saboda rashin
dawowarshi, babu wanda yasan abunda ya faru a gidan baba obie sai wadanda ke zaune
agidan.
Bai sanar da ita komai ba, Saman gadonsu Ya haye ya kwanta yayin da idanuwanshi ke
fuskantar ceilling, tayi mamakin ganin damuwa atattare da mijin nata, har
tambayarshi tayi meke damunshi amma sai yace mata babu komai, bacci yake ji,
ƙoƙarin faranta mashi tayi har saida ta tabbatar ya fara yin bacci tukunna
hankalinta ya kwanta.

*SIR MUBARAK✊*

Babu wanda ya motsa acikinsu, tun da suka ji muryar mutumin daya kira layin jazz,
Jikin kowannansu yai sanyi laƙwas tamkar an zare masu laka, har sun fara danasanin
jahilin bugun da sir mubarak yaiwa jazz domin kuwa sun tabbatar sune sukayi
kuskuren yanke hukunci batare da sun fara bincikarshi ba.
Yarinyar dake a zaune dirshan idanuwanta sun kaɗa jawur yayin da hannuwanta ke
asaman fuskar jazz.

kafin Sir mubarak Yai ƙwaƙƙwaran motsi, Muryoyin yaran dake tunkaro ɗakin Ya
karaɗe kunnuwan sojojin
Kusan atare suka ɗago suna kallon baƙin ƙofar shigowa ɗakin.

Matasan ƴan mata ne kowaccensu sanye cikin rigunan bacci, babu huluna akansu sai
zallar sumar kansu mai tsayi har gadon bayansu, namiji ɗayane acikinsu shima kayan
baccin ne ajikinshi, fuskokinsu a yamutse sai hamma suke Yi, ga dukkan alamu kukan
ƴar uwarsu ne Ya farkar dasu daga bacci.

“Meya faru da yaya jazz dinmu? Su wanene ku”? Har suna haɗa baki wurin tambayar
sojojin.

Cikin shessheƙar kuka Yarinyar dake ruƙe da dr. Jazz ta kware murya tana kallon
ƴan uwan nata tace”Sun kashe mana shi, bansan su wanene su ba, kawai sun shigo mana
gida sun kama bugunshi”
Fashewa sukayi da kuka kamar gidan mutuwa, da gudu suka nufi inda yarinyar take a
zaune, a kewaye da dr jazz suka zuƙunna Suna ambaton sunanshi tamkar ransu zai
fita.
Ba zato ba tsammani, sojojin suka jiyo muryar babban mutun Yana fadin”meke
faruwane? Su wanene suka shigo gidan”?
Fadowa cikin ɗakin Yayi, daga shi sai short a jikinshi babu riga, yana da
faffaɗan kirji ga ƙirar ƙarfi kamar ɗan dambe, kallon ɗaya zaka yi mashi ka shaida
farar fatane, fatarshi jawur take daga gani bature ne.
Lokacin da yai arba da su sir mubarak a ɗakin Ras yaji gabanshi yai mugun faɗuwa,
adabarbace ya furta”su wanene ku? Meya kawo ku cikin gidan nan”? Kafin wani ya
furta kalma, Mutumin ya wurga idanuwanshi akan yaran dake kuka.
Zaro idonshi waje yai ganin yadda suka raunata jazz, da ƙarfi yace”don ubanku ku
faɗamin su wanene ku? Uban me yayi maku da kukayi mashi wannan bugun? Waye ya turo
ku? Babu alamun tsoro akan idanuwanshi, sai ma dunƙule hannayenshi da yai da niyar
yakai masu hari,
An rasa me magana tsakanin Sir mubarak da su tiger.
Gigitacciyar tsawa ya daka masu Yana fadin”bakuji ina magana ba? Idan har baku
faɗamin ba, daya bayan ɗaya zan salwantar da rayuwarku”
A harzuƙe tiger da Major suka zaro bindigunsu tare da saita shi, maimakon yaji
tsoron bindigar hannunsu sai gani sukayi Ya sanya hannu ya daki ƙirjinshi da ƙarfi
Yana fadin”Kunyi kuskuren shigowa gidan nan, abun hannunku bai isa yasa inji
tsoronku ba, tunda kuka ta6a jazz sai kunyi danasanin haihuwarku da uwarku tayi
acikin duniyarnan, kawai saboda zalunci saiku faɗo gidan mutane kukama bugun mutun
baiyi maku laifin komai ba”? Tamkar mayunwacin zaki haka yake yi masu magana yana
fitar da huci mai ɗumi
Daƙyar sir mubarak Ya iya sarrafa kanshi, muryarshi a haushine ya furta”dan Allah
ka faɗamin wanene kai, Ni da kake gani mahaifin jazz ne, mun shigo gidan nan batare
da sanin shi ba, saboda mu atunaninmu wani mugun abun yake aikatawa.....” a tsanake
sir mubarak Ya kwashe duk abunda Ya faru dangane da zargin da yake yima jazz ya
sanar da matashin saurayi
Lokaci ɗaya sukaga ya sassauta fushin fuskarshi, ga dukkan alamu ya fahimce su.
“Amma baku kyauta mashi ba, shiyasa akace zato zunubi koda ya kasance gaskiya,
jazz dai ba mugu bane, mutumin kirkine fiye da tunaninka, waɗanda yaran kuma dakuka
gani marayune basu da gata aduniyar nan daya wuce Allah sai kuma waɗannan bayin
Allahn da suka taimaki rayuwarsu” yai maganar yana nuna jazz da hannunshi, Yaran
dake sauraron su idanuwansu sunyi luhu luhu sunsha kuka kamar ransu zai fita don ba
ƙaramin ƙaunar jazz suke Yi ba
Cikin karyayyar murya sir mubarak yace”kana nufin Chief owais shine ke kula daku?
ya tambayeshi saboda yaji muryar owais a wayar jazz yana da tabbacin shine Ya kira
layinshi

Jinjina kai mutumin yai”ƙwarai kuwa, a ƙarƙashin kulawarshi muke gaba ɗayanmu, shi
kuma jazz shine likatan daya dauki nauyinshi don kula da marasa lafiyan cikinsu,
Yarinyar nan kuma daka ganshi atare da ita saman gado, bata da koshin lafiya, tana
da ta6in hankali, ga magungunanta can saman drawer da alluran da yake yi mata,
abunda yasa kuka same shi asaman kanta, ni nasan saboda babu mai iya rike mashi
itane, idan dare yayi bayason tashina daga bacci, ni ne nake taimaka mashi wurin
ruƙeta ayi mata allura saboda buge bugen da take Yi, idan har ba a ruƙeta ba baza a
iya yi mata allura ba, tana da ƙarfine, kunyi zargin jazz yana aikata fasiƙanci da
ita bahaka bane abunda na faɗa maku shine gaskiyar zance’
Dafe kai Sir mubarak yai da hannu ɗaya, Wani irin matsanancin ciwon kaine ya
farmashi, su tiger sunyi danasanin zargin jazz da sukayi jikin taƙaura yayi la’asar
“Dan Allah ku taimaka mashi kada ya mutu, har yanzu baidaina bleeding ba” ɗaya
daga cikin matasan yaran ce tayi maganar, fashewa sir mubarak yai da kuka tamkar
ƙaramin yaro, cikin rauni na murya yake fadin”Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’u!
Jazz baka kyautamin ba, meyasa baka sanar dani ba, kabar ni inata zarginka gashi
har nayi maka illah! Yanzu ya zanyi? Me zan faɗama mahaifiyarshi? Matar da ko bacci
bata iyayi idan har bai dawo gidaba saboda ƙaunar da take yi mashi!
Juyawa yai da sauri ya nufi inda yaran suke, bai bi takansu ba, ya sanya
hannayenshi biyu ya cuccu6i Jazz Ya ɗaura shi saman kafadarshi, ya dubi su Tiger da
rinanun idanuwanshi yace”major muje mu kaishi asibiti, kai kuma Tiger ka tsaya
atare da army ku lallashi yaran dan Allah” ya ƙare maganar da sauri ya nufi ƙofar
fita, Major yabi bayanshi bayan ya kar6i key din motar a hannun tiger.

Har sun kusa futa daga dakin, matashiyar nan mai fama da ta6in hankali ta fasa
ƙara hadi da yunkurawa ta mike aguje tabisu tana fadin”mugaye ku dawo mana da ɗan
uwanmu kada ku kashe shi, wayyo Allahna Yaya kana gani zasu gudu dashi “ har takusa
fucewa daga ɗakin, Mutumin Ya damƙo damtsen hannunta, Ya rungumeta a chest dinshi
yaci gaba da lallashinta.
Tiger ne ya soma lallashin ƴan uwanta dake kuka
“Kuyi haƙuri, kuskure mukayi wurin bugunshi, mu ba mugaye bane kamar yadda kukayi
tsammani, mutumin daya dauki jazz mahaifinshine ba wani ba, kuma asibiti zasu
kaishi inda za’a duba lafiyarshi, da zarar yaji sauƙi za’a dawo maku dashi” cikin
shessheƙar kuka suka amsa mashi da toh, banda mahaukaciyar yarinyar daketa ɗura
masu ashar, kamar zata bugesu, mutumin ya ƙankameta ya hana ta kubce mashi.

Kusan rabin awa da tafiyar Sir mubarak, motar Big guy ta shararo da gudu cikin
unguwar, tunkafin ya ƙarasa bakin gate din gabanshi ya fara faɗuwa ganin ƙofar gate
din abude kusan ƙarfe goma sha ɗaya na dare, nan take ranshi ya bashi cewar wani
mummunan abunne ya faru watakil shiyasa lokacin da chief Ya kira wayar jazz yace
mashi ya ɗaga baiyi mashi magana ba!!!!😳😳😳

*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️*

A tsiyace yai parking din motar, tsabar sauri a buɗe yabarta, da gudun gaske ya
nufi cikin gidan batare da jin shakkar komai ba, Shigar shi keda wuya cikin falon
ya soma jiyo sautin kukan yarinyar nan mai fama da ta6in hankali, ta dage sai
zazzaga masifa take yi tana fadin”wallahi saina tona maku asiri ranar lahira,
dukanku sai kun shiga wuta tun da ku ka ta6a min yaya jazz ɗina”. Zuciyarshi ce ta
soma dukan uku uku, zaro bindigarshi dake soke a ƙugunshi yai, cikin sanɗa yake
tafiya yana tunkarar Upstairs, Ya haura second floor, daga ƙofar ɗakin Ya la6e Yana
sauraronsu.

“Ki daina magana mana, bakiji suna bada hakuri ba? Kuskure suka yi wurin
bugunshi, bada son ransu ba”

Jin muryar mutuminsu yasa shi yin wuff Ya afka cikin ɗakin, Jin takun tafiyarshi
ne Ya janyo hankulansu ga dubanshi, kusan atare suka ɗago suna kallon shi.

Nauyayyar ajiyar zuciya big guy ya sauke haɗi da furta”Ya Allah” kafin Ya daura
eyes dinshi akan face din mutumin yace”meke faruwa ne ? Waya ta6a khadeeja take
kuka? ya akai naga yaran duk sun farka daga bacci”?

A ruɗe yake jefa mashi tambayoyin, sam bai lura da Sojojin ba, waɗanda tun da ya
shigo suke dubanshi da mamaki.

da ido mutumin Yai mashi nuni da sojojin”gasu nan, mahaifin Jazz ne yazo tare
dasu, wani abune ya faru na rashin fahimta da yajawo har suka bugi jazz shine take
ta kuka”

A hanzarce ya mayar da dubanshi ga Sojojin, Kusan atare suka buga ƙafa tare da
Sara mashi.

Jinjina kanshi yaɗanyi da mamaki ya furta”Tiger ! Army Boy! Ya akai kukazo gidan
nan?

“Tsautsayi da ƙaddara” acewar Tiger, Army ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar
da Big guy, sai lokacin ya lura da jinin dr jazz daya daskare saman floor, ga kuma
Dressing mirror da daya fashe ta silar buga kan jazz jikinshi, cikin matsanancin
tashin hankali ya furta”Inna lillahi wa’inna ilaihirraji!”

Cikin sanyin murya Army Boy yace”sai haƙuri yalla6ai, rashin sanine, tabbas munyi
kuskure, amma shima jazz din hada laifinshi, Yakamata ace komai zai yi ya sanar da
Sir mubarak a matsayin shi na mahaifinshi bawai yayi gamon kanshi ba, kuma a
yanayin yadda Sir mubarak yake riskarshi Yana yin waya ta sirri, kalaman da yake
furtawa sun yi kamanceceniya dana masu safarar mutane”

Tiger ya ɗaura da cewa”yanzu haka sun tafi asibiti dashi, Muna jira muji daga gare
su, In sha Allah zaiji sauƙi”
Numfasawa big guy yai, jikinshi duk yai sanyi kamar wanda aka zarewa laka, babban
tashin hankalin shi halin da suka jefa jazz basu ta6a tsammanin abun zai jaza mashi
matsala ba.

Tuni idanuwan big guy sun kaɗa jawur tamkar zai fashe da kuka Ya soma yin magana”ba
laifin shi bane, laifinmu ne da muka hanashi yasanar ma kowa dangane da aikin da
muka sanya shi, saboda bama son kowa ya sani”

komawa yai daga gefen gadon dakin Ya zauna, Yana duban Yaran dake raku6e jikin
bango, idanuwansu sunyi luhu luhu.

Mai ta6in hankalin tuni tayi shiru, sai faman zazzare idanuwanta take Yi tana
dubansu.

Tiger yace”shi kanshi Chief Owais bazai ji dadi ba, ranshi zai Iya 6aci amma
nasan zai fahince mu”
Ganin yadda yaran suketa Yin hammar bacci, yasa Big guy yi masu magana”Kuje ku
kwanta, Zuwa gobe idan Jazz Yaji sauƙi zamu dawo maku dashi”

Miƙewa su ka yi a jere suka nufi hanyar fita daga ɗakin jikinsu babu ƙwari,
hankalinsu ba kwance yake ba saboda Jazz dinsu da babu lafiya.

Har sun kusa fita daga ɗakin, Big guy ya kwaɗawa ɗaya daga cikinsu Kira “Hawwa!
zonan, matashiyar daya kira da hawwa ta juyo tana dubanshi, Ki ruƙe hannun khadeeja
ku tafi da ita daki ta kwanta” ya fadi hakanne don yasan su kadaine zasu Iya
control dinta har asamu tayi bacci.

Muryarta ashaƙe take fadin”ni bazan bisu ba, kuma bazan Yi baccin ba, wallahi
sai kun dawo mun da jazz dina”

Lallashinta mutumin dake ruƙe da ita ya somayi”kinsan dai bazanyi maki ƙarya ba
khadeejata, da kaina zan dawo maki dashi, Yanzu dai kije ki kwanta gobe zaki
ganshi, amma idan har bakiyi bacci ba, toh bazan dawo maki dashi ba”
Kwa6e mashi fuska tayi”kayi alƙawari”?
Jinjina mata kai yai”in sha Allah” ta amsa mashi da toh, sakarni inje in kwanta”
sakinta yai, tafiyarta sam babu natsuwa da sauri ta nufi su hawwa ta ruƙe hannunta
acikin nata suka fuce daga ɗakin.

Bayan fitarsu, Big guy ya miƙe ya dubi mutumin”Muna buƙatarka da gaggawa, ka koma
ɗaki ka sanya sutura a jikinka, idan kuma zamu Iya tafiya haka toh,” ya fada yana
nuna gajeran wandon jikin shi da hannu.

Mutumin yace”bari naje na sanya jallabiya, ƙwara aganni da mutuncina” da zolaya


ya faɗa, murmushi sojojin suka saki, fice wa yai daga dakin.

“Yalla6ai wani abu na faruwane”? Tiger ne ya jefa ma Big guy tambaya”kusan haka
sai dai kasan yanayin aikin mu” jinjina kai big guy yai don ya fahimce me yake nufi
Shigowa ɗakin matashin saurayin yai, Jikinshi sanye da jallabiya fara tayi mashi
kyau.
Miƙewa big guy yai tare da kallon su tiger”zamu tafi gidan chief, babu tabbacin
zamu dawo yau, wani muhimmin aikine me girma agaban mu, dan Allah ku kula da yaran,
babu wadataccen tsaro agidan” amsa mashi sukayi da toh, army boy yace”Amma yalla6ai
zaku sanarma chief abunda ya faru tsakanin Jazz da sir mubarak”?
Big guy yace”ya zama dole mu sanar dashi, sai dai ba yanzu ba tunda shi kanshi
hankalin shi ba akwance yake ba, amma idan komai ya lafa zamu fada mashi” gyaɗa kai
army yai”okey, Allah ya tsare hanya”
Amsa mashi yai da ameen, kafin Yaja hannun mutumin suka fito daga gidan, jin ƙarar
tashin motarsu, Yasa Army da tiger suka sauko down, zuwa sukayi bakin gate din
gidan suka datse shi, kafin suka koma palour suka zauna saman sofa suna fuskantar
juna
Army boy yace”tiger ya kaga yaran? Nayi mamakin kyawunsu, Allah yasa oga ya amince
min in samu matar aure acikinsu” tunkan ya ƙare maganar tiger ya wurga mashi kallon
harara”amma baka da hankali, kai waɗannan yaran sunyi maka kama da matan yaku bayi?
Ka manta matsayinka ne? Karfa ka cika zaƙewa, wallahi yazu kaji ka a saman kujerar
lantarki kana kar6ar punishment, ni kaina ƴan matan sun burgeni, gaskiya Oga ya iya
kiwo, fatarsu har ƙyalli take Yi sunji hutu abunsu, yara kamar matan aljanna gashi
har gadon baya, gaskiya dakyar idan iyayensu ƴan nigeria ne”

Ya fada yana yin hamma”ni yanwa ma nake ji, Allah yasa suna da abinci agidan,
nasan ba za’a rasa farfesu ba tunda Chief owais ne ke kula da cinsu nasan za’ayi
harka ta arziƙi, duba mana kitchen dinsu” yai maganar Yana duban Army boy, miƙewa
yai da sauri ya nufi hanyar kitchen, har zai wuce yaci karo da freezer, buɗewa yai
ya leƙa ciki, Kayan marmarine nunannu, da drinks”

washe baki yai yana faman shafa ciki yace”mutumin yaufa kakarmu ta yanke saƙa”
Tiger yace”ba kallo zaka tsaya yi ba, ka shiga kitchen ka dauko tray ka kwaso mana
sauran abincin da suka rage” amsa mashi yai da toh, da sauri ya shiga kitchen.
Jim kaɗan sai gashi ya fito hannunshi ruƙe da katon tray, daga saman tray din
plate biyu ne, ɗaya na fried rice daya kuma na chicken wings, saida ya fara tsayawa
agaban freezer ya buɗe ya dauko masu kayan marmari ya jera gefen plates din ya ƙara
da robobin juice masu sanyi, tiger sai faman haɗiye yawu yake yi,.

Zama su ka yi saman lallausar carpet din falon, kamar masu fama da ciwon yunwa
haka suka dumbuza hannu, sunaci suna fira.

Kamar daga saman suka jiyo muryar matashiyar nan mai fama da ta6in hankali tana
fadin”wayyo Allah, mayu zasu cinye mana abincinmu!” afirgice suka ɗago suna
kallonta, daga can saman bene take zazzaga masu masifa, gashin kanta duk ya rufe
gefe da gefen fuskarta, da gudu ƴar uwarta hawwa ta fito daga ɗaki, Taja hannunta
suka koma ciki, ta rufe kofar ta yadda bazata sake fita ba.

Tiger yace”jarababba, wallahi hartasa gabana ya fadi” ya fada yana dariya


Army yace”ai daga ganinta anyi rashin ji a ƙuruciyarta, kunnuwanta tsaitsaye suke
irin na zomo, gata kyakkyawa da ita” cigaba da cin abincinsu sukayi hankalinsu
kwance, bayan sun kammala army boy ya tattara kayan abincin ya maidasu kitchen, a
saman sofa suka kwanta ga sanyin A.c, sufa ashar kakarsu ta yanke saƙa.

*Daular Alhaji Musa*

*BENAZIR💔*

Tayi nisa acikin baccinta, ba zato ba tsammani taji an shaƙe mata wuyanta, shaƙa
bata wasaba, nan take numfashinta ya soma kiciniyar ɗauke wa, mutsu mutsu ta somayi
yi tana harba ƙafafuwanta, hannayenta biyu ta daura saman wuyanta a ƙoƙarinta nata
kwace kanta daga hannun mutumin dake yunkurin kasheta, wata irin zuface ta soma
tsastsafo mata saman goshinta, zuciyarta tashiga harbawa da ƙarfi da ƙarfi, ta
zazzare idanuwanta cikin duhu bata Iya ganin komai saboda sun kashe ƙwan dakin, duk
yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa, an toshe mata baki babu halin ta ƙwala kira don
azo ataimaketa, hannunta tadinga lalubawa saman mattress cikin sa’a ta cafko
hannun zeenatu dake akwance gefenta, cikin fitar hayyaci take tsunkulinta har
saida zeenatu ta farka tana shessheƙar kuka ta furta”wai.. wanene ke cunkulina”
tunda zeenatu tayi magana, Benazir taji an sakar mata wuyanta, fashewa tayi da
matsanancin kuka, sakamakon raɗaɗin azabar da taji wuyanta nayi mata, a matuƙar
ruɗe zeenatu takai hannu saman bedside drawer ta kunna fitila haskenta ya haskaka
saman gadon, muryarta adabarbarce take fadin”Auntyna meya faru kike kuka? Baki da
lafiya ne”? da rarrafe ta ƙarasa gaban benazir tana duban fuskarta, a lokacin ta
zabura a furgice ta mike zaune tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta biyu ruƙe da
wuyanta, fuskarta tayi sharkaf da zuba, maƙoshinta ya bushe ƙamas, tsananin
rudanine ya kamata, kokwanto ta somayi akan abunda ya faru da ita shin dagaske ne
wani ya shaƙe mata wuyanta ko kuwa mafarkine take yi”?

“Aunty Benazir dina, dan Allah kiyi min magana, meyasa ki yin kuka? Ko kinyi
mafarki ne? Sam takasa buɗe baki tayi ma zeenatu magana sai faman zazzare manyan
idanuwanta take Yi tamkar kwayar zasu faɗo kasa, haƙika ta shaƙi ƙamshin mutuwa.
Dafa kafaɗarta zeenatu tayi”mafarki kikayi aunty? ko wuyanki yana yi maki ciwo
ne” ta fada cikin kulawa da nuna damuwa take duban fuskar benazir.

Dogon numfashi benazir taja yayin da zuciyarta ke harbawa da sauti mai ƙarfi,
tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta, gaba ɗaya ta dabarbace tarasa
gane meke shirin faruwa da ita! Idan mafarki ne tayi an shaƙe mata wuya meyasa take
jin raɗaɗin bayan tafarka daga bacci?

Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya fargar da ita, tana faman haɗiyar yawu idanuwanta
da fargaba take duban zeenatu
Daƙyar ta iya buɗe baki ta yi mata” magana”zeenatu ruwa! Ruwan zan sha”
Tsagaitawa zeenatu tayi da yin kukan jiki na rawa ta sauko daga saman gadon, ta
nufi ƙaramin frigde din ɗakin, ta buɗe ta ɗauko mata bottle water me sanyi ta dawo
ta haura saman gadon ta miƙe ma benazir, yatsun hannunta na kerma ta kar6i roba
ruwan tacire nurfin ta kafa abaki tana sha, maƙoshinta har sauti yake badawa kwat !
kwat!. zeenatu ta natsu tana kallonta, gaba ɗayansu sleeping dress ne ajikinsu.
Bayan ta gama shanye ruwan ta daura bottle din saman drawern gefen gadon,
Ajiyar zuciya tadan sauke, kafin ta dubi zeenatu data kwa6e fuska idanuwanta
sunyi luhu luhu bacci bai isheta ba an tashe ta daga bacci
“Aunty ki faɗamin meke damunki”
Lumshe ido benazir tadanyi kafin ta waresu akan fuskar Zeenatu
“Babu komai ƙanwata, mummunan mafarkine nayi”
Ajiyar zuciya zeenatu tasauke”amma aunty kin tada min hankalina, nayi tsammanin
wani abunne ke damunki ko baki da lafiya, kuma naji kina cunkulina” ta fada tana
nuna mata damtsen hannunta, fatar wurin tayi jawur saboda tsunkulin da benazir tayi
mata kiris ya rage ta fashe.
Jikin benazir ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin irin illar da tayi mata
“Kiyi haƙuri ƙanwata, bansan nayi ba, cikin magagin baccine na cunkule ki”
Murmushi zeenatu tasakar mata”kada ki damu auntyna, na fahimce ki,” ƙaƙalo
murmushi benazir tayi yarinyar ba ƙaramin burgeta take Yi ba, ta damu da ita sosai,
“Ki koma baccinki, kada ki makara a school gobe”
Muryar zeenatu da shagwa6a tace”ae bana zuwa makaranta tunda na kammala secondry
school daddy ya hanani cigaba da karatu, yace wai sai idan nayi aure mijin da zan
aura ya amince min in cigaba da karatu tukunna zani barni”

Jinjina kai benazir tayi har yanzu bata warware daga fargabar abunda ya faru da
ita ba, dauriyace kawai take Yi don kawar mata da damuwar dake atare da ita.

“Idan kina son karatun, meyasa ba zaki fidda miji ba? Duk da ni aganina kinyi
ƙaranta da aure, gaskiya uncle bai kyauta maki ba”
Sunnar dakai ƙasa tayi cikin jin kunyar benazir tace”to ai nima inason nayi auran
kuma ma ina da mijin da zan aura” da zolaya Benazir ta zaro idanuwanta masu dauke
da bacci, da sauri zeenatu ta daura kanta saman pillow tana dariya
Kallon bayanta benazir tayi fuskarta dauke da murmushi,
“Faɗamin sunan saurayin naki inji idan yayi mani”
Muryarta ƙasa ƙasa tace”ki tambayi yaya shureim, yasan shi zai fada maki sunanshi”
benazir bata kawo komai aranta ba, tace”to zan tambayeshi idan Allah yakaimu gobe,
yanzu dai mu kwanta muyi bacci” amsa mata tayi da toh, atare suka kwanta, hankalin
benazir yaƙi kwanciya gani take tamkar abunda ya faru a mafarkinta zai faru gaske,
hakan yasa ta rungume Zeenatu ajikinta, gudun kada aƙara shaƙeta, addu’o’i ta
karanto ta tottofa masu kafin ta lumshe idanuwanta.
Bakomai take tariyowa ba face fuskar tajuddeen, da fuskar baby din data bari
acikin kwamin wanka, tuni hawaye sun wanke fuskarta, taƙosa su dawo ƙasar, fatanta
Allah Yasa taj dinta baiyi aure ba, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.

*Ex-prisoners💔*

Tsoro da fargaba ya hanasu runtsawa, sunyi zazzaune saman dining chairs, ummin
america bata ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, sam takasa samun natsuwa,
jefi jefi takan dago da ido ta dubi su Batul, Har yanzu hanna bata fito daga
ƙarƙashin table ba.

Jemimah tana azaune saman laps din Haris Ta ƙankameshi tuni bacci yajima da yin
awon gaba da ita, abun duniya ya ishi Parveen, Jikinta sai rawar ɗari yake yi
saboda ruwan data watsa ma rigarta, ta jiƙe sharkaf, ga sanyin a.c abu goma da
ashirin, azeeza data suma ta farfado tun bayan da sajeed Ya yayyafa mata ruwa, sai
faman firgita take Yi, macijin tamkar Yana yi masu gizau, ga bacci a idanuwansu sai
dai sun kasa runtsawa, kowa da abunda ke damunshi basu san meke wakana acikin gidan
ba.

“Dan Allah Ku bani mayafinku In lullu6e jikina sanyi nake ji” parveen ce tayi
maganar, babu musu Batul Ta curo mayafinta ta miƙa mata ta sanya hannu ta kar6a ta
lullu6a shi ajikinta.

“Ni nakasa gane meke faruwa! ya akai maciji Ya shigo gidan nan? Ummi ce ta jefa
ma kanta tambayar da bata da amsarta.

Shiru sukayi babu wanda ya tanka mata, babban abunda suke jima fargaba kada ace
mutanan prison ne suka kawo masu hari, shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.

“Ni abunda ke damuna, Danish dinmu da unaisah, bansan awani hali suke aciki ba,
Allah yasa babu abunda ya same su” In a cool voice Batul ta furta maganar.

Tamkar ta tsokano Jemimah, cikin bacci ta fashe da kuka tana sambatun”wayyo Allah
genie dina, dodo zai cinyeta, kuje ku dauko mun ita” da sauri Haris Ya toshe mata
bakinta da tafun hannunshi”kiyi mana shiru, ko so kike dodon Ya jiyo kukanki yazo
wurinmu”?

Ba tare data buɗe idanuwanta ba tace”a’a amma genie fa? Tana can ita da Danish
dodo zai cutar dasu, Ni dai ku ƙyaleni inje wurinsu” ta faɗa tare da buɗe
kumburarrun idanuwanta, da ƙarfin hali tasoma kiciniyar saukowa daga saman laps din
haris don ta fita daga dakin
Ummi tace”kada ka bari ta sauko ka ruƙeta, idan ba haka ba zata iya janyo mana
macijin nan”
Amsa mata yai da toh, ya rurruƙe jemimah ajikinshi.
“Ki kwantar da hankalinki, babu abunda zai samu Unaisah, ai naga mutanan nan
masu baƙaƙen kaya, wata’ƙil ma harsun kashe shi”

Javed ne yayi maganar, jemimah dai taƙi haƙura, tacika masu kunnuwa da shessheƙar
kuka.

Ƙwanƙwasa glass din ƙofar da akayine ya firgitar dasu, arazane suka dago duka a
tunaninsu macijin ne Ya daki glass ɗin, ganin Boss Man yasa suka sauke ajiyar
zuciya, jiki na rawa Ummi ta miƙe ta nufi ƙofar, ta bude mashi bai shigo ba daga
waje Ya tsaya.

“Ina macijin”? Tambayar data fara jefa mashi kenan”


Yayi mamakin ganin yadda jikinta ke rawa, har saida yadan saki murmushi ta cikin
face mask dinshi
“Haba ummi tsoronshi kike ji kema”?
Ta6e baki tadanyi kafin tace”bazaka gane bane, wallahi na firgita macijin yayi
girma dayawa”
“Ki kwantar da hankalinki, ba maciji bane mutunne nasan ko nayi maki bayani ba
lallai ki fahimce ni ba”

Zaro ido waje tayi”what! Kana nufin mutunne? Tayaya haka zata yiwu”? A rude ta
jefa mashi tambayar

“Kodai kana nufin abunda naji unaisa tana faɗi gaskiyane? Na cewa Danish ne ya
zama maciji”!

Jinjina mata kai yai”hakane, gaskiya ta faɗi”

Cikin jin faɗuwar gaba ummi tace”ni dama najima ina zargin yaron nan ba mutun bane,
saboda kyanshi yayi yawa ashe aljanine”

Boss yace”ba aljani bane, mutunne shi kamar kowa, yanzu bani da isasshen lokaci,
zuwa gobe da safe zanyi maki bayani,” tsantsar mamakine Ya kamata.

Muryar Jemimah ce tajanyo hankalinshi ga kallonsu”Boss man ina genie ɗita? Dodon
nan ya cinye min ita ko”
Shiga cikin ɗakin yai, sam sun kasa motsawa suna jin muryarshi sai dai tsoro Ya
hana su je gare shi
Ɗaya bayan ɗaya yake dubansu,
“Dan Allah ku kashe abunnan bamu son ganinshi duk ya firgitar damu” parveen ce
tayi maganar tana dubanshi
Batul tace”boss ina ƴan uwanmu suke ne? Bamusan awani hali suke ciki ba”
Goya hannayensa yai saman ƙirjinshi Yana dubansu
“Basai nayi maku bayani ba, unaisah ce zata faɗa maku komai, abunda nakeso daku
Yanzu ku kwantar da hankulanku, Ku tashi muje na raka ku ɗaki ku kwanta kuyi bacci,
dare yayi sosai kusan ƙarfe goma sha daya da rabi”

“Nidai bazan kwanta bacci ba, sai naga genie dita” acewar jemimah
Azeeza sarkin tsoro tace”bazan Iya kwana aɗaki ba, wannan abun zai Iya faɗowa
ɗakin Ya cutar damu”
Dama yasan da wuya su iya kwantar da hankalinsu.
Kallon Ummi yai”please ki tafi da dasu ɗakinki su kwana kafin zuwa gobe idan komai
ya lafa, sai su koma nasu ɗakin”
“Badamuwa, ku tashi mu tafi” acewar ummi.

Miƙewa sukayi daga saman kujerun, matan dake acikinsu, Batul azeeza da jamimah,
Boss Yace”Ina ƴar uwarku Hannah”?
“Gatanan ƙarƙashin table,” sajeed ne ya faɗa tare da duƙawa ya janyota da ƙyar, ta
ƙudundune kanta kamar kifin gwangwani,.
“Hanna ki tashi ku tafi” daƙyar ta miƙe tsaye zufa duk ta wanke fuskarta,
“Sannu da jiki” boss ne yai mata maganar, sai faman zazzare idanuwanta take Yi.
“Zanje na rakasu ɗaki, Sajeed ka tafi da sauran ƴan uwanku maza” amsa mashi yai
da toh,
Tamkar karsu fita daga dining room din, gani suke kamar macijin zai dawo masu,
badan boss na atare dasu ba dakuwa babu wanda zai Iya fitar dasu saboda tsoratar da
suka Yi, asaman bayanshi Ya goya azeeza, ummi ta dauki jemimah abayanta, Batul ta
ruƙo hannun parveen dana Hannah, Ahaka suka jera suna tafiya har suka ƙarasa ga
second floor, a ƙofar dakin ummi suka dakata dayin tafiyar, ta buɗe kofar suka
shiga daga cikin, bayan boss Ya sauke azeeza daga saman bayanshi yayi masu sallama
ya juya ya fuce.

Sai faman baza ido suke Yi, Yau gasu adakin Ummi, Bedroom ɗinta Ya haɗu kamar na
amarya, an zuba mata kayan alatu.
Ganin ya fuce daga ɗakin Yasa tayi saurin zuwa tayi locking din ƙofar, tabi
windows din dakin ta zugesu, tukunna hankalinta Ya kwanta.
Dubansu tayi sunyi tsaitsaye curko curko suna jiran umarninta
“Parveen ki shiga toilet ki ƙara tsarkake jikinki” amsa mata tayi da toh, a
tsorace ta shiga toilet din.
Kallon jamimah da azeeza tayi”akwai wadda takeyi fitsarin kwance acikin ku”?
Girgiza mata kai sukayi alamar a’a
“Ke fa”? Ta jefa ma batool tambayar
Itama tace a’a,
Gyaɗa kai tayi”okey, amma gadon bazai ishemu ba, Ni ban saba kwana atakure ba,
mutun biyune zasu samu damar hawa gado, Biyu sai su kwana saman carpet” tayi
maganar tana nuna masu carpet din dake a shimfiɗe.

“Ga kuma Sofa wazai kwana asama”? Ta fada tana dubansu


Maƙe kafaɗa jemimah tayi”ni wallahi bazan kwana saman carpet ba, tsoro nake ji,”

“Nima bazan Iya kwana ƙasa ba, dan Allah kibari mu kwana saman gadon mu duka”
Azeeza ce tayi maganar tana marairaice mata fuska don taji tausayinta.

Ta6e baki Ummi tayi”takura ke bana so, na saba kwana ni kadai asaman gado”
Cikin sanyin murya batool tace”ni da parveen zamu kwana saman carpet din, Azeeza
da jemimah sai su kwana saman gadon”
Ummi tace”kinyi kyan kai, haka akeson babba yakasance mai sadaukarwa ga ƙannansa”
ta fada tana sakin murmushin shaƙiyanci.

“Kuje ku kwanto tom and jerry” ruƙo hannun jemimah Aziza tayi suka nufi gado atare
suka haye saman mattress din.

Fitowa parveen tayi daga toilet, duk ta jiƙe jikinta


“Dakata daga nan kada ki 6ata min ɗaki da ruwa, meyasa baki tsane jikinki ba”? da
wulakanci take Yi masu magana.
Shiru parveen tayi batare datace komai ba sai batul ce tace”kiyi hakuri dan Allah,
parveen ki koma toilet ki tsane jikinki, aunty ummi ki taimaka mata da kayan da
zata sanya kafin gobe”
Yamutsa fuska ummi tayi jin abunda batul tace”wato raini yafara shiga tsakanina
daku ko?! Ke ba ki ji kunyar cewa In ara mata kayana ta sanya ba”!
Idanuwan batul tuni sun ciko tab da ƙwalla
“Kiyi haƙuri in na 6ata maki rai” tsoki ummi taja,
Atsawace tace”kai ni dallah kuzo ku kwanta inaso zan kashe hasken ɗakina”
Jikin parveen yai sanyi ga sanyi da take ji, gani suke kamar ummi ta canza masu
kodan saboda sunzo kwana dakinta ne shiyasa take yi masu wulakanci”
“Aunty ummi dan Allah ki kashe mana sanyin ɗakin kodan saboda parveen” harara
ummi ta watsa mata
“Bana iya kwana babu a.c, sai dai kuyi hakuri” ta faɗa tana faman sakin shu’umin
murmushi.
Gyaɗa kai Batul tayi tare da kallon parveen tace
“bari na baki rigata ki sanya, ni saiki bani taki” dariyar shaƙiyanci ummi tasaki
jin abunda batul tace
“Kibarshi batul ke kuma fa”? Idanuwanta acike tab da kwalla ta furta hakan
Murmushin yaƙe batul tasakar mata”kada ki damu dani, zan iya jure sanyin muje
cikin toilet din ki canza rigar”

Komawa cikin toilet din sukayi, Batul ta cire rigarta taba parveen ta sanya ita
kuma ta zura rigar parveen da ruwa ya jiƙeta, ahaka suka fito hannunsu ruƙe dana
juna.
A kishingiɗe suka sami ummi saman gado ta ɗaura kanta saman pillow. Jemimah da
azeeza suna can gefe ɗaya sun rungume junansu bacci tuni yajima dayin awon gaba da
su.

Ko kallon inda take basuyi ba, tabasu mamaki ga uban space a gadon amma ta hana
su kwanciya.

Asaman carpet suka kwanta, sanyi ya fara ta kurama Batul, Jikinta ya hau yin
kakarwa, don mugunta ashe bayan shigarsu toilet ummi ta ƙara gudun A.c din dakin,
tasan dole su nemi alfarmar ta basu bargo su lullu6e, don taji dadin zabga masu
rashin mutunci
Kasa runtsawa batul tayi atakure ta miƙe zaune tana faman ƙanƙame jikinta,
tace”aunty ummi ki taimaka mana da bargo, sanyi muke ji”
Tamkar bata ji me batul tace ba, saima ta runtse idanuwanta kamar mai yin bacci.

Batul tayi tunanin bacci takeyi hakan yasa ta ƙara ɗaga murya tana fadin”Aunty
ummi bargo dan Allah” banza tayi da ita, a ƙarshe sai dai batul ta haƙura, jikinta
nata kakarwa ahaka ta kwanta, sanyi tamkar zaiyi mata illa, bacci ya ƙauracewa
idanuwanta, ita kadaice acikinsu batasamu damar runtsawa ba, parveen tuni ta nutsa
cikin baccinta.
Sai da ummi ta tabbatarwa kanta cewa bacci ya ɗaukesu tukunna ta sauko daga saman
gadonta, leƙen fuskokinsu tadinga yi don taga idon akwai wanda baiyi bacci ba, a
lokacin batul ta runtse idanuwanta, sai tayi tsammanin tayi bacci.
Lalla6awa tayi a hankali ta nufi jikin bango ta kashe switch din ɗakin, kafin ta
dawo ta nufi gaban dressing mirror inda ta ɗaura wayarta ƙirar iphone
Shu’umin murmushine dauke akan fuskarta, wayar ta dauka ta shiga call logs ɗinta
ta dannama wata number kira bugu uku kafin mai wayar ya ɗaga
Muryar babban mutunce ta dako mata sallama.

“Yalla6aina ina da labari mai daɗi agareka”. 😳😳😳😳

The appearance of SALSABEEL😳🔥

On the other hand ƙasaitacciyar muryar mutumin ta furta mata”babu buƙatar ki sanar
dani, na riga da nasan da zuwanki Nigeria”! Cikin nuna isa Ya furta mata hakan.

Yayi matuƙar bata mamaki, muryarta da alamun ruɗi tace”tayaya akai kasan nazo
nigeria? Bayan ni ban faɗa ma kowa ba”!

“Saboda ina kallonki, duk wani motsinki a tafin hannuna yake Ummi”

“Okey, idan har dagaske kana gani na, Yanzu faɗa min wasu kayane na sanya a
jikina”! Ta faɗa yayin da take shafa kirjinta da hannu ɗaya.

Ba zato ba tsammani taji yace”skirt launin yellow, tare da riga white colour sun
yi tighting dinki, sun bayyana zazzafar surar jikinki mai jan hankalina”

Har saida gabanta ya faɗi rass jin ya canka dai dai, tsabar ruɗu kiris Ya rage ta
saki wayar hannunta, a firgice ta juya tana ƴan waige waige don taga ko yana acikin
ɗakin ne! Muryarta adabarbace ta furta”am... ma tayaya akai kasan launin kayan dake
a jikina”?
Sautin wata shu’umar dariyar daya saki ce ta karaɗe kunnuwanta,
“Meyasa kake yi min dariya? Ka amsa min tambayar dana maka”?
“Kin manta dawa kike yin waya? Idan kin manta bari na tuna maki.....” bata bari
ya ambaci ƙarashen zancen ba, tayi hanzarin katse shi da cewa”ni ba wannan na
tambayeka ba...”
Da kakkausar murya ya furta sunanta”Ummi!” amsa mashi tayi da na’am babe.
“Duk duniya babu macen da ta isa ina magana ta katse ni sai ke! Meyasa”?
Farfari tayi da ido tamkar tana agabanshi tace”saboda ka mutu akaina, babu yadda
ka Iya dani, na zame maka ƙarfen ƙafa, mutu karaba takalmin kaza, sannan ni kadaice
macan da zata Iya sarrafa ka cikin sauƙi nake rikatar dakai” ta ƙare maganar tana
cizon lower lip dinta da tongue dinta, cikin jin shauƙin shi.

Duk wannan wayar da take Yi, Batul tana sauraronta, baiwar Allah, jikinta ya gama
sandarewa da sanyi, sai kakarwa takeyi, tuni azababbiyar mura ta rufeta, kasa
jurewa tayi gani take kamar sanyin zai halakar da ita, hakan yasa ta yunkura ta
miƙe cikin duhu ta nufi ƙofar fita daga ɗakin ta fuce ba tare da sanin Ummi ba.

Sautin hucin numfashinshi har ta cikin kunnanta, shiru bai tanka mata ba,
Hakan Yasa tace”Naji sautin numfashinka Ya cika min kunne na, ko jarabar taka ce ta
motsa? gashi bana akusa balle in ɗebe maka kewa”

Muryarshi ƙasa ƙasa ya furta”Ummi, muryarki kaɗai tayarmin da jarabata take Yi,
abuƙace nake dake, Inason ganinki ayanzu ya za’ae”

Shu’umin murmushi tasaki, muryarta da kwarkwasa tace”babu halin ganina, nayi


maka nisa, kayi tunanin zan baka damar ganina cikin sauƙi? Bayan irin wahalar daka
bani? Ka tafi ka barni da kewarka, ba ka damu dani ba, kasa ina kokwanton anya
dagaske kana ƙaunata? Saboda kawai mun samu sa6ani shine ka nesanta kanka dani? Ka
hana rayuwata sukuni.....” bata samu damar ƙare maganar ba, ya katse mata
hanzarinta”bazan iya jurewa ba, nayi kewar jikin ki, nasan ni mai laifine agare
maki amma inaso ki sani kina araina.

Ta6e baki tayi tana sauraron shi


“Ki bani dama, zan gyara kuskura na, adaran nan” dariyar shakiyanci tasaka
mashi”fadamin me zaka yi min”

“ zan kiraki video call, i wanna show u something that will make u happy”

Murmushin gefen fuska tasaki”okey my baby, amma fa kada ka nuna min abunda zai
hanani runtsawa adaren nan” ta ƙare maganar tare da juyawa ta nufi toilet ta bude
kofa ta shige ciki.

*CHIEF OWAIS✊❤*

Babu alamun zai iya runtsawa a daren yau, duba da abubuwan da suka sha mashi kai,
idan har bai shawo kan matsalar ba to kuwa hankalin shi bazai ta6a kwanciya ba,
halin shi ne hakan.

Safa da marwa yake yi a room dinsa, Ya zura hannayensa biyu cikin aljihun short
dinsa, babu riga a jikinshi hakan ya bayyana zazzafar surar ƙirjinshi, jefi jefi
yakan dan wurga eye balls dinsa kan wall clock din dakin domin duba lokaci, akan
kyawawan idanuwanshi ƙarfe 1:30 na dare ta buga, a hankali ya kau da idanuwan daga
kan agogon.

Alert ne Ya shigo wayarshi, a hanzarce Ya nufi wayar tashi dake ajiye saman
bedside drawer, ya duba ta, ƙofar room dinsa ne ake buƙatar shigowa, Unclock button
ya danna, nan take ƙofar ta soma zugewa, agaban dressing mirror Ya tsaya yana jiran
ƙarasowar su.

Big guy ne tare da Mutumin nan, nesa da bayanshi suka tsaya tare da Buga ƙafa
suka sara mashi atare, cikin girmamawa Big guy ya soma yi mashi magana

“Assalamu alaikum Sir Barka, yanzu muka samu damar ƙarasowa gidan, aimin afwa na
6ata lokaci”

Koda big guy yai maganar, basu samu damar ganin fuskarshi ba, saboda Ya juya
masu baya, ta cikin mirror yake dubansu.

“Yalla6ai fatan na same ka lafiya” mutuminne ya furta maganar.

Lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kafin calmly ya furta”barka da zuwa, ina fata Big guy
ya fada maka komai, Dangane da halin da ɗan uwanka ke a ciki”

Jinjina kanshi yai cikin girmamawa yace”eh yalla6ai, ya sanar dani komai, Inaso na
fara ganin shi”

“Okey, Big guy you can take him to the room, but before that....” gently ya
waiwayo baya batare daya kallesu ba.

Ya ɗaura da cewa”Ina so na saurari komai da zaku tattauna”

Amsa mashi yai da okey.

“You Can Go” amsa mashi sukayi da toh, kafin suka juya suka nufi ƙofar fita
dakin.

Bayan fitarsu, hayewa yai saman shimfiɗeɗɗan gadonshi, yayin da yake fuskantar
jigunannan ceilling din room nashi.

Slowly ya daura wayar hannunshi on his broad chest, yadan lumshe sexy eyes
dinshi.

Idan muka koma 6angaren big guy da mutumin, cikin takun sauri suka nufi elevator,
bayan sun shiga tayi sama dasu zuwa second floor ta sauke su, fitowa sukayi daga
ciki, a hanzarce suka nufi bedroom din Danish.

Abakin ƙofar dakin suka dakata dayin tafiyar.

“Ina buƙatar face mask” mutuminne Ya furta maganar.


Kallon shi big guy yai”meyasa? Ko bakasan taga fuskarka ne”

Jinjina kanshi yai alamar eh big guy yace”bazai yiwu ba, dalilin dayasa nace
hakan, yarinyar bata da kwanciyar hankali daga ita har yaron, silar ganinka da
zasuyi shi zaisa suji sauƙin radadin abunda ke damunsu, Ina fata ka fahimce ni”

Gyaɗa kanshi yai”na fahimta ba damuwa mu shiga ciki”

Dafa ƙofar room din dakin big guy yai da tafin hannun shi, a hankali ƙofar ta zuge
kanta, shi yafara shiga kafin mutumin yabi bayanshi, tunkafin su ƙarasa shiga ya
hango abunda ya basu mamaki da al’ajabi, har kallon juna sukayi kafin suka mayar da
dubansu garesu, wato abunda yabasu mamaki ƙarfin halin Unaisah, Ta lullu6esu da
bargo daga ita har Giant snake din, kana Iya hango ƙafarta da jelarsa.

“Ban ta6a ganin ƙauna irin wannan ba, arayuwar mu ta zahiri, ƙarfin halin
unaisah da jarumtakarta ba ƙaramin burgeni suke yi ba” big guy ne ya fada.
Mutumin yace”Ni shaida ne akan ƙaunar dake a tsakaninsu, tamkar anta da
jini ....” bai ƙare maganar ba, big guy yai mashi nuni da abun sauraron daya sanya
a kunnanshi, da sauri Yaja baki yai shiru don ya fahimci abunda yake nufi wato
chief yana sauraronsu ta hanyar earbuds din kunnan big guy.

Abakin gadon suka dakata suna ƙare masu kallo.


Kiran sunanta big guy yai”Unaisah! Muna son yin magana dake” shiru babu alamun
zata farka
Ɗaga murya yai da karfi ya ambaci”Unaisah Angel, ki tashi zamuyi magana”
Har cikin dodon kunnanta kiran ya kai mata, firgigit tafarka tana sambatun
ambaton sunan Danish, saboda ta kwanta dashi aranta, jin shi ajikinta yasa taji
hankalinta Ya kwanta, sai kuma ta fara tunanin wanene ke kiran sunanta, kafin brain
dinta ta tariyo mata muryar mai magana ya kuma cewa”Ni ne Big guy, ki fito daga
cikin bargon muyi magana” ya fada ne don ya lura tafarka duba da yadda bargon da
suka lullu6a yake motsi.

Ta rasa ya zatayi ta raba jikinta daga giant snake din, Ya shige mata sosai, sai
faman jan numfashi take Yi da sauri da sauri.
“Kinyi shiru Unaisa!” muryarta da kasalar bacci ta soma magana

“Ƙoƙari nakeyi in fito, ya rurruƙeni ne”

murmushin gefen fuska mutumin ya saki jin muryar daya daɗe yana kewarta.
Kallon big Guy yai”bari na taimaka mata” clapping hands dinsa yai sau uku, wani
abun mamaki macijin ya farka, Ya warware jikinshi daga nannaɗetan da yai, ya soma
ƙoƙarin yakice bargon don ya fito, hannu mutumin yakai Ya ruƙo ƙarshen bargon ya
yaye shi gaba daya ya jefar dashi gefe ɗaya.

Biji biji Unaisah take dubansu, idanuwanta sun kumbura sunyi mata nauyi bata iya
ganin su dakyau, a kasalance ta miƙe zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, baiwar
Allah gyaran gashin da take ta kaffa kaffa dashi don kada ya tarwatse tuni yafara
fita hayyacinshi.

Abun da ya ɗaure ma Big guy kai, ganin yadda macijin duk yabi ya ruɗe, ƙoƙarin
saukowa yake Yi daga saman gado, kuma ga dukkan alamu wurin mutumin yake son zuwa,
Allah sarki ɗan uwa yaga ɗan uwanshi.

Hawa saman gadon mutumin yayi, agaban giant snake din Ya tsaya, cikin rauni na
murya furta”ko baka furta min ba, nasan halin da kake aciki Danish! Saboda ina jin
raɗaɗin acikin zuciyata, amma kada ka damu, Allah yana atare dakai muma kuma muna
atare dakai, wallahi duk runtsi duk wuya ba za su ta6a cin galaba akanka ba, tunda
har su ka yi kuskuren haɗaka da ƙaddararka wadda tayi silar barinka *GIDAN KURKUKUN
ƘADDARA!!* Tun da ya fara magana Unaisa ta dabarbar ce, tarasa gane a ina ta ta6a
jin muryarnan, sai da yazo ƙarshen maganarshi ya amabaci sunan kurkukun ƙaddara,
tamkar ya buga mata guduma a kirjinta, la66anta na rawa ta soma ambaton
sunanshi”SAL... SABEEL! SALSABEEL! MAFARKI NAKE YI KO GASKE NE KUNNUWANA SUKE JIYO
MUN MURYARKA” amatuƙar ruɗe sai faman ƙoƙarin murza idanuwanta take da yatsun
hannunta duk don ta samu damar ganinshi.

Muryarshi ce ta dakatar da ita daga ambaton sunanshi da take Yi


“Angel! Nine ba mafarki kike yi ba, SALSABEEL ƊINKU NE NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA”
daƙyar ta iya ware idanuwanta akan fuskarshi, kwamtsa duk ta kakkama idanuwanta
saboda kukan da tayi idon ciwo yake mata, sosai ta zazzaresu tana dubanshi tamkar
wadda taga abun tsoro, ruɗani ya hana ta yi magana, lamarin yayi mugun ɗaure mata
kai, ko amafarki bata ta6a tsammanin hakan zata Iya faruwa ba, kamar yadda take
kallonshi haka shima yake kallonta, fuskarshi dauke da murmushi, yayin da
idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, macijin kuwa tuni Ya ɗaura kanshi saman
laps din salsabeel.
Miƙa mata hannu yai alamar tazo gare shi, ta zabura ta nufeshi, haɗi da faɗawa
saman kirjinshi ta ƙanƙameshi, lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma
zuciya.

Big guy dake atsaye yana kallonsu zuciyarshi tuni ta karaya, duk irin dauriyar
shi baisan sa’adda ƙwalla ta cika idonshi ba.

Muryarshi arauna ce ya furta”Sir, are you listening?”

On the other hand, chief owais dake a kwance saman tattausar mattress na gadon
shi, Ya amsa mashi da”Yes, I’m listening.”

Ajiyar zuciya big guy ya sauke, ya fahimci sautin kukan Unaisah ba ƙaramin ta6a
zuciyar chief yai ba, tun daga kan yanayin muryarshi.

Bubbuga bayanta Salsabeel yai da hannun ɗaya cikin sigar lallashi, yayin da ɗayan
hannun nashi yake asaman kan giant snake din”

Tamkar yana ƙara tunzurata, kuka take yi na fitar hayyaci.

Big guy dake amanne da earbuds, muryar Chief ce ta janyo hankalinshi ga


sauraronshi”

“Tell her to stop crying, I don’t want to hear it.(Ka faɗa mata ta daina kuka,
bana son ji”) amsa mashi yai da toh, kafin ya ɗaga murya yace da salsabeel”ka
lallashi ƴar uwarka, tadaina yin Kuka, umarni ne daga chief”
Jinjina mashi kai yai, da karyayyar murya ya ambaci sunanta”Unaisa, Ki daina
kuka, danish baya jin dadi, ya fadamin idan baki daina ba shima zai fara kukan
saboda kina ƙara tayar mashi da hankali” jin wannan maganar yasa tayi saurin haɗiye
kukanta, a hankali ta dago da kanta tana duban fuskar salsabeel, tsananin
tausayinta ne Ya kamashi, kumatunta sunyi jawur, pink lips dinta sunyi suntum dasu,
tasha kuka baiwar Allah.

Cikin shessheƙar kuka take fadin”Sal... Sal... Sabeel, ka fadamin ya akai ka


tsira daga gidan kurkukun ƙaddara? Ina ƴan uwana suke? Ina deeja take da mubeen?
Suma sun rayu ko sun mutu? Inaso nasani, gaba ɗaya na rikice”

Shafa gefen fuskarta yai da hannun shi, Cikin sanyi murya yace”Unaisah, ki kwantar
da hankalinki, yanzu bana acikin natsuwar da zan Iya yi maki bayanin komai, nayi
maki alƙawarin zan fayyace maki komai idan Danish ya dawo mutun, amma fa sai kin
daina yin kuka, kin kuma natsu” jinjina mashi kai tayi alamar zata daina.

“Danish yana yi min magana, yanzu haka” ba ta yi mamakin jin abunda yace ba,
tunawa da cewa shima giant ne, abune mai yiwuwa suyi magana ta sirri acikin
zuciyoyinsu harma su Iya jin juna, big guy ne kadai al’ajabi ya cika shi, tun yana
daga tsaye har yakai ga samun wuri saman sofa din dakin ya zauna yana dubansu
“Ina son jin me yake fada maka” acewar big guy
A lokacin Unaisah ta mayar da kanta saman kirjinshi, ya tallabeta da hannu ɗaya,
zazza6i jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi.
Calmly Salsabeel Ya soma faɗa masu tattaunawar da suke Yi da danish.

“Ya faɗamin bayason unaisah tana yin kuka, Zuciyarshi tana karaya, sannan yana
roƙona akan in taimaka mashi ya rikiɗa ya koma mutum baya son ganinshi a suffar
maciji, yana jin ƙyanƙyamin kanshi, yana acikin mawuyacin hali na ƙunci da raɗaɗi,
idan har ya ɗauki tsawon lokaci bai dawo mutum ba Giant’s heart dinshi zata motsa
ne, idan kuwa ta motsa gaba ɗayanmu zai Iya cutar damu, saboda awannan matakin babu
wanda zai Iya sarrafa shi har ita unaisah” hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba
jin abunda salsabeel yake fadi, ita azatonta giant’s heart dinshi ne ya motsa
shiyasa har ya iya rikiɗa ashe ba zuciyar bace ta motsa.
Ba ita ba hatta big guy ya ɗan girgiza da jin kalaman salsabeel, har saida ya
daura eye balls dinshi akan macijin dake a nannaɗe saman gadon har yanzu bai ɗago
da kanshi daya daura saman laps din salsabeel.

Cigaba da yin magana yayi”danish yana acikin damuwa, ina jin shessheƙar
kukanshi, roƙona yake yi akan mu taimaka mashi ya canza halittarshi ya gaza rikiɗa
baisan ya zaiyi ba, bayason ƴan uwanshi su guje shi, idan kowa ya ƙyamace kamar
yadda ya ƙyamaci kanshi hakan zai yi silar motsawar giant’s heart dinshi kuma idan
ta motsa zai nesanta kanshi da kowa saboda baya son ya cutar da mu, zai koma inda
yasan baza a ƙyamace shi ba, yana nufin tushen shi gidan kurkukun ƙaddara....”
tunkan salsabeel Ya ƙare maganar, Unaisah ta tari numfashinshi “A’a danish, ka
daina fadin zamu ƙyamace ka, Ni yanzu ma nafara ƙaunarka saboda ina tausayin
rayuwarka nasan cewa bayin kanka bane, mugayan mutanan can ne suka assasa faruwar
hakan duk don ka koma garesu, sunyi maka hakanne don mutane su guje ka kai kuma
kaji ka ƙyamaci kanka saboda sunsan ta wannan hanyarne kadai zakaje gare su, Ni
kuma wallahi bazan ta6a bari hakan ta faru ba, Yanzu nafara sonka, Danish ba maciji
ba, kowace irin halitta zaka koma a duniyar nan ina atare dakai, har abada har
ƙarshen numfashina, kai koda ace zaka dinga cutar danine bazan rabu dakai ba, sai
inda ƙarfina ya ƙare, akanka babu gudu babu ja da baya wallahi bazan barka
ba.......” kukane yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar.

Macijin yana sauraron duk abunda take cewa, ya ɗago da kanshi daga saman laps din
salsabeel, mitsi mitsin idanuwanshi na fuskantarta.

Big guy bazai Iya jurar tausayinsu da yake ji ba, Jikinshi yai sanyi laƙwas kamar
wanda aka zare ma laka.

Duk abunda ke faru Chief Owais Yana sauraronsu, yayin da yake a kwance cikin
bedroom dinshi saman gadonshi, Muryar unaisah ta cika mashi kunnuwanshi tamkar
agabanshi take Yin kukan, A hankali ya dauki wayarsa daya daura saman broad chest
dinshi ya dawo da ita saitin kunnanshi, don yaji dadin sauraronta dakyau.

Shafa sumar kanta Salsabeel yai da hannunshi”Ki daina kuka yace min in fada maki
bayaso” da sauri ta hadiye kukanta tana fadin”toh na daina, bazan ƙara ba my Man,”
ta faɗa tana kallon macijin har girgiza mata kai yake yi, batasa sa’adda tasaki
murmushi ba, ta fahimci lallashinta yake yi.

“Abun da Unaisah ta faɗi gaskiya ne, tsammaninmu yazo ɗaya, azzaluman kurkukun
ƙaddara ne suke sarrafashi ta ƙarfi da yaji bada son ranshi ba, kuma sunayi mashi
hakanne don mutane su ƙyamace shi kowa ya gujeshi, shi kuma zaiji ya tsani kanshi
saboda ƙyarar da mutane suke yi mashi, daga haka zai fara tunanin komawa prison
wannan shine abunda suke ƙoƙarin yi”

Tun da yafara magana big guy yake jinjina kanshi alamar gamsuwa da jawabin shi,
Muryar chief ce ta sa shi dakatawa yana sauraronshi, babu mai iya jin voice dinshi
sai shi da yasanya abun sauraron akunne.

Cikin harshen turance yace “Ka faɗa mashi, muna atare dashi, bazamu ta6a rabuwa
dashi ba har iya ƙarshen numfashinmu, babu wanda zai ƙyamace shi, duk runtsi zamu
kasance atare dashi don mu bashi ƙwarin gwiwa kuma zamu tallafa masa don ganin mun
raba shi da miyagun dake atare dashi, in sha Allah komai yazo ƙarshe ya kwantar da
hankalinshi”

Jinjina kai big guy yai haƙiƙa yaji daɗin kalaman Chief owais, magana yasoma yi
masu”chief yace in isar mashi da sakonshi zuwa ga Danish .....” mayar da hankalin
sukayi akanshi suna sauraronshi, a tsanake ya faɗa masu abunda chief yace.

Wani irin farin cikine ya lullu6e Unaisah, har cikin ranta taji daɗin kalaman shi
duk da batasan wanene shi ba, ba ta ta6a ganin fuskarshi ba, ko ɗazu da taji an
dauketa lokacin data lullu6e Danish da bazar rigarta batasan wanene ya dauketa ba
saboda bata acikin hayyacinta, idanuwanta sun makance.

“Wanene chief? Yaushe ya faɗa maka sakon”? Ta jefa ma Big guy tambayar yayin da
take dubanshi.

Nuna mata earbuds din kunnanshi yai da yatsan hannun shi, nan take ta gane abun
jin magana ne a ear dinshi tanan suke yin communicating da shi.

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke muryarta adisashe ta furta”idan na samu natsuwa


zaka kaini wurinshi muyi mashi godiya” Big guy yace”a’a shi ba’ayi mashi godiya,
sai dai idan kinason ganinshi zan nema maki izni daga gare shi, amsa mashi tayi da
toh inaso”

Kallon salsabeel Yai”menene mafita? Muna son musan wani hali yake aciki” kafin
ya bashi amsa unaisa tayi saurin cewa”nayi magana da boss man, na fada mashi inda
na ajiye wasiƙar adreshin gidanku daka bani, inda zamu samu ruwan zam zam din”

Fuskarshi da matsanancin damuwa yace”ai babu zamzam din nan! Tun lokacin da kuka
faɗa hannun sojin america suka damƙa case dinku hannun hukumar Isod, nasan da
zamanku, munyi ƙoƙarin samu ruwan zam zam saboda gudun kada giant’s heart dinsa ta
motsa, sai dai kash lokacin da muka je gidanmu na kaduna tare da jami’an isod bamu
samu komai ba, Gidan ma an canza mashi kamanni, magada ne suka koma da zama
cikinshi, su kansu da mukaje basu san Wanene ni ba, munyi ƙoƙarin yi masu bayani
amma sai suka fada mana cewa babu komai na habibullah dayai saura agidan....” aruɗe
Unaisah tace”ya zamuyi yanzu”? Ta faɗa tana zazzare idanuwanta.
Salsabeel yace”akwai hanyoyi da dama, da zamu Iya samun ruwan zam zam sai dai
bamusan wasu irin addu’o’ine ko ayoyin alƙur’ani ake amfani dasu ba wurin tofe
ruwan ba” ya faɗa yana dubanta.

“da za’a samu babban malamin addini kamar mahaifina habibullah ina da tabbacin
zai iya taimaka mashi”

Shiru suka ɗanyi suna kallon kallo atsakanin Salsabeel da Unaisah, ga macijin
yayi kwance saman jikinshi daya nannaɗe.

Chief Owais dake a kwance saman bed matress dinsa Yana sauraronsu, ƙarar shigowar
message ce ta janyo hankalinshi ga buɗe eyes dinshi, phone dinsa Ya ɗago da ita
yana duban screen din.

Text message ne aka turo mashi, yayi mamakin ganin saƙon Uncle dinsa, A irin
wannan lokacin ƙarfe biyu da rabi na dare, hakan na nufin bai runtsa ba.

Karanta text message din Ya soma yi acikin zuciyarshi.

_”My son, I can’t sleep because of that child, I don’t know why I’m so worried
about him. Please help me. I want to see him before I go back to Canada next week.
na jaraba kiran layin Sheikh imam munyi magana dashi ashe baya kasar ya tafi sudan,
na nemi alfarmar inason ganinshi da gaggawa, yace min in sha Allah zai dawo ƙasar a
gobe, saƙo daga Prime minister Hateem Obinna_

Bayan kammala karanta message din, Owais Yai mashi reply kamar haka

_”Nima ban runtsa ba kawuna, saboda yaron, ƙoƙarin da muke Yi kenan don ganin
mun taimaka mashi ya canza halittarshi zuwa ta suffar mutane, amma inaso ka kwantar
da hankalinka ka yi bacci, in sha Allah zaka haɗu dashi kafin komawarka kanada, har
ma kuci abinci atare”_
Tura mashi sakon yai, within minutes saiga wani sakon daga prime minister

_thank u, sai mun hadu gobe da wuri zan shigo gidan naka idan sheikh iman ya
ƙaraso_

Lumshe ido owais yai, A hankali ya furta sunan big guy, on the other hand big
guy ya amsa mashi da na’am yalla6ai”

“Sako ya shigo min daga Uncle Hateem, Zuwa gobe da safe Sheikh Imam zaizo
Nigeria, yayi tafiya ne zuwa sudan, ka yi ma brother din yaron nan magana ya
tambaye shi idan yana jin yunwa ya fadi me zai iya ci akawo mashi” amsa mashi yai
da toh.
Ya mayar da dubanshi ga su salsabeel”tun da yana jin maganarka ka tambayar mana
shi me zai Iya ci akawo mashi, sannan pls kace mashi ya kwantar da hankalinshi zuwa
gobe insha Allah sheik imam zai shigo Nigeria, shahararran malamin addinine muna da
tabbacin zai Iya taimaka mashi”

Gyaɗa kai salsabeel yai”ay yana sauraronka, Yanzu haka magana yake yi min.

“Meyasa kuka harbe shi? Duk da harsashin bai fasa jikinshi ba yayi mashi illah
saboda babu kakin giant a jikinshi”

Hankalin Unaisah dana Big guy ya tashi matuƙar, muryarta na rawa ta furta”meya
faru dashi? Yaji ciwo ajikin shi”
“Bazan Iya sani ba, sai ya dawo suffarshi ta mutane tukunna zamu ga illar da yayi
mashi, sannan ya fadamin yana son kayan marmari su kadai yake sha’awar sha”

Damuwace ƙarara akan fuskar Angel”meyasa bazai Iya cin abinci ba”? Ta fada tana
duban salsabeel.

“A halin yanzu Danish dinki, ba mutun bane Giant snake nake, bazai Iya cin kalar
abincin mu ba, har sai ya dawo cikakken mutun.

Kwa6e fuska tayi tana duban kan macijin, har yanzu bai dagoba tunda ya kwantar da
kanshi saman jikinshi daya nannaɗe.

Miƙewa tsaye big guy yai”ka zauna atare dasu, zan je na kawo mashi kayan
marmarin” amsa mashi salsabeel yayi da toh.

Bayan fitar big guy, ta ƙura ma salsabeel ido, har yanzu mamakin ganinshi take yi,
abubuwa dayawa sun cunkushe mata brain dinta, tana son jin ya akai ya tsira daga
kurkukun ƙaddara? Shin ya sauran ƴan uwansu suka ƙare sun mutu ko sun rayu? Tayaya
Akai Ya haɗu da jami’an da suke kula dasu? Ko dai dama shima jami’insu ne!? ta
ɗaura mashi alamar tambaya, tadai haƙura ne har zuwa time din da danish zai rikiɗa
ya dawo mutun donjin amsar tambayoyinta, kamar yadda take kallon Salsabeel haka
shima yake kallonta, yayi kewarsu sosai, kuma yaji dadin ganinsu, da ransu da
lafiyarsu, bakomai yake tunawa ba face ranar daya fara haduwa da ita har yakaita
dakin da suka tattauna, da kuma ranar da ya ceci rayuwarta lokacin da matsafa
sukayi mata wanka da jini, ranar da ta azabtu ta galabaita, Allah kenan mai yadda
yaso mai jujjuya al’amurra, yanzu tamkar ba’ayi ba, tayi haske abunta gwanin kyau
har girma ta ƙara mashi akan yadda suka yi rabuwar ƙarshe a kurkuku.

Murmushi yasakar mata, itama ta mayar mashi da martanin murmushin, ya fahimci


aƙagare take da son jin labarin ƴan uwanta daga gare shi.

*PRISONERS✍️*

Tun bayan fitowar Batul daga ɗakin Ummin america, a tsakar dare ta nufi down stair,
baiwar Allah tana tafiya jikinta na kakarwa, hatta haƙoranta kerma sukeyi suna
hadewa jikin juna, tsoro take ji ita kaɗai kamar aljana, sai faman firgita take yi
gani take yi kamar macijin zai kawo mata hari.

Daƙyar take iya taka ƙafarta saman floor din falo, ga wani azababban tari daya
farmata.

Sam ba ta ji takun tafiyar mutum ba, saboda hankalinta ba akwance yake ba, sai
ƴan waige waige take yi tana faman hadiyar yawu.

Yayi mamakin ganin ɗaya daga cikin yaran tana yawo a tsakar dare, babu mayafi a
jikinta, ƙura mata ido yai a ƙoƙarinshi naya gano wacece acikinsu, ya rasa gane
batul ce ko Unaisah, saboda launin gashinsu kala ɗaya ne ga kuma nannaɗewar sumar
kan nasu daya kasance iri ɗaya, zuciyarshi ce ta raya mashi cewa Unaisah tana adaki
fa ya barota tare da salsabeel wannan ba ita bace sai dai ko ƴar uwarta ce Batul.

Da ƙarfi ya ambaci sunanta”Batul” rass taji gabanta Ya faɗi, a firgice ta waiwayo


don ganin wanene, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar big guy dake sanye cikin
face mask,l.

Tsabar tsoro da ruɗu yasa ta zabura zata watsa da gudu, sai dai kafin tayi hakan
yai saurin haura ƙafa ya damƙo damtsen hannunta ya janyota zuwa jikin shi, ƙanƙame
shi tayi atsorace ga tari da take yi.

Lamarin ya ɗaure mashi kai, ɗago da kanta yai daga saman ƙirjinshi ya furta”ke!
Daga ina kike? Ya akai kika fito daga ɗaki”?
Daƙyar ta Iya buɗe baki tace”sanyi nake ji babu bargo shine na fito zani ɗaki in
ɗauko”
“Awani ɗaki kike”?
“Ɗakin aunty ummi, boss man ne yace muje can mu kwana, saboda munajin tsoron kwana
ana mu dakin”

“Meyasa baki tambayeta ta baki bargo ba”?


A tsoroce take yi mashi magana”tayi bacci ne, kafin ta kwanta ma saida nace ta
taimaka ma parveen da kaya ta sanya saboda tayi ma nata fitsari sunjiƙe sharkaf
amma taƙi bata sai dai ni na cire nawa muka yi musanya ta bani nata, kuma ɗakinta
sanyi sosai”
Tunda tafara magana Big guy yake jinjina kanshi, ga dukkan alamu ya fusata matuƙa,
bashi ba hatta chief owais dake acan room dinsa yana sauraron maganganunsu.

Ruƙo hannun Batul yayi acikin nashi ya juya da ita suka nufi ɗakin.

A lokacin Ummin america tana ƙoƙarin fitowa daga cikin toilet, ta gama sheƙe
ayarta da gardin daya kirata awaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, zura
ƙafarta keda wuya hasken ɗakinta Ya kama, a firgice takai idanuwanta kan masu
shigowa ciki, tunda tayi arba da big guy tare da batul gabanta yai mugun faɗuwa.

Wani irin kallon tuhuma yake jefa mata, ranshi amatuƙar 6ace ya soma magana.

“Ke baki da hankaline? Kin ajiye yara aɗaki kin kure masu sanyin A.c ? Idan
ƴa’ƴankine na cikinki zaki Iya yi masu haka”?

Muryarta adabarbarce tace”am..ba haka bane ni ai bansan basu iya jure sanyin A.c
din ba, na saba kwana.....” bata ƙare maganar ba, Ya daka mata tsawar data firgitar
da ita, sakin hannun batul yai ya matsa kusa da ita, abunda wani ɗa namiji bai ta6a
gigin yi mata ba, da yatsan hannunshi ya nuna ta”ki shiga taitayinki, This is the
last time I’ll warn you. Don’t be reckless in your work. We don’t accept mistakes,
koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara maimaita laifin nan” yana huci ya faɗa
“Yarinya harta fara mura tana tari! Ke ko ajikinki ai nayi tunanin zanzo na
sameki kina bacci ashe idonki biyu hakan na nufin da gangan kika kure sanyin A.c
din dakinki, Ke bari kiji bana so gobe da safe inji yarinyar nan tana yin mura, ki
san yadda zakiyi ta dawo daidai, bama itaba hatta sauran ƴan uwanta kada ki bari
ɗaya daga cikinsu ya tashi da mura, idan ba haka ba zaki fuskanci hukunci mai
tsanani daga hannun chief.. “ hankalin ummin america ba ƙaramin tashi yai ba, duk
tabi ta susuce musamman daya ambaci sunan owais, muryarta na rawa take fadin”na
kar6i laifina bazan ƙaraba, kuma aini bansan sanyin zaiyi masu illa ba...” bai bari
ta ƙare maganar ba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu”bana sonji, kawai
kiyi abunda ya dace don ki ceci kanki, nabarki lafiya” afusace ya juya zai bar
dakin har ya kusa fita karaf idanuwanshi suka sauka akan parveen dake kwance saman
carpet tana yin bacci, Arude ummi ta furta”yanzu zan maida ta saman gado, bansan ya
akai ta faɗo ƙasa ba” wani ɗan iskan kallo big guy ya watsa mata.

Kafin ya maida dubanshi ga batul”ke ina yar uwarku take? ya akai naga ku huɗune?
Where’s hannah”!

Sai daya ambaci hakan batul ta tuna da babu hanna acikinsu, waige waige ta soma yi
jikinta na rawa tace”bansan a ina take ba, tare da ita muka nufo dakin aunty ummi,
ni na ruƙo hannunsu ita da Parveen bansan ta kufce min ba, dama aruɗe take”

Gyaɗa kanshi yai”okey, wuce kije ki kwanta, zanje na nemota” ya faɗa tare da
juyawa ya kalli ummi dake ta rawar jiki”ina ƙara jaddada maki kada ki bari yaran
nan su wayi gari babu lafiya, idan kunne yaji jiki ya tsira” yana fadin hakan ya
haura ƙafa yabar ɗakin.
Fitar shi keda wuya, Ummi ta ɗaure fuskarta tamau babu annuri, ranta ya 6aci
matuƙa, hankalin batul ba ƙaramin tashi yai ba ganin tana tunkarota, girgiza kai
tadinga yi tana nufar bango harta kure mashi,
“Dan Allah kada ki ta6ani, bani da lafiya...”daƙyar ta furta maganar,
“Ni ki ka kai ƙarana a wurinsu? Yaushe kika fita daga dakin munafukar banza,
harni zakija ma bala’i ina zaman zaman lafiyana? Kinsan wacece ni? Don ubanki!

Girgiza kai batul tayi tuni hawaye sun wankan fuskarta”aunty ummi kiyi hakuri
bazan ƙaraba, dan Allah kada ki ta6ani”
Tsawa ta daka mata”kashe ki zanyi, kinyi kuskura batul da kika gaya mashi abunda
ya faru tsakanina daku, wallahi sai kinyi danasanin sanina da kikayi, don kuwa daga
rana irinta yau bazaki ƙara dariya ba zan ƙuntata maki har sai kinji kin tsani
kanki”

Fashewa batul tayi da kuka mai tsuma zuciya, saboda rashin imani ummi ta sanya
hannu ta shaƙi wuyanta tamkar zata kashe ta,
“Jibarki dallah, jahila dake, bakisan komai ba sai cin abinci da bacci, ni ban
ta6a ganin daƙiƙiya ba irinki”

“Batul ! Batul! Meyasa kike kuka”? Jin muryar Parveen yasa ummi yin saurin
sakin wuyan batul, jiki ba ƙwari ta sulale ƙasa tana cigaba da yin kuka

“Kiyi min shiru idan kika bari wani yaji wallahi saina naƙasa ki wawuya” da sauri
batul ta haɗiye kukanta, baiwar Allah hada sanya hannu ta share hawayen fuskarta.
Shu’umin murmushi tasaki kafin ta juya tana kallon parveen data farka tana faman
mutsustsuke idanuwanta
“Ke tashi ki koma saman gado ki kwanta” muryar ummi ce ta fargar da Parveen ta
ware idanuwanta sosai akan fuskokinsu
Muryarta da kasalar bacci tace”batul make faruwa? Meyasa kika zauna a ƙasa”? Tai
maganar tana kokarin miƙewa da niyar taje wurin Batul, ummi ta dakatar da ita”cewa
nayi kije ki kwanta saman gado, babu abunda ya sameta, kaya zan bata ta sanya
ajikinta” jiki asanyaye parveen ta nufi gadon donta kwanta sai dai hankalinta bai
kwanta ba da yanayin data riski batul
“Parveen ki kwanta kiyi bacci, lafiyata ƙalau, yanzu aunty ummi zata bani kaya in
canza na jikina sai inzo mu kwanta a gadon” ajiyar zuciya parveen ta sauke jin
batul tayi mata magana, hayewa tayi saman gadon ta kwanta batare data rufe
idanuwantaba.
Ta6e baki ummi tayi tare da mayar da dubanta kan Batul, badan taso ba
tace”shashasha, Ki jirani in dauko miki kayan” cikin sanyin murya batul tace”toh”
Wuce wa tayi cikin ɗakin can inda katafaren closet dinta yake, ta bude ta dauko
jibgegiyar sweater tare da dogon wando, ta haɗo da duvet, ta nannaɗosu ta dawo inda
batul take a zaune ta wurga mata su saman jikinta
“Salon kuma kiyi min ƙazanta, ni bana sharing kaya da wani don yazamarnin dolene”
ta faɗa tare da juyawa ta nufi gaban mirror inda ta daura A.c remote ta kashe ta
gaba daya, ta kunna masu room heater, duk don saboda gudun kada gobe aji basu
lafiya, shiyasa tayi hakan.
Miƙewa batul tayi hannunta ruke da sweater din, ta zame hannun doguwar rigar
jikinta, da dabara ta zura sweater din, tayi mata girma, haka wandonma yayi mata
faɗi, ahaka ta sanya su, kafin ta cire rigar jikinta, anan ƙasa tabarta, ta nufi
saman gadon ta haye gefen parveen ta kwanta, ta lullu6e masu bargon su dukansu,
kafin ta rungume parveen a jikinta, duk don ta samu sauƙin raɗaɗin da take ji, ta
tsorata da ummi kalaman da tayi mata sun tsaya mata arai, fargabanta kada ta kashe
ta, tuni idanuwanta sun cicciko da ƙwalla
Cikin muryar raɗa parveen take yi mata magaba”batul tayi maki wani abu ko? Ni naji
ajikina” daƙyar ta iya furta”kiyi shiru parveen kada tajimu, ni batayi min komai
ba, bana jin daɗin jikinane”
Sautin kuskus din da suke yi ne yaja hankalin ummi ga kallon bargon da suka
lullu6a dashi atsawa tace”kada in kuskura in ƙarajin maganarki! Ko tari bana sonji”
tsit sukayi shiru suna faman ƙanƙame junansu .........

*Daga Alƙalamin Boss Bature✍️*

Idan muka koma 6angaren Hajiya saratu data garƙame kanta acikin toilet, tsoro da
fargaba sun hana ta sukuni, ta haɗa uban gumi zufa ta ko’ina take tsastsafo mata,
ga wani takurarran bacci daya addabi idanuwanta, ta rasa ya za ta yi, ta kasa tsaye
takasa zaune, sai zarya take yi acikin toilet, jin shiru tsit babu sautin komai
daga waje hakan yasa tayi tsammanin ko dai jami’an sun kashe macijin ne, cikin
sanɗa take yin tafiya tana tunkarar toilet door, ta ruƙo handle din ƙofar ta
buɗeta, shigowa ɗaki tayi ta nufi wayarta dake ajiye saman bedside drawer takai
hannu ta ɗauke ta tana ƴa waige waige duk tabi ta ruɗe.

Layin pravin ta danna ma kira, kusan sau uku bai ɗaga ba, hankalinta ashe take
fadin”pravin ka ɗaga kirana mana”

Sake kiran layin tayi, a lokacin da kiran ya shigo mashi yana a kwance saman
shimfiɗeɗɗan gadon hajjaty, sleeping dress ne ajikinta, shi kuma shorts ne babu
riga, ya rungumeta a kirjinshi, sun manne ma juna, duvet din daya lullu6a masu iya
saitin kafaɗunsu ya tsaya.

Bacci ya ƙaura ce ma idanuwan hajjaty, tun da tayi tozali da narkekan macijin nan,
lallashinta yake yi duk don ya samu ta kwantar da hankalinta.

“Pravin wayarka fa tana ringing yakamata ka duba me kiranka”

“Nasan wa ke kira na, bai wuci hajiya saratu bace, ta gama ci min mutunci shine
yanzu take kirana saboda ta tsorata da ganin maciji, wallahi ba zan je ba, nafi so
taji a jikin ta”

Muryar hajjaty ƙasa ƙasa tamkar me yi mashi raɗa ta furta”please, matarka ce,
yakamata kana darajata”

“Ni ma ai batasan darajata ba, saratu bata girmamani, tayi min gori ta gaya min
maganganun da suka ƙona min rai, sauƙin ma ba ita ka ɗai bace Ina dake”

Lumshe mashi ido hajjaty tayi,


Yaci gaba da cewa”kina ƙaunata tsakani da Allah, baki ta6a guduna ba, kin rabu da
kowa naki kin biyoni Nigeria, a zaman da mukayi dake ni baki ta6a yi min laifi
ba...” ƙayataccen murmushi tasakar mashi.

“Ina fata kai ma ba zaka ta6a guduna ba, Kuma ba zaka ta6a yi min laifi ba, pravin
bani da kowa a halin yanzu Allah ne gatana sai kuma kai, dan Allah ka ruƙe min
amana kada ka aikata abun da zaiyi silar rabuwar mu, ka ji tsoron Allah a dukkan
lamuranka na rayuwa, idan kana tunawa da mutuwa zaka ƙara jin tsoron Allah, bana so
wata rana muyi abun da zamu yi danasani arayuwarmu...”

Bai bari ta ƙare maganar ba yai hanzarin katse ta”my woman, bansan yaushe kika fara
yin wa’azi ba, idan ban manta ba, Ni ne na koya maki alwala ko”

Dariya ta saki jin abunda pravin yace, kafin ta ƙara cewa wani abu ya rigata
fadin”muyi bacci please dare yana ƙara nutsawa” da shagwa6a hajjaty tace”ni dai ka
tafi ɗakin matar ka, ita yakamata ace kana atare da ita bani ba”

“Bana so in bar ki ne saboda na lura haryanzu jikin ki bai daina kerma ba”

“Amma itama saratun ai tsoron take ji, tana buƙatarka agefenta, pls ka tafi
wajenta, Ni nafiso kana kamanta adalci a tsakanin...” bai bari ta ƙare maganar ba,
yai saurin haɗe bakinsu, ya zura hannayenshi biyu cikin rigar baccin jikinta,
sarrafata ya soma yi cikin ƙanƙanin lokaci ya fara caza mata kai, yayi mata hakanne
don ya mantar da ita zancen tafiyar da take yi mashi, kuma yaci galaba akanta, bai
rabu da ita ba har saida yaji ta fara yin bacci tukunna ya ƙanƙameta.

Phone dinsa sai ringing take yi, tana daga can gefe daya saman mattress din, a
hankali ya raba jikinsa daga nata.

Ya laluba hannu ya damƙo wayar, murmushin mugunta ya saki kafin ya ɗaga kiran.

Ko sallama babu hajiya saratu tace”pravin ina ka shiga? Ina ta kira baka picking!
Ba zaka dawo daki ka kwanta ba ne”?

Tun daga kan muryarta ya fahimci babu natsuwa atare da ita


“Me zan dawo nayi maki? Ni da bani da amfani awajenki”?
Muryarta tamkar zata fashe mashi da kuka tace’kaga ni ba wannan na tambayeka ba,
ina son ganinka ka, pravin, hankalina ba akwance yake ba, nasan kaga abunda ya faru
ɗazu”

Tuntsirewa yayi da dariyar mugunta, ran hajiya saratu ya 6aci matuƙar masifa ta
soma zazzaga mashi sai da tayi mai isarta tukunna ya katse ta da cewa”saratu kenan,
kefa da kanki kikace nine ɗan kwali ke ce hula, hakan na nufin kece namiji ko? To
meyasa kike neman mace donta baki kariya? A tunanina ni yakamata inji tsoro bake
ba, shi namiji da jarumta aka san shi bada ragwantaka ba”!

Takaicin duniya ya ishi hajiya saratu, cikin lalama tace”pravin dan Allah ka dawo
ɗaki, idan saboda abun da na fada maka ne ya 6ata maka rai, zan baka haƙuri”

“Bana buƙatar haƙurin ki saratu, lokacin daya dace ki lallasheni ki tarairayeni ki


bani hakuri bakiyi ba till now da buƙatar kan ki ce ko? An gaya maki ni shashashane
bansan ciwon kaina ba”?

Shiru bata tanka mashi ba, kuma tana sauraronshi.

“Ko gobe kada kiyi tunanin zan dawo gida, ni yanzu haka ma gani akwance tare da
wadda tafi ki iya tarairayar miji.....”tsawar da ta daka mashi ce ta sanya shi yin
shiru, tamkar zata fasa mashi screen din wayarshi”ya isa haka! Ya isa! Kada ka
ƙara maimaita min maganar da kayi idan ba so kake ranka ya 6aci ba......” bata ƙare
maganar ba, yai rejecting kiran, Ya jefar da wayar saman mattress, Ya janyo hajjaty
a jikinshi, ya daura hannunshi saman sumar kanta, har cikin ranshi yana ƙara jin
ƙaunarta, bai da tamkarta a duniyar nan, saboda kyautata mashin da take Yi, yana
matuƙar ƙaunarta, kiss ya manna mata saman forehead nata, kafin ya cusa kanshi
gefen wuyanta, ƙamshin turarenta ya daki hancinsa ahaka bacci yai awon gaba da shi.

Jefar da wayar hannunta tayi saman gado, ranta ya 6aci matuƙa pravin ya ƙona mata
rai, kishine da ita, gani take kamar dagaske ne abun da ya faɗa mata yana can shida
wata suna sheƙe ayarsu, kokwanton maganarshi take Yi, ta riga ta yarda da pravin
tasan bazai Iya cin amanarta ba, wata’kil ya faɗa mata hakanne don ya huce raɗaɗin
abunda tayi mashi.

Damuwace ƙarara akan fuskar hajiya saratu, adaddafe ta nufi gado ta haye ta
kwanta idanuwanta suna fuskantar ceilling, babu alamun zata runtsa adaren Yau.

*Hajiya Turai💔*

Safa da marwa take Yi acikin ɗakinta, Hannunta ruƙe da wayarta, night gown ce a
jikinta.

Fuskarta tayi jawur tamkar wadda tasha kuka, musamman kumatuntu, green eyes dinta
kuwa sun ciza launinsu, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, since wuraren ƙarfe
goma take kiran layin dr.jazz babu alamun zai ɗaga, gashi har dare ya nutsa bai
dawo gida ba, ta kira layin Sir mubarak kusan sau talatin shima Bai daga ba tamkar
ta fasa ihu haka take ji.

“Mom” kamar daga sama taji an ambaci sunanta, tsabar ruɗi sai taji kamar
muryar jazz ne.

A firgice ta juyo don ganin wanene, Yana daga tsaye bakin ƙofar ɗaki, cikin shiga
ta kayan bacci ya zura hannayenshi cikin aljihun wandonshi, matashin saurayi ne
kamanninshi sak dana Sir mubarak.

“Ibad kai ma baka yi bacci ba”? Muryarshi da kalasa ya furta” How can I sleep,
Mom? Jazz hasn’t come home yet. na jaraba kiran layukan wayarsu duk akashe, bansani
ba shi jazz ko aikin kwana yake yi a asibiti, nazo ne naji ko sun faɗa maki meya
hana su dawowa gida”?

Ta lura da yanayin shi tsantsar damuwace akan face dinsa, batayi mamaki ba saboda
ƙaunar da suke yi ma Jazz, sun dauke shi tamkar shaƙiƙinsu

“Ibad, I don’t know why they haven’t come home yet, I’ve been trying their phones
since 10 o’clock, and nobody is picking up. I’m really worried, inajin fargabar ace
wani abun ne ya faru da su” tuni idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla.

Ruƙo hannunta Ibad yai”haba mommy, kada ki zubda hawayenki please, ki kwantar da
hankalin ki, Everything is going to be okay. They’ll come home safely.”
girgiza mashi kai tai”basu ta6a yi min haka ba ibad, daga jazz din har daddyn naku,
kullum ne idan zasu kai dare awaje, sai sun kira awaya sun faɗa min, amma yau shiru
babu wanda ya tuntu6eni” muryarta na rawa ta furta maganar, tausayinta duk ya kama
ibad, jinta yake yi tamkar mahaifiyarsu data rasu.

Gyaran muryar da akayi masu ne Ya janyo hankulansu ga duban shi, tafiya yake yi
yana tunkarosu tamkar baisan da su ba, Hannun shi ruƙe da apple laptop dinshi, daga
shi sai short a jikinshi, Ƙirar jikinshi da komai kalar na daddynsu ne, sai dai shi
yafi ibad da daddynsu hasken fata nashi chocolate colour ne mai kyan gaske, sumar
kanshi tasha gyara luf ta kwanta saman bayanshi, Yana da kirar karfi kamar ɗan
wrestling, wani irin daddaɗan kamshin turarene ke fita sako da lungu na jikinshi,
komai nashi da aji yake yin shi, mutunne shi maiji da kanshi, baida wasa a
aikinshi, yana ruƙe da muƙamin CEO na babban Companynsu dake a ƙasar canada.

Kafafuwanshi suna asanye da slippers, magana ya somayi tamkar baisan furtata

“Mom, yanzu major ya kira ni awaya, ya fadamin suna atare da jazz wani aiki ne
mai muhimmanci ya tsayar da su, so they couldn’t come home tonight. But they’ll be
back early tomorrow”

Ajiyar zuciya ta sauke, har cikin ranta taji dadin jin hakan, Murmushi Ibad ya
saki yana fadin”mun samu nutsuwa yanzu, Mom ki koma daki ki kwanta, ƙarfe 3 fa
ta buga, gobe nasan zakiyi ramuwar bacci, murmushi tasakar mashi”bari na koma ciki,
mu kwana lafiya My Sons,” ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakinta, saman gado ta
haye idanuwanta suna fuskantar ceilling, bakomai take jimawa ba face kwanan da za
ta yi ba tare da mijinta ba, sun saba faranta ma junansu kafin su runtsa yau kuma
babu shi atare da ita, ga kuma ɗanta da take jin kewarshi,
Pillow ta janyo ta rungume a ƙirjinta.

“Babban yaya nan fa ba kasar canada bace, taya zaka dinga yi mana yawo da
short a tsakar falo? Kai ala dole ga bature ko? Ko kunyar mommy baka ji,” Ibad ne
ya fada da zolaya.

Ko kallo bai ishe shi ba, saman Sofa mai mazaunin mutun uku ya kishingiɗa kanshi
saman sofa hand, Ya daura laptop dinsa saman flat stomach dinsa.

In a husky voice ya furta”ibad! Ina buƙatar abun sha”

Ruƙe qugu Ibad yai sam baya gajiya da zolayar yayan nashi duk da tazarar shekarun
dake atsakaninsu, domin kuwa Zaki ba ƙaramin mutun bane

“nan fa ba canada bace, Nigeria ce daddy Ya hana ana aikena idan dare yayi” yamutsa
fuska Zaki Yai Ibad ya fara hayaƙa shi.

Calmly ya furta”Don’t make me repeat myself” kama kunne ibad yai”sorry big bro,
na tuna kada ka hanani silallan kashewa” ya fada tare da nufar frigde Ya bude ya
dauko mashi coke mai sanyi, ya dawo Ya daura mashi saman sofa table din gabanshi.

“Babban yaya gashi na kawo, Ni zan cire maka murfin?” banza yai mashi tamkar
baiji me yace ba.

Bottle opener yaje ya dauko ya zuƙunna agaban table din Ya soma kiciniyar bude
murfin, sai nishi yake yi, sam bai saba da wahala ba, ibad mugun sangartacce ne
yayanshi ya 6ata shi da hutu, dogon tsoki zaki Yaja, ya yunkura ya miƙe Ya ajiye
laptop din gefe ɗaya, ya kai hannu ya kar6e coke din da bottle opener din, sau ɗaya
ya murɗa murfin ya cire.
Washe baki Ibad Yai”babban yaya ba za ka yi bacci ba? kana buƙatar hutu fa, kai
kullum aiki baka gajiya”!

Banza yai dashi baice komai ba, a tsanake yake kur6ar coke din me sanyi, Ibad ya
ƙura mashi ido yana kallon bakinsa har haɗiyar yawu yake yi.

Janye coke din yai daga bakinshi, Ya galla mashi harara”meyasa kake kallona kana
haɗiyar yawu kamar wani maye? Idan so kake kasha bakasan inda zaka dauko bane”

Kwa6e mashi fuska ibad yai”Ai ni nafi so kasha ka rage min”

Sakin baki yai galala yana dubanshi”oh dole sai na baka ragowa na zaka sha” ɗaga
mashi gira yai alamar eh.

Babu musu Ya miƙa mashi, don ya san rigimar ibad idan har ba bashi ragowar yai ba
to kuwa zasu kwana azaune”

Yana sha yana kallon fuskar Zaki, aiku sarkin ɗumi.

“Big bro, where’s my sister pretty ? You told me she came back to Nigeria. When
can we see her? Should we go to their house, or will she come to ours? (Babban yaya
Ina sister pretty dina? Ba ka ce min ta dawo Nigeria ba, to yaushe zamu haɗu da
ita? mu zamuje gidansu ko ita zata zo gidanmu?)

Dafe kanshi yai da hannu ɗaya”Ibad, I don’t like making noise, Please go to your
room, lie down on your bed, and sleep.”

“Shikenan zanje na kwanta amma kafin nan inaso ka fadamin gaskiya, dagaske babu
soyayya atsakaninku”?

Ji yake tamkar ya dauki laptop din gefenshi Ya kwalama ibad saman kanshi, Ya
takura mashi.

“Ka yi shiru bakace min komai ba”!

Miƙewa zaki yai ya dauki laptop dinsa Ya nufi sashen bedroom dinsu, da sauri Ibad
Yabi bayanshi, har yakusa shiga dakin ya ɗan dakata da yin tafiyar, in a cool voice
ya soma magana

“Ibad, she is married and even has a daughter, And she loves her husband. But
there is no love between me and her. taimakon da nayi mata dan Allah nayi shi”

Da mamaki Ibad yace”babban yaya kana nufin duk tsawon shekarun data dauka a
canada a gidanka, da auranta? To ya akai ta gudu tabar mijinta da ƴarta? kuma take
rayuwa agidanmu harma kuke rungume juna ai ina ganinku idan kuna shan soyayya....”
kafin ya ƙare maganar, afusace zaki ya waiwayo da niyar ya kwaɗa mashi laptop din
hannunshi da gudu Ibad Yabar wajen yana dariya.

Guntun tsoki Zaki Yaja, Ya faɗa katafaren room dinsa, saman gadonshi ya kwanta,
haɗi da daura laptop dinshi on his broad chest, hoton fuskarta dake akan wallpaper
din laptop nasa ya ƙurawa ido yana kallonta, bazai Iya misalta ƙaunarta da yake ji
ba, yana sonta baya jin zai iya son wata ƴa mace aduniyarnan kamar yadda yaso
baiwar Allahn nan, sun rayu na tsawon shekaru tamkar ma’aurata rana ɗaya Allah ya
ƙaddara rabuwarsu, yana fatan sake haɗuwa da ita, da tunaninta bacci yai awon gaba
da shi.

*ANEELERH❤*
Kiran sallar asubar farko, ringing din wayarta ya daki kunnanta, firgigit ta farka
daga bacci tana faman sauke ajiyar zuciya, yayin da la66anta ke ambaton sunan baby
junaid, mafarkin da tayi da shi ya ɗaga mata hankali, a ruɗe ta mike zaune, rigar
baccin jikinta duk ta yamutse, haka zalika sumar kanta a hautsine take.

Daukar wayar tayi dake ajiye gefenta, ta duba me kiranta, missed calls ta gani
sun kai biyar na hajiya adama, aranta ta ayyana Allah yasa ba mafarkin da tayi bane
ya zama gaske.

Bin kiran tayi nan take kiran ya shiga, bugu uku kafin hajiya adama ta ɗaga.

“Assalamu alaikum, daughter in-law, fatan dai ban katse maki baccin ki ba” da
buɗar bakin Aneelerh sai cewa tayi”mommy ina junaid”
Sautin dariyar hajiya adama ne ya fargar da ita, da sauri ta dafe baki tamkar tana
agabanta tace”au...namanta ban gaishe ki ba, ina kwana mommy”

“Lafiya lou Aneelerh, lallai yau na shaida kin ƙosa kiga ɗanki, tun da gashi har
kin fara ambaton sunan shi tunkafin ki gaishe ni”

Cikin jin kunyar maganarta Aneelerh tace”ba haka bane mommy, daga bacci na tashi
bansan Na ambaci sunanshi ba”

Hajiya adama tace”oh am sorry na tada ki daga bacci tun da asubahi, agafarce ni,
jikana ne ya takura min akan in kira mashi ke awaya, yaban mamaki da sunanki Ya
farka yanata kuka yana fadin wurin mommy zaije shine nace bari na kiraki kuyi
magana wata’ƙil hankalinshi zai kwanta, kafin mu shigo gidan zuwa anjima in sha
Allah”

Hankalin Aneelerh yaɗan tashi jin abun da mommy adama tace, aranta ta ayyana
kodai shima yayi kalar mafarkin da tayi da shi ne?

“Aneelerh kinyi shiru, ga shi ku gaisawa” muryarta adabarbace tace”toh mommy”

Sautin kukan baby junaid ne ya cika mata kunnanta, murmushi tasaki tana fadin”My
baby boy, ba hello ba hi sai kuka? So kake hankalina Ya tashi ko”?

Cikin shessheƙar kuka yace”mom..my wallahi kizo ki ɗoke ni, idan ba haka ba
bazaki sake gani na ba, mutuwa ma zanyi” rass taji gabanta ya fadi,

“Junaid kadaina ambaton mun mutuwa, banaso, idan wani abu ke damunka ka faɗamin
mana!” aɗan tsawace ta furta mashi maganar, tunawa da hajiya adama yasa ta sassauta
muryarta,
“My baby boy, ka kwantar da hankalin ka, Yau in sha Allah mommy adama zata dawo
min da kai”

Tsagaitawa yai da yin kukan, Muryarshi da shagwa6a yace”Ai ni tsoro nake ji, bana
son zama agidansu....” bai ƙare maganar ba tayi sauri furta”shiru! Agaban mommy
adaman kake fadin haka”?

“A’a mommy, ba agabanta bane, ai ta fita daga dakin”

Ajiyar zuciya ta sauke”yanzu fada min me ke baka tsoro? Ko wanine yake bugunka”?

“A’a mommy, idan ina bacci, sai ina ganin wani mutun sanye da baƙaƙen kaya hannun
shi ruƙe da ɗan kwano, kalar wannan abun na ɗakin mami, wanda ake zuba fura a cikin
shi, hannun shi zaƙo zaƙo da akaifu kalar na Ana mai girka mana abinci, wai yake ce
min inzo mu tafi” zaro ido waje aneelerh tayi”Junaid ka natsu kayi min bayani, a
mafarki kake ganin shi ko kuwa a zarihi? Kai kaɗai ka ke kwana aɗaki idan dare
yayi”

“Ni ba mafarki nake yi ba, dagaske nake ganin shi, kuma a ɗakinsu nake kwana”
aneelerh duk tabi ta ruɗe.

“Junaid kaji tsoron Allah, ka faɗamin gaskiya, nasanka da ƙarya, Idan baka fada
ba, to bazan baka zoben Angel ba”

“Kin siyane”? Ƙumshe dariya tayi don tundaga kan yadda ya tambayeta ranta ya bata
cewar ƙarya ya shirga mata.

“Na siya mana, ai jiya naba mahboob kuɗi Ya siya maka zoben mai kyan gaske”

Tuntsirewa yayi da dariya yana fadin”to mommy wasa nake yi maki, wallahi dama
awani cartoon ne da muke kallo a tv, anan naga mutumin” fashewa tayi da dariya
sosai har fararen haƙoranta suka bayyana”yanzu naji magana ɗan rainin wayau, duk
kabi ka tasar min da hankalina, Yau har mafarkin ka nayi saboda nayi kewarka babyn
mommy, ina sonka Yarona”

Yace”nima inasonki mommyn baby” dariya tasaki, idan yana yi mata magana kamar
wani babban mutun daya mallaki hankalin shi, sai idan yayi wata kwa6ar ne zaka gane
ƙaramin yaro ne.

“Mommy ina mamina? da abie, da uncle mai ƙaton hanci, da mahboob mai son kuɗi,
da zahrah mai dogon wuya”

Tsabar yadda take yin dariya hada dafe ciki,


“Junaid baka da mutunci, Uncle dinne mai ƙaton hanci”!
Kaitsaye yace mata”eh mana, baida kyau Allah, mummuna ne uncle dan Iya, ni naji
dadi ma bashine daddynki ba, da wallahi bazanyi kyau ba”

Mamaki ne ya kama Aneeleerh, jin yadda yake kushe mata kawunta.

“Junaid dan Allah ka yi shiru kada wani yaji ka, Ni zan ajiye wayar, ka koma bacci
zuwa anjima Mommy adama zatayi maka wanka ta shiryaka sannan zata dawo mun dakai
gida, fadamin me kake so in tanadar maka”?

Da shagwa6a yace”fura nakesho, asanya kwakwa da yoghurt aciki” bakomai ya tuna mata
ba face Angel, tana son furar da aka sanya kwakwa da youghurt, kusan kullun idan
tazo gidansu sai ta sanya Aneelerh ta haɗa mata ita, musamman saboda Angel take
ajiye damarmar fura cikin robabi ta sanya mata su a frigde don su yi sanyi.

Tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, Muryarta na rawa ta furta”zan ajiye
maka my baby boy, ka kwanta ka huta zuwa anjima zamuga juna” daƙyar ta samu baby
junaid Ya ƙyaleta, badan ta gaji dashi ba, ta ajiye wayar on pillow, ta sauko daga
saman gadon, A hankali take bin bedroom dinta da kallo, har idonta ya sauka akan
hotonsu da ta liƙa shi a bango, wanda sukayi tare da aminnanta, su uku abunsu,
kowacce ta ca6a uban adon lace, fuskokinsu ɗauke da murmushi.

Ta natsu tana kallon hotunansu, sam ba ta ji takun tafiyar mutun ba, har ta ƙaraso
gefenta ta tsaya, Ƙamshin turaren zahra ne yaja hankalinta ga dubanta, tayi mamakin
ganinta a ɗakinta, tun ranar da abunnan ya faru na hajiya falmata ko magana bata
ƙara haɗa su ba, amma yau sai gashi ta tako ta shigo room dinta, dogon hijabi ne a
jikinta daga ƙasa har sama launin maroon hannayenta biyu ta fiddo dasu ta cikin
hannun abayar, hada cazbaha ta ruƙe tana ja kamar wata matan limam.

“Aunty Aneelerh Ina kwana, kin tashi lafiya”?


Daƙyar ta iya amsa mata da lafiyalou, ina fata kema haka”
Daga mata kai tayi alamar eh, idanuwanta sam basa akan Aneelerh suna akan hoton da
take kallo, wani irin kunyarta take ji, tunawa da rashin mutuncin da tayi mata akan
ta bata shawarar ta ba Hajiya falmata haɗin kai, tayi danasani tun jiya da Mahboob
Ya fayyace mata komai.

“Nayi mamakin ganinki a ɗakina zahra, ai nayi tunanin mun rabu kenan har abada”

Girgiza kai zahra tayi”Idan kinga mun rabu to mutuwace ta raba”

Aneelerh sam batasan Mahboob ya fada ma zahra ba, bayan ta gargade shi akan karya
gaya mata, shi kuma bayason suna gaba atsakaninsu, don ya fahimci zahra ta fusata
sosai, Idan har bai fada mata gaskiya ba to kuwa zata cigaba da zabga ma Aneeleeh
rashin mutunci abisa rashin sani shiyasa ya yanke shawarar ƙwara ya faɗa mata, don
ta yi takatsantsan kada ta wuce gona da iri azo aji kunya.

“Kiyi haƙuri da abunda Ya faru atsakanin mu, nasan na 6ata maki rai, tuntuni nake
taso in nemi yafiyarki, sai dai baki bani damar yin hakan ba” Aneelerh ce tayi
maganar tana duban zahra.

Cikin sanyin murya zahra tace”ni yakamata nabaki hakuri auntyna bake ba, saboda
ni ce mai laifi, ban kyauta maki ba, duk irin shaƙuwarmu da kyautatamin da kike yi
amma nagaza fahimtarki, har takai takawo ina zarginki, maimakon na kyautata maki
zato, wallahi naji kunya, daren Jiya daƙyar na runtsa tsabar takaici, Ƴan kwanakin
da muka samu sa6ani atsakaninmu aunty Aneelerh naji jiki ba kaɗanba, na ƙuntata, na
gane mahimmancinki agareni, Ina da abubuwa dayawa da suka faru wadanda nakeso in
samu abokin firar da zangayama wa ya tayani farin ciki sai dai kash babu, ke kaɗai
ce nake jin dadin tattaunawa dake akan duk wani abu daya shafi rayuwata saboda
nasan zaki ƙarfafa min gwiwa ki kuma bani shawarar da zata amfane ni....” zafafan
hawayene suka wanke fuskar Zahra, tuni idanuwanta sun kaɗa jawur da su.

“Meyasa banyi dogon nazari ba akan shawarar da kika bani”?

Zuciyar aneelerh ba ƙaramar karaya tayi ba”zarah! Mahboob Ya fada maki ne”?

Jinjina kai tayi”ƙwarai kuwa ya fadamin komai, har gargaɗi na yayi akan kada na
nuna na sani, saboda kince mashi kada ya gaya min, shi kuma a ganinshi bai kamata
ki zubda mutuncinki a idanuwana ba, saboda ku rufa ma hajiya falmata asiri awurina,
don in cigaba da ganin darajarta, hakan kuma bazai ta6a yiwuwa ba, saboda shi
mutunci madarane idan ya zube baya kwasuwa, sai dai naji dadi da ke kika yi silar
shiriyarta, ke din ta dabance Auntyna”

Rungume Aneelerh tayi, atare suka fashe da kukan farin ciki, yau sun shirya da
juna, babu wanda baiji jiki ba acikinsu.

Bubbuga bayanta Aneelerh tayi da hannunta Cikin shessheƙar kuka take fadin”komai
ya wuce zahra, abunda ya faru laifina ne dana baki shawarar banza duk da ko a
lokacin bawai zan zuba maki ido bane don ina jarabaki ne nayi hakan, wallahi duk
wani motsinki atafin hannuna, tun bayan dana baki shawarar, fargabana kada ki
amince da shawarata ki kama hanya ki tafi kai mata kanki, shiyasa na sanya maki
ido, akarshe na yanke shawarar zuwa gidanta don in gargadeta akan ta fita sabgarki,
Cikin Ikon Allah sai gashi na 6uge da yi mata nasiha, ashe nice silar shiriyarta,
naci ribar jarabawar da nayi maki zahra, Naji dadi kuma nayi farin cikin samun ƴar
uwa mai tawakkali irinki, zan iya cewa duk namijin daya mallaki mace irinki yayi
nasara sai dai fatan ya cika da imani”

Dariyar farin ciki zahra tasaki, tare da dago dakanta daga jikin Aneelerh
“Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin yi maki godiya saboda babu su
auntyna, Ina fatan nima Allah yabani abunda zan kyautata maki da shi, sannan
mahboob Ya faɗamin cewa kin bashi kyautar kuɗi duk da yaƙi gayamin nawa ne kinsan
halinshi May be Yana gudun kada Ince ya bani kasona, baisan cewa Nima na samu
alheriba, abunda nake ta so in faɗa maki kenan”

Waro ido Aneelerh tayi da alamun farin ciki akan fuskarta tace”masha Allah, kice
kun samu abun arziƙi” Jinjina kai Zahra tayi”zakisha mamaki auntyna, naga yanzu
kika farka daga bacci, da anjima idan muka kammala yin breakfast zan fada maki
komai”

Murmushi Aneelerh tasaki”Yau zansha kanun labarai, Yanzu bari na shiga toilet in yi
wanka”

“Auntyna wai yaushe za’a dawo mana da baby junaid dinmu, nifa nayi missing dinshi,
Allah na kusa zuwa in dauko shi, Jiya har mami na tambaya game da zancen
dawowarshi”

Aneelerh tace”kada ki damu, Babyn mu yau zai dawo gida, Hajiya adama zata kawo
shi, Nima yau da shi na tashi araina”

“Allah ya kawo su lafiya, shima na tanadar mashi kyautarshi ta musamman da zan


bashi” Aneelerh taji dadin maganar zahra.

“Kada na cika ki da surutu, nayi kewarki ne auntyna, bari nabarki kiyi wankan in
kin fito mun tattauna, amma kafin nan niko inaso in tambayeki wani abu in ba
takura” dariya aneeleh tayi kafin tace”okey ina jinki fadamin menene”

Da ido tayi mata nuni da hoton dake amanne jikin bango.

“Wacece wancan black beauty din mai diri? Ita kadai ke bansani ba cikin
ƙawayenki, nadai san Benazir mahaifiyar kyakkyawar yarinyar nan Angel”

Jim Aneelerh ta ɗanyi kafin ta furta”Aishatu bintu sheikh Iman Malik, shine
sunanta, kamar yadda na fada maki aminnan juna ne mu”

Cike da son jin ƙarin bayani Zahra tace”to amma ta rasu ne ita? Naga ko waya ba
ku yi, Ita dai benazir nasan abunda ya faru da ita” a kagare ta jefa mata tambayar.

Cikin sanyin murya Aneelerh tace”ƙaddarace ta afka mata wadda tayi silar
tarwatsewar farin cikin rayuwarta, baiwar Allah, nan da kike ganinta mahaddaciyar
alƙur’anice, tun tana ƴar shekara goma sha wani abu ta haddace shi, Tana da kaifin
basira mace ce mai kamun kai, tana da aji, idan nace zan baki labarin rayuwar Aisha
wallahi saikinyi sha’awar yin koyi da ita, saboda kyawawan ɗabi’unta da halayanta,
Ni kaina ban ta6a tsammanin zamu rabu da itaba.....” tun da ta fara magana zahra ta
kafe ta ido tana sauraronta, idanuwan Aneelerh sun kaɗa jawur, sam bata son tuna
baya, hakan zai fama mata ciwon dake acikin zuciyarta.

“Aunty Aneelerh kinyi shiru? tun da kika ambaci kyawawan halayanta naji na
kwaɗaitu da son jin tarihin rayuwarta”

Girgiza kai Aneelerh tayi”Am sorry zahra, bana son tunawa, “ bubbuga ƙafa zahra
tayi tamkar zata fashe mata da kuka tace”please Aunty Aneelerh, wallahi tana
burgeni duk da ban ta6a ganinta ba”

Murmushin yaƙe Aneelerh tasaki tana duban hoton yayin da hawaye ke bin fuskarta”Ni
kaina bani da masaniyar tana araye kota mutu, tunkafin muyi aure tabar gidan
iyayenta, Silar wani mummunan abu daya faru, wanda ni nayi imanin bata da laifi,
tuggune da makirci aka shirya mata.....” dakatawa Aneelerh tayi dayin maganar tana
kallon zahra, tsabar son jin gulma har ta jefar da cazbar hannunta batare da
saninta ba.

“Aunty Aneelerh kinyi shiru! Meya faru da ita? Wanda yaja har tabar gidan
iyayenta? Wani irin tuggune aka kitsa mata”?

Tuntsurewa Aneeleeh tayi da dariya, juyawa tayi da sauri ta nufi toilet door tana
fadin”Zahra ƙwara ki fidda rai da son jin labarin Aishatu Bintu sheikh imam malik,
dan zan baki shi ba yanzu ba sai kin ƙara hankali” ta kare maganar ta shige toilet
taja kofa ta datse.

Ta tafi Tabar Zahra da cizon yatsa, idanuwanta akan hoton fuskar Aisha, aranta ta
ayyana ai wallahi saina ji labarinki baiwar Allah, Ai ni dama tun da naga hotonki
na shaida kinbar tarihi arayuwarki, Oh ni ƴar ubansu, gata kyakkyawa, mace har
mace, ga diri kamar nicki minaj, ko tana ina ahalin yanzu”? Sambatu zahra tadingayi
tana kallon hoton aisha, sai daga bisani ta duƙa kasa ta dauko cazbaharta, ta futo
daga ɗakin ta nufi nata dakin don ta kimtsa kafin lokacin yin break fast.

*Daular Alhaji Musa🏙*

A zaune take kan darduma, bata jima da kammala sallar asubahi ba, hijab din data
sanya launin milk, gaba ɗaya ta tattara natsuwarta akan addu’ar da take Yi, ta ɗaga
hannayenta sama cikin harshen larabci take karanto addu’o’i, yayin da hawaye suka
cika idanuwanta, bakomai take roƙo ba face Allah ya dawo mata da mijinta lafiya da
ƴarta, bata da burin daya wuce tayi tozali da su, tayi matuƙar ƙagara da son
ganinsu.

Ƙamshin turaren dr.shureim ne Ya dakatar da ita daga yin addu’ar da take yi, da
sauri ta shafa saman fuskarta, A hankali ta fuskance shi, yana daga zaune gefen
gadonta, bai jima da shigowa ɗakin ba, fuskarshi dauke da annurin farin ciki, Daren
jiya da tunanin ƴar uwarshi ya kwana, ya damu da ita.

“Yayana nakaina, Ina kwana ka tashi lafiya”?

“Lafiyalou rabin raina, ina fata kin yi kwanan farin ciki agidan Uncle” shiru
tadanyi tunawa da abunda ya faru duk da ta dauki hakan amatsayin mafarki, jinjina
mashi kai tayi”Alhamdulillah, jiya naji dadin bacci, hada munshari, balle ni da
nake atare da Zeenatu, yarinyar akwai shiga rai”

Murmushin gefen fuska dr shureim yasakar mata”hala tacika ki da surutu”?


Girgiza kai benazir tayi”a’a, ai yarinyar kunya gareta, tana jin nauyin yi min
magana yadda kasan bafullatana”

Dariya dr. Shureim yai kafin ya tsagaita yace”hakane tana da kunya, amma fa ta iya
zuba kamar aku, sai kun saba da ita zata saki jiki dake”

Dr shureim yasaki baki yana maganar zeenatu, baisan cewa tana la6e cikin toilet
tana sauraronsu, hannunta ɗaya ruƙe da qugunta, kalmar akun daya furta ta ta6a
zuciyarta.

Murmushi benazir tasaki, abunda baisani ba tun jiya tasan da surutun zeenatu, kafin
su kwanta bacci, sunyi firar dare, ta saki jiki da ita tamkar abokiyarta.

“Yaya shureim, Ni yanzu damuwata Mijina da ƴata, mami ta fadamin cewa basa ƙasar,
amma sun kusa dawowa, ni namanta ma ban tambayeta sunan ƙasar da suka tafi ba” ta
fada tana dubanshi”yaya shureim ko kana da number wayar taj”? Ras yaji gabanshi ya
fadi, saboda shi baisan komai dangane da mijin benazir ba.
Shiru yai mata batare da ya iya furta mata kalma ba, don baisan amsar da zai bata
ba

“Au namanta, kaima bakasan mijina ba ko? Lokacin dana aure shi......” bata ƙarasa
maganarba cak ta ɗago suna kallon juna.

Cikin sanyin murya yace”ai ba laifi kikayi ba, lokaci bana acikin hayyacina, ban
kaiga farfaɗowa daga radadin abunda ya same ni ba, Benazir bansan mijinki ba, bana
zumunci dashi, saboda ni kaina bana cikin natsuwata, kuma hada ƙarin ni ba azaune
nake ba, idan baki manta ba, da abun duniya ya isheni, tattarawa nayi na koma egypt
wurin ammim mu da zama” daƙyar yake furta maganar, launin idonshi harya fara
canzawa
Numfasawa yai kafin ya ɗaura da cewa”nasan ban kyauta maki ba, amma kiyi hakuri,
daga ni har ke ƙaddarar rayuwace ta afka mana,”Wallahi bazan Iya misalta maki ƙunci
da radadin da naji ba, lokacin da labarin tafiyarki ya same ni, idan bazan manta
ba, aunty zainab ce ta sanar dani komai dangane da guduwarki da jinjirar da kika
bari, bayan haka bansan komai game da rayuwarsu ba nima ban jima da dawowa gida
ba.......”

Bai ƙare maganar ba ta tari numfashinshi da cewa”kana nufin baka ta6a haduwa da
ƴata Angel ba? Amma ni ayadda mommy ta fadamin taj yana kawota gidan mu, suna
daukar dawainiyar kula da ita kuma suna nuna mata hotona harma tana tambayarsu
Yaushe zan dawo”

Zaro ido dr.shureim yai alamar mamaki da jin ƙaryar da mommynsu ta shirgawa
benazir, duk da ba a ƙasar yake zaune ba, yasan komai dake faruwa a gidansu, ta
hanyar aunty zainab dake fada mashi akai akai, shi dai a iya saninshi Hajiya layla
bata zumunci da tajuddeen, hatta auran benazir da Alhaji ubaid ya bashi bada son
rantaba, saboda ita ta tsani bare, balle shi da yakasance mai rufin asiri ba
attajirin mai kuɗi ba, har fada saida sukayi da Alhaji ubaid saboda yabama ɗan
jarida auran ƴarsu.

Ganin yanayin fuskarshi ya canzane yasa jikin benazir yin sanyi,

“Yayana kayi shiru baka ce min komai ba! Mommy ba gaskiya ta fadamin ba ko”?
Adabarbarce ya girgiza mata kai yana kokarin tattara natsuwarshi yace”bahaka bane,
ai ni bana a ƙasarne, bani da masaniya akan komai, lokacin dana dawo Nigeria shi
taj din da yarinyar sun riga sun bar ƙasar, nima awurin Aunty zainab naji labarin”

Ajiyar zuciya benazir ta sauke, fatanshi Allah yasa kada ta kuma tambayarshi wani
abun da zai kasa amsa mata.

“Mommy ta fadamin cewa yarinyar kamanninta sak dana tajuddeen amma hasken fatarta
nawane ta dauko, yarinyar kyakkyawace idan zan iya tunawa, kafin na gudu nabarta
dana haifeta saida na kalleta har naga launin idanuwanta ruwan tokane kalar na
amminmu, kuma tana da curly hair kalar nawa, ni dai fatana Allah yasa bata dauko
halina ba, banason ace bata jin magana.

Dariyace ta kubce ma dr shureim, sambatun benazir ba ƙaramin kayatar dashi suke


Yi ba.

Zeenatu dake a la6e tana sauraronsu, takasa fitowa daga toilet din, zuciyarta ta
kwaɗaitu da son jin wacece yarinyar auntynta benazir? Ya akai bata ta6a ganinta ba?
Kamar dai ta ta6a jin labarin jinjirar da benazir ta bari awajen mommynta sarah.

Lokaci ɗaya dr shurem yadaina yin dariyar, hawayen dake taruwa cikin idanuwanshi
suka soma gangarowa saman kuncinsa.

Da sauri ya kifa kanshi on his laps,


Hankalin benazir ba ƙaramin tashi yai ba, Jiki na rawa ta mike daga kan dardumar ta
koma gefenshi ta zauna haɗi da daura hannunta ɗaya saman bayanshi”yaya shureim meke
faruwa? Meyasa ka zubar hawaye? Yanzu fa kake yin dariya? Kona fadi wani abune daya
6ata maka rai? Shiru bai ɗago ba, duk tabi ta ruɗe, zeenatu dake yi masu la6e
jikinta yai sanyi jin dr shureim dinta yana zubar da hawaye, muryar benazir taci
gaba da jiyowa tana fadin”dan Allah kayi min magana yayana nakaina, kasan bana son
ganinka acikin damuwa” bazata iya jurar halin da dr shureim dinta ya shigaba, Har
ta miƙa hannu zata buɗe kofar toilet din, sai kuma tafasa ta dan buɗe kadan ta
yadda zata iya leƙen su

Ɗagowa yai da kanshi, hawaye sun wanke fuskarshi, benazir dake kallon shi itama
hawayen ke fita a idonta
Zura hannunshi yai cikin aljihun jallabiyar jikinshi ya zaro wayarshi, batare
dayace komai ba, Ya miƙa mata wayar, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskarta
Yarinyar dake akan wallpaper dinshi.

Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ya sanya tafin
hannunshi ɗaya ya toshe mata bakinta, haɗi da girgiza mata kai, alamar tayi shiru,
daƙyar ta haɗiye kukanta, yayin da suke kallon juna, sai yanzu tagane dalilin zubar
hawayenshi.

A hankali ya zame tafin hannunshi daga saman bakinta, hakan ya bata damar yin
magana Cikin rauni na murya ta furta”munyi babban rashi yaya shureim, babu rabon
suyi rayuwa tare da ƴata Angel, yarinyar tana kama damu, kamar ni na haifeta,
mutuwa tayi mana yankan ƙauna, Allah ya jiƙanta” daƙyar ta ƙare maganar a hankali
ta mayar da rinannun idanuwanta kan hoton jinjirar yarinyar dake a nannanɗe cikin
towel fari ƙal, an sanya mata kayan sanyi, farace sol kamar ka ta6a jini ya ɗigo,
dara daran idanuwanta sun buɗe sosai.

“Bani da abun kallo daya wuce hotonta, da ita nake kwana da ita nake tashi, na
mutu akan ƙaunarta, bazan ta6a daina sonta ba, kuma bana tunanin koda ace nayi aure
zan samu madadinta a duniyar nan........ ⁉️

“Nayi danasanin abunda na akaita mata, har yau idan na tuna cewa da hannuna nayi
hakan sai inji gaba ɗaya na tsani kaina....” cikin jin ƙunar yai ya ƙare maganar.

Tsananin tausayinshi ne ya kama Benazir, idanuwansu sun kada jawur


Harta bude baki zatayi magana, Motsin buɗe kofar toilet Ya dakatar da ita, sam ta
manta da zeenatu a toilet, da sauri ta goge hawayenta, dr shureim ma ya share
hawayen shi muryarshi adisashe yace”wanene a toilet”?
Kafin ta bashi amsa, zeenatu ta fito, fuskarta da alamun lemar ruwa, tamkar
batasan me suke tattaunawa ba, Har kuka tayi masu saboda sun bata tausayi duk da
bata fahimci kan zancen nasu ba, ita a tunaninta Yaya shureim dinta ya ta6a son
wata, sannan hoton daya ta6a nuna mata awayarshi amatsayin nata yake kallo yanzu ta
gane ba ita bace, ya 6oye matane, har cikin ranta ba ta ji dadin hakan ba, jikinta
yai sanyi tamkar wadda ka zarewa laka.

Sun ƙura mata ido suna kallonta, fatansu Allah yasa bata ji me suke tattaunawa
ba”

“Zeeentu dama kina acikin toilet tsawon lokacin dana shigo ɗakin”?

Jinjina mashi kai tayi”eh yaya shureim bansan ka shigo dakin ba, Uziri ne Ya ruƙe
ni a toilet”

Ajiyar zuciya ya sauke jin tace batasan ya shigo ba.

“Ina kwana, ka tashi lafiya” muryarshi araunace ya amsa mata”lafiyalou” duban


benazir tayi wadda tayi shiru tana kallonta, daga ita har dr. shureim din
fuskokinsu sunyi jawur saboda kukan da suka sha, a hake suke ƙoƙarin 6oye mata
damuwarsu bayan ga alama nan ta gani.

“Aunty Benazir, bari naje daki in yi sallar acan, namanta jiya ban ɗauko hijabina
ba” ta fadi hakanne don ta basu damar cigaba da tattaunawarsu

Benazir tace”A’a basai kinje daki ba, Ga hijab dina kiyi da ita” ta fada tare da
cire hijabin ta miƙa mata, da sauri zeenatu tace”a’a, Kibarshi, nafison naje daki
nayi acan, naga kamar kuna yin magana ne keda ya shureim”

Murmushin yaƙe Benazir tasakar mata”kada ki damu ƙanwata, bawani abu muke
tattaunawaba, kema zamu Iya yin firar dake”

“Assalamu alaikum!” Mom layla ce ta doko sallama, gaba ɗaya suka ɗago suna
kallonta, doguwar rigace a jikinta milk colour, ta yafa mayafi akanta, fuskarta
dauke da fara’a take dubansu
Har suna haɗa baki wurin gaishe da ita”ina kwana mommy? Kin tashi lafiya”?

Cikin kulawa ta amsa masu da cewa”lafiyalou Alhamdulillah, fatan na same ku lafiya,


zeenatu ya akai naganki atsaye”?

Washe baki zeenatu tayi tana fadin”yanzu na fito daga toilet, nayi alwala ne zanyi
sallah”
Mom layla tace”okey, yakamata kiyi kada ki makara” amsa mata tayi da toh, da sauri
ta nufi kofar fita dakin ta fuce cike da fargaban kada Aunty Benazir ta dakatar da
ita, bayan ta fita daga dakin ajiyar zuciya ta shiga saukewa, haƙiƙa taji takaicin
halin da taga dr shureim dinta da aunty benazir, ta shiga damuwa tabbas tana ji
aranta wani mummunan abunne ya ta6a faruwa da su, a ƙagare ta ke da son jin wacece
Yarinyar benazir dinta? Sannan kuma wacece matar da taji yaya shureim dinta yana
magana akai har yake fadin bazai samu madadinta ba koda ace yayi aure, burinta
ayanzu shine taga hoton matar da ya shureim yake nunawa benazir a wayarsa.

Da wannan tunanin ta nufi dakinta dake acan upstairs.

Bayan fitar zeenatu, dr shureim da Benazir suka miƙe tsaye suna fuskantar
mahaifiyarsu dake binsu da kallon mai tattare da alamar tambaya.

“Meke damunkune? Ya akai naga fuskokinsu sun yi ja kamar wadanda suka yi kuka”!
Tambayar data fara jefa masu kenan

Benazir ce tayi kokarin cewa”Ni da ya shureim ne muke yin firar yaushe rabo, mun
tuna da rayuwar mu ta bayane kafin mu rabu”

“Hmm, yakamata ku manta da abunda ya wuce, tuna bayan nan baida amfani, tun da ba
abun arziƙi bane ya faru”
Dr shureim yace”hakane mommy, zamuyi kokarin yin hakan”
Shiru tadanyi na wani lokaci tana kallonsu.

Har dai Benazir ta fahimci kamar akwai wani abu dake akasan zuciyar mahaifiyar
tasu
“Mommy, kina son yin magana damu ne”?
Girgiza kai tadanyi kafin tace”tausayin rayuwarku nake ji, ina jin fargaban ranar
da zan mutu in barku a duniyar nan mai cike da ruɗani, saboda mahaifinku bazai iya
tsaya maku ba, shi kanshi juya shi akeyi.....” jikinsu ne yai sanyi jin abunda
tace, tamkar tana basu wasiyya ne, matsawa tayi kusada su tare da ruƙo hannayensu
acikin nata.

“Bazan 6oye maku ba, ji nake kamar wani abu zai faru”

“Mommy ki daina fadin hakan, Ki kwantar da hankalinki, Allah yana atare damu, ni
bana so naji kina zancen mutuwa” dr shureim ne yai maganar.

“Addu’arki kadai muke buƙata mama, kidaina sanya damuwa aranki” benazir ce ta fadi
hakan.

Gyaɗa kai Mom layla tayi”shikenan nadaina, Benazir yaushe zaki je gidansu
Aneelerh?
Murmurshi benazir tasaki kafin ta bata amsar tambayarta dr shureim ya riga ta fadi
“zuwa jibi in sha Allah, zan kaita gidan dakaina”

Mom layla tace”naji dadin jin hakan, zanyi magana da mahaifinku shi yake da layin
mahaifin Aneelerh, in yaso saiya fada mashi game da zuwanku, tun da babu wanda
yasan gidan nasu, sai sun tura mana da adress dinsu.

Benazir tace”hakan yayi mun gode mommy, ki kwantar da hankalinki, don na lura
kamar bakya jin dadi”

Murmushi mom layla tasakar masu, lokaci ɗaya kuma yanayin fuskarta ya canza ganin
wani abu ajikin benazir, harta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa tana
kokwanto acikin zuciyarta.

“Mommy lafiya”? Benazir ce ta fargar da ita, ganin ta ƙura ido tana kallon
wuyanta”
Girgiza kai tayi’bakomai, bari na koma daki, namanta banyi azhkar ba, Ina fata
kuma kunyi naku, koda yake nasan ma shureim yayi ke fa”? Ta fada tana kallon
benazir hankalinta yafi karkata akan jan ta6on da tagani gefen wuyan benazir kamar
Yakushinta akayi fatar wurin duk ta karkarce.

“Nayi mommy, bayan na kammala sallar asuba”


Jim ta danyi kafin tace”okey, ku cigaba da firar ku, amma dan Allah adaina tuna
bayan nan”
Murmushi kowan nan su yasaki, insha Allah mommy”

Juyawa tayi ta nufi kofar fita dakin, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, ta
rude da abunda tagani, tambayoyi ta shiga jefa ma kanta me yakawo jan tabo da sahun
yakushi saman wuyan benazir?
Da wannan tunanin ta nufi dakinta.

(Abunda ya faru bayan Big guy ya fita neman hannah)

Cikin takun sauri Big guy ya nufi bedroom dinsu dake a down stairs, wata’ƙil aci
sa’a ya ganta, hankalin shi ba akwance yake ba, saboda ya bincika ko’ina na part
dinsu saƙo da lungu babu cikon yarinyar da yake nema, ba ƙaramin ruɗewa yai ba,
fargabanshi kada ace wani wajen taje ta faɗa takasa fita, ɗaya bayan ɗaya ya ke
shiga dakunan matan babu kowa, yabi hanyar da zata kaishi bedrooms din mazan, A
bakin ƙofar dakin su Naufal Yaci burki, Ya dafe jikin glass door din, slowly kofar
ta zuge, leƙawa ciki yai, a kwakkwance ya same su saman shimfiɗeɗan gadonsu, sun
cunkushe kamar kinfin gwangwani, gaba ɗaya sun lullu6e jikinsu da bargo, buga ƙofar
yai ranshi a jagule Ya juya zai fuce daga ɗakin ganin mazane zalla kuma gaba
ɗayansu suke aɗakinsu naufal, Cak Ya tsaya da tafiya kwakwalwarsa ta soma tariyo
masa abunda ya gani, da sauri Ya koma dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallon
ƙafafuwansu da suka leƙo daga cikin bargon, a hankali ya ɗaura eye balls dinsa kan
kafar da yake hasashen ta macace bata namiji ba, shape dinta ya banbanta data mazan
kuma tafi kafafuwansu ƙaranta, hannu ya miƙa ya damƙi kasar bargon ya yaye shi,
lokaci ɗaya big guy yasauke nannauyar ajiyar zuciya, hankalin shi ya kwanta ya samu
natsuwa, Hanna ce a tsakiyar mazan ta ƙanƙame gabriel kamar zata koma cikinsa, Yayi
mamakin ganinta tsumu tsumu acikinsu, gefenta na dama naufal ne da haris, daga
6angaren hagun katifar gabriel ne da javed, sunyi nisa acikin baccinsu.
Acikin zuciyarshi ya furta”Kin tayarmin da hankalina” ya ambaci hakan tare da
sakin bargon Ya juya ya fuce daga ɗakin nasu.

*Unaisah Angel💋❤*

Fitowa tayi daga cikin toilet, fuskarta da alamun lemar ruwa, Salsabeel yana daga
zaune saman gadon Ya jingina bayanshi jikin headboard yayin da Giant snake din yake
a kwance gefenshi ya daura kanshi saman laps dinsa.

Jin motsin fitowarta ne ya janyo hankalin salsabeel ga kallonta, baiwar Allah ba


ƙaramin tausayi take bashi ba, ƴar ƙarama da ita ta ɗaurama kanta damuwar da ko
wani babban bazai Iya jurarta ba, ganin yana kallontane yasa ta dan sakin fuskarta
data kumbura suntum.

“Fuskarki kika wanko”?

Girgiza mashi kai tai”a’a alwala nayi”


“Amma ba’a fara kiran sallar asuba ba”
“Nafila nake so nafara Yi, kafin a kira sallar asuba, Inaso zanyi ma danish ɗina
addu’a ne”
Murmushi salsabeel yasakar mata, dama saida ya ayyana hakan aranshi
“Kina kaunar ɗan uwan nan naki”
“Fiye da yadda nake ƙaunar kaina” ta furta hakan tare da juyawa ta nufi kofar fita
dakin don taje nasu ɗakin ta ɗauko Hijabin da zatayi sallah, har ta kusa fita daga
dakin kamar ance ta waiwayo ta kalli gadon

Ba zato ba tsammani macijin Ya girgiza Yana kokarin tashi


Da sauri ta furta”yanzu zan dawo my Man, kada ka biyoni, Nima bazan Iya yin nesa
dakai ba, Hijabin sallah zan ɗauko a ɗaki” komawa macijin yai tare da daura kansa
saman laps din salsabeel.

Ajiyar zuciya ta sauke haɗi da yin ƙayataccen murmushi, salsabeel dake kallonta
shima murmushin yake yi, lamarin Danish na matuƙar bashi mamaki.

Juyawa tayi da sauri ta fuce daga dakin.

Moving quickly take tattaka matakalar benan, kasancewar ko’ina na part din da
haske tamkar da rana baka ta6a gane lokaci saika kalli agogo, a tsanake take bin
ginin da kallo Yayin da take saukowa down, zuciyarta tayi mata nauyi, zazza6in
jikinta sai ƙara nunkuwa yake yi, Ita kadai tasan halin da take aciki, da ace zata
Iya dauke ma danish abunda ke damunshi da kuwa tayi hakan, zaifi mata sauƙi akan
taganshi a wuyanci hali.

Tana gab da zata dira ƙafarta kan floor din falo, ranta ya bata cewar akwai mutun
awurin, wurga eye balls dinta tayi akan first floor bataga kowa ba, A hankali ta
mayar da eyes din nata kan Second floor, rass taji gabanta Ya faɗi ganin mutumin
nan da ta ta6a gani a gym room yana motsa jiki, Ya juya mata baya, bata Iya ganin
fuskarshi da kyau, batasan ya akai ta tsinci kanta da yi mashi kallon kurulla ba,
bakomai take son gani ba face fuskarshi, sai dai kash takasa ganinta, faffaɗan
bayanshi kadai take kallo, Ba ƙaramin jikine da shi ba, murdadden damtsen
hannayensa take kallo, da alama Ya ruƙe wani abu yana sha a cup, duba da yadda
hannun shi na dama ke motsi, yayin da ɗayan hannun nashi ya zura shi a shorts
pocket dinsa.

Aranta ta ayyana ko wanene wannan mutumin? daga gani yana da ƙarfi da tarin
dukiya, komai nashi cikin ƙasaita yake yin shi, dai dai da yanayin tsayuwarshi abun
kallo ce, yaɗan jingina bayanshi jikin benan.

Hankalinta ya karkata akanshi, ta manta da hijabin da zata je daukowa, ta tafi wani


tunanin daban, ita so take taga wanene shi? Ranta yafi bata cewar Chief din da
taji ana fadi ne,

“Unaisah” firgigit ta ɗauke idonta daga kallon chief da take Yi, Jin muryar Boss,
da sauri yake tunkarota shigowarshi kenan part din, jallabiya ce a jikin shi, Ya
sanya face mask a fuskarshi, tayi mamakin ganinshi a irin wannan lokacin, abunda
bata sani lokacin da boss Ya ambaci sunanta, Chief owais Ya juya don ganin wanene
ke magana, dai dai sa’adda ita kuma ta kawar da kanta, Natsuwa yai yana dubansu
daga can saman second floor.

“Ba ki yi bacci ba”? Tambayar da boss ya jefa mata kenan a yayin daya ƙaraso
gabanta yaci burki ya tsaya yana kallon fuskarta.

“Banjima da farkawa ba, amma meya hana ka bacci” ta tambaya tana kallon rinannun
idanuwanshi masu dauke da tsantsar damuwa
“Taya zan Iya yin bacci? Bayan kema bakiyi ba”
Matashin murmushin ta ɗan saki, har cikin ranta taji dadin maganarsa, shi kuwa ji
yake kamar ya rungumeta ko dan yaji sanyi aranshi, ya damu da halin da suke aciki
ita da ɗan uwanta, tausayinsu ya hanashi sukuni har ya gaza runtsawa shiyasa ya
fito don yazo ganin su.

“Yakamata ka kwanta ka huta boss, na fahimci ka damu dani, meyasa”?


“Taya bazan damu dake ba? Kefa jinina ce, jinin dake yawo ajikina shi yake yawo
ajikin ki.....” da sauri Ya katse maganar, Jin su6ul da bakan da yai, murmushin
gefen fuska tayi mashi, ga dukkan alamu taji dadin maganarshi

“Boss kayi shiri baka ƙarasa zancen ba? Ni wallahi idan kana Yi min magana sai
inji kamar mahaifina”

“Meyasa kikace haka”?

“Saboda Yana ƙaunata fiye da yadda yake kaunar kansa, ya sadaukar da farin
cikinshi saboda ni, nayi rashin ji aƙuruciyata, na azabtar da daddyna amma duk idan
na tuna ayanzu sai inji haushin kaina......” sambatu take yi mashi sam batasan me
take furtawa ba, abune ya haɗe mata ga radadin da zuciyar ta keyi mata shiyasa take
yi mashi zuba, tana magana hawaye na taruwa acikin idanuwanta.

“Amma meyasa kike jin haushin kanki ayanzu”? Muryarshi araunace ya furta mata
maganar.
Shesshekar kuka ta soma yi mashi tana fadin”saboda nagane cewa bani da masoyi a
duniyar nan daya wuce shi, bani da tamkar shi har abada, Har yau idan na tuna cewa
shine silar duk wani abu dana koya aduniyarnan ba ƙaramin dadi nake ji ba.....”
kasa ƙarasa maganar tayi, sakamakon janyota da yai zuwa jikinshi ya rungumeta
sosai, haɗi da daura hannayenshi saman bayanta yana lallashinta, bata kawo komai
aranta ba, sai dai bugun zuciyarta da taji ya ƙaru, tajima tana mamakin yanayin da
take tsintar kanta idan Boss yana akusa da ita, sakankancewa takeyi taji kamar
daddyn ta ne ya dawo.

“Ya isa haka, ki daina kuka Unaisah, In sha Allah, daddynki zai bayyana, bama ke
kadai ba da sauran ƴan uwanki duk zamu binciko maku danginku”

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, takasa raba jikinta daga nashi, tamkar zata koma
cikinshi.

Duk wannan abun dake faru atsakanin Boss Man da Unaisah, akan idon chief owais,
yayin da yake kur6ar coffee dinsa.

Tunawa da Hijabin da zata daukone yasa tayi saurin furta”boss namanta, alwala
nayi zanje daki na dauko hijabi da prayer mat, yakamata na tafi idan danish yaji na
dade zai Iya biyoni, yanzuma da ƙyar ya bari na fito” ta fada tana raba jikinta
daga nashi.
“Nagode da kulawarka agaremu,”
“Kada ki damu, muje na rakaki ɗakin,”
“Banaso na takura maka, naga idanuwanka sun kaɗa jawur, baccine a idonka yakamata
kaje ka kwanta” ta fada tana kokarin kakaro murmushi
Ruƙo hannunta yai acikin nashi da zolaya yace”saifa na biki Allah, ai tunda baki
runtsa ba nima bazan yi bacciba, zan zauna atare daku har sainaga abunda ya turema
buzu naɗi”
Dariya tadan saki jin maganarshi ta ƙarshe, atare suka jera zuwa bedroom din nasu.
Koda suka ƙarasa dakin, arude ta furta”Boss babu batool fa”! Ta fadi tana
faman zare ido akan gadonsu.

“Calm down ur mind, nasan inda suke, ba sace su akayi ba, abunda ya farune dazu
ya tayar masu da hankulansu, shine na rakasu dakin Ummi, nasan yanzu haka sunyi
nisa acikin baccinsu” ajiyar zuciya ta sauke, har taji sanyi aranta.

“bayin Allah, nasan daƙyar suka Iya runtsawa, musamman Azeeza tafi kowa tsoro a
cikinsu” ta furta hakan tare da kama hanyar closet dinsu, bin bayanta yai da kallo
harta 6ace ma ganin shi.

Maganar amininshi ce ta fado mashi aranshi, a ranar daya kira shi video call yana
daga kwance saman gado shida Angel dinsa.

Tuni idanuwanshi suka cicciko tab da ƙwalla, haƙiƙa yayi babban rashin da bazai
ta6a samun mai maye mashi gurbinshi ba”
A hankali Ya furta”Allah Yajiƙanka aminina”
“Boss mu tafi” muryar unaisa ce fargar da shi ga kallonta, Harta zura hijabin
ajikinta launin milk, Iya gwiwa ta tsaya mata, hannunta a ruƙe da prayer mat.
Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, dama ranta babu daɗi, dauriya kawai take
Yi,
“Meyasa kika 6ata fuska”?
Zumbura mashi baki tai kafin tace”kaine mana, kaƙi jin maganata ni nasan baccine
ke addabarka, amma kaƙi zuwa ka kwanta, kalli idanuwanta har sun canza launi sun yi
jawur da su...” cikin kulawa tayi maganar
In a cool voice ya furta”karki damu dani, babu bacci atare dani, idona ne keyi min
ciwo, kafin na fito daga gida saida na ɗiga magani”
Unaisa sarkin tausayi, duk sai taji ba dadi, jin baida lafiya.
“Allah yabaka lafiya boss, amma dan Allah kaje ka kwanta kayi bacci”
Bakomai ya tuna ba face maganarta lokacin da tana yarintarta, Idan baida lafiya ya
kwanta don yai bacci, saman jikinshi take hayewa tana fadin ai wallahi bazan bari
kayi bacci ba, ka jira sai lokacin da nima zanyi sai muyi atare, idan ta fadi hakan
to bai isa yai bacci ba, dole yajira har zuwa time da zata gama wahalar dashi
tukunna suyi bacci, yayi zurfi acikin tunanin shi muryarta ta dawo dashi
“Ka ƙura min ido kana kallona, ko nayi maka kama da wanine”? mamaki take bashi idan
tana magana.
Adabarbarce ya furta”um...bakomai mu tafi kawai”
Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Suka nufi ƙofar fita daga dakin.

Kafin dawowarsu dakin danish, Tuni Big guy ya kawo mashi fresh fruit, a faffadan
tray ya ajiye mashi saman mattress, abunka ga maciji, ɗai ɗai yake ɗauka da baki
Yana lunkuma shi, Cikin ƙanƙanin lokaci Ya shanye kayan marmarin, bayan Ya kammala
ci, Big guy ya tambayi Salsabeel Ina Unaisah take? Yaga babu ita adakin salsabeel
Yace ta fita dauko hijabin sallah ne, amsa mashi yai da okey, kafin Ya dauki tray
din Ya juya yabar dakin.

Adai dai lokacin daya sauko down hannunshi ruƙe da tray, Unaisah da Boss man suna
kokarin nufar benan,
Da mamaki big guy ya furta”wa nake gani kamar Boss namu? Me ye hana ka runtsawa”?
Fuska asake Boss Ya nufe shi yana fadin”abunda ya hanaka runtsawa nima shi yahana
in runtsa”

Dariya big ya saki”kai dai fadi gaskiya mutumina, nasan me ya hanaka yin bacci,
damuwace ta isheka da fargabar kada maciji ya sari ƴarka, koba haka ba”? Ya faɗa
yana ɗage mashi gira da zolaya.
“Baka da dama Big guy, ai dole na damu, ita kaɗaice fa ƙwallin ƙwal, bugun
zuciyar,”ya fada idanuwanshi akan unaisah wadda tuni Ta haura saman bene don ta isa
ga dakin danish
“Na fahimci ba ƙaramin so ka ke yi ma yarinyarnan taka ba, nima kuma inasonta, me
zai hana ka bani auranta?da zolaya yai maganar
Harara Boss Ya watsa mashi shima da zolayar yace”ka dai bi a hankali, kada
mamallakinta Yaji ka, kaima kasan me zai biyo baya,”
Da sauri Big guy ya toshe baki yana fadin”au namanta, ashefa ka bayar da ita, balle
ma nasan koda baka bada ita ba da wuya ka bani ita, don na fahimci kafison inda
zata huta” dariya boss yasaki yana fadin”kamar ka sani, kaima din ai ba daga baya
ba, sai dai kayi mata tsufa, ina laifin ka nemi ummi mana zata dace dakai.....”
tunkan ya ƙare maganar, Big guy ya galla mashi harara”Allah Ya kiyaye, in rasa
wazan nema sai karuwa”
Boss yace”abar dai kaza cikin gashinta, kaima din ai tubabbe ne, nima labari naji”
“Ina ganin girmanka man, mu bar maganar, bana son tuna baya, Ni bansan ma wani
munafukinne yabaka labari ba, wallahi da zan sani saina takaita jin dadinsa”
Dariya Boss yai ganin yadda ya 6ata fuska.

“Sorry mutumina, zolayatace kawai, ni bansan komai ba, kaine ka kama kanka,”

“Next time idan ka ƙara min wannan wasan, A jikin ƴarka zaka gani” Ya fada tare da
bi ta gefen Boss Ya wuce yana dariya, shima Boss din dariyar yakeyi
“Ai kai ƙaramin ɗan iskane, sai dai ka cika baki indai akan Angel dinane, don kuwa
kasan ko kallon banza kayi mata a jikinka zaka gani,”
Big guy bai juyo ya dube shi ba, Yai tafiyarshi.

Bayan komawar Unaisah dakin, a kishingiɗe ta samu salsabeel harya gaji da zama,
macijin yana nannaɗe gefenshi.

Tayi tunanin bacci yake yi hakan yasa ta soma yin sanɗa tana tafiya duk don kada ta
farkar dashi, shimfida dardumar hannunta tayi, kafin ta daidaita natsuwarta, ta
kabbara sallah.
Boss na kokarin shigowa dakin aka fara kiraye kirayen sallar asuba, daga bakin
kofar ya tsaya yai gyaran murya, salsabeel daya lumshe idanuwanshi jin gyaran
muryar da Boss yai mashine yasashi bude idanuwanshi
“Sannu da kokari, Mun hana ka bacci,” yamutsa fuska salsabeel Yai, bacci yana
neman yaci ƙarfin shi
“Baku kuka hanani bacci ba, ni na hana kaina saboda ɗan uwana” ya fada yana duban
macijin.
Kallon shi Boss Yai, gwanin ban tausayi ya langwa6e kansa, bawan Allah takaicin
duniya ya ishe shi.
Shiga cikin ɗakin Boss Yai, a bakin gadon ya dakata da yin tafiyar yana kallon
Giant snake din
“Bacci yake yi”? Ya jefa ma salsabeel tambayar
“Bazai Iya runtsawaba, idan har ba Ƴar uwarshi tana atare da shi ba, sai kuma idan
ya dawo ainihin halittarsa”
Cikin tausayawa boss yace”kayi hakuri, wata rana sai labari, In sha Allah ƙarshen
wahalarka ne Yazo, wadanda suka yi silar ƙuntata rayuwarka, bi’iznillahi ajalin su
ne yazo, zasu ɗanɗani kuɗarsu har sai sunji dama ba a halitto su a duniyar nan ba,
sai sunyi danasanin rayuwarsu.....” kalamai masu dadi da kwantar da hankali Boss
yake fada ma giant snake din, yayi lamo yana sauraronshi.

“Naji an fara kiran sallar asuba, Bari nashiga toilet inyi alwala, idan na
fito kaima saika shiga ka yi mu tafi masallaci,” yai magabar yana duban salsabeel.
Batare da 6ara lokaci ba, Boss ya shiga toilet ya dauro alwala, bayan ya futo
salsabeel Ya shiga shima yai alwalar,, sallama sukayi ma Unaisah dake zaune saman
darduma, kafin suka tafi.

Kamar jira take Yi, subar ɗakin, jiki na 6ari ta miƙe ta nufi gadon ta haye gefen
shi tana kallonshi, ta fahimci bacci yake ji, hakan yasa ta janyo bargo ta
lullu6asu don ta taimaka mashi yai bacci.

*EX-PRISONERS❤*

Lokacin da Batul ta farka daga bacci, jikinta duk ba daɗi, tamkar mai fama da
zazza6i, mura tayi mata mugun kamu, muryarta daƙyar take fita, fitowa tayi daga
cikin bargon idanuwanta sunyi luhu luhu, ƙoƙari take tabar dakin duk don kada ta
ƙara haɗa ido da ummi, tayi tsammanin zata ganta asaman gadon sai ganinta tay
kwance saman carpet, ta lullu6e half body dinta da bargo, tafi ƙarfin ta haɗa
shimfiɗa da su shine ta dawo kan carpet ta kwanta.
Muryar batul kasa kasa ta ke ambaton sunan parveen,
Daƙyar ta samu parveen ta farka daga bacci, tana faman yin miƙa haɗi da yin
hamma, juyawa tayi 6angaren su Jemimah ta soma tada su daga bacci ɗaya bayan ɗaya
suka farka suna faman mutsustsuke idonsu.

Cikin muryar rada take yi masu magana”ku tashi mu tafi ɗaki, lokacin sallar asuba
yayi,” ruƙo hannun jemimah tayi ta sauko da ita daga saman gadon, Parveen ta ruƙo
hannun Azeeza suka sauko.

“Bana so ta farka ta ganmu, kada ku yi surutu mu lalla6a mu bar mata ɗakinta” ta


faɗa tana dubansu, Jinjina mata kai su ka yi alamar toh.

Cikin takun sanɗa suka nufi ƙofar fita dakin, sai da suka fita Batul ta tuna da
kayan ummi dake a jikinta, dafe kai tayi da hannu ɗaya”nashiga uku ashe ban cire
mata kayanta ba, Parveen ki ruƙe hannun Aziza dana jemimah ku tafi ɗakin mu zan
biyo ku daga baya”

Maƙe kafada jemimah tayi”ni tsoro nake ji, idan abun nan ya ganmu fa”?
“Kada ki damu, babu shi ai, waɗannan mutanan sun kashe shi” daƙyar batul take Yi
masu magana
“Batul baki lafiya? Idanuwanki sun kumbura jawur, muryar ki kamar ba’aji sosai”
Azeeza ce tayi magnar.

Kafin batul ta bata amsa parveen tace”sanyine ya kamata, sai da na hana ta kar6i
rigata amma ta kar6a tasaka”

“Amma ai aunty ummi ta bani kaya na saka, Kawai bana jin daɗine bawani abu ke
damuna ba, Ku tafi ɗaki zan biyoki” Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin.

A tsananin tsoroce suke tafiya suna tunkarar benan, parveen tana aruƙe da hannun
azeeza dana jemimah, har yanzu basu daina jin fargabar macijin ba.

Bayan batul ta koma dakin Ummi cikin sanda take tafiya, harta ƙarasa gaban
gadonta, ta cire mata kayanta, ta ɗauki doguwar rigar parveen data jefar ƙasa, ta
zura a jikinta, Juyawar da zatai keda wuya, taji sautin datse kofar ɗaki, rass taji
gabanta ya fadi ganin ummi atsaye bakin kofar ta goya hannayenta kan ƙirjinta,
fuskarta a murtuke babu annuri, idanuwanta sun ƙanƙance.

Hankalin batul ya tashi matuƙa, agigice ta furta”aunty ummi ina kwana”


Harara ta galla mata”daban kwana ba kin ganni atsaye? Kilbabba uwar iyayi”

Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Ai na cire maki kayanki, gasunan kan gado,
Ni dakinmu zan tafi, wajen unaisah”

“Idan kinga na ƙyale ki kin fita daga dakin nan, to kuwa kin gyara sautin muryarki
ne, wallahi baki isa kija min bala’e ba, Har kayan sanyi na baki, na kuma kashe
sanyin a.c, saboda baƙin hali irin naki saida kika bari mura tayi maki mugun kamu
duk don kija min masifa ko”?

Hawayene suka soma wanke fuskar batul, muryarta na rawa tace”ba haka bane aunty
ummi, nima bayin kaina bane, bansan mura ta kamani har haka ba, dan Allah kibarni
in koma cikin ƴan uwana”

Shu’umin murmushi ummi tayi mata,


“Zan barki ki tafi, amma kafin nan saina fara kawar maki da murar nan, don haka mu
shiga toilet inyi maki wanka da ruwan zafi”

Zazzare ido batul tayi hadi da girgiza kanta”dan Allah aunty ummi ki ƙyaleni, ai
ni ba yarinya bace, da zaki min wanka, ni kawai ki rabu dani nayi maki alƙawarin
babu wanda zaisan ina yin mura”

Ɗaure mata fuska ummi tayi zaki wuce mu shiga toilet ko saina 6ata maki rai”?

Cikin jin ƙunar rai, batul ta maƙe mata kafaɗa”ni bazan shiga ba, Na fada maki
banaso, ki ƙyaleni,” atakure take Yi mata magana, makoshinta radadi yake yi mata.
Ganin ummi na tunkarota ne yasa ta soma ja da baya tana kuka, kokarin kubce mata
tayi da sauri ummi ta damƙo sumar kanta, tajata ta ƙarfi ta shigar da ita toilet
tana fadin”Ke har kin isa ki kufce min, ƙaramar ƴar shila dake, me zan gani a
jikinki? da har kike fadamin ke ba yarinya bace” sautin kukan batul ya cika dakin
ummi, gigitacciyar tsawar data kwatsa matane yasa tayi saurin jan baki tayi shiru,
hawaye na cigaba da bin fuskarta.

Ummi tafi ƙarfinta, da girmanta da komai, Tayi mata wanka da ruwan zafi, tamkar
zata sale mata fatarta, fitowa ummi tayi daga cikin toilet din, ta nufi closet din
kayanta, tana faman sakin murmushin mugunta, riga da wando ta dauko masu kyan
gaske, na saƙa launin pink, waɗannan kayan tsohuwar ajiyace tuntana ƴar shekara sha
bakwai a duniya take 6oyansu, tana matukar son kayan, rigar tana da hula hannunta
dogone.

Komawa toilet din tayi kamar yadda tabar batul haka ta sameta, ta ƙanƙame kanta
jikin bango, dan pant ne ajikinta, hannunta biyu tallabe da kirjinta ta kakkare
boobs dinta.

Jefa mata kayan ummi tayi da sauri ta kar6esu.

“Ina jiranki aɗaki, salon kuma ki daɗe, idan kika ƙara mintuna wani wankan zan
sake yi maki” cike da isa ta furta maganar, kafin ta juya ta fuce daga toilet din,
abakin ƙofar ta dakata tana jiran fitowar batul.

Jin motsin buɗe toilet door dinne yasa ummi kai idonta ga dubanta, har saida taji
gabanta ya fadi, ganin kyan da kayan sukayi ma batul, rigar tayi mata daidai,
wandonma haka, kamar don ita aka saƙa kayan, bata sanya hular ba, yalwatacciyar
sumar kanta ta sauko har gadon bayanta dark brown.

Sai faman ƙanƙame jikinta take yi, ganin yadda ummi ke kallontane yasa ta duƙar
da idanuwanta ƙasa, duk tasha jinin jikinta.

Batasan ya akai ta tsinci kanta dayi ma fuskar batul kallon sani, sai dai tarasa
tuna dawa take yi mata kama.
Matsawa tayi kusa da ita, takai hannu ta ruƙo hular rigar ta sanya mata ita, sai
taga ta ƙara yi mata kyau.

“Ki daina ganin ina kallonki, ba kyau kikayi min ba, Munin fuskarki nake kallo”
shiru Batul batace mata komai ba, bayan ta kammala gyara mata hular rigar, ta nuna
mata gado”ki koma ki kwanta, har zuwa time da muryarki zata dawo dai dai kinji ko”?
Maƙe mata kafaɗa batul tayi”ni bazan kwanta ba, dan Allah kibarni in tafi daki
wajen ƴan uwana, Inason ganin Unaisah” muryarta shaƙe ta furta maganar.
“Wato saboda kinga makwancina shiyasa kika fara rainani ko? Har kina da bakin fadin
Bazaki yi abu ba idan nasaka ki, Dalla ni wuce ciki ko inyi ball dake”

Ƙin matsawa Batul tayi, gani take kamar ummi zata iya kasheta, furucin da tayi
mata jiya sun firgitar da ita, sun kuma tsaya mata aranta.

Zabura tayi da niyar ta nufi kofa don ta gudu, ai kuwa azafafe ummi ta damƙota
kamar ɗiyar roba haka ta ɗaga ta sama, ta nufi gado ta jefar da ita, ta kuma janyo
bargo ta lullu6eta tana fadin”idan kika kuskura kika leƙo koda kankine saina
murƙusheƙi”
Muryar batul da shessheƙar kuka take fadin”aunty ummi dan Allah kibarni in tafi,
banason kwanciyar, ni wajen ƴan uwana zanje” ummi dake tsaye tana kallon bargon
tace”idan kina son fita daga dakin nan to ki fara gyara muryarki”

“Ai ni bansan yadda zan gyarata ba, ki bani magani in sha”

Ta cikin bargo batul take Yi mata magana.

Tunani ta somayi aranta, ina zata samo mata maganin mura? Tasan ba’a rasa dakin
ajiye magani a gidan tun da na jami’ae ne kuma yaran an tanadar masu komai da zasu
buƙata saboda rayuwar kullece aka shirya masu.

Boss man kadai take da contact dinsa, awayarta, daukar wayar tayi dake ajiye on
bedside drawer ta danna ma Boss kira, cikin sa’a ya ɗaga kiran.

Cikin girmamawa ta gaishe da shi”barka da asuba yalla6ai”


On the other hand muryar boss ta amsa mata da cewa”wa’alaikum salam, ummi barka da
safiya”
“Yawwa barka, Allah yasa dai ban katse maka baccinka ba”

“Kada ki damu, idona biyu yanzu nake shirin zuwa cikin gidan, ko akwai wani abu da
kike buƙata”?
“Taimako nakeso kayi min in ba takura, maganin mura nake buƙata”

“Wanene ke baida lafiya”? Da sauri tace”nice zan sha, Yaran dake atare dani
lafiyarsu ƙalau’ amsa mata yai da okey, idan zan shigo gidan zan taho maki da shi”

“Nagode” katse kiran tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, Batul dake a ƙumshe cikin
bargo, abun duniya ya isheta.

Muryarta shake tace”aunty ummi banyi sallar asubaba, kuma ina jin yunwa”
Guntun tsoki ummi taja”kiyi min shiru malama, ni ma ai banyi sallar ba, kuma ina
jin yunwar bawai bana ji ba”

Ta fada Tare da samun wuri daga gefen gadon ta zauna tana gadin Batul, hannunta
ruƙe da wayarta, chatting ta kama yi, batul tayi shiru cikin bargo tana faman matse
ƙwalla.

A katafaren Villa Mallakin Hateem Obinna, haddadiyar daula kuma aljannar duniya
wadda idan ka zura ƙafarka acikinsa sai ka yi tsammanin ƙasar dubai ka shiga,
Hamshaƙin Gidanshi a kewaye yake da Jami’ae sojoji da ƴan sanda, mugun tsaro ake yi
mashi, babu wanda ya isa ya ƙetare gidan hateem cikin sauƙi idan ba Mahaifinsa ba
da yayyansa, amma bayan wadanda kafin mutun ya samu iznin shiga ciki sai ya ci
baƙar wahala don kuwa daga ƙasa har sama zasu bincike ka da na’ura, har ƙwara mutun
ya shiga masarauta yafi mashi sauki, akan Gidan prime minister, tsaruwar ginin
gidan kuwa da haduwarshi ba’a magana, gaba ɗaya Obie estate babu gidan da yakai Na
prime minister In ka cire Villah din Owais.

*Gimbiya Mujeedat👑*

A kishingiɗe take saman Katafaran gadonta na alfarma, kalar na sarakuna waɗanda


suka gaji Arziƙi, gadon a kewaye yake da labulaye launin royal blue, an ƙawata shi
da lallausan zanen gado fari ƙyal, haɗi da matassan kai launin blue and white, gefe
da gefen gadon bedside drawers ne suma launin royal blue, daga saman su Fitilune
masu bada haske launi daban daban, an zuba mata tsadaddun furniture a ɗakinta, ya
ƙawatasu sosai da kayan alatu.

ta ɗaura kanta saman pillow, Rigar dake a jikinta Silk robe ce launin ice blue,
tabi shape dinta ta bayyana dirarran dirin jikinta, A halitta Gimbiya Mujeedat
doguwace, fara sol tana da dogon wuya, hutu ya zauna mata ta ko’ina Allah Ya hore
mata, Kyau kamar ita ta zana kanta, fararen idanuwanta tamkar an ɗiga masu zaiba,
launinsu dark black ne, ga tarin ziraran eye lashes dinta da suka ƙawata kewayen
idanuwanta sun yi mashi rumfa, dogon hacinta a tsaye yake babu lanƙwasa, siraran
la66anta launin ja tamkar na jarirai tsabar ƙarantarsu da laushin fatarsu, tana da
yalwatacciyar sumar kai baƙa wulik mai santsi da silbi, har gadon bayanta,
Tabarakallahu ahsanul khalilin Gimbiya mujeedat maƙurace afagen kyau, uwa uba ta
fito daga tsatson masarautar daular larabawa, bugu da ƙari First Lady ta ƙasar
Canada, ajin farko ce ita, zan iya cewa baba Hateem Ya more mata 😉

Ziririyar sarƙar wuyanta ta zallar diamond ce, haka zalika Ziraran yatsun
hannunta na dama suna sanye da Ring set na Gold komai nata me tsadane ita kanta
lu’u lu’un ce.

Yanayin yadda ta kwanta da alamun kasala atattare da ita, ta ɗan lumshe idanuwanta,
fuskarta sam babu walwala, kamar akwai wani abu dake damunta.

A lokacin da bata yi tsammani ba, muryar prime minister Hateem ta karaɗe


kunnuwanta, sallama ce yai mata yayin da yake shigowa dakin, Cikin shiga ta
jallabiya launin maroon, daddaɗan ƙamshin turarenta dana ƙamshin turaren wuta ne Ya
daki hancinsa Har saida Ya lumshe idanuwanshi, mutunne shi ma’aboci son ƙamshi, sai
kuma Allah Ya haɗa shi da mace ma’abociya son kamshi da son ado, shiyasa a kullum
take ƙara shiga ranshi, soyayyarsu bata tsufa, Idan suna atare da juna daukar kansu
suke Yi tamkar sabbin ma’aurata.

Bata samu damar amsa mashi sallamar shi ba, daƙyar ta iya buɗe idanuwanta da sukayi
mata nauyi, launinsu ya rikiɗa zuwa ja, saboda rashin baccin da batayi ba adaren
jiya kuma shine sila, Ya hanata sukuni, bai ta6a burkice mata ba irin Na jiya, Ƙiri
ƙiri Ya takura kanshi, Ya hana kanshi runtsawa, kuma yaki fada mata abun da ke
damun shi, daga ita har shi jiya babu wanda ya runtsa, saboda ta maida damuwarshi
tata.

Koda ya shigo dakin, a hankali ya daura idanuwanshi kan fuskarta, sai yaji ba
daɗi har cikin zuciyarshi yasan bai kyauta mata ba, tunda ya riga da yasan halinta
na damuwa da damuwarshi.

Daga gaban gadon Ya dakata dayin tafiyar, ya goya hannayenshi on his broad chest
yana fuskantarta.

Ba zato ba tsammani, yaga ta galla mashi harara haɗi da murguɗa mashi ƙaramin
bakinta.

Nan take ya fahimci fushi take yi da shi, ranta ya 6aci.


Cikin harshen turanci tace”Sannu da dawowa”

Ta inda gimbiya mujeedat take burge shi, duk mun fushin da zatayi dashi hakan bai
hanata kula da shi

“Yawwa, fatan na same ki lafiya”

Yamutsa fuska tayi fuskarta babu annuri ta soma magana tamkar bata son furtata.

“Mijina baka kyauta min ba, ka hana kanka runtsawa nima kuma ka hanani runtsawa,
nayi koƙarin faranta maka duk don na kawar maka da damuwarka amma babu abunda ya
canza, Ka jefa ni cikin wani hali daga daren Jiya zuwa yau, meyasa ba zaka fadamin
meke damunka ba? Ko ban isa nayi maka magani bane? Nasan ka yarda dani, sannan baka
6oye min komai, sirrinka nawa ne amma meyasa jiya kaƙi fadamin damuwarka” sautin
muryarta tamkar ana busa sarewa tsabar daɗinta.

Idanuwanta aruntse take yi mashi magana, don ta fahimci idan tana kallon cikin
idanuwanshi bazata samu ƙwarin gwiwar yi mashi magana ba”

Sauke hannayenshi yai daga saman kirjinshi, ya zagayo ta gefen da take a kwance
Ya zauna, yana duban fuskarta
Ƙayataccen murnushine kwance kan la66ansa, yasan ta kan mace, idan ranta ya 6aci
cikin sauƙi yake faranta mata

“Uwar gida sarautar mata, Gimbiyata, Ina neman afwarki ranki shi daɗe, bai
kamata gimbiya tana fushi da bawanta ba, Ni fa a karkashin inuwarki nake, da
taimakonki nake samun natsuwa da kwanciyar hankali, taya zanso na 6ata maki rai?
Bayan kece linzamin dake sarrafa ni....”
Tun da yafara gaya mata daɗaɗan kalamansa, ta fara sassauta fushin fuskarta,
A hankali ta buɗe idanuwanta kan fuskarshi, da sauri ya kama kunnuwansa Yana
fadin”Am sorry My wife, na gane kuskurena”
Ta6e mashi baki tayi”Ni so nake ka fadamin meke damunka? Da har yai silar hanaka
runtsawa, kalli fuskarka duk ta yamutse, idanuwanka sun ƙanƙance saboda rashin
baccin da baka yi ba” ta faɗa tana faman 6ata fuska, yayi shiru yana kallonta
batare daya furta mata komai ba.

“Kai nake sauraro! Meke damunka? Sannan naji kana waya ɗazu, akan za’a tura da jet
zuwa sudan, wa za’a ɗauko”? Ta jefa mashi tambayar cike da son jin amsar shi.

Ya rasa amsar da zai bata, Ta kafe shi da ido.


Gyara muryarsa yadanyi kafin yafara magana a tsanake.

“Sheikh imam nake son gani, baya a ƙasarne ya tafi sudan, Ina buƙatar ganinsa da
gaggawa akwai taimakon da zaiyi mani”

Fuskarta da alamun mamaki ta furta”meyasa kake son ganin shi? Wani kalar taimako
zaiyi maka”

“Wani matashin yarone yake fama da aljanu sun hana rayuwarshi sakat, jiya ina
zaune tare da baba muna yin firar yaushe rabo, a lokacin da bamuyi tsammani ba,
yaron ya faɗo falon gwanin ban tausayi, duk mai imani idan yaji irin jarabtar da
yaron yake fuskanta sai ya tausaya mashi.....” tun da ya fara magana gimbiya
mujeedat ta yunƙura ta miƙe daga zaune tana dubanshi, Ya fayyace mata komai sai dai
bai faɗa mata da suffar da ya ga yaron ba.

“Na yanke shawarar yin magana da sheikh Imam akan halin da yaron yake aciki, Ina
da tabbacin zai taimaka mashi In sha allah, yanzu haka da nake yi maki magana,
sheikh imam Yana akan hanya, Ina tsammanin nan da ƙarfe goma jirgin daya ɗauko shi
zai yi sauka a nigeria.

Yanayin fuskartane Ya canza, yayin da take kallonshi, Ya rasa gane kallon menene
take yi mashi, har dai yagaza jurewa jin shirun yayi yawa yace”baki fahimci abunda
nake fadi bane? Ko bakiji dadi bane”?
Girgiza mashi kai tayi”ko ɗaya mijina, wani abune yadan bani mamaki, nasan halinka
ne yin taimako, indai abune daya shafi aikin Allah kana akan gaba, amma tunda nake
arayuwata ban ta6a ganin tausayi da ya kai wannan ba atare dakai, saboda yaron jiya
ba ka yi bacci ba, aduk lokacin da ka dawo gida a yanayi na damu nasan yadda zan
shawo kanka in kwantar maka da hankalinta harma kayi bacci, amma adaren jiya saboda
damuwar halin da yaron yake, waɗannan dabarun nawa basuyi maka aiki ba, bayan haka
ka tura da jirgin da zai dauko malamin da zai duba shi daga Sudan zuwa Nigeria,
saboda kana buƙatarshi da gaggawa don ya duba yaron....” ta faɗa fuskarta da alamun
ruɗani, yayin da Hateem ya natsu yana sauraronta abunda bata sani ba ayanzun ma da
take yi mashi magana hankalin shi yafi karkata kan agogon dake sanye a wrist din
hannun shi, burinshi goma ta buga.

“Abunda yafi ɗaure min kai mijina, wanene yaron? Menene alaƙarka da shi? Yanayin
yadda ka nuna damuwa akanshi ko ɗan cikin ka sai haka”

Jim ya ɗanyi kafin ya furta”bani da alaƙa da shi, bansan shi ba! Kuma ban ta6a
ganin shi ba, kamar yadda na faɗa maki adaren Jiya idanuwana suka fara yin tozali
da shi, tun daganan sai naji ƙaunarsa ta kama ni, har naji ina son na taimaka
mashi, sai nake jima kamar nike da alhakin ciwon shi, idan har ban taimaka mashi
yaji sauƙi ba Allah zai iya kamani da laifin ƙin tallafa masa da banyi ba”

Murmushin gefen fuska Gimbiya mujeedat ta sakar mashi har fararen hakoranta suka
bayyana.
“Kai din na dabanne mijina” ta faɗa tana matsawa kusa dashi, ta ɗaura hannunta na
dama saman sumar kanshi.

“Samun miji kamarka a duniyar nan abune mai wuya, kana da tausayi da jinƙan na ƙasa
dakaina, sannan kowa naka ne, burinka ka faranta ma wanda yake acikin kunci koda ta
silar hakan kai zaka rasa naka farin cikin, ni kaina ina ilmantuwa da kyawawan
ɗabi’unka da halayanka, shiyasa nake alfaharin mallakarka da nayi a matsayin
mijina” lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kalamanta ba ƙaramin faranta mashi suke Yi ba,
tamkar tana ƙarfafa mashi gwiwane.

Zame hannunta tayi daga kan sumar shi zuwa gefen fuskarshi idanuwansu cikin na
juna
“Kamar yadda ka sani, duk abunda kakeso nima inason shi, koda bana son shi saina yi
kokarin koya ma kaina yadda zanso shi saboda mijina yana son shi, don haka nima ina
goyan bayanka akan Yaron, Allah ya baka sa’a mijina ya cika maka burinka na ganin
yaron ya samu lafiya, A shirye nake dana bada gudummuwata wurin ganin mun inganta
rayuwarshi”
Murmushine ya bayyana akan fuskar prime minister, kallonta kadai da yake yi natsuwa
yake samu, musamman idan tana ƙarfafa mashi gwiwa da daɗaɗan kalamanta.
“In sha Allah zamuyi nasara, yaushe zaka bani iznin zuwa ganin yaron”?

“Na yanke shawara idan yaji sauƙi, zan gayyace shi zuwa gidan mu, zamu shirya
mashi dinner.”

Tsantsar farin cikine akan fuskarta”naji dadin jin hakan mijina, wallahi har na
ƙosa naganshi, duk na kagu gashi bazamu daɗe a ƙasar ba, kwanaki kadan suka rage
mana” ta fada tana 6ata fuska alamar bataso hakan ba.
Damƙo hannunta yai da take kokarin shafa wuyanshi, fari sol dashi, ga wani
shu’umin kamshi dake fita sako da lungu na jikinta, sumbatar tafin hannu yai, ba
tare da ya sake shi ba ya dago da reddish eyes dinshi akan fuskarta”yaron marayane
bashi da kowa, Owais ne ke kula da su, zan nemi alfarmar yabar min shi mu tafi
canada atare, inaso ya maye min gurbin abunda narasa” sai yanzu ta fahimci
damuwarshi.

Tausayinshi ne ya kamata, tuntuni tasan yana da burin samun ɗa Namiji, yaso ta ƙara
haifa mashi ƴa’ƴa sai dai shiru babu alamun zasu sake samun ƙaruwa, kuma lafiyarta
ƙalau saboda shi yasa bata yin tsarin Iyali, Allah ne bai nufa zata ƙara haihuwar
ba.

Kafin ta buɗe baki tayi mashi magana, wayarsa dake ajiye cikin aljihun shi ta
soma yin ringing, ya riga da yasan wanene Ya kirashi.
Da sauri Ya saki hannun Gimbiyarsa, Ya zura hannu ya zaro wayar picking call din
yai tare da karata a kunnanshi, gimbiya mujeedat ta kura mashi ido tana kallon shi
“Alhamdulillah, Allah ya kawo ku lafiya,” iya abun da taji ya furta kenan, zame
wayar yai daga kunnanshi yana dubanta yace”sun sauka lafiya”
Gimbiya mujeedat tace’shiyasa naga farin ciki akan fuskarka, sheik imam yaƙaraso
kenan, bari nayi magana da masu aiki su shirya maku breakfast dinku”
Ta fada tana kokarin daukar phone dake ajiye on nightstand da sauri ya ruƙo
hannunta, ta dago da ido suka kalli juna
“An shirya mashi breakfast dinshi, tun acikin jirgi, ina da tabbacin babu yunwa ko
gajiya atare da shi, nafi buƙatar idan ya ƙaraso mu tafi gidan Owais din”
“Amma kaifa? Baka ci komai ba, Yakamata kayi breakfast dinka, zaka fi samun
kuzari”
Girgiza mata kai yai”Bana buƙata, saboda bani da natsuwar cin abinci, Idan har
yaron nan bai dawo dai dai ba, nafi son idan Ya samu sauƙi, muci abincin atare da
shi”
Tsantsar mamakin kalamansa ne ya daure mata kai, bata ta6a ganin ƙauna kalar wannan
ba, Ko a shirin film.
“Amma kasan bana iya yin breakfast ba atare dakai ba, idan har baka ci ba, nima
bazan ci komai ba, har sai ka dawo gidan” cikin tausasa harshe tayi maganar.

“Yau kawai, Kiyi hakuri kiyi breakfast tare da su Yazrin, bazan jima ba, in sha
Allah atare zamu yi lunch dinmu”

Kwa6e mashi fuska tayi hadi da marairaice mashi tamkar zatayi mashi shagwa6a ta
furta”bazan takura maka ba, Na kar6i uzurinka”

“Ki tashi ki shirya inaso ku gaisa da shekh imam kafin mu wuce gidan owais” amsa
mashi tayi da toh, kafin ta sauko daga saman gadon, shima ya miƙe yana bin bayanta
da kallo, har ta 6ace ma ganinsa, jim kadan ta fito sanye da Abaya launin Maroon
tayi rolling mayafi akanta, ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka nufi kofar fita
daga dakin.
Lokacin da suka shigo babban katafaren palourn gidan, masu yi masu hidimane suke
ta gudanar da aikace aikacen su, kowan nan su sanye da uniform baƙin wando da farar
shirt, matasan ƴan mata, duk inda Suka gifta jiki na 6ari suke gaishe dasu cikin
girmamawa, yayin da su kuma suke amsa masu da fara’a.

Yanke shawarar zuwa bedrooms din Ƴa’ƴan su suka Yi, kafin ƙarasowar Ya sheikh,
Yana da buƙatar suma su kasance cikin shiri donsu yi mashi kyakkyawar tarba.

elevator suka hau ta daukesu zuwa upstairs, bayan ta sauke su suka fito batare
da sun saki hannayensu da suka ruƙe acikin na juna ba, kaitsaye suka nufi bedroom
din ƴan matan su.

Gaba ɗaya ta tattara hankalinta akan Apple laptop din dake agabanta, yayin da take
zaune a tsakiyar katafaren gadonta dake acikin hamshaƙin ɗakin kwananta daya gaji
da haɗuwa, ko dakin sarauniya Albarka, farace sol kamanninta sak dana Mahaifinta
Hateem, yadda kasan ta macen aljanna saboda kyanta da dirinta, kamanninta sun 6aci
dana Hateem, tamkar yayi kakinta, Hasken fatarta ne kadai ta dauko na mom mujeedat
da doguwar sumar kanta, mace ce mai aji, mai ji da ƙasaita da izza, bakowa bace
wannan face NAZLI, itace first born dinsu, a ƙalla zata kai shekara ashirin da
takwas a duniya, tana asanye da lace Camisole daga sama ta ɗaura silk robe launin
hot pink, a tsanake take operating laptop dinta cikin ƙwarewa, yayin da kyawawan
idanuwanta dake a manne da farin glass suke akan screen din laptop nata, daga gefen
gadon ƙayataccen round table ne daga saman shi china tea set ne, jefi jefi takan
kai hannu ta dauki cup ta kur6i coffee din dake aciki, Nazli agogo sarkin aiki bata
gajiya tana da hazaƙa da ƙwarewa a 6angaren Iya kasuwanci, Company guda take juyawa
na mahaifinsu dake a ƙasar Canada, ƙamshin turaren jikinta ya buɗe ko’ina na room
dinta, hatta sumar kanta kamshin turaren data turara ma gashinta ne ke fita, kullum
ne sai ta turara jikinta da gashin kanta, Nazli badai tsafta ba.

“Assalamu alaikum” Muryoyinsu ne suka janyo hankalinta ga duban ƙofar shigowa room
dinta dake a kulle, daga inda take tana Iya hangen su ta cikin kofar, saukowa tayi
daga saman gadon, sumar kanta ta rufe bayanta tamkar hijabi tayi mata, daura idonta
tayi akan cashmere slippers dinta dake ajiye saman lallausan carpet, ta zura su
cikin kafarta, kafin ta nufi kofar cikin takun izza, ta sanya hannu biyu ta ruko
handle din kofar ta buɗe ta.
Fuskokinsu dauke da murmushi suke kallonta, sai dai ita babu alamun murmushi akan
fuskarta, haka take bata da fara’a, taji dadin ganinsu amma bazaka Iya gane hakan
ta yanayinta ba saboda tsabar ji da izzarta,
Cikin harshen turanci tace

“Good morning, Mom and Dad! I’m so glad to see you, yau kun riga ni zuwa room dina,
yanzu nake koƙarin kammala aikin da nakeyi a laptop....”

Ta ƙare maganar tare da matsawa ta rungume daddynta, hannu biyu ya daura saman
bayanta”barka da safiya daughter, Ina fata kin tashi cikin koshin lafiya”

Muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mashi da cewa”

“I’m doing well, Dad. I’ve been thinking about you since yesterday. I’ve missed
you.”

Gimbiya mujeedat tace”oh shi kaɗai ki ka gani shiyasa kika rungume shi ko? Da
zolaya tayi maganar.

Ɗagowa Nazli tayi tare da miƙa hannu zata rungume mujeedat, da sauri gimbiya
mujeedat taja da baya tana fadin”nayi fushi, ba tun yauba na lura kinfi ji da
daddynki, shiyasa nima nafi ji da Yazrin daboda tafi nuna damuwa akaina”

Marairaice mata fuska Nazli tayi haɗi da kama kunnanta”agafarce ni sanyin


idaniyata, mahaifiyata abun alfaharina”
Sakin fuska mujeedat tayi”nayi hakuri amma kada ki ƙara yi min hakan, Daga yau ni
zaki fara hugging kafin daddynki” ta faɗa tana kallon Hateem dake kallonsu,
fuskarshi dauke da murmushi yace”na fahimci kishi kike yi dani akan Nazli, Yarinya
tafi son ubanta, da ni da ita ƙaunace mai ƙarfi, baki ga kamannin fuskarmu ba?
Shiyasa take ji dani, ke kuma kije da Yazrin itace take kama dake”

Farfari tayi mashi da ido batare datace komai ba, ta rungumo nazli ajikinta tana
ɗan bubbuga bayanta da hannu tace”sannu agogo sarkin aiki, tun da sassafe ko
breakfast bakiyi ba kin fara danna laptop, Ina fata na same ki lafiya”?
Ɗagowa tayi da kanta tana fadin”Ina lafiya mommy, bana so aiki yai min yawa
shiyasa nake ragewa” ta fada tana dubansu.

“Naji dadin ganinku, duk da ni yakama naje na sameku, ban samu damar yin hakan ba,”

Prime minister yace”bakomai daughter, muma munji dadin ganinki, Inaso ki shirya
Zanyi baƙo Ƴan mintuna suka rage su ƙaraso, daga sudan zaizo, gaisawa zakuyi da
shi,”
Batare da ta tambaye shi wanene zaizo ba tace”in sha Allah daddy, yanzu zan sauko
down”

Amsa mata yai da toh, kafin ya dubi mujeedat, muje ko” ya runƙo hannunta suka
juyawa zuwa dakin Yazrin,

A lokacin Yazrin tana daga kwance cikin bathtub dake a bathroom dinta, ta jiƙe
jikinta da ruwan kumfa mai ɗumi, ta lumshe idanuwanta yayin da take shaƙar ƙamshin
bath soft dinta daya karaɗe toilet din tamkar an fesa turare, A kalla zata kai
shekaru ashirin da biyar, Yazrin ƙarshe ce afagen haduwa bata baro komai na
mahaifiyarta mujeedat ba, launin fatartane kadai kalar na hateem, haskenta bai kai
na mujeedat ba, daga ita har Yazrin babu wanda yafi wani kyau, ta inda suka
banbanta Yazrin tafi Nazli sauƙin Kai da iya mu’amala da mutane, Ita Nazli bata son
bare, ƙiwuya gareta kamar ƙaramar yarinya ga ji da izza, magana ma wuyar furtata
take ji.

Sautin ƙarar door belt ne ya katse mata jin daɗinta, A hanzarce ta ɗaure
jikinta da ruwan dumi, kafin ta fito ta ruƙo towel dake sagale jikin hanger ta
ɗaure qugunta da shi,
Shigowa Bedroom din tayi da sauri ta nufi wardrobe dinta, shaf shaf ta zura
jallabiya a jikinta, ko tsane jikinta bata samu damar yi ba, sumar kanta duk ta
nannaɗe saman kafadunta.

Buɗe kofar ɗakin tayi fuskarta dauke da kayataccen murmushi, dimples dinta biyu
sun lotsa
Su kansu da sukayi tozali da ita saida suka saki fara’a, Yarinyar akwai shiga rai,
da wuya kaga fuskarta adaure, kafin su bude baki suyi mata magana ta ware
hannayenta biyu ta hadasu ta rungume tana fadin”Mom dad, tunkafin nazo gaishe ku
kun riga ni zuwa, kunsa naji nauyin hada ido daku”

Ta faɗa tare da ɗagowa da kanta tana faman kare fuskarta da tafin hannunta
Dariya kowan nan su yasaki, Prime minister yace”barka da safiya daughter, fatan
mun same ki lafiya”? Jinjina mashi kai tayi”lafiyalou daddy, amma ni baku kyauta
min ba, maimakon ku bari ni in fara zuwa gaishe daku” ta fada tana bubbuga
ƙafafuwanta da shagwa6a.

“Ladar da nake kwaɗayin samu, Kun rigani kwashe ta” dariya mujeedat tasaki tana
fadin”Wato ke har yanzu baki girma da shagwa6a ba”

Hateem yace”barta tayi abunta, don bata da ƙanine shiyasa take yi mana shagwa6a”

Nuna kanta tayi da yatsanta”saboda nice auta mommy, dagani babu ƙari, kunga kuwa
dole nayi shagwa6a” ta fada tana ruƙe masu qugu,
Ba ƙaramin nishaɗi take basu ba, Hateem yace”baki fada mana ya kika wayi gari ba,”

“Na tashi lafiya daddy, tun safe nasha coffe, yanzu haka wanka nakeyi a toilet
naji ƙarar knocking dinku shiyasa na fito”

“Kina nufin baki ƙarasa wankan ba”? Acewar mujeeda.


Yazrin tace”tun ɗazu fa na kammala, kawai inajin daɗin kwanciya acikin ruwane”

“Okey, Ki koma ciki ki shirya muna jiranku a downstairs, daddynku ne zai yi bako
daga kasar sudan, yanaso ku gaisa dashine”

Yazrin tace”okey mom, bari na shiga ciki in shirya”

Ta fada tare da kallon Daddynta, harta buɗe baki zatayi mashi magana, sautin ƙarar
dirar motocin dake shigowa gidan nasu ya katse mata hanzarinta, muryarta tamkar
tame yin raɗa ta furta”bakon ya karaso kenan, bari nayi sauri naje na sanya kayan
mutunci” ta juya da sauri ta shige cikin dakin
Murmushi kowan nan su yasaki, mujeedat tace”yazrin kenan, tana bani nishaɗi, sai
dai narasa gane halin wa ta dauko atsakanin nida kai”
Nuna ta yai da yatsa”ke mana, har sai an fadi, ni dai kin san ba haka nake ba,
idan kika dubi ɗabi’un Nazli sak kalar nawane”
Hararar zolaya ta yi mashi”nazli fa hada izza ta sarauta ke ɗawainiya da ita, kai
ina kaga sarauta? Nice na gajeta, sai dai ta 6angaren siyasa nan kafi karfi, kuma
shi ɗan siyasa da fara’a aka sanshi, hakan na nufin halinkane yazrin ta dauko bani
ba”

“Gorin sarauta zaki yi min”? Ya faɗa yana kanne mata ido.

Tana dariya tace”ni dai bance ba, ai kafi ƙarfin ayi maka gori, dani dakai babban
gorone magogin ƙarfe”

Ta fada tare da ruƙo hannun shi”muje kada su jimu shiru, ina tunanin sune suka
ƙaraso” atare suka nufi down stair.

Adai dai lokacin zungureriyar motar da ta ɗauko Sheikh imam daga airport, ta karaso
bakin entry hall nagidan Prime minister a hankali tayi parking, gaba da bayanta
motocin sojoji ne da suka dauko shi domin bashi tsaro, fitowa sukayi daga cikin
motocinsu, wani ƙato daga cikinsu ya buɗe mashi murfin mota, A hankali sheikh Imam
malik Ya zuro kafarsa ta dama dake asanye cikin takalma na alfarma, kafin Ya ƙarasa
fitowa, masha Allah, magadan annabawa, kallon ɗaya zakayi mashi ka shaida
maluntakarsa, yayi shiga ta alfarma shiga ta larabawan saudi arebiya, farar throbe
ce, daga sama ya daura wata shara sharar riga, kanshi yana asanye da kufi ƴar
karamar hula ta malamai, an nannaɗeta da black turban, Yana da godon gemu, babban
mutunne ya manyata don harya fara tsufa gashin gemunshi hada furfura ta manyantaka,
duhun fatarsa mai kyau ne, kai daga ganin shi baida wasa irin malaman nan ne masu
zafi akan addini, babu tsoro a idanuwanshi, mutunne mai cikar kamala, ya shahara a
6angaren wa’anzartawa da yin da’awa ta addinin musulunci, yayi gwagwarmaya a
kasashe daban daban babu inda bai shiga, kuma yana cin nasara akan da’awarsa,
shaidanun aljanu kansu tsoronshi suke Ji, Suna jin shakkar zama a inda shekh imam
malik yake, mutunne shi mai koyi da sunna ta manzon Allah SAW, Ya ruƙe Allah ɗaya
azuciyarshi, kainuwane shi dashen Allah, badai mutun ba sai Allah, ta ko’ina
jikinshi ƙamshin turarensa ne mai dadin shaƙa a hanci, hannun shi na dama ruƙe da
cazbaha.

A hankali Yake bin ko’ina da kallo, Yayin da yake shaƙar kamshin iskar data
gauraya da ƙamshin turarensa.

“Ya mu’allim, mu ƙarasa shiga ciki,” ɗaya daga cikin Sojojin ne yai mashi magana
haɗi da nuna mashi kofar shiga babban falon, ɗaga kafarshi yai atsanake yake yin
tafiya, suna gab da zasu shiga falon, Prime minister ya fito tare da gimbiya
majeedat, Murmushin dake kan fuskokinsu ne ya ƙara faɗaɗa, da sauri hateem Ya mika
mashi hannu suka gaisa cikin girmamawa”Marhaban bika babana, barka da sauka, ya
gajiyar tafiya” ya fada tare da rungumeshi, bayan sun raba jikinsu daga na juna
Sheikh imam yace”ai ni babu gajiya atare dani, ni da aka gatantani kamar wani
basarake haka aka daukoni a privet jet, hankali akwance naci na koshi na cika
tumbina” Ya fada yana nuna tumbinshi da cazbahar hannunshi, gaba daya suka sanya
dariya gwanin ban sha’awa, sheikh imam mutunne mai son barkwanci amma fa sai idan
yaso.

Prime minister yace”Akara makallah ai kafi karfin basarake awurinmu, ku fa


magadan annabawane, kunfi duk wani mai muƙami a karkashin tafin kafarku Yake”

Murmushi Shekh imam Yasaki, Tare da daura idanuwanshi kan fuskar Gimbiya mujeedat,
kafin yayi magana tayi saurin gaishe shi cikin harshen larabci.

Da zolaya yace”Hateem dama ana ganin fuskar matarka? Ya akai yau baka rufe lu’u
lu’un ka ba”? Koba ita bace matar nan da ake yi mana 6oyanta ba? Kodai Ƴarce”?
Kunyace ta rufe gimbiya mujeedat, Ta sanya hannu ɗaya ta kare fuskarta
Hatta jami’an dake a kewaye da Ya shekh Imam saida suka saki murmushi .

Dariya prime minister yasaki a fakaice ya harari Jami’an dake atsaitsaye suna
kallonsu, jiki na 6ari suka juya kowa yakama gabanshi, don sun fahimci me yake
nufi, wato suna kalle mashi matarshi.

“Ya sheikh Mu ƙarasa cikin falon, mun barka atsaye gashi ka kwaso gajiya” prime
minister ya fada tare da ruƙo hannun shi, Suka nufi babban falon Gidan, Gimbiya
mujeedat tana abiye da su.

“Hateem Irin wannan daula haka? Anya kuwa kuna tunawa da mutuwa? Ka ajiye lu’u
lu’u agidanka ga kuma kayan alatu ta ko’ina, maimakon ku bari sai mun shiga Aljana
muji daɗi” Ya faɗa yana Jijjiga cazbahar hannunshi, Dariya suka sanya gaba dayansu,
A saman Royal sofa kowan nan su Ya zauna, suna fuskantar juna da sheikh imam, sai
faman jinjina kai yake yi yana bin gidan da kallo, duk maganar da sheikh imam zaiyi
yanayin amfani da harshen turanci saboda mujeedat yasan bata jin hausa sai dai
turanci da larabci.

“Yanzu kai hateem, Har kake iya kwana acikin daular nan? Wannan haɗuwa haka ai
sai mutun ya manta da tur6aya aka halicce shi”
Murmushi suka saki suna dubanshi
Sautin takun takalman Yazrin da Nazli ne Ya janyo hankulansu ga dubansu,
Hannunsu ruƙe cikin na juna suke yin tafiya suna tunkarosu, kowaccensu ta yafa
mayafi akanta,
Bayan sun ƙaraso, Cikin girmamawa suka gaishe da shekh Imam, Abunda Ya burgeshi da
yaran tarbiyarsu, A saman lallausan carpet din dake a atsakankanin Royal sofa din
suka zauna kowaccensu ta nade kafafuwanta
“Masha Allah, Matan hurul aini har a duniya, Hateem, wacce zaka bani acikinsu in
cike sunnah”? Ya faɗa yana duban faces din Yazrin da Nazli, Yazrin sai famam sakar
mashi murmushi take Yi, Nazli kuwa tunda ta gaishe dashi ta sunnar da kanta ƙasa.
“Duk wadda ka za6a malam, zamu baka Ita” acewar mujeedat,
Shekh imam yace”Uwargida maganarnan taki bata kai zuci ba, ni nasan kin faɗine
kawai, taya zaku ba yarinya auran dattijo? Mai jan cazba, balle ƴan matan zamani
basu son auran malamai”
Murmushi kowannansu yasaki, banda Nazli.
Biyu daga cikin masu aikin gidanne suka nufo falon, hannunsu ruƙe da faɗaɗan
farantai daga sama an jera drinks masu sanyi da snacks.
Tunkafin su karaso sheikh imam yace”waɗannan fa? Badai ni zasu kawo mawa ba?
Bayan abincin da naci acikin jirgi har wani ƙari za’ayi min? A’a gaskiya Ni a koshe
nake, Ko ruwa bana jin zai Iya wucewa ta makoshi na”
Prime minister yace”babana adai daure ko ruwan ne kasha,”
Gyaɗa kai yai toh, naji iya ruwan zansha, Asaman carpet suka daura farantan, mai
aikince ta zuba mashi Apple juice mai sanyi a cup ta miƙa mashi, Yasa hannu ya
kar6a, Kur6a uku yai ya dawo da dubanshi gasu Nazli”ƴan matan hateem ina fata na
same ku lafiya? Ya karatu? Ko da yake nasan kun kammala, to Ya aiki”
Atare suka amsa mashi da cewa”lafiyalou Alhamdulillah,” jinjina kanshi yai”Masha
Allah,” bayan ya ajiye cup din alamar ya kammala sha, Prime minister hateem
Yace”nasan yanzu ka kwaso gajiya, ko zamu bari zuwa anjima idan ka huta sai mu fara
shiga gida ku gaisa da baba kafin mu wuce can gidan Owais din inda Yaron yake”?
Girgiza kai sheikh imam yai”A’a, tun da mahaifin naku baisan da zuwana ba, to ba
yanzu zanje gaishe shi ba, nafi buƙatar ganin yaron, don agaskiya ni babu gajiya
atare dani, ka tashi mu tafi kawai,”
Kallon mujeedat Hateem yai”zamu tafi, in sha Allah bazamu daɗe ba, a taya mu da
addu’a” murmushi tasakar mashi”ubangiji Allah yasa ayi asa’a, Ina yi maku fatan
alkhairi” amsa mata yai da ameen, kafin ya maida dubanshi gasu Nazli da
Yazrin”daughters ku tayamu da addu’a, ga mommynku nan zatayi maku bayanin komai
dangane da zuwa sheikh imam” amsa mashi sukayi datoh, kafin ya ɗago Ya kalli Ya
sheik wanda tuni Ya miƙe tsaye, miƙewa hateem yai atare suka nufi kofar fita falon,
tunkafin su ƙarasa Jami’en dake atsaye bakin motar data dauko sheikh daga Airport
Yai saurin bude masu motar, Bayan sun shiga daga ciki, jami’en Ya zauna a driver’s
seat Ya tashi motar, atsanake Yake yin driving dinsu........

*Chief Owais✊❤*

Tun bayan daya dawo daga masallaci, Yin sallar asuba bacci ya addabi idanuwanshi,
adaddafe ya shiga bathroom yai wanka, within minutes ya fito waist dinshi ɗaure da
white towel, kan mirror chair ya zauna da niyar ya kimtsa kanshi, sai dai yakasa
tabuka komai saboda kasalar data kame sassan jikin shi, idan har ba baccin nan yai
ba to kuwa bazai ta6a samun sukuni ba, kyawawan idanuwanshi sunyi mashi nauyi
daƙyar yake iya buɗe su, miƙewa yai bai nufi ko’ina ba sai saman katafaren
gadonshi, Ya haye ya kwanta tare da jan bargo ya lullu6e rabin jikinsa, In a short
time bacci yai awon gaba da shi.

Tsawon awanni yanata sharar baccinsa, tun karfe shida har goma da rabi ta buga,
Yayin da numfashinshi ke fita cikin natsuwa da kwanciyar hankali, phone dinsa dake
ajiye gaban dressing mirror ta soma yin ringing, da zarar kiran ya katse wani ke
shigowa, ringin din ya fara takura mashi, mutsu mutsun farkawa daga bacci ya
somayi, A hankali Ya ware fararen idanuwanshi dake fuskantar ceillin din dakin
nashi
Tsawon minutes, kafin Ya laluba hannunshi Cikin kasala Ya ruƙo wayar ya duba sunan
me kiranshi, sunan Uncle Hateem ne Ya bayyana akan screen din wayar,
Kiran harya kusa katsewa yai saurin yin picking, tare da manna wayar akan kunnansa
“My son, Ina fata ban takura maka ba”
Yamutsa fuskarshi yadan kafin ya furta”Barka da safiya uncle, fatan ka tashi
lafiya”?
“Lafiyalou, naji muryarka da alamun bacci bai isheka ba”
“Kiran wayarka ne Ya tashi ni daga bacci, Ina fata lafiya”
“Banji dadiba amma kayi hakuri da takura makan da nayi, ni kaina bansan dililin
dayasa na damu da yaron ba”
“Ba damuwa uncle”
“Yanzu haka da nakeyi maka magana Muna akan hanyar zuwa Gidan naka tare da sheikh
imam”
Lumshe ido owais yai har cikin ranshi yaji dadin jin zuwan Sheikh imam
“Ina yi mashi barka da zuwa, Allah ya kawo ku lafiya” Hateem Ya amsa mashi da amen
mun gode son,” daga haka sukayi sallama da juna.
Daura wayar yai saman side drawer ya sauko daga saman gadon Ya nufi dressing room
din dakin shi, badajimawa ba ya fito sanye da jallabiya launin sky blue, tayi
bala’en yi mashi kyau, Gaban dressing mirror din dakin ya tsaya tare dakai hannu
cikin jerin turarurrukansa ɗaya bayan ɗaya yake dauka yana feshe jikinshi, tuni
ƙamshinshi ya karaɗe dakin.
Diamond wrist watch din shi dake ajiye gaban mirror ya dauko Ya zura a
hannunsa, Kafin Ya miƙa hannu Ya dauki Phone dinsa, A tsanake Yake pressing dinta,
Layin Boss Ya danna ma Kira, Bugu Uku Yai picking, gaisawa suka farayi kafin Ya
furta”Sheikh Imam Ya ƙaraso, Ina buƙatar ganin kowannanku a main falo, domin mu
tarbesa”

Boss Ya amsa mashi da Toh, In sha Allah, Yanzu zan sanar da su” daga haka Yai
rejecting kiran.

A dai dai lokacin, Unaisah ta kuma farkawa daga baccin da yayi awon gaba dasu ita
da giant snake din, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadon, tana tafiya tana
waiwayon gadon, ta kudundune shi da bargo, ta ƙagu da son ganin ƴan uwanta shiyasa
zata fita taje gare su, batasan a wani hali suka kwana ba.
Bayan ta fito daga dakin down ta sauko, Moving quickly ta nufi Hanyar da zata
hau bene taje dakin ummi, Har ta kusa haurawa saman staircases miryar boss man ta
katse ta”Unaisah”! Cak ta tsaya haɗi da waiwayowa tana dubanshi,
“Ina zakije ne”?
Muryarta adisashe ta furta”dakin aunty ummi, Inason ganinsu batul ne, ai ka
fadamin acan suka kwana”
“Hakane, Nima dakinta zani je, amma tunda gaki bari in baki sako ki kai mata” ya
fada tare da zura hannu cikin aljihu ya curo maganin mura ya miƙa mata.

“Wanene bai da lafiya”? Hankalinta atashe ta fada tana bin maganin da kallo.

“Ummi ce ke bata jin dadi, mura ce ta kamata” Ajiyar zuciya Angel ta sauke tayi
tunanin ko cikin ƴan uwanta wani ke bai da lafiya.

Kar6ar maganin tayi, har zata juya muryarshi ta dakatar da ita”Sheikh imam yana
akan hanyar zuwa gidan nan, malamin da zai duba ɗan uwanku danish” Waro ido waje
tayi lokaci ɗaya ta fashe da dariyar farin ciki, Murmushi yasaki Dama ya fada
matane don ya faranta mata rai.
Idanuwanta cike tab da ƙwalla take fadin”Alhamdulillah, wayyo Allah wallahi naji
dadi, fatana Allah yasa ayi asa’a danish ɗina yaji sauƙi ya dawo kamar kowa”

Boss yace”in sha Allah zamuyi nasara, yanzu kije ki kai mata maganin, idan kin
fito ki same mu a falo,
Amsa mashi tayi da toh, jiki na rawa ta nufi benan ta haye sama, burinta takai
mata maganin sannan ta kwantar masu azeeza hankalinsu kafin ta dawo falon don taga
sheikh imam”
Abakin ƙofar dakin Ummi ta dakata tare dakai hannu ta dafi glass door din A
hankali kofar ta buɗe, Zura kafarta keda wuya sukayi kicibus da batul, sam
hankalinta ba akwance yake ba, ganin ummi ta shiga toilet tsawon lokaci bata fitowa
ba shiyasa ta yi dabarar guduwa daga dakin don ba ƙaramin takura tayi ba, baiwar
Allah suna haɗa ido da Unaisah, ta faɗa jikinta, Hannu biyu ta ƙanƙameta dasu kamar
zata koma cikinta, tun daga kan yadda ta rungumeta ranta ya bata cewar babu lafiya,
A hankali itama ta zagayo da hannayenta saman bayan Batul.

“Meke damunki sister? Baki da lafiyane”? Ta fada batare data raba jikinsu daga na
juna ba
Muryar batul ashaƙe da mura ta furta”babu komai, Mu tafi dakinmu, Ni kadaice na
rage su azeeza sun tafi tun ɗazu, Ni ko sallar asuba banyi ba”
Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yai ba, Jin muryar Batul ashaƙe kamar an ɗaure
mata makoshi, A hanzarce ta raba jikinsu, ido cikon ido suke kallon juna, ta ɗanyi
mamakin ganin kayan dake ajikinta masu kyan gaske.
Aruɗe ta furta”batul! Dama kece baki da lafiya ba aunty ummi ba? Garin yaya mura
tayi maki mugun kamu”?
Shiru batul tayi mata batare data furta komai ba, saboda tana jin tsoron ummi
taji ta fada ma wani.
Da sauri ta canza akalar maganar tasu”Meke damunki? Naga fuskarki ta kumbura
idanuwanki sun yi ja, ko kema baki lafiya”?
“Ni lafiyata qalou, damuce ta hana ni yin bacci...” bata ƙare maganar ba batul ta
kuma cewa
“Ina danish dinmu”?
“Inaso zanyi maku bayanin komai amma sai mun koma ɗaki, Yanzu ki fada min ya akai
mura ta kama ki? Ina kuma aunty ummi”?
Murya ƙasa ƙasa Batul tace”nima bansan ya akai ta kamani ba, aunty ummi kuma tana
a toilet, itace ma ta kira awaya don akawo min magani, kuma kinga ta bani kaya na
sanya” tayi maganar tana nuna mata kayan sanyin jikinta.
Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke” mun haɗu da boss man shine ya bani maganin mura
in kawo, ni nama yi tsammanin aunty ummice ba lafiya kamar yadda ya fadamin ashe
kece”
Jinjina mata kai batul tayi”Allah ya baki lafiya sisterna, kayan jikinki sunyi
maki kyau, a ina aunty ummi ta samu kayan nan dai dai size dinki kamar donke aka
dinka su”?

“Nima bansani ba, Mu tafi daki” atakure tayi maganar, tare da ruko hannun Angel,
tajata suka nufi down stairs.

*Daga Alƙalamin Boss Bature✍️*

Adai dai lokacin Su parveen suna a zazzaune tsakiyar gadonsu Batul, sun kewaye
juna, sai faman zazzare idanuwansu suke yi don har yanzu basu daina jin fargabar
macijin nan ba.

Motsin buɗe ƙofa ne Yaja hankalinsu ga kallonta, Atare suka shigo hannun su ruƙe
cikin na juna, wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da gudun gaske Jemimah da
Azeeza suka diro daga saman gadon suka nufi unaisah, tunkafin su ƙaraso ta ware
masu hannayenta fuskarta dauke da yalwataccen murmushi, zubewa tayi saman
gwiwowinta yadda tsawonta zaiyi dai dai da nasu, gaba ɗayansu ta haɗasu ta rungume
a ƙirjinta, tare da zagaya hannayenta saman bayansu, jemimah tuni ta fashe mata da
kuka hada bubbuga bayan Unaisah alamar ranta ya 6aci.

Batul dake a tsaye tana kallonsu sam bata ji takun tafiyar Parveen ba, Sai dai
taji muryarta”Batul tun ɗazu muna ta jiran ki shiru baki zo ba, Ina fata babu wani
abu daya same ki”?

Kallonta Batul tayi da ido tayi mata alamar tayi shiru bata son Unaisah taji
komai daya faru, jinjina kai parveen tayi don ta fahimci me take nufi.

“A ina kika sami kayan jikin ki masu kyau”? Ta fada tana duban Kayan sanyin
jikin batul”
Murmushi batool tasaki kafin tace”Aunty ummi ce ta Bani su”
Parveen tace”ko a ina ta same su, ban ta6a ganin kayan da suka yi maki kyau ba
kalar waɗannan” kafin batool tayi magana muryar Jemimah ta katse mata hanzarinta, A
lokacin sun ɗago da kansu daga rungumar da Unaisah tayi masu, fuskokinsu sharkaf da
hawaye kamar waɗanda suka yi shekara basu ganta ba.

“Meyasa jiya kika tafi kika barmu? Inata kiran sunanki baki amsa ba, tsoron wannan
abun ya kamamu”

Shafa fuskarta Unaisah tayi”Am sorry nasan ban kyauta ba, amma kuyi haƙuri, bawani
wuri na tafi ba, Ina atare da ɗan uwanmu Danish bashi da lafiya......”

Tunkan ta ƙare maganar, hankalinsu yai mugun tashi jin cewa danish dinsu baida
lafiya, damuwace ƙarara akan fuskokinsu

“Unaisah meke damun shi? Meyasa jiya ba kizo kin kaimu mun ganshi ba”? Acewar
parveen
Batul tace”ni da ma saida naji araina ɗan uwanmu baida lafiya, Allah sarki danish
din mu, Yanzu yana a ina? Ina son ganin shi” ta fada idonta akan unaisa dake
ƙoƙarin miƙewa tsaye tana dubansu.

Ruƙo hannunta Azeeza tayi acikin nata”dan Allah ki kaimu wurin shi, muna son
ganin shi” idanuwanta sun ciko tab da ƙwalla tayi maganar.

Numfasawa Unaisah tayi kafin ta soma yin magana”na yanke shawara ƙwara na faɗa maku
halin da danish yake aciki, saboda bana son ku guje shi ko ku dinga jin tsoron zuwa
wurinshi.......” shiru ta ɗanyi na wani lokaci duk sun ƙura mata ido cike da
zumuɗin son jin ƙarashen zancen.

“Amma kafin nan inason ganin sauran ƴan uwanmu, naga babu Hannah! Ina taje ne”?
Atare suka hada baki wurin bata amsar cewa suma basu sani ba, tun daren jiya basu
ganta ba.

Aruɗe Unaisah take dubansu, Kafin ta furta magana, sallamar Big Guy taja
hankalinsu ga duban ƙofar, shigowa cikin ɗakin yai hannun shi ruƙe dana Hannah,
daga bayansu Ƴan uwansu ne maza tun daga kan Sajeed, Haris, Javed and Naufal,
ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, Hannah sai faman zare ido take yi kamar wadda
aka faɗa ma saƙon mutuwarta, sakin hannunta big guy yai jiki na rawa ta nufi
Unaisah ta rungumeta, sunyi farin cikin ganin ƴan uwansu, Sajeed ya nufi azeeza
fuskarshi dauke da murmushi yai hugging dinta, Naufal yajanyo parveen ya rungumeta
Yana bubbuga bayanta da hannu ɗaya,
Batool da Haris suka rungume junansu, Ran jemimah ya 6aci ganin babu wanda ya
rungumeta, harta fara tatta6e la66anta za ta yi masu kuka, javed yai saurin
ɗaukarta saman jikin shi, Fashewa tayi da dariya saboda an dauketa.
Big guy dake a tsaye yana kallonsu ya goya hannayensa saman broad chest dinsa,
Yaran sun yi matuƙar burgeshi.
Tsawon mintuna suna a manne da juna, kafin daga bisani kowan nan su ya rabu da
jikin ɗan uwanshi, gyaran muryar da Big guy yai masu ne yasa suka mayar da
hankalinsu gare shi a tsanake Ya soma yin magana.

“Inaso ku natsu ku saurareni, dalilin dayasa na tara ku a ɗakin nan, saboda na


fahimci haryanzu baku daina jin fargaban abunda ya faru jiya ba, Ga ƴar uwarku nan
Unaisah zatayi maku bayanin komai yadda zaku fahimta, sannan please bama buƙatar
ganin gifcin kowan nan ku a falo! Ku tsaya a ɗaki, mai buƙatar shiga toilet ya
shiga, wanda zai yi bacci ga gado nan ya kwanta,........” kafin Ya ƙare maganar
Parveen tayi ƙasa ƙasa da murya tana fadin”breakfast din mu fa? ni ina jin yunwa,
Jiya da dare bamu ƙarasa cinye abincinmu ba” murmushi big guy ya saki ta cikin face
mask dinshi
Da zolaya yace”ki kwantar da hankalinki foodie, Indai abincine har sai kin gaji da
shi, kamar kina a gidan manomi ne, Yanzu zansa a kawo maku lafiyayyan breakfast” ya
faɗa tare da nufar kofar fita yana fadin”Unaisah Ki kula da su” amsa mashi tayi da
toh, kamar jira su ke yi ya fita, Har suna haɗa baki wurin tambayarta meke faruwa
da Danish.

“Zanyi maku bayani, amma kafin nan ku jira waɗanda basu yi salla ba su yi
tukunna, batool tace min ba ta yi sallah ba”
Badan sunso ba suka amince mata

“Kunyi sallah”? Ta jefa masu tambayar


Sajeed yace”munyi a ɗaki”
“Kufa” ta faɗa tana nuna su Azeeza
Girgiza mata kai su kayi alamar a’a, Hannah ma tace nima banyi ba, saboda babu
hijabi.

“Okey, yanzu abun da za’ai ku shiga toilet ku yi alwala, kafin ku fito zan dauko
maku hijabin” amsa mata sukayi toh.

Ɗaya bayan ɗaya suka shiga toilet, bayan sunyi alwala kowaccensu ta sanya hijabi,
asaman carpet din da ta shimfiɗa masu su ka yi sallar, bayan sun kammmala suka cire
hijaban suka bata ta ninke ta maida su a wardrobe.

Zama sukayi kan carpet din gefen gado, mazan suna fuskantar matan, sun ƙurama
Unaisah ido suna jiran jin me zatace masu.

“Kin yi shiru ba ki ce komai ba sister, ke muke sauraro meke faruwa da ɗan uwan
mu”? Acewar Haris
Sajeed yace”tun jiya da abun nan Ya faru mun ganki kina kuka kina fadin danish ya
rikiɗa ya koma maciji, abun ya tsaya min araina” da damuwa a fuskarsa yai maganar.

“Akwai abun da na 6oye maku tun muna a prison ban samu damar faɗa maku ba.......”
a tsanake Unaisah ta labarta masu dukkan abun da ya faru tun daga kan tattaunawarsu
da Salsabeel farkon haɗuwarsu a gidan kurkukun ƙaddara da kuma gwagwarmayar da suka
yi wajen shawo kan Danish da ruwan zam zam, Har izuwa kan abunda ya faru jiya daya
rikiɗa ya zama maciji, tunda tafara basu labari hankalinsu ya tashi matuƙa, sun
girgiza da jin cewa Danish dinsu GIANT ne, Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu,
idanuwansu a zazzare, Jikin ta ƙaura yai la’asar, wato an gudu ba atsira ba.

La66an Sajeed na kerma ya furta”kina nufin Danish Giant ne’? Jinjina mashi kai
tayi alamar eh, dafe kai haris yai da hannu ɗaya da wata irin karyayyar murya ya
furta”inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un! Mun shiga uku! Wai su waɗannan azzulaman
mutanan wani zunubi muka aikata masu ne? Da suke azabtar da rayuwarmu? Meyasa suka
cutar da rayuwar Danish? Me bawan Allahn nan yayi masu”? Idanuwanshi tuni sun kaɗa
sunyi jawur da su
“Ni dama nasani bazasu ta6a ƙyale mu ba, zasuyi amfani da danish ne donsu maida mu
kurkukun ƙaddara”!
Cikin sanyin murya Batool tace”bawan Allah danish, shine abun tausayi, wallahi
ina jin baƙin ciki da takaicin azabtar mana da rayuwar ɗan uwanmu da suke Yi,
danish tun yana ƙarami suke juya shi, sun hana rayuwarshi sakat, narasa gane
dalilin dayasa suke yi mashi haka, Ya Allah ga bawanka nan kai kadai kasan a wani
hali yake aciki, Ya Allah Ka fitar dashi, ka kawo mashi ɗauki acikin rayuwarshi’,
tuni hawaye sun wanke fuskar Batool.

Cikin shesshekar kuka Azeeza tace”Allah ya isa ba zamu ta6a yafe masu ba, Mugaye
azzalumai ƴan wuta, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara danasanin cin zalunmu
da su ka yi da kuma ƙuntata rayuwar ɗan uwanmu da suke Yi”

Azeeza na rufe baki, Naufal da takaici ya ishe shi, cikin jin ƙunar rai Ya soma
magana”wannan wace irin rayuwace? ya zamuyi da ranmu? Ni yanzu na fahimci KURKUKUN
ƘADDARA RAYUWARMU CE!! mune kurkukun ƙaddara saboda duk inda zamu kasance gidan
kurkukun ƙaddara yana atare damu, Meyasa!!!”? Ya jefa tambayar idanuwanshi akan
fuskar Unaisah, wadda tayi shiru tana sauraronsu, tabbas maganar Naufal abun
dubawace, Yanzu ta fara zargin wani abu.

“Naufal, kamar yadda ka faɗi nima haka nake tunani, rayuwarmu itace gidan kurkukun
ƙaddara, amma meyasa zai kasance haka? Su wanene suka sadaukar da mu?....” ta jefa
ma kanta tambayar da bata da amsarta.

Sajeed yace”yakamata mu fallasa asirin komai ke faruwa agidan kurkukun ƙaddara ga


mutanan da suka taimaki rayuwarmu ina da tabbacin zasu taimaka mana don ganin an
gano su wanene munafukan dake sadaukar damu ta hakanne zamu tabbatar da zarginmu”

Javed yace’nima ina goyan bayanka Sajeed! Mu tona masu asiri kawai, idan da rabon
mu rayu zamu rayune duk runtsi duk wuya, kai koda ace zamu mutu ne bayan mun tona
masu asiri wallahi munci galaba akansu, tunda har muka yi nasarar guduwa daga cikin
kurkukun ƙaddara, wanda ko a tarihi ba’a ta6a samun prisoners da suka gudu suka
tsira ba sai akanmu”!

A hankali unaisah take binsu da kallo, ta fahimci ransu yakai maƙura wurin 6aci,
Jininsu akan akaifarsu yake, kowannansu atsorace yake da abunda ke faruwa da
danish.

Fashewa da kuka jemimah tayi haɗi da ɗaura hannayenta biyu saman kanta tana
fadin”Wayyo Allahn mu mun shiga uku, Yanzu shikenan danish din mu ya zama dodon
kurkuku zai ɗauke mu ya maida mu can mu cigaba da cin ganye” fuskarta sharkaf da
hawaye, ruko hannunta Unaisah tayi acikin nata”Ya isa haka, Ki daina kuka, kanki
zai Iya yin ciwo,” girgiza kai ta dinga yi tana fadin”genie ba zaki gane ba,
wallahi banason komawa kurkukun nan, haushinsu nake ji, Allah zuciyata zata Iya
bugawa in mutu kowa ya huta”
Gaba ɗaya idanuwansu na akan fuskar jemimah, ta haƙiƙance tana yin magana shatun
jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu saman fatarta.
“Sun kashe mun majnoon dina, sun kashe mana Unaizah, Yanzu kuma mu suke son
kashewa fa” ta ƙare maganar tana faman jan majina’
Kwanto da kanta Angel tayi saman cinyoyinta, ta ɗaura hannunta kan sumarta cikin
sigar lallashi take yi mata magana”in sha Allah bazamu ta6a komawa gidan kurkukun
ƙaddara ba, Har bada, munbarshi kenan bi’iznillahi mune zamu kawo karshen kurkukun
da fasiƙan Shuwagabannin su, zamu tarwatsa baƙin tarihin da suka kafa, zamu shafe
babinsu a doron duniyar nan, zasu ɗanɗanin kuɗarsu har sai sunji inama ace ba’a
halitto su a duniyar nan ba, wannan Alƙawarine!” da ƙwarin gwiwa unaisah ta ƙare
maganar.

Shiru jemimah tayi tuni ta haɗiye kukanta, Jikin kowannansu yai sanyi, maganganun
da suke yi yai silar fama masu tabon dake acikin zuciyoyinsu.
Daƙyar Hanna ta Iya buɗe baki tace”ni yanzu damuwata a wani hali danish yake
aciki”? Tayi tambayar idanuwanta cike tab da ƙwalla

Angel ce ta bata amsa da cewa”har yanzu bai dawo mutun ba, amma ɗazu boss man
ya fada min cewa malamin da zai duba jikinshi ya ƙaraso Ina da tabbacin Yana acikin
gidan nan, shiyasa Big guy Yace mu zauna a ɗaki bayason ganin gifcinmu, yakamata mu
tayashi da addu’a, ita yake buƙata daga gare mu” tunkan ta rufe baki, sukayi saurin
daga hannayensu sama, Itama ta ɗaga nata,
“Jemimah ki tashi muyi ma ɗan uwanmu addu’a” Unaisa ce tayi mata magana, daƙyar ta
ɗago da kanta haɗi da ɗaga hannayenta sama kamar yadda sukayi
Addu’o’i unaisah ta soma karantowa suna amsa mata da ameen ameen, bayan ta
kammala kowan nan su Ya shafa saman fuskarshi, kafin su zame hannayensu, kunnuwansu
suka soma jiyo masu motsin buɗe ƙofar dakinsu, A hanzarce suka ɗago suna kallonsu.

Big guy ne ya shigo hannun shi ruƙe da faffaɗan tray Na kayan breakfast dinsu,
Daga Bayanshi Ummin america ce, Ta ɗauki wankan turkish gown launin brown anyi mata
adon stones launin yellow, mayafin da tayi rolling kala ɗaya ne da stones din
rigar, ta sanya high heels a ƙafarta, daga sama rigar ta matseta ta bayyana surar
kirjinta, daga bayan rigar tudun mazaunanta ya fito sosai.
Tunda batool taji ƙamshin turaren ummin america hankalinta ya tashi, tasan dole ta
hukuntata akan fitowar da tayi daga ɗaki batare da saninta ba.
A tsakiyarsu big guy ya ɗaura tray din kayan abincin kafin Ya soma yin magana.
“Ga auntynku nan Ummi, zata zauna atare daku don ta ɗebe maku kewa, idan kuna
buƙatar wani abu, ita zaku faɗa mawa” amsa mashi sukayi da toh.

Big guy ya maida dubanshi ga ummi dake atsaye ta ruƙe qugu da hannu ɗaya,
Hadaddiyar agogon hannunta sai ƙyalli take yi.

“Ummi, ki kula da su, bana so asamu matsala, malamin ne ya buƙaci a tattara


sauran yaran wuri ɗaya sannan aja hankalinsu gudun kada suji sautin abunda zai
rikitar da su”
Lumshe mashi ido tayi, alamar taji mai yace, shi kanshi daurewa yake yi, domin
kuwa wankan da ummi ta ɗauka yaja hankalinshi, musamman shu’umin ƙamshin humran
dake fita a jikinta.

Muryarta da kwarkwasa tace”okey, baka da damuwa”

Bayan fitar big guy daga ɗakin.

Ummi ta kalli su unaisah, atare suka haɗa baki wurin gaishe da ita.

“Ina kwana aunty ummi” yamutsa fuskarta tayi”lafiyalou, Ina batool”? Ta jefa masu
tambayar tana kallonsu, kafin su bata amsa idanuwanta suka sauka akan yatsun hannun
batul, ta 6oye kanta abayan haris, duk don kada ummi ta ganta.

Babu wanda ya fahimci wani abu, sai ita data san meya haɗasu.

“Kunyarki take ji Aunty ummi, shiyasa ta la6e” acewar Unaisah.


Ta6e baki ummi tayi kafin tace”Ina maganin muran da boss man Ya baki”? Ta fada
tana nuna unaisah da hannu.
sai lokacin ta tuna da maganin batasan tun yaushe ta jefar dashi ba.

“Kin yada kenan”? Girgiza kai tayi a’a, Yana a hannuna tun ɗazu, namantane ban
kaiga bata ba”
Juyawa baya ummi tayi tana kallon tsakar dakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan
Blister pack din dake ajiye ƙasa, cikin takun Isa Ta nufi floor din ta zuƙunna ta
ɗauki maganin”ajiyar zuciya unaisah ta sauke ganin ta gano shi’
“Ku matsa min anan zan zauna muyi breakfast,” ta faɗa tana nuna tsakankanin
Batool da Haris, da sauri Ya matsa mata, taje ta zauna idonta akan batool data
ƙanƙame haris, ruƙo hannunta ummi tayi tare da rabata daga jikin haris, duk tabi ta
ruɗe, taƙi yadda su haɗa ido.

Bottle water Unaisah ta ɗauka ta buɗe murfin, ta tsiyaya ruwa acikin cup, ta miƙa
ma ummi, kar6a tayi tare da fadin”thanks” kafin ta curo maganin ƙwaya biyu ta miƙa
ma batul, yatsun hannunta na kerma ta kar6a ta sanya abaki, ta kar6i cup din hannun
ummi ta kur6i ruwan ta haɗiye maganin, Bayan ta gama ta ajiye cup.

“Bata da lafiya ne”? Sajeed ne ya tambaya, parveen tace”Mura take Yi,”

“Shiyasa naji muryarta ashaƙe, sis Allah ya baki lafiya” amsa mashi da tayi da
ameen, sauran mazan sukayi mata sannu ta amsa masu.
Kafin ummi ta fara serving dinsu, A plates ta zuba ma kowannansu abinci banda
batool, ɗaya bayan ɗaya ta miƙa masu, suka kar6a suna ci, kallon Batul tayi”atare
zamu ci” ta faɗa tana sakar mata shu’umin murmushi afakaice batare da su Unaisah
sun gani ba.
A plate ɗaya ta zuba masu farfesun naman kaza, Yaji kayan kamshi ga uban romo.
Daƙyar batool take iya shan farfesun, saboda Ummi ta hanata sakat, da zarar ta
ɗago sai ta haɗa ido da ita, ta rasa gane dalilin dayasa ummi take son takura
rayuwarta.

Hankalin Unaisah ba akansu yake ba, saboda damuwar data bijiro mata, ta ƙosa taji
me ke wakana da Danish, Malamin Ya fara Yi mashi aiki ko kuwa.......?

Shin meya faru bayan zuwan Sheikh Imam malik!?

Bayan ƙarasowar motarsu akatafaren Gate din shiga gidan Owais Jami’in dake driving
dinsu yayi parking a agaban entry hall, Ya fito a hanzarce Ya zagaya ya buɗe masu
murfin motar, A hankali Prime minister hateem ya fito daga Ciki, Kafin Sheikh Imam
Ya zuro ƙafarshi waje shima Ya fito Yana ƙarema ginin gidan kallo, ya yaba da
haɗuwar daular Owais, har saida ya furta masha Allah.

Kafin su ƙarasa falon, Glass door dinsa ta buɗe, Chief Owais Ne Ya bayyana gefe
da gefenshi, Boss man ne tare da Big guy, da kuma sauran jami’an isod da suka
hallara domin tarbarsu.
Murmushi prime minister hateem yasakar mashi, tare da nufarshi tunkan ya isa
gare shi, Chief owais Ya riga shi zuwa Ya haɗa hannayenshi biyu yai hugging din
uncle din nasa”
Kafin Ya ɗago Ya nufi Sheikh Imam Ya rungume shi, fuskar kowannansu ɗauke da
murmushi.

“Owais fatan na sameka lafiya, tsawon lokaci bamu haɗuba, aiki ya 6oye ka,”
Sheikh imam ne yai mashi maganar
Calmly ya furta”Ina lafiya, nayi missing dinka, amma naji dadin ganin ka yau,
Ina fata uncle dina bai takura maka ba? Nasan shine Ya matsa maka akan zuwa
Nigeria” da zolaya ya fada,
Shekh Imam Yace”kai dai bari, kamar yadda baiyi bacci ba adaren jiya nima haka ya
hanani Yin bacci, babu shiri yasa na fara shirye shiryen zuwa Nigeria hada ƙoƙarin
turamin jirgin da zai ɗaukoni” Da zolaya yai maganar,
Hateem dake sauraronsu, baice komai ba sai dai murmushin dake akan fuskarsa bai
washe ba.
Dubanshi chief yai”uncle, sannu da zuwa, Mu shiga daga ciki, nabarku atsaye”
Atare suka jera zuwa babban falon gidan, saman sofa mai mazaunin mutun uku,
prime minister da Sheikh imam suka zauna, Chief Owais Yana daga zaune kan 2 seater,
Yayin da Big guy da Boss suke atsaye sun goya hannayensu saman kirjinsu.
Kallonsu chief Yai kafin Ya soma magana”Taj wannan uncle dina ne Prime
minister Hateem na ƙasar Canada, Kai kaɗaine bakasan shi ba, wannan kuma Sheikh
imam kenan, Aminin kakanmu Obie...”
Cire face mask din fuskarshi Yai, Cikin girmamawa ya soma gaishe da hateem”ina
yi maku barka da zuwa, najima ina jin labarin prime minister awurin Owais sai dai
ban ta6a ganinsa ba, ashe da rabon zamu haɗu, kuma tunda naga fuskarshi raina ya
bani cewar Uncle dinka ne saboda kamanceceniyar dake a tsakaninku”

Ƙayataccen murmushi prime minister yasaki a yayin da yake kallon fuskar taj
yace”Nagode da karramawarka agare ni, kuma naji dadin haɗuwa dakai, Ina fata zamu
cigaba da yin zumunci a tsakaninmu”
Tajo yace”in sha Allah” har cikin ranshi mutumin ya kwanta mashi, kuma Yayi mamakin
haɗuwarshi donshi a hoto yasanshi, kuma yayi mamakin sakar mashi fuska da ya yi a
matsayinshi na babban mutun mai ruƙe da babban muƙamin shugaban ƙasar Canada, koda
yake yasha ji awurin mutane cewa baida girman kai ko kaɗan, mutunne najama’a kowa
nashine mai kudi da talaka awurinshi duk ɗayane.

Chief Owais Ya ɗaura dacewa”Uncle sunan shi Taj, Mahaifin Yarinyar nan, dana ta6a
baka labari, ina fata ka gane shi”
Jinjina kai Hateem yai da mamaki akan face dinsa yace”masha Allah, ina ita
yarinyar take ne? An gano ta”?

Ɗaga mashi kai yai alamar eh.


“Na tayaka murna my son, Allah ya tabbatar da alkhairinsa, Ina fata Yaya
sharafudden Yasan da maganar mahaifinta da kuma ita kanta yarinyar”!?

Chief owais Yace”Ya sani, na faɗa mashi, sai dai basu ta6a haɗuwa da daddynta ba,
amma na yanke shawarar zan haɗasu kwanan nan idan muka shawo kan matsalar yaron
nan”
Ga dukkan alamu Hateem yaji dadin ganin tajuddeen, duba da yadda yake kallon shi.
Gyaran murya sheikh Imam yai masu”Idan kun gama magana ina jiranku, Kun ajiyeni
kamar buhun masara, Yakamata ku bari in kammala aikina inyaso kunyi firar taku”
gaba ɗaya suka sanya dariya banda Chief daya ɗan murmusa.
Prime minister yace”ay mana afwa ya sheikh, nayi kewar yarona, Mun jima bamu haɗu
ba” Murmushi sheikh imam yasaki, da zolaya yace”wani yaro kake nufi? Wanda yahanaka
runtsawa daren jiya? ko kuwa wanda kuke Yin fira da shi a yanzu”?
Prime minister yace”dukansu biyun nake kewa”
Sheikh imam yace”yanzu naji magana, bismillah owais Muje ka nuna min ɗakin da yaron
yake” amsa mashi yai da okey
Atare suka miƙe tsaye tare da nufar Up stairs, tunkafin su ƙarasa ɗakin, suka soma
jiyo kururuwar macijin Yana gurnani.
Sheikh Imam yace”Da alama Yasan da zuwana” murmushi kowannansu ya saki, abakin
ƙofar ɗakin suka tsaya kafin su shiga sheikh imam Ya dubi Chief owais”naji kace
akwai yarinya agidan nan ɗiyar mutumin da naji ka kira da taj ko”? Kafin owais ya
bashi amsa Boss man ya riga shi cewa”ba ita kaɗai bace, akwai sauran ƴan uwanta
dake rayuwa agidan”

Sheikh imam yace”Toh, ina buƙatar a killace su wuri ɗaya, sannan aja hankalinsu ta
yadda baza su iya jin abun da ke faruwa cikin gidan ba, Idan ba haka ba zasu iya
firgita arasa gane kansu” boss man ya amsa mashi da toh.
Kafin Ya dubi big guy”please kaje wajensu, ka aiwatar da abunda malam yace” da
sauri big guy ya nufi hanyar komawa down stairs, Ya rage saura su uku.

“Bismillah mu shiga daga ciki” dafe ƙofar boss Yai, ta zuge a hankali kafin suka
shiga dakin.

Jin motsin shigowarsu dakin Yaja hankalin salsabeel dake atsaye kai idonshi ga
dubansu.

Hankalinsu na akan narkeken macijin dake zarya tsakiyar gadon wata irin kururuwa
yake fitarwa yana huci.
Gaisawa sukayi da salsabeel, daga bisani, Chief Yai mashi alama da hannu,
salsabeel Ya fahimci ƙarin bayani yake nema game da halin da Giant snake din yake
aciki”

“Ni kaina bansan meke damun shi ba, Yanzu ya farka daga bacci, Yana huci, zai Iya
yiwuwa saboda rashin ganin ƴar uwarshi akusa dashi ne”

Hankalin prime minister hateem ba ƙaramin tashi yai ba, sai yanzu yaga girman
macijin Ya wuce misali.

Sheikh Imam Yace”Saboda ni yake wannan hucin, ku dan bamu wuri zan fara aikina”
babu musu suka fito daga dakin, anan second floor suka tsaya suna jiran tsammani
Bayan fitarsu ya rage saura sheikh imam da Macijin a ɗakin, Toilet Ya shiga jim
kaɗan ya fito da alama alwala ya ɗauro, Bakin gadon Ya tsaya tare dakai hannu Ya
damƙi bargon dake a nannaɗe kan mattress, manyan Addu’o’i ya soma karantowa Yana
tottofe bargon, kafin ya fara yin karatun alƙur’ani, Yayin da idanuwanshi suke akan
macijin dake ta ƙoƙarin saukowa daga saman gadon Hanyar guduwa yake nema sai dai ya
kasa yin hakan saboda ɗaurewar da Sheikh imam Yayi mashi da karatun kur’anin da
yake yi, Bayan Ya kammala yin ƙira’ar, Ya daddage Ya haye kan gadon, Ya kifa mashi
bargon saman jikinshi, Ya daddanne shi da ƙafafuwanshi, da hannayenshi yabi ko’ina
ya dafe, wata irin kururuwa macijin yake saki tamkar ana ƙona jikinshi da wuta,
hatta waɗanda ke a wajen ɗaki saida suka jiyo sautin, Har saida prime minister ya
dafe kunnanshi da tafin hannun shi.
Jami’an dake a kewaye da gidan da gudu suka shigo part din hannayensu ruƙe da
bindigu, sunyi tunanin wani mugun abunne ke faruwa, daga saman bene Boss Man Yai
masu magana akan su koma bakin aikinsu hakan yasa suka juya da sauri suka bar part
din.

Sheikh Imam Ya hada uban gumi, zufa ta wanke fuskarshi duk da sanyin A.c na ɗakin,
Yaƙi Sakin bargon daya daddanne Macijin, sai ƙoƙari yakeyi donya kubcema ɗaurin da
yayi mashi.
Maƙoshin shekh imam tamkar zai 6allo tsabar yadda yake cigaba da karanta mashi
ayoyin ƙur’ani tare da addu’o’in karya sihiri, Yaci gaba da tottofe bargon da yake
kudundune.
Ba zato ba tsammani, suka soma jiyo wasu irin muryoyi na baƙaƙen shaiɗanun aljanu
suna fadin”kashe ka zamuyi sheikh imam! Dole ka mutu tunda ka shiga sabgarmu, zaka
mutu”
Da karfin hali sheikh imam yace”Idan kunga na mutu lokacin mutuwatane yayi don
ubanku, Ni da Allah na dogara bada ku ba, Raina a hannunsa yake, Ku bakusa ku cutar
dani ba, face da izninsa, Kunsan bana jin tsoronku tun fil azal......” bai ƙare
maganarba, sautin dariyarsu Ya karaɗe ɗakin, tamkar ana buga ganga, Hankalinsu boss
man ya tashi matuƙa, damuwarsu kada wani abu ya samu sheikh imam.
Cigaba da magana sukayi da kakkausar murya suke fadin”mutuwa zakayi sheikh Imam,
ajalinka ne Yazo, kai ka sani ba’a shiga huruminmu a zauna lafiya, mun kashe ire
irenka da dama waɗanda suka yi ƙoƙarin yi mana shisshigi, Sheikh Imam kadaina janyo
mana ayoyin alkurni bazasu ta6a yin tasiri akanmu ba, Mu ba kalar shaiɗanun da ka
saba ƙonawa bane”
Runtse ido sheikh imam yayi, jin numfashinshi na ƙoƙarin ɗaukewa tamkar an shaƙe
mashi wuyanshi, idanuwanshi suka kaɗa jawur tamkar garwashin wuta, sautin muryarshi
daƙyar yake fita ahaka yake kokarin cigaba da yi mashi karatun kur’anin..........”

“Hankalina bai kwantaba, Inajin fargabar wani abu ya sami malamin nan, Mutanan nan
fa ba ƙananun shaidanu bane” salsabeel ne yai maganar.
Boss man yace”ni kaina fargaba nake ji, gaskiya akwai matsala, kada mu jefa
rayuwarshi cikin hatsari,”
Duk maganganun da sukeyi akan kunnan Chief owais da prime minister Hateem,
jikinsu yai sanyi babu mai magana acikin su.
Lokaci ɗaya bugun zuciyar Prime minister ya ƙaru, arude ya furta”ku buɗe kofar nan”
ya fada yana nuna ƙofar dakin danish” da sauri Bossman Ya nufi ƙofar ya sanya hannu
ya dafe glass din wani iko na Allah ƙofar taƙi buɗewa, gashi sunji shiru babu
motsin sheikh imam da kuma kururuwar macijin.

“Babu lafiya, salsaleel zoka taimaka min mu buɗe ƙofar” matsawa salsabeel yayi
gaban kofar, suka haɗa ƙarfi shida boss suka dinga bugun ƙofar taƙi buɗewa.

Da ƙarfi suke ambaton sunan sheikh imam shiru bai amsa masu ba, babu alamun
motsinshi.

Hankali atashe Chief Owais Ya ɗago da ido suka kalli juna shida prime minister.

“Bana so wani abu ya sami malamin nan, Ni ne silar kiranshi daga sudan, Idan wani
abu ya same shi bazanji dadi ba, zanyi danasani Owais, Yakamata kuyi wani abu akai”
damuwace ƙarara akan fuskar Hateem.

“In sha Allah Uncle babu abunda zai faru da shi, ka kwantar da hankalin ka” chief
na ƙarasa fadar hakan, Ya nufi ƙofar ɗakin, da sauri salsabeel Ya matsa mashi
hanya, Boss man Yaja gefe ɗaya, bismilla ya furta da kyakkyawar niya, kafin ya daki
ƙofar da kafaɗarshi, nan take ƙofar ta zuge da gudun gaske, ajiyar zuciya kowan nan
su ya sauke, salsabeel yayi mamakin ƙarfin owais.
An rasa wazai fara shiga dakin, kowa fargaban ganin abunda zai taras yake yi,
hatta shi kanshi chief din....... 😳😳😳

*Something Unexpected*

*WAIWAYE🌹*

*A Obie International Hospital*

Emergency room

Abun da ya faru daren Jiya da Sir mubarak Ya dauki Dr jazz zuwa asibiti, tunkafin
su ƙarasa Ya kira Dr fawan awaya ya sanar dashi game da zuwansu, tuni nurses sun
fito da stretcher bed din da zasu dauke shi, motarsu nayin parking a harabar ajiye
motocin asibitin, Sir mubarak Ya fito jiki na 6ari ya cuccu6i dr jazz ya daura shi
kan gadon, A gaggauce nurses suka gungurashi zuwa Emmergency room.

Fitowa Major yai daga front seat na motar, Yabi bayan Sir mubarak dake tafiya
yana nufar inda nurses din zasu kai Dr jazz, duk inda ya gifta manyan likitocin
dake zarya cikin girmamawa suke gaishe da shi, a bakin ƙofar emmergency room din
suka dakata da yin tafiyar, damuwar duniya ta isheshi, ya rasa ina zai tsoma ranshi
yaji daɗi, haƙika yaji takaicin bugun da yayi ma jazz bisa rashin sani.

“Yalla6ai, ka zauna” Major ne yai mashi maganar yana nuna mashi waiting seat
dake jingine da bango
Girgiza kai Sir mubarak yai”bazan iya zama ba, Idan har jazz bai farfaɗo ba, Ni
kadai nasan halin da nake aciki, Major ka tayani da addu’a Allah yasa yarona ya
farka bana so wani abu ya same shi”
Cikin kwantar da murya major yace”Sir in sha Allah babu abunda zai same shi, zai
ji sauƙi, ubangiji Allah ya bashi lafiya”

“Ameen” ya amsa mashi.


Tunda aka shiga da jazz cikin emmergency room, likitoci suka taru akanshi, yadda
kasan zasu hana shi mutuwa idan tazo daukar shi.

After some minutes, Dr fawan Ya fito daga medical room din, sanye cikin shiga ta
likitoci, fuskarshi da face mask, tunkan ya ƙaraso wurin su sir mubarak yai
hanzarin nufarshi yana fadin”fawan ya farfado? Ko hanyar yanzu”?
Calmly dr fawan yace”daddy ka kwantar da hankalinka, har yanzu bamuyi nasarar
farfaɗo dashi ba, jazz ya bugu sosai, yanzu dai muna ƙoƙarin ganin munyi mashi
treatment din raunukan dake akan goshinsa, In sha Allah nan badajimawa ba zai
farfaɗo, ina da tabbacin hakan” ya ƙare maganar yana duban fuskar sir mubarak, babu
alamun zai kwantar da hankalinsa, fuskarshi duk ta yamutse.

Dr fawan baiyi mamakin ganin hakan ba, yasan da irin shaƙuwar dake atsakaninshi da
jazz, dole ya damu.
Duk da yana jin shakkar shi saida yai ƙoƙarin jaraba tambayarshi ya akai jazz
yaji mummunan rauni saman goshinsa.
Kasancewar baya acikin natsuwarshi, da kanshi ya labarta ma dr fawan abunda ya
faru.
Dafe kai fawan yai da hannu ɗaya tunawa da ranar da sukazo asibitin suka tirkeshi
kan ya fada masu abunda jazz yake aikatawa shi kanshi yayi tsammanin wani mugun
abun Jazz yake kullawa ashe ba haka bane sun yi mashi mummunan zato.
Ruƙo hannun shi sir mubarak Yai”fawan ka taimaka min, bansan ya zanyi ba, ina
jin fargabar jazz ya farfado ya juya min baya saboda bugun da nayi mashi nasan
daƙyar zai fahimce ni, nayi kuskure fawan na yanke mashi hukuncin cikin fushi
batare dana saurare shi ba” cikin rauni na murya ya ƙare maganar, tsananin
tausayinshi ne Ya kama dr fawan, hatta major ya tausaya ma shi.

“Daddy, har abada bana tunanin jazz zai Iya juya maka baya, Saboda ni shaidane
akan ƙaunar da yake yi maka, balle kuma baka da laifi, laifin shine dabai sanar
dakai ba a matsayinka na mahaifinsa, sannan duk abun da kayi mashi daddy kayi ne
saboda ba ka son ya jefa rayuwarshi cikin hatsari, ni aganina kayi abunda ya dace
kowani uba na gari yayi, shine ya tsaya tsayin daka don ganin yaronshi bai 6ace
hanya ba.....” tunda dr fawan ya fara magana sir mubarak ya natsu yana sauraronshi,
major sai faman jinjina kanshi yake yi alamar gamsuwa da bayanin Dr fawan
Sai da ya kai aya a maganarshi kafin major ya daura da cewa”yalla6ai gaskiya ne
abun da dr fawan ya ke gaya maka, kuskuren da mukayi bisa rashin sani ne, tun da
kake da jazz baka ta6a nuna mashi wariya ko acikin ƴa’ƴanka ba sannan baka ta6a yi
mashi koda tsawa bane don yayi maka badai dai ba, don haka bana tunanin jazz zai
juya maka baya saboda abunda ya faru, zai fahimce ka kuma zai gane kuskuren shi”

Nauyayyar ajiyar zuciya sir mubarak ya sauke, fatanshi Allah yasa maganar su dr
fawan ya tabbata, don bayason jazz ya guje shi saboda ƙaunar da yake yi mashi.

“Major ka kira layin Zaki ka faɗa mashi muna atare da jazz sai zuwa gobe zamu
dawo gida”

“Okey Sir” Major ya faɗa tare da zaro wayarshi daga aljihu, Ya danna ma Zaki Kira,
Bugu Uku kafin Yai picking, bayan sun gaisa Ya isar mashi da sakon Mahaifinsu kafin
daga bisani su ka yi sallama.

“Daddy ku zauna mana, ko zamu shiga daga cikine ka kwanta a resting room dinmu”

Girgiza kai Sir mubarak Yai alamar a’a,


“Bazan Iya runtsawa ba, Nafi buƙatar farfaɗowar Jazz hankalina sai yafi kwanciya”

Gyaɗa kai Dr fawan yai”bari na koma ciki daddy” juyawa yai da sauri ya shiga
medical room din, Sir mubarak Yana atsaye ya dan jingina bayanshi da bango, major
yana daga gefenshi, idanuwansu sunyi masu nauyi, ga gajiyar hidimar shagalin da
akayi ga bacci da damuwar halin da jazz yake aciki.
A ƙalla sun kwashe awanni a tsaye, dare ya nutsa sosai, a lokacin da basuyi
tsammani ba, sautin muryar jazz ya karaɗe kunnuwansu, da ƙarfi yake fadin”daddy
zanyi maka bayani ka daina buguna, wayyo Allah kaina zai fashe zafi yake yi min”

A gigice Sir mubarak Ya nufi dakin da aka kwantar da shi da sauri major Ya take
mashi baya suna shiga suka tarar da Dr Jazz zaune tsakiyar gadon hannayenshi biyu
tallabe da kanshi dake a nannaɗe da bandage, gefen gadon dr fawan ne atsaye Yana
lallashinshi, gaba ɗaya ya birkice sai sambatu yake yi masu.

A hanzarce Sir mubarak Ya zauna gefenshi, Muryarshi a raunace ya ambaci


sunanshi”Jazz My son”

Har saida ya firgita jin muryar sir mubarak, adabarbarce yake dubanshi da rinannun
idanuwanshi waɗanda suka kaɗa jawur, abunka ga farar fata fuskarshi tayi ja
la66ansa sunyi suntum bawan Allah Ya bugu ba kaɗan ba.
Ido cikin ido suke kallon juna,
“Am sorry jazz, na gane kuskurena na bugunka da nayi ba tare da nayi bincike ba,
Dan Allah ka yafe min” a hankali ya ruƙo hannun jazz acikin nashi ya ruƙe shi
sosai.

Babu alamun zai furta mashi kalma, sai faman jan numfashi yake yi haɗi da lumshe
idanuwanshi har yanzu allurar da dr fawan yai mashi bata sake shi ba.

Daƙyar ya iya buɗe baki ya furta”meyasa ka buge ni daddy? Dama kaine kake
bibiyata daddy? Laifin me nayi maka? Kai da kanka ka faɗamin ba zaka iya ta6a
lafiyar jikina ba, kuma bazaka bari wani ya cutar dani na, Ko a mafarki ban ta6a
tunanin zaka yi min haka ba, sai gashi yau ka nemi ka raba ni da rayuwata.....” a
wahalce ya ƙare maganar yana fitar da huci.

Girgiza kai sir mubarak yai hawaye tuni sun taru cikin idanuwanshi.
Muryarshi asanyaye ya ce”Jazz ba laifina bane abun da ya faru, rashin sani ne,
Jazz kaine tun farko baka sanar dani game da aikin sirrin da kake yi ba, a tunanina
ka ɗauke ni kamar mahaifinka wanda yai silar zuwanka duniya but why kake 6oye min
abunda ya shafe ka? jazz kamanta alƙawarin da muka ɗaukarwa junanmu’? Runtse ido
jazz yai hawaye suka soma wanke fuskarshi.
Cikin shessheƙar kuka ya furta”ban manta ba daddy, kayi hakuri, yaya Owais ne
Yahana in faɗa maka, shiyasa ban gaya maka ba, nayi ƙoƙarin fahimtar dashi kuskuren
yin hakan amma sai yace min kaima kasan da case din Yaran.......” jin wannan
maganar yasa hankalin sir mubarak ya ƙara tashi aruɗe yake kallon fuskar jazz
tamkar yana karanto wani abu, Major da dr fawan suka kalli juna, da alama sunyi
mamakin jin abunda jazz ya furta, dafe kai sir mubarak yayi da hannu ɗaya tunawa da
zancen case din yaran da sojojin ƙasar ghana suka nemi hukumar sojin nigeria data
kar6i case din daga hannun su, a lokacin basu kar6i case dinba sai suka nemi
hukumar Isod da su shiga lamarin yaran, bai ta6a ganinsu ba ko a hoto yadaisan da
zancen, sannan baida masaniya akan aikin da owais ya ɗauki Jazz Na kula da lafiyar
yaran shiyasa aka samu matsala.

Jinjina kai sir mubarak yayi, cike da danasanin hukuncin daya yanke mashi,

“Jazz ina ƙara baka haƙuri, dan Allah kada ka ruƙeni a zuciyarka, da ace bana
sonka wallahi bazan damu da rayuwarka ba, amma saboda ƙaunar da nake yimaka ne yasa
harna yi maka shisshigi......” a tsanake sir mubarak ya labarta mashi duk abunda ya
faru tundaga rana ta farka daya fara jin shi yana waya a garden kan maganar kaji
har zuwa ranar daya yi mashi la6e a toilet yajiyo shi yana fadin akasheta...
“Jazz kasan ba mummunan abu kake aikatawa ba, amma meyasa kake amfani da kalamai
masu hatsarin gaske kamar kalmar kisa da naji kana faɗi”?
Numfashi jazz yaja kafin ya bashi amsa da cewa”saboda yaya Owais ya gargaɗeni
akan kada na kuskura wani ya san aikin da nake yi, koda kuwa mommyna ne shiyasa
nake yin amfani da waɗannan kalaman, lokacin da kaji nace bayasan hanyar da zai
kashe ta ba, Ina nufin yasan hanyar da zai magance matsalarta, a lokacin Salsabeel
ne ya kirani a waya, ya fada min haukan khadeeja ya motsa, shine nake fada mashi
maganganun da kaji inayi”
“Wanene salsabeel”?
“Shine babban cikinsu, atare da yaran yake, ba ƙaramin mutun bane ya girmi yaya
owais”
Shiru Sir mubarak yayi, still bai kawar da idanuwanshi daga kan fuskar jazz ba.
“Ya jikin naka? Ina fata babu inda keyi maka ciwo”?
Ɗaga mashi kai jazz yai alamar Eh.
“Yunwa fa”?
“Bana jin yunwa, ina son yin magana da mommyna”
“Ba zamu iya kirantaba a yanzu, tayi bacci, sai zuwa gobe zamu tafi gida”
Don dole jazz ya haƙura da sonyin magana da mommynsa.
A daren ranar major a resting room din dr jazz Ya zauna, shi kuma sir mubarak ya
kasa tafiya yabar jazz, kan kafaɗarshi jazz ya ɗaura kanshi, anan bacci yai awon
gaba da su manne da juna.

Ataƙaice kenan abunda Ya faru daren Jiya dangane da sir mubarak.

*Daga Alƙalamin Boss Bature✍️*

Idan muka koma 6angaren Sheikh Imam tun bayan da Chief Ya buɗe ƙofar dakin Danish,
Kowa fargaban Abunda idanuwanshi zasu gane mashi yake yi, ƙarfin hali chief owais
yayi wajen zura ƙafarshi cikin ɗakin, rass yaji gabanshi yai mugun faɗuwa ganin
hular sheikh imam da arab turban dinsa yashe kan floor kamar an wurgo dasu sun
tarwatse, ga takalmansa ware ɗaya bakin gadon ware ɗaya kan carpet, a ruɗe chief Ya
wurga eye balls dinsa kan katafaren gadon Danish, lamarin yayi matuƙar ɗaure mashi
kai, ganin bargo lullu6e da mutun, ƙafafuwansa sun leƙo waje, farare sol da su, Iya
neck dinsa bargon Ya lullu6e hakan ya bayyana lallausar sumar kanshi data tarwatse
saman wuyanshi hatta gefen fuskarshi ta lullu6e, Chief Ya fahimci yaron ya dawo
suffarshi ta mutane sai dai abunda bai gane ba Ina sheikh imam yake? Saboda kwata
kwata babu shi a ɗakin babu alamar shi.

“Yalla6ai lafiya”? Salsabeel ne Ya ambaci haka yayin da yake shigowa ɗakin daga
bayanshi boss man ne da prime minister hateem suka shigo ɗakin suna ƙarema ko’ina
kallo.

Idanuwan mai girma prime minister basu sauka akan kowa ba sai akan matashin dake
lullu6e da bargo, tun daga kan shantala shantalan ƙafafuwanshi yasoma kallo har
izuwa kan brown hair dinsa, aruɗe ya furta”dama yaron macace ba Namiji ba”? ya jefa
tambayar yana dubansu.

“ba maca bace, Namijine Yana da sumar kai ne” acewar Boss man

“Ni abunda bangane ba, Ina sheikh Imam”? Chief ne ya faɗa yana bin ko’ina na room
din da kallo.

“Allah dai yasa ba wani abunne ya faru da shi ba” acewar Boss man.
Sunyi tsaitsaye cirko cirko bakin gadon fuskokinsu da alamun ruɗanin rashin
ganin sheikh imam.

Prime minister ya kasa kau da idonshi daga kallon sumar kan Danish da yake yi,
Ya ƙagara da son ganin fuskarshi.

A lokacin da ba su yi tsammani ba, suka soma jiyo motsin buɗe toilet door, kusan
atare suka kai idanuwansu ga kallon ƙofar, bakowa bane yake fitowa face sheikh imam
malik, hannun shi ruƙe da cazbaharshi, hankalin shi kwance sai dai da alamun damuwa
akan fuskarshi.

Nauyayyar ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, har suna haɗa baki wurin ambaton
sunan shi”Sheikh Imam! Muna fata babu abunda ya same ka”?
Jinjina masu kai yayi batare da yace komai ba, har saida ya dawo gefen gadon ya
zauna tare da ɗaura idanuwanshi kan bargon dake lullu6e da danish tukunna
A hankali Ya furta”Alhamdulillah, cikin Ikon Allah nayi nasara, Yaron ya canza
halittarshi........”ya faɗa fuskarshi da matsakaicin annuri.

Har cikin ransu sunji daɗin jin hakan, musamman prime minister, atare suka haɗa
baki suna ambaton Alhamdulillah sannu da ƙoƙari malam.

Girgiza kai sheikh imam yai kafin ya ɗaura da cewa”sai dai ina mai baƙin cikin
sanar daku cewa Har yanzu baƙaƙen shaidanun dake atare da shi suna nan daram daƙam,
babu alamun zamu yi nasarar raba shi da su..........”

Kallon juna su ka yi kafin suka maida dubansu ga sheikh imam


Cigaba da yin magana yayi”Ina buƙatar neman ƙarin bayani dangane da abunda ke
faruwa da yaron? Shin Menene Yajaza mashi faɗawa tarkon miyagun matsafa? da har
suka samu ƙarfin ikon Juya shi son ransu’?

Kallon salsabeel Boss man yayi”kai kaɗaine kasan komai Ya kamata ka sanar da
Sheikh Imam, kada ka 6oye mashi komai dangane da rayuwar yaran ta hakanne kaɗai zai
Iya shawo kan matsalar.

Jinjina kai salsabeel yayi alamar ya gamsu da bayaninshi.


“Labarine mai tsayi, zai ɗauki tsawon lokaci,” acewar salsabeel.

Sheikh Imam Yace”tun da kace labarine mai tsayi, inaga mubarshi zuwa lokacin da
yaron zai wartsake, Yanzu Yana buƙatar kulawarmu”

Prime minister yace”Ni kaina zanso naji tarihin kyakkyawan matashin saurayin
nan, In sha Allah saboda shi zan nemi iznin ƙara kwanakin tafiyata, but abunda nake
son sani, Yaron idonshi biyu? Ko bacci yake yi”? ya tambaya yana kallon sheikh
imam.

“Ba bacci yake yi ba, idonshi biyu, sai dai bazai iya ɗaga ko yatsan hannunsa ba,
shaiɗanun sun sakar mashi da kasala Ya jigata sosai, Bayan haka akwai tabonni saman
fatar bayanshi” sheikh Ya faɗa tare da miƙa hannu ya ruƙo bargon tare da janshi Ya
yaye shi gefe ɗaya, faffaɗan bayan danish ne Ya bayyana, Fari sol sai dai ko’ina da
tabon ja.

“Wannan tabon na bayanshi, sahun harsashin bindigar da jami’an isod suka harba
mashi ne, dama ya faɗa min sunyi mashi illah” acewar salsabeel.

Tsananin tausayinshi ne ya kama prime minister, ji yake tamkar ya rungumoshi,


baisan ya akai ya tsinci kanshi da son ganin fuskar yaron ba, shi dai ya kwanta
mashi arai,
“Nayi mamakin ganin suffarshi, naji kace min yarone amma surar jikinshi bata yara
bace” prime minister ne yai magnar yana duban owais
Chief dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa ya furta”wata’kil
halittarsace haka, Girman jiki da ƙananun shekaru”
Jinjina kai prime minister yayi kafin ya kuma cewa”baba Yanzu me yakamata muyi
mashi don mu taimakashi ya dawo normal? Ko dai zamu kira likitane Ya duba shi”?
Sheikh Imam Yace”kada ayi haka, saboda bakowa bane zai Iya tunkararshi a wannan
yanayin ya zauna lafiya, kawai kubi shi da addu’a in sha Allah zai warware”
“Akwai ruwan zam zam na addu’a da na ta6a jaraba bashi, inaga da za’a same shi
wata’kil Ya taimaka mashi wajen samun lafiyarshi, Kafin rasuwar mahaifina Yana yin
amfani da ruwan zam zam din wurin yin treatment din mutanan dake fama da irin
lalurarshi.
Salsabeel ne ya kora masu jawabin, sheikh Imam Yace”ƙwarai kuwa zam zam Yana da
amfani, idan akwai inda za’a same shi kuyi ƙoƙarin samun shi”
Prime minister yace”in sha Allah zamuyi ƙoƙarin samun zam zam din, baba mun gode
da ƙoƙarin da kayi mana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka”
Boss man yace”ya sheikh ya akai rawaninka da hular suka faɗo ƙasa? Allah yasa
dai ba wani abun bane ya faru” Ya furta maganar tare da juyawa ya nufi bakin ƙofar,
Ya dauko mashi rawanin da hular.
Murmushi sheikh imam yasaki kafin yace”kai dai bari, sha’ani da baƙaƙen shaidanu
ba abune mai sauƙi ba, ai dambe muka yi dasu, suna bugu ina bugu na haɗasu da ayar
Allah, Ni ban ma lura babu rawanin akaina ba sai da ka yi magana” murmushi
kowannansu yakeyi, maganarshi ta basu nishaɗi.
“Yaron nan fa sai mun dage da yi masa addu’a, Yana buƙatarta, domin kuwa
shaiɗanun dake atare dashi mugayen shu’umaine suna da hatsarin gaske, ba’a ta6a su
a zauna lafiya, amma da yake mu da Allah muka dogara kuma munyi imanin cewa shi
kadaine gatanmu in sha Allah babu wani mahaluƙi daya isa Ya karya mu sai dai mu
muga bayanshi, Na tausaya ma rayuwar yaron kuma ashirye nake da in bada gudummuwata
don ganin mun raba shi da su” da kakkausar murya sheikh imam yayi maganar, gaba
ɗaya sun natsu suna sauraronshi, har ya kai ƙarshen maganarshi kafin chief owais ya
soma yin magana a tsanake”sheikh zamu iya sanin me yaron yake buƙata a yanzu”?
Numfasawa sheikh imam yai yayin da yake bin sumar kan danish da kallo ya furta”Idan
zaku Iya taimaka mashi yai wanka, tabbas zaiji daɗin jikin shi, sannan ashirya
mashi lafiyayyan abincin da zaici inyaso ko abakine sai abashi tunda bai iya ci da
kanshi, Bayan haka daga rana irin ta yau duk wani abu da zai yi amfani dashi kada a
kuskura abashi batare da an tofe shi da addu’a ba, tun daga kan ruwan da zaisha,
shimfidarshi, ruwan wankan shi da suturar sanyawarshi........”kafin malam ya ƙare
jawabin, Boss man yai hanzarin tarar numfashinshi da cewa”Allah yaja da ran malam,
yaron ba musulmi bane, hakan zai yiwu kuwa? Yar Uwarshi unaisah ta fada min cewa
sunyi fama dashi akan ya musulunta amma yaƙiya, ko kalmar bismillah bai ta6a
furtawa ba”

Har cikin zuciyar prime minister baiji dadin jin cewa Yaron ba musulmi bane,
Sheikh Imam yace”in ba wani iko na Allah ba zaiyi wuya ya musulunta idan har
shaidanun jikinshi basu rabu da shi ba, sune suke hana shi ambaton sunan Allah
saboda lagwon su ne, In sha Allah zamu magance matsalar nan badajimawa ba”
Ajiyar zuciya prime minister ya sauke, haɗi da numfasawa yace”Ina son ganin
fuskarshi” ya furta hakan Yana duban chief owais, da sauri salsabeel Ya zagaya ta
6angaren daman gadon, Ya haye tare da ruko bargon da hannun shi ya tattare shi gefe
ɗaya kan mattress, santala santalan cinyoyinsa farare sol sunyi sambal dasu, sai
uban tabonni, kafin komawarshi maciji short ne ajikinshi haka zalika A yanzu haka
da yake akwance gajeran wandonne.

Sanin nauyin jikin Danish yasa salsabeel nannaɗe hannun jallabiyarsa ya daddage
Ya ruƙo kafaɗunsa da hannayensa ya juyar dashi ya fuskanci ceilling, still
fuskarshi bata bayyana ba saboda yalwatacciyar sumar kanshi data rufeta.
Cike da zumuɗi prime minister yace da salsabeel”please, ka jinginar dashi kan
headbored, Ka nannaɗe min sumar kanshi daga kan fuskarshi inason ganinshi da kyau”
Cikin girmamawa Salsabeel Ya amsa mashi da toh, Kafin Ya daddage Ya ɗago da
Danish Ya jinginar dashi jikin headboard, A hankali Ya soma janye sumar kanshi daga
kan fuskarshi,
Tunkafin Ya ƙarasa kau da sumar, Hankalin prime minsiter yai matuƙar tashi
haiƙam, zuciyarshi ta soma harbawa da matsanancin speed, Yayin da idanuwanshi suka
zazzaro waje, tamkar eye balls dinsa zasu fado ƙasa, haƙiƙa yayi matuƙar girgiza da
ganin abunda idanuwanshi suke nuna mashi, kowa dake a ɗakin saida ya lura da
yanayin da prime minister ya shiga na tsantsar mamaki da Al’ajabi, bashi ba hatta
sheikh imam da Chief owais al’ajabine akan fuskokinsu.
Muryar prime minister na rawa ya furta”Sheikh...! Owais Kuna ganin abunda nake
gani kuwa? a ruɗe ya furta maganar yana ƙarema fuskar Danish kallo.
Sheikh Imam da al’ajabi Ya gama kamashi, Baisan sa’dda ya furta”amma dai wannan
yaron Jininka ne ko? don wannan yafi ƙarfin ace kamanceceniyace ta halitta sai dai
ta jini, saboda kamanninshi sun 6aci dakai da kuma yarinyar wurinka Nazli, Tamkar
kayi kakinsa, komai nashi kalar naka ne, tun da Allah Ya halicceni ban ta6a ganin
kama irin wannan ba, gaskiya nayi mamaki.....”
Boss man yace”ai ba tun yau ba, nasha faɗama chief owais cewa Yaron Yana kama
dashi, bani ba hatta abokanan aikin mu sun shaida hakan, sai dai wani abu daya ƙara
ɗaure mun kai ayau, Yaron yafi kama da prime minister hateem, bai baro komai nashi
ba, tun daga kan shape din bakinsu, dogon hancinsu da idanuwansu, Yalla6ai da zaka
ga launin idonshi zaka sha ruwan mamaki, domin kuwa kalar nakune”
Dafe kai prime minister yayi da hannun shi ɗaya, Hankalinshi Yaƙi kwanciya da
kamanninsu da yaron.
Gyaran murya salsabeel Yayi kafin ya soma yin magana yana duban su
“Ni kaina na jima ina mamakin kamannin dake a tsakanin Chief owais da Danish,
komai nasu kala ɗaya ne banbancinsu launin fata ne da kuma tsayin sumar kai, wani
iko na Allah sai gashi Yalla6ai Hateem Yafi kama da Danish”
Runtse ido prime minister yayi, baisan ya akai yake jin wani irin yanayin
atattare dashi ba.

Muryarshi araunace ya furta”ban haɗa komai dashi ba, bani da alaƙa da shi, Yauce
rana tafarko dana fara yin tozali da fuskarshi, amma meyasa nake jin wani abu agame
dashi? Dan Allah ku fahimtar dani na shiga ruɗani, ya akai komai nashi kalar nawa”?
Yana magana la66ansa na kerma.

“Owais ka faɗamin wanene Yaron nan? Su wanene Iyayenshi? Meyasa yake kama dani
da ƴata Nazli”? Da kakkausar murya ya furta maganar saboda aruɗe yake da lamarin.
Shi kanshi chief owais din Ya kasa furta komai, Lamarin Ya ruɗar dashi ya
rikirkitar mashi da tunaninshi, bai ta6a tsammanin kamanninshi da yaron sun 6aci
har haka ba.

A hankali Ya soma yin taku Izuwa gaban Prime minister hateem dake dubanshi
fuskarshi a yamutse.

Cikin kwantar da murya ya furta”Uncle, bamu da masaniya akan su wanene Iyayen


shi, saboda bai dasu a halin Yanzu, da shi da ƴan uwanshi dake ahannunmu bamusan
komai nasu ba, tamkar marayu suke a hannunmu, Yarinya ɗayace mukasan Mahaifinta
tajuddeen” ya faɗa yana nuna Boss man da hannun shi.
Girgiza kai yaɗanyi numfashinshi na fita da huci yace”Owais kada ku maidani
mahaukaci, nafasan me nake yi, taya za’ace babu danginshi? Kyakkyawan yaro kamar
wannan?ni kawai so nake ku faɗamin meyasa muke Kama”!!! Ga dukkan alamu prime
minister ya fara zaucewa, wata irin zuface take tsastsafo mashi saman goshin shi.
Hankalin kowan nan su Yana akanshi, owais baisan taya zai fahimtar da uncle din
nashi ba, Miƙewa Sheikh Imam yai tare da nufar prime minister Ya tsaya agabanshi,
tare da kai hannu ɗaya ya dafa kafaɗarshi, a tsanake Ya soma yi mashi magana
“Ka kwantar da hankalinka, yakamata ka fahimci abun da Awaisu Yake ƙoƙarin faɗa
maka, su kansu basu da masaniya akan yaron, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan,
kowani ɗan adam yana da masu kama da shi A duniya.....” tunkan sheikh Imam Ya ƙare
maganar, prime minister yace”baba, wannan yafi ƙarfin ace kamace kawai, ka dubi
fuskarshi dakyau, tamkar anyi photocopy dina, kamar dai nina haife shi, Ina jinshi
tamkar jini na, ƙaunar da nake yi mashi kaɗai abun dubawace, ta zarce misali,
saboda shifa na kasa runtsawa adaren Jiya, na damu da shi fiye da
tunaninku.........” gaba ɗaya sun rasa taya zasu shawo kan prime minister, a iya
sanin su da shi bai ta6a haihuwar ɗa Namiji ba, balle ace yarom shine daya 6ata.

“Yanzu abun da za’ai, tun da kana ƙaunarsa kuma yaron baida iyaye, mai zai hana ka
ɗauki ragamar kula dashi kafin komawarka canada? Wata’ƙil hankalinka zaifi
kwanciya” acewar sheikh Imam, ya fadi hakanne donya kwantar masa da hankalinsa
ganin irin ruɗun daya shiga.

“hakan yayi shiekh, Uncle ka ƙaddara cewa jininka ne shi, kana da damar da zaka
Iya bashi kyakkyawar kulawa” Chief owais na ya furta hakan.

Kalamansu sun tausasa mashi zuciyarshi, har cikin ranshi Yaji dadin jin hakan.

“Inaso na taimaka mashi yayi wankan ya sanya sutura a jikinshi, zan kira ɗan
uwana awaya don yazo ya ganshi, nasan shi kadaine zai ƙara tabbatar min da abunda
nake gani a idona, sannan Idan yaron yaji sauƙi kafin in koma canada, zan je dashi
gidana don in nuna ma gimbiyata shi da ƴa’ƴana nasan zasuyi mamakin kamanninsa dani
musamman Nazli, hatta hasken fatarshi kalar nata ne” murmushi ne akan fuskokinsu,
sunji daɗin sakewar da prime minister yayi, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba.

Naɗe hannun rigarshi yayi, tare da cire agogon azurfarshi, da zoben hannun shi,
Ya miƙa ma owais su, da sauri owais ya sanya hannu ya kar6a, gaba ɗaya kallon shi
suke da mamaki akan fuskokinsu.

Murmushin gefen fuska yasaki har dimple dinsa ya lotsa”kada kuga ina zumuɗi
akanshi ƙaunarsa nake Yi” da zolaya ya furta maganar kafin yace” wazai taimaka min
mu shiga da shi bathroom room”? da sauri Salsabeel Yace”ni Yalla6ai”
“Yawwa, ruƙo min shi mu shiga ciki, ko da ya ke naga yana da girman jiki zaiyi
nauyi, bari na kama maka” a hanzarce Ya zagaya ta 6angaren da salsabeel Yake, a
lokacin sabeel Yayi koƙarin janyo danish da ƙyar ya kawo shi bakin gadon.
Kafaɗunshi suka rurruƙe shi da prime minsiter suka miƙar dashi tsaye, wanda badan
ƙarfin giant da sabeel yake dashi ba da kuwa babu mai iya ɗaga shi, jikin shi ya
saki tamkar wanda baida ƙashi, kanshi ya kalli kasa sumar kanshi ta lullu6e
fuskarshi, idanuwanshi suna arufe gam, zufa ta ko’ina take tsasstsafo mashi, a
hankali suke tafiya dashi suna nufar toilet, har suka yi nasarar shigar da shi
ciki’
Bayan shigarsu, sheikh imam ya dubi boss man da owais
“Inason ganin sauran Yaran da kuke ruko a hannunku”
Da sauri Boss Man Ya amsa mashi da toh, Ya miƙa ma sheikh imam rawanin shi daya
ruƙe a hannunshi tare da hularshi, godiya yayi mashi, har ya juya zai fuce muryar
chief owais ta dakatar dashi
“Boss, Ka tara yaran a main falo, Yanzu zamu sauko down”
Amsa mashi yai da toh, kafin yasa kai ya fuce daga dakin Ya sauka down.

A hanzarce yake tattaka staircases din benan, har ya kusa saukowa down yai tozali
da big guy dake tafiya cikin takun sauri, ganin boss yasa shi fadin”Ya ake ciki
mutumina?
Boss yace”Alhamdulillah Danish ya dawo ainihin suffarshi, Sai dai babu kuzari
ajikinshi, Ko yatsanshi bai iya ɗagawa, ga tabonnin harbin bindigar da akayi mashi
ta ko’ina saman fatar shi”
Cike da jin alhini Big guy yace”bawan Allah, banji dadin jin hakan ba, wallahi
yaron tausayi yake bani, ashe munyi mashi illa da harbin bindigar amma ina fata
baiji mugun rauni ba ko”?

Ɗaga mashi kai boss yayi alamar eh, fuskarshi da damuwa yace”ubangiji Allah yaba
shi lafiya, Allah kuma ya kawo mashi ƙarshen wahalar shi”Boss ya amsa mashi da
ameen kafin yace”yanzu haka Prime minister da ɗan uwanshi, sun shiga dashi bathroom
zasuyi mashi wanka, sheikh imam ne ya bada shawarar yin hakan”
Zaro ido big guy yai da zolaya yace”Yanzu wannan ƙaton balagaggen zasuyi ma
wanka? Yaron fa yakai chief dinmu girman jiki,”
Harara Boss man ya jefa mashi”laifina ne dana tsaya yin magana da ɗan ƙwaya, sai
kace ba ka ji nace maka bai iya ɗaga koda yatsansa ba, lalura ce ko kai kanka akwai
ciwon da sai dai adinga yi maka wanka, ba fata nake yi maka ba, ina dai kwatanta
maka ne babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara”
Dariya big guy yasaki”Haba mutumina, nima fa wasa nake yi, nadai jinjina lamarin
ne, amma baka fadamin ba prime minister baiyi mamakin ganin fuskar yaron ba”?
Dariya boss yayi kafin yace”daɗina da kai shegen son gulma uwa mace”
Cike da zumuɗi big guy yace”ni dai ka amsa min tambayata na ƙosa naji”
Boss man yace”kallo yabarka, hankalin prime minister ba ƙaramin tashi yayi ba,
kusan fa hauka yayi mana gaba ɗaya ya rikice tunda yayi tozali da fuskar yaron,
daƙyar fa muka shawo kanshi, duk yabi ya ruɗe......” a tsanake Man ya labarta mashi
komai.
Dariyar shaƙiyanci Big guy yasaki hada tafa hannayensa yana fadin”ni dama nasan
za’a rina wallahi, nifa tuntuni nake mamakin kamanninsu da yaron, koda ake maganar
yana kama da chief namu saida na raya arainacewa duk ranar da hateem yayi arba da
yaron sai ya sha mamaki, donni nafi ganin kamanninshi da nashi, sai gashi maganata
ta tabbata” da ƙwarin gwiwa ya ƙare maganar, boss da zolaya yace”sannu malamin
duba, aikinka na kyau, ka tsareni da surutu kamar kanyar da bata da daɗi, ka hanani
ƙarasawa inda zanje”
“Ina zakaje ne”? Big guy ya jefa mashi tambayar.
“Sheikh imam ne Ya buƙaci atara mashi sauran yaran yana son ganinsu”
Big guy yace”ai ƙwara yagansu domin kuwa suna buƙatarshi kodan saboda wannan
jarin taka, ni ina da tabbacin ba’a rasa almatsutsai akanta.....”dariyace ta kubce
mashi daƙyar ya ƙare maganar, ganin yadda boss man ya haɗe fuskarshi.
Harara ya jefa mashi”Idan ka isa ka maimaita maganarnan agaban chief”
Big guy yace”ai ko giyar wake nasha bazanyi wannan gangancin ba,”
Fuskar boss ɗauke da fara’a Yabi ta gefen big guy Ya yi gaba abunshi
Ɗaga murya big guy yai tare da cewa”Yaran suna a ɗakin Jarinka gaba ɗayansu na
tarasu anan”
Murmushi taj yasaki, haɗi da girgiza kanshi, bakomai yasa shi yin hakan ba face
sunan da big guy yake kiran Babynsa angel, wato JARI, saboda yace mashi chief zaiba
auranta yafi son inda zata huta shine fa ya ruƙe abun azuciyarshi har yake
tsokanarshi da sunanta.

Idan muka koma 6angaren su unaisah, tuni sun kammala yin breakfast dinsu, kowa yaci
ya ƙoshi yayi hani’an, sai dai damuwa ta hanasu sakat, Hankalinsu ba akwance Yake
ba, sunyi zugudum saman carpet, kowa ya zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki,
jefi jefi sukan buɗe baki suce Allah sarki danish dinmu, ko awani hali yake a
yanzu, a lokacin ummin america ta shiga toilet din dakin nasu.

Batool ta kwantar da kanta kan kafaɗar unaisah, Azeeza ta ɗaura nata kan a
shoulder din Sajeed, hannayensu ruƙe cikin na juna, Jemimah ta haye bisa laps din
haris idanuwanta alumshe sai faman firgita take Yi tana jan numfashi kamar baccine
ke ƙoƙarin yin awon gaba da ita, parveen da naufal sun jingina bayansu jikin gado
fuskokinsu babu walwala, hannah kuwa ta ɗaura kanta saman laps din javed, sunyi
shiru babu mai magana, daga tsakiyar carpet din tray din kayan abincin da suka
kammala ci ne ba akaiga kawar da su ba, wasu daga cikinsu sai faman lumshe
idanuwansu sukeyi alamun bacci suke ji.

Jin motsin buɗe ƙofar toilet yasa Batool yin saurin runtse idanuwanta ta ƙanƙame
unaisah, gudun kada ta haɗa ido da aunty ummi, fitowa tayi daga cikin toilet din,
sautin takalman ƙafartane ya fargar da masu gyangyadin cikinsu, gaba daya suka ware
idanuwansu akan ummi dake tunkarosu.

Ta fahimci tsantsar damuwace atattare dasu, tun ɗazu da suna cin abinci ta lura
da kyar suke cusa abinci abakunansu, tasan bai wuci damuwar halin da ɗan uwansu
yake aciki bane”
“Aunty ummi, Inaso zanje dakin danish in duba jikinshi” unaisah ce tayi maganar
Ummi tace”a’a, ba’a bada iznin wani daga cikin ku Ya fita ba”
Ya mutsa fuska unaisah tayi tamkar zata fashe da kuka ta kuma cewa”aunty ummi
batool ta manta doguwar rigarta a ɗakinki jiya da su ka je kwana, zanje na ɗauko
mata”
Girgiza kai ummi tayi”basai kinje ba, zuwa anjima da kaina zan dauko mata
rigarta” zumbura mata baki Unaisah tayi duk yadda taso tayi ma ummi wayau taƙi
barinta ta fita.
A ƙule unaisah tace “To waimu haka zamuyi ta zama a ɗaki kamar an kulle kaji a
keji”
Dariya ummi tasaki har fararen haƙoranta suka bayyana tar dasu kamar gonar auduga
“Kin gaji ne”? Ɗaga mata gira unaisah tayi alamar eh.
Gyaɗa kai ummi tayi”okey, bari na taimaka maku ku girgije jikinku,” basu
fahimci me take nufi ba.
Zura hannu tayi cikin aljihun doguwar rigar jikinta ta zaro iphone dinta, duk
sun ƙura mata ido suna jiran ganin me zatayi da wayar.
Zira ziran yatsun hannunta ta ɗaura kan screen din wayar ta soma yin pressing
dinta, jim kaɗan daddaɗan sautin kiɗa ya soma karaɗe bedroom din nasu, taken waƙar
ed shareen mai suna Shape of you.

Fuskarta ɗauke da shu’umin murmushi take kallonsu, sun ƙura mata ido suna
kallonta, ganin ta fara jujjuya qugunta tana taka rawa.

“Idan kuna ra’ayi ku taso muyi rawa” ɗaure fuska Unaisah tayi ranta a6ace take
dubanta har ta buɗe baki zatace mata bazasuyi rawarba, Sajeed Ya miƙe Yana taka
rawa ya nufi tsakiyar ɗakin, miƙewa Azeeza tayi da sauri tabi shi Ya ruƙo hannunta
Yana jujjuyata, tuntsirewa Ummi tayi da dariya tana kallon su, abu kamar wasa
sautin kiɗan yafara kai masu karo, Naufal ya miƙe ya ruƙo hannun Parveen suka nufi
tsakiyar ɗakin suma suka fara yin rawa, Aruɗe unaisah take kallonsu kamar waɗanda
akayima asiri, lallai ummi ba ƙaramar shaidaniya bace hakanan taja hankalinsu da
sautin kiɗa, ruƙo hannun Hanna javed yai suka miƙa suma suka nufi tsakiyar dakin,
Haris Ya miƙe Jemimah ta like mashi tana fadin itama zatayi rawar, ya ruko hannunta
suka bi sahu, Ya rage saura Unaisah da Batool su kadai ne suka ki tashi.

“Sanya damuwa aranku bazai ta6a yi maku maganin matsalarku ba, Ni taimakon ku
nake sonyi don na fahimci baku san me ake nufi dajin dadin rayuwa ba, kunfi so
kuyita ƙuntata kanku bayan kowani ɗan adam yana da damar da zai sanya kanshi farin
ciki, If you let me do my job, you’ll see the positive results soon.”......”
muryarta da kwarkwasa take yin magana tana kallon Batool da Unaisah.

“Idan kunaso mu zauna lafiya daku, to ku bani haɗin kai, Ni kuma zan wayar maku da
kanku, zan sanyaku farin cikin da zai kawar maku da damuwarku” da shaƙiyanci take
yi masu magana tana ɗage girarta.

Sunyi shiru babu alamun zasu tanka mata, shu’umar dariya tasaki tare da cewa”Na
fahimci unaisah kece mai taurin kai, Saboda ke Batool taƙi tashi ta taka rawa ko”?
Murguɗa mata baki unaisah tayi.
“Idan kika bani hadin kai mukayi rawa zan barki ki fita daga ɗakin nan kije
wurin ɗan uwanki danish....”tunkan ummi ta rufe baki unaisah tayi saurin furta”a’a
sai dai ki bari in fara zuwa dakin shi, Idan na dawo sai muyi rawar”
“Zaki rasa damar da kike da ita” acewar ummi, Ta furta maganar tare da miƙa ma
batool hannunta alamar ta taso suyi yawa, cike da jin shakkarta Batool take
kallonta, fuskar ummi a ɗaure tace da ita”Come to me” sai da batool tafara kallon
unaisah jikinta sukuku kafin ta yunƙura ta miƙe tare da ɗaura hannunta na dama
saman hannun ummin america, gam ta ruƙe hannun tajata zuwa tsakiyar ɗakin rawa suka
soma takawa kamar mace da namiji haka take juya batool tana rungumeta idonta akan
unaisah data haɗe fuska tana satar kallonsu.

Canza masu waƙa tayi ta sanya masu waƙar rema mai taken baby come down, tunda
sautin kiɗan Ya fara ratsa mata zuciya takasa jurewa ji tayi kamar ana janta a
hankali ta miƙe tsaye tana kallon ƴan uwanta dake ta tiƙar rawa suna dariya, itama
sai taji tana buƙatar yin nishaɗin kota ɗebe kewar danish dake damunta.
Ganin ta miƙe tsaye sototo tana kallonsu yasa ummi miƙa mata hannu ɗaya alamar
tazo gareta.
Maƙe mata kafaɗa tayi alamar bazata zo ba, batool tace”please sister kizo muyi
yawa atare dan Allah” harara ta watsa ma batool, muryar sajeed ce ta janyo
hankalinta ga dubanshi.
“Sister zo mu taka mana, muna buƙatarki afilin nan” murguɗa mashi baki tayi.
“Genie dan Allah kizo muyi rawa, kinga ni banda abokin yi haris baiyi dani” da
shagwa6a jemimah tayi mata maganar, hada marairaice mata fuska.
Magiya suka dinga mata akan tashigo suyi rawar, tun tana maƙe masu kafaɗa, har
dai jemimah tazo taja hannunta suka shiga filin, ai tunda tafara taka rawa kamar
ɗiyar roba, daɗi ya kamasu ganin unaisah ta saki jiki tana tiƙar rawa, nan fa kowa
ya bada himmah, sosai suke jijjiga qugunansu, wani abun ƙayatarwarma sai sun yarfar
da sumar kansu kamar indiyawa, sautin kiɗan ba ƙaramin ƙara masu ƙaimi yake yi ba,
ummi ce kaɗai take bin waƙar suma tun basu iyaba har suka fara bi saboda harshen
turancine tamkar yarensu ne........:
Dawo da waƙar farko tayi jin sun fara dauka suna bi, aikuwa gaba daya suka
kware murya suna bin waƙar

Baby, calm down, calm down


Girl, this your body e put my heart for lockdown
For lockdown, oh, lockdown
Girl, you sweet like Fanta, Fanta
If I tell you say I love you no dey form yanga, oh, yanga
No tell me no, no, no, no, whoa-whoa-whoa-whoa
Oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh-oh
Baby, come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love
You got me like, “Whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa-whoa”
Shawty come gimme your lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-lo-love, mm-mm

Cike da nishaɗi suke bin waƙar suna dariya fararen hakoransu kamar gonar auduga,
ita kanta ummin america ba ƙaramin burgeta sukayi ba, Kamar sakarya haka tasaki
baki tana kallonsu, a ƙarshe saita bar masu filin rawar ta koma gefe ɗaya tamkar dj
ta goya hannayenta saman kirjinta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya fuskarta ɗauke da
ƙayataccen murmushi, sun bata mamaki, daga kunna masu waƙa har sun haddace ta,
aranta ta ayyana lallai yaran suna da kaifin basira, yanayin yadda sukeyin rawar
suna jujjuya qugunansu yafi komai tafiya da hankalinta, musamman unaisah da parveen
sunfi zaƙewa sai kuma uban gayya Sajeed dama shine yafara koya masu rawa tun agidan
kurkukun ƙaddara, salon rawarshi kalar ta ƴan club ce, da aji yake yinta hannun shi
ruƙe dana Azeezarshi Sun tsunduma suna tiƙar rawa ko gajiya basayi.
Da ƙarfi Sajeed Yace Aunty Ummi ki canza mana wata waƙar mai daɗi”
Da sauri ta ɗauki wayar ta kunna masu waƙar alen walker.
Unaisah na soma jin taken waƙar tayi saurin kamawa tafara bi saboda tasanta tun
da jimawa, sajeed ma ya iya waƙar, atare suka haɗa baki suna bin waƙar
Lost in your mind, I wanna know
Am I losin’ my mind?
Never let me go
If this night is not forever, at least we are together
I know I’m not alone
I know I’m not alone
Anywhere, whenever
Apart but still together
I know I’m not alone
I know I’m not alone
I know I’m not alone
I know I’m not alone
Unconscious mind, l’m wide awake
Wanna feel one last time
Take my pain away.......”

Abun da basu sani ba, tun ɗazu boss man Ya shigo ɗakin, yana daga tsaye bakin kofar
Ya goya hannayenshi saman kirjinshi, ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo kafin ya
tsayar da idanuwanshi akan Unaisah da ta zaƙe tanata jujjuya qugu tana bin waƙar,
tsabar mamakine Ya hanashi yi masu sallama, bai ta6a tsammanin zata Iya yin rawa
har haka ba,Yarinyar da kullum take acikin damuwa.
Ummin america tana faman wurwurga eye balls dinta akansu karaf idanuwanta suka
hango mata boss man dake atsaye yana kalonsu, da sauri ta kashe sautin, ta kama yin
ƴan kame kame, su kuwa prisoners koda ta kashe sautin basu lura da shi ba, a
shagwa6e Jemimah ta bubbuga ƙafa tana fadin”wayyo Allah aunty ummi, meyasa kika
kashe mana abun, ni wallahi bangaji ba, dan Allah ki sake kunna mana muyi rawa mu
girgije” ta faɗa tana karkaɗa ƙaramin qugunta, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya.

Banda ummi data kame kanta

“Please aunty ummi ki kunna mana mu ƙarasa yin rawar” acewar parveen
idanuwanta akan fuskar boss dake tsaye yana kallonsu, Sun juya mashi baya
shiyasa basusan da zaman shi ba, ita kadaice take Iya ganin shi.

A wayance tace”nifa ba don wani abu na kunna maku sauti ba, kawai na fahimci kuna
acikin yanayi na damuwa shiyasa nayi ƙoƙarin don in sanyaku nishaɗi, kuma
Alhamdulillah naga canji atare daku....” tunkan ta ƙare maganar, Boss man ya ɗaga
hannayenshi yai clapping da ƙarfi haɗi da furta”Sannunku da ƙoƙari” a firgice suka
waiwayo baya suna dubanshi kamar wadanda suka ga dodo.
Unaisah hada dafe ƙirji tana fadin”Boss tun yaushe ka shigo dakin nan”?
“Tun time da kika fara rawa ina atsaye ina kallonki” wata irin kunyace ta kamata
da sauri ta juya ta nufi saman gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow tana dariya.

Hakan da tayi yayi matuƙar bashi dariya.

ɗaura idanuwanshi yayi akan fuskar ummin america sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta
take yi.

“Ummi Amanar da muka baki kenan? A matsayinki na mamansu kin tarasu akan idonki
suke tiƙar ruwa, ke da kanki kika kunna masu sauti, ƙiri ƙiri so kike ki maida mana
ƴa’ƴa ƴan rawa ko”?

A ruɗe ta furta”I’m sorry Sir if I offended you, but I didn’t have any bad
intentions. I was just trying to make them happy because I noticed they were
worried about their brother’s illness. That’s why I tried to cheer them up......”
aladabce tayi maganar, tana matuƙar girmama boss man saboda karamcin da yake yi
mata, yafi sakar mata fuska akan sauran jami’an isod.

“Kada ki damu babu komai nima nayi maganarne kawai bawai ina nufin hakan ba, ai
nasan ba zaki ta6a yin abunda zai 6ata masu tarbiyaba ba, yau dinma kinyine donki
ɗebe masu kewa kuma naji dadin hakan Na yaba da tunaninki, tunda gashi nagani da
idona kin taimaka masu da kika sanya su nishaɗi, Na jinjina maki” ya faɗa hadi da
yi mata alamar jinjina da yatsanshi.
Ƙayataccen murmushi tasakar mashi”nagode da ka fahimce ni”
Mayar da dubanshi yayi akan su sajeed dake tsaye suna kallonsu
“Ay min afwa na katse maku jin daɗin ku, nima ba laifina bane laifin sheikh imam
ne daya buƙaci son ganinku don haka in akwai mai ƙorafi ya tanadi abunsa idan munje
gabanshi sai ku faɗa mashi” da zolaya yayi masu maganar, murmushi kowan nan su
yasaki.
Unaisah jin an ambaci sunan sheikh Imam da kuma maganar yana son ganinsu yasa tayi
sauri saukowa daga saman gadon,
A kunyace ta kalli boss man tana faman noƙe kai tace”mu tafi boss”
Ruƙo hannunta yai acikin nashi, da sauri Batool ta ruƙe ɗayan hannun nashi sukayi
gaba su naufal suna abiye da bayansu, gaba ɗayansu suka nufi falon hada Ummin
America.

A tsakiyar falon su ka dakata da yin tafiyar Boss Man yace”Ku jira anan bari naje
na sanar dashi” harya kama hanya zai tafi Unaisah ta kwala mashi kira, a hanzarce
ya juya yana kallonta.

Sosa kai ta ɗanyi da hannunta kafin tace”am..dama inaso ne na tambayeka awani


hali danish dinmu Yake aciki ne”?

“Ya dawo mutun” wani irin farin cikine Ya lullu6esu, musamman unaisah bakinta
yaƙi rufuwa
“sai dai babu ƙarfi a jikin shi, bai iya yin komai ko yatsan hannun shi bai iya
ɗagawa” lokaci ɗaya murna ta koma ciki jin abun da Boss man Yace.
jikinsu duk yai sanyi, Unaisah tace”baida lafiyane”? Ɗaga mata kai yai alamar
eh, ya ƙara da cewa”kada ki sanya damuwa aranku, zaiji sauƙi in sha Allah,
addu’arku yake buƙata”
Cike da zumuɗi tace”zan Iya binka zuwa ɗakin nashi”
Jim ya danyi kafin yace”No, ki tsaya tare da ƴan uwanki, zuwa anjima za’a baku
damar ku ganshi” jiki asanyaye ta amsa mashi da toh.
juyawa boss man yayi da sauri Ya haye upstairs.
Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke, ummi dake atsaye harta fara gajiya, wuri ta
samu saman sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafarta ɗaya bisa ɗaya, taci gaba da danna
wayar hannunta.
“Mu zauna kafin malamin Ya ƙaraso acewar Unaisah”
Amsa mata su ka yi da toh, kowa ya samu wuri Ya zauna, sanyin A.c sai ratsa
fatar jikinsu Yake Yi, sunyi shiru babu mai yin magana acikin su, sai faman
ƙyafƙyafta idanuwansu suke Yi, duk sun ƙagara da son ganin malamin

Tsawon mintuna ƙalilan, suka soma jiyo takun takalmansu, a hanzarce su unaisah suka
kai dubansu gare su.

Sheikh imam ne agaba, daga bayanshi boss man ne tare da Big Guy.

Tunkafin Ya ƙaraso cikin falon Yake binsu da kallo, hannunshi ruƙe da cazbaharshi,
a tsakiyar sofa set din suka dakata da yin tafiyar, ummi sam bata lura da su ba,
hankalinta na akan wayarta da take dannawa.
Cikin girmama su unaisah suka sauko daga saman sofa, suka dawo kan carpet, atare
suka haɗa baki wurin gaishe da shi, hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai faman
sakin murmushi yake,
“Masha Allah, kyawawan ƴan mata da samari, fatan na sameku lafiya” amsa mashi
sukayi da lafiyalou.
“Alhamdulillah, ubangiji Allah ya Albarkaci rayuwarku...” kafin Sheikh Ya ƙare
maganar, Boss man Ya kira sunan ummi, a hankali ta ɗago tana kallon shi”bakiga
sheikh imam bane”? Adabarbarce ta mamaita sunan malamin da boss Ya kira mata,
kasancewar Ya juya mata baya bata samu damar ganin fuskarshi ba, Jin muyarta yasa
sheikh imam yin saurin juyowa baya don ganin wacece..........”

Wani irin mugun bugu zuciyar ummi tayi lokacin da idanuwanta su ka yi tozali da
fuskar sheikh imam, tsabar firgita har wayar hannunta sai da ta kubce mata, sheikh
imam kuwa tunda ya tsayar da kwayar idanuwansa akan fuskarta bai ko ƙyafta ba, wani
irin kallo yake binta dashi mai wuyar fassaruwa, lamarin ya ɗaurewa boss man kai,
shi da big guy tare da Unaisah gaba ɗaya Hankalinsu na akansu babu wanda yayi
yunƙurin dakatar dasu daga kallon da suke jefawa junansu tsawon mintuna ganin abun
nasu ba mai ƙarewa bane yasa Boss man yin gyaran murya, adabarbarce ummi ta soma
ƙoƙarin tattara natsuwarta duk tabi ta ruɗe kamar wadda taga wani mugun abu.
Da sauri ta zuƙunna tare dakai yatsun hannunta dake kerma da niyar ta ɗauki
wayarta data faɗi kan floor, sai dai kafin ta kai ga yin hakan sheikh imam ya
rigata ɗaukar wayartata, lokaci ɗaya ta miƙe ta juya da gudu ta nufi cikin falon
sai da tafara taka stairs sautin shessheƙar kukanta ya karaɗe falon.....

Hankalinsu Batool ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin sautin kukan aunty umminsu ya jefa
su cikin yanayi na damuwa.

da mamaki akan fuskar Boss man Ya furta”Sheikh meke faruwa? Ko kasan ta ne”?

Shiru ya ɗanyi jim yana jujjuya wayar ummi dake a hannunshi na tsawon sakanni,
kafin ya soma magana da karyayyar murya”bansanta ba, Yau na fara ganinta” ya faɗa
tare da juyowa yana fuskantarsu
Da alamun ruɗu akan fuskar big guy yace”amma meyasa kuka dauki lokaci kuna kallon
juna kai da ita? Sannan meyasa ta watsa da gudu tana kuka”?
Fuskar sheikh imam babu walwala Yace”dan Allah kubar maganar nan, kasan dai
bazanyi maka ƙarya ba geme geme dani, nima abun da yasa nake kallonta saboda kallon
da take yi min, kuka kuma da take yi wata’ƙil nayi mata kama da wani ne da ta rasa
a rayuwarta”

Jinjina kai big guy yayi badan Ya gamsu da bayanin shi ba.

“Ga wayarta ku ruƙe mata” ya faɗa yana miƙa ma Boss man, wanda yayi zugudum yana
kallon yadda jikin sheikh imam ke tsuma sun fahimci da akwai wani abu da ya 6oye
masu wanda baison su sani dangane da ganin ummin america da yayi.

Cikin sanyin murya Unaisah tace”Ni zan kai mata wayar,” ta fada tare dakai hannu
ta kar6e phone din daga hannun sheikh imam, ta nufi cikin falon da sauri.

Bayan tafiyarta, sheikh imam Ya mayar da dubanshi kansu Sajeed da suke a tsaye
cirko cirko suna kallon shi.

“Allah ya yi maku albarka, ubangiji Allah ya kareku daga sharrin duk wani abun
cutarwa, Allah ya daukaka rayuwarku......” addu’o’i ya dinga karanto masu suna amsa
mashi da ameen ameen
Bayan ya kammala yi masu addu’o’i, yace dasu”Ku faɗamin sunayenku ina son ji”
hatta maganarshi da ƙarfin hali yake yinta duk ya rasa kuzarinsa.

Sajeed ne ya fara cewa”Ni sunana sajeed, wannan kuma Azeeza’ ya faɗa yana nuna
Azeeza, kafin Ya ɗaura yatsan shi kan Naufal”Sunanshi naufal ta gefenshi Parvin, ga
kuma Jemimah da Hanna, sai Javid and Haris, da Batool, ƴar uwarmu data tafi kaima
aunty ummi waya sunanta Unaisah”

duk wanda ya nuna sai ya fadi sunanshi bayan ya kammala sheikh imam yace”sannu da
ƙoƙari Sajeed, nagode daka faɗamin sunayen ku” murmushi Sajeed yayi ba tare da ya
ce komai ba.

A hankali Sheikh Imam Ya dubi boss man da big guy, bai yi mamakin ganin kallon da
su ke yi mashi ba, yasan dole suyi tunanin wani abun daban, launin idanuwanshi har
sun canza zuwa ja, kau da idonshi yayi daga kansu ya kalli su Haris muryarshi
asanyaye yace”ku zauna muyi fira ƴan jikokina” zazzaunawa su ka yi kan carpet shi
kuma ya zauna kan sofa, su boss ma suka zauna suna fuskantar shi.

*UNAISAH❤*

Koda Unaisah ta ƙarasa ƙofar ɗakin ummi dafe glass door din ƙofar tayi a hankali ta
zugeta, bata sameta a adakin ba, sai dai ta jiyo shessheƙar kukanta acikin toilet.
Ɗaga murya tayi tare da cewa”Aunty Ummi, ga wayarki na kawo maki” shiru ummi
bata tanka mata ba, kusan sau biyar tana maimaita maganar babu alamun za’a amsa
mata.
Saman gado ta ajiye mata wayar, kafin ta nufi ƙofar toilet din ta sanya
hannu tayi mata knocking,
“Aunty Ummi dan Allah ki daina yin kuka, bamu jin daɗi, idan wani ne ya 6ata maki
rai, ki yi haƙuri” lallashinta Unaisah taci gaba da yi tun tana jin shessheƙar
kukan ummi, har tadaina jiyo sautin kukanta, hankalinta ya ɗan kwanta juyawa tayi
da sauri ta fuce daga ɗakin, maimakon ta sauka down ta koma falo sai ta kalla6a ta
nufi ɗakin Danish, dama abun take yima zumuɗi kenan shiyasa ta kar6i wayar ummi da
sunan zata kai mata.

Idan muka koma 6angaren Danish tsawon mintuna da suka shiga da shi bathroom, kafin
su fara yi mashi wankan saida prime minister ya tofe ruwan da addu’o’i kamar yadda
sheikh imam yace adinga yi mashi, batare daya cire mashi short din jikinshi ba yayi
mashi wanka da ruwa mai ɗumi, tamkar ya samu jinjirin yaro, saƙo da lungu na
jikinshi sai da prime minister ya cuccuɗa shi, bayan ya kammala ya ɗauko farin
towel cikin jerin waɗanda ke sagale jikin hanger, ya ɗaure mashi a waist dinshi da
dabara ya zame short din daya jiƙe duk don kada yaga tsiraicin shi, shanya short
din yayi kafin salsabeel Ya taimaka mashi suka fiddo da shi daga cikin kwamin
wankan.

Kafin fitowarsu Chief Owais kadai ya rage a ɗakin, Cikin takun sauri ya nufi
faskekiyar closet din Danish ya buɗe yana bin jerin tsadaddun suturunsa da kallo A
hankali ya tsayar da idanuwanshi wurin jerin jallabiyoyi yana da tabbacin zaifi
samun walwala acikin jallabiya, launin fara ya ɗauko mashi, ya dawo ya ɗaura kan
gado.

Jin motsin buɗe toilet door ne yaja hankalinshi ga kallon su


A daddafe suka fito da danish hannayensu tallabe da shi, da sauri chief Ya ƙarasa
gabansu Ya tallabo masu shi a saman shimfiɗeɗan gadonshi suka kwantar da shi.
“Sannu da ƙoƙari Uncle,” acewar chief
Prime minister yace”yawwa my son, kaima sannunka da ƙoƙari, tun jiya mun hana ka
runtsa”

“Bakomai uncle kada hakan ya dame ka aikina ne”

Murmushi prime minister yasaki haɗi da bubbuga kafaɗar chief owais alamar
jinjina.

“Uncle yakamata ka koma gida, za’a iya nemanka, ni zan cigaba da kula maka shi”

Girgiza kai Prime minister yayi”No, ba yanzu zan koma gida ba, sai zuwa anjima”
Chief bai musa mashi ba don ya fahimci baison tafiya yabar Danish.

“Sabeel, bring me some body lotion and perfume” cikin girmamawa salsabeel ya amsa
mashi da toh sir.

Ya juya da sauri ya nufi dressing mirror ya ɗauko body lotion tare da turare yazo
ya ajiye su kan gadon.

prime minster ne ya soma bin ko’ina na jikin danish yana shafe shi da mai haɗi
da yi mashi tausa don yaji dadin jikin shi, chief ne ya taimaka mashi wurin burkito
mashi da danish Ya juya mashi bayanshi, Ya shafa mashi man kafin yabi da turare ya
feshe shi.

da taimakon chief suka sanya mashi jallabiyar, masha Allah, tayi bala’en yi
mashi kyau, a karo na farko kenan don bai ta6a sanya jallabiyaba, tabi shape
jikinshi ta bayyana kyakkyawar surar jikin shi, musamman broad chest dinsa da
strong arms nasa sun fito ruɗu ruɗu ta jikin jallabiyar.

Ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke, ganin sunci nasarar gyara mashi jikin shi,
hatta sumar kanshi saida prime minister ya sharceta ya shafe mashi ita da mayukan
gyaran gashi, ƙamshin turaren danish ya cika ɗakin kamar wanda akayi ma wanka da
ruwan turare.

“Yanzu me ya rage mana”? Acewar chief, prime minister yace”nasan yana jin yunwa,
Yana buƙatar abincin da zai ci”

Salsabeel yace “Yayi bacci yanzu, naga lokacin sallah yakusa cika, may be kafin mu
kammala yin sallah ya farka sai mu bashi abincin”

“Kana nufin har muka yi mashi wanka bacci yake yi”? Prime minister ne ya faɗa yana
duban salsabeel.

“A’a yalla6ai, idonshi biyu, tun lokacin da muka shiga dashi bathroom, Yanzu nan
yayi bacci”

“Taya akai ka gane yayi bacci” da mamaki yayi mashi tambayar, chief dai yana
atsaye yana sauraronsu.

“Yatsun hannun shi dana ƙafarshi, suna kerma yanzu kuma sun daina gaba ɗaya sun
tsaya yadda su ke”
Fuskar prime minister dauke da murmushi yace”ka karanci ɗan uwan nan naka sosai,
naji dadin jin hakan, may be wankan da mu ka yi mashi ne yasa shi jin daɗi har yayi
bacci”
Saldabeel yace”ƙwarai kuwa yalla6ai, ay kayi ƙoƙari, Allah yasaka maka da
mafificin alkhairinsa kamar yadda ka faranta mashi rai ka gatanta shi kaima inayi
maka fatan Allah ya faranta maka ya ƙara ɗaukaka ka” Har cikin ranshi yaji daɗin
kalaman salsabeel,
“Yalla6ai kaima ban barka abayaba, domin kuwa kayi namijin ƙoƙari wurin ganin ɗan
uwana ya samu lafiya, Allah ne kaɗai zai Iya biyanka” ya faɗa yana duban chief
owais.
Jinjina mashi kai yayi batare daya furta komai ba.
Kiraye kirayen sallar Azhar da aka farayi ne Yaja hankalinsu
da sauri chief ya zaro agogon azurfar hateem tare da Zobensa daga aljihu Ya
miƙa mashi.
Bayan ya saka a hannun shi, ɗaya bayan ɗaya su kayo alwala, kafin fitarsu daga
dakin saida prime minister yaje har gaban gadon danish ya ɗan duka tare da kai
small lips dinsa saman forehead din danish Ya manna mashi peck, ji yake kamar karya
tafi yabar shi, ganin abun nashi bamai ƙarewa bane ga time ɗin salla na tafiya ya
kafe danish da ido babu ƙyaftawa da sauri chief yaje ya ruƙo hannun shi ya janyo
shi a hankali suka nufi ƙofar fita ɗakin.

Adai dai lokacin Unaisah dake la6e bakin ƙofar ɗakin tana sauraron su, jin motsin
tafiyarsune yasa tayi saurin watsawa da gudu ta la6e a wata ƴar corner.
Akan Idonta, Chief Owais Ya fito hannun shi ruƙe dana prime minister, still bata
samu damar ganin fuskokinsu ba, sai dai salsabeel daya biyo bayansu shi tagani da
kyau, tunani ta somayi aranta ko wanene wannan babban mutumin, taso ace taga
fuskarshi shida chief, Allah bai bata sa’a ba, Har saida suka 6ace ma ganinta
tukunna cikin sanɗa take bin bango tana nifar ɗakin danish cikin sa’a ta buɗe ƙofar
ta shige, daddaɗan ƙamshin turarenshi ne ya daki hancinta har saida ta lumshe
idanuwanta tana shaƙar shi ......

Cikin takun sanɗa ta nufi gadon, yayin da idanuwanta suke hango mata Man dinta,
hayewa saman gadon tayi daga gefenshi ta dakata tana bin body dinsa da kallo, from
head to toe, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin shi cikin shiga ta farar
jallabiya yayi mata kyau, aranta ta ayyana nasan waɗannan mutanan ne suka taimaka
mashi wurin gyara jikinshi saboda boss ya faɗamin cewa ko yatsanshi bai iya ɗagawa,
idan kuwa hasashena gaskiya ne naji daɗi ubangiji Allah ya saka masu da gidan
Aljanna, ta ƙare zancen zucin fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki.

Ta rasa gane bacci yake yi ko idonshi biyu, amma dai tayi missing dinshi na
tsawon awannin daya ɗauka tun jiya a halittar maciji, ashe dai da rabon zata sake
ganinshi da ainihin suffarshi, yayin da take kallonshi karaf idanuwanta suka sauka
akan jan tabonnin dake akan farar fatar dogon wuyansa, harzuwa saman fatar
hannunsa.

Ras taji gabanta ya faɗi, ta zazzaro idanuwanta waje tana fadin”My man meke
damunka? Jan tabon menene nake gani a jikinka”? Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da
matsananciyar damuwa, hawaye tuni sun jiƙe gashin idonta.

Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura saman wuyanshi ta soma shafa tabonnin slowly ta
zame fingers din daga neck dinsa zuwa kan broad chest dinsa, a hankali take 6alle
links din gaban jallabiyar don ta samu damar ganin sauran tabonnin da ke akan
fatarshi, da ta buɗe faffadan kirjin nashi, hankalinta yayi matuƙar tashi da ganin
tabonnin ta ko’ina, ji tayi tamkar zuciyarshi bata bugawa da sauri ta kanga
Kunnanta na dama saitin zuciyarshi, natsuwa tayi tana sauraran yadda take harbawa
cikin kwanciyar hankali, tsawon mintuna bata ɗago da kanta ba saboda dadin sauraran
heart beat dinsa da take ji, A hankali ta ɗago da kanta karaf idanuwanta suka sauka
akan soft lips dinsa batasan ya akai ta tsinci kanta dayi masu kallon ƙurulla ba
sun ɗan kumbura, zuciya ce ta soma tunzurata akansu, unaisah da kasada ta ɗaura
yatsun hannunta na dama kan la66ansa tayi squeezing ɗin su, ba zato ba tsammani
taji yaja dogon numfashi da ƙarfin gaske, tsabar kiɗima jiki na rawa ta rarrafa ta
ta wulkita can ƙasan gadon ta faɗo ta labe zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi
jikinta ya hauyin kerma duk tabi ta ruɗe gani take yi kamar ta fama mashi ciwon
shi...

Runtse idanuwanta tayi hadi da matse pink lips dinta wani irin yanayi take ji mara
misaltuwa atattare da ita, Jin shiru ya daina jan numfashin ne yasa ta lalla6a ta
ɗago da kanta tana leƙenshi, babu abun da ya canza yaci gaba da yin baccin nashi.
Ƙasa ƙasa da murya ta furta”I’m sorry to disturb you, I’ve missed you so much. I
can’t take my eyes off you.”

Lalla6awa tayi a hankali ta haura saman gadon da rarrafe ta nufe shi, rumfa tayi
mashi da sumar kanta ta natsu tana shaƙar ƙamshin turaren jikinsa, tabi ta addabi
rayuwarshi da sunan tayi kewarshi tahana mashi sukuni abaccinsa, don taga babu kowa
aɗakin shiyasa take yi mashi iya shege....

Lokacin da Chief da prime minister tare da salsabeel suka sauko down, kaitsaye suka
nufi babban falon, tunkafin su ƙaraso takun takalmansu Ya isar da saƙon zuwansu, A
hanzarce Sheikh imam da su Boss man suka mimmiƙe tsaye suna jiran ƙarasowar su, su
sajeed dake zazzaune kan carpet suna kallonsu, lokaci ɗaya suka shiga ruɗanin ganin
fuskar prime minister Hateem data chief Owais, duk da shi chief ya sanya face mask
a fuskarshi, a matuƙar ruɗe suke kallonshi bakunansu asake babu alamun zasu motsa.

“Sannu da fitowa Yalla6ai” Boss man ne yayi maganar, Big guy yace”barka da
fitowa” amsa masu yayi fuskarshi asake,
Sheikh Imam yace”ya jikin yaron?
Prime minister yace”Yayi bacci shiyasa muka ƙyale shi zuwa time da zai farka”
“Alhamdulillah, naji dadin jin hakan, baccin nan da yayi hutu ne agare shi”

“Babana, muna ƙara yi maka godiya bisa ƙoƙarin da kayi mana, mun hana ka sakat mun
kuma hana ka huta, Allah ne kadai zai iya biyanka.....” fuskar sheikh imam dauke da
murmushi ya furta”bakomai Hateem, kada kaji komai, ai indai akan aikin lada ne
bazani ta6a gajiyawaba, koda zan shekara inayi ne, ni dai fata na shine Allah ya
dubi kyakkyawar niyarmu akan yaron nan ya bamu nasara akan ƙudirin da muke dashi na
ganin mun raba shi da miyagun dake bibiyar rayuwarshi” jinjina kai kowan nan su
yayi, shiekh imam ya daura da cewa”idan na samu natsuwa kafin zuwa dare, Zan turama
shi Awaisun addu’o’in daya kamata arunƙa mashi akan komai da zaiyi amfani dashi,
kada a kuskura abarshi ya yi gamon kan shi, tun da shi ba musulmi bane bai yi imani
da Allah ba, shaidanun dake ajikinsa bazasu ta6a bari ya ambaci sunan Allah, ko
ruwan addu’a zaku bashi ku tabbatar yasha akan idonku idan bahaka ba shaidanun zasu
iya zubar dashi ko su canza mashi ruwan batare da kun ankareba, tun da su ba
ganinsu akeyi”

“Insha Allah malam zamuyi ƙokarin yin hakan” acewar Boss man.

Ga dukkan alamu Prime minister Hateem bai lura dasu Batool ba, hatta shi kanshi
chief owais din, wani iko na Allah salsabeel dake kallonsu har kallonshi sukayi
babu alamun sun gane shi, nan take ya fahimci basu ruƙe kamanninshi ba, saboda sau
ɗaya suka ta6a ganinshi kuma a lokacin basu acikin hayyacinsu, jamimah da Azeeza da
parveen su dama basu ta6a ganinshi ba, asume aka fitar dasu daga kurkukun.

“Lahh! Ji wani mai kama da Danish dinmu” muryar Jemimah ce ta fargar dasu, kusan
atare suka daura idanuwansu akan yaran
Zumbur jemimah ta miƙe taje gaban prime minister ta tsaya hada ruƙe qugu tana ƙare
mashi kallon mamaki da al’ajabi

Ɗaya bayan ɗaya yake bin yaran da kallon, Ya fahimci kallon mamaki suke yi mashi,
Boss man ne yai masu gyaran murya tare da cewa”Sajeed, kuzo ku gaishe da Kawun
Chief dinmu Owais sunanshi prime minister Hateem, wannan kuma shine chief dinmu
Owais” ya faɗa yana nuna masu chief da hannun shi.
Atare suka miƙe tsaye suka nufi prime minister cikin girmamawa suka gaishe da shi,
kafin suka gaishe da Chief Owais.
Murmushi prime minister yasakar masu har dimple dinshi ya lotsa, da mamaki suka
kalli juna ganin yadda kamanninsa da danish suke ƙara bayyana.
“Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, My Son ina kuka samu kyawawan ƴan mata da
samari masu kama da jinin family dinmu? Ai ni nayi tsammanin Danish ne kadai yake
kama damu amma sai nake ganin fuskokin ƴan uwana akan faces dinsu kodai idanuwana
ne suke nuna min badai ba”?
Sheikh imam na murmushi yace”ba kai kadai ba Hateem, ni kaina tun da nayi tozali
da yaran nan nake ta mamakin kamannin ku dasu”

“Uncle, waɗannan sune sauran yaran da muke kula dasu, Ƴan uwan danish ne” chief
owais Ne ya faɗa yana nuna su da hannun shi.
“My son Allah Ya tayaku ruƙo, Ina ƙara yaba maka da jinjina maka akan ƙoƙarinka”
calmly chief ya furta mashi thanks”
“Sajeed, mu tafi masallaci, Batool kija sauran ƴan uwan naki ku tafi ɗaki ku yi
sallah, Boss man ne yayi masu maganar,
Cikin sanyin murya batool tace”Idan muka kammala yin sallah zamu Iya zuwa ɗakin
ɗan uwanmu Danish mu duba shi” da ta furta maganar har chief owais saida ya kalleta
kafin ya kau da idon shi.
Salsabeel ne yace”ku ƙara hakuri yanzu bacci yake yi, sai dai zuwa anjima idan sun
farka” amsa mashi tayi da toh, tayi mamakin ganin yana sakar mata murmushi, yayi
tsammanin idan sukaji muryarshi zasu gane shi amma still babu alamun zasu gane ɗin.
“Ina ƴar uwarku Unaisah”? Ya jefa mata tambaya, kafin ta bashi amsa boss man ya
rigata cewa”taje ɗakin ummi ne”
Prime minister yace”In sha Allah zuwa anjima idan na dawo gidan zanyi magana daku”
ya faɗa yana nuna su batool,’ amsa mashi sukayi da toh, hadi da yi masu godiya.

Bayan tafiyarsu Batool taja sauran ƴan uwanta mata suka nufi ɗakin su.
*SIR MUBARAK✊*

Tun wuraren ƙarfe takwas na safe suka baro asibitin kafin tafiyarsu saida Sir
mubarak yayima Dr fawan Alheri saboda yaji daɗin Yadda ya taimaka mashi wurin ganin
Jazz Ya samu lafiya, da matsakaicin gudu motarsu ta haura saman titi, Major ne yake
yin driving dinsu, yayin da sir mubarak da jazz suke zaune a back seat na motar.

Ya ruƙe hannun jazz acikin nashi, kamar ance za’a ƙwace mashi shi, Jazz sai
faman lumshe idanuwanshi yake yi kamar mai jin bacci,
“Jazz me kake tunani naji kayi shiru tun da muka fito daga asibitin baka ce komai
ba,” cikin kulawa Sir mubarak yayi mashi magana yana dubanshi
In a cool voice ya furta”Ina tunanin khadija, bata sha maganinta na safe ba
bansani ba ko salsabeel Ya bata”
Murmushin gefen fuska Sir mubarak yayi”idan na fahimceka kana magana ne akan
Yarinyar nan mai ta6in hankali ta gidan kajin da kuke kiwo ko ba haka ba” ya fada
da zolaya yana ɗaga mashi gira, tuntsirewa sukayi da dariya gaba ɗayansu hatta
major dake driving dariyar yake yi.
“Daddy dan Allah mu daina tuna abun da ya wuce” sir mubarak ya ce”okey na daina
my son, tun da baka so”
Gyaran murya Major yayi sir mubarak ya dago yana kallon fuskarshi ta cikin
mirror.

“Sir, ina zamu nufa? gidanka ko can gidan da Yaran suke?”

Shiru sir mubarak ya danyi kafin yace”mu wuce gida, jazz yana son ganin
mommynsa, nasan tayi kewarshi, in yaso daga baya sai muje can gidan” Amsa mashi
yayi da toh.

“Idan mun isa gida please ka kira tiger A waya ka tambaye shi awani hali yaran
suke aciki, inason sani”
Cikin girmamawa Major Ya ce”in sha Allah Yalla6ai zan tuntu6e shi’
Ajiyar zuciya sir mubarak Ya sauke tare dakai dubanshi ga Dr jazz,
“My son, ya zamuyi? Bansan ta yadda zanyima mommynka bayani ba, gashi ni ban iya
ƙaryaba, nasan dole ta shiga damuwa idan ta kalli fuskarka,” fuskarshi a yamutse
yayi maganar, har cikin ranshi baison 6acin ran turai duk da yasan zata fahimce shi
amma dole taji ba daɗi.
“Daddy kada ka damu, idan mukayi mata bayani zata fahimce mu in sha Allah”
“Allah yasa my son” daga haka babu wanda ya ƙara yin magana acikinsu, har suka
shigo estate, Motarsu bata nufi ko’ina ba sai katafaren gate din Gidansa
A harabar ajiye motocinsa sukayi parking, babu wanda yasan da zuwansu, da sauri
Major ya fito ya zagaya ta baya ya buɗe masu mota, sir mubarak ne ya fara fitowa
kafin Ya taimaka ma Dr jazz shima Ya fito, hannunshi ɗaya dafe da waist din shi.
saboda baya iya tafiya dai dai, tun lokacin da sir mubarak ya cakumi rigarshi ya
buga shi da ƙasa ƙafarshi ɗaya ta lanƙwashe daƙyar yake iya takata a yanzu.

A haka suka nufi cikin gidan, banda Major wanda tuni Ya nufi sauran ƴan uwanshi
sojoji dake kai komo a cikin gidan.
A zaune yake saman Sofa, ya ɗauki wankan dark jeans and white V-neck shirt
kayan sun bi shape din jikinsa, hankalinshi a kwance yake operating laptop din
gabansa dake ajiye kan table,
Fitowa mom turai tayi daga cikin kitchen hannunta ruƙe da mugs guda biyu na
coffee, ta nufi cikin falon fuskarta asake taje gaban table din Zaki ta ɗaura cup
ɗaya
“Ga wannan My son, Nasan zaka buƙace shi” ɗagowa yayi fuskarshi ɗauke da murmushi
ya furta”mom nagode da kulawarki agareni, kina ji da ɗan nan naki”
Kafin ta kuma cewa wani abu muryar ibad ta janyo hankulansu ga dubanshi,
fitowarshi kenan daga cikin ɗaki Sai faman yin miƙa yake yi haɗi da yin hamma, daga
shi sai short a jikin shi
Muryarshi da shagwa6a ya furta”mommy nifa”?
Zaki ne ya bashi amsa da cewa”Na ƙarfi ne zoka ƙwata, ɗan rainin wayau sai yanzu
ka ga damar tashi daga baccin”
Tur6une fuska yayi”babban yaya jiya fa bamuyi wani isasshen bacci ba, shine nake
yin ramuwar na jiyan”
Dariya mom turai tayi shagwa6ar ibad har mamaki take bata, duk da shima jazz idan
abun ya motsa yana yi mata shagwa6a
“Ranka zai 6aci ne idan ka ci gaba dayi min shagwa6a kamar wani ƙaramin yaro,”
Bubbuga ƙafafuwanshi yayi hada ruƙe qugunsa wato yayi sai dai ayanka shi
Mom turai tace”sai fa kana haƙuri da shi, kasan autane kuma kai ka rainesa duk
abun da yayi kai ne ka sangartar da shi”
Ta6e baki Zaki yayi tare da kau da idonshi daga kan fuskar Ibad Ya miƙa hannu ya
ɗauki mug Ya soma kur6ar coffee..
“last born zoka kar6i wannan” girgiza mata kai yayi”no mommy, na hannun shi
nakeso yasha ya rage min, wannan nakine ki sha” a sukwane Zaki ya dakata da shan
coffeen Ya waiwayo yana dubanshi, Ya rasa gane dalilin dayasa Ibad yake yi mashi
haka, aduk lokacin da zai ci abu saiya sa rigima akan yaci ya rage mashi kamar wani
tsaran wasan shi
“Kada ka damu zan shiga kitchen in haɗa nawa, kai dai kar6i kasha” mom turai ce
tayi maganar
Ibad ya maƙe mata kafaɗa”mom ni ai nafison yasha ya rage min”
Girgiza kai Zaki yayi tare da kallon mom turai yace”zan rage mashi”
“Amma ai baida yawa taya zai isheku ku biyu abunda baifi rabin cup ba”
“Idan bai ishe mu ba, zan turo shi ya ƙaro mana wani a kitchen”
Gyaɗa kai tayi okey, Har ta nufi sofa zata zauna, sallamar sir mubarak ta katse
mata hanzarinta,
Kusan atare suka kai idanuwansu ga duban ƙofar falon
Shigowa Sir mubarak yayi hannunshi dafe da dr jazz, tsabar firgice Yasa mom turai
ta saki mug din hannunta gaba ɗaya ruwan coffeen Ya zube kan floor, Jikinta na 6ari
ta nufe su, Hankalin kowan nan su ya tashi, zaki tuni ya dakata da shan coffeen a
hanzarce ya miƙe ya nufi sir mubarak, Ibad kuwa hannayenshi biyu ya ɗaura saman
kanshi yana ambaton”mun shiga uku, ɗan uwa Jazz meya same ka? Kayi hatsarin mota
ne?

Muryar turai na rawa take fadin”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, babe meya faru
da jazz ɗina? idanuwanta har sun fara fitar da ƙwalla,
Sir mubarak bai sauraresu ba, Ya nufi sofa da sauri zaki Ya taimaka mashi suka
zaunar da jazz.
A Hankali Ya ɗago Yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya tsayar da idanuwanshi kan
mom turai da tafara sharar ƙwalla, Jikinta asanyaye ta nufo su ta zauna gefen jazz
ta ruƙo hannun shi acikin nata,
“Kayi shiru bakace komai ba? Meya faru da jazz”?
“Daddy kai muke sauraro,” acewar Ibad wanda tuni ya dawo gefen ɗan uwanshi zaki ya
tsaya hadi da ruƙe qugunshi
A tsanake ya soma yi masu magana”ku kwantar da hankalinku.....” tunkafin ya
ƙarasa maganar, mom turai ta katse shi ta hanyar yi mashi tsawa tana fadin”taya
zakace mu kwantar da hankalin mu? Yaro ya fita gida lafiyarshi qalau yanzu kuma ka
dawo dashi goshi ɗaure da bandage ga tabonni akan fuskarshi, sannan babu kayan da
ya fita da su a jikin shi, ni dama tun jiya hankalina bai kwanta da fitar jazz ba,
babe ka faɗamin meya faru da yarona”!! idanuwanta azazzare tayi mashi maganar.

Tun da yake da turai bata ta6a gigin katse shi yana cikin yin magana ba sai yau,
hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa ranta yakai maƙura a wurin 6aci,
“Mommy, yaya zaki, Ibad” dr jazz ne ya ambaci sunayensu, a hanzarce suka kai
dubansu gare shi.

“Zanyi maku bayanin komai”


“A’a jazz shi nake so yayi min bayani, gaba daya a raunace kake, ka daina yin
magana zaka fama ciwonka” ta faɗa tare da kallon sir mubarak wanda yayi shiru yana
kallon fuskarta...
“Meyasa ka tsareni da ido? Ba zaka yi min bayani ba”?
Bai tanka mata ba har saida ya samu wuri saman sofa dake fuskantar su, Ya zauna,
tukunna ya samu natsuwar yin masu bayanin komai daya faru.......
A ƙarshe yace”bana buƙatar wani yaji abun nan saboda aikin sirri ne sukeyi, basu
buƙatar kowa ya sani, Na faɗa maku ne don na wanke kaina daga zargin da zakuyi min
na halin da na jefa jazz”
Cikin sanyin murya turai tace”am sorry dear, nayi maka tsawa bisa rashin sani,
kayi hakuri dan Allah, hankalina ne ba akwance ba”
“Na fahimce ki,” atakaice ya furta hakan
Mayar da duban ta tayi akan jazz”dan Allah nan gaba kada ka ƙarayin wannan
gangancin, duk wani abu da zakayi ka sanar da mahaifinka koda ace ni bazaka sanar
min ba,” amsa mata yayi da toh,
Kafin ta juyo da dubanta kan sir mubarak”Babe, babu wasu kalmomi da zan iya yin
amfani dasu wurin yi maka godiya saboda irin kulawar da kake ba jazz.....” kafin ta
ƙare maganar sir mubarak yai hanzarin katseta”Kada na sake jin kinyi min godiya
saboda nayiwa jazz abu, kinsan banaso” cikin sanyin murya tace”nadaina in sha
Allah”
“Daddy, sannu da dawowa, nayi missing dinka sosai, meyasa jiya baka faɗamin halin
da kake aciki ba ai da nazo asibitin na tayaka jinya” zaki ne yayi maganar yayin da
yake ƙoƙarin zama gefen jazz
Murmushi sir mubarak ya sakar mashi”sanyin idaniyata, ina fata na same ku lafiya”?
Mayar mashi da martanin murmushin Zaki yayi”lafiyalou, sai dai jiya dukkanmu bamu
runtsa ba saboda rashin ganinku da bamuyi ba”
Sir mubarak yace”shiyasa naga idanuwanku sun kumbura, ashe bani kadai na kwana
azaune ba”
Tun da suka fara magana ibad ya haɗe ranshi,
“Daddy ni baka ganni bane”? Ya faɗa yana duban sir mubarak
Girgiza kai ya ɗanyi kafin yace”naganka ibad, amma nida kai wanene ya dace ya
fara gaishe da wani? Yamutsa fuskarshi yayi ƙasa ƙasa da murya ya furta”sannu da
dawowa dad” ta6e baki sir mubarak yayi saida na roƙa, bubbuga ƙafa ibad yayi
Mom turai tace”mu shiga ciki, in taimaka maka kayi wanka” zaro ido Ibad yayi haɗi
da furta”Mom wa zaki ma wanka? Jazz ko daddy”? Duk da halin da suke aciki na
damuwa hakan bai hanasu yin dariya ba, shi kanshi jazz din saida ya murmusa,
“Daddynku nake magana akai,” hannu biyu yasa ya toshe bakinshi, Idan ya kalli sir
mubarak sai ya kalli mom turai
Ko kaɗan batajin kunyar ƴa’ƴanshi, saboda ita aganinta bawani abu bane donta
furta hakan agabansu.
“My son, zamu shiga”
Zaki yace”okey, zan tafi da jazz ɗaki, zan taimaka mashi yayi wanka ya canza kayan
jikinshi’
“Hakan yayi,” ta faɗa tare da duban Ibad Har yanzu mamaki bai sake shi ba, sai
kace baiyi rayuwa a turai ba.
“Akwai kayan abinci dana shirya mana a kitchen, ka shiga ka dauko su a dining
zaka jera”
Amsa mata yayi da toh, da sauri ya juya ya nufi hanyar kitchen
Miƙewa zaki yayi tare da ruƙo jazz ya miƙar dashi,
“Allah ya baka lafiya my jazz,” amsa mata yayi da ameen, kafin suka nufi ɗakin
shi
Bayan tafiyarsu ta dubi sir mubarak”ina ƙara baka hakuri, kasan ba halina bane”
Murmushi yasakar mata”kada hakan ya dame ki, ni dama fargabana halin da zaki
shiga, but Alhamdulillah tun da kin fahince ni, yanzu bani da sauran damuwa” Ya
faɗa tare da ruƙo hannunta suka nufi bedroom dinshi
“Jiya nayi kewarka, idanuwana sunyi maraicin ganinka, dole na haƙura na rungume
pillow amadadinka” tayi maganar ayayin da take taimaka mashi wurin cire Rigar
jikinshi
Daɗaɗan kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba, shiyasa akoda yaushe
yake ƙara jin sonta, saboda ƙaunar da take nuna mashi, tun farkon auransu bata ta6a
barin ya shiga toilet yin wanka shi kadaiba sai idan wani uzirinne mai ƙarfi ya
hanasu shiga atare, sannan ta hana ya ajiye mata masu aiki agida ba yadda baiyi da
ita ba akan baison tanayin aikin wahala amma taƙiya saboda kishinshi da take yi,
batason wata ta ƙwace mata mijinta,
Atare suka shiga toilet.

*ANEELERH*

Tun bayan da ta shiga toilet tabar Zahra atsaye tana kallon hoton su, lokacin da ta
fito daga wanka bata taras da zahra a dakinta ba, shaf shaf ta shirya kanta cikin
shiga ta abaya maroon colour, ta yafa mayafi akanta, fitowa tayi daga dakin a
dining room ta taras da su gaba ɗaya sun hallara kan dining chairs, tun daga kan
abie dinta, uncle ɗan iya, mami da ummi da kuma mahboob, sai zahra kaf dinsu ne,
kowa ya kimtsa domin yin ɗa’amin, Ana ce take yin serving dinsu tana daga tsaye
hannunta ruƙe da serving spoon.
Sautin takun takalmantane Yaja hankulansu ga dubanta, fuskarta da fara ta
ƙarasa cikin girmamawa ta soma gaishe da iyayenta
“Barka da safiya, ina kwananku, kun tashi lafiya”
Fuskokinsu asake suka amsa mata.
Mahboob Yace”Gm Auntyna, bismillah zoki zauna gefena” ya faɗa yana nuna mata
empty chair din dake gefenshi
Zahra dake kallonsu, murmushi tasaki ganin yadda mahboob Yake yima Aneelerh
fadanci abunda bai saba Yi ba.
Bayan Aneelerh ta zauna, Ana ta gaishe da ita, a mutunce ta amsa mata”two days
bana ganin ki, kin 6oye min sai kace ba gida ɗaya muke a zaune ba, sai dai idan ni
na matsu da son ganinki in shiga kitchen time da kike Yin girki ko”? Sunnar dakai
ƙasa Ana tayi yanayin fuskarta babu walwala,
Mami tace”Ai ba tun yauba na lura halinta ne batasan sakewa cikin mutane, kullum
kina ƙumshe daga kitchen sai ɗaki, yakamata kina fitowa falo muna yin fira dake”
cikin kulawa mami tayi maganar.
Cikin sanyin murya ta furta”ay min afwa zan dinga futowa daga yanzu”
Mami tace”haka nakeson ji, ki daina daukar kanki a matsayin ƴar aiki, damu dake
duk abu ɗayane awurin Allah, so please adaina kuntata kai adaki” murmushi Ana tadan
saki har cikin ranta taji dadin maganar mami, zahra tace”idan ma bata fitoba ni
dakaina zan dinga zuwa dakinta ina takura mata da surutu” dariya Ana tasaki,
ummi tace”dako ta shiga uku dake, har bacci sai kin hanata saboda zafin ɗuminki”
tur6une fuska zahra tayi, jin abun da ummi tace, harara ummi ta jafa mata”lafiya
kike kallona, ko nayi maki ƙaryane? Kafin zahra tayi magana mahboob yace”wallahi
ummi gaskiya kika faɗi” yai maganar yana kokarin tura chips abakin shi”Zahra badai
ɗumiba, kamar aku, inta fara zuba kamar radio mai jini, ga tambayar tsiya kamar
tsohuwar ƴar jarida” gaba ɗayansu suka sanya dariya, ran zahra ya 6aci a ƙule
tace”hmmm mahboob ai ƙwarani, wai talla zaiwa audi gori, idan ni surutu gare ni kai
fa? Saboda shegen maƙonka ko kuɗi zaka ƙirga sai ka shiga toilet don kada wani ya
gani” dariya su ka yi, Abie Da uncle ɗan Iya sun kasa kunne suna sauraran su, ganin
surutun nasu bame ƙarewa bane yasa uncle dan Iya yi masu gyaran murya hankalinsu ya
dawo kanshi”surutun Ya isa haka, kun cika mana kunne, Yakamata ku maida hankalinku
akan abun da ku ke ci, kun riga da kunsan babu kyau ana cin abinci ana surutu”
tunda ya ambaci hakan kowan nan su yaja baki yayi shiru, baka jin sautin komai
saina cokulansu kwas kwas tamkar zasu fasa plates din abincinsu, gaba daya hankalin
Mahboob dana Aneelerh yana akan Ana, ga dukkan alamu sun fahimci babu lafiya
atattare da ita, tun daga kan yadda take faman zazzare idanuwanta.

Cup din lemu Aneelerh ta dauka takai baki tana kur6arshi, bayan ta kammala sha
tace”ki koma ɗaki ki zauna ki hutu” ta fada tana duban Ana
“Inaso ne ku kammala cin abinci in kwashe kayan, akwai sauran aiki da zanyi wanke
wanke da gyaran kitchen idan na kammala sai in huta”

Aneelerh tace”kada ki damu zanyi maki aikin, just ki tafi ɗaki ki huta”

Harta buɗe baki zata kuma yin magana mahboob ya tari numfashinta da cewa”Sis Ana,
kiyi abunda aunty Aneelerh ta fada maki, nima zan tayata yin aikin”
Gyaɗa kai Ana tayi cikin sanyin murya ta furta”nagode madam, Mahboob thank u” ta
fada tare da juyawa ta nufi bedroom dinta da sauri, hatta yanayin tafiyarta babu
natsuwa.
Kallon juna Aneeelerh da mahboob sukayi, da ido tayi mashi nuni dayabi bayan Ana
yaji masu meke damunta.
Jinjina mata kai yai alamar toh, miƙewa yayi daga kan kujerarsa yakai hannu ya
yago tissue Ya goge bakinsa.
“mahboob harka kammala cin abincin”? Uncle ɗan Iya ne ya jefa mashi tambayar.
“Ban ƙoshi ba daddy, ina son zan shiga toilet ne uziri gare ni” uncle ya amsa
mashi da okey.
Da sauri Ya juya yabar dining area din,
Kasancewar Bedroom dinsa dana ana a 6angare daya suke shiyasa yai ƙaryar cewa
toilet zai shiga.
Tunkafin mahboob Ya shiga ɗakinta ya soma jiyo shessheƙar kukanta, Hankalinshi
yayi mugun tashi, koda ya ruƙo handle din ƙofar room din nata adatse ya Ji ta,
muryarshi ƙasa ƙasa Ya ambaci sunanta shiru bata amsa mashi ba, knocking kofar
yayi”sis ana ki buɗe min ƙofa dan Allah, Inason yin magana dake, Aunty Aneelerh ce
ta aiko ni”
Jin ya ambaci sunan aunty aneelerh yasa tayi saurin shiga toilet ta wanko
fuskarta, jiki na rawa tazo gaban ƙofar ta buɗe mashi ita.
Ajiyar zuciya ya sauke yana bin fuskarta da kallo, idanuwanta sun kaɗa jawur da
su.
Ruƙo hannunta yai acikin nashi kamar wani babban mutun Yajata zuwa cikin dakin,
Ya kulle ƙofar.
Tare da goya hannayensa saman ƙirjinsa Yana kallon fuskarta
Ganin ya tsareta da ido yaƙi yin magana ne yasa tace”mahboob lafiya kake kallona?
Me aunty Aneelerh tace ka fada min”
Numfashi yaja kafin ya soma yi mata magana
“Meke damunki? daga ni har aunty Aneelerh mun fahimci bakya jin daɗi kamar akwai
wani abu dake damunki”
Adabarbarce ta furta”babu komai mahboob lafiyata qalou....”
“Bazai yiwu ba Ana, saboda kafin na shigo ɗakin ki na jiyo sautin shessheƙar
kukanki, taya zakice min bakomai? Bayan ga alamu nan nagani akan fuskarki, dan
Allah Ana kada ki 6oye mana abunda ke damunki, kinga mun damu dake ni da aunty
aneelerh dama sauran mutanan gidan”? A marairaice mahboob yayi mata maganar
Baiwar Allah tayi zuru da ido, komai nata ya canza.
Ƙoƙarin danne damuwarta tayi hawayen da suka taru acikin idonta tayi saurin
mayar da su.
Can ƙasan makoshi sound din muryarta ke fita

“Dagaske nake yi maka mahboob, babu abun da ke damuna, idan ma saboda shessheƙar
kukan da kaji ina yi ne to ka kwantar da hankalinka, sister dina ce janet ta kirani
awaya tana fadin halin da take aciki Na rashin kuɗin da zatayi amfani dasu, gashi
bata da koshin lafiya ko aikin da take zuwa yi a hotel yanzu komai ya ta6ar6are
mata, idan ba zaka mantaba na ta6a baka labarin ƴan uwana Janet da esther, har na
fada maka cewa mu marayune bamu da kowa neman na kanmu muke Yi, A halin yanzu dai
nice nake taimaka masu da kuɗin da suke siyan abinci da suturar sanyawarsu, nima
idan natara kudin albashina ne nake samun wanda nake tura masu.....

tunda tafara magana jikin mahboob yai sanyi, tausayinta duk ya kama shi, har cikin
ranshi ya yarda da abunda ta faɗa mashi.
“kinsan da abun da ke faruwa da ƴan uwanki shine baki faɗa mana ba? Meyasa? Meya
amfanin zaman taren Ana”?
Fashe mashi tayi da kuka tana fadin”bana so ne na takura maku, shiyasa ban fada
maku ba”
Dafe kai mahboob yayi dahannu ɗaya ranshi ya 6aci afadace yace”kin ban mamaki
yanzu ko aunty aneelerh baki Iya faɗama damuwarki ita da ta dauke ki tamkar
jininta, gaskiya ni baki kyauta min ba Ana, banyi zaton hakan daga gare ki ba, ashe
baki daukemu kamar yadda muka dauke ki ba”
Ruƙo hannayenshi tayi acikin nata yayin da hawaye ke fita akan fuskarta
tace”mahboob am sorry, idan ranka ya 6aci”
Ta6e mata baki yayi”Ni zanje na fada ma aunty aneelerh halin da ƴar uwarki take
aciki, nasan zata taimaka maki, Nima zanyi kokarin baki wani abu, ki cika, itama
zahra zan mata magana, sai mu haɗa maki kudin da zaki tura masu ......”
Godiya ta soma yi mashi
“Nagode mahboob, naji dadin taimakon da zaka yi min”
Sakin fuskarshi yadanyi”dan Allah daga yau ki daina sanya damuwa aranki, ni
nafiso in ganki cikin kwanciyar hankali, fuskarki da annuri, idan ma wani abu na
damunki, please ki runƙa sanar dani, zan taimaka maki da abun nake dashi, ga kuma
aunty aneelerh itama ki dinga fada mata damuwarki”
“Zanyi hakan mahboob nagode da kulawarku agareni”
Sai da mahboob ya tabbatar ya sanyata farin ciki, kafin Ya fito daga dakin Ya
nufi dining area Koda ya ƙarasa bai taras da Aneeleerh da zahra ba, Har sun kammala
yin breakfast dinsu, daga can falo Ya hango mami da ummi, zaune suna fira tare da
Uncle ɗan Iya da abie.
Hatta kayan abincin an kwashe su daga dinning, harya juya zai nufi dakin Aneelerh
ta wutsiyar idonshi Ya hango gifcinta a kitchen, da sauri Ya nufi kitchen tun kafin
Ya ƙarasa ya jiyo muryar zahra ta zaƙe tana ba Aneelerh labarin shagalin birthday
din obie da akayi, maimakon Ya shiga sai ya la6e gefe daya ya kasa kunne Yana
sauraronsu.

Babu wanda ya lura dashi acikinsu saboda sun bashi baya.


Aneelerh tana gaban Sink Ta tattara kwanukan da suka 6ata tana wankesu, zahra
tana agefenta
“Aunty Aneelerh ina baki labari, wallahi Anyi 6arin dollar a wurin nan, dangin
obie sun gaji arziƙi gaba da baya, wai kinga manya manyan mutanan da suka halarta?
Attajiran masu kuɗi masu manyan muƙamai, kowa kika gani a filin taron da
matsayinsa, daga governor sai president, ga sanatoci da ministoci......”
Murmushi Aneelerh tasaki tana fadin”Gaskiya naji takaici da ban biki munje taron
nan ba, da nima na kashe kwarkwatar idanuwana”
“Aunty Aneelerh duk yadda zan baki labari bazan iya fada maki kwatankwacin abun
da idanuwana suka gane min ba, nifa lokacin da ƴa’ƴan baba obie suka fito tsakiyar
fili sunayi mashi liƙi Yana taka rawa wallahi ji nayi kamar inyi wuff in shiga
filin in tattara kuɗin in saƙe a hammata”
Tuntsirewa aneelerh tayi da dariya tana duban zahra, hada kwatanta mata yadda zata
kwashe kudin ta saƙe ahammata.

Mahboob dake a la6e yana sauraron su dariya ce kumshe abakinshi.

“Ni abun da yafi burge ni, haɗuwar ƴa’ƴan baba obie da jikokinsa, da surukansa
sun ɗauki wanka na mutunci na kece raini kai komai ma sun haɗa, waɗanda suka fi
burgeni kinga prime minister Hateem, da president dinmu Sharafudeen sun iya
dattako, komai nasu da aji suke yin shi, matayensu sunfi kowa haduwa gimbiya
mujeedat da Hajiya malikat sarauta, sai kuma mutuniyata Hajiya saratu inayin
matarnan saboda tana ƙaunata mutane suna fadin masifarta ni wallahi bata ta6a yi
min koda tsawa ba kamar ƴar cikinta haka take yi min magana....” da farin ciki akan
fuskarta tayi maganar.

Aneelerh tace”Jinin ku Ya haɗune dana juna, Allah yasa ta zama surukarki kinga
shikenan kema zaki samu matsugunni a obie estate” wani irin ihun farin ciki zahra
tasaki hada jujjuya qugu tana fadin”Amen Ya Allah, Aunty Aneelerh Allah ya kar6i
addu’arki”

Dariya Aneelerh tasaki yayin da take ɗauraye plates din da take wanke wa da ruwan
dake fita a faucet.

“Zahra baki faɗamin haduwarki da mutumin ba”?


Kwa6e fuska zahra tayi annurin fuskarta ya ragu.

“Bai zo taron ba, duk irin burin dana ci nason ganinshi bai halarta ba, banji
dadi ba dama nasan zai yi wuya yaje saboda mutunne shi da baisan hayaniya”

“Eyyah zahra najiye maki baƙin ciki, in sha Allah wata rana zaku haɗu da shi”

Ta6e baki tayi”Ni yanzu ba wannan ba auntyna, Inataso in baki labarin Nazli da
Yazrin Ƴa’ƴan Prime minister da ƙanwar Chief Owais hindu, kinga waɗannan dana
lissafa maki ƙarshene su afagen kyau da aji, cikin maza kuwa in ka cire chief owais
sai wani ɗan uwansu menene ma sunanshi.....” ta faɗa tana cizon yatsa takasa tuna
sunan.

“Namanta, shima a canada yake zaune, mutumin ya iya ɗaukar wanka, ga kyau da aji
bayan shi sai twins sun haɗuwa sunyi kyau kamar dollars.

Dariya Aneelerh tayi, jin yadda zahra ta haƙiƙance tana bata labari ko gajiya
batayi.
“Yanzu faɗa min alherin da sukayi maki naji ɗazu kince zaki fada min”
Gyara tsayuwa zahra tayi kafin tace
“Kinga da farko Hajiya saratu tayi min kyautar tsadadden leshi guda biyu, da hand
bag, hada set na agogo da zobe, da turarurruka......” jinjina kai Aneelerh ta yi
tana fadin”masha Allah, zahra najiye maki daɗi, kin samu na sallah”

“Bangama fada maki ba, bayan kuɗin aikin decoration da hajiya saratu ta biyamu,
prime minsiter yayi mana kyautar kuɗi duk mutun ɗaya 1.5 million” waro ido waje
Aneelerh tayi mahboob dake la6e jin an ambaci kuɗi sai gashi ya dawo gefen zahra
Yana raira waƙa.

“In rabo ya tsago dakai kuma abun ya tabbatar saida kai to rabbine yace sai da
kai in sai da kai kawai sai da kai, don haka nima Allah ne ya tsaga da rabona ashe
arziƙine ke kirana......” gaba ɗaya suka sanya dariya, Aneelerh tace”mahboob yaushe
ka shigo kitchen din nan”

Da murmushi akan fuskarshi yace”tun ɗazu ina la6e bakin ƙofa na kasa kunne ina
sauraron aku sarkin ɗumi, yau surutun zahra yayi min rana wannan arziƙi haka, wato
saboda baƙin ciki zahra ƙiri ƙiri kika hana in rakaki obie estate da yanzu hadani
za’ayi rabon kuɗin nan....”

Dariya zara tayi tana fadin”ai baka ji komai ba, bayan kuɗin da prime minister
yabamu, president Ya ƙara mana, duk mutun ɗaya dubu ɗari takwas” dafe ƙirji mahboob
yayi kamar wanda yaji wani mugun abun
“Sannan Abokin Baba Obie, Jan kunne ya raba mana dubu ɗari biyar biyar da dollar
ya bamu su”
Kallon juna mahboob da Aneelerh su kayi.
“Anya zahra dagaske kike kuwa? Wannan kuɗi haka kamar akan bishiya ake tsunkosu”

Hararar shi zahra tayi”an gaya maka kowa mai maƙone irinka, ai su a wurinsu kuɗin
da suka bamu bakomai bane”

Jinjina kai mahboob yayi”Allahumma arzuƙni, Sister Yanzu ina kuɗin suke? inaso zan
tayaki ƙirgawa”

Dariyar shaƙiyanci zahra tayi kafin tace”suna kwance cikin account bank dina suna
bacci, dollar din da aka ba mu ne kaɗai suke a dakina kuma na 6oye su saboda nasan
halinka sarai, tsaf zaka Iya zuwa ɗaki yi min halin 6era”

Dariya Aneelerh tasaki, a lokacin ta kammala yin wanke wanken, ta mayar da


hankali akan fuskar zahra
Mahboob Yace”kar dai kice zakiyi min rashin mutunci wallahi sai inyi zuciya inje
in nemi auran ɗaya daga cikin jikokin baba obie”

Dariya suka saki gaba dayansu bayan sun tsagaita Aneelerh ta dubi mahboob”Ya ake
ciki? Kunyi magana da Ana”?
Ɗaga mata kai yai alamar eh, zahra tace me ya faru ne ko bata da lafiya”

Nan mahboob Ya kwashe komai Ya sanar dasu dangane da halin da Ana take aciki.

Shiru sukayi jikin kowa yayi sanyi, musamman Aneelerh, ranta Ya dan 6aci bata ji
dadin ƙin gaya matan da tayi ba.

“Idan kuwa hakana Ana bata kyauta min ba,Yanzu har akwai abunda zata 6oye min duk
irin shaƙuwar dake atsakanin mu?”

“Aunty Aneelerh please kada ranki ya 6aci, na riga da nayi mata faɗa, abun da ya
dace ku harhaɗa mata kudin da zata turama ƴan uwan nata”

Zahra sarkin tausayi tace”nida da halima wallahi da sun dawo gidan nan da
zama.....” wata uwar harara Mahboob Ya watsa mata”saboda ke zaki ciyar dasu ko”?
Fashewa sukayi da dariya.
Aneelerh tace’baka da dama mahboob, yanzu fa ka gama fadin a harhada mata kudi
aturawa ƴan uwanta shine kuma don tace su dawo nan da zama kake tada jijiyoyin wuya
daga maganar taimako”

Yamutsa fuska mahboob yayi”abun da nake nufi Aunty Aneelerh, ɗan adam ba abun yarda
bane, muna iya mu taimake su su kuma su butulce mana shine abunda nake jiye mana,
kawai dai ƙwara in taimakon zamuyi masu mu tura masu can su ƙarata”

“Ka faɗi gaskiya mahboob, nima nayi wannan tunanin, Yanzu me yakamata muyi”? Acewar
Aneelerh.

Zahra tayi karaf ta kar6e dacewa”kowa ya kawo abunda yake dashi hada kai mahboob
nakama sai yafi yawa tunda kaine jagaba atafiyar”

Harararta yayi”zahra ki daina wannan maganar, ni bawai bazan bada ba, idan na bada
ai ba faduwa nayi ba, duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai ji ƙansa, ga lada
da mutun zai samu, kawai dai ni bani da kuɗinne Yanzu.....” ya fada yana soso
keyarshi.
da zolaya zahra tace”hmmm, Ana fa ba musulma bace, ta ina zamu samu lada idan muka
taimake ta”?
Banza yayi da ita baice komai ba, Aneelerh tace”babu ruwanmu da wannan, don Allah
zamuyi da kyakkyawar niya, kidaina wannan tunanin” gyaɗa kai zahra tayi”shikenan
naji, zan bata wani abu cikin kuɗin dana samu, Mahboob Idan kana da acct number
dinta ka tura min” Aneelerh tace”Ina da ita, Idan muka koma ɗaki zan tura maki,
Nima zan sanya nawa kudin”
Farin ciki ne tsantsa akan fuskar mahboob, Yaji daɗi zasu taimaki Ana batare da ko
sisin shi ba.
“Allah yabarmun ku sisters dina, zahra Allah ya baki miji nagari mai sonki mai
ƙaunarki, and aunty Aneelerh ubangiji Allah ya bayyanar mana da mijinki da ƴan
uwansa , Allah ya raya mana baby junaid dinmu....” addu’o’i yadinga yi masu suna
amsa mashi da ameen, kafin Ya juya zai fuce daga kitchen din
“Mahboob” kiran sunanshi da Aneelerh tayine ya dakatar da shi daga yin tafiyar ya
waiwayo yana kallonta
“Please idan ka fita ka faɗama su mami, zuwa anjima Hajiya adama zata zo kawo
mana baby junaid nasan bata sanar da ita ba”

“Aunty Aneelerh ashe yau muna da babban baƙo agidan namu, mutumina zai dawo, zamu
dasa daga inda muka tsaya”

Murmushi Aneelerh tasaki, zahra tace”wallahi har na kosa in ganshi,Yau zaisha


daƙuna duk saina sale mashi fatarshi” Aneelerh na murmushi tace”inaso zamu shirya
masu abincin da zasu ci, tun da Ana bata jin dadin zuciyarta mubarta ta huta sai
muyi aikin atare”

Zahra tace”Lafiyalou, dama na kwana biyu banyi girki ba, har cake zan haɗama baby
junaid dina”

Sun jima suna yin fira a kitchen kafin daga bisani suka fuce zuwa ɗakin domin yin
sallar azhar da aka fara kira.

*OBIE ESTATE🌃*

Idan muka koma 6angaren dattijon arziƙi, tunda garin Allah ya waye Hankalinshi ba
akwance Yake ba, gaba ɗaya yabi ya furgice masu sun rasa gane kanshi, ko jiya da
dare bai runtsa ba, sambatu yadinga yi masu yana firgita yana fadin ga macijij nan
zai sare shi, Ina owais dinshi Yana gani za’a cutar da shi bazai kashe macijin ba,
mutun biyu da suka taya shi kwana a ɗaki his excellency Deen ne tare da His
excellency abdul razak, su kansu basu yi bacciba jiya saboda halin da baban nasu
yake aciki, hatta sallar asuba agida sukayi ta yaƙi fita daga ɗaki, kuma ya hana su
tafi subarshi, bawan Allah ba ƙaramin jiki yaji ba, hada ruɗun tsufa ke damun shi,
daƙyar suka samu nasarar sanya shi yin baccin dole.

A yanzu haka Yana daga kwance saman gadonshi Ya ɗaura kanshi kan pillow, deen da
Abdul razak suna a zaune saman arm chairs din dakin idanuwansu akan fuskar baba
obie.
Jin motsin buɗe kofane Yaja hankalinsu ga kallon mai shigowa
Senate lateef ne, fuskarshi babu walwala.
Daren jiya da damuwar abunda ya faru ya kwana
Miƙa masu hannu yai suka gaisa da ƴan uwan nashi
Kafin ya dubi baban nasu dake kwance kan gado yace”Bacci yake yi ko idon shi
biyu”?
His excellency Deen ne yace”bacci yake yi, daƙyar muka samu Ya runtsa” ajiyar
zuciya senate lateef ya sauke kafin yace”banji dadin abunda ya faru jiya ba, gashi
har yana neman zautar mana da mahaifinmu, wai taya ma akai har maciji ya shigo part
din nan”? Rai amatuƙar 6ace yayi maganar
His excellency Abdul razak Yace”abun da yafi ɗaura min kai shi Owais din Yace ba
maciji bane mutunne ya rikiɗa....”tunkan Ya ƙare maganar Senate lateef yace”inko
dagaske ne wannan maganar to kuwa ba mutun bane dama, Aljani ne sannan ita wannan
ifritun yarinyar mai kasada dana gani atare da shi wacece ita!”? Kafin wani ya
bashi amsa sallamar Pravin ta katse masu hanzarinsu,
Shigowa yai cikin shiga ta black suit.

Cikin girmamawa pravin ya gaishe da su, bayan sun amsa masu fuskokinsu babu
walwala, pravin ya soma yin magana
“Baba bashi da lafiya ne? naga da asuba bai halarcin masallaci ba”
“Baka ga abun da ya faru jiya bane”? Acewar senate lateef.

“Nagani, kar dai ace shi ne ya hana shi sukuni”? Cikin nuna kulawa yayi maganar.

His excellency abdul razak Yace”ai kuwa dai shine, don jiya ko bacci baiyi ba
tsabar firgici, yanzu haka ma da kake ganin shi a kwance daƙyar muka samu yayi
bacci’
“Abu baiyi daɗi ba” pravin ya faɗa yana ɗan girgiza kanshi”ubangiji Allah ya
bashi lafiya” atare suka amsa mashi da Ameen.
Senate lateef ya ɗaura da cewa”ni yanzu so nake naji daga bakin shi Owais, ya
faɗa min wanene macijin menene alaƙar shi dashi”
“Bari na kira shi awaya, ai jiya yace zai shigo yai mana bayani amma shiru kake
ji wai malam yaci shiru” Deen ne yai maganar tare da curo wayarshi daga aljihu ya
danna ma Chif Owais Kira, kusan sau uku tana yin ringing bai yi picking ba.

“Bai ɗaga ba, may be baya akusane da wayar” ya fada yana kokarin maida wayar cikin
aljihun, kwatsam kiran owais ya shigo wayar tafara ruri, ajiyar zuciya ya sauke
tare da duban su yace”shi ne ke kira,” ya fada tare da yin picking din kiran Ya
kara wayar a kunnanshi, bayan sun gaisa deen yace”muna ta tsammanin zuwanka gida
shiru baka shigo ba, ga babanku nan kwance ba lafiya saboda abun da ya faru jiya ko
runtsawa baiyi ba sai firgita yake yi”.

On the other hand chief Owais ya furta”I will come later, insha’Allah,”

“Okay, we’ll be waiting for you, sannan inason sanin Ina macijin nan yake? Naji
kace mutunne”
Muryar chief owais tamkar bai son furta maganar yace”please uncle can i text you”
deen yace okey ba damuwa”, rejecting call din yayi, kafin wani ya furta magana
ƙarar shigowar saƙo Ya dakatar da su.

Karanta sakon Deen ya soma yi duk sun ƙura mashi ido suna jiran jin me zaice
masu, musamman pravin har wani zoƙa kai yake yi yana leƙen wayar Deen.

Ɗagowa yai da alamun mamaki akan fuskarshi yace”tabɗijancan, wallahi dagaske


macijin mutunne wai shaidanun aljanune a jikinshi, yanzu haka ya rikiɗa ya koma
mutun acan gidanshi yake zaune,........” aruɗe suke kallon shi.

“Wai ko kunsan Prime minister namu shine ya tura da jet din da zai ɗauko sheikh
imam daga sudan saboda kawai ya taimaka ma macijin ya dawo halittarsa”?
Jin wannan maganar ba ƙaramin firgita senate lateef yayi ba ranshi a6ace ya
furta”what? Bangane me kake nufi ba! Yaushe akayi hakan?batare da sanin mu ba!” a
kausashe ya furta maganar,, a sukwane his excellency abdul Razak Ya miƙe Yana
fadin”Anya ka karanta saƙon nan dai dai, bani wayar na duba, ya furta hakan tare da
kar6ar wayar Deen Yana duba sakon, bayan ya gama yace”ba shakka, kuwa owais dinne
ya rubuta da kanshi, magana ta tabbata prime minister namu shi ya tura da jet din
daya dauko sheikh imam daga sudan don kawai a duba yaron, muna nan zaune muna
jinyar ubanmu shi yana can wajen taimakon yaron da bamusan wanene shi ba, bamu haɗa
alaƙar komai da shiba, bansan meke damun prime minister ba, daga shi har owais din
shegen son taimakonsu shi zaija su jefa family dinmu cikin matsala ......” kafin
Deen Ya ƙare magana senate lateef daya gama fusata yana huci yace”Wallahi basu isa
ba, ni bani buƙatarma jin wani ƙarin bayani daga garesu, Yaron nan bazai zauna a
estate dinmu ba, tunkafin aje ko’ina harya fara mallake zuciyar ɗan uwanmu hakan na
nufin da wata manufa ya shigo family dinmu, zai iya yiyuwa wasu mugayen ne daga
maƙiyan jam’iyarmu sukayi amfani da shi don su tarwatsa family dinmu, ku duba kuga
fa duk gidajen dake a estate dinmu bai shiga kowanne ba, Ya tsallake nasu Ya faɗo
gidan babanmu saboda shine target dinsa.....” a harzuƙe senate lateef Ya ƙare
maganar.
Kanwa uban Ƴan Zigi Pravin Ya haɗe girar ƙasa da sama yace”Ni dama tun Jiya
hankalina bai kwanta da shigowar macijin nan ba, Ai daga jin yadda abun ya faru
zaka shaida makircine aka shiryama baba, so suke kawai su kashe shi, in ba haka ba
taya za’ai ace wai mutun ya koma maciji ai sai dai idan sihirine da shi, munafuki
kawai wallahi bazamu yarda ba, Yaron nan bazai zauna mana a estate dinmu ba, dole
ne owais Ya kore shi daga estate dinmu, sannan A yanke alaƙarshi da kowa na family
dinmu idan ba haka ba zaija mana masifar da bazamu Iya shawo kanta ba” Rai a6ace
pravin yayi maganar Yana kallon fuskokinsu.

Jinjina kai kowan nan su yayi alamar gamsuwa da bayanin pravin,


His excellency abdul razak Yace”Ai bazamu ta6a yin gangancin nan ba, mu jira
owais din ya shigo anjima, shima hateem din Zanyi waya da shi”
Pravin yace “yamakata atara kowa har shi kanshi yaya sharafuddeen din yazo yaji
abun da owais ke shirin janyo mana a family, wallahi jiya Saratu batayi bacci ba,
saboda fargabar macijin nan, sambatu ta dinga yi min tana kuka tana fadin gashi nan
zai sareta, duk tabi ta haukace ta rikice min aɗaki, daƙyar nashawo kanta da ayar
Allah”
Aruɗe Senate lateef yace”kunji ko? Tun yanzu ana kokarin ganin bayan ahlinmu”
Damuwa ƙarara akan fuskar Deen yace”Pravin kana nufin saratu batayi bacci ba jiya
saboda macijin”? Batare da ɗar ba yace”bata yi ba yaya, yadda taga rana haka taga
dare, ni na zauna ina yi mata fifita saboda zufar dake tsastsafo mata gafa ac a
daki amma haka ta dinga zubda gumi”
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar pravin
Murya na rawa his excellency abdul razak Yace”Yanzu awani hali take ciki? Tayi
bacci da safe?
Girgiza kai pravin yai fuskarshi da alamun jimami yace”batayi ba idonta biyu ko
abinci takasa ci,”
“Inason ganinta pravin” acewar abdul razak”
Pravin yace toh, bari naje nazo da ita ya juya jiki na 6ari ya fuce daga ɗakin.

Yana fitowa daga dakin su ka yi kici6us da Hajjaty, ta ɗauki wankan bubu gown ta
lace a jikinta, ta ca6a uban ado, ƙamshin turarenta ya buɗe ko’ina, mayafin rigar
asaman kafaɗa ta daurashi, doguwar suman kanta ta zubo har gadon bayanta,
Hannayenta biyu ruƙe da faffaɗan tray daga saman shi an ɗaura jerin kayan abinci.
Wani mugun kallo da pravin ya watsa mata saida gabanta Ya faɗi, duk tabi tasha
jinin jikinta, sarai tasan ya hanata yin kwalliya idan har bashi zatayi mawa ba
amma taƙi jin maganarshi.
Sai faman ƙyafƙyafta idanuwanta take yi, tayi mashi kyau sai dai yaji haushin
adon data ca6a.
“Kin manta gargaɗin da nayi maki? Baki jin maganata ko”? muryarta na rawa ta
furta”am sorry dear, na saba ne” guntun tsoki Yaja “yanzu ahaka zaki shiga dakin
obie, bayan kinsan bashi kaɗai bane aɗakin, Balagaggun ƴa’ƴansa duk suna aciki, duk
kamun kansu bazasu iya jure shaƙar ƙamshin turaren jikinki ba batare da kin jefa su
yanayi ba, ko kallon ki su ka yi sai sun ayyana wani abun aransu....” shiru tayi
mashi ba tare da tace komai ba, numfasawa yayi kafin ya ɗaura da cewa”bazan bari ki
shiga ɗakin ahaka ba, sai dai ki haƙura da kai masu abincin ki koma ɗaki ni sai in
kai masu”

muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”dan Allah dear ka barni in kai masu, Jiya
fa bansamu damar gaishe dasu ba”da shagwa6a tayi mashi maganar, nan take kasala
tafara kama shi, matsawa yayi dab da ita, ya ruƙo mayafinta data ɗaura kan
kafaɗarta, ya janyoshi zuwa saman kanta ya lullu6e mata sumar kanta da kirjinta
saboda yana jin kishin agane mashi majiyar dadin shi, ƙoƙarin manna mata kiss yayi
saman red lips dinta, kamar daga sama yaji ance”Daddy!” A firgice pravin ya ɗago
yana faman zazzare idanuwanshi Jin muryar zayn, su biyune hannayensu ruƙe cikin na
juna shida Zaid, fuskokinsu da alamun ruɗani, kafin ƙarasowarsu pravin yayi saurin
ɗaukar juice dake acikin jerin drinks din tray din hannun hajjaty ya buɗe murfin ya
watsa mata ruwan lemun gefen galenta, baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, mugun
tsoron Zayn take yi, tasan muddin ya gane abun da pravin ke ƙoƙarin yi mata sai ta
yaba ma aya zaƙinta, ajiya juice din pravin yayi, ya dai daita natsuwarshi, ya
nufesu fuskarshi dauke da murmushi ya ware masu hannayensu da niyar yayi hugginsu
dinsu,
Sai dai sunƙi bashi haɗin kai, wani irin matsiyacin kallon zayn yake watsama
hajjaty data juya masu baya.

Adabarbace pravin yace”kun ganmu atsaye ko? na fito daga ɗakin baba ne na
bankaɗeta batare dana ankara ba” kallon tuhuma Zayn yayi mashi kafin yace”daddy
mayafinta fa naga ka ruƙe a hannunka akan wani dalili”
“Baka ji mena ce ba, bugeta nayi har tray din hannunta ya girgiza lemu ya 6arar
mata jikin gyalenta shine fa na ruko gyalen ina ƙoƙarin goge mata” yayi maganar
tare da juyawa ya ruƙo bakin gyalen hajjaty yana nuna masu,
Ajiyar zuciya zayn ya sauke, zaid yace”daddy barka da safiya, ya gajiyar jiya” ya
faɗa tare da yin huggin dinsa, pravin yadan bubbuga bayanshi”Alhamdulillah My son,
Ina fata kun tashi lafiya, Yau ba zaku shiga office bane” cikin kulawa yayi
maganar, hankalinshi na kan zayn, ya lura yafi ɗaukar zafi halinsa ɗaya dana
jatumarsa wurin iya masifa.

Ɗago da kai zaid yayi daga kan shoulder din daddyn nasu yace”mun tashi lafiya
daddy, ba zamu je aiki yau ba sai zuwa next week, mun ɗauki hutu saboda zuwan Ƴan
uwanmu” jinjina kai pravin yayi”hakan yayi, kunyi tunani,” ya faɗa still idonshi
akan fuskar zayn daurewa yayi tare da ce mashi”Son ba magana? Ka tsareni da ido
kana kallona ko akwai wani abune”
Ta6e baki zayn yayi, kafin yace”bakomai, daddy ni me zance? Tun da ga zaid nan
yana yi maka magana dani dashi duk abu ɗayane”
Hajjaty tuni ta shige ɗakin Obie, batare da sun ankara ba.
Dafa kafaɗar shi pravin yayi”kaima ina buƙatar yin magana dakai, bai kamata kana
faɗamin haka ba, Ni mahaifinka ne yakamata kana tuna wannan” ya faɗa tare da
janyoshi yayi huggin dinsa, zayn fa ji yake kamar ya haɗa jikinsa da allon bango,
shifa sam mahaifinsu baya burgeshi baisan dalilin dayasa yake jin haka ba, kamar
bashi ya haife shi ba” bayan sun raba jikinsu zayn yai ƙoƙarin furta”am sorry
daddy, idan na 6ata maka rai,” murmushin gefen fuska pravin ya sakar mashi”kada ka
damu, inayi maka uziri saboda har yanzu kallon ƙaramin yaro nake yi maka, akwai
sauran kuruciya atattare dakai,” dan zaro ido zayn yayi”dady nine ƙarami”? Pravin
yace ƙwarai kuwa, ko ka manta shekarunkane? Idan ka manta bari na tuna maka you’re
just 2O something years, wata’ƙil don kana ruƙe da muƙami a company shiyasa kake
jin kanka wani babba”
Dafe kai zayn yayi da hannunshi, arayuwarshi ya tsani ana fada mashi shekarunshi,
haushi yake ji, zaid dai sai faman murmushi yake saki, yana jin dadin tsokanar da
daddynsu yake yima zayn.
“Jiya a ina kuka kwana ne”?
“Muna agidan daddy deen, munyi fira tare dasu justice, shine yace mu tsaya ayi
firar yaushe rabo” zaid ne yayi mashi bayani
Pravin yace”naji dadin jin haka amma ya akai Justice ya tsaya yin fira da ƙannansa
maimakon ya tuntu6i Zaki shi da yake sa’ansa” da biyu yayi maganar yana kallon
zayn, haɗe girar sama da ƙasa yayi”daddy, zolayar ta isa haka, nima zan ƙara
shekarunne nan bada jimawa ba” dariya zaid da pravin sukayi, bayan sun tsagaita da
yin dariyar pravin yace”bakusan abun da ya faru jiya da dare a part din baba”

A ruɗe suka furt”meya faru daddy”? Nan fa ya labarta masu kaf abunda ya faru tun
daga shigowar macijin, da firgicin obinna, Hankalinsu yayi matuƙar tashi.

“Daddy kana nufin mommy batayi bacci ba saboda macijin? Sannan baba shima bai
runtsa ba? Kuma naji kace chief owais ne Ya kau da macijin yaushe yazo ƙasar? Taya
akai macijin ya samu damar shigowa estate dinmu dake acike da tsaron sojoji da ƴan
sanda”? Zayn ne ya kora jawabin.
Pravin ya ta6e baki haɗi da cewa”macijin fa mutunne wai ya rikide, acewar shi
owais....”tunkan ya ƙare maganar, zayn da zaid suka kalli juna da alamun al’ajabi.
“Tayaya haka zai yiwu? Kamar dai ashirin film, ko atarihi ni ban ta6a jin mutun
ya rikiɗa ya koma dabba ba” acewar zaid.

Pravin yace”ai shine muma abunda ya ɗaure mana kai, ni dai nafi tunanin yaron
aljanine ko kuma wasu miyagunne da suke son cutar da kakanku suka yi amfani da
sihiri a jikin yaron donsu kashe shi”
Hankalinsu zayn ba ƙaramin tashi yayi ba, jikinsu har tsuma yake yi,
“Ku shiga daga ciki, ku duba jikin baban naku, Sauran uncles dinku suna a cikin
dakin, idan kun shiga ku tayasu jimamin abunda ya samu babanku, sannan please kada
ku goyi bayan yaron yaci gaba da zama a estate din nan, tunda shi owais din bai san
ciwon kanshi ba, idan ba haka ba taya zai ɗauko mugun abu ya ajiye agidan shi da
sunan taimako”? Ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar.

Zayn daya gama harzuƙa yace”wallahi bazai yiwu ba daddy, wannan ai ba maganar da
hankali zai ɗauka bace, in banda an rainawa mutane wayau taya za’ace wai mutun ya
zama maciji? Kuma ya rasa inda zai farmaka sai gidan baban mu, bayan ga sauran gine
ginen dane akusa dana shi owais din duk ya tsallakesu Ya nufo nan so ake kawai
akashe mana shi, dama ya lafiyar giwa, ga mahaifiyarmu itama da firgici ta kwana
bazan lamuntaba dole mu dauki mataki....” Yana huci ya ƙare maganar.

Cikin sanyin murya zaid yace”Allah ne kadai yasan dai dai, kada mu yanke hukunci
cikin fushi, bayan bamu da masaniya akan wanene yaron? Menene silar canza halittar
shi, da son ranshi ko kuwa ƙaddarace ta afka mashi, duk waɗannan amsoshin zamu same
su abakin Yayanmu owais tun da shi yasan komai dangane da yaron....”tunkan ya ƙare
maganar, Pravin yai hanzarin katse shi da cewa”babu wata hujja da zamu jira zaid,
ka duba kaga fa yadda ya siye zuciyar kawunku Hateem, meye alakarshi da yaron da
har zai tura da jet din da zai dauko sheikh imam daga sudan, duk irin manyan
malaman da muke dasu A nigeria, basuyi mashi ba sai da ya kashe makuɗan kudi don a
dauko mashi sheikh, don baku agidan macijin ya kawo farmaki da baka furta maganar
da kayi ba ayanzu, badan Allah yasa Owais Ya kau da macijin ba da tuni Ya sari
kakanku saboda shi kadai yake kokarin kaima hari” jin wannan maganar yasa zaid shan
jinin jikinshi
“Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un, wannan wace irin masiface daddy? In sha
Allah koma su wanene miyagun da ke son ganin bayanshi bazasu ta6a yin nasaraba,
sannan Nima na goyi bayan a kori yaron daga estate dinmu” gyaɗa kai pravin
yayi”yanzu naji magana my son”ya faɗa tare da dafa kafadar zaid din”ku shiga dakin
baban, Ni yanzu zan je nataho da mahaifiyar taku”Amsa mashi sukayi da toh, kafin
suka nifi ɗakin baba obie suka shiga da sallama abakunansu.

*HAJIYA SARATU❤*

Fitowa tayi daga bathroom, jikinta sanye cikin bathrobe fara ƙal, wanka ta samu
tayi don taji daɗin jikinta, don tun da safe data farka bata motsa daga kan gadoba
saboda fargabar abun da ya faru jiya da kuma damuwar da pravin Ya haddasa mata.
Agaban mirror ta tsaya fuskarta babu walwala, idanuwanta sun ƙanƙance saboda
rashin baccin da batayi ba a jiya, hatta kanta ciwo yake yi mata.
Expensive body lotions dinta ta soma shafama skin dinta, bayan ta kammala ta
nufi closet din kayanta, jim kaɗan ta dawo harta cire rigar wankan ta maida doguwar
riga bubu ta material, turare ta dauka ta feshe jikinta da shi.
Kafin ta kammala wayar ta dake ajiye kan pillow ta soma ringing, yamutsa fuska
tayi kamar bazata ɗaga kiran ba, ta nufi wayar ta duba sunan me kiranta, ajiyar
zuciya ta sauke kafin tayi picking call din
Ko sallama batayi ba ta furta”daughter, sai yaushe zaki shigo gida”?
On the other hand muryar faryat ta ratsa kunnanta

“Mommy, tun jiya nayi niyar shigowa in kwana anan part dinku, Zulaihat ce ta
ruƙe ni wai dole saina kwana a gidansu, mom madina ma tace in tsaya in kwanar masu
shiyasa kika ji ni shiru kuma ma bani kaɗai bace, hada su Yusra duk muna agidan”
Ta6e baki hajiya saratu tayi”okey, duk lokacin da kika ga damar shigowa ina
jiranki,” faryat ta amsa mata da toh, kafin sukayi sallama, Landline din kitchen ta
danna ma kira, Bugu uku Abla tayi picking call din
“Jira kuke yi sainace akawo min breakfast dina”? A faɗace tayi masu maganar
Cikin girmamawa abla tace”Ina bada haƙuri aunty, Yanzu nan zan shirya maki” guntun
tsoki taja tare da katse kiran ta wurga wayar kan mattress.

Bakomai take tariyowa ba face Rashin mutuncin da pravin yayi mata, Ya ƙona mata
rai adaren jiyan nan, wai har ita zata kirashi yaƙi zuwa sannan yayi rejecting call
dinta? bata motsa daga gaban mirror din ba, ƙarar knocking din ƙofa Ya katse mata
zancen zucin nata
Sai da ta mula tasha iska tukunna ta furta”Come in” muryar abla da ƙarfi ta
furta”Aunty ƙofar a kulle take” tunawa tayi da ta datse dakin jiya ta ciki, juyawa
tayi taje ta buɗe ƙofar, shigowa abla tayi hannayenta biyu ruƙe da wooden tray daga
saman shi kayan breakfast ne.

Wuce wa ciki abla tayi, ta daura tray din kan table, Kafin ta juya tana fuskantar
hajiya saratu data ruƙe qugu da hannu ɗaya, har saida taji gabanta ya faɗi ganin
6acin ran dake kwance akan fuskarta, cike da jin shakkarta ta furta”ko akwai wani
abu da kike buƙata”? Atsiwace hajiya saratu tace”ke nake buƙatar ki fuce min daga
ɗaki, kin wani tsareni da ido kina kallona kamar yau kika fara gani na” Jiki na
6ari Abla ta nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ta fuce hajiya saratu ta nufi gefen
gadon ta zauna, ta soma cin breakfast dinta, farawa da bismillah kakkauran tea ta
ɗauka ta kur6eshi dukanshi, kafin ta rarumi roasted chicken takai baki tana
cizgarta atsiyace, daɗina da hajiya saratu damuwa bata hanata cin abincin, adai dai
lokacin da ta ɗauki burger da hannu biyu ta gutsireta da baki, Muryar pravin ta
dakatar da ita daka taunar burger din da takeyi, lokaci guda yanayin fuskarta ya
canza ta haɗe rai kamar baƙin haɗari.

shigowa ɗakin yayi fuskarshi ɗauke da murmushi, yasan tsiyar daya tsula mata
shiyasa yake jin shakkar tunkararta
Daga nesa da ita ya tsaya haɗi da goya hannayenshi on his chest cikin muryar
lallashi ya furta”My wife, ina neman afwarki, dan Allah ki yafe min nasan ban
kyauta maki ba, duk da ba laifina bane, laifin ki ne saboda kece kikaja nayi maki
hakan, kin nuna bani da mahimmanci awurinki...” kau da idonta tayi daga kallon
fuskarshi, taci gaba da cin burger dinta ta share shi kamar batasan da zaman shi
ba.

“Dan Allah kiyi min magana sanyin idaniyata, kamar yadda na 6ata maki rai nima
haka raina ya 6aci, saboda tunanin awani hali kika kwana jiya ko runtsawa banyi ba,
nayi kewar rashinki atare dani, da pillow na kwana rungume a kirjina ina jin tamkar
kece na rungume”

fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yayi mata maganar, duk don ya samu ta yafe
mashi, burinshi ta aminta dashi su sasanta tsakanin su, duk don ya tunzurata akan
maganar macijin daya tsoratar da ita jiya, yasan muddin saratu ta ƙyamaci zaman
yaron a estate dinsu dole kowa ya amince saboda ƙaunar da yayyanta su ke yi mata.

“Bugun zuciyata, please ki kula ni mana, bana son sharenin da kike yi, wallahi
ashirye nake dana kar6i duk wani horo da zaki bani ni kawai so nake mu sasanta
tsakaninmu bana so kina fushi dashi” ƙara ɗaure mashi fuska tayi batare data juya
ta dube shi ba.
Zuƙunna pravin yayi, tare da kama kunnansa Ya soma yin tsallan kwaɗi Yana nufar
gaban table dinta Yana fadin”Am sorry my wife, nagane kuskurena bazan ƙara ba”
Tunkafin Ya ƙaraso gabanta, ta tsiyaya ruwan lemu acikin cup mai sanyi, ta ruƙe a
hannunta, Yana zuwa dab da table din ta daddage ta watsa mashi ruwan lemun saman
fuskarshi, da sauri ya runtse idanuwanshi jin raɗaɗin da ya shigar mashi, burger ta
ɗauka ta yunƙura ta kifa mashi ita a fuskarshi, tunda tayi mashi hakan sai taji
sauƙi acikin ranta, komawa tayi ta zauna tana dubanshi tace”Ina fata ka tashi
lafiya” shiru pravin bai furta komai ba, ƙoƙarin buɗe idanuwanshi yake yi sai dai
ya kasa, shu’umin murmushi hajiya saratu tasakar mashi tare da cewa”malam, ka tashi
ka shiga toilet ka wanke fuskarka,” babu musu pravin ya miƙe kamar makaho Yana
laluban hanya daƙyar ya gano ƙofar toilet......”

*✊💋ALHAMDULILLAH, END OF MIDDLE STEP, FATA NA SHINE ALLAH YA BANI IKON KAMMALA
TAKUN ƘARSHE LAFIYA KAMAR YADDA NA KAMMALA TAKUN FARKO DA TAKUN TSAKITA💋✊*

(Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i layukan mu (08103884440 0r 08169856268)

You might also like